Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?".

Ibrahim yayi Murmishi yace"eh ba ita bace, wannan sunan ta lami diyar wan mai aikin Ummana ce Laure,yarinyar batada matsala,tana da hankali,amma Sam ni banfiye son a turon yaran aiki ba nafison komi Aisha tamin ,saboda itace autar mu,hankali yafi kwanciya"

Nabeel ya numfasa aransa yace" ga alama nan nagani,yarinyar tamasa,anya ba ita ko zai aura ba duk da babu batun Aure a tsarinsa yanzu".

Ibrahim ya dafa kafadar Nabeel yace "yadai Abokina,sauko Dan Allah me zan zuba ma kaci? "
Ya bude kulan farko,Sinasir ce wadda taji albasa,kuma tayi irin Jan nan tayi kyau a ido gwanin sha'awa ga kamshi tana fitarwa mai dadin shaka,sai kula ta biyu itace ta danbun kuskus,ga kuma wata hadaddiyar jalof din shinkafa ,wadda taji kayan lambu,sai kamshi kawai ketashi mai dadi,yaka duban Nabeel yana Murmishi yace "wanne zan zuba ma Ogana?"

Nabeel Wanda kamshi ya kusan cika masa ciki,ya dubi Ibrahim yayi Murmishi yace"to yanxu dai zubamin Sinasir domin itace Best Food dina kasan muna makoftaka da Bauci,shiyasa duk inda muka ganta muke bata nata hakkin".

Ibrahim yayi Dariya yace "kuma fa hakane to bada muwa ,amma fa kasan duk sai kaci sauran Dan wannan girkin Dan kai akai yi shi Dan haka Bismillah,ya fada yana me tura masa flet din gabansa,kai kamshin miyar Ogun wadda taji Bushasshen kifi da kashin a waza,mai laushi,taji nama miyar nan,gashi tayi kyau ko a ido,Nabeel ya sauka kan Capet ya zauna yasoma wanke hannunsa cikin nutsuwa,kamin ya damki Sinasir din nan ya kai bakin sa,Nabeel dinka fa yaji wani ni'im taccen dadi ya ziyarci kunnensa,Dan har na hango su kamar suna kadawaπŸ˜‚ ,Ibrahim shikuma ya zuba danbun kuskus yanaci suna hirar da tashafi shi Ibrahim din ,Nabeel kam komi yaci hakika girkin yahadu kamar a hotel a ka girka aransa yace" gaskiya duk wadda tayi girkin nan bakaramar gwana bace domin komi yayi Allah kaban macen da ta iya girki ba wadda ni zan koya mata ba,Murmishi naga yayi komi ya tuna oho,bayan sun kammala suka mike suka nufi cikin gidan Dan yagaida iyayen Ibrahim, da dakin Umma suka fara ,Nabeel fadi yake tsarki ya tabbata ga Allah domin falon Umma ya tsaru iya tsaruwa kamar na wata Amarya,a kujera Nabeel ya zauna inda Ibrahim shikuma ya nufi dakin Umma inda yake fadin "Ummana kina ciki?",Umma tayi murmishi tace" tace eh ina ciki Baba na shigo ina yaron nawa?"
(Wato Nabeel take nufi)

Ya shiga yasamu Aisha wai ita a dole tana Bacci yayi Murmishi,yasan fushi tayi saboda yamata fada dazu,yace "Umma ga shinan a falonki yazo ku gaisa".

Umma ta mike tana fadin to masha Allah tare suka fito Fallon ,Nabeel ya zame ya gaida Umma cikin girmamawa.

"Umma ta amsa da ya mutan gidan ko wa dai lafiya ko?".

Nabeel yace" lafiya lau Umma suna gai daki".

Umma tace" ina amsawa".

Haka Umma ta dunka jansa da hira cikin hikima,Nabeel kam yana bata amsa,sun dade a dakin kamin daga bisani suka nufi dakin Abbansu ,anan akai ma Nabeel karamcin da har ya bar duniya bazai manta da shi va,wato maganar Makaranta,andauki nauyin sa na komi anbiya masa Jam sannan kuma idan yafito an sa ma masa admition na BUK,Nabeel rasa bakin godiya yayi Sai ga wasu hawayen faran ciki suna sauka a idanunsa,gamida godiya .

Abba kam Murmishi yayi yace"haba Nabeel kai ma fa da nane, kamar Ibrahim ka daukeni kamar mahaifinka,Abba yakara da cewa kai Dan inane wait?".

Nabeel ya share hawayen da suka zubomasa gamida Murmishi yace "nagode kwarai Abba Allah ya kara ma dukiya albarka ya kuma jikan mahaifa Ameen".

Abba da Ibrahim harsuna hada baki,wajen fadin Ameen ya Allah.

Nabeel ya kara gyara zama yasomafadin" Abba ni haifaffan Jos ne a nan cikin Barikin ladi,an an na girma,tiryan tiryan Nabeel yasoma ba Abba labarin sa harzuwa sanadin da ya kawo sa nan Kano,sai dai bakomi ya fadamasa ba na gameda rayuwarsa ta nan Kano ba,yabarma Allah wannan, kuma bai kamata ya zubarma da yayansa kimaba a idon
Duniya ba".

Abba yagama sauraren Nabeel tsaf cike da tausayawa ,yayi ma mahifiyarsa addu'ar Allah ya jikanta,ya sa ta huta tare da sauran Musulmai Ameen".

Nabeel kam ji yake kamar yaune akamasa rasuwar,ya amsa da" Ameen ya Allah Abba,nagode".

Wannan shine sanadin komawar Nabeel makaranta.

Aisha kam aranan tadade a falo tana shakar kamshin Nabeel turaren yamata kamshi sosai tanaso takara jin kamshin nan ,sai da yatafi kuma take jin haushin kanta da taki fitowa falon su gaisa,ta dade tana cije labe.

Umma na lura da yanayinta amma ita Sam taki ta kulata,sai dai ita kanta tayi ma diyar tata sha'awar Auren Nabeel domin Nabeel mijine kuma na nunawa sa'a.

Zata cigaba da gayawa Allah akan Allah yama Autar ta zabi da miji nagari,amma gaskiya zataso ta hada zuri'a da Nabeel.

Wannan kenan.

******************

Aisha zaune take a dakinta ta baje takaddu tanata faman juyawa,Sam ba karatun take ba hankalinta na kan wannan Handsome guys din nan,kullum kamar kara rikida yake,tarasa yadda zatayi da kaunarsa,gashi Sam shi Mata da alama basa gabansa,gashi kamar walkiya,in tagansa yau to sai tafi sati basu haduba,yauma Allah ne yayi zasu hadu,sun taho itada da kawayenta,suna tafiya suna hira suna dariya,akan Samira wadda Lekcoran su ya mutu akan sonta,yau kam yabasu tausayi domin yau kasa jurewa yayi saboda yana sonta,yau ya fallasa mata a sirin zuciyarsa, wani kallo da take masa na irin nima na amincen nan shine in muka tuna yake bamu dariya,inda sukai Ido 4 da shi yana zaune shi kadai da handouts a hannunsa yana biyawa ,yayi saurin dauke idonsa daga nata,yacigaba da karatunsa,wai mai yasa yake matay'anmazawulakancine,meyasa shin kodai ita mummunace,da bayason kallonta a duk sanda suka hadu,ko don ya na tunkahon shi din Dan manyane,shiyasa yake min abinda yaga dama? Shin ko dai a jikina,akwai wata tawayane wadda Sam baya so?,mikewa tayi tanufi dress mirror tadunga juyi,tarasa gane makusa a jikinta,amma tanajin yadda su Firdausi suke kwadata in tataho gunsu suna mata kirari da Babbar yarinya,mai ruda y'anmaza,anya ba zolayata kawai sukeba?,kai to ai kullum Mustapha cikin yaba kyawuna yake,ya Allah ina rokon ka kacire mun wannan bawan naka,kar nayi Son maso wani.

Maman Khaleel
dinkuce✍️ .Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

Daga marubuciyar :

Habiba
Kishiyar zamani
Nike da gaskiya
And nowπŸ‘‡

Y'an uba ne

Wannan page din sadaukarwane ga Mahaifina Ubangiji Allah ya jaddada rahma garesa ya sa aljannace makoma da sauran musulmin duniya baki daya.

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 49&50

___ Ya Allah ina rokonka ka cire min wannan bawan naka a zuciya ta ,Ya Allah yasa kar nayi son maso wani( koshin wahala).

Ranan dai Aisha takwana da tunanin Bahagon Masoyinta,Wanda bai Masan tanayi ba.

Washe gari tatashi jikinta Sam babu kuzari gashi yau tana da Lectures 9:00 dai dai aiki take amma jikinta Sam babu kuzari da ta rufe ido shi take gani,yau kam ko Karin kirki batai ba ,tai ma Umma sallaman sai tadawo,Umma kam yau takudiri aniyar insha Allah yau sai ta tanbayi diyarta mai yake damunta in ta dawo,Murmishi tayi "tace to Auta Allah yabada sa'a yasa a dawo lafiya".

Tana isa shima yana isa ya sauka a cikin keke napep yana kokarin Ciro kudi a aljihunsa,Aisha ta cika da mamaki,dama bai da motane koko ta samu matsalane ya hayo Kekenapep ?.

Tambayar da babu mai amsa mata tashigayi har yasoma tafiya cikin makaranta cikin takunsa na Kasai ta,Wanda yake matukar burge y'anmata.

Nabeel irin mazan nan ne da ake kira sankowa kin Wanda yarasa,Aisha ta lumshe idonta ta bude a hankali ,Sam yanxu kuma ya bace mata,tadaki sityarin Motar da karfi tare da dafe goshinta,tana fadin ya Allah ka kawon dauki ni Aisha, wai meyasa nake son kai kai na inda akafi karfina?,can wata zuciyar tace "hakin wasune yake bibiyarki,ko kinmanta da Suhail ne Wanda sanadinki yabar kasarnan saboda kin amincewa dakikai da soyayyarsa,ga Amir ga kuma Musty,ko kinantane ,afili tace ban mantaba,sudin ba rabonsu bace ni, ni Aisha ta Miskilin Masoyi , Allah yayimu ne don murayu da juna kuma shima zai soni kamar yadda nake son sa.

Wani murmishi naga ya kufce mata da sauri kuma naga ta tayar da Motar tana zuwa tayi parking tafito takara gyara mayafinta sai yanzu ne kara kare ma Aisha Kallo,Masha Allah Aisha fara ce kyakkyawa gata doguwa kirar Fulani tana da diri ,gata da manyan idanu Wanda gashin ido yazagaye su Zara Zara gata da gira takwanta tayi luf luf gwanin sha'awa kamar tayi cabins tana da hanci Wanda ya dace da fuskarta,gata da Dan karamin baki Dan daidai Wanda tazagaye shi da janbaki pink kalar shaddar jikinta wadda taji aiki ,doguwa ce ta sa takalminta mai tsini kalar shaddar nahangi zaratan yatsunta ta zagayeshi da Jan lalle Wanda suka kara ma kafar kyau nadago da kai na nadubi hannunta naga shima tayi masa ado da jallale irin Wanda ake yayi,ta rufe Motar tasoma tafiya cikin taku dai dai har ta isa cikin department dinsu.

A bangaren Nabeel kam in dai yashigo makaranta to abinda yakawosa yake Sam babu ruwansa da kowa, iyakarsa da yan aji sallama daganan bai kuma cewa kowa komi har a tashi wannan shiyaja ra'ayin Hashim Salis Wanda shima Sam bai da hayaniya karantunsa shine a gabansa ba kula yan matan Jami'a ba ,dashine kawai suke hira shima Dan talakane amma yafi Nabeel gata dankuwa shi mahaifin Hashim tsohon malamin makarantar sakandare ne,anan kura makarantar yan mata,abotar Hashim da Nabeel abin gwanin bansha'awa ,Nabeel zaune suke suna hira shi da Hashim hirar dai akan karatunsune kawai sai ganin mutum sukai a gabansu sai faman murmishi take gami da yauki,tace Hello guys sannun ku sunana Fa'iza Musa Matawalle babana shine me Company MM international limited company da ya shahara wajan sarrafa robobi da sauran su,ta karasa maganarta tana murmishi.

Nabeel kam taso bashi Dariya wannan fadin ba a tanbayekiba haka,yayi Dan murmishi Wanda hakan kuma yayi dai dai da fitowar Aisha daga site dinsu na yan Foodtech ,Wanda kuma yasa Fa'iza kuma jin karason Nabeel din ,

Tako kara gyara zaman gilashin idonta ta dubi kawarta tace "wannan kawata ce sunan ta Halima ".

Hashim yadubesu yace" ok to sannunku ya a kayi?".

Fa'iza tayi far da ido tace "malam bakomi kawai dai kullum sai naga kamar abokinka yana da damuwa shine nace yau dai bari nazo na Dan dauke masa damuwar da hira irin ta Boyfriend din nan ko ya kikace Hali?"

Fa'iza tafada tana mai karya murya da wani ya mutsa fuska.

Nabeel kam yanzu Yan mata sun soma bashi tsoro dama shi yagaya ma wani ne yana da damuwa? shin yaushe ma yataba ganinta bare har tace masa haka,ya hade fuska ,Hashim da yalura da Nabeel yasha kunu yace "Am mungode Fa'iza da kulawarki ga abokina mungode kwarai ".

Fa'iza kam shi take kallo tanaso yakara mata wannan murmishi amma yaki ko da kallonta ne ,sai Dan kanzaginsa ke magana,tayi yake tace" karka damu yiwa kai ne domin tuntuni na kamu da son sa sai dai rashin maganar sa bazai dameni ba Dan arayuwata inason mijina yakasance mai daure fuska domin hakan yana kara masa kyau da kwarjini a idona .

Nabeel ya dago fararan idonsa ya sauke a na Fa'iza sai Murmishi take hankalinta kwance ,shikam Sam bayason mace mara kamun kai ,bare wannan yarinyar da idon ta yagama budewa ga sangarci nan muraran,aransa yace bari dai na sallameki kitafi kiban waje Dan bazan iya wulakanta masoyi yiba.

Yayi Murmishi yadubi Fa'iza yace "nagode da kaunarki gareni

Maman Khaleel din kuce✍️Y'AN UBA NE

(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Nike da gaskiya

And nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 51&52

____Yayi Murmishi yadubi Fa'iza yace"nagode da kaunarki gareni amma ina mai baki hakuri ni yanzu Aure na yakusa amma ina maki fatan Alkhairi tare dafatan Allah yabaki mijin da yafini komi a rayuwa Nagode. "

Nabeel na kaiwa nan yamike yadubi Hashim yace "Abokina zan lallaba naje gurin aiki".

Hashim Wanda yalura da hawayen da Fa'iza take zubarwa yace " to ba Matsala sai gobe kenan?".

Nabeel Wanda Sam zuciyar sa tasoma yin rauni da ganin hawayen Fa'iza Dan bayason yaga mace tana kuka gashi ta kafe shi da yan kananun idon ta ,yadubi Hashim yace "Allah ya kai mu".

" Ameen "in ji Hashim.

Bayan tafiyar Nabeel Hashim yadubi Fa'iza yace "kiyi hakuri ki dai na kuka Dan bai da magani kinji y'ar uwa kamar yadda ya fadane Allah zai baki Wanda yafishi kinji?".

Hashim yafada cikin sigar lallashi .

Fa'iza ta share hawayenta tace " to nagode amma Sam bazan manta da shi ba Dan Allah menene sunan sa?".

Hashim yayi Murmishi aransa yace "ikon Allah ance ba a yi da ke kuma meye nason sanin sunan sa, yadago Fuskarsa sukai ido hudu yayi Murmishi yace " sunan sa Nabeel ".
Sannan inason Jan hankalin ki ba keba da sauran mata masu hali irin naki da surage ganin namiji suce suna sonsu Dan yin hakan bai dace ba ga diyar kwarai koda kuwa ya maki kiroki zabin Allah akansa sai kiga in rabonsa ce ke da kansa zai furta maki Kalmar nan mai tsada wato " SO" kinji kanwata.

Fa'iza ta ji dadin kalaman Hashim tace "nagode Yaya na da kaban wannan shawara Insha Allah hakan bazai sake faruwaba insha Allah na dai na".

Hashim yayi Murmishi yace " karki damu nima nagode da kika dauki maganata,Sunana Hashim Salis ".

Tace" nagode Ya Hashim sai anjima "

Aban garen Aisha kuwa takasa shiga mota sai tunani take dama yana kula yan mata,meyasa zuciyata take shirin tarwatsewa meyayasa zuciyata kike son inda ba tani a ke ba,kamshin turarensa taji tarasa a ina ta taba jinsa kamshi yana da dadi sosai ta shaka ta dago kai a hankali shine tagani ya gota ta yana tafiya kamar wani jinin sarauta ,kifa kanta tayi ajikin Murfin mota tayi kuka mai isarta kamin tashare hawayenta ,ta fada motarta tayi mata key ko da taje gida tara sa yadda zatayi da dakon sonsa da ta kulle ido shitake gani yana yima wata wawiya Murmishi kishin Nabeel Aisha take sosai domin jitake kamar ta shake su dazunnan ,amma vabu yadda ta iya dan da alama yanason yarinyar shiyasa har yake mata Wannan Murmishin.

Bayan Aisha taci abinci ne Umma tadubi Aisha tace" ni ko Auta inason na tanbayeki mana?".

Gaban Aisha ya yanke fadi jikake dam !

Ta dago a hankali tace " tambaya kuma Umma ?"

Itama tajefeta da tata tambayar .

Umma tace " eh "

Aisha takara gyara zama tace "to Ummana tambayarni Allah yasa nasan Amsar".

Umma da Aisha sukai Dariya a tare Umma tace" kin ma sani Auta,dama cewa zanyi kwana biyu naga kamar kina da damuwa dan kincanza kwarai dan da Autana nasanta sarai da kuzari amma yanxu tazama wata sai a hankali da zaran kin zauna to sai inga bakida wani aiki sai tunani shin mai yake damunki Aisha kar ki boyemin damuwarki dan baki da wata Uwa wadda ta wuceni".

Aisha wadda ida nuwanta sun cika da kwalla na tausayin kanta gashi bata son yima Umma karya dankuwa bata sababa .

Sukai ido hudu da Umma ta girgiza mata kai alamar kar tayi kuka, gamida fadin ina jinki Autar Umma.

Aisha tai shiru aranta tace "yanzu sai in fadama Umma wannan zancen kai abin da kunya".

Babu kunya Aisha fadamin kinji,Umma tafada tana Murmishi.

Aisha Sam batasan zancenta yafitoba filiba,sai kuwa kunya ta kamata,ta rufe idonta tana Dariya kamin tace Umma bazaki min fadaba ?.

Umma tagyara zama tace " Um bazan yi ba gayamin".

Nan fa Aisha takwashe komi tagaya ma Mahaifiyar ta yadda take ji dan ta ganshi har da ganin su datayi nayau da wata sai da tagayama Umma akarshe Aisha tace'Umma kiban shawara ya zanyi wallahi inason sa so kuma mai tsanani Ummana"Aisha takarasa fada cikin Murya mai ban tausayin.

Umma a bin kam yaso bata Dariya tuno yadda sukai ita da Mai martabanta Haka sukai ta nuku nuku da son juna dan ko har da kwanciya a godon Asibiti sai da Wambai yayi akan yazo yaganni ina zance da wani.

Tayi Murmishi tace "tab abin Babbane Auta karkicemin kinayin Son masowani ?

Ai tuni hawayen da suke makale suka soma suntiri akan kyakkyawar fuskarta zuba kawai suke takasa magana Umma tadubeta cike da tausayi ta rungumeta tace " Aisha wannan waye kuma ya sunan sa?"

" Umma nima ban San sunan saba."

Umma aranta tace "tashin hankali ,afili kuma tace ikon Allah yanzu baki San sunan gwarzon naki ba,tab to a hoki y'an mata".

Aisha tasake tusa kanta cikin jikin Mahaifiyarta cike da jin kunya,Umma tace " a'a Auta kar ki karasa Umman Mana ".

"Umma to kiban shawara to" .

Umma ta gyara zama tasoma fadin "dafarko inason kinutsu ki kama kanki So Makaho ne kuma shi Kurmane in ya shiga fitarsa sai a hankali ,dan haka ina son ki dage da Addu'a akan Allah ya maki zabi da miji nagari Wanda sonsa yafi naki Wanda zai dunga lallabaki akoda wani likaci mai gudun bacin ranki, Wanda zai jibanci al'amuranki da na yaranki ,bance kidai na son wannan bawan Allah ba tayuwu shima inyaganki yace shima yana sonki kedai kikasance mai kamun kai a ko ina,kizama jaruma idan kinganshi dan kar yagane kinason sa kinsan mazan yanzu ba kamar na da ba ne Aisha ,nayanzu sai suyi amfani da damar ke kika nuna kina sonsa bashi ba to zai iya Neman kwace maki budurcinki ta wannan hanya ,dan haka kokusa kar ki nuna masa kina sonsa ni kuma namaki alkawarin tayaki Addu'a duk da dama kullin cikin yimaku nake keda sauran y'an uwanki kinji Autana,sannan kuma zansa Malam Mujitaba yayi maki istihara akan lamarin kuma kema zan baki kiyi kikuma roki zabin Allah akan lamarin,Aisha sotari abin da muke so bashine yake zama Alkhairi a gare mu ba ,dan haka ki kiyaye kibi komi a sannu dan nima nataba tsintar kai na cikin irin wannan yanayin .

Aisha ta dago da sauri ta dubi mahaifiyarta tace" Umma kema kinso wani kamar yadda nake son Hubby na ".

Sai da Aisha tafada Sai kuma kunya ta kamata,Sam ta manta da mahaifiyar ta take magana.

Umma tayi Dariya tace " haka ne Aisha nashiga yanayin da kika tsinta kanki a ciki kuma ba kowa bane illa mahaifinku,Sai dai ni a kwai banbanci da naki ni da mahaifinki munshaku da juna sosai dan kullum sai yazo gidan mu sai ya bata lokacinsa yana sauraren shirmena shikam yayi ta biyemin dan ance tun ina yarinya na tantance muryarsa ,ko da yaushe cikin yimin hidima yake har nasoma zama budurwa akasoma maganar yimin Aure dan samari sun cika ma Hakimi kofa kowa na son Aurena ,shikuma mahaifinki alokacin baya kasarnan yatafi Egypt karo karatu kwatsam nikam duk Wanda yazo wajena zance alokacin kallonsa nake sakarai bai iya zance ba sai Yayana kullum burina bai wuce ace yadawo ba ace za a mana Aure da nafi kowa farin ciki bayan shekara Uku mai martabana ya dawo kasarsa ta haihuwa yazo damin da tsaraba ta ta musanman amma me sanda ya iso yaganni da dan gidan galadima shima Baffanku Mubarak nan fa yasoma cika yana batsewa ,nikam ganinsa yasani nashiga yanayin da bantaba shigaba na shaukin So ,da sauri na bi bayansa muka shiga cikin gidanmu ina ta murna shikam gogan ya tsiri cin magani,in ta kaice maki Aisha tunda ga wannan gani da yamin da wani muka koma abokan gaba nikam gashi kamar kullum karamin sonsa a ke ,har mahaifiyata ta gane, in dai yashigo cikin gidan mu to banida sukuni,har sai ya fita,sannan zakaga walwalata,ana cikin haka akace na fidda miji ,nan fa hankalina ya tashi.......!

Maman Khaleel
din kuce✍️. YAN UBA NE
( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Nike da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'an Uba ne

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 53&54

Hankalina yayi matukar tashi gashi Wanda nake so shi Sam bayatani haduwarda muka sabayi Sam yanxu ya datseta ,nashiga damuwa sosai kullum ina sauraren zuwan mai martabana amma shiru Ummana tayi min tambayar duniyar kan ramar da nake amma nace mata bakomi lfy ta kalau,Umma tace "to shikenan amma ya kamata ta sanar da ita damuwarta in kuma kan maganar Aure ne to ki kwantar da hankalink acikin mane manki ki fidda guda".

Hawayen da Umma talura inayine yasata saka Salati,tare da Fadin" Rabi'a mai namaki ta hade rai ta watsomin wani kallo tare da fadin ki gayamun abin da nai maki da zai saki zubda hawaye?".

Na dubeta nashare hawayena nace" Umma ina kukan rabuwa da kene da yan uwana nikuma Sam banason nayi nesa da gida nafison kullum ina ganinki kusa da ni".

Ummana tayi dariya ta matso gareni tace" in Dan wannan ne karki damu kowace mace ahankali take sabawa kema zaki saba insha Allah kuma ai muna tare zamu dunga zuwa muna dubaki akai akai kinji?".

Nace "to Umma "

Abangaren mai martabana kuwa yaji komi a gun mahaifinsa na zancen Aurena yashiga damuwa sosai fargabansa daya karnazabi wani bayan shi,gashi tun ganina da yayi da wani ba shiba haryanxu abin yakasa barin zuciyarsa,duk da yama abokin takararsa kandagarkin shine zai Aureni Dan angama magana ,shikam da jin haka ya janye,bai kuma zuwa ba,shikuma gashi har yanxu fushi yake da ita,haka dai yayi ta sake sakensa bayan kwana 2 yashirya tsaf cikin shiga ta alfarma yau sarautar ta tashi alkyabba ya sa baka ta amshe shi yayi kyau sosai sai tashin kamshi yake mai sanyin dadi ita kawai yake son gani ,yana zuwa kuwa yaganni duk nafita hayyacina narame sosai ko da muka kebe na sunkuyar da kai na kas nakasa cemasa komi tunda yadawo garin yauce rana tafarko da yanemeni da kyar ya amsamin gaisuwa daganan bai kuma cewa komi ba nima haka,nine na katse shirun da fadin inajin Bacci zan iya tafiya?"

Yi yayi kamar bai jiba nasake satan kallonsa nace" Yaya Zan iya tafiya ina jin bacci ne. "

Ko kallona baiyi ba yace "ai dole kice haka Dan ni ba'a so na shiyasa ake min kora da hali,dama nazone natayaki Murnan samun zabin ranki da kikayi ,Allah yasa Alheri ,nakafe shi da idanuna nakasa ko motsi bare kwakkwaran motsi,ya dubeni yace " Malama karki cinyeni danye mana da kindan sassautamin kallon ko?".

Maganarsa taso taban dariya saidai ba hali, na sunkuyar da kai na kasa nace waye zabin rannawa Yaya gayamun shi Dan ni bansan shi ba ,Dan ni Sam ba mai zuwa wajena kuma ni zanma Baba magana yadaka min da maganar Aure har sai nasamu Wanda yake so na kuma nima nake sonsa,amma a halin yanzu ni Matar mai rabone (Sunana littafina mai zuwa ).

Yayi Murmishi yaji dadi har cikin ransa ,yace hakane kamar yadda ni ma nake na masu rabo ba mai raboba,dan haka sai kishirya zama da ni Muhammad Wambai amatsayin Matar Aurena,Ai ranan in gayamaki Auta nayi farin ciki sosai ,jin zabina yagayamin da bakinsa yanasona,aiko ba a jima ba akai mana Aure Wanda yake cike da zallar so da Kauna.

Aisha tace "lallai Umma nima zan gwada yadda kikai ma Abban mu insha Allah ".

Umma tace" rike kimarki ta Mace yanada mahimmanci Auta ko kina son mutum karki yadda ya gane kina son sa, domin wasu mazan suna amfani da wannan dama suyi ta ma Matan wulakanci da cin kashi wani ma yasamu damar da zai dunka juyaki kamar waina saboda yasan bazaki iya rayuwa babu shi ba,Dan haka ki ki yaye kinji Auta ta".

"To Umma insha Allah zan kiyaye nagode ma Allah da yabani ke a matsayin Uwa tagari gareni".

*************************

Nabeel zaune yake a kofar shagonsu yau basuda aiki sosai zaune yake yana latsa wayarsa ta zamani wato Moto rola wadda ake mata lakabi da reza yanata game gamida sa wa'azin Malam Jafar yana saurare ,amma Sam hankalinsa yanacen wajen yarinyar nan tahadu sosai sai dai yarinyar tafi karfinsa shi ba kowa bane a garin nnan face talaka mai Neman na Abinci ,kacire ma zancen ta aranka,kanemi dai dai da ajinka wadda zaku so junan ku, kuyi arzikin tare,yayi Murmishi tuno yarinyar gidan su Ibrahim yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment