Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tambayoyin da Mum Irfaan take mata tace" wannan kuma nabar ma kaina sanin, ina fatan tambayoyin sun kare, saboda nima amsar da take gareni ta kare" ta fadi hankalinta kwance kamar ba a gaban media take ba, wanda Allah kadai yasan dubbannin mutanan dake kallonta.




Murmushi tayi tare da fadin" yes sun kare, muna godiya". Sannan ta juya bangaren Doctor Suleim" ya kamata ka gabatar mana da kanka"



Cikin babbar muryarshi yace" sunana Doctor Suleim, Likita a Asibitin A.A. Abdulrahman memorial hospital kafin Doctor zahrah ta koreni".




"Ko zaka iya fada mana dalilinka na zuwa station dinmu"cewar Mum Irfaan.



" A kan maganar Doctor zahrah ne, Tabbas nima shaida ce akan Doctor zahrah tana daya daga cikin 'yan kungiyar Asiri".



Cikin zakuwa tace " ko zaka fada mana dalilinka na wannan kikirarin"


"Tabbas da idona naga doctor zahrah da kwarya cike da jini a hannunta a lokacin da aka kawo wata yarinya, wanda sanin da tayi na ganta ne ta koreni a Asibitin tare da mun sharrin, na karbi cin hanci na saida jini, wanda nayi sanadiyar mutuwarta.......".


Jin wannan batun ba karamin sandarewa zahrah tayi a wurin ba, don hakika maganganun huwailat basu wani bata mamaki, kasancewa duk mai hankalin da yaji maganar yasan kagene da hassada ke cinta, amma sabanin Doctor Suleim da shi yace ya ganta da kwarya jini a hannu wato yana nuna lokacin take performing din rituals.




Karar bugun kofa ne ya dawo da ita daga gajeran tunanin da ta isa, inda take jiyo muryar Yaya Abdul yana kiranta ta bude kofa tare da kikirarin in bata bude ba sai ya ballata.



Mikewa tayi domin tasan aikin gama ya riga ya gama, saboda tana da tabbacin su Yaya Abdul sun kalli hirar su huwailat, wanda sai mai zurfin tunani ne zai fuskanci yanayin maganar.



Toilet ta shiga tare da dauro alwala, sannan ta dauki Qur'an izu sittin ta daura akanta, don tasan rantsuwa dashi kawai zai iya fitar da ita daga zargin da 'yan uwanta zasu yi mata.



Cikin natsuwa ta bude kofar, ganinta da qur'ani a saman kanta yasa jikinsu yayi sanyi, basu hanya tayi suka shiga ciki.


Gyara tsayuwarta tayi tare da fadin" na rantse da All......".saurin karbar Qur'anin Aunty Naina tayi tana cewa" zahrah baki da hankaline kike kokarin rantsewa da Qur'ani".



Durkushewa tayi a wurin ta saki wani marayan kuka, duk mai imani ya ganta a wannan yanayin sai ya tausaya mata, sai da taci kukanta ta gaji, ba tare da kowa ya bata hakuri ba sannan tayi shiru.



Cikin muryarta ta kuka tace" wallahi Yaya duk abunda suke fadi banda masaniya akanshi, abu daya nasan da zaman kungiyar *PINK LADIES* a doron kasa, amma ban daya daga cikin members dinsu".



Sun kai tsawon lokaci ba tare da wani cikinsu yayi magana ba, ba kajin komai sai shasshekar kukan zahrah.



Yaya Abdul ne yayi gyaran murya tare da cewa" ina ga mubar wanna maganar sai Basma da su Baffa sun iso zuwa gobe, ko ma samu matsaya, don ni gaba daya kaina ya kulle zahrah".




A takaice ranar zahrah yanda taga dare haka taga rana, don kwata² bata rintsa ba, ji take dama Allah ya dauki ranta ta huta da wannan bala'in da take ciki, ta rasa mai ta tsare ma mutane da suke bibiyarta da sharri.




Karfe goma dai², gaba daya sun hallara a babban parlourn gidan, baffa, baba karime, Dada ladingo da gaba daya yayyin Abba.


Dayan bangaren kuma Aunty Basma ce wacce tun da tazo take jefa ma Zahrah kallon tsana don ta yi amanna harta 'ya'yanta da suke mutuwa dasa hannun zahrah aciki.


Gyaran murya Baffa yayi tare da fadin" bismillah zahrah, ke muke saurare, muna so ki wanke kanki daga maganar da babbar aminiyarki ta fadi akanki"






Idan ka ganta gaba daya ta sukurkurce ta koma wata kala, cikin jarumta ta tattaro gaba daya matsuwarta tare da fadin" Tabbas akwai wani sirri da ba wanda ya sani sai ni, amma ya zama dole in warwareshi a yau..........".




*Pls manage,*


*Don jin kullun da zahrah zata warware sai kubiyoni zuwa jibi.*





*Comment*
*Share*
*Follow*




*Fateeyzah✍*
*08161734851 whatsapp only*
[6/28, 9:21 AM] ~Fateeyzah✍✍:





*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 61 to 65_*


Nabar *Nigeria* cike da kewa, inda na wuce *New Delhi* dake kasar *India* , bayan isa ta, duk na gama wani processing da zanyi har na samu daki a hostel, inda already na tarar da *Tamannah* a dakin, sai ya kasance ni ce ta biyu, wanda a lokacin saura space din mutum daya.



A sati daya da nayi ba karamar shakuwa mukayi da Tamannah ba, saboda mace ce mai fara'a da sauran sabo, wanda ita 'yar garin *Kolkata* ne, sannan ta yawata da ni gurare da dama.



A sati na biyu ne Huwailat tazo makaranta inda aka kawo ta dakin mu, muka cika mu ukun, ba karamar murna nayi da kawota da akayi ba, kasancewarta 'yar Nigerian, kuma 'yar jaha ta, haka muka ci gaba da karatun mu cikin kwanciyar hankali, ga kuma shakuwar da ta shiga tsakaninmu especially tsakanina da Huwailat, hakan kuma ya farune saboda tausayinta da nake, kasancewa iyayen ta basu da karfi, don ta dalilin scholarship tazo makarantar, hakan yasa nake taimaka mata da abubuwan bukata, saboda a lokacin ba karamin kulawa nake samu a wurinsu mummy ba, ga kuma su Aunty Basma suma suna min sako akai².



A lokacin da muka cika wata uku ne, wasu seniors students suka zo mana tallan shiga kungiyar *PINK LADIES* , kamar yanda Huwailat ta fadi da farko dukkanmu uku mun amince da shiga kungiyar, amma jin sharuddan da aka saka mana yasa muka fasa shiga, hakan yasa suka ja mana kunne sosai akan indai muka tona musu Asiri zasu kashemu ko kuma su wulakanta mana rayuwa, wannan dalilin yasa muka manta ma da sunan kungiyar kwata².



Haka muka ci gaba da karatun mu cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba, har muka yi exams na farko, wanda ba mu dawo hutu Nigeria ba, kasancewa hutun bai da yawa, sai muka bi Tamannah Gidansu, muka yi hutunmu, hakika iyayenta sun karrama mu a tsawon lokacin da mukayi a gidansu, don a kalla munkai sati biyar, sannan muka dawo makaranta.



Bayan mun dawo hutu da sati biyu aka kafe mana result, sai dai gaba dayansu na fisu ci, hakan yasa Huwailat ta fara canza min, kwata² ta dena bani fuska, ganin hakan yasa na fita sabgarta na maida hankalina akan karatu, har muka yi jarabawara karshen shekara, sannan na shiryo na zo hutu Nigeria ba tare da nabi takan huwailat ba.




Ba karamar tarba mummy ta min ba, don tun daga airport mummy ta sabani a baya ta goya ni saboda tsananin murnar ganina, hakan ta kasance ma a gida, don hatta Aunty Basma na tarar da ita tazo tarbata, a ranar an nuna min gata, don kowa Habibty kake ji a bakinsa.


Haka nayi hutuna cikin natsuwa da kwanciyar hankali, ga uwa uba soyayya da kula danake samu daga wurin iyayena da 'yan uwana.



A hutun da nayi wata biyu na lura mummy na cikin damuwa hakan yasa take samun attack na ciwonta a koda yaushe, amma duk da na dame ta da tambaya amma taki fadamun abunda ke damunta , sannan duk tsawon hutun da mukayi Huwailat bata neme niba , nima kuma haka, har dai na gama hutuna na koma makaranta.


Bayan komawa tace na tarar da Huwailat acan, ashe ita bata je hutun ba, sai ta kuma zuwa gidan Tamannah, sai dai wannan komawar na samu sauyi a wurinta, don zan iya cewa mun koma kamar yanda muke da.



Wannan results dinma na fisu, sai dai duk basu tada hankalinsu, sai dai a dai² wannan lokacin naga alamun tabarbarewar tarbiya a wurinsu Tamannah da Huwailat, kamar tara samari, zuwa clubbing da sauransu, hakan yasa na ja baya dasu sosai daga gaisuwa ba wani abun da ke hadani dasu, nidai na maida hankali akan karatuna.



Wata shekarar ma da ta zagayo, nazo hutu gida, but anan ne na tarar da maganar Auren Daddy da Aunty ni'eemah, kasancewa acewar Inna karime wai shine wasiyyar da kakata ta bari, ba karamin tashin hankali akai a gidanmu ba, tsakanin mummy da daddy don gaba daya ta tada hankalinta, hakan yasa ta ringa samun matsala ta fannin lafiyarta, amma daddy ya dage akan shi bazai fasa cika wasiyyar da mahaifiyarshi ta bari ba, hakan ko yasa a kalla mummy sai data kwanta Asibiti so kusan hudu, sai dai alokacin likita ya tabbatar akan zuciyarta ta kumbura, ba karamin tashin hankali muka shiga ba, da ni da ' yan uwana, haka mukayi ta rokon Daddy amma yaki janye maganar auren ni'eema, hakan yasa muka fita shirginshi, muka ci gaba da kula da mummy hade da bata baki kan tayi hakuri.




Bayan auren Daddy da Ni'eema, abubuwa da yawa sun faru, ciki har da juya ma mummy baya da yayi, don hatta ni baya kulani don yace duk ni nake zuga mummy, kasancewa ni kadai ce a gidan don Aunty Naina lokacin ta fara aiki a Abuja.



A Wannan lokacinne ne kuma aka samu wasu 'yan ta'adda da suka tada tarzoma a cikin india, wannan dalilin yasa school Authorities dinmu suka ce, koma wa makaranta till further notice.


Bayan nanne Aunty Hafsat ta haihu, inda yarinya taci sunana fatima zahrah, sai ake ce mata little, anyi suna da kwana biyu, yaya yace in shirya in je kagarko in kai kayan suna.



Ko da na shiga gidan, dakin Inna karime na wuce, don ko da bama shiri da Aunty Ni'eema, ina respecting din inna karime, haka nayi ta sallama ba'a amsa ba, hakan ya sani shiga dakin kai tsaye don a tunani na babu kowa a dakin, sai dai ina shiga na fara juyo magana kasa², inna karime na fada ma kawarta, ai auren Daddy da Ni'eema da ta hada ba wasiyyar yaya fateema bane, kawai tayi haka ne don itama ta dangwali arziki, saboda malaminta ya fada mata ba karamin arziki gareshi ba, ita kuma kasancewa dama can ba kaunar mummy take yiba, kawai sai tayi amfani da wannan dama ta hada auren tare da taimakon malaminta saboda shi ya bata maganin mallaka yanda Aunty Ni'eema zata mallaki daddy don malamin nata ya fada mata zuciyar daddy cike take da soyayyarmu especially ni, ina gama jin haka na ajiye sakon ba tare dana jira komai ba na fice daga gidan na dawo kaduna.



Wannan shine dalilin da yasa na tsani Inna karime wanda duk cikinku ba wanda yasan wannan sirri sai ni, don ko Aunty Ni'eema ban ji tasan da haka, hakane inna ko a'ah?



Inna da tun da zahrah ta tabo fannita ta fara zubar da hawaye tace "hakane zahrah, duk abunda kika fadi gaskiya ne, amma kuma tun mutuwar Ni'eema nayi nadama".



Ba tare da zahrah ta kuma bi ta kanta ba ta ci gaba.


Tun da na dawo daga kagarko hankalina ya kasa kwanciya, kuma na kasa fada ma kowa, hakan yasa naga ya kamata in nemi wanda zai karya wannan asirin mallakar da inna karime tayi, amma duk yanda naso hakan, abin bai yiwuba, saboda a wannan satin ciwon mummy ya tashi, kuma na kira number Daddy a kashe, hakan yasa na nufi part din Aunty Ni'eema don ko zan ganshi, saboda tun daya aureta ya dena shigowa part din mu, don sai dai muji karar motarshi, ko zai fita ko ya dawo.




Ko da naje, sai da ta gama iyayinta sannan take sanar dani ai baya kasan, yana daya daga cikin commanders din da suka jagoranci tafiya peace keeping a kasar india, da tashin hankali na baro part dinta, ko da nazo na fada ma Mummy, nan jikinta ya rikice ta fara aman jini, haka na dauketa na kaita asibiti bayan na kira Yaya Abdul na sanar dashi.



Ko da likita ya dubata sanar damu yayi zuciyarta ta kusa bugawa, don haka ya mana wani kwatan can Asibiti a Egypt yace mu kaita nan a mata surgery.


Take yaya Abdul dasu Aunty Naina suka fara processing din fita da ita, ba karamin kudi suka kasheba, don Aunty Naina da Aunty Basma karkab suka yi ma Account dinsu.


Ana sauran sati daya mu tafi,ni da Yaya Abdul muka nufi yobe don sanar da 'yan uwan mummy halin da take ciki, amma ko da mukaje an rasa mai biyomu domin muyi jinyar mummy saboda acewarsu, tunda daddy yayi kudi ta watsar dasu, hakanan muka tattaro muka dawo.


Mun dawo da kwana daya Aunty Basma ta haifi fawaz dinta na farko, saboda rashin lafiyar mummy ba wani taron suna tayi ba.



Sati na zagayowa muka daga zuwa Egypt, dani da Yaya Abdul muka tafi, inda asibitine mai zaman kanshi na wani balarabe, amma kuma ya mika ragamar Asibitin ga Doctor Shareef, wanda haifaffan dan jihar kano ne.


Sun bincike mummy sosai, sannnan suka saka ranar da za suyi mata *surgery* , haka muka ci gaba da kula da ita ni da yaya Abdul, sannan muna waya dasu Aunty Basma sosai suna jin yanda ake samun improvement na lafiyar mummy, ta bangaren kagarko kuwa, da Baffa kadai muke waya don kusan kullun sai ya kira yaji lafiyarmu data mummy, Aunty Ni'eema kuwa bata taba kira ba, ballantana muyi maganar daddy.







Ana gobe za'ayi surgey, Aunty Naina da Aunty Basma suka zo, ba karamin dadi najiba da ganinsu, haka muka kwana muna sallah dani da Aunty Naina, muna rokon Alllah,akan surgery din da za ayi washe gari.


Shi kuma Yaya Abdul a ranar ya juyo Nigeria saboda kiran da ya samu a wurin aiki.


Washe garin ranar da wuri nurses suka zo suka tafi da mummy, haka muka rakata har bakin *theater* muna kuka, muna mata Addu'ar samun nasara.


Bayan kamar Awa daya sai gashi an fito da mummy ba tare da an mata surgery ba, sai aka shige da wani yaro, tunda aka fito da ita take aman jini da kyar nurses din suka tsayar dashi, don kwata² ba doctorn da yazo wurinta, hakanan mukayi jigum² muna kallonta har bacci ya dauketa.



Haka na ringa sintirin zuwa office din Doctor Shareef ban samunshi, har na hakura don daga baya an sanar dani ya tafi gida, kuma na nemi number shi ban samu ba.


Zuwa dare ko da mummy ta farka ta dan samu sauki don har tana iya magana, nan dai nurse tazo ta bata abinci tare da magani, sannan ta mata allura.


Wayewar garin ranar, mijin Aunty Basma da Hajiyarsa suka zo duba mummy, bayan gaishe² na fice domin duba Doctor Shareef, Aunty Naina kuma ta fita karbo b magani a pharmacy, yayin da Aunty Basma ta fita tare da mijinta, sai ya zamana munbar mummy tare da hajiya.


Ko dana isa office din, da kyar secetary dinshi ta bari na ganshi, bayan mun gaisa, sai na tambayeshi dalilin da yasa ba a yi ma mummy surgery ba, sai dai budan bakinshi sai cewa yayi, wai 'yan minister akayi replacing da ita, raina ba karamin baci yayiba, ban iya masa magana ba na bar office din.


Ko dana koma wurinsu mummy na tarar da ita tana ta aman jini don duk ta bata ma hajiya jiki, cikin hanzari na karasa gurinta na rike ta, dakyar na samu aman ya tsaya, sai dai gaba daya ta maida direction din kallonta zuwa ga hajiya, ganin nima ina kallonta yasa ta saurin mini sallama akan zataje ta canzo kaya ta dawo, sai dai fitar hajiya yayi dai² da fitan ran mummy.


Bata farga ba, sai ji tayi an kwasheta da mari, ko da ta dago kai, Aunty Basma ta gani tana huci,tare da cewa" mai kike son cewa zahrah, kina tunanin duk wannan tatsuniyar taki zata fidda kene, da kike kokarin lika ma Hajiya alhakin mutuwar mummy, alhalin ko da muka shiga ke muka tarar da gawar mummy a hannuki kuma jikinki kace² da jini".



"Ke Basma kar in kuma jin kina jifan 'yar uwarki da wannan mummunan kazafin"cewar baffa wanda yayi magana cikin bacin rai"



Haka Aunty Basma ta koma ta zauna yayin da take wani huci kamar macijiya.



Yaya Abdul ne yace" Habibty ci gaba, ke muke sauraro" ya fadi muryarshi cike da rauni.


Sai data ja majina tare da share siririn hawayen dake bin kuncinta, sannan tace" babban sirrin da nake so sanar daku shine Daddy da Aunty Ni'eema suna nan suna rayuwa a doron kasa don basu mutubaaaaa".



_Tofa🤔, wannan shine *CHAKWAKIYA* Book din Mum Irfaan._

_Don jin yanda za a Kare, sai jibi in Allah ya kaimu._




*Comment*
*Share*
*Follow*





*_Fateeyzah_*✍✍✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*Inalillahi wa'ina illaihir raji'un, Allah ya jikanki, ya gafarta miki zunubanki, ya haskaka muki kabarinki, ya raya miki zuri'a, in tamu tazo Allah yasa mu tafi a sa'a😭😭😭*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 66 to 70_*



Gaba dayansu sun shiga cikin firgici da jin maganar Zahrah.


cikin rawar baki Aunty Naina tace" anya kuwa kwakwalwarki bata tabu ba zahrah?, kin taba jin wanda ya mutu ya dawo?, koko damuwar da kika shigane yasa kwakwalwarki juyewa?." Ta fadi tana mai zaro idanu.


Dajin zancen Aunty Naina ko gaba daya dakin ya kaure da hayaniya, Kowa yana fadin albarkacin bakinsa.


Zahrah kuwa wani makirin murmushi ta saki, don ta riga ta shirya ma wannan rana.


Gyaran muryar da Baffa yayi ne yasa parlourn yayi shiru, maida hankalinsa yayi kan zahrah tare da fadin" ko zaki iya fada mana dalilin da yasa kika ce mahaifinku na raye.


Fuskarta dauke da damuwa tace" bayan likita ya tabbatar mana da rasuwar mummy, sai na kira yaya a waya na sanar dashi, anan ne ya ke fadamin dawowar daddy, raina ba karamin baci yayi ba dana ji ya ambato daddy, amma kasancewa mutuwar mummy ce a gabana yasa nayi shiru. Haka muka gama cike ciken takardu har muka samu aka bamu gawarta, muka dawo Nigeria aka yi jana'izar mummy aka rufeta, hakika duk wanda yaga daddy a wannan lokacin yasan mutuwar mummy ta bige shi, amma ni wata irin tsanarshi ce ta shiga zuciyata, ranar da zai tafi Abuja shi da Aunty Ni'eema ba irin maganar da baimun ba, naki kulashi, wanda a hanyar dawowarsa ne aka sanar da hatsarin motar da suka yi, wanda aka ce ya mutu".


Cikin zakuwa Baffa yace "zahra'u duk mun san wannan, ki fada mana dalilin da yasa kika ce Aliyu yana raye".



Wani lallausan murmushi ta saki tare da fadin" tabbas Daddy na da rai, don har na hadu dashi munyi magana ta fahimtar juna".


Wani kallo Aunty Basma ta watsa mata tare da fadin" mu dai ba wannan muke son ji ba, ki fada mana ta yadda har kika san yana raye kuma har kuka hadu".



"Bayan sanarwar rasuwarshi da kwana uku, sai aka fara min text message da wata number ta kasar dubai, kullin safiya za a turo mini text na gaisuwa, tun ina share abun, har yazo in naga ni ina kokarin kiran number sai in jita a kashe, Ana sauran sati biyu in koma makaranta sai ga Alert din dubu dari uku ya shigo wayata, duk a daukana mistake ne na bank, sai dai da safe sai ga text message ya shigo da wannan number akan kudin da aka turo inyi siyayya dashi na koma wa school, sannan already an biya kudin makaranta na, hankalina ba karamin tashi yayi ba har na sanar da Yaya Abdul tare da nuna masa number, duk irin binciken da yayi bai samu komai ba, wannan dalilin yasa ya zolaye ni akan ko wani boyayyen masoyi na samu, ganin dai na kasa gano mai min text message sai na share maganar".



Sai data sauke numfashi sannan ta ci gaba da cewa" ko dana koma makaranta haka abin ya kasance, sannan duk wata ina ganin Alert na 1000 rupees, a haka na maida hankali kan karatuna wanda a wannan lokacinne na fara shaye² saboda rashin bacci da nake samu da daddare saboda tunani dana sa a gaba, wanda hakan har ya fara taba karatuna. Tun dana koma ban dawo Nigeria ba sai dai Yaya Abdul dasu Aunty Basma da suke zuwa mini, kuma har a wannan lokacin ba a fasa turomin da text message ba tare da alert duk karshen wata, a haka har na gama karatuna mukayi *oat taking* na dawo gida, bacin na dawo gidane lauyan daddy yazo mini da document din Asibiti, akan daddy ya bada contract din ginin ne da saka machines da sauran kayan aiki tun kafin ya rasu, wanda sai a lokacin aka gama, sannan ya kawo mana dukiyar daddy aka raba gado aka ba ma kowa nashi, sai dai cewar da yayi daddy yabar wasiyya akan kar a raba da gidanshi, a bari kowa yazo ya zauna, ba karamin farin ciki nayi ba da Asibitin nan wanda haka yasa duk wani bakin daddy da nake gani na share shi a raina sannan na masa addu'ar samun rahama ".



Muryar shi cike da kosawa hade da bacin rai yaya Abdul yace "duk mun san wannan, abunda muke bukata muji kawai a wurinki ya akayi Kika san daddy na raye".



Wani kayataccen murmushi ta saki tare da ci gaba da cewa" wata rana ina zaune a Asibiti, sai aka kawo lawyern daddy yayi Accident, hakika a lokacin yana jin jiki, don dakyar muka tsayar da jinin da ke zuba a kafarshi, anan ne yake sanar dani daddy yana da rai amma kar in fada ma kowa saboda na jikinmu sune munafukan mu, hatta adress din daddy ya bani na dubai tare da number waya, sai dai bai kara cikakken minti talatin ba, ya amsa kiran ubangiji, sai dai muce Allah ya jikansa, hakika na kadu da abinda lawyer ya fadamin, sai dai inda na kuma tabbatarwa da zanyi saving din number da ya bani na daddy, sai naga number iri daya ce da wadda ake turo min text message shekarun baya, wanda yanxu an dena turo min da safe sai dai duk ranar jumma'a".


Sai da ta dan tsagaita na some seconds, tukunna ta ci gaba da cewa" bayan rasuwar lawyer da sati biyu, sai nayi shirin zuwa dubai, inda ku kuma na rufe ku akan zanje yin wani course ne a babban Asibitin Abu Dhabi City na sati biyu, bayan na sauka a Abu Dhabi sai na nemi hotel kasancewa saukar dare nayi, sai washe gari dana shirya na dau shatar mota tare da bama drivern address din ya kaini har kofar gida, ko dana kada bell din kofar, na dan jima kafin azo a bude, wanda wani kyakyawon yaro da bazai wuce shekara biyar ba yazo ya budemun tare da tambayata wanda nake nema cikin halshen turanci, kallo daya zaka masa kaga tsantsan kamaninsa da Yaya Abdul, ganin haka yasa gaba daya na kame a tsaye na kasa bashi amsa, shima ko sai ya zuba mini ido, ganin ya dade bai dawo ba yasa mahaifiyarshi biyoshi, wanda maganarta ce tasa na dawo cikin hayyacina, hada idon da mukayi da ita yasa ta kira sunana cikin mamaki, nima da mamakin na tsaya kallonta don gaba daya ta canza inba kayi mata sanin sosai ba baza kace Aunty Ni'eema bace, don ta kara kyau ga wani fresh da ta kara, ganin na kasa magana yasa taja hannuna da na yaron nan ta shige damu ciki tana kuka"ta karasa magana muryarta cike da rauni.



Gaba daya palourn yayi tsit bakajin komai sai kukan Inna karime da ke tashi a hankali, sauran ko fuskarsu zaka kalla kaga tsantsan son jin karshen labarin zahrah.



"A zaune akan wheel chair na taradda da daddy a zaune, ganina da yayi ba karamin firgita yayi ba, don kamar mai tsoron fadin sunana haka ya fada

Please Login or Register in order to submit comment