Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka mika lamuranmu gareka, bamuyi tunanin akwai abinda zai gagare ka ba a duniyar nan, don haka idan kungiya tayi ma madam sailuba haka ba a kyauta mata ba, duba da matsayinta na mai jiran gado, sannan tayi sadaukarwa da yawa tun tana teenager, don haka muna ganin a duba wannan Lamari, nagode". Ta karashe magana tana mai zama.



Girgiza kai shugaban yayi tare da tambayar" akwai mai magana?".



Wani tsamurarran bafulatani ne ya tashi tare da fadin" ina ganin abunda shugaba ya fadi yayi gaskiya, don littafin nan namu ba karamin power gareshi ba, don haka bai kamata abar madam ba, ko da ma za a barta, sai dai ta sauka daga kan mukaminta tabama masu jira".




Nan ma hayaniya ce ta kuma tashi, yayyin da suka kashi gida biyu, yayin da bangare daya suke goyon bayan a sauke hajiya sailuba, dayan kuma suna goyon ba barinta.




Wata tsawa shugaban yayi, wanda bakinshi har tattatsin wuta yake fitarwa, gaba dayansu suka yi tsit, yayin da suke jefawa juna kallon banza.




Gyaran murya yayi tare da cewa" hukuncin da zan zartar bayana nufin madam tabar kungiya bane, kawai zamu karbi duk abunda yake hannunta wanda ya jibanci kungiya, yayin da zamu yi amfani da power dinmu wurin taimakonta daga wurin wadan can mutanen" yana gama fadin haka yabar wurin, yayin da wata guguwa tazo ta kewaye hajiya sailuba wacce take zaune kamar gunki.


*Wacece hajiya sailuba?*

Haifaffiyar garin kano ce, a cikin unguwar galadanci, iyayenta suna da dukiya dai² gwargwado, asalin mahaifinta Alhaji Aminu dan cikin garin bichi, inda aiki ya kawo shi garin kano, anan ya hadu da mahaifiyarta Hajiya Asiya, wacce suke zaune da iyayenta a fagge, soyayyace mai karfi ta shiga tsakaninsu, inda cikin kankanin lokaci a ka daura musu aure ya tare a gidansa daya gina a galadanci.




Sailuba ita kadai suka haifa, kasncewarta ita kadai yasa suka dauki son duniya suka daura mata, basu kaunar abunda zai tabata ko kadan, tayi makarantar primary a nan kano, inda ta wuce secondary zuwa girls college dake marabar kubau,wanda anan ta fara shiga kungiyar asiri ta black mafiaans ta dalilin wata kawarta bakatafiya, anan ta sadaukar da mahaifiyarta ba tare da shayin komai ba, kasancewa sadaukarwarka ta farko a kungiya, shine ka bayar da wanda kafi so a rayuwarka.



Daga nan kuma sai aka ci gaba da bata assignment kamar sadaukar da 'yan mata virgin zuwa jarirai, sannan da kawo ma kungiya sababbun members.



A haka har ta yi candy, inda ta samu admission a A.b.u zaria da taimakon kungiya kasancewa kwakwalwar ta kamar dusa take, don kwata² bata gane karatu, hakan yasa kungiya sukayi siddabarun su aka bata admission acewarsu anan ma zata samo musu jama'a, hakan ce ta kasance don ta janyo musu mutane da yawa hakanne yasa har aka bata shugabanci.




Tana level 3 ta hadu da Alhaji sulaiman ,a lokacin shi kuma yana masters, tun daya ganta Allah ya daura masa sonta tare da sha'awar aurenta a mata ta biyu( kasancewar yana da mata da yaro daya a lokacin), ko da ya tunkareta da kokon baransa sai ta amince masa, cikin kankanin lokaci soyayya ta kullu tsakaninsu, wanda ko da wasa sailuba bata bashi hanyar sanin wani abu mara kyau daga gareta, kasance wa mace ce wacce ta iya takunta baka gane farinta balle bakinta.



Suleiman cikakken bazazzagi ne,wanda yayi karatunsa tun daga primary har degree dinsa a garin zaria, auren gida aka masa da matarsa, wacce babu wata soyayya a tsakaninsu.



Ba tare da daukan tsawon lokaci ba, aka daura aurensu, inda ya tare da ita a sabon gidanshi da ya gina a kaduna, yayin da yabar uwargidanshi a zaria, watansu biyu da aure ta sadaukar da danshi ga kungiya, inda kuma ta mantar da suleiman matarshi gaba daya.



Cikin shekara daya ta haifi danta Najib, wanda daga nan kuma ta bayar da mahaifarta ga kungiya, wanda aka bata mukamin mataimaikiyar shugaban kungiyar, a wannan shekaran ne kuma suleiman ya shiga siyasa, wanda da taimakon sailuba yayi ta samun daukaka har zuwa matakin sanata.



Ya rasu sanadiyar hatsarin mota, inda da shige² har hajiya sailuba ta samu mukamin mai ba ma shugaban kasa shawara.




*Pls manage.*



*Nayi kokarin kammala littafinnan kafin sallah, amma hakan bai yiwu ba, don haka ina ba ma masoyan littafin nan hakuri zuwa bayan sallah.*


*Ayi sallah lafiya.*



*Comment*
*Follow*
*Share*


*Fateeyzah*✍

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

_Ina mika gaisuwar sallah gareku, da fatan anyi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana, ina nan ina jiran naman sallata dani da Doctor zahrah._


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 111 to 115_*



Tun da Alhaji suleiman ya rasu, tayi bake² akan dukiyarsa, babu mai ci daga ita sai najeeb, acewarta su kadai ne magadansa.


Sai dai Allah ya jarabci Hajiya Sailuba da masifar son Najeeb, bata kaunar abunda zai taba shi komin kankaninshi, wannan dalilin yasa take neman shugabanci a kungiyarsu, domin kariya gare shi, don tasan ko mu jima, ko mu dade wata rana kungiya sai ta nemi jininshi, hakan yasa ta yanke solution ta yadda kungiyar zata dawo hannunta.

Duk wannan tunanin tana yinshine yayin da take zagaye a tafkekan bedroom dinta, wanda zamu iya kiransa, Aljannar duniya tsayawa tsegun ta muku bata lokacine, wani irin sumbatu take yi wanda baka gane mai take cewa, sai tayi² sai ta saki tsaki.


**********************************

Wayewar garin Ranar, gaba daya matan gidan sun tashi da hidimar daura sanwa, kasancewa za a gabatar da taron da aka dauki tsawon shekara goma baa tare da an yishi.


Bangarensu Zahra kuwa duk sunsha wanka sun sha kwalliya( da kayan jiya🤪🤪), yayin da suke Cikin nishadi, karma uwar gayya taji zahrah wacce iyanxu ta warware.


Karfe tara gida ya fara cika da 'yan gidan na nesa dana kusa, wanda duk kusan jikokin gidanne, manyan tabarmi aka shimfida a tsakar gidan bayan an share wurin, yayin da karfe goma kowa na zaune a wurinnan, sai dai mutum daya da bayanan wato Yaya Abdul.

***
Sanye take cikin bakar abaya, yayin data yane kanta da bakin gyalle, sai dai fuskarnan tata ta kumbura hade da idanunta ta yanda kallo daya zaka mata kasan ta kwana kuka, gefenta mama ce dake sanye da Atamparta kirar chiganvy wacce aka mata dinki riga da zani, yayin da fuskarta ke dauke da damuwa, kulle gidan suka yi sanna suka tsare mai napep din da zai kaisu motor park domin hawa motar kagarko, ko da suka isa, mutum biyu ta rage motar ta cika, aikuwa cikin kankanin lokaci motarsu ta tashi ta lula titi, *save journey huwailat and mama😍*



***************************

Ganin har lokacin yaya Abdul bai karaso ba, sannan an kira wayarshi a kashe yasa Baba Mahmood cewa a fara taron, wanda dukkansu suka yadda da shawararshi, nan dai aka umurci Baba Abubakar ya bude taro da Addu'a.



Gyaren murya Baffa Yayi tare da cewa" Dalilin taron gaggawar mun yi shine saboda Zahrah da usman, wanda na dade ina tunanin mai yasa basu jituwa, wanda ko da yaushe suka hadu fada ne kamar masu ganin hanjin juna, kwata² Usman bai kama girmanshi da matsayinshi na uba a wurin zahrah ba yayin da ita ma bata bashi Wannan girman, ( ya dan tsagaita tare da sauke numfashi sannan yace) sai dai kwanaki zahrah tazo mana da wata magana wanda kalilan cikinku ne suka son da ita, rashin gamshashiyar sheda yasa na kasa bayyanar da maganar balle mu tambayi shi usman, sai dai kuma jiya , zahrah ta kuma fadin wata magana ta yanda ya kamata mu duba mu gani" yana kai karshen zancenshi gaba daya mutanen wurin dau hayaniya tare da maida kallonsu zuwa ga zahrah da Baba Usman kasancewa tabarma daya aka shimfida musu, a wurin da kowa zai iya ganinsu.



Sai da hayaniyarsu tayi kasa sannan Baffa ya maida kallonsa ga zahrah tare da cewa" Zahra'u ina son ki maimaita maganar da kika fadi jiya tare da hujjojinki ko shedarki tace wa haka".


Ba tare da fargabar ko jin nauyin kowa ba ta fara rattafa bayani kamar haka"Huwailat Aminiyata ce wacce muka hadu a makaranta a kasar India, kasancewa kasarmu da jahar mu daya yasa muka shaku sosai, muna bala'in nuna ma junanmu so, a inda abun ya fara shine, munje Asibitin cikin makaranta test din jini wanda makaranta ta bukace sababbun dalibai irinmu suyi, bayan an dibi jinin mu muka tsaya jiran sakamako, sai ya kasance gab da zamu karbi sakamakon huwailat ta zaga bayi(toilet), ko da ya kawo mana batanan anan yake tambaya amma mu 'yan uwan juna ne, yayin dana bashi amsa da A'ah, sai yake fada mini mu bincika muna da dangantaka saboda jininmu ya zo daya, murmushi kawai na masa tare da karbar result din na shashantar da maganan don a tunanina ba yanda za ayi haka ta kasance, haka dai muka ci gaba da karatunmu yayin da ko maganar ban sanar ma huwailat ba. A shekaranmu ta biyu ne bayan mun dawo hutu na kai mata ziyara, ko da na isa gidansu na tarar suna kwalima, bayan mun gaisa, nima na shiga tayasu, nan mahaifiyarta ta fito da wasu takardu take cemun in duba mata masu muhimmanci in cire mata sauran kuma in mika ma huwailat ta kona, anan naci karo da wata wasika wacce ta hargitsa mun kwakwalwa, da farko nayi tunanin Daddy ne ya rubuta ta saboda ganin irin rubutunshi da na gani, sai daga karshe da naga an rubuta sergeant Usman Abdulrahman Kagarko, wacce takarda ke dauke da jan kunne ga mahaifiyar Huwailat akan ta zubar da cikin nan, in kuma ba haka ba, ta nemi uban danta ko 'yarta saboda kar ta sake ta zo wirinshi, ba karamin tashin hankali na shiga ba, yayin da cikin dabara na soke wasikar tare da sanar ma huwailat ana nema na a gida, haka dai ta rako ni na hau motata nayo gida, ko da nazo gida ko dakin mummy ban leka ba na shige dakina, fadawa kogin tunani nayi, don take maganar mutumin nan mai awon jini ya fado min arai, sai dai wani sashi na zuciyata na karyata abun, akan sunan ne yazo daya, haka dai nayi ta yawo da zancen a zuciyata har na sati daya, ganin na kasa cireshi a raina ne yasa na kira kawata da suke kayi daya da huwailat wato *ZUHURA (YAKIN MATA, novel dina na gaba)*, na tambayeta bayani a kan huwailat, anan take sanar da ni itama abunda taji iyayensu na fadi akan huwailat ba 'yar malam Adamu ne ba, 'yar wani soja ce, wanda a yawon siyasa Hajiya Asabe ta samo cikinta, sannan kuma ba Kowa bace ta fadi haka sai Hajiya Gaje wacce Aminiyar Hajiya Asabe ce, kuma sanadiyar wani fada da suka yine ta fasa wannan kwan, A lokacin na tabbatar da Huwailat 'yar Baba Usman ne, sai dai ina bukatar muhimmiyar sheda, a ranar na kuma komawa Gidansu Huwailat, inda nayi dabara na samu gashin kanta, kasancewa ta taje gashin ta barshi a jikin comb, washegari na zo nan kagarko, na samu shagon da kake aski, na biya sa kudi akan ya saman mun gashin kanka, da kuma na karaso nan gida na samu ana ma 'yarka Husna kitso, itama nan nayi dabarar da na sami gashinta, sati biyu tsakani nazo na karbi gashinka da a ka saman mun, sannan na wuce dasu wani private hospital aka bincikamin, aka tabbatar mun da huwailat 'yar kace, na yanke shawarar samunka da maganar sai dai kuma a wannan lokacin aka fara rikicin Auren Daddy da Aunty Ni'ima da kuma jikin Mummy da yayi tsanani, wanda hakan yasa na manta da batun, ban kuma kawoshi a raina ba balle in fada ma wani sai case din da muka fara kwanannan nida Huwailat , wanda bacin da raina yayi yasa na fada mata, kaima kuma zagin daka mun jiya yasa na fasa zancen a gaban kowa" ta karasa magana tana mai sharce gumi, duk da iskar hantsin dake kadata.

Gaba daya wurin suka dauki salati yayin da matar Baba Usman da 'ya'yanshi manya suke ta cika suna batsewa, shiko uban gayyar zufa kawai ke keto masa, ga hawaye dake zuba a idonshi.


Cikin Bacin Rai Dada Ladiyo ta daka masa tsawa tare da fadin"kai manu mai ye gaskiyar lamari?" Shiru yayi mata, ganin baida niyyar amsata tace " wallahi ko ka bude baki ka yi magana, ko kuma ince Nono na dakasha ban yafe ma ba" ta karasa magana tana mai zubar da kwalla.


Jin zancen Dada yasa hankalinsa ya kuma tashi, cikin jarumta irin na soja ya tattaro gaba daya natsuwarsa tare da fadin" Tabbas haka ya faru tsakanina da Asabe a wurin campaign din Senator Suleiman, sai dai ta fada mini tana da ciki, inda na tura mata wasika akan ta zubar dashi, kuma ina da yakinin wasikar Zahrah ta gani", gaba daya wurin suka dauki salati kowa na fadin albarkacin bakinsa, yayin da wasu ke zubar da hawaye, matarshi ko barin wurin tayi cikin sauri ta shige daki, yayin da Dada Ladiyo ta nufeshi zani a hannu ta fara kwasa masa mari tana kuka, tana surutai, uwar gayya ko Zahrah ko a jikinta, don jin ranta tayi fes.

Ganin basu da niyar yin shiru kuma ga Baffa yana son magana, yasa Baba Mahmood buga dan wani karfe dake kusa dashi, hakan yasa duk suka yi tsit sai dai tashin maganganu da koke² da kake ji kasa², Baba Abubakar kuwa, Dada ya nufa ya ruko ta ya zaunar da ita kusa dashi.


Cikin bacin rai Baffa ya fara magana" Hakika Usman baka kyauta ma zuri'armu ba, wannan wani irin sakaci kayi da tarbiyar da aka baka a gidan nan har ya kai ka kayi zina da matar aure, Da kana tunanin Asirinka ya rufune, sai gashi yanxu wacce ke matsayin 'yarka ita ta tono abunda ka rufe lokacin da girma ya kamaka, ina zakaje da kunyar mahaliccinka, gata mata, 'ya'ya, surikai, jikoki ga kuma tamu da sauran 'yan uwanka, tun wuri ina baka shawarar ka tuba zuwa ga Allah, sannan kaje ka nemo 'yarka ka nemi yafiyarta saboda haifota da kukayi ta hanyar zina, bayan nan kuma ka roki yafiyar zahrah duk da tsanar da kamata, data hako abunda ka shuka bata fallatsaka a duniya ba har sai da ta kaika bango".

Ba abunda yake yi sai zubar da hawaye, yayin da wata nadama da kunya suka lullubesa.


A wannan lokacin suka ji ana bugun gida, kasancewa kulle gidan sukayi da zasu fara taron, zahrah ce tayi karfin halin mikewa ta nufi kofar ta bude, cikin mamaki take kallon huwailat da Hajiya Asabe da fuskarsu ke tsuke kamar wadanda aka aiko ma sakon mutuwa, ganin tayi shiru, sannan ta tare hanyar shiga yasa huwailat fadin" Bamu wuri mu wuce", murmushin yake zahrah tayi sannan ta juya ta bar wurin, harara huwailat ta raka ta dashi sannan tabi bayanta, yayin da Mama Asabe ita ma ta bi baya _( hohoho huwailat🤔🤔🤔, halin dai yana nan, ina tausaya miki wallahi, don zahrah ba tsaranki bace😏😏😏)_.


Ganin shigowarsu yasa gaba daya ido ya dawo kansu , yayin da zahrah ta dan yi yake sannan tace" Baffa ga huwailat da mahaifiyarta" nan fa wuri ya dauki hayaniya, yayin da Baba Usman ya dago kanshi, karaf suka hada ido Mama Asabe, yayin da jin hayaniyar su yasa matarshi ta fito daga daki, nan kuma ido ya koma kanta kowa naso yaga abunda zata aikata, don an santa da again kishi, a dai dai lokacin kuma Yaya Abdul yayi sallama cikin husky voice dinshi, hannunshi dauke da wata beauty girl mai kama da zahrah, bayanshi kuma Aunty Ni'ima ce rike da hannun wani fine boy mai kama da Yaya Abdul, bayanta kuma Daddyn Zahrah ne, ganinsu fa yasa gida ya kuma kacamewa yayin da yawanci suke neman wurin boyo, suna ihu ga fatalwa.


***********************

Zumbur ta mike tare da cewa " shikenan sun watsa min shiri, sun karya min lakani na shiga uku ni sailuba, wannan wasu irin matsiyatan dangine". Ta karasa magana tana mai buga cinya tare da kewaye tsararren Parlourn ta, dai² nan Najib ya fito daga wani daki dake cikin fadi tare da fadin" mummy lafiya naji kina wadansu maganganu", kallonsa tayi cikin tashin hankali tare da fadin " dauko key din mota ka kaini kagarko", cikin zaro ido Yace "mummy mai kuma zaki yi a kagarko", cikin hargagi tace" don ubanka kar ka bata mini lokaci ka dauko mu wuce" yayin da ta karasa magana tana nufar bedroom dinta, ko da ta shiga mayafinta kawai ta dauka ta fito, wanda yayi dai² da fitowar najib, mota kirar prado suka shiga , yaja suka fice daga gidan. *Safe journey hajiya Sailuba anda Najeeb.*

*****

Dagudu zahrah ta tashi ta nufi Daddy tare da rungumeshi, su ko Aunty Basma sai zubar da hawaye sukr, don ayau suka kuma gasgata maganar zahrah da tace Daddy na nan da ranshi, Aunty Ni'eema kuwa Baba Karime ta nufa ta fada jikinta ta saki wani irin kuka mai tsuma rai, yayin da sauran da suka yi jarumta basu gudu ba suna nan sun kame suna kallon ikon Allah, dukkansu fuskarsu dauke da Mamaki, Dada Ladiyo kuwa suma tayi a zaune🤣🤣🤣🤣.

Cikin jarumtar da ta rage ma Baba Usman ya bude baki tare da fadin" Yaya Aliyu dama kana raye"

Wani kallon banza tare da tsana Daddy ya wurga masa tare da Fadin" Allah ai bai baku ikon kasheni, nidin ne dai a gabanka Usman"...




*Chau chau🤺🤺🤺🤺🤺, wallahi novel dinann akwai chakwakiya,nayi nan🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️*



*Ga Daddy dai ya dawo*
*Ga Mama Asabe da Huwailat*
*Ga kuma Hajiya sailuba tafe🚗🚗🚗🚗*

*Da Alamar dai za a saki bama bamai a Gidan Galadima, jama'ar Kagarko kuna da manyan baki fa*🎯🎯🎯🎯

*Sai gobe*👏


*_Fateeyzah_*✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 116 to 120_*




Jin zancen da Daddy yayi yasa gaba daya mutanen wurin suka shiga rudani, yayin da a Baba Usman ya maida kansa kasa yana mai zubar da hawaye.


Jaye zahrah yayi daga jikinsa tare da nufar wurin da Baffa yake tsaye, hugging dinshi yayi sannann da fashewa da a kuka kamar wani karamin yaro, yayin da Baffa shima yake ta zubar da hawaye.


Bayan Awa daya ,gaba dayansu suna zaune yayin da dukkaninsu idonsu na kan Daddy dake zaune su zahrah da Naina sun sashi a tsakiya, Aunty Ni'eema kuwa tana nan nanike da inna karime kamar zata shige mata ciki, nan na hango su huwailat da mama Asabe suna ta zaro idanu, kamar wadanda suka yi sata🤣🤣🤣🤣.


Baffa ne yayi Gyaran murya tare da cewa" Hakika dawowarka ba karamin farin ciki ya sanya dukkaninmu ba, a lokacin da Zahrah tace kana raye hakika ban wani gasgasta maganarta ba, na dauka Aljanin da yake jikinta yake kokarin bude mata ido, ashe ba haka bane, Alhamdulillah, Allah ya tsare gaba, ya kuma karewa" cewar Baffa fuskarshi dauke da murmushi.


Gaba dayansu suka amsa da Amin, sannan masu tofa albarkacin bakinsu suma suka ci gaba da kwararo masa addu'a tare da Allah ya tsare gaba.


Sai da suka tsagaita sannan Baba Mahmood yace" Ali ko zaka iya fada mana abunda ya faru na bacewarka wanda aka sanar mana ka mutu, sanna kuma da abunda ke tsakaninka da Usman".

Wani murmushin mai kama da yake Daddy yayi tare da muskutawa ya gyara zamansa.


*Gaskiyar Lamari*

Daidai gate din da zaka shiga barack na hadu da Usman, shi zai shiga yayin da ni zan fita, haka dai muka gaisa yanda muka saba gaisawa dashi fuskarshi a tunkushe, sannan naja mota ta nayi gaba, direct sheraton hotel na wuce na dauki ni'eema muka dauki hanyar dawowa kaduna, mun dan yi nisa da tafiya, don har mun fara shiga daji mota ta ta fara jerking, ganin haka yasa nayi parking a gefen hanya don duba wa, ba zato ba tsammani naji an buga mini abu akai, nan na yanke jiki na fadi, kaina na juya min yayin dana fara gani dishi², ina ta kokawa da numfashina, yayin da jini yake zubowa daga kaina, jin ihun ni'eema ne ya sa nayi kokarin mikewa ina dafa motar, mutane biyu ne sun rufe fuskarsu da kyalle suna kokawar jawota daga cikin mota, lalubar bindigan aljihu na nayi, inda cikin hukuncin Allah na samu na zarota na saita daya daga cikinsu na sakar masa harbi, take ya fadi a wurin, hakan yasa dayan yayo kaina yana kokarin kwace bindigar hannuna, nan muka fara kokawa, sai dai karfi ba daya ba nan ya zubar dani a kasa, ya saitani da bindiga, yayin da ni'eema ke ta kwala ihu tana neman taimako, bige hannunshi wani yayi, wanda yayi shiga irin tasu tare da kulle fuskarshi, kacamewa da dambe sukayi , inda wancan sabon zuwan ya samu galaba akanshi, ganin hakan yasa na lallaba , jini na ibana na rarumi bindigata na buga masa akai, nan ya sulale ya fadi kasa, ni kuma na samu damar bude fuskarshi don in samu evidence, sai dai ina budewa naci karo da fuskar Usman, nayi matukar razana, wanda dalilin haka numfashina ya dauke.


Ko da na farka, a Asibiti na ganni kwance, kaina daure da bandeji, yayin da Ni'eema, lawyerna da wani Abokina *RULWANU* damu je peace keeping tare suke zaune dani a dakin, kiran likita suka yi ya dubani tare da min tambayoyi sannan yace zamu iya tafiya.


Suleja suka wuce dani, kasancewa *RULWAN* nada gida acan, nan nayi wanka na canza kaya naci abinci, sannan muka zauna, inda yake sanar dani ya gama mini processing din komai zamu bar kasar nida ni'eema saboda kauce ma masu neman ranm don yasan baza su taba barina ba.

Abunda ya faru shine yaje shiga office din ogana sai yaji yana magana acikin wayar akan na dauki hanya yanxu, karsu bari in karasa kaduna su kasheni, ba karamin firgita yayi ba, wannan dalilin ne yasa yayi ta kiran wayata bata shiga ba, ganin haka yasa ya dauki mota ya biyo hanya, a hanyar ma yana ta kira, sai daga baya ta shiga, wanda Ni'eema ce ta dauka ta sanar dashi abunda ya faru, wanda ni kuma a lokacin ina can ina kiciniya ni dasu, koda ya karaso wurin na riga na tsume, hankalinshi a tashe ya kinkimeni yasa ni a mota, ya yaga rigar jikina ya kulle min kaina inda jini ke zuba, sannan ya nufi ni'eema inda ta kuma sanar dashi abunda ya faru, kwashe duk wani valuable abu nawa dake cikin motar yayi, sannan ya kinkimi gawar wadan nan makasan ya zuba a motar ya bude tankin fetur sannan yayi using din leater ya cinna ma motar wuta, inda Allah ya kyauta masa ma shine ranar hanyar ba mutane kasancewa weekend ne, shine ya wuce asibiti dani tare da kiran lawyerna.

Ko daya gama sanar dani abunda ya faru, hankalina ba karamin tashi yayi ba, mai nayi ma oga yake son ganin bayana, kasancewa ko da naje barack, wurinshi naje nayi submitting din wasu papers tare da masa sallamar zan dawo ranar monday, sai dai amsar da *RULWAN* ya bano shine saboda sunga inaso in kawo rank dinsu, kasancewa bayan mun dawo peace keeping din da mukaje india an kara mini girma wanda ya zama rank daya ne tsakaninmu.


Bayan mun gama duk wani tsare tsaren tafiyarmu na danka amanar komai nawa a hannun lawyer da duk wani will nawa,

Please Login or Register in order to submit comment