Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasha banban da nasauran samarinta ,nashi na dabanne ,amma Dan yacigaba da zaluntar su yaki yabada kai bori ya hau.

Ibrahim yayi Murmishi yace " Haba Autar Umma daga munhada Ido sai kuma kidauke kewai baki yi kewa na bane ba ".

Aisha ta turo baki cike da shagwaba tace " Um ba kai ne ba Yaya kayi ma kowa magana shine ni inata Murmishi da zumudin ganinka,shine kai banza dani ba ai sai nagayama Umma in mukaje gida ".

Ibrahim yayi Dariya tare da rike kunnensa yace " kai na Bisa wuyana Auta natuba wallahi kinga Wanda ya dauke mun hankali nan kinsan Mundade ba mu haduda Brother ba shi yasa ,amma ya zanki kula kanwata taho kinji nayi maki tsaraba ta musan man da ke da duk Wanda kikeso ".

Sai kuma kunya ta kamata ,Fahat yace " yauwa Yaya nine nan Masoyinta Dan Insha Allah ni zandauki Autar Umma Dan haka muje gida abamu tsarabar mu kinji Babyn Yayanta".

Wani tukukin bakin cikine Yakama Nabeel gawani kishi mai zafi da yake tasomasa yawun bakinsa yasoma canza launi yana masa daci kamar ya kai ma wannan Dan shisshigin naushi a bakinsa ganin yana kokarin kara jikinsa da nata yasa shi saurin nufan Mota da sauri yabarsu anan tsaye .
...!

Maman Khaleel
dinkuce......✍️Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rqbee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

Dasunan Allah mai rahma mai Jin kai.

Page 63&64

Aliya tayi Dariya tace "Malam Allah dai ya tabbatar ,dasafe zan ma Salma bayani nasan bazata bamu kunyaba ,kai kuma sai kayima shi uban gayyar magana ko?"

Danjummai ya washe baki yace "hakane Aliya ai harda Yayansa zan ma magana nasan shima zaiji dadi".

*******

A bangaren Nabeel kam tunda yashiga makaranta yake ta raba ido yaga ta ina zai ganta gashi yau yanason ganinta ko zai samu nutsuwa acikin aikinsa da kuma Fefarsa ta yau kuma ta karshe ,ya waiga inda take yin parking din motarta yaganta aransa yace " yau tarigani zuwa kenan yakarasa Department dinsu yau jarabawar tayi zafi gashi da yadora bironsa kan paper hotonta yake gani tanayimasa Murmishi ,da wannan ne ma yasamu kwarin gwiwar rubutunsa bai jimaba yayi Something yafita cike da kwarin gwiwa insha Allah paper tayi kyau ,gurin zamansa ya nufa inda yake zama kullum yasoma wasa da wayansa amma gabadaya hankalinsa yana gunta baya kan wayar ,burinsa yagan ta anacikin haka sai ko yaji Muryarta da kawayenta tana basu labari karaf akunnensa inda yaji tace "hmmm wallahi Asma nayi mamakin ganin sa a gidan mu jiya kuma kinsan menene ?"

Asma tace "a'a sai kin fada kawata".

Aisha takara kankame takaddunta na karatu ta lumshe ido tana Murmishi Wanda yakara fitowa da ainihin kyau wunta dinful dinta ya lotsa tace" muna masa kallon mai girman kai a she ba haka yake ba shi mutum ne mai saukin kai ma a bocin Murmishi kuma shi ingarma ne ,sadauki ne shi mai cikakkiyar haiba ".

Aisha na kaiwa nan Kamshin sa ya cika mata hanci kara lumshe ido tayi takara dai daita takunta suka cigaba da tafiya yau kam koda tazo mahadarsu bata ko Wai wayaba shikam ganinta yasa yaji sanyi a cikin zuciyarsa duk da bai kalli kwayar idaniyarta ba ,Aisha kam takasa kunne taji ko zai kirata amma taji shiru abin yaso yabata haushi amma ta basar ,Asma ta dubeta tace " Esha gafa mutumin can da alama mu yake kallo anya bazamuje mugaisaba ?".

Aisha tayi Murmishi bata ko Wai gaba tace "Asma basshi kawai zamu hadu anjima a gida kingane in ma yana da magana zamuyi ta anjima kuma yagama kauce kaucensa zai zo hannu".

Asma tayi Dariya tace " ai sai Babbar yarinya kina wuta Eeshat din Abbanta ,to bari na wuce gida kinsan nawa Gwaskan yau zai shigo gari gara naje nasoma hada masa kayan tarba.Asma tafada tana Murmishi".

Murmishi Aisha tayi tace "Allah sarki Musaddiq bawan Allah a gaidamin shi da kyau in ya karaso".

Asma tace " Karki damu Eesha Insha Allah zan isar da sakonki ,ahaka kowa ya fada motarsa yamata key suka bar harabar makarantar duk akan idon Nabeel Murmishi yayi ya Mike a fili yace "Aisha Manyan Mata Allah ya mallakamin ke kizamo Uwa ga yarana".

Nabeel shima yasoma tafiya yaci karo da Fa'iza a bakin gate cike da Murmishi tace " a'a Yaya Nabeel manya dama talaka na ganin Ku?.

Nabeel yayi dariya yace "kanwata ya karatun ya su Mama ?.

"Lafiya lau wallahi har kuntashi kenan ?"
Inji Fa'iza

Nabeel yace "wallahi kuwa anshigo ne to Allah ya taimaka karasa kar nasa ki latti ko".

Fa'iza tayi yake tace " ai kuwa hakane kam nagode ka gaida Aunty. Yayi Murmishi yace " zataji Insha Allah ".

********

Gidan su Aisha yau yacika da murna yau Ibrahim Wambai zai dawo daga doguwa tafiyar da yayi ta karo karatu akan aikinsa na masu kula da abincin Dan Adam ,Alhamdulillah Ibrahim yayi zarra aciki aikinsa domin yanzu yazama kwararra a wajen sarrafa abubuwa da dama na abincin da kowani Dan Adam zai ci .

Karfe 5pm dai dai Ibrahim yasauka ababban filin jiragen da ke Kano ,abinka da dangata nan da nan yan uwa da abokan arziki ciki kuwa harda Nabeel a wajen tarban Abokinsa ,Daya bayan Daya Ibrahim yadunka rungume yan uwansa har yazo kan Amininsa Nabeel Wanda ya canza masa yazama dangayu bakar Nabeel din da yasani daba yakara cika da haiba da kamala irin ta mazan Kwarai ,yace " Dan uwa ya kake ya karatu anya kuwa kana kallon Madubi kuwa kaganka kuwa Masha Allah".

Gaba dayansu suka sa Dariya ,Nabeel yace "Kai Aboki baka da dama kaga kasa hankula sundawo garemu muje gida kahuta sai muyi maganar cigaban da muka samu ko ".

Tare suka jero kamar wasu tagwaye sunyi kyau cikin shiga ta alfarma kowannansu,Aisha kam ji take yi kamar itama taje garesu amma ta tsaya a hannun daman Gwaninta Wanda yake azabtar da rayuwarta da Soyayyarsa mai tsayawa a kahon zuciya ,suka hada ido da shi ta kauda kai Dan yanzu tasoma jin haushin sa tasoma zarginsa da zama azzalumi akan So domin yanayin kallon da yake mata yasha banban da nasauran samarinta ,nashi na dabanne ,amma Dan yacigaba da zaluntar su yaki yabada kai bori ya hau.

Ibrahim yayi Murmishi yace " Haba Autar Umma daga munhada Ido sai kuma kidauke kewai baki yi kewa na bane ba ".

Aisha ta turo baki cike da shagwaba tace " Um ba kai ne ba Yaya kayi ma kowa magana shine ni inata Murmishi da zumudin ganinka,shine kai banza dani ba ai sai nagayama Umma in mukaje gida ".

Ibrahim yayi Dariya tare da rike kunnensa yace " kai na Bisa wuyana Auta natuba wallahi kinga Wanda ya dauke mun hankali nan kinsan Mundade ba mu haduda Brother ba shi yasa ,amma ya zanki kula kanwata taho kinji nayi maki tsaraba ta musan man da ke da duk Wanda kikeso ".

Sai kuma kunya ta kamata ,Fahat yace " yauwa Yaya nine nan Masoyinta Dan Insha Allah ni zandauki Autar Umma Dan haka muje gida abamu tsarabar mu kinji Babyn Yayanta".

Wani tukukin bakin cikine Yakama Nabeel gawani kishi mai zafi da yake tasomasa yawun bakinsa yasoma canza launi yana masa daci kamar ya kai ma wannan Dan shisshigin naushi a bakinsa ganin yana kokarin kara jikinsa da nata yasa shi saurin nufan Mota da sauri yabarsu anan tsaye .
...!

Maman Khaleel
dinkuce......✍️
Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 65&66

Aisha tayi saurin ja da baya ta turo baki gaba tana hararar Fahat kamar zatai kuka tace "hava Yaya Fahat haka fa bai dace ba karka kara cewa zaka tabani sai ko ga hawaye sun taho shar- shar ,Nabeel yayi saurin kauda kansa gefe domin jin hawayen yake kamar saukar dalma acikin zuciyarsa ,runtse idonsa yayi Wambaine yaga Aisha da gaske kukan take yayi Murmishi yace " kai Autar Umman nan tafiye shagwaba zonan Nana Aisha rabu da Fahat kinji Muje Mota mutafi gida karki tsammasa tsarabar kinji?"

Aisha dai tayi lamo akafadar mahaifinta tana ajiyar zuciya,bayan sun koma gida anci ansha inda Nabeel ya ware kansa a dakin Ibrahim ya kwanta yana ta tunanin wannan Dan shisshigin shi waye wannan ?ya suke da shi da zai rungumo masa mata? ,kai gaskiya zanjamasa kunne karyakara kuskuren tab'a ta Dan kuwa wallahi wataran zai iya naushin kowa akanta.

(Hmmmm gaskiya ne Jarman Aisha to ka fito mata a zahiri kai ma kakamu mana in ko ba haka to kanaji kana gani to ba Fahat ba wani ma zai fito mata a irin wannan siga kuma da zarar ta amince shikenan sai inga ta Jan aji Mqlam Nabeel).

Kai Maman Khaleel kin soma dawo dani daga nannauyan baccin da nake kin kawo shawara zan jaraba nagani inkuma wani ya rigani to sai inja baya nikuma na nemi dai dai ni.

Karasa maganar sa yayi dai dai da sallaman Aisha a bakin kofa wadda take dauke da wani katon ture ,sai da tai sau uku kamin ya amsa tare da zuba ma kofar ido yace "Bismillah "

Aisha ta aje turen ta bude dakin tare da wata yar siririyar sallama avakinta ,acikin wata Murya wadda shi kansa bai San yanada ita ba ,yace "Amin wa'alaikissama ,ya fada yana Murmishi".

Kai Aisha ta sunkuyar ta aje ture tare da fadin "sannu da hutawa ga abinci inji Umma".

Nabeel Wanda yasoma rasa nutsuwarsa da salon Aisha yakafeta da ido ta canza shiga dazu doguwar rigace a jikinta baka tayi rolin din gyalen kai kace bakuwar balarabiya ce a Nigeria, duk da fuskarta bavu wani Makeup amma tayi kyau sosai ,haka ma shigarta ta yanzu tafi ta dazun yima ta kyau domin atamface kirar Gana kalar ta amshi fatar ta dinkin riga da zani ne kayan sun mata cas gata da dukiyar Fulani masha Allah sun tsaya d'as da su acikin rigar gashi tasha Makeup tasha d'aurin d'ankwalinta na zamani gaskiya wannan shigar tafi komi burgesa duk da yasaba ganinta cikin wannan kayan amakaranta amma nayau ya sha banban da na kullum,gaskiya yaran Hausawa insukai shiga irin wannan to tabbas suncancanta ayabamusu domin girma da cikar zati iya kwalliya babu kamar matar Bahaushe,sunkai wajen minti 2 a haka babu Wanda yace ma kowa komi ,kowa ya zurma cikin duniya tunani .

Shine ya katse shirun da fadin" to sannu da kokari Autar Umma nagode sai dai sauranki Abu daya kizubamana sannan kizauna muci tare Dan da alama murnan ganin Yaya tahanaki cin komi".

Aisha ta dago idonta sukai ido hudu da shi wani yar taji yatasomata tundaga babban danyatsanta harzuwa tsakiyar kanta, ya daga mata gira yace "Um kin kafeni da ido kamar zaki sacen zuciya, ko bazaki ci abinci da maraya bane kuma talaka ?".

Aisha tayi saurin dauke kanta tace " ni fa bana sata kuma ni bance ma ba ..um..um!".

Gyara zama yayi yace" um hum bakice meba ?".

Aisha ta soma wasa da y'anyatsunta Wanda tai masu ado da Jan lalle,wadanda suka dauki hankalin Nabeel kamar ya jawo hannun yakai masu kiss masu zafi koyasamu sassaucin zuciyarsa duk ta bi ta kashe masa jiki, tace" ni fa bance na rai nakaba ai talaka da mai kudi duk daya suke awajen Allah Dan haka kadai na fada kaji Yaya ".

Aisha ta fada cikin wata murya mai sanyi.

Nabeel kam kalamanta sun matukar bashi mamaki yace " to nagode da kika fahimci haka ,oya to matso kizuba mana duk abinda kikeso sai muci".

Aisha ta matso tasoma bude kular farko tace "ni alkubus zanci nazuba ma ?".

Nabeel ya gyad'a kai duk da bai tabaciba Dan ba cimar Jasawabace ,ta soma zubawa awani plate Wanda tagogeshi da Dan karamin towel wani ni'imtaccen kamshin ne ya ziyarci hancinsa alkubus din yayi kyau a ido sosai kamar alale bude wajen 8 sai kuma ta dago da niyyar tambayarsa takasa saboda kamashinda tayi yana kallonta ,aranta tace " Ashe barayin suna da yawa"amma azahiri tace "am am nabarshi haka ko nakara?".

Murmishi yayi yace " To basshi haka kinsan ni bakone a cin wannan cimar taku ta kanawa kece zakisa yau naci wannan cimar ".

Aisha tayi Murmishi tace " kuma Yaya inkasoma ci bazakaso ka daina ciba."

Tana magana tana bude kular miyan Ogun wadda taji agushi ga bushasshen kifi da naman rago ya dahu yayi sala-sala acikin miyar...!

Maman Khaleel
dinkuce......✍️
Y'AN UBA NE
( TRUE LIFE STORY)
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 67&68

Ta zuba miyar cikin wani kwanan tangaran mai ban sha'awa tazuba masa ruwa awata roba mai zurfi ta d'an saci kallonsa tace "to Bismillah Yaya ko nasa ma cokali ?".

Nabeel yayi Murmishi yace " bari na naci da Wanda Allah yabani ya kalleta yace mai kike shirin yi?".

Tayi Murmishi tare da juya fararen idonta cikin wani salo tace "Yaya zan zuba nawane nima ."

Nabeel tsayawa yayi kamar wani sakarai yana kallonta cike da burgewa yace "um um ajiye muci tare in ba hakaba to nafasa ci tunda dama ba abincin Jasawabane ba".

Aisha tayi Murmishi dama tanason haka shiyasa yana magana ta ajiye farantin, tacigaba da wasa da yatsun hannunta wadanda tayi masu ado da Jan lalle sun matukar burge Nabeel Wanda yasa alkubus abakinsa yasomata taunawa ahankali wani dadine ya ziyarci kunnensa sai faman lumshe idonsa yake yana budesu ahankali ya saykesu akan na Aisha wadda yakamata tana kallonsa yayi Murmishi yace" matso mana kici kinbarni nikadai ashe da dadi dai abincin naku ,Nabeel yafada cike da zolaya".

Aisha cikin jin kunya tace "ai nagayama Yaya akwai dadi haka suka cigaba da ci Nabeel yana kod'a dad'in girkin Aisha kam taji dadin yabon da yake mata ,yace gaskiya Umma ta iya girki Y'an Mata Allah yasa kema kin iya Dan kinsan babu abinda Namiji yafiso arayuwarsa irin Matarsa ta kasance gwana awajen girki gamida kwalliya da tsafta indai Namiji yanasamun haka to tabbas wannan Mata zatazamo abinso awajen mijinta ,dan haka ina jan hankalinki da ki dage kwarai ki koyi girki Dan kema kizama y'arlele awajensa ".

Ta dago idonta sukai ido hudu yadaga mata gira gamida Murmishin nan nasa mai kashe mata jiki ,tayi saurin sunkuyar da kai ,yace "gaskiya ni dai ina baki shawara Dan karyazo yana koro ma Umma ke gida akan girki".

Aisha ta turo baki cikin shagwaba tace" kai Dan Allah Yaya wai nagayama ina da saurayine kuma in dai sai na iya girkine ze soni to ai na iya kuma wannan ma ai ni da Umma mukayi tayi Alkubus nikuma nayi miya ".

A'a'a kice shidin yayi dace niko zan so naji sunan sa kai inda hali ma zanso na gansa Dan nasoma tayashi murnan yasamu gwanan iya girki koπŸ₯°.

Aisha dai tasoma takaicin ambaton wani da yake shin wai ita bata cancanta bane ya sota koko yayima wata tanadin kansane ita kadai take kidanta take kuma rawarta?shin me kalaman Hubby na suke nufi?".

Aisha !Aisha !!!

Dasauri ta dawo daga Dan tunanin da ya afkata ciki jin ya ambaci sunanta anya baifi kowa iya kiran Aisha ba jin Muryar tayi kamar da yare ya kira sunanta ai batayi auneba yasake fad'in Nana Aisha wai tunanin me kike ko tunaninsa kike ne?".

Aisha tayi Murmishi gamida takaicin kalamansa na karshe tace " kai Ya Nabeel ".

Dasauri yace mai kikace Dan mai mai ta naji Dan vanji sosai ba πŸ§β™‚οΈ.....!

Maman Khalil
din kuce...✍️
Y'AN UBA NE

(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 69&70

Rufe fuska Aisha tayi cikin jin kunya tana Murmishi yace "banji ba sosai fa dan mai mai ta najiπŸ§β™‚οΈ".

Aisha ta dago kanta a hankali sukai ido 4 da shi sai faman Murmishi yake yau gaba daya ya canza mata ya zaman mata wani yaro kuruciyarsa takara bayyana ,gakuma mamakinsa da ya hanata sakat shin dama haka ya iya surutu shine a makaranta yake kamar kurma,iska taji a cikin fararen idonta Wanda azahiri shi take kallo a badini kuma talula duniyar tunani,ta lumshe ido tana Murmishi ,yace haba wannan kallo sai kin gano min munina salon in budurwata tazo kece tafarkon fara cemata ni mummunane ..!.

kai !kai !!!!Dan Allah Yaya ni fa baruwana da shi ga abinda ba ruwana .

Kuma ni ina ruwa na da budurwarka ai nasan kanada y'an mata ba sai kafad'a minba,kuma...!

Assalamau alaikum Sorry Brother Nabeel nabarka kai kadai ko wallahi..sai kuma yayi shiru ganin Aisha a zaune a gefensa ga kwanuka nan birjik alamar yaci ya koshi ,Murmishi yayi ya dubi kanwarsa wadda taci ado yace Autar Umma gaskiya nagode da kika kulammin da Abokina wallahi ina can wajensu Umma ,Aisha taji dadi tayi tunanin fada zai mata da yaganta tare da Nabeel din ta mike badan tagaji da ganin Nabeel dinba tace" to Yaya ni bari nakoma ciki tafada tareda kallon gefen Nabeel Dan taji ko zayyi magana amma sai tajima yace ki gai da Umma kimikamin gaisuwa kamin nashigo ,to kawai tace tafita tareda turen da ta shigo .

********

Nabeel zaune yake a dakin Aunty Mariya wadda takawo masa tuwon shinkafa miyar danyar kubewa vako kifi bare kuma nama wai danma ta iya girki yanaci suna hira cikin hirar ne tace "Nabeel nikuwa in bazaka damuba inason ka nemi kanwata Asma'u domin itace dai dai da yanayin rayuwarka na dade ina maka kwadayin Aurenta domin kun yi matukar dacewa da juna".

Ai tuwon da Nabeel yasa abakinsa yagaza hadiyewa da kyar ya samu ya wuce jikake makwut Wanda yasa Aunty Mariya yin shiru badan tarasa abinda zataceba ,tadubesa tace kasha ruwa mana wallahi yau hannuna yaso ya kufce naso nacika gari a tukin".

Da sauri yace hakane kam Aunty yako sha ruwan kamar yadda ta buk'ata ya tsame hannu daga cin tuwon da yake ,tab dijam a na wata ga wata anya Nabeel zai iya hada Mata 2 yadauki mizanin son Aisha ya daura a skeli sannan ya dauki vatun hada Auren sa Asma'u da ake shirin yi shima ya daura batun akan skeli yana aunawa ya jinjina kalaman ta kafin yadaga Soyayyar Aisha Sam bazasu hadu ba Sam wannan abun ba mai yiwuwa bane shin ta ina zai bullo wa lamarin...!

Nabeel bakace komiba wallahi abinda yasa kaji nafada ma naga kai ba mai hayaniya bane haka itama Asma ba tada hayaniya wannan da lilin yasa naga yadace nafada ma amma in kana da wata azuciyarka wadda ta kwanta ma to ba bu damuwa karka boyemin kaji,ni ba matan nan bane wadanda suke tauye wani akan farin cikinsu dan su suji dadi,yarinyar nan kai zaka zauna da ita ba niba, Nabeel karkaji nauyina kafadamin abinda yake ranka.

Wata zufa ce tasoma kelayoma Nabeel ya zaiyi ya budilcema mai sonsa da gaskiya kamar Mariya wadda tarikesa amatsayin Kaninta tabasa dukkan farin ciki tun zuwan sa gidan tamasa abinda ko dan uwansa bai masa shin taya ya zai gujema jininta? Tabbas Asma'u taci a sota domin itama tana da kyau tana da hankali ,sai dai kash! duk da haka Aisha tagama kwashe kaso 90 β„… cikin 100 na soyayyar da yake mata tunranan da yasoma haduwa da Aisha a makaranta tunda idanuwansa suka kyallota yaji duk duniya yagama samun Mata duk da kasancewarta diyar Babban gida yasama ransa indai yana numfashi to zai dage da Addu'a har Allah ya dai dai tasu ,kwatsam sai kuma ya ganta inda bai yi zatoba ,"a ina wannan Aishan take Nabeel?"

Tambayar da Mariya tajefoma masa kenan wadda kuma tadawo dashi dogon tunanin da ya afka,Wanda baisan zancen zucinsa ya fitoba.

Kai yasoma shafawa cikin in da in da yace "am ..am.. Aunty mubar maganar Aisha muyi ta Asma'u na amince zan Aureta".

Murmishi Mariya tayi tace Nabeel kenan nifa ba yarinya bace da Aisha da Asma'u duk d'aya na daukesu dan haka mubar batun Asma'u na janye domin bazan zamo Azzaluma ba akan zuciyoyinda suka dade a cikin kogin so ,Nabeel a shirye nake na goya ma baya akan dukkan abinda kake so ".

Wani farin cikine mara misaltuwa yagama cika ma Nabeel zuciya ya kuma jin Mariya takarasamun mazauni na musanman a cikin zuciyarsa,bai boye mata komiba gameda labarin Aisha sai dai Aunty har yau nakasa fadamata ina sonta,Aunty kinga tunda bansanar da ita ba to gara na Auri Asma a hankali zan roki Allah ya yayemin son ta,Aunty ina son Asma sosai ba tunyauba tunkamin ki firta hakan gareni Aunty ".

Mariya taji dadin kalaman Nabeel na karshe amma duk da haka zataso ya Auri Aisha domin Auren Aisha shine zaman lafiyar kanwarta a gidan Nabeel in Allah yaso ,ta nisa tace Nabeel a labarin da kaban na Aisha kamar itama tana sonka ,sai dai kai ne namiji kasan mu mata munada kawaici indai muna son abu bare so kaine zaka fayyacemata abinda yake ranka kamin wani yazo ya shiga gaban ,ka kula da abinda ta fiso sai ka dunga kyautata mata ta wannan fannin shima zai tai maka ma wajen jawo mata hankali zuwa gareka,kazama namiji mana kana namijin da kowa yaganka sai ya ji ina ma yasameka a matsayin mijin Aure ,dan haka kayi hanzarin nuna kanka.

Yace to Aunty nagode sai dai fa ina ga Nabeel fa zai hada Taura biyu a baki yafada yana mikewa tare da Murmishi a fuskarsa ,yace zanyi hakan insha Allah sai da safe yana kaiwa nan ya juya yanufi dakinsa Wanda Yakama anan gaban gidan Yayansa ,ko da yaje gida y'an matan kawai yake gani a idonsa tabbas ya dauko abinda zai fi karfinsa anya zan iya hada mata 2 zanko iya kwatanta adalci kuwa atsakanin su ina son Aisha da yawa ga Asma'u itama ina sonta ko dan nafaranta ma Aunty itama ina sonta ,Murmishi naga kawai yanayi har bacci ya daukeshi mai dadi mai cike da mafarkai kala kala .

A bangaren Aisha kuwa kullum da tunaninsa take kwana take tashi gashi kwana 2 nan tana yawan mafarkin Nabeel da wata mace tarasa gane kan mafarkin ,kamar dai yau cikin mafarkin ta hangi Nabeel da wasu mata guda biyu anata rigima kowacce na ikrarin Matarsace rigima ake sosai shikam yana gefe yayi tagumi bai ce masu komiba sai gata tafito daga wani daki tana dauke da Kofi na ruwa ta dunfaro shi yanaganinta ya mike yanata Murmishi ya miko mata hannu zai karba kenan sai Matan nan suka juyo a fusace daya daga cikin matan ta kabar da ruwan hannunta nan fa kokawa ta kwace da kyar Nabeel ya kwaci Aisha yayi ma Matan nan Jan ido yajata daki yana lallashi,tana cikin Mafarkin ne Umma ta tasheta shin suwa ye wad'nnan Matan? kalman da Aisha tarasa mai bata amsa dakyar tamike daga kan gado bayan tayi sallah tadade tana rokon Allah akan Allah yabata Nabeel amatsayin miji na har abada.

*****

Nabeel zaune yake a ma aikatar da yake Service aiki yake kanjiki kan karfi yana ta faman cike ta kaddu na cinikin da Company yayi bayan yagama yadauki Wayan sa ya soma neman layinta bugu 2ta d'aga yaji tace Assalamu alaikum warahmatullah ya ma'abocin Murmishi ........!.

Maman Khaleel din kuce ....✍️
Y'AN UBA NE

(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 71&72

"Bugu 2 ta dauka tace Assalamu alaikum warahmatullah ya ma'abocin kyau da Murmishi".

Murmishin ko yayi kamar yana gabanta yace " wa'alaikumussalam warahmatullah kanwata kina lafiya ya Umma ?"

Aisha tayi wani juyi akan makeken gadonta gami da yin wani fari da idonta tace lafiya lau take Yayana ya aikin ?".

To aiki badadi Aisha gashinan bayana ya gaji babu mai min tausa koda nadawo gida kai gaskiya yakama ta nasamu abokiyar rayuwa ko

Please Login or Register in order to submit comment