Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji wata yarinya nafad'in" Baba ina kasamo D'anfulani me kyau haka?".

Suleiman yadubi Nabeel nan da nan sai kuma wani kishin sa yataso masa najin Nabeel fa duk gidansu yafikowa kyau da nutsuwa uwa uba kuma gashida ilmi da sanin yakamata,ko dayake yarone,amma sai yadake yadubi y'ar tasa yace "muje gida Saratu Babanku ne kinji ?".

Saratu dai tanata faman murna tadubesa " sannu da zuwa Baba k'arami".

Abin yaba Nabeel dariya yadubi yarinyar dabatafi shekara 6 amma sai wayau ,yarike mata hannu tare da fad'in "yauwa yarinyar Baba ".
Tare suka shiga gidan ,inda gaba daya dakunan gidan uku ne said Dan karamin tsakar gida da kicin a gefe sannan ban daki ,sai kuma nahango d'an karamin bene naleka can nahango Suleiman na kokarin bude dakin wannan shi ke alamtamana nan ne turakarsa.

Nabeel yana tsaye atsakar gidan yaran Suleiman sun zagayesa suna ta masa d'umi ,sai ga Matar gidan tafito fuskarta dauke da Murmishi tanufosu,tana fad'in kai Salma kuna da abin mamaki,ai kwabari yahuta mana daga zuwansu.

Nabeel yayi Dariya wadda takara fito masa da ainihin kyansa gawata wushirya nan wadda take atsakanin shiryayyun hakoransa farare tas,kamin yadube yace
" sannu da gida Yaya mun sameku lafiya?".

Mariya wadda mamaki yacikata Dan kuwa Sam wannan shi ne Wanda Suleiman yake bata labari Wanda Mamansu tarasu,Tace Nabeel ko Ahmad? ".

Nabeel yayi Murmishi yace " Nafarkon dai nike wato Nabeel Autan Baba".

Gabadaya akasa Dariya,Dariyar da tai saurin fito da Sulaiman yadubi matarsa Mariya wadda take ta Dariya itada su Nabeel, nan da nan sai wani kishi yataso masa,yace wannan wani irin sha shancine Mariya da hankalinki da komi kintsaya sai Raman washema yaro baki kike kamar wata sauna? Mutum yadawo daga tafiya babu wata tarba sai ma shashanci da yara ke wata kalar macece?."

Maman khaleel

dinkuce ✍️.

Y'AN UBA NE

(TRUE LIFE STORY)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel ) ________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 17&18

Mariya tayi shiru duk da bayau Sulaiman yasoma yimata tijaraba amma na yau yafi ta daban dan mamaki,to me tayi wanda za'ace ankirashi da shashanci?.

Shin wai me hakan yake nufi,naga sam sanda kannansa suka zo gidan nan ba haka yayi ba ,gashi nan sai ma raini da rashin kunya babu abinda suka iya ,idanun ta suka ciko da hawaye,nan da nan shima Nabeel idanunsa suka ciko da hawaye kamin yace" Yaya karki yi kuka dan Allah kinji,jeki kinji gurinsa karya kara fitowa kuma".

Cike da son Nabeel da kyawawan dabi'unsa tasa gefen hannunta tashare hawayenta tanufi saman sa,kallo ma bata isheshiba ,takara sa inda yake zaune sai faman cika yake yana batsawa,dan yanzu yasoma kishin Nabeel ai ba ta raha da su Salisu haka sai ma kawo masa korafinsu da take kullum ,tadubesa cike da kula tace "haba baban su Salma kaya hakuri nataho sai Nabeel yagai dani naga sam bai dace ba ace yaro na ma magana ka hofintar da shi kuma...!".

Yakatseta cike da masifa da fadin" Eh badole ba tunda shi ya aje ki badole kitsaya kita bude masa baki nake ga ni kaina nadade banga dariyar kiba irin tayau,to bari kiji in gayamaki indai kinason zaman lafiya babu ruwanki da yaron nan in ba haka to wallahi sai kingwammace kida da karatu na gayamaki.

Mariya dai tayi shiru tanajin tijarar da yake har yakai a ya ,kamin tace"to kayi hakuri nabarka lafiya".

Ta kai wa nan ta mike tafita abinta.

Da dare su Salisu suka dawo da ga kasuwar kwari ,sai ganin Nabeel sukai a gidan ,nan da nan dan annurin zuciyarsu ya koma Salisu aransa yace Maye sai da yabiyosa kenan ,Nabeel kam da bai san dawan garin ba yanufi Salisu cike da farin ciki dan sudade basu ga juna ba,sai yau yace"la dama kai ma kana nan ne Yaya Salisu? ".

Salisu ya turbune fuska batare da yasake kallon inda Nabeel ya keba yace " um magulmaci kazo ko kai ma hmmm sai kuma naga yayi shiru ko me ya tuna oho,naga dai yafada daki,Nabeel dai duk wani farin ciki da yazo dashi sai yanema ya rasa domin tun ayau yasoma ganin canji awajen wanda ya dauko shi ,ga kuma wata matsala kuma tana son kunno masa ,duk jajircewa da kuma da kakkiyar zuciya irin ta Nabeel sai da tai rauni,kawai sai ji yayi wasu hawayen tausayin kansa ya kamasa tare da nadamar biyo Yayansa ,to yanzu ya zayyi ,haka yayi kuka mai isarsa kamin ya kwanta bayan yayi sallah isha.

Haka rayuwar Nabeel takasance acikin gidan Yayansa yau dadi gobe babu,gashi yau wajen satinsa 2 da zuwa Kano sam yaga babu alamar za'a kai shi aiki,sai dai yayi ta yawo in yagaji kuma yakoma gida suyi ta hira,da Mariya,amma da zarar taga yamma tayi sai kuma tace yatafi waje kar yayansa yazo yagansu tare dan gudun fitina.

Aranda yacika kwana 20 ne yau yak'udurta ma ransa yau zayyi ma Yayansa maganar aikinsa ,a dakin sa yasameshi yana shirin tafiya kasuwa bayan sun gaisa yace " Yaya daman kan maganar aikina ne ,nace bari natuna ma ka sannan da kuma maganar makaranta".

Yajuyo yamasa wani kallon wulakanci ,kafin yace naji ai dubawa nake, nama wani abokina magana yace ajirashi zai ma wani dan uwansa magana sai kadunga zuwa inafatan ka fahimta ,sannan kuma maganar karatu babu shi Dan ni kai na nauyi yamin yawa sai dai kasamu daya wato aikin ,ai badole bane sai kayi karatun boko ba ,naga ai mu ba yi mukai ba kuma me yafi karfinmu?.

Dan jin amsar da Nabeel zai ba ma Yaya yansa , sai kubiyo ni gobe in meduka yabani dama .

Nagode.

Maman Khaleel

dinkuce✍️

Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Dedicated to:
Ibrahim Aliyu Bros wannan page din nakane Baba na Ubangiji Allah yasaka maka da mafificin Alkhairinsa Ameen.

Special gifts to:
Duk Masoyana ana ko ina kuke maza da mata ,face book da WhatsApp ina matukar jin dadin Comments dinku Allah yabar mu tare πŸ₯°Ameen.

Daga Marubuciyar:

Habiba

Kishiyar zamani

Ni ke da gaskiya

And nowπŸ‘‡
Y'AN UBA NE

Page 20&21

Nabeel yayi shiru tuno alkawarin da yayan nasa ya daukarwa mahaifinsu,in da yake cewa"in sha Allah Babu wata tawaya da zata samesa Baba na maka Alkhawari kamar yaddan nakulada su Salisu haka shima Nabeel zan kula da shi ,hatta da karatunsa Baba zai cigaba insha Allah.

Ya na kaiwa nan wasu hawaye ne suka soma rige-rigen fitowa daga fararen idanuwansa,aransa yace "ai gara ka kai ni Makaranta Yaya da da ka kaini wajen aiki domin wannan rayuwar in baka da ilmi da kai da jaki duk daya kuk..!

Kau! kau!!kau!!! Lafiyayyun Marinda Nabeel yaji kenan a saman kyakkyawar fuskarsa,Wanda shi kansa bai San zancen xucinsa ya fitoba.

Afirgice ya dago yadubi Yayan nasa yaga sai faman haki yake yana ta zazzare ido ,Nabeel yayi saurin kas da nasa Idon ,sai faman zubda hawayen bakin ciki suke.

Sulaiman yadaka masa tsawa tare da fad'in" ni Nabeel kake kira da Jaki,Mara ilmi ko?".

Da sauri Nabeel yasoma fad'in ni Yaya Suleiman bance ma kaba wallahi,kayi hakuri wallahi kayi duk abinda yadace a kai na,Dan Allah Yay..!

Dasauri yakara dakamasa tsawa tare da fad'in ni tashi kaban waje sha shasha kawai karatu dai in dai kana nan gidan to bazakai ba sai dai kabiya da kudinka".

A bakin kofa Nabeel yacikaro da Salisu ,suka kyalkyale masa da wata dariya mai ban haushi,Umar ne kawai naga fuskarsa Sam abinda d'an'uwansu,babu halin magana yanzu shima yasamu kasasonsa ,amma tabbas bai ji dadin ganin Nabeel ba a haka,domin wallahi da yasan za a taho da Nabeel garin nan Sam baxan yarda ba ,gashi yanxu anrabosa da gatansa anzo ana wulakantasa,duk da suma gatansa ne amma bakamar yadda su Ahmad zasu kula dashi ba,kamar ya dawo baya ya lallasheshi,sai dai ba dama,haka Nabeel yacigaba da rayuwa acikin gidan d'an Uwansa,ankaisa gun aiki awata mak'era inda yake kirar tukwane na holoko,da bokitai,da kaskon tuya,Matsami da sauransu,haka zai yini yana aiki amma sai dai abashi na abinci ,haka zai amsa yama sa godiya mai yawa yanufi gida.

Kwanci tashi babu wuya awajen Allah yau gashi Nabeel shekararsa daya acikin garin Kano,a cikin shekara dayan nan babu kalubalen da bai ganiba,yanzu shekarunsa sha 14 kenan kullum yaje aiki yana Dan tara kudinsa,dasuka kai 5000 yasiyo ma kansa Uniform na makarantar Islamiyya da na Boko, islamiyya yabiya ma kansa kud'in Register ,boko yashiga Jss1 dake nan cikin Kabara ,Uniform din sun amsheshi sosai haka yasoma zuwa,in yadawo aiki ya tafi wajen aiki gashi ya karbu awajen aiki,Dan shikansa ogan Nabeel mesuna D'anjimmai yakara samun Kostoma sosai domin yanxu cininkinsa karuwa yake kullum,gashi yana son durkusar da shi da wannan karatun nasa,domin in dai a kaxo siyan tukunya ko Murhu ko Matsami,na juya wainar fulawa Wanda shi Nabeel d'inne yasoma yi gashi ya karbu sosai gashi mata nata tururuwar zuwa siye,yau ma hakan ta kasance anxo siyan abin juyin wainar fulawa ,gashi d'aya yarage gashikuma suna da nisa kuma guda biyar suke so ,gashi babu kuma Yau Nabeel bai zo ba,yana ji yana gani cinikin ya wuceshi,Dan koda yadauko masu na Sani yaron da suke aiki a shagon cewa sukai basuso Dan wannan yafi tsayawa,sun hakura wataran in sun zagayo sazo su saya,wannan abin ba karamin yima oga D'anjummai ciwo yayi ba, gashi yanxu yasoma ganin kamar karatun nasa yafi aikin ,yayi kwafa tare da fadin zan yi maganin karatun naka ne yaro sai dai ya zabi daya ko karatu ko kasuwanci.

Kuyi hakuri da wannan baya wa saboda wasu aiyuka da nakeyi ina barar addu'arku.

Maman Khaleel

dinkuce✍️.

Y'AN UBA NE

( True life story )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan Page din nakune d'ungurin gun masoya na ako ina kuke bisa nuna soyayyarku ga wannan littafi ina godiya da kulawarku gareni ,gashinan kuyi yadda kukeso dashi πŸ₯°.

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now πŸ‘‡
Y'an uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 21&22

Oga D'anjummai ya zauna yayi shiru yana bakin cikin samun rashin cinikin da Nabil yajamasa,Habu yadubi oga D'anjummai cike da karya murya yace"Oga wallahi abin nan da yaron nan yake yima Muguntane yo in ba haka meye ?. ace yaro sai mugunta,dan ya iya abu haba,wallahi kai kabarshi ,muda bamuje makarantar ba munkasa cin abincine ko ko ince munkasa rayuwa ?".

Oga D'anjummai fa maganganun Habu fa sun soma shigarsa,yako gyara zama yadubi Habu yace"abinda nazauna nake ta tunani kenan Habu yaron nan yagama rai nani wallahi indai yazo to zai zabi daya aiki ko karatu,haba dayanxu ban samu 2000 ba amma yanxu duba fa ka ga 500 kawai akai yau gaskiya da sake,ai kaima Habu hadda kai da bakason kai aiki mekyau".

Habu dai maganar taso tab'ata masa rai,amma dan yatunzura Oga yace" to ai kasan oga baka koyamana ba ,shikam dama ai ya iya bak'in ciki kawai yake gwadama dan yaga bamu iya ba".

Nan dai suka cigaba da kulla yadda zasu ma Nabeel in yaxo wajen aiki.

Nabeel kam yana makaranta Test ya rikesu sun kusan fara jarabawar shiga Ss 2 bayan sun gama yafito yanufo gida ga wata yunwa dake addabarsa,har yashigo gida,yasamu matar gidan bata nan wai taje barka,can Sagagi,gidan kanin Ummanta,matarsa ta haihu,ya tanbayi Salma yace "akwai abinci kuwa a gidan nan Salma?".

Salma tadubesa cike da girmamawa tace " Baba Nabeel yakare muncinye da zun nan da mukadawo makaranta kana jin yunwane kai ma Baba Nabeel?".

Nabeel yayi Murmishin yake yashafa cikinsa wanda yake ta kara tun a hanya yadubi diyar yayan nasa yace "a'a banaji Salma dama kawai na tambaya ne dazun amakaranta nasiyi abinci naci kawai na tanbayane nagode".

Nabeel yafada dakinsu yayi shiru yarasa sukuni ,abin duniya ya shesa,yau sam bai ci komi ba tuno kalamin yayan sa inda yau dasafe yake tanbayarsa yana zuwa kuwa aiki?.

Nabeel yace " eh Yaya ina zuwa amma sai ranan da banida makaranta na k...!

Ai baiko bari yarufe baki ba yalailayo wata uwar ashariya yajefa ma Nabeel.

Nabeel ya runtse idonsa ,Sulaiman kam yadora da fadin wallahi nagaji da ciyar da kai din da nake,bazaiyuwuba ni da wahala kai kuma da cinye min abin cin gida,wallahi sai dai kaxaba ko karatun boko ko kayi sana'a dan bazan iya ciyar da kato kamarkaba ,kawai sai dai kaci kai kashi ka kwanta kai shememe da kai ba,dan haka indai kanason zaman lafiya to sai dai kazabi daya ko makarantar ko kuma aiki,ko kuma kabarmin gidana kaje can kakaraci iskancinka da bokonka kaje shiyama komi dan haka indai makaranta yau ma zakaje to ni Sulaiman na haramta ma abincin gidan nan yau kaje kaci boko".

Nabeel yasharce hawayen da zubomasa afili yace :dama haka horon yunwa yake ,gashi yana son karatunsa shin yanxu meye mafita?.

Haka Nabeel ya wuni cikin wannan kunci ga yunwa ,aranan bai samu yaci komiba sai dare .

Haka Nabeel yasoma daukar sabuwar rayuwar da ya tsinta kansa aciki,a haka har yasamu ya suka i jarabawa sungama lafiya,suka samu hutu,Nabeel ya mai da hankalinsa zuwa wajen aiki sosai sai dai yanxu Ogansa yarage basa kudin kashewa haka zaici aiki yataso yadawo gida ba ko sisi,gashi yana son yakai kudin makarantar allo da yake zuwa ,yau sati 3 uku kenan bai bada kudin Laraba ba,yau dai yace bazashiba tunda bashi da kudin biya.

Haka rayuwa tacigaba da juyawa Nabeel yau fari gobe baki,gashi yasoma gajiya da rashin bashi nakashewan da oga Danjummai ya dai na yi,zai ga yaba kowa kudi me 100 me 200 akwaima wanda akeba 500 kullum amma shi 200 da akebasa yau kusan wata da wani abu ba a bashiba,gashi ankusan koma wa makaranta babu kudin da zaisayi littattafai nashiga sabon aji bare kuma aje da maganar kudin makaranta, ga shi suturar sa suna neman yimasa karanci,dankuwa tunkayansa dayazo dasu sune yake ta jalautawa dan kuwa ko sallah yayannasa bai taba yin hankalin yimasa ba,abubuwa sun soma taruwanma Nabeel suna son yimasa yawa ,kallo daya zakamasa kagane yarame yayi wani duhu nawahala,abinda Nabeel bai sani ba shine Yayansa yahana abasa kudi shike amsa duk karshen wata yaje yasha shagalinsa da kudin ,bai taba nunawa yana amsaba sai dai yanxu yaga yasakin masa fuska sosai zai ci abin ci sau uku arana ,bai da Matsala yanxu ta gurin wannan.

Nabeel Yana zaune abakin shagonsu ya hangi wasu yara suntaso daga makaranta suna sanye da Uniform suna tafiya suna turanci harsuka gifta shi ,bai saniba hawaye naga yanata zuba akuncinsa nabakincin rashin zuwan sa makaranta,gashi yau wajen satin su Uku da komawa tunda yaje satin da yawuce akace yaje ya kawo kudin makaranta tundaga ranan bai koma ba,saboda bai da kudin da zai biya,yatuno rayuwarsa acan gidansu a jos wanda kullum makaranta bata wuce su basu yin latti bare kuma fashi in ko sukai fashi to larura ce me karfi,yatuno kalamin mahaifiyarsu inda takance Nabeel Kai dai kanason kayi karatu me zurfi amma sai nake jin dakyar zakasamu saboda nan gaba bansan irin rayuwar da zata riskekuba kai da y'an uwanka,sannan ina son fadama aduk inda kasamu kanka ,dakazamo mai hakuri da juriya kakasance me wa Allah godiya adukkan halin da kashiga ,sai kaga in yatashi sai yama ka wani canji da abinda zai zamo maka alkhairi ,Nabeel aduk cikin yarana kai kafita daban da sauran y'an uwanka saboda Allah yama wata baiwa wanda bakowa yakema wa ba ,zaka ga jarabawa kala kala in kai hakuri sai kaga kaci nasara.......!

Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Dasunan Allah mai rahma mai jun k'ai.

Page 23&24

_____Nabeel yayi kukan rashin uwa yau sosai fiye da tunani ,dan da ace mahaifinsu ne yarasu to da basu tagayyara hakaba domin da yanxu suna hannun mahaifiyarsu ,dole duk wanda yarasa uwa yayi kuka saboda uwa wata bangoce ,inuwace mai dadin zama in ko karasa ta to tabbas karasa wani bari na rayuwa ,Mahaifiya jigo ce ga rayuwar yaranta,ba Nabeel ba hattani sai da na tausaya ma Nabeel din domin tauye hakkin yayi yawa.

A ranan da zazzabi yakwana shiru shiru bai fitoba Mariya tana lura da shi,tayi shiru bata ko ambaci sunan saba wajen karyawa sai da tabari kowa yafita agidan ciki kuwa hadda yayansa, kamin taleka d'akin kudindine tagansa yanata rawarsanyi ,ai dasauri ta k'arasa cikin d'akin tana salati ta yaye lullubin da yayi ta tab'a goshinsa taji shi zafi rau nan fa tasoma Ambaton Sunan sa" Nabeel mekedamunka haka?".

Nabeel Wanda da kyar yake iya bude baki cikin makekkera ta me zazzabi yace "kai na ne Aunty ".

Mariya cike da tausayawa ta fita takoma dakinta sai gani nan ta nai tafito da kofin kunu da Dankalin Hausa Wanda tasoya tashiga d'akin ta tadasa tabasa yasha yadan ci dan kalin kad'an kamin ta ballamasa paracetamol guda 2 tabashi,ya amsa yasha yamata godiya,yakoma ya kwanta wani bacci ne yayi a won gaba da shi ba shi ya farka sai misalin 12:30 yamike zazzabin yasauka yaji yana jin zafi yafito yasamu Aunty Mariya tana kokarin yin girkin rana tana ganin sa ta fad'ad'a fara'arta tadubesa cike da kulawa tace " Nabeel har katashi ya jikin naka?".

Murmishi Nabeel yayi kamin yace "naji sauki Aunty wanka ma nake son yi yanxu ,nagode da kulawa".

Tayi Murmishi tace" to masha Allah ga wani ruwan zafi nan da zanma d'anka wanka d'auko bokitin na juye ma".

Yace "to Aunty nagode".

Bayan yayi wanka ya d'auki ya mutsattsun kayansa Wanda suka Kod'e suka fita hayyacinsu Dan ma yadine amma duk yatashi saboda sawa gabadaya yanxu kayansa basu kala takwas ba sai dai ko da yaushe fes suke sabo da shi Sam bashi son k'azanta,yafito Mariya ta dubesa cike da tausaya masa Dan kuwa ko ba'a fad'aba daka kallesa kasan ya rame haskensa ma yaragu,fuskarnan tasa tayi fayau da ita sai hanci kawai.

Abinci tabasa yaci yakoshi kamin yafita yaxauna a bakin soron gidan, wani matashi na hango yadun faro inda Nabeel yake zaune fuskarsa dauke da Murmishi ga ba d'ayan sa bai fi shekarun Nabeel din ba wato shekara 17 da haihuwa ba yaro bakine kakkaura gajere ne shi yana da fadin fuska kyakkyawane shi babu lai fi yayi shigarsa ta alfarma ,yana yawan ganin Nabeel dasafe in yafito zashi makaranta shikuma zai tafi kasuwa shagon mahaifinsa.

Ya karaso yamika masa tare da fad'in " Assalamu alaikum Abokina".

Nabeel yayi Murmishi shima ya mika masa hannu yace "wa alaikumus-salam yakake?".

Matashin nan yayi Murmishi yace " lafiya Alhamdulillah,Nasan bakasanniba ko?".

Nabeel yayi dai Murmishi yace "hakane d'an uwa".

Shima Murmishi yayi kamin yace" to ni sunana Ibrahim wambai ni yaron wamban kano ne, an haifeni anan cikin garin kano anan cikin kabara can bayan gidan koguna ,ina yawan wuce wa tanan layin in zani kasuwa dayake ban dade da dawowa garin ba dayake ina karatune a garin Abuja American University Wato Maryam Abbaca...!

Maman Khaleel

d'inkuce✍️.

Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 25&26

"Dayake ina karatune a garin Abuja a American University wato Maryam Abbaca,mu muna son d'aga martabar kasarmu ta haihuwa wato Nigeria".

Nabeel yayi Murmishi tare da jin sha'awar ina ma shine yasamu wannan gatan ,yasan shi har 'abada bazai samuba ga shi nan Secondary ma ta gagaresa,wasu hawayene masu zafi suka soma sintin a kyakkyawan fuskarsa Wanda bai shirya zuwansu ba.

Ibrahim yakai faffadan hannunsa kan kafadar Nabeel ya girgizasa yace " Abokina mai nafadamaka Wanda bai maka ba yasa ka kuka?".

Nabeel ya kai hannu ya soma dauke hawayen da yazubo masa ,yayi Murmishi yace "Abokina baka gayamin maganar da zata bataminba ,natuno da wani abune amma nagode da kulawa ,ni kuma Sunana Nabeel Saminu nan ne gidan mu yakarasa fada tare da nuna masa gidan Yayansa Sulaima".

Ibrahim yayi Murmishi tare da fad'in " Masha Allah yau baka fita bane ?".

Nabeel yaji tanbayar tasoma gundirarsa ,Dan baifiye son surutu ba,amma kuma Sam wulakanci ba halinsabane,dadin dadawa kuma Wanda yake tare da shi d'in D'an manyane ba matsaransa bane amma yaxo yake masa magana yanisa kamin ya ba sa amsa da fad'in "wallahi yau banji dadibane shiyasa banje aikiba".

"Ayya sannu ko Allah ya baka lafiya ".
Ibrahim ya fada cike da tausaya ma Nabeel, hannu naga yasa a aljihu ya ciro wasu kudi bansan konawabane naga yamika ma Nabeel.

Nabeel yabisa da ido ,Ibrahim yayi Murmishi tare da fad'in " amsa mana ai ba rokona kai ba ra'ayinane kawai nidai kayimin addu'a ,kuma daga yau kadaukeni D'an'uwa,Aboki kuma Amini Wanda zamu baiwa juna shawara in wani yashiga matsala ko Farin ciki ".

Nabeel yayi Murmishi ya amsa tare da yimasa godiya yace" Insha Allah Allah dai yasaka maka da Alkhairi".

Ibrahim yace "ai munriga mun xama daya ".

Karar waya yasa Ibrahim zira hannu acikin aljihun gaban rigarsa naga yaciro wayan nan motorolla, mai katon kan nan gurin tsinin yana ta haske ,gani nai ya risna cike da girmamawa ya latsa kore ,naji yace " Assalamu a laikum Baffa gani nan karasowa insha Allah".

Banji mai akace ba daga daya bangaren ba nadai ga Ibrahim yanata Murmishi naji yace to sai nakaraso".

Ibrahim yadubi Nabeel yace "to Abokina Nabeel xan wuce Baffa na ya jirana a kasuwa ".
Nabeel yayi Murmishi suka karayin musabaha kamin suka rabu suna masu begen juna.

Nabeel kam mamaki yagama cika sa Dan baiyi tunanin Ibrahim nada waya mai kuma tsada ba irin haka,lalle Ibrahim Dan manyane,yasoma kirga kudin da yabashi dubu 5000 ne cike da wani farin ciki Nabeel ya mike yana ta Murnan zai koma makaranta Allah yasoma kawomasa mafita ,a she ciwonsa zai zama Alkhairi ga rayuwarsa,ko da ya koma gida yasamu Aunty Mariya yagamata komi ,tayi mamaki sosai dan kuwa tasan Gidan wambai dimin tarihin gidan nan akwai Alkhairi sunada girmama d'an adam basuda wulakanci su Sam "kai Nabeel nayi maka farin cikin haduwa da yaron nan me sunan sa?"

"Ibrahim yace sunan sa, nan dai Nabeel ya gayamata yadda zayyi da kudin da Ibrahim yabasa ,ta ko tayasa murna ya ciro 500 yabata da kyar ta amsa ,shikuma yasoma shirye shirye komawa makaranta,bayan yagama komi yasoma karatunsa cikin kwanciyar hankali,kwatsam sai rannan Suleiman yaje shagon su Nabeel yaje amsan kudin da akebasa,nan fa yasamu labarin rashin zuwan Nabeel gurin aiki,D'anjummai ya kara da cewa shi rabonda ya sa Nabeel a ido wajen waya 1 kenan ,baya xuwa Dan haka yatafi bai da abin bashi tunda Wanda yake aikin mugune yamin vakin cikin a bin da nake samu ,kaga kai ma yaja ma ,Dan haka sai anjima .

Suleiman fa yacika yayi fam ga wani takaici ga talauci ,Dan kuwa yau tunsafe yake zaune a kasuwa bai yi cinikiba,daga shi sai 150 ,azafafe ya juya yasoma masifa yana ta kumfar baki bai zame ko ina ba sai gida yana xuwa bai ga Nabeel ba ,Mariya kam dayake tasan halin mijinta bata tankamasa ba,yana ta mita wallahi sai yayi nadamar rashin zuwansa ,tagane sarai Nabeel yake nufi......!

Maman Khaleel

din kuce✍️ .

Y'AN UBA NE

( TRUE LIFE STORY )

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar :
Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya
And now
Y'an Uba ne

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 25&26

"Dayake ina karatune a garin Abuja a American University wato Maryam Abbaca,mu muna son d'aga martabar kasarmu ta haihuwa wato Nigeria".

Nabeel yayi Murmishi tare da jin sha'awar ina ma shine yasamu wannan gatan ,yasan shi har 'abada bazai samuba ga shi nan Secondary ma ta gagaresa,wasu

Please Login or Register in order to submit comment