Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fizgo kofin gilashi na rotsa masa aka, ba shiri ya saki sirinjin ya fasa wata razananniyar kara. Ni kuwa na mike na nufi wani dakin daban cikin mawuyacin hali, dan abu uku ne suka hadu suka haifar min da rashin hayyaci. Na farko yunwa ga tashin hankali ga kuma sinadarin gusar da hankali da aka fesa min. Da kyar na rarrafa na isa dakin, na maida kofa na murza key, sai na soma wani irin nishi. Daga nan kuma sai naji dif! Komai ya dauke min. Ban san iya adadin lokacin da na dauka cikin wannan hali ba, sai farkawa nayi na ganni a yashe a kas! Na yunkura da kyar na mike cikin galabaita na isa kan gadon dakin, na daga labule sai naga ashe akwai taga a wajen, ko da na leka sai naga a she a saman bene nake, na hango can kasa da nisa, nan fa na shiga tunanin yadda zanyi in gudu in tsira daga gidan nan. Idan nace zan dira ta tagar nan hakika na san zan iya fadowa in farfashe, dan haka na girgiza kai
na canza shawara. Dabara ta fado min, sai kawai na shiga laluben abinda zan daura a jikin taga in rike shi in sauka. Kamar ance in leka kasan gadon, ina lekawa na hango igiya, sai kuwa nayi saurin janyowa, sai dai me zan gani? 'Kafafuwan mutane na gani a daddaure a jikin igiyar, na zabura na ja da baya...


Apropos 17.05 19:00#4
  Shulamanoff-line
S-Group PM
12

KARHE!!!!

Toh! Ai Hikenan!!

==> Na ja da baya cikin matsananciyar fargabar da tunda Allah ya halicce ni ban taba shiga irin ta ba. Rawa kawai jikina yake, idanuna sun firfito waje tamkar wacce tayi arangama da namijin zaki a daji... Kaina ya daure sosai, na rasa abinda zanyi, ina tsoron komawa falo dan ban san abinda zai same ni ba in na koma, nan kuma bazan iya tsayawa ina ganin wani bangare na halittar dan adam ba. Na rasa mafita, sai zazzare ido nake ina kara lafewa a jikin kofar kamar zan shige cikinta. Na rintse idanu amma hawaye ya kasa fita saboda girman tashin hankali. Da na rasa abinda zanyi sai na sunkuya na leka ta 'yar kofar dake jikin kofar na hango babu kowa a falon, sai kuwa na zabura na bude kofar cikin sauri na fita a guje na doshi daya dakin dake kusa da shi, na tura kofar da karfi na shiga... Sai dai ban kai ga daidaita tsayuwa ta ba na ga wani abunda ya kara daga min hankali. Wato wata kyakkyawar farar budurwa na gani a kwance a kan gado, jikinta babu komai, kuma an daddaureta da igiya a jikin gadon bata ko kwakkwaran motsi. Sannan an sakala mata abinda ake yiwa mutane karin ruwa, amma ba ruwan ake kara mata ba, jininta
ake zukowa yana taruwa a cikin ledar... Na zabura nayi waje da gudu cikin wani irin yanayi da bazan iya fassara shi ba. Sai na tsaya turus a falon na kasa shiga daki na gaba, na tsaya jikina sai rawa yake yi. Jin motsin da nayi ne yasa na zabura nayi daya dakin da gudu. Na mayar da kofar na rufe, na jingina baya na a jikin kofar ina maida numfashi. Daga nan kuma na soma kalle kalle ina tunanin me kuma zan gani a wannan dakin? Na jima ina dube dube amma ban ga komai ba, hakan ya dan kwantar min da hankali, na samu 'yar nutsuwa. Na nemi waje na zauna a gajiye ina numfarfashi. Can kuma sai na mike na nufi toilet din cikin dakin babu fa komai a ciki na amma haka nan naji cikina na hautsina wa, na dade a zaune a toilet din amma na kasa yin komai, da na gaji sai na mike na kunna famfo na sha ruwa kadan dan kar cikina ya kulle, na kumayi alwala na fito na fara ramuwar salin da aka biyo ni tun jiya, karshe a zaune na karasa Sallahr saboda galabaita. Haka naci gaba da kasancewa a cikin wannan dakin cikin kunci da damuwa, ga yunwa wacce nake magance ta da ruwan famfon cikin toilet din. Allah ne dai yayi akwai sauran kwanana a gaba, amma na san da babu abinda zai hana wahala ta kashe ni. Sai a yau da safe ne na farka daga mawuyacin baccin da ya sace ni naji ana bubbuga kofa, na zabura na mike a tsorace ina zaro idanu. Jin kamar muryar daddy na tasa na dan nutsu, sai naji yana cewa in bude sune tare da 'yan sanda. Duk da haka saida na leka ta windo sannan na bude, aikuwa ina ganin mahaifina sai na fada kanshi na rushe da kuka. Ganin Kawu da nayi cikin ankwa ya kara tayar min da hankali, na dinga tambayar daddy na waye yasa a ka kawo ni nan? Amma sai yaki yi min bayani. A haka har muka isa gida.... Ya mai girma mai shari'a, wannan shine abinda ya faru dani lokacin da Kawu yasa aka sace ni. A karshe kuma ina rokon wannan kotu mai adalci da ta shiga tsakanin mu dashi da mijina dan kar ya hana mu zaman aure..." Safina tayi shiru kamar yadda kowa ma a kotun yayi shiru. Mahaifinta kuwa sai faman girgiza kai yake cikin fargaba da tashin hankali. Alkali ya gama rubuce rubucen sa ya dago kai ya soma bayani. "Duba da wadannan abubuwa da suka faru a jere-a jere, kotu ta samu gamsuwa da a binda ji daga bakin mutum biyu, saboda haka an dage shari'ar zuwa nan da wata guda, kafin nan anyi bincike dan samun cikon shedar da ake nema... Yanzu za'a tafi da Alh. Tanimu tare da yaran nasa izuwa gidan ajiya. 'Yan sanda kuma zasu je gidan sa su bincike shi dan samu cikon shedu..." Alkali na gama fadar haka ya buga gudumarsa, kotu ta tashi. To fa! Nan fa ake yinta! Ya kaga idanun Kawu a lokacin da aka buga masa ankwa aka tusa keyar sa zuwa motar gidan maza.... 'yan uwan Safina kuwa suka dinga sauke a jiyar zuciya da godiya ga Allah da ya tsare musu 'yar uwar su. Shi kuwa Abdul kin fita yayi daga kotun, ya nufi wajen barista Kamal ya rungume shi cikin farin ciki da godiya ga Allah da ya fara nuna gaskiya, hakkinsu kuma ya fara bibiyar kawu. "barista na gode kwarai da taimakonka a gare mu, sannunka da jihadin aure, hakika bani da bakin godiya gare ka sai dai in roki wanda kayi domin sa da ya biyaka da dukkan alkairinsa. Hakika ka cika amini na gari mai jajircewa kan damuwar aminin sa, kai dai Allah ya biyaka." Shima Kamal ya rungume shi yana dafa bayansa. "Ba komai abokina, ka cancanci fiye da haka a wajena. Allah dai ya nuna mana karshen wannan rikicin da nasara Ameen."** Kunyar duniya ta hadu ta rufewa Alh. Bashir idanu, ya kasa hada ido da kowa. Ya san dai kuskure ya riga ya tafka shi, abin duniya ya riga ya rufe masa ido ya
zubda girmansa a kasa. Abubakar ne ya karaso gurin mahaifin nasu yana murmushi yace. " daddy kaga abinda muke ta nusar da kai ka gane amma abin duniya ya hanaka ka gane yanzu kaga gashi ka kusa jazawa Safina shiga matsananciyar rayuwa. Allah dai ya kiyaye allah qara kiyayea..bayan kwanakin da akadiba yau gashi andawo xa'a yankema kawu hukunci.. Qarken munfiki jin kunya..


www.shulaman.wapka.me

==>Abdul yana sane yaki bi takan Safina, karshe ma zamewa yayi daga kotun ba tare da ya yadda sun hadu ba. Sam baya so su hadu har sai an kammala shari'ar, hakan
ya sa shi barin kotun ba tare da sun sani ba. Wayar sama ya kashe dan kar a dame shi da kira. Ya koma gida cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali. Su ma su Safina suka dun guma zuwa nasu gidan cikin farin ciki, yayin da duk kunyar duniya ta taru ta hana Alh. Bashir sakat! Ya yi nadamar abinda yayi, dama ashe mahaukatan kudi Kawu ya turo masa dan ya aurar masa da Safina, bayan ya sa an saketa. Hakan yasa shi ya kusa zaucewa ya kuma rintse ido ya yadda girman sa. Haka dai ya zauna ya dinga bawa iyalan nasa labarin abinda ya faru tsakaninsa da Kawu. Daga karshe kuma a ka nemi Abdul dan a maida Safina amma aka rasa, wayar sa in an kirawo a kashe ta take. Safina ta damu kwarai ta koma gidan mijinta amma ba yadda ta iya. A haka a daddafe har akayi wata daya. Suka koma kotu dan a yanke hukunci. Kotun tayi cikar dango da mutane, dan kuwa har a jarida sai da aka watsa sanarwar zaman kotun. Bayan kowa ya hallara, aka gabatar da shari'o'i, sannan aka shigo da su Kawu. Wayyo Allah! Kar kaso ka ga
yadda Kawu ya koma a lokacin. Da gani ba sai an baka labari ba ka san ya sha wahala, dan kuwa yayi bakin kirin da shi, jikin duk a farfashe alamun yaci duka.. Alkali yayi 'yan rubuce rubuce, sannan yasa 'yan sandan da suka yi bincike a gidan Kawun suka fito suka yi bayani rahoton da suka samo. Tabbas Kawu ya cika cikakken matsafi, irin abubuwan da aka gani a gidan wani abinma ba zai fadu ba. Sassan jikin bil adama kuwa kala kala a gidan. Hakan shi ya kara tabbatarwa da alkali abinda ake tuhumar Kawun da shi, an kuma samu cikakkun shedu. Saboda haka kotu ta yanke masu hukunci kisa ta hanyar rataya shida yaran nasa bayan an gana musu mummunar azaba ta kwana uku. Sannan kuma kotu ta karbe gidajen sa za'a maida su makarantu da kuma masallatai. Shi kuma Abdul aka mayar masa da matar sa. Daga nan Alkali ya buga guduma. Katu ta tashi. Kawu idanunsa sunyi tulu tulu, bakinsa sai motsi yake alamun yana so yayi magana amma ya kasa. Haka aka wuce da su zuwa gidan kaso shida yaransa suna kukan nadama (karshen su kenan) **. Alh. Bashir ya kasa hada ido da Abdul, shi kuwa zuwa yayi ya tsugunna ya gaida shi sannan ya taya shi murnar samun nasara. Alh ya dafa kan Abdul yace "Kayi hakuri yaron kirki, hakika na yadda kai mai kaunata ne tunda kana kaunar jinina har gashi akanta ka jajirce ka ke ta gwagwarmaya. Hakika na kusa in in tafka babban kuskure, amma na godewa Allah da ya ganar dani. Ga Safina nan kuje ku ci gaba da zama Allah ya baku zaman lafiya ya kare ku daga sharrin dukkan mai Sharri Ameen." Abdul ya girgiza kai yace "Ba komai Alh. Komai ya wuce, Allah dai ya kiyaye gaba" "ameen dan albarka". Ya juya ya nufi wajen barista kamal ya dukurshe har kas yana zuba masa godiya. Kamal ya tashe shi tsaye yana fadin "ka daina yin min godiya, Allah zakayiwa dan shi yafi cancantar ta" "haka ne. Banida kalmar da zan gode maka kamal, sai dai fatan Allah yayi maka sakayya da gidan aljanna"* Karshen komai ya zo, an maida Safina gidanta, sun ci gaba da zuba
soyayyar su ita da mijinta. Kamal yayi aure, suna zaune da matarsa lafiya. Zumunc da shakuwa a ke yi tsakanin Safina da matar barista Kamal mai suna Naja'atu. Kansu ya hadu sosai, haka suma, mazajen kansu ya kara haduwa sosai. Allah kuma ya budawa Abdul an kara masa mukami a ma'aikatar su dan haka albashin sa ma ya karu... Kai! Suna dai zaman lafiya har Allah ya dinga azurta su da haihuwa Daya bayan daya..... ALHAMDULILLAH MASHA ALLAH. KARSHEN LABARIN KENAN, DA FATAN ALLAH YASA AN AMFANA DA ABINDA AKA KARANTA.
ABINDA MUKAYI DAI DAI ALLAH YA HADA MU A LADAN WANDA MUKAYI KUSKURE KUMA YA YAFE MANA. NA GODE DA JUMURIN BIBIYATA DA KUKAYI TUNDAGA FARKO HAR ZUWA KARSHE.
Allah yasa a anfana da darusan dake ciki..

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment