Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na abincin ta ' ta bata gamida cewa."Umma ga abinci ki ' tuwon shinkafa ne, Ki daure kici."Ansa Umma tayi ta aje agefenta ' tace."Safna ina aka sami kud'i haka?"Nan Safna ta bawa Umma labarin duk abinda ya faru ' da yadda sukayi da doctor.Umma ajiyar zuciya tayi ' tare da girgiza kai alaman damuwa."Yanzu a ina zamu sami wannan mak'udan kud'in?.""Umma karki damu, Abokin Oga na yace ' babu matsala inhar taje na tambayeshi zai bani."Safna ta fad'i haka cikin walwala, Umma kuwa ajiyarzuciya kawai tayi ' ta fara cin abincin ta.Haka rayuwa ta cigaba da juyi dasu Safna ' Hafiz abokin Mr-Fauzan shi ke zuwa yana maidasu gida, Ita kuma Umma nurses na kula da condition d'inta.*** *** *** *** *** *** *** ****Yau take Monday...*Da sassafe Safna ta tashi daga bacci, Ta had'a musu koko suka sha ' sannan suka yi wanka.Bayan sun gama shiri ne ' sukaji ana sallama."Wannan muryar Abokin Oga ne."Safna ta fad'i haka tare da sanya hijabinta ta fita domin dubawa.A tsaye ta ganshi, Nan taimashi sallama suka gaisa tukunna yace."Amm.. Kundai shirya ko?.""Eh mun shirya.""To ku fito inkaiku hospital d'in, Daga nan sai muje wajen Abokin nawa."Safna juyawa tayi ta koma ciki domin su fito ta kulle gidan, Cikin 'yan k'ank'anin lokaci suka fito gaba d'ayansu Rumaisa na rik'e da kwanon kokon Umma wanda zata karya dashi.Dukkansu mota suka shige ' shima Hafiz ya shiga yatada motar, Sannan yaja suka wuce.Bayan *2hours*, Suka isa hospital d'in, Bayan yayi packing ne yace."Safna, Kije kiyiwa Ummanki bayanin inda zakije ' kuma sannan kice inai mata sannu.""To."Abunda tace kenan ta bud'e k'ofar ta bar motar, Rumaisa da Anisa na biye da ita.Safna sai da tad'an jima, Sannan ta fito daga hospital d'in.Hafiz kuwa wak'a ya saka a motar ya k'ure sauti, Yana facing left side d'inshi.Haka Safna ta iso wajen motar ta dunga sallam ' amma sam baiji ba, Sai da ta bud'e motar ta shiga tarufo k'ofar da k'arfi tukunna ya juyo da sauri ya kalleta tare da rage volume d'in sautin, Sannan ya tada motar suka wuce.Hafiz gudu kawai yakeyi babu abinda ya dameshi, Cikin 'yan lokuta k'alilan suka isa company d'in.Hafiz packing yayi, Sannan suka fito suka shiga ciki, Safna kallon mutanen da ke ciki taitayi kasancewar kallon komai takeyi sabo, Domin ko kad'an bataga idon sani ba.Hafiz tafiya kawai yakeyi zuwa office d'in Mr-FauzanSafna na binshi abaya.Bayan sun kai bakin office d'inne Hafiz yace."Ki jira anan ' tukunna."Yana fad'in haka ya bud'e office d'in ya shige.Safna dai tsaye take tana ta baza ido tako ina, Don batasan abinda suke tattaunawa ba.Hafiz bai wani b'ata lokaci ba ya fito gami da cewa."Ki shiga kuyi magana, In kinfito ina mota."Kai ta d'aga mashi kawai ' zuciyar ta na bugawa, Don kuwa bazata mance wanene Mr-Fauzan ba.Bayan wucewar Hafiz ne Safna ta bud'e office d'in ahankali tamkar wacce tai k'arya.Sallam tayi sannan ta k'arasa ciki, Koda ta shiga ta iske shi a zaune amma ya juya bayan sa."Ki nemi wajen zama."Abunda taji yace kenan, Taje ta zauna tana kallon bayansa."Hafiz ya fad'amun cewa Mum d'inki bata da lafiya."Murmushi tayi tace."Eh ashema yayi maka bayani, Wallahi bata da lafiya' tun a gida ta fara rashin lafiyan to shine...."Bata k'arasa ba Mr-Fauzan ya dakatar da ita da cewa."Idan surutu zakimun ' tun wuri ki tashi ki fita."Ya fad'i haka tare da juyowa.Safna sunkuyar da kanta kawai tayi, Don kokad'an batason suna had'a ido."Amm... Dama taimako nazo nema wajenka, Sir please ka taimakamun da kud'in da zan bada aima Umma ta aiki, Likita yace idan ban nemo kud'in ba zata iya rasa ranta.""Are you afraid to loose her?."Safna saurin d'ago kai tayi ta kalleshi ' da hawaye cike da ido, Ita dama abun kuka baya mata wuya."Ita kad'ai ce ta ragemun sai kuma 'yan k'annai na, Kuma likita yace miliyan d'aya suke buk'ata, Sir don Allah ka taimaka mun."Safna ta fad'a haka tana share hawaye."Zan baki kud'in da sukafi haka muddin kika amince da abinda zan fad'a miki yanzu.""Sir, Indai akan infanshi ran Umma na ne ' to nai maka alk'awari zan amince da duk abinda kace."Safna sam ta manta tayin da Mr-Fauzan yayi mata.Mr-Fauzan murmushi yayi ' sannan yayi calming hands d'inshi yana kallon ta."Zan kaiki gidanmu In gabatar dake amatsayin wacce zan aura."Zaro ido Safna tayi tana mamakin abunda Mr-Fauzan ke fad'a."Yes! And after that zan aure ki! Ba don komai sai don banason Mummyna ta aura mun wata, If not ' kema kinsan babu abinda zanyi dake amatsayin mata."Sunkuyar da kai tayi ' idanunta cike da k'walla, A zuciyarta tace."Nasan dama saina fuskanci wulak'anci awajen mutumin nan, Amma babu komai...""Taimaka miki zanyi kawai ' amma ba don inasonki ba, Kuma cikin wannan satin nakeso ayi auren!, Za'a cigaba da kula da Ummanki a hospital har ranar aure kin cika alk'awarin da kika d'auka sannan zanbaki kud'in."Safna saurin kallon shi tayi tana girgiza kai."Sir, Kada kaimun haka don Allah ' likita yace zata iya rasa rayuwarta a kowane irin lokaci, Ka taimaka mun.""Ke zaki taimaka ma kanki ' kibi duk abinda nace, Muddin kika kwantar da hankalinki to babu abinda zai sami Ummanki."Dogon numfashi Safna taja ' sannan tayi shuru nad'an lokaci tace."Kana ganin baza'a sami matsala ba?.""Bana buk'atar tambayoyi daga gareki, And mind you ' koda na Aure ki kada kiyi kuskuren sakani aranki because zakisha wahala a banza."Safna kuwa k'asa kawai take kallo don kuwa hawayen ma sunk'afe, Zuciyarta a bushe take ' tsantsar tsanace ke d'awainiya da ita."Gobe, *Around 11:00am* zan turo P.A Kamal ya d'auko ki, And make sure kin fad'ama Ummanki."Safna harzata tashi da niyyar wucewa ' ya dakatar da ita."Ki sanarma Ummanki ' cewar mun dad'e tare so mun riga mun fahimci juna, If not zaki iya rasa ta inhar aka sami delay!!!."Safna kai kawai ta d'aga mashi, Sannan ta tashi ta fita cikin sanyin jiki.Tafiya kawai takeyi amma hankalinta baya jikin ta ' Safna condition d'in Umma kawai take tunawa.Inda Hafiz ya tsaya ta nufa ' tana isa ta bud'e motar ta shiga, Hafiz bacci ma ya fara jin anrufo motarne yashi yin firgigit ' ya bud'e ido.Ganin Safna yayi cikin wani yanayi ' yanayi na damuwa."Safna lafiya kuwa?."Shuru tayi bata bashi amsa ba ' hakan yashi sake tambaya."Ko ya hanaki kud'in ne?.""Ka kaini wajen Umma na ' ita kawai nakeson gani."Hafiz tab'e baki yayi gamida nuna halin ko'ajikin shi, Tukunna yaja motar zuwa hospital._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1*
@Seemaluv1*B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_I proudly dedicated this page to you my sweetest and lovely Samra, Am so much proud of Baby..._**34-35*Bayan sun isa hospital d'inne Hafiz ya ajeta, Sannan ya juya ya wuce.Haka Safna ta k'arasa cikin hospital d'in sukuku jikinta babu k'wari, D'akin da Umma tace ta nufa ' bayan shigarta ne ta sami waje ta zauna, Sannan tace."Umma ya k'arfin jikin naki?.""Toh 'yan nan da dadi sauk'i, Amma nikam ji nake kamar ciwon k'aruwa yake."Umma ta fad'a haka tana kwance, Safna kai kawai tagirgiza tace."Umma dama akwai maganar da nakeso muyi dake.""To inajinki."Safna wasa da 'yan yatsunta ta farayi fuskarta na kallon k'asa tace."Umma dama Oga nane ' ya dameni yanason ya turomagabatansa domin ayi maganar aure.""Ogan ki kuma? Safna?.""Eh Umma!.""Inace shine wanda kike bani labarinsa!.""A'a Umma bashi bane ' wannan wanine daban, Kuma yace cikin wannan satin nan yakeso a d'aura wai saboda iyayensa sun matsu."Umma shiru tayi tana nazari akan maganar."Kuma Safna ayi biki ina kwance a asibiti?, Amma idan yazo kice masa inason ganinshi."Doguwar ajiyar zuciya ta saki, Sannan tace to ' tare da kallon su Rumaisa da suke kwance saman tabarma a k'asa suna bacci.*AROUND 2:00PM*Safna da Umma suna cikin fira ' Sir Kamal ya shigo tare da yi musu sallama rik'e da ledar a hannun shi, Alamun abinci ne ya kawo musu.Sir Kamal ciki ya k'arasa Safna ta tashi ta bashi wajen zama ya zauna, Sannan ya gaishe da Umma da jikinta."Dama Oga nane yace inkawo muku wannan."Sir Kamal ya fad'a tare da mik'awa Safna ledar take away d'in."Amma ai jikin da sauki ko?.""Eh da sauk'i Alhamdulillah."Cewar Safna."To shikenan, Ni bari intafi.""Har zaka wuce? To nagode kace mashi mungode."Cewar Umma.Sir-Kamal tashi yayi ya fita Safna na binshi a baya, Bayan sun isa wajen mota ne yace."Oh God! Na manta Oga yace inbaki waya kuyi magana, Amma kafin nan dai bari infara fad'a maki abinda ke cikin raina Safna ' kinsan nace miki akwai maganar da zamuyi."Kai Safna ta d'aga mashi alaman Eh, Sannan ya cigaba da cewa."Safnaaa... Na kasa hak'uri da abinda zuciya ta take fad'amun a koda yaushe, Ya zama dole yau in bayyana maki."Ita dai Safna kam k'asa kawai take kallo, Tana sauraron shi."In fact! Ina sonki Safnaaa..."Gabanta ne yayi mugun fad'uwa tayi saurin d'ago kanta ta kalleshi cike da mamaki da d'aurewar kai."Yes Safnaaa... Ina sonki ' kuma so na gaskiya, Inason inga na mallakeki a matsayin mata ta."Safna bata san lokacinda hawaye suka zubo mata ba ' tayi sauri ta share."Why are you crying Safnaaa, Meyasa kike kuka?."Cikin kuka tace."Babu komai, Bakace zamuyi magana da Oganka ba?."Kai ya d'aga mata, Sannan ya ciro wayar a aljihun shi gami da dialing Number d'in Mr-Fauzan tukunna ya bata."Kisa a kunne ' idan ya d'auka sai kice kece."Ringing uku tayi Mr-Fauzan yayi picking tare da karawa a kunne."Assalamu alaikum!, Safna ce."Jin haka yasa Mr-Fauzan lumshe idanu ' sannan yace."Nasan zaki nemi ni shiyasa nace abaki wayar.""Amm.. Dama Umma ne tace tana son kazo.""Ok, Kice mata zanzo zuwa anjima *Around 9:00pm*."Abunda yace kenan ya kashe wayar ' jin haka yasa ta mik'awa Sir-Kamal wayar shi ta juya zata wuce yayi saurin tsaida ita."Meyasa zaki tafi bayan bamu gama magana ba?."Safna juyowa tayi ta kalleshi cike a tausayawa tace."Saboda maganar batada wani amfani a halin yanzu."Waro ido yayi yana mamakin furucin Safna."Safna wannan maganar itace mafi amfani awajena, Ki tsaya ki saurareni please..."Yayi maganar ta wata muryar data kasa tantance soyayyace ko kuwa damuwa!.Nan take hawaye suka fara yimata zarya a fuskarta, Sir-Kamal yayi sauri matsawa kusa da ita tare da cewa."Please inhar abunda na fad'ine ya saki kuka ' to kiyi hak'uri bazan sake ba.""Kayimun komai a rayuwa ta ' haka zalika ka taimakeni a lokacinda nake da buk'atar taimako, Amma a halin yanzu kazomin da abinda bazan iya taimaka maka da shiba ' kayi hak'uri ka cireni a cikinranka."Ta gama rufe baki ta juya ta wuce ' saida takai bakink'ofar shiga hospital d'inne taji tada motar shi, Nan ta tsaya cak gami da dafe kanta."Ya salaam! Mena aikata?."Juyawa tayi da sauri taga harya wuce, Nan ta sami bango ta jingina hawaye kawai ke fita daga idon ta tana cewa."Nima ina sonka! Ina sonka."Safna ji tayi ance."Baiwar Allah idan kina son shi ' to ki fad'a mashi zaifi."Jin abinda akace ne yasa Safna saurin kollon side d'inta taga Nurse ce a yatsaye kusa da ita."Bazai sameni ba.""Meyasa? Ba kince kina sonsa ba? Then, ki fad'a masa kawai."Safna kai kawai ta girgiza gamida cewa."Bazaki tab'a fahimtar komai ba."Abinda Safna ta fad'a kenan ta wuce cikin hospital d'in, Saida ta tabbatar ta share hawayenta sannan tak'arasa cikin ward d'in da Umma take.*** *** *** *** *** *** *** ***B'angaren Hafiz ' tunda ya koma gida yaketa aikin akan computer d'inshi kasancewar he's a business man.Hajiya ce ta fito tsakar parlor ta iske 'yar aiki na gogegogen inda yad'anyi k'ura, Nan ta sami waje ta zauna gami da cewa."Wai ina Aleeza take ne?.""Hajiya tana d'akin ta."Cewar 'yar aiki."Je kikira min ita."'Yar aikin aje tsunman tayi ta tafi d'akin Aleeza ta isar da sak'on Umma tukunna ta baro d'akin.Aleeza tashi tayi daga kwanciyar da tayi tahau gyarakanta ' gaban mirror taje ta tsaya ta shafa powder, Sannan ta gyara d'aurin kanta gamida d'aukan gyaleta yafa bisa kafad'anta gefe d'aya, Tukunna ta fito parlor ta zauna kusa da Hajiya."Hajiya gani.""Na fito ne banji motsin ki ba! Shine nace aje akira mun auta."Murmushi Aleeza tayi cikin shagwaba tace."Yawwa Hajiya ki d'an bani key d'in motarki inje wani waje.""Ina kuma zakije?."Langwab'ar da kai Aleeza tayi tace."Gidan k'awata.""Toh amma dai kar a dad'e kinsan dai halin Yayanki."Kai kawai Aleeza ta d'aga, Sannan Hajiya tayi mata nuni da saman kujera gamida cewa."Ga key d'in cen."Aleeza tashi tayi ta d'auki key d'in ta fice, Tana fita taumarci mai gadi daya bud'e mata gate.Cikin hanzari ta bud'e motar ta shiga taja ta wuce.Company d'in Mr-Fauzan ta nufa, Cikin mintoci ta isa wajen.Aleeza gefe ta samu tayu parking sannan ta fito ta k'arasa ciki, Bayan shigarta ciki ne security suka taretare da 'yan tambayoyi."Mtsw look! Banazo wajen nan domin ku rufeni da questions bane, Office d'in Mr-Fauzan nakeson ku kaini."Nan ma wani dogon surutun suka tsareta dashi, Hakan yasa Aleeza yin magana cikin fad'a."Hey!! Kun san wacece ni? Ni matarsa ce, Saboda haka ku kaini inda yake."Jin abinda ta fad'ane yasa suka sunkuyar dakai gamida bata hak'uri, Sannan d'aya daga cikinsu yayimata jagora zuwa Office d'in.Saida ya tabbatar ya kaita bakin office d'in tukunna ya juya ya tafi.Aleeza dogon numfashi ta saki tare huro iskar bakinta waje, Sannan ta bud'e ta shiga ciki.Koda ta shiga iske shi tayi yana aiki bisa laptop d'in shi tare da cike wasu documents.Sallama tayi mashi ' hakan yasa shi d'ago kai ya kalleta tukunna ya amsa sallamar ya cigaba da aikinshi, Aleeza waje ta samu ta zauna sannan tace."Fauzan...""Can you please introduce yourself?."Mr-Fauzan ya fad'i haka ba tare daya kalleta ba."Am Aleeza ' ni kanwar abokin ka Hafiz ne.""Can I help?."Ajiyar zuciya tayi mai k'arfi wanda har saida ya juyo ya kalleta."Fauzan... Bansan yadda zan furta maka ba ' but koma ta yayane inason ka fahimce ni.""Go ahead!.""Tun lokacin da kazo gidan mu naji inasonka a cikin raina ' kuma naga dakai na dace."Wani mugun kallo Mr-Fauzan yayi mata hakan yasa ta kauda kanta, Domin kuwa babu abinda zai hanatafad'in abunda ke ranta."Wallahi inasonka ' ina sonka Fauzan..., Inason ka bani dama so that I can prove it to you please...""So! Aleeza haka kika lalace da son maza ko? I will definitely tell your bro, Now ki tashi kibarmun office ' tunkafin in b'ata miki rai.""Fauzan, Ka so mai sonka ' wallahi zan iya shiga wani hali muddin bansame kaba.""Get out of my office I said!!!."Tsawar da yayi mata ne yasa ta razana ' tayi saurin mik'ewa, Hakan yasa ta turgud'e ta fad'i.Mr-Fauzan tab'e baki yayi gamida nuna halin ko inkula da ita, Aleeza kuwa dakyar ta iya jan k'afarta ta bar Office d'in.Bayan fitar tane Mr-fauzan ya girgiza kai tare da cewa."Ladies of nowadays ' sam basu da kunyar fad'ama namiji suna sonshi, Amma yaushe Aleeza ta fara hauka haka?."Tsaki yaja sannan ya cigaba da aikin shi.B'angaren Aleeza kuwa ' tunda ta samu takai kanta cikin mota take hawaye, Damuwa ce sosai ta bayyana a fuskarta.Ganin kukan bazai amfana mata komai bane yasa tabud'e dose lock box d'inta dake cikin motar ta ciro wasu k'wayoyi tasa abakinta ta tsotse, Sannan ta tada motar ta wuce.Tana cikin driving ne ' taji wani dizziness na d'ibanta,Hakan yasa ta fare k'ok'arin samun wajen packing amma ina! Abun yaci k'arfinta, Ji kake kararaf!!!._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1*
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Real Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*

*_@ Dedicated This page to you Samra, Because I choose you. and i'll choose you, over and over. without pause, without a doubt, in a heartbeat, i'll keep choosing you,I love you. _*

*36-37*

Tun daga nan Aleeza bata sake samun kanta ba ' sai dai ta farka ta ganta a gadon asibiti, Sam bata lura da wanda yake zaune a gefenta ba ' hakan yasa ta yunk'ura zata tashi sai jitayi ance.
"A'a, Ki kwanta abunki ' kin d'anji rauni dayawa."
Da sauri Aleeza ta juyo ta kalli mai magana tare da dafe kanta tace.
"Naji rauni? Rauni? How?."
"Amm... Sunana Dr Khalil Muhammad!, Nine wanda mukayi karo da junanmu ' amma ni banji komai ba Allah ya tsare, Kema d'in bakiji ciwo sosai ba saidai buguwa da kikayi."
Aleeza tsayawa tayi tana kallon shi ' shima d'in kallonta yakeyi yana smiling, Hakan yasa tayi sauri ta d'auke kanta tare da cewa.
"Bani phone d'inka inkira Yaya na!."
Khalil ciro wayar shi yayi k'arar IPhone8 ya mik'a mata gamida cewa.
"Meyasa bazaki kira Mum ba?."
"A'a, Banason hankalinta ya tashi ne."
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.
"Ita ya dace ki kira not your brother."
Aleeza ba tare da taimashi gardama ba tayi dialing number d'in Hajiya, Cikin sa'a kuwa ringing d'aya tayi ta d'auka, Aleeza tayi gyarar murya tace.
"Hello Hajiya!."
"Na'am Aleeza ' wannan number d'in waye."
Aleeza kallon Khalil tayi tace.
"Meye sunan wajen nan?."
"Private Hospital Girmi."
Nan ta maida wayar a kunnenta tace.
"Hajiya ina private Hospital Girmi, Kuzo."
"What! Subhanallah ' meyafaru dake Auta?."
Umma ta fad'i haka tare da mik'ewa tsaye.
"Hajiya please ki kwantar da hankalinki ' accident ne but banwani ji ciwo ba."
"Shikenan gamu nan zuwa da yayanki."
Abunda Hajiya tace kenan ' ta shiga kiran Hafiz, Bayan ya fito tsakar parlor ne Hajiya ta sanar dashi komai, Hakan yasa shi matsawa kusa da ita ya zaunar da ita sannan yace.
"Hajiya ki kwantar da hankalin ki, Ki sanya hijab ' ni bara inje intada mota."
Hajiya sawa tayi 'yar aiki ta d'auko mata hijab, Sannan shi kuma Hafiz ya fita harabar garage ya umurci gate man ya bud'e masa gate.
Bayan shigarsa mota ne Hajiya ta fito ta shiga motar suka wuce.
B'angaren Aleeza kuwa tunda ta gama wayar ' taketa juya wayar a hannunta, Shi kuwa Khalil smiling kawai yake sakar mata.
"Tai maki kyau ne?."
Taji tambayar kamar daga sama, Hakan yasa ta juyo ta kalleshi ' sannan ta maida kallonta kan wayar tare da mik'a mashi.
"Idan kinaso ' to nabaki halak malak."
Had'e rai tayi ta wurga mashi wayar shi tace.
"Cemaka akayi banda waya? Kokuwa fad'a maka akayi inada buk'atar wayarka?."
"Allah ya baki hak'uri! Amma meyasa kike yawan tunani?."
"Bangane ba."
"Yes dear, Kina cikin damuwa ko! Hakan yasa kikasha maganin da yafi k'arfin jinin ki which is very bad, Karki sake shan magani irin haka kinji ko?."
Kai ta d'aga mashi cike da shagwab'a idanuwanta duk sun cicciko da hawaye.
"Nima d'in badason raina nasha ba, Hasalima niba ma'abociyar shan kwaya bane."
"To meye dalilin da yasa kika sha."
"Wani nakeso and shi kuma baya sona, Shiyasa kullun nake shiga damuwa."
"It's OK! I can understand how you feel, Amma kibar damuwa aibazaki rasa masoya ba ' ballema ke d'in kyakkyawa ce."
Murmushi kawai Aleeza tayi mai kama da kuka, Sannan yace.
"Can I have your number?."
Ganin bata bashi amsa bane yasa shi dank'a mata wayar a hannunta, Nan Aleeza ta rubuta mashi ta mik'a mashi.
"Thank you dear."
"You're welcome."
"Da wane sunan zanyi saving?."
Yayi tambayar yana kallon fuskarta.
"Aleeza."
"Nice name."
Suna cikin haka ne su Hajiya suka shigo cikin hospital, Nan suka tambayi nurse aka nuna musu ward d'inda take.
Bayan sun shiga ne Hajiya ta zauna kusa a Aleeza ' shi kuma Hafiz ya mik'a ma Dr Khalil Hannu suka gaisa.
"Hajiya ina mai baku hak'uri da abinda ya faru, Nayi k'ok'arin kauce mata abinda yak'i ' kunsan tsautsayi baya wuce ranar sa, To amma Alhamdulillah bataji rauni da yawa ba."
Cewar Dr Khalil.
Hamdala Hajiya tayi ' sannan Dr Khalil yayi musu bayanin abinda yayi causing accident d'in.
"Bari in rubuta maku antibiotics wanda zata ruk'a sha."
Ya fad'i haka yana k'ok'arin ciro paper da pen daga cikin aljihun shi, Aleeza tace.
"Dama a Hospital d'in nan kake aiki?."
Kai kawai ya d'aga mata ya fara rubuta mata magunguna.
Bayan ya gama ne ya mik'awa Hafiz paper d'in, Tare da basu iznin tafiya gida.
Cikin kamala Dr Khalil yayiwa su Hajiya rakiya har inda sukayi packing motar su, Sannan ya juya ya koma ciki.
Bayan shigarsu mota ne kiran Mr-Fauzan ya shigo cikin wayar Hafiz, Hafiz ciro wayar yayi daga aljihun shi yayi receiving gamida da karawa a kunne.
"Hello Babban mutum ya'akayi ne?."
"Aboki so nake kazo muje wajen yarinyar nan ' Mum d'inta keson ganina."
Cewar Mr-Fauzan.
"To yanzu dai ina hospital d'inma amma zan koma gida yanzu in aje su Hajiya, Sai inzo mutafi."
"Hajiya ce ba lafiya?."
"A'a Aleeza ce k'anwa ta, Bari dai idan naje gida zan kira ka."
OK kawai Mr-Fauzan yace ya kashe wayarshi.
Mr-Fauzan aikinshi ya cigaba dayi a office hankalinshi kwance.

*AROUND 5:00PM*

Mr-Fauzan ganin haryanzu Hafiz bai iso bane yasa shi sake kiranshi a waya, Cikin d'an k'ank'anin lokaci Hafiz ya d'aga wayar.
"Haba Hafiz! Kaifa naketa jira since, Wallahi na k'osa inbar company d'in nan inbarwa P.A aiki."
"Ohhh so sorry Aboki, Sam na manta wallahi ' gani nan zuwa yanzu."
Abinda Hafiz yace kenan ya kashe wayar ya fito daga cikin gida ' ya shiga mota yaja zuwa Company d'in Mr-Fauzan.
Mr-Fauzan kuwa bayan sun gama waya da hafiz ne ya kira Sir-Kamal ya dank'a mashi wasu documents akan ya cigaba da aiki sai *9:00pm* zai bar office.
Mr-Fauzan bayan ya kammala harhad'a komai ne ya fito waje zuwa inda yake hutawa, A nan ya zauna.
Zaman shi keda wuya yaji hone, Hakan yasa shi juyawa domin yaga waye.
Hafiz ne ya fito daga cikin motar ' ganin shine yasa Mr-fauzan yin saurin tashi tare da k'arasawa wajen shi suka gaisa.
"Muje ko?."
Cewar Mr-fauzan.
"Eh."
Hafiz ya bashi ansa.
Mr-Fauzan shiga cikin motar Hafiz yayi suka tafi.
Cikin 'yan mintoci suka isa cikin hospital d'in, Cikin sa'a sunayin parking ana kiran sallar magrib.
Saida sukayi sallah tukunna suka k'arasa ciki.
Direct ward d'inda Umma take suka nufa, Cike da sallama suka shiga ciki Safna ta amsa.
Ganin sune yasa ta fara kintsa wajen da kauda kwalin takeaways da sukaci abinci dashi.
Hafiz zuk'unnawa yayi ya gaishe da Umma da jiki ' Sannan shima Mr-Fauzan ya d'an sunkuya ya gaisheta.
"Amm Rumaisa ku d'agamin tabarman nan in shinfid'a musu."
Cewar Safna.
Har su Rumaisa sun tashi Mr-Fauzan ya dakatar dasu ' cike da nuna k'yamata.
"A'a kuma barshi we are OK here!."
Ya fad'a yana yatsine baki tamkar mace.
Ita dai Safna kanta a sunkuye yake ' zuciyar ta babu abinda takeyi in banda suya, Wurin ne yayi tsit nad'an lokaci ' sannan Safna ta d'ago kai ta kalli Umma wacce take kwance don ita tama mance zatayi bak'o.
"Umma ' gafa bak'in nan sunzo."
"Wane irin bak'i kuma 'yan nan?."
"Umma maganar da mukayi dake d'azun mana."
Nan Umma ta yunk'ura cike da ninshi ta zauna.
"Oh Allah sarki ' anyi haka kuwa, To Alhamdulillah sannun ku da zuwa."
"Yawwa sannu Umma."
Cewar Hafiz.
Umma gyaran murya tayi ' ta fara fad'awa Mr-Fauzan tarihhin Safna da yadda danginsu suka juya musu baya Tare da cewa.
"Ba muda gata ' sai Allah, Kuma yaro na amince maka na kuma baka auren Safna ' idan za'a d'aura

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment