Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fulani ya gani a bakin kofan, Zubewa sukai suka kwashi gaisuwa, baice komai bah ya basu hanya suka wuce. Kan dinning suka aje suka fita. Kicin ya shiga yadauko plate da spoon ya fito, Kulan ya bude fried rice yagani ya zuba kadan ya bude dayan, Pepper chicken neh a ciki, ya zuba Ya rurufe ya nufi dakin Parveen...

Ganinta yayi zaune kan gado ta jingina da jikin gadon idonta a lumshe, tun sanda aketa buga kofan ta tashi. Qarsowa bakin gadon yayi ya xauna yana Kallanta, kamar bazaiyi magana bah chan ya nisa yace
"Ya jikin??"
Dasauqi tace a takaice
Abincin ya aje kan gadon gabanta, "kici dan nasan kinajin yunwa"
Girgiza mai kai tayi kawai. Kafada Ya daga ya miqe zai bar dakin, Muryanta kamar zatai kuka yana rawa ta kalleshi
"Pls ka kiramin fulani"
Juyowa yayi yana kallanta
"Saboda meh?, ki fadi meh kikeso sae bayi su miki yanzu dare yayi"
Batace komai bah ta zame ta kwanta tareda fashewa da kuka sosai..

Kallanta yayi da mamaki, Jin kukanta yayi har cikin ranshi. Tsintan kanshi yayi yana cewa
"Plss stop crying, banaso naga mace na kuka"
Ganin tana neman tayar mai da hankali yasa ya bude kofan zai fita.
Jin muryanta yayi tana cewa
"Dan Allah inaso naje Gida, inaso naje naga Ummana"
Saurin juyowa yayi yaga shi take kallo, ya qaraso bakin gadon yana kallanta.
"Abinda yasaki Ciwo knan??"
Batace komai bah kanta na qasa. Kafada ya daga tareda kauda kai
"Duk sanda kika shirya uh shld let me knw"
Bai jira mai zatace bah ya bar dakin...

Neman ciwon dake jikinta tayi ta rasa, mikewa tayi tsaye Ta fada toilet don watsa ruwa Cikeda Farinciki. Tana fitowa ta dau abincinda ya kawo mata ta fara ci tana tunanin randa zatacemai zata gidan. Shiko gogan dakinshi ya shiga, mamakin kanshi yake yanda Kwana biyun nan ya chanza, a Fili yace
"Wai meh ke Faruwa dani neh?"
Shiru Yayi yana tunani, anya kuma shine? Ta baya ya fada Yayi pillow da tafikan hannayenshi yana tunani...

Washe Gari da wuri ta tashi ta gyara gidan, dan yarima ya koran mata Atika. Share ko ina tayi ta goge sannan ta shiga kicin ta daura musu break, tana gamawa ta koma daki tayi wanka ta shirya ta fito. Zama tayi ta soma break din chan sai gashi ya fito shima cikin Shiri, suit bak'i da white shirt. Wiyanshi daure da red bod tie, kayan sunmai kyau sosai. parveen kasa dauke idonta tayi daga kallanshi, Har abin ya bashi mamaki..

Saida Taji yaja kujera ya zauna sannan tai saurin kauda kai, dan murmushi kawai yayi yana kallanta
"Good morning hw's ur health"
Kanta na qasa murya chan qasa ta amsa
"Am Fine Alhamdulillah"
Shiru ne ya biyo baya na kusa Mintina, Ganin Shirun Yayi yawa yasa tadan dago suka koh hada ido. Maida kanta qasa tayi dakyar murya chan ciki tace
"Thank uh for ur help yesterday"
Dan murmushi yayi yana Shafa suman kanshi dayasha Gyara
"Uh dnt hav to. Its my responsibility to du dat"
Bata cemai komai bah ta mike ta fara Serving dinshi...

Kasa cin nata tayi a gabansh ta dau plate din ta shiga dashi kicin ta fito, daki ta koma tadau jakanta da litatafanta ta fito. Yana nan zaune yana Break tazo zata wuce, Sunanta ya kira Murya a Sanyaye
"Parveen!"
Jin abin tayi kamar a mafarki, yau neh rana ta farko daya taba Kiran sunanta. A Hankali ta lumshe ido, jitayi kamar duk duniya bah wanda ya Iya kiran sunanta kamarshi.
A Wani bangaren kuma gabanta neh ya fara faduwa, kada yauma ya hanata zuwa School, gashi yau tanada test...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

*PWF*

Page4⃣1⃣ to 4⃣5⃣

Dedicated dis page to *MMN YUSRA* Allah ya barmu tare😘

Ana cikin haka Allah ya jehomin Yarima dayazo wucewa da motarshi shida dogaranshi. Da Taimakon Allah da taimakon yarima aka koresu, shi ya Tsayamin har kotu dan bimin Haqqina, Saboda na gane daya daga cikin Yaran. Mahaifina koh ajikinshi, Karkice bai rasa abinda zai kai qaran kotu bah. Yana dashi"

Kukan Yasmeen ta cigaba cikeda takaici, Kallan Parveen tai wacce itama kukan take a hankali
"Yanzu parveen wazai tunkareni Yace zai aureni??, koh Saurayi yazo wajena so daya so biyu bai qara zuwa indai yaji labarina"
Ajiyan zuciya parveen ta saki ta share hawayen Fuskanta
"Karki damu Yasmeen, Allah yana Tare dake. Kuma Insha Allahu zan rike miki sirrinki, kada ki cire tsammani ga rahamar Allah insha Allahu xaki samu miji kiyi aure kamar kowacce mace"
Murmushi Yasmeen tai
"Nagode Parveen, Allah Ya barmu Tare. Dalilina knan danake neman Yarima dan na Qara gode mai"

"Karki damu, Shi kanshi nasan ya manta"
Yasmeen ta kalli agogon hannunta,
"Kai Har an fara lectures"
Dasauri suka miqe suka Qarasa class din danma Allah yasa lecturan bamai zafi baneh..

K'arfe Hudu saura Kwata suka fito daga Class, ga mamakinta motar Yarima ta hango yayi parking a Inda ya ajeta, Kallan Yasmeen tai dake magana da Wani dan Class dinsu
"Yasmeen ni zan tafi kinga anzo daukana"
"Ayyah Friend shiknan Tho Sai Gobe"
Suna Gama Sallama Ta qarasa wajan motan, A Tunaninta Yarima neh. Dan ladi driver ta gani zaune a motan, Gaidata yayi sannan Ya fada mata yarima ne yace yazo ya dauketa. Tabe baki tayi ta shiga motan yaja suka bar school din...

Tana zuwa gida ta fada toilet ta watsa ruwa ta Fito, garin da xafi dan haka 3quater da Vest tasa ta Fito ta shiga Cikin, Yau tuwo miyan Kubewa take Sha'awa. Tana Kicin tana tuqa tuwo Yarima ya shigo falon da Sallama, motsin dayaji a Kici neh yasa yaqarasa. Mutuwar Tsaye yayi, bah qaramin kyau tamai bah. Maranshi neh yaji ya juyamai. Rike Wajan Yayi yana Cije lebe. Sam batasan ya shigo bah dan hankalinta nakan Tuqa tuwon datake..

Saida ta gama Ta juyo zata duba miyan Taji a jikinta kamar ana kallanta, a hankali ta daga ido suka Koh hada ido. Murmushi ya sakarmata tai saurin kauda kai, Kicin din ya shigo ya amsa Wuqan dake Hannunta.
"Yau tare zamuyi girkin"
Dan murmushi kwai tayi batace komai bah. Rasa mai zatace mai tai Chan Kuma ta dake tadan dago tana kallanshi

"Thursday nakeso naje Gida, Coz rannan bamuda Wani lectures"
Jim Yayi kamar mai tunani, jin shirun Yayi yawa yasa ta dago tana kallanshi. Murmushi ya mata,
"Shiknan Allah Ya kaimu. Idan kika tafi kwana nawa zakiyi"
"Ranan Sunday zan dawo saboda School"
Kafada ya daga Yana Kallanta
"Ok bah damuwa, Allah Ya kaimu"
Ameen Tace Tana cigaba da aikinta..

Albasan dayaga tana qoqarin yankawa ya dauka Ya fara kici kicin yankawa, da gefen ido parveen ke kallanshi, gunshe dariya tai tana cigaba da Kallanshi. Qara ya saki
"Ouch!"
Tareda yarda Albasan da Wukan, Hannunshi ya riqe ya soma Yarfe hannun, Dasauri parveen ta qaraso
"Lapia? Wh happen?"
Hannun ya soma nuna mata yana Yamutse Fuska..

Yanda Yake bata Fuska Bah qaramin dariya Ya bata bah, Dakyar ta samu ta danne ta Rike Hannun dakyar. Tap ta bude ta tara hannun tana Goge mai
"Am Sorry! Kaga fah Baka iya bah. Ni bance ka yankamin bah"
Wurin daya yanken tasa dan yatsanta tana goge jinin wajan. Dasauri ya zame hannunshi yana k'ara. Kasa daurewa tai ta saki Dariya tana Kallanshi, Kallanta Yake da Mamaki. Yaune Rana ta farko daya taba ganin dariyanta, kallanta yake baiko kyaftawa
"She Looks Cute wen She's laughing"

Hade Rai yayi yabar kicin din yana cigaba da Yarfe Hannu, Jitayi kuma bataji dadi bah. Kodai dariyan datamai neh ya batamai rai??
Kafada ta daga ta cigaba da girkinta. Tana gamawa ta Hada komai a Kula ta kira waya akazo aka dau na maimartaba Sannan Ta dau na Yarima ta aje kan dinning...

Daki ta koma ta sauya kaya zuwa bak'in after dress, tai Sallah sannan ta fito. A Falo ta tarar dashi yana kallan news, Abinda ya faru dazune ya dawo mata ta sauke Lallausan Murmushi. Dinning ta qarasa ta fara zubamai abincin, Jim tayi tana tunanin yanda zata fadamai ta gama, chan ta dake ta qarasa inda yake zaune. Bah tareda ta kalleshi bah tace

"A nan zakaci abincin koh na barshi a dinning??"
Tsuke fuska yayi yana kallanta
"No thank uh am Ok"
Shiru tayi tana kallanshi. Shi wannan dan kawai nayi dariya??
Barin wajan tayi a ranta tana cigab da fadin
"Ni nace neh kazo ka tayai?? Karkaci cikin wah??"
Guntun Tsaki Taja tahau dinning din ta faracin nata..

Zumbur taga ya mike ya kashe tvn ya shige daki, Ji tayi kuma bataji dadi bah. Sam bai taba qin cin abincinta bah, Tafi zargin Kanta saboda dariyan datamai. Tana gama cin abincin ta dawo falo ta zauna ta kunna tv tana kallo. Anma sam hankalinta ba'akan Kallan yake bah. Tana nan har aka kira sallan Isha'i, Daki ta koma ta gabatar da Sallah ta Fito. Har k'arfe tara tana daki, hankalinta neh yaq'i kwanciya ta fito falon ta duba dinning din koh yaci. Ganin baici bah yasa hankalinta ya qara tashi ta nufi dakinshi a sanyaye...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page1⃣9⃣

Qarasa Maganan Tai Rai Bace
"Kai Qoqari ka Koma Islamiya Dan Har Yanzu jahilci na Dawainiya Dakai!"
Wani Kukan Kura Yarima Yayi ya Mike Tsaye, Mari kyawawa Guda biyu Ya Saukewa Parveen Wanda Saida Taga Stars.
Shaqeta Yayi Fuskan nan Nashi Na Chanza zuwa ja, inda Abinda Yarima Ya Tsana Bai wuce Parveen Ta kirashi jahili bah.
Huci Yake Sosai, Hannunshi Na Kan wuyanta Daya Maqure, Parveen ko Sai Tari Take Dakyar Idanunta Sun Firfito, Ganin Bah sarki Sai Allah Gashi Bah Iya Magana Zatai bah Yasa Ta Rarumi Glass Cup dinda Ke kusa da Ita Ta Bugamai Akai. Sakinta Yayi dasauri ta Fadi Kasa Tana Rike Da Wuyanta, Wurin data Bugamai cup din Ya Dafe Ta mike Dakyar Ta nufi dakinta A Guje Tareda Sa Key..

Ranshi Bace Ya bita Da Kallo, Hannunshi dake kanshi Ya Sauke Yana Dubawa, Allah Yaso Cup din Bai jimai Ciwo bah. Wayanshi Ya dauka Yabar Falon a Zuciye. Parveen Kan Gadonta ta Fada Ta Saki kuka Mai Karfi, Anya Kuwa Zata Iya cigaba da Zama a Gidan nan Da Yarima?? Tsagaita Kukan tai Tana Tunani. Inko Har Zata Cigaba da Zama dashi to dole Tadau Damara Dan Ta Nunamai Itama Macece. Da Wannan Tunanin Ta Yini Yar Yanma..

Satin Parveen Biyu kullum Idan tai Girki Sai Tasama Mai Martaba Da Fulani, Shiko gogan Idan ya Dawo Atika take Sawa Tai Serving Dinshi. Ranar data Cika Sati biyu Kuma a Ranan Zata Fara zuwa Schl, Da Safe Ta shirya Cikin Hadadden Shaddanta Purple, Dinkin Riga da Skirt. Side din mai Martaba ta Fara nufa Don Kwasan Gaisuwa, Tana Shiga Ya tareta Da Fara'a, har qasa ta Tsuguna Ta Gaidashi. Ya Amsa Fuska a Sake, Godiya ya Mata Akan Abincinda Take aikomai, Dan murmushi kawai Tai Sannan Tace
"Bakomai Ranka Ya Dade. Kaima Ai Mahaifina neh"
Gyada Kai Mai Martaba Yayi
"Hakaneh Parveen, Inajin Dadin Girkin da kike Min, Yanzu duk na aje Girkin Turawan nan"
Dan Dariya tai Qasa Qasa, Ta Sadda Kai
"Ranka Ya Dade Yau kace Zan Fara Zuwa Makaranta"
Kai Mai Martaba Ya Gyada
"Hakaneh yanzu idan kin Shirya sai Aima Sarkin Mota Magana Yakaiki, Kije ki Zabi duk motar da Kikeso a Kaiki a Ciki"
Dan Murmushi Tai Tareda Godiya, ta mike Tabar Side din Cikeda Farinciki..

Side din fulani Taje Ta Gaidata Sannan Ta Mata Sallama. A Wani Hadadden Buggatti aka Dauketa Zuwa Makaranta. Ta samu An Gama Mata komai, Lectures Kawai Zata Fara Attending, Dadi Taji Sosai, A Ranan Tai Sabuwar Qawa mai Suna Yasmeen...

A Gida Kuwa yarima Cikin Shiri Ya Fito dan Zuwa office, Dogarinshi na Binshi dauke da Jakan laptop dinshi. Wajan Motocin Gidan Suka Nufa, Ganin Bah Motan Da yayi niyan Fita Dashi Yasa Ya Hade Rai, juyawa Yayi Ya Kalli Dogarin. Jeka Kiramin Sallau, Tho Yace Ya Tafi dasauri.
Chan Sai Gasu Tare, rai Bace Yarima Ya Kalleshi, Ina Motar danasaka Ka Wanke. Sosa Kai Sallau Ya Fara. Tsawa Yarima Ya dakamai
"Kai make Saurare"
"Ranka Ya Dade Gimbiyace Tace Abata Motan Dashi Za'a Kaita Makaranta"
Wace Gimbiya??"
"Amarya Ranka Ya Dade"
Tsawa Yarima Ya Dakamai
"Har Ni Inyi Magana Akan Inason Abu, Anma ka Dauka Kaba Wani Chan??"
Dogarin Dake Gefe Ya Kira Tareda Bashi Umarnin A Tafi da Salihu amai Bulala Hamsin Sannan A koreshi.
Dasauri Sallau Ya rusunna yana Bada Haquri
"Dan Allah Ranka Ya Dade Kamin Rai, Da Wannan sana'an Nake Cida Iyayena da Iyalina. Na Yarda Amin Bulalan Anma Kar a Koreni"
Tsaki Yarima Yayi, ya Shiga benz dinda Ke Kusa Dashi Drivern Ya Tada Sukabar haraban Gidan...

Parveen bata dawo gidan bah Sai Bayan La'asar, Side dinta ta nufa Saboda ta Gaji, Wanka tai ta Sauya Kaya Zuwa 3quater da Yar Qaramar Pink Tshirt, Saboda Lokacin Xafi neh. Kicin Ta Shiga ta Fara Hada Abincin Dare, Qulunta na waina ta bude Ta duba taga ko ya tashi har Yafara zubewa, Nan da Nan ta Fara Hada Miyan Alehonta Dayasha Kayan Hadi. Tana Gamawa Tahau Suyan Wainan. Bata Gamaba Saida Aka Kira Sallan Magrib, Sallah taje Tai Sannan Tazo Ta bada namai Martaba..

Zama Tai Taci Nata Sannan Ta koma Falo Ta kunna Tv tana Kallo, Yarima Bai Shigo Gidan bah Sai Wuraren Karfe Shadaya. Har Barci Ya kwasheta Tana Zaune Taji Bude Qofan Falon, Juyawa Tayi Taga Mai Shigowan, Yarima neh Ya Shigo Hannunshi Cikin na Wata Budurwa wacce bata wuce Sa'ar Parveen bah, Sanye Cikin wani dan qaramin Skirt, da Riga Half vest. Tsaki Parveen tai ta Mike Tabar Falon Zuwa Dakinta..

Washe Gari da Safe Tana Idar da Sallah Tadau qur'aninta Tana Karantawa, Bude Qofan Dakin Akai Aka Shigo, ganin Yarima neh Yasa Tace
"Sadaqallahul Azim"
Ta Rufe Tareda Hade rai Tana Kallanshi
Shima Fuskan Nashi a Hade Ya kalleta
"Yau Zan Fita da Wuri, Ki Tashi ki Hadamin Breakfast, Sannan Babyna Plantain Takeso da Egg Yau. Idan Na Fita Kiyi Qoqari Ki Gyaramin Dakina Kafin nadawo"

Bai Jira Cewarta Bah Ya Juya Zai Fita.
Murmushin Takaici Parveen Tai Tace
"Ai Baka Aje Yar Aiki bah a Gidan da Zata Maka Duk Wannan Aikin. Koh Ka Ajene ni Bansani Bah"
Juyowa Yayi ya Kalleta Rai Bace
"Ai Dake da Bayin Gidan nan Babu Maraba a Wajena, Duk daya Kuke. Dan Haka Ina Jiran Breakfast Nan da 1hour idan Bah Haka bah..kwafa Yayi Yabar dakin Tareda Bugo qofan Dakin"

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 5⃣1⃣ to 5⃣5⃣

Bude mata yayi ta shiga shima ya bude mazaunin driver ya zauna ya jasu suka bar gidan.
Tafiya suke na kurame, bah wanda ya cema kowa komai, tafiya sukai mai nisah. Wani hadadden wajan shaqatawa suka nufa, Yana shiga yayi parking inda aka tanada dan parking ya fito ya xagaya ya bude mata itama ta fito..

Cikin wajan suka nufa, suna tafiya a jere kamar wasu masoya, parveen taji dadin zuwa wajan. Wurare ya dinga nuna mata wanda bata sani bah, Sunyi yawo sosai rannan har qarfe shadaya, Gyangyadi ta fara yi yadan kalleta
"R uh sleepy?"
Kai ta gyada mai, yyi murmushi ya qarasa wani eatry ya siyo musu abubuwa iri iri, Cake, shawarma, meatpie, da gasheshen kaza. Sai Freshmilk. Koda ya dawo motan tayi barci, kallanta ya tsaya yi yanda take barci sai ta qara kyau. Fuskanta yadan shafa murya chan qasa yace
"Sleeping Beauty, she look's cute wen she's sleeping"
Dan motsawa tayi hakan yasa yayi saurin kauda kai ya tada motan xuwa gida..

Yana parking ta bude ido dakyar, ya kalleta da murmushi dauke a fuskanshi
"We're back"
Tadan Turo baki ta bude motan ta fito, kallanta tsaya yi. Bata kara kallanshi bah ta nufi side dinsu.

Kayan ya kwasa ya rufe motan ya wuce side din. Bai ganta falon bah hakan ya tabbatar mai tana dakinta, dakin ya wuce kai tsaye. A hankali ya murda kofan ya shiga a sanyaye, kwance ya sameta kan gado har ta koma barcin koh kayan jikinta bata cirebah. Ledojin ya aje kan bedside ya zauna bakin gadon kusada ita, shiru yayi yana tunanin yanda zai tasheta. Wata dabara ta fado mai ya mi'ke ya fita zuwa kicin, plate da cups ya dauko ya dawo dakin. Har yanzu barcinta take sha abinta

Iska ya fara hura mata a kunne, tadan bude ido tana turo baki. Murmushi yayi yana kallanta
"Tashi kici wani abu saiki koma ki kwanta"
Mikewa zaune tayi tana kallanshi
"Ni banajin yunwa. What are you doing here?"
Da mamaki ya kalleta
"Nida dakin matata har sai kin tambayeni mai nazoyi??"

Hade rai tayi ta kauda kai gefe, Muryanshi taji mai sanyi yana cewa
"Hakkina nazo karba"
Kallanshi tai da mamaki
"Wani hakki? Koh kabani ajiyanshi neh??"
Wani malalacin dariya ya saki yana shafa suman kanshi
"Haba Mallama koh ince Ustaziya, bai kamata kimin irin wannan tambayan bah. Look banason long Story, hakkina nake buqata yanzu."

Tsaki tayi ta mi'ke zata bar dakin, da zafi zafi ya mi'ke ya kamota tareda matseta a jikinshi, Mutsu mutsu ta farayi tana qoqarin tureshi
"Ka Sakeni menene haka??"
Qara matseta yayi yana kallan kwayan idonta
"Idan keh bakisan inda na ajeshi bah ni nasani"
Tureshi ta soma yi anma kamar bata tureshi, Saida ya tabbata ya matseta a jikinshi yanda bazata iya motsawa sannan ya hada bakinshi da nata, zaro ido tayi nan da nan jikinta ya soma rawa saboda wani baqon Alamari dake faruwa da ita..

Hawaye ne ya shiga zarya a fuskanta, Sun dade a haka saida ya tsotsi bakinta sosai sannan ya sake yana maida numfashi, idanunshi har sun qanqance. Kallanta yayi
"Pls coperate, I dnt want to force uh kinji"
Ganin ya sassauta mata riqon Yasa Ta tureshi daduk iya qafinta, dagudu ta shige toilet tasa key. Muryanta ya jiyo tana cewa
"Allah ya isa, mugu kawai. Kasa bakinka a na kowace arniya kazo kana samin"
Dariya abin yaso ya bashi, bakin gadon yasamu ya zauna dakyar, saboda yanda maranshi ke juyamai. Ya dade a zaune yana maida numfashi, daga nan inda yake yana jiyota sai brush take. Dan Dariya yayi ya mi'ke riqe da maranshi yabar dakin..

Tanajin ya fita ta dauraye bakinta ta bude qofan toilet din tadan leko kamar wata munafuka, ganin bai dakin yasa ta fito dagudu ta rufe kofan dakin ta danna key. Tsaki tayi yana qara yatsine Fuska
"Allah ya isa Wallahi, Mugu kawai. Sai Allah ya sakamin, mutum na baccinshi yazo ya tasheshi"
Kayan jikinta ta sauya zuwa na barci ta fada kan gadon. Naiman Barcin dake idonta tayi ta rasa, abinda ya faru dazu keda dawo mata. lips dinta ta shafa tareda sakin lallausan murmushi, ta dade sannan barci ya dauketa...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page4⃣6⃣ to5⃣0⃣

Dedicated is page to *Yar Mitsila n ol Perfect Writers Forum Members*

Ganin baici bahyasa hankalinta ya qara tashi ta nufi dakinshi a sanyaye.
Yarima na kwance kan Gado, yayi filo da hannunshi Yana kallan sama. Tunanin sauyawarshi kwana biyun nan yake, koda yayi niyan yi mata rashin mutumci sai ya kasa. Yana cikin wannan tunanin yaji an bude kofan dakinshi, da mamaki ya mike ya zauna dan yasan bah parveen bace. Ganinta yayi ta shigo dakin da sallama suna hada ido ta duqar dakai tana wasa da zoben zinarin dake hannunta..
Baice komai bah ya koma ya kwanta kamar yanda yake dah, qarasowa tayi dakin chan nesa dashi ta tsaya tana kallanshi. Rasa yanda zatamai maganan ma tayi dakyar murya chan qasa tace
"Am very sorry. Bansan dariyan danai ze batama rai bah"
Baice komai bah kuma bai kalleta bah.
Sunkai minti goma a haka, ganin baida niyan magana yasa tadan kalleshi
"Pls am sorry, naga bakaci abinci bah. Pls ka tashi muje kaci"
Nan ma shiru ya mata. Haushi ne ya kamata ta fara danasani meh mah ya kawota dakinshi har taje wani bashi hakuri. Juyawa tai zatabar dakin har takai bakin kofan ta riqe handle din taji muryanshi yana cewa
"Bah fushi nayi bah, kawai na gaji neh"
Tadan juyo tana kallanshi da narkakun idanunta
"Tho mai yasa bakaci abinci bah??"

Shiru yayi baice komai bah, chan kuma ya mike yana kallanta
"Muje tho zanci"
Murmushi tamai ta Fito yana binta a baya, kallan bayanta yake yanda take tafiya cikin natsuwa koh ina na jikinta na motswa, idonshi ya lumshe ya bude. Kujeran yaja ya zauna ta fara serving dinshi, miyan da yagani neh yasa ya yatsine Fuska ta kalleshi da mamaki
"What??"
Qara yatsine Fuska yayi
"Banasan Wannan Miyan"
Dan Murmushi tamai
"Why??! Akwai dadi fah. Try it"
Girgiza kai yayi ya mike, da mamakinshi gani yayi ta rikeshi ta zaunar dashi. Hada ido sukai, ita kanta abin mamaki ya bata. Dasauri ta sakeshi tareda juya baya, dayake dan duniya neh murmushi kawai yayi
"I can't eat dis mess"
Juyowa tayi tana kallanshi da dan Murmushi
" Try it, Akwai dadi"

Fuska ya yatsine tareda kauda kai, hade rai tayi ta bar wajan ta koma palour ta zauna. Ji yayi bah dadi, knan tayi fushi neh. Plate din dake gabanshi ya dauka ya qarasa falon ya zauna kusa da ita. Kauda kai tayi kamar bata ganshi bah, murmuahi ya saki ya tashi ya dawo gabanta ya zauna a qasa yana kallanta.
"Am Sorry tho! Na yarda zanci but on 1 condition"
Tadan kalleshi har yanzu fuskanta bah walwala
"What condition?
"Sai idan kin yarda zaki bani a baki"

Kallanshi tayi da mamaki, gira ya daga mata yana yar murmushi. Kauda kai tayi tana tabe baki
"Nikam bazan baka abinci a baki bh, kadai ci kawai"
Kafada ya daga
"Shiknan."
Ya ture abincin gefe ya mi'ke zai bar wajan, Ganin dagaske Yake yasa ta kira sunanshi a hankali
"Fardeen!"
Juyowa yayi da mamaki yana Kallanta. Tunda suke da ita yaune Rana ta farko data taba kiran sunanshi, Ya dago yadan Rankafo yana kallan Fuskanta
"Call my name again pls"
Kunya neh ya kamata tadan kauda kai tana Murmushi. Shima murmushin Yayi ya kalleta
"Ki shirya ynzu zamuje wani waje mu dawo"
Da mamaki ta kalleshi
"Ina??"
"Kedai kawai ki shirya"
Bai jira meh zatace bah yabar falon zuwa dakinshi.

Plate din ta dauke takai kicin ta fito dakinta ta shiga ta sauya kaya zuwa Shadda Purple, dinkin dogon Riga. kayan sun matuqar amsanta, gyale light purple ta dauko ta yafa Tareda Takali White. Kallan kanta a madubi tayi, ta saki murmushi tareda qara juyawa. Jikinta ta feshe da turare ta dau wayanta ta fito..

Dai dai shima ya fito sanye da White polo da brown chinox. Gashin nan yasha Gyara sai kyalli yake. Kasa dauke idonta tayi daga kallanshi, Ganin yana neman Ganota yasa ta dauke idonta dasauri daga kanshi. Batreda Ta kalleshi bah tace
"Am ready"
Murmushi yayi yana kallanta, hannunta ya rike yana cigaba da kallan kwayar idonta.
"Uh Look Beautiful"
Dan dariya tayi tareda zame hannunta daga nashi
"Oh sorry! Bakyaso na riqe hannunki koh? Ok lets go"
Yana tafe tana binshi a baya Har inda zasu hau mota. Kallanta yayi qasa qasa
"Wacce kikeso mu hau??"
Murmushi tayi tareda nunamai Sabon Prado dinda Mai martaba Ya siyan mai..
Shima murmushin Yayi yana kallanta
"Dats my choice"
Bude mata yayi ta shiga shima ya bude mazaunin driver ya zauna Ya jasu suka bar gidan...

Niko Ummy abduol nace Ina Yarima zaikai Parveen??

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

*Perfect Writers Forum*
*P.W.F*

Page 5⃣6⃣ to 6⃣0⃣

Lips dinta ta shafa tareda sakin lallausan murmushi, ta dade sannan barci ya dauketa...
Kasancewar tana Fashin Sallah yasa Ta fada toilet tayi wanka ta fito, dakin ta fara gyarawa ta sa turaren wuta. Palour ta fito shima ta gyara tayi mopping ko ina sannan ta shiga kicin, tsayuwa tayi tana kallan kicin din yau batasan meh zatayi bah na Break. Dan tsaki tayi
"Yauma Za'ayi Break din bah"
Tea kawai ta hada tasha ta koma daki ta shirya ta fito tana sand'a tabar side din...

Bangaren fulani ta nufa da Sallama ta Shiga Falon, yarima ta samu zaune

Please Login or Register in order to submit comment