Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balaifina bane ' kunsan al'amarin yadda ciwo yake!, To a yanzu dai na sami sauki.... ( Always in my heart ' baby!..S2😘.)_*

*14-15*

Mr-Fauzan tunda yaja Safna bai tsaya ba saida ya tabbatar sun shiga cikin mutane, Sannan ya tunkud'ata tsakiyar su, Hakan yasa gaba d'ayansu suka juyo suna kallon shi.
Sir-Kamal ya fito kenan rik'e da files a hannunshi zai shiga Office d'in Mr-Fauzan, Yaji surutai ' hakan yasa shi juyawa ya nufi wajen.
Bayan isarshi wajen ne ' ya lura da yanayin da Safna ke ciki, Sir-Kamal harya bud'e baki zaiyi magana yaji Mr-Fauzan yace.
"Attention please!!, Musamman securities ' muddin bazaku rik'a kula da properties na company d'in nan ba to tabbas zan cenja ku in nemi wasu, Look at her."
Ya nuna Safna da yatsa, Hakan yasa dukkansu suka maida kallonsu akan Safna ' wacce hawaye kawai ke zubowa a fuskarta a sunkuye.
"Ta shiga guess-room d'ina da niyyar sata ' domin kuwa aciki na kamata, Shi dama tsiyar talaka kenan! Bai iya samun waje ba, let me warn everyone of you here! Especially securities ' dole ne ku zama masu lura, Idan kuma ba haka ba ' to lallai zan d'auki mummunar mataki.
Muneeba dake tsaye a wajen ne zuciyar ta cike da farin ciki.
"So disgusting!, Nan gaba korar ki za'ayi ma."
Ta furta hakan in murmured.
Mutanen da ke wajen ' daga mai cewa aida ganinta zata iya sai masu suratai kala kala, Safna kuka takeyi sosai ' tana girgiza kai.
Mr-Fauzan nuna Safna da yatsa yayi yace.
"And let me tell you something Ki tsaya ' a matsayin ki kawai zaifi, If not! To kina tattare da wahala arayuwarki ' k'azama kawai."
Yana gama fad'in haka ya juya ya koma office, Safna kam kasa motsawa tayi ko nan da cen saboda kunyar data sha.
Sir-Kamal, Wanda ya dad'e tsaye a wajen ranshi a b'ace cike da tausayawa ne, Ya k'arasa wajenta tare da maida kallon shi akan mutanen da sukayi carko carko awajen.
"Ina son kowa ya koma kan aikin shi ' yanzun nan!!!."
Ya fad'a a tsawace, Hakan yasa kowa ya juya ya koma kan aikin shi.
Sir-Kamal, Files d'in dake hannun shi ya aje gefe ' sannan ya cire Suit d'inshi ta saman ' ya rufema Safna jikinta dashi tare da cewa.
"Kije office d'ina ki jira ni."
Haka Safna ta juya ta nufi office d'inshi a gaban idon shi, Tukunna shi kuma ya wuce office d'in Mr-Fauzan.
Bayan ya kammala duk wani aiki ne ' ya dawo cikin office d'in shi, Ya iske Safna a zaune tana kuka.
Kai kawai ya girgiza ' sannan ya k'arasa ciki ya zauna, Gami da yin gyaran murya.
Safna kai ta d'ago ta kalleshi da rinannun idanun ta.
"Inason ki daina kukan nan haka, Ki fad'amun gaskiyar abunda ya faru."
"Sir, Wallahi babu abunda nayi ' babu abunda na d'auka, Kawai wajen ne..."
Safna k'arashe maganar tayi cikin kuka, Kuka mai tsuma zuciya.
Sir-Kamal runtse ido yayi domin kuwa kukan har cikin ranshi yake jinsa.
"Calm down Safna! Is ok, Na fahimci cewa ya yanke hukunci ne abisa rashin sanin gaskiyar lamarin, But it's ok."
"Sir, Nidai kawai ina ganin ban shigo company d'in nan da sa'a ba, Ina ganin zan aje aikin kawai..."
"What!!! Don't you ever say that again!."
Sir-Kamal ya fad'a cikin fad'a.
"Yau yau da baki aiki ' sannan kice zaki aje? For what reason? Kinsan yadda aiki yake da wuyar samu kuwa? Ko don kinga kin samu cikin sauk'i?."
Safna lura tayi ranshi ya b'aci, Hakan yasa ta sunkuyar dakai ' tare da cewa.
" Sir!, idan abunda na fad'a ya b'ata maka rai kayi hak'uri..."
Ajiyar zuciya kawai yayi ' sannan yace.
"Idan lokacin tashi yayi ' karki tafi ki tsaya ki jirani, Ina hijab d'inki?."
"Yana a d'akin nashi."
"D'aki kuma? Uhm! Guess-room ake cewa."
Sir-Kamal wayar shi ya d'aga wacce ake amfani da ita cikin company d'in, Ya umarci security da su binciko hijab d'in Safna cikin guess-room d'in Mr-Fauzan.
Haka ko akayi ' cikin lokuta k'alilan security man d'in nan ya shigo da hijab d'in Safna cikwikwiye a hannun shi, Tare da cewa.
"Sir, here it is."
"What!!! Haka kaga ya dace ka kawomin shi? Because bakasan darajar hijabi ba ko?."
"Am sorry Sir."
Security man d'in ya fad'i haka, Sannan ya ninke hijabin ya mik'a mashi.
"Ita zaka bawa, Ba niba."
Sir-Kamal ya furta hakan cikin isa.
Safna hannu ta mik'a ta karb'a hijab d'in nata ta sanya a jikin ta, Sannan security man d'in ya juya ya fice.
"Yanzu ki tashi ' ki kawomin coffee."
Safna tashi tayi cikin hanzari ta nufi store ta had'a mashi coffee d'in cikin d'an k'an k'anin lokaci, Sannan ta dawo office d'in ba tare da tayi knocking k'ofar ba ta fad'a.
Safna sallama tayi Sir-Kamal ya amsa, Tukunna ta k'arasa ciki ta aje mashi coffe d'in gami da cewa.
"Sir, Gashi."
Sir-Kamal d'ago kai yayi ya kalleta, yace.
"Sami waje ki zauna!."
Babu musu ta sami waje ta zauna.
Nan yayi gyarar murya yace.
"Safna Habib!."
Ta d'ago kai ta kalleshi.
"Ki kasance mace mai nutsuwa, And in tambayeki?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh.
"Kinaso ki shirya da Ogana?."
"Eh Sir, Inhar hakan mai yuwuwa ce."
"Good!."
Ya furta ' sannan ya d'auki coffee yakurb'a, Tukunna ya cigaba da cewa.
"This your dressing! Dole saikin cenja shi."
Cikin mamaki ta kalleshi.
"Yes! Zaki daina sanya wannan kayan na jikin ki, da wannan hijab d'in."
"Sir! Bangane abinda kake nufi ba."
"Very soon! Zaki gane, Yanzu ki koma kan aikin ki ' After closing karki tafi ki tsaya ki jirani, Ok?."
"Ok."
Tana fad'in haka ta tashi ta bar office d'in ta wuce cikin ma'aikata, Safna koda taje wajen mutane kallonta kawai sukeyi suna zund'en ta. Ganin haka ne yasa ta juyo ta dawo bakin store taja kujera ta zauna.








*SEEMALUV NOVEL'S GROUP*
📚📚📚
[10:29PM, 8/19/2017] Hannatu: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄

Follow me on wattpad @Seemaluv1

*16-17*

Bayan ta zauna ne da 'yan lokuta k'alilan, Muneeba ta iso wajen cike da shan k'anshi taja kujera ta zauna tare da cewa.
"Safna?."
Safna d'ago kai tayi ta kalleta ' ba tare da tace komai ba, Sannan Muneeba tace.
"Ko zaki fad'amun gaskiyar abunda ya faru?."
Cikin mamaki Safna tace.
"Bangane ba!."
"Ina nufin kinyi satar ko bakiyi ba? Kamar yadda Oga ya kamaki, Kuma da yadda naji mutane na fad'a don kuwa kaf workers d'in da ke cikin company d'in nan sun yarda cewa kinyi sata.
Safna nan take idonta ya cika da k'walla tace.
"Muneeba, ni nasan cewa ba sata nayi ba ' kawai dai k'addara ce."
"Well. Ban yadda dake ba Safna, Because dama irin ku sai a hankali."
"Me kike nufi?."
Ya tsine baki Muneeba tayi ' ta tashi tabar wajen, Ba tare da tace komai ba.
Safna girgiza kai kawai tayi cike da damuwa, Tana cikin haka ne lokacin tashi yayi *2:00pm* hakan yasa ta tashi gamida kakkab'e jikinta zata wuce suka had'e da Muneeba ta dawo d'aukar hand-bag d'inta domin wuce gida.
Safna fita daga company d'in tayi taje ta tsaya bakin gata, Harta tsaida mai keke-napep kenan ta tuna da abunda Sir-Kamal yace mata.
"Ohh Sam! Na manta zan tsaya injira wani, Bawan Allah kayi hak'uri ka tafi kawai."
Abunda ta cewa mai keke-napep kenan ta koma k'ark'ashin bishiya ta tsaya jiran Sir-Kamal.
Safna bata dad'e a tsaye ba Sir-Kamal ya fito cikin company rik'e da wasu documents tare da Ogan shi Mr-Fauzan, Sir-Kamal sai da ya tabbatar Mr-Fauzan ya shige cikin motar shi ' sannan ya mik'a mashi documents d'in gami da rufe mashi mota.
Ganin haka yasa Safna k'arasawa inda yake tare da cewa.
"Sir?."
Sir-Kamal jin ankira shine yasashi juyowa a uzurce, Ganin Safna ce yasa shi sakin smiling.
"Yes! I keep you waiting koh?."
Safna girgiza mashi kai tayi ' tukunna yace.
"Alright, Muje toh."
Sir-Kamal k'arasawa wajen motar shi yayi, Sannan ya umarci Safna ta bud'e motar ta shiga.
Babu musu Safna ta bud'e ta shiga ' tukunna shima ya shige, Bayan shigar shine yace.
"Safna, Nasan hankalin ki yana gida ko?."
"Eh."
"Inason in kaiki gida ' da kaina."
"No Sir, da kabarshi ma wallahi."
"Meyasa?."
Yayi tambayar yana kallon fuskarta.
"Gani nayi bazaka rasa aiki ba sosai, Kuma...".
"No ni nasa kaina ai, So just let me."
Zatayi magana kenan yayiwa motar key ' yaja suka wuce, Safna kwatancen k'auyen nasu taimashi, Sir-Kamal mamaki ne ya cika shi jin inda Safna ke zaune.
"Kai!!! Tun daga cen kike zuwa?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh.
"Okay! Insha Allah za'a nemi mafita."
Jin haka yasa Safna ta d'ago kai ta kalleshi, Shi kuwa tuk'in shi kawai yakeyi.
A haka har suka isa cikin k'auyen ' tukunna suka shiga cikin unguwar har k'ofar gidan su Safna.
"Na gode."
Abunda ta furta kenan ' ta juya zata bud'e motar, Sir-Kamal ya tsaida ita.
"Saurin me kikeyi?."
"Am... Babu komai."
"Good! Well, Yanzu kije kawai we will talk tomorrow Ok?."
Kai ta d'aga mashi tare da cewa.
"Na gode sosai."
Safna bud'e motar tayi ta fita ' ta shige gida, Sannan shi kuma yaja motar shi ya wuce.
*WANENE Sir-Kamal?*, A tak'aice Sir-Kamal mutum ne mai kyautatawa iyayen sa ' shi kad'ai ne wajen mahaifiyarsa, Mahaifinsa kuwa Allah yai masa rayuwa...
Sir-Kamal bayan ya koma gida ne, Yayi packing motar shi a packing space ' tukunna ya shige ciki ya iske mahaifiyarsa a zaune tana kallo, Hakan yasa yashiga ciki d'auke da sallama a bakinshi.
Bayan ta amsa sallamar ne Sir-Kamal ya nemi waje ya zauna, Sannan yace.
"Ammi, Yana sameki?."
"Lafiya kalau Kamal, Ya aikin naku?."
"Lafiya Ammi..."
Ya fad'a tare da sauke ajiyar zuciya.
"Kamal ' yau da farin ciki ka shigo, Meke faruwa?."
"Uhm! Ammi kenan, Ai dama kullun haka nake shigowa."
"A'a, ba kamar na yau ba dai."
Murmushi mai k'arfi Sir-Kamal yayi, Sannan ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Uhm! Ammi kenan idan tayi wari zakiji ' yanzu dai kice ma mai aiki ta kawomin abinci na."
Yana fad'in haka ya juya ya haye sama ya wuce d'akin shi.

*AROUND 3:00PM*

B'angaren Mr-Fauzan, Zaune yake a d'akin shi rik'e da pen a hannun shi, Yana duba documents.
Bayan ya kammala ne ya tashi ya wuce garden ' inda yake hutawa ya same waje ya zauna, Yana nazarin ayyukan dake k'unshe cikin company d'inshi.
Yana cikin haka ne Safna ta fad'o mashi a rai, Yana tuna da irin wulak'ancin da yayi mata.
"But i see passion in her eyes!, Tana k'unshe da wasu abubuwa ' dana kasa gane meye su!."
Abunda Mr-Fauzan ya furta kenan a fili, Sam baisan Mummy na tsaye a bayan shiba ' sai ji yayi tace.
"Son?."
A razane ya juyo ya kalleta, sannan ta sami waje ta zauna d'auke da murmushi a fuskarta.
"Son! Wacece wannan wacce naji kana maganar ta?."
"Mummy wa kikaji ina maganar ta?."
"Yakamata ka kawo man ita ' ta gaisheni."
"Mummy ' nifa bakiji da kyau bane."
Mummy b'ata rai tayi tare da nuna fushin ta fili.
"Fauzan! Karka sake ka k'ure ni, Don kuwa inhar ka bari raina ya b'aci game da maganar nan to tabbas zan aura maka wacce baka so!!!."
Mummy na gama fad'in haka ta tashi ta koma cikin gida, Shi kuwa Mr-Fauzan in ranshi yayi dubu ya b'aci, Don kuwa babu abinda ya tsana irin auren had'i.
"I really have to do something!, Dole in nemi mafita."
Abunda yace kenan ' ya tashi ya wuce part d'in shi shima.










*SEEMALUV NOVELS GROUP*📚
*FACEBOOK @SEEMALUV HAUSA NOVELS*
[10:36PM, 8/19/2017] Hannatu: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄

Follow me on wattpad @Seemaluv1

*18-19*

Safna kuwa tunda ta dawo ta shige d'aki, Sam babu walwala a tattare da ita ' Umma ta lura da haka, Hakan yasa ta tashi tabi Safna d'aki ta iske ta a kwance saman gado tayi ruf da ciki.
"Safna?."
Jin ankira sunanta ne yasa ta tashi ta zauna ' tare da cewa.
"Na'am Umma!."
Umma bakin gado ta zauna ' daidai saitin Safna.
"Na lura dake tunda kika dawo ' sam babu walwala a fuskar ki, Kuma baki fad'amun komai game da aikin kiba ' ince dai babu wata matsala ko?."
"Eh babu komai Umma, Aiki kuma Alhamdulillah nasamu."
Safna na gama fad'in haka ta koma ta kwanta.
"Ha'a ya ina magana kin koma kin kwanta, Safna akwai abunda ke damunki fa."
Safna sake tashi tayi ta zauna cike da damuwa, Tace.
"Umma karki damu ' kawai wasu 'yan matsala dana fuskanta yau, Amma babu komai."
"To Allah ya k'ara tsarewa."
"Amin."
Har Umma ta tashi zata fita Safna ta tsaida ita ' da cewa.
"Umma abinci na fa? Yunwa nakeji wallahi."
"Abincin ki ' gayacen a kwano ki d'auka."
Umma taiwa Safna nuni da wani kwano ' dake a k'asa a gefen gado tukunna ta fice, Cikin sanyi jiki Safna ta sauko daga saman gadon ta d'auki abincin ta fara ci da sauri.
Bayan ta gama ne ta fito daga d'akin ta iske Rumaisa da Anisa zaune saman ta barma Umma kuma na zaune a saman turmi tana gyara shinkafa.
Safna bakin rijiya ta nufa ta wanke hannunta ' Sannan ta dawo ta zauna cikin su Rumaisa.
"Umma, Me za'a dafa ne da yamman nan?."
"Gashi kuwa ina gyarawa shinkafa!."
"Yauma shinkafa da mai da yaji?."
"Eh."
Ajiyar zuciya kawai Safna tayi, Sannan ta tashi ta nufi bakin murhu ta hau had'a wuta domin d'aura ruwan zafi.

*AROUND 6:00PM*

Mr-Fauzan na zaune a babban parlor Khairat ta sauko daga saman steps ' tazo ta zauna a parlon rik'e da popcorn a hannunta tana ci.
"Ehen! Bani pop-corn d'in nan inci."
"Haba Yaya don Allah! Bafa shida yawa."
Ta fad'a tana turo baki, Ganin haka yasa shi fizge ledar popcorn d'in gaba d'aya tare da cewa.
"Ni kike turowa baki ko? To aisai kici ingani."
"To nida abuna?."
"Yes!!! Ke da abun naki ' na hanaki."
Khairat ganin baida niyyar bata ne ' yasa ta barin parlon cikin gunguni.
Mr-Fauzan kuwa cin pop-corn yakeyi yana kallon news, Yana cikin haka ne maganar Mummy ta fad'o mashi a rai ' hakan yasa shiyin zambur ya mik'e tsaye tare da dailing number d'in babban abokin shi mai suna Hafiz.
Ringing d'aya zuwa biyu wayar tayi Hafiz ya d'auka.
"Hello Hafiz?."
"Babban mutum! Ya akayi ne?."
"Where are you?."
"Am at home now."
"Good! Hafiz i really need your help, Ya za'ayi inganka?."
Cewar Mr-Fauzan.
"Kazo gida kawai ' sai muyi magana."
OK kawai Mr-Fauzan yace, Sannan ya kashe wayar ya fita zuwa garege ' ya shiga motar shi, Ganin haka yasa mai gadi yin saurin bud'e gate tukunna Mr-Fauzan yaja motar shi ya fice.
Hafiz kuwa tunda suka gama waya da Mr-Fauzan ' yaje part d'in hajiya wato mahaifiyar sa ya sanar mata da cewa babban abokin shi zaizo, Hakan yasa Aleeza wato k'anwarsa yin saurin shiga kitchen ita da 'yar aiki suka fara preparing abinci.
"Wayyo Allah! Dama yace yana sona."
Cewar Aleeza.
"Amma wai daman bak'on kine ko kuwa bak'on Yayan ki?."
Inji 'yar aiki.
"Nidai banason surutu! Kiyi abunda na saki."
Aleeza barin kitchen d'in tayi ta wuce parlor inda Hafiz ke zaune, Ta zauna.
"Yaya Hafiz, Haryanzu abokin naka bai iso bane?."
Hafiz d'aure fuska yayi, Tare da cewa.
"Kinada sak'on da zaki bashi ne?."
"A'a kawai dai na matsune ingansa, Saboda inajin labarin sa ' Allah Yaya guy d'in..."
Bata kaiga k'arasawa ba Hafiz ya daka mata tsawa da cewa.
"Ke! Don Allah kin isheni da surutu, Inma sonsa kikeyi gwara kin cireshi a ranki ' don ba ajinki bane."
Aleeza tashi tayi ta wuce part d'in hajiya tana gunguni.
Aleeza kyakkyawar yarinyace 'yar shekara 19 tana, Cikin wannan year d'in zata gama school d'inta na fannin jami'a.
Hafiz na cikin danna wayar shine yaji tsayawar mota ' a cikin garege, Hakan ya tabbatar mashi da cewa Mr-Fauzan ne.
Hafiz tashi yayi taje ya shigo dashi cikin gidan ' tare da yimashi maraba, Sannan Mr-Fauzan ya nemi waje ya zauna.
"First bari in kira hajiyata ku gaisa, Tunda ka dad'e rabonka da gidan nan."
Cewar Hafiz.
Hafiz wuce part d'in hajiya yayi ya sanar da ita cewa abokin nasa ya iso, Saboda haka ta fito su gaisa.
Hafiza da hajiya tare suka fito zuwa parlor sai kuma Aleeza dake binsu a baya, Koda suka isa parlor Aleeza bata k'arasa wajen ba ' saidai ta rakub'e jikin bango tana lek'en Mr-Fauzan har suka gama gaisawa da Hajiya ta koma part d'inta.
"Wayyo... Allah na! Jibeshi cikin fararen kaya, Wallahi guy d'in nan ya riga ya lashe zuciyata inason shi."
Abunda Aleeza ta fad'a kenan tare da dafe k'irjinta tana sauke ajiyar zuciya, Tukunna ta juya ta nufi kitchen ta iske 'yar aikin sai kai da komowa takeyi.
"Oh my God! Yanzu baki gama abincin ba?."
"Eh, Kiyi hak'uri kinsan halin shinkafa."
Girgiza kai kawai tayi gamida jan tsaki, Sannan ta d'auri trey ta bud'e fridge ta had'a drinks kala kala, Sannan ta d'auka ta nufo parlor d'in dashi a hannu.
Koda Aleeza ta doso parlon idonta na kanshi, Haka ta k'arasa ciki da sallama a bakinta ' dukkansu suka amsa, Sannan Aleeza ta ajiye trey d'in a k'asa daidai saitin Mr-Fauzan.
"Sannu da isowa!."
"Yawwa."
Abunda ya fad'a kenan ba tare da ya d'ago kai ya kalleta, Hakan yasa ran Aleeza ya b'aci ta juya ta wuce tamkar zatayi kuka.
Bayan wucewar tane Mr-Fauzan yace.
"Ehem! Hafiz nazo wajenka akan wata magana ne."
"Fad'amun inajinka."
Nan Mr-Fauzan ya gyara zama, Tare da yin gyaran murya.
"Wato Mummy ce ' take nema ta huramun wuta! Akan lallai saina kawo mata wacce zan aure."
"Fauzan, To meye aciki? Ai kawai malam kayi aure musha biki."
"No please! Ka daina zaulaya! This is a serious issue, Babu matar ne ai."
"Kamarya? Kana nufin duk 'yan matan dake sonka babu wacce taimaka?."
Mr-Fauzan d'an k'aramin tsaki yaja.
"Is ok! I understand your pain, Ya kamata mu sami lokaci mu fitane ' domin kaga wacce taimaka."
Nan Mr-Fauzan yayi saurin taron numfashin Hafiz, Da cewa.
"Ehen! And ita Mummy ta nace dole sai 'yar gidan masu kud'i, And to tell you the truth? Ni gaskiya bazan auri yarinya tazo tana raina ni ba, Su suna da raini ne."
"Eh kwarai haka ne ' suna da wannan, Yanzu dai you know what?."
Mr-Fauzan ya girgiza kai alaman a'a.
"Insha Allah zan zauna ' inyi tunani domin muyi finding solution, Gobe kuma zanzo company d'inka sai a tsayar da magana."
Mr-Fauzan dad'i yaji sosai, Sannan ya mik'awa Hafiz hannu alaman gaisuwa.
"Gaskiya na gode sosai Abokina da time d'inka."
Cewar Mr-Fauzan.
Haka suka tashi ' Mr-Fauzan yayiwa Hafiza sallama, Sannan ya fita ya shige motar shi yaja ya wuce.







*SEEMALUV NOVELS GROUPS*📚*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*® ```Written```By*_Seemaluv_*Follow me on wattpad @Seemaluv1*_Kuyi hak'uri jina da kukayi shuru! Na d'anyi fama da ciwon kai ne shiyasa INASON KU MASOYA NA, i love you too JAMEESHA Wannan page d'in naki ne ke kad'ai..._**20-21*Bayan Mr-Fauzan ya dawo gida ne, Yayi packing motar shi tukunna ya shige cikin gida ' kasancewar bai sami kowa a parlor bane yasa shi wucewa kitchen kai tsaye domin ya zuba abinci.Koda Mr-Fauzan ya shiga kitchen d'in 'yar aiki ya iske tana ta k'okarin kammala abincin."Haba! Me akeyi since ' ba'a gama ba?."Cewar Mr-Fauzan."Kayi hak'uri an kusa gama wa."'Yar aikin ta fad'a tana k'okarin duk'awa k'asa.Mr-Fauzan juyawa yayi ya wuce part d'in, Yayi wanka tukunna yayo alwala kasancewar baiyi sallar isha'i ba.Bayan ya fito daga bathroom ne ya bud'e wardrop d'in kayan shi, Ya ciro jallabiya ya sanya ' sannan yashinfid'a dadduma yayi sallar sa.*AROUND 9:00PM*Safna na kwance a d'aki saman tabarma, Umma da Anisa da Rumaisa kuma suna saman gado suna ' kowannen su yayi shuru yana tunanin zuci."Yaya Safna? Ranar bikin ki ba k'aramin casu za'ayi ba."Inji Rumaisa."Hmm... Lallai Rumaisa zuciyar ki tana fad'a miki k'arya, To Allah dai ya hore mana."Amin dukkan su sukace ' sannan Umma tayi gyaran murya, Tace."Yaro yaro ne ' inbanda abunku, Ai walima tafi rufin asiri ' Allah dai ya baku mazaje na gari."Amin Safna da Rumaisa suka ce."Umma halan Anisa bacci tayi ne, Najita tsit ne."Cewar Safna."Tab wannan ai tunda taji cikin ta ya d'auka shikenan!."Haka su Safna sukaita fira har bacci yayi awon gabadasu.*** *** *** *** *** *** ***Washe gari da sassafe ' wajen k'arfe *7:00am* Umma ta tada Safna daga bacci."Tashi mana! Kinfa makara, Yanzu bakwai tayi fa."Safna najin haka tayi wuf ta tashi cikin hanzari ' ta fito daga d'akin ta nufi wajen rijiya taja ruwa a buta, Sannan ta shige bayi.Bayan fitowar tane ' ta iske Rumaisa a bakin rijiyar zataja ruwa itama."Yawwa Rumaisa jamun ruwan wanka ' don inayin sallah zan shiga wanka.""Da ruwan sanyi?.""Eh mana! To dame kikeso inyi bayan na makara."Nan wajen Safna ta zuk'unna tayi alwala a gurguje ta shige d'aki tayo sallah, Sannan ta fito ta.Safna ruwan wankanta ta d'auka ta nufi bayin, Cikin 'yan lokuta k'alilan ta fito.Tana fitowa ta iske Umma na dama koko, Hakan yasa Safna shigewa d'aki a tsanake ta shirya ' sannan ta kalli agogo taga wajen k'arfe *7:30am*."Ya salaam! Lallai na

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment