Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dariya kuma ciki safwan y kama yace saboda kasan xanyi dariya shiyasa kaki bani lbrn da farko ai tsaki Aslam yayi y bude fridge y dauko faro y balle murfin y kafa a baki ko takan cup baibi ba saboda yadda xuciyarsa take tafarfasa ji yakeyi tamkar yanxu islam ta xuba masa karkashi.

*Aslm plz kuyi hakuri da rashin posting din _goyon kaka_ kwana 2 hakan y farune sanadiyyar xaxxabi danayi ina*
*bukatar* *addu'arku* *yan'uwa*

Taku har kullum *sisin mama*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs hamisu taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:30 PM] β€ͺ+234 803 841 7219‬: (6/11/2016 3:00pm) *na* *umma* *yahya* *musa*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*47*
Kamar yadda canal yace cikin dare around 9 o'clock Aslam yaji alert dadi y isheshi,sai a lokacin yayiwa safwan magana yace friend kaga nima kudin y shigomin cikin jin dadi safwan y miki,saboda kawai daurewa yakeyi bayason ko kadan Aslam yayi masa fushi danshi akwai san raha,safwan yace to kaxo muje shopping ko akwai abinda kakeso,Aslam yace a'ah ba abinda nakeso nasiyo komai safwan yace shikenan daganan sukaci gaba da hirar yadda tafiyar tasu xata kasance.

Kamar yadda akace yaune ranar tafiyar su Aslam kowanne soja sanye yake da unifoam fuskarnan a daure tamkar a filin yakin suke(nidai da nake a gefe tuni cikina y bada kuuu my Afma kuwa data rakani dauko rahoto tuni ta fara xawo a wando saboda ganin wani soja y saitata da bindiga πŸ˜‚πŸ˜‚) sai da suka dadayin training sannan aka bawa kowanne soja wata jaka tamkar skul bag amma tafi skul bag girma in da xasu xuxxuba kayan da xasu bukata kowanne da bindiga a gurinshi a hankali kowa yaje yahau motoci xasu wuce airport suhau flight xuwa somalia.

Su islam anata shirye2 xasu shiga j.s 1 yau iyayi ake tayi an fara xama yan mata dayake a primary skul din da suka gama acikinta xasuyi secondary unifoam ne kawai na secondary section white shirt ce mai dogon hannu da skirt maroon sai hijab fari mai hula sunyi kyau sannan suka futo isya y daukesu a mota sai makaranta.

Jere suke a assembly akayiwa dalibai barka da dawowa makaranta dftn sun daura damarar karatu akayi bayanai kowa y wuce class j.s 1A nanne ajinsu islam,again uncle hasheem shine foam master dinsu dadine y ishesu saboda yadda ya iya tallerating students.

Su Aslam suna sauka a somalia,ana saukesu a airport akaxo da manyan motoci aka debesu sai head quater aka babbasu masauki sukayi wanka musulmi sukayi sallah,sannan sukaci abinci,anan shugaban yasa aka kirawo su yayi musu brk da xuwa sannan y fara musu bayanin irin gurin da xasuje da haxarin da yake gurin,da irin ta'asar da yan kunar bakin waken sukeyi,yayi musu fatan samun nasara aka basu taswira ta gurin aka dada hadasu da wasu sojojin na garin duk da akwai wadansu acan jejin,su Aslam tunda suka futa kallan garin suka fara saboda yadda duk yan tada xaune tsaye suka bata garin,wasu gurin an rurrushe gininnika an kokkona,a haka har suka karasa dajin da sauran sojoji yan'uwansu suke suma duk an kakkashe wadansu ga gawarwakinan birjik na sojoji dana yan kunar bakin waken,suka ajiye jakunkunansu suka fara buga runfuna,suka shishshiga ciki musulmi sukayi alwala sukayi sallah.

Misalin 4:00pm sukaji harbe2 da tashin bomabomai nan suka fara shiri suka futa,kurar yan tada kayar bayan suka gano har suka karaso daf dasu nanfa aka fara dauki ba dadi akayita misayar alburushai su sunaso su shigo cikin gari su sojoji kuma sun hana,haka akayita bala'i su Aslam sunga tashin hankalin da basu taba gani ba dan irin wannan yakin sai a film suke gani haka suka kwana ana abu daya sai daf da asuba suka tabbatar da yan kunar bakin wakennan sun koma,dan cikin dare sai sunyi tunanin sun tafi saisu dawo,in lokacin sallah yayi kuwa sai dai musulmi 10 da keister 5 masu gadinsu da haka sukeyin sallah.

Taku har kullum *sisin mama*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs hamisu taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:30 PM] β€ͺ+234 803 841 7219‬: (6/112016 4:30pm) *na umma yahya musa*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON KAKA*
*48*
Sai lokacin su Aslam sukayi sallar asuba sannan suka shishshiga rumfunansu,wadanda sukaji ciwuka akayi musu treatment dinshi Allah y taimaki Aslam da safwan dai basuda rauni ko daya sai gajiya abinci sukaci sai pracitamol suka kwanta,sai axahar sannan mafi yawansu suka tashi wasu rumfunane dai sukayi bathroom dashi nan wasu suka shiga suka watsa ruwa dan sai suyi sati basuyi wanka ba.

Su islam ana tashi aka kamo hanya anata wani yauki (nikuwa nace kaga berayen j.s masu gigi πŸ˜‚),islam ana shiga aka fara fatali da kayan makarantar sai da akayiwa komai daidai pant dinta kawai ta bari sai best haidar ne a lokacin a dakin kaka shiya fatatakata daki ta dauko xanin kaka danshima ba sauki haka tafuto tanata xumbura baki.

Bangaren su Aslam kuwa abin ba sauki dan yan ta'addan yau sunfi na jiya haka akayita artabu yauma basu samu hutawa ba sai da akayi asuba.

Su Aslam har sunyi 3 month acan kwata2 agida ko an kirasu ba'a samunsu saboda jejin da suke babu sabis sannan uwa uba tashin hankalin da suke ciki baxai iya barinsu su futa suyi wayaba,saboda yanxu ko bacci ma basa samun damaryi saboda yadda yan ta'addan sukaga anayi musu ta'adin mutane sosai to koda yaushe cikin kawo farmaki suke ko sallah sai dai su hada axahar da la'asar magruba da isha'i asuba kuwa sai gari yayi rana,dukkansu kuwa sunyi wani irin mugun rama uwa uba wani mugun baki da sukayi dan rabonsu da watsa ruwan ma da sukeyi harsun manta.

Aunty amarya ce take xaune kuwa takeyi wiwi harda majina,tana haba Abbn amir y xakace baxan tashi hankalina ba kafa gani yau my son watanshi 3 da tafiya amma bamu tabayin wayaba koda yaushe nakira wayarsa a kashe take haka ta safwan din to in banyi kuka ba y kakeso nayi in my son y rasune y kamata ku fada mana ta dada rushewa da kuka,cikin sanyin murya danshima dakewa kawai yakeyi yace haba fateema waya fada miki Aslam y rasu yanayin inda suke aikine haka,sannan kuma gurin da suke ba service cigaba tayi da kukanta,haka y tashi y tafi part din yayansa anan y xayyane musu abinda ke faruwa Fateema duk ta tashi hankalinta,mommy ce tayi murmushi duk da itama dakewa kawai takeyi tace in banda abin auntyn yara ai addu'a itace y kamata tayi musu bata xauna tana kuka ba,kallanta Abba yayi yace nikam nakasa rarrashinta daddy y kalli mommy yace khadeeja jeki kirawo ta mommy tace toh ta futa.

Kukan ta tarar aunty amarya tanayi tana ta kiran waya murmushi mommy tayi ta karasa tace daddy yana kiranki,haka aunty amarya tanajan hanci suka fita.

Suna xuwa suka samu guri suka xaxxauna anan daddy y kalli aunty amarya yace haba fateema y xaki tashi hankalinki akan abinda hasashe kawai kikeyi yanxu acema Aslam din y mutu haka xaki xauna kina kuka baxakiyi masa addu'a ba,kuma kinsan rikicin Hajiya (kaka)kullum muka shiga gurinta saitayi mana xancen Aslam bai taba kiranta ba kuma in itace ta kirawo shi sai yara suce ance a kashe take,kinsan cemata mukeyi mu munayin waya dashi kila ita lokacin da take kiransa y kashe wayarne saboda aikin da yakeyi akwai wahala,to yanxu intaji irin maganar da kikeyi y xamuyi da ita,shiru aunty amarya tayi tana goge kwalla,daddy yace dan Allah ki daina kuma nakira abokina yace yaje head quarter sunce suna lfy kawai jejin da sukene ba service kici gaba dayi musu addu'a kinji tace toh.

Taku har kullum *sisin mama*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs hamisu taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:31 PM] β€ͺ+234 803 841 7219‬: (7/11/2016 4:00pm) *na umma yahya musa*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON KAKA*
*49*
Kamar yadda daddy yayiwa aunty amarya nasiha,haka ta daure tana danne damuwarta duk kuwa data damu,sannan haka ta tsaya tsayin daka ta dage da nafilolin dare akan Allah y bawa su Aslam nasara kuma y karesu daga sharrin duk wani abu daxai cutar dasu.

*AFTER 1 MONTH*
Yau su Aslam tashin hankalin da suke ciki yafi na kullum,saboda yau harda shugaban yan kunar bakin waken aka futo musayar wuta kawai akeyi a tsakaninsu da tashin bomb ko ina ka kalla a ko kone gawarwaki kuwa tamkar ba yan adam ne a kwance ba bala'in yayi bala'i tashin hankalin yakai,su har mamaki sukeyi inda wadannan mugaye suke samun kayan fada,safwan ne da Aslam a bayan wata bishiya da aka sare a lafe,cikin nuna gajiyawa safwan yace my friend wlh nagaji yau 2 days ana yaki in banda ruwa babu abinda cikinmu y samu ruwan ma bamusha mu koshi ba wlh nagaji anya xamu iya kama wadannan mutanen kuwa Aslam ne y hango wani dan kunar bakin wake y harbo bindiga a daidai saitin kirjin safwan da sauri y hankada safwan yayi kasa shikuma bullet din y shigar masa kafada ohch yace a lokacin y saita kan dan kunar bakin waken y harbeshi a take y fadi y mutu.

Daidai lokacin islam ta futo daga kitchen din aunty amarya ta dauko wa aunty amarya ruwa a try y fadi glass cup din y tarwatse dafe kirjinta tayi tace wayyo,aunty amarya tace ke kuma lfyrki islam tace wlh aunty amarya kawai ji nayi gabana y fadi,aunty marya tace toh ba addu'a y kamata kiyi ba,islam tace toh kitchen ta koma ta dauko broom da packer ta tattare glass din ta xuba a dausbing ta dawo jikinta duk yayi sanyi,tana shirin futa aunty amarya ta kirata tace xonan islam,komawa tayi ta xauna a gefen aunty amarya ta sunkuyar da kanta,aunty amarya tayi murmushi a ranta tace Allah ngd maka yarinyata tafata hankali (nikuwa nace anya kuwa)tace islam meyake damunki naga yanayinki kwana 2 duk y canja kin xama so silent,kawai sai islam tahau kuka mamaki aunty amarya ta fara tace daga tambaya sai kuwa,dakyar ta lallasheta tace ki fadamin damuwarki koda addu'a natayaki kinji cikin xumburo baki islam tace toba yaya bane,da mamaki aunty amarya tace wanne yaya dan tasan kaf gdan abokin tsamarta 1 Aslam to kuma yanxu bayanan,islam ta kara xumburo karamin bakinta tace yaya Aslam,aunty amarya tadan xaro idonta tace a'ina kika ganshi,islam tace a haccina kullum saina ganshi yana can a wani daji yana tashan wahala saiyace naxo nikuma naji tsoro saina gudu saiya dinga kwalamin kira yana cemin nadinga yi masa addu'a saina saina farka in duba naga bayanan,to yanxuma nafito a kitchen naji kamar ihunsa,hawayene y xubowa aunty amarya ta goge,tace toh kinayi masa addu'ar,girgixa kai islam tayi,aunty amarya tace toh daga yau duk lokacin da kikayi sallah ki dingayi masa addu'a kina Allah y bawa yayana nasara y kuma dawo dasu lfy kinji,murmushi islam tayi har dimple dinta y loba tace to,aunty amarya itama murmushi tayi tace that gud my girl give me 5 ta mika mata hannu suka tafa islam ta tashi tana dariya tace bari natafi gurin kaka ta tashi tatafi da gudu murmushi aunty amarya tayi itama ta mike ta shiga kitchen ta dauko ruwan dan islam bata daukoba(kalubale ga iyaye y kamata aduk lokacin da kuka fahimci yaranmu suna cikin wani damuwa y kamata ku jawosu ajikinmu muji damuwarsu tanan xamu samu su fadamana abinda ke damunsu,amma ba muga yaranmu a damuwa ba kuma mu kasa magance musu karmu manta amanace Allah y bamu kuma saiya tambayemu).

Cikin kidima safwan y dago yace y sameka ganin jini na bulbulowa a kafadar Aslam kuma yanata hada uban gumi shiya sakashi saurin sauko da jakar bayansa y xuge y dauko wata karamar wuka mai dan tsini yayi saurin farke rigar y luma wukar a jikin Aslam,Aslam sai runtse idonsa yakeyi saboda yadda y kaje wani irin xafi yana ratsashi tundaga kwakwalwarshi har xuwa dan yatsanshi,wata kara y saki lokacin da safwan y xaro bullet din sai kuma y lumshe idonsa y jingina da bishiyar yana maida numfashi,daure masa hannun safwan yayi sannan sukaci gaba da yakin danyau abin yayi tsanani (nikuma nace Allah y rabamu da yaki 😰).

Taku har kullum *sisin mama*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs hamisu taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:31 PM] β€ͺ+234 803 841 7219‬: (7/11/2016 4:30pm) *na umma yahya musa*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON KAKA*
*50*
Cikin ikon Allah haka akayi ta artabu inda Allah y taimaki su Aslam yau dai komai yaxo karshe dama rana 99 ce ta barawo rana 1 tamai kaya ayau Allah y nunawa su Aslam karshen wannan tashin hankalin dama masu iya magana suna cewa karshen tuka tuki tuk kuma duk nisan jifa kasa xai dawo yau sun kama bbn yan kunar bakin waken da sauran yaransa 20 dan sauran duk sun kashesu har cikin jejin su Aslam suka shiga aikuwa makamai kala2 wadansu ma su Aslam basu taba ganin irinsu ba,a healcopter aka sassaka ragowar sojajin da sukaji ciwo masu tafiya kuma suka shiga motoci tun kafin na mota su karasa aka turo wadansu jiragen suka tattara gawarwakin akaje aka binnesu dan na nigeria an kira an fada musu akwai nasu mutane 20 da suka mutu sun yadda a binnesu acan.

Gwamnatin somalia ba karamin dadi tajiba yadda aka samu nasarar kama wadannan axxalumai tuni aka kaisu magarkama😜 aka garkamesu.

Treatment ake basu sosai dan ko mutum ba'a harbeshi ba to baya rasa wani ciwon kamada masu karasa da sauran ciwuwwuka.

*2 week latter*
Yauce ranar dasu Aslam xasu dawo gda nigeria saboda duk sunji sauki sai dai dan ragowar ciwukan da ba'a rasa ba,inda yayi dai2 da 5 month 2 weeks kenan da tahowarsu,bakaramun kuka sukayi ba ganin babu wadansu acikinsu sun mutu,gwamnatin somalia ta jinjinawa sojojin nigeria tare da godiya sannan tayi alkawarin lokacin karin girmasu xata xiyarci nigeria,bakaramin biliyoyin kudi ta tura nigeria ba da xa'a biya wadannan xaratan sojojin domin sunyi rawar gani,haka aka debesu har airport tare da tawagar shugaban kasar can domin rakiya saida saida sukaga dagawarsu niga sannan suka juya (nikuwa nace wash yau sai kwanan niga πŸ™„)

Bakaramin tarba akayi musu ba a nigeria lokacin da suka sauka haka aka dada dibansu sai headquarter canal yusuf safana yaji dadi,sauran major da general sai jinjina masa sukeyi saboda yadda yaransa sukayi kokari sosai a wannan tafiyar kuma ba karamin alheri da girma suka samowa kasarsu ba,bayan bayanai da girmamawa da akayi musu akace an sallami kowa yaje gda y wuta har tsahon 2 months xuwa lokacin da xa'ayi promoting dinsu sannan kowa xaiji alert dadine y ishesu kowa aka saka drivern office y kaishi gda.

Aunty ce xaune a palo ta xurfafa cikin tunaninta dan bata da aiki sai tunanin tilon danta mutane ta gani tsaye a kanta kafafunsu ta fara gani takalman sojoji ta gani da wando da sauri ta dago kanta safwan ta gani amma yayi baki da sauri ta mike ta rungumeshi tana kissing din fuskarsa hawayene y wanke musu fuska duk su 2,Aslam dayake gefe shima idanunsa sun kada sunyi ja,dan yasan yan gdansu sunacan suma sunyi missing dinshi aunty ce ta saki safwan taje tayi hugging din Aslam shima tayi kissing dinshi a goshi,komawa tayi ta xauna suma suka xaxxauna tace my sons munyi missing dinku,muma munyi missing dinku sukace,tace wanne irin guri kukaje wanda bashida service haka,safwan yace wani kungurmin dajine wlh bari muje muyi wanka tukun mudawo kisha lbr,sallama akayi,suka amsa mai gadine y shigo y miko wata envelope Aslam y karba yace yauwa harya dawo,aunty tace menene haka Aslam yace ticket ne aunty nima yau xantafi gda,aunty tace haba my son memakon ka kwana safwan yace nima haka nace masa to yace a'ah wai yasan hankalin yan gda y tashi saboda rabonshi da waya dasu tun kafin mu tafi baxai iya dada kwana ba,aunty tace kuma yayi gaskiya bari nakira dadynka nayi masa albishir safwan cikin shagwaba yace a'ah aunty surprising dinshi xanyi y hade hannunsa yace plz karki buga tayi murmushi tace toh.

4:30pm suka futo Aslam yana sanye da t.shirt purple sai black trouser y ratayo jakarsa sai kanshi yakeyi yace aunty bye sai bayan 2 months kuma,tace toh Allah y kiyaye hanya ka gaishemin da mutan gdan,yace ameen xasuji.

A waje sukayi clashing da daddy driver y dawo dashi daga office,cikin mamaki yake mutsitstsika ido yace suwa nake gani kamar maxaje da sauri suka tafi sukayi hugging dinsa,a tsatstsaye daddy suka gaisa da Aslam yaje driver y daukeshi xai kaishi airport,safwan kuma suka koma da daddy.

Taku har kullum *sisin mama*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs hamisu taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:31 PM] β€ͺ+234 803 841 7219‬: (8/11/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON KAKA*
*51*
A jirgi Aslam sai murmushi yakeyi,saboda wani farin ciki dayaji maramisaltuwa wanda y kasa sanin dalilin farin ciki(nikuwa nace waya sani ko farin cikin nassarar da suka samu ne nace kai a'ah farin ciki yakeyi yau y dawo gdan cikin hukuncin ubangiji).

Islam ce ta sheko da gudu sakamakon chocolate din data kwatowa Amira,itama amiran ta biyota a guje Amira tace wai baxaki tsaya ki bani chocolate dina ba cikin shagwaba tayi maganar tamkar datayi kuka,lokacin islam ta lunkuma chocolate din a baki tace Allah gwnda ki hakura danma na cinye kuma nasan baxaki iya kamani ba,Amira ganin islam wahalar da ita kawai takeyi dan ba iya kamata datayi va yasa cikin kuka ta koma part din kaka,islam kuwa da gudunta batasan Amira ta komaba tayi hanyar gate,lokacin yayi daidai da shigowar Aslam islam ji tayi ta bugi mutum tagal2 ta koma xata fadi,da hanxari y rikota da hannu daya y daidaita tsayuwarta sororo ta tsaya tana kallan wanda y rikota tundaga kafarsa ta fara kallo har xuwa fuskarta kuwww cikinta y bata kara,sakamakon ganin fuskarsa a tamke tamau tamkar bai tabayin dariya ba a duniya,cikin tsawa yace ke wannan wanne irin rashin hankaline gudun ubanme kikeyi,cikin tsoro da rawar jiki islam tace Amira ce ta biyoni,kallon bayanta y fara baiga Amira ba,islam kuma wani bala'in kwarjini yayi mata tuni taji wani mugun tsoronsa y shigeta wanda bata tabajin irinsa ba,saboda yadda taga yaya Aslam din y dada girma,yace ina Amira din waige2 ta fara tana xaxxaro ido irinna marasa gaskiya,a ranta tace wlh dabadan ka rikemin hannu ba da tuni na dade dayin nisa a daki,yace saboda bakida hankali a haka xaki futa dubeki fa,kallan kanta take ready made ce a jikinta iya gwiwa rankwashinta yayi mata,wani xafine y ratsata tamkar ta saki futsari wata gigitacciyar kara ta saki lokacin y cika hannunta yace kama gabanki da sauri ta juya ta kwasa da gudu sai da tayi nisa ta juyo tace kuma Allah y isana ta murguda baki,kafin yayi wani yunkuri ta bace bat tamkar kiftawar ido,murmushi yayi yace Ashe haryanxu tsugune bata kareba karasawa yayi suka gaisa da baba mai gadi da isya sukayi masa y hanya yace alhmdllh y wuce.



Da gudu ta fada cinyar kaka tana maida numfashi,kaka tana lfyrki kuwa amma ta kasa magana sai waje da take nunawa da hannunta,kaka tacewa Amira ke ganomin wane y biyota y tsoratata haka tashi Amira tayi ta leka ta dawo tace nifa kaka banga kowa ba,kaka ce ta kalli islam da haryanxu ta kasa magana sai jikinta da yake rawa tace to dagani in baxakiyi magana ba,dakyar islam ta daidaita nutsuwarta tace yayane fa y rankwasheni kaka tace haidar ko narasa meyasa yakeson mushiga kafar wando daya dashine,na hanasa dukanki yaki ji,xumbura baki islam tayi tace bafa shiba yaya Aslam,shekeke kaka ta kalleta tace watako shirmen mafarkin da kikeyi harya fara xama gaske,yaron dayau watanshi 5 da sati 2 da tafiya shi xakice kingani,islam ce tace kiji kakannan to yaushe nakeyin mafarkin yayan,harda xan fada miki magana kice shirme nayi,kaka tayi dariya tace ai in kina mafarkinnasa surutai kikeyi saina tofeki da falaki da nasi tukunna,dariya Amira tayi tace koma waye dai y rankwasheki hakkina ne Allah y fara sakamin duka islam ta

Please Login or Register in order to submit comment