Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin littafin DOCTOR ZAHRAH*


*RAYUWAR CAMPUS!* 🗣️
*RAYUWAR CAMPUS!!* 🗣️🗣️
*_RAYUWAR 'YANCI_*

_Littafine da ya kunshi labarin babbar makarantar jami'a, yadda dalibai, lecturer, cleaners securities suke rayuwa a campus._

_A nan zaku ji yanda securities da cleaners taka mihimminyar rawa wurin gurbata tarbiyyar dalibai, sanna da yanda manya masu kudi kuma masu shekaru suke tada muhimmiyar rawa wurin maida dalibai mata karuwai._


_Sannan da yanda wasu iyayen suke da hannu wurin lalacewar 'ya'yansu a makaranta._


*Shin laifin na waye, school Authorities ko iyayen daliban?.*

*Laifin waye, na masu bata sune ko na daliban?.*



*Domin samun karantawa zaka turo da katin waya ko kuma ka tura 200, zuwa account dina ta banki, domin karin bayani zaku tuntubeni ta wannan lambar 08161734851.*


*Comment*
*Share*
*Follow*




_*Fateeyzah*_✍




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 81 to 85_*


" Wa ya aiko ka?" Tambayar da Alaramma ya jefa mata kenan.


Wani ihu ta saki, sannan cikin muryar nan mara dadin saurare tace" bazan fadi ba, saboda za a gana min azaba, idan na koma garesu".


Jin haka yasa Alaramma sakin wani lallausan murmushi, jakar shi ya bude ya dauko wani magani a kwalba, ya sheka mata, ihu ta saki tare da fadin" don Allah karka kasheni zan fadi, Hajiya sailuba ce ta aikoni domin in shiga jikinta, saboda in lalata mata basirarta ta yanda aikinta zai dena tasiri. Saboda taga tana bibiyar lamarinta, wannan dalilin yasa, duk wanda tayi ma theater sai ya mutu, wanda nine nake shanye jininsu,saboda jini shine abincina".

Dukkansu dake dakin sun girgiza yayin da Aunty Basma da Aunty Naina ke zubar da hawayen tausayin zahrah, yaya Abdul kuwa idon nan ya kada yayi jawur sai ajiyar zuciya yake saukewa.


Alaramma ne ya kuma watsa mata tambaya tare da cewa" to zaka fita jikinta, koko sai na kona ka da ayoyin Allah".


Cikin sauri ta amsa da "wallahi zan fita, don banso ka kasheni, kasancewa ni yaro ne ban wuce shekara hamsin a duniya ba".


Alaramma ne yayi murmushin samun nasara tare da cewa " ka taimaki kanka, don haka fice yanxu"


Atishawa zahrah ta saki so uku, jin hakan yasa gaba daya dakin fadin "Alhamdulillah".


Nan Alaramma ya bada magungunan da zahrah zata ringa amfani dasu, sannan yayi musu sallama don yana da wurin zuwa a cikin nan kaduna, duk yanda yaya Abdul ya cikasa da Alkhairi kin karba yayi, don acewarsa tsakaninsa da zur'ar Galadima babu haka, Baba Muhammad ne ya dauke shi a mota don saukesa.


Kukan da Aunty Basma ta fashe dashi ne yasa gaba dayansu suka dawo da hankalinsu wurinta, babu wanda yayi yunkurin tunkararta, don sun san kukan nata shi zai sa zuciyarta tayi sanyi, rungumeta Aunty Naina tayi itama ta saki nata kukan, don hakika tana tausaya ma 'yar uwarta halin da take ciki.


Sai bayan awa dayada zahrah ta farka,ji tayi jikinta ya mata shagwal kamar an cire mata wani kaya mai nauyi da aka daura mata akai, gaba daya binta sukayi da sannu, yayin da Ita kuma take binsu da idanu, don son karin haske, saboda gani take duk abunda ya faru kamar a mafarki.

Ganin haka yasa Baffa koro mata bayanin abunda ya faru, nan ta dirkushe ta saki wani marayan kuka, zuciyarta sai bugawa take kamar zata fito, sannan ga tsanar Hajiya Sailuba data kuma ninkuwa a ranta, sai dai tasan rijiya ba wurin wasan yaro bane, don ta ko ina Hajiya sailuba tafi karfinta ba zata iya karawa da ita ba.



Nasiha sosai Baffa ya musu kafin dawowar Baba Muhammad daga kai Alaramma.

Karfe sha daya ya dawo, wanda nan Baffa ya musu sallama suka tafi, tare da yi musu Alkawarin dawowa bayan sati daya, don sanin ta yanda zasu bullo ma Hajiya sailuba don Aunty Basma tayi rantsuwa bata koma wa, ta gama auren.


Nan dai suka shige dakunansu yayin da Yaya Abdul ya nufi wurin aiki, duk yanda Aunty Basma ta yita ma zahrah magana taki amsata, don ba karamin haushin ta take ji ba, don gani take duk iya ta jawo musu wannan bala'in na auren Najib da tayi.


Karfe biyar daidai wayarta tayi kara, kamar dai wancan karan, don wannan ma ce mata akayi ta kunna Tv.


Ba tare da bata lokaciba ta kunna, wanda dai² an nuno fuskar Doctor Sulaim da huwailat, tare da gabatar dasu a matsayin makusantar Doctor zahrah, wani irin tukiki zuciyarta keyi, zaran mukullin motar ta tayi tare da veil ta nufi kofar fita, wanda yayi da² da fitowar Aunty Basma da Aunty Naina daga kitchen, ganin yanayinta ne yasa Aunty Naina tambayata sai dai ko kallon bangaren da suke bata yiba ta fice daga parlourn, motar ta ta nufa direct, wanda bayan ta shiga ta ja motar da wani mahaukacin gudu, don har ta kusa take ma Baba mai gadi kafa.


Pls manage, sorry for errors banyi Editing ba.


*Tofa ina kuma ta nufa*


*Comment*
*Follow*
*Share*


*Fateeyzah*✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 86 to 90_*


Sharara gudu takeyi akan titi kamar zata tashi sama, yayin da motoci sai kauce mata suke don duk yanda ake mata horn baji take yiba, inda Allah ya tsare babu motoci da yawa akan titin.



Bangaren su Aunty Basma kuwa, gaba daya sun shiga damuwa, don sun kasa tsaye,sun katsa zaune, don yanayin da ta fita , susan ba lafiya ba, ganin hakan bazai fishesu ba, yasa Aunty Naina ta dauki wayarta ta kira Yaya Abdul,sai dai har wayar ta gama ringing bai yi picking ba, hakan yasa suka zauna suka yi tsuru².




Shiko Yaya Abdul gaba daya hankalinsa ya koma kan program din da akeyi, mamaki yake yanda huwailat ta karkace baki take ta yi ma zahrah sharri yake, sai dai a tunaninsa duk mai hankalin da yaji abunda take cewa, yasan kyashi ne da hassada yasa ta fadin haka, don cewa take zahrah ta kirata a waya tace mata ta rufa mata asiri, sannan har ta yi mata tayin aiki da ita, indai komi ya kammala.


Zahra bata zarce ko ina ba, sai *hikima station* , parking tayi sannan ta fito cikin fushi, bata bi takan security din dake mata magana ba ta kutsa kai cikin building din.



Ganin yanda da shigarta, ma'aikatan wurin suka zubo mata ido yasa tambayarsu ina directorn ku, gaba daya wurin suka bata amsa da tana office, bari a kaiki, daga bayanta ta jiyo wata zazzakar murya tana fadin "barka da zuwa Doctor, gashi ko kin iya zuwa a dai², saboda yanxu ake hira da huwailat".



Murmushi tayi mai kama da yake" tace dalilin hakan yasa nazo ai".


Cikin kankanin lokaci aka gama shirye² komi sannan aka tafi gajeran tallah, don ba ma zahrah daman shiga wurin da ake gabatar da shirin.




Shigar zahrah wurin, cikin huwailat da Doctor suleim ba karamin kada wa yayi ba, don dukkansu sun shiga cikin firgici wanda har sai da ya nuna a fuskarsu, wani makirin murmushi zahrah ta saki musu, sannan ta zauna, wanda yayi dai² da dawowa tallar da aka tafi.



"Mai saurare barka da dawowa, a yanxu ne muka samu ziyarar Doctor zahrah, sannu da zuwa doctor".


Murmushi doctor ta saki tare da cewa"ina godiya sister".


"Muna so ki gabatar mana da kanki"


Fuskarta dauke da fara'a ta ce" sunana fateema zahrah Aliyu Abdulrahman, mamallakiyar Asibitin A.A Rahman Specialist Hospital".


Ta bangaren masu kallo kuwa sunyi mamakin bayyanar Doctor zahrah a wannan shiri,wanda yawancinsu suna ganin rashin mutuwar zancen ne yasata zuwa, yayin da masoyanta suke ta farin ciki don da alama sune da nasara.


Yaya Abdul ba karamin sandarewa yayi a zaune ba, don bai taba tunanin zahrah zata bayyana baha, domin wanke zargin da ake mata, sai dai addu'arshi a gareta Allah ya bata sa'a.


Dukkansu suna zaune a parlour sunyi jigum², don sun kagara su ga Zahra ta dawo saboda koda suka kira number ta danna musu busy tayi. Mama Nanny ce ta fito daga daki ta ke sanar dasu ga zahra can a Gidan Tv za a na yin hira da ita, jin hakan ya saka Aunty Basma kunna Tv.



A bangarensu zahrah kuma, mai gabatar wace ta kara dace" Doctor zahrah a kwanakin baya an samu wani videon ki da kike tozarta wani daga cikin patient dinki, wanda har kika sa aka dauke shi aka fita dashi daga Asibitin, wanda hakan ya jawo cece kuce a social media, amma ba wanda yaji bakinki akan maganar, ko zaki iya mana karin bayani"



Wani lallausan murmushi ta saki tare da cewa"hakane kamar yanda kika fadi, but abunda yasa ban yi magana ba, ai babu wanda ya fito ya tambayeni dalilina na aikata haka, kawai abunda mutane keyi sai comment, a yayin da cikin 100%, 40% ne suke goyon bayana, 60% ko aibanta ni suka yi, kinga kuwa babu dalilin da zai sani fitowa ko gaiyato 'yan jarida akan maganar nan".



"Amma baki tunanin hakan da kikayi zai bata miki career a lokacin?" Cewar mai gabatarwa.


"Ban kawo haka a raina, saboda nasan duk wanda ya rike Allah yana tare da nasara, kuma Allah ne ya sa na kawo wannan matsayin" ta karashr magana tana kallon su huwailat da suka yi tsuru².


" hakane Doctor, Amma mai zakice akan zargin da ake muki, na cewa kina daya daga cikin 'yan kungiyar Asiri, wanda kuma Aminiyarki ta tabbatar da haka".



Murmushi tayi mai kama da yake, sannan tace" inaga ya kamata mu ba huwailat dama ta kuma maimaita maganar data fadi, ta hakane zan iya wanke hukunci".



Nan danan huwailat ta fara zara ido, amma ganin yanda aka dawo da camera kanta yasa ta dake tare da nemo natsuwa tasaka ma kanta.


"Gare ki Huwailat, muna so ki maimaita abunda ki kace a satin da ya wuce akan zahrah".



Cikin natsuwa huwailat ta fara maimata maganar ba tare da tayi kuskureba ko canza kalma, don zakayi tunanin a rubuce take karantawa.


" gareki Doctor, kinji abunda Huwailat tace, kina da abunda zaki ce akan haka".



"Ina bukatar zulaihat ta bani number Tamannah da tace, don itace kadai zata iya warware wannan sirrin"cewar Zahra.


Wani miyau huwailat ta hadiye da bata shirya ba, sannan tace" a yanxu gaskiya banda number ta,don shekaran jiya waya ta ta fadi".



Wata dariya Zahrah ta saki, sannan ta zaro wayarta daga cikin jakka, dialing din number tayi, cikin kankanin lokaci wayar ta fara ringing, hakan yasa mai gabatarwa tayi connecting din kiran a babban speaker,a ringing na uku akayi picking call din, wata zakakkar muryace tace "hello"

Kakaro murmushi zahrah tayi sanann cikin turancin tace" yakike Tamanna"


Daga can ta saki wani uban ihu, sannan tace" zahrah kece, dama kina nan".



Fuskarta dauke da murmushi tace" ina nan tamannah, ina yawan kiran wayarki bata shiga, yau ma gwadawa nayi, sai gashi na sameki".


Wata siririyar dariya ta saki sannan tace"kinsan bana india, saboda wadannan 'yan pink ladies din sun dami Rayuwata, hakan yasa dana sanar da Papa, ya maidani singapore wurin Uncle dina, a can ma nake aiki, yanxu ma nazo bikin yaya katrina ne, shi yasa kika sameni, gaskiya nayi missing dinku, kullun kuna raina, amma kuma nayi missing din numbers dinku, shiyasa ban nemekuba, ina huwai, rabona da ita tun ranar candy, gwara ke, munyi waya kafin in koma can".


Wani murmushi zahrah tasaki, tana maida kallonta ga huwailat da kirjinta ke dukan tara², tana zazzaro idanu, sannan tace "tana nan lafiya lau, itama take cemun kunyi waya, shiyasa na kiraki".


"Tace miki!, ni banyi waya da ita ba, sai sai in da wata tamannan tayi waya, hmm, ki gaisheta, kice mata nayi missing dinta sosai,don itace abokiyar harka" ta karashe magana tana dariya.



Cikin sanyin murya ta amsa mata da "zan fada mata, bye"ba tare da ta jira amsawarta ba ta kashe wayar.


Idan ka kalli bangaren huwailat, babu abunda takeyi sai zuba, hade da zaro ido, haka ma suleim, kallonsa kawai zakayi kasan yana cikin tashin hankali, a yayin da ma'aikatan wurin da masu kallo suke cikin jimamin abunda yake faruwa, bangaren su Yaya Abdul dasu Aunty Basma kuwa, wani farin cikine ya lullubesu, don koba komai wayar ta wanke zahrah daga zargin da ake mata.



Cikin kwarewa, mai gabatarwa ta fassara wayar da Doctor zahrah tayi, a harshen hausa tare da jefa ma huwailat tambaya" Huwailat mai za kice akan abunda kawarku Tamannah tace?".


Amsawa tayi tana zaro ido, sannan ta dake zuciyarta sannan tace" ban yadda ba, don zai iya yiwuwa kafin kiran nan,ta riga ta hada baki da ita" .



"Doctor zahrah kinji abinda Huwailat tace".


Wani murmushi tayi mai dauke da takaici sannan tac"Naji, amma wannan kuma ita ya shafa, don ni na gama nawa". Ta fadi tana mai mikewa ya fice daga wurin.


Bangaren yaya Abdul kuwa, ranshine yayi masifar baci, wayar shi ya dauka tare da fadin "ku sameni a Hikima Station", ya fadi yana mai ficewa daga office.



Yayin da jama'a suka kasu kashi biyu, wadansu suna ganin gorin kunya ne ya saka doctor zahrah fadin hakan, dan gani suke abunda huwaila ta fadi zai iya zama gaskiya, wadansu ko sun yadda da hujjar da Zahrah ta bada.


Ko da zahrah ta fito,direct motarta ta nufa ta bude ta shiga tare da kifa kanta a jikin sitiyari, tana mai saukar da numafashi da sauri.



Bangaren huwailat ko ganin zahrah ta fita, hankalinta ya kwanta tare da tunanin aikinsu yaci, kuma dai jaddada batunta tayi sanann aka kammala shirin.


Fitowarsu yayi dai² da isowar motocin sojoji guda biyu, yayin da yaya Abdul shima ya iso, nuna musu su huwailat yayi da yatsa, hakan yasa suka yo kansu, wanda hayaniyarsune ta dawo da zahrah daga gutun tunanin data shiga,saurin fitowa tayi ta nufi Yaya Abdul data hango a tsaye.


Yayin da gaba daya ma'aikatan wurin sun fito waje,domin ba ma idonsu abinci, yayin da wasu a cikinsu suka juyo satellites dinsu wurin, suka fara nuna shirin *live* a Tv.



Dana kai dubana wurinsu Huwailat da Doctor suleim kuwa, sojojine sun taso su gaba zuwa wurin Yaya Abdul.



Ko da zahrah ta karasa wurin Yaya Abdul, magana ta rada masa a kunne, wanda hakan yasa shi sakin murmushi, tare da nuna ma yaronsa alama da hannu akan su saki su Huwailat, bin umurnin shi sukayi suka sakesu tare da shigewa motocinsu suka bar wurin.


Hakan yasa su sauke wata karfaffar ajiyar zuciya, don har Sun fara tausayin kansu a hannun sojoji, daga kan da zatayi taga zahrah a gabanta tana jifansu da wani irin kallon raini, hakan yasa kirjinta ya buga, sannan ta saukar da kanta kasa.



Karasowa gefenta zahrah tayi tare da cewa" huwailat kinyi Babban kuskuren shiga gonata, amma ki jira yanxu wasan zai fara, ba duka ba zagi, amma sai nasa rayuwarki a cikin tashin hankali, sannan in kika kuma yin kokarin aikata mun wani mugun abun, zan fito duniyar in sanar da duniya ke shegiyace, 'yar zina, don uwarki Hajiya Asabe zina tayi da aurenta ta haifoki duniya, nasan baki san da haka ba, amma kije kin binciketa ba.





*Wash, na gaji.*


*Sorry for errors, banyi Editing ba* 🙏

*Rashin comment dunku yasa nadena typing kwana biyu*



*Kamar yanda zahrah ta fadi, nima nace yanxu aka fara wasan🤺🤺🤺*

*Comment*
*Follow*
*Share*


*_Fateeyzah_*✍

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 91 to 95_*


Wani kayataccen murmushi ta sakin mata, sannan ta wuce ta shige motar ta taja tabar wurin.


Ba karamin kaduwa huwailat tayi ba da zancen da Zahrah ta sanar mata, ta kasa motsi kwata², haka ta tsaya kamar gunki, don gaba daya ta rasa abinda take ciki, gani take garin na juya mata, Ganin halin da take cikine yasa Doctor Suleim karasowa gareta ya girgizata, take ta dawo hayyacinta, tare da saukar da wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan tace" Don Allah Doctor kayi sauri ka kaini Gida".


Daga mata kai kawai yayi sannan ya nufi motarshi kirar Peugeot 406,, yayin da ita kuma ta bishi a baya, budewa yayi ya zauna a mazaunin driver, ita kuma ta zagaya ta zauna a gefenshi, tukunna ya ja motar ya fice daga wurin.


Anan dai ma'aikatan wurin suka watse,kowa ya nufi bangarensa.


Sai da suka hau babban titin da zai kaisu Rigasa sannan taji hawaye na zubo mata, hakika zahrah ta kamo mata gyambon dake damunta acikin zuciya, sannan yau tabbas sai ta turke mama ta fada mata waye ubanta, saboda mutane da yawa especially dangin Babanta sunsha jifan ta da wannan kalmar ta shegiya, sai dai in basu je kauyen su *ANDI* dake karkashin karamar hukumar *KAURU* ba anan jahar Kaduna, annan ma ana yawan jifanta da wannan kalmar, tun bata son ma'anar kalmar ba, har tazo ta sani, amma in ta tambayi mama sai tace mata kiyayya ce ta dangin uba, amma a yau ta tabbatar da abinda ake fadi akanta, kasancewa ta ji abakin Zahrah, wacce ita shaida ce, zahrah bata karya, duk abunda zai fito bakin ta ta tabbata gaskiya take fadi.


Ta bangaren Doctor Suleim kuwa, ba karamin tausayi Huwailat ta bashi ba, kasancewa duk yaji maganar da Zahrah ta fadi mata, wanda su basusan da haka ba saboda a yanda zahrah tayi mata magana a hankali kamar mai rada, sai dai kunnanshi kamar na maciji yake wurin jiyo magana daga nesa.


A bangaren Zahra kuwa, ranta fes, don tun da ta sanar ma huwailat taji ta cikin farin ciki, koba komai itama zata dandani irin bakin cikin da ta sata ta hanyar hada baki da ita aka mata sharri, sai dai dayan bangaren zuciyarta, ta tausaya ma huwailat, don ko ba komai tana jin ta a cikin ranta ,don a 'yar uwa ta dauketa ba kawa ba, shi yasa duk da tasan wannan zancen sama da shekara biyar, amma bata taba gigin sanar da ita ba, amma wannan karon tayi haka ne saboda ta hana ta sukuni da kwanciyat hankali har ta samu ta aiwatar da binciken da zata yi.



Haka ta ci gaba da driving cikin farin ciki, yayin da ta kure motat ta da wakar *"pepper them"* , tana bin wakar tana kada kai.


Ko da ta iso gida, da gudu ta shige ciki inda ta tarar dasu Aunty Basma zaune a palour, zuwa tayi tai hugging dinsu a tare, sannan ta fashe da kuka, tana fadin" yau Allah ya bani ikon wanke kaina a gaban dimbin mutane, wallahi Aunty na dade inaso in je *Hikima Station*, amma sai in kasa, don ji nake kamar an daureni" ta karashe magana fuskarta na nuna damuwa.


Murmushi Aunty Naina ta yi a, sannan tace"tabbas Allah ne abun godiya zahrah, sannan kuma sai ki kira Baffa ki masa godiya, saboda ina tunanin ta sanadiyar maganin da aka miki ne kika samu aiwatar da haka".



Janye jikinta tayi sannan tace "Hakane fa Aunty, don Wallahi tun daga ranar na jini sakayau, duk wata damuwa da nake cikin ta gushe, kai dole inma Baffa da Alaramman nan Babbar kyauta".


"Yanxu dai kafin kyautar ki fara kiransa, kinga daga baya maje can kagarkon ki kai musu kyautar" cewar Aunty Basma.


Zaro wayarta tayi daga Aljihun Doguwar rigarta, sannan ta dan yi danne danne, inda ta saka kiran a speaker, take wayar ta shiga, zuwa can muryar Baffa ta Bayyana yana cewa" Assalamu Alaikum".


Fuskarta dauke da fara'a tace"wa'alaikumussalam, An wuni lafiya Baffa".


"Lafiya lau Zahrah, yanxu nake shirin kiranki in miki murna, naga abunda ya faru a Tv, hakika naji dadi da kika fito kika wanke kanki, Allah ya kara tsarewa" cewar Baffa.


"Amin Baffa, nima na kirane in maka godiya, don har da maganin da Alaramma yayi minne na samu kwarin gwiwar tunkaransu".


"Hakane Zahrah, Allah shine Abun godiya, Allah ya dada tsarewa, ya su Naina".


"Amin Baffa, su Aunty na lafiya, suma suna gaisheka".


"Ina amsawa, matar babanki usman ma ta haihu jiya, ta samu diya mace".


"Allah shi raya, insha Allahu zamu zo taron suna"..

Nan dai sukayi sallama kowa ya kashe wayarshi.yinin ranar sunyi shi cikin farin ciki ne, sannan haka masoyan zahrah su kayi ta kira suna taya ta murna, don da yawan mutane sun gamsu da hujjojin da zahrah ta gafatar, na kiran tamannah da tayi.


Bangaren su Huwailat kuwa, Ko da suka karaso gida, fita tayi da sauri tana masa godiya, sannan ta shige ciki, shi kuma ya ja motarsa yayi gaba.


Gidane madaidaici, wanda floor dinshi ya ji sumunti yana ta kyalli daga cana karshen gidan, bayine guda biyu daya toilet, daya bathroom, sai gefen dama da akayi kitchen madaidaici, daga tsakiya kuma parlour ne mai dauke da bedroom guda biyu.


Tun daga tsakar gidan tace kwala kira da karfi "mama!, mama!" har ta shige cikin parlourn, wande ke dauke da set din kujeru leather seat, kallon brown, sai madaidaicin plasma da recorder, kasan yasha tiles masu ruwan kasa, sai labule kalar ruwan kasa daya kewaye dakin.


Dakin dake bangaren dama ta shiga inda ta iske ta kwance akan lallausan italian bed dinta tana bacci yayin da tv keta faman aiki, fita tayi ta nufi kitchen dake kunshe da kaya,zaka dauka kitchen din Amarya ce, wuka ta dauka ta kuma komawa dakin tare da dan bubbuga mata kafafu tana Kiran "mama", firfigif ta tashi ta amsa da "baby kin da.....", ganin wukar da ke hannunta yasa ta kasa karasa fadin abunda tayi niya, harara huwailat ta watsa mata tare da fadin" wallahi yau ko ki fada min asalina, ko kuma in kasheki sannan nima in kashe kaina" tayi magana cikin kausassar murya tana mai nuna ta da wuka.



Pls manage, har yanxu ban jin dadi.





*Comment*
*Share*
*Follow*


*_Fateeyzah_*✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 96 to 100_*

Zaro ido mama tayi sannan tace" baby kinsan abunda kike yi kuwa, ni kike nunawa wuka, nice fa baby" ta karasa magana tana mai nuna kanta.


"Yes mama na san kene, ayau naji zancen nan a bakin wacce bakinta bai furta karya, duk abunda zai fito bakin zahrah da gaskene, don haka mama inaso ki fada min waye babana, don na tabbatar malam adamun da kike fadi ba shi bane mahaifina" tayi magana hawaye na zubowa daga idonta.


Dafe kirji mama tayi tare da fadin " na shiga uku ni Asabe, zahrah ce ta fada miki haka, so da yawa ina fada miki zahrah ba sonki take ba, amma kinki ji, yanxu gashinan, na tabbata ta fada miki maganar nan ne saboda son ta zartar da wani kuduri nata".


Cikin hargagi tace" mama ya isa haka, a kullun baki da aiki sai kushe zahrah a wurina, wanda gashinan sanadin haka kinsa naje na aikata abunda nazo ina dana sani, son zahrah a jinina yake, don jinta nake kamar 'yar uwa, don haka na baki nan da sati daya wallahi indai baki kaini wurin mahaifina ba sai na kasheki sannan in kashe kaina". Ta na gama fadin haka ta fice daga dakin.


Hajiya Asabe daura hannu akai tayi tare da fadin" na shiga tara ni Asabe, wai mai ke shirin faruwa dani ne.


******************************.


Bayan kwana biyu da faruwar haka sai ga Najib mijin Aunty Basma ya biyo ta, don yana ta kiran wayarta Ba ta dauka.

A main parlour aka saukeshi yayin da zahrah ta cika masa gabansa da snack da drinks sannan ta wuce daki.

Tun da Aunty Basma ta shigo ya zuba mata ido, don kwanakin nan da basu

Please Login or Register in order to submit comment