Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fada. Bari in shigo da
bakon, ya kika bar shi a waje. Lokacin
ne ya fita ya shigo da shi..
Haleema kuwa sun gama koke koken su
taja Anne ta nufi dakin su tace bari in
shiga inyi wanka tukun, Anne ta amsa
to, halima gani tayi anne ta tsaya a tsaye
sai kale-kalle take, ji dallah kamar wata
baffalata na ki zauna mana, Hmm abin
hada ba'a ko haleema, nan dai tayi
dariya ta fada toilet din. Anne kuwa
kama baki tayi tace “wai dama halima
cikin wannan daular take amma har ta
iya rayuwa a gidan mu wai hadda cin
abinci, Hmm gaskiya na jinjina miki.
Tashi tayi taje gaban mirror tana kallan
kayan make-up kala-kala, lokacin
halima ta fito, anne Ta kalli haleema,
nifa wallahi mamaki kiki kara bani wai
dan Allah ya kika ji dan zaman gidan
mu da kikayi, Haleema tayi murmushi
tace to ke mene nufin ki, ai ni dan
banbanci kadan na gani, Hmm kadan fa
kika ce? Nan dai sukai tayi. Da suka gaji
da surutun sune anne ta shiga toilet
itama domin yin wanka.
BANGARAN DEENI KUWA:
Karfe 11:00 PM
Masifar yunwa da yake ji tayi yawa
haka yasa shi tashi yaje ya taba kofa, Ya
taba kofar kamar wasa yana murdawa ta
bude kuwa, lekowa yayi ya duba ko 'ina
baiga kowa ba, ya juya ya kalli abokan
nasa wato yan sandan nan sunci abinci
sun koshi sai barci suke harda minsharin
su. A hankali cikin sanda ya fita kamar
ba kasa yake takawa ba dan sanda shine
har falo yana yi yana waige-waige.
Wajan makeken kofar fita ya nufa, zuwa
yayi ya kama kofar da niyar budewa
bisa mamaki sai ji yayi.......................
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
Shida dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 35
Share This:
Wata mahaukaciyar dariya yaji an barke
da ita "hahahaha" can kuma ya hanga
bai hangi komai a gurin bam, hakan ya
kara basa damar sake kama kofan da
niyan ya bude ta, amma kamar dazu
dariyar kartai kawai yaji ya juyo kuma
baiga kowa ba, hakan ya basa damar
budewa duda yaji dariyan amma yasa
hannu biyu iya karfin sa ya ja kofar, ai
kuwa ta bude, waige-waige ya dingai a
tsakiyan wannan makeken gidan baiga
komai ba. Da gudu ya karasa gate in
gidan, basa kulle kofa domin tarkon ne
su a gunsu na barin gidan a bude, irin
dai darkon da su deeni suka fada.
Yana fitowa daga gidan yayi wata
hamdala “Alhmdulilah” ya juya ya kalli
gidan amma baiga koda alamun gida ba,
yunwa yake ji matuka, hk ya rinka
tafiya jiri na daukan sa domin yau
kwanansa uku baisa komai a bakinsa ba.
Haushin karnuka ya ringa ji a bayan sa
sai matsowa suke, ai kuwa kafin kace
me, washi manya-manyan karnuka ya
hango sai haushi suke sun nufo shi, ai
kuwa yace kafa me naci ban baki ba,
take yaji wani sabon karfi a tare da shi
tuni yaji yunwar ta baci saboda wani
masi fafan gudu suke yi.....
**************
Bayan gari ya waye
Tun 5:00 su alhaji bashir suka dau
hanyar dake alhaji sunusi ya fada musu
tun jiya cewa halima ta dawo, shi yasa
suke ta zumudi domin su zo taya dan
uwan nasa murna.
Ban garan su halima kuwa tun a daran ta
shaidawa su abban nata cewa tare da
yayan anne suke su sun wuce gidan su
maryam ne shine ya tsince ta. Sunji dadi
matuka, haka dai suka cewa yar tasu taje
ta huta domin tana bukatar hutu, ita
kuwa duk ta damu tunanin deeni take
kuma har yanzu ta tambaye su yafi a
kirga amna basu bata lafiyayyar amsa ba
domin suma basu da amsar.
Haka shima bangaran su maryam
Aliyu kam kamar can dama abokai ne
shida isah domin daren jiya ma a gado
daya suka kwana. Maman deeni tayi
farin ciki sosai sai dai kuma in ta tuna
har yanzu batasan inda deenin ta yake
ba sai taji bakin ciki. Maryam tun da
suka dan natsu take tambayam yayanta
wato deeni. Amina ce ta kwantar mata da
hankali tace ta bari ba yanzu ba tukun
sai gobe sayi magana.
Tun safe kafin su karya alhaji sanusi ya
aiko da mota yace yana bukatar ganin
kowa da kowa na nan gidan kawu,
kawun deeni yace a bari suyi breakfast
mana, amma dan aiken alhaji sanusi
yace “yace a gaya muku ya tanadar
muku abun breakfast a can”. Haka
driver ya tsaya ya jira su suka dan
kintsa tukwanan suka tafi.
A falo aka hadu gaba daya, ga kayan
breakfast nan kala-kala, gasu nan an
jejjera sai abinda mutum yake san yaci.
A zazzaune suke suna jiran su maman
deeni, cikin sacan 30 sai gasu sun iso
ko wanne cike da farin ciki fal a zuciyan
sa, haleema kam sai dubawa take amma
bataga gwanin nata ba, wato deeni. Haka
suka je aka jejjeru, kawu da alhj sanusi
saiti daya suke, haka maman deeni da
maman haleema da amina maman aliyu
suma gefan su daya, a kan carpet suke a
zaune, haka suma su haleema bangaren
daban, suma su isah haka, abin dai abin
sha'awa kamar dama family ne.
Bayan duk anyi gaishe-gaiishe, Alhaji
sunusi ne ya fara magana “Assalamu
alaikum”, kowa ya amsa. Yace to a
gaskiya baxan iya bayana muku farin
cikin da nake ciki ba a yanzu,
sakamakon wannan al'amari mai ban
al'ajabi da ya faru wato batun mutuwar
haleema. To a hakikanin gaskiya
wannan jaraba wace daga Allah sannan
idan...... Wayarsa ce tayi kara ya fiddo
da fara'ar sa ya daga ganin wanda ke
kiran nasa, wato yayan sane alhj bashir
da suka taho daga abuja. Yace gasu nan
sun karaso cikin kano motar su ce ta dan
sami matsala a turo driver ya dauko su,
cikin farin ciki yace to shikenan yaya
gashi nan yanzu zai zo ya dauko ku
kuna daidai ina ne? Ya kwatan ta musa.
Nan da nan aka kira driver ya tafi dakko
su yazeed..
Jin sun taho ne alhji sanusi yace ayi
breakfast kafin su karaso, sai muyi duk
abinda ya dace. Ba gardama nan aka hau
ciye-ciye da shaye-shaye su ya isah
kuwa sai satar kallan maryam yake dan
kayan da tasa sun mata mugun kyau.
*****************
Deeni kuwa gudu yake kamar me dan
tsabar gudu ko gaban sa baya tsaya wa
kallo ,daga ya juyo sai ya ga kamar
karan zai kama kafar sa sai ya kara wuta.
Sanda suka share kusan raibin sa'a suna
gudun tukunna deeni ya waiga yaga ba
karnukan, sannan ne ma ya lura da wai
har ya kawo bakin titi, gaskiya ko shi
yayi mamaki domin yanda ya tuna irin
nisan da sukayi, tsaye yake bakin titi ya
kai minti 20 a gun baiga ko wucewar
mota daya ba, tukunnan ya hango
fitulun mota ta nufo inda yake kamar ya
gudu kuma sai ya tsaya. Motar in police
ce yaga ta faka, godiya yayi ga allah a
tunanin sa ga masu taimakon sa nan sun
kara so.
Abun mamaki wani kurtu yan sanda ne
ya fito dauke da kulki a hannunsa bai
tsaya wata-wata ba ya fara kwadar deeni
a kwauri yana fadin daga ganin wannan
mugu ne, shi kuwa deeni da yake ta
faman kare duka kira yake wallahi
yallabai ni ba mugu bane ka saurare ni
yallabai, ai ina kawai kwadar sa yake
saida suka mar likis tukuna suka dauke
shi suka jefa a bayan mota, yan sanda
uku ne biyu suka hau baya wato inda
deeni yake dayan kuma ya tukasu, basu
zame a ko'ina ba sai a office in su...
*****************
Tuni driver ya kawo su, suka nufi cikin
gidan, yazeed ne yaji kirjinsa na
bugawa da sauri ya rasa dalilin haka
gashi kuma sai karuwa abin yake. Su
hajiya saratu ne a gaba, wato alhj a
gabanta shi kuma yazeed bayan umman
nasa. Baban yazeed ne ya fara shiga da
sallamarsa, ganin mai shigowa ne yasa
alhaji sanusi washe baki yana wata
kalan dariyan farin ciki, sanda duk suka
shigo. Yazeed tsayawa yayi tsitt yana
kallan wani abu, sannan gaban sa na
dada bugawa da sauri.
Halima ce da maryam yake kallo shi
kam abin gani yayi kamar a mafarki,
saida ya ji tana gaida su abban nasa
sannan ya tabbatar ita ce ba mafarki
yake b,. dama haleema na raye, dama su
mugu karya suke ashe basu kashe
haleema da maryam ba, hmm tabbas bai
cancanta su mugu su kara koda sacan a
duniya ba. Ko gaishe da su abba bai
tsaya yi ba direct dakin sa ya wuce, bai
ko kalli su abba ba ya shige dakinsa
dake a gidan. ...................
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
Bakwai dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 36
Share This:
RECOMMENDED ARTICLES
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 37 Na
Isah Bigboy
Yana shiga dakin a fusace ya duba cikin
wata jaka ya dauko wata Pistol ya bude
ta ya zube harsashi sannan ya sakata a
tsakanin belt din sa na wand, ya sake
fitowa a fusace sannan cikin hanzari
yazo ya wuce, har ya kama kofa zai
bude sai abbansa yace: “yazeed mene
haka ina zaka kake sauri haka ko gaida
abbanka bakayi ba” daddy ina zuwa
abinda kawai ya fada kenan bai jira
wata amsa ba ya bude kofa ya fita. Gurin
motoci yaje yasa makullin motar ya
warce ta kamar wanda zai tashi sama....
Deeni kuwa cikin cell kake hango sa
yayi tagumi duk an bubuge masa kafa,
tunani yake tayi kala-kala a zuciyarsa, a
gaskiya idan ya makara fa yazeed zai
kai kawun haleema gidan gunkin su, shi
isa duk ya matsu da su sallame sa amma
ina sunki wai shi mugu ne sai sunyi
bincike a kansa. DPO suke jira kuma
wai shi sai 9:30 yake zuwa.
Wani makeken gida yazeed ya faka tare
da yin hoon, mai gadi ya leko yana
ganin yazeed ne da sauri ya bude gate
din dake shima yasan yazeed, a millon
ya shiga gidan motar ma bata gama
tsayawa ba ya bude murfin motar ya fito
a fusace ya nufi cikin falon. Ko
kwankwasawa bai tsaya yi ba ya tura
kofar ai kuwa ta bude. A dinner ya iske
su mugu suna breakfast shayi da biredi
ne da wainar kwai sai indomei, ko
sallama baiyi ba, tsaye cik yayi yana
kallan su, a zuciya yana cewa wato na
baku aiki bakuyi ba kun min karya kuma
gashi sai holewa kuke abinku. Oga ne
ya dago kai, Yazeed ya gani a tsaye ya
zuba musu na mujiya fuska a murtuke
ba ko walwala a fuskarsa..
Ah mai gida yazeed barka da zuwa kana
tafe ashe kuma shine ko kira babu ai da
mun tanadar maka special break da
munsan zaka zo, sai a lokacin ne su
mugu suka lura ma da yazeed din take
duk suka tsare shi da kallo suna mai
wani dan murmushi...
Shi kuwa maganar ce ta ogan ta bata mai
rai yaji wani tiririn bakin ciki yake ji a
zuciyar sa, wata zuciyar tace ya harbe su
kawai, me yake jira da su wata kuwa
zuciyar tace, ya tambaye su yaji me zasu
ce karya zasuyi ko kuwa..
Karku min karya, kunce min kun kashe
maryam da haleeema?
Dukkan nunsu saida hantar cikin su ta
kada domin duk sanda suka firgice
domin kuwa sun san tambayar nan ba’a
banza ba, ruwa baya tsami banza kuma
sun san yazeed ba imani a tare da shi,
duk shiru sukayi suka kasa cewa komai,
duk sun shiga tunani, ogan cikin sune ya
katse tunanin da yin wani dan
murmushi, Hmm oga yazeed kenan kaga
ya daga hannu, Ni na kasheta Halima....
Harbi uku kawai akaji sai gasu duk a
kasa, ya juya da bindiga a hannunsa
tana wani tiriri.
Fita yayi da waya a makale a kunnan sa,
barka da safiya shi ne abinda ya fara
furtawa dake mu Journalisms in zamani
ne har mgnr wancan in naji. Morning hw
ur day shine abunda yce: im 5yn: dad
haleema an maryam they ar living. Me
kake cewa kasan me kake fada kuwa.yes
srry dad wllh nayi da nasani sa su mugu
aikin da ni na aikata da duk hkn bata
faru ba amma saukin abu ba alamun
cewa sun fadi abunda suka gani.gud ka
take care of ur self. Ok dad bye. Ya
kashe wayan sannan yi shiga motan sa
yazo gate yayi oda da nufin mai gardi
yaxo ya bude mai gate amma ina yaji
shiru.
Abinda bai sani ba shine mai gadi yana
jin harbi yayi waje da gudu, dole ce tasa
sai shi yazeed ne ya fito a motan yaje ya
bude gate in.
Can gidan su haleema tuni an gama
breakfast kowa ya kama harkokin gaban
sa su alhaji bangaran su daya su uku,
yau dai kawu an kashe mai zuwa kasuwa
du da yaso ya fita amma haka bai samu
ba, su alhaji sanusi sun hanashi dole
tasa shi hakura, yanayi yana surutu a
zuciya “hmm wato ku masu kudi ko?
kun tara! ku bar bawan Allah ya fita ya
nemo na kansa amma kunki ku barni...
Haka shima isa yayi niyar jan yar
kanwar sa su nufi gida in yaso sai ya
dawo batun maganar auran maryam
amma alhaji ya hana yace dole ya bari
sai gobe domin akwai kyauta ta
musamman da zaiyi mai na ban mamaki.
Haka ya hakura gashi aliyu ma ya fita ya
barsa shi kadai ne a wajan yayi zuru sai
kale-kalle yake dake a lambu ne. Ji yayi
an rufe mai ido daga baya da wasu
tatausan hannaye, wani sanyi ne yaji ya
ratsa duk kannin jikinsa, baiji anyi
magana ba murmushi kawai yayi tare da
cewa hmm anne, to na gano ki. Shiru
yaji ba'a tanka ba kuma sai yaji abin
zobe a hannun nan ya tabbatar da ba
anne bace domin yasan ita bata da
zobe............
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 37
Share This:A GAFARCE MU NA RASHIN KAWO
MUKU CIGABA DA WURI
Wata zazakar murya ce yaji ta daki
dodan kunnansa, ta shiga cikin
kwakwalwarsa ta dinga yimar yawo.
Tabbas bazai taba mantawa da zazzakar
muryar maryam ba, “Hmm maryam”
yace, Hmm taya ka gane nice lokacin da
ta sake shi tana zagayowa ta zauna a
kusa dashi, haba tayaya ne zan ji muryar
abar sona in kasa gane wa ai da bakiyi
magana bane shine sai in kasa ganewa.
Murmushi tayi tare da cewa ya isah baka
gayawa su umma abinda ke tsakanin mu
ba kuma dazu kake cewa wai zaka tafi,
dan marairai cewa yayi tare da cewa ai
ko na tafi ma to annesah zan kai in dawo
gare ki sahibata, idan ka aure ni a wane
gari zamu zauna? Tabbas ta debo
babbar magana, shin yanzu shi mema
zaice mata ne, shima kansa ba san
zaman a wancan kauyen yake ba balle
ita da take dama yar birni, kai gaskiya
da sake, to yanzu me zaka ce mata. Yana
cikin yan sake-sake ne tace “yaya isah
ina sanka, so na gaskiya kasani cewa ko
a kauyenku zamu zauna zan aure ka.
Wani murmushi yayi wanda ya kara
bayyano kyawunsa, baice komai ba,
hada ido sukayi, sun dade a haka suna
kallan juna.
Yazeed ne ya shigo ya faka motar sa
kafin ya fito, da murmushin sa ya fito ya
nufi inda su abban suke ya gaida su da
kawu wato baban aliyu sannan yake
gayawa abban sa ya shirya yanzu zasu
je domin yaga gun aikinsa da kuma mai
gidansa. Alhaji bashir ya kalle sa yace
to ai a shirye ma nake, yi sauri ka zo mu
tafi, amma ina kaje ne naga kana
hanzari haka ko karyawa kuma bakayi
ba ka fita inji abban nasa.
Daddy naje wajansa ne domin ya kira ni
namai wani dan aiki ne, ok to allah yama
albarka tashi jeka. Tashi yayi ya nufi
falo, Haleema da Maryam da Anne su
duk ukun suna zaune a falo sun kunna
kallo sunayi hade da hira sama-sama.
Baima bi ta kansu ba kai tsaye dakinsa
ya nufa, “ina kwana Ya yazeed”, Yaji
ance. Juyowa yayi bisa mamaki yaga ai
haleema ce, lfy lau yace har ya juwa zai
bude dakin ya karaji an gaida shi da
murya biyu, Maryam da Anne ne, suma
haka dai ya cije lebe ya amsa sannan ya
wuce dakin nasa. Kan gadonsa ya haye
yana jin wani tiriri da zafi a zuciyar sa.
Wanni bangaran kuma tunani yake taya
zai hallaka su tun kafin su tona mai asiri
domin tunani yake sun san ko shi waye,
amma yayi mamaki da basu fadawa
kowa ba, yaji kamar ya kyale su
hallarcin da suka mai na kin tona masa
asiri, saidai kash!! Lokaci ya kore dole
ya kashe su domin kuwa a duniya banda
su ba wanda ya san ko shi waye sai yan
kungiyar su.
Mutanan gari a yaro mai ladabi mai
girmama na gaba da shi, mai kyauta, san
addini, kyakykyawar tarbiya kawai suka
sanshi, ba wanda yasan mugun abinda
yake aikatawa, kuma ya shafe sama da
shekaru 4 a cikin wannan kungiya.
Tashi kawai yayi rai a bace, ya fito da
wayarsa yayi kira wata number “da fatan
ashirye kuke domin ina zuwa da
mahaifina”. Eh a shirye muke kawai a
ka fada ya katse wayar ya shiga
bandakin dake cikin daki, yayi brush
tukwanan ya dan watsa ruwa ya fito ya
chanza kaya, Jeans baki yasa sai wata
riga T-shirt mai layika shudi da fari, ya
taje gashinsa, yayi kyau sosai tukwanan
ya fiton daga dakin.
Su haleema da ke zaune a falo suna
shiriritar su. Tun kafin ya karaso gunsu
kanshi ya cika su,gaba daya kamar
hadin baki suka juya suna kallan sa shi
kam ko damuwa baiyi da su ba ya wuce
waje abinsa. Haleema kam yayi mata
kyau yau, tace wa maryam kinga
mutumin yau anci gayu ko dai zance
zashi, kinga ba ruwana kinsan dai halin
sa ... Hhhhh dariya halima tayi au ashe
baki manta ranar ba, Maryam ta kama
baki tare da cewa hmm wane ni in
manta, Anney kuwa tambaya ta shiga yi
wai me akayi wancan ranar, suka share
ta. Can halima ta dago ta kalli anney
"ohh yi hakuri anneesat, bari in gaya
miki abin da ya faru wancan rana."
Kamar kullum duk weekends maryam na
kawo min ziyara ko ni in kai
mata............
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 38
Share This:HALIMA TACI GABA DA BAWA
ANNE LBR: Ranar wata lahadi maryam
ta kawo min ziyara kamar yanda kika
ganmu yanzu to haka muka zo falo
muka kuna kallo sai hira muke abun mu,
yazeed yana gidan wato ya kawo ziyara.
Maryam ta tambaye ni miye tsakani na
da yazeed da muke faman fada da shi
haka, nace mata wai kawai dan na shiga
dakin sane kinsan ya hana, “to miye a
dakin nashi da yake hana shiga, naga dai
ba komai ne a dakin gauro ba daga kati
fa sai jakar kaya” inji maryam. Nace
mata to shi wannan ba haka yake ba
domin shi abubuwa sunyi yawa a dakim
nasa domin harda wani abu na gani ma a
rufe da wani zane, haka nake gayawa
maryam a lokacin, ita kuwa kin ganta
nan da karan bani tana jin haka naga ta
mike.
Nake tambaya ina zata tace wai dakin ya
yazeed, wai in taso muje tunda baya
gida nace mata wallahi ni bazan je ba
kuma kema ban goyi bayan kije ba idan
kika je duk abinda ya same ki toh ni ba
ruwa na, tace ita dai wai yasin sai taje ta
bincike dakin taga wai miye da yazeed
baya san a shiga.
Ai kuwa kamar wasa maryam ta nufi
dakin ya yazeed ni kuwa kallo ya dauke
min hankali ban kula ba har ta bude
dakin ta shige ba tare da fargabar komai
ba domin nace da ita baya nan. Nidai ina
nan sai kallo na nake nama manta da
maryam ta shiga dakin, ita kuwa
bincike-bincike ta hau yi chan ta hango
laptop dinsa, ai kuwa taci sa'a ba
password a jiki, haka ta haye mai kan
gado tana ta danne-danne abinta.
Ganin shiru-shiru maryam bata fito ba
yasani tashi na bita, abin mamaki a kan
katifa na ganta da kwamfuta sai wangale
baki take bata ma ko kula da na shigo
ba, hakan yasa naje da sauri ke maryam
wai me kike yi ne haka, kinzo kin wani
zauna a dakin mutum bayan kinsan idan
ya dawo ya tarar dake sai ya wulakanta
ki gashi kuma kinsan mama bata nan
wallahi duka zai miki. Yayin da nake
karasa wa wajanta ta dago min wani
hoto dake jikin laptop din, yazeed ne
cikin wasu jajayen kaya, fuskan sa duk
ya shafe ta da wasu zanuka.
Nan muka yada zango a kan gadonsa
muke ta kallan hotunansu shida wadan
su abokan sa, mun kusan share minti 30
muna kallan hotunan amma bamuga
karshen su ba haka yasa muka koma
wani bangaran. Da nace aje videos
amma Maryam taki yadda, haka yasa na
kyale ta badan naso ba ta kamo games
nan ma mukata bugawa, ni dai na nace a
kan sai an shiga videos nashi, “ kin cika
naci da yawa wallahi ke da almajira ce
da masu masu sun shiga uku wallahi,
bari a shiga videos din"
Mu kam sai shagalin mu muke yi ba
ruwan mu mun ma manta da a dakin wa
muke. Nan maryam ta nufi kan videos ni
kam nayi mamakin yanda ta iya
computer haka ma domin nasan bata da
ita, hakan yasa na tambaye ta a ina ta
koya tace a laptop din yaya deeni mana,
ta shiga bude videos, video farko ya
ruda mu gaba daya jikin mu ya fara
rawa a tare tuni muka kankame juna
domin kuwa abinda muka gani ne yafi
karfin tunanin mu.
Anne tayi zugum ta saki baki sai
sauraren labari take yi, gani tayi halema
na waige-waige saida taga ba kowa
sannan ta yi kasa kasa da murya sosai
sannan take cewa “anny wallahi in gaya
miki annesah yazeed ne a videon ya rike
wuka yana yanka mutum, kuma dan yaro
gashi nan jage-jage duk jini shi kuwa
sai yanka sasan jikin wannan yaran
yake, yaro ne fa dan shekara baifi 7 ba.
Ganin haka ya firgita mu da gudu muka
tashi a tare ni da maryam da niyar muyo
waje ko laptop din bamu wani tsaya
kashewa ba, abin mamaki ina kama
kofar yazeed shima ya turo da niyar zai
shigo.
Karki so kiga yanda mukayi baya a wani
firgice ni kam bansan lokacin da na
shiga basa hakuri bama, maryam kam
tuni ta fara kuka, shi kam da ya shigo
tsayawa yayi chak ya kare wa dakin
kallo yaga duk an bincike mar daki can
ya hango laptop dinsa a kunne tana
kallo. Daga jin sautin video ya gane ko
wannene, haka yasa shi kulle dakin da
mukulli ya koma can gefan katifarsa ya
jawo computer ya kashe tukun,ya hada
hannuwa biyu ya dora a goshi alamun
yana tunani kenan..
Anne in takaice miki labari wallahi ranar
mun daku domin samun mu yayi kamar
yayan sa ya dinga lafta yana fadin zaku
kara, muna kuka muna a’a, saida yayi
mana dukan tsiya sannan yace muyi
shiru, ya zazzare mana ido tare da cewa
wallahi muka sake muka kuskura
wannan maganar ta fita duk sai ya kashe
mu. Hakika mun tsorata ba yanda muka
iya haka ya bude mana kofar muka dawo
falo muka sha kukan mu. Kinga zancen
nan dana fada miki ko to wallahi ba
wanda na fadawa ko ummana da abbana
basu sani ba domin nasan wannan
mugun zai iya aikata komai, Halima da
tazo nan ta juya ga maryam, “ke ko kin
taba gaya wa wani”, “ni nama isa” inji
maryam. Ai tun lokacin na kama baki na
nayi shiru gidama da naje mama tayi
kokarin gane miye ya same ni amma
naki fada mata nace ba komai. Anne ta
rike baki tare da girgiza kai chabb!!
Wallahi idan nice sai na tona asirin sa a
kan me, ke rufawa kanki asiri idan kika
fada akaje kuma ba'a kama sa da hujja
ba ya zaki ce? Jikin anne yadan yi sanyi,
kinga ba muda mafita ne, kawai kedai ki
bari rana dubu ta barawo rana daya ta
mai kaya ko ba haka bane? Haka ne inji
anne sannan ta mike “matar yaya zo ki
dan rakani mana” inji anne take fada
mawa maryam, maryam ta mike tare da
cewa ina? “Dakin yazeed mana da sauri
maryam ta koma ta zauna tare da cewa
ba dani ba, ai kuwa duk suka kyalkyace
da dariya.
*******************
Deeni kuwa yana can sai fargaba yake,
shi kam yama rasa me ke mai dadi
domin yasan jinkirinsa nada mummunan
hatsari indai har yazeed ya samu damar
tafiya da abban sa wancan gidan tabbas
akwai matsala, domin kuwa dodansu
za'a bawa shi, gashi yayiwa yan sandan
nan bayani amma ina sunki sauraran sa
wai kawai basu yarda dashi ba muna fiki
ne. Shigowar DPO ce ta dansa zuciyar sa
ta danyi sanyi........
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 39
Share ThCan yaji shigowar DPO hakan tasa ya
sami yar natsuwa, saida suka yiwa DPO
din bayani tukwanan ya nufi wajan
deeni, shi kuwa dama kamar shi yake
jira, yana isa deeni ya gaida shi ya amsa
tare da karewa deeni kallo, “kai gaskiya
wannan ba mugu bane” haka ya fada a
zuciyar sa tare da zuwa gab da deeni ya
tsuguna a cikin cell din, " kalle ni nan
ina so ka fada min gaskiya who ar u?
Deeni da hawaye tuni sun cika mar ido
ya fara bayani sunana zahradeen kaza
da kaza dai ya fada mai kaff labarin sa
har mutuwan halima, dama tserowar sa.
DPO ya yi wani ajiyar zuciya sannan
yayiwa deeni wani kalan kallo yace “ka
tabbata?” eh na tabbata, ban maka
karya ba, ok yanzu kace yazeed ya
bayar da mahaifin sa? kwarai da gaske
kuma yallabai jinkirin mu ma ba
karamin hatsari bane ya kamata muje ka
tabbata da kanka.
Bai gardama ba yace a kunce deeni,
wani kurtun dan sanda ne yaje ya cire
mai ankwar dake sanye a hannunsa,
sannan DPO din ya dauki mutum 4 daga
cikin yaransa tare da shi da kuma deeni
suka hau mota kai tsaye suka nufi gidan
su haleema, shikam deeni godewa Allah
yake yayi da DPO nan ya fahimce shi, a
zuciyar sa da yana tunanin ko DPO in
mugune amma yanzu kam yaga sabanin
haka..
***************
Yazeeed kuwa yana fita daga falo ya
nufi gun da su abbansa suke a zaune, su
uku ne suna hira, da baban sa da kuma
wan babansa sai kuma baban aliyu wato
kawu. haka yaje cikin ladabi (kunsan
ance mai san kayan ka yafika dabara)
yaje ya sami abbansa yace dad na
shirya, “ok mu tafi kenan” a cewar
abban nasa, yauwa ai kuwa ina ganin
gwara kawai mu tafi mu duka tunda
kaga wadannan suma iyayan ka ne ya
nuna su kawu, lokaci daya yazeed ya
bata fuska yaji ana shirin bata mai shiri,
a’a dady kawai gwara dai mu tafi mu
biyun kasan mai gidan nawa bai cika san
hayaniya da yawa ba, abban haleema ne
ya kalle sa tare da yimai dakuwa uku
“nace wato mune zamu mai hayaniyan
ko, to dai mu nan duk iyayan kane kaji
na gaya maka” sunkuyar dakai kawai
yayi. Wayar alhaji sanusi ce tayi kara
ganin wanda yakira ne yace to ni ga ma
kira ya shigo wayana kuje kawai domin
wani abokin kasuwanci nane kuma zamu
dade muna waya, alhaji bashir ya tashi
yana murmushi to ai shikenan

Please Login or Register in order to submit comment