Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren aje masallaci ayi."
"Amm... Wannan duk ba abin damuwa bace ' gobe insha Allah zanzo da mahaifina domin ayi maganar auren, Don ni nafison nan da next week ayi bikin."
Cewar Mr-Fauzan.
Umma ajiyar zuciya tayi cike da jinjinawa al'amarin, Tace.
"To shikenan ba matsala."
"And then, Insha Allah bayan bikin za'ayi miki aikin ciwon dake damunki."
Umma zaro ido tayi tare da nuna jindad'in ta, Gamida cewa.
"Yaro na gode, Alhamdulillah! Allah ya sanya alkairi."
Nan sukayiwa Umma Sallama ' Mr-Fauzan ya sanya hannu a aljihu ya ciro band'ir d'in 'yan dubu ya ajiyewa Umma bisa gadon da take, Suka juya suka fita.
"A'a'a'a... Yaro harda wahala haka? To angode."
Abinda Umma tace kenan ta koma ta kwanta, Sannan Safna tabi bayansu.
Bayan sun fita daga cikin hospital d'in Safna na biye dasu, Hafiz yace.
"Fauzan bari inshiga mota injira ka, Ka tsaya ku gaisa ko?."
Hafiz ba tare daya tsaya yaji abinda Mr-Fauzan zaice ba ya shige mota ya barsu nan tsaye.
Mr-Fauzan da Safna, Shuru sukayi nad'an lokaci sannan Safna tace.
"Amm... Na gode da duk alkairin da kaimun."
"Don't Mention."
Ya fad'a yana k'ok'arin wucewa, Cikin k'arfin hali tace.
"Harzaka tafi?."
Jin abinda tace yasashi juyowa ya kalleta, Hakan yasa ta sunkuyar da kai.
"Yes, Wucewa zanyi don banga amfanin tsayuwa anan ba! Besides ' taimakon ki nayi nazo wajen nan, Kamata yayi ki kwana kinamin godiya ' zan taimaki Umman ki ' ni a yanzu haka inajine tamkar infasa aurenki but I will not do that because ' banason zab'in wasu zab'in kaina nakeso."
Safna had'e rai tayi kanta na sunkuye hawaye na mata zarya a fuska, Mr-Fauzan yazo daf da ita suna facing juna yace.
"And let me remind you Safna, Zan aure ki ne kawai don na ajeki cikin gida na ' har sai lokacin da naga wacce taimun, Sannan na aure ta ' ke kuma na sake ki."
Abinda Mr-Fauzan yace kenan ya juya zai wuce ' Safna cikin kukan da bashida sauti da radad'i ta tsaida shi da cewa.
"Naji dad'i tunda akwai saki aciki, Kuma ina k'ara yi maka godiya."
Tana gama fad'in haka ta juya aguje cikin kuka ta shige cikin hospital d'in.
Mr-Fauzan wucewar shi yayi ' tare da nuna halin ko'inkula ya shige mota, Hafiz yaja suka wuce.

*AROUND 8:00PM*

Hafiz ya aje Mr-Fauzan gida, Sannan shima ya koma gida.
Mr-Fauzan koda ya shiga cikin gida ' a harabar parlor ya tsaya ganinsu Mummy da Daddy zaune suna kallo.
Mr-Fauzan sallama yayi Daddy ya amsa ' sannan ya k'arasa wajensu ya sami waje ya zauna, Tukunna yace.
"Daddy, Na sami wacce zan aura ' kuma mahaifiyar ta tace inturo zuwa gobe."
Daddy maida kallon shi yayi kan Mr-Fauzan yace.
"To Alhamdulillah, A ina suke?."
Nan Mr-Fauzan ya fad'awa Daddy komai da duk abinda abinda ya k'unshi rayuwar da suke ciki, Sannan ya k'ara da cewa.
"Amma Daddy Mahaifiyar ta tana hospital a yanzu haka, Kuma tace babu damuwa zama a iyayin bikin tana kwance."
"Subhanallah! Meke damunta kuma?."
"Eh aiki dai za'ai mata, But nina d'auki nauyin aikin ' bayan biki I mean next week za'ayi mata aikin."
Maganar Mr-Fauzan ne yabawa Daddy dariya, Hakan yasa yace.
"Wato dai Son, Kana nunfin next week za'ayi auren kenan?."
"Eh Daddy, Saboda abunda na riga na tsara kenan."
"Very Good!, To Allah ya kaimu goben sai muje hospital d'in, Allah kuma ya maka albarka."
Ameen Mr-Fauzan yace ' ya tashi zai wuce Mummy tace.
"Fauzan?."
Juyowa yayi ya kalleta with cares.
"Na'am Mum."
"Ina fatan dai ba dangin talaka zaka kawo mana ba!."
Har Mr-Fauzan ya bud'e baki zaiyi magana Daddy yayi saurin cewa.
"Yi tafiyar ka Son."
Mr-Fauzan part d'inshi ya nufa, Sannan Daddy yace.
"Wai kekam meyasa kike haka? Haba! Su talakawan ba mutane bane?."
"Mutane ne amma..."
"Amma what!?."
Mummy tashi tayi ta haura sama cikin k'unk'uni, Tukunna shima yabi bayanta.
B'angaren Mr-Fauzan kuwa, Yana shiga bedroom d'inshi ya cire kayan jikin shi ' ya bari daga shi sai boxer ya fad'a bathroom domin yin wanka.
Mr-Fauzan yana jikin wanka ne ' maganganun daya fad'awa Safna sukaita fad'o mashi a rai, Nan tausayin ta ya kamashi ' sam yasan cewa bai kyauta.
"She's hurt! She is really hurt."
Abunda ya dunga furtawa kenan harya gama wanka, Sannan yayo alwala ya fito.
Mr-Fauzan wardrobe d'inshi ya bud'e ya ciro jallabiya ash color ya sanya, Sannan ya fara sallar isha'i.
Bayan idarwarsa ne ' ya fito daga d'aki ya nufi kitchen ya had'a Coffee ya koma bedroom d'insa.
Mr-Fauzan a bakin gado ya zauna ' ya shanye coffee d'in tass, Sannan ya haye gado tare da kamo pillow ya rungume.
"Is like I miss something!."
Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya, Nan bacci yayi awon gaba dashi.









_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

*Follow me on wattpad @Seemaluv1**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*® ```Written```By*_Seemaluv_*https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/*_@I Dedicated This Page To My Love Ones, Thank You For Support And Cares..._**38-39**_Washe gari_**AROUND 8:00AM*Mr-Fauzan ya tashi bacci, Bathroom ya shige yayi taking bath d'inshi gamida d'auro alwala sannan ya fito.Mr-Fauzan shinfid'a praying mat yayi ' yayi sallarsa, Bayan ya idar ne ya tashi ya shirya cikin black suite da takalmin shi black built sannan Mr-Fauzan ya dawo gaban mirror ya tsaya.Fauzper perfume ya fesa kamar kullun sannan ya d'auki wayarshi ya rik'e.Mr-Fauzan parlor ya fito ya iske Mummy da Daddy zaune a dinning tareda Khairat suna breakfast.Mr-Fauzan k'arasawa wajen yayi yayi joining d'insu, Nan ya gaishesu suka amsa sannan Daddy yace."Son kenan! Harka shirya kenan.""Yes Dad."Mr-Fauzan ya fad'a tare da tsiyaya tea a cup."Fauzan?."Cewar Mummy.Mr-Fauzan d'ago kai yayi ya kalleta with cares tare da cewa."Na'am Mummy.""Fauzan karka kawomin dangin talakawa am repeating myself."Mr-Fauzan aje cup d'in hannun shi yayi zaiyi magana Daddy ya dakatar dashi da cewa."Haba! Meyasa kikeyin haka? Why? Shi talakan ba Allah ne yayi shiba?.""Ainasan Allah ne yayi shi but ni kawai banaso, Akanme?."Mummy ta fad'i haka."Wow, Za'aje ganin auntyn mune? Daddy zan biku."Cewar Khairat."Yes, Tare dake ya dace aje ai ' ki gano min kalarta."Umma ta fad'i haka.Mr-Fauzan ne yayi saurin shiga maganar da cewa."No ' no need, Karma kisa ran zaki bimu, Besides ba school zaki tafi ba?."Khairat zunb'uro baki tayi tare da cewa."Ai wannan ba problem bane.""Na dai fad'a miki bazaki bimu ba, Hole I make myself clear."Mr-Fauzan ya fad'i haka tare da mik'ewa tsaye gami da cewa."Daddy bara in jira ka cikin motor.""Son, Harka gama breakfast d'in kenan?.""Yes Dad, I just lost my appetite that is it."Ok kawai Daddy yace sannan Mr-Fauzan ya juya ya fita."Haba! Why are you doing this iye? Ki bar fad'in irin wad'an nan magan maganun gaban su fa am warning you."Daddy ya fad'i haka."A'a allow me, Kuma idan har bai kawo min ita na gani ba ' to bazan tab'a karb'ar ta a matsayin suruku ba Alhaji."Daddy girgiza kai kawai yayi gami da cewa."Duk ma haka bata taso ba, Bara muje mu dawo."Mr-Fauzan yana fita direct ya nufi wajen mota, Mr-Fauzan key yasa a jikin motar k'irar Mercedes yabud'e tukunna ya shiga driver seat ya zauna.Mr-Fauzan dialing number d'in Hafiz yayi, Ringing d'aya Hafiz ya d'aga wayar."Ya! Babban mutum."Cewar Hafiz."Hafiz do you know what? Yanzu zamuje Private Hospital Girmi nida Dad fa.""Kai! Aboki da sauri sauri haka? Kanason yarinyar nan fa.""Oh come on! I just wanted to help her kawai, Me zanyi da k'azama irin ta? Kaima kasan she's not my type."'Yar dariya Hafiz yayi gami da cewa."Hm! Kada dai reshe ya juye da mujiya, Fauzan ka rik'a sassauci fa.""Don't change my mode, I will hang up now ' we will talk later."Abinda Mr-Fauzan yace kenan ya kashe wayar shi, Daddy ne ya bud'e motar ya shiga front seat ya zauna sannan ya rufe."Let me just assign driver to drive us."Daddy harya bud'e motar zai kira driver Mr-Fauzan yace."No Dad, Bara nayi driving d'in kawai."Ok kawai Daddy yace tukunna Mr-Fauzan ya tada motar gate man yayi hanzarin bud'e gate, Mr-Fauzan yaja motar suka nufi Private Hospital Girmi.B'angaren su Safna kuwa tunda ta tashi daga bacci tayi sallah sannan tayi wanka.Safna saida ta gama kintsa Umma tukunna Rumaisada Anisa suka shirya.Safna fita tayi daga cikin hospital d'in ta tsaya bakin titi tasiyo musu kunun gyad'a, Sannan ta dawo cikin hospital suka karya.Bayan sun karya ne Safna ta tashi tare da sanya hijab d'inta gami da cewa."Umma, Zanje in d'auko muku kayan da zaku cenja ke dasu Rumaisa, Daga nan nima incenja."To Umma tace, Safna har ta juya zata fita ward d'in Umma ta tsaida ita da cewa."Kud'in wajen ki zasu isheki ne?.""Eh Umma zasu isa har su rage."Umma d'aga kai tayi alaman gamsuwa sannan Safna ta juya ta fice.Safna a bakin titi ta tsaya ta tari mai keke-napep ta shiga ta wuce.Bayan wucewar tane Mr-Fauzan da Daddy suka iso cikin hospital d'in.Mr-Fauzan parking yayi a gefe tukunna suka fito daga motar, Mr-Fauzan jagaba yayiwa Daddy zuwa ward d'inda Umma take.Sallama sukayi sannan suka shiga ciki, Umma ganinsune yasa ta tashi zaune suka gaisa.Rumaisa da Anisa gaishesu sukayi Mr-Fauzan ya amsa a yatsine."Ke tashi ki shifid'a mashi tabarma ya zauna mana."Cewar Umma."A'a tama barshi, Am okay here."Mr-Fauzan ya fad'i haka cike da nuna kyamata.Daddy gyaran murya yayi ' yayi introducing kanshi ma Umma, Sannan ya fad'a mata dalilin zuwanshi.Umma nuna farin ciki tayi matuk'a tare da yima Daddy godiya."Kinsan halin yaran yanzu, So shiyasa mukeson ayi bikin nan da wuri."Cewar Daddy."A'a ba damuwa, Wannan ba wani abu bane ai."Umma ta fad'i haka."To mu ta fanninmu bamu son auren ya wuce nan danext week wato nan da wani sati kenan."Umma aminta tayi da abinda mahaifin Mr-Fauzan ya fad'a, Domin ita duk ta k'osa taga auren Safna.Umma kwatance tayiwa Daddy, Inda dangin uban suSafna suke, Domin kuwa sune zasu gindaya yadda sadakin zai kasance.Daddy nuna gamsuwa yayi sannan ya tashi gamida ciro bandir d'in duba d'aya ya aje ma Umma saman gadon da take zaune."Ga wannan.""Alhaji harda d'awainiya haka?.""Bakomai."Cewar Daddy.Nan sukayi sallama Daddy da Mr-Fauzan suka bar ward d'in.Bayan sun fito cikin hospital d'inne Daddy ya tsaida Mr-Fauzan da cewa."Fauzan, Amma ya abun nan zai kasance haka?.""Daddy meke nan?.""Lafiyar ita mahaifiyar yarinyar nan, Menene? Me take buk'ata ne?.""Never mind Dad, Na riga na d'auki nauyin komai a hannu na' Bayan aure za'ayi mata aiki."Ok Daddy yace sannan suka k'arasa wajen mota, Shiga Daddy yayi tukunna Mr-Fauzan ya zagaya ya shiga ya tada motar suka nufi unguwan da dangin mahaifin su Safna suke.B'angaren su Aleeza, Zaune take a parlor da bucket of warm water a gabanta Hajia na gaggasa mata inda yayi mata tsami Hafiz na gefe tare da laptop yana dannawa bisa cinyarsa."Auta ya kamata kiyi taka tsantsan fa! Wannan yawon banzan ki rage shi."Hajia ta fad'i haka tana dannawa Aleeza goshinta dad'an k'aramin towel.Wayar Aleeza ce ta fara ringing alaman kira, Hakan yasa ta d'an juya ta fuskanci wayar.Wata new number ce wacce batasan da ita ba, Hakan yasa tayi ignoring call d'in.Aleeza k'ara ta saki sakamakon Hajia ta tab'a mata inda ke mata ciwo sosai."Hajia a kwai zafi fa."Aleeza tayi maganar a shagwab'e.Suna cikin haka ne kira ya sake shigowa cikin wayarAleeza.Aleeza picking call d'in tayi gami da tashi ta wuce d'aki.Bayan ta zauna saman gado ne tace."Aleeza speaking.""It's Dr Khalil Muhammad.""Oh!."Aleeza ta furta."Are you surprise?.""Surprise of what?.""Nothing, Well ' yaya jikin naki? Ko sai nazo?."Yayi maganar cikin zolaya."Naji sauk'i ma, Ana d'an min warming d'in wajen ciwon ne ma ka kira.""Ok then, Aje acigaba da warming up, Inason ki kasance cikin lafiya I will call later.""Ok thanks for your cares."Nan Aleeza tayi hanging up d'in kiran, Barin phone d'in tayi saman gado ta koma parlor ta zauna Hajia ta cigaba da duba lafiyar ta.B'angaren su Mr-Fauzan, Cikin unguwan da aka yi musu kwatance suka shiga.Tambaya sukayi aka kaisu har gidan, Bayan sun shiga zauren gidanne sukayi sallama wata mata wacce ta manyanta ta fito sanye da zani ta lullub'e jikinta.Bayan sun gaisa ne suka sake tabbatarwa ko nanne gidan da Mahaifiyat Safna tayi musu kwatance, Matar amsawa tayi da cewa."Eh k'warai nan ne, Amma Allah yasa dai lafiya."Nan Mr-Fauzan ya fad'a mata dalilin zuwansu, Jin haka yasa ta koma cikin gida ta d'auko tabarma ta shinfid'a musu.Mr-Fauzan a zuciyar sa yace."Oh God! Tabarma tabarma dai, Meyasa sukeson tabarma? So irritating."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a cikin ranshi kenan, Ganin Daddy ya zauna ne yasa shima ya zauna tare da tank'washe k'afa.Nan suka tsaida magana Daddy ya ciro 50 thousandya ajiye kamar yadda matar nan ta ambata a matsayin sadakin Safna.Ganin hakan yasa ta tashi ta shiga cikin gida ta kira sauran dangi dukda cewar basu da wani yawa.Dukkansu sanya albarka sukayi, Ciki kuwa harda masu bak'in ciki.Nan aka tsaida gamsas-shiyar magana akan next week ne za'a d'aura aure a cikin babban masallacin juma'a.Daddy da Mr-Fauzan sallama suka yiwa mutanen wajen sannan suka juya suka nufi wajen mota.Bayan sun shiga mota ne Mr-Fauzan yayi ajiyar zuciya cike da nuna gajiya, Sannan ya tada motar suka bar wajen.Mr-Fauzan yana cikin driving ne kiran Sir-Kamal ya shigo ta wayar shi, Kasancewar akwai Bluetooth ear set a kunnen shi, Hakan yasa shi amsa calling d'in kai tsaye."Hello Sir.""Yes Kamal, Any problem?.""Sir, Akwai meeting d'in da zakayi attending around 12:00pm."Sir-Kamal ya fad'i haka yana cikin office d'in shi zaune.Mr-Fauzan wristwatch d'in hannun sa ya duba ganinit's almost 12 ne yasa shi cewa."And kuma sai yanzu ne zaka fad'amin ina da meeting da zanyi attending?.""Am sorry Sir, Abubuwa ne suka shigemin gaba.""I can't attend that meeting, Just cancel it."Ya fad'i haka yana driving."But Sir, You have to ' because it's very important.""Kamal you had what I said, Right?.""Yes Sir, And then wasu sunzo suma kai suke jira.""Kamal, Just handle everything, I need to rest today."OK Sir-Kamal yace sannan Mr-Fauzan ya danna Bluetooth ear set yayi ending call d'in.Daddy ne ya kalli Mr-Fauzan yace."Son, You have to go and check what's going on ' on that company.""Okay Dad, But ba wani abu bane fa, Just lazy P.A gareni baya son yin abinda ya kamata."Mr-Fauzan ya fad'i haka yana driving.B'angaren Safna kuwa har taje gida ta dawo cikin hospital d'in.Umma fad'awa Safna tayi yadda sukayi da mahaifin Mr-Fauzan.Ganin Safna bata nuna jin dad'in ta bane, Yasa Umma cewa."Safna?."Safna d'ago kai tayi ta kalli Umma kamar zatayi kuka."Na'am Umma."" 'Yan nan idan har akwai wata matsala wanda bansan da itaba ki fad'amun tunda wuri, Farin cikin ku kawai nakeso na gani."Safna mik'ewa tsaye tayi tare da juya baya tace."A'a Umma babu wata matsala, Ni kaina farin cikinkinake
buk'ata, Don duk na k'osa ki sami lafiya Umma.Nan hawaye suka zubo Safna a fuska tayi sauri tasa hannu ta share."Karku damu idan harni mai rayuwa ce ' zan rayu, Kuma bakiji likita yace za'aimun aiki nan da sati uku ba?."Safna juyowa tayi ta kalli Umma gami da d'aga matakai alaman Eh, Sannan ta maida kallon ta kan Anisah dake kwance saman tabarma tana bacci.39
*40-41**AROUND 2:00PM*Bayan Mr-Fauzan ya ajiye Daddy wajen business d'in shine ya kama hanyar komawa gida.Mr-Fauzan a bakin gate ya tsaya gate man ya bud'e mashi sannan ya shigo.Bayan yayi parking ne ya bud'e motar ya fito ya k'arasa ciki, Mr-Fauzan koda ya shiga parlor a zaune ya iske Mummy rik'e da remote a hannunta sanye da medicated glass a idonta.Mr-Fauzan sallama yayi tukunna ya k'arasa cikin harabar parlor.Bayan ya zauna ne Mummy ta kalle shi tace."Son?.""Mom."Ya furta a gajiye."Inaso gobe ka kawo min ita domin mu gaisa, Inasonnaga surukata.""To Allah ya kaimu."Ameen Mummy tace, Sannan Mr-Fauzan ya tashi yawuce part d'in shi.Bayan ya shiga bedroom d'in shi ne ya cire suit d'in jikin shi tare da takalmin shi built, Sannan ya haye gado ya kwanta.Mr-Fauzan janyo wayar shi yayi ' yayi dialing number d'in Sir-Kamal, Ringing d'aya zuwa biyu yayireceiving."Kaje GIRMI hospital kuwa yau?."Cewar Mr-Fauzan."No Sir.""OK then, Kaje yanzu! ka siya musu abinda zasuci, I will transfer 10k into your account now!."Dogon numfashi Sir-Kamal yaja, Sannan yace."OK."Nan Mr-Fauzan yayi ending call d'in.Mr-Fauzan transfer yayiwa Sir-Kamal through mobile bank.Nan ya ajiye wayar saman side drower ya koma ya kwanta tare da rungume pillow.B'angaren Sir-Kamal, Fitowa yayi daga company ya nufi inda yayi parking motar shi cikin hanzari.Shiga yayi gami da yiwa motar key ' yaja ya nufi restaurant.Sir-Kamal abinci ya siyowa su Safna, Sannan ya shiga motar shi ya nufi Girmi-Hospital.Bayan isarsa cikin hospital d'in ne ya fito daga motarcikin sauri rik'e da ledar takeaways a hannun shi.Cikin hospital d'in ya shiga ya nufi ward d'in da Umma take.Sir-Kamal shiga yayi cike da sallama a bakin shi.Safna ce tayi saurin mik'ewa tsaye tare da amsa sallamar, Nan su Rumaisa suka gaishe shi ya amsa, Sannan ya mik'awa Safna sak'on da aka bashi.Sir-Kamal maida kallon shi yayi akan Umma yaga bacci takeyi."Yaya jikin Umma?.""Da sauk'i."Cewar Safna."Am.. Abinci ne a ciki inji Oga."Sir-Kamal ya fad'i haka fuskar shi babu annuri atattare da ita.Safna karb'a tayi tare da cewa."Gashima har na siyo mana abinci munci ' wannan sai dai anjima da yamma."Sir-Kamal juyawa yayi zai wuce, Safna tayi saurin tsaida shi da cewa."Kamal?."Sir-Kamal tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ya kalleta ba yace."Safna.""Kamal, Zan iya magana da kai don Allah?.""Eh."Ya fad'a a tak'aice, Hakan yasa Safna ta mik'awa Rumaisa ledar takeaways d'in, Sannan tabi bayan Sir-Kamal suka fito bakin hospital d'in."Am...Kamal...,Nasan zaka d'auke ni a matsayin butulu wacce tak'i karb'ar soyayyar ka ko?."Safna ta fad'i haka tana kallon gefen fuskar shi kamar zatayi kuka.Sir-kamal smiling d'in k'arfin hali yayiwa Safna gamida cewa."Ko kad'an, Ai nasan kina da dalilin yin hakan.""Kamal, Yin hakan shine alkairi a gareni, Banaso na amshi soyayyar ka daga k'arshe kaga kamar na yaudare ka."Na fahimce ki Safna, Amma inaso ki sani bazan daina sonki a cikin zuciya ta ba."Safna girgiza kai tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa idanuwan tane suka cicciko da kwalla."Kamal, Ka cewa Ogan ka nagode ' kuma don Allah inaso ka cire zancen sona a ranka, Mu zama abokai."Safna na gama fad'in haka ta juya ta koma ciki, Sir-kamal right hand d'in shi ya dunk'ule zuciyar shi na mashi k'una.Sir-Kamal wajen motar ya nufa cikin hanzari ya tadamotar ya bar hospital d'in.Sir-Kamal gida ya wuce direct, Bayan yayi parking motar shi a compound ne ya fito ya shige cikin gida.Kasancewar bai sami kowa a parlor bane yasa shi shigewa bedroom d'in shi kai tsaye.Sir-Kamal kayan jikin shi ya cire ya ya shige bathroom, Koda ya shiga shower ya kunna ya tsaya tsakiya ruwa na ratsa jikin shi.Takaicin maganganun Safna kawai ke fad'o mashi a rai."Meyasa baza kice kina sona ba? Why? Didn't I deserve to be loved?."Abinda Sir-Kamal ya rik'a fad'a a cikin zuciyar shi kenan, Nan ya rufe shower d'in gami da d'aura towel a k'ugunshi tukunna ya fito.Sir-Kamal koda ya fito k'ana nan kaya ya ciro ya sanya sannan ya fito daga d'akin.Ta parlor ya biyo zai fita suka had'e da Ammi tana shigowa cikin parlon."Kamal?.""Na'am Ammi.""Ina zuwa kuma ' ka dawo ko hutawa baka yi ba?."Ammi ta fad'i haka tare da zaunawa saman kujera."So nake inje ziyarar wani friend d'ina.""Kamal dawo ka zauna na tambaye ka."Jin hakan yasa Sir-Kamal dawowa harabar parlor ya zauna a k'asan kujerar da Ammi ke zaune."Ammi gani.""Kamal, Kana cikin damuwa ko?."Cewar Ammi.Sir-Kamal 'yar dariyar k'arfin hali yayi yace."Ammi kenan, Ni banda wata damuwa please karki d'aga hankalin ki.""Ka tabbata?.""Eh Ammi."Sir-Kamal ya fad'i haka tare da duba wristwatch d'in hannun shi yace."Ammi, Bara inje."To Ammi tace sannan Sir-Kamal ya tashi ya fice.*** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 4:00PM*Mr-Fauzan ya tashi yayi daga baccin da yakeyi gamida sakin doguwar mik'a tare da yin salati.Mr-Fauzan d'aga kanshi yayi ya kalli a gogon d'akin,Yaga *4:00pm*."Oh God!."Ya furta, Sannan ya sauko daga saman gadon gami da cire wandon suit d'in da ke jikin shi ya dawo dagashi sai singlet.Mr-Fauzan d'aura towel yayi a jikin shi sannan ya shige bathroom don yin wanka.Bayan ya fito ne ya shirya cikin jeans and white shirt mai tambarin polo.Mr-Fauzan wristwatch ya d'auko ya sanya a right hand d'in shi mai k'irar gold sannan ya sanya sun glass.Mr-Fauzan takalmin sa ya sanya ' gami da d'aukan car key.Fitowa yayi daga d'akin shi ya shigo cikin parlor zai fita ya had'e da Khairat tana shigowa da alaman daga school ta dawo.Mr-Fauzan harya kama hanyar fita Khairat ta tsaida shi da cewa."Yaya Fauzan?."Nan Mr-Fauzan ya juyo ya kalle ta tare da cewa."Any problem?."Cikin shagwab'a Khairat tace."Bro, Kud'ina ne suka kusa k'arewa.""So?.""Yaya Fauzan, Kad'an bani one hundred thousand nad'an si..."Bata kaiga k'arasa maganar ba Mr-Fauzan ya tsaidaita da cewa."Naji, Basai kinmin dogon surutu ba ' kiyimin sending account number d'inki, I will send more than that."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya juya ya fice, Nan Khairat ta k'arasa d'akin ta cike da murna.Mr-Fauzan wajen motar shi yaje ya bud'e ya shiga ya zauna, Sauke ajiyar zuciya yayi yace."What am I going to do now? Nasan halin Mom, Ana iya samun matsala idan na kawo mata wannan yarinyar a yanayin da take."Mr-Fauzan jinginar da kanshi yayi a jikin seat d'in mota, A zuciyar shi yace."Or should I take her out for shopping? To idan tak'i yarda fa? Oh no!...."Mr-Fauzan d'an k'aramin tsuki yaja, Sannan ya tada motar shi tare da cewa."Dolenta ma ta yarda ' Whether she like it or not."Abinda ya fad'a cikin ranshi kenan, Gate man ya bud'e mashi gate ya fice.Mr-Fauzan GIRMI hospital ya nufa, Bayan ya isa cikin hospital d'inne yayi parking motar shi sannan ya fito.Mr-Fauzan ciki ya k'arasa, Nan yaga wata attender tana goge goge.Mr-Fauzan aika attender d'in yayi taje ta kira mashi Safna gami da fad'a mata ward d'in da suke.Ba'a wani wasting time ba attender d'in ta dawo wajen tare da Safna.Safna ganin shine yasa mode d'in ta ya cenja, K'arasawa wajen shi tayi ta tsaya tare da sunkuyar da kanta.Jin shurun yayi yawa ne yasa ta d'ago kai ta kalle shi taga wayar shi kawai yake dannawa."Kazo lafiya?."Cewar Safna.Mr-Fauzan maida kallon shi yayi akan ta yace."Lafiya.. Akwai maganar da nakeso muyi but bazan iya yinta anan ba."Safna kwalalo mashi Ido tayi tace."To sai a ina kenan?.""Ki biyoni cikin mota na."Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya juya ya wuce wajen motar shi, Mr-Fauzan bud'e motar yayi ya shige Safna na tsaye tana kallon shi."In biyo ka cikin mota kuma?."Safna girgiza kai kawai tayi cike da takaice ta nufi wajen motar tashi.Safna tsaye tayi a wajen tana tunanin ta shiga ne ko karta shiga?.Tana cikin haka ne Mr-Fauzan ya danna mata hone, Hakan yasa ta razana tayi saurin bud'e motar ta shiga."Wace magana za muyi?, Don Allah kar kace ka cenja shawara ' Umma na tana buk'atar taimako."Cewar Safna.Mr-Fauzan tab'e pink lips d'in shi yayi gami da sakinshu'umin smiling."Inaso in kaiki wajen Mom d'ina ta ganki."Nan Safna ta zaro ido tare da rufe bakin ta cike da kunya, Hakan yasa Mr-Fauzan ya tsaya yana kallon ta nad'an lokaci tukunna yace."And I can't take you to her ' cikin k'azanta, The way you are now."Nan take Safna ta dubi jikin ta, Girgiza kai kawai tayicike da tausayawa kanta tace."To ko zaka bari naje gida na cenja kaya?.""No need of that, Zan siya miki kayan sawa ina kud'i kuma na tarasu I got a lot of money, Babu abinda zaimin wahalar samu a duniya."Safna, Jin abin ya fad'a yasa ta fahimci inda ya dosa."Ka barshi ba saika siyamun ba, Inada kayan sawa."Ta fad'a a tak'aice tare da calming hands d'in ta tanakallon waje.Mr-Fauzan juyowa yayi ranshi a b'ace ya kalle ta, Tare da cewa"Ke..? Harni zance zan siya miki abu kice bakyaso?.""Kayi hak'uri, Kamar yadda kake k'yamatar talaka haka nima nake k'yamatar duk wani abinda zai fito daga wajen ka, Taimakon da zakaiwa Umma na kad'ai ya isa."Safna ta fad'i haka ba tare da ta kalle shi ba.Mr-Fauzan cije pink

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment