Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka wuce, saida Taga Jirginsu ya Daga Sannan Suka dawo gida..

*MASARAUTAR ZARIA*

Hidima sosai ake na tarbar Gimbiyar Kasar Zaria, Umma tunda ta tashi da Safe bah zama. Duk abinda tasan xai faranta ran yar nata shi tasa Ayi. Jirginsu na sauka suka tarar da Yan tarbansu. Ciki harda Umma, dasauri Parveen sauko daga matatakalan jirgin ta rungume Umma tana dariya, itama dariyan take tana Shafa kanta. A hankali tace
"I Missed uh ummana"
Dagota tayi daga jikinta tana Kallanta
"Kinganki kuwa yanda kikayi qiba"
Turo baki parveen tai tana dan bubuga Kafa. Hannunta umma ta kama suka shiga mota sai gida..

Suna Shiga gida ta fito daga motan dagudu tai part din mai martaba, dogaran dake wayan suke shaida mata yana Fada dan haka side din Umma ta wuce. Taci tasha Tayi nak itada Atika, saida Suka Huta Sannan Aka nunama Atika dakinta. Umma Dake ta kallan Yar nata cikeda Sha'awa Tace
"Tun dazu kuka iso kuma banga kin bugama Mijin naki bah"
Dam! Gaban Parveen ya fadi, ita sam koh numbernshi ma Batada shi..

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤👑

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 8⃣1⃣ to 8⃣5⃣

"Tun dazu kuka iso anma banga kin bugama mijin naki bah"
Dam! Gaban Parveen ya fadi, ita sam koh numbernshi ma batada shi, Tadan kalli umman
"Tun dazu na kira baya zuwa ai"
Kallan rashin yarda tamata tadai Kyalle. Sai Bayan Isha'i ta samu Mai martaba a part dinshi da murna ya tarbeta, sunsha Hira sosai. Suna tsaka da hira wayanta ya soma ruri, dubawa tai taga Fulani ce. Da Fara'a ta dauka tareda karawa a kunne
"Haba Parveen, shiknan dan anga Umma kuma sai a manta damu"
Dan dariya parveen tai
"Aa Fulani bah haka bneh, yanzu nake shirin kiranki"
"Fadi dai gaskiya, yanzu nagama waya da Ummanki"
"Tho kiyi haquri"
Murmushi Fulanin tai
"Na hakura, ki gaida kowa da kowa"
Tho Parveen tace sukai sallama ta kashe Wayan..

Mai martaba ta kalla Tana Dan Murmushi
"Fulani ce tace na gaida ku"
Ina amsawa. Ai Fardeen na kirana muna gaisawa, yaran nada kirki"
Jim Tai tana Kallan Mai martaba.
Yadan mata murmushi yana cewa
"Tashi kije ki kwanta nasan kin gaji"
Bah musu ta mik'e tai mai saida Safe ta koma Dakinta..

Dare ya tsala ko ina shiru, Parveen idonta biyu. Juye juye take kan Makeken Gadonta, in ta rufe bah abinda take gani sai Yarima, Tsaki Tayi tadan daga murya
"Ka Fita daga idona!, meyasa nake tunaninka?? I hate uh"
Dakyar ta samu barci ya dauketa Cikeda mafarkan Yarima kala kala..

A Bangaren Yarima kuwa, gidan neh yamai Girma. Sai yau ya yarda da maganar hausawan nan da ake cewa
"Da rashin abokin fada gwara yana nan"
Zagewa yayi yaci Breakfast dinda tamai sosai, saida yayi nak sannan Ya shirya ya tafi office. Yinin ranan sukuku Yayishi har saida mahdi ya kaiga Tambayanshi koh baida lapia neh
Furzar da iska kawai yayi yace
"Bkmai am Fine"
Gyada kai Mahdi yayi na Rshin yarda bai kara cemai komai bah Har suka Tashi. Da wuri ya dawo gidan ya shiga side din fulani, saida suka Gaisa yadan dubeta
"Fulani kunyi waya da Parveen kuwa??"
Ta kalleshi da mamaki
"Bakuyi waya bneh??"
Yadan sosa Keya
"Eh munyi, nadai tambaya neh"
Ta dubeshi dakyau
"Fardeen!"
Kallanta Yayi da mamaki, rabonda ta kirashi da sunanshi har ya manta
"Ka fadamin meke Faruwa??, ni nasan akwai wani abu da kuke boyemin"

Yadan wayance Yana kallanta
"Na meh fah??"
Hade Rai tai
"Bakaji meh na Fadama bah knan??"
"Bkmai fah Fulani"
Kauda kai tayi gefe
"Shiknan"
Baice Mata komai bah ya mik'e yabar falon..

Tsayawa yayi a kofan side din ya rik'e kugu yana Tunani, chan ya soma tafiya a hankali har side dinshi na dah, bude Kofan yayi ya shiga da Sallama. Bilal ya samu zaune Yana Kallo, dogon tsaki yaja yana kallanshi
"Naga Ranan da zaka daina kallan nonsense din nan"
Kyalkyalewa da dariya Bilal yayi yana kallanshi
"Yarima Yau kaine a nan??, wato madam bata nan yanzu ka sake"
Tsaki ya Ja yana Hararanshi
"Ko lokacin da take nan din ban gadaman Zuwan baneh"
Fadawa kan kujeran yayi
"Pls find me something am Hungry"
Bah Musu Ya mik'e Yabar Falon, Chan sai gashi dauke da Tray ya aje a gabanshi ya koma ya zauna.
Binshi da Kallo yayi
"Tho wah zaiyi Serving dina"
Gintse fuska bilal yayi
"Kaifa abinda ke hadani dakai knan"
Yana gungunai ya zuba mai abincin ya koma ya zauna ya cigaba da kallanshi..
A side din ya kwana cikeda kewan Parveen dan Bazai iya Kwana shi kadai chan Side dinsu bah..

A Gurguje Pls...

Kwanan Parveen biyu a gida, kullum cikin tunanin Yarima take, hakanan saita zauna tai shiru ita kadai tana Tunani. Yau Saturday Tana garden ita kadai kan Carpet tayi xurfi cikin tunani, Ummace ta shigo ta zauna Kusada ita tareda dafata. Razana Tai ta juya suka hada ido
"Wai Parveen meke damunki??, narasa ganeki kullum sai ki zauna kita tunani ke kadai"
Dukar dakai tayi tana Yar Murmushi
"Bkmai Umma"
Haba Parveen bai kamata ki boyemin damuwarki bah, ki fadamin meke damunki??"
Kallan Umman tai Kasa Kasa
"Bah komai fah Umma"

Ajiyar Zuciya Umma tai tana Kallanta
"Shiknan tho, gobe zaki koma koh?"
Nan da nan Parveen ta hade rai ta turo baki
"Ni Umma bazan koma bah"
Mamaki Karara a fuskan Umma
"Ban ganeh bazaki koma bah??"
Turo baki Parveen tayi tana kallan kallan Umman
"Nidai Umma bazan koma bah, na dawo nan knan"
Ran Umman neh ya fara baci
"Wanne irin magana kikeyi neh Parveen, har yanzu banfa ganeh magananki bah"

Ummah bakiga kayanda nadawo dasu bah, na dawo gida knan. Ni banasan na koma"
Hade rai Umma tai ta mik'e tana Kallanta rai bace
"Kada kiyi Gigin Sanarda Mai marbata wannan Maganan da ranki bah Qaramin baci zaiyi bah"
Bata jira mai zatace bah tabar wajan dasauri..
Hada kai da Guiwa Parveen tai ta Fashe da Kuka
"Yanzu baza'a tsaya aji Dalilinta bah Sai Adau fushi da ita"

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤👑

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 8⃣6⃣ to 9⃣0⃣

Hada kai da Guiwa Parveen tai ta Fashe da kuka
"Yanzu baza'a tsaya aji Dalilinta bah sai adau Fushi da Ita"
Kuka take Sosai, saida tai mai isarta Sannan ta tashi tabar wajan...

Wuraren La'asar Deeza tazo gidan cikeda zumudin san ganin aminiyar nata, Tana shiga dakin ta rungumeta tareda sakin ihu, tureta Parveen tai tana hararanta.
"Sai Yau kika gadaman zuwa?? Tun fah Thursday nake Garin nan"
Dan murmushi tai
"Am Sorry Bae, Wallahi School neh kinsan Mun Soma exam"
Qara hararanta tai Cikin Wasa
"Shiknan anma dah har nayi fushi"
Dariya sosai Deeza tai tana kallan Parveen Up and down
"Kai! Bae"
Yadai?? Cewar Parveen
"Naga kin Chanza neh bah kamar sandah nazo bah, fadamin Sirrin mana Yanmata"
Duka Parveen ta daka Mah Deezan tana dariya. Sun jima Suna Hira Sannan Deezan tai mata Sallama Ta tafi..

A bangaren Yarima kuwa Keyar Parveen neh ke dawainiya dashi, gashi ko numbernta bashida. Kunyar Ya tambayi Fulani, Gashi tun yanzu ta Fara ganeh akwai wani abu a Tsakaninsu. Yau sati yana side din fulani zaune ya daura System dinshi a kan Cinya, Latse Latse kawai yake wanda shi kanshi baisan abinda yake dannawa bah. Hankalinshi sam bai wajan, Fulani data shigo falon ta lura da halin dayake Ciki tai gyaran murya tareda Dafashi
"Lapia yarima??, meke damunka?"
Murmushi ya Qirqiro yana kallanta
"Bah komai meh kika gani"
"Haba Yarima Duk wanda ya ganka zaisan akwai abinda ke damunka, gaba daya duk ka chanza"

Girgiza kai Yayi
"Bkmai Fulani, Am Fine. Kawai Stress neh"
Kirkiran Murmushi tai Tana Cigaba da kallanshi
"Shiknan Tho"
Mik'ewa tai zata bar wajan Yadanyi gyaran Murya yana Kallanta
"Fulani Kun koyi waya da Parveen??"
Juyowa tai Ta harareshi cikin sigan wasa
"Bamuyi bah, ai kai zan tambaya."
Shiru yayi baice komai bah ya maida idonshi kan System.

"Yarima nifa har yanzu na kasa Ganeh kanku daga kai har Parveen din. Anma Bkmai idan ta dawo ni dakaina zan tambayeta mai keh Faruwa, bah gobe zata dawo bah?"
Kai ya gyada mata batareda yace komai bah.
Barin Falon tai Zuwa bedroom dinta, kamar ance ya dago ya hango wayan fulanin kan kujera inda ta tashi, dasauri ya Mik'e ya dauka Ya shiga Contact. Cikin Sa'a yaga numbern ya dauka a wayanshi ya mayar ya aje. System dinshi ya dauka Yabar Falon Cikeda Murnan ya samu abinda yakeso cikin Sauqi..

Bayan Sallan Magriba Sarki Khaleed yasa amai Kiran Parveen. Sakon na samunta ta mik'e dasauri ta Nufi part dinshi tareda Rakiyan Atika, a daidai bakin kofan tama Atika Alaman gmta tsata. Bah musu taja baya ita kuma ta shiga da Sallama, Amsawa Yayi ta nemi guri ta zauna tareda gaidashi. Saida ya Amsa Sannan ya kalli Dogaran dake Falon yana cewa
"Ku bamu Guri"
Bah Musu sukar Falon Dasauri.
Mai martaba ya Kalli Parveen Cikin Kulawa Yace
"Gobe zaki koma koh??"
Shiru Parveen tai batace komai bah
Qara Kallanta Yayi dakyau
"Ina Magana Kinyi Shiru koh bah Gobe baneh??"
Turo Baki Parveen Tai tadan Kauda kai
"Ranka Ya dade ni...Ni..Bazan koma.."
Daka mata Tsawa Yayi tareda Xaro ido yana Kallanta
"Meh kike nufi da bazaki koma bah??"

Tsorata Tayi har saida tadan matsa
"Ki Fadamin Meya Faru?? Wani abu akai miki??"
Girgiza kai tayi alamar Aa
Idanunshi neh sukai Ja
"So knan kike ki maidani mutumin banza koh??, haba Parveen keda nake miki Kallan Yarinya mai hankali"
Fashewa tai da kuka kanta na Kasa sai Jan Majina Take.
Ran Mai martaba neh ya Soma baci yadau Waya ya kira Umma, Cikin Mintinan da basu Wuce Biyar bah ta shigo falon da Sallam. Ganin Parveen na kuka yasa ta Qaraso dasauri Ta Zauna kan Carpet din

"Ranka ya dade Lapia meke Faruwa"
Batareda ya kalleta bah Yace
"Ki Tambayi Yarki"
Umma ta hade Rai ta kalli Parveen
"Keh meke Faruwa"
Kuka Sosai Parveen take, dakyar ta Iya bude baki Tace
"Umma ni bazan koma bah, Ni anan zan za.."
Marinda Taji a Fuskanta neh ya hanata Qarasa maganan datake yi
"Parveen Lallai Na yarda kin Zama mara kunya, yanzu A gabana nida mahaifinki kike irin Wannan maganan??"
Kuka Sosai Parveen take Dafe da kuncinta.
Mai Martaba ya Mik'e Tsaye Fuskanshi a hande
"Ki Kyalleta zan Kira Sarki Kabeer gobe Naji meh ya Faru, ni nasan da Wani abu"
Saurin Katseshi Umma tayi
"Aa Ranka ya Dade, Baza'ayi haka bah. Karka Sanar dasu Yanzu, Iskanci neh kawai na Parveen"
Baice Komai bah yabar Falon Rai bace..

Kallan Parveen Umma tai
"Tashi kibar nan"
Dasauri ta mik'e tana cigaba da kuka tabar Falon. Kwana tai Kuka har zuwa Washe Gari bata Runtsa bah, Ana Idar da Sallan Asubah Umma ta Shigo dakin Parveen. Zaune ta sameta kan Sallaya tayi tagumi.
Zama Umman tai kan Gado tana Kallanta
"Parveen!"
Dago idanunta tai da Suka kukumbura tana Kallan Umman
"Parveen ki Fadamin meke Faruwa, Meyasa kikace bazaki koma bah??"
Kanta na Kasa Tace
"Bkmai. Umma Na Muku biyaiya na Auri wanda kuka zabamin, dan Allah kuyi hakuri ku raba Auren nan dan bana Sanshi"
Gaban Umma neh ya fadi, Ranta ya Baci
"Parveen kinsan meh kike fada kuwa, Me aka miki??"
Girgiza kai Tai Alamar Aa

"Fardeen ya miki wani abu neh??"
Nan ma Girgixa kan tai alamar Aa
"Tho Mai Martaba fah koh Fulani"
Girgizan kan Ta kara yi kanta na Qasa
Ran Umma neh Ya Qara baci
"Wai Meh kike nufi neh Parveen, Yanzu a matsayinmu na Iyayenki har Mu zaba miki miji Kice Bakyaso Parveen"
Fashewa Da kuka Parveen Tai Ta Mik'e ta Qarasa kusada Umma ta zauna tana Cigaba da Kuka
"Umma ban taba San Yarima bah daidai da rana Daya, Na dai xauna dashi ne Kawai saboda Nayi muku biyaiya"
Mik'ewa Umma tai Tabar Dakin Ranta Bace.

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤👑

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 5⃣1⃣ to 5⃣5⃣

Bude mata yayi ta shiga shima ya bude mazaunin driver ya zauna ya jasu suka bar gidan.
Tafiya suke na kurame, bah wanda ya cema kowa komai, tafiya sukai mai nisah. Wani hadadden wajan shaqatawa suka nufa, Yana shiga yayi parking inda aka tanada dan parking ya fito ya xagaya ya bude mata itama ta fito..

Cikin wajan suka nufa, suna tafiya a jere kamar wasu masoya, parveen taji dadin zuwa wajan. Wurare ya dinga nuna mata wanda bata sani bah, Sunyi yawo sosai rannan har qarfe shadaya, Gyangyadi ta fara yi yadan kalleta
"R uh sleepy?"
Kai ta gyada mai, yyi murmushi ya qarasa wani eatry ya siyo musu abubuwa iri iri, Cake, shawarma, meatpie, da gasheshen kaza. Sai Freshmilk. Koda ya dawo motan tayi barci, kallanta ya tsaya yi yanda take barci sai ta qara kyau. Fuskanta yadan shafa murya chan qasa yace
"Sleeping Beauty, she look's cute wen she's sleeping"
Dan motsawa tayi hakan yasa yayi saurin kauda kai ya tada motan xuwa gida..

Yana parking ta bude ido dakyar, ya kalleta da murmushi dauke a fuskanshi
"We're back"
Tadan Turo baki ta bude motan ta fito, kallanta tsaya yi. Bata kara kallanshi bah ta nufi side dinsu.

Kayan ya kwasa ya rufe motan ya wuce side din. Bai ganta falon bah hakan ya tabbatar mai tana dakinta, dakin ya wuce kai tsaye. A hankali ya murda kofan ya shiga a sanyaye, kwance ya sameta kan gado har ta koma barcin koh kayan jikinta bata cirebah. Ledojin ya aje kan bedside ya zauna bakin gadon kusada ita, shiru yayi yana tunanin yanda zai tasheta. Wata dabara ta fado mai ya mi'ke ya fita zuwa kicin, plate da cups ya dauko ya dawo dakin. Har yanzu barcinta take sha abinta

Iska ya fara hura mata a kunne, tadan bude ido tana turo baki. Murmushi yayi yana kallanta
"Tashi kici wani abu saiki koma ki kwanta"
Mikewa zaune tayi tana kallanshi
"Ni banajin yunwa. What are you doing here?"
Da mamaki ya kalleta
"Nida dakin matata har sai kin tambayeni mai nazoyi??"

Hade rai tayi ta kauda kai gefe, Muryanshi taji mai sanyi yana cewa
"Hakkina nazo karba"
Kallanshi tai da mamaki
"Wani hakki? Koh kabani ajiyanshi neh??"
Wani malalacin dariya ya saki yana shafa suman kanshi
"Haba Mallama koh ince Ustaziya, bai kamata kimin irin wannan tambayan bah. Look banason long Story, hakkina nake buqata yanzu."

Tsaki tayi ta mi'ke zata bar dakin, da zafi zafi ya mi'ke ya kamota tareda matseta a jikinshi, Mutsu mutsu ta farayi tana qoqarin tureshi
"Ka Sakeni menene haka??"
Qara matseta yayi yana kallan kwayan idonta
"Idan keh bakisan inda na ajeshi bah ni nasani"
Tureshi ta soma yi anma kamar bata tureshi, Saida ya tabbata ya matseta a jikinshi yanda bazata iya motsawa sannan ya hada bakinshi da nata, zaro ido tayi nan da nan jikinta ya soma rawa saboda wani baqon Alamari dake faruwa da ita..

Hawaye ne ya shiga zarya a fuskanta, Sun dade a haka saida ya tsotsi bakinta sosai sannan ya sake yana maida numfashi, idanunshi har sun qanqance. Kallanta yayi
"Pls coperate, I dnt want to force uh kinji"
Ganin ya sassauta mata riqon Yasa Ta tureshi daduk iya qafinta, dagudu ta shige toilet tasa key. Muryanta ya jiyo tana cewa
"Allah ya isa, mugu kawai. Kasa bakinka a na kowace arniya kazo kana samin"
Dariya abin yaso ya bashi, bakin gadon yasamu ya zauna dakyar, saboda yanda maranshi ke juyamai. Ya dade a zaune yana maida numfashi, daga nan inda yake yana jiyota sai brush take. Dan Dariya yayi ya mi'ke riqe da maranshi yabar dakin..

Tanajin ya fita ta dauraye bakinta ta bude qofan toilet din tadan leko kamar wata munafuka, ganin bai dakin yasa ta fito dagudu ta rufe kofan dakin ta danna key. Tsaki tayi yana qara yatsine Fuska
"Allah ya isa Wallahi, Mugu kawai. Sai Allah ya sakamin, mutum na baccinshi yazo ya tasheshi"
Kayan jikinta ta sauya zuwa na bacci ta fada kan gadon. Naiman Barcin dake idonta tayi ta rasa, abinda ya faru dazu keda dawo mata. lips dinta ta shafa tareda sakin lallausan murmushi, ta dade sannan barci ya dauketa...

Ummy Abduol✍🏻
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤👑

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 9⃣1⃣ to 9⃣5⃣

*Kuna Raina My Fans, Kuyi Min Afuwa. Banida Lapia neh yasa kuka jini shiru, Anma Yanzu Alhamdulillah dan Haka zamu Cigaba daga inda muka Tsaya*

A Gurguje Pls..

"Umma ban taba san Yarima bah dai dai da Rana daya Nadai Xauna dashi meh kawai saboda nai muku biyaiya"
Mik'ewa Umma tai tabar Dakin Ranta bace. Kasa Haquri tai Gari ya Waye Sosai, Part din Mai martaba ta Nufa Hankalinta tashe. Tana Kokarin shiga Suka hadu ya dawo daga Masallaci Shida Waziri da Dogaranshi, Saida Suka gaisa da waxiri sannan Ta kalli Mai Martaba
"Inada Magana neh Ranka Ya dade"
Dogaran najin Haka suka bar Wajan dasauri
"Shigo Ciki mana"
Bah musu ta Bishi suka Shiga Falon

Saida Ya zauna Sannan Itama ta xauna
"Lapia Aisha naganki haka meya Faru"
"Ranka Ya dade, Akwai Magana fah Gaskiya"
Gyara zama Mai Martaba yayi yana cigaba da Kallan Umma
"Lapia meh kike nufi?"
Ajiyan xuciya tai Tana Kallan Mai Martaba
"Ranka Ya dade har Yanzu Parveen nakan Bakanta na Kin komawa Gidanta, na Rasa Meke Faruwa"
Furzar da iskan Bakinshi Yayi
"Ai na fada miki Yanda Za'ayi tun Jiya"
Shiru Umma tai
"Shiknan Ranka ya dade haka Za'ayi"

Gari na qara wayewa Sarki Khaleed yadau wayanshi ya kira Sarki Kabeer, Yana Fara ringing ya dauka da Fara'a
Saida suka Gaisa Sannan sarki Kabeer Yace
"Yar tawa sai anjima zata taho??"
Jim Mai martaba Yayi har saida Sarki Kabeer yace
"Kanaji nah kuwa"
Dasauri Mai Martaba yayi gyaran murya
"Ina Jinka. Akwai Yar matasala neh tadan taso a nan"
"Matsala na meh fah?? Meya faru??"

Duk abinda Ya faru Sarki Khaleed ya fadami, jim yayi nadan Mintina Sannan Tace
"Zan sameshi naji meke Faruwa, anma Ni nasan bah laifinta bneh. Wannan mai Kunnen Kashin neh"
Dasauri Sarki Khaleed ya tareshi da Cewa
"Aa Kabeer, Itama fa yarinyan nan bajin maganan take bah"
Murmushin takaici Sarki Kabeer ya saki
"Hmm Khaleed knan, bakasan Halin Fardeen baneh"
Sun jima suna tattauna Yanda zasu bulloma Lamarin Daga Qarshe Sukai Sallama Akan Duk yanda ake ciki zasuyi waya..

Suna gamawa Sarki Kabeer Ya soma neman Layin Yarima, Yana Fara Ringing ya dauka Tareda sallama. Bah Tareda Ya amsa bah yace
"Kaso Inasan Ganinka"
Bai jira meh zaice bah ya kashe Kiran
Fulani Ya Nema itama ya sanar da ita ta sameshi a Side dinshi
Amsawa tai cikin girmamawa ta kashe kiran.
Kusan a tare suka shigo side din, Tsaye suka samu Maimartaba Ya goya Hannayenshi a baya Sai safa da marwa yake Ranshi bace. Kan Carpet Yarima Ya zauna Dan Ya tsargu a yanda Yaga mai martaba, Fulani ta zauna Kan Kujera tana Kallanshi
"Lapia Ranka ya dade, meya Faru??"
A Fusace ya juyo yana Kallan yarima
"Kai Fardeen! Ka Fadamin mene Tsakaninka da Parveen"
Gaban Yarima ya fadi Ya dago Manyan Idanunsh yana Kallan Mai Martaba..

Fulani ce Tayi Qarfin Halin Cewa
"Lapia Me akace Anyi"
Hannu Mai Martaba ya dagama Fulani alamar Tai shiru. Tsit Tayi tana cigaba da kallanshi
"Kai naye Saurare"
Cikin In ina Yarima Sunkuyar da kai Kasa
"Ranka Ya dade bah..B.."
Ran Mai Martabane Ya Qara baci
"Oh! Tho hakan da Kayi ya nuna Akwai Wani abu knan, Na dade da Sanin da Wani Manufa ka Auri Yarinyan nan. Tho Gashi nan tace Bazata dawo bah, Yanxu muka gama Waya da Sarki Khaleed"

Fulani ta Zaro ido da mamaki
"Bazata dawo bah?? Iya Sanina Ranka ya dade bah Abinda Akaima Yarinyan nan, kum"
Katseta Mai Martaba yayi da cewa
"Ba ke kike Aurenta bah, dan Haka Bazaki san Abinda Yake faruwa bah. Sannan kuma bah Tare Kuke dasu bah"
Hankalin Yarima ya tashi, Nan da nan zufa Ya fara Karyo mai, duk da Sanyin Ac da kuma Fanka dake Dakin. Hulan dake Kanshi ya cire Ya Aje Gefe
"Yarima ka bani kunya, Ban taba Tunanin Haka daga gareka bah. Inace Kai kace kanasan Yarinyan nan akayi auren nan, Ashe Muzguna mata kake"
Dasauri Yarima Ya dago Jajayen Idanunshi Ya daura kan na Mahaifinshi
"Wallahi Abba Bansan menai Mata bah, Nadai san kwanakin Baya Mundan samu Sabani da Ita kuma na bata Hakuri"
Kallan Fulani Mai Martaba Yayi
"Kinji Koh! Anzo gurin ni nasan Yarinyan nan Hakanan Bazatace Bazata dawo bah"
"Dan Allah Ranka Ya dade kai Haquri, Yanzu Mafita Yakamata A nema" cewar Fulani

Zama Mai Martaba Yayi Yana Kallan Yarima
"Kamar Yanda Ka bata mata rai Haka zaka koma Ka bata Haquri, idan Ta Yarda ta Haqura Tho. Idan Kuma Taqi Shiknan Sai Ku Haqura da Juna"
Bai Jira mai Zasuce Bah Ya mik'e Yabar Musu Falon.
Fulani Ta kalli Yarima Cikeda Damuwa
"Kaga Irin Abinda Nake Fadamaka Koh Yarima, Why! Why!! Meyasa Zakai Haka?? Tunda Kasan Baka Santa Meyasa ka Aureta"
Dagowa Yayi Yana Kallan Fulanin Idanunshi Taf da Hawaye
"Believe me Fulani, Dah Banasan Parveen Anma Yanzu Ina Santa. I Cnt Do wit out Her, I So much Love Her Fulani"
Kanshi ta shafa Itama Hankalinta Tashe
"Karka Damu evrytyn Will be Fine, Yanzu Ka Shirya Gobe Kaje Ka Sameta Kaji"
Tho Yace Kanshi na Qasa.
Bata Qara cemai Komai Bah, Ganin Shirun Yayi yawa yasa ya mik'e yamata Sallama Yabar Falon...

A Qasar su Parveen kuwa, Mai martaba da umma Ransu Yakai Qololuwan Baci, fushi Sukeyi da Yar Tasu. Hakan Yasa Hankalin Parveen ya Qara Tashi, Inama Batai Wannan Katobaran Bah, Anma Hakan da Tai Tana Ganin Shine Yafi Mata. Ganin Ta Kasa warware Matsalanta Yasa ta kira Deeza Akan Taxo Tanada Magana da ita.
Yanmacin Rannan Tazo gidan Hankalinta tashe Saboda Yanda Parveen tai Mata Kiran. Sun Kure Cikin Daki Nan Parveen ke Labartawa Deexa duk abinda ke Faruwa. Sosai Deeza Ta Hade Rai
"Haba Parveen! Yanzu ke a Ganinki Hakan da kikai Ya dace??. Wallahi bakya bina Bashin Rantsuwa Yarima na Sanki"
Kallan deexan tai da Mamaki
"Kinyi Kuskure Deeza, Kamar Yanda Bansan Yarima Haka Shima Baisona"
Murmushin yak'e Deeza Tai Tana Cigaba da Kallanta
"Kinada Hujjan Da zaki tabbatar min da hakan?"
Shiru Parveen Tayi ta Shiga Tunanin Wani Hujja Zataba D[truncated by WhatsApp]
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤👑

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 9⃣5⃣ to 1⃣0⃣0⃣


"Kinada hujjan da zaki tabbatar min da hakan?"
Shiru Parveen Tayi ta Shiga Tunanin Wani Hujja zataba Deeza. Ganin Batace komai bah Yasa Deeza ta saki Murnushi Tana Kallanta
"Uh See! Wallahi Bazanyi Kaffara Bah Yarima Na sanki, ki Manta da abinda ya faru a baya. Wannan zan iya cewa Lokacin Bakwa San Juna, anma Yanzu Believe me Kunasan Junanku"
Kallanta Parveen Tai ranta Bace
"Kada ki taba Tunanin Inasan Yarima, A duniya bah Wanda na Tsana Kamarshi"
Dariya Maganan Deeza tai Sosai
"Bae! Tun Muna Primary school muke Tare, kinsan Halina Nasan Naki. Lemme tel uh something, Kinasan Yarima Wallahi. Kawai dai Kice Baki Fahimci Hakan Baneh"

Tsaki Parveen tai ta mik'e tana Turo Baki
"Idan na Biyemiki Bazan Samu nai abinda ya kamata bah"
Binta da kallo Kawai deeza take tana Girgiza kai tareda Murmushi...

A Bangaren Yarima Kuwa Hankalinshi ne Ya tashi, meyasa Parveen zatamai Haka?? Kasa Barci Yayi har wuraren Karfe Goma na Dare. Numbernta dayayi Saving Da "Queen" ya Lallubo Yana Kallo, Cikin Karfin Hali Ya Danna Ya soma Kira. Saida Ya kira Sau Uku ana Ukun aka daga Tareda Sallama. Lumshe ido Yayi saboda yanda Muryanta ya Ratsa Shi, dakyar Ya tattaro natsuwarshi. Amsa Sallaman Yayi Tareda Yin Shiru
Itama Shiru Tai Kamar Taso ta gane Muryan Anma ta dake tace
"Wanene??"
Jim Yayi kamar karya amsa tuna abinda Yake Faruwa Yasa Yace
"Bakida Mah Number na Koh Queen!"
Jin Sunanda Ya kirata dashi yasa ta Gane Wanene tadan Ja guntun Tsaki Mara Sauti
"Pls wanene?? Ni banida Mumbern"
Murmushi ya saki Sannan Yace
"Fardeen Kabeer ke magana"
Chan Kuma yace
"Mijinki"
Shiru tai nadan Wani lokaci Sannan Tace
"Lapia??"

Sassauta Murya yayi kamar mai Rada Ya Qara kara Wayan a Kunnenshi
"Meyasa Zakimin Haka Queen? Meyasa zakice Bazaki dawo bah. What hav I done 2 you??"
Tsaki Taja Tareda daga murya tana cewa
"Mallan Bansan Jin Wannan Surutun, Abinda nakeso shine ka

Please Login or Register in order to submit comment