Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwalliyarki kamin Nabeel din yazo? ".Aisha ta fada cikin jikin Umma tace ba shi bane wai yau nayi hakuri wajenta zashi yau.

Umma tayi Murmishi tace " Auta shine kuma na kuka ,to share hawayenki kinji Autana ,karki damu kinga hakan ai ba laifi bane Aisha kusan kullum nan yake zuwa ,itafa bai je wajenta ba,ko wannan zai nunamaki cewa kece a zuciyar Nabeel ba Asma'u ba ,Aisha Nabeel na sonki so mai tsanani kitayashi son Asma'u karki zama mai son kanki, dayawa kinga in baizuwa wajen ta ba zataji dadiba ,a kaddara kece Asma'u sai Nabeel yayita zuwa wajenta ke bai zo inda kike ba shin ya zakiji avin aranki?".

Aisha ta yi shiru kamin tadubi Umma tace bazanso hakan ba .

Umma ta yi Murmishi gamida shafa ma Aisha baya tace yauwa haka nake son ji .

*******

A bangaren Asma'u kam yau tacika da dokin zuwan Nabeel yaushine zuwansa na Uku gareta tunda magana ta yi karfi ,ta shirya sosai cikin Riga da zani na wani Material mai rawa kayan sun amshi fatarta sosai kasancewarta baka ce amma ba wulik ba.......!

BARI NAHUTA A NAN SAI KUMA IN MEDUKA YA KAIMU GOBE.

Yan uwa kuciga ba da min uziri wallahi aiki ne yayi min yawa shi'isa bakujina a kai a kai amma kuna raina ina maku fatan Alkhairi Masoya na ako ina kuke

Maman khaleel
din kuce ✍️.
Y'AN UBA NE

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

Assalamu alaikum warahmatullah yan uwa na Maza da Mata ina maku sallama irin ta addinin musulunci.
Bayan haka inama kowa da kowa barka dasallah dafatan Allah ya amshi ibadunmu Allah ya mai mai tamana amin.

Wannan page goron sallah ne gare Ku masoya kuyi yadda kukeso dashi.

Godiya ta musanman zuwa gareku yan uwa masu bibiyata akan cewa ko na aje rubutune to ban ajeba sai dan wani aiki da nakeyi,insha Allah zancigaba da kawo maku daddad'an littattafaina masu fadakarwa ilmantarwa gamida nishadantar daku masoya na ina ma kowa da kowa fatan alkhairi .

GAISUWA MAI TARIN YAWA GAREKU.
Arewa writer's Association Allah yakara hada kanmu yakuma karamana kaunar juna da zaman lafiya.
Fatan alkhairi gareki Aunty Hauwa Allah ya raya iyali amin.

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 79&80

Taku take dai dai har ta isa kofar gida inda tasameshi ya jingina da farar Frajen dinsa ya hard'e kafarsa cikin daya yamata kyau kyau sosai haskensa yakara baiyana alamar hutu ga sajensa Wanda ya kwanta yayi luf-luf baki sidik gwanin ban sha'awa tabbas nayi dacen miji nakwarai ingarma tafada acikin zuciyarta ,Murmishi tayi gamida sallama .

Shima Murmishin yayi gamida gyara tsayuwarsa ya amsa mata sallama ,yace" Babyna kinganki kuwa wai gaskiya yazama dole na biya wannan kwalliyar" ta dubi jikinta tayi Murmishi hijab ne ajikinta harkasa tace" to ai kaima Yaya Nabeel kayi kyau amma dai yanzu mushiga daga ciki ".

"To " ya amsa tana gaba yana binta a baya harsuka isa cikin gidan sai da suka gaisa da Umman su Asma'u kamin suka sh iga dakin Yayansu inda Asma'u ta shirya masa girki mai rai da lafiya dankuwa danbun kuskus tayi Wanda yaji ganyen Ogun ga kayan lambu sai kamshi yake tashi yaci sosai kamin suka Dan taba hira kamin daga bisani ya mata sallama tareda yimata ihsani yatafi yana mai farin ciki ,Sam ya manta da alkawarin da yayima Aisha sai da yaje gida yayi wanka ya kishingida akan katifarsa wayarsa CE tasoma Neman agaji ya jawota Murmishi yayi yace Ashnab Baby yadaga wayar tare da fadin" My Ashnab Baby kaina bisa wuya aimin afuwa yau dai nasan nayi lefi sai dai ayafemin kinji yawan ?".

Murmishi tayi mai sauti Wanda Nabeel baisan sanda ya lumshe ido ba ya bude a hankali tare da ganin hoton Aisha a fuskarta ta katse masa tunani da fadin" to nayi maka Uzuri Baban Soyayya ya Asma'u ?".

Yaji dadi harcikin ransa yace "Eshat tana nan Kalau ,ina Umma ?.

Aisha tayi yake tc " Umma na dakin Abba tundazu"

yace" to masha Allah yau wai saura kwana nawa ne Dan gaskiya nifa nakosa naji ki kusa da ni Aisha anya kina sona kuwa kamar yadda nake jinki acikin zuciya ta anya ?"

Dariya ce ta subuce mata wadda tazo mata babu shiri tace "My Ashnab ni bansan yadda zan fadama ba amma ni dai nasan Ina son ka amma ni nasan dole acikin mu biyun nan kafi son wata acikin mu kilama ita kakeso bani ba kake so ka wayance min amma bakomi bari na barka ka huta kar na dameka".

"Kul kika kashen waya Dan bangaji da jin Muryarkiba Aisha bazaki gane cewa ina sonki sai randa na mallakeki anan ne zaki gane cewa ni Nabeel Masoyinki ne na har abada ".

Aisha kam taji dadin kalaman sa dankuwa sai faman Murmishi take haka suka cigaba da hirarsu mai dadi daratsa zuciyar Masoya kamin suka yi sallama kowa ya aje waya yana mai farin cikin, bayan ya aje waya yakir Asma'u itama tayima sa bangajiya kamin suka sha hira kamin wani daddad'an vacci yayi a won gaba da su duka Masoya kowa yayi Bacci mai dadi mai cike da mafarkin kowacce itace tauraruwa acikin binnin zuciyar Gwarzonsu wato Nabeel.

******

Shiri a ke sosai kowani fanni gidajen Amaren kai harma da gidan Mijin kowanata shiri, Inda Nabeel ya shirya yatafi Jos wajen Yayyensa Mata wadanda suke daki guda suntattauna akan yadda bikin zai kasance sunvashi gudun muwarsu suma mai yawa tare da alkawarin zasuzo kano in bikin yarage Saura sati biyu Dan ayi komi akan idonsu ,ai ko haka akayi gidan Sulaiman yasha fenti yasha gyara yanzu fa yasoma saukowa da ga tsattsauran ra'ayinsa tunda yaga fa Nabeel fa ya wuce da tunaninsa yanzu yasoma shan kwana inbayyi wasaba to za'ayi ba shi sai dai ya dauki aniyar sisinsa fa bazai kasheba kama da ga abincinda za a ci zuwa omo ko Sabulunwanka Dana wanki duk shine zayyi ,koda ya samu Nabeel da zancen cewa yayi ai Yaya natanadi komi anjima za a kawo yasa hannu a aljihu yaciro 100k yace kasa wannan a aljihunka Yaya koda za a bukaci wani abu, ai tuni Sulaiman ya kaima kudin nan cafka yana fadin ai nike da abinda zanyi da kudi dama banyi dinkiba kaga yanzu nayi ko yadin nan ne nasiya nima nasa idan zamuje ansoma Auren."

Nabeel yayi Murmishin takaici yace "badamuwa ina zuwa Dan jirani ya Shiga dakinsa bai jima ba yafito hannunsa dauke da wata katuwar leda bak'a yamik'a masa yace kayan da nadunka maku ne na fitar biki Yaya kai da su Yaya Salisu kowa kala 2 ne kuyi hakuri naso ace namaku kala uku uku to hidimar ce sai godiya."

Baki Sulaiman yasaki kamar wani sakarai yana kallon Nabeel aransa yace anya yaron nan bai fara yankan kai ba kuwa inba hakaba ina yasamu wad'an nan kudin tuno urban kayan lefen da ke dakin Matarsa Mariya set 4 kowa 2&2 babu Wanda yasa masa hannu acikin lamarin Aurensa anya kuwa ?".

Nabeel yayi Murmishi yace" Yaya ni zanwuce gidan su Aisha ne yanzu ."

"To! to !!to!!! badamuwa adawo lafiya inji Suleiman".

Nabeel yabarsa atsaye rungume da kaya ya kulle dakinsa ganin ya hau mashin dinsa yasashi shiga cikin gidansa cike da tunani barkatai lalle yaron nan wai garin yayane Yaron nan yazo yafisu kudi ne gaba dayansu fa babu Wanda da yake samun kudinda yake samu tun yana karami har kawo yanzu yazama dole insa bincike kan Yaron nan ban yarda da shiba gaskiya dakinsa ya wuce baikoyi ko sallama ba anata masa sannu bai ma jiba saboda idonsa ya kulle da bakinciki gamida Hassada Wanda masu iya magana kema lakabi da hassada ga mai rabo taki kuma kowa yayi hakuri zaicinma nasara a rayuwa ,Mariya ta bi bayansa hannunta dauke da farantin abinci tashiga dakin bakinta dauke da sallama tasamesa yana ta sintiri abin duniya duk yadamesa ganin kaninsu daya yanzu banda shaye shaye babu abinda yake gamida daukan magana gashi Wanda sukai masa hasashen tawayan rayuwa yau gashi Allah yasoma dagashi,Mariya tadubi Suleiman tana Murmishi tace ya akayine Abban Salma kai da wa?".

Ya juyo yadubeta tayi masa kyau sosai acikin zuciyarsa yadan ji sanyi aransa ya jawota garesa yace bakomi Mariya banda tunanin Yaron nan anya Nabeel bai fara yankan kaiba Mariya ?."

"Subhanallah tafada tareda janye jikinta daga nasa tacigaba da cewa gaba Abban Salma ya kasance kana ma Dan uwanka kyakkyawan zato Dan kuwa kai shedane tun yaron nan na karami bai da abokin fada shi ba abokiba abokinsa dayane Wanda kowa ya sansa da shi shine Ibrahim yayan Aisha Dan gidan wambai Iowa yasan Nabeel a unguwar nan, kowa yana yaba mass visa kyakkyawar dabi'arsa ,Dan Allah wannan maganar kavarta anan wannan ai in wani yaji sai yace kana masa bakin........!"

Ai kamin ta karasa Sulaiman yasauke mata gardin hannunsa a fuskarta tare da nuns ta da yatsa yace fitarmin a daki ni ai na manta ke ai munafukace har nakawo maki maganar sa to kisani daga shi harke din ba barinku zanyi ba nagayamaki ki kiyayeni tunkafin na sabautaki .

Ai tuni Mariya ta fito daga dakinsa batakoma dakintaba sai da ta daidai ta kanta kamin takoma wajen kannan mijinta kuma makusantar Nabeel suka zauna suna ta hira kamar komi bai faruba ,saura kwana 7 aka kai akwatin Aisha mai ruwan madara da pink tsayawa bada labarin kayan da Nabeel ya zuba acikin akwatunan Amarensa fadama bata vakine ,sunje gidan Wambai sun sami tarba ta Musanman domin Umma yau kamar tagoyasu Dan tarairaya .....

Maman Khaleel dinkuce....✍️
Y'AN UBA NE
(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'ar Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 81&82

An masu shatara ta arziki a gidan wamba yayinda Umma tabada tukwicin 100k suka amsa ahannun aminiyar Umma sukai godiya kamin suka tafi suna masu farin ciki ,kowa na yaba ma iyayen Aisha Dan ko suna da karamci sosai ,kai Uncle Gaskiya kayi dace kaga yadda Umman su Aisha tamana dako mukamace muna son ganin Auntynmu Ummance tasa akarakamu can wani sashi na gidan muka ganta itama tana da kirki basuda kyamatar talaka,inji Hajara diyar Yayar Nabeel .

Nabeel yayi Murmishi gamida karajin son Aisha na ratsa kowace kafa da jijiyar jikinsa hakika son da yakema bazai faduba ya Allah kabani ikon yima matana adalci a tsakaninsu ,to amin Nabeel.

Yakara duban Hajara yace " haka nake son ji dama Aisha mace ce mai sanyin hali ".

"Ai kuwa kawu dankuwa mun gani.

Washegari da yamma kuma aka kai na Asma'u suma sunyi masu kyauta dai dai karfinsu yayinda kowa yake yaba kayan akwatin ana yaba ma Nabeel can naji wata yar kanzagi na fadin ba kayan ba a zauna lafiya,aikuwa inji Jummai makwafcirsu Asma'u ,wata kuma daga gefensu naji tace koma dai menene kaya sunyi Allah kuma yahada ma sa kan matansa Ameen tana kaiwa nan ta mike taleka dakin Ummansu Asma'u tayi mata sallama tanufi soro,baki suka tabe Jimmai tace " kai ni yau inaganin kitifirfirar Mata,suka sa Dariya tareda tafawa sukace wai wayaga San asani.

******

Nabeel fa bashida sukuni bashinan ba shi can ma'ana ba shi gidan Wambai kuma ba shi Kabara gidansu Asma'u kan yadda shagalin bikin zai kasance ,Wambai yataka muhimmiyar rawa wajen sha'anin domin yakira Nabeel shima yabashi tasa gudunmuwar a matsayinsa na Uba garesa ko da ko ba zai Auri diyarsaba kyautar kuwa itace Motace sabuwa dal kirar 4matik bakace wadda aka lullubeta da tinted tare da kyautar Muhalli mai dauke da Flat guda biyu ginin zamani gidan ya tsaru sosai, lokacin da Nabeel ya shiga cikin gidan yarasa bakin magana domin Wambai da iyalansa sunzamemasa garkuwa a rayuwarsa ,Wambai shine tsanin da yake kai a yanzu sa'an nan kuma yadauki diyarsa wadda yake ji da ita ya basa amatsayin Mata tabba Wambai da iyalansa sungama masa komi ya rungume Ibrahim cikin hawayen farin ciki yana ta godiya tare da fadin Ibrahim banida bakin da zangodema kai da iyayenka kune kuka maidani Mutum Ibrahim banida abinda zance sai dai Allah yabar mu tare Yakuma karawa dukiya albarka ya Allah...!

Rufemasa baki Ibrahim yayi yace "Haba Nabeel ni da kai daya muke a wajen mai martaba bana son naji kasake irin wannan zance in yaji kana wannan magana zai dauka ba daya muke ba ."

Nabeel ya share hawayenda suka zubo masa yasake rungume Ibrahim yana Dariya ,da dare yaje yama Sirikinsa godiya yace "Abba ina godiya Allah yama dukiya Albarka ".

Wambai yayi Murmishi yace " haba Nabeel banda abinka ai duk abinda namaka kai na nayi wa domin daya kuke da Ibrahim sai in ce Allah yasa alkhairi Angon mata biyu Allah ya hada maka Kansu ,yafada yana murmishi ."

Nabeel shima Murmishin yayi gamida kara yimasa godiya kamin ya mike yakoma wajen abokansa inda suke tsaye da y'an mata inda yasamesu suna ta fafatawa sun basu kudin su sannan kuma sukace gobe zasu kawo masu kayan drink ,Aisha sun kebe da angonta zaune suke agefe can wajen lambun gidan iska na kadasu mai dadi Nabeel ya dubeta ya gamida tsinko wata fure mai kyau ya kai hancinsa ya shaka wani kamshi mai dadi ya lumshe ido ya bude a hankali Aisha sai faman Murmishi take tace "ya dai Ashnab yau narasa gane kanka nalura yau nishadi kawai kakeji ".

Hannun ta yakama yasoma murzawa a hankali cikin wani salo yace " My Eeshnab kasancewarmu tare kadai ma nasani cikin farin ciki wallahi Aisha zuciya ta da gangan jikina duk ta kosa tajiki a kan kirjina ji nake kamar najawo jibin nan na ganki a cikin dakina mallakina wai Hmmm ranan bansan wani farin ciki zangwada maki ba ,Aisha Dan Allah kutaru kuzauna lafiya da Asma'u kinga itama bata da hayaniya kitaya musauke nauyin da Allah yaratamin akaina akanku duk da nasan kedin ta dabance cikin mata ,Aisha zaki sameni mutum mai bautamaki akan so ni bawankune ina sonki Aisha Dan Allah yau inason kimin abinda danaje gida zandunga tunawa yanasani farin ciki."

Aisha wadda Nabeel yagama kashemata jiki da kalamansa masu taushi ta dubesa tace "Yaya na kamar yadda nafada ma ni Aisha zakasameni mai kwantar da murya akowani lokaci ,idan inacikin kuncin kainake gani zuwaciyata ta samu sukuni ,haka idan ina cikin nishadi hotonka shine abokin hira ta kasani tarayyarmu da kai daga Allah ne ina sonka farin Masoyi sanyin idaniyata ".

Ai Nabeel bai San sanda yaja Amaryar sa ba ya rungume yasakarmata wani kyakkyawan kiss mai tsada sundade a haka kamin Aisha ta soma zamewa a hankali tana samun nasarar kwacewa tayi cikin gida da gudu bako wai waye zuciyarta fes.

Maman khaleel din kuce .... ✍️
Y'AN UBA NE
(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'ar Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 83&84

Aisha ta soma zamewa a hankali ,tana samun nasarar kwacewa tayi cikin gida da gudu ba ko wai waye zuciyarta fes.

πŸ‘†πŸ‘‡

Nabeel kam kallon ta yake cike da wata muguwar sha'awa gamida wani farin ciki Mara misaltuwa,wayarsace tasoma neman a gaji ya duba yaga Abokanansane ya mike da murmishi a fuskarsa yace "Hello ya akayine kungama ne?" Nabeel yafada cike da zolaya.

Isma'il yace" oho hakama zaka ce ko to Baban Soyayya mu mungama zamu wuce ko mutafi ne mubarka tunda nalura kafi Romeo iya soyayya ,shima ya fada cike da zolaya ."

Nabeel yace "kai Isma'il bana son sa ido fa ,to in ba haka va to zan hadama bom wajen uwar gida nace dazuwanka gidan su Aisha kasamo cingam ".

Dariya sukai su duka ,Isma'il yace " tab da bankoma gidan ba yau Dan Saudat fa karshece wajen kishi karufamin asiri nawan ".

Nabeel bai a je wayaba har sai da yakaraso inda a bokansa suke ,suka rankaya kowa yatafi gida cike da farin ciki .

Washe gari yakama shine ranan kamu inda suka kowacce amarya tashirya tsaf sai faman kamshi suke kowacce tanata fitar da wani sihirtaccen kyau Matan fa na Nabeel fa sai dai muce masha Allah sai dai kuma kowacce azuciyarta tana tunanin kila waccen tafini kyau haka suke ta tunani har aka gama kwashe kawayensu tsaf yarage sai su kadai Nabeel Wanda yayi wani masifar kyau cikin wata d'anyar Shaddarsa coffee wadda akai mata dinkin gidan sarakai kai kace wani jinin sarauta yakafa hularsa zanna bukar Milk da ratsin coffee ajiki,takalminsa shima milk ne kirar Italy mai yatsa, Wanda yakara fito masa da zaratan yatsun kafarsa masu kyau, ya dauki silver agogo mai tsada ya daura a tsintsiyar hannunsa yayi kyau matuk'a sajen fuskarsa yakara kwanciya Wanda yakara fito masa da ainihin kyansa yafito a ingarman namiji mai cike da kuruciya , Nabeel kenan yaro Dan kwalisa ,tabbas ko ba a fadaba ni kai na nasan namiji kyakkyawane ko bai yi shafe shafe ba lolπŸ₯°.

Haka ma ban garen Amare kowacce tayi kyau har tagaji ,na leka gidan su Aisha inda nahangota cikin wani Dan yen leshi milk color doguwace wadda dinkin yadace da me kayan anmta wani kalan daurin dankwali kalan na amare tare da yafa mata wani hadadden gyale Wanda Wambai ya sai musu ita da Asma'u domin akwati set dai dai yamasu na kaya nafitar biki badan ya raina Wanda Nabeel din yamasu ba komi iri dayane yamasu ,kai Aisha fa masha Allah hannunta da kafarta sai faman daukar ido suke inda akai mata wani lalle mai dankaran kyau ,fuskarta kam tasha kwalliya gaskiya Amarya fa tafito d'ad'as angonta kawai take jira wayarta ce tasoma Neman agaji Murmishi naga tasoma yi Wanda yakara fito mata da kwalliyarta ,My Ashnab baby nagani tadaga cikin wata kwantattar Murya mai sanyi da dadin saurare tace "Assalamu alaikum ya farin watana mai haskaka taurari kuma sanyin idaniya ta".

Nabeel lumshe idonsa yake tayi tareda shiga cikin wani shaukinso bai San shima ya iya magana ahankaliba mai taushi ba kamar ta yau din nanba yace " Amin ya sahibatil kalbi ,ina fatan dai kin shirya gani a kofar gida ke dai muke jira da kanwarki.

Wata faduwar gaba Aisha taji yayinda taji Nabeel na ambaton wata ,ita fa Sam mantawa take su biyune Amare gawani kishin Asma'u Wanda yataso mata lokaci daya,amma sai ta danne tace cikin sanyin murya"nashir my Man ganinan fitowa ,tana kai was nan ta aje wayar zuciyarta cike da tunani kala kala harsuka fito a ka budemata kofar Motarda Nabeel yake ciki wani ni'imtaccen kamshine yadoki hancincinsu mai dadin shaka kowannansu yana ta Murmishi gamida lumshe ido ta shiga aka rufe mota suka soma ta fiya ahankali Nabeel ya kama hannun Amaryarsa yana Murzawa ahankali cikin wani salo mai isarda sakonni kala daban daban asansan zuciya da bargo da jini da jijiyar masoyan, jikin Angon da Amarya taushi kamar Auduga ya sunkuyo yace "Baby na wannan kyau haka gaskiya nagode Allah da yabani ke yafada tare da kai ma hannunta sumba,har suka isa lokon su Asma'u inda itama ya shaida mata isowarsu bata bata masu lokaciba tunda daman itama ashirye take itama tayi kyau kayansu iri daya ne kamu kam yayi kyau sosai kowa nata yaba kyawu irin na amaren anci ansha anrab abubuwa kama da ga kalandu ,manyan bowl da sauran kayan rabo mai dauke da hoton amaren da zankadedan angonsu wato Nabeel .

Washe gari lahadi da misalin shadaya dai dai nasafe dubban jama'a suka shaida daurin Auren Nabeel Saminu da Amaryarsa Aisha Muhammad Wambai inda yabiya sadakinsa lakadan ba a jalan ba akan sadaki mafi karanci 50k domin samun albarkar Auren.

Maman Khaleel din kuce ...✍️
Y'AN UBA NE
(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'ar Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 85&86

Farin cikin Nabeel kam yau fadansa ma bata lokacine ,yayi kyau har ya gaji cikin wata danyar Shaddarsa gezna fara kal Babbar Riga da wando da yarciki wadda taji aikin hannu da wani bakin zare yadauki bakar zanna bukar da bakin takalmin sa Italy sai gaisawa yake da abokansa na wajen aikine da wadanda sukai karatu tunda ga secondary har zuwa jami'a hotuna kam duk inda yayi anata daukarsu shi da amaryarsa wadanda sukai matukar dace wa da juna sai faman kamshi suke fitarwa gamida wani annuri da wani sihirtaccen kyau da sukai sai dai muce tubarakallah masha Allah, kowa na fadin sundace da juna .

A bangaren Asma'u kam itama tayi kyau sosai karfe 2:30pm aka daura nata guda kawai taji alamar andaura wani farin cikine ya ziyarceta Wanda bazai faduba yau tazama mallakin zabin ranta Wanda dama bata da burin da ya wuce ace ta Auri Nabeel yanzu sauranta a bu daya shine taji ta a faffadan kirjinsa ta kwanta tayi bacci mai dadi Murmishi kawai take lokacinda ta daga kiran wayar Nabeel inda yace tafito sugaisa da abokansa itama sunyi hotuna kala kala kamin suka tafi gida inda su Nabeel sukai walimarsu mai rai da lafiya , anci ansha walima ta tashi lafiya daka kowacce ban gare na amaren da angonsu ,Asma'u fa ta kosa fa akai ta gidan miji domin ita take so tazama uwar gidan Nabeel kama mai fada a ji a cikin gidan Nabeel din ,yanzune zata nuna masa zallar son da take masa ,bazata yadda da wulakancin da ya dunga yimata a vayaba narashin zuwa inda take sosai Wanda in tai masa korafi sai yace aikine yamasa ,yanzu kam babu wannan ,Asma'u duk wannan tunanin tanayi ne ita da zuciyarta ,kawarta mardiya ta dubeta tadafata tace "Amarya tunanin me kike tundazu sai faman yimaki magana muke kintafi can wata duniyar Nabeel ne kuma kinsamu sai dai fatan kizama tauraruwa a cikin binnin zuciyarsa gamida kissarmu ta mata domin yanzu kowaccenku abinda zata soma fafutuka kenan Dan haka kidage sosai in hakan baiyuwuba to kimin magana mu mikaasa gurin malam me gobe da nisa a bugasa a allon karfe Mardiyya ta fada tare da Murmishi a fuskarta".

Asma'u tayi Murmishin gamsuwa da zancen kawarta tace " kawata shawararki. Tayi ni wallahi babban burina shine a ce nazama Uwargida ya kΓ sance nice zan soma bare angon ba wata ba Wallahi Mardy haushin tinkiyata nake ji domin komifa sai yadunga gwadamin ita ce Babba kuma wai nabita sauda kafa".

Mardiyya tace tab ba wannan magana ai ita kishiya ba abun yadda bace kuma ba a bata amana bare kuma garanti ,suna cikin hirar ne Mariya ta shigo tace Asma'u ta zo za ayi mata fada za a kaita dakin miji ,ita kanta Mariya burinta bai wuce ace kanwarta itace Uwargidan Nabeel ba an mata nasiha sosai kamin da ga bisani da karfe biyar daidai aka dauki amarya akanufi sharada face 2 inda gidan Nabeel yake .......!

Tabdi wata sabuwa mai karatu bari na Dan huta anan sai kuma gobe in meduka ya kaimu gobe Dan jin yadda zata cigaba da wakana .

Maman khaleel din kuce ....✍️
Y'AN UBA NE
(True life story)

πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'ar Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 87&88

Tuki ake atsanake har suka isa gidan inda gaban Mariya ya yanke ya fadi inda ta hangi Moticin gidan Wambai Jere reras ,suna ta kaiwa da komowa acikin harabar gida suka shiga sukai parking inda wata tsohuwa mai Murya ta rangada guda jikake ayyiririii! Shine shaidar suma sunshigo Asma'u tasake fashewa da kuka burinta bai cika ba ,ahaka suka shiga sashinta Inda

Please Login or Register in order to submit comment