Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

kwanakinsa yatarasu a d'akin Sahura inda yake tan bayarsu,"shin me kika yanke game da girki da kwana Uwargida ?"yafad'a yana Murmishi.

Sahura wadda take tam da takaicin wai Saminu yau kecemata yabatun raba kwana,cike da gadara tadubesa awulakance kamin tace"kwana d'ai d'ai nake so".
Murmishi yayi shi yaji dadi ma da furucinta,yadubi Amarya Binta yace "to kinji abinda Yayarki tafad'a yamaki?".
Binta cike da ladabi tace " eh yayi "

Yaji dadi sosai,Bayan yamasu nasiha akan Binta ta bi Sahura su zauna lafiya duk abinda take nema tazo tasamu Sahura ta tanbayeta kuma sam shi baya son kananun magana,su zauna lafiya shine burinsa,Binta tadubi Angonta tace i"nsha Allah zakasameni me bin Umarninka nagode".
Yaji dad'i har ransa,amma ita Uwargida sai hura hanci take dankuwa ita kadai tasan ukubar da zata ma wannan bakar jaraba,dan da alama taga Saminu yana wani rawar kafa .

Jin Shirun Sahura yasa Malam Saminu yadubi Amarya yace to tashi kije dakin ki ,tarusna tace dan Allah in babu damuwa Aban ni su Salisu su tayani kwana .
Aiko bari taru baki tayi tamike tana kad'a hanu lala,banhaifarma kishiya yarana ba,dan haka kima tashi kibarmin daki kema ki haifi naki wannan nawane! tafad'a a tsiwace.

Bako musu Binta ta mike tace to kiyi hakuri Yaya nabarku lafiya.

Bayan shekara 1 da Auren Binta wahalakam tashata iri da ban da ban ga makirci kala kala,a wahale ta haihu inda tasamu diya mace inda taci suna Surayya,Surayya nada wata Takwas Binta ta shirya ta nufi garinsu da nufin ganin gida, yabata sati 3 aiko Binta na tafiya, tace ita sam bazata dawoba,akai akai tace sam ita takarda take bukata ,domin tagaji da azbtarwar Sahura, ita bata taba samun matsalada shi ba sai matar sa dan haka tahakura ,tako samu daurin gindin wajen iyayenta,dan komi yan rakiya sunfad'a basu boye komiba wannan shine sanadin futar Binta gidan Saminu.

Sahura kam sai hura hanci take tazama free mijinta yazama nata ita kad'ai.

Bayan Shekara Uku darabuwar Saminu da Binta sam bai hakura ba dan akace in namiji yasoma hada mata 2 to da wuya kuma ya iya zama da mace daya dan ya dan dana yaji dadi,yaciga ba da sawa aransa aduk lokacinda yasamu ya yarinya da tamasa to tabbas zaiyi Aure tunda yanzu Alhamdulillahi yamallaki gidan kansa kuma ginin mace 2 yayi,amma ita Sahura tana ta daga hanci gidan tane da yaranta,(kuji shirmeπŸ€”)
Kwatsam rannan yazo mata da batun karin Aure wai zanso kuka yadda Sahura tayi ma Saminu danko ranan vata barsu sunruntsaba,tun yana lallasahi ,har yagaji,shidai yasan Aure babu fashi dama tayi hakuri.

Tundaga ranan bai sake tada zancenba,ita atunaninta banbaminta ya ci ,anfasa Aure,kwatsan rannan taga masu gyaran gida ansoma gyara batakawo komiba taga anshafe gida da fenti duku gidan da d'akuna ,blue fent irin na da ,taga sai mata siyayya yake ayau kuma gashi yakawo mata dinkunanta kala uku da turmi 2da janbaki ,gazal,da hodan nan tada Babba ta gari fara,da takalminta Dan madina me tudu da na kwalliya guda,abindai gwanin sha'awa kayan fadar kishiya zir,hankalinta yayi matukar tashi tayi holi da kayan tace" yo Auren kuwa zakayi Malam ?yanxu karasa cin amanar da zakamin sai na Aure ,Wallahi Malam kacuceni ka siyo kuka kuma rashin zaman lafiya a gidan ka.

Yayi Murmishin takaici kamin yace "Sahura dama muntab'a zama nace da ke zan zauna ke kadai batare da abokiyar zamaba?to kicanza wannan karon Auren Budurwa zanyi ki kama girmanki domin ni nasan Halima zata biki sau da kafa,kuma gobe gidan nan kina da baki daga Gumel dan haka ki canza kinutsu ayi taro lafiya,atashi lafiya, dan harda su Baban Soro zasuzo da sauran y'an uwa dan haka komi ya rage naki,nidai harkullum ina kara gayamki Sahura ki rike girmanki to.

Sahura wadda tarasa bakin bagana wadda runda taji sunan mahaifinta yasa tasan lalle Malam Saminu abin nasa da gaskene kuma tasan Babanta shine waliyyinsa,dan Babanta tasansa sarai bashida wasa,lalle tasake taku tabari suwatse kamin tafito da sabon salon rashin mutumci.

Haka kam akayi bata nunama kowa komiba,ta saki jikinta akai komi da ita wanda yasa Babanta jintausayinta,sabanin da dayataho daxafinsa inyasamu tana ma mijinta rashin mutumci, dansun sha zagi kan mutuwar Auren Binta.

Bayan Biki da kwana 2 su Baban Soro suka tarasu adakin Malam Saminu sukai masu nasiha sosai ,da zasu tafi Babanta yaja mata kunne akan karta cutar da abokiyar zamanta dai dai kwayar zarra ,inta cutar da ita Allah bazai barta ba.
Takosa kukan muna furci tasoma share hawaye tana fad'in insha Allah Baba babu komi nidai agaidamin da Baabanmu.

Yace "to zataji share hawayen Allah yamakuAlbarka."
"Ameen Baba".

Bayan kowa ya watse akabar daga Ango sai matansa,inda Halima takasance marasanjiki,taja yaran nan ajikinta,yakasance ita ke masu komi harda wanki da sharan tsakargida da sauran aikin gida,wannan abun ba karamin Dadi yama Sahura ba domin ita yanxu tasamu y'ar aiki ,domin yanzu harda kayanta take kwasowa ta ba Haliman tawanke,kwanci tashi bawuya a wajen Allah yau Halima takwashi wajen shekara daya da rabi agidan Saminu Wanda kullum aikinta agidan karuwa yake danyaxu haka sahura tasake haihuwa ta biyar India tasamu Nafisa,komi na Nafisa yakoma kan Halima ,ga gorin Haihuwa kullum da take sha agun Sahura ,wadda bata da kugun haihuwa sai dai aci ai kashi,tun abin bai damun Halima har yasoma damunta,wata rana Malam Saminu yana dakinta,suna hira cikin hirarne Halima tasako masa zancen da ke matukar da munta,tace" wai Malam da gaske ni Bazan haihuba wai banida rabon haihuwa aduniya?kuma banida kugun haihuwa Dan Allah Malam da gaskene?tafada idanuwanta suka cuccuko da kwalla ta takaici.

Yadubeta cike da tausayi shikansa yana tausayamata,yasanta da San yara ,yasan duk yadda akai sahurace take mata gori,yakamo zaratan hannunta yahada da nasa, yana murzawa a hankali yana murmishi yace "kar naga sun zubo kinji,waye yafada maki haka ?wayace bazaki haihuba?"

Ta share hawayenta cike da kuruciya tace Maman Salisu ne kullum sai naji tace min wai ni banida abin haihuwa πŸ€¦β™€οΈnike nan daga ci sai kashi.

Abin yaso bashi Dariya ya rungumeta tsam ajikinsa tare da karajin wani sonta naratsa dukkan gabbansa,gakuma takaicin matarsa,yakawar da takaicin yasashi gefe,cikin wata murya naji Saminu na fadin" kema kina so ki haihune?".

Tai shiru tarasa bakin magana dan kunya sai kuma Murmishi take,ya dagota fuskarta,yace Halimassadiyya,tasunkuyar da kanta kasa,yace" dubeni kinji Matata?".

Tadago dakanta tadubesa tasauke idonta kannasa, tana Murmishi, shima yamayar mata da martani,kamin yace kema zaki haifamin yara masu Halayya da d'abi'u irin naki sannan kuma kyawawa insha Allah,ayau Allah zai karbi Addu'armu wadda kika dade kina najima da sanin kina tashin dare kiyi sallah don rokon Allah ,duk wani motsinki Halima akan idona da kunnena yake indai bama tare,bare kuma in ina tare da ke, kinji Matata, cike da son mijinta ta fad'a jikinsa tana zubda hawayen farinciki ,yasoma lallashinta dawasu kalamai masu taushi kamin daga bisani naga kidan yasoma canzawa rawarkuma anacanzata ahankali,tunkamin akoreni nama kai na kiyamullaili nafita nabarsu nace Allah yakawo maki Y'an biyu Halima.

Yau wajen watanta biyu Halima bata ga al'adarta ba ,batadamuba ,gakuma canji datake samu ajikinta,yawan bacci kamar kasa,wannan abin yasa Sahura jin wani takaicin Halima sakamakon rashin yimata aiki akan kari,a,a abudai kullum karuwa yake datasoma wanki sai taji tasoma jin bacci kamar wadda tasha kayan maye gashi tayi wani fresh da ita na shanunta sun kara tasawa,gaban Sahura ya buga ,kar dai ace yarinyar nan cikine da ita,tab aiko da masifa agabanki yarinya indai ko na tabbatar ko sai na zubar da shi ko ta halin k'ak'a......!!!!

Maman Khaleel
dinkuce✍️

Y'AN UBA NE
(True life story )
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Dedicated to: My Sister Aishanty Baby Allah yakawo miki miji nagari Musha biki yakuma baki lfy me dorewa AmeenπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ.

Special gifts to:
Aunty Hauwa (maman Uswan)

Ibrahim Aliyu Bros(Baba na)
Yusuf Nuhu
Maryam Ibrahim (Momina)
Fatima S Rabi'u (Besty na)

Ina godiya sosai Allah yaraya zuri'a ,wadan da kuma basu shiga daga cikiba kuma Allah ya kawo macen kwarai,da miji nagari Ameen.

Godiya nake da Addu'arku Masoya ina gani Sakonninku ga kadan daga ciki :

Sunana Maimuna Abdullah
Maman Khaleel
Barka dafara sabon novel Allah subahanahu wata'ala yanufeki dagamawa lfy san nan muna tare.

Sunana Fateema Hassan
Sis Maman khaleel na taya ki murnan fara sabon litafin ki Allah ya kara baseera da karfin ido,muna biye da ke sisπŸ‘πŸ‘.

Ina godiya sosai wadan da ma ban ambacesu ba ban manta dakuba ina tare dakumasoya Allah yabarmu tare a ko ina kuke🀝.

Daga Marubuciya:

Habiba
Kishiyar zamani
Ni ke da gaskiya

And nowπŸ‘‡
Y'AN UBA NE

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 7&8

____ Tab aiko da masifaa gabanki yarinya indai ko na tabbatar ko sai ba zubar da shi ko ta halin k'ak'aπŸ‘†.

Halima kam tana daki tana ta shirgar bacci,hankalinta kwance gashi baccin yana mata dad'i ,har kusan shabiyu bata fito ba,bare ta Dora masu Abincin Rana,Sahura fa tacika tayi fam ga yunwa tana ji gata da shegenci kamar gara,bare yanxu kuma ga tsotso,tamike tadaga labulen dakin Halima,tab aljannan duniya dama haka dakin ta yahadu tab lalle wadan nan yarinyar iyayenta y'anta y'ank'arya ne,ta tab'e baki kuma dai dakin balaifi yadanyi amma sai nasa yara sun rugurguza wadan nan tangaraye Dan Silva bazasu fasuba,bayan tagama karewa ko ina nadakin kallo,dan ko dawa sa kishi yahanata ziwa dakin Amarya tunda aka kawota sai yanzu da bala'i ya ciyota ,dayake Halima farace jajir ko ina najinkinta yadashe hatta tafin kafarta ,hannayanta kai gabad'aya jikinta ya dashe, ko ba 'a fad'amata ba ,tasan cikine,wani kishine ya turniketa tashiga d'akin dasauri tad'aga kafcecen Hannunta tasaukeshi a gadon bayan Halima jikake tas!!!.

Afirgice Halima ta tashi bakinta dauke da Addu'a ta bude idanunta sosai ta saukeshi kan na Sahura wadda take ta aukin zabga mata harara,kamin tace"to sannu kasa uwar bacci angayamaki bacci kikazo yi gidana,to kisani wannan baccin bazan lamuncesa,kifita maxa kiduba tsakar gida kamar na mahaukata,ga shi har lokacin girki yayi baki doraba,ubanki zaki basu suci ko me?".

Halima ta runtse ido domin tatsani duk rashin mutumcin da za'amata a zagi Iyayenta ,domin yana shigarta sosai,gashi bahalin da zatafad'a sai dai gani nai hawaye suna suntiri a kyakkyawar fuskarta,Sahura ta ta bude wagegen bakinta tana fadin" Au iyeee!!".
Lalle bari Malam din yadawo zanji dalili ko shine ya daure maki gindin kar ki mana komi Dan kinsamu cikin ajalinki,dasuri ta dago rinannun idonta wadan da tuni suka canza kala ,Sahura tace "eh ajalinki ki dauko domin sai naga bayanki Halima indai ina numfashi ni Sahura,ai dasauri Malam Saminu yashiga dakin dankalmar karshe ita yaji sai na ga bayanki Halima indai ina numfashi!,ganin ta tasa yarinyar mutane agaba kamar wata y'arta sai faman masifa take,yaji wani takaici da danasanin Aurenta da baitaba yiba arayuwarsa yau yayisa,kamin daga bisani yadubeta cike da takaici yace " fitan mata adaki Mara mutumci wadda bata kama girmanta,Babbar kwabo kawai,tadubesa shekeke,kamin tace" Au dama kai ka daure mata gindin yimin rashin mutum ci saboda za'a haifa maka d'an gol ,ai naga kamin wata tahaifama yaro ni nafara haihuwa agidan nan amma Baka taba cewa yau ki huts da aikin cikin gida ba sai ita wallahi Sam banlamuntaba dole tagirka muci".

Yakasa ce mata komi domin wani farin cikine ya lullubesa Wanda bai taba jiba,tabbas Sahura kincancanci tukuici mai tsoka inda kina da mutumci ,domin Sam shi baisan tanadauke da dansaba,yadubi Halima cike da so ya kamo hannunta yasoma ya dago fuskarta yana murmishi yasomayimata mai kwantar da hankali,yasa danyatsansa d'aya yasoma d'auke mata hawayenta tare da fad'in Halima ki dai na kuka kinji share hawayenki,aikine dai ko to daga yau ni Saminu naharamta maki yinsa,indai ba ranan aikin kibane,ke hattama da wankan yara na hana ai yaranane,suma suna da uwa tamasu kicigaba da rainon cikina har Allah yarabaki da shi lafiya,Wallahi duk abinda yasameki Halima ni yasama domin jin cikin nake kamar yadawo jikina,Halima ko k'uda ya tabaki indai nagansa to sai nayi maganinsa ballantana Dan Adam,kotu ce zata rabani da duk Wanda yatabamin ke,tsaki suka ji anja mai sauti tare da fad'in aikin banza ,tafita fuuuuuu!.

Yayi Murmishi yasan yanxu koda zatama Halima wani abun to zata rage dankuwa tasansa sarai babu sauki,yamaida dubansa ga Haliman wadda tayi shiru takasa ko motsi,yakara manta garesa,cikin wata murya mai tsaushi yace "haba Halima yanzu dama ciki gareki shine baki sanar daniba,sai dai naji abakin abokiyar zamanki?".

Cike da wata irin kunyaY'AN UBA NE

Cike da wata irin kunya tace" kaya hakuri Malam nikaina bansan INA dashi ba ".

Yayi Murmishi yace "badamuwa kinga a in Allah ko? shiyasa komi kai hakuri zai wuce Allah yarabaki da sh lfy".

Tayi Murmishiba tace komi saboda kunya Duk ta lullubeta .

Sahura kam Duk tahana kanta nutsuwa ,ta manta Allah shine mai yadda yaso, tamanta gori da cin mutumci da tadunka yimata ,itama yau gashi Allah ya bata, tafe take yanxu zatajegidan kawarta mai suna Asabe Birom ce ,amma ba Musulmabace ,tana zuwa tazayyanema Asabe komi ,nan fa Asabe ta soma tunzurata,tare da bats shawarar India tanaso da takaita gurin wani mai maganin da zai tai maketa,Sahura tayi shiru Duke iskancinta batason had a Allah da wani batta dai da rashin mutumci da mugunta,race a'a banaso amata komi domin yaja mn kunne sai dai I nada dabaru kala kala,Dan sai na zubar da shi Insha Allah.

(Nikuma nace insha Allah hakarki bazata cimma ruwaba)

Bayan kwana 2 Sahura tasoma Jan Halima ajiki bata ko sauraranta da aikinta tanuna ma Malam Saminu komi ya wuce said ma tayashi murna da samun karuwar da zasuyi ,hatta da Abinci, yau Halimance da Malam Saminu kusan tare suke aikin ,Suna cikin aikine Sahura tadubi Halima tace" gaskiya yakamata kisoma shan maganin Shawara saboda kasala da rashin karfin jiki,kinsan wani cikin babu laulayi sai dai kasala shine nace in babu damuwa da nabaki wani jiko,kinsha ko zaki samu kwarin jikin naki ko?".

Halima tai Murmishi tace "to nagode ".

"Kai ai yiwa Kaine kimsan Ku ciki bakinsane don't kowanne da kalansa."

Washegari kuwa naga takawo ma ta wani Abu akofi,tadubeta cike da kissa race "Halima gashi kisha wannan insha Allah zaki ji dad'in jikinki ,jikinki zayyi karfi".

Ta amsa zuciyarta fes, tai mata godiya ,batakawo komiba tai Bismillah takai baki tako sha,gani nai ta wani had'a rai tana runtse ido wani azababben d'acine ya ziyarci kwakwalwarta,ko ba 'a fad'aba wannan shuwakace da Mad'aci domin dacin yayi yawa,tadibi ruwa fari tasha amma Sam bakinta bai dai na ba .

Ai kamin minti biyar taji y'an hanjinta nakad'awa tare da wani hautsinawa nan take kuma mararta ta amsa....!

Kuyi hakuri da wannan bayawa saboda wasu aiyuka ne suka sha kaina shiyasa jiya bansamu yimaku typing ba amma kuna πŸ’–rai na.

Maman Khaleel
D'inkuce✍️
Y'AN UBA NE
(True life story)
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Daga Marubuciyar:
Habiba
Kishiyar Zamani
Ni ke da gaskiya
And nowπŸ‘‡
Y'AN UBA NE

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 9&10

Mararta ta soma daurewa, nan take tasoma karanto duk addu'ar da tazo bakinta,gawani tashin xuciya yana addabarta,can kuma sai yunkurin amai,da sauri tafito tanufi bakin kwararo tasoma sheka amai kamar zata xubda y'an cikinta,sai da ta amayarda komi na cikinta tas hatta da abinda takarya ya fita,ga wani ciwon ciki kuma da yake addabarta,dakyar ta iya dawowa bakin kofarta,ta wanke bakinta,tashiga daki,ta kwanta sai addu'a take, cikin wasu y'an dakiku taji ciwon cikin yana sauka a hankali,sai kuma wani bacci wanda zan iya kiransa da na wahala ya d'auketa.

Duk halinda Halima tashiga Sahura na lekenta ta windonta danhaka zance taga komi sai faman murmishi take ,afili naji tace yarinya sai dai kiga ana haihuwa acikin gidannan badai nan ba ,nan gidan su Salisu ne takara yin wani mugun murmishi.

Dayamma lis Malam Saminu ya dawo yaga bai ji motsin Halima ba ,ganin haka yasa yadubi Sahura da yake yaga suna shiri tunbayan hukuncin da yayanke akansu yace"Sahura lafiyan Halima kalau kuwa naga bangantaba?"

Sahura takarkace tasoma tattaro karyarta tasoma rerawa kamar haka"wallahi malam yau da amai ta wuni tagala baita sosai dan har saida na jikamata tazargade nabata sannan nace tashafa ma jikinta shine fa akasamu ya tsaya".

Cike da tausaya ma Halima gakuma farin cikin tai makon da Sahura tabata,yamike yace "nagode bari na dubata".

Tqbi bayansa da wata muguwar harara ,aranta tace ai insha Allah cikin nan kamar ya fita inga ta rawar kai.

Halima kam komi taji ,aranta tace Allah karabamu da makiran kishiyoyi,wadanda basu tsoron Allah.

Tana cikin tunanin ne taji Sallaman Malam Saminu takara gyara kwanciyarta,jikinta bakwari sosai dan dakyar tai sallar la'asar ko cire hijab din bataiba ,ga casbaha a hannunta tana ta tasbihi akan Allah ya tsare ta da abinda ke cikinta.
Ta amsa masa sallama cike da ladabi,yashiga ,ta mike tazauna sosai,shima zaman yayi a gefenta,yace " ya jikin naki?".

Bataiyi mamakiba dan taji komi abakin Sahura kawai sai tabisa dayadda aka fad'amasa.
Lafiya lau naji sauki sai dai tashin zuciya kad'an".

Yadubeta cike da tausayi yace "Allah yaye maki bari na nemomiki goro ko gauta ?".

Tayi Murmishi tace "to nagode".

********

Kwanci tashi ba wuya awajen Allah yau cikin Halima yakai wata 7 duk yadda Sahura zata bulloma wannan ciki Allah yana karesa,da alama Allah yayi alkawarin sai ya fito duniya,dankuwa wahala kam Halima tagani iyakar ganinta,ga yawan aiki da take kullum ,babu kakkautawa,har Allah ya sauke ta lafiya inda tahaifi d'iyarta mace sak Halima inda Malam yadauki son duniya ya dora wa jaririyan nan ,ranan suna yarinya taci sunan Mahaifiyar Samin wato Saudatu,inda suke kiranta da Inna.

Halima taga rayuwa ta kunci sosai agidan nan ita da d'iyar ta ,haka Sahura zatace ma Halima ta fito da Inna waje tasata aboki ta ajeta arana, haka zatai ta zufa dayake Allah yasama Innan hakuri,wannan yamangare wannan yakaimata rankwashi,musan man Salisu Wanda yadauki Sak halin Uwarsa Halima kam bata cewa komi,watarana anfito da Inna anshanyata kamar kayan wanki,gashi yau garin ana rana sosai sai faman diga take tana tsala kuka,gashi bahalin uwarta ta dauketa ace bata da kunya batada alkunya akan dan fari,gashi kukan yana cimata rai sai dai balin magana,ga y'an uwantanan suna ta mata dariya Nasiru yace kai nidai wallahi Inna tana bantausayi gaskiya bari nakaita gun Baabarta .tsawa Sahura ta daka masa to sarki gwanin na iya ban aikekaba kama wallahi ko dawasa kaje kataba yarinyarcan mekama da Aljana sai kagane bakadawayau kaji nafad'ama .

A na cikin haka sai ga Malam Saminu yayi mantuwa yadawo gida sai faman gumi yake domin yau akwai rana kowa yasan dai ranan rani tana da zafi ga sa kishirwa,tundaga nesa yajiyo kukan Innarsa ai dasauri yakarasa shiga gidan turus yayi yana ambaton Allah tare da kwalawa Halima kira ,tare da fad'in kina da lafiya Halima Uwartawa kika shanya da wannan uwar ranan kuma kinshige daki abinki!!

Yafad'a cikin kakkausar murya mai cike da takaici.

Halima tafito idanta cike da hawaye yatazo ta dauki yarinyar ya fixgota tadawo baya tai taga taga xata fad'i ya cakumota,azafafe yace "Halima wayace ki aje min yarinya da wannan uwar rana?".
Halima tai bakam takasa bashi amsa sai hawaye sai da yasake magana cikin tsawa kamin ta dubesa a firgice tace " um..um...um.!"

"Um wa? natan bayeki waye?".
Yaya ce tace " nasata acikin bokitin shine nasata ,tafad'a
Cikin rawar baki".

Wai wai wai zanso kuga yadda Sahura kebaza hanci da idanuwa sai zaresu take dan tasan Malam Saminu basauki ,aikamin tagama yanke me zatace sai jin saukar mari tayi kyawawa a kumatunta,2 masu kyau ,zatai magana

Please Login or Register in order to submit comment