Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watsar da abincin tsawa y daka mata tundaga lokacin ta fara tsoronsa harya dawo bata yadda y dauketa inya dauketa kuwa tadinga ihu kenan har saiya sauketa.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:53 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (4/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*7*
Tun daga lokacin y daina daukarta in tayi laifi shine yake tsawata mata tsoronsa takeji sosai,har y tafi tana fara fitina in kaka tace ga aslam nan yanxu xata nutsu.
Aunty amarya ta kara haihuwar ihsan da tasleem ita kuwa mommy daga kan ameera haihuwar ta tsaya,su islam duk sunxo suna yanxu haka rabon islam da cikin kano tun haihuwar tasleem yanxu da take shekara 3 wannanne dalilin dayasa islam dawowa hannun kaka,yanxu islam tana makaranta a garin gwarxo tana aji 2 amma asha ruwan tsuntsaye takeyi yau taje gobe taki xuwa,sannan duk ranar da raje sai ta nemo magana bata kyale kowa ba daga malaman har daliban kaka kuwa daure mata gindin rashin mutunci takeyi duk laifin da islam tayi in akaxo aka fada mata sai ta bugi kirji tace bata aikata ba,makaranta ma tana xuwa allo dan an korosu itada kawarta hanne daga islamiyya ance basa fahimtar komai sai neman fada duk randa akayi hadda in basu iya ba aka dakesu indai yaro yayi musu dariya to dukan da xasu masa sai yafi wanda malami xai musu shine shugaban makarantar yace y gaji y mayar dasu gda,kaka da aka fada mata cewa tayi tafi nono fari dama me suke koyawa yara in banda xalunci kullum cikin dukan islam sukeyi tayi xamanta ta kaita makarantar allo wannan kenan.
*cigaban* *labari*
Islam tana futa bata xarce ko indaba sai gidansu hanne da guntun hawayenta hanne najin sallamarta ta futo da gudu tana waya dakeki islam bakinta ta cuna gaba tace ba wancan mugun yaya aslam din bane y rangwasheni hanne tace Allah y saka miki islam tace ai wlh dabadan yau xai tafi ba da saina rama dariya hanne tayi tace da munyi masa irinta uncle idris itama dariya islam tayi tace kuma shi da wlh a ruwan wanka xan xuba masa karara dariya sukayi gaba dayansu babar hanne tace Allah y shiryaku gidansu ilah da yusufa avokabansu suka je suka biya musu suka tafi kogi dayake yau ana kamun kifi kowa da fatsarshi a hannu.
Aslam kuwa tasha yaje y shiga mota ana kiran sallar magriba y isa gda direct part dinsu na samari y shiga dakine gado daya sai wardrop sai bathroom aciki wannan nasune shida ameer wanka yayi y futo y tafi masallaci sai da akayi sallar isha'i sannan y dawo direct cikin gda y shiga yaje y gaida maman sa take cemishi yau kwananka 3 fa harka dawo kai da kace sati xakayi a lokacin Abbansa da daddy (aliyu)suka shigo bayan y gaishesu yace wlh mommy dawowa nayi saboda kwata-kwata islam bataji gashi duk abinda takeso shi takeyi kaka bata tsawata mata anan y basu lbrn duk abinda y faru sannan,ran Abba y baci sosai yace dama inaso nasamu dama muje mu taho dasu gaba daya y kalli aslam yace karka damu insha Allah xasu dawo very soon aslam cikin farin ciki yace Allah y yarda,ya tashi yace xashi gurin aunty amarya su kuma suka xauna suna tattauna yadda xasu shawo hankalin kaka ta yadda ta biyosu.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (5/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*8*
Da farin cikin shi y shiga part din aunty amarya a xaune y taradda ita ita dasu taslem y karasa y xauna a gefenta dora kanshi yayi akan cinyar aunty amarya,yace aunty na nayi missing dinki ina wuni,tace lfy my son i miss u too yayi dariya,kallan su taslem yayi y hararesu yace baku iya gaisuwa ba cikin rawar murya sukace ina wuni yaya lfy kawai yace,yace dallah can ku tashi ku bamu guri kun tsareni da ido naxoyin magana da aunty na da gudu ihsan ta tashi taslem kuwa kafadarta ta make dariya yayi yace kai aunty wlh yarinyar nan rashin jinta daya da islam itama dariya tayi tacewa taslem taho autata wlh wannan tafi islam jin magana yace aini xan baki lbrn rashin jinta yanxu fa ita ta koroni daga gwarxo ga kaka ta daure mata gindin rashin mutunci komai tayi daidai ne,shiru aunty amarya tayi tace to y xamuyi sai dai mu dinga binta da addu'a.
Aslam yace au ashe fa albishir naxo yi miki ai nasamo solution very soon islam xata dawo,murmushi ne y subucewa aunty amarya tace Allah yasa my son yace ameen y dade suna hira sai wajen 10:00pm yayi mata sallama y tafi part dinsu.
Islam baxaki tashi ba 7:30am fa tayi ko so kikeyi ki makara,kaka ce take tashin islam daga baccin safe saboda ta tafi makaranta,juyi tayi ta cuno karamin bakinta gaba tace wlh ni kaka baccinnan bai isheni ba,kaka tace ashe bakyaso ki xama mai lbrai a gidan radio ko da sauri islam ta mike dan dalilin dayasa take xuwa makaranta saboda tanaso taxama yar jarida shine babban burinta,amma da tuni ta daina xuwa wanka ta cire kayanta ta shiga,baccinta taci gaba dayi a toilet kaka ganin islam ta bata 15 minute bata futo ba shine yasaka ta bita a xaune ta tarar da ita akan kujera tana bacci tsaki kaka tayi tace wlh islam kedai anyi yarinyar banxa ta karasa ta sheka mata ruwa firgigit islam ta farka ihu ta kwala tana kururuwa kaka tace yimin shiru wlh yau in angle idris yayi miki dukan latti ba inda xanje,dariya naga islam ta tuntsire a raina nace mai kuka yana dariya,tace ba angle idris ba uncle idris ake cewa tsaki kaka tayi tace xancen banxa ai nayi kokari ma,amma menene tsakanina da yaran bokoko a wuta a haka kaka ta gamawa islam wankan suna fada.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (5/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*9*
Sun fito daga toilet hanne dasu yusufa suka biyowa hanne mai ta shafa ta xauna sukaci abinci,ilah yace wlh wannan taliyar irinta gurin mai shayi dadinta y baci yusufa yace sosaima hanne kuwa lokacin da takai loma tace ai wlh saboda ita bana taba yadda nayi fada da islam,dariya islam tayi tace ba sunanta taliyar gurin mai shayi ba sunanta indomie ta karkatar da baki tace wannan mugun yayan nawa ne y kawomin ita dasu madara harsa biscuit da choculate wai na xuwa makaranta murmushi hanne tayi tace gaskiya y kyauta sai wajen 8:30am suka gama ci dan sunayi suna hira kaka harta gaji da magana islam ta shiga daki ta daukowa kowa chocolate da biscuit kaka kuma ta basu 20 naira sababbi sannan suka tafi.
A hanya hanne tace islam mu biya gonar malam tanimu islam tace a'ah ki bari mu dawo tukun tinda kinga munyi latti kar a dakemu nikuwa nace latti na yaushe basu suka karasa makaranta ba sai 9:00am dudu du tafiyar batafi ta 10 minute ba amma suka dinga canta sai data kaisu 30 minute islam tace yanxu muje mu haura ta katanga dan wlh baba mai gadi ko muna yawo da uwayen mu baxai barmu mu shiga ba yusufa yace haka xa'ayi daraf naga suna kama katanga sai ka rantse da Allah yan biraye ne sai da suka gama durawa Ashe wani fripect y gansu kuma dokar makarantar ce an hana shigowa ta Katanga.
Y kamasu sai office din head master akayiwa kowa bulala 5 masu xafi suka dinga kuka sannan aka sakasu neal down sai da sukayi na 30 minute sannan akace su tafi class aikuwa su islam sunsha takaici saboda basu samu sun siyi komai ba a break gashi an buga bell kowa y koma class.
Nan ma suna xuwa sabon mass teacher dinsu y shigo gashi ranar friday y bayar da assighment cikinsu ba wanda yayi nan y kuma futar dasu y sasu kamun kunne ranar dai su islam sunce da kafar hagu sukaxo makaranta nikuwa nace rashin jinsuπŸ˜‚.
Gonar malam tanimu suka wuce sai da suka tsinko mangwaro 1 yahau kai islam tace ainice boss dan haka nixan dauka nan fa dambe y sarkesu har malam tanimu yaxo y kamesu yace gurin mai gari xai kaisu suka dinga bashi hakuri yace wlh sai y kaisu mai gari y musu tsakani.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (6/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*10*
Mummy da aunty amarya suka futo suna Allah y kiyaye y tsare hanya Allah y doraku akan hajiya ta yadda ta biyoku sukace ameen suka shiga mota Aslam ne yake driving inda daddy da Abba suke a seat din baya,Aslam driving yakeyi cikin nitsuwa har suka karasa gwarxo parking yayi a kofar gidan kaka suka futa y rufe motar suka shiga ciki.
Shiga sukayi bayan sun gaggaisa da kaka ta kawo musu ruwa da lemo kallon aslam tayi tace baka tafi koyon aikin sojan ba ai naxata wannan satin ka tafi yace a'ah sai wani watan xan tafi,Aslam yace kaka ina aljanar jijarki ne hararararsa tayi tace ban sani ba murmushi daddy yayi yace aslam islam dince aljana yace ai wlh daddy tafi aljana yanxu muna xaune ma kila a kawo kararta,kaka tace to makaranta ta tafi aslam yace Allah yasa.
Sallama sukaji anayi aslam ne y tashi yaje y gano dan aikene daga fadar mai gari ana neman kaka aslam yace toh gatanan xuwa y koma y fadawa kaka aiken da a kayo gurinta mayafi ta saba Abba yace haba hajiya ki tsaya mu muje mana kaka tace a'ah dole na amsa kiran mai gari ai kudaixo muje dayake ba nisa a kafa sukaje.
Su islam suka gani sunata kuka suna sun daina baxasu kara ba iyayen su hanne ma sunxo cikin tashin hankali kaka take tambayar meyake faruwa,su Abba kuwa guri suka samu suka xaxzauna suka gaishe da mai gari,suka tambayi dalilin kiran mahaifiyarsu anan mai gari y fadawa su Abba irin ta'asar da islam da abokananta sukeyi masa a gari sannan da karar da malam tanimu y kawo anan yaja hankalin iyayen sauran yaran daya xama dole su tsawatar da yayansu in ba haka ba kuwa xai dauki kwakwkwaran mataki,sannan yace kowa y tafi da yaranshi sukayi godiya kowa y kama danshi y tafi gda.
Tun a hanya kaka take sababin masifa akan an tsanar mata jika,anan su daddy suka dinga bata hakuri Abba yace yanxu kawai hajiya ki yadda ki biyomu mu tafi kinga acan ba ruwan wani da wani,islam tace eh kaka mu tafi birni dama wlh nagaji da yadda ake sakamin ido,kaka tace toh shikenan muje mu tattara kayanmu farin ciki sosai ne y kama aslam saboda yanaji y kusa gyara islam.
Nikuwa nace anya kuwa mudaije xuwa yanxu lbrn y fara ku biyoni danci gaban lbrn😊.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (7/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*11*
Harhada kayansu sukayi a jaka,da gudu islam ta fice a gda gidansu hanne taje tararwa tayi innar hanne tana mata fada akan y kamata ta gyara halinta inba so takeyi ta rasa mijin aure a kauyen ba.
Sallama islam tayi tace hanne naxo nayi miki salama yau xamu koma birni gidansu babana ko nasaka ta na wala da yadda kowa y sakamin ido,innar hanne ce ta girgixa kai tace Allah y shiryaki islam to ina kudan yake balle romonsa da har xakice an saka miki ido,murguda baki islam tayi tace yanxu ke inna baki gani ba umh hanne xo muje gidansu ilah da yusufa nayi musu sallama,da sauri hanne ta tashi innarta tana kiranta kota kanta batabi ba suka fice.
A hanya hanne tace yanxu shikenan islam in kin tafi binni xaki manta damu ko,wata dariya islam tayi tace mai xaisa na mantaku kunefa abokanai na na hakika kuma ba ai Abba yace xamu naxuwa hutu washe baki hanne tayi tace Ashe nima wataran xani birni islam tace sosai a kofar gidan su ilah suka tarar da ilah da yusufa anan islam ta sanar dasu tafiyarsu birni suma basuji dadi ba suka dunguma suka tafi raka islam.
Acan bayan sun gama saka kaya a mota daddy yace to ina kuma islam din,kaka ce ta kama baki tace la'ilah ha illallah in ka bibiya ta tafi gidansu hanne yi musu sallama amma mu jirata.
Xaman jiran islam sukayi harna tsahon 10 minute amma shiru ba ita ba dallinta tsaki Aslam yayi yace amma yarinyar nan yar raunin wayoce in ba rainin hankali ba tasan jiranta mukeyi xata tafi yawo kaka ce ta hararesa tace to sai taki yiwa abokananta sallam...,bata karasa ba suka hango islam itada su hanne,Aslam yaja dogon tsaki yace saboda yarinya an batata wai har abokanai ne da ita maxa kaka ta hayayyako masa tace saika fadi waya batata kai wlh da badan islam tanason komawa birni ba kuma baxan iya bari ta tafi ita kadai ba wlh da ba inda xani,daddy ne yace hajiya dan Allah kiyi hakuri y kalli Aslam yace be carefull in ba haka ba kuma y girgixa kansa.
Islam ta karaso ta shiga mota daddy y bawa su hanne kowa 100 ganin da gaske islam tafiya xatayi suka hau ihu da kuka suna bin mota,islam itama ihu takeyi kaka ma harda goge kwallah😒.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (7/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*12*
Aslam ne yaji kukan islam yayi yawa kuma su Abba sunata rarrashinta taki yin shiru,tsawa y daka mata yace da Allah kiyiwa mutane shiru kin cikawa mutane kunne ke gaki mai kawaye ko,dago fuskarta tayi shabe-shabe da gawaye ta murguda masa baki tace to ina ruwanka in baxaka jiba ka toshe kunnanka da wanda ya tilasta maka dole kaji kukana xaro ido yayi yakai mata rankwa shi ta goce,daddy yace Aslam y kake wasa da rayuwarmu ne Aslam yace I'm sorry dad,sannan yace mamana rabu dashi kinji ta washe baki kamar ba ita take kuka ba tace toh.
Tunda suka tafi take surutu komai ta gani sai tayi magana na tambaya kuma ta tambayi Aslam ko kallanta bayayi sai tayi tsaki tace daddy ko Abba menene wannan saisu fada mata.
Aslam kuwa duk haushinta yakejin ganin yarinya karama tana shirin rainashi yadda kowa yake girmama shi a gdan amma yanxu xataxo da nata salon na daban murmushi yayi daya tuno da irin axabar da xaiyi mata har saitayi biyayya tsinto ihunta yayi ta kwalla kara tana yeah kiiiii yaja birki saura kadan y bugawa motar gabanshi dan ma Allah y nufa babu mota a bayansa da hatsarin da xasuyi ba kadan bane.
Kaka firgigit ta farka daga gyangyadin daya dauketa tana salati,su Abba ne suka kalli islam sukace ihun me kikeyi ko kinaso muyi hatsari mu mutu daddy yace kai Aslam kai kuma tunanin me kakeyi,kaka tace so yakeyi y kashemu kawai dama bai damu da rayukan muba.
Islam tace nifa tsoron wannan nakeyi gani nake in mun hau xamu fado,dariya Abba yayi yace islam rigima wannan fa gadace da ana fadowa ai da bakiga wasu motocin suna biba(nikuwa na kyalkyale da dariya nace kai aradu kauyanci baiyi ba yanxu hawa gadar takewa ihu hakaπŸ˜‚πŸ˜‚).
Aslam kuwa wani bakin cikine y turnike shi a ranshi yana watako ita duk iskancin nata ma tsoron mutuwa takeyi aikuwa xakici ubanki y figi motar,islam kuwa idanunta ta runtse sai da suka sauka akan gadar ta bude idonta.

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*daga* *sisin* *mama*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 8:54 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (8/10/2016 4:00pm)na umma yahya musa

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*13*
*GOYON* *KAKA*
Tafiya sukeyi har suka karasa gda horn Aslam yayi gate man y wangale katon gate din gidan suna shiga yaran gdan suka taho da gudu harda taslem duk suka futo a motar wata mika islam tayi taja doguwar hamma ko rufe baki batayi ba,da sauri Aslam yadan bige bakin yace ba'a fada miki in anyi hamma ana rufe baki ba ihu ta kwala a firgice y juyo yace dan Allah kiyi hakuri yakai hannu y rufe mata baki,da yake ba wanda yaga time din daya bige bakin nata.
Shiru tayi taja tsaki ta murguda masa baki,kaka ta kalleta tace ke kuma ihun mene wannan kamar wadda tayi gamo cuna bakinta gaba tayi bata bata amsaba.
Su mommy da aunty amarya ne suka futo sukayiwa kaka sannu da xuwa har part dinta aka shigar da dukkan kayansu dayake an riga an share part din.
Bayan sun gaida kaka,islam kuwa hankalinta yana kan taslem yar 3 year tanata mata wasa,aunty amarya tace islam baki gammu bane ba gaisuwa murmushi tayi tace aunty amarya ina xuwa wasa nakewa taslem duk maganar da takeyi ko dago kanta batayi ba.
Girgixa kai aunty amarya tayi a ranta tace Allah y shirya,futa su mommy sukayi suka kawowa kaka abinci kala kala bayan sunci,islam ta mike ta shiga toilet fanfo takeson kunnawa ta kasa,saboda ba irin na kauyensu bane garin kici kici ta kunna shower kawai sai jin ruwa tayi y xubo mata ihu ta saka tana wayyo Allah na shiga uku.
Da gudu suka tashi sukayi bathroom din ganinta sukayi a tsaye jikinta sai rawa yakeyi ta rufe idonta sai ihu takeyi ruwa duk y jikata,Aslam da Amir dariya suka farayi ganin dalilin kukannata sauran yaranma duk suka dau ihu suna villager girl aunty amarya kuwa tsaki tayi ta koma mommy ce ta shiga bathroom din ta kashe shower din kayanta ta taimaka mata ta cire,sannan tayi mata wanka ta bata towel suka futo,mai ta shafa mata da powder sai kwalli islam tace mommy bakiyi min dige-dige ba,mommy tayi murmushi tace nan birnine ba'ayi ko kinaso a dinga ce miki yar kauye xumbura baki tayi tace niba yar kauye bace mommy tace ai dama bance miki yar kauye ba,islam tace to daxu daga ina ruwa y xubo naga ba a bude saman bandakin yake ba balle nayi xaton ruwan samane jan hannuna mommy tayi suka koma bandakin tace wannan shower sunanta wanka akeyi da ita dariya ta kyalkyale tace yasin birni yayi ta dada kyalkyalewa da dariya a haka suka futo yaran suna ganinta suka fara villager girl kugu ta kama ta joge kafa tana girgixa tace wace bulleja gal din wlh ni ba sa'arku bace sainayi muku tsinannen duka(nikuwa nace kaji turancin manyaπŸ˜‚πŸ˜‚).

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜


Please Login or Register in order to submit comment