Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lips d'inshi yayi ' yayiwa motar key, Da sauri Safna ta juyo ta kalle shi.Mr-Fauzan figar motar yayi a 360 suka bar cikin hospital d'in."Ina zaka kaini?."Ta fad'i haka idanun ta cike da k'walla.Mr-Fauzan shiru yayi ya kyaleta gudu kawai ya tafkawa."Meyasa ka kasance mugu a gareni?."Ta fad'i haka cikin shauk'i na kuka, Mr-Fauzan kuwako a jikin shi driving d'in shi kawai ya keyi."Na tsane ka Fauzan Na tsane ka! Ka maida ni inda ka d'auko ni."Mr-Fauzan dogon burki yaja ya tsaya.*_FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS_*
*42-43*Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalli Safna tare da cewa."Muje.""Ni babu inda zanje, Don Allah ka maida ni inda ka d'auko ni.""I don't want to argue with you Safna, Don't forget akwai yarjejeniya tsakanin mu, Kar kuma ki manta da Mahaifiyar ki dake hospital ba lafiya."Safna sunkuyar da kanta tayi tana nazari, Sannan Mr-Fauzan ya cigaba da cewa."Sabida haka ya zama dole kibi abinda nace, Because I can change my mind at any time.""Saboda kana azzalumi? Meyasa ku masu kud'i bakwayin abu tsakani da Allah?."Safna maganar cikin rawar murya."Daki aure ni Mahaifiyar ki ta warke, Da kik'i amincewa kuma ta mutu wane kika zab'a?."Mr-Fauzan ya fad'i haka ba tare da ya kalle ta ba."Wai kai wane irin azzalumi ne? Wane irin mugu ne kai? Meyasa bakwa taimako tsakani da Allah?.""Why? I thought ke kina da tarbiyyar da zaki iya sadaukawar Mahaifiyar ki farin cikin ki."Mr-Fauzan ya fad'i haka tare da jan tsuki, Sannan yak'ara da cewa."Let me just call the doctor ' na fad'a mashi cewa nina cire hannuna game da mahaifiyar ki."Ya fad'a tare da d'aga wayar shi zaiyi dialing numberd'in Doctor, Safna saurin dakatar dashi tayi da cewa."A'a Don Allah... Kar kayi haka...Kayi hak'uri naji na amince zanbi duk abinda tace."Ta fad'i haka hawaye na gangaro mata saman fuskar.Mr-Fauzan handkerchief ya mik'a ma Safna domin ta share hawayen dake fuskar ta, Haka ta karb'a ta share cike da takaici."Kuma as from today ' inaso ki adana hawayen ki, Because am not bullying you."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya bud'e mota ya fita.Safna itama budewa tayi ta fito, Wani babban shop suka shiga wanda ya k'unshi komai da komai.Bayan shigar sune Mr-Fauzan ya nufi b'angaren Abayas Safna na biye dashi a baya.Safna tsayawa tayi wajen wata Abaya mai kyau, Ganin haka yasa Mr-Fauzan tsayawa ya duba kud'inAbayan da Safna ke kallo."So cheap."Ya fad'a gami da kamo hannun ta yaja ta suka k'arasa ciki.Mr-Fauzan bai tsaya ko ina ba sai a wajen wasu Abayas masu kyau wanda daka gansu kaga kud'i.Safna k'ok'arin raba hannun ta take da nashi amma ta kasa.Mr-Fauzan kuwa Abayas kawai yake jida, Yana sakawa cikin basket.Suna cikin hakanne Suhailah ta shigo cikin shop d'in,Itama wajen Abayas d'in taje tana zab'ar wanda yai mata.Suhaila hango Mr-Fauzan tayi rik'e da hannun Safnayasa ta aje basket d'in nan wajen ta nufi inda yake.Mr-Fauzan kuwa tunda suka had'a ido da Suhailah yasa ke rik'e hannun Safna sosai."Fauzan?."Suhailah ta ambaci sunan shi cikin mamaki.Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalle ta, Safna kuwa k'ok'arin ta shine taga ta raba hannun ta da nashi."Who is she?."Tayi tambayar tana yi mashi nuni da Safna."She's my wife to be."Ya furta with proud.Suhailah zaro ido tayi gami da k'arewa Safna kallo, Ganin haka yasa Safna sunkuyar da kai.Nan Suhailah ta matsa kusa da Safna tare da fincikar hijab d'in gami da cewa."Wannan abun ce kakeso ka aura Fauzan? Dame ta fini?."Mr-Fauzan kab'ewa Suhailah hannu yayi tare da yi mata kasheda yace."Don't try something stupid here Suhailah, And i advise you to leave us alone...!!' kafin ki raina kanki awajen nan!.""Fauzan abinda zakace kenan? Ni kake fad'awa haka akan wannan k'azamar?."Suhailah ta fad'i haka cike da tsirawa Safna hannu.Mr-Fauzan tsuki yaja suka bar wajen."What! Ni Fauzan zaima haka? Ni zai yaudara? Ni zai ciwa fuska sabida wannan abin? Lallai zan nuna mishi kad'an daga cikin aikin Suhailah."Abinda Suhailah ta fad'a kenan tare da karkad'a kanta ta koma wajen inda take zab'an Abayas.A wajen mai karb'ar kud'i Mr-Fauzan ya tsaya, Ciro wallet d'in shi yayi ya zari ATM card d'in shi ya mika musu domin su cire kud'in su.Tunda suka tsaya wajen Safna ke kallon Mr-Fauzan jikin ta a sanyaye."Sona kake da gaske ko kuwa?."Ta fad'i haka cikin ranta.Tana cikin wannan tunanin ne taji ya jata sun nufi wajen k'ofar fita.Fita sukayi daga cikin shop d'in, Mr-Fauzan saida suka isa wajen mota tukunna ya sakar mata hannu.Key ya sanya ya bud'e motar, Sannan ya saka kayancikin bode ya koma cikin mota ya zauna, Tukunna itama ta bud'e front seat ta shiga ta zauna.Mr-Fauzan tada motar yayi suka nufi hospital dominmaida ta.Mr-Fauzan driving d'in shi kawai yakeyi Safna na satar kallon shi.Tabbas Mr-Fauzan kyakkyawa ne kuma ya cancanciduk wata mace ta kalle shi ta yaba.Cikin 'yan mintoci suka isa cikin hospital d'in, Bayan yayi parking ne ya danna wani waje cikin motar hakan yasa bode ya bud'e."Kije ki cire kayan ki."Ya fad'a cike da tak'ama ba tare da ya kalle ta ba."Na gode."Safna ta fad'a, Sannan ta bud'e motar ta fito.Safna wajen bode ta zagaya ta d'aga ' ta d'auki ledarkayan, Sannan ta rufe bode d'in.Nan Mr-Fauzan yaja motarshi ya wuce.Safna koda ta shiga cikin hospital d'in cikin ward ta wuce kai tsaye.'Yan uwan su Umma ta iske a ciki hakan yasa gabanta ya fad'i.Da sauri Safna ta k'arasa ciki, Ganin yadda su Rumaisa ke kuka ne yasa nan take k'afafun Safna suka fara rawa.Anisah ce ta taso ta rungume Safna cikin kuka tace."Aunty Safna, Likita yace wai Umma ta rasu..."Raras gaban Safna ya sake fad'uwa, Nan take idanuwanta suka ciko da hawaye.Safna maida kallon ta tayi ga mutanen da ke tsaye a wajen, Ganin yadda suke girgiza kai alaman tausayawa ne yasa Safna ta matsa wajen gadon Umma.Safna ganin an rufe Umma da farin k'yalle ne yasa tazubewa k'asa, Cikin kuka take cewa."Umma don Allah ki tashi...karki mana haka... Ummaki tashi don Allah."Safna ta k'arashe maganar cikin kuka.Rumaisa tasowa tayi tazo kusa da Safna ta tsaya gami da dafa kafad'an ta.Hakan yasa Safna d'ago kai ta kalle ta."Rumaisa meyafaru da Umma haka?.".Tayi maganar cikin disashewar murya.Rumaisa share hawayen da ke mata zarya tayi tace."Lokacin da kika fitane ciwon ta ya tashi harta kaiga yin kashin jini, Shine na fita na kira likita, Koda yazo ya duba ta sai kawai naga ya rufe mata fuska yace in kira 'yan uwanmu, Shine na d'auki kud'i naje na kira su Goggo mariya."Da sauri Safna ta rungume Rumaisa cikin matsanancin kuka.Goggo Mariya ce ta taso tazo inda Safna take."Kiyi hak'uri Safna ki kuma d'auki k'addara."Cewar Goggo Mariya.Goggo Mariya k'anwa ce ga Umma.Wani ne ya shigo ya cikin ward d'in tare a cewa."Ga motar cen an kawo."Abinda ya fad'a kenan ya shigo ciki tare da Nurses guda biyu suka d'auki gawar Umma suka d'aura ta atrolley chair, Suka nufi wajen mota da ita.Safna dasu Rumaisa kuka kawai sukeyi har suka shiga cikin mota, Aka sanya gawar Umma a baya.'Yan uwan Umma suma shiga suka yi cikin motar, Kasancewar boss ce motar shiyasa ta d'auke su gaba d'aya..*_@Dedicated to SEEMALUV NOVELS GROUP & B'OYAYYEN AL'AMARI FANS GROUP,,,,,,,,,Masoya na ina ganin sak'on nin ku ' Seemaluv really appreciate it._**44-45*Koda su Safna suka isa gida kafin kace kwabo gidanya cika da mutane, K'ofar gidan kuwa cike yake da maza.Bayan anyiwa gawar wanka ne, Safna tana ji tana gani aka d'auki gawar aka fita a ita domin yi mata sallah, Daga nan akaita masaukin ta.“Wayyo Allah na shiga uku... Ni yanzu yazan kasance da k'annai na?.”Safna dake zaune cikin hijab ta fad'i haka cikin matsanancin kuka.Goggo Mariya ce, Ta taso tazo inda Safna take tace.“Haba Safna meyasa bazakiyi tawakkali ba? Meyasa? Karfa ki manta duk mai rai mamaci ne, Kuma ai Allah yana tare daku.”Haka duk mutanen dake wajen suka dunga lallashin Safna.*** *** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 5:00PM*Bayan ankaita andawo ne, Mutane suka fara watsewa ya rage daga su Safna sai Goggo Mariya.“To Safna ki daiyi hak'uri kuma ki cigaba dayi mata addu'a kawai, Kuma kinga irin rayuwar da muke ciki ' yanzu tashi zakiyi da sana'a saboda ki samu ku kare mutuncin kanku.”Cewar Goggo Mariya.“Yanzu Goggo Mariya, Bazamu sami tallafi daga wajen ku ba kenan?.”Safna ta fad'i haka.Goggo Mariya ajiyar zuciya tayi tare da girgiza kai cike da nuna tausayawa tace.“Safna kenan! Yanzu wa kike ganin zai baku wani tallafi? Toh ni d'innan kinga nima ba wani hali gareniba ' sai mijina ya nemo ya kawo, Gani kuma da 'ya'ya ' kuma yanzu masu kud'in nan ba taimako sukeyi ba.”Safna wasu zafafan hawaye suke kwaranyo mata, Kallon Rumaisa tayi taga babu abinda takeyi sai kuka.Nan ta maida kallon ta kan Anisah ta ganta rakub'e jikin bango tayi shuru.“Bakomai Goggo Mariya, Nagode sosai da shawararki kuma insha Allah zan nemi aikin yi.”Nan Goggo Mariya ta tashi sukayi sallama sannan ta wuce.Bayan anya sallar isha'i ne, Safna da su Rumaisa suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shigo tare da yin sallama.Bayan an amsa masa ne yace.“Wai ance ana sallama da Safna.”“Kace gata nan zuwa.”Cewar Safna.Yaron juya wa yayi ya fita, Sannan Safna ta tashi ta fita domin duba wanda ke kiran ta.Safna koda ta fita Ganin Sir-Kamal tayi tsaye, Hakanyasa ta k'arasa inda yake jingine jikin motarshi.Bayan sun gaisa ne Sir-Kamal yace.“Safna naje hospital d'in akace min an sallame ku, To yaya jikin Mahaifiyar taki? Anyi mata aikin ne?.”Safna d'ago kai tayi ta kalli Sir-Kamal tare da cewa.“Umma Allah yai mata rasuwa d'azu.”“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...”Cewar Sir-Kamal.Shuru sukayi na d'an lokacin, Sannan Sir-Kamal ya lura da kukan da Safna keyi.“Kiyi hak'uri Safna, Allah ya gafarta mata Allah kumayasa hutun kenan.”“Amin na gode.”Ta fad'a da disash-shiyar murya.“To yanzu waye ke zaune daku?.”“Ba kowa.”“Toh... Insha Allah idan akayi sadakan uku, Zan dawo domin akwai maganar da nakeso muyi.”To Safna tace, Sannan Sir-Kamal ya bud'e mota ya ciro abincin da Mr-Fauzan ya umurce shi daya siya masu as usual.Sir-Kamal mik'awa Safna yayi ta amsa, Sannan yace.“Inji Mr-Fauzan, Oga na kenan ' yace inkawo muku wannan, Baima san da rasuwar ba shiyasa but zan fad'a mashi idan na koma.”Nan Safna ta mayar mashi ledar gami da cewa.“Ka mayar mashi da abincin shi, Domin bama buk'ata.”“Ha'a Safna meye dalilin yin hakan?.”“Kamal... Abubuwa da dama sun faru ba tare da saninka ba, Saboda haka kawai abarni inji da mutuwar rasuwar Umma na kad'ai ta ishe ni.”Ta fad'i haka gami da share hawayen ta.“Insha Allah Safna komai zaizo maki da sauk'i, Kuma as far as am alive ni zanyi maki komai, Yanzu kuna da abinda zaku ci ne?.”Kai Safna ta
girgiza mashi alaman a'a, Tukunna yace.“To, Kiyi hak'uri ki ansa wannan kuci, Saboda kada ku kwanta da yunwa.”“Kada ka damu Kamal, Zan nema mana abinda zamu ci don akwai sauran kud'i a waje na.”OK kawai Sir-Kamal yace sannan ya maida ledar takeaways d'in cikin mota.Sir-Kamal dawo wa yayi ya tsaya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya ciro 10k ya mik'awa Safna gami da cewa.“Kiyi amfani da wannan, Kafin na sake dawo wa.”Nan Safna ta fashe da kuka, Cike da cewa.“ hak'uri, Amma ni kunyar ansan kud'in ka nakeyi yanzu, Sabida na kasa karb'ar soyayyar ka.”Murmushin takaici Sir-Kamal yayi tare da cewa.“Karki damu Safna, A yau koda ace ban furta miki kalmar so ba ' to zan cigaba da kasancewa inuwa a gareki.”Safna d'ago kai tayi ta kalle shi cikin shauk'in kuka da sautin shagwab'a tace.“Da gaske kakeyi?.”“Uhm.. Da gaske nake mana! Idan har kika bani dama.”“Na gode.”Ta fad'a tare da sunkuyar da kanta, Nan sukayi sallama Sir-Kamal ya shige motar shi yaja ya wuce sannan Safna ta shige gida.Bayan shigar ta gida ne ta iske har Anisah tayi bacci.“A'a Rumaisa tada Anisah, Babu wanda zaiyi bacci baici abinci ba.”Safna ta fad'i haka gami da cire hijab d'in jikin ta.Bayan Rumaisa ta tada Anisah ne Safna tace.“Indomie zaki je ki siyo mana dafaffa wajen mai shayin cen.”To Rumaisa tace sannan Safna ta cire d'ari biyar ta mik'a mata tace.“Kice uku zai dafa maki.”Kai Rumaisa ta d'aga alaman to, Sannan ta sanya hijab d'inta ta fita.B'angaren Sir-Kamal, Bayan ya koma gida ne yayi shirin bacci ya kwanta ya d'auki wayar shi yayi dialing number d'in Mr-Fauzan.Ringing tai tayi bai d'aga ba har sai da Sir-Kamal yayi four missed calls sannan Mr-Fauzan yayi receiving call d'in.“Good evening Sir.”“Evening, Any problem?.”“Well, Yes Sir, Mahaifiyar Safna ce Allah yayi mata rasuwa d'azu.”Mr-Fauzan a kwance yake amma jin haka yasa shi yin saurin tashi zaune.“What!! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Why didn't you tell me earlier??.. Meyasa sai yanzu kake fad'amin?.”“Am sorry Sir, Nima bansani ba sai da naje kai musuabinda zasuci ne ake fad'amun an sallame su shine nabi ta gidan nasu.”“Ya salaam!...”Mr-Fauzan ya furta tare da dafe goshin shi.Mr-Fauzan ending call d'in yayi ya jefar da phone d'in saman gado, Ya fito yana kwala wa Mummy kira.“Mom! Dad!.”Mummy da Daddy kwance suke suna bacci, Jin yadda kiran yayi yawa ne yasa Mummy tayi firgigit ta farka.Parlor ta sauko cikin sauri tana cewa.“Son what's wrong? Meyafaru?.”Mr-Fauzan dafe kanshi yayi, Gami da cewa.“Mom, Yanzu ake fad'amin Mahaifiyar Safna ta rasu.”“Wacece Safna?.”“Ita ce wacce zan kawo miki ita gobe, Surukan ki Mom.”Mummy rufe baki tayi tare da girgiza kai alaman tausayawa.“Ya salaam!... Allah ya jik'anta.”Amin Mr-Fauzan yace gamida dafa saman kujera.“Shit!!.”Ya furta tare da bugun kujerar.“Calm down Son, Yanzu kaje ka kwanta gobe sai ayi mata ta'aziyya.”“I can't sleep at this time Mom... I can't, I know that Safna will never forgive me...”Mummy tsayawa tayi tana kallon shi cikin mamaki.“Meyasa? Me kai mata?.”Mr-Fauzan shuru yayi na d'an lokaci Sannan Mummy tace.“Kaje dai ka kwanta, Saboda abinda safiya batayi badare bazai yi shiba.”Mr-Fauzan juyawa yayi ya wuce part d'in shi, Mummy girgiza kai kawai tayi itama ta koma b'angaren su ta kwanta.Mr-Fauzan koda ya kwanta, D'aga kanshi yayi ya duba clock yaga *10:00pm*.“Huh! Lemme call Hafiz.”Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan, Yayi dialing number en Hafiz.B'angaren Hafiz kuwa kwance yake a d'akin shi ya kwanta harya fara bacci wayar shi ta fara ringing.Jikin shi a mace ya tashi gami da d'aukar wayar ya duba yaga Mr-Fauzan me ke kiran shi.“At this time!!??.”Ya fad'i haka tare da picking call d'in.“Babban Mutum! Ya akayi ne?.”Cewar Hafiz.“Hafiz, Ba lafia ba fa!.”“What is the problem?.”“Wallahi Hafiz an yanka ta tashi.”Hafiz wata doguwar hamma ya saki gami da cewa.“What does that means?.”“Please idan ma zaka aje bacci agefe ka aje, Mahaifiyar Safna ce ta rasu yau.”Jin hakan yasa Hafiz ya saki salati, Sannan Mr-Fauzan yace.“Hafiz I don't think zan iya bacci seriously, Yarinyar nan tana iya cewa bazata yarda na aure ta ba ' nasan ta taurin kaine da ita, And she can even blameme for her mother's death!.”“Ai kaga abinda nake guje maka, Shiyasa tuntuni nakeso abi komai a hankali.”“Oh come on! Yanzu meye nayi wanda ba daidai ba a ciki? Kawai son nake na taimaka mata na aure ta that is it.”Mr-Fauzan ya fad'i haka a gadarance.“You fall for her didn't you?.”Hafiz yayi tambayar cike da zolaya.“Haba dai!...”“Oh har yanzu bazaka bada kaiba ko? Aboki kabi a hankali fa.”“Yanzu dai what's the solution?.”Cewar Mr-Fauzan.“Kawai ka bari sai gobe, We will find a way out.”OK Mr-Fauzan yace sannan suka yi sallama ya kashe wayar shi, Ya kwanta.Mr-Fauzan koda ya kwanta tunani iri iri kawai suke zuwa mashi a rai har bacci yayi awon gaba dashi.*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.44*46-47*Washe gari misalin k'arfe *7:00am* Mr-Fauzan ya tashi, Bathroom ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala sannan yayi sallah.Mr-Fauzan shiryawa yayi kamar yadda ya saba cikin suit sky blue colour, Komai nashi matching color ne.Mr-Fauzan perfume ya fesa Sannan ya fito zuwa parlor, Ko da ya isa parlor iskewa yayi har house girl ta gama shirya breakfast su Mummy sun zauna suna karyawa.Mr-Fauzan k'arasawa wajen dinning table d'in yayi ' yayi joining d'insu ya zauna.Mr-Fauzan Daddy da Mummy ya gaisar sannan Khairat da ke gefe tace."Yaya Good morning.""Ehem, Morning Khairat.Cewar Mr-Fauzan.Mr-Fauzan tsiyaya tea yayi cikin cup at fara sha."Fauzan, Yau da safe Hajia ke fad'amin cewar Safna tayi rashin mahaifiyar ta, Allah ubangiji ya gafar ta mata."Mr-Fauzan cikin nutsuwa ya aje cup d'in hannun sa tare da cewa."Amin Dad.""Idan ka tashi zuwa wajen ta'aziyyar, Zaka tafi da Khairat ' ita ce zata wakilce mu nida Alhaji."Mummy ta fad'i haka."OK, Aima yanzu zan tafi ' because inaso in lek'a office yau."Abinda Mr-Fauzan yace kenan ya cigaba da sipping tea d'in shi.*Some minutes later...*Bayan sun gama breakfast ne Daddy ya tashi ya wuce wajen aiki, Mr-Fauzan shima mik'ewa yayi gami da gyara necktie d'in shi yace."Ki same ni cikin motor."Ya fad'awa Khairat haka, Jin haka yasa Khairat ta ajiye cup d'in tea d'inta ta wuce d'akin ta cikin hanzari.Gele ta yafa a k'irjin ta ' ta d'auki side back d'in ta ta fito, Khairat parlor ta dawo ta sallami Mummy tukunna ta fita.Koda ta fito cikin motor ta sami Mr-Fauzan zaune, Hakan yasa ta bud'e front seat ta shiga ta zauna tareda cewa."Yaya, Na shirya."Nan take Mr-Fauzan yayi dialing number d'in Hafiz.Ringing d'aya tayi Hafiz yayi receiving."Babban Mutum!."Cewar Hafiz."Hafiz, Am on my way coming to your house now ' kashirya tare zamu je ta'aziyyar.""Shit!... OK to sai ka iso."Nan Mr-Fauzan yayi ending call d'in ya tada motor suka nufi gidan su Hafiz.B'angaren Hafiz, Bayan ya gama waya day Mr-Fauzan ne ya tashi ya fad'a bathroom yayi wanka, Sannan ya shirya cikin milk d'in yadi mai tsada.Hafiz shiryawa yayi tsaf ' ya fito parlor yayi breakfasta tsaitsaye, Hajia na lura da hakan.Hafiz harya kama hanyar fita ne Hajia ta dakatar dashi da cewa."Hafiz lafiya kuwa? Ina zuwa haka?."Hafiz juyowa yayi ya fuskanci Hajia tare da cewa."Akwai inda zamuje ne nida Fauzan, Banaso yazo ban gama shiryawa bane."Aleeza dake gefen Hajia a zauna gaban ta ya fad'i dasauri ta juyo ta kalli Hafiz."Oh shine yasa kake ta abu baga baga kamar zaka tashi sama?."Hafiz juyawa yayi ya fice cikin walwala tare da cewa."Eh mana."Aleeza tashi tayi zata wuce kitchen Hajia ta tsai da ita da cewa."Ina kuma zakije Auta?.""Hajia, Kitchen zanje zan yiwa mai aiki magana ne."To kawai Hajia tace, Sannan Aleeza ta wuce kitchen, Iske 'yar aiki tayi tana goge goge."Yawwa, Don Allah inason kimin wani abu ne."Cewar Aleeza."To.""Kije harabar garage ki tsaya, Akwai wani abokin yaya Hafiz da zaizo ' da zarar yazo please kizo ki fad'amin."To kawai 'yar aikin tace ta cigaba da gogen ta, Hakan yasa Aleeza tayi saurin ansar tsumman tare da cewa."No! Kije kawai, Bara na cigaba kafin ki dawo."Haka 'yar aikin ta wuce harabar garage ta tsaya wajen flowers, Shi kuwa Hafiz na zaune k'ark'ashin rumfa rik'e da wayar shi yana jiran zuwa Mr-Fauzan.Aleeza jefar da tsumman tayi nan wajen ta dawo parlor ta fara safa da marwa.Hajia na zaune gefe tana kallon ta, Aleeza tana cikin haka wayar ta dake saman three seater ta fara ringing ' hakan yasa tayi sauri ta je ta d'auka.Ganin Dr Khalil ne yasa tayi receiving cikin fara'a, Bayan sun gaisa ne kamar kullun ' Dr Khalil yace."I hope kin shirya ma zuwa ko?.""Insha Allah."Nan suka cigaba da hirar su, Hafiz na zaune yaji hone hakan yasa shi yin saurin mik'ewa tsaye tare da cewa."Yawwa, Bud'e gate d'in da sauri."Hafiz ya fad'awa gate man haka.Bayan gate man ya bud'e gate ne kamar yadda aka umurce shi, Mr-Fauzan ya shigo da motar shi ciki.Bayan yayi parking motar shine ya fito, Cikin fara'a Mr-Fauzan da Hafiz sukai hands shake.Ganin haka yasa 'yar aikin ta juya ta koma da sauri.Aleeza na cikin wayan ne 'yar aikin ta shigo cikin parlor gami da cewa."Gaya cen ya zo."Jin Hakan yasa Aleeza tayi saurin cewa Dr Khalil."We will talk later, Babye."Abinda tace kenan tayi ending call.Aleeza wajen window ta koma tana lek'en su Mr-Fauzan."Wa kike lek'e ne wajen?."Cewar Hajia."Ohhhhhh! Hajia bafa kowa! Naji kamar tsayawar mota ne shine fa nake dubawa."Aleeza ta fad'i haka cikin shagwab'a."To ai shikenan, Ba sai naji duka ba kuma."Aleeza murmushi tayi tare da karkad'a kai ta koma ta zauna kusa da Hajia.B'angaren Mr-Fauzan bayan sun gama gaisawa da Hafiz ne yace."Hajia na nan ko?.""Eh tana nan, Kuma na fad'a mata zuwan ka.""To bari Khairat taje su gaisa.""Oh! Dama tare da Khairat kuke? Shine ta lafe cikin motor?."Hafiz ya fad'i haka, Sannan yace."Bari naje nayi mata magana da kaina toh."Haka Hafiz ya zarce wajen motar ya bud'e, Da sauri Khairat ta d'ago kai ta kalle shi tare da sakar mashi smiling."Ina kwana?.""Kina nufin da bazaki je ku gaisa da Hajia ba kenan?."Khairat kunya ce ta rufe ta yasa sunkuyar da kai gamida
cewa."A'a dama ina da niyyar yin haka."Abinda ta fad'a kenan ta fito daga cikin motar, Hafiz ya nuna mata hanyar shiga ta wuce ' Hafiz binta yayida kallo harta shige ciki Sannan ya koma wajen Mr-Fauzan.Bayan sun zauna ne Hafiz ya fara tsarawa Mr-Fauzan yadda suyi."Aini matsala ta da kai shegen girman kai."Cewar Hafiz."Hafiz, You know me very well ' bani son raini at all...and you know that.""Just admit it ' kana son yarinyar nan... Meye a ciki? Ni banga abin raini a ciki ba ai...""Shikenan... Naji I love her and I admit that... Yanzu meye abin yi? What if tak'i yarda dani?."Hafiz dogon numfashi yaja, Sannan yace."Idan tak'i yarda da kai sai ka barta kawai don ba'a so dole, Although nasan Safna na sonka ' sai dai idan kak'i bata hak'uri.""Oh come on... Meya kawo maganar bada hak'uri? Hafiz babu abinda yake bani wahala irin in bud'e baki in bada haku'ri, Musamman ga mace!.""You see your life? Aiko hak'uri ya zama dole ka bata, Because ita mace 'yar tarairaya ce."Mr-Fauzan nuna gamsuwar shi yayi game da maganganun Hafiz, Nan suka tashi suka nufi mota."Af! Wannan taje ta shantake, Let me go and call her."Hafiz ya fad'i haka, Sannan ya nufi cikin gida domin kiran Khairat.Mr-Fauzan kuwa cikin motor ya shiga yayi zaman shi.Hafiz koda ya shiga ciki a parlor ya iske Khairat tare da su Hajia suna fira."Toh, Ke muke jira fa."Hafiz ya fad'i haka.Jin haka yasa Khairat ta mik'e tayi sallama da su Aleeza, Hafiz fita yayi yaje ya shige motor.Aleeza rakiya taiwa Khairat har wajen motor, Sannan sukayi exchanging number tukunna Khairat ta bud'e back seat ta shige.Aleeza harta juya zata wuce taji ance."Madam babu gaisuwa ne?."Aleeza wani farrrrrr taji cikin ranta, Cikin sanyin jiki ta juya ' Ganin Mr-Fauzan tayi yana kallon ta a cikin mirror d'in jikin motor.Hakan yasa Aleeza k'arasawa side d'in da yake tace."Ina kwana?."Mr-Fauzan kasa ansawa yayi, Sakamakon ganin bandage d'in da ke forehead nata."Meya faru dake haka?."Yayi tambayar with cares."Oh! Wai goshi na? I had an accident.""How comes?.""Well... Bayan na bar Company d'in ka abin ya faru dani.""Hafiz kaga irin ta ko? Shiyasa banaso ana barin k'ananan yara suna driving by their selves, I don't like that at all..."Aleeza tsuki taja Mara sauti cikin ranta tace."Ji rainin hankali don Allah! K'aramar yarinya ma yake d'auka ta kenan mtsw."Nan Aleeza ta juya ta wuce rai a b'ace.Mr-Fauzan kallon wucewar ta yayi ta glass sannan ya tab'e baki ya tada mota suka wuce.```MY FACEBOOK FANS, NA GODE SOSAI DA ADDUAR KU GARE NI THANK YOU SO MUCH, YOU GUYS MEAN A LOT TO ME.```*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.*46roups/1649808818646464/*_FAN'S KUYI HAK'URI DA JINA SHURU DA KUKAYI, BANJIN DAD'I NE..._**48-49*K'auyen su Safna suka nufa ' kasancewar tsakanin k'auyen da cikin gari akwai d'an nisa hakan yasa suka b'ata *2hours* kamar kusan kullun.Bayan sun isa cikin unguwar ne, Mr-Fauzan yayi parking daidai k'ofar gidan su Safna."Khairat you get in first, Sai ku gaisa tukunna ki fad'amata zuwan mu.""Okay."Khairat tace, Sannan ta bud'e motor ta fito, Ganin yanayin gidan nasu yasa jikin ta yayi sanyi ta shige cikin gidan."Huh! Ni tausayin yarinyar nan nakeji....Just take a look at the house she is living in!..."Mr-Fauzan ya fad'i haka with sound of sympathy.Bayan shigan Khairat cikin gidan ne ta iske su zaunea tsakar gida saman tabarma.Khairat sallama tayi Safna ta juyo ta kalle ta gamida ansa sallamar.Khairat k'arasa tayi ciki Safna ta bata kujera ta zauna, Sannan suka gaisa Khairat tayi mata ta'aziyya."Sai dai ban gane wacece ke ba."Khairat murmushi tayi ta numfasa, Sannan ta fad'awa Safna wacece ita.Safna ajiyar zuciya tayi ' ta tashi ta d'ebowa Khairat ruwan rijiya ta bata.Khairat kurb'a d'aya tayi ta ajiye ruwan."Ku kad'ai kuke zama ne?."Khairat tayi tambayan cikin tausayawa."Eh mu kad'ai muke zama yanzu, To wama muke dashi da zaizo ya zauna damu? Kinga kuwa dole na

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment