Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin in'ena,cikin sassarfa na karasa na rungume shi, gaba daya kuka muka saki, babu mai lallashin kowa, kamar an tsikare shi ya sakeni tare da fadin "karkice an kashemun lawyer", fuskata dauke da al'ajabi nace" ya akayi kasan ya rasu" cikin razana yake fadin" Ni'eema fara hada mana kaya da hanzari dole mu bar kasarnan, tunda dai suka kashe lawyer yanxu na tabbata kan zahrah zasu dawo, kuma inada tabbacin sun biyo ta kasarnan ", jin maganar nan nasa gaba daya kaina ya kulle amma ba daman tambaya saboda ganin yadda daddy da Aunty Ni'eema gaba daya hankalinsu ya tashi, cikin kankanun lokaci suka gama hada kayan da zasu bar kasar dashi, sannan suka fitowa, kallona daddy yayi tare da fadin"Habibty gobe ki koma Nigeria, don zamanki mai tsawo anan babban risky ne, idan kin koma ki kula da kanki, don nasan yanxi gareki zasu dawo, sannan kisaka ma kofofin gida da kofarki ta Asibiti security lock, wanda nan gaba zaki ga amfanin haka, ki gaishe da 'yan uwanki, insha Allahu ko ba nan kusa ba zan dawo gareku",tsurewa nayi da jin maganar daddy, Aunty Ni'eema kallona kawai tayi tare da girgiza kai taja danta ta fice tana kuka, wanda Daddy ma ya rufa mata baya yana mai hawaye, ina daskare a inda suka barni sai dai tashin motarsu da na ji, dakyar naja kafata na fice daga gidan tare da kullo musu kofawa baa kasancewa security lock ne a jikin kofar, tun daga ranar ban kuma jin duriyar daddy ba, don number shi ma bata shiga, wannan ya tabbatarmun da basu kasar dubai".






Gaba dayansu parlourn ya dau shiru kamar ba mutane a cikinsa.


Wani irin wulakantattacen kallo Aunty Basma ta watsa ma zahrah sannan tace " wai don ki raina mu kina so mu yadda da duk maganar da kikace ce, koda na yadda da labarin daddy amma har yanxu ban yadda baki cikin kungiyar Asiri ba"



Cikin tamke fuskar Aunty Naina tace" tabbas zahrah bata cikin kungiyar *PINK LADIES* saboda ban santa a ciki ba"


Gaba daya dakin aka dau salati, don maganar Naina ba karamin duhu ta sasu ba, dakyar Yaya Abdul ya bude baki tare da fadin" me kike cewa hakane Naina"



Wani makirin murmushi ta saki tare da cewa " tabbas sati daya wuce ina daya daga cikin members na kungiyar *PINK LADIES*, sannan kuma anan na kuma tabbatarwa da Hajiya sailuba tana daya daga cikin member na kungiyar mafiaaaaaaaaaa.






*Pls manage*

*Tofa🤔 ko ya za a ka*
*Ana zatan wuta a makera*




*Sorry banyi Editing ba nayi posting*




*Comment*
*Share*
*Followers*





*_Fateeyzah_*✍✍🙏



*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*Wannan page din nakuna, Doctor zahrah fansa*

*Ummulkairi*
*'yar Asali*
*Aisha Aj*
*Maman Abdul*
*Maman yusrah*
*Maman sayeed*
*N hidan*
*Raheenah*
*Rabi'atu(first lady)*
*Haseena*
*Munaiya marafa*
*Aunty Aisha Ashir*
*Mg*
*Farida bintu luqman*
*Fadiey*
*Zee baby.*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 71 to 75_*


Ba karamin firgita suka yi ba dajin zancen Aunty Naina, wanda yawancinsu sai da suka shiga shock , yayin da ita ko, ko a jikinta, ganin ba wanda yake da niyar magana a cikinsu yasa ta bubbuga table din dake gabanta, wanda karan yasa hankalinsu dawowa jikinsu.



Duk jarumtar da akasan soja da shi sai da Yaya Abdul ya zubar da hawaye, don gaba daya he is confused, gani yake kamar mafarki yake wanda yake addu'ar farkawansa.



Ta bangaren Aunty Basma kuwa, gaba daya zuciyarta ta kekashe, miyan bakinta ya kafe, yayin da idanunta suka soye, ji takeyi kamar kunnuwanta basu jiyo mata zancen dai² ba.



Yayin da Baffa ba abun da yake yi sai ambaton Allah a zuciyarshi, ga kuma Dada Ladiyo da inna karime da hawaye ke ta zuba a idanunsu, sauran yayyin daddy kuwa, sai karkada kai suke, alamun suna jinjina girman furucin da Aunty Naina tayi.



Bangaren zahrah kuwa suman zaune tayi don jin maganar tayi kamar saukar aradu, gani take Aunty Naina ta furta haka ne don ta wanke ta, wuf tayi ta tashi tare da karasawa wurin Aunty Naina ta durkusa tare da fadin" don Allah Aunty kar ki fadi haka, don nasan ba gaskiya bane, kawai nema kike ki wanke ni a gabansu Baffa" ta karashe magana tana mai hada hannunta wuri daya alamar roko.




Rungume ta tayi hade da fashewa da kuka tana fadin "wallahi habibty gaskiya nake fadi, ba karyab......." tunkudeta Zahrah tayi tare watsa mata wani irin kallo, hakan yasa ta katse maganar da takeyi.




Ganin haka yasa baffa gyaran murya tare da fadin" Naina ko zaki fada mana ya akayi kika shiga cikin wannan kungiyar Asiri".




Sai da ta dan ja lokaci sannan ta share hawayen dake bin fuskarta sannan tace" A lokacin dana tafi camping a osun state, a nan na hadu da wata yarinya mai suna falmata wacce dakin mu daya da ita, ba karamin ji da ita akeyi ba a wurin saboda tana da kyau, dukiya, sannan uwa uba ilimi don da first class tayi graduating daga bayero university, ba a dau tsawon lokaci ba muka kulla kawance tare da ita kasancewa nima taga alamun daga gidan masu shi na fito, don zan iya cewa ba karamar tsana falmata tayi ma talakaba, ana sauran kwana biyu zamu yi POP sai muke zancen posting dinmu da ita, inda take fadamin ai ita sai ta zaba, a lokacin maganarta bata wani bani mamaki ba kasancewa yanda kasarmu ta Nigeria take, indai kana da kudi zaka samu abunda kake bukata, amma ita sai ta kara da cemun ita ko a university bata attending din class sai exams, sannan a exams dinma ba wani abun kirki take rubutawa, annan kaina ya kulle har mamakin abunda ta fada yasa na tambayeta ya akayi ta fito da first class, ko biyan kudi take yi, anan take cemun tana d daga cikin 'yan kungiyar *PINK LADIES*, I am confused a lokacin don ban taba jin sunan ba, sai na nemi ta min bayanin kungiyar". Ta karasa magana tare da maida kallonta kan zahrah sannna ta ci gaba dacewa" *PINK LADIES* kungiya ce data kunsa 'yan mata masu ji da kyau, dukiya, an kirkire tane don samun ci gaba da daukaka a kan dukkan abunda kake bukata, sannna kungiyace ta 'yan mata zallah wanda inka shiga babu aure, babu bin maza, sai dai lesbianism in kana bukata, yawancin 'yan kungiyar *PINK LADIES* ne zaki ga budurwa tana hawa latest motoci, latest kaya,latest phones sannan zaka ga ana damawa dasu sosai a duniya, a Nigeria kungiyar bata cika karfi ba akan sauran kasashe especially india, Korea, china da America, wadanda duk karshen shekara suna meeting a tsakanin kashashen da members dinsu ke ciki".




Wata muguwar harara Aunty Basma ta watsa mata tare da fadin" sai kika bada wane a matsayin sacrificing" jin tambayar Aunty Basma yasa gaba daya suka zubo ma Aunty Naina ido.




Murmushi tayi mai kama da yake sannan tace" a *PINK LADIES* bada mutum ake sacrificing ba da dabbobine, don ko dana shiga ansa na bada bakar akuya, bakar kaza, bakar sanuwa da zakara mai ido daya, sai pink din yadi da...." ba tare da ta karasa ba Aunty Basma ta katse Cikin hargagi ta fara fadin " karya kike munafuka, ai ba haka zahrah ta badi sharuddan kungiyar ba, ke dai kice kawai kin bada mahaifiyarmu shi yasa lokacin har karin girma aka kara miki a wurin aiki, kuma wallahi zan bincika indai da sa hannunki akan mutuwar 'ya'yana wallahi zan dau babban mataki akanki, don bazan duba alakar dake tsakaninmu ba na jini zan sa......." cikin hargagi itama ta mike tare da fadin" dallah can rufe mana baki wai kin dauka tsoronki akeji ne da tunda kika zo kina ta mana hayaniya kin maida mana da gida kamar gidan kallo, yara ne na fada miki banda hannu a mutuwarsa, kije ki tuhuma uwar mijinki wanda take neman kujerar shugabar *black mafiaaaaans..*




Wani irin kukan kura Aunty Basma tayi tayo kan Aunty Naina, tsawar da Yaya Abdul yayi ne ya hanata karasa abunda tayi niya, gaba daya jijiyoyin jikinsa sun tashi, jikinsa sai karma yakeyi yayin da ya hade fuskarsa kamar hadari, wani rikitaccen kallo ya watsa musu tare da fadin" wai wani irin iskancine haka, kuke mana hayaniya kamar wasu kananan yara, wallahi duk ku shiga hankalinku in ba haka ba kuji a jikinku.



Gaba daya parlour yayi tsit, sai kallon kallo da akeyi tsakanin Aunty Naina da Aunty Basma.




Baba mahmud ne ya katse shirun tare da cewa "muna sauraranki Naina"



Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace" bayan na gabatar da wannan kayan sai kuma wanka da akamun da wani farin abu daga nan aka bani kayan sawa pink, a kungiyar *PINK LADIES* ba a shan jini sai dai yanka da akeyi a birne jinin sannan a soya naman a raba, bayan an gama min register da kungiyanne aka yi posting dina a ministry of finance, shine bayan na gama serving suka bani aiki mai tsoka a wurin kuma na cigaba da samun daukaka, a lokacin ne na ringa haduwa da manya mutane sai dai basu nema na da aure sai da fasikanci, hakan yasa na bana basu fuska kuma ban taba yadda da wace mace ba da sunan lesbians, na bar kungiyar ne saboda aure da nakeso inyi, wanda dama a tsarin kungiyar zaka iya fita a duk sanda kaso,sai dai za a raba dukiyarka daka samu sanda kake kungiyar kashi uku, kaba ma kungiya kashi daya".




Cikin alamun zakuwa Aunty Basma tace"to meye dalilinki na cewa hajiya na cikin kungiyar *black mafiaans*



Wani killer smile ta saki tare da cewa" saboda akwai kyakyawar alaka ta lesbianism tsakanin *black mafiaans da pink ladies,* but please mubar zancen nan haka don duk abunda zan kara fada miki zai iya bugar miki da zuciya. "




Gaba daya wurin suka dau salati yayin da Aunty Basma ta daskare a zaune.




Baba Muhammad ne yayi gyaran murya tare da fadin" Alhamdulillah tunda dukkan wani boyayyen kuli ya warwaru, sai dai muce Allah ya tsare ya kiyaye gaba, sannan Abdul, Basma, Naina da zahrah muna mai baku hakuri akan rashin kula da zumunci da muka yi, muka wareku ba tare da munsa ido akan tarbiyyarku ba especially Naina da Zahrah da basu aure muka barsu suke zama su kadai ba tare da muharramansu ba, don da munsa ido da duk haka bai faru ba, don haka muna neman yafiyarku".




"Baba ba abunda kuka mana kuma koda kunyi, mu mun yafe muku, muma kuma muna neman yafiyarku na rashin baku girmanku da mukeyi especially Zahra"cewar Yaya Abdul.



Murmushi baba mahmud yayi tare da cewa" baku da laifi Abdul, laifin duk namu ne, da mun jaku a jiki duk da baku yi haka ba".




Gyaran murya Baffa yayi sannan yace" Alhamdulillah tunda duk an fahimci juna, sai dai muce Allah ya yafe mana gabaki daya, sannan ke Basma banso kije ki tunkara sirikarki da wannan batun ki bari ayi bincike akai, sannan abu abun a hankali, sannan zahrah zamuje wurin wani Babban malami akan matsalarnan, sannan dangane da batun Aliyu zan ma usman magana sai su hadu da Abdul su gudanar da bincike akan inda Aliyun yake".




Cikin sanyin jiki Zahrah tace" Baffa kar ka sanar da Baba usman saboda da sa hannunsa a abunda ya faru da daddy".



*Rikita rikita kenan, akwai fa sauran rina a kaba.*

*Kuyi hakuri na rashin jina da kukayi kwana biyu.*


*Comment*
*Share*
*Follow*


*Fateeyzah* ✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

__________________________________

*_Page 76 to 80_*


Cikin rawar baki baffa yace" wa...... wa.....wata irin magana ne wannan kike yi zahrah?, tukunna ma wai ina kika ji wannan zance?, shi Aliyun ne ya fada miki haka?".


Dago ido tayi ta kallesa, sannan tace" lawyern Daddy ne ya fada mun kafin ya rasu, sannan dalilin gano haka da yayine shima aka shirya kashe shi ta hanya bata masa burkin mota, wanda hakan ya jawo masa accident, ba Baba Usman ne kadai ba, akwai wasu daga cikin manya sojojin kasar nan, shi dai kawai an hada baki da shine wurin aiwatar wa" ta karashe magana tana mai share hawayen da ya silalo zuwa kuncinta.


Cikin sanyin murya Yaya Abdul yace" Habibty kina mana magana a dukun kune, ki fito ki fili, ki sanar damu abunda ya faru".


"Abunda ya sanar dani kenan, don lokaci bai basa damar warware mun komai ba, but don Allah ina rokonku, Wannan maganar ta tsaya tsakaninmu kawai, har lokacin da gaskiya zata yi halinsa, mu san su waye sauran wadanda suke da hannu cikin wannan lamari, sannan mu kiyaye, don duk motsin da muke yi akan idanunsu ne" cewar Zahra


Cikin fushi da harzuka Dada ladiyo tace" inaahh!, wallahi bazai taba sabuwa ba, ina zaune a laka ma dan auta na sharri, bai ji ba, bai gani ba, yarinya 'yar kankanuwa dake sai jawo magana, daga Wannan kice wancan, ku kuma sullutaye, kuna zaune ana bata ma dan uwanku suna, sai kada kai kuke kamar wasu kadangaru, yanxu ko zan kirashi in sanar dashi" ta karasa magana tana lalubar 'yar nokia ta dake cikin lalita.


"Wallahi kika sanar dashi, sai naje media na tona masa asirin da ya dade yana birnewa wanda ke kanki sai kin ji kunyar fita a kagarko, ballantana ku kauye da dama jira ake" ta fadi cikin fushi.


Take Dada ta harzuka ta fara bambamin fada wanda baka jin maganar da take fadi, zahrah ce ta kuma gyara zama tare da cewa" oho dai, ke kika sani, ki karata".


" kunga zahrah wannan tone tonen ya isa haka, lokacin azahar yayi ku tashi kuje kowa yayi sallah, Baffa mu wuce masallaci" Baba Mahmud ya fadi yana mai mikewa.


Jin haka yasa Baffa da su yaya Abdul mikewa suka fice, yayin da itama zahrah ta tashi ta wuce dakinta ba tare da ta tanka ma kowa ba.


"Inna, Dada ku taso kuzo muyi sallah" Naina ta fadi tana mai wucewa dakinta ba tare da ta kallesu ba.


Inna karime ce ta mike tare da cewa" Dada taso muje, kinga lokaci yana wucewa".


"Inje ina, salon in shiga ciki nima a cinye ni lokacina bai yi ba, kinga makewa yin parlourn nan zan shiga inyo alwala ta" ta fadi tana mai tabe baki.


Murmushi inna tayi mai kama da yake, sannan tace" shikenan ni bari in shiga ciki, basma taso muje". Tayi magana tana mai dago basma da tun dazu take fada dogon tunani, don duk abunda ya afku daga baya ma bata san anyi ba.


Firgigif ta mike tare da bin bayan inna karime, wanda suna zuwa kofar dakin Aunty Naina ta kauce ta shige dakin zahrah, girgiza kai kawai inna tayi tare da shigewa ciki.


Dada ko tabe baki tayi tare da cewa" kwa dai ji da shi dangin mayu, ni dai kurwata kur wallah" ta karasa magana tana mai buga cinya, sannan ta tashi ta nufi toilet din parlourn.



Karfe biyu dai² little da Areef suka dawo daga Tahfeez da suke zuwa , direct dakinsu suka shige inda nan suka samu Nannynsu tana sallah, bajewa sukayi akan gado, suna jiranta ta idar.




Gaba daya matan sun hallara a parlourn, sai dai bamai kallon kowa tsakaninsu, don duk zuciyoyinsu a cinkushe take, buga kofar parlourn da ake yine kamar za a balla yasa zahrah ta tashi taje ta bude, hafsat ce ta shigo cikin kasaita tana wani yamutsa fuska, tare da daddaga kai, tana kallonsu a daddage, ganin ba wanda ya kulata yasa ta kulu don ko zahrah da taje ta bude mata kofa dawowa tayi ta zauna ta bi layinsu Naina da suka zuba ma hafsat ido suna kallonta.



Wani dogon tsaki taja tare da fadin" nazo karbar 'ya'ya nane saboda ban shirya sake wata nakudar ba, ballantana in haifi wasu bayan an cinyesu a cult" ta karashe magana tana mai yarfe hannu.


Ba wanda ya motsa daga wurin ballantana ta sa ran zasu tankata, ganin haka ne yasa ta kara kulluwa, balla musu harara tayi tare da nufowa cikin parlourn, direct stairs din dazai sada ka da dakunan su zahrah ta wuce, ganin haka yasa suka mike su uku a tare suka tunkareta, suna karasawa Aunty Basma ta daga hannu ta sharara mata mari tare da janyo ta ta watsar da ita a tsakiyar parlour.



Wani irin uban ashariya tayi tare da fadin" uban mai na miki da kika mareni, kawai don ina kishin 'ya'yana nazo daukansu shine zaki mareni".


Cikin bacin rai Aunty Naina tace "dallah rufe mana baki a wurin nan, ke don baki da kunya shine zakizo har tsakiyar parlourn ubanmu kina mana kallon raini, sannan har kina da bakin cewa kinzo iban 'ya'yanki, ina sha sune 'ya'yan da kika zabi aiki akansu, kika watsar dasu, yaran da tun suna jarirai baki san kashinsu ba, balle fitsarinsu, shine don baki da mutunci yanxu kika ibo kazamiyar kafarki kinzo daukansu, to su little dai 'yan gidan nan ne, in ma zamu cinye sun mai ruwanki, don haka ki tashi ki bar gidan nan tun kafin mu canza shawara mu muki dukan kawo wuka" ta karasa magana tana mai nuna mata kofa.


Yake hafsat tayi tare da fadin" zan fita amma kison da cewa, ko ta halin kaka sai na karbi 'ya'yana, don bazan barsu inaji ina gani su halaka ba sannan wall............" muryar Little ne ya katseta wanda ta fito daga daki tana cewa "wallahi ba zamu biki ba, ai ba son mu kike ba, tunda kike tafiya aiki ki barmu mu kadai da mai aiki".



Mutuwar tsaye tayi a wurin, don bata taba tunanin wannan kalmar zata fito daga bakin karamar yarinya irin little ba, wani murmushin bakin ciki ta saki tare da fadin" little ni ce fa, mummy ce fa kike fada ma haka".


Ko kallonta yarinyar bata yiba, ta juya ta shige dakinsu, wani lallausan murmushi zahrah ta saki tare da cewa" kin gani ko, a gabanki ma tace baza ta bikiba, don haka sai ki kara gaba, idan munyi farfesun su zamu kawo muki hanji".


Cikin sanyin jiki ta juya ta fice, ba tare da ta tanka musu ba, don yanxu ita ta 'ya'yanta take, domin tunanin yanda zasu dawo wurinta kawai.


Yatsina fuska Dada tayi tare da fadin" kun dai ji kunya wallaahi, ku baku aje 'ya'yanba, amma kuna so ku yanke alakar uwa da 'ya'yanta".


Ba wanda ya tanka ta, haka ta karaci suruntun ta tayi shiru, haka suka zauna har aka kira la'asar, ba tare da sun nemi abinci ba, don dukkansu babu mai jin yunwa, don abunda ma ya faru, yasa basu tunanin abinci.


Karfe hudu da minti sha biyar su Yaya Abdul suka shigo gidan dauke da ledoji a hannu mai sauke da tambarin *hikima restaurant,* umurtan zahrah yayi akan ta dibo plates, spoon da cups a kitchen, sannan ya wuce fridge dake dinning ya ibo drinks, tana dawowa ya mika mata leda biyu yace ta hada da plates ta kaima Nannynsu little.


Aunty Naina ce tayi serving din kowa, fried rice ne da chicken, sannan suka fara ci, ba wani da yawa suka ciba kowa ya ajiye da sunan ya koshi, zahrah ce ta kwashe kayan ta nufi kitchen da su.


Gyaran murya Baffa yayi tare da fadin" Abdul mu zamu wuce saboda lokaci yana kurewa, amma zan dawo jibi da ni da alaramma don ina ganin al'amarin zahrah akwai aljanu ko sammu aciki, sannan ke basma zan yi magana da mijinki akan ya barki zuwa jibi, don ko kin koma can gidan hankalinki bazai kwanta ba, sannan kowaccan ku tasa salama a zuciyarta kar inji wata magana ta fito daga baya" ya karasa magana yana mai mikewa.


Ganin mikewar sa yasa su Baba mahmud dasu inna karime mikewa, nan dai su zahrah suka musu rakiya har bakin mota, Baba muhammad yaja su suka tafi.


Bayan sun dawo parlour yaya Abdul yayi gyaran murya tare da cewa" yau abubuwa sun faru masu cike da mamaki da al'ajabi, hakika zahrah da Naina kun zo mana da wasu maganganu masu hargitsa kwakwalwa, wanda duk wani mai hankali sai ya daura su akan mizanin tunani, amma ina ganin hukuncin da Baffa ya yanke ya isa, sannan inaso in nusar daku, wannan fushi fushin da kuke yi tsakaninku bai kamata ba, dukkanmu nan 'yan uwane kuma gatan junan mu, don haka mu nemi yafiyar juna, sannan ke Basma abunda Naina ta fadi akan Hajiya Sailuba gaskiyane, don koni nasan da haka, amma nayi shirune saboda wasu dalilai da zan sanar dake nan gaba".


Ba abunda Aunty Basma keyi sai zubar da hawaye, nan dai yaci gaba da musu nasihohi tare da jan hankali.



Karfe shidda ya sallamesu tare da shiga ciki don duba ' ya 'yanshi, wadanda tun safe bai sa su a ido ba.



Daren ranar ba wanda yayi bacci a cikinsu,don kaurace ma idansu baccin yayi, yanda suka ga rana haka suka ga dare.


Washe gari, haka suka tashi suku², haduwa sukayi suka gyara gidan tare da yin breakfast, abun ka da 'yan uwa, nan da nan suka ware, kowacce ta sauke fushin da takeyi da 'yar uwarta, bayan breakfast suka yi wanka sannan ko wacce tabi lafiyar gado, don rama baccin da ba suyi ba.


Har yanxu a media babu latest news irin na doctor zahrah, duk social network din daka shiga cece kuce akeyi, yayin da wasu suna ganin tunda bata fito media ta kare kanta ba, ya tabbata abunda aka fadi gaskiya ne, inda wasu kuma suke ganin, ba class dinta bane tsayawa tanka² a media, don saboda hakan ma zubar da class ne.

Yayin da 'yan *FATEEYZAH NOVEL GROUP* kullin suke mata addu'a Allah ya saka mata, ya tona asirin wadanda suka aikata mata haka.



Washe gari, wacce ta kama monday, sannan ranar da Baffa yace zai kawo Alaramma, da wurwuri, suka tashi, suka kintsa wajen tare dayin breakfast, wanda already Mama Nanny ta shirya su little, an kaisu makarantar boko.


Karfe tara su Baffa suka iso, inda wannan karan tafiyar daga Baffa, Baba Mahmud, Baba muhammad, sai Alaramma suka iso, bayan gaishe² yasa aka dibo mai ruwa akofi, yayi Addu'a a ciki ya bama zahrah ta shafe jikinta, da goshinta, ai kuwa tana shafawa da 'yan mintoci sai ga jikin yana ta karkarwa, sannan nan da nan idonta ya koma ja, ganin haka yasa Alaramma ya dauko qur'anai guda biyu, ya mika ma Baffa daya, nan fa suka fara karatu, cikin mintuna kadan sai ga zahrah tana wani irin ihu tare da juyi a kasa, ganin haka yasa Alaramma ya kuma watsa mata ruwan addu'a tare da ci gaba da karatu, karfin ihunta ta kara sannan ta yi magana cikin wata katuwar murya" wayyo kana kona mu fa, don Allah ka dena ka tsaya muyi sulhu", jin haka ya sa suka dakata da karatun tare da dauko wani magani a cikin kwalba ya shaka mata, wani irin ihu tayi tare da buga kanta a jikin tiles din parlour.


Aunty Naina da Aunty Basma sun rungume juna suna ta kuka, don ba karamin tausayin zahrah bane ya shigesu, na yanda take ihu tana bige².

Gyaran murya Alaramma yayi tare da cewa" uban mai ya kawoka jikintaa" yayi magana muryarshi a kaurare.

Cikin katuwar murya zahrah ta amsa da "aiko ni aka yi jikinta".

Wata tsawa Alaramma ya buga tare da cewa" waye ya aikoka".

"Uhm uhmmm, nayi alkawarin bazan fadi ba"cewar zahrah cikin katuwa, muryata.


Kara shaka mata maganin nan yayi, wani rikitaccen ihu ta saki tare da cewa" wallahi zan fada, don Allah kabar konani"

"To fadi ina jinka"cewar Alaramma.


Wata irin zillo tayi tare da fadin" An aiko nine daga kungiya *Black mafiannns........*


*Wannan shine gumuzu, sorry ciwon kai ya hana in muku posting jiya, a mini hakuri.*

*Don jin yanda za a kare, ku biyoni daki² a

Please Login or Register in order to submit comment