Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne Ya Baci. Lalai Yarinyan nan na Qorarin qureshi. Wurgi Yayi da Takardan Ya Bar Falon A Fusace... Bai Dawo Gidan Bah Sai Bayan Isha'ai, Yana Shigowa Gidan Yayi Parking Motarshi Ya Fito. Sallau ne Ya Tareshi Yana Mai Sannu da Zuwa, Da Mamaki Yarima Ya Kalleshi
"Meh ka Qara dawowa yi gidan nan??"
Nan da Nan Jikin Sallau yadau Rawa dan Yasan Halin Yarima, Daidai Nan Parveen Itada Atika Sunzo wucewa Zuwa Side Din Fulani, Dan An Aiko Mata Batajin Dadi. Jin Abinda Yariman Ke Cewa Yasa Ta Qarasa Wajan Dasauri
"Ni Nasa Ya Dawo Saboda banga Dalilin Koransh Bah"
Juyawa Yarima Yayi Yana Kallanta Ido Cikin Ido
"Akan Wani Dalili?? Har ni na Kori Wani Banza Talaka Ki Dawo Dashi. Koh Nan Masarautar Ubanki neh"
Ranta Neh Yayi Mugun Baci, Ta kalli sallau Tace
"Jeka Abinka"
Rusunawa Yayi Ya Mata Godiya Yabar Wajan
Atika Na Ganin Yabar Wajan Itama Tai Saurin Barin Wajan..

Kallan Yarima Parveen Tai Ranta Bace, Nan Bah Masarautan Ubana Baneh kamar Yanda Ka Fada, Anma Ka Sani, A Namu Masarautar Ansan Mutumci da Darajan Dan Adam. Kuma Dawowa Ya Dawo Knan, Kai Baka Isa Ka Koreshi Bah. Nunashi Tai da Dan Yatsa, Zan Zauna a Masarautarku Nakuma Fika Iko da Masarautar. Hannu Ya daga Zai Kai Mata Mari Sukaji Muryan Fulani, Qarasowa Wajan Tai Dasauri Tana Kallan Yarima Rai Bace
"Karka Kuskura Hannunka Yakai Kan Kuncinta, idan Kuwa Yakai Ni dakaina Zan Rama Mata. Dama Yarima Dalilin Auren Nata kenan Kaci Mata Mutumci?? Duk Abinda Ke Faruwa a Gidan nan Atika Na Kawomin Labari Sharewa Kawai Nake"

Nagode Sosai Ka Kyauta. Hannun Parveen Taja Suka Bar Wajan. Mutuwan Tsaye Yayi Ya Bisu da Kallo Har Suka Bar Wajan. Dukan Motan Yayi Rai Bace Yabar Wajan, Suna Shiga Side din, Fulani Ta Kalleta
"Ki Cigaba da Hakuri Parveen, Nidai Bazan Rabaku Bah. Nasan Watarana Sai Labari kinji"
Dan Murmushi Parveen Tai Kanta Na Qasa
"Bakomai Fulani, Dama Nazo neh Naga Jikinku. Dazu Atika Take Fadamin Bakida Lapia"
"Naji Sauki, Dama Dan Ciwon Qafa neh Kuma Yayi Sauki"
"Allah Ya Qara Sauki"
Fulani ta Amsa da "Ameen"

Shawarwari Fulani Ta Dinga Bah Parveen Akan Yanda Zatai Hakuri Ta Zauna Da Mijinta, Sun Dade Tana Mata Nasiha Sosai sannan Tai Mata Sallama Tabar Side Din itada Atika. A Falo Suka Tarar da Yarima Kan 1seater Fuskan nan Yayi Jawur, Yayi Crossing Kafa Yanata Kad'a Na Saman, Alamar Ita Yake Jira...

*Kuyi Manage da Wannan Banida Chargi neh dts Y"

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page2⃣4⃣

A Hankali ya sauke wani lallaudan murmushi ya mike yadau wasu files ya fita.
Yarima na fita parveen taima danladi waya yazo ya amsa sakon ya yafi. Kwanciya tai barci ya dauketa dan dama da daddare batasamu barcin kirki bah. Bata tashi ba sai wuraren karfe daya da kusan rabi, Tashi tayi ta fada toilet tai alwala ta Fito. Tana idar da Sallah ta jiyo knocking a kofar Falo, Ta tashi ta fito ta bude. Ihu parveen ta saki Cikeda murna.
dasauri Deeza ta qarso tareda rungume parveen
"Deeza Wannan Suprise??"
Dariya deeza tai Tana Kallan Parveen
Hannunta ta kama suka shiga Ciki, Kan kujera suka baje Parveen na cigaba da mamakin Ziyaran bazatan da Deeza ta kawo mata..

"Bae na dauka zanzo na sameki Kina Amai ai"
Dukan wasa Parveen ta kaimata
"Allah ya kiyaye, keh kina tunanin zan haihu da Yarima neh??"
Girgiza mata kai deeza tai
"Bai kamata kina irin furucin nan ba bae, komin lalacewarshi mijinki neh. Yakamata ki rinka furuci masu kyau akanshi"
Dogon tsaki Parveen tai ta yamutse fuska tareda kauda kai
"Deexa knan, koh kinsan Yarima har neman mata ya..."
Saurin rufe mata baki deeza tai tana Girgiza mata kai
"Sirrinki neh parveen bai kamata kina gayama kowa bah. Nifa laifinki nake gani bae"
Kallanta tai da mamaki
"Kamar ya??"
Gyada kai tayi tana cigaba da kallanta
"Kwarai kuwa, haba bae sai kace ba mace bah. Keh zaki sa ya daina neman mata, look lemme tl uh zaki iya juyashi yanda kikeso kece dai in baki so bah"
Murmushin takaici Parveen tai tadau jakan deeza tana cewa
"I hope wata zakimin"
Bude baki tai da mamaki
"Wata?? Haba dai sai kace mara hankali. Jibi ran sunday insha Allah zan koma"
Tsuke fuska parveen tai
"Haba wasa kike yarinya. Tashi mu shiga Ciki"
Sun dade suna hira har akai Sallan la'asar sannan suka shiga kicin dan daura girki. Suna girkin take bah deeza labarin hanata zuwa schl dinda yarima yayi...

Dariya kawai deeza tai batace komai bah, har abin yaso bah Parveen haushi.
Bayan magrib Yarima ya shigo gidan, Lokacin sun zaune kan dinning suna cin abinci, Jin hayaniya yasa ya qaraso wajan dinning din da sallam, Deeza ce ta amsa tareda gaidashi. Da fara'a ya amsa tareda tambayanta tazo lapia, Ta amsa da lapia lau. Dakinshi ya wuce kai Tsaye. Deeza ta kalleta
"Ya dawo baki kai mai abinci bah"
Tsaki parveen tai ta cigaba dacin Abincinta
"Keh fa matsalata dake knan bae, Bai kamata bah abinda kikeyi. Kada ki biye halinshi ko kin manta maganan da mukai dazu"
Mikewa deezan tai ta shiga kicin ta hado abinci a tray ta ajema parveen a gabanta
"Pls tashi ki kai mai"
Turo baki tayi
"Nifa indai abinda ya kawoki knan gwara gobe da sassafe ki kom gida. Nifa da kika gani bana shiga dakinshi, yanzu idan nakaimai saiya raina ni"
Kafadanta ta dafa
"Bah wani raini bae, Kiyi qoqari ki gyarashi zaki samu lada, ina miki kwadayin ladan da zaki samu nan gaba neh"..

Turo baki parveen tai ta mike tareda daukan Trayn har ta doshi dakin deeza tace
"Ki Tambayeshi akan maganan zuwa gaida fulanin"
Batace komai bah ta qarasa dakin, Bata tsaya knocking ba ta tura qofan ta shiga kai Tsaye. Har ya zame towel dinda ke Jikinshi yana qoqarin sa Kaya ta shigo, Ihu ta Saki Tareda rufe idonta, ta saki trayn ta fita dsauri. Dariya Sosai ta bashi, Kayan Ya qarasa sawa Ya zauna bakin Gadon Yana cigaba da dariya..

Qanqame Deeza tai idonta a rude tana ihu, rufe mata bakin tai Tana jijigata
"What?? Menene??"
Sakin ta tayi ta ruga daki dagudu. Girgiza kai Kawai tayi ta zauna tacigaba dacin abincinta. Gado parveen ta fada tana maida numfashi, Ganin Surar Yarima tayi cikin idonta. Dasauri ta qara rufe ido tana Turo baki. A Hankali ta furta
"Allah ya isa ban yafe bah"
Kwanciyanta tayi tana chating har deeza ta shigo.
"Wai wane irin abu wannan parveen??"
Tashi tayi ta zauna tareda hade rai

"Allah ya isa deeza, kin cuceni Wallahi. Gashi kinsa naje..kasa qarasawa tai ta ja tsaki"
"Nidai yanzu kin tambayeshi maganan Zuwa gaida Fulanin"
"Nifah karki dameni deeza, bazan koma dakin nan bah" cewar Parveen
Tsaki deeza taja ta mike
"Natafi Kallan Players a bollywood"
Wup Parveen ta tashi tana washe baki
"dan Allah dagaske??"
Batace mata komai bah ta bar dakin, itama binta tayi zuwa Falon.


Zama sukai suka soma kallo bah wanda ya qara cewa kowa komai, chan sukaji bude kofar dakinshi, ya fito ya qaraso falon. Parveen ya kalla Fuskan nan a daure
"Hu wil clean up dah mess"
Tsaki taja ta mike dan tasan zai iya dizgata a gaban deeza.
Dakin ta shiga ta soma tattara wajan, tana gamawa ta dawo ta tarar dashi zaune a falon sunata hira da deeza kamar dama sunsan juna.
Guntun tsaki taja tana kallan deeza
"Ni natafi na kwanta"
juyowa tai tana kallanta
"Bazaki tsaya ki qarasa kallan bah??"
Girgiza kai tayi alamar Aa
Harta juya taji muryan Yarima yana cewa
"Tashi to kuzo muje ki gaida fulanin sai naraka ki koh"
Parveen ta qarasa daki ta zauna bakin gado, deeza ta shigo tana kallanta


"Tashi muje pls ya rakamu, kinga ma dare ya soma"
Dakyar ta lallaba parveen ta mike tasa hijabi suka fito. A hanya Deeza da Yarima sai hiransu suke parveen ko ta hade rai tana bayansu suna gaba.. Tare suka shiga side din da yarima, deeza da parveen suka zauna kan Carpet tareda gaida Fulani, Parveen ke fadama Fulani wacece Deeza a wajanta. Ta Taresu dakyau sun dade suna yarima ya fito falo ya zauna yana kallan news, Sai wuraren sha daya suka baro Side din, Kamar dazu hiransu sukaitayi suka barta a baya, Haushi abin ya bata sosai. Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu..

Tho fah kodai Parveen kishi takeπŸ€”??

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page2⃣5⃣

Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu..
Ganin ran parveen ya baci yasa tama Yarima sallama ta shigo dakin. Kayan barci tarar parveen nasawa, ta qarasa ta zauna bakin gadon tana kallanta.
"Lapia?? Naga ranki ya baci"
Aiko kamar jira take tako hayayaqo mata
"Ina ruwanki dashi?? Menene hadinki dashi?? Kin wani barni ni kadai kinata wani washemai Baki waike kuna hira"
Dariya sosai abin yaba deeza, ta dade tana dariya hakan yasa parveen ta qara quluwa. Saida Ta gama Sannan ta Kalleta
"Parveen kishi??, Ana cewa ba'asan yarima anma gashi ana kishinshi"
Tsaki parveen taja tana yamutse fuska
"Allah ya kiyaye nai kishin yarima. I hate him!"
Dan murmushi deeza tai
"Umm zakizo kiban labari"..

Pillow parveen ta wurga mata
"Banasan iskanci deeza, Bakisan yanda na tsani guy din nan baneh"
Shawarwari deeza ta dinga bah Parveen Har barci ya daukesu..

Da Safe suna Kicin yarima ya leqo, Murmushi deeza tamai Sannan tace
"Morning"
Morning shima Yace Yana Kallan Parveen, Fuskanshi bah yabo bah Fallasa Yace
"Haba Amarya bah Gaisuwa"
Dagowa tai ta kalleshi da mamaki
Gira ya daga mata, tai saurin kauda kai tareda hade Rai
"Good Morning"
Kintashi Lapia??" chewar yarima
Batareda ta kalleshi bah tace
"Lapia"
Deeza ya kalla Yana yar murmushi
"Frnd idan kun Gama ki Shirya xan kaiki yawo tunda yau saturday"
Murmushi tai tana Kallanshi
"Thank you very much Frnd"
Baice komai bah Yabar Kicin din.
Tsalle Deeza tai Tana cewa
"Woaw! Kamar yasan abinda nakeso knan, Allah yarima nada kirki. Kece dai baki gane hakan bah"
Dogon tsaki Parveen taja tacigaba da abinda takeyi.
Murmushi Deeza tai tareda girgixa kai..

Suna Gamawa Deeza ta shirya Ta Kalli Parveen, pls ki tashi muje. Mugun Kallo ta bita dashi tareda jan tsaki
"Bah inda zani, keh dai da kike uwar yawo sai kin dawo"
Bah Yanda Deeza bataiba Akan Parveen tabisu taqi, Hakana ta haqura suka Fita itada Yariman. Yawo yakaita Sosai, Sun jaje wurare dayawa, dan Zaman da Yayi da Deeza ya samu Labarin parveen sosai da Halayenta. Basu dawo gidan bah Sai Qarfe tara na dare, kwance suka samu parveen kan 3seater har ta soma barci. Dagudu deexa ta qarasa inda Parveen take tai tsalle ta fada kanta..

Ihu ta saki tareda tureta, Dariya Sosai Abin yaba yarima yabar Wajan zuwa daki yana cigaba da dariya
"Yarinya sai Rashin kunya ga shegen Tsoro"
Tsarabanta Deeza ta bata, taqi amsa, saida tace mata da kudinta ta siyan mata sannan ta amsa tana dubawa. Abinci ta hada takai mai daki, Wannan karan knocking tai, saida Ya bata izini Sannan ta shiga, Gabanshi ta ajiye Ta juya zata Fita. Muryanshi ta jiyo yana cewa
"Were are you going bayan mijinki na buqatarki a kusa dashi"
Qarasawa tai Zata bude kofan taji yace
"Haba Mallama uwar Malamai, Koh kin manta Malaiku na Tsinewa Macen da ta qauracewa Shinfidar mijinta"
Juyowa tai tana Kallanshi gabanta na dukan uku uku
"Nibah Malama bace, Har yanzu ni daluba ce. Bana tutuiya da ilimin danake dshi, bah kamar kai da kake iqirarin wani bazai iya karatun dakayi bah."
Murnushi Yayi yana Kallanta
"Bah Wannan na tambayeki bah"
Tsaki taja tana kallanshi ido cikin ido
"Kada ka Taba Tunanin taraiya dani a rayuwarka, Allah ya kiyaye. Mutumin da yagama zina da matan arna yace yanzu kaizo gareni, Allah ya kiyaye"
Bata jira mai zaice bah tabar dakin dasauri..

Murmushi kawai yayi tareda girgiza kai, Baisan meyasa bah yanzu sam Maganganun Yarinyan basa batamai rai, Saima burgeshi datake Yanda take tsayawa a gabanshi tana fadamai maganan da ranta yake so. Kofan ya kalla tareda yin kwafa ya koma ya zauna...

Washe gari deeza zata koma, Sam Parveen bataso haka bah. Tun da safe take qunci, Taso ace ta Qara mata koda kwana biyu neh anma Taqi, Hakanan ta Haqura. Da zata tafi parveen harda dan kukanta, Side din fulani ta rakata tai mata Sallama suka fito. Taso raka Aminiyar nata anma jin Yarima neh zai kaita Airport yasa Ta Fasa sukai Sallama tashiga motan suka tafi..

Side dinsu ta koma Cikeda kewar aminiyar nata, Yarima na kaita tasha Ya juyo ya Wuce Gidansu Mahdi. Yakoci Sa'a Yana Gida, Hira sosai suka shiga yi har suka gangaro kan maganan Parveen
"Yadai mutumina Ina fata komai ya wakana"
Girgiza kai Yarima yayi
"Bbu komai mutumina Wallahi, ni Har mamakin kaina nakeyi. Narasa yanda zan tari yarinyan nan, tanamin kwarjinin dayawa"
Dariya Mahdi Yayi
"Haba Yarima bansanka da Tsoro bah, yanzu kasan meh za'ayi??"
Girgiza kai Yarima yayi kallanshi
Tashi mahdi yayi ya qaraso inda yarima keh zaune, magana yamai a kunne wanda ni kaina bansan meh ya fadamai bah.
Kallanshu Yarima yayi
"Are you sure hakan zaiyi?"
Gyada kai mahdi Yayi
"Kwarai kuwa mai zai hana"
Sun dan jima Suna hira Sannan yarima yamai Sallama yabar Gidan...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page 3⃣6⃣to 4⃣0⃣

A wani bangareb kuma gabanta neh ya fara faduwa, kada yauma ya hanata zuwa school gashi yau tanada test. A hankali ta juyo suka hada ido, Cikin sanyayar murya yace

"Were are you going?? I hope ba school bah kinsan baki gama warwarewa bah"

Saida ya gama maganan ya farajin haushin kanshi, dan Tsuke fuska Yayi yana kallanta

Parveen tsintan kanta tayi dayimai shagwaba
"Dan Allah kai haquri kaga fah Ran friday banje bah, jiya ma banje bah kuma yau munada test"
Dan murmushi yayi
"Shiknan"
ya mike yadau jakan Laptop dinshi yana kallanta
"Muje Tho Sai nayi droping dinki"

Bataso hakanba Anma ta kasa musamai, har sun nufi wajan dazai dauki mota ta dan kalleshi qasa qasa
"Every morning ina zuwa ina gaida fulani da Mai martaba"
Maganan datai yabash kunya, aje Jakan yayi cikin motan Sannan yace
"Muje tho"

Fulani tayi farinciki sosai yanda tagansu sun shigo gaidata tare, Sannu taima Parveen. Yarima ya kalli agogon hannunshi
"Fulani zamuje mu gaida Mai martaba kuma patient na jirana, Gashi saina tsaya nayi droping dinta sannan na wuce. Ki bari idan ta dawo sai kuyi hiran"

Saurin miqewa Yarima yayi itama parveen ta mike sukaima Fulani sallama suka bar side din..

Mai martaba yaji dadi sosai shima yanda ya gansu, duk da shi baisan akwai wani qulaliya a tsakaninsu bah. Suna fitowa Suka hau motan yayi reverse yabar gidan a guje, tafe suke akan hanya bah wanda yacema wani uffan har suka qaraso makaranta. Droping dinta yayi ya juya har zai wuce ya dawo
"Qarfe nawa zaki gama?"
Jim tayi kamar bazatai magana bah chan kuma tace
"Karfe hudu"
Kai ya gyada yaja motar yabar wajan dasauri..

Bin motan dakallo tayi, a ranta tana tunanin anya Yarima neh kuwa??
Kodai akwai wani boyayen manufa neh dayake dashi a kanta. Jitai an dafata ko bata juyaba tasan yasmeen ce. Dan murmushi tai batareda ta juyaba
"Yasmeen!"
Dariya yasmeen tai
"Ashe kin gane nine. Yau naga oga neh dakanshi ya kawoki"
Juyowa parveen tai da mamaki

"Kinsanshi neh"
Murmushi yasmeen tai tareda kamo hannun parveen suka fara tafiya
"Duk garin nan waye baisan Yarima fardeen bah?? Sai da'i da'i. Yanada farinjinin Yan mata, zakiga kowacce mace na qoqarin ace ya santa"
Hakanan Parveen taji ranta ya baci, ta dake tana kallan yasmeen da sigar wasa
"Oh! Harda keh knan"
Murmushin takaici tayi tareda kauda kai
"Kwarai kuwa, bazan miki qarya bah parveen. Anma ki bari mu gama lectures zan baki wani labari"
"Tho kawai parveen tace suka qarasa Class...

Ana Fitowa parveen taja Hannun Yasmeen suka qarasa wani waje suka zauna. Ta kalleta Tana Yar murmushi
"Labarin da kikace zaki bani nakeson ji"
Dan dariya ysmeen tai
"Ashe haka kikeda son gulma??"
Maganana Yasmeen dariya yaba parveen sosai, ta dade tana dariya. Saida ta tsagaita Sannan Tace
"Pls Yasmeen keh nake saurarao..

Nan da nan idon Yasmeen ya ciko da kwalla ta kalli Parveen
"Ni ban daukeki a matsayin qawa bah, na daukeki a matsayin aminiyata kuma yar uwata wacce zata iya riqemin sirrina."
Hawayen dake maqale a idonta ya zube tayi saurin sharewa, tadanyi murnushi tana kallan Parveen
"Na Kasance Marainiya ce ni, mahaifiyata tana haihuwana ta Rasu. Ni kadaice banida Yanni wanda muka fito ciki daya dasu. Na tash hannun kishiyar mahaifiyata, Banji dadi a hannunta bah tun ina qarama har zuwa sanda na fara secondary school"

Wasu zafafafn hawaye suka gangaro mata
"Mahaifina mai hali neh, munada Yan aiki burjik a cikin gidan mu. Anma Hakanan Kishiyar mahaifiyata kan hana yan aikin gidan yin aikinsu Nice keyin komai. Kasancewar inason nazama Likita yasa Duk Rana duk ruwa nakanyi qoqari naje makaranta dan banaso wannan damar ta wuceni"

"Wata Ranar lahadi da bazan manta da itaba a tarihin Rayuwata, lokacin ina Ss2 kishiyar mahaifiyata Ta tasoni da daddare har nafara barci, Wasu kaya tabani tace nakaima Qawarta dake chan qasan gidan mu. Bah dare baneh sosai dan zai kai qarfe tara zuwa tara da kwata, bah musu na dauka dan nasan idan naqi duka zansha a wajanta. Gashi qasan wajan duhu neh bah wani haske kuma taqi bani torchlight...

Hakanan nadau hijabina na dau hanyar gidan data aikeni, tafiya kawai nake bansan inda nakesa qafana bah, har nayi nisa najiyo muryan wasu a bayana Suna Kirana"

Ban juyaba na cigaba da tafiya nah, Chan naji an jamin hijabi wanda hakan yasa nayi baya kamar zan fadi, Wasu maza nagani wanda bansan koh suwaye bah saboda rashin wadataccen Haske a wajan. Daya daga cikinsu dake chan gefe yace
"Ku dauko min ita"
Ina jin haka na fara kwarma ihu a wajan, Anma shiru babu wanda ya fito kuma kar kice bah gidaje, akwai gidaje sosai a wajan..

Kuka neh ya kufce mata, Parveen da itama Hawaye ke bin kuncinta ta rike kafadanta tana Lallashinta, Saida ta Tsagaidata Sannan Ta cigaba
"Haka inaji ina gani Suka Rabani da pride dina, Ana Cikin Allah ya jehomin Yarima dayazo wucewa da Motarshi shida dogaranshi"...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page 2⃣6⃣ to 3⃣0⃣

Sun dan jima suna hira sannan yarima yamai sallama yabar gidan. Gida ya wuce direct, yana parking mota suka hadu da bilal, Qarasowa inda yarima yake yayi yana yar fara'a
"Ango Ango, Koda yake yanzu kai bah ango baneh wata biyu fah"
Dan murmushi kawai yarima yayi
"Yaushe a gari??"
"Wallahi jiya daddare" Cewar Bilal
"Tho ya Service din"
suman kanshi ya Shafa
"Service Alhamdulillah. Anma akwai wahala wallahi"
Murmushi Yarima yayi
"Tho dama dan dadi ake zuwa?? Ni kaga barin je fada yau achan zan wuni"
Da Mamaki bilal ya kalleshi
"Iyeh! Yaushe ka fara zaman fada?? Lallai yanzu na yarda kayi aure ka chanza"
Dukan wasa yarima yakaima bilal yayi saurin gocewa yana dariya...

Bai shiga side dinsu ba sai bayan isha, Bai ganta a falo bah sannan bah komai kan dinning, dakinshi ya Wuce Yayi kwanciyansh. Jin yunwa na naiman mai lahani yasa ya mike ya fito, Kicin din ya shiga ya hado coffee ya fito. Kujeran dinning yaja ya zauna, Yana gama sha ya mike ya koma dakinshi..

Washe gari da safe karfe bakwai da rabi ya fito, yau ma kamar jiya bah komai kan dinning din. Guntun Tsaki yaja ya fita ya wuce office, yau kasancewar an samu sababin doctors qarfe hudu yabar Asibiti ya wuce Gida, Falon ya shiga da sallama, baiko kalli kan dinning din bah ya wuce daki. Fadawa yayi kan gado yayi ruf da ciki, Runtse idonshi yayi, saboda yanda yaji maranshi na Juyamai. Dakyar ya iya tashi ya fada toilet ya sakar ma kanshi Shower, Ya dade a toilet din Sannan Ya fito. Kwanciya yayi nan da nan barci mai nauyi ya daukeshi...

Bai tashi bah sai bayan magrib, shima dalilin tashin Wayanshi neh dayaji yana Ringing, dakyar ya miqa hannu ya janyo wajan. Sunan Fulani ya gani yana yawo jikin screen din, ya dauka tareda karawa a kunne yace
"Hello"
Daga Chan bangaren Fulani tace
"Yarima yadai lapia kuke koh??, jiya ban qara ganin Parveen bah kuma naji mai martaba na tambayanta wai jiya baiga Abinci bah"
Jim yarima yayi yana tunanin qaryan da zaiyi, chan ya dake yace
"Batadan jin dadi neh jiyan shi yasa, anma dasauqi"
"Allah ya Qara sauki, ina fata ka dubata"
Eh kawai yarima yace
"Koh shiyasa banga wucewanta makaranta bah yau"
Nan mah eh kawai Yace Yana wani muzurai
Sallama tamai tareda cewa
"Anjima ina nan zuwa Gaisheta"
Tho yace Ya mata sallama ya kashe kiran...

A Dari da tamanin ya sauko daga kan gadon, Toilet ya fada ya sake Wanka tareda alwala ya fito. Saida Yayi sallan Magriba Sannan ya Mike Ya nufi dakin Parveen.
Knocing Yayi yaji Shiru, chan ya qara yi nan ma Shigo. Tsaki yaja danshi bai saba jira bah ya murda kofan dakin ya shiga, bin dakin ya somayi da Kallo. Chan Saman gado ya hangota ta qudundune cikin bargo sai rawar sanyi take, A hankali ya qarasa bakin gadon ganin ta rufe har fuskanta yasa yakai hannunshi kan Bargon ya yaye..

Idonta a rufe haqoranta sai karo suke da Juna, dagota yayi dasauri yana taba Goshinta. Muryanshi chan kasa yace
"Whats wrong? Meke Damunki??"
Bata iya cemai komai bah sai hawaye dake gangarowa ta gefen idonta. Qara Riketa Yayi ya Taba goshinta da Wuyanta, baice komai bah ya ajeta ya feta dasauri. Chan sai Gashi da Wasu pills ya Aje ya koma Ya hado mata tea da ruwa Ya Kawo, Jinginata yayi jikin gadon. Tean Ya mikamata
"Amsa kisha"
Girgiza kai tayi hawaye na cigaba da gangarowa daga idonta
Tsintan kanshi yayi da Lallabata, ita kanta abin ya bata mamaki har tadan bude ido ta kalleshi. Dakyar yasamu tasha kadan Sannan ya balli pills din ya dau ruwa ya mika mata. Bata fuska tayi ta kauda kai gefe..

Murya chan qasa Yace
"Kisha zaisa kiji sauki"
Batacemai komai bah kuma bata amsa maganin bah. Zama yayi kan gadon yana kallanta
"Take it pls, saiki kwanta kisamu barci kinji"
Dan dagowa tayi ta kalleshi, ganin yanda yadan damu yasa ta amsa maganin tasa a baki ta kora ruwa, dakyar ta hadiye tana yamutse fuska.
Murmushi yayi mata, tai saurin kauda kai. Zamewa tai ta kwanta shikuma ya mike ya gyara mata blanket din yabar dakin..

Side din Fulani ya Nufa, Zaune ya sameta tana Kallo kuyangarta na matsa mata qafa. Zama yayi kan kujera Yana kallan fulanin, Cikin sigar wasa Yace
"Fulani kedai bakya gajiya da Matsa qafa"
Dan dariya tai
"Kasan Abinka da tsohuwa"
Tsuke Fuskq yayi
"Haba dai, ai baki tsufa bah."
Kuyangarta ta kalla murya chan kasa
"Tashi kije zan nemeki"
Toh tace ta mike tabar wajan...

Fulani ta gyara zama tana kallanshi
"Aiko ni tsohuwa ce tunda gashi na kusa aje jika"
Kallanta yayi da mamaki
"Aina Kuma kika samu jika??"
Hararanshi tai cikin sigar wasa
"Ah Yaronda Zaku haifamun mana koh ba jikana baneh"
Dariya sosai ta bashi, Ya dade yana dariya Itako sai kallanshi take da mamaki.
Saida ya tsagaita Yace
"Nifah Fulani bah wannan baneh ya kawoni"
Gintse fuska tayi
"Tho meya kawoka??"
Kinsan Batada lapia, tho wallahi yau bamuci komai bah
Zaro ido fulani tayi tana kallanshi
"Bataci abinci bah?? Haba Yarima kafasan mace mai juna biyu na buqatar abinci sosai, meyasa baka fadaba tuntuni"
Mikewa Tai tabar falon dsauri
Shiko Yarima binta yayi da kallo mamaki qarara a fuskarshi. Tashi yayi yabar falon ya koma Side dinsu dan hankalinshi nachan wajan Parveen...

Tho Fah kunji Fulani da Wani batu..

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Page 3⃣1⃣to 3⃣5⃣

Tashi yayi yabar falon ya koma side dinsu dan hankalinshi nachan wajan parveen. Yana shiga dakinta ya wuce direct, murdawa yayi ya shiga a hankali, kwance ya sameta tana barci. Ajiyan zuciya yayi yana cigaba da kallanta, yakai kusan minti goma a haka. Ganin ta motsa yasa ya bar dakin dasauri tareda jawo mata kofa..

Zama yayi kan kujera, mamakin kamshi yake yanda akai ya sauya kwana biyu, shidai yasan bah santa yake bah. Tausayinta kawai yake musamman yanzu da batada lapia, sai kuma tsananin Sha'awanta dake hanashi barci kullum. Yana nan zaune Akai knocking kofan falon, mikewa yayi a tunaninahi Abincin Fulani ta aiko, ganin budurwarshi Juliet yayi tsaye tanamai murmushi. Tsaki yaja ya hade rai yana kallanta...

"What dah hell are you doing here"
Marairaice Fuska tayi ta langwabar dakai
"Why prince! Why are you doing dis to mie??, I love uh so much I cnt t..."
Saurin katseta yayi ranshi bace
"Leave here before I show you my tru color"
Idonta ya Ciko da kwalla tana qoqarin magana kulle kofan da qarfi ya barta nan tsaye. Tsaki yayi ya koma ya zauna rai bace, knocing kofan akaitayi yayi banza, Ganin taqi daina buga kofan yasa ya tashi Ranshi bace ya bude kofan...

Kuyangin

Please Login or Register in order to submit comment