Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawayene masu zafi suka soma sintin a kyakkyawan fuskarsa Wanda bai shirya zuwansu ba.

Ibrahim yakai faffadan hannunsa kan kafadar Nabeel ya girgizasa yace " Abokina mai nafadamaka Wanda bai maka ba yasa ka kuka?".

Nabeel ya kai hannu ya soma dauke hawayen da yazubo masa ,yayi Murmishi yace "Abokina baka gayamin maganar da zata bataminba ,natuno da wani abune amma nagode da kulawa ,ni kuma Sunana Nabeel Saminu nan ne gidan mu yakarasa fada tare da nuna masa gidan Yayansa Sulaima".

Ibrahim yayi Murmishi tare da fad'in " Masha Allah yau baka fita bane ?".

Nabeel yaji tanbayar tasoma gundirarsa ,Dan baifiye son surutu ba,amma kuma Sam wulakanci ba halinsabane,dadin dadawa kuma Wanda yake tare da shi d'in D'an manyane ba matsaransa bane amma yaxo yake masa magana yanisa kamin ya ba sa amsa da fad'in "wallahi yau banji dadibane shiyasa banje aikiba".

"Ayya sannu ko Allah ya baka lafiya ".
Ibrahim ya fada cike da tausaya ma Nabeel, hannu naga yasa a aljihu ya ciro wasu kudi bansan konawabane naga yamika ma Nabeel.

Nabeel yabisa da ido ,Ibrahim yayi Murmishi tare da fad'in " amsa mana ai ba rokona kai ba ra'ayinane kawai nidai kayimin addu'a ,kuma daga yau kadaukeni D'an'uwa,Aboki kuma Amini Wanda zamu baiwa juna shawara in wani yashiga matsala ko Farin ciki ".

Nabeel yayi Murmishi ya amsa tare da yimasa godiya yace" Insha Allah Allah dai yasaka maka da Alkhairi".

Ibrahim yace "ai munriga mun xama daya ".

Karar waya yasa Ibrahim zira hannu acikin aljihun gaban rigarsa naga yaciro wayan nan motorolla, mai katon kan nan gurin tsinin yana ta haske ,gani nai ya risna cike da girmamawa ya latsa kore ,naji yace " Assalamu a laikum Baffa gani nan karasowa insha Allah".

Banji mai akace ba daga daya bangaren ba nadai ga Ibrahim yanata Murmishi naji yace to sai nakaraso".

Ibrahim yadubi Nabeel yace "to Abokina Nabeel xan wuce Baffa na ya jirana a kasuwa ".
Nabeel yayi Murmishi suka karayin musabaha kamin suka rabu suna masu begen juna.

Nabeel kam mamaki yagama cika sa Dan baiyi tunanin Ibrahim nada waya mai kuma tsada ba irin haka,lalle Ibrahim Dan manyane,yasoma kirga kudin da yabashi dubu 5000 ne cike da wani farin ciki Nabeel ya mike yana ta Murnan zai koma makaranta Allah yasoma kawomasa mafita ,a she ciwonsa zai zama Alkhairi ga rayuwarsa,ko da ya koma gida yasamu Aunty Mariya yagamata komi ,tayi mamaki sosai dan kuwa tasan Gidan wambai dimin tarihin gidan nan akwai Alkhairi sunada girmama d'an adam basuda wulakanci su Sam "kai Nabeel nayi maka farin cikin haduwa da yaron nan me sunan sa?"

"Ibrahim yace sunan sa, nan dai Nabeel ya gayamata yadda zayyi da kudin da Ibrahim yabasa ,ta ko tayasa murna ya ciro 500 yabata da kyar ta amsa ,shikuma yasoma shirye shirye komawa makaranta,bayan yagama komi yasoma karatunsa cikin kwanciyar hankali,kwatsam sai rannan Suleiman yaje shagon su Nabeel yaje amsan kudin da akebasa,nan fa yasamu labarin rashin zuwan Nabeel gurin aiki,D'anjummai ya kara da cewa shi rabonda ya sa Nabeel a ido wajen waya 1 kenan ,baya xuwa Dan haka yatafi bai da abin bashi tunda Wanda yake aikin mugune yamin vakin cikin a bin da nake samu ,kaga kai ma yaja ma ,Dan haka sai anjima .

Suleiman fa yacika yayi fam ga wani takaici ga talauci ,Dan kuwa yau tunsafe yake zaune a kasuwa bai yi cinikiba,daga shi sai 150 ,azafafe ya juya yasoma masifa yana ta kumfar baki bai zame ko ina ba sai gida yana xuwa bai ga Nabeel ba ,Mariya kam dayake tasan halin mijinta bata tankamasa ba,yana ta mita wallahi sai yayi nadamar rashin zuwansa ,tagane sarai Nabeel yake nufi......!

Maman Khaleel

din kuce✍️ .

Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin k'ai.

Page 27&28

Nabeel bashi yadawo gida ba sai misalin 2:30pm ga yunwa ya kwaso kunsan yadda Dan makaranta yake inyadawo ,da Yayansa yaci karo a kwar gida ,gabansa yabuga dam!bai taba ganin Yayan nasa a irin wannan lokacinba ,da sauri ya karaso kusa da shi cike da girma mawa yasoma fadin"Yaya lafiya na ganka a gida ?"

Ai kamin Nabeel yagama rufe baki Sulaiman ya kai ma bakin Nabeel naushi ,ai ko sai jini bai sarara masa ba ya shararamasa mari nan fa yasoma dukansa ta ko ina tare da fadin Dan ubanka wallahi sai ka fadamin in da kake zuwa da baka son zuwa wajen aiki ,yau ga d'an iskan yaro mara mutumci ,Suleiman haka yadunga dukan Nabeel yana ta kuka,jin kukanne yasa Mariya fitowa gida da gudu nan fa tasamu mijinta yasamu D'an mutane yanata kila kamar yasamu d'an banza,tai tai ta karbai amma takasa gashi layin ba maza sai mata wadanda suka leko da ga gida jensu suma suna ta ba Suleiman hakuri duk wacce tazo da niyyar zata amshi Nabeel sai ya daka Mata tsawa tare da fad'in munafukai kuban waje Dan uwanku ko nawa in ya lalace dawa za'ai kuka.

Can daga sama sai gashi Allah ya jefo wani bawan Allah zai wuce da sauri ya karaso wajen yanufi Suleiman tare da fad'in" megida kai masa hakuri,yako bangajeshi, nan wannan bawan Allah dayake shima Dan bana bakwai ne yasoma nad'e hannun riga ya dunfari Suleiman gadan gadan yajanye Nabeel da karfin tsiya yawurga gefe ,nan fa fad'a yagaure tsakanin Suleiman da me ceto Suleiman yanufo Nabeel wannan bawan Allah yace wallahi kana tabasa sai na taka ka dan ka haifeshi ai ba kai ka hallicceshi ba duk mugun halinsa,Dan haka karka kuskura ."

Suleiman fa yaga Wanda yafishi fitsara babu yadda ya iya dole yajuya suka hada ido da Mariya yako sakar mata wata uwar harara,ai da sauri ta nufi gida ta fad'a d'akinta ta bankosa Dan batasan me zai shigo yamata ba,Dan zai iya hucewa akanta.

A zafafe ya shima yashiga gidan ,sai a sannan jama'a suka soma jefa kalaman bakinsu akan Suleiman, akan abinda ya ai kata bai kyauta ba.

Wannan bawan Allah dai ya aika akasiyo masa ruwa mai sanyi ya ba Nabeel Wanda yayi tumu tumu da shi ,ya amsa yasha aka kawo masa ruwa anan makota ya wanke fuskarsa ,wannan bawan Allah yace" yakuke da wancen da ya dakeke?"

Nabeel cikin wasu hawaye masu zafi yace "Y'AN UBA NE mu Yaya na ne shi uban mu daya".

Wannan bawan Allah dai cike da mamaki yace " Y'an uba,lalle biri yayi kama da mutum haba gaskiya naga cin zalin yayi yawa da ma haryanzu ana wannan kazamin Y'an ubanci haka, Allah ya kyauta,wai ma me kamasa?".

Nabeel ya kara sharce hawayen bakin cikin kamin yace "Yaya nima ban sani ba kawai na dawo makarantane nan dai yafada masu yadda abin ya faru,ya kara da cewa kuma ina zuwa wajen aikin ,sai dai tunda muka fara C'A banjeba sabida karatu ,kuma in nadawo inje makarantar Allon na dauki karatu,gurin malam Mai rauhani ,shima kyauta nake zuwa .

Wanda Nabeel ya kira da Yaya naga ya dubesa cike da tausaya wa idonsa yaciko da kwalla dankuwa shima ya gamu da bakin halin Y'an uba dankuwa shima yasha wahala,Sam bai San tunawa abinda ya wuce ,yace" naji ka kara hakuri kaji shi ke biya ma kudin makaranta?".

Nabeel dan yasiya ma Yayansa mutumci sai yace "eh shi ke biya mun ".

"Nan dai wannan bawan Allah yasoma ba Nabeel shawara akan ya dunka zuwa aikin yayi hakuri watarana sai labari ,kaji duka biyun kaje ma'ana kaje aikin ka kuma je Makaranta domin duka a in nema ne ga d'an'adam ,ni sunana Yusuf ina nan sagagi da zama nan dai yaciro katinsa yaba Nabeel tare da basa 1k yace yasiyi omo ya wanke Uniform d'insa ,akarshe yace wannan katin shagonane ina cikin kwari ne aduk sands kake neman wani tai mako to kabiyo wannan address din kowaye kanuna masa wannan katin zai kawoka har in da nake kaji kanina ,kayi hakuri wataran zasuyi mamakin abinda zaka zama ,domin nima na D'an d'ani kwatankwacin halin da kashiga amma yanxu fa komi yaza ma tarihi kaji".

Nabeel ya amsa ya masa godiya shikuma ya wuce cike da takaicin abinda ya faru yanxu.

Kowa ya koma gida akabar Nabeel shi kadai a kofar gida yana ta juya katin da kuma kudin da Sabon Yayansa Yusuf yabashi,ya mike yaja jikinsa ya nufi lungun da zai fitar da shi bakin titi ,dai dai wajen shagunan nan nagefen hanya gaban gidan koguna ya hangi wata bafulatana tana damun fura Nabeel ya karasa wajen yamata sallama,

"ta amsa ".
Nabeel yasiyi Furarsa yasha ya koshi kamin ya nufo gida zuciyarsa tana ta d'ar - d'ar kar kuma ya shiga gidan bai abinda zai biyo baya ba.

Juyawa naga yayi yanufi masallaci yaje yayi sallah yaroki Allah ya sassauto da zuciyar Yayansa ,daga nan yanufo gida cike da kwarin gwiwa tare da kuma addu'a a bakinsa.......!

Maman Khaleel

d'inkuce✍️.Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dan Allah ina Neman Afwan d'inku masoyana najina shiru na tsawon kwana 2 sakama kon zazzabin da nayi amma yanzu Alhamdulillah nasamu sauki .

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page29&30

Da addu'a ya shiga cikin gidan gamida sallama bai samu kowa ba a tsakar gida ya shiga dakinsu yama wannan katin b'oyo maikyau ,bai hadu da yayansa ba sai bayan sallah isha ,yasamesa adakinsa yana kallon talabiji yayi sallama bai ko kallesa ba bare ya amsa masa sallama,Nabeel yakarasa shiga dakin ya durkusa har kasa ya sunkuyar da kai cike da ladabi ya dubi Sulaiman yace "Yaya Dan Allah ina Neman a fuwarka bisa b'ata ma rai da nayi d'azu amma insha Allah ba zan sake ba ,kuma insha Allah daga yau zan cigaba da zuwa makera indai hakan zai fantama amma ina rokon Alfarma guda d'aya Yaya dan Allah...!"

Sai kuma yayi shiru maganar ta mak'ale a makoshi.

Sulaiman ya wurgomasa wata uwar harara kamin yadubesa a wulakance yace "um hum ka karasa maganar ka in mai yuwace naji in zan iya dauka in kuma abin watsarwace kuma to kai nake sauraro munafuki".

Wasu hawayene suka soma zuboma Nabeel a kyakkyawar fuskarsa ,ya sa hannu yasoma dauke hawayen kamin yace " kayi hakuri Yaya dama zan ce ne Dan Allah zan dunga zuwa makaranta innatashi sai nawuce wurin aiki kamar yadda nasoma a baya, amma in kace na hakura to nahakura da karatun har a bada".

Jikin Sulaiman fa yayi sanyi tuno kalaman mahaifinsu in da yace "Sulaiman kai Babba a cikin Y'ay'ana ga fa amanar Autana nan na baka wallahi in dai kaci amanarsa to kasani Allah bazai barkaba kuma Nabeel yarone zakaji dadin zama da shi ,karkabari yayi kukan rashin iyaye ka k'addara nima bana raye, azaman mu ka zamemasa gata kazama abin nan da hausawa kamma lak'abi da Babban wa Uba,Karka tauye shi game da karatunsa damin yaron mai tsananin son yaga yayi karatune me zurfi".

Sulaiman ya sauke wata a sararriyar a jiyar zuciya,(eh mana Dan kuwa da yayi amfani da maganar mahaifinsu da Nabeel bai yi kuka ba).

Ya dubesa yace "naji amma kasani babu naira ta da zanzuba ajikinka wai da sunan kai karatu, kuma daga yau kasani kudin aikin ka ni nake karba nake yimana cefane a cikin gidan nan,saboda da kai a ke ci dan nalura kamar kafi su Salisu ci, Dan haka kar ka ma sa rai da kudin aikinka ,bare kayi tunanin biyan kudin makaranta kaji nagaya ma Dan kar kace na ba ka a b'oye katashi katafi kaban waje jikan mangofak".

Nabeel dai yamike cike da wani bakin cikin abin da Yayansa yayi masa,wasu hawaye ne suka soma masa sintiri a fuskarsa da Salisu sukaci karo abakin kofa ya haskasa da tocila yako sa dariya har da buga kafa yace " yaro d'an garin Kano gaka a cikinta,sai dai kai da farin ciki har a bada,in dai kazabi cigaba da zama a garin nan yakuma sa masa dariya ".

Nabeel da sauri yakarasa shiga dakinsu yafashe da wani kuka mai ban tausayi yasoma fad'in Allah ga bawanka a tsanani kai ne kai sanadiyyar zuwa na garinnan Allah ka kawomin karshen zamana a garin nan indai babu alkhairi acikin zamana agidan Yaya na".

Haka Nabeel yaciga ba da rayuwa acikin gidan Yayansa yakuma cigaba da zuwa aiki da makaranta har term ya kare akasoma maganar kudin wayek,wanda zasuyi ,Principal din makarantar Nabeel ya sama bayan antashi break wannan kuma shawarar wata malamar su ne mai suna Malama Rabi saboda ta dade da fahimtar halinda Nabeel yake ciki dan wata rana Nabeel yazo makaranta kayansa sunyi cud'u-cud'u sai kyallin daud'a suke shine yakirasa yake masa fad'a" halinda kasoma dauka na kazanta ba a bu ne mai kyau ba,dan haka Nabeel ka canza kar ka ban kuya mana kanina, kaga fa makarantar nan tana ji da kai kar ka bari a saka a gaba duk k'ok'arinka kaji".

Nabeel ya nisa sai kuma ga hawaye shar - shar ,nan fa malama Rabi ta ruke ma Nabeel hannu tajasa bayan aji tace meyasa ka kuka daga fad'ama gaskiya ko abinda nafad'a ne yasaka kuka?".

Nabeel ya share hawayensa yace 'Aunty ba haka bane".

"To menene?".
Nabeel ya yi shiru dan bayason yabada labarin halinda yake ciki,domin bai kamata duk abinda Yayansa yake masa yagayama wani ba dan Yayansa yafisa gaskiya in bai tai makasa da abinda yake samuba to wa zai tai makamasa?
Yayi zurfi sosai wajen tunani.

Aunty Rabi ta dafa kafad'ar Nabeel tace" tunanin me kakeyi ne haka Nabeel? gayamun matsalarka in yakamata nabaka shawara ne a matsayina na Malamarka wadda daga nan banwuce komiba tafada cike da hikima ,a matsayinta na uwa dan ta haifi Nabeel dan ko Malama Rabi bayarinya bace amma in ka ganta bazaka taba cewa ta a je yara 5 ba ciki kuwa harda siriki.

Kuyi hakuri da wannan dan Allah .

Maman Khaleel

Dinkuce✍️.


Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 31&32

Nabeel ya dubi Malama Rabi yayi Murmishi Yace"Aunty ai kinwuce Malama a guna ke uwa ce a gareni nan dai Nabeel yagayamata kadan daga cikin halinda yake ciki".

Malama Rabi ta tausaya masa kwarai tundaga wannan rana duk bayan kwana 2 zataba Nabeel naira 100 wai ya sayi sabulun wanki,sannin hakanne yasa ta tura Nabeel wajen shugaban makarantar saboda
yasan Nabeel, bayan Nabeel sun gaisa da Pc Malam Aminu ,sai kuma yayi shiru.

Malam Aminu yadubi Nabeel fuskarsa dauke da Murmishi yace "Muhammad Nabeel me ke tafe dakai ne ?".

Nabeel yasoma sosa kai yasoma inda inda am...am Malam dama wani tai mako ....!" sai kuma yayi shiru yakasa karasawa saboda nauyin maganar da zayyi.

Malam Aminu yakara gyara tsayuwar glass dinsa yakara mai da hankalinsa kan Nabeel Yace "Nabeel yi maganar ka kai tsaye kaji karkaji fargaba".

Nabeel yakara rusnawa tare da fadin "nagode kwarai Malam kamin yagaya masa tai makon da yake nema agunsa".

Malam Aminu yayi gyaran murya yace " naji bayaninka Nabeel zanyi ma wani tai mako dama dubu 15,000 ne kudin ko ?".

Nabeel Yace "eh hakane".
Malam Aminu yayi Murmishi kamin yace" to ni zan baka 10,000 sai kaje ka kawo cikon 5000 kaji ".

Nabeel yaji dadi sosai yayi masa godiya yabar office din cike kuma da tunanin in da zai samu cikon 5000 shidai bai da hanyar da zai samu 5k da wannan tunanin ne yaje yasamu Malama Rabi yagaya mata Malam ya dauki nauyin jarabawarsa,itama tayi
murna sosai tayi masa fatan alkhairi tare da fadin kadage da karatu kaji ko Insha Allah Allah zai zama gatanka kaji.

Nabeel Yace" insha Allah zan dage nagode ".

Ko da Nabeel yakoma gida yarasa yadda zai yi ya samu 5k yacika kudin makaranta can yatuna da katin nan da wannan Yayan ya basa yako hau duba cikin kayansa dafarko bai ganiba yashiga tashin hankali sai da yasoma daga kayan d'aya bayan d'aya yana zazzagewa kamin yafado yamakale a cikin wata riga yasauke wata ajiyar zuciya ya na hamdala ga Allah ya dauka yasa katin a aljihu ya fita yau kam bai je aikiba,kwari bai sha wuyaba wajen neman shagon Yusuf Entepricess ba wannan katin yayi matukar temaka masa kwarai har ya isa shagon sa ,Yusuf ya na ganin Nabeel ya fadada Murmishinsa yace " Nabeel yau kai ne a shagon mu to sannu da zuwa Yusuf yasa aka kawomasa abinci yaci yakoshi dama yau yadawo makaranta akace abinci yakare yayi hakuri gashi yazo yasamu me lafiya yaci harda nama bayan yasha lemun kwalba mai sanyi ,Nabeel yadubi Yusuf Yace"nagode Yaya Allah ya saka da Alkhairi Allah ya jikan mahaifa".

Yusuf yayi dariya yace "Ameen ya Allah Nabeel nagode ,Yusuf sukacigaba da hira da Nabeel har suka kai kan maganar karatu,nan ne Nabeel ma yasoko maganar cikon kudin jarabawarsu ta waec,bai boye masa komiba na tai makon da pc yamasa ba,kamin yadora da fadin yanzu 5k kawai yarage ita nake so in nasamu nacika kamin lokacin".

Yusuf yayi Murmishi aransa ya yaba da hikima irinta Nabeel, wanda sam a maganarsa babu roko aciki.

Yadubi Nabeel yace " to nima zan bada tawa gudun muwa yasa hannu a aljihu yaciro 7,000 yamika masa yace ganawa kaje kacika kadage kafito da result me kyau kaji kanina,ka kuma kara hakuri da yadda ka tsinci kanka kar ka sa rai a abin wani ,kuma dan Allah kadage da zuwa wajen aikinka watarana sai labari kaji .

Nabeel harda kwallan farin ciki yayi ganin kudin dumus a hannunsa lalle na Allah basa karewa a duniya yamasa godiya yatafi suna masu farin ciki.

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah yau su Nabeel sun kammala jarabawarsu ta Waec kowa kagani acikin daliban nan suna cikin farin ciki tare da addu'ar Allah yasa su samu sakamako me kyau.

(Da wannan nema nima nake ma masu jarabawar bana ta Waec fatan nasara Allah yasa tafito da kyau Allah yasa corona tazaman maku AlkhairiπŸ˜„ ga jarabawarku Allah yasa a samu sakamako me kyau fatan nasara ga masu waec2020.)

Nabeel sun jero da wasu abokanansa suna ta fiya suna hira kowa addu'arsa bata wuce ace jarabawrsu tafito da kyauba ,naji wani Hashim nacewa wai in waec din mu tayi kyau kuma naci jam sai bayero wai wayaganni nazama Enginia ,can kuma wani naji yanacewa niko wallahi nafison nayi aikin banki,bawani acikin su kuwa naji yace shi Soja yakeso haka dai kowa yake ta fadin ra'ayinsa amma banda Nabeel wanda shi yasan yagama karatu kenan tunda bai da halin cigaba da karatunsa ,dankuwa ko da abokanansa suka ce kai Nabeel kai ogane kila kai Babban aiki zakayi dan kafimu kokari shiyasa ma bakace mana komiba.

Nabeel yayi yake yace"kai ya ni dai nabarwa Allah zabi duk abinda Allah yayi mai kyaune a rayuwata banda wani zabi face nasa".

Sukace hakane zabin Allah kuma shine zabi ba namuba muma munbaiwa Allah zabi sai kaga abinda kakeso ba alkhairi bane abinda bakakawosaba kwata kwata a rayuwarka sai ka ga shine alkhairi agreka in ji Hashim.

Haka suka ciga ba da tafiya har suka kai mararrabar da kowa zai tafi gida sukai bankwana kowa ya tafi nasu gidan cike da farin ciki,Nabeel kam makera yatafi yasamu aiki sosai oga Danjummai ya aje masa bayan yayi sallah ya yasoma aiki bashi akabashi kudin abinci ba sai karfe 3:30pm yaje yasiyi shinkafa da wake mai da yaji wadda taji kayan lambu kunsa kanawa mai da yajinsu ba cimar talaka bace πŸ˜‚ yaci ya koshi daganan ya wuce masallaci yagabatar da sallar la'asar ba shi ya tashiba sai 6:30pm ya nufi gida jikinsa na masa tsami,haka rayuwa taciga ba da tafiyarma Nabeel gashi yau yasamu kusan shekara 4 a Kano wanda yayi dai dai da shekarunsa 18 dai dai a duniya yanzu takura ta ragu wajen Yayansa yanxu za' a iya cewa Nabeel yana dancin gashin kansa ,ana cikin haka wata rana yadawo kasuwa yadawo yasamu Malam Saminu ya kawo masu ziyara shida Yayan Nabeel Aliyu kai Murna kam wajen Nabeel ba sai nafada maku ba mai karatu ,kallo daya Malam Saminu yayi ma Nabeel yagane yana cikin wani hali,ya rame yayi duhu gashi bashida wata suturar arziki ,aransa yace anya kuwa Sulaiman ya rike amanar da nabashi kuwa?......!

Maman Khaleel

dinkuce ✍️.Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 33&34

Nabeel ya rungume d'an'uwansa suna masu farin cikin ganin juna ,cike da tausayawa malam Saminu ya dubesu,sai kuma suka tuno masa da mikinda yaki warkewa a zuciyarsa,wato rasuwar Halima mace tagari macen kwarai mace mai hakuri da dattako ,macen da tasan hakkokin mijinta,nan da nan idanunsa suka kawo ruwa sai alokacinne su Nabeel suka farga da halinda mahaifinsu yake ciki ,Nabeel ya matsa kusa da shi ya ruko hannunsa yace"Baba lafiya me yasaka kuka haka?".

Malam Saminu yayi Murmishi tare da dauke hawayensa yace "bakomi Nabeelu ganinku ya tunamin da haifiyarku hakika narashin macen kwarai Allah yajikan Halima y'ar 'aljanna".

Gabadaya sai da suka zubda hawaye ji suke kamar yau suka rasata musanman ma Nabeel Wanda yafi kowa shakuwa da ita, hakika sun ban tausayi matuka Dan nima sai da nakoma gefe na share kwalla.

Kamin naji Nabeel nafadin Ameen ya Allah.

Malam Saminu ya dubi Nabeel yace "Auta ya aikin anatayi ko ?".

Nabeel yace " eh Baba muna tayi gashi yanxu ma anfito da wasu samfur din kira kala daban daban yanzu ma wani keji ya fito na kaji shima da karfe a ke yinsa na gidan gona ,anan Kano mune muka farayinsa daga waje ake kawosa ,shine wani mai kudi yazo yakawo ma oganmu hoton kejin shine fa ogan ya nunamin nace masa zamu gwada mugani,aiko kamar wasa aka kawo min kayan aiki nan da nan muka hada guda daya, Alhajin nan na zuwa yagani yayi ta mamaki shine ma yace ai masa guda 50 yanzuma ana kan aikin ne Baba".

Malam Saminu yayi farin ciki da samun cigaban da yaronsa yasamu cike da karfafamasa gwiwa yace "Nabeel kace muma kasarmu ta ci gaba muma muna da masu yin abubuwan waje,kaga da gomnati zata nemo irinku a daukaka darajar aikin nan wallahi da kasa ta zauna lafiya da matasan mu basu sa rai da abin wasu ba ,ko su tsaya shaye shaye,ko sara suka kai da sauran wasu al'amura ,gaskiya Nabeel in dai anason kasar mu ta cigaba to sai anjawo kalarku ajiki masu sana'ar hannu a tallafamaku da jari kaga kuma wasu zasuci abinci ta karkashinku,kai ba kai ba ma saurayi na tabbata har da magidanta irina zasuzo ma aikatar ko da ko kwashe karfene zasuyi kuma zasu samu abin sawa abaki tare da iyali,Allah dai ya shige mana gaba Allah kuma yabama ikon yima shuwagabanninmu biyayya sukuma Allah yabasu ikon kyautatamana Ameen".

Aliyu da Nabeel suka amsa da Amin suma da dare gabadaya suna dakin Sulaiman yau kam Nabeel yaga tattali wajen y'an uwansa ta yadda baka isa kaga ne komiba domin kowa cikin su sai sama Nabeel albarka suke ,alokacin da Malam Saminu yake cewa Sulaiman ashe d'an' uwanka ya kammala karatun sa na Secoundry ,Sulaiman yawani washe baki tare da bugun zuciyarda suka zomasa lokaci daya,yace " Wallahi kuwa Baba gashinan rashin kudi ne ma yahana asaman masa gurbin cigaba da karatunsa anan BUK tunda kasan Autan naka a kwai kwakwalwa...!

Tofa kunji karyafa a gun Sulemanu dayasoma girbota yanzunnan mudai je zuwa dan jin yadda labarin zai cigaba.

Maman Khaleel

dinkuce✍️.

*Y'AN UBA NE*

*( TRUE LIFE STORY )*

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ



Please Login or Register in order to submit comment