Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerar sofa tare da janyo laptop d'inshi zai hau aiki.Mr-Fauzan yana cikin hakan yaji wayarshi ta fara k'ara alaman kira, D'auka yayi ya duba ' ganin Number ce yasa shi tab'e baki gami da cewa."What a trashy!"Ya fad'a gami da maida kallon shi zuwa kan laptop ba tare da yayi receiving call d'in ba.B'angaren Aleeza kuwa zaune take a d'akinta rik'e dawayarta a hannu tana kiran number d'in Mr-Fauzan, amma baya d'agawa."Meyasa bazakayi picking ba? Please pick up my call Fauzan..."Abunda Aleeza taita nanatawa kenan a zuciyar ta, Gami da sake dialing number d'in ' ganin baiyi receiving bane yasa tayin wurgi da wayan saman gado cikin zafin rai.Aleeza kwalla ne suka ciko Idonta ' tayi saurin mayarda hawayen."Wallahi inason shi..."Abunda ta furta kenan, ta bud'e wadrope ta ciro nightgown ta sanya ' sannan ta haye gado taja blanket.*** *** *** *** *** *** *** ****Washe gari...*Da assussuba Safna ta tashi ' ta tada su Rumaisa daUmma, Sukayi Sallah ' sannan Umma ta koma bacci kasancewar ta tashi da zazzab'i.Safna Umarni ta bawa Rumaisa dataje ta fara wankewanke, Ita kuma sai tayi shara daga nan ta d'aura ruwan zafi a murhu domin dama koko.Misalin k'arfe *6:00am*, Su Safna suka kammala aikin gidan ' Safna d'aki ta nufa ta tada Anisa daga bacci."Jeki wajen Rumaisa ta zuba maki koko kisha, Ki kuma wanke baki tukunna."To kawai Anisa tace ' ta wuce, Sannan Safna ta fara yiwa Umma magana cikin siga ta tausayawa."Umma?."Umma d'an motsawa tayi tare da sakin ajiyar zuciya."Umma, Ki tashi kisha koko ' daga nan sai inje chemist in anso maki magani."Umma tashi zaune tayi ' tana shivering, Safna ta fita cikin hanzari ta d'iboma Umma kokon a cup ta kawo mata."Gashi Umma! Ki daure ki shanye ' kinga ko suga bansa ba, Ni bari inje chemist d'in insiyo maka magani.""Toh."Abunda Umma ta iya furtawa kenan ' Safna ta d'aukihijabin ta ta sanya ta bar d'akin, Harta kama hanyar fita sai kuma ta dawo."Rumaisa! Ku tashi ku koma d'aki wajen Umma, Donbatajin dad'i."Rumaisa da Anisa, Tashi sukayi suka koma d'aki wajen Umma ' Sannan Safna ta fice.Kai tsaye Safna ta nufi chemist aka harhad'o mata magun guna kala kala sannan ta juyo ta kama hanyar dawowa gida.Cikin sauri take tafiya ' daka ganta kasan a uzurce take.Bayan ta dawo gida ne ' ta kaima Umma magun gunan had'e da ruwa tasha.Haka Umma ta ansa tasha maganin ' tukunna ta koma ta kwanta, Safna dasu Rumaisa sannu kawai suke mata tana ansawa agajiye.Safna kwantawa tayi k'asa saman tabarma ' tare da cewa."Rumaisa bari ind'an runtsa, Nad'an lokaci."To kawai Rumaisa tace, Sannan Safna ta fara bccinta cikin kwanciyar hankali.*AROUND 11:30AM*Hafiz yazo gidansu Mr-Fauzan tare dayin packing motar shi a packing space, Sannan ya ciro waya yayidialing number d'inshi.Mr-Fauzan na zaune a garden d'inshi yaga shigowarkiran Hafiz cikin wayar shi, Nan yayi receiving
call gamida karawa a kunne."Ya! Kaifa gani na k'araso cikin gidanku yanzu.""OK, just give me 5minutes ' gani nan fitowa."Mr-Fauzan cikin gida ya shiga ' direct ya wuce d'akinshi ya bud'e side drower ya d'auko bandir d'in y'an dubu sababbi fil, Ya fito wajen dashi a hannu.Bayan ya isa wajen Hafiz ne suka gaisa ' tukunna ya mik'a mashi kud'in tare da cewa."Behave well!.""OK."Abunda Hafiz yace kenan, Ya shige motar shi yaja ' ya wuce, Sannan Mr-Fauzan ya juya ya koma gida.Koda ya shiga gida kai tsaye ya wuce part d'insu Mummy, Bayan sun gaisa ne Mummy tace."Son? Kunfara magana da Nafee kuwa?.""Oh Mummy come on! Nifa bazan auri wannan ' mara tarbiyar ba."Cewar Mr-Fauzan.Mummy zaro ido tayi cike da mamaki and at the same time tare da nuna b'acin ranta."What!!! Son? Yarinyar k'awar tawa ce mara tarbiyya?."Mr-Fauzan sunkuyar dakai yayi ' gami da nuna ko a jikinsa."OK! Lallai zan sanar ma Daddynku bari ya tashi bacci, Tunda ni bakajin magana ta yanzu."Mr-Fauzan tashi yayi yawuce ' Mummy ta bishi da kallo, Kai tsaye ya nufi kitchen ya bud'e fridge ya d'auki yoghurt domin kuwa yunwa yakeji ' kasancewar baiyi breakfast ba.Mr-Fauzan harya d'auko ya juyo zai bari kitchen d'in suka had'e da Nafee itama zata shigo kitchen d'in.Wata fitinanniyar rigar bacci ne a jikinta ' wacce takeiyakarta gwiwa gata armless, Mr-Fauzan tunda ya kalleta sau d'aya ya d'auke kanshi daga kallonta zai wuce ' ta tsaida da cewa."Good morning ' Sweetheart.""Morning."Ya fad'a yana tafiya bata tare daya juyo ya kalleta.Ganin haka yasa Nafee yin smiling gamida girgiza ' tace."Zakazo hannu."Abunda tace kenan ' ta k'arasa cikin kitchen d'in itama ta d'auki yoghurt ta nufi bedroom d'in Mr-Fauzan dashi.Nafee shiga tayi ba tare da tayi knocking ko sallama ba, A zaune ta iske Mr-Fauzan rik'e da yoghurt hannu d'ayan hannun kuma yana danna laptop dashi.Mr-Fauzan tsayawa yayi yana kallon ta ' daga bisanikuma ya kauda kanshi, Tare da cewa."Get out of my room! Now."Ya fad'a a uzulce."Why?."Tayi tambayar tana k'arasowa tsakiyar d'akin.Ganin haka yasa Mr-fauzan mik'ewa tsaye cikin b'acin rai."Don't you dare come near me!.""Meyasa bazaka bi umurnin Mummy ba? Meye aibuna?."Mr-fauzan ganin zata b'ata mashi lokaci ne yasa shi fizgota suka nufi bakin k'ofar."Get out! And be out of my life forever."Yana gama fad'in haka ya bud'e kofar ya tunkud'a ta waje, Sannan ya rufe k'ofar shi ya koma ya zauna.Nafee juyawa tayi ta koma d'aki tana dannan hannun ta inda ya rik'eta, Ba k'aramin zafi wajen ke mata ba."Dole sai na gasa wajen."Abunda nafi tace kenan ' ta tashi ta cire rigar baccin jikin ta ta d'aura towel, Sannan ta shige bathroom._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad *....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**28-29*B'angaren Safna kuwa ' baccinta kawai takesha, Rumaisa da Anisa suna cikin yima Umma tausane sukaji ana sallama ' hakan yasa suka amsa.Rumaisa ce ta tashi tare da sanya hijabin ta ' ta fita.Hafiz ne tsaye a k'ofar gidan, Yayi calming hands d'in shi."Ina wuni."Hafiz jin maganar yayi kamar daga sama kasancewar baiga zuwan ta ba, Hafiz kallon Rumaisa yayi cike da tausayawa yace."Y'an mata ya kike? Ya mama?.""Lafiya lau.""Nan ne gidan su Safna ko?."Yayi tambayar yana kallon cikin idon Rumaisa."Eh nan ne! Yaya tace ma, Bari in kirata."Rumaisa juyawa tayi ta shige ciki ' Hafiz ya girgiza kai alaman tausayawa.Bayan Rumaisa ta shige gida ne ' ta fad'a cikin d'aki jikinta na rawa."Yaya Safna! Ki tashi wani mutum yazo wajen ki ' mai mota."Safna cikin magagin bacci ta tsinci maganar, Hakan yasa tayi firgigit ta farka cike da mik'a."Wai meye? Waye shi?."Cewar Safna."Wallahi wanine dai ' kuma ba wanda yazo jiya bane."Rumaisa ta fad'i haka with full of excitement.Safna mik'ewa tayi ta fito tsakar gida ' ta wanke fuskarta, Tukunna ta dawo d'aki ta sanya hijabi ta fita domin duba wanda ke kiranta.Safna koda ta fita a tsaye ta iske Hafiz jingine jikin bangon gidansu ' yana kallon mutanen da ke wucewa, Hakan yasa tayi mashi sallama ' shima ya amsa tare da juyowa ya fuskance ta.Bayan sun gaisa ne ' Hafiz yace."Nasan dai baki sanni ba ko?."Ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan Hafiz ya cigaba da cewa."Sunana Hafiz Khalif, In short dai ni Abokin Mr-fauzan ne wanda kika tab'ayin aiki a k'ark'ashin Company d'insa."Sunkuyar da kai tayi ' domin sam batason ta tuna darayuwar da tayi awajen."Safna! Maganan da nakeso muyi dake ' inason ki natsu kuma ki fahimceni.""Insha Allah."Ta fad'a a natse."Abokina ne ' yace inzo wajenki domin neman wata alfarma.""Alfarma?.""K'warai kuwa!."Ajiyar zuciya tayi ' sannan tace."Wace irin Alfarma?.""Good! Alfarma ce ta yagani yana so kuma yana so ku daidai ' domin ayi maganar aure."Safna still tayi a wajen ta tana kallon shi ' domin kuwa makamanciyar wannan ranar take jira."Ko kad'an banga laifin ka ba, Domin kuwa kai abokinsa ne ' kuma shi yasan cewa bazan saurare shiba shiyasa ya turo ka kai."Dogon numfashi Hafiz yaja ' yace."Ki kasance mai yafiya Safna... Kasancewar bazai iya had'a ido dake bane yasa shi ya turo ni.""Mutumin da baisan darajar mutane ba? Mutumin dayake kyamatan talaka?."Cewar Safna."Kiyi hakuri ki amince masa Safna, Kuma ki gwada ki gani..."Tunda kafin ya k'arasa rufe baki, Tace."Bazan tab'a iya saka sonshi a zuciyata ba, Balle harna auresa ' domin kuwa tsanarsa ce cike a cikin raina.""Is OK! Na fahimce ki."Ya fad'a tare da saka hannun shi cikin aljihu, Ya ciro bandir d'in kud'in da Mr-Fauzan ya bashi ' ya mik'a mashi tare da cewa."Ga wannan, Ko zaki sai wani abun."Safna kud'in ta kalla ta had'iye miyau don kuwa sunacikin buk'atar su, Lokaci d'aya kuma ta kauda kanta tare da cewa."Ka barshi na gode.""A'a ki karb'a ni da zuciya d'aya na baki."Safna k'in ansa tayi ' shi kuwa ya nace, Suna cikin haka ne Rumaisa ta fito a guje tana haki ' cikin tashin hankali Safna ta rik'ota."Ke lafiya?."Cikin rawar baki Rumaisa tace."Yaya Safna, Umma ne ke aman jini.""Innalillahi!."Hafiz ya fad'i haka, Ganin yadda Safna ta shige gida a rud'e ne yasa shi bin bayanta.D'aki Safna ta fad'a cikin rawar jiki taga Umma rigingine a k'asa tana aman jini, Hafiz d'akin ya shiga shima."Subhanallah this is a critical condition."Safna kuwa hawaye kawai ke zuba daga idonta ' Rumaisa da Anisa ma kuka kawai sukeyi."We have to rush to the hospital, Safna ku kamata asata a mota ' akaita hospital.""To."Ta fad'a, Sannan ita da Rumaisa suka d'aga suka fito waje Hafiz ya bud'e mata motar suka saka ta a back seat."Rumaisa keda Anisa ku tsaya gida ' kafin indawo."Safna ta fad'i haka tana share hawayen fuskarta."Haba, Ya zakice su tsaya gida su kad'ai? Su shiga mu tafi kawai.Cewar Hafiz.Haka kuwa akayi ' Rumaisa ita da Anisa suka zauna a back seat kusa da Umma, Sannan Safna ta shiga front ta zauna.Hafiz zama yayi cikin motar ' yayi saurin tadawa suka tafi, Kai tsaye ya wuce dasu wani babban private hospital ' yayi packing motar shi a ciki tukunna ya bud'e suka fito.Safna ce ta bud'e inda Rumaisa ke ciki suka fito da Umma tukunna Hafiz yayi musu jagora zuwa cikin hospital d'in.Bayan shigar sune ' Nurses suka zo cikin hanzari suka anshi Umma daga hannun su Safna."Please kuyi admitting d'inta kuma kuyi duk abinda ya dace, Kafin inga Doctor d'in."Hafiz ya fad'i haka yana k'ok'arin ciro waya daga aljihun shi, Safna ta tsaida shi tayi da cewa."Bawan Allah na gode da k'ok'ari."Ta fad'a cikin rawar murya ' idanu ciccike da hawaye."Karki damu babu komai, Yanzu dai kije ki sami wajeki zauna ' kafin inga doctor d'in."Safna hannun Anisa ta kama Rumaisa na biye da ita suka sami waje suka zauna a wajen.Hafiz kuwa dialing number d'in Mr-Fauzan yayi ' ringing biyu tayi yayi receiving."Hello! Aboki?."Cewar Hafiz."Na'am Hafiz how far? Ya ake ciki?.""Aiba k'aramar matsala aka samu ba ' in fact madai bata amince da maganar ka ba, And you know what?.""Kai nake saurare ai.""Muna hospital yanzu ' Mum d'inta is in critical condition, Yakamata inbaka Safna kuyi magana.""No! No need of that."Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin gadara."Wai meyasa kake haka ne?.""Hm Hafiz raini ne bana so!!! You know me very well,Kunyi magana da Doctor d'inne?."Mr-Fauzan yayi tambayar."A'a, akwai patients d'inda yake dubawa ne, Idan ya gama zamu sameshi.""OK then, Duk yadda kukayi dashi ' you let me know.""OK."Abunda Hafiz yace kenan ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Cikin sa'a saiga doctor d'in ya fito daga wani Ward.Nan ya tsaya suka gaisa da Hafiz ' tukunna Safna ta taso tazo inda doctor d'in ke tsaye, Nan ta fara mashi bayanin condition d'in Umma.Doctor juyawa yayi ' ya nufi ward d'inda aka kwantarda Umma, Hafiz dasu Safna suna biye dashi a baya.Bayan ya shiga ne ya fara yima Umma y'an dube dube ajikin ta, Sannan yace."Za'a dib'i jinin ta yanzu, Akwai blood test da za'ayi mata da Scanning kafin a tantance abunda ke damun ta."To kawai Hafiz yace ' sannan Doctor d'in ya fita, Hafiz ya sami waje ya zauna kasancewar ba k'aramar gajiya yayi ba.Safna kuwa idon ta na kan Umma wacce take unconscious ' batama san inda take ba, Bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye suna sauko mata."Yaya Safna, Ki daina kuka ' ai Umma zata warke ko?."Cewar Anisa.Safna jin abunda Anisa ta fad'ane yasa tayi saurin goge hawayen, Tare da cewa."Anisa ba kuka nakeyi ba ' karki damu."Suna cikin haka ' aka shigo aka d'ibi jinin Umma, Sannan akayi settling scanning machine ' cikin y'an lokuta k'alilan aka kammala komai aka fitar da duk wani abunda ke damun Umma.Hakan yasa Doctor ya kirasu ita da Hafiz ' sukaje Office d'inshi suka sameshi.Bayan sun zauna ne Doctor ya fara yi masu bayani ' yadda zasu fahimta, Sannan ya k'ara da cewa."Ba komai ke damunta illa hunhunta da kitse ya rufe."Nan gaban Safna ya fad'i, Cikin rawar baki tace."Likita ban gane ba!.""OK!, Ina nufin kitse ya shiga cikin hunhunta, Yayi causing problems da dama ' Sannan kuma aka bata maganin da bai dace da wajen ba tasha! Wanda hakan shine yasa ta fara aman jini.""Yanzu Doctor meye abunyi?."Hafiz
yayi tambayar."Well, Aiki za'ayi mata idan kun amince, Wannan shine kawai solution d'in inba haka ba kuma zata iyarasa ranta ' Kuma wannan aikin yanada buk'atar kimanin kud'i har miliyan d'aya! (1 million)."Safna zaro jajayen idonta tayi wanda suka rune saboda kuka, Tace."Likita ka taimakeni ' ka kuma rufamun asiri, Wallahi ita kad'ai ta tarage mana gashi kuma ba muda kud'i don... "Bata k'arasa ba Hafiz ya dakatar da ita da cewa."Karki damu ' wannan aiba wasu kud'i bane masu yawa."Safna baki ta saki ' tana kallonshi cikin mamaki, Sannan Hafiz ya maida kallonshi kan doctor."Doctor, wannan bazai zama matsala ba ' yanzu dai a d'aurata akan magunguna kafin kud'in su samu.""Alright, To shikenan ' yanzu na baku nan da sati d'aya ku kawo kud'in."Cewar Doctor.Safna da Hafiz tashi sukayi suka bar Office d'in zuwa ward d'in da Umma tace, Safna ta tsaida shi da cewa."Amma a ina zaka sami wad'an nan kud'i?."Ta furta haka cikin sanyin jiki"Safna kenan! Ai kinada inda zakije ki nemo kud'in.""Wallahi babu inda zanje abani wad'an nan kud'in masu yawa.""Akwai!."Hafiz ya fad'i haka, Hakan yasa ta juyo ta kalleshi ' taga fuskar shi babu wasa aciki."Ina kenan?.""Wajen wanda kika tsana ' kika k'i yarda da abunda ya nema a wajenki, Tabbas zaki sami kud'in wajen Abokina Fauzan."Ajiyar zuciya ta saki mai k'arfi, Sannan ta fara tuna halin da Umma ke ciki ' da kuma bayanin da Doctor yayi masu.Cikin Muryar kuka ' tace."Amma kana ganin zai bani kud'in?.""Why not?, Karki damu zanyi mashi bayani ' kuma am very sure zai baki, Yanzu ki koma wajen Ummanki ' zanje indawo."Abunda yace kenan! Ya juya bar Hospital d'in, Sannan itama ta wuce wajen Umma.*** *** *** *** *** *** *** *** ****AROUND 1:00PM*Bayan Hafiz ya koma gida ' yayi wanka yaci abinci, Tukunna ya kira Mr-Fauzan awaya ' bayan ya sanar dashi komai da duk damuwar da Safna ke ciki a yanzu, Mr-Fauzan yace."Zanyi amfani da wannan damar ' in tursasa mata dole sai ta aure ko tana so ko bata so.""Hmm... Aboki kenan bakada dama ' kamar kana sonyarinyar nan fa!.""Oh Come on! Sam babu sonta a raina ' me zanyi da wannan k'azamar? Kawai zan aureta ne don banason Mummy na ta auramun wanda banaso, You know me very well Hafiz."Murmushi kawai Hafiz yayi ' yana jinjina maganar Mr-Fauzan."Yanzu a wane hospital suke?."Cewar Mr-Fauzan."Suna private hospital girmi, And please ka aika akai musu abinda zasuci ' because basuci komai ba.""Alright, Zan tura P.A Kamal, Hafiz inason Monday ka kawo ta Office d'ina."Ya fad'i haka agadarance."OK I will do that."Nan sukayi sallama da junan su ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Sannan yace."Duk abunda ' na buk'ata saina sameshi!!!, Zaki aureni ko kinaso ko bakyaso ' That's Fauzan."Yana gama fad'in haka ya fito daga d'akin shi zuwa garden._we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_@My Bestie~Jameesha..., Wannan page d'in naki ne ' kuma zanyi amfani dashi domin Nuna how muchI care about you! You're just different Besty, You're different indeed... Bari dai inyi shuru saboda sa'idawa!, In short! I love you... _**30-31*Bayan ya zauna ne ' Mr-Fauzan ya d'aga wayar shi ya kira Sir-Kamal, Ringing d'aya tayi ya d'aga."Hello Sir.""Amm... Kamal ' what are you doing now?.""Nothing Sir.""Good!, Inason kaje private Hospital Girmi ' yanzun nan, Wannan yarinyar na nan Mummyn ta batada lafiya, So I want you to go there! Ka siya musu abunda zasuci ' Ok?.""Ok Sir!."Cewar Sir-Kamal."And if you guys need something ' you let me know.""Ok Sir."Abunda Sir-Kamal yace kenan, Mr-Fauzan ya kashe wayar shi.Sir-Kamal mamaki ne ya cika shi ' zuciyar shi na rayamai wani abun daban.Tashi yayi ' ya fito daga gida ya shige motar shi gateman ya bud'e gate, Sannan ya fice a guje.B'angaren Mr-Fauzan zaune yake a garden tunda suka gama waya da Sir-Kamal, Tsuntsaye da furanni kawai yake kallo.Yana cikin hakan yaga Nafee tazo wajen taja kujera ta zauna ' tunda ya kalleta sau d'aya bai sake kallon taba, Nafee gyarar murya tayi zatayi magana ya d'aga mata hannu alaman dakatarwa."Meyasa kika zamo tamkar karya ' wacce batada zuciya?."Kalmar daya fad'i ne ta bugi zuciyar Nafee, Don kuwa abunda tayi hating arayuwarta shine akira ta da karya."Ko ce miki akayi ana so dole? Mum tana deceiving d'inki ne kawai ' amma babu yadda za'ayi na aura wacce bana so."Cewar Mr-Fauzan.Nan Nafee ta sunkuyar da kai ' hawaye na shirin zubo mata, Tace."Fauzan! Inason ka! Kuma nid'in mai k'aunar kace, Ka zageni ka kuma muzantani iya muzantawa ' amma inason ka sani cewa a yau d'in nan zan bar gidan nan naku... Kuma tabbas zan dawo domin saina rama abunda kaimun."Hawayen idonta ne suka zubo ' tayi sauri ta share, Sannan ta tashi tabar wajen.Mr-Fauzan karan kanshi yasan she is hurt, Amma sam baiyi nadamar abunda ya fad'a ba.Haka ya tashi yabi bayanta domin ya tabbar ko dagaske takeyi, Mr-fauzan koda ya shiga parlor a zaune ya iske Mummy da Daddy suna fira, Nan ya sami waje ya zauna shima.*After 5minutes...* Nafee ta fito along with her trolley' Khairat nabiye da ita abaya sai faman bata hakuri takeyi, Ganin haka yasa Mr-fauzan yatsine baki tare da nuna halin ko inkula.Mummy ne da Daddy suka mik'e tsaye cike da mamaki."Nafee lafiya?."Cewar Mummy."Mum! Ina d'aki fa naga tashigo tana kuka, Sannan tace mun ita gida zata wuce yau she will no longer stay with us again."Khairat ta fad'i haka cikin damuwa."Nafee? Lafiya? Ko mun maki wani abun ne?."Inji Mummy."No ni bakuyi mun komai ba, Nidai kawai inason in tafi gida yau am tired."Nan Daddy ya shiga cikin maganar."Nafeesat, Zo zo ki zauna nan muyi magana."Nafee sakin trolley d'in nata tayi ta sami waje ta zauna, Sannan suma suka zauna."Inason ki fad'amun dalilinki nacewa zaki wuce gida yau!.""No reason! Ni dai kawai I just want to go home, And please don't stop me."Daddy ajiyar zuciya yayi ' tare da girgiza kai."Shikenan Nafee bari insa driver ya kaiki."Mummy ta fad'i haka tana k'ok'arin mik'ewa tsaye, Nafee ta tsaida ita da cewa."Na riga na kira driver d'in gidanmu and am sure thathe's on his way now, Nagode da hallaccin da kika nunamin."Nafee na gama fad'in haka ta mik'e tsaye tare da jan trolley d'inta ta fice, Nafee cen wajen gate ta nufa ta bud'e, Sannan ta fice ' nan ta tsaya tana jiran driver d'in gidansu.B'angaren Mummy kuwa tunda Nafee ta fice ' take kallon Mr-fauzan, Tasan cewa duk yadda akayi he isresponsible."Son?."Mr-fauzan kai ya d'ago ya kalleta ' idon shi kawai ta kalla taga rashin gaskiya k'arara."Me kaiwa Nafee?.""Mum! Ta fad'a miki naimata wani abune?.""Son! Nasan abunda zaka iya da abunda bazaka iya ba, Haka nan kawai Nafee bazata ce zata wuce ba.""Mum, Kawai fa na fad'a mata gaskiya ne ' cewa bana sonta, Nothing else."Mr-fauzan ya fad'i haka tare da maida kallon shi akan TV."What!!!?."Daddy ya furta haka cikin mamaki."Haba Yaya Fauzan ' wallahi tana sonka sosai."Cewar Khairat."Ke ni abokin wasan kine ko? Sai na kakkaryaki awajen nan ' muddin kika sake sako bakin ki cikin maganar nan."Zumb'uro baki Khairat tayi ' taje kusa da Mummy ta zauna."Wane irin rashin hankali ne wannan? Yarinya tabaro gidansu duk saboda kai!, Sannan kayi wasa da feelings d'inta haka?."Nan Mr-fauzan ya d'an nutsu, Don ko kad'an bayason yaga ya b'atawa Daddy rai."To bari kaji in fad'a maka, Tunda har ka wulak'anta yarinyar nan haka! Na baka nan da 2weeks ka kawomin wacce zaka aura, Idan kuma ba haka ba! To kasa aranka tamkar Nafeesat taga gama matar kace."Nan hankalin Mr-fauzan ya tashi, Sunkuyar da kai kawai yayi ' sannan yace."Daddy ' karka biyema Mum mana, Kuma... "Bai k'arasa abunda yake shirin fad'a ba Daddy ya dakatar dashi ' ta hanyar yimasa tsawa."Fauzan!!, Zaka b'acemun da gani ko saina sab'a maka?."Mr-fauzan tashi yayi ya wuce d'akin shi sumumu tamkar wanda yai k'arya.Bayan wucewar Mr-fauzan ne Daddy yace."Kinji mun ja'iri? Please ki tabbatar kin kira mahaifiyar yarinyar nan.""Insha Allah."Daddy tashi yayi ya wuce part d'inshi, Mummy da Khairat kuma suka cigaba da kallo.B'angaren Mr-fauzan, Yana shiga d'akin shi ya zauna a kujerar sofa tare da jinginar da kanshi yana sauke ajiyar zuciya, Wayarshi ya d'auka datake gefensa ya kira number d'in Sir-Kamal.Sir-Kamal yana restaurant tare da Safna da k'annan ta, Yaga shigowar kiran Mr-fauzan ' d'agawa yayi cikin sauri."Hello Sir?.""Kamal! Ina fatan kayi abunda nasaka.""Eh nayi ' gamu nan ma tare dasu a restaurant, Yanzu zan maidasu Hospital d'in.""Ok ' ka tabbatar kayi abunda ya dace.""Ok Sir."Abunda Mr-fauzan ya furta haka ya kashe wayar shi,Nan Sir-Kamal dasu Safna suka fito daga restaurantd'in gami da rik'oma Umma nata abincin ' domin ta samu taci bayan ta dawo conscious.Bayan sun shiga cikin mota ne ' Sir-Kamal yace."Kinga wannan Restaurant d'in?."Safna ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan yace."To anan na sama miki aiki ' kuma anriga anyi settling komai, Sunci inhar kin shirya zaki iya zuwa Ranar monday!."Safna wani dad'i taji har cikin ranta, Batama son lokacin data bud'e motar ta fito ta tsaya tana kallon restaurant d'inba don kuwa babban restaurant ne.Safna saida ta kai 5minutes a tsaye a wajen ' tukunna ta koma cikin mota."Na gode!, Na gode sosai ' Insha bazan yi maka butulci ba, To amma ya maganar school d'in da kacezaka sani?.""Wannan duk ba matsala bace ' sunce zaki iya zuwa haka nan."Safna juyawa tayi ta kalli su Rumaisa ' da farinciki ya bayyana a fuskarsu, Tace."Rumaisa kuyi masa godiya."Rumaisa da Anisa godiya sukayi mashi tare da nunafarin cikin su a fili, Sannan Sir-Kamal ya tada motar shi yaja suka d'auki hanyar komawa Hospital.Bayan sun isa cikin hospital d'in ne ' yayi packing a gefe, Sannan yace ."Amm... Safna akwai maganar da nakeso muyi dake,Amma ba yanzu ba tukunna ' sai Umma ta sami lafiya .""To."Tace cikin nutsuwa, Sannan sukayi sallama ' ta fito daga motar, Suma su rumaisa suka fito.Sir-Kamal saida yaga shigewar su ciki tukunna yaja motarshi ya wuce.*_Fan's d'ina kuyi hak'uri
da wannan!, kuma kuyi hkr da rashin yin posting in time ' duk da dai dama banyimuku alk'awarin zaku ruk'a samu kullun ba kasancewar nima inada abunyi!!! And then Aisha Inaso ki gane cewa bazan mayar miki da martani ba har saikin je kin koyi yadda ake magana tukunna..._*_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_*Follow me on wattpad @Seemaluv1**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_**_@Been in love ' is something special, Ever since I meet you Samra ' my heart keeps telling me that you are the right person to be with,You are my Sweetheart' my lollipopty. This page is yours kawai..._*_And for you my Besty(Jameesha), Am very sorry, you know I heart you, so inasonku both._*32-33*Bayan shigarsu Safna cikin hospital d'inne ' suka zarce ward d'in da Umma take, Suna shiga suka iskeUmma zaune ita da wata nurse ' tana mata settling drip.Safna dasu Rumaisa waje suka samu suka zauna, Sannan Safna tace."Umma ya jikin?.""Da sauki."Rumaisa da Anisa sannu sukabi Umma dashi, Bayan nurse d'in ta gama ne ta juyo ta fuskanci Safna gamida cewa."Yanzu ansa mata ruwa, Ki tabbatar taci abinci domin akwai wasu magungunan da zanzo inbata."To kawai Safna tace, Sannan Nurse d'in ta juya ta fita.Bayan fitar tane ' Safna ta bud'e ledar da suka shigo da ita, Ta d'aukowa Umma take away

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment