Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana da hankali duk da itadin bawata bace amma tana da kyau sai dai ko rabin kamota batayi ba ko da yayi emerging din hoton fuskarsu,kowacce da nata kalan kyau din amma ita din ta dabance a zuciyarsa,yazama dole yakara gyara zamansa Dan samun cikan burinsa na karatu,gashi yanzu yana level 3 sun kusan zuwa bautar kasa ,ga Ibrahim bai kasarnan yatafi karo karatu a Egypt bashi da wani shakikin abokin da ya wuce shi,shine Amininsa kuma Dan uwansa,gashi ya kwana biyu bai kaima iyayensa ziyaraba,Wanda suke a yanzu iyayensa haihuwarsane kawai su Umma basuyiba,domin samun gida irin na Wambai sai antona Dan kuwa sunsan darajar Dan Adam,yamike ya kashe komi na wayan, yasa a aljihu ya leka cikin shagonsu yace "Oga zani gida sai in Allah ya kai mu gobe".

Oga Danjummai yayi Murmishi Dan ko yanxu yagama gane Nabeel yanxu shine shi acikin shagonsu dan kuwa yakawo masa abubuwan cigaba da dama,yadubi Nabeel yace " to Allah ya kai mu ka gaida mutan gidan".

"To Oga zasuji insha Allah".

Nabeel bai zame ko ina ba sai gida yau kam jinsa yake gashinan dai bayan yayi wanka yashirya cikin wani yadi skyblue yana da manyan Zane yadin harkana iya hango fara kal din singlent dinsa,yasa takalminsa Baki mai yatsa kirar Italy bai sa hula ba,amma in ka gansa kamar kasa cesa kagudu dan kyau ,kunsan su Maza Allah yamasu kyau na Musanman Wanda ko mai kawai suka shafa suna da wannann sihirtaccen kyau din.

Yafito sai tashin kamshi yake, Aunty Mariya wadda take zaune yana cin tuwo ga yaranta nan wadanda sums sun soma zama yan Mata, sun sata a tsakiya,wannan abun bakaramin yima Nabeel dadi yayi yakarajin shima din yanxu namijine Wanda yakamata shima yanxu yakasance yana da iyali,to wacece gwanar amsar dai a yanxu babu dan bai da budurwa ko ta wucin gadi,Mariya tace yadai Angina tunanin me kake ne yasa inata magana amma ba amsa?."
Nabeel yayi Murmishi yace kawai natuna gida ne yakamata ma in samu lokaci naje Jos".

"Gaskiya ya kamata kam Nabeel yanxu sai ina ?".

Cewar Mariya

Yayi Murmishi yace "yau ina son zuwa na dubo Umman su Ibrahim ne nakwana 2 banlekasu ba shine yau nake son zuwa na gaidasu".

Mariya taji dadi tace "to ka gaidasu da kyau kaji kuma banda kallon yan mata dan nayi ma kamu,in kadawo kazo kaji kowacece".

Murmishi kawai yayi yace" to Aunty Mariya andawo naji wacece kika zabamin dan kuwa ni Nabeel amma bari dai nadawo ma tattauna.

Mariya yayi Dariya tace "adawo lafiya".

Yace" to Aunty Allah yasa".

Ko da zuwan Nabeel gidan su Ibrahim yasamu mai aikin gidan Wanda yake ba Flawa ruwa ,yafito dauke da kulan abincinsa dayake Nabeel yasan ma aikatan gidan sosai saboda wani lokacin in yazo kamin Ibrahim yafito to zai tsaya anan suyi ta hira ,Nabeel yace "dan Allah dan uwa in bazaka damuba dan Allah kace ma Umman su Ibrahim Nabeel ya zo ".

Musa'udu yayi Murmishi yace "haba ranka yadade yazakace haka kawai Umarni zakaban naje na ai watar,yanagama fada yajuya Yakoma cikin gida ,bai jima ba yadawo yace tace kashigo".

Nabeel yace "to nagode kwarai dan uwa "

Yasoma tafiya bai zame ko ina ba sai Babban Falon Hajiya Rabi uwa ga Ibrahim da su Aisha tana zaune a kujerarta ta alfarma,Nabeel yashiga Falon bakinsa dauke da Sallama.

Umma ta kara gyara zama fuskarta cike da fara'a ta ke fadin" Lale marhabin da yarona yau Kaine agidan namu Nabeel to shigo mana ka zauna .

Nabeel Wanda shima bakinsa yaki rufuwa ya samu waje kasan Carpet ya sauna ya tankwashe kafa yasoma gaida Umma .....!

Kuyi hakuri da wannan .

Maman Khaleel
dinkuce ✍️.YAN UBA NE
( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Nike da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'an Uba ne

Dedicated to:
Bamu fara Dan mudaina Rubutune mu akidar mu,wani tsarin baya burgemu ,domin ganamu tsarin mu,Arewa Writer's ce a kidar mu ,munrike Allah mafifici domin shike bamu baiwa mu,sharri na mutum da aljan mugu da muwa sukyalemu,gaba dai gaba dai Muje Aunty's Y'an baiwa ,rubutun na dakyau gamida fadakarwar al'umma ,Gashugaba jarima, takware wajen adalci y'arbaiwa.
πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
Kai jama'a muna ta murna da rawa da juyi kungiyar Arewa tacika shekara daya da kafuwa Muna rokon Allah ya mai mai taman wasu shekarun masu albarka yakuma kara hada mana kawunan mu,mucigaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya,Aunty Hauwa ina kara jinjinaπŸ’ͺ.
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 55&56

Ya soma gai da Umma ,yace" Umma munyini lafiya ya gidan da yara?".

Umma ta dubi Nabeel cike da son sa domin Nabeel yaro Dan halak Wanda bai manta Alkhairi, tadubesa tace" Lafiya lau Nabeel ya Su Auntyn naka suke?

Nabeel yayi Murmishi yace "Suna nan kalau tace ma a gaidaki ".

To ina amsawa ya karatun duk da dai nasan yanzu shiri ake na tafiya bautama kasa ko ,wata jahar suka ce za'a turaku?.(in ji Umma)

Nabeel yakara gyara zama cike da ladabi yace " Umma naji ana cewa mu za akai mu Kaduna ne cen wata ma aikatar Gomnatin tarayya.

To Masha Allah Allah ya tai maka,tuni Lami tagama jera masa kayan motsa baki, inda shikuma yake ta Satan kallonta yarunyar tadanyi masa amma Sam batakai ta akomi ba,Umma ta katse masa da tunani da fadin Nabeel kaci abinci bari nashiga ciki ina zuwa .

Nabeel yakara rankofawa yace"to Umma nagode ".

Ta muke ta nufi kicin tadubi lami wadda take ta leken Nabeel ,ta watsa mata wani kallo tace" haba Lami wai yaushe ne zaki waye ne? kin kafe mutum da ido kamar wata sauna ,to bana so yakamata kinutsu ki daidai ta Sahunki,wannan da kike gani Mijin Autane Dan haka ki kiyaye,kinji ko?".

Lami da sauri ta daga kai tare da fadin aiko Umma sundace sa dunka haifo yara farare kamar zabiya Dan kyau.

Umma tayi Dariya tace "ko Lami ?".
" eh Umma sosai ".

Umma ta juya ta nufi dakinta tana Addu'ar Allah yasa Nabeel ya zamo Uban jikokinta da Autanta.

Nabeel yaci ka tunbinsa da tuwon shinkafa miyar Ogun wadda taji bushasshen kifi da naman rago,yasha ruwan gora mai sanyi, ya koma gefe yacigaba da kallon shirin da ake a tashar Arewa ,can yaji motsin bude kofar falon tare da fadin wash Allah Ummana nagaji wallahi Umma ,kinga yau Al..!

Gaba d'ayan su jisu kayi gabansu ya yanke yafad'i saboda ko amafarki basuyi tsanmanin zasu hadu awaje daya ba,cab to wannan gun wa yazo a gidan nan kar dai a ce d'an uwan mune shi bansani ba.

Kallon Kallo suke ma junansu mai cike da tambaya,barkatai shi kam tunanin bai tab'a kawowa cewa ita din Kanwar Ibrahim bace sai yanzu yaga kama tabYAN UBA NE
( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Nike da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'an Uba ne

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 57&58

Shine ya soma dauke Kansas da ga kallon da suke ma juna ,yacigaba da kaollon talabaijin,ya ma yi kamar bai San da mutum ba a wajen.

Aisha wadda jikinta duk yagama mutuwa jitake kamar batada sauran lakka a jikinta ,Lami kam sunmatukar burgeta har take ai yanawa ina ma ace hajiya ta tura ta gidan su aiki da tasha kallon so,da alama suna son junan su,nima. Allah ya kawon mai so na.

Haka lami tayi ta zancen zucinta.

Aisha kam dakin Umman ta ,ta shiga tana wai waye Umma wadda tacika da mamakin ganin Autarta,tasan anriga angama sunhadu tace "Auta lafiya ke da wa kika shigo min daki bako sallama kuma kina ta waiwaye ?".

Aisha ta fada jikin Umma tana Murmishi tace" Umma ba Wanda ya biyo ni sai dai naga bakuwar fuska ki gayamin waye shi Dan Allah Umma,Aisha ta fada cike da shagwava".

Umma tacika da mamaki tace "shi wa kina nufin baki sanshiba?".

Ni dai Umma kigayamin na shiga rudani wallahi tunda nadoso falon ki kamshinsa ya gama cikan hanci da cikina,tare da faduwar gaba ,haka kawai ".

Umma ta dago diyarta tayi Dariya tace " Aisha Autar Umma to wannan da kika gani shine Aminin Yayanki Wanda kika ki kuhadu tunzuwansa na farko gidan nan Sunan sa Nabeel shikenan?".

Aisha taji wani sanyi na ratsata har cikin zuciyar ta,aranta tace suna mai dadi gaskiya yaci Nabeel din yadace da sunan sosai.

Umma Tadubeta tace" ya akai kuma?".

Aisha tayi Murmishi tace "Umma bakomi ,yazo gai daki kenan?".

" Um tundazu ke bari nakoma nabarsa tundazu a falo wai Dan yasake ya ci abinci".

Umma ta mike ta bar Aisha tana ta faman Murmishi har takai kofa ta juyo tace amma yakama kizo Ku gaisa ko kun gaisa ne?".

Aisha ta mike tace "bamu gai saba amma wallahi Umma da kinbarshi wataran ma gaisa ".

Umma tace " ruwan ki kuma tunda ni ban isa ince kiyiba sai abinda ki ke so".

Zaune yake yana ta kallon inda tabi tabbas wannan itace Aisha Auta ,yayi Dariya Mara sauti lalle kan ni Nabeel akwai aiki a gabana anya zan iya ? Anya Aisha bata fi k'arfina ba ,yarinyar da tajiku da Hutu,sannan ince ina sonta, kai zuciya karki kai ni inda a ka fi karfinki ,jani inda zanyi popular acikin zuciyar dai dai ni.Aisha ba Matar talaka bace bare kuma ni Nabeel Wanda nake cin arzikin Mahaifinta, Sallaman Umma ne yadawo da Nabeel dogon tunanin da ya fad'a,ya gyara zamansa tare da Sosa kai,cikin taushin Murya yace "Sannu Umma da fitowa "

Umma tayi Murmishi tace "yauwa Nabeel kayi hakuri nabarka kai kadai ko?".

Nabeel yayi Murmishi kamin yace" kai Umma sai kace bako ai ni ba bako bane".

Ya dubi agogon da ke daure a hannunsa yaga Tara saura minti 5 ,kamar daga sama yajiyo zazzakar Muryar Aisha tana fadin Munyini lafiya Yaya,ya karatu?".

Bai San sanda ya dago kansa ba ya dubeta sai kuma naga ya dauke kai kamin ya amsa da lafiya lau Sister kema yanaki karatun?".

Aisha cikin daburcewa da jin Muryarsa tasoma motsa labbanta a hankali kamin naji itama cikin wata murya wadda Umma batasan Aisha da itaba tace "lafiya lau Yaya nagode".

Nabeel fa yashiga cikin wani yanayi Wanda bai taba shiga cikinsaba yanajin wani abu najansa gareta,yana ayyana masa yaje gareta yazauna dab da ita suna shakar kamshi junan su,haka ma Aisha abin yake yau kam zata iya bacci kuwa dankuwa yau zata raya wannan dare ne da nafilfilu a wajen me saka so acikin kahon zuciyar bayinsa ,yau takasance mata rana ta musan man ya Allah ka mallakamin wannan bawa naka ,ya sa naji acikin wannan faffadan kirjin Dan da alama zayyi dadin bacci....!

Dan Allah masoya na kuyimin a fuwa narashin jina bakuyi a kai a kai hakan yafarune sakamakon karatun da nakeyi wallahi van samun lokaci sosai ga gida ga iyali shiyasa ina kara baku hakuri inasonku masoya na a ko ina kuke Maman Khaleel takuce tanayinku overπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°.

Maman Khaleel
din kuce✍️.bas suna yanayi sosai .

Shine ya d'auke kansa da ga kallonda suke ma juna yacigaba da kallon talabijin...!

Maman Khaleel
din kuce✍️.Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

Daga Marubuciyar:
Habiba
Kishiyar Zamani
Nike da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 59&60

Aisha ta zurme da yawa data ganshi ya mike ,yana fadin to Umma ni zan koma sai ankwana 2 kamin natafi Service zan zo insha Allah .

Umma tayi Murmishi tace "nagode Kwarai Yaro na Allah yama albarka,ka gai da Auntyn naka da kyau".

Nabeel ya rusna yace" to Umma zataji".

Kamar daga sama Aisha taji Umma na fadin "Auta to takama Yayan naki mana zuwa gate? ".

Aisha fa dama abinda a ke nema ,shima bai ce komi ba yasoma tafiya Yana fita Umma tadubi Aisha tace Auta jeki mana karyayi nisa kinsa nafada rashin zuwanki bazaiji dadi ba ,Aisha ta mike cikin sassarfa tayi waje har yasoma yin nisa, gashi tana jin nauyin kiran sunan ,gashi kuma yanata sauri,dataga dai yana ta karayi mata nisa sai ta daddage tace " Bak'on Yaya kajiranima sai sauri kake ko bakason naraka ne?".

Nabeel kalamanta sun bashi Dariya yako dara ya tsaya cak ,yalura yanxu gidan babu yawan jama'a ganinta yayi a gabansa tana ta faman haki,yadubeta kamar wadda tasha tseren gudu kallonta yake sosai,yanajin wani maganadinsun son ta na fizgarsa gareta,ita kam ta sunkuyar da kai Sam batason hada ido da shi,domin batasan shi wani kala bane ,ko amakaranta bata taba yadda suhad'a ido sai dai Satan kallo,domin Nabeel yana da wata baiwa ta musan man gashi da kwarjini.

Sundan sami kamar minti 2 a haka kamin yace "ke ni ba sunana Bak'on Yaya ba,kin gane?".

Aisha ta juyar da kai gefe,cike da shagwaba tace " to ai ban San sunan kaba ".

Nabeel yayi Murmishi lalle wannan tafini tabara,to in tana tunkahon ita Autace shima ai Autane, ko don shi babu Wanda zai mawa ne shine take gwada masa, yakara gyara tsayuwarsa yace " to kisani daga yau Sunana Nabeel Samin ba Bakon yayanki ba dafatan kin gane".

Aisha bata San sanda ta dago kantaba sukai ko Ido hudu,yakafeta da idanuwansa masu sata kasala,Murmishi yayi ,itama tayi Murmishi yace nasan kinji abinda nace Dan haka muje kirakani ki koma gida kar saurayinki yazo yaganmu tare ya sa a ballamin kamafar hagu,narasa da wacce zani gida.

Aisha bata San sanda Dariya ta kufce mata ba tace "wai dako nasha kallon tafiya "

Kallon ta yatsayayi kamar wani Sakarai,in yabiyemata yaga alama sai sukwana anan batada damuwa yace "koma nagode da rakiyar nan kinji sai da safe".

Aisha ta hada rai tace "Um um ba Umma tace narakaka har gate ba shine zaka koreni,kuma sai nagayamata ince korata kadunka yi ,ita kuma tadage akan sai na rakaka".
Tafada cikin shagwaba .
Ta juya tasoma tafiya dasauri ya jawo hannunta tako yi tuntube tatafi luuu!kamar zata fadi,ai tuni Aisha tajita a lafiyayyen kirjin Nabeel yana shafa mata baya a hankali yana fadin amsory Babyn Umma ,nine ko zansa kiji ciwo daga rakiya kuma sai Umma taga Autar ta ta turgude kafa ,to rufamin Asiri naje gida lafiya".

Aisha fa sai faman lumshe ido take tana shakar kamshinsa mai sanyi jitake kamar ta dawwama a haka karyadai na shafa mata baya,ya iya lallashi Sosai .

"To dagani kar nafad'i, Dan kinsakar min nauyinki kuma karkisa ni yau nakasa bacci mana ni ba Mataba".

Nabeel yafad'a ahankali a cikin kunnenta.

Wayyo Allah kunya gamida wani magana dinsun sonsa sune sukataru suka kama Aisha, tasoma kiciniyar kwace kanta ,yakara kai bakinsa saitin kunnenta yace " yi a hankali karkijimin ciwo kinga ni Marayane.....!

Maman Khaleel
din kuce✍️.
Y'AN UBA NE
(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 61&62

"Yi a hankali karkijimin ciwo kinga ni Maraya ne tausayamin kinji".

Tausayi ,da wani mahaukacin Son sa ne suka kara Duran ma Aisha acikin zuciyarta ,a hankali tasoma zare jikinta daga nasa, shikam sai faman lumshe ido yake yanajin wani yanayin da bai taba jinsaba atarin rauywarsa ,Aisha kam tana gama zamewa tayi cikin gida da sauri,babu ko wai waye, abin yaso yabashi Dariya gani sauri kawai take kamar zata tashi sama ,Murmishi yayi Yasoma tafiya yayi ma Baba Mai gadi sallaman sai ankwana 2 gamida ihsanin da yasaba yimasa ,Baba Bello ya amsa yamasa fatan Alkhairi.

A bangaran Aisha kam yau tatsinci kanta cikin wani yanayi na shaukin so ,lalle ta yadda komi kabarwa Allah to zai biyamaka wannan bukatar da ka kai masa wajensa ,kamshin daddan turarensa shikadai take shaka Wanda yakama kayanta gaskiya wannan turaren akwai dadi,Aisha ta fada tare da lumshe ido ,aranan dai da Aisha da Nabeel sun raya wanan dare da nafilfilu wajen rokon Allah ,akan yasama kowannen su ,son juna .

Bayan sun shafane kowannan su ya kwanta ,wani bacci mai dadi ya suresu .

To masoya Allah yabamu alkhairiπŸ₯°.

***********
Nabeel yashirya tsaf yanufi Makaranta kamar yadda yasa ba ,yafito tsaf da shi kai kace dan wani attajiri ne ,nan ko aljihunsa 500 ce kawai kudinda zai kaisa BUK yadawo da shi yakuma samu na abinci koda garau garauce,yafito yaje ya gaida Yayansa Wanda yakara manyanta Sulaiman fa and'an saduda saboda rayuwa tayi masa daurin minti kusan Nabeel din ne ke kula da gidan ,Dan kuwa sauran kannan nasa kam kowa cewa yake bai dashi yanaji da iyalinsa,bayan sun gaisa ne Nabeel yamike yace to sai nadawo Yaya natafi Makaranta daga can zanwuce Tiga daura wani Cage da zamuyi .

Badan yasoba Sulaiman yace "to a dawo lafiya"

Bayan fitar Nabeel Sulaiman yashiga tsinewa Nabeel wai gabadaya yazo yanaso yafi su arziki shidai da yasan hakane da bai daukosaba,gashinan daga shi harsu Salisu ba Wanda ya aje komi har gara ma shi ya tsira da wannan gida to sauranfa ,yayi tsaki gamida fadin ai sai da nace masu sudakata da maganar Aure sukaki ai gashinan suke da wahala ba ni ba ,yanzu wannan marahankalin Salisu wai tabiyu yake nema kai Allah dai ya kyauta".

To Ameen dai Sulaiman.

*****************

Dan jummai zaune yake acikin gidan sa cikin iyalinsa suna hirar aikinsa da Matarsa mai suna Aliya,suna cikin hirar ne Aliya ta sako zancen Nabeel inda take cewa "ni kam Baban Salma da abin nan zai yiwu wallahi nadade ina son akulla alaka mai karfi tsakanin Salma da yaron nan Nabeel ,wallahi ni dai na yaba da hankalin yaron tun yana karami kuma yaro bashida da muwa,dagani irin su Nabeel ake kira Mijin Marainmasa".

Malam Danjummai yayi Murmishi tare da gyara zama yace "Maman yara kenan wallahi nadade ina tunanin wannan al'amari sai dai bansan yadda su yaran zasu dauki abinba kinga wallahi dama nagaji da Samarin shahon da ke zuwa wajen Salma Dan ba Auren bane agabansu,kuma ni yaron sanyin halinsa da biyayyarsa zata nai masa komi ,kai da Salma tayi dace da mijin kwarai tabakin nakine Aliya Salma tasamu mijin Marainiya domin ni nasan waye Nabeel gashi yanzu daukaka tazoma yaron Dan gaskiya nan gaba kadan Zakiji ana labarin Yaron a garin nan da ma Nigeria gaba daya domin yaron yana da Manya yanzu ,dama ni tunda akakawon yaron nan nake cin albarkacinsa na aiki har yau ina ga na dauki yarinya ta na Aura masa,kinga kenan nan gaba kadan zakiji mutanan gari na kirana da Alhaji Danjummai ko uwargida ". Yakarasa maganar yana Dariya.

Aliya ma Dariyar tayi tace" hakane Baban Salma kila ma a fara kaini kafin kai ,tunda ni Mahaifiyace ,kai kuma Babanta ".

"Tab ai baki isa ba Aliya nine mai gidansa kinga kuwa kamin ya kai ki sai ya kai ni " inji Malam Danjummai.

Hhhhhhhh kunfaji mai karatu ,gawata sabuwa nan tana shirin bullo kai ,shin yaza a kwashe idan Nabeel yaji wannan zance ,kuma in baku mantaba Mariya tana son tayi masa wata magana shin wata magana ce wannan ?

Duk sai kunbiyoni gobe in meduka ya kai mu .

Maman Khaleel
din kuce... ✍️Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rqbee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

Dasunan Allah mai rahma mai Jin kai.

Page 63&64

Aliya tayi Dariya tace "Malam Allah dai ya tabbatar ,dasafe zan ma Salma bayani nasan bazata bamu kunyaba ,kai kuma sai kayima shi uban gayyar magana ko?"

Danjummai ya washe baki yace "hakane Aliya ai harda Yayansa zan ma magana nasan shima zaiji dadi".

*******

A bangaren Nabeel kam tunda yashiga makaranta yake ta raba ido yaga ta ina zai ganta gashi yau yanason ganinta ko zai samu nutsuwa acikin aikinsa da kuma Fefarsa ta yau kuma ta karshe ,ya waiga inda take yin parking din motarta yaganta aransa yace " yau tarigani zuwa kenan yakarasa Department dinsu yau jarabawar tayi zafi gashi da yadora bironsa kan paper hotonta yake gani tanayimasa Murmishi ,da wannan ne ma yasamu kwarin gwiwar rubutunsa bai jimaba yayi Something yafita cike da kwarin gwiwa insha Allah paper tayi kyau ,gurin zamansa ya nufa inda yake zama kullum yasoma wasa da wayansa amma gabadaya hankalinsa yana gunta baya kan wayar ,burinsa yagan ta anacikin haka sai ko yaji Muryarta da kawayenta tana basu labari karaf akunnensa inda yaji tace "hmmm wallahi Asma nayi mamakin ganin sa a gidan mu jiya kuma kinsan menene ?"

Asma tace "a'a sai kin fada kawata".

Aisha takara kankame takaddunta na karatu ta lumshe ido tana Murmishi Wanda yakara fitowa da ainihin kyau wunta dinful dinta ya lotsa tace" muna masa kallon mai girman kai a she ba haka yake ba shi mutum ne mai saukin kai ma a bocin Murmishi kuma shi ingarma ne ,sadauki ne shi mai cikakkiyar haiba ".

Aisha na kaiwa nan Kamshin sa ya cika mata hanci kara lumshe ido tayi takara dai daita takunta suka cigaba da tafiya yau kam koda tazo mahadarsu bata ko Wai wayaba shikam ganinta yasa yaji sanyi a cikin zuciyarsa duk da bai kalli kwayar idaniyarta ba ,Aisha kam takasa kunne taji ko zai kirata amma taji shiru abin yaso yabata haushi amma ta basar ,Asma ta dubeta tace " Esha gafa mutumin can da alama mu yake kallo anya bazamuje mugaisaba ?".

Aisha tayi Murmishi bata ko Wai gaba tace "Asma basshi kawai zamu hadu anjima a gida kingane in ma yana da magana zamuyi ta anjima kuma yagama kauce kaucensa zai zo hannu".

Asma tayi Dariya tace " ai sai Babbar yarinya kina wuta Eeshat din Abbanta ,to bari na wuce gida kinsan nawa Gwaskan yau zai shigo gari gara naje nasoma hada masa kayan tarba.Asma tafada tana Murmishi".

Murmishi Aisha tayi tace "Allah sarki Musaddiq bawan Allah a gaidamin shi da kyau in ya karaso".

Asma tace " Karki damu Eesha Insha Allah zan isar da sakonki ,ahaka kowa ya fada motarsa yamata key suka bar harabar makarantar duk akan idon Nabeel Murmishi yayi ya Mike a fili yace "Aisha Manyan Mata Allah ya mallakamin ke kizamo Uwa ga yarana".

Nabeel shima yasoma tafiya yaci karo da Fa'iza a bakin gate cike da Murmishi tace " a'a Yaya Nabeel manya dama talaka na ganin Ku?.

Nabeel yayi dariya yace "kanwata ya karatun ya su Mama ?.

"Lafiya lau wallahi har kuntashi kenan ?"
Inji Fa'iza

Nabeel yace "wallahi kuwa anshigo ne to Allah ya taimaka karasa kar nasa ki latti ko".

Fa'iza tayi yake tace " ai kuwa hakane kam nagode ka gaida Aunty. Yayi Murmishi yace " zataji Insha Allah ".

********

Gidan su Aisha yau yacika da murna yau Ibrahim Wambai zai dawo daga doguwa tafiyar da yayi ta karo karatu akan aikinsa na masu kula da abincin Dan Adam ,Alhamdulillah Ibrahim yayi zarra aciki aikinsa domin yanzu yazama kwararra a wajen sarrafa abubuwa da dama na abincin da kowani Dan Adam zai ci .

Karfe 5pm dai dai Ibrahim yasauka ababban filin jiragen da ke Kano ,abinka da dangata nan da nan yan uwa da abokan arziki ciki kuwa harda Nabeel a wajen tarban Abokinsa ,Daya bayan Daya Ibrahim yadunka rungume yan uwansa har yazo kan Amininsa Nabeel Wanda ya canza masa yazama dangayu bakar Nabeel din da yasani daba yakara cika da haiba da kamala irin ta mazan Kwarai ,yace " Dan uwa ya kake ya karatu anya kuwa kana kallon Madubi kuwa kaganka kuwa Masha Allah".

Gaba dayansu suka sa Dariya ,Nabeel yace "Kai Aboki baka da dama kaga kasa hankula sundawo garemu muje gida kahuta sai muyi maganar cigaban da muka samu ko ".

Tare suka jero kamar wasu tagwaye sunyi kyau cikin shiga ta alfarma kowannansu,Aisha kam ji take yi kamar itama taje garesu amma ta tsaya a hannun daman Gwaninta Wanda yake azabtar da rayuwarta da Soyayyarsa mai tsayawa a kahon zuciya ,suka hada ido da shi ta kauda kai Dan yanzu tasoma jin haushin sa tasoma zarginsa da zama azzalumi akan So domin yanayin kallon da yake mata

Please Login or Register in order to submit comment