Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to kasan dayake ba layina bane shiyasa banyi maganaba, Allah ya kara sauki ya kuma tsare gaba".


Sai daya dan muskuta yace " Amin Habibty, amma inaga gidanki zan wuce da ita sai inna ta ringa kula dasu don zan dauko Areef shima, sai ki zabar musu daki"


"Kai wallahi yaya har naji dadi, nima na ringa jin motsin mutane" tayi magana cikin shagwaba.


Murmushi ya saki sannan yace" jiya munyi waya da Basma take fadamun abunda ya faru na videon ki a social media, kinsan ni ban cika hawa ba ballantana in gani don ita ta turomin ma" ya karasa magana fuskarsa so serious.


Cikin natsuwa tace "hakane yaya kuma a binciken danayi na gano Doctor Suleim ne ya dauka ya watsa a social media".


"Waye Doctor Suleim?, sannan meye hadinki da shi?"


Hankalinta a kwance tace" Doctor ne a Asibitinnan, amma na koreshi saboda samunshi dana yi da cin Amanar patient".


Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta fada masa.

Take ya hade fuskarshi tare da cewa "wai ke wace irin yarinya ce zahrah, bakisan ta haka kike creating din ma kanki enemies ba, kinsan yanda aiki keda wuyar samu a kasarnan, amma ke kenan kullun cikin korar Ma'aikata saboda wani naki dalilin can, kega mai tausayin talakawa ko, wallahi ina fada miki, inkika ci gaba da haka wata rana sai kin rasa ingantattun ma'aikata".


"Haba yaya, rai fa ake magana, inban tsaya n kula da hakkin patient ba mai zanyi?" Tayi magana tana gwawgwalo idanu.


"Hmm Habibty kenan baza ki taba gana abunda ake fada miki ba, sai nan gaba, don wallahi in kika ci gaba da haka sai kinga abunda yafi wannan, yanxu kuma mai kika shirya yi ma Doctor Suleim din don nasan ba hakura zakiyi ba"


Sai da tayi murmushi sannan tace" na shirya kaishi kara kotu ne, don abi mun hakkin tozartani da yayatani da yayi, tunda dai inada proof na abinda yayi"ta fadi sounding so serious.


Cikin tamke fuska yace" wallahi karki fara indai ba kinaso ki kara tona ma kanki asiri ba, wandan da basu son da videon ba ma susan dashi, kewai baki yafiyane, duk abunda aka miki kice sai kin rama, to wallahi bada yarda taba, kar in sake inji kin kai maganarnan court in ba haka ba zanyi mummunar bata miki rai kinji na rantse, tunda naga Alamar kamar shaye shayen da kike ke saki iskanci, codien na fada miki ba daidai ba" yana gama fadin haka ya fice daga office din.


Cike da rashin kunya tace" haka kawai don bakai aka bata ma suna ba, wallahi ko ban kaishi kotu ba, sai na rama a bun......" karar telephone dintane ya katse mata magana.


Dauka tayi tare da fadin"yes (pause), ok I am coming".


Cikin hanzari ta cire hijab din jikinta tare da daukan veil din ta ta fice daga office din cikin sauri.



Direct *ICU* ta nufa wanda tana shiga ta nufi wurin patient din da tayi ma surgery, ganin computer na wani irin kara, ga kuma Doctor Haroon na danna kirjin patient din yasa gabanta ya fadi, wanda adai dai lokacin gaba daya computer tayi wani kara, Ganin hakan yasa Doctor Haroon kada kai tare da janyo mayafi ya rufe ma patient din fuska.


Take jikinta yayi sanyi,wanda dakyar ta daga kafarta tabar wurin ta nufi office, ba karamin kaduwa tayi ba, don wannan shine karin farko datayi surgery aka mutu, a kullin cikin success take, wanda ta wannan dalilin ne yasa Asibitinta yayi suna.

Cikin dauriya ta saka hijabi ta tada sallah.


Tana idarwa ta tattara kayanta ta fice daga office din ta nufi *ICU*, ko da taje an dauke gawar a wurin, wasu takaddu ta cike ta mika ma Doctor Haroon sannan ta nufi gida.



Ko da ta isa ta tarar da Yaya Abdul acan dasu Little, gaisawa kawai sukayi da Inna tare da nuna mata dakinsu da kitchen sanna ta wuce dakinta.


Wanka kawai tayi tabi lafiyar gado, amma kwata² ta kasa bacci don dazaran ta kulle idon ganin patient din da tayi ma surgery take, haka dai ta karasa ranar cikin tunani da bacin rai.


A cikin satin nan ba karamin tashin hankali Doctor zahrah ta shiga ba, don duk wanda zata saka hannu da sunan masa surgery sai kaga ya mutu, amma in wasu team dinne sukayi sai kaga anyi surgery very successful, hakan ya fara damunta, don yanxu wannan zancen shike yawo a Asibitin tsakanin nurses da Doctors.


Yau Asabar, tana kwance a daki, kasancewa bata je Asibiti ba don ta tashi da wani zafaffan ciwon kai, turo kofar da akayine ya dawo da ita daga gajeran tunannin data shiga, ganin Aunty Naina yasa tayi saurin tashi tare da fadin" oyoyo Aunty Nai......) kasa karasawa tayi don ganin goshinta nade da bandeji.

Cikin kaduwa tace" Aunty mai ya sameki?".

Murmushi tayi wanda daga ganinsa kasan bai kai zuciya ba tace" yanxu nazo Habibty, ki taso kizo parlour su Yaya na jiranki" tana gama fadin haka ta fice daga dakin ba tare da ta jira amsawarta ba.


Wayarta kawai ta dauka sannan ta fice zuwa parlour, tana saukowa tafara cin karo da Akwatina, hakan yasa gabanta ya fadi, daga kan dazata yi kuma ta saukesu akansu, suna zaune su uku, yaya Abdul, Aunty Basma, sai Aunty Naina, hakan ya kuma karyar mata da zuciya don tunda taga Aunty Basma tasan ba lafiya ba, don ko Yaya Abdul rabonta dashi tun ranar da yazo office dinta, don ko yazo gidan bai nemanta, yaranshi kadai yake nema, don fushi yake da ita, ita ma kuma fushi takeyi dashi.


Cikin sanyin jiki ta gaishesu ta samu wuri ta zauna.


Yaya Abdul ne yayi gyaran murya tare da fadin" Basma nace ki biyo Naina ne kuzo saboda shekaran jiya ta kirani take sanar dani ta ajiye aiki zata dawo gida, dana tambayeta dalili, sai tace in tazo zata fadamin, shiyasa na nemi da kema kizo, yanxu Naina ke muke sauraro".


Maida kwallar dake barazanar sauko mata tayi tare da fadin" yaya tun dana fara Aiki a Abuja nake fuskantar matsaloli, kasanacewa wasu ganin ba tare da iyayena nake zaune b suke min kallon kamar bai zaman kanta, a lokacinne kuma Allah ya daura min son Aure, amma duk mazan da suke zuwa wurina ba da aure suke zuwaba da iskancinsu suke zuwa ciki kuwa har da na wurin aikina, yaya naga manyan masu kudi da 'yan siyasa da yawa sun nemeni amma bana basu hadin kai, wata shidda da suka wuce akwai sanatan da ya nemini da auran mutu'a, amma naki yadda, haka ya ringa bina, saboda shi har na canza gidan haya na koma quarters din wurin aikinmu, yaya wannan karan Allah yasa kwana na na gaba, don manajan *NNPC* nayi dating kuma har muka kulla Alkawarin Aure, wannan dalilinne yasa matarshi ta turo min da 'yan daba har cikin gidana suka min duka, sai makwaciyata ce ta taimaka ta kaini Asibiti, shiyasa ni kuma naga gwara inbar aikin in dawo gida, don banga amfanin kudin dana ke ta tarawa ba ba miji ballantana 'ya'ya"


Gaba dayansu jikin su yayi sanyi, da kyar Aunty Basma ta bude baki tace" Amma Naina baki kyautamin ba, duk abunda yake faruwa muna gari daya baki taba fadamin ba, nifa 'yar uwarkice uwa daya, uba daya, me yasa haka?"


Basma kiyi hakuri, a duk sanda nayi kokarin fada miki, inajin wani iri, saboda kema baki taba fadamun matsalar ki ba, infact bari in fada muku, dukkanku babu wanda ya taba tambayata rayuwata a Abuja, gaba daya kun wareni kamar ba 'yar uwarku ba, kun hada kanku ku uku, especially kai Yaya Abdul indai bani na kiraka ba baza ka taba daukar waya ka kirani ba, Haka Habibty kema, wani zubin ma inna kiraki baki dauka, kuma baki taba zuwa kin ga missed call dina ki kiraba, ta yaya kuke tunanin zan fada muku matsalata tunda baku bani time dinku ba, Basma tun da nakoma Abuja baki taba tako kafarki kinzo wurina ba, koda so daya" ta karashe magana cikin kuka.


Gaba dayansu hawaye suka fara, har yaya Abdul duk jarumtarshi sai da yayi kwalla don tabbas zancen Naina ya taba masa zuciya, saboda shi kanshi yasan bai kyauta wa.

Cikin sanyin murya yace" Naina duk mun amsa laifinmu, hakika banda kalmar dazan baki hakuri, saboda girman laifin da muka miki, kiyi hakuri, duk laifina ne, insha Allahu zamu gyara, yanxun wani aiki kikeso ki fara anan sai a nemo miki, don nasan in Habibty ta tafi Asibiti baza kiji dadin zamaba".



"Bana bukatar ko wani aiki, aure nake bukata, yaya I am not getting younger, yanxu inada 28 years a duniya, wallahi yaya ko me garuwa ne ka saman mun indai zai aureni zan siyar masa gida da mota sananna in bude masa shopping mall" ta fadi idonta na zubar da hawaye.


Cikin kuka Zahra tace "Aunty kiyi hakuri da izinin Allah zaki samu miji, amma zamanki a gida bazai yiwuwa ba, gwara ma mu ringa tafiya Asibiti dake tunda akwai vacancy na accountant sai ki fara aiki anan, kinga atleast anan ma zaki iya dacewa da samun miji anan kasancewa wurine na mutane".



"Zahrah anya kuwa, saboda wani zakiga yana sonka, amma ganin yanayin aikinka,motar hawa, gida da suturarka sai yaga kamar kafi karfinsa" tayi magana cikin muryar tausayi


Anan Aunty Basma ta saka baki tare da fadin" Abunda Habibty ta fadi is a good point, inkina gida waye zai ganki har yace yana sonki kiyi auren, kawai dai muyi addu'ar Allah yasa haka yafi zama Alkhairi".

Gaba dayansu suka amsa da Amin, nan dai yaya Abdul yadan musu nasiha tare da umurtansu su hada kai su dena wasa da zumunci, sannan ya tafi.

Gaba daya suka hadu suka gyara ma Aunty Naina dakin dake kusa dana zahrah, ranar sai da suka raba dare suna hira, wanda wata hirar suyita dariya wata kuma su saka kuka especially in suka tabo ta iyayensu.


Washe gari, bayan breakfast Aunty Basma ta tafi ta barsu cike da kewa, yinin ranar sunyi shine cike da farin ciki, ga wata sabuwar kulawa da suke nuna ma su Little da Areef.



Ranar monday da wuri zahrah ta tafi Asibiti don tana da Surgery din dazata yi karfe bakwai.


Kamar ko wani lokaci ta canzo kaya ta fito wanda Already amma patient din Allurar *Anaesthesia*, wukar surgery aka miko mata zata fara kenan patient din tafara wata jijjiga tana sumbatu, gaba daya nurses da Doctors din tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah, don haka bata taba faruwa ba a rayuwarsu, saboda indai akayi allurar *Anaesthesia* tana kashe jikine, wani ihu da ta kwala ne ya dawo dasu hayyacinsu, mikewa patient din tayi ta shako Doctor zahrah tana fadi cikin wata irin murya"shegiya mai *God'iyarmu* tayi miki zaki kasheta, ki koma ki fada ma Shugabar ku jinin *God'iyarmu* yafi karfinku"

Babu wanda yayi kokarin kwatarta sai dai hasken flash din waya da kake gani......



*Yanxu aka fara wasan*

_Kudai biyoni cikin littafin Doctor zahrah don jin yanda za a kare._




_Gaskiya bazan samu damar ringa muku posting kullunba, zandai daure in ringa yi so uku a sati ko so hudu, don abubuwa sun min yawa🗣️🗣️🗣️_


*Comment*
*Share*
*Follow*



*Fateeyzah✍*


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 51 to 55_*


Ba wanda yayi yunkurin cetonta har sai da ta sumar da ita, wanda yayi dai² da zuwan Doctor Haroon kasancewar tunda ga office dinsa ya jiyo karar patient din.



Dakyar ya kwaceta a hannunta kasancewa rikon data mata bana wasa bane, saurin daukar ta yayi ya nufi *ICU* da ita don gaba daya numfashinta ya dauke, taimakon gaggawa ya fara bata, tare da sa mata *oxygen* , sannan numfashinta ya daidaita.




Ko da ya koma *theater* *room* patient din ta dawo normal har sun maida ta gado, ba tare da bata lokaci ba ya hada nashi team din suka fara mata *surgery* din saboda zuciyarta tana gab da bugawa, ba tare da sun samu wata matsala ba suka yi aikinsu successful, sannan suka fito da ita zuwa dakin hutu.






Har zuwa wannan lokacin Doctor Zahrah bata farfadoba, amma numfashinta na fita dai², ganin hakan yasa Doctor Haroon ya kira number Yaya Abdul ya sanar dashi abunda ke faruwa.





Hankalin Yaya Abdul ba karamin tashi yayi ba da jin abinda ya faru da Zahrah, don har sai daya zubar da hawaye, nan yasa a tara masa Doctors da Nurses din da abin ya faru a gabansu, ba tare da bata lokaci ba suka hallara, tambayansu yayi akan su bashi full detail din yanda abinda ya faru, nan Doctor Kabeer ya labarta masa komai ba tare da tangarda ba.





Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa" ina umurtarku da wannan abun ya zama sirri a wurinku, bansan jin maganar nan a bakin wani na waje face mu daku, saboda......" karar wayarshi ce ta dakatar dashi daga maganar da yakeyi.





Picking din call din yayi tare da fadin" hello Naina, ya akayi (pause), what!, (pause), ki shirya ki tawo Asibitin yanxu, ina jiranki" yana gama fadin haka ya kashe wayar.





Kallon Doctor Haroon yayi fuskarsa daure yace" A matsayina na Director Asibitinnan na baka izini ka bama dukkansu suspension har sai ranar da komai ya daidaita, sannan kar abawa kowa salary acikinsu".




Ba karamin firgita sukayi da jin zancen Yaya Abdul ba, cikin rawar baki Doctor Haroon yace "yallabai me kuma ya faru haka da zafi, ba yanxu ka gama Addressing nasu ba akan......"





Saurin katse shi yayi ta hanyar cewa" babu amfani addressing nasu saboda aikin gama ya riga ya gama, don yanxu Naina ta kira take sanar dani taga abunda ya faru a whatsapp, wannan yana nuna daya daga cikinsu ya fitar kenan, don haka ka basu suspension sai na gama binciken da zanyi".






Cikin bacin rai Doctor Kabeer ya kallesa tare da cewa" gani nayi ko mun watsa ba wani abu bane, tunda dai ai abun ya faru, sannan ba mu zaka bincika ba, kanwarka zaka bincika, don alamu sun nuna tana da hannu a mutuwar da ake tayi last week a Asibitin nan, wata kila ma tana daga cikin 'yan *cult* ne waya sani, don haka ka fara bincikar kanwarka kafin mu " yana gama fadin haka ya juya cikin sauri ya fita daga cikin *ICU*






Jin maganar Doctor Kabeer ya sa Yaya Abdul ya fusata, nan da nan idonsa ya wani irin ja, a harzuke ya kalli Doctor Haroon yace" inason Information din wannan yaron, don wallahi in bai yi wasa ba sai na shigar dashi kotu akan sharrin da yayi wa Habibty, nawa take da har zai danganata ta wani *cult*.






"Kayi hakuri yallabai, abi abun a sannun" cewar Doctor Haroon tare da kallon sauran nurses din sannan yace "kuje ku jirani a *board hall*".





Karfe uku Aunty Naina ta shigo a rude, ganin Habibty da *oxygen* ba karamin firgita tayi ba, kallon Yaya Abdul dake zaune a gefen gadon yayi tare da fadin" don Allah Yaya ka fadamun yadda abin nan ya faru, ji yanda fuskarta ta kumbure kamar wadda tayi Accident".






Zuciyarshi cike da kuna ya labarta mata yanda abun ya faru, ba karamin tausayi zahrah ta bata ba, don acewarta da kananun shekarunta wadan nan abun suke ta faruwa da ita.





A takaice zahrah bata farka ba sai karfe biyar na Asubahin washe garin ranar, wata kara ta kwala tana fizge² tare da fadin" please help me, she want to kill me".




Karar da tayi shi ya tashi Aunty Naina daga bacci, cikin sauri ta nufota tare da fadin" yi shiru Habibty, ni ce a kusa dake bazata ta kasheki ba"





Jin hakan yasata tsagaitawa da kukan da take sai dai hawaye dake bin idonta, cikin rashin kwarin jiki tasa hannu ta cire *oxygen* din dake hanjinta tare da mika ma Aunty Naina, cikin sauri ta karfa ta ijiye, sannan tazo ta taimaka mata ta shiga bayi tayi wanka tare da dauro Alwala, sannan ta fara rama sallar da ake binta a zaune.





Bayan ta idar da sallah Aunty Naina ta hada mata tea tasha sannan ta koma ta kwanta.





Karfe takwas dai², Doctor Kabeer ya shigo, sai da ya mata ya jiki, sannan ya dubata ya mata allura tare da bata magani, sannan ya fita.





Fitarshi da mintina kadan Yaya Abdul ya shigo, ganinshi ne Zahrah tasa rigima akan zata tafi gida, nan ya umurci Aunty Naina ta hado kayansu su wuce don shima hankalinsa yaki kwanciya akan zamanta a Asibitin, don a zuwa yanxu labarinta ya karade gari, don shi kanshi sai da ya kashe waya don kiran da ake masa don jin gaskiyar lamarin.





Sai da suka biya ra office dinta, ta dauki abinda take bukata, sannan ta bar ma Doctor Kabeer alhakin kula da Asibitin kasancewa shine mataimakinta.




Koda suka fito, bakin asibitin cike yake da 'yan jarida, hakan ba karamin mamaki yaya Abdul yayi ba,don ko san da zai shigo basu a wajen, ganin fitowar Doctor zahrah yasa gaba dayansu su kayo kanta cikin sauri ko wanne na kokarin yi mata tambaya, inda da kyar Aunty Naina ta tura ta cikin mota ta tada motar, duk da haka sun baibaye motar, dakyar ta samu ta fice daga Asibitin.




Tun da suka hau kan hanya Zahra take kuka, don ganin yanda 'yan jarida suka hayayyako mata sai kace wata barauniya, duk yanda Aunty Naina bake bata baki ta kasa dakatar da hawayen dake zuba a idonta, don ta riga tasan kowa ya riga yasan abunda ya faru.



Ko da suka iso gida, bata bari Aunty Naina ta gyara parking ba, ta fice daga motar, dakinta ta nufa tare da saka key, zubewa tayi akan gado ta fashe da wani irin marayan kuka, duk wanda ya ganta a lokacin sai ya tausaya mata.



A can ko Asibiti, da kyar Yaya Abdul ya lallaba 'yan jaridan nan suka watse tare da musu alkawarin zai neme su idan sun gama bincike, daga nan ya nufo gida.



Duk yanda suke buga mata kofa hade da magiya ta ki bude dakin, sannan duk wani code da suka san zata iya sama kofar sun gwada amma yaki buduwa, haka dai har suka gaji suka kyaleta, don a cewar Yaya Abdul inta ji yunwa zata bude, don ranshi ba karamin baci yayi ba.




A bangaren Zahra kuwa, duk tana jin bugun kofar da suke hade da magiya, amma tayi biris da su, don a halin da take ciki bata bukatar wani a kusa da ita, cikin haka bacci ya kwasheta.




A can Asibiti kuwa, gaba daya patients da masu jinya sun tsere ba tare da sun jira sallama ba, don gaba daya sun tsorata da abinda ya faru, ba karamin tashin hankali akayi da security ba kafin su barsu su fita, shima sai da suka samu izini daga Doctor Kabeer sannan suka bude musu gate, ganin haka yasa ya sanar da Yaya Abdul, inda shi kuma ya bada umurni a sallami kowa a kulle Asibitin.



Sai wurin karfe uku ta farka, nan ta lallaba ta shiga toilet tayo wanka tare da dauro alwala, shafa mai tayi, sannan ta zura doguwar riga ta tada salla.


Jin cikinta ya fara juya wa alamun yunwa, yasa ta bude kofa ta sauko kasa domin neman abunda zata ci, ko da ta fito babu kowa a parlourn, hakan yasa ta nufi kitchen ta zubo abincin da ta samu a warmers.



Duk yadda Yaya Abdul yaso Zahrah ta masa bayanin abunda ya faru taki, don daya taso da maganar zata hau kuka, ganin haka ne yasa ya kyalleta, sai dai yana nan yana bincike akan lamarin.




Yau sati daya da faruwar lamarin, wanda in kaga zahrah gaba daya ta rame ta dashe,zaka dauka wacce tayi jinyar wata biyu ce.



Kira ne ya shigo wayarta na bakuwar number, cikin rashin kwarin jiki ta saka hannu ta daura tare da fadin "hello"


"Ki kunna Tv, tashar *HIKIMA STATION,* zaki ga abun mamaki" kit aka kashe wayar.


Ba tare da shawara da zuciyarta taba ta kunna tv tare da searching din *HIKIMA STATION*, fuskar Huwailat ne ta bayyana a fuskar tv, gefenta kuma Doctor Shareef ne, ba karamin kaduwa tayi ba da ganinsu.


"Sunana huwailat Adamu Bello, ni ce babbar kawar Doctor zahrah wacce munyi karatu da itane a kasar india, Tabbas Zahrah tana daya daga cikin members na *cult* wadda ake kiran kungiyar da *PINK LADIES*................


*Tofa🤔, yanxu aka fara wasan, ku dai ku biyoni.*


*comment*
*Share*
*Follow*



*Fateeyzah* ✍
*08161734851 whatsapp only*


[6/25, 9:34 AM] ~Fateeyzah✍✍: *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 56 to 60_*


Jin wannan zance na huwailat ba karamin tada ma Zahrah hankali yayi ba, da duk wani masoyinta da yake kallo a wannan lokacin, saboda tsananin firgicin da ta shiga bata san sanda ta saki remote da phone dinta da yake hannuta a kasa, ji kake yi "fas" alamun fashewa.




Wata daddadar murya na tsinkayi tana cewa huwailat " ko zaki iya yi mana cikakken bayani akan kungiyar nan?" ko da nakai dubana ga mamallakiyar muryar sai na ga mum irfaan *( garararin rayuwa, chakwakiya)* , wadda ita ce shugabar *HIKIMA STATION*.




"A lokacin da muka yi wata daya a makaranta, sai wasu daga cikin seniors dinmu suka kawo mana tallar wanna kungiya, wanda kungiyace da ke kara ma mutum power tare da bude masa kwakwalwa ya zama zakaran gwajin dafi, sannan yawancin members din kungiyar lectures ne da students daga courses daban², take muka amince da batunsu nida zahrah, amma kuma da aka lissafo mana sharuddan sannan da sacrifices din da zamu ma kungiyar, sai muka ga baza mu iya ba, wannan yasa muka ki yadda, amma sai dai sun ja mana kunne akan in muka sake muka tona musu asiri karshen mu yazo kenan" ta fadi fuskarta dauke da damuwa.



"Ko zaki iya fada mana sharuddan nan" cewar Mum Irfaan.




Share gumin dake fuskarta tayi tare da fadin" sharuddan sune, a lokacin da ka shekara biyu a kungiya zakayi sacrificing din mutum uku, wanda suka kasance makusantanka, daya ya kasance namiji, daya mace sannan dayar mace mai ciki, daga nan kuma duk bayan shekara biyu zaka yi sacrificing din jariri ko karamin yaro namiji , shima kuma ya kasance makusantanka, sannan kuma duk sanda suke bukatar jini zasu sanar da kai domin kabasu abinda suke bukataka, indai kana cika wadannan sharuddan zaka samu kudi da daukaka a bangaren aikinka, inda sunanka zai je inda baka tsammaniba".




Saukar da ajiyar zuciya mum irfaan tayi tare da cewa"Kin fada mana ke da zahrah kunyi rejecting din wannan kungiya, ko zaki fada mana dalilin da yasa kika ce kuma zahrah tana cikin wannan kungiyar ta *PINK LADIES*".




"Sati biyu da suka wuce, nayi waya da kawarmu mai suna *TAMANNAH* wacce dakin mu daya da ita a lokacin muna ajin farko, bayan mun gaisa ne sai muke tambayar juna yanayin aiki, anan sai take cemin ai itama ta mallaki Asibitin kanta, anan na mata murna tare da ce mata, ita da zahrah dai Allah ya daukakasu, anan take sanar dani ai suma suna cikin kungiyane ita da zahrah, shiyasa naga sun samu daukaka haka, hakan da naji ba karamin sanyayamun jiki yayi ba, amma kuma a lokacin bazan iya tunkarar zahrah akan nasan wannan zancen ba"



Cike da tu'ajjabi Mum Irfaan tace" kina nufin kice Zahrah ta cika wadannan sharuddan da kika lissafa"





Cikin rashin damuwa da abunda zata furta tace" tabbas ta cika wannan sharuddan da na lissafo,sannan ta samu zama a cikin wannan kungiya".




"Zamu iya sanin dalilinki na tabbatar mana da zahrah ta cika wadannan sharuddan?"cewar Mum Irfaan.



Sauke ajiyar zuciya tayi tare da cewa" wannan amsar baza ku jita a bakina ba, don ance waka abakin mai ita tafi dadi".




Cikin kwarewa da gogewa a harkar aiki tace" meye sa kika bukaci zuwa media kika fallasa wannan sirri na Aminiyarki".



Cike da kosawa

Please Login or Register in order to submit comment