Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne
Dedicated to:
Aunty Hauwa and Besty na Fatima S Rabee'u ina godiya da kulawarku Allah ya sa ka da alkhairi ya bar zumunci AminπŸ’‹.
Special gift to:All
Masoya na nagode kwarai da Addu'ar ku nagode kwarai maza da Mata ina maku jin jina wannan page din na duk Masoyanane masu son wannan littafin na kowani group Facebook da nan WhatsApp ina godiya ga kyautar page nan na baku kuyi yadda kuke soπŸ₯°πŸ’‹.

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 35 & 40

To mun tsaya a gunda Sulaiman yake zankadama mahaifinsu karya akan Nabeel🀣.

Malam Saminu yayi Murmishi yaji dadi har cikin ransa ,sab'anin da dayayi tunanin ko ya tauye masa Auta,ashe ba hakabane ,Nabeel kam gabadaya maganar Sulaiman jinta yake kamar saukar aradu Dan ko amafarki bayyi tunanin zaiji maganar nan ba a vakinsa ,gashi mahaifinsu ya yarda, Malam Saminu ya dafa kafadar Nabeel yana Murmishi yace "Nabeel Allah ya albarkaci rayuwarka yasa kafi haka.

Nan Sulaiman da sauran y'an uwansa suka ji zafin maganar mahaifinsu musanman Sulaiman Wanda yake jin maganar kamar shagub'e yake masa,Ahmad Da Nabeel kam sun sha yawo a cikin garin Kano ,duk yadda Ahmad yaso yaji cikin Nabeel game da halin da ya tsinci kansa a zamansa a garin amma magana dayace yake fada" lafiya lau nake babu wani kalubale ".

Ahmad yayi Murmishi yasan bai son sanar da su ne Dan kar ransu ya b'aci,Dan shikansa ya lura da kame kamen da Yayansu yake .

Kwanan su 3 suka tattara suka koma garin Jos ,Mariya kam tasha albarka wajen Malam Saminu domin tayi masu abin da ko yar da ya haifa iyaka kenan.

Sai dai muce Allah ya sauke Ku lafiya.

*******************
Nabeel na hango zaune yana ta hada wani keji awata gidan gona mai girman gaske a cikin garin Tiga gonar katuwa ce ,Nabeel nata aikinsa cikin kwanciyar hankali,kowa na yaba irin kokari da baiwa irin ta shi hatta mai gidan sa Danjummai yanzu yagama sallamawa Nabeel wani rahmane a gunsa domin tasanadinsa gashi yanzu iyalinsa suna ci suna koshi dai dai gwargwado cikin rufin Asirin Allah,wannan ne yasa Nabeel yashiga ran Danjummai komi sai ya ambaci Nabeel wannan kuma bakaramin bakanta ran abokan aikinsa yake ba ,ciki kuwa harda Wani abokin aikinsa me suna Auwalu,Auwalu yarone mai hassada da bakin ciki,komi Nabeel yayi sai yaji kamar ya shakesa wannan ne yasa Duk abinda Nabeel yayi to Sam bazai taba ba ,Nabeel kam gaba daya yana zaune da abokan aikinsa da zuciya daya.

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah Nabeel nahango yasoma zama cikakken ingarman Namiji yayi kyau sosai ,Nabeel dogo fari ne shi gashi da doguwar fuska mai kyau gashi da dogon hanci har baka, yana da gashin gira kamar na mace ya kwanta yayi luf-luf yana da fararen idon masu Dan girma gashi dawani nan na daddan gashi baki sidik,Wanda yanzu yake samun kula na musanman,Nabeel kyakkyawa ne yana da kirar jaruman nan ,yafito tsaf dashi cikin Riga da wandonsa na jeans wando bakine Wanda gayu kema lakabi da cinus da rigarsa pholo ja da anmata rubutu abayanta da bakin rubutu ,daga bayansa na ga an rubuta I like you ya dauki wani jan takalmi kanbas kiraKhaleel
wandanaga anja mark da baki ya dauki bakar hula kirar pholo ya sa naga ya dauki wani hadadden agogonsa ya daura a saman tsintsiyar hannun sa ya dauki wani turare mai sanyin kamshi ya fasa ma jikinsa yafito sai kamshi yake,Kallo daya zakamasa kasan lalle Nabeel ya tsaru iya tsaruwa,Mariya ta dubesa cike da zolaya tace "a'a Ango na har ka fito wannan kyau haka kamar zakaje gurinta?".

Nabeel yayi Dariya yace" kai Aunty ina ni ina wata budurwa kirufa min asiri, to ma wai Aunty in naje nace mata me karya?,tab baruwa na ni aikina nasa a gaba sai karatuna burina yanzu bai wuce akan karatuna ba da aikina Dan banshirya Aureba yanzu".

Mariya tayi dariya tace" kai Nabeelu sai yaushe to zakai Auren?".

Yayi Murmishi sai ankawarda nagaba na kamin najajibo masu nawa kuma ma vawannan ba ma Aunty Y'anmatanfa ma tsoro suke ban ,ya dubi agogon hannunsa yace kai kai Aunty Mari jibi zakisa narasa lectures,um kinga tafiya ta sai nadawo".

Mariya dai tayi Murmishi tace" to adawo lafiya Allah ya tsare" .
"Ameen kawai yace ya sa kai abinsa ya bar gidan".

Kuyi hakuri namanta bansanar da Ku Nabeel ya koma makaranta ba to kubiyoni bashi zakuji yadda abin yakasance insha Allah a Next page.

Maman Khaleel

dinkuce✍️.

Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'AN UBA NE

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 41& 42

Nabeel ya nufi BUK in da ke karatunsa akan Engineering yake karanta akan aikinsa ,Y'AN mata dayawa na kyasa Nabeel amma Sam shi matan basu ne a gabansaba,ko a cikin class dinsu bai fiye kalle kalle ba iayakarsa yayi abinda yakaisa in akatashi ya kama kafarsa yanufi wajen aikinsa.

Nabeel yakoma makaranta ne da tai makon abokinsa Ibrahim Wambai ,wata rana yakawo masa ziyara suna zaune a kwar gida da maraice sunacikin hirarne suka sako maganar karatun shi Nabeel, Nabeel yayi Murmishi yace " kai Ibrahim in banda abinka ni yanzu ina ni ina cigaba da karatu bani da hali ni ,nahakura Wanda nasamu Allah ya sa masa albarka,Nabeel ya fada yana murmishi".

Murmishi Ibrahim din shima yayi yace "hakane amma yakamata ka koma ,ko da yake kace bahali Allah yakawo mafita".

Nabeel yayi Murmishi yace " Ameen ya Allah kai dai nagode ".

Haka suka cigaba da hirar su cikin nishadi Ibrahim ya dubi Nabeel yace " kai ko Nabeel kaki zuwa gidan mu ni ne kullum nake zuwa gidan Ku ko sau daya baka taba cewa yau banga wancan sakaran ba,bari na nemesa naji ko ya nanan bakomi ni da Allah ya dora ma sonka sai nai ta hakuri ...".

Nabeel yayi saurin toshe masa baki kai Ibrahim kayi min uzuri mana, kasan yanayin aikina ,kuma kai ma ba mazauni bane ,shiyasa ban taba zuwa ba ,amma tunda haka kace gobe da yamma insha Allah kashirya tarvar bako a gidan ku,shikenan Nabeel ya fada yana Murmishi ".

Ibrahim yaji dadi da furicin Nabeel, haka suka cigaba da hirarsu
kamin daga bisani suka rabu suna masu farin ciki.

Ibrahim yana zuwa gida bai zame ko ina ba sai dakin mahaifiyarsa in da ya sameta suna zaune ita Autar ta Aisha ta kishingida acinyar ta ,sai faman Dariya suke ,da alama hirar tayi dadi,yayi sallama abakin kofar,Hajiya Rabi ta amsa masa cike da wani nishadi mara misaltuwa,tace Babana shigo mana dayake sunan sirikinsu kenan kuma kani ga mahaifinta,Ibrahim ya shiga ya samu guri gefen mahaifiyarsa ya zauna ,cike da zumudi yasoma fadin Umma gobe Nabeel zai zo gidan nan,gaban Aisha yayanke ya fadi haka kawai gamida wani farin ciki ita dai tanason ganin wannan Nabeel din da Yayanta bai da magana sai tasa duk yadda akai iyayensa shima kusoshine a garin nan ,ta mike tana Murmishi,tadubi mahaifiyarsu,wadda bakinta yakasa rufuwa,tace " kai kace gobe muna da Babban bako agidan nan Baba Allah ya kai mu ,har suna hada baki Aisha da Ibrahim wajen fadin Ameen".

Ibrahim ya kara gyara zama yadubi Aisha yace" ke tashi ki bamu waje inason muyi magana da Umma ".

Aisha ta turo baki gaba irin na shagwababbun nan tasoma yarfe hannuwa tana fadin kai Bro Dan Allah .

Ibrahim ya hada rai nan da nan ya wani watsa mata harara yace" OK zamuyi sirri sai kuma inyi a gabanki kiji dadin bada labari da alla wuce dakinki kibamu waje in mungama kidawo in ma ciki zaki koma sai Umma ta mai daki Dan so".

Umma tayi Dariya tace" Auta rabu da shi kinji jeki jiramu" .

Aisha tayi Murmishi tace" to Ummana da yagama ki koresa kinji tafada cikin shagwaba".

Bayan fitar Aisha Ibrahim ya gyara zama ya mai da hankalinsa ka cokan gun mahaifiyar,itama ta lura maganar da zayyi tana da muhimmanci ta basa hankalinta gabadaya ,tayi Murmishi tace" ya akai Baban Umma?".

Ibrahim bai boye ma mata komi banagame da tai makon da yake so ai ma Nabeel na game da karatunsa ,ya kara da cewa Umma kinga Nabeel Marayane kuma kinsan falalar tai makon Maraya sannan kuma in mukai sanadin cigaban karatunsa to tabbas Allah zai bamu lada sosai.

Umma bata katse Ibrahim ba har sai da yakai aya a maganarsa,kamin tayi Murmishi tace "to yanxu me kake so nayi ?".

Yayi Murmishi ya kara matsawa jikin mahaifiyarsa yakamo hannunta yace " yauwa Umma so nake ama Abba magana yama Uncle Usman magana tunda nasan takardunsa sunyi kyau kinga dama yanzu anfara biyan Jam sai yaje yayi ,idan yaci sai a sama masa gurbin karatunsa anan BUK ko ya kikace Umma ?".

Umma tayi Dariya tace "hakane Maganarka Babana Allah ya shige mana gaba Zamuyi magana da Abban naku, kai ma yanzu kasamesa da maganar nasan bazai kiba nikuma dasafe zan kara tuntubarsa ,insha Allah Nabeel sai yayi Karatu,Wai ya ko Yayansa amma dai ya canza ko?".

Ibrahim yayi yake yace " um ni ai yanzu banabi ma ta kansa tunda na lura bai da kirki,kinsan kwanaki sai da yaxo fada wajen Abba wai a rabani da Nabeel Dan iskane yana shaye - shaye zai batani Dan haka arabani da shi,shine fa Abba ya nemeni yake tanbayata wai waye Nabeel, nikam cikin zumudi nace "Abba abokinane nan dai nasoma bashi labarin sa ,yacika da Mamaki shine yake cewa to ai kaji abinda Yayansa yace ,shine fa nace Sam Nabeel bai shan ko sigari bare kuma wani abun maye, shine yace to bakomi kacigaba da tai makonsa in abin kuma ya fi karfinka to ka sanar da ni nima nabada tawa gudun muwa".

Umma tace " ikon Allah Allah to ya shiryi Sulaiman din nan".

Ibrahim yace "Ameen dai "

Maman Khaleel dinku ce.

Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mun gode.

Daga Marubuciyar:
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
and nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 43&44

Umma ta dubi Ibrahim tace "ka bar komi a hannuna zan ma Yaya magana zakaji komi da safe insha Allah sai su Sulaiman sunyi na damar abinda suka aikata".

Ibrahim yaji dadi sosai yama Umma sallama sai da safe ,yamike yanufi dakinsa .

Washe gari Umma tasanar da Ibrahim yadda sukai da wambai ya amince yace ba nan BUK ba in ma jami'ar Ibadan yake son zuwa yayi karatu to a shirye yake da ya tai makesa.
Ibrahim yaji dadi har cikin ransa,ya rungume mahaifiyarsa yana mata Godiya,tace Ibrahim kai da Nabeel na daukeku kamar ni nahaifeku,kar ka da mu.

Ibrahim yaje ya samu mahaifinsa shima yamasa godiya kamin ya shirya ya fada motar sa kirar Honda yana shirin tada wa Aisha ta nufosa da dan gudunta tana daga masa hannu yadakata yana Murmishi yanason Aisha sosai aransa yace sarkin kwalliya halan hodar takare ne,ai baigama tunaninba ta karaso,tana Murmishi tace" Yaya Ibrahim har zaka fita?".

Yadubeta cike da kulawa yace "um zan fita ya a kai ne?".

Ibrahim shima yaje famata tasa tanvayar .

Aisha tayi Murmishi tace" kai Yayana shikenan babu halin tanbaya kuma,to dama cewa zanyi um....umm".

Yayi Murmishi yace" Aisha wai dan Allah me kike so ne nasan tatsuniyar gixo bata wuce ta koki,kayan kwalliya sun kare kenan ko kuma yauma kuna da ankonne?".

Aisha tayi Dariya wadda takara fito mata da wani sihirtaccen kyawunta,ta dan turo baki cike da shagwava kamin tace "kai Ya Khaleel ina da kayan kwalliya,kuma ni ba anko zakaminba,dama fa cewa zanyi um ..um sai kuma kamar anfizgi maganar naji tace"bakace yau Yaya Nabeel zai zoba".

Sai sannan ya gane inda ta dosa yakara gyara zamansa jin an ambaci sunan Amininsa,yayi Murmishi yace" eh Aisha yau zai zo insha Allah, to ya a kai?".

Tasoma sosa kai kamin tace "dama cewa zanyi idan na shirya maku table banyi shisshigiba?".

Murmishi yasakeyi yace " bakiyiba sai ma kika sani farin cikin kalamanki , kuma naji dadi kihada mana gara mai dadi kinji kanwata,yamiko mata kudi yace takaro kaza amma ga mamakinsa sai cewa tayi kabar shi Yaya nima akwai kudi a guna kasan jiya fa Abba yabamu 20k musayi kayan kwalliya bakon ka ai bakonane nima zanyi gudun muwa tafa da tana Murmishi".

Ibrahim yace "to nagode sai nadawo".

Aisha tace" to Yaya a dawo lafiya".

Aisha kam yau jinta take cikin wani farin ciki wanda bata taba jin irinsaba,haka kawai take dokin ganin Nabeel din nan ta kosa ta ganshi,yini tayi dora tukunya da ta sauke wannan ta dora wancen Umma kam tanata kallon ikon Allah duk abinda aka gama sai ankawoma Umma ta dandana ko yayi dadi,Umma sai dai tayi Dariya tace "Aisha manya takarbi wani danbun kuskus da tayi wanda yaji hanta da ogun da albasa,gamida kayan dan dano sai kamshi yake fitar wa mai dadi, Umma ta sa cokali ta diba takai bakinta,cike da son takara karfafama diyarta gwiwa tace " wai can ca di wannan dadi haka Aisha dama haka kika kware wajen iya girki,shine baki tayani,wajen yima mai martabana,amma gaskiya yayi ,takara diba takai bakinta.Aisha kam farinciki yagama cikamata zuciya,tadubi Umma tace "Ummana duk wanda ya zauna da ke ai dole ya iya girki ,Umma ni dai yan fadamin komi yaji gishiri bayyi yawaba?".

Tafada cikin shagwaba.

Umma tace " wai ai kinfini ma Aisha girki yayi Yau Nabeel inaga duk cikin girkin nan duk wanda yaci nakega kunnensa yau sai yamike ya kusan tabo silif,yana kadawa dan dadi.

Aisha taji dadin yabon da Umma tai mata,sai kuma can wata xuciyarta tace ,kila ma duk wannan wahalar da kikai in yazo yace yakoshi,wai da nasha takaici tafada a baiyane,ta nufi kicin tagama hada komi a Dining ga juice kala kala da ta hada masa,kamin ta koma daki ta rangada wanka,kai kace wata sabuwar amarya, ko ince wadda akace mata yau Saurayinki zai zo saboda doki,dan tafi kowa san ganin Nabeel.

****************

A bangaren Nabeel kam yau yasha aiki sosai hannunsa yayi kanta ,a gajiye ya dawo gida gashi garin da zafi,kowa yasan garin kano da zafi gashi dama yau anyi rana,ruwa ya diba yacika bokiti ya dauki soson sa yau yanxufa su Nabeel anshigo gari da sabun Dettol yake wankaπŸ˜‚,bayan yafito ne yasoma shafa Basline mesuna Excellent baby care na kamfanin IB Marwa man ya amsheshi gashi da kamshi da rike jiki da sa laushin fata,yagama murje jikinsa da shi ya mike yajawo jakar kayansa yaciro wani Yadi mai ruwan madara yadin yayi kyau yana da manyan zane kana iya hango fara kal din singlet dinsa,ya daura agogonsa da siya kwanaki ba wani mai tsada bane amma ya amshi tsintsiyar hannunsa bakine ,ya dauki hularsa me kube yakaryata bakace ya dauko takalminsa kirar italy mai yatsa shima baki ne yasa yako amshi kafarsa yafito tsaf da shi ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi ,yafito yasamu Mariya tana ta aikin abincin dare,yace "Aunty yau dai zani gidan su Ibrahim zankai masa ziyara ,yafada yana Murmishi".

Mariya tai Murmishi itama tace " gaskiya ya kamata amma ni wannan wankan fa da farko ya tsoratani,har gabana yasoma dukan tara tara ,nadauka zance zaka ,dan wannan wanka bai kamata wata taganiba".

Yayi Murmishi yace "kai gaskiya kinfiye kishi da yawa da banda shirin karin Aure amma yau kinsani jin son karin Aure ".

"Kai !kai !!kai !!! haka zakace lalle ashe yau bakai acikin tukunya ta sai dai kaje can wajenta ta baka abinci amma ba ni Mariya ba kaji nagaya ma ,tab aiko da sake".

Wai amba mai kaza hanji,inji Nabeel wanda yafada yana dariya,yadubi Mariya yace to natuba da wasa nake in kika hanani abinci to wa zai ban,kingani zan kulle idona bazan kalli kowa ba".

Yadda yayi yaba Mariya Dariya ,tace "yau wa ko kai fa ,adawo lafiya agaida iyayen Ibrahim din da kyau".

Nabeel ya amsa da zasuji,bayan yayi sallah magriba ne ya dauki hanya sai gidan Wambai bai sha wahala ba wajen gano gidan dayake basuda nisa kuma gidan ba boyayye ba ne,da yake Nabeel ya siyi waya Nokiya karama mai dan kyau saboda abokan kasuwanci ya siya,kusan shine yasoma rike waya ashagonsu,yana zuwa yanemo no din Ibrahim tana ta ringin bai daga ba,yasake kira akaro na 2 takusan yankewa ya ji wata Murya mai sanyi ta doki dodon kunnensa ,tana fadin" Assalamu a laikum"...

Maman Khaleel
dinkuce✍️.

Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mun gode.

Daga Marubuciyar:
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
and nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Ga kyautar page nan ga Babana na kai na Ibrahim Aliyu Bros Allah ya saka da alkhairi Allah ya kawon Uwa tagari πŸ₯°.

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 45&46

A jiya muntsaya ne inda mukaji Nabeel yaje gidan su Ibrahim inda ya kira layinsa mukaji amadadin muji muryar sa sai Nabeel yaji wata murya mai sanyi nafadin" Assalamu a laikum".
anan muka tsaya yanxu zamu dora.
*****

Lumshe ido naga Nabeel yayi yakara gyara tsayuwa ya sauke wata ajiyar zuciya wadda yasa Aisha lumshe shanyayyun idonta ta kau da wayan gefe kamin ta mayar ,dai dai lokacin kuma Nabeel ya amsa mata da "wa'alaikumussalam,dan Allah mai wayan baya nan ne ?".

Gaban Aisha ya yanke yafadi jikake damm!jin muryar tayi tunda take a duniya bata taba jin murya mai dadi da son jin cigaba da magana ba kamar wannan bawan Allah,cikin da burcewa tace " um yana dakinsa yanxu ya makala caji ya fita bari na kaimasa".

"Ok ba damuwa nagode"

Nabeel ya fada yana mai kashe wayan yana duban ta,wani Murmishi naga ya subuce masa,ko wannan wacece zan so naganta domin muryar tama kawai naji ina ga naganta ido cikin ido?".

Aisha kam tana sauke wayan tanufi kofa da niyyar zata kaima Yaya Ibrahim waya,sun kusan zabga karo ,yayi saurin ja da baya,yana harararta,yace "dalla malama saurin me kike zaki hankadani kiragen farashi".

Maganar Ibrahim taso tabata dariya sai dai bahali ta hadiye ta dan yayi mugun hada rai,tawani marairaice tace " Yaya dama fa kai zan kai ma wayanka Bak'onka yakira shine nace bari na kai ma ".

Da sauri Ibrahim ya karbi wayan yace Allah yasa baki masa shirmen da kika saba ba,ya danna Number Nabeel, ring daya tayi yayi Murmishi ya daga wayan tare da sallama,Ibrahim ya amsa yace " dan Allah kai hakuri Allah yasa yari yar nan batai ma kwab'a ba nashiga daki ne nadawo shine daga kiran waya har ta daga".

Nabeel yayi Murmishi yace"haba malam ka amsa min sallama ai kamin ka hau fadan,to ni bata min komi ba,hasalima ni banda girmamani ma da tayi dan haka ai mata a fuwa Yaya".

Ibrahim yayi Murmishin jin dadi,yace "oho haka ma xakace ko in dai Aisha ce to ga ka ga tanan ".
" Um naji, gani baki kofar gidan ku ina jiran ka".

"Ok to gani nan zuwa, ya fada yana kashe wayan".

Yadubi Aisha yace bari na shigo da shi kifadama Umma gashi nan ya zo kikawo masa abinci da ruwa d'akina kinji?".

To yana tafiya tace aranta ba in da zata ,tunda abin naka wulakancine ,sai da ka gama kwancemin zani a gabansa sannan kuma kace na kai ma abinci,ta juya ranta a bace,ta nufi dakin Umma ranta a bace ,Umma wadda take zaune bisa dadduma tana lazimi,ta zauna ta dora kanta bisa kafadarta,Umma ba ta hanata ba sai da tashafa addu'a kamin tace " Autana lafiya wa ya tabamunke?".

Ta turo baki gaba irin na shagwab'abb'un nan tace "ba Yaya bane yake ta ce ma bakonsa ni mashirmaciya ce wai dan yakira na daga waya,haba Umma wai dan Allah me nakeyi na shiririta?".

Umma tayi dariya gani idon Autarta ya ciko da kwalla gashi ya soma lalatamata kwalliyar da tasha,tasoma fadin kai ! kai !! kai !!! rabu da shi karki bata kwalliyarki kinji Auta rabu da shi ai shi abokin nasa bazai yarda ba rabu dashi ,kuma zai zo ya saman yana ganin Autana ta girma taza budurwa ,kwanan nan zan samu jika sannan ya dunga fadin Auta na shiririta,rabu da shi zai zo yasameni".

Aisha kam sai wannan sunkwi da kai take taji an ambaci Aure,ita dai tanason Aure amma batason su rabuda Umman ta.

Umma tace" yanxu ina yayan?"

Aisha tace yana dakinsa yanxu wai na kai masu abinci,ni kuma Wallahi Umma baxani ba sai dai kisa Lami ta kai masu dan bazan yarda bakonsa shima ya rainani ba".

Umma tayi dariya aranta tace duk zumudin son gani Nabeel din yatashi awofi kenan,Umma naga kina ta Murmishi tunanin me kike ne?"
Umma tadubi Aisha tace "bakomi ai yadda kikace Auta haka za ai kinga gobe bai sake cewa kina shirmeba dan kin daga masa waya.

Aisha tace " yauwa bari ma nai kwanciya ta anan dan in yaji ni shiru kar yazo yace zai dakan,Umma tace hakane ,Umma da kanta ta Umurci Lami da takwashe kayan Dinning da takai dakin Ibrahim, Lami ta rusna tace to Umma,Lami tanufi kicin ta dauko katon ture tashirya komi akai,tarage cup din juice guda 2 da cups dinsu kanana,ta nufi dakin Ibrahim cikin nutsuwa takara sa dai dai bakin kofar part dinsa tayi sallama,Ibrahim ya amsa tare da fadin Bismillah.

Lami tashiga dakin da sallama,tare suka amsa mata Nabeel ya kafeta da mayun idonsa,tsaf take cikin riga da zani masu kyau a idonsa a ido irin nasu Ibrahim kuwa tayi shigarsu ne irin ta masu aiki,ta durkusa ta aje kayan, tasoma gai dasu.

"Nabeel dai ya shiga rudu anya wannan itace Aisha, anya kuwa wannan muryar naji dazu?"

Tunanin da yake kenan a zuciyar sa Dan yakasa amsa gai suwar lami yana tuno muryar ta yana hadawa da wannan,Ibrahim ne kawai ya amsa ,tasoma aje kayan, ahankali Lami ma ba laifi tana da kyau dai dai misali,itama kyakkyawace,bakace wankan tarwada,Nabeel dai sai satan kallonta yake adole kuma shi yana kallon tauraron Dan Adam har tagama sai sannan ya dubeta yace Sannu Sister da kokari.

Lami tawani washe baki tana fadin kai bakomi Alhaji,tana kai wa nan sai kuma tai waje,abin yaso yaba Nabeel Dariya wai shine Alhaji,cab yayi murmishi,jin cikinsa na kugi,sai lokacinne ya tuna da bai ma ci abincin ranaba,lami bata jima ba ta dawo takarasa kawo sauran ,tana aiki tana Satan kallon Nabeel Wanda yagama tafiya da imanin ta,sai dai ko giyar wake take sha wannan gayen yafi karfinta,tana yar aiki ,sai dai tayi hakuri amma ba lefi ai tadawo ta kara ganin sa kuma koda bata kara ganinsa ba zatabada labari taga wani balarabe mai kyau yau Dan yau sai ta ba Innanta labari .......!

To fa kun dai ji wata sabuwa hhhh to muje zuwa gobe in me duka ya kaimu gobe Dan jin cigaban wannan labarin naku.

Maman khaleel

d'in kuce
Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mun gode.

Daga Marubuciyar:
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
and nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 47&48

Lami ta fita tana mai farin cikin ganin balarabe,Wanda a iya saninta batai tunanin yanajin Hausaba,haka takoma tazauna a kicin tana tunaninsa A fili tace Allah kaban miji mai kyau mai sona tsakani ga Allah irin balarabe,sunan da ta sama Nabeel kenan.

A bangaren Nabeel kam yayi mamakin ganin wannan Uwar gara da aka girke masa a gaba,Ibrahim ya dubesa yace" Nabeel Bismillah sauko nai Saving dinka tunda Aisha ta ki zuwa kuma ni Sam banfiye son yan aiki su sa min abinciba".

Nabeel ya cika da Mamaki,Wanda yakasa boyuwa harsaida ya furta,yace"kana nufin wannan ba ita bace

Please Login or Register in order to submit comment