Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi tare ba, ba karamin kewarta yayi ba, cikin tsartsarfa ya taso zai yi hugging dinta, tayi saurin dakatar dashi tare da kaucewa ta zauna, cikin sanyin jiki ya koma ya zauna tare da cewa" meye haka sweetheart, baki yi missing dina bane?".



Wata irin harara ta zabga masa tare da cewa" ba wannan ne matsala ta ba, me ya kawoka wurina?".

Kallonta yayi cikin mamaki tare da cewa" Haba Basma wace irin magana ce wannan, don miji yazo wurin matarsa laifine?,".


"Ba laifi bane, amma kuma in matar bata bukatar ganinsa fa?" Ta fadi kanta tsaye.

Fuskar shi dauke da mamaki yace" wai duk mai ya kawo wannan magananne, akwai laifin da na miki ne?, haba basma da wanne zanji, idan na kiraki baki daukar wayata, sannan kuma yanxu nazo kina fada min wasu maganganu marasa dadin ji". Ya fadi cikin bacin rai.


Daure fuska tayi sannan tace" Ba kamin laifin komai ba, kawai na gaji da zama da kaine, inaso ka sawwake mun aurenka, don gaskiya bazan iya koma wa gidanka ba".


Hankalinsa tashe yace" wace irin maganane wannan kike fadi, anya ko basma kina cikin hankalinki, ni bance bazan iya zama dake ba , sai kece zaki ce haka, keda already kanwarki tayi ma family dinku tabo, wanda inda ba don mummy na sanki ba sai tace in sakeki saboda haka zai iya kawo mata matsala a siyasarta, shine ke har zaki iya bude baki kice in sakeki, who are u?" Ya karasa magana cikin daga murya.


Wata irin dariya ta saki tare da cewa " anzo wurin najib, ni har kake kallo kake so kamin gori wai kanwata ta bata sunan family dinmu, to duk wa ya jefa mu a cikin Wannan tashin hankalin in ba mummy dinba, duk wani abu daya faru ita ce sila, hatta su fawas da suka mutu da sa hannunta a ciki, kaga ya zama dole in...." saukar marin data jine ya dakatar da ita da fadin abunda tayi niya, najeeb ne a gabanta yake huci kamar 'yan zaki, yayin da yake watsa mata wani mugun kallo, zubewa tayi a wurin ta saki wani irin marayan kuka, wanda sautin kukanta ne ya fito da zahrah da Aunty Naina da suke dakin su little, cikin sauri suka karaso wurinta yayin da Naina ke kokarin tambayarta mai ya faru.


Cikin huci najib ya fara magana" don kina son rabuwa dani basai kinyi ma mahaifiyata sharri ba, sannan tunda abun ya zama haka, kije na sakeki, saki daya".yana fadin haka ya dauki key din motarsa ya fice daga parlourn.

Gaba daya jikkunansu yayi sanyi kar ma uwar gayyar taji labari don wani ihu da ta saki sai da ya fito da mama Nanny, Allah yasa ma su little na makaranta.


Nan dai suka zauna suna bata baki, tare da nuna mata kuskurenta, don mama Nanny fada mata tayi ba haka ya kamata ta biyo masa ba.



A haka Yaya Abdul yazo ya samesu, inda shima bai ji dadin hukuncin ba don rufe Basma yayi da fada.


_A gurguje_


Ranar lahadi suka shirya tafiya kagarko wurin sunan matar Baba Usman, Mama Nanny kadai suka bari a gidan, don har da su little suka tafi.


Karfe biyu tayi musu a kagarko, yayin d suka tarar da gidan sunan a cike, abinka da kauye, kuma ana yamadidin matar soja ta haihu, dakin mai jego suka sauka, inda nan da aka gaigaisa, yayin da mai jego ta hade rai taki mika musu jariri, ganin haka yasa zahrah fizgar dan a hannunta, nan ko ta saka ihu wai Zahra zata cinye mata da, ran zahrah ne ya baci tare da fadin" naga dai abunda yayi ni shi yayi jaririn nana don haka dabge zanyi dashi inci dadi" tana gama fadin haka ta fice dakin da jaririn a hannu, nan suma su Aunty Basma suka bi bayanta, aiko nan mai jego tasa kuka har da tirje tirjen kafa, hakan yasa wata yayarya ta dauki wayarta ta kira Baba Usman kasancewa yana gari.


Suko su zahrah dakin inna karime suka shige, nan ko ta tarbesu cikin murna, bayan an gaigasa ne Naina ke bata labarin abinda ya faru tsakanin zahrah da mai jego, nan fa aka hau dariya har da jama'ar dakin kasancewa duk na jikine.


Tun daga kofar gida yake Bambami tare da zage², har ya shigo cikin gidan, nan fa mata sukayi tsit suna binsa da ido.


A fusace yace "don ubanki ina kike, kizo ki kawo mini dana kafin inci ubanki, shegiya mara kunya, dangin mayu, wallahi Aliyu yayi Asarar Haihuwa".

Maganar daya yine yasa duk jama'ar da suke cikin dakunan gidan suka fito, ciki kuwa har da Zahra, wacce tun da ya shigo ta jishi, kuma tayi niyar fita amma Aunty Naina ta dakatar da ita.


"Wai ina kike ne, shegiya, tsinanna"ya kuma magana a fusace.

Dada ladiyo ce da ta fito zani a hannu tace" wai wani irin abune haka manu, kazo kana so ka watsa mana taro akan wannan shegiyar masifar taka ta sojoji" ta yi magana goro cike da baki.

Zahrah ce ta karaso gabansa tare da fadin" ni ba shegiya bace wallahi, kasan inda shegiya take, tana can sangamemiyar budurwar daka ajiye ka boyeta a idon duniya". Ta fadi dai² shigowar su Baffa dasu Baba Mahmood wadanda akaje aka sanar dasu abinda ke faruwa.

Gaba daya jama'ar dake wurin daskarewa sukayi, zuciyoyinsu cike da kokwanto.

Baba usman kuwa jarumta yasa ma Kansa sannan yace" me kike fadine haka, sharrin da kika saba yi ma mutane nima yi mini zakiyi" ya tambayeta fuska a sake yana gwalalo mata idanu.


Wani malalacin murmushi ta saki tare da mika ma mai jego danta sannan tace" kafo kowa sanin ba sharri na maka ba, wallahi ka bini a hankali, sirrinka ba wanda ban sani ba, don haka in ka kuma zagina ko iyayena sai na tono abinda kayi shekaru kana rifew...." shakan wuyanta yayi yana muzurai kamar wani damisa, sannan yace ke karamar 'yar iska ce, idan baki tona ba kin raina 'dan iskan ubanki".

Cikin tsartsewar murya Dada tace" wallahi manu idan baka sake taba, sai na daga maka nono".

Jin maganar Dada yasa Baba Mahmood da suke tsaye kamar gumaka ya karaso ya fara kokarin banbare hannunsa daga wuyan zahrah wacce ta fara kif kif da idanu, da kyar aka samu ya saketa, yanata hura hanci, yayin da zahrah take gefe tana ta tarin wahala su Aunty Basma suna riketa.


Gyaran murya Baffa yayi ya kalli jama'ar dake wurin tare da cewa "don Allah ku fice ku bamu waje".


Sif sif suka fita, yayin da kusan dukkansu suke sauri don su karar.




Hajiya zahrah mai zamani🤪🤪🤪🤪🤪🤪, Alqur'an ina yinki.





*Comment*
*Share*
*Follow*


*Fateeyzah*✍

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*


_Wannan page din nakine my evalasting sister, Alhafs, ga page 101 nan kar ki cinye ni danya._

_Hafsat s Bello( maman fadila) ina godiya, Allah ya kara zumunci._


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page101 To 105_*

Maida kallonshi yayi wurinsu zahrah ranshi a bace yace ma Baba Mahmood" ka kira sauran ka sanar dasu muna da taro gobe da safe, sannan su zahrah karsu koma yau, sun kwana anan zuwa gobe in mun gama taron sai su wuce" yana gama fadin haka ya fice daga gidan.


Gaba daya jikkunansu sunyi sanyi, don sun dade basu ga Baffa cikin wannan yanayin, saboda mutun ne shi mai saukin hali, da wuya kaga bacin ransa ya fito fili haka.

Da dai dai suka fara barin wurin suna shigewa daki yayin da mazan sukayi waje har da Baba Usman da yake ta hura hanci.

Zahra kuma Aunty Naina ce ta mikar da ita suka shige dakin inna karime, don shakar da ya mata bata wasa bane, yayin da Aunty Basma dasu little suka bi bayansu, inna karime kuwa kama Dada tayi ta nufi dakinta da ita, don gaba daya ta kasa motsawa daga wurin, kana ganinta kasan ta na cikin bacin rai.

Su hajiya mai jego dama tuni ta wuce daki da 'yan uwanta, suna can sun bude chapter na zagin zahra.

******************************

Kwance take tana ta faman sake², gani take abinda take ma mama bata kyauta ba, ko ba komai ai mahaifiyarta ce, wanda ta bata tsawon rayuwarta tana nema ba don komai ba, sai don ta gina rayuwarta, turo kofar da akayi ne ya tsinke ta daga tunanin da take, mama ce ta shigo fuskarta dauke da damuwa, zama tayi a bakin gado, cikin sanyin murya tace "baby tashi ina so muyi magana".


Sai da ta dauki tsawon lokaci sannan ta mike ta zauna sannan tace" ina sauraranki"

" Nayi tunanin ranar wanka ba a boyen cibi, sannan da kiji wannna labarin a bakin wani gwara in fada miki da kaina, don ko mu jima, ko mu dade sai maganar nan ta fito , ina rokon yafiyar ki, sannan da fatan bazaki juya mini baya ba" cewar mama idonta cike da hawaye.

*Asalin Labari*
*Kauyen Andi*, kauye ne dake karkashin karamar hukumar kauru da ke nan kaduna, sana'ar mazaunan wannan kauye ita ce noma wanda suka gada tun zamanin kaka da kakanni, mahaifina malam Audi da mahaifiyata inna Huwaila mazauna wannna kauyen ne, inda suke sana'ar su ta noma, mu hudu ne 'ya'yansu, wanda yayyina uku maza wato basiru, sirajo da Amadu sai nice cikon ta hudunsu suwaiba da suke kirana da Asabe kasancewa an haifeni ranar Asabar, ba karamin so ake nuna mun, harta kai babu mai kwabata duk abunda nake so shi nake aikata wa.

Nayi makarantar primary, wanda na gama ina da shekara goma sha biyu, a wannan lokacin samarin kauyen nan suka mun cha saboda Allah tayi ni da kyau ga kira, wannna dalilinne yasa nasaka ma kaina girman kai na bazan yi aure in zauna a kauye ba, kuma su yaya basiru da baba suka daure min gindin haka, hakan yasa aka kafa teburin zagina a garin, niko ko a jikina.

Adamu shine da na uku a wurin sarkin noma kuma yana daya daga cikin masoyana, kyakkayawa ne na karshe don har ya fini kyan fuska, jin abunda na zartar yasa yabar gari ya tawo garin kaduna neman aikin yi saboda ya samu ya aureni, cikin hukuncin Allah kuwa ya samu aikin gadi a gidan wani attajiri dake nan unguwar rimi, kuma ana biyansa da kyau, albashinshi na farko ya kafa dan teburi ya fara saida kayan miya a bakin gate din gidan, ganin haka ne Alhaji ya kara masa jari, kasancewa mutum ne shi mai matukar kirki.


Ba karamin ciniki Adamu yakeyi ba har ta kai ya kara girman teburinsa, ana cikin haka ne tafiya ta kama Alhaji da iyalinsa ta shekara uku zuwa wata kasa, hakan yasa ya sallami Adamu tare din bashi kudi mai tsoka, sannna ya siyar masa rumfa a kasuwa, inda ya koma da sana'ar shi nan.


Cikin shekara daya da rabi, Allah ya buda ma Adamu akan sana'ar nan tasa, wanda ni kuma har lokacin ina nan banyi aure b Saboda ban janye maganata ba, shi kuma adamu yana samun labarina a wurin 'yan gidansu.


Shekarar sa biyu cif, ya kawo ziyara gida inda kana ganinsa kasan yana jin dadi , don rayuwar da banbanci, kwanan sa daya yazi gurina ya gabatar min da kansa tare da neman aurena, aiko banyi wata² ba na amince don ko ba komai zan cika burina na aure a birni dama can da soyayayyarsa a cikin raina, ba tare da bata lokaci ba aka saka ranar bikinmu wata daya, don duk kusan sa'annina a kauyen nan sunyi aure wadansu har sun haihu.



Satin Adamu daya ya koma tare da alkawrin dawowa ana sauran sati daya biki,aikuwa cikin hukuncin ubangiji ana sauran sati dayan ya dawo, inda a ranar aka kawo kayan lefena, lefen da aka ringa tururuwar zuwa gani, don ba yarinya da aka taba mawa irinshi, saboda akwati biyu yayi mini da, nan fa kaina ya kara kato, na fara ma mutane kallon hadarin kaza ina tinkaho zan auri mai kudi.


Sati na zagayowa aka daura aurena akan sadaki mafi daraja a wannan lokacin, washe gari aka tafi kaini inda munsha kukan rabuwa dasu inna da yaya Ahmad, motoci biyu aka tafi kaini dasu, don sarkin noma yace baza ayi zuga a tafi da yawa ba kar aje a karya ma danshi tattalin arziki, iyayena ma sunyi kokari wurin yi mini kayan daki, don saboda su birgeni a *pambegua* aka siyomin gado da su katifa har da kujeru.


Anguwan rigasa aka ajiyeni don nan Adamu ya kama hayan wani dan madaidacin gida, mai dauke da uwar daka da falo, sai daga waje akayi bayi da kitchen, yayin da 'yan kauyenmu suke ta santin gidan, tare da sha'awarsa, niko bakina har kunne ganin na shigo birni, don gani nake nafi kowacce mace a kauyenmi sa'a.


Zama na da Adamu zamane na so da kauna, bai rageni da komai ba, tun daga cimata har sutura ta, yana kokarin faranta mini, saboda sana'ar shima Allah ya samata Albarka.

Wata na shidda na fara tsiro masa da wasu halayya ta banza, don duk abunda zai mini sai na raina, kuma hakan ya samo asaline daga shige shigen makota danake yin, wadanda duk kusan yara mata ne sa'annina, kuma duk 'yan nan kaduna ne, don ni kadaice aka auro daga kauye, tun daga wannan lokacin zaman lafiya yayi kaura a gidan nan, don sai in kawo lace din dubu goma ince sai ya siyan mun, wanda a wannan lokacin saka lace din dubu goma sai matan masu kudi, idan kuwa bai siyan mun ba, ko bacci bana barinsa yayi har sai ya siye shi.


Haka dai ya ci gaba da hakuri dani, nikuma abun nawa ma dada gaba yake, don nayi sababbin kawaye masi kudi, don hatta matan unguwarmu na dena hurda dasu.

A lokacin da muka cika shekara dayane da aure ya siya gidan da muke ciki, wanda banso haka ba, don a cewata dama zuwa yayi unguwar masu kudi ya kama mana haya, amma yayi kunnan uwar shegu dani.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kullun da sabon halin da nake fito mai dashi, hakan yasa jalinshi ya karye, don hidimar da yakemin wadda tafi karfinsa, a haka dai yaje *Andi* ya siyar da daya daga cikin gonarsa wacce yaci gado, (kasancewa sarkin noma ya rasu a shekatan) yazo ya farfado da sana'arsa.


A lokacin da muka shekara biyu da aurene, na fara fuskantar tsangwama wurin danginsa kasancewa ban haihu ba har lokacin, hakan yasa ma na dena zuwa garin ko da kuwa sha'anine, saidai inyima baba da inna sako, a wannan shekaranne kuma yayyina suka yi aure a can andi, inda suka tare da matansu a gidan da suka gina anan bayan gidanmu.

Dawowar *GAJE* nan kusa da gidanmu yasa komai nawa ya tabarbare, Dalili kuwa shine gaje irin tambadaddun matan nane wadanda suke yawon siyasa, mijinta ya rasu, kuma bata taba haihuwa ba, hakan yasa 'yan uwansa suka kwace gidanshi a hannunta, wannan dalilin yasa ta dawo unguwar mu ta sayi gidan kusa damu, ganin yanda manyan motoci da manyan mata ke zarya gidanta yasa nayi sha'awar hulda da ita, don a ganina ita ce dai² ni, tun ina shiga bata bani fuska har dai ta soma sakin jiki dani, abunka da mara sirri nan na kwashe labarina kaf na sanar mata, anan ko ta mini tallan shiga harkar siyasa, nan ko na amince, ba karamar murna nayi ba, don na taka babbar sa'a, don lokacin ne aka fara yakin neman zabe.

Mun kai ruwa,rana da Adamu don sam yaki amincewa, hakan ne yasa na sami wani malami ya rufe masa baki, ni kuma anan na fara bidiri na, don anan ne na hadu da hajiya sailuba, lokacin mijinta na neman takara a majalisar wakillai, hakika siyasa ta mini rana don na samu kudi, sai dai kudin babu albarka, su kuma acan kauye ana can ana labarin nayi kudi, saboda har gyara gidan mu nayi, yayin da 'yan uwan Adamu suke yamadidin kudin dan uwansune.



A garin yawan campaign ne na hadu da mahaifinki, inda yake cikin masu tsaron mijin Hajiya sailuba, a lokacin bai da aure, amma ni na sanar dashi ina da aure, nan muka kulla alaka,wacce har ta kai yana daukata muje hotel mu kwana, ta haka ne har na samu cikinki.

Adamu kuwa Allah yana ta buda masa a sana'arsa, sai dai lamarina na damunsa, saboda har takai ina daukar sati biyu bana gida, haka dai yayi ta hakuri dani don bai da yarda zai yi dani saboda na riga na mallakeshi.

Cin zaban dasu hajiya sukayine yasa na samu zama a gida, sannan a lokacinne cikinki ya bulla, ba karamin farin ciki mukayi ni da Adam ba, don zuwa nayi akaa sa masa son cikin, saboda nasan cikin ba na sabane, ta bangaren mahaifinki kuma cewa yayi in zubar da cikin, inda ni kuma naki, hakan ne yasa muka raba hanya dashi, yayin da na ci gaba da rainon cikina.

Bayan wata tara na haifeki, duk wani masoyina ya tayani murna, yayin da ana gobe suna bus uku 'yan kauye suka ciko suka zo sunanki, ba karamin kudi na kashe ba, shima kuma Adamu yayi rawar gani a sunan, inda na saka miki sunan mahaifiya, mahaifinki kuma ban neme shiba koda na haifeki.



Haka muka ci gaba da rainonki nida Adamu, inda kuma bangaren siyasa kuma sai abunda yaci gaba.

Kina da shekara hudu, Adamu yayi hatsari inda motace ta bigeshi, nan dai aka kaishi asibiti, yayin dana kira 'yan uwanshi na sanar dasu halin da yake ciki, don yana jin jiki, washe gari kuwa suka tawo, inda akace sai an masa operation don yayi mugun buguwa a mararshi, nan dai muka saka hannu tare da biyan kudin aikin.


Bayan an fito da shine likitan kema na bayanin sun samu nasara zai iya haihuwa, saboda sakamakon buguwar da yayi kwayoyin haihuwarsa sun fara aiki, ba karamin tashin hankali na shiga ba don ganin asirina yana shirin tonuwa, nan dai 'yan uwansa suka fada ma likitan ai dama yana da 'ya, inda shikuma yace hakan bazai taba faruwa ba, yace a kawoki a muku test din jini, kafin inyi wani kwakwaran motsi har sun kaiki, yayin da gwaji ya tabbatar ke ba 'yarshi bane, ba karamar tijara na sha awurin 'yan uwan Adamu ba, inda kafin kice chas, sun gama yadawa acan kauyen, wannan maganar ita tayi sanadiyar rasuwar Adamu, Saboda zuciyarshi bugawa tayi.



Ana yin uku 'yan uwanshi suka saka rigimar a raba gado a bani tuminin takaba, tunda ke baki da gadonsa, ganin haka yasa naje wurin malam nasaka aka rufe bakinsu.


*Ci gaban labari*

"Wannan ne abunda ya faru" ta karasa magana, tana mai share hawayen idonta.



Huwailat ko kuka ta keyi kamar karamar yarinya, dago idanta tayi da suka yi jajawur kamar gauta tace" ya sunan Mahaifina?"


*Tirkashi*🤔

*Comment*
*Share*
*Follow*

*_Fateeyzah_*✍

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 106 to 110_*

"Sunansa sergeant Usman Abdulrahman Kagarko".



A razane huwailat ta dago kai tare da fadin" kina nufin "Lieutenant Usman Abdulrahman Kagarko ne mahaifina".

Cikin sanyin jiki tace" tabbas shine, amma sanda na sanshi sergeant ne".



Cikin tashin hankali tace" na shiga uku, wallahi bazan taba yafe muku ba, daga shi har ke, kun saka rayuwa ta cikin dana sani".



"kar ki cemin a yawon bin mazan da kike yi kin hadu da babanki" mama ta fadi cikin rudani.



Wata muguwar harara ta watsa ma mama tare da fadin" duk bata mun rayuwa da kikayi, kika haifoni ta hanyar zina shine kuma kike jifa na da kalmar nan, insha Allahu bazan ga haka a rayuwata ba, tarayya da mahaifina".



Sauke ajiyar zuciya mama tayi sannan tace" Alhamdulillah, amma ya akayi kika sanshi ?, don tun kafin na haifeki rabona dashi, ke ko sannin abinda na haifa bai mayi ba".


Kai tsaye tace " kina nufin kice min baki san uncle din zahra ne".


"Ya za'ayi in sani baby, tunda ko da nayi mu'amala dashi, sunansa kawai na sani sai garinsu" cewar mama cikin sanyin jiki.



Wani mugun kallo huwailat ta watsa mata tare da cewa" karki raina min hankali kice baki sani ba, to in baki sani ba, meye dalilin da yasa kika kaini makarantarsu zahrah tare da umurtata in nemi kusanci da ita, sannan meye dalilin da kika sani nayi shedar zur a media akan zahrah 'yar cult ce". Ta karasa magana tana mai zuba mata idanu.



"Wallahi huwailat ni kaina ban san dalili ba, don sani akayi, duk wahala makarantarki hajiya sailuba ce ta dauki nauyinki, yayin da tace in nuna miki scholarship ne na saman miki, sannan ita tayi cuku cukun da har aka hadaki daki daya da zahrah, sannan ita tace ki nemi kusanci da ita, kuma ko abin nan da ya faru,duk aikinta kikayi, wanda ni kuma take biyana kudi mai tsoka" ta karasa magana tana mai kallon huwailat.



Cikin bacin rai tace" Da farko na dauka kince in kusance tane saboda tana 'yar gidan masu uku, sannan 'yar gata, daga karshe kuma na dauka saboda a koda yaushe tana fina samun nasara da daukaka shi yasa kika tsaneta, nima kuma kika zugani har na aikata mata haka, sai yanxu na gane saboda son abin duniya kika sani na tozarta 'yar uwata, wace irin uwace ke haka, bacin kawo ni duniya da kikayi ta haramtacciyar hanya, sannan kika daurani a turbar zina duk saboda abin duniya" ta yi magana tana mai zubar da hawaye.



Tashi mama tayi, tana zubar da hawaye tare da kokarin matsowa kusa da huwailat, tsawar data daka mata ne ya dakatar da ita tana fadin" kar ki matso kusa dani, wallahi na tsaneki, bansan ganinki, ki fitar min daga daki".



Zuciyar mama kamar zata fito, yayin da hawaye ke ambaliya akan fuskarta, haka taja kafarta ta kama hanyar fita daga dakin, ta daura hannu zata bude kofar kenan ta jiyo huwailat na fadin" kuma ki shirya, gobe karfe goma zamu je kagarko" kada kai tayi ta fice.



Wani irin marayan kuka ta saki ta kifa kanta akan filo, hakika duk wanda ya ganta a wurin sai ya tausaya mata.



A kagarko kuwa gaba daya duk wanda ka gani a gidannan yana cikin damuwa karma zahrah da Baba usman suji, duk yanda inna karime ta takura zahrah taci abinci taki ci, haka nan dai suka gaji suka kyaleta, yayin da karfe goma ko wannansu ya nemi makwanci.


********************************

Zaune suke akan wani dogon table, dukkansu suna sanye da kaya mai dauke da launin baki da ja, a inda matan ke daure da wani jan kyalle a kawunansu tare d tamabarin kwarangwal.




Daga can gaba, Hajiya sailuba ce zaune kusa da wani katoton mutumi, baki huluk mai jajayen idanu, suma dai suna sanye da irin kayan sauran , ba abinda sukeyi sai tsabace tsabacen su tare da wasu surutai da baka iya gane mai suke cewa.



Gyaren murya wannan katon mutumin yayi, da alama shine shugabansu, sanna ya fara magana cikin harshen turanci" na kira wannan taron gaggawar ne saboda wani abu dake shirin tunkaro mu ta bangaren madam sailuba, ba komai bane sai ganin da nayi zamanta cikinmu akwai hatsari saboda akwai masu kawo mata hari, wanda kuma nayi iya kokarin shawo matsalar, amma sun fimu power kasance wa suna amfani da wannan littafin na musulmai, shi yasa na yanke shawarar karban duk wata power dake hannunta kasancewa in abin nan ya sameta tana tare da shi muma zai shafemu".



Take wurin ya kaure hayaniya, yayin da hajiya sailuba ke cikin tashin hankali duba da yanda idonta yayi fari fat, baka ganin bakin ciki.



An dau tsawon lokaci kafin hayaniyar ta mutu, yayin da wata mace wacce kana ganinta kaga bayerabiya ta mike tsaye, cikin turanci tace" my lord, bamu yi tsammanin haka daga gare kaba, duba da yadda duk

Please Login or Register in order to submit comment