Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi jarabawa, inda Daddy yayi a jaji, kawu Usman yayi a Zaria, wanda duk suka fito da sakamako mai kyau, daga nan kuma suka tafi training.




bayan wata tara akayi passing out inda Daddy ya fito a second lieutenant, daga nan kuma aka hada shi acikin special force, inda suka tafi peace keeping a kasar libiya.




Kawu usman shima anyi passing out shi kuma akayi posting dinsa Benue.




Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da dadi gobe akasin haka.




Bayan sheka biyu abubuwa da yawa sun faru, ciki har da rasuwar Adda da samun girman da Daddy yayi bayan sun dawo daga peace keeping, da kuma rasuwar sarki wato mahaifin ladiyo, da auran dasu kawu mahmud, kawu Muhammad, kawu Abubakar sukayi, wanda duk suka tare da matansu duk a gidan Galadima.






A wannan lokacinne aka yi posting din Daddy jahar yobe inda anan ya hadu da momyna.




Garin garzarma, garine dayake karkashin karamar hukuma damaturu dake jahar yobe, garin ya kunshi yaruka biyu wato fulani da shuwa, wanda yawancin fulani sunfi yawa.





Aishatu wato mummyna diyace ta sha hudu a cikin jerin 'ya'yan hakimin garin, waddata ta kasance diya ta uku a wurin amaryarshi mai suna salamatu, ta kasance kyakyawace wanda daka ganta sak balarabiya, macece mai matsifar kishi ga saurin fushi amma kuma tana da saurin sauka, ta kasance 'ya mafi soyuwa a wurin Hakimi kasancewa an haifeta da matsalar ciwon zuciya, hakan yasa duk ahalin gidan suke bata kulawa sosai saboda gujewa tashin ciwontaa.





Ta hadu da mahaifina ne a lokacin da sukaje biki danmaturu, cikin kankanin lokaci soyayya ta kullu a tsakaninsu, har manya suka shigo ciki aka saka rana, cikin wata shida akasha biki inda Daddy ya biya sadaki da sulallen gwal, nan aka dauki Amarya daga garzarma aka kawota kadarko, dakin Adda aka gyara aka saka Amarya.



Zaman nasu dai sai godiyar Allah, don gaba daya matan gidan sun hade mata kai, inna karime ne kawai me janta a jiki, duk da haka bata sa damuwa a cikin ranta ba saboda tasan yanayin ciwonta.



Watanta biyu a Gidan ta samu ciki, zokaga murna wurin daddy, lokacin haihuwa nayi ta haifo kyakyawan danta wanda yaci sunan Galadima wato Abdulrahman, tsakanin yaya Abdul da Aunty Basma shekara daya da rabi, sannan tsakanin Aunty Basma da Aunty Naina shekara biyu da wata daya.


Kwasam bayan haihuwar Aunty Naina sai ga inna karime da ciki ba karamar murna baba Abdulaziz da Galadima suka yi ba, don har ya riga ya cire rai da samun haihuwa, duk wani matsoyinsu sai daya taya su murna badda Dada Ladiyo da Ahalinta, don gaba daya ta gama koya musu bakin halinta.



Wata tara na cika ta haifo kyakkyawar 'yarta wacce aka rada ma suna ni'eematullah, don acewar baba Abdulaziz babbar ni'ima ce wannan Allah ya basu, don a lokacin yana da shekara sittin da uku a duniya, inna karime kuma nada hamsin cif cif.



A wannan lokacinne kuma aka dawo da Daddy kaduna nan cikin jaji, nan ya tattaro mummy da su yaya Abdul suka dawo, wannan shine silar dawowar mu kaduna.



Makaranta mai kyau da tsada ya sasu both islamiya da boko don yace babban burinshi yaba 'ya'yanshi nagartattan ilimi.



Bayan shekaru hudu, a lokacin inkaga su mummy baza kace sunyi zaman kadarko ba, sun yi kyau ga wayewa, saboda Allah ya kuma daga Daddy har ya sayi fili ya fara Gini a Unguwar Rimi, adaidai wannan lokacinne mummy ta samu cikina, zo kaga murna wurinsu especially yaya Abdul don acewarsa mummy zata haifar masa dan uwa, haka suka ci gaba da tattalin cikina har ya kai wata tara, sannan na fito duniya, ba karamar murna sukayi ba, don yaya Abdul ma cewa yayi gwara da mummy bata haifo namiji ba, ranar suna aka rada min sunan Kakata wato fateema zahrah, amma gaba daya gidan tun daga kan Daddy har yaya Naina da Habibty suke kirana ba karamin soyayya suke nuna min ba.



Shakarata biyu, muka tare a katon mansion din Daddy ya gina mana, don gidane na kece raini saboda duk unguwar babu gida irin namu.


Bayan shakara sha hudu, abubuwa daya wa sun faru masu dadi da akasin haka, rasuwar galadima da samun karin girman da daddy yayi.

Alokacinne yaya Abdul ya tafi aikin soja, wanda Daddy yace sai yayi dole badon son ransa ba, da shirin bikin Aunty basma da akeyi wanda zata auri dan minister, sai Aunty Naina data tafi bautar kasa, a shekaran ni kuma na gama secondary school inda akemin processing din tafiya kasar India domin karatun medicine.


Biki akayi na kece raini don ba karamar dukiya Abba ya kasheba, don dai ya kankaro ma Aunty Basma girma awurin dangin miji don da farko uwar mijin taki yadda sai da tazo taga Aunty basman tukunna ta yadda da auren, nan dai aka kaita gidan mijinta dake maitama.



Bayan passing out din su yaya Abdul ne, shima akayi bikinsa da Aunty Hafsat wacce itama Babanta Aminin Daddy ne.


Bayan bikinne ni kuma na tattara na tafi india, nabar Nigeria cike da kewan iyayena da 'yan uwana.




Karar hon din da tajine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga, cikin sauri ta taka burki don da ta buga ma wani mai mota, saida ta samu relief sannan ta ci gaba da tuki.



Isarta Gidan Aunty Basma ne kuma ta samu wani Tashin hankali, don mijinta ya dauko mai magani akan zai turare gidan da magani, duk wani mai hannu a mutuwar 'ya'yansa zai yi composing(tona ma kai Asiri) da kansa.



Tofa yanxu xa a fara game din, kar ku yadda kuyi missing.

_Shin yazata kaya a gidan Aunty basma tsakanin mai magani da mutanen gidan?_


_Kar ku manta bamu gama jin tarihin Doctor Zahra ba_

_Duk ku biyoni cikin Littafin_ *DOCTOR* *ZAHRAH*



*More comment, more posting*


*Comment*
*Share*
*Follow*



*Fateeyzah* ✍✍
*08161734851* *whatsapp only*





*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 36 to 40_*

Abin mamaki harda Aunty Basma ta yarda da batun mijinta, nan fa malam yasa asamo rushin wuta, batare da bata lokaci ba sai ga rushi an kawo, nan dai ya gama tsibace tsibacenshi, sannan yace a kullo gate din gidan.


Saukar maganarta naji akaina kamar saukar aradu, daga kai nayi domin inga mai magana, wata hamshakiyar mace ce a tsaye 'yar duma², kallo daya zaka mata kasan naira ta zauna, cikin gadara da isa take magana.



"Wai Najib mai yasa baku da dangana ne, nace ku Mika lamuranku ga Allah, ku yadda shiyake karban ran yaran nan, saboda ban isa da kaiba shine zaka je ka kawo wannan dirty witch din da sunan malam, idan kura na maganin zawo tayi ma kanta mana, don haka indai ni na tsugunna na haifeka ina so ka tattara wannan shirmen kayi dashi waje tun kafin in saba maka" ta karashe magana hade da juyawa tabar wurin ba tare da ta kalli kowa ba.


Hajiya Sailuba Kasim kenan Mahaifiyar Najib mijin Aunty Basma, cikakkiyar 'yar siyasace tun bayan rasuwar mijinta daya rike mikamin senator da minister kafin Allah ya mai rasuwa, danta daya Najib, shi yasa ba karamin sonsa takeyi ba, macece mai fuska biyu, wanda a zahiri take nuna ma mutane ita ta kwarai ce, amma a ba'ini kuma, Allah kadai yasan iyakar abunda take aikatawa, sannan macece mara yadda, don ita kanta bata yadda da kantaba, ballantana ta yadda da wani, a yanxu haka tana rike da mukamin mai bawa shugaban kasa shawara akan harka mata da kananan yara.


Jin haka yasa malam ya tattara kayansa ya fita, nan ma Yaya Najib ya bi bayansa, ganin haka yasa Aunty basma ta fashe da wani irin marayan kuka, gaba daya ta fita hayyacinta sai sumbatu takeyi wanda baka iya jin mai take cewa, ganin haka yasa Doctor Zahra wadda tun zuwanta take tsaye a wurin karasawa wurinta tare da tada ita takaita daki ta zaunar bakin gado.



Anan na samu damar zagayawa gidan, Gidane hadadde wanda aka ginashi kamar ba a san zafin nema ba, koko ince kamar masu shi ba sa tunanin mutuwa, tsayawa fasalta muku gidan bata bakine, don ko a Abuja mallakar Gidan nan sai wanda yaci ya tada kai.


Dakin Aunty Basma na ko ma, nan na tarar dasu su uku, Aunty basma, zahrah da wata katuwar mace, wanda kallo daya zaka mata ka gano kammaninta dasu Zahrah.


Fuskarta dauke da hawaye tace" wani irin hakurine banyi ba,haba Naina dole fa inyi kuka yara uku suna mutuwa kuma duk ranar dasuka cika shekara biyu a duniya, kinsan wannan ai dakwai alamar tambaya aciki, Wallahi akan rasuwar fawas na kuma tabbatar akwai abu akasa, lafiya lau fa muka kwanta dashi, wurin karfe uku kawai sai naji ya tashi yana kuka yana ta fizge²,wallahi cikin kannanin lokaci sai ga jini na fitowa ta bakinsa, nan danan kanshi ya karye, kuma adai dai lokacin naji motsi a bayan window na, nayi kokarin tashi in duba, amm ganin yanayin da fawas ke ciki na kasa tashi in barshi" ta karashe magana cikin shashsheka"



Idonta dauke da kwalla tace"Basma duk da haka hakuri zakiyi, ki tattara komai ki bar ma Allah ikonsa, ki karbi kaddara a yanda take, mun rasa iyayenmu ma gaba daya, amma mun hakura mun barma Allah, sannan kafin fawas kin rasa biyu, don haka don Allah kiyi hakuri muyita addu'a, Allah sa masu ceton mune".

"Wallahi abunda yasa nafi damuwar da mutuwar Fawas, saboda irin Mutuwar mummy yayi da yanda take fizge², har yanda jini ya gangaro ta bakinta wallahi duk daya".

Zahrah ne taja dogon numfashi tare da fadin" gaskiyane Aunty Basma Mutuwar su Fawas akwai alamar tambaya especially fawas dinki na biyu, don dana dubashi babu alamar jini gareshi, shi yasa lokacin har na tambayeki ko yayi rashin lafiyane kafin birthday din kikace a'ah, ko dazu kafin a rufe fawas nayi kokarin ganin gawarshi amma hajiya tace an ruga an masa wanka bazan iya ganin saba".


Cikin firgice tace"kin gani ko Naina ai na fada miki akwai rina acikin kaba"

Naina ce ta kalli zahrah hade da watsa mata harara sannan tace" wai meye hakane habibty , maimakon ki kwantar mata da hankali, amma ke kike tada mata dashi, wallahi kar in kuma jin wannan maganar ta fito daga bakinki, don baki da hujjar fadin haka".



A takaice dai, nan aka bar magananr, inda aka ci gaba da karban gaisuwa amma ba karamin sa ido takeyi akan Hajiya sailuba da Yaya Najib ba, don tana ji a jikinta akwai wani babbab al'amari a tsakanin su biyun don yanda suke behaving kwata² kamar mutuwar bata damesu ba, don sigma Najib din duk dauko mai maganin da yayi a ganinta duk burgane.


A rana ta biyu Yaya Abdul yazo gaisuwa ya tafi, don shima kwata² jininsa bai hadu da Najeeb ba ballantana uwarsa Hajiya Sailuba, wanda suma ta bangaren su kusan haka ne, don kallon mage da bera suke ma juna.


Ranar da akayi uku da rasuwar, a ranar zahrah take shirin dawowa kaduna don tana da surgery din da zatayi ranar monday.




Tana cikin hada kaya, wayarta tadau ringing, ganin mai kiran yasata ta saki wani lallausan murmushi tare da daukar wayar sannan tace " Hello besty kin manta dani"


Daga can aka amsa" da ba haka bane besty, I am busy ne this days, amma ba lokacin bayani, ki duba IG ko facebook kiga videon dayake yawo" kit ta kashe waya ba tare da ta jira amsawartaba.



Cikin rawar jiki ta kunna data tare da shiga IG don tasan nan zai fi mata saurin dubawa, cikin mintuna kadan sai ga video a inbox dinta mzz huwailat( besty) ta turo mata, cikin sauri ta shiga videon, fuskarta ce ta bayyana aciki tana ta zuba masifa, nan da nan ranar ta dawo mata, ba kowacce rana bane illa ranar data kori doctor Shareef a Asibitinta, amma abun duba shine, gaba daya an yanke video, sai akabar inda take ma nurses masifa kan Doctor Shareef, da inda ta umurci securities su fita dashi, fuskarta dauke da mamaki don tama kasa furta komai.



Cikin jarumta ta fara duba news feed inda nan ta tsince videon hade da dubban comment wanda duka kusan na zagine tare da aibantawa, ganin haka yasa ta saki wayar ba tare da ta sani ba.






Is just the start of the battle, follow don't miss.






*Comment*
*Share*
*Follow*





*Fateeyzah*✍





*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)



*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

_This page is for you, my Facebook fans, inajin dadin comment dinku da likes, nima ina yinku._


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 41 to 45_*


Gaba daya she is speechless, don ta rasa ma ta ina zata fara.


banko dakin da akayine ya dawo da ita daga gajeran tunanin da take, Aunty Naina ce ta shigo hannunta rike da phone dinta, fuskarta dauke da bacin rai.

A harzuke ta fara magana" zahrah meye wannan nake gani a media?, kinsan ko abunda kikeso ki jawo ma kanki a matsayinki na specialized doctor".


Kasa bata amsa tayi don gaba daya kanta ya kulle, tunaninta wani irin tashin hankaline yake zuwa musu daya bayan daya, an gama na Yaya Abdul aka koma Aunty Basma, yanxu kuma ita, tabbas tana zargin cikin nurses din da abun ya faru a gabansu daya ta dauki videon, saboda dai dagasu sai patients a wurin, wanda kuma su suna ji da ciwonsu tasan baza su iya haka ba, amma koma waye, she will find out.


Dago kai tayi ta kalleta tare da fadin" Aunty Naina nafiki sanin Abinda zaije ya dawo, amma what I ama going to do, abin nan ya riga ya faru, kuma nabar ma Allah shi zai saka min"ta karasa magana tana kokarin maida kwallar datake barazanar saukowa daga idonta.


Cikin sanyin jiki Aunty Naina ta dafa kafadunta tare da fadin"shikenann Habibty, amma ki ringa kula don yanxu mutum ake kiwo ba dabba ba, kiris ake jira kayi abu mara kyau za a fara yayataka, sabanin inda mai kyau kayi, wani ko addu'a da fatan Alkhairi bazai maka ba, amma me ya hadaki daa wannan patient din da kika masa haka?"

"Aunty kina nufin baki gane Doctorn Shareef ba?"ta tambayeta fuskarta cike da Al'ajabi.


"Wallahi Habibty ban gane saba in ba da kika kira sunansa, duk naga ya canza be, gaba daya ya rame ya fizge kamar bashiba, ai habibty bazan taba mantawa dashi a rayuwa taba, mutumin da ta dalilinsa, ko ince sanadinsa muka rasa mummy, ai kema kinsan don kamaninsa ya canza ne, amma da ina zance ban ganesa ba" tayi magana fuskarta cike da Alhini.



Sai data saki wani lausassan murmushi sannan ta fara bata labarin abinda ya faru.


Cikin farin ciki tace" kin min dai² habibty, ai kadan ya gani wallahi naso ace ina wurin abinnan ya faru, da ko dayake kwance rai a hannun Allah sai na nuna masa shayi ba ruwa bane" ta karasa maganar sounding so proud.


Kwashewa da dariya zahrah tayi tare da fadin"ai wallahi shiyasa nake sonki Auntyna, baki bari ta kwana balle tayi tsami".


Aunty Basma ce ta shigo dakin hannunta rike da waya tare da fadin" Naina, Zahrah kunko ga Abunda na gani a whatsapp?" Tayi tambaryar fuskarta dauke da damuwa.


Hada baki sukayi wurin cewa" Abunda muke zance kenan kika shigo".

"Wallahi nima Honey ya turomin yanxu, wai inga videon dayake yawo, amma Zahrah me kike gani zamuyi?, saboda kinsan kina da makiya da yawa, yanxu in ba a dauki mataki ba, wani shima zaije ya kumayi, kuma alamu sun nuna career dinki ake so ayi running" ta fadi cikin alhini.


Sai datayi jim sannan tace" hakane Aunty, don nasan in badon wannan dalilin ba blackmailing dina zasu yi dashi su karbi kudi, da dai nabar maganar, amma karku damu zan bincika CCTV cameran dayake ward din, don duk cikin staff din Asibitin ba wanda yasan dasu inba niba, kuma ina kyautata zaton daga cikin nurses dinne wani yayi videoing din".


"Toh habibty, Allah ya tona Asirin wanda yayi haka, kuma kici gaba da kiyayewa, sannan ki rage saurin fushi don ba kowane zaki yi masa abu ba ya kyaleshi batare da yadau fansa ba"cewar Aunty Naina.


Gaba dayansu suka amsa da Amin.

"Aunty bari inzo in tafi, don inaso in tsaya kagarko kafin in wuce gida" cewar zahra tana kokarin daukar veil dinta.


Amsawa tayi da "Toh Habibty, kiyi driving a hankali Allah ya saukeki lafiya, Allah kuma ya kareki, in kinje ki gaishemun da Baffa"

Nan Aunty Naina ta karba tare da cewa "kuma ki tabbatar kinyi bincike akan abinda ya faru".


Amsawa tayi da "insha Allahu, nagode"

Anan dai sukayi sallama inda suka rakota har bakin mota, nan ta tada motar ta fice daga gidan suna masu daga mata hannu yayin da idonsu ke cike tab da hawaye, wanda ya riga ya zaman musu jiki indai suka hadu, dazaran zasu rabu sai sunyi kuka don ba komai suke tunawa ba sai iyayensu da kasa ta rufe musu ido.



Karfe biyu da rabi tayi parking a kofar gidan Galadima, bude jakar ta tayi ta ciro cingum ta saka a baki tare da maida daurin dankwallinta har goshi, nan danan ta canza kamanni bazakice Doctor zahrah bace, fitowa tayi a motar fuska a hade sannan ta shige cikin gidan.


Da sallama tashiga cikin gidan, duk matan gidan na zaune a gindin itaciyar mangoro,saurin amsa sallamarta sukayi hadi da saurin gaisheta, ba wadda ta samu arzikin amsa mawa a cikinsu, sai kallon raini da tsana da ta bisu dashi.

Cikin takunta na kasaita ta tunkari dakin Baffa Abdulaziz(galadima na yanxu), sallama tayi a kofar dakin, Inna Karime ce ta amsa mata tare da fadin"shigo mana Likita".


Cike da takama ta shiga dakin tare da fadin"ba wurinki nazoba ai, ballantana kibani izinin shigowa"


Fuskarta dauke da damuwa tace" wai zahrah yaushe zaki cire tsanata acikin zuciyarki ne, ki yadda da abunda ya faru shekara biyar baya Allah ya tsara, sannan kuma wasiyar kakarku na isar tare da aiwatar wa" ta karasa magana cikin raunin murya.

Cike da rashin kunya hade da fitsara tace" a koda yaushe ina fada miki indai na cire tsanarki a raina wallahi mummy ce ta dawo duniya, kinga ko ba ranar cirewa saboda duk wanda ya mutu bazai dawoba, ina Baffa?" ta tambayeta cike da gadara.

Cikin sanyin jiki inna karime ta amsa da"ya shiga wanka don yanxu ya dawo daga fada" ta karashe magana tana mai fita daga dakin.

Bayan mintina kadan yayi sallama tare da fadin" yau amarya tace a gidan?, yanxu karime take fadamin zuwanki".



Fuskarta dauke da murmushi ta amsa da"ni ce Baffa, nazo karban kudin cefane ne"


Sai dayayi murmushi sannan ya amsa da"ke da kika gudu kika bar mijinki, ai baki da kudin cefane".

Nan dai suka gama barkoncinsu suka gaisa, sannan suka dasa hira, wanda yawanci hirartasu ta 'yan uwantane da wurin aikinta.


Karfe uku da rabi tayi masa sallama tare da bashi bunch na dari biyu sannan ta fito.

Tana fitowa tayi Kicibis da baba usman sanye da kakin soja(su Baba usman har sunday ma ana yawo da kaky🤪🤪), saurin hade rai tayi tare da rabawa ta gefensa zata wuce, cikin hanzari ya riko hannuta tare da fadin" ke don ubanki baki iya gaisuwa bane, kina ganina zaki wuce"


Daga bayansu Dada ladiyo ce ta fito daga daki daurin zaninta a hannu, wacce kallo daya zaka mata kasan ta tsufa sosai don har ta rangwaba, tana cewa" ina fa zata gaisheka, tunda koni bata iya zuwa ta gaisheni ba, har tana niyyar tafiya".

Jin maganar Dada ladiyo yasa duk matan gidan tasowa daga gindin bishiya suka nufo wurinsu,don kallon dramar da za ayi.


Sakin hannunta yayi tare da fadin" kibar ganin kin girma wallahi yanxu sai in zaneki inkaiki guardroom, mara kunyar banza kawai, zakije ki zukunna ki gaida Dada ko sai na tattakaki a wurin, ko ubanki ya buga damu ya kyalle ballantana ke haihuwar jiya²" ya karashe zance yana nuna ta da yatsa.

Kallonsa tayi cikin ido tare da jan tsaki tace"wallahi kar ka kuma zagin ubana don yafi karfinka, ni dinnan na isheku gaba dayanku, inkuma ka kuma magana anan sai na fasa kwai, asirinka ya tonu a wurin nan kowa yaji abinda ka aikata"tayi magana fuskarta dauke da murmushin mugunta.



Gaba daya daskarewa sukayi a wurin, domin tasa musu shakku a zuciyoyinsu, yayin da Baba Usman ke tunani wani sirrin nashi zahrah ta sani, matan gida da Dada Ladiyo kuma na tunanin maganar da zahrah ta fadi.


Baffa ne ya fito daga daki tare da fadin" ke zahrah yi hakuri ki wuce ki tafi kar dare ya miki a hanya".


Sai data watsa musu harara tare da jan tsaki sannan ta fice ba tare da ta kuma magana ba.


Sai bayan sallar magariba ta karasa gida, ba karamar gajiya tayi ba, don haka wanka kawai tayi ta bi lafiyar gado, saboda tana fashin sallah.

Washe gari karfe shidda na safe ta fita zuwa Asibiti, wurin little ta nufa don ganin jikinta, nan ta tarar da ita da tsohuwar da Yaya Abdul ya dauko don jinyarta.


Daga wurin Little office ta wuce, inda tadauko laptop ta kunna, cikin kankanin lokaci tayi connecting din CCTV din bangaren emergency ward, sannan tayi playing, ganin lokaci na wucewa yasa tayi forwarding dinshi zuwa ranar da ta kori Doctor Shareef daga Asibiti sannan tayi playing, sai gashi ya hasko tundaga shigarta ward din har fitarta sai dai babu inda taga alamar wani na videoing din ta, har zata rufe laptop din sai ta lura da waya an turota ta Window, saurin zooming din wajen tayi, fuskar da ta gani ya sa mata faduwar gaba, ba kowa bane illa *DOCTOR* *SULEIM.*


Wash🤦‍♀️, aradu na gaji😁😁.


*More comment, more typing, daily update.*

*Tofa🤔, wasa farin girki,*


*Wace irin tsama ce tsakanin Doctor Zahrah da Inna Karime?.*

*Wani sirrin Baba Usman ne Doctor Zahrah ta masa barazana dashi?.*


*Wani mataki Doctor zahrah zata dauka akan Doctor Suleim?.*





_Duk ku biyoni cikin littafin_ *DOCTOR ZAHRAH* _don jin yadda za a karke._





*Comment*
*Share*
*Follow*






*Fateeyzah✍*
*08161734851 whatsapp only*




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)




*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 46 to 50_*


Wani irin kayataccen murmushi ta saki tare da jijjiga kai, sannan ta rufe laptop din.



Karfe takwas saura minti goma ta fice daga office, ta nufi theater room, ko da ta isa ita ake jira don har an ma patient din allurar *Anaesthesia* , direct wani room ta shiga acikin theater, cikin few seconds sai gata ta canza kayan jikinta, ta sako wani blue gown da hula,sannan ta sako face mask da hand glove.



Cikin kwarewa da natsuwa take aikinta gwanin ban sha'awa, sai team members dinta dasuke taimaka mata, sai da suka dauki kusan awa uku suna wannan surgery din kasancewa surgery din zuciyane.



Karfe sha daya da rabi ta fito daga theater, wanda kallo daya zaka ma fuskarta, kaga alamun damuwa, nurses biyu ne suka gunguro patient din, inda suka wuce *ICU* , sai da ta tabbatar an patient din duk abunda ya kamata sannan ta wuce office dinta.


Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala, sallaya ta shimfida zata tada sallah, jin motsin bude kofa yasa tayi saurin juyawa, Yaya Abdul ne ya shigo, suna hada ido suka sakar ma juna murmushi, sannan yace" my Habibty, ya aiki".

Cikin kulawa ta amsa da lafiya lau yayana, ya aiki".


"Lafiya lau, nazo duba Little ne, sai kuma Doctor yace zasu sallameta ta karasa jinya a gida"


Fuskarta dauke da fara'a tace "Alhamdulillah, dama yau danaje dubata naga kamar wurin ya kame,

Please Login or Register in order to submit comment