Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga zuwa gidan ka na nemi zobe narasa ina bazai yiwu ba afito min da zobena kawai" tak'arasa zancen tana hararar Kausar,Kausar kuwa tuni tafara nadamar d'auke mata zobenta,Khalid kasa magana yayi yana mamakin ya akayi zoben Habiba ya bata,kwalla masa kira su babangida sukayi da mai suke jirana suna bata musu lokaci,jiki asanyaye ya nufi Palo yaje yagaya musu abinda ke faruwa,Fahad mijin Habiba mamaki ne yarufeshi ya k'wallawa Habiba kira tafito ya tambayeta abinda yafaru takara kora masa jawabi,Khalid hakuri yabata yace bari su kara dubawa ko zasu gani,yana shiga d'akin yaga Kausar sai dube dube take tana had'a gumi shima tuni yaji yafara zarginta dan yanayinta yanuna bata da gaskiya,fita yayi daga d'akin Yakoma palo yana cewa Habiba anya kuwa tazo da zoben gidanan"a "fusace Habiba tafara magana " wlh Nazi dashi gidanan agaban amaryarka ma nacire zoben nasa ajaka lokacin su badariyya suna sallah,kaga Khalid babu wani batun boye boye Amaryarka ce ta d'auke min zobe kace mata tabani zobena kawai" Khalid kasa magana yayi yana kallon Habiba dan yarasa tacewa Fahad kuwa yana ganin haka yacewa Habiba ta wuce sutafi careless ness d'inta ne yasa tarasa zobenta,Kausar kuwa data tsaya daga bakin k'ofa dafe k'irji tayi tace yazata ce ita ta d'aukar mata zobe, wani mugun ashar Habiba ta dura mata tace wlh itace ta d'auke mata tafito mata da zobenta kawai "ganin da Fahad yayi inya bar Habiba haka zata yi ta rashin mutunci ga Khalid yakasa magana kuma yanajin kunyar Khalid, tsawa ya dakawa Habiba yace ta wuce su tafi,Habiba tak'i sai daya nuna mata zai sassab'a mata tayi waje tana Allah ya isa taringa cewa Kausar B??R??UNIY??R ??M??RY??,


Fahad hakuri yabawa Khalid yace yashareta ta yar da zoben ne awani wajen batasani ba yabawa Kausar hak'uri,su babangida ma hakuri suka bawa Khalid da Kausar dake ta kuka sukayi waje,Khalid rakasu yayi har bakin mota,Kausar tana ganin sun fita tayi sauri taciro zoben daga breziyarta ta bude drawern mudubinta ta jefa shi aciki,Khalid kuwa rai abace ya dawo ya wuce Kausar dake zaune apalo tayi tagumi tana goge hawayen munafirci,d'akinta ya wuce direct yafara hargitso da kayan ta Kausar kuwa ta tsaya tana kallonsa cikin tashin hankali,tambayarsa tayi ya yard a kenan ta dau zoben,ko kallonta baiyi ba ya cigaba da birkita kayanta,ba Inda bai duba ba har akwatunanta ya sauko dashi, gaban Kausar inbanda fad'uwa babu abinda yake jikinta sai rawa yake, duk karatun dayazo bakinta sai ta karanta,ganin ya nufi gaban mudubi cikinta yayi wani irin murdawa dasauri tasha gabansa tace yanzu ya yarda zata iya sata, tureta yayi daga gabansa dan ransa ya masifar back,haka kawai ya yarda Kausar ce ta d'au zoben,drawern janyo yafara hargitsawa aikuwa sai ga zoben,d'auko zoben yayi ya juya yana kallon Kausar.
[7/11, 8:19 PM] Sadnaf: ????????????????????????????
B??R??UNIY??R
??M??RY??
????‍♀

N??
*SADNAF*????
*&*
*ʍʀs ʄaաաaʐ*??

®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


Dedicated to all Readers of B'??R??UNIY??R ??M??RY??


Page 60-70

??



"Zoben waye wanan Kausar " ?

Khalid yace ransa a mutukar b'ace yana nufarta,



Kausar d'ora hannu tayi aka tana ja da baya dan da akwai yanda zata iya hak'a rami ta binne kanta da ta binne kanta wanan abun kunya da mai yayi kama,



"Tambayarki nake kibani amsa kafin na k'wada miki mari" Khalid yace a tsawace,



Kausar durkusawa tayi agabansa tace,


"Khalid kayi hak'uri wlh ba halina bane sharrin shaidan ne narasa yanda zanyi nasamu kud'i na biya basukan dake kaina dan Allah ka rufa min asiri" wani wulak'antacen kallo ya ringa mata can yafara magana,



"Kausar dama Ashe ke B'??R??UNIY?? ce bansani ba?,Kausar kinsan yanda na tsani mai halin b'era kuwa? namiji ma ya yak'are ballantana mace, mai kika nema kika rasa Kausar in badan rashin godiyar Allah irin naki ba,wane irin bashi kika ci da bazaki gayamin inbaki kud'i ki biya koda banida shi ko ranta ne Kausar sai nayi da ki kunyatani agaban abokaina yanzu dawane ido kike san suringa kallona,sun San kece kika d'au zoben,gaskiyar Aunty zulaihat datace ke kika d'auke mata zobe Ashe shiyasa kika bi kika rud'e dakikaji zata zo, , kafin ki mata kikayi a saloon Kausar wanan wane irin masifa ne ahaka in aka ganki kamar bazaki aikata ba,nagode wa Allah daya nuna min halinki tun wuri dan nasan kunyar da zaki sani naji nan gaba sai yafi Wanda naji yau dan haka Kausar wlh duk San da nake miki hak'ura zanyi dake dan wlh bazan iya zama da B'??R??UNIY?? ba, dan haka ki tafi gidanku idan kin gyara halinki na dawo dake," Kausar kuka ta fashe dashi tana


"Khalid karka yimin haka wlh Sharrin shaidan ne bansan ya akayi nake sata ba yanzu inkace natafi gida Khalid ka tona min asiri sati biyu da aure aga nakoma gida,tsaki yayi yabarta awajen yace kar yadawo ya sameta bazai iya zama da b'arauniya ba,kuka Kausar taringayi sosai tana nadamar d'aukewa Habiba zobe yanzu wane riba taci daya wuce shan kunya ga aurenta na rawa, Khalid k'ara dawowa yayi da mukullin mota ahannu yace tazo ta fita zai kulle gida dan zai mayarwa da Habiba zobenta,ba irin rok'on da Kausar bata masa ba yak'i sai daya ga ta d'auko hijabinta yayi waje ,itama tafito tana kallonsa kamar ba Khalid mai k'aunarta ba dan yanzu ita k'iyayyarta ta hango k'arara a idonsa,motarsa yaja yabarta a tsaye.



Kausar data isa gida kuka take sosai inda hankalin Hajjo ya tashi ba irin tambayar da bata mata ba akan ta gaya mata mai yafaru tak'i akarshe yayanta ta k'ira Murtala yazo shima yana tambayarta fir tak'i tagaya masa,Hajjo sa Murtala tayi ya kira Khalid awaya suji lafiya,Murtala yabi shawararta ya kira Khalid bayan sun gaisa yake cemasa sun ga Kausar ta dawo gida ko lafiya,ce masa yayi maganar bata waya bace zai zo gida ya samesu ya katse wayar,bayani yayiwa Hajjo abinda Khalid yace taringa sallati tana mai yafaru haka sati biyu da aure Allah yasa dai Kausar ba wani gagarumin Abu tayi ba.




Khalid kuwa dayaje gidan Fahad bai sameshi ba, Habiba yasamu a zaune a Palo sai cika take tana batsewa dan fad'a sukayi sosai da Fahad dan dagewa tayi ita fa Kausar ta biyata zobenta ko Khalid ya biyata sai da Fahad ya mata kaca kaca tukuna yabar mata gidan,tana ganin Khalid taja tsaki,hakan datayi kuwa ya masifar k'ona mishi rai,matar datake masifar girmama shi sai gashi Kausar ta janyo mishi raini agurinta,mik'a mata zoben yayi yace mata bayan sun tafi suka d'aga karkashin gado suka gani,dasauri ta amshe tana murna shikuma yajuya dan yatafi bud'ar bakin Habiba sai cewa tayi,


"Danji naji amma ban yarda akarkashin gado aka gani ba kai dai bakayi dace mata ba,ga k'yau amma ba hali", bai ce mata komai ba yafice zuciyarsa na tafasa da bacin ran abinda Habiba tayi masa yanufi gidansu Kausar tana can a kunshe a d'aki tana ta kuka,sallamarsa dataji ne yasa ta Mik'e ta zauna ta dafe k'irjinta dan tasan yau Hajjo sai ta kusa kasheta da duka intaji abinda tayi,Hajjo tabarma ta shimfid'a masa ya zauna bayan sun gaisa ya gaya mata abunda Kausar tayi masa, sallati Hajjo taringayi tana tafa hannu tana tunanin anya kausar ita kad'ai ce batada aljanu masu sata, sata hak'uri tabawa Khalid tace dan Allah kar dan haka yafaru yace zai saketa tana tunanin Kausar Aljannu ne ajikinta dasuke sata sata zata sa mallami yamata ruk'iya jikin Khalid ne yayi sanyi daya tuna fa kad'an da aikin aljannu,cemata yayi babu komai zai dawo yaji mai mallamin yace,sallama ya mata ya tafi,Kausar dake d'aki sai kuka take data ga yatafi baice akirata ba,Hajjo zuwa tayi ta sameta tace mai yakai ta sata Ashe har yanzu bata daina sata ba,fad'a sosai Hajjo taringayi uwa ta ari baki Kausar ita dai sai kukanta take tana nadamar abinda ta aikata.



Washegari wajen wani babban mallami Hajjo takai Kausar tace ya dubata ko tana da Aljannu,Mallamin kuwa dayayi yan adduoinsa yace Kausar bata da wani aljannu San zuciya ne kawai da tariga tasaba tun tana karama sai andage mata da adduar Allah ya shiryata,itama a matsayinta na mahaifiyata ta Dage da addua,ahaka suka koma gida Hajjo ta dage da adduar Allah Ya shurya Kausar taku ma sa ana tayata yiwa Kausar addua,kullum sai anyo mata rubutu tasha.



Khalid kuwa tunda yabar gidansu Kausar ya kira Hajiya zulaihat yaga mata abinda Kausar tayi masa, amadadin Hajiya zulaihat taji haushin Kausar tausayinta ne yarufeta dan tana tunanin Kausar ba ita kad'ai bace,hak'uri tabawa Khalid akan ya maida Kausar tana tunanin ba yin kanta bane Aljanu ne da ita,yadage ya ringa taya Kausar addua,da wanan shawarar da hajiya zulaihat tabawa Khalid zuciyarsa tayi sanyi,amma dayake Khalid yanada zuciya da ruk'o yakasa manta abinda Kausar tayi masa, sai da Kausar tayi wata d'aya a gida yaje gidansu ya d'aukota Kausar tabi tayi baki ta rame kullum cikin kuka take da nadamar abinda tayi.


Tunda ta koma Khalid yake k'afa k'afa da ita indai zai kwanta bacci sai yayi pillo da kud'insa Wanda hakan kesa Kausar kuka sosai dan yanzu Khalid baya baya yakeyi da ita baya sakin jiki da ita,ko waje zasuje sai yaja mata kunne akan karfa tayi d'an halin.



ALLAH MAJI ROK'O


shekara d'aya kenan da Auren Kausar bata k'ara sata ba tun zoben Habiba data sata, dan Khalid babu irin gwajin da bai mata ba dan yaga ko har yanzu inta ga Abu zata d'auke da gangan zai ajiye kud'i yanda ya ajiye haka yake zuwa yasamu abunsa,gwaji iri iri yamata amma Ina ba Kausar d'in data sani bace a da,dan ALLAH SAMIU DUA NE MAJI ROK'ON BAWANSA MAI KUMA SHIRYA BAWANSA A DUK LOKACIN DAYASO.


Khalid kuwa bak'aramin murna yayi da canzawarta ba ahaka zamansu Yakoma normal,Kausar duk lokacin data tuna irin b'arnar datayi kunya kan kamata dan kwanaki ta had'u da Aunty Oke a hanya bud'ar bakinta sai cewa tayi B'??R??UNIY??R ??M??RY?? dafatan ka daina sata dan sata ba cyau,aranar bak'aramin kunya kausar tasha ba da kuka ta dawo gida tana ta data sanin abinda tayi abaya.





Whuuuuuuuh Readers Allah yarabamu da San zuciya irin na Kausar masu hali irin nata Allah ya shiryesu Allah ya shiryemu gabaki d'aya bisa tafarkin addinin musulunci kuskuren da mukayi a wanan novel d'in Allah ya yafe mana anan muka kawo karshen wanan novel mai tak'en B'??R??UNIY??R ??M??RY??.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment