Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya na kula da k'annai na.""To, Kina da wata sana'a ne da kike yi Aunty?."Uhum! A'a bana yin komai, 'Yan kud'in da muka d'an samu ne wajen jinyar Umma kafin rasuwar ta shine nake amfani dashi kafin in nemi aikin yi."Khairat hawaye ne suka zubo mata, Safna tayi saurin share mata hawayen."Haba... Ke kuwa! Idan kina mana kuka ai zakisa na karaya, Kuma a hakan ma aimu munajin dad'i, Idan kikayi la'akari da yanayin da ake ciki."Safna ta fad'i haka cike da bama zuciyar ta k'warin gwiwa.Khairat hannu tasa ta share hawayen ta, Ta maida kallon ta akan Rumaisa dake zaune tare Anisah suna kallon ta."Haka ne..., Bai kamata na zubar maku da hawaye ba, Sai dai tare da Yaya Fauzan nake suna k'ofar gida suna jiran ki."Safna bata rai tayi tare da mik'ewa tsaye, Ganin haka yasa Khairat itama ta tashi tsaye tana kallon Safna."Auntyn mu, Lafiya?.""Kiyi hak'uri Khairat, Bazan iya ganin Yayan ki ba.""Haba Auntyn mu, Ko yayi laifi ne?."Nan take idanun Safna suka ciko da hawaye, Tayi saurin juyawa don kada Khairat ta lura da hakan.Safna d'aki ta shige ta d'auki hijab d'inta ba tare da ta cewa Khairat komai ba, Ta fito ta sanya zata fita Rumaisa tayi saurin cewa."Yawwa, Aunty Safna kafin Umma ta rasu tace kiyi k'ok'ari ki cika mata burin ta."Da sauri Safna ta juyo ta kalli Rumaisa sannan ta kalli Khairat, Safna dawowa tayi ta zauna kusa da Rumaisa."Wane irin buri ne wannan Rumaisa?."Cewar Safna"Tace don Allah ki tabbatar auren nan ya yuwu."Safna saurin kallon Khairat tayi ganin sun had'a ido ne yasa ta d'an sakar mata murmushin k'arfin hali, Sannan ta tashi ta wuce.Safna a zaure ta tsaya ' jikin bango ta jinginar da kanta tana tunanin yadda komai ya juya mata."Insha Allah zan kasance mai biyayya a gare ki ko a bayan ranki ne."Safna ta fad'i haka.Nan ta fita ta k'arasa inda motar su take ta tsaya."Here she comes... Bari na baku guri, And please Aboki kayi abinda ya dace.""Oh come on... You can't tell me what to do!."Cewar Mr-Fauzan."Daga baya kenan dai!."Hafiz ya fad'i haka tare da bud'e motar ya fita, Nan yayiwa Safna ta'aziyya sannan ta zagaya ta bud'e front seat ta zaune gamida ta rufe motar."Ina kwana?."Cewar Safna."Lafiya! Ya k'arin hak'uri?.""Alhamdulillah.""Allah yai mata gafara."Ameen Safna tace, Sannan sukayi shuru na d'an lokaci."Am... Safna...Am..."Safna ita dai ido kawai ta zuba mashi, Tana jiran abinsa zai fito daga bakin shi."Am here to apologize... Safna..."Safna sunkuyar da kai tayi tana sauraron shi."Inason ki manta da duk wani abu da ya faru mara dad'i tsakanin mu."D'ago manyan idanun ta tayi wad'an da sukayi ja ta kalleshi, Hawaye cike a idanun, Phalanges d'inta d'aya kan d'aya."I know that I hurts you several times with my words..."Mr-Fauzan ya fad'i haka in a husky voice."I really regret what I did to you..."Ya fad'i haka With sounds of sympathy tare da dunk'ule hannun shi.Safna d'agowa tayi ta jinginar da kanta jikin seat d'ingami da share hawayen fuskar ba tare da tace mashik'ala ba.Mr-Fauzan harya kai hannun shi zai janyo nata hannun ' sai kuma ya fasa."You totally changed everything in me Safna... Nasanmeye tausayi duk ta dalilinki."Safna juyowa tayi cikin mamaki take kallon cikin idanun shi, A zuciyar ta tace."Anya wannan shine Fauzan d'in da na sani kuwa?.""Surprise right? Yes Safna... Ni d'inne dai Fauzan."Ya fad'i haka tare da janyo hannun ta ya dunk'ule cikin nashi."Please Safna... Will you marry me? Zaki aure ni?."Mr-Fauzan ya fad'i haka.Safna sunkuyar da kai tayi bakin ta yayi mata nauyi, Kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon hannun shi dake saman nata."Bazan ta kura ki ba, Kuma bazan matsa miki ba, Amma inaso ki amince muyi auren nan Safna... Da yardar ki za'ayi komai.""Babu abinda zai cenja akan maganar auren, Na amince."Cewar Safna."Alhamdulillah,And I promise you that ' zan baka duk wani abinda kike buk'ata na rayuwa."Mr-Fauzan ya furta haka da murmushi akan lips d'inshi.Safna zame hannun ta tayi gamida cewa."Ni zan koma cikin gida.""No wait... Ai ban gama magana ba, Inason ki fad'awa Khairat k'anwata duk abinda kike buk'ata a yanzu."Cewar Mr-Fauzan."A'a, Babu abinda nake buk'ata.""Okay then..."Ya fad'a tare da d'aga wani abu ya ciro kud'i masu yawa ya mik'a mata."Take this, Ki d'an fara rage abinda kike buk'ata na biki.""A'a don Allah ka barshi, Ni a yanzu bana buk'atar komai illa kwanciyan hankali.""Yes, I know that... But ki daure ki ansa wannan, Don't you think zaku buk'aci kud'i na hidiman biki?."Cewar Mr-Fauzan.Safna hannu tasa ta ansa kud'in tare da yimashi godiya, Sannan ta bud'e motar ta fita.Bayan wucewar tane Hafiz ya nufi wajen Fauzan.Hafiz motar ya bud'e ya shiga, Ganin fuskar Mr-Fauzan cikin fara'a ne yasa Hafiz cewa."Tofa! Allah yasa dai bakayi abinda zai dagula komai ba, Don nasan halinka.""I totally changed, Hafiz ' duk ta cenja ni wallahi... I truly love Safna with all my heart, Bansani ba ko asiritaimun cikin k'ank'anin lokaci.""Alhamdulillah,And did you tell her that you love her?.""I haven't... But na nuna mata hakan da baki na... Hafiz bansan nayi iya tausasa murya ba sai yau."Hafiz tsayawa yayi yana kallon shi at the same time yana dariya."Fauzan please be a man mana! Duk kabi ka wani rud'e... Mu dai ka saisaita kanka don driving zakayi yanzu."Nan dukkansu suka hau dariya cike da farinciki.B'angaren Safna, Shigar ta cikin gida ta iske Khairat zaune a inda ta barta tana hira dasu Rumaisa.Safna waje ta samu ta zauna, Ta sauke ajiyar zuciya."Auntyn mu har kin gama?."Cewar Khairat."Eh, Na gama ke kawai suke jira.""To amma Auntyn mu, Zaman nan naku ku d'ai is very risk fa akwai had'ari, Don Allah ku koma wajen 'yan uwa mana."Khairat ta fad'i haka cike da nuna damuwa."To ai Khairat jibi ne fa auren dududu bai wuce mu k'ara kwana d'aya anan ba, Su kuma k'an naina wajen dangin Baba zasu koma."Khairat numfasawa tayi ta mik'e tare da cewa."Indai akwai matsala kawai ki fad'a mana, Babu abinda zai gagara kinji Auntyn mu."Safna kai kawai ta d'aga ma Khairat, Sannan ta tashita raka ta har k'ofar gida tukunna ta koma cikin gida.*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVEL.**50-51**Around 4:00pm*Bayan Mr-Fauzan ya maida Hafiz gidane
' tukunna ya koma gida ya aje Khairat, Sannan ya juya zuwa company.Khairat ko data shiga ciki, Iske Mummy tayi a main parlor zaune sanye da medicated glass a idanun ta tana filling out wasu takaddu.Da sallama Khairat ta k'arasa inda Mummy take ta zauna."Har kun dawo?."Cewar Mummy."Eh wallahi Mom.""Ina shi Fauzan d'in?."Mummy tayi tambayar kanta akan takaddun da take filling."Aje ni kawai yayi ya juya wai he got many things to do."To kawai Mummy tace, Sannan Khairat ta tashi zata wuce side d'in ta Mummy ta tsaida ita."Khairat?."Cewar Mummy.Khairat dawowa tayi ta zauna tare da cewa."Na'am.""Ya ita yarinyar?.""Oh Aunty Safna? Lafiyar ta k'alau, Amma saidai Mummy suna da buk'atar taimako sosai ' gaskiya natausaya musu."Jin hakan yasa Mummy cire glass d'in da ke idon ta."Kar dai Fauzan dangin talakawa ya nemo!."Cewar Mummy."Haba Mummy don Allah."Khairat ta fad'i haka.Khairat tashi tayi gami da bubbuga k'afa da gunguni ta wuce side d'inta.Mummy k'wafa tayi ta cigaba da abinda takeyi.B'angaren Hafiz, Tunda ya koma gida ya kwanta yake bacci abinshi.Aleeza kuwa safa da marwa kawai takeyi bata d'aki bata parlor.Hajia ce ta shigo cikin parlon ta iske Aleeza tsaye tamkar wacce ke jiran tsammani, Kwalliya kuwa tamkar wata amarya ' fannin ado kam ba'a magana."Auta?."Cewar Hajia.Aleeza dake fuskantar window, Juyowa tayi ta kalli Hajia."Na'am.""Akwai wanda kike jira ne?."Hajiya tayi tambayar.Aleeza waje ta samu ta zauna, Sannan tace."Hajiya dama, Wannan Doctor d'inne yace zaizo mu gaisa, Shine naji shi shuru."Ta fad'a tare da nuna damuwa."Wane Doctor kenan?.""Hajia, Doctor Khalil mana... Wanda ya duba ni.""Ohwoo... Allah sarki, To ki sake bashi lokaci mana, K'ila akwai abinda ya tsayar dashi ne."Abinda Hajia tace kenan ta mik'e zata koma part d'inta Aleeza taji k'arar bud'e gate.Hakan yasa tayi saurin tashi taje wajen window domin dubawa."Shine..."Aleeza ta fad'i haka tare da kama hanya zata fita, Hajia tayi saurin dakatar da ita."Ke Auta! Meye haka? Bazaki aji ba?.""Hajia zanje na taroshi ne fa."Hajiya zaunar da Aleeza tayi ta fad'a mata yadda akeyi, Sannan Hajiya ta wuce part d'inta.Koda Dr-Khalil yayi parking motar shi ya fito, Sai da yayi 5minutes a tsaye a wajen banda missed calls da ya dunga yiwa Aleeza.Aleeza saida taja aji tukunna ta fito garage ta nufi inda Dr-Khalil ya tsaya jiranta.Aleeza sanye take da wata had'ad'd'iyar gown blue ' kanta kuwa rufe yake da blue tie sai kuma high hill bak'i a k'afar ta.Bayan ta isa gare shine taimashi sallama, Dr-Khalil d'ago kai yayi ya kalle ta."Ya Salaam!."Abinda Dr-Khalil ya furta kenan yana k'arewa surar jikin Aleeza kallo."Baza ka ansa sallamar tawa ba?."Cewar Aleeza.Nan Dr-Khalil ya amsa sallamar but still idanun shi na kan fuskarta."Mu shiga daga ciki ko?."Aleeza ta fad'i haka.Haka suka nufi cikin gida suna taku.Bayan shigar su parlor ne, Aleeza ta umurce shi daya zauna ita kuma ta wuce kitchen ta d'auko drinks ta kawo mashi, Sannan ta koma ta zauna.Haka suka sha firar su Dr-khalil yana yi yana kora drink a baki.*35minutes later...*Bayan sun gama hirar tasu ne Dr-khalil ya tashi domin yin haramar komawa, Haka Aleeza ta tashi itama suka fito harabar garage suka tsaya inda yayi parking motar."Let's get in ' ko?."Cewar Dr-Khalil."Okay."Aleeza ta fad'a sannan suka shige cikin mota.Bayan shigar sune Dr-Khalil yaja dogon numfashi yace."Na gode da tarba mai kyau Aleeza.""Anytime..."Ta furta a tak'aice cikin fara'a.Nan Dr-Khalil yasa hannu a aljihu ya ciro d'an k'aramin box ya mik'a mata."Please take it."Aleeza kai ta girgiza mashi alaman a'a."I said please... Ba don ni ba."Ya fad'i haka with sounds of pleading.Aleeza karb'a tayi ta tsaya tana kallon box d'in."Open it."Dr-Khalil ya fad'a.Aleeza bud'ewa tayi taga necklace fari mai hasken diamond."Wow..."Ta furta a hankali."I love you Aleeza..."Jin maganar tayi ta doshi cikin k'wak'walwar ta tayi saurin kallon shi."Yes Aleeza, Ki amince dani."Aleeza harta bud'e baki zata yi magana sai kuma ta tuna da maganar Hajia, Cewan ta dunga jan aji."Thank you for the splendid visit..."Abinda ta fad'i kenan ta bud'e motar ta koma cikin gida cikin sauri.Dr-Khalil ajiyar zuciya yayi tare da yin k'wafa yace."Zaki shigo hannu."Nan ya tada motar shi ya wuce.Aleeza tana tsaye wajen window tana kallon shi wucewar, Ganin ya tafi ne yasa ta buga uban tsalle cike da farin ciki ' ta fara rawa."Rawa da girgiza... Zanyi gaban ka in jujjuya! Zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyy..."Bata kaiga k'arasa wak'ar ba taji kamar motsin Hafizzai shigo cikin parlon.Hakan yasa Aleeza tayi saurin hayewa sama ta nufi d'akin ta.Aleeza koda ta isa cikin d'akin k'arar shigowar text taji cikin wayar ta.Hakan yasa tayi saurin d'aukar wayar ta duba, GaninDr-Khalil ne yasa tayi smiling."Ina sonki Aleeza, Ki amince da soyayya ta ' ke kad'ai nake buk'ata a halin yanzu."Aleeza wurgi tayi da wayar saman gado, Ta haye gadon Tare da rungume pillow tana sakin murmushi mai d'auke da sak'onni iri iri.*** *** *** *** *** *** *** *** *** ****2DAYS LATER...*```YAU TAKE SATURDAY, RANAR BIKI...```Gidan su Safna cike yake da mutane, Gaggo Mariya da dangin Mahaifin su Safna ne keta hidima cikin gidan.Duk da dai dangin mahaifin nata d'aid'aiku ne suka zo, Amma Safna tayi farin ciki matuk'a.Safna zaune take a k'ofar d'aki anayi mata lalle mai kyau.Goggo Mariya ce tazo inda Safna take ta zaune."Ke kuwa mai lalle kiyi sauri fa, Domin nan *1:00pm*za'a d'aura auren kuma yanzu gashi *12:00pm*."Goggo Mariya ta fad'i hakane tana yiwa Safna murmushi.Safna kuwa kunya ce ta rufe ta yasa ta sunkuyar da kanta tana murmushi."Safna?."Cewar Goggo Mariya.Safna kai ta d'ago ta kalle ta tare da cewa."Na'am.""Safna, Na yarda zan rik'e su Rumaisa kinji ko?."Safna waro idanu tayi cike da farin ciki."Alhamdulillah,Goggo Mariya na gode sosai ' gaskiya bamu da kamar ki."Safna ta fad'i haka tamkar zatayi kuka."Haba.... Yo idan ban rik'e ku ba waye zai rik'e ku?."Goggo Mariya ta fad'i haka gamida tashi ta koma wajen girkin da suke yi.Suna cikin hakane wani yaro ya shigo cikin gida."Wai ance ana kiran Safna."Abinda yaron nan yace kenan ya juya yayi gaba abinsa."Kinga bar lallen nan, Bara naje na duba wanene..."Cewar Safna.Safna tashi tayi ta fita, Ganin Sir-Kamal tayi a tsaye jikin motar shi.Haka Safna ta k'arasa wajen shi da d'anyen lalle a hannun ta tare dayin sallama ' ya amsa."Naga kamar kuna hidima ne."Safna murmushi tayi ta sunkuyar da kai."Eh, Kayi hak'uri bansami damar fad'a maka ba...""Me kenan.""Aure zanyi..."Ta fad'a a tak'aice.Sir-Kamal shock yaji at the same time kanshi ya d'aure.Wani irin tafasa zuciyar shi keyi idan da zaku lura dafuskar shi jijiyoyin shi duk sun tashi.Sir-Kamal dakyar ya iya bud'e bakin shi yace."Amma... ina taya ki murna Safna, Wane ne ne Angon?.""Ogan ka Fauzan."Cikin mamaki Sir-Kamal ya tsaya yana kallon ta."Am... Safna dama kawai nazo duba ki da lafiyar ki ne, Ni yanzu zan koma."Ya fad'i haka tare da bud'e motar shi zai shiga."Am... A babban masallacin juma'a za'a d'aura auren, Ina gayyatar ka."Safna ta fad'i haka cike da nuna farin ciki."To! Na gode."Ya fad'i gamida shigewa cikin motar shi yaja ya wuce.Safna komawa gida tayi ta zauna aka idasa lallen, Sannan ta aka kai mata ruwan wankan ta ban d'aki.B'angaren Mr-Fauzan kuwa, Gidan nasu shima mak'il yake da jama'a.Cikin garage kuwa cike yake da Abokan Ango, Da kuma Abokan Daddy.Mr-Fauzan ne ya iso cikin garage d'in cikin manyan kaya ' Hafiz yazo ya tareshi suka k'arasa cikin mutane.Mr-Fauzan farar shadda ce sanye a jikin shi riga da wando da kuma malin malin, Da hular shi black color ' sai wristwatch golden mai tsada.Mr-Fauzan komai na jikin shi to-match ne kuma maitsada.Haka aka shish-shiga motoci masu tsada na gani nafad'a, Suka nufi Babban masallacin juma'a domin d'aura aure.B'angaren Safna kuwa, Har tayi wanka ta shirya tayi kwalliya ta k'ure kwalliya iyakar yinta.Kayan dake jikin ta atampa ce gadagalle sabuwa ' wacce Goggo Mariya ta kawo mata.Haka Safna ta k'unshe d'aki sabida kunya da 'yan k'annanta.*1:00pm dot* aka d'aura auren *Mr-Fauzan&Safna*.Safna na zaune a d'aki ne, d'aya daga cikin wakilen nata ya shigo ya sanar musu cewar Aure ya d'auru.Gaba d'aya gidan hamdala suka shiga yi, Safna kuwa ji tayi tamkar ta nutse sabida kunya."Aunty Safna zan biki cen..."Inji Anisah."Toh Anisah, Karki damu awajen Goggo Mariya zakuzauna ' ni kuma kullun zanzo na rik'a duba ku."To kawai Anisah tace, Goggo Mariya ta shigo d'akin.'Yan nasihohi Goggo Mariya taita yiwa Safna, Yi nayibari na bari da dai sauran su.*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS."groups/1649808818646464/*52-53*Suna cikin haka ne, Abokan Ango suka iso k'ofar gidan su Safna da manya manyan motocin su.Saida suka dunga hone, Sannan wata ta fito taimusumagana.Hafiz ne ya fito daga motar shi ya jigina jikin shi."Ni zan d'auki Amarya!."Abinda ya fad'a kenan yayi calming hands d'in shi.Safna kuwa, Koda aka zo aka sanar mata cewar abokan Ango sunzo d'aukan Amare kuka ta fashe dashi.Goggo Mariya ce keta lallashin ta sai kuma wad'an da ba'a rasaba.Haka aka shirya Safna tsaf aka lullub'e mata fuskarta da gyale, Sannan kowa ya sanya hijabin shi.Wasu fita sukayi suka fara shiga mota, Wasu kuma tare da Amaryar zasu fito.Goggo Mariya shirya su Rumaisa tayi ta hanyar mik'a masu hijabansu suka sanya, Domin dasu za'a kai Amarya.Haka da k'yar aka samu Safna ta daina kuka aka fitoda ita aka sata cikin mota.A seat d'in baya aka sanya Safna sai 'yan k'annan ta da take tsakiyar su sai kuma Goggo Mariya data zauna front seat."Aff! Ina zuwa don Allah, Bara na sanya kwad'o (padlock) a gidan."Cewar Goggo Mariya.Goggo Mariya bud'e motar tayi ta fita domin kulle gidan."Amarsu Amarsu... Amarsu ansha k'amshi..."Hafiz ya fad'a cikin zolaya."Nifa har yanzu banji kin fara kuka bane, Don nafiso kiba Ango wahala."Cewar Hafiz."Ai tasha kuka sosai kafin mu fito, Saida aka dunga lallashin ta..."Rumaisa ta fad'i haka."Aww! Lallai yau Abokina sai yayi dagaske kenan, Kafin a kalle shi."Safna da fuskarta take a lullub'e,
Shuru kawai tayi batare da tace dashi komai ba.Suna cikin haka ne Goggo Mariya ta dawo, Hakan yasa Hafiz tada mota suka jeru ' motar Amarya na tsakiya, Haka suka d'auki hanyar kai Amarya ' duk tainda suka bi sai an kalle su.B'angaren Sir-Kamal kuwa, Bayan ya kai gidane yayiparking motar shi ya shige ciki ranshi a b'ace.Ammi dake zaune a parlor ne taga yazo zai wuce ba tare da yayi sallama ba talk less of ya gaishe ta."Kamal?."Ammi tayi saurin tsaida shi, Sir-Kamal juyowa yayi ya kalli Ammi idanun nan nashi sunyi ja."Meya faru ka shigo a haka?."Sir-Kamal zuciya ce ta tik'o shi ya juya kawai zai wuce d'aki, Ammi ta dakatar shi."Kamal! Ba tambayar ka nakeyi ba?.""Ammi... Yarinyar da nakeso nake muradin kasancewa tare da ita, Yau na wayi gari Oga na ya aure ta Ammi!."Sir-Kamal yayi maganar yana huci tamkar zaki, Idanun shi kuwa duk sun kawo ruwa.Ganin hakan yasa Ammi tashi taje ta kamo hannun shi suka zauna."Kamal... Wace yarinya ce da har ran maza ya b'aci haka?.""Yarinyar da na dad'e ina baki labarin ta, Ammi bantab'a sanin Safna kwad'ayi keyi da ita ba... Kumaban tab'a sanin Safna hawainiya bace Ammi..."Ammi shuru tayi nad'an lokaci, Sannan tace."Kardai yarinyar da kake cemin ' zaka nemowa aiki kwanakin baya!.""Ammi, Ita ce..."Sir-Kamal yayi maganar ta wata irin murya tamkar zaiyi kuka, Wanda ni kaina Seemaluv saida yayi matuk'ar bani tausayi."Kamal, Hak'uri shine kawai abinyi... Kuma tunda kaga haka to dama Allah baiyi zata zama matar ka ba.""No... No... Ammi! Banason jin wata kalmar hak'uri a halin yanzu Ammi, I must revenge... I must revenge...She betrayed me! Duk irin alkairin da nayi masu??."Sir-Kamal ya furta hakan tare da tashi zai nufi d'akinshi."Kamal, Karka sawa ranka mugun abu fa! Kayi tawakkali mana... Kuma dama ai ba kullun mutun yake nema yake samu ba."Cewar Ammi.Sir-Kamal d'aki ya shige ya kulle ta hanyar sanyamak'ofar key.*** *** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 3:00PM*Aka isa gidan Amarya, A bakin gate d'in wani d'and'areren gida aka tsaya ' tabbas gidan *BABBANGIDA* ne.Hafiz ne yayi hone gateman ya bud'e gate sannan motocin suka shiga.Bayan shigar sune Goggo Mariya ta tsaya k'arewa gidan kallo, Duk tabi ta k'agara ta shiga ciki.Bayan motocin sunyi parking ne, Aka fito da Amarya ' Dangin Amarya suka dunga gud'a har suka shiga ciki basu daina ba.A parlor suka tsaya kasancewar basu san inda zasu dosa ba, Don gidan lungu lungu ne gashi kuma upstairs.Goggo Mariya ce ta tashi ta haura sama domin dubayanayin gidan.Cikin 'yan mintoci k'alilan ta dawo cikin farin ciki."Yo ku ai ga d'akin amaryar cen na gano.... Nidai tunda nake ban taba shiga irin wannan waje ba!."Goggo Mariya ta fad'i haka tare da kamo hannun Safna suka haura sama.Wasu daga ciki, Lek'e lek'e suka shigayi lungu lungu domin bama idonsu abinci.Bayan Goggo Mariya ta zaunar da Safna saman gado ne ta d'age mata mayafin fuskarta."Kinga yadda Allah ke d'aukaka d'an adam ko? Sabida haka bud'e idon ki kiyi kallo, Wannan d'akin ki ne Safna."Cewar Goggo.Safna d'aga kai tayi ta kalli yanayin d'akin tayi murmushi ta sunkuyar da kanta.Da misalin k'arfe *4:00pm*, B'angaren Mr-Fauzan ' wanka ya sake yi ya shirya cikin milk d'in shadda komai nashi ya tafi daidai.Mr-Fauzan wayar shi ya d'auka yayi dialing number d'in Hafiz, Bayan Hafiz ya d'aga wayar ne Mr-Fauzan yace."Hafiz, Nifa am well ready... Duk na k'osa, Azo a d'auke akai ni gida na.""Ahhh... Kaji mara kunyan Ango, Lallai aboki baka data ido ' to shikenan am on my way."Hafiz ya fad'a.Mr-Fauzan parlor ya fito ya iske mutane kowa na nuna farin cikin shi.Mummy ce tare da Khairat suka shigo cikin parlon hakan yasa Mr-Fauzan k'arasawa inda suke."Bro, Kayi kyau sosai... Ni zanyi maka rakiya har wajen Amarya."Cewar Khairat.Mr-Fauzan murmushi yayi irin na manya yace."Thanks K'anwa ta."Mr-Fauzan maida kallon shi yayi akan Mummy wacce idanun ta suka cika da hawaye."Mum, Nayi kyau?."Cewar Mr-Fauzan."Eh mana Son, Kayi kyau sosai ma..."Mummy tayi maganar cikin sigar kuka ' muryar ta narawa."Oh come on Mum... Please don't cry, Yin aure ba shine cewar na barku kenan ba Mum, Am your son and we will forever be together."Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin tausasssar murya.Mummy hannun tasa ta share 'yan hawayen dake shirin zubowa, Tare da cewa."Nidai fata na kada matar ka ta raba ni da kai Fauzan.""Shhhhhh..."Mr-Fauzan ya furta tare da hugging Mummy ta sigarlallashi, Khairat dake gefe hawaye ne suka zubo mata tayi saurin sharewa, Mr-Fauzan yayi hugging d'inta ta d'ayan hannun.Haka Camera man ya dunga d'aukan pictures iri iri, Har su Hafiz suka iso cikin gidan.Mr-Fauzan na cikin lallashin Mummy ne kiran Hafiz ya shigo cikin wayar, Hakan yasa shi d'aga wayar."Babban mutum, Ka fito ' kai kawai muke jira."Cewar Hafiz.Okay kawai Mr-Fauzan yace ya kashe wayar, Sannan ya sanarwa Mummy.Mummy da Khairat ' da sauran mutanen wajen, Rakiya suka yiwa Mr-Fauzan zuwa garage.Nan suka iske Daddy da jama'an shi shima.Haka suka d'unguma suka yiwa Mr-Fauzan rakiya har cikin motor, Saida suka ga wucewar shi sannan suka koma cikin gida.Koda Mr-Fauzan da Hafiz suka isa, Iskewa sukayi har angama kwashe dangin amarya an maida su gida.Goggo Mariya ce kawai dasu Rumaisa suka rage, Suma d'in parlor suka fito zasu fita ' suka had'e da Mr-Fauzan.Nan suka tsaya suka gaisa, Sannan Goggo Mariya tace."Toh... Ga 'yar mu nan amana, Amana muka bar maka ita ' domin kuwa duk wanda yaci amana to amana shima zata ci shi."Mr-Fauzan cikin kamala ya nuna gamsuwar shi game da abinda Goggo Mariya tace.Nan Goggo Mariya ta kama hannun Anisah suka fito domin a maida su gida."To kai, Bari nai maka rakiya wajen Amaryar ko."Cewar Hafiz."A'a! No need ' na hutar da kai... Duk na k'osa naga My Infinity."Mr-Fauzan ya fad'a gami da sanya hannun shi cikin aljihu."Ah! Banda cika baki fa! Don na sanka..."Na sukayi sallama cike da fara'a, Hafiz ya juya ya wuce, Sannan Mr-Fauzan ya juya ya haye sama ' ya nufi d'akin da Safna take.*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS."53*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*® ```Written```By*_Seemaluv_*https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/*54-55*Mr-Fauzan, Cikin bedroom d'in ya shiga tare da yin sallama Safna ta amsa.Bayan ya k'arasa bakin gado ne ya zauna while Safna na tsakiyar gadon a zaune.Mr-Fauzan shuru yayi nad'an lokaci sannan yasa hannu ya cire built d'in k'afar shi ya tashi ya bud'e wardrobe ya ciro dadduma ya shinfid'a ya zauna, Sannan ya umurci Safna itama tazo ta zauna.Safna cikin sanyin jiki ta sauko daga gadon ta dawo ta zauna saman dadduma suna facing juna.Mr-Fauzan murmushi yayi yasa hannu ya d'age gyalen dake fuskar ta, Nan yayi hamdala ya mik'a godiyar shi zuwa ga Allah.Sannan Mr-Fauzan ya shiga yiwa Safna tambayoyi kamar yadda musulunci ya tanadar.Duk tambayoyin da Mr-Fauzan yayiwa Safna duk ta amsa ' hakan yasa Mr-Fauzan sauke ajiyar zuciya."Ki tashi kije kiyi wanka, Sannan kiyi Alwala ' ki same a d'aki na.."Mr-Fauzan ya fad'a a tak'aice.Safna shuru tayi kamar bataji abinda yace ba."Okay?."Mr-Fauzan ya fad'i haka.Safna kai ta d'aga mashi alaman toh, Sannan Mr-Fauzan ya tashi ' y wuce.Safna saida tayi 5minutes a zaune a wajen tana tunani iri iri a cikin ranta."Yau ni'ce a gidan Mr-Fauzan a matsayin matarsa? Allah kasa hakan shine mafi alkairi da kwanciyar hankali a gare ni."Safna ta fad'i haka gamida k'arewa d'akin kallo.Komai na d'akin purple ne, Paint d'in d'akin ma purple ne, Hatta globe d'in d'akin purple ne, hakan yasa color d'in d'akin ya koma purple.Safna tashi tayi tayaye mayafin dake kanta, Ta d'agerigar ta taja zanin sama sannan ta cire rigar ta nufi bathroom.Safna hannu tasa ta bud'e bathroom d'in ta shiga, Haske ta gani fauuu... Kasancewar komai na bathroom d'in fari ne.Haka Safna ta shiga ciki ta maida k'ofa ta rufe, Tsayawa tayi tana kallon yanayin bathroom d'in na d'an lokaci."Wannan kuma wane irin bayi ne? To ina ruwan suke?."Safna ta fad'i haka tana waige waige.Juyawa tayi ta fita ' fita tayi daga d'akin ta tsinci kanta a parlor, Parlon ko haske babu sakamakon kashe wutar da akayi.Wani tsoro ne taji ya riske ta lokaci d'aya, Hakan yasa ta juya zata koma d'aki sai jitayi anyi back hugging d'in ta.Safna wani shock taji ya ratsa jikin ta, Cikin tsoro tace."Hasbunallah..."Abinda ya fito daga bakin ta kenan ta runtse idanun ta."My infinity..."Mr-Fauzan ne ya furta haka.Nan ya juyo da ita suna facing juna.Mr-Fauzan hannu yasa ya d'ago fuskar ta suna kallon juna."Har kin shirya ne? Ni kike jira ko?"Kai Safna ta girgiza mashi, Sannan yace."Then, Mene ne?.""Dama... Dama... Ruwan wankan ne babu acen d'in ' shine na fito nema."Cewar Safna.Mr-Fauzan kallon ta yakeyi surprisingly daga bisani ya

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment