Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dunga yimin tausa ".

Aisha ta lumshe ido ta bude a hankali tace " gaskiya ya kamata um ..um to Yaya wa za ka Aurane Allah dai yasa ba masifaffiya ba ce Aunty tawa".

Murmishi yayi gamida gyara wayar a kunnensa yace "um to nake ga ma kamar kinsanta".

"Anya kuwa bansantaba. inji Aisha ".

Ke kuwa kika Santa bari ma namaki kwatancenta ,ita dai dafarko farace doguwa tana da d'an k'iba kad'an sannan ita bata son hayaniya ,tanada kuma dogon hanci kuma gatada gashi dai dai misali, kinsan abin burgewa atare da ita Aisha?".

Aisha da sauri tace " a'a Ya Nabeel sai kafad'a".

Yayi Murmishi mai sauti yace gata da tarbiyya duk da kasancewarta ta taso gidan masu hali amma hakan bai sa tarbiyyarta ta gurbaceba ,kuma dadin da dawa abin sha'awa ita Auta a gidansu nima Autane a gidanmu ,gashi ta iya shagwaba sosai kamar wata yarinya,kuma sunan Ku daya ,ina fatan yanzu kinga neta ".

Tayi dariya tace " tab nikam ai sa ni kai a cikin kwali ka kulle .

Shima dariyar yayi yace" Allah ko Aisha to tunda baki gane ba shikenan amma ina son natambayeki Aisha?".

Aisha tagyara kwanciyarta sosai akan gadonta gamida rungume filo a kirji tace" ina jinka tambayan".

Nabeel yace" zaki iya Auren mai mata kuwa?".

Gaban Aisha ya yanke yafadi harda dafe kirji tace me mata kuma Yaya ni gaskiya a tsarina nafison na Auri mijina ni kadai zanyimasa biyayya kamar yadda mata hudu suke ma mijinsu biyayya ko ince zanmafi haka Dan nadauke masa sha'awar Neman Wata mace bare kuma ya Aura.

Gaban Nabeel ne yace dam!!!! Yayi ajiyar zuciya yace "tab lallai Aisha kina da kishi sosai wai da har ina shirin turo maki wani gaye ne Wanda ya jarabtu da soyayyarki sai dai kash ita din bata son mai mata ,kuma shi gayen yace idan bai Aurekiba to tabbas zai iya rasa rayuwarsa Dan haka Kanwata ki tausaya masa tayuwu rana daya ne ma bikin naku da waccen kingani ba'asan wacece Uwar gida amma fa zanfison ace kanwata ita ce tazamo Uwargida a gidan mutumin nan".

Aisha tayi Dariyar yake tace um kayya ni dai kabarwannan zance zuciya ta tafi ga wanin sa ,wallahi Yaya ba kishiyar bace abin tsoro halinta bakasan da wani hali zata zo ma ba ,amma kace masa yayi hakuri zuciyar Aisha ta mutum dayane Wanda yake ta mata yawo da hankali akan soyayyarta,yake kuma wasa da zuciyarta,Yayana Nabeel katayani Addu'a Allah yasa yadai na jin kunya yafito ya bayya na kansa, nikuma namasa alkawari ba'a raina Masoyi domin shi So bashi duban dukiya matsayi ko Mummunan talauci ,So wani gubane Wanda yake shiga lokaci daya futarsa kuwa sai ahankali,Dan haka ina rokonka katayani Addu'a.

Nabeel kam kalamanta jinsu take kamar gugan zana take masa ko dai tagane yana sontane inko hakane to meye na yimata wasa da kwakwalwa,"Hello Yayana naji kayi shiru kana jina kuwa?".

Aisha tafada tare dason jin amsar da zai bata.

Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda sai da yasa Aisha saurin dauke wayan a kunnenta tana Lumshe ido gamida wani Murmishi,tace bakace komi ba ko kana taya abokin naka kishine?.

Tafada cikin shagwab'a.

Yace Aisha ni narasa me zance maki in ma kishine dole nayi saboda ni a tunanina Aisha kina Sona kamar yadda nima na dade cikin mayen Sonki yakamata Aisha ace kin gane nufina ashe ke kinma wani tanadin kanki,Aisha zantaya ki son abinda kike so bazan maki dole ba amma kisani ni Nabeel Samin har'aba da vazan dai na Sonkiba kece mace tafarko dana fara So a rayuwata duk macen da zan zauna da ita Aisha bayanki take amma zan tayaki da Addu'a Allah ya dai dai taku da Wanda kike so wannan alkawari ne Wanda nadaukarwa kai na .

Aisha fa hawayen farin ciki take takasa magana tunda Nabeel yafara magana har yazo karshe godiya kawai take ga Allah da ya amsa mata addu'arta yau gashi Nabeel da bakinsa yake shaida mata yana Sonta lallai Umma Uwace kuma tagari mai dora d'an ta bisa turbar kirki .

Aisha naji kamar kuka kike to kiyi hakuri abinda ke raina nafadamaki amma Dan Allah kiyi hakuri inda nasan kalamai na zai saki hawaye da ban fadamaki ba duk da ni nasan Aisha ni ba a jinki bane ke matar.....!

Kai !kai!!!! haba Yaya Nabeel kadai na fadin haka wallahi ni Aisha zuciya ta tuni ta mallakamaka komi Aisha Allah ya haliccetane da wani sashi najikin Nabeel kai ne zabin nawa ba wani ba kai naima tanadin kaina ba wani ba,kai zanma kallon So ba wani ba kai ne majinginata Nabeel nadade ina walagigi nima acikin kogin So nan fa Aisha tabashi labari duk sanda taga wata mace takalleshi acikin makaranta to ranan fa bacci sai dai barawo,musanman ranan da wata y'ar daba tace tana sonka ,wallahi kalma daya ce ta burgeni da kace mata bakasonta tayi hakuri wannan yakara tabbatar min da kai Namiji ne mai cikar kamala da tsantseni kakara wani matsayi a zuciya ta .

Su Nabeel fa anji ankarbu sai wannan Murmishi yake, yana fadin Aisha nagode da kika zabeni a matsayin a bokin rayuwa duk da kasancewata talaka acikin manemanki niko Aisha zanbaki labarin abinda yahanani bacci akanki amma sai mun hadu ido cikin ido zan gayamaki ,nagode kwarai da jin wannan labarin naki mai dadi insha Allah yau zan zY'AN UBA NE

(True life story)
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammed
(Maman Khaleel )

rabiatumuhammed181@gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 73&74

Dan haka bari nabarki kihuta Amaryata ,ki gaida min Umma kamin nazo anji ma.πŸ‘†πŸ‘‡

Aisha tayi Murmishi tace "Insha Allah zataji Allah kuma yakawo ka lafiya Yaya".

Ameen ya Allah kuma kar nazo anjima fa ki kama noke noke kawai inason kinuna min yadda kika damu da ni,nabarki lafiya kiyi tunani mai kyau Eesha.

Aisha fa sunan yamta dadi duk da kawayenta suna kiranta Esha amma bata taba jin dadin sunan ba irin na yau,tace" to nagode Yaya ."

Suka a je waya.

Aisha da gudu tafita daga d'akinta ta nufi falo inda take jin muryar Umma suna magana da mai aikinta,Aisha tazo ta rungumeta ta baya tana Dariya tana fadin Umma zai zo anjima.

Umma tayi saurin dawoda Autarta gabanta itama da Murmishin a fuskarta taja hannunta suka zauna a kan kujera tace "Auta waye wannan Wanda zuwansa yasaki farin ciki haka?"

Aisha tadubi Umma cike da zumudi takwashe komi tagayama Mahaifiyarta ,hamdala Umma naga tanayi gamida daga hannayenta wadanda basu rabo da Jan lalle tana fadi Masha Allah Allah ka nunamin ranan Auren nan Auta wai zamusha shagali kinga to tashi mushiga kicin kiyima sa abin tarbar bako tare suke mike suka nufi kicin din aiki suke yau cikin nishadi har suka kammala komi ,Aisha fa yau ansha wanka anzauna anata faman kwalliya tafito fes da ita kamar wata Amarya ,tayi kyau cikin wata doguwar shadda brown anmata din kin zamani taji aiki sosai tun daga Samantha har kasa, wai zanso kuga Aisha , har tafi Hajiya Nafeesat tacikin Izzar so haduwa πŸ˜‹lol,Aisha karshe ce wajen iya kwalliya gawani kamshi yana tashi,na Humran Maman Khaleel mai Dan karan kamshi tashafa fara kamin tashafa Bak'a tacika dakinta dawani mahaukacin kamshi mai kwantar da zuciya sannan ta Dora da sassanyar turare na feshi shima mai sanyin kamshi da dadin shaka,ta fito rike da waya a hannunta ta nufi dakin Umma Masha Allah kawai Umma take fadi domin ita da kanta tasan Auta fa karshe wajen haduwa da burge yan maza ,gakuma abin burgewa Auta ga iya kwalliya, ga iya girki kala kala,tace kai Autar Umma karfa kisa min yaro a kwana fa wannan kyau haka ai saikisa ya karaji duk duniya babu take.

Aisha fa sai wannan fari take tana Murmishi tace Umma shima fa Ya Nabeel din vafa baya bane wajen iya wanka kingani kuwa dole nageko saboda wallahi Umma akwai masu kawo farmaki".

Umma da Aisha sukai dariya Umma tace "hakane diyata kizama kece guda tamkar da dubu,yakasance baya kallon kowace mace inba keba Aisha ki rike Nabeel duk da nasan kema ba abin wasa bace a wajen maza ,wallahi INA mai baki shawara Nabeel koda Mata hudu yayi karki daga hankalinki akansu domin nasan ke din Aisha ta dabance acikin Mata kuma zaki bani labari Aisha inko bana raye zakice Umma tagayamaki dama, Aisha ke ba macen da za 'a wulakanta bace sam.

Jikin Aisha yayi sanyi jin kalaman Umma ,kodai maganar da Nabeel yagamata gaskiya ne dazu dayake cemata zata iya Auren me mata ,tabbas yazama dole ta tambayesa me maganarsa take nufi ,inko hakane tabbas yazama dole ta zage damtse Umma tace Auta tunanin me like?

Murmishi tayi tace " Umma bakomi ".

********

A bangaren Nabeel kam yau tunda ya dawo gida yake ta zumudi ya kosa yaje gidansu ya gayama Auntynsa lavarin Aisha fa ta karbi Soyayyarsa ,sai kuma yaji zuciyarsa na fadin anya zako taji dadi in nafada mata bayan har yanzu banje gun Asma'u ba ,yayi Murmishi yace Allah sarki Asma'u karki damu kema INA nan zuwa gareki ,bari nagama da wannan nashawo kanta tukun kamin nazo gareki duk da nasan ke labari ya riskeki ,in zai yiwu ma kila a hadamin Ku rana daya a kai min Ku gidana ,gabansa yafadi tuno bai da gudan da zaisaka mata biyu anya da hayar da zai kama air gwanda ya tattala kudinsa ya siyi gida ,ko a can ja'een ne ,da wannan tunanin yagama shiryawa cikin shaddarsa Brown din kin zamani jamfa ce mai gajeran hannu ya dauki hularsa ya kafa kalan zaren da a kai masa aiki ya dauki takalminsa kirar italy shima kalan hular yadaura agogonsa silver mai kyau ya feshe turarensa mai kamshi yafito fes dashi masha Allah tubarakallah. Da kafa yasoma takawa harzuwa gidan Wambai Wanda a yau zai je gidan a matsayin siriki ba kamar yadda yasaba zuwaba ,Ibrahim yasan da zuwan Abokinsa sai dai Nabeel bai fada masa zancen soyayyarsa da Aisha ba.

Kuyi hakuri da wannan bayawaπŸ₯°.

Maman Khaleel din kuce ....✍️o a matsayin saurayin Aisha ba wajen abokina ba Kuma sirikina ba a yanzu,Dan haka bari nabarki kihuta Amaryata ki gaidamin Umma kamin nazo...

Maman Khaleel
din kuce......✍️
Y'AN UBA NE

(True life story)
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page75&76

Yana zuwa yadaga waya ya yasoma Neman layin Aisha bugu biyu ta dauka cikin wata murya mara amo mai taushi tace "Assalamu alaikum Yayana "

Murmishi yayi kamin shima yace cikin karya muryarsa "Ameen wa alaikissalam ya kyakkyawar kanta,gani a kofar gate ko zan iya shigowa ?".

Aisha tayi Murmishi aranta tace kai namiji halinsa sai shi ,ko da wa yake masa iso oho,amma a fili tace " kai Yayana kana abin Dariya banda abinka gidan ai nakune kashigo kai tsaye ganinan fitowa ".

Yayi Dariya mara sauti yace "nagode da wannan karramawa".

Suna a je waya ya kira layin Ibrahim ya shaida masa ya shigo cikin dakinsa yana ciki,suna ganin juna Nabeel yace kai Sirikina kaci lafiya wallahi wannan kyau haka sai ina ?".

Ibrahim yayi Dariya yace " Da dina da kai Nabeel zolaya kai bance kayi kyauba dubeka fa kamar wani ango kuma ma tsaya ta ina nazama sirikinka naga dai ni ba yarinya garen da zanbaka ba ".

Nabeel yayi Murmishi yasamu guri ya zauna yace " kai bisa wuya Yayanmu ayi min a fuwa "
Yadda yayi Dariya yaba Ibrahim Wanda yake kokarin kiran Aisha tana daga wa yace "Auta ki kawoma wani Autan abinci ,sannan ki shaidawa Umma Nabeel ya zo".

Dariya tayi tace " to ai Yaya Umma tasan da zuwansa gani nan zuwa kai masa lale kamin nazo kaji Yayana".
Sai yanzu yagane tsiyar da Nabeel yake yi masa cike da zumudi Ibrahim yace "Abokina kana nufin Aisha kanwata kake so ?".

Nabeel ya sauko kasa alamar girmamawa gamida zolaya yace " eh ranka shi dade Aisha nakeso Allah yasa ba'a mata miji ba,ya dafa kafar Ibrahim yacigaba da cewa Ibrahim Dan Allah kar kace nayi hakuri wallahi tuntuni nadade da Soyayyar Aisha a zuciya ta tun Amakaranta,tun bansan ya kuke da ita, Ibrahim wallahi randa naga Aishat acikin gidan nan tana matsayin kanwarka bakuma jin yarinyar ta shiga rayuwata sosai Dan haka Yayanmu katayani kamfe.

Dariya sukai su duka ,farin ciki yaki boyuwa a fuskar Ibrahim yace "Nabeel in dai Aisha na sonka wallahi to ni nafikowa farin ciki ,da wannan zumunci mai karfi da zaikara kulluwa a tsakanij mu, Nabeel sai dai ina rokonka abu daya ka kula min da Aisha domin yarinyace duka duka yanzun ta shiga 18 girmanne kawai .

Nabeel yaji dadin kalaman Ibrahim yace" insha Allah zankiyaye Ibrahim bazan iya wulakanta jininkaba ,domin kai ne mutum nafarko da ya tsaya min.....!.

Hannu Ibrahim yasamasa a baki yana girgiza kai yace " haba Nabeel bana so kamanta alkawarin da kai min?.

Murmishi naga Nabeel nayi suka rungume juna suna Dariya ,sallaman Aisha itace ta dawo dasu haiyacinsu kowannensu cike da walwala suka amsa mata sallama tare da bata izinin shiga.

Kai tubarakallah masha Allah abinda zuciyar Nabeel ke fadi kenan,sai faman hadiyan yawu yake dakyar,gawata sha'awa tana bijiromasa kamar yajawo ta garesa ko yaji sanyi,sun kafe juna da idanuwa kowanne yana aikama Dan uwansa wani sako Wanda ni kaina duk kwakkwafina ban isa nagane yaranba amma bansan ko kuba Fans🀣.

Ibrahim yayi Murmishi yace ke kinwani zo kin tsayamana a gaba ko ance maki wani zai sace Nabeel dinne wannan kallo haka?".

Aisha cike da jin kunya ta ajiye turen gamida turje kafa tace kai Yaya kavari fa ,tafada cikin shagwabarta mai burgewa.

Nabeel ya jawo turen gabansa yace rabu da wannan Yayan Kanwata matso gareni kinji Uwar gidana ta kaina kalle ni yadda kike so ,ta ko zauna tajuyar da kanta alamar kunya ,Nabeel ya dubi Ibrahim cikin marairaicewa Yace "Dan Allah kabamu aron dakin ka kaji kadanje daga waje kamin muyi namu dakin kaji Yayanmu Iro"?.

Ai ba Ibrahim ba har Aisha sai da tadara jin sunan da yakira Yayanta da shi ,wai har ta tuno da Kakansu wanda yake tsikanar da iroro Umma ".

Aisha ta saci kallonsa tasake yin Dariya .

Ibrahim yace lalle yarinyarnan nagode bari na tafi wajen uwata nima naje tasamin albarka ,Auta kekuma ko hmmmm Nabeel zai tafi zakisan Wanda kikema Dariya yana kai wa nan ,yafita yana Dariya zuciyarsa fal farin ciki.

Bayan futar Ibrahim Nabeel ya gyara tsayuwar hularsa gamida gyara zama yace Uwar gidan Nabeel barka da dare da fatan nasameki lafiya?".

Aisha tayi Murmishi tace " Walaikumussalam dafatan ka iso lafiya ya aiki?".

Nabeel shima Murmishin yayi yace "to aikin Alhamdulillah Dan yau nayi shi sosai ."

"Masha Allah haka a ke so Allah ya taimaka".inji Aisha .

"Ameen ya Allah "

Hira suke yau Sosai kowannan su yana dauke da wani farinciki mara misaltuwa ,yau tare suka ci Abinci Dan yau ya rikice yace indai bazataciba to shima ya koshi,Nabeel yaci sosai ya du beta yace "Aisha Allah yasa kin iya girki kamar na Umma domin Umma gaskiya gwana ce wajen iya girki,kinsan mu Maza muna son Macen da ta iya girki, kwalliya ,gamida tsaftar mahalli da jiki".

Aisha tayi Dariya tace " hakane kam Yaya ,insha Allah zaka sha mamaki watarana ,amma za'ayi yadda kace mai gida".

Nabeel yaji dadi sosai ,yace yauwa Uwargida haka nake son ji daga bakinki.

Aisha tayi Saurin fadin yauwa Umm..Umm...Dan Allah ko...um...!

Sai kuma tayi shiru tacigaba da wasa da Dan y'atsunta .

"Y'an mata fadi maganarki mana kai tsaye meye kuma na yin canki canki? yi maganar ki kai tsaye shirye nake ni Nabeel nabaki amsarta indai nasani".

Aisha tayi Murmishi tace " um dama fa cewa zanyi muna zaka Aura ne naji kana cemin Uwar gida shine kawaiπŸ‘Œ,tafada ahankali kamar batason yin zancen.

Nabeel yayi Murmishi yace" to baki da labarin Ku hudune ? Tab yarinya kishirya zama da abokan zama .

Cikin zare idon da batasan ma tayi ba tace" dagaske kake? tab anya kuwa zan iya zama da kishiya?"

Sakkowa yayi a kan kujera ya zauna dab da ita ahnakali ya soma neman hannunta har yasamu nasarar kamashi cikin wani salo yasoma lasan hawayenda suke zuba a fuskarta ta bude idonta yasakarmata wani kallo Wanda ni kai na sai da najuyar da kai gefe,saboda kunya,yace Aisha ki yarda da ni wallahi da gaske nake kubiyu ne zan Aura ,amma kar abin ya dameki ,Aisha kece mace ta farko Dana fara So a rayuwata,Aisha ki bani hadin kai na Aureku me da Asma'u ,itama yarinya ce Mara son rikici,Aisha ki goyamin baya kar ki ce min a'a ,wadda ta hadani da Asma'u bazan iya kallonta nace banason jininta ba,nan dai ya labartama kadan daga cikin labarinsa,akarshe ya Dora da fadin Aisha banyi tunanin zaki soniba saboda ke Matar manyace ba ta talaka ba Irin...!.

Hannunta tasa ta to she masa baki tace kadai na fadin haka bana so kaji ,tafada cikin shwagwaba .

Yayi Murmishi ya rike hannun yace Aisha dole na fada haka kin a mince zaki Aureni ?".

Aisha ta sunkuyar da kanta kas cikin jin kunya tace " na amince murayu da juna cikin Aminci,Nabeel ka rikemin Alkawari duk rintsi duk wuya bazaka juyamin baya ba".

Yaja ta jikinsa ya rungume yace Aisha nayi miki Alkawari zan rayu da ke harkarshen rayuwata,Nima kimin alkawarin zaki rayu da ni duk tsanani duk wuya da dadi.

Cikin kuka tace "nayi ma Masoyina ".

Yaji dadin kalamanta kamin yacigaba da shafa mata baya tareda gayamata kalamai masu dadi.

Soyayyar Aisha da Nabeel gwanin sha'awa koda yaushe suna makale da juna in ko yana office to suna tare a waya,kowa yasan Soyayyar Aisha da Nabeel haka nan kowa yasan Nabeel su biyu yake nema,anata kawo ma Umma cikas din Nabeel amma tayi bakam haka ma wajen Wambai shima ankawo mass tsegumin Nabeel ba zai iya rike Aisha ba ma bare kuma ya had a mata har'biyu,amma amass daya yake fadi Aisha Iowa race tana so bazai hanata shi ba bare Nabeel Wanda ya daukesa kamar danda ya Haifa.

A bangaren Sulaiman kuwa dayaji Nabeel na Neman Auren Y'ammata guda biyu abin mamaki yabashi,yayi Dariya sosai yace "kaji yaro mai zarin tsiya magani."

Maman Khaleel din kuce...✍️

Y'AN UBA NE

(True life story)
πŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈπŸ™†β™‚οΈ
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 77&78

Washe gari Nabeel da wuri ya shirya ya nufi wajen aiki ,aiki yake tayi a natse cikin kwarewa ,bashi ya samu kansa ba sai misalin karfe 1pm na rana tashi yayi yanufi masallacin Company bayan ya dawo ne ya tarar da miss call har guda 10 yabi Nombobin 6 daga ciki Yayansa ne na Jos wato Umar sai kuma abokinsa Suhail,sai kuma number da takirasa sau 2 ,haka kawai yaji yanason yaji waye mai Number nan, duk da yakwana 2 bai ji muryan Yayansaba mai kula da lamarinsa da bashi shawarwari akan duk abinda ya sa agaba,har yasoma Neman Umar sai kuma ya yanke kiran yabi kiran bakuwar Number nan ,tasoma ring sai da shima yakira sau uku kamin ta mike da ga kwancenda take ta share hawayenda suka wanke mata fuska tace "
Assalamu alaikum"

Gabansa ne yafadi jikake ras -ras ,yayi saurin daidai ta kansa ,kamin yace "amin wa alaikumussalam Dan Allah zan iya sanin ko wacece?".

Tayi yake kamin tace ita dayar idan ta kiraka ai ba sai ka tambayeta ba ko wacece nasan har haddar no dinta kayi saboda ita kadamu da ita nikam fa sai dai hakuri tunda nasan matar cushe batada daraja,tana kai wa nan sai kuma tasa kuka saboda tsabar takaici".

Lumshe idonsa ya shigayi a hankali yana budewa baya son kukan mace kokadan yana tayar masa da hankali yace" haba Asma kiyi min Uziri mana kizama mai ba ni uziri kinji ,wallahi kullum kina raina aiki ne yayi min yawa ,kwana 2 amma insha Allah yau daga Office ba zanje gida ba gidanku zansauka,hakan yayi making?".

Murmishi tayi mai sauti Wanda shikansa ya fahimci jin dadinda take ciki ,shima yayi Murmishi yace "Asmy bakice min komiba ko ba za a karbi bakunci angonba ne ?ya fada cikin wata kwantattar murya mai taushi"

Nan fa yakara kashe ma Asma'u jiki da wannan kalaman nasa,Dan ta kara tabbatarwa yanayi da ita ,sai tace "um Yaya kenan ni nasan ai sai Aisha tace ma kazo wajena kamin zakazo, wallahi nayi nadamar sanar da Aunty umm..!".

Kai Asma'u bana son korafin ki wallahi wayace maki ni Yayanki Nabeel bansanki ina sonki sosai ba tun yau ba kuma kisa aranki cewa ni na nuna inasonki ba nason nakuma jin irin kalamannan abakinki kina jina".

Tayi murmishi tace " to kayi hakuri insha Allah bazan karaba".

Yauwa tawan sai nazo a gaida min da su Umma kamin nazo ."

Asma'u tace" insha Allah zan gayamata sai kazo Allah ya tsare min kai daga dukkan abinki My Man."

Suka aje waya kowannansu yana mai farin ciki ba ma kamar Asma'u wadda kullum kamar karamata son Man din a ke a cikin zuciyarta.

Shikam suna sauke waya yakira Yayansa suka sha hira kamin sukai sallama,ya cigaba da aikinsa ya na kan hanya ne Aisha ta kirasa yau ta tsantsara masa kwalliya gamida hada masa girki mai dadi yau saboda shi ta yi Sinasir gashi tayi kyau sosai ,hakama miyar taji agushi da naman rago da bushasshen kifi gashi taji Ogun ,angama shirya komi shikadai take jira yau ya iso gidan su,yana dagawa yayi Murmishi yace "Hello My Baby ya kike ya Umma yau kinje School ko?".

Aisha tayi fari da fararen idonta gamida wani yalwataccen Murmishi mai ban sha'awa da janhankalin Wanda akai domin shi gani take kamar suna tare tace " hubbyn Eeshat ina lafiya ina fatan kai ma kana lafiya kamar yadda nake.
naje School yau munfara Exam gashi tayau ta yi yaji wai danma nayi karatu".

Yayi Dariya yace"
Allah Uwargida na Allah dai yasa kicinye duka jarabawar kina ina ne yanzu?".

Ta kara yin juyi kan kujera ta lumshe ido ta bude a hankali kamin tace "Ina falon Umma cike da kewarka amma yau dai zakashigo ko ?dan gashi nan nahadama Delicious yau na musan domin farin cikin ka".

Nabeel yaji dadin kalaman Aisha sosai aransa yace wai ni Nabeel Dan gatane ni ko ta ina anata tarairayata ko ina ni gwarzone ,yace " Madam Nabeel nagode da kulawa amma yau amin Dan uziri mana naje na ga kanwarki mana kinsan fa tunda akasoma maganar Auren mu bata sani ko saudaya ba acikin Idontaba shiyasa nace yau zani mudan gaisa ko bahaka ba Madam dina, ai in akai hakan kaman yayi ko ?".

Aisha taji wani tukukin kishi yataso mata Sam ita mantawa ma take da zancen wai subiyu ne fa Amaren ,cikin takaici aranta tace to ni ina ruwana da rashin zuwanka can tunda ni ai ina ganinka ,! yace kai kai kai Malama EshNabeel ke da nake fatan zaki bani hadin kai mutaru muzauna lafiya shine kike fadin haka haba Eshnab dina kikasance mai son abinda Dan uwanki yake so mana .

Aisha wadda kunya duk tabi ta kamata bataso zancen zucinta yafitoba ,cikin wayancewa tace kai Yayana dafa wasa nake ma wallahi inason Asma'u kamar yadda nake son ka My Eshnab nahakura amma naso kaci abin con nan amma bakomi kaje kaci na kanwartawa ka gai damin ita kaji sosai ,tafada cikin sanyin Murya ,yace to tawan zataji amma kinsan ki aje min zan biyo na amsa na tafi da shi gida naci kinyar da ?".

Tayi Murmishin yake tace um na amince ka gaida min ita ,tana fada takashe wayan batare da sunyi sallamaba,kuka Aisha tasa na takaici yanzu haka zasu dinga share dinsa anya zata iya share din Miji kuwa ita da wata anya kuwa .wazata sama ne da matsalarta waye zai bata shawara ta tuno Najeeb Wanda ita kadai ce zasu zauna suyi rayuwa babu kishiya amma takafe sai Eshnab sai ga wasu hawaye masu zafi Suna kwaranya a fuskarta Wanda dagani nakishi ne tsagwaronsa ,Umma ta fito taganta cikin wannan hali ,tace Auta na wayasamin ke kuka zaki bata

Please Login or Register in order to submit comment