Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KA SAKE TA NA AURA
Hausaebooks.cf
Ebook creator:- Shuraih Usman
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) http://hausaebooks.cf


=>ma'auratane,
Suna manne da juna tamakar wasu tif da taya sobada tsabar tsantsar kaunar da sukewa juna wacce ta zarce ta Laila da Majnun...
Zallan so wanda ba mis ko na kwayar zarra shi ke tasiri a wajen ma'auratan.. Kai duk yadda mutum ke zaton wadannan masoyan sun shige nan. Auren cikar buri sukayi da juna wanda suka shafe sama da shekaru biyu suna zuba 'yar ubansun soyayya, karshe kuma Allah yayi ikonsa a kansu ya cika musu barinsu suka mallaki juna a lokacin da suke muradin hakan.
Mako biyu cif-cif da yin auren masoyan, amma basu taba rabuwa da juna na sama da minti goma ba. Kullum suna tare komai tare suke yi...
Kai! Wadannan masoya fa sun wuce kwatancen mai kwantance, sun zama ma'aurantan da kowa zaiyi sha'awar inama shine?
A hankali kuma cikin shagwaba Amarya Safina ta dago ta dubi angon nata sai ta wani cuno baki kamar wata yar bebi. Ta kara lafewa a faffadan kirjin sa.
Ya sunkuyo da kansa ya kalle ta shima cike da nashi salon na soyayya yace da ita
"Sweety kiyi hakuri dan Allah ki saki ranki, wallahi ba dadewa zanyi ba, dan dai ma Kawu ne yake kira na amma wallahi da babu inda zani kema kin sani."
Ta kara mannewa a jikin shi kamar tana so ta tsaga kirjin shi ta shige. Muryarta bata fita sosai saboda shagwaba ta ce dashi.
"Ka san fa in ka tafi ba zanji dadin gidan ni kadai ba.... Wallahi dan dai kawai Kawu ne da kanshi amma da bazan barka ka tafi a lokacin da nake tsananin bukatarka a kusa dani ba wallahi..."
Ta kare maganar cikin matso hawaye. Yayi saurin sa hannayensa ya soma share mata hawayen, ya cigaba da bata baki har dai ya samu ta rabu da shi ya mike ya fice, sai da ta rako shi har bakin gate, a nan ma rike shi tayi, sai da kyar ta sake shi ya fice.
Kai tsaye gidan kawun nasa ya nufa cike da tararradin kiran da Kawun ke yi masa.
*
A babban falo ya iske kawun shi kadai, ya harde a bisan doguwar kujera, kai da ganinsa kasan babban gwaska ne mai shuni a hannu.
Ya nunawa Abdul wajen zama ya zauna, suka fuskanci juna sosai.
Shiru ne na wasu yan dakikoki ya ratsa tsakanin su kowa na taraddadin abinda zai ji daga bakin kowa....
Daga can dai Kawu ya katse shirun nasau ta hanyar yin gyaran murya, kana ya karkace babbar rigar sa ya zaro rafar kudi yan dubu dubu har guda biyar ya dire a gaban Abdul...
Gaban Abdul ya fadi rass! Cikin zazzarowar idanu ya kurawa kudin ido gabansa na cigaba da bugawa. Daga can kuma ya dago ya dubi kawu wanda fuskarsa ta yalwatu da murmushi, sai faman girgiza kai yake ya kadangare...
Ya gama nazarin Abdul din sosai ya fahimci yadda ya rude, abinda yakeso kenan.
Cikin sarkewar harshe Abdul ya shiga inda indar cewa.
"Kawu.... Me....wannan kudin.... Na mene....ne?"
Kawu ya tuntsire da dariya harda kyakyatawa, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru. A nutse kuma yace da Abdul "Wadannan yan kudaden ba komai bane matukar zaka yi amanna da bukata ta, to ni kuma naci maka alwashin ninninka
maka su har sai kai da kanka kace sun isa....."
Ko kadan Abdul bai taba tsammanin kudi zasu iya rudashi haka ba, sai gashi da saurin bakin cewa.
"Wacce irin bukatace wannan Kawu?"
"Me kake ci na baka na zuba? Kabi sannu zan sanar dakai kamai" Inji Kawu, sannan ya dora da cewa.
"Bukatace mai sauki kuma mai wahala, abinda yasa nace haka kuwa shine, na san a duniya a wannan zamani kudi suna tasirin siyan komai musamman ma idan aka hada da bude kwanji....
Wadannan kudin da kaga na baka su a yanzu na baka sune a matsayin toshiyar baki kafin inji amincewar ka in baka mamaki da kyautar da baka taba jin anyiwa wani ba a iya tsawon rayuwarka....
Zan baka kudade masu yawa muddin ka ce ka amince zaka saki matarka Safina......"
Wata irin zabura Abdul yayi cikin dimuwa da gigitar jin abinda kawu ya fadi, amma kafin ya tanaka kawun ya rigashi da cewa.
"Hold on abdul! Bance ka daga hankalinka ba akan wannan batu, shi yasa na cemaka bukatar tana da sauki tana da wuya, kuma a karankanka in kaso a kana iya daukarta mai sauki ko akasinta...
Na sani kwarai rabuwa da masoyi yana da wahala da ciwo a rai, amma kar ka manta nace zan baka arzikin da sai ka bada labari. Mata suna da yawa a duniya, ko ina kaje
zaka same su birjik kamar kaji, ledar fiyowata ma tafi su wahalar samu. Kana iya zuwa ka nemo ko wace irin mace ko yar waye a duniya ni kuma nayi maka alkawarin zanyima komai dan ka aure ta... Ni dai kawai buri na matarka KA SAKETA NA AURA!"
Tunda Abdul yazo duniya bai taba cin karo da bakar rana irin ta yauba, bai taba jin kalaman da suka munana ransa irin na yau ba.
Kau! Zufa ce ke keto masa ta ko ina
gashi dai falon cike yake da na'urar A.C amma bai hana shi jikewa shakaf da gumi ba...
Ya laluba ya rasa kalaman da zai mayarwa da Kawun nasa, kansa ya
dau caji, kwanyarsa tayi zafi rau! Ba dan Kawu ya kasan kani a wajen mahaifinsa ba yau da ko buzunsa bazai bari ba. Maimaita abinda ya fada kawai yake a zuciya...
Ya mike a fusace ya dubi Kawu cikin tashin hankali yace da Kawun.
"Wallahi kawu duk duniya babu wanda ya isa ya rabani da matata wallahi........."

www.shulaman.wapka.me

==>Kawu yayi zumbur ya mike ya sha gaban Abdul. Cikin zazzare ido da kausasa murya ya tari Abdul din da cewa. "kayi kuskuren yin wannan furucin yaro! Kuma ni kanin mahaifinka ni zan zama makarin furucin naka.... Bazan tausaya ma ba muddun baka tausayawa kanka ba ta hanyar sakkowa daga dokin nakin da ka hau, yaro kar ka bari buri akan mace ya kaika ga tafka babbar asara,domin kuwa biyu babu zakayi wato baka ga tsuntsu baka ga tarko! Na riga nayiwa kaina alkawarin ko ta wani hali sai na mallaki matar ka. Gwara ma ka yiwa kanka kiyamul laili ka karbi dukiya kayi arziki, sannan kuma kaje ka auri duk diyar da kake so... Na fada maka cewa mata basa wahala a wannan zamani kullum sabbi akeyi kuma masu kyau...." Gaba daya kam Abdul ya gama kullewa, hankalinsa ya kai kouwar tashi, wazu zafafan kalamai ne ke artabun fotuwa daga bakinsa, amma yaki bari harshensa su furta saboda sanin mutumin dake a gabansa. Matsayinsa ya wuce yayi masa rashin kunya, amma da yake bahaushe yayi azancin cewa tsohon da baiji kunyar hawa jaki ba, jiki bazai ji kunyar nika shi da kasa ba, sai da ya furta cewa. "Kawu bazan taba yin nadamar furuncin da nayi na cewa babu wanda ya isa ya raba ni da matata sai wanda ya bani ita... Kawu dukiyar ka bata isa ta fanshi soyayyar Safina a zuciya ta ba.... Kawu mai yasa kake son yi min karfa-karfa ne akan rabani da abinda ba karamain tashin hankali bane? Kawu kar kayi amafani da damar da Allah ya baka ta dukiya ka cutar dani a matsayina na da a wajenka?" Kawu ya tuntsire da dariyar mugunta, ya dinga kyakyatawa kamar ba zai daina ba, daga can kuma sai yayi dif ya kuma zubawa Abdul idanu. Gaba daya hankalin Abdul din a tashe yake, idanunsa sunyi jaja wur! Gumi na ci gaba da keto mishi ta ko ina. "Abdul! Tun farko kai kayi gangancin jefa kanka a inda ba ka kai matsayin da ya kamata ka jefa kan naka ba, ka je ka auri hamshakiyar mace irin wacce mu ya dace mu aureta, sam Safina bata dace da kai ba, safina MATAR MANYA ce, kai kuwa yarone karami, kuma talaka, dan albashinka da kake dauka bai taka kara ya karya ba, amma kayi ganganci aurar ta. Tun ranar da na fara yin tozali da ita wato ranar da kuka zo gaishe mu, a ranar da na ganta na kamu da sonta, kuma ka sani ni bana neman a bu in rasa a rayuwata, musamman idan a wajen da nake ganin aljihuna da kwanjina zasuyi tasiri... Saboda haka nake shawartar ka da ka hakura da matarka ta cikin ruwan sanyi ka saketa, ni kuma in baka arzikin da zai isheka har karshen rayuwar ka, amma idan ka bijire, to zanyi amfani da karfina wajen mallakarta ta ko wani hali, na baka awa uku kaje kayi tunani.... Idan kuwa naji shiru...hmmmmm kaima kasan karashen bayani ....." Abdul ya kauda ya kansa ga barin kallon kawun, bakinsa na rawa ya ce, "wallahi kawu sai dai kayi duk abinda zakayi dan banga wanda ya isa ya rabani da mai so na ba wallahi... Ni na dogara ga Allah kai kuwa ka dogara da kudi, to ka jaraba ka gani na san Allah bazai taba barinka ka zalince ni ba dan baya goyon bayan zalunci...." Ya juya a fusace ya fice fuuu! Kawu yabi tsayinsa da kallo yana girgiza kai da murmushin mugunta. Cikin cije lebe yace "Hmmm! Yaro yarone! Yaro bai san wuta ba sai ya....... **Safina kuwa ta kule a can saman gado sai faman cika take wai ita ala dole tayi fushi saboda Abdul ya ja lokaci bai dawo ba. Jin motsin shigowar sa da tayi yasa ta kara cuno baki, shagwaba fal a fuskarta. Ta zubawa kofar shigowa ido tana jiran shigowar tasa. Ya turo kofar a hankali ya shigo da sallamar sa cikin sassanyar murya... Kallon farko da tayi masa gabanta ya yanke ya fadi. Dukda Abdul din yayi iyaka kokarinsa dan gani ya kau da halin da zuciyarsa da gangarjikinsa gaba daya suke ciki amma hakan ya faskara sai da ta harbo jirginsa. Ta zuba masa ido zuciyar ta na ayyana abubuwa masu yawa da suka sanya tashin hankali ga mai gidan nata. Murmushi ya kakalo na karfin hali ya wanzar a fuskar sa, ya karasa gare ta ya zauna gefen gado. Tuni ta ware daga shwagabar da ta shirya tararsa da ita. Bai ce mata komai ba ya mika hannu ya rungumota,yana kokarin cusa bakinsa cikin nata ne ta kwace tare da ture shi gefe, ta tsare shi da ido cike da tuhuma. "My dear, na ga canji sosai a fuskar
ka, ni dai na san ba da damuwa ka bar gidan nan ba amma gashi ka dawo da damuwa, me Kawun ya cema?""Ba komai" ya bata amsa a takaice. Ita kuma ta ce "Baka taba boye min damuwar ka ba, dan me baza ka fadamin ba?". Ya karkace kai yana neman amsar bayarwa, da kyar dai ya tattara wasu yan kalmomi ya furta mata, cewa yayi "Ki yarda dani my love" Ta girgiza kai cikin saduda,sannan ta kwanta a jikinsa, ya ci gaba da aikamata sakonnin soyayya.... Saura kiris su kai can kouwar fita daga hayyaci sai wayar sa tayi karar shigowar sako. Dogon tsaki ya ya ajiye wayar ba tare da ya cuba sakon ba. "Ya kamata ka duba sakon wata kila akwai abu mai mahimanci a ciki" Bai musa ba ya bude ya fara karan tawa... Tunda ya fara karantawa yanayinsa ya fara canzawa... Ya mike a fusace bayan ya gama ya mata. "Ina zuwa...." ya fice da sauri bai saurare ta ba....


www.shulaman.wapka.me

==>**Wayam! Ya iske dakin babu kowa, kuma anyi kaca-kaca da komai na cikin dakin. Wannan ya tabbatar masa da cewa lallai Kawu ya aikata abinda ya ce zai yi a sakon da ya turo masa a dazu... Nan da nan nadamar fitarsa ta fado masa, yayi da na sanin fita ya bar matar sa gashi ya dawo ya iske abin tashin hankali, Kawu ya turo an sace Safina... Fitar da yayi sam bata yi masa amfanin komai ba sai zamowa silar karin tashin hankali. Dama da ya fita ofishin yan sanda ya nufa dan yin report bisa ga sakon da Kawu ya turo masa na cewa zai aiko a dakko masa Safina a kudirinsa na son kafa hujja da sakon da ya turo masa , to amma wani abin takaici shine, da ya isa ofis din yan sandan kai tsaye ofishin D.P.O ya nufa.. Kwatsam kuma sai yaci karo da daya daga cikin yaran Kawu yana direwa DPO wata yar karamar akwati makare da kudi... A kan kunnen sa yaji sakon da kawun ya bayar na cewa kar a karbi case din da zai kawo. Baya bukatar tsayawa yin wani abu don ya riga ya gama jin komai. Gumi ne kawai ke karyo masa ta ko ina a jikinsa, wai kawu wani irin mutum ne mai tsananin son zuciyarsa? Wani irin mutum ne shi mara adalci da tausayi? Wani irin azzalumin mutum ne shi? Ya runtse idanuwansa zafafan hawaye suka surnano daga idanun sa, ya juya ya koma gida don kokarin sanin abinyi, to gashi ya dawo ya iske kawu ya cika aikinsa....... Ya zube a kasa sharab! Cikin hauhawar tashin hankali. Hakika Kawu ya tashi kurar zata jima bata lafa muddin bai dawo masa da matarsa ba sai inda karfinsa ya kare. A da baiyi niyyar bayyanar da abin a duniya ba dan babu wanda ya sani, amma ya lura abin ba karami bane don haka
dole ne ya shigar da kara kotu dan a karbar masa iyalin sa a hannun azzalumin kanin mahaifinsa....... Ya mike zumbur! Kamar wanda aka tsirawa allura, ya sharce hawayen idanuwan sa, ya kulle ko ina na gidan ya fice ya nufi gidan Kawu. Sai dai me? Loakacin da ya isa kofar gidan mai gadi yashi da saurin sa yare shi, ma'ana ya hana shi shiga gidan, sai ma ya turo kofar tare da garkama mata katon makulli. Abdul ya tsaya yana duban sa sororo cike da takaici da bakain ciki. "Kai mallam bude min kofa in wuce" Abdul ya fada yana mai kurawa mai gadin ido. Wani irin na kaskanci da wulakanci mai gadin ya jefe shi da shi, kafin daga bisani ya dora da cewa. "Alhaji bai bada wannan umar ni ba, ya umar ce ni da kar in sake in bude maka gate, saboda haka sawunka a likkafa ka juya ka koma inda ka fito..." Saboda tsabar takaici Abdul kasa tankawa yayi, sai ido da ya zubawa mai gadin yana mamakin wai mai gadi ne ke gaya masa wadannan maganganun! Wato dai kenan ta ko ina sai Kawu ya bi ya tozarta ya zaluncesa a matsayinsa na da a wajen dan uwansa. Nan dai ya sake duban mai gadin ya ce,
"Wai bazaka bude min kofar bane?" kafin mai gadin ya kuma tankawa suka ga na bude karamar kofa ta ciki. Kawu ne ya fito fuskar sa dauke da maketacin murmushi wanda har fara zame masa madubin fuska. Ya dubi Abdul ido cikin ido, yace dashi. "Ina fatan tafe kake da takardar sakin matarka...?" wani abu mai nauyi ya tokare makogaronsa, da kyar ya hadiye, sannan kuma cikin sartun hawaye ya fara gayawa Kawu duk kalmar da tazo kan harshensa. "Hakika Kawu ka cika cikakken azzalumi mara imani, mai son raba sunnar ma'aiki, mai son rushe katangar masoya... Kawu wacce irin zuciya ce a kirjinka wadda babu digon haske a cikinta? Kawu me yasa ka nace lallai sai ka rabani da matata dan kai ka aureta alhalin kai da kanka kai ne waliyyi na? Ko dan kaga babu ran mahaifina yasa kake son cutar dani? Me yasa kai baza ka je ka nemi wata macen ka aura ba? Haba kawu! Haba kawu! Idan dan rashin mahaifina baisa ka taimake ni ba ai bai kamata ka cuce ni ba... Ka gaggauta fito min da matata tun kafin in kai abin kotu a kwatar min yancina...." Kawun ya zuba masa idanu har sai da ya tabattar da Abdul din ya gama fidda kalaman ciwon rai sannan ya tare shi cikin cije lebe da girgiza gami kuma da mamakin naci da taurinkai irin nashi yace "Taurin kai! Taurin kai! Abdul ka faye taurin kai, kuma baka san cewa taurin kai shi yake cutar dan jaki yake cin bugu a iska ba... Har yanzu kana da sauran lokaci da zaka iya karbar kudi ka sakar min matar ka, idan har ka bari lokaci ya kure maka zakayi asara biyu ne wato ta matar ka da kuma da makudan kudi, dan tun da na riga na kyalla ido akanta na kamu da ciwon sonta... A halin yanzu tuni anyi nisa da ita dan na tabbatar tuni sun fita daga nigeria a jirgi, na tura a kaimin ita can kasar england domin a tsare min ita har zuwa lokacin da zaka gaji ka sakko ka saketa... Idan kuma kana ganin zaka sanya hukuma cikin al amarin kamar yadda ka fada to ka gwada ka gani in zakaci riba.... Mu zuba ni da kai yaro!" Karshen maganar kawu tayi dai dai da juyawar sa cikin gidan ya kuma maida kofa ya garkame.... Mai gadin ya dago ya dubi Abdul dake tsaye kamar gunki, komai na jikinsa ya daina aikin wucin gadi, yace "To alarmma sai ayi gaba ko? Mu zamu bude gidan saboda mabukata..." ya kare maganar cikin watsawa abdul wani munafikin gwalo mai ciwo a rai....

www.shulaman.wapka.me

==>Abdul ya runtse idanu, wasu zafafan hawaye suka kwaranyo masa. Sabon tashin ya sake dirar masa, ransa ya jagule gaba daya nutsuwar ta gudu. Rawa kawai jikinsa yake saboda tsananin damuwa da bacin rai. Ikon Allah ne kawai ya maida shi gida, dan kuwa sam bai sake sanin abinda ke
faruwa ba sai bude idanu yayi ya ganshi kwance bisa gadonsu. Numafarfashi kawai yake kamar mai ciwon asma. Yana jin lokacin da wani zazzafan ruwan tashin hankali na kwaranyowa izuwa birnin zuciyarsa. Allah ne dai kawai ya wunar da shi wunin ranar lafiya ba tare da ya sheka barzahu ba. Sai yamma sosai sannan ya dan samu yar nutsuwar da zai iya saka tunani tsakanin zuciyarsa da kwakwalwarsa. Kamal wani abokinsa lauya shi tunanin sa ya hango masa a lokacin da yake tunanin mafita. Zumbur! Ya mike kamar wanda aka tsikara da allura, yayi wura- wura ya dauki abinda zai dauka sannan ya fice. Ya gark'amawa gidon katon mukulli ya juya ya nufi gidan abokinsa barista Kamal. Ya taki babbar sa'ar samun sa, dowowarsa kenan daga ofis, ya dawo a gajiye, saboda haka ya zauna a stroom din gidansu yana shan iska. Abdul ya dauko wayarsa ya kira shi ya sanar masa gashi a kofar gidan su. Jim kadan sai ga shi ya fito sanye da doguwar jallabiya. Yana ganinsa ya washe baki, sannan cikin zolaya yace. "A'ah! Kai ango, kaga ango na amarsu, ba'a ganinka sai amarya ta yadda..." Ya hadiye zolayarsa ganin babu fara'a a fuskar wanda akewa. Sai ya dan sassauta cikin sanyin jiki, ya mika masa hannu suka gaisa. "Lafiayar ka kuwa Abdul? Kaga yadda ka zama kuwa? Kamar ba ango ba, meke faruwane?". Abdul ya girgiza kai ya cije lebe ya rintse idanu, sai ga hawaye shar-shar! "Ya salam. Subahanallahi, Abdul muje ciki ka min bayani" Kamal ya fada tare da juyawa ya nufi cikin sitroom din, ta kofar soro suka shiga. Bayan sun zauna Kamal ya bude firij ya dauko masa ruwa da gwangawanin maltina ya dire masa. Sam Abdul ya manta da cikinsa, wunin ranar baisa komai ba a cikinsa ba, amma sam bai damu ba, dan kuwa tashin hankali yayi masa maganin yunwar. Sai a yanzu da Kamal ya gabatar masa da maltina sannan ya tuna cikin sa wayam yake. A lokacin kuma cikin sa ya fara yi masa korafin tauye hakkinsa da yayi. Hakansa yasa sai da ya fara shan malt din sannan ya dago ya dubi abokinsa Kamal idanu fal da hawaye. "Kamal! Ina cikin matsala ina cikin tashin hankali...." ya labarta masa duk abinda ke faruwa. Girgiza kai kawai Kamal keyi yana ambaton 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un'. Sannan ya dora da cewa "Lallai sai yau na tabbar da abinda kake fadamin wato kawu baya kaunar ka kokadan... Kai! Hakika mutum bashi da imani ko kadan a zuciyar sa" ya danyi shiru yana kallon Abdul dake sharar kwalla. Ya kara da cewa "Na yi mamki da wannan aiki na Kawu. Kamar ba kanin mahaifinka ba? Kai! Allah wadaran naka ya lalace." Abdul ya matse hawaye. "Ba abin mamaki a cikin irin kiyayyar da Kawu ke min. Tun mahaifana suna da rai dama baya kaunar su musamman ma mahaifiyata, saboda tana bawa baba na shawarar hanyar da zaibi ya horar da shi(kawu) shiyasa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment