Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu banbanci a cikinsa na rantse maka”.
        Har ƙasan zukata zancen nata ya dake su, ganin bayyanar rauni a fuskokinsu ya saka Babiy yin murmushin ƙarfin hali yana shafa kanta. “Shaiɗanu zasu iya dawo miki da makamancin sa ai Ibnati, dan haka ki kwantar da hankalinki Arfa na lafiya a gidan aurenta”.
     Bazata cigaba dayin jayayya da su ba, amma tana cikin matsanancin damuwa tamkar yanda take hango tasu akan fuskokinsu. Maimakon komawarsu barci sai duk suka miƙe zuwa tsakar gida, alwala suka ɗauro, suka koma can runfar dake matsayin falon iyayensu suka fara salla da miƙa kukansu ga UBANGIJIN talikai da fatan hana tabbatuwar abinda zukatansu ke cikin tsananin fargaba. Haka suka kasance har sallar asubahi gaban mahaliccinmu, bayan idar da sallar asubahi maimakon kwanciya sai suka riski kansu a zaman jugum-jigum na jiran tsammani. Har fitowar rana babu wani yunƙuri daga ɗayansu. Sai ko ga isowar abinda suke fargabar ya riskesu ya iso garesun. Shigar bugun gidan a cikin kunnuwansu ta sakasu miƙewa a zabure gaba ɗaya kuma a lokaci ɗaya, kowanne cikin rawar jiki da fidda tsammani. Babiy ne yay jarumtar ƙarasawa ga soro cikin jan ƙafa. Tunda yay tozali da hadiman masarauta zuciyarsa tai wata irin masifar wulƙitawa.....
     “Kun kasheta itama ko?!”.
Da shi da hadiman suka riski muryarta a cikin kunnensu a bazata. Sam babu tsoro ko shakka irin wadda akema duk wani mai alaƙa da masarauta a ƙasar cikin idanunta a yau. Sun soye sunyi jazur irin na tashin hankali. A harzuƙe cikin hadiman ɗaya ya daka mata tsawa da faɗin, “Hattara ɗiyar talakawa, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane”.
     “Idan yaron ya kasance rago ba!!”.
Ta bashi amsa itama a tsawace. Shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa ya ɗaga zai zuba mata Babiy ya kare cikin rawar jiki yana mai zubewa ƙasa a kan gwiyawunsa. Sosai a zaba ta ratsashi, ya rimtse idanu cikin aro dakiya da jarumtar dole, “A gafarceta ita ɗin yarinyace masu nasara”. Ya faɗa cikin rawar murya saboda azabar tasirin shigar bulalar.
    Ƙasa Iffah takai durƙushe gaban Babiy tana mai fashewa da kuka, kafin ta ɗago ta dubesu zatayi magana Babiy yasa hannu ya rufe mata baki jikinsa na tsuma. Jikin nata itama tsumar yakeyi, sai dai ita bana tsoro bane na tsananin baƙin ciki ne da bushewar zuciya. So take ta amayar da abinda ke bakinta an hanata. Batare da hadiman sun sake bi takantaba suma suka isar da saƙon dake tafe da su.
        “Kasancewarka mai biyayya da bin umarnin masarauta a karo na biyu an sake baka damar halartar jana'izar ɗiyarka kai da zuri'ar ka. Mun barka lafiya”.
     Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Babiy ya shiga ambata, kusan a tare Ummu da Fariha suka saki razananniyar ƙara wadda ta jawo hankalin maƙwafta da mutanen dake tsaitsaye a ƙofar gida tun wucewar hadiman masarauta. Dan sun san dai labarin gizo bazai wuce na ƙoƙi ba........

       *_WASA FARI GIRKI_*

    Dole ne zuri'ar mal. Zayyan su ambaci rasuwar Arfa da kalmar WASA FARIN GIRKI a jerin zaren ƙaddarar da ta kutso a rayuwarsu mai ɗauke da almakashin da ya datse farin cikinsu. Sun rasata tamkar labarin hikayoyin marubuta ko wasan kwaikwayo na film. Ta tafi tafiyar da bazasu sake ganita ba, tafiyar da babu wanda aka bawa damar yin cikkakkiyar sallama da ita a cikinsu hatta mahaifansu. Ta shuɗe a ƙaddararsu tamkar yanda ruwan damuna kan tafi da duk wani yayin dakan tare masa hanya a lokacin wucewa. Komai ya faru tamkar ba'aiba. Babu mai iya koda tari balle bin ba'asi. Iyakarsu kukan idanu dana zuci wanda muryarsu kan tsayane kawai iya filin gidansu ko katanga basu isa bari ta haura ba. A yau ma dai Babiy da Hanash ne sukaje domin jana'izarta. Suko aka barsu da amsar gaisuwa a cikin gida wadda mutanensu talakawa na zuwa musu itane a ɗarare.......
  
         Kwanaki sun cikagaba da shuɗawa tamkar ba'ai komai ba, yayinda ɗayar matar Tajwar da aka aura masa tare da Arfa itama dai ta mutu bayan wasu watanni. Bayan su Arfa ba'a sake jin Tajwar yayi wani aure ba, sai dai mutane na raɗeraɗin a duk randa aka kaisu domin ziyartar turakarsa babu fashi gawarsuce take fitowa. Hakan yasa kowa ke danganta mutuwar matan da tsafi yakeyi dasu.
      Wata huɗu da sati ɗaya cif tarihi ya sake maimaita kansa, dan kuwa Fariha ta sake faɗowa a jerin matan da aka ɗaurama Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed aure da su. Batare da wani shawara ba a safiyar alhamis suna zaune kira ya riski Babiy daga masarauta, babu wanda bai shiga tsoro da firgici ba a cikinsu, sai dai babu wanda ya isa hana hakan a duk faɗin ruman. Sunaji suna gani babiy yay shiri ya amsa kiran. Tafiyarsa da awanin da basu gaza biyar ba sai ga hadiman masarauta sunzo sunma Fariha ɗaukar amarya itama babu wani bayani daga garesu. Ranar dai kam Iffah bata gazaba kojin tsoro wajen gwada musu hauka, dan bata bari an fita da Fariha ba har sai da basamuden nan ya zabga mata bulalar dorinar hanunsa data sakata zubewa, bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wucewarsu da kusan awa guda. Zuwa lokacin har Babiy ya dawo. Kamar dai Arfa itama Fariha an ɗaura mata aure da sarkin da kowa yake masa inkiya da fir'aunan wannan ƙarnin. Sai dai a ɓoye wannan suna ke fita a bakunan talakawan gari irinsu Iffah. Sakamakon bulalar da aka zabga ma Iffah bayanta yay mugun fashewa har akan mazaunanta, ga wani raɗaɗi mai azaba na ratsata har ta kasa riƙewa sai da ta saki ƙara. Babiy da Ummu suka rufu a kanta, hawaye suke suna jeramata sannu, Hanash na gefe zaune idanunsa jajur alamar tsananin ɓacin ran da babu ƙarfin ɗaukar mataki......
      Tayi jiyya ta kwanaki uku, wajen ya warke, daga haka kwanaki suka cigaba da tafiya, inda a cikar watanni biyu itama Fariha mutuwarta ta riskesu tamkar ba'ayita ba. Sun sake rasa Fariha a dalilin auren Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed.............✍😭

3

.........A wannan gaɓar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raɗaɗi da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke ɗaukar tama zare kawai. Daga ƙarshe maganin barci aka ɗura mata. Bata tashi farkawa ba sai a ƙauyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a ƙauyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun ɗaura ɗammarar ɗaukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba ƙaramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira'a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke'a ranta sai buri da ƙudirin ɗaukar fansa. Tama kanta alƙawarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir'auna a ƙasarta a cikin al'ummarta....

  *_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah😱? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa....? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura😬🤧🚴🏼)_*

       

      ★★★

       “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taɓaren daka a tsakkiyarsa, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar ƴan uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saɓanin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.
     “Nina Arfa! Nina Fariha!”.
Ta ambata a zahiri zuciyata na ƙara ƙarfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu ƙarfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin ƙofar ɗakin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiɗar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta ɗauka ta yanama jikinta, ta ƙarasa ga ƙofar ta buɗe...
      “Kina lafiya kuwa ɗiyar nan?”.
Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.
    “Ina lafiya Kaka”.
  Jin shiru bai sake cewa komai ba ta ɗago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai ƙasa, hawayen da take faman riƙewa suka ɓalle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na ƙwace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaɗarta ya sata haɗiye kukan, ya ɗagota tsaye yana ɗan murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya ƙare, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.
    Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani ɗan lokaci. “Kije kiyi addu'a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.
     A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.
        Da sauri ya girgizamata kansa. “A'a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuɓutar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina ƙanƙanin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saƙa kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi ƙanin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa ɗan uwan mahaifiyarku a yaƙin kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke ɗaya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta...”
     Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga ƙangin fargaba, da gaske tanajin matuƙar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni ƙalilan da suka shuɗe itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya ɗauka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raɗaɗi da saka ƙuna a ƙirji......

          ★★★

   “Iffah! Iffah!!.....”
Sautin ƙwala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banɗaki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haɗiye maganar da zatayi tana mai kallon ɗan-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a ƙarƙashin bishiyar ɗoruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta ƙarasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai ɗan rungumesa ta gefe da faɗin, “Ina kewarku Akhi”.
        Murmushinsa ya sake faɗaɗa yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daɗi”.
   Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.
         “Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baƙo a garinku”.
  Baki ta ɗan tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miƙe tana bata amsa cike da shagwaɓa. “Iyyani laifinkine fa, ban taɓa ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.
     Daƙuwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
         Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faɗi abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haɗu da Iyyani sai ta hasalashi take jin daɗi shi da Arfa akan ƙinyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da ɗaya. Iffah nada goma sha takwas....
        Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
    Ya nisa a hankali bayan ya dire moɗar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan ɗin muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za'ai masa”.
    Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin ƙarfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haƙuri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waɗanda kansu kawai suka sani.......”
      “Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da ƴaƴansu daga auren jeka nayika. Karatun ƴammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huɗu fa, a tunaninki kafin ƙarewar wannan shekarar ba'a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”
         Wasu hawayene masu ɗaci da ƙuna suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu ɗaga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a ƙasar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran ƙasashen duniya akwai wanda suka fisa...”
    “Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
  “Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.
          “Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faɗa a yanayin jin raɗaɗi a maƙoshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta ɗauke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a ɗan gefen gari suke acan ɗin ma. Sai dai su shigo cikin ƙauyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen ƙauyen suke. Sun ɗan jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona ɗebo sassaƙe-sassaƙen magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga ƙarshe ma tashi tai ta shige ɗakin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. Sassaƙe-Sassaƙen magungunan daya ɗibo ɗazun ne a gabansa, kowanne ya ɗauresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki... “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. Waɗannan kuma hayaƙine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaɗan ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
        “Tofa kaka wannan ɗin kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.
   Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar ƙaddararmu bashi ke nuna baza'a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuɗe da ɗaci zata iya yuwuwa yau ɗinmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al'amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaɗai masanin mi zaizo.”
        Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta ɗan ɗage kafaɗa cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaɗamata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buƙatar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko'oho. Sai kuma ta miƙe tana mai faɗin, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauƙi gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
       Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaɗa kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alƙalamin da ba'a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da ƙarfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
        A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunƙulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faɗa...”
      “Hanash! Lokacin faɗar baiyiba ai, nima kurman baƙin kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
     Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al'amarin ba yasa ake shakkar faɗa, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai ƙarfinsu da shaiɗancinsu. Sannan yana sana'arsa ta saƙa kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta'allaƙa sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka ɗinne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaɗai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su............✍


Page 4

.........Iffah tayi mamaki da kaka ya bari salin alin tabi Hanash washe gari, duk da Iyyani taso borewa ita. Amma wasu lafuza daga cuɗaɗɗun kalamansa ya sata yin shiru ta bisu da addu'a. Kaka yayma Iffah gargaɗi matuƙa akan abubuwan daya bata, ya kuma tabbatar mata ko guda ɗaya taƙiyi zaiji hakan a jikinsa.
        A hankali ta murza awarwarayen hannunta da shine ya sakamata, ta sake lumshe idanunta da sakin ajiyar zuciya. Haka kawai takejin awarwarayen da girma da kuma banbanci da irin wanda take sakawa a baya domin kwalliya, ko miye dalili oho.

       Daga Ummu har Babiy a tsorace suke kallon Iffah da Hanash da suka shigo. Hanash ya girgiza musu kansa cikin sauri yana faɗin, “Wlhy ba laifina bane Babiy. Itace ta bore akan saita biyoni, kaka kuma ya bata goyon baya. Dan a cewarsa _(Babu wani nisa dake bada tazarar gujema ƙaddara. A wani ajin jarabawar data biyoka ma gara kai ka tunkareta. Dan ba kowane kogo bane ke zama kogo ga ma'abocin gudun ceton rai)._ Babiy na kasa fassarawa, akoda yaushe cirkuɗaɗɗun kalamai daga bakin Kaka masu tsaurine da wahalar fahimta. Dan ALLAH idan kun sani ku fassara mana”.
        Maimakon amsa daga Babiy baya sukaga yayi tamkar zai faɗi, sai dai cikin sa'a ya dafe gini tare da dafe kansa alamar hajijiya. Ummu ma ƙasa takai zaune jikinta na rawa, hakan sai ya ƙara firgitasu. Da sauri duk sukai kansu suna mai tambayarsu suna lafiya kuwa?. Da kai kawai suka amsa musu, Babiy harda ƙoƙarin ƙaƙaro murmushi. Cikin son kwantar musu da hankali yake kallonsu. “Kunga karku sakama zukatanku wata damuwa, ba maganar Baba bace ba, kawai dai bana jin daɗine kwana biyun nan dama”.
       Jimm sukai alamar tunani, sai dai kuma babu damar yin musu ko ƙin aminta da cewar tasa. Hanash ya taimaka masa suka koma cikin runfa, Iffah kuma tana riƙe da Ummu..

★★★

          Washe gari batare da sun sani ba Babiy yay sammakon yin tafiya zuwa ƙauyen Jumna. Ya samu tarba daga surukan nasa ko ta girmamawa....

      Ƙyaƙyƙyawan tsohon da Tattarowar fatarsa ta tsufa bai hana bayyanar ƙyawun cikar halittarsa ba ya sake kallon dattijon gabansa a karo na babu adadadi. Murmushi ya saki a karon farko, cikin karyar da kai da ƙanƙan da idanu ya kai hannu bisa kafaɗar dattijon. Numfashi yaja kakkaura da juyowa alamar dawowa hayyaci. Ya maida kansa ƙasa ya sunkiyar saboda girmamawa ta surukuta dake a tsakaninsu na tsahon shekaru.
        “Humm Muhammadu Zayyanu!”.
   Tsohon ya kira sunan tamkar mai sake bita a ranar da aka raɗa ga mai shi. Ɗago idanu ya sakeyi a karo na biyu sai kuma ya risinar tare da amsawa da “Na'am Baba”.
       “Tun isowarka magana nake gani shimfiɗe a fuskarka amma bakinka ya kasa furtawa, ko wani abu ya sami Hanash da ƴar uwarsa ne a hanyarsu ta komawa gida jiya?”.
    “A'a baba ko ɗaya, lafiya lau sukaje cikin ƙoshin lafiya kuma, sai dai.....”
  Sai kuma yay shiru ya kasa ƙarasawa. Kaka dake kallonsa yay ɗan murmushi, “Sai dai baku so komawar Iffah ba ko?”.
    “Hakane baba. Domin kuwa babu abinda ya canja a daular Ruman, muna jin tsoron rasata itama kamar ƴan uwanta, duk da bamu da tabbacin zasu sake waiwayrnmu, sai dai kalamanka sun sakamu a ruɗani har muka kasa rumtse idanu a daren jiya domin yin barc......”
          “Hana ido barci bashi ke nufin damar iya sauya abinda bakai ka rubuta ba. Muhammadu Zayyanu! Da ace ƙaddararmu a hannayenmu take da kaf mutane bazasu zana zaman duniya ba a littafinsu musamman idan sun san koda daɗin busawar iskar dake cikin aljanna ce. Karka damu kanka da sanin sirrin cikin dutsen da ko'a kallo abin firgitarwa ne. Mumini yakan kasance mai azumtar yini daga UBANGIJI, ya kuma sallaci duhun dare daga UBANGIJI domin yaye damuwa ko samuwar nutsuwa a duniyarsa. Gaibu daga ALLAH take, zahirin da yaso mu sani kawai yake iya nuna mana ta isharar rayuwa ko canjawar tunanin zuciyo
yi”.
      Nannauyan numfashi yaja ya fesar tare da jinjina kai, bawai kwanciyar hankalin da yazo nema ya samu ba, sai dai rashin zaɓi ko bakin zaren kamawa ya sashi fahimtar tsohon na masa nuni da shiru ne kawai a zubama sarautar ALLAH ido dan shine kawai gagara misali.....

_________________

       ★Kwanaki biyu kenan da dawowar Iffah gida, inda dawowar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment