Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dauki karan tsana ya dora mata nima kuma abin yazo ya shafe ni. Zakayo mamki idan nace mahaifina shi ya rike kawi tun yana yaro, ya masa hallacin da ba kowane dan uwa ne keyiwa dan uwansa ba, musammanma su da suke yan uba. Ba fa uwar su daya ba. Amma da iyayensu uka rasu ya dakko shi daga kauye ya kawo gabansa ya rufa masa asiri ya sashi a kasuwa. Duk rashin ji irin nasa baisa kawu ya gaza daga rikon sa da yake ba, sai dai fada da
nisiha, amma abin takaici idan an masa fada sai ya hau fishi, wani lokacin ma yaki kwana a gida sai yayi sati bai kwana a gida ba... Tin yana karamin sa yake sata ga cin zalin kanan yara da keta, sau uku ana kamashi ya ja yara soro yana lalata su. Kai karshe ma bakinsa ne ya kashe iyayena. Saboda kamashi da akayi da laifin shiga gidan wani malami yayiwa yarsa fyade. Shi kuwa mallamin da yazo zai yi masa ihu yasa karfi ya makure shi har sai da ya ce ga garinku nan .. Daga nan kuma ba'a sake sanin inda yake ba. Wato ya gudu. Matar
mallamin ita tayi bayanin bayanin wanda ya aikata hakan, tana kuka tana bayani gwanin tausayi... Ai kuwa sai jami'an tsaro suka kama mahaifina a madadin sa a cewar su
sai ya nemo shi sannan za'a sake shi. A lokacin fa ni ina dan karami, ko da na ga an kama mahifina sai muka hadu nida Innata mukayi ta kuka... Daga nan kuma na kudri aniyar nemo Kawu a duk inda yake matukar za'a sakar min mahaifina. Innata ma bata san na tafi ba dan in na fada mata niyyata bazata bar ni ba. Haka na dau hanya na shiga duniya ina neman Kawu. Na sha wahala nayi garari na ga rayuwa iri-iri, karshe na dawo da bakin cikin rashin samun nasarar nemo kawu. Ina


Apropos 17.05 18:51#2
  Shulamanoff-line
S-Group PM
12

Daga nan kuma na kudri aniyar nemo Kawu a duk inda yake matukar za'a sakar min mahaifina. Innata ma bata san na tafi ba dan in na fada mata niyyata bazata bar ni ba. Haka na dau hanya na shiga duniya ina neman Kawu. Na sha wahala nayi garari na ga rayuwa iri-iri, karshe na dawo da bakin cikin rashin samun nasarar nemo kawu. Ina dawowa gida kuwa na tarar da abin tashin hankali. Gidanmu akulle.. Ashe Innata ta mutu, tunda ta nemeni ta rasa ciwo ya kamata, kwananta biyu Allah yayi mata rasuwa, mahaifina ma acan inda yake a tsare labari yaje masa bakin cikin yasa shi hadiyar zuciya ya mutu.. Nayi kuka nayi nadamar tafiya da nayi na bar mahaifiya ta gashi yanzu na rasa su dukka......" yasa kuka.....


==> Abdul ya cigaba da magana cikin kuka yana cewa ".... Tun daga sannan rayuwata ta shiga kunci, ya zamo na shiga cikin gararin rayuwa. Dama bani da wasu dangi na kusa bare na koma wajensu, haka nacigaba da rayuwata ni kadai a gidan, na sanya kaina a makaranta ta gwamnati, a gefe guda kuma ina taba neman kudi. Rayuwa dai ta min tsada sosai nasha wahalar rayuwa har zuwa lokacin da na gama karatu na samu aikinyi. Sai da aka shekara kusan goma sha biyar kwatsam! Sai ga Kawu ya dawo, amma sai dai abin mamaki ya dawo a hamshakin mai kudi wanda babu wanda yasan sana'ar da yake yi. Kawai dai an wayi gari an ganshi ya sai tafkeken gida ya tare. Babban abin da yafi bakanta min rai shine, babu wanda ya taso da zancen laifin da ya aikata a can shekarun baya. Ko ganin ya dawo a hamshakin mai kudi ne yasa idanun mutane suka rufe suka kasa tuna abinda ya aikata ne? Oho! Tsakanina da shi sai gaisuwa, dan ban ma taba shiga cikin gidan sa ba, ko lokacinda na tashi neman auren Safina ban neme shi ba. Dattijan unguwar mu su suka shige min gaba wajen neman aure har Allah ya mallaka min ita, gashi yanzu Kawu yazo yana neman yi mana karan tsaye....." Kuka ya sake kufce masa. Kamal na ta aikin bashi hakuri, kwarai shima al'amarin ya girgiza shi. Duk yadda yake kallon Kawun ada a yanzu yafi ganinsa da rashin kima... Ya dinga girgiza kai yana ambaton, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". Sun jima a cikin yanayi na shiru, kowa yana saka a ransa. Daga can Abdul ya dago ya dubi Barista kamal. "barista ina mafita?" Kamal ya gyada kai yace. "Abinda za'a yi yanzu shine, zamu je mu sanarwa da iyayen safina abinda yake faruwa dan mu kara samun kwarin gwiwar kai kara kotu..." da sauri Abdul ya katse shi da cewa "A canza wata shawarar, dan kuwa kokadan bana so wani a dangin Safina ya san abinda ke faruwa" "Ai kuwa ya zama dole a sanar dasu, dan ta hakane zamu samu sahihiyar hanyar da zamu shigar da kara kai tsaye batare da wani tuhume-tuhume ko zargi ba, kuma zamu samu karin goyon baya baya da wasu taimakon a nasu bangren, amma idan aka ki sanar da su ya kake ganin abin zai kasance?". Abdul ya girgiza kai, baida wata makama, dole ya gyada kai ya ce "shikenan, a je a sanar musun" "Bari tunda an kirawo sallar magariba, sai muyi sallar in yaso sai muje bayan mun idar". Abdil ya amsa da "To".** Bayan sun idar da sallar suka dunguma zuwa gidan su Safina a mashin din barista Kamal. Suna isa kofar gidan suke iske ana ta hayaniya wacce mutim bazai iya fuskantar me yake faruwa ba! Suka dira daga kan mashin din cikin sanyin jiki, kowa a ransa na mamakin me yake faruwa? Kamal ya gaza barin abin a ransa sai da ya dubi Abdul yace. "Anya lafiya kuwa Abdul? Meke faruwa ne a gidan nan?" Abdul ya dan yamutsa
fuska yace. "banida masaniya, sai mu karasa mu gani". Suka karasa kofar gidan tare da yin sallama. Aikuwa sai ga mahaifin Safina ya dako tsalle ya damki wuyan Abdul, ya zaro masa jajayen idanusa,murya a kausashe yace da shi. "Kai matsiyaci! Yi maza ka rubutawa 'yata takardar sakinta, dan kuwa daga yau ta gama aurenka". To fa! Kunji wata sabuwa inji yan caca. Abdul ya kidime ya rude da jin kalaman surikin nasa. Hankalinsa kuma yayi mammunan tashi, idanuwansa suka firfito waje tamkar wanda maciji ya rutsa a daji. Ya juya kalli Kamal wanda shima nashi idanu ke a waje, kamar ma yafi Abdul razana, sai kada kai yake kamar kadangare. Wani matshin saurayi ne ya fito daga cikin gidan ransa a bace ya dubi mahafin nasa yace. "Dady me yasa abin duniya zai rufe maka idanu ka manta da kimarka da darajar ka ka barsu su zube a idanun duniya.. Shifa mutunci ba'a....." da sauri Alh. Bashir wato mahaifin Safina, ya katsa dan nasa da cewa "Kai rufe min baki shasha mara hankali, wallahi idan na sake jin bakinka anan sai na tsine maka, dabba kawai mara tunani." Da sauri Kamal ya dubi Saurayin wanda ya kasance yayn Safina yace "Abubakar kayi shiru kar ka sake magana" ya juya ga Abdul wanda har wannan lokaci wuyansa na damke a hannun Babansu Safina, kafin ya yi magana Alh ya sake dakawa Abdul tsawa "Kai! Ka sakar min 'yata nace ma idan ba so kake yanzun nan in shake ka ba... Na fada maka Safina ta gama aurenka, ta gama auren matsiyaci, wallahi tun farko ban san haka kake talaka fakiri ba wallahi da bazan dauki zukekiyar 'yata na baka ba, ni sai yanzu ma nake nadamar aura maka ita da nayi..." Abdul ya juya ya kalli Kamal a karo na dayawa, ya kasa magana saboda kyakkyawan rukon da mahaifin Safinan yayi masa. Suka hada ido da kamal, ya gyada masa kai, sannan ya juya ya
kalli Alhajin yace "Ammm! Alh. Kayi hakuri ka sake shi, ya amince zai saki Safina" jin hakan yasa ya sake shi sannan ya juya ga Kamal, "kai kuma wanene? Waye kai nasa?" Kamal ya gyara tsayuwa, "Ni abokinsa ne" a dai dai lokacon matan cikin gidan suka yayyo waje suna ta hayaniya. Alh ya kalle su a fusace "Kar wanda ya sake ya ya tanka min, duk kuwa wanda ya kuskura ya magantu sai na saba masa wallahi" aka yi tsit cikin jimami da da alhini. Abdul kuwa ya gyara rigarsa ya kuma koma bayan Kamal yana zare ido.........


www.shulaman.wapka.me

==>Barista Kamal ya kalli Alh. Bashir cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da bacin rai yace, "Alh kayi hakuri, Abdul zai saki safina amma bisa sharadin sai an kawo Safina, sannan ya saketa a gabanta
tunda da alama kana da masaniyar kome yake faruwa". Alh ya gyada kai, "Kwarai, na san komai, shi yasa ma nasa shi ya sakar min 'ya, dan ko da baku zo ba ni zan zo har gida in karbar mata takardar ta". "Shikenan Alh, mu zamu tafi, idan an kawo ta sai a yi mana magana" Kamal na gama fadar haka ya ja hannun Abdul cikin hanzari suka bar gurin batare da ya saurari abinda Alh ke fada ba...** Suna tafe kan hanya a mashin, Abdul sam ya kasa nutsuwa, zuciyar shi harbawa take da karfi kamar tana shirin keto kirjin shi ta arto waje. Ya sa hannu biyu ya dafe kai. "Kamal! Me yasa ka amsawa mutumin nan cewa zan saki Safina? Wa ya gaya maka zan iya sakinta duk rintsi duk wuya? Ina son ta sosai fiye da komai a rayuwata, bazan iya sakin ta ba,amma gashi kana nema kayi min karan tsaye" "Ka fahimce Abdul, idan bamu bi ta wannan hanyar ba ba zamu taba samu mu zame daga hannun bawan Allahn nan ba. Amma kaga hakan da mukayi mun rabu cikin sauki ba tare da wani mummunan al'amari ya faru ba. Hikimata a nan ita ce. Tunda mun samu mun kufce, gobe idan Allah ya kaimu zamu shigar da kara kotu, kawai sai dai su ga sammace, ina fatan ka fahimce ni? Kamal ya karashe da tambayar sa. Abdul ya jinjina kai irin na gamsuwa. Shiru kuma ya dan ziyarce su na wani dan lokaci, daga bisani Abdul ya sauke hannayensa da ya dora a ka yace. "barista, wani irin duba kayiwa wannan al'amari da ya faru?" Kamal bai amsa ba, saboda kokarin da nayi na ratse wata katuwar mota dan kar ta hargitsa masa tunani. Sai da ya nutsu sannan yace. "Eh, abinda na fuskanta game da sirikinka shine, Kawu ya siye zuciyar sa ne kudi, shi yasa ya nemi da ka sakar masa Safina dan ya aura masa!" Abdul ya gyada kai. Ya matso hawaye a idanunsa yace "Kawu bashi da imani ko kadan a zuciyar sa, kawu azzalumi ne shi na kwatance, amma Allah bazai taba barinsa yana zalunci a doron duniya ba, kuma in sha Allah bazan rabu da mata ta ba" Kamal yace, "bari in wuce in sauke ka a gida in yaso gobe da safe sai kazo" "To" Kawai Abdul ya iya furtawa. Daga nan suka ci gaba da tafiya, kamal ya sauke Abdul a gidansan shi kuma ya wuce nasu gidan cike da alhinin abinda ke faruwa daga jiya zuwa yau*** Bayan kwana biyu sai ga dan aiken alkali tare da 'yan sanda sunjewa da Kawu sammacin kotu. Nan fa hankalin Kawu ya tashi dan bai taba zaton abin zai kai ga kotu ba. Ya san kudinsa baza su yi masa
tasiri a kotun ba saboda ya dan razana. Amma da yake gagararre ne sai ya nuna kamar bai damu ba, sai ma ya dinga zuba murumushi yana bude fararen hakora... Zaman farko da akayi a kotun ta cika makil da jama'a, sai da aka gabatar da wasu shari'un sannan aka fara da ta su Abdul. Barista Kamal shi ya zamo lauyan Abdul. Yayinda shi kuma Kawu ya dauko wani lauya shima mai zaman kansa mai suna Barista Mukhtar. An fafata sosai, kotu ta bawa kowa damar yayi magana. Al'amura sun cakude dan haka Daga karshe kotu ta yanke shawarar daga shari'ar zuwa makonni biyu masu kamawa, sannan Kotun ta rufe shari'ar tasu ta kuma bada damar a gabatar da shari'a ta gaba. Nan aka shigo da wasu karti guda uku, a tube suke ba riga sai wando. Kallo daya mutum ya zai musu ya fassara irin matsananciyar wahalar da suka sha koma suke kan sha. Jikinsu a farfashe yake saboda duka, sai wani irin gunji suke irin na wahala.
Daya daga cikin su ne ya kyallara ido ya hango Kawu. Ai kuwa sai yayi zumbur ya nuna shi, muryasa a shake ya ke magana. "Ya mai girma mai shari'a, ina so kotu ta bani damar in fadi wanda ya samu muke aikata wannan danyen aikin". Alkali ya bashi dama. Yatsunsa na fuskantar Kawu yace. "Wancan shine Alh Tanimu wanda yake samu muke aikata haka". Turkashi!! Ai fa sai kallo ya koma sama. Kowa ya juya kallon sa ga Kawu wanda alokacin da za'a yanka jikinsa baza'a samu ko digon jini ba saboda tashin hankali. Idununsa suka firfito waje , gumi kuwa kamar an bude famfo... Shi kanshi alkalin al'amarin yayi matukar girgiza shi.
Kawu ya mike cikin tashin hankali yana sambatu irin na marasa gaskiya. "ni... Ni?... Kai... Sharri zaka.. Ni?" Alkali ya daka mishi tsawa. Nan da nan ya shiga nutsuwar sa. Alkalin ya juya ga wanda yayi maganar yace dashi. "Mecece shedar ka ta cewa Alh Tanimu(wato Kawu) shine yake saku kuna aikata laifin da aka kama ku da shi?" Mutum ya gyara tsayuwa murya a toshe yace "Tabbas Alh wannan shine wanda yake samu muna aikata laifi yana biyan mu makudan kudi wanda shima yake samu daga kungiyar su ta asiri...." Kau! Ido me naci ban baka ba? Haka idanun mutane suka firfito waje cikin dimauta da jin abinda ke fita daga bakin mutimin. A can gefe kuwa Abdul farin ciki ne ya dira a zuciyarsa dukda abin ya matukar girgiza shi. Ashe Kawu dan mafiya ne? Shiya sa sam baida imani? Ya daga kai ya kalli kamal, ya mika masa sakon jinjina ta idanu, sannan ya juya ya fuskanci mai lefin dake bayanin abinda su Kawu...
suke aikatawa........


Apropos 17.05 18:54#3
  Shulamanoff-line
S-Group PM
12

==>Mutumin ya cigaba da cewa, "mun jima muna yiwa Alh. Tanimu aiki yana biyan mu kudi masu yawa. Amma babban abin da ya bata min rai ya kuma sa na niyyar fasa kwai shine, ganin yadda dubun mu ta cika, alkadarin mu ya karye, hukuma suka kama mu, suka dinga gana mana mummunar azaba saboda sun nemi da mu fada musu wanda yasa muke aikata laifin da aka kama mu da shi mun ki fada. Saboda haka aka dinga azabtar da mu, amma abin takaici da labarin ya riske shi sai yayi fumfiris ya ki zuwa ya karbe mu alhali an kama mu ne ta sanadin aikin sa. To wannan ne yasa nayi niyyar tona asiri, sai gashi cikin ikon Allah muka ganshi a kotu yau, duk da bamu san da laifin da ake tuhumar sa dashi ba amma mun san bazai wuce shima dubunsa ce ta cika ba..." ya danyi shiru yana shakar iska. Yayinda kotun tayi tsit! Tamkar babu wani mahaluki a cikinta. Daga can gefe Alh. Bashir(mahaifinSafina) idanunsa sun firfito waje kamar su fado kasa saboda firgita da jin abinda ake fada, ya dinga rarraba idanu ya na juyawa ya kalli Abdul, sai ya juya ya kalli Kawu da aka saka shi a wajen da ake tuhumar masu laifi. Sannan sai ya juya ya kalli Safina da take ta faman rusa kuka. Sai ya girgiza kai, ya maida hankalinsa ga mutumin da ke cigaba da cewa "..Aikin da Alh. Tanimu ke samu shine, duk inda muka ga farar mace kyakkyawa sai mu dinga bibiyarta a matsayin masu sonta, zamu yi mata basaja ne sosai ta yadda ba zata taba fahimtar manufar mu ba. Zamu sakar mata kudi sosai har sai ta yarda mu masu sonta ne. Daga nan ne zamu nemi da ta zo muje mu gaida iyayen mu.. Idan muka samu ta bamu hadin kai sai mu dauketa mu kaita wani gida da Alh. Tanimu ya gina mana, idan muka kaita sai mu bata lemo wanda a cikinsa akwai abinda yake
gusar da hankali. Idan ta sha lemon sai ta bingire ta kama bacci. To a sannan ne mu kuma zamu fara aikata aikin mu... Dukkanin mu Alh. Tanimu ya bamu wasu manya manyan sirinjin da akeyiwa marasa lafiya allura guda biyar biyar. To wadannan sirinjin da su muke zukar jinin duk macen da muka samu. Kawannen mu zai cika sirinjansa guda biyar sannan sai mu dauketa mu kaita kofar gidan su mu ajiyeta cikin tsakiyar dare. Duk macen da muka yiwa wannan aiki bazata kara magana ba har abada, kuma ba zata dade a duniya ba za ta mutu... Idan mun kammala haka sai mu dauki sirinjin da muka zuki jinin mu juye a wata farar kwalba da ake bamu sannan mu kaiwa Alh. Tanimu, shi kuma sai ya biya mu makudan kudade... Sai da muka tsananta bincike sosai sannan muka gano kungiyar da su Alh. Tanimu suke tsafi. Wata shahararriyar kungiya ce wacce ba kowani karamin matsafine ke iya shigarta ba. Duk wanda ka gani a kungiyar to hakika yakai kouwa. Sannan kuma dukkanin membobinta shahararrun masu kudi ne, dan kuwa dodon tsafin su yana basu dukiya ta fitar hankali. Shi kanshi dodon tsafin nasu kasurgumi ne, dan kuwa baya shan jinin kowa sai na kyakkyawar farar mace budurwa wacce bata taba haihuwa ba. Shiyasa dukkan yan kungiyar suke yawa aurar kyawawan mata wadanda basu taba aure ba, ta hakane suke samun damar zukar jininsu ba tare da fargabar komai ba. Idan da za'a bi duk yan kungiyar da matayen da suka aura
za'a ga cewa matayen nasu basa dadewa sannan kuma suna samun tabin hankali sakamakon zukar jinin su da akayi....." A zafafe barista Mukhtar(lauyan kawu) ya mike ya daka wata uwar tsawa bayan ya nemi izini daga alkali, ya dubi mutum dake jawabi, cikin karaji yace. "Bai kamata kotu ta tsaya tana sauraren wannan mai laifin ba, domin hankali bazai taba daukar abinda yake fada ba. Ta yaya daga ganin mutum zaka kala masa laifi? Shin kotu bazata duba cewa azabace ta sanya wannan mai laifin dorawa Alh. Tanimu laifi ba?" Alkali ya dakatar da shi, sannan kuma ya ce "Kotu bata karbi korafinka ba" cikin bakin ciki da jin haushi barista Mukhtar ya gyada kai sannan ya koma ya zauna. Alkali ya dubi mai bayar da labari ya ce. "ka fadi sunanka ga kotu sannan ka ci gaba" "Sunana Aminu, amma anfi kirana da Ezike. Yadda akayi asirin mu ya tonu kuwa shine, a dalilin bin wata budurwa da mukayi, bayan ta amince mana muka dauketa muka kaita wani otel, muka gabatar da aikin mu. Har mun gama komai zamu gudu sai muka ji an bude kofar da karfi, mukayi tozali da yan sanda. Babu bata lokaci suka buga mana ankwa suka tafi damu. Ashe wai duka abinda muke aikatawa akwai wanda yake hango mu ta windo wanda muka manta bamu rufe ba, shine yayi maza ya kai report yan sanda suka
zo sakayi gaba damu... Ya mai girma mai shari'a, iyakar abinda ya faru kenan, kuma muna rokon kotu da ta sassauta mana, dan kuwa munyi nadamar abinda muke aikatawa har cikin ziciyoyin mu...." Kotu tayi tsit! Kai kace duk mutanen ciki ruwa ya cinye su. Idanuwan Alh. Bashir kuwa kamar su fado kasa saboda tsorata da yayi. Wai! Saura kiris ya tafka babban kuskure! Da ace yayi gangancin aurar da Safina ga Kawu da me zai faru? Shi kuwa kawu gaba daya jinkinsa rawa yake, gumi ya gama jike shi jagab! Shikenan tashi ta kare! Safina ta mike ta nemi da a bata izinin ta fadi abinda ya faru lokacinda Kawu
yasa aka saceta...


www.shulaman.wapka.me

==>Alkali ya gyad'a kai, bayan ya gama 'yan rubuce-rubucensa sannan ya dago ya kalli Safina yace "Kotu ta baki dama ki fito kiyi bayani" Safina ta tako a hankali ta fita zuwa inda mutane ke tsayawa, gaba daya idanun mutanen dake cikin kotun sun koma kanta. Sai da ta nutsu sosai sannan ta fara da cewa. "Tun ranar da abin ya fara faruwa muna zaune nida mijina, bayan ya dawo daga kiran da Kawunsa yayi masa. Tunda naga ya shigo cikin damuwa a lokacin na sha jinin jikina, na san akwai wani abu da ya faru, amma da na nemi da ya sanar dani abinda ya faru sai ya cemin ba komai. Daga nan sai aka turo masa sakon text a waya, da ba zai ma duba ba, nice na sa shi ya duba. Tunda ya soma karantawa naga yanayinsa ya canza sai hankalina ya tashi, kafin in kai ga tambayarsa me aka turo masa sai naga ya mike a fusace ya fice. Hankalina ya dad'a dungunzunma, na rasa abinda ke yi min dadi a lokacin. Fitar sa ba jimawa sai naji karar tsayuwar mota a kofar gidan. Kafin nayi wani yunkuri sai naga wasu girdagirdan katti su uku sun shigo. Na yi matukar firgita da ganin su, na takarkare zan fasa ihu, sai daya daga cikinsu, yayi wuf! Ya damke min baki, sauran kuma suka karaso suka suka rirrike ni. Suka zaro wata zabgegiyar igiya suka shiga daure min hannuna da kafa. nan na shiga zille zille da kufce kufce amma na kasa kwacewa saboda karfina da nasu ba iri daya bane. Suka daddaure ni tamau suka rufe min baki ta yadda ko kwakkwaran motsi bazan iya ba. Suka rufeni da wani koren mayafi kamar gawa haka suka dauke ni sukayi waje dani. Suka saka ni a motarsu suka tafi. Nayi mamaki kwarai da babu wanda ya fahimci abinda ke faruwa a duk fadin unguwar. Haka nan mutanen nan suka tafi dani a mota ba na ko motsin kirki. Ban san iya adadin tafiyar da akayi ba. Amma dai na san munyi tafiya mai nisa. Motar ta tsaya a wani guri da ban san ko ina ne ba, can naji an bude but aka fito dani suka yi cikin gidan dani. Sai da suka kaini falo sannan suka ajiye ni, suka kuma kwance min daurin da sukayi min. Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka....." Safina ta rushe da wani irin kuka mai jefa tausayi a cikin zuciyar wanda ya tsinkaya. Kotun ta sake yin shiru fiye da ko wani lokaci. Safina ta sharce hawaye taci gaba da cewa "Daga nan suka kawo min abinci da lemo. Kallo daya nayiwa abincin naji sam bai kwanta min ba, dan haka naki ci. Sai kuka da nake ta faman rerawa. Babu yadda basuyi dani na ci abincin ba amma fafur na ki ci, dan
jikina yana bani akwai wani mugun abu a cikin abincin. Sam ni bana ma jin yunwa, tashin hankalinda nake cikin ya wadatar dani daga yunwar. Haka na wuni ranar banci komai ba. Suma kuma basu daina kawo min a binci ba. Koda dare yayi sai hankalina ya yi mummunan tashi, dan ban san a inda zan fake in kwanta ba, dan naji a jiki na mutanen nan wata dama suke so su samu wacce zasu cutar dani. Can sai na hango wani daki a bude sai kuwa nayi zaraf na shige dakin na maida kofa na rufe. Na kwanta akan gadin da na gani a
dakin ina maida numfashi. Ranar dai yadda naga rana haka naga dare. Banko rintsa ba har zuwa wayewar gari. Na rasa ruwan da zanyi sallah da shi saboda haka na fito falo, sai dai ina fitowa naga daya daga cikin su yayi zaraf ya rufe dakin da na kwana, sannan naga ya fesa wani abu kamar turare a kwalba a dakin sannan ya juya ya nufi wani sashi na gidan. Ba'a dauki lokaci mai tsawo ba na fara jin jiri na diba na, tun ina daurewa har abin yafi karfin kwakwalwata na zame kasa dabar!
Sau wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba dani.... Kamar a mafarki naji jikana yana wani irin yammm yammm! Kamar ana taba ni, sai kuwa Allah ya bani sa'a na farka a gigice. Hankalina ya tashi sakamakon ganin abinda ke shirin faruwa. Wani na gani daga cikin mutanen da suka dauko yasa wani katon sirinji (syringe) yana shirin tsikara min. Ai sai nayi wuf

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment