Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk sanda kika samu kanki a baccin rai ki ringa daukar Alqur'ani kina karantawa, zuciyarki zatayi sanyi, amma kinki, sai dai ki ringa dura ma cikinki totaline, yanxu abun nakima ya kara gaba tunda kin kara yawan kwalabe, haba Zahrah kudin da kike sayo magungunan nan dasu da sadaka kikeyi dasu , Allah ya kai ladan kabarin iyayenmu".

Cikin muryar mai kama da shagwaba tace" yaya nace maka na daina, kaidai kaci gaba damun addu'a"

"Shikenan habibty, Allah ya shiryeki" cewar Yaya Abdul.

Ta amsa da" Amin"

Gyara zama yayi tare da fadin" wani patient ne naji ana fadin kin masa koron kare yau a Hospital, haba habibty wannan ba dabi'arki bace".

Cikin turo baki tace" Doctor Shareef ne fa yaya, danshi ne ya kawoshi yana fama da heart problem"

Dajin sunan Doctor Shareef fuskarsa ta canza, sai dayayi dan jim tukunna yace"habibty dakin sani baki koreshi ba, sai ki dubashi, Allah yana son mai yafiya, duk abunda Doctor Shareef ya mana, ki tabbata hakan yana daya daga cikin kaddararmu, sannan ki sani Allah ya yasa ta hakanne mummy zata bar duniya, indai akace duk abunda aka maka zaka rama, to a duniya ma baza a taba zaman lafiya ba".

Cikin zumbura baki tace" gaskiya yaya bazan iya dubashi ba, wai yaya wama ya fada maka?"

Sai da ya kalleta na some seconds sannan ya girgiza kai tare da fadin" babanki ya fadamin da naje kai little Asibitin".

Cikin sauri ta tambayeshi" me ya samu little din".

"Zahrah ai ni naga tashin hankali daga jiya zuwa yau"ya fadi fuskarsa dauke da damuwa

Cikin zakuwa tace "don Allah yaya ka fadamin me ya faru"

Sai da ya furzar da iska sannan yace"Zahra jiya da daddare Aisha ta turo min higher killers su kasheniiiiiiii".

Yanxu aka fara wasan.

*Tofa🤔 ana wata ga wata, wacece kuma Aisha?*

*Wacece little?, me ya sameta ya kaita Asibiti ?*

*Wani irin laifine Doctor Shareef ya aikata ma wannan family din??*


*Su waye family dinnan?, meye cikakken tarihinsu?*

*Duk ku bini acikin littafin Doctor Zahrahhhh.*


_Gaskiya rashin comment dinku yasa ina tunanin dena typing, wannan dalilinne yasa jiya bakuga post dinaba, comment dinku shine kwarin gwiwana._


*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*

*Fateeyzah* ✍
*08161734851 whatsapp only*




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us:*
*kundin hikima writers association@facebook*
*Hikima writers novels@facebook*


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*



*_This is your page sharifat niamey, Allah bada sa'ar jarabawa._*



*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 16 to 20_*

Cikin tashin hankali tace" what!!, yaya da gaske kakeyi, koko kunne nane baiji da kyau ba"

"Hmm hakan ne habibty nima kaina na dade ina mamakin hakan, da farko dai kinsan basma da naina suka bani shawarar kara aure Saboda matsalolin da nake ta fuskanta nida hafsat, na yanda tafi bama aikinta muhimmanci akan mu familynta".

Cikin bacin rai ta kada kai tare da fadin" hakane yaya nikuma nace maka ka auri 'yar talakawa ne saboda sunfi iya kula da miji".

" habibty tunda kafin na auri Aisha sai da mukayi yarjejeniya akan baza tayi wani aiki ba,saboda inason ta ringa kula dasu little hakan yasa na yanka mata sadaki naira dubu hamsin duk wata, kuma ta amince, Amma kuma tunda akayi auren sai itama tabi layin hafsat suka daura ma mai aiki alhakin kula dasu little".

"Amma yaya ni banga laifinta ba, tunda uwar da ta haifesu ma ta kasa basu kula, kana tunanin wacce batason zafinsu ba zata kula dasu ne, don Allah yaya ka fadamin yaya abin ya faru" tayi magana cikin zakuwa.

"Kinsan 2months back Aisha ta tada mun da hankali sai na bata jari zata je dubai ta saro kaya zata fara business, hakan yasa na bata 2millions taje ta saro kayan, to after 3weeks sai ta kuma tambayata wata 2millions din wai tanaso ta saro kitchen equipment kuma wanda suka siya wadancan kayan basu riga sun hada mata kudin ba, nan nikuma nace bazan bada ba, nan fa tayita tada mun da hankali acikin gida ranar har ta kureni nayi mata duka, kawai jiya around 12 kuma sai ga 'yan fashi a gida, nan hankalina ya tashi don ba karamin bindigogi bane a hannunsu, da farko su kusan bakwai suka shigo nan suka kulleni sannan suka tankado keyar Aisha da hafsat zuwa falona, yin haka da 5minutes sai ga ogansu ya shigo da mutum biyu, nidai dana ganshi sai naga kamar na san fuskar amma na manta, sai da naji ya ambato sunan lieutenant A.A .Galadima, sannan na kuma dago kai".

Cikin kidima tace" yaya badai kunsan juna ba?"

"Tabbas habibty, don shekara daya data wuce na taba bugeshi da mota a Ahmadu bello way, wanda ni nakaishi Asibitin mu na sojoji aka yimasa medication".

"Chab di jab, to yaya akayi kasan Aisha ce ta aiko a kasheka"tayi magana fuskarta dauke da mamaki.

Sai daya gyara zama sannan yace" bayan yasa yaransa sun kwanceni sai ya nemi kebewa dani, nan ya fadamin daya daga cikin matana ta bashi contract din kasheni bayan sun karfi miliyan hamsin a wurina, dana tambayeshi wacce a ciki, sai yace a waya suka hada contract din amma tace masa sunanta hafsat amma data tashi yi masa transfer na kudi sai akayi da account din Aisha, nan kwakwalwata ta tunkushe, amma duk tunanina su biyu suka hada baki don a kasheni, nan dai ya nemi gafarata tare da kwashe yaransa sukayi gaba bayan sun kwance su sergeant dasuke gadi".


"Amma yaya kana soja kabar kasunguman 'yanfashi suka tafi batare da ka dau wani mataki ba"

"Habibty lokacin nan batasu nake ba, gaba daya hankalina ya dugunzuma ya tashi, tunani na mai na ragesu dashi, especially hafsat me zatayi da dukiya, ga gadon mahaifinta, ga salary dinta a matsayinta na ma'aikaciyar C.B.N (kaduna branch), ita kuma Aisha a ganina duk kudin danake bata basu ishe taba".

Pls manage ban da ishasshen time.

Ko yaya lieutenant A. A. Galadima zai warware wannan sarkakiya tsakanin matansa sai mun hadu next page.

Kuyi hakuri da error, banyi Editing ba.


*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow*



*Fateeyzah* ✍




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us:*
*kundin hikima writers association @facebook*
*Hikima writers novels@facebook*


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*_Inalillahi wa'ina ilaihir raji'un, Allah ya jikanki Aunty Ummy(hauwa'u), ya gafarta miki, ya amshi shahadarki, ya raya abinda kika bari, Ameen.😭😭_*

*_Hakika mutuwarki ta girgiza kowa, Allah ya bamu hakurin rashinki.😭😭_*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page_* *_21 to 25_*


"Tunda na nufi falo, naga basanan na tabbatar da kowacce ta nufi side dinta, nan na zube a kan kujera, don abun ba karamin kada ni yayi ba, matan ka wanda kullum kake kokarin faranta musu, su suke son su kawar dakai a doron kasa, ina nan zaune narasa abunyi don kwata², I am out of speech, nan wata dabara tazo mun, natashi na nufi dakin hafsat, as usual tana nan gaban laptop, yanayin yanda naganta batare da fargaba ko wani abubu ba yasa na fara shakka akanta, don duk wanda ya aikata wannan abun, kuma ya tabbatar da asirinsa ya tonu bazai kasance haka ba, nan na bar side dinta, don har na shiga, na kuma fita bata sani ba hankalinta nakan laptop"ya karashe magana fuskarsa dauke da damuwa.

Wani siririn tsaki doctor Zahrah taja tare da fadin" wallahi ban taba ganin mata irin Aunty Hafsat ba, gaba daya rayuwarta ta ta'allarata akan aiki, sai kace in taje lahirar aikin za a tambayeta".

Ya lumshe idonshi cikin bacin rai sannan ya bude tare da cewa" ina shiga part din Aisha na tarad da ita tana ta kuka, gani na datayi yasa ta kuma fashewa da wani marayan kuka tare da fadin ( don girman Allah kayi hakuri na tuba bazan sakeba, sharrin shedan ne da kawaye, su suka ban shawarar kashe....) jin wannan statement din nata yasa naji wani karfi yazomin ban bari ta karasa magana na hambareta, na shiga dukanta, wallahi habibty dukan danayi ma Aisha, ko wani sojan aka mawa shi sai yaji jiki, don harsai data sume, Asuba nayi naba masu sergeant ita nace su kaita jaji su samin ita a guardroom".

Nan danan hawaye ya wanke mata fuska tare da fadin" yaya mai ka ragi Aisha da shi da har zata maka haka?".

"Hmm habibty kenan, Aisha really break my heart, sannan tasa na dena yadda da kowa, saboda abun duniya kisa a kashe mutum, mutumin ma mijinki, kinga kuwa ai tunda matarka ta maka, kowa ma zai iya maka, aranar nayi kukan rashin iyayenmu, kukan da rabo na da inyishi tun ina yaro, abun bakin ciki hafsat ko ta ta dubani don nasan duk tanajin abunda ya faru tsakanina da Aisha, amma sai turo min text messages tayi akan tana da meeting karfe bakwai ta wuce wurin aiki, wallahi Habibty indai haka halin ko wacce mace yake bazan kuma aureba, 'yar talakawar banji dadi ba, yar masu kudin itama gashinan, nidai haka tawa kaddarar ta ta zomin na rashin dace da matan kirki" ya karashe magana yana share kwallar data zubo masa a fuska.

Cikin kuka tace "yaya yanxu wani mataki na ka dauka akanta"


"Zuwa can jaji nayi na hadata da fushin recruit shine take fadamin wai a Facebook group ta hadu da wata kawa, saboda tayi posting tana neman a bata shawara akan na hanata teaching amma nabar kishiyarta na aikin banki, shine waccen tabita private tabata shawarar ta nemi kudi a wurina ta fara business, daga nan suka sata a group dinsu na manyan mata, don tare dasuma taje dubai saro kaya, acan ne take fada musu Doctor yace bata da Eggs na haihuwa, shine fa suka bata shawarar ta ringa tatsa na kudi masu yawa, don ko na mutu tumunin takaba kawai za a bata, bayan na hanata wannan kudinne har na mata duka, shine taje ta basu labari, su kuma suka zugata akan ta kasheni kawai bayan tasa an karbar mata 50million sannan suka hadata da higher killers tare da hadama hafsat makirci ko da alamari ya baci, ace hafsat ne, mistake din dasukayi shine transfer kudi data masa na 1million a account dinshi da ya nemi deposit, kinji yanda suka tsara abun".

_( wallahi mata ku shiga taitayinku, kowacce sai ta tafi facebook tana tona sirrin aurenta,wanda yawanci in ba ayi dace ba anan ake haduwa da baragurbin mata, wanda wata baza ma tayi comment ba saidai tabiki private ta baki shawarar banza ke kuma da yake kin zama doluwa,wawiya sai ki dauka baki da wata masoyiya sai ita, in abin gaskiyace ta baki shawara cikin mutane mana inda kowa zai gani, saboda tasan Admins da sauran mutanen kirkin dake group din zasuyi blistering din shawararta, su nuna miki hakan ba dai² bane, wallahi ku kiyaye shawarwarin da ake baku)._

_(Sannan wallahi mata mu rage buri, wasu sun riga da sun yi ma aure mummunar fahimta, kowacce dai ita tayi aure ta zama mai kudi, ko ta fara business tana kama kudi ta zama babbar hajiya, wai da kudi zamu lahira ne, bama tunanin zamu mutu mubarsu a duniya,especially yanda yanxu zakiga mata masu karancin shekaru suke mutuwa, haihuwa daya, biyu, uku, ace mace ta rasu amma duk da haka mun kasa hankalta, mu dai burinmu kawai mu samu kudi, don Allah mu rage dogon buri don duk mu gama da farin kyalle za a mana sutura a birnemu, sai wanda ya ga dama zai maka addu'a, sai wanda yaga dama zai shafa kan danki ko 'yarki, Allah yasa mu dace)_

"Lallai yaya kaga jarabta, kuma shine dazaka je jajin ko ka kirani mu tafi tare, ni nama manta, me yasamu little ne?"

"Ita kuma na dawo daga jaji na sameta ta kone cinyoyi da ruwan zafi" ya bata amsa yana zuba coke a glass cup.

Cikin razana tace "inalillahi wa'ina illaihir raji'un, garin yaya ta kone"

Kafa cup din yayi a bakinsa sai da ya shanye tukunna ya sauke tare da fadin"wai sun dawo daga school suna jin yunwa, kuma sun tashi salaha tace karsu dameta ta gaji, shine fa taje ta kunna hot plate ta daura ruwan tea, bayan ya tafasa garin juyewa ta juye a cinyoyinta, nan na sameta tana ta ihu ita kadai a kitchen Aiman na ta faman jera mata sorry, ita kuwa salaha na kwance tanajinsu, don ko dana shiga dakin samunta nayi tana chatting".

Lallai yaya gidanka akwai gyara, Allah dai shi kyauta gobe insha Allahu zan shiga da wuri in dubata".ta karashe magana tana mirza ido.

Mikewa yayi tare da fadin "Allah ya kaimu bari in wuce gida nabar Aiman wurinsu sergeant, nasan yanxu yayi bacci"

Cike da son karin bayani tace "wurinsu sergeant kuma, ina Aunty hafsat?"

"Na yi mata message da sakinta daya nace kuma karta dawo mun gida indai bazata ajiye aikin bank ba in samo mata a ministry of finance ko NDIC".

"Inalillahi wa'ina illaihir raji'un, gaskiya yaya baka kyautaba da ka saketa da dai ka turata gida ne kace kabarta ta dan jima"ta fadi fuskarta cike da alhini

"Hakan shine ya kamaceta habibty, don na tabbata hafsat bazata taba canzawa ba, kedai kiyita tayani da addu'a".

"Insha Allahu yaya, Allah ya zaba maka mafi Alkhairi a rayuwarka gaba ki daya"

"Amin habibty ni na tafi, ki tabbatar dakin saka security gaba daya gidan kafin ki kwanta" yayi magana fuskarsa so serious.

Ta amsa da "insha Allahu yaya, goodnight".

Ya fice yana mai amsa mata da" goodnight habibty, sweet dreams".


Tadau tsawon lokaci a zaune a wurin daya batta hannunta dafe da habarta, kafin ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da mikewa ta shiga kitchen, few minutes ta fito hannunta dauke da cup din coffee dayan hannun kuma rike da dan karamin plastic plate mai dauke da cupcakes a kai, nan ta hau dinning ta fara shan coffee dinta hade da cake.


Karfe sha biyu dai² ta gama, ta dauki cup da plate din takai kitchen ta wankesu ta ajiyesu a mazauninsu.

Tana fitowa ta nufi main door na parlourn tare da saka wasu numbobi mai hade da securities, sannan ta nufi dakinta dake upstairs, brush kawai tayi tare da sa night gown tabi lafiyar gadonta. *GOOD NIGHT DOCTOR ZAHRAH.* /

Karar wayarta ya tasheta daga nannauyar baccin daya dauketa, wanda agogon dakin ya nuna karfe shidda na safe, cikin magagin bacci tayi picking din call din tare da sawa a speaker, muryar Aunty basma ce tana kuka tana fadin "inalillahi wa'ina illaihir raji'un,zahrah fawas shima ya mutu ya barni....... "



*Tofa🤔, ana wata ga wa ta.*

*Wai kamar yanda Aunty basma tayima Doctor zahrah complain meye sanadiyar rasuwar da 'ya'yanta maza keyi a duk ranar da suka cika shekara biyu da haihuwa?*

*Ku biyoni daki² cikin littafin Doctor Zahrah don jin amsar tambayoyinku.*

*pls magana daya tak akan Aisha da Hafsat*

*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow*


*_Fateeyzah_* ✍




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us:*
*kundin hikima writers association @facebook*
*Hikima writers novels@facebook*


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉


*_Written by fateeyzah_*😍😍

*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*_Innah sheriff, wannan page din kine dake da unborn baby, Allah ya saukeki lafiya._*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 26 to 30_*

Take ta wartsake daga ragowan baccin dayake idona, hakika so uku kenan Aunty basma tana sanar da ita irin wannan sakon mutuwar, amma yanda taji wannan ya banbanta dana baya, don jitayi kirjinta ya dsu zafi, zuciyarta kamar zata faso kirji ta fito, hakan yasa bata san sanda wayar ta sulale daga hannun taba, ta dau tsawon lokaci zaune dafe da kirjinta, tana cikin tunani da alhini, dakyar ta iya bude bakinta da yayi mata nauyi ta ambaci kalmar inalillahi wa'ina illaihir raji'un, haka tayi ta maimaitatawa tukunna ta samu natsuwa a cikin zuciyarta.

Kiran wayarta da aka kuma yine yasa ta dawo daga guntin tunanin da ta shiga, picking din call din tayi tare da fadin" good morning yaya,(pause), eh ta kirani,(pause), yanxu xan shirya sai in biyo ta asibiti kafin in wuce chan din,( pause), ok sai na zo"

Tashi tayi ta nufi toilet tayi wanka hade da dauro alwala, sannan tayi sallar asubahi, cikin sauri ta shirya cikin atamfarta chiganvy, wacce akama dinkin riga da skirt, sannan ta dauko katan veil ta rufe jikinta, hand bag ta dauka wadda kalarta ta dace da kayan jikinta, daga nan ta nufi shoe rag ta dauki wani plat shoe ta saka, daukar key din motarta tayi, sannan ta fice daga dakin.

Direct Asibitinta ta nufa, wanda tana shiga ta wuce dakin da aka kwantar da little, anan ta sami yaya Abdul, bayan gaisuwa, ta duba jikin little, sannan ta fice ta dauki hanyar Abuja.

Yau ma as usual, mutanen nata na Binta a baya, amma ko ta kansu batayiba, don abunda ke damunta yasa bata da lokacinsu.


*TUSHEN LABARI*

Garin Kagarko, garine dake karkashin jahar kaduna, yawancin mutanen garin fulani ne, wanda suka kafa garin shekaru da yawa baya.

Alhaji Mamuda Galadima, wanda shine Galadiman kagarko a wannan lokacin ,matarshi daya inna Ramatu, da yaransu biyu Abdulrahman da Abdulaziz.

Abdulrahman da Abdulaziz sun taso cikin kulawa hade da soyayya da suke samu daga wurin iyayensa da mutanen gari saboda yarane masu farin jini, ga ladabi da biyayya, ba karamar soyayya bace da shakuwa tsakaninsu duk da suna da tazaran haihuwa, don akalla Abdulrahman yaba ma Abdulaziz shekara sha hudu tsakaninsu, sunyi karatun addini dai² gwargwado.

A lokacin da Abdulrahman ya cika shekara ashirin da daya, aka masa auren fari, wanda aka hadashi da 'yar limamin garin mai suna fatima, yarinyace mai ilimi, kunya da kawaici, ga uwa uba hakuri, bayan an daura aure suka tare a gidansu da Galadima ya gina masa.

Suna matukar son junansu, wanda cikinsu babu mai son bata ma dan uwansa, watansu uku da aure Allah ya karbi ran galadima, ba karamar kaduwa sukayiba, don mutuwar ta shigesu sosai.

Bayan anyi sadakar uku aka nada Abdulrahman Galadima, a haka ya ci gaba da kula da inna da 'yan uwansa Abdulaziz.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya hat suka shekara biyar da aure amma fatima ko batan wata bata taba yiba, hakan ya tada ma inna hankali tace sai Abdulrahman ya kara aure don tana bukatar ganin jikokinta kafin kasa ta rufe mata ido, an kai ruwa rana kafin Abdulrahman ya amince da batunta na kara aure, anan dai inna ta shiga ta fita ta nemo masa auren ladiyo diyar sarkin garin.

Ladiyo macece fitinanniya ta karshe, bata da hakuri ko kadan, ga kishi, ga hassada, ga kyashi, wannan yasa cikin karamin lokaci ta fitini mutanen gidan, ciki kuwa har da inna, Abdulaziz ne kawai bata ma wa don shi bai daukar nosense hakan yasa basa shan inuwa daya, fatima ba karamin hakuri take yi da ladiyo ba, don ma Galadima yana tsawatar ma ladiyo.

Watan ladiyo uku a gidan Galadima ta samu ciki, zo kuga murna wurin ahalin nan, ciki kuwa har da fateema, amma ladiyo tace murnar munafunci takeyi, randa ko ta haife cikin inna kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, don har kyautar bajimin sa tabama yaron da aka haifa wanda yaci sunan marigayi Galadima wato mahmud, a takaice acikin shekara biyar da aure sai da ladiyo tayi haihuwa uku duk kuma maza,Muhammad, Abubakar, sannan cikon na ukun mahmud, nan fa ladiyo ta kara girman kai don ita a ganinta ta cinye gida, don kullun sai ta sakar ma fateema habaici duk ko da kusan ita take kula da yaron.

Kwatsam sai ga fateema ta ciki, ba karamar murna ahalin gidannan sukayi ba musammam Galadima da Abdulaziz, haka aka hadu harda innah aka ci gaba da rainon cikin, wanda ladiyo zuciyarta ke kunshe ta bacin rai don ganin yanda kowa yake lallaba fatima tamkar kwai.

Cikin fateema wata shidda, itama ladiyo ta samu wani cikin, nan feleke ya karu,don kullun saita yada ma fateema magana akan tadai fita ko yanxu Galadima ya rasu ita keda gida.

Cikin fateema nacika wata tara ta haifo sankadeden danta wato Daddyna, zo kaga murna gurin masoyan fateema, ranar suna na zagayowa aka rada ma yaro Aliyu, nan ko inna tabama mutane mamaki don kyautar danmariki biyu tabama Aliyu don acewarta wannan shine asalin maigidanta, hakan ko ba karamin bakanta ran ladiyo yayi ba inda wanda hakan ya kara haddasa wutar tsanar Aliyu a zuciyarta.

Watan Aliyu biyar da haihuwa, ladiyo ta haifo danta mai kama da ita,wanda aka saka ma suna usman,daga kan usman aka rufe haihuwa a gidan Galadima.

Rayuwar Gidan Galadima rayuwace mai cike da jin dadi sai dai ladiyo datake kawo musu cikas, don gaba daya ta gama koya ma 'ya'yanta halinta, saboda tsakaninsu ma suna ma junansu hassada, hakan yasa kullun dakinta cikin fada ake.

Aliyu yaro ne natsatse, domin ko ya samu tarbiya mai kyau wurin Adda(fateema) da kawu( Abdulaziz), yayi makarantar primary dinsa anan kagarko tare da 'yan uwansa, sannan suka yisecondary a Birnin gwari boys secondary schoo, bayan nan duk sauran basu ci gaba ba ,sai shi da ya tafi jami'ar Ahmadu bello dake Zariya inda ya karanci public Administration.

A lokacin da Daddyna(Aliyu) yake level one ne kawu Abdulaziz yayi aure, inda ya tare da matarsa (karime) anan Gidan Galadima, nan suka hada kai da Adda don in kagansu zaka dauka yaya da kanwane, ba karamar shakuwa bace a tsakaninsu hakan yasa Ladiyo(Dada) ta kuma tsanar Adda don gani take duk munafuncinta ne yasa duk wanda ya shigo Gidan sai dai yace.

Kwatsam aka wayi gari innah ta amsa kiran ubangiji, hakika ba karamin girgiza sukayi ba, don inna wata babbar bangoce ta wannan Ahali.

Lokaci ya ja, inda har Daddy ya gama degree dinsa yaje service ya dawo, wanda har wannan lokacin matar kawu Abdulaziz bata taba ko bari ba, hakan yaja mata gori wurin Dada, kusan kullun sai tasata kuka,saukin tama Daddyna dakinta yake wanda in ta kallesa take samun farin ciki don ko bata haihu ba tasan tana da Aliyu.

Wata babbar offer aka bama maigari na yakawo mutum daya daga garinsa mai takaddar degree don a sama masa aikin soja, nan suka yanke hukuncin kai Daddyna.

Zo kaga murna wurin Daddy, Galadima, kawu Abdulaziz, Adda, baba karime, sabanin da ladiyo har yaji tayi wai Galadima bayason yaranta yafi son Aliyu tunda har ya nemo masa Aikin soja, bai nemon ma yarantaba, rashin sani bata son babanta ya bama Aliyu offer ba.




*More comment,more typing*


*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow*




*Fateeyzah*✍




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our reader)


*_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉
*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Fateeyzah@wattpad_*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*Wannan page dinkune:*
*Aunty Aisha Ashir*
*Haseenert Muhammad*
*Umulkhairi*
*'yar Asalee*
*Thanks for your love and support.*



*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 31 to 35_*

Ba karamin rikici akayi da ladiyo ba, don har sai da tayi kikirarin ko da zatayi yawo tsirara sai taga karshen Adda da Aliyu, jin wannan furucin datayi yasa mahaifiyarta cewa Indai tayi ma Adda wani abun mara kyau bata yafe mata ba kuma ta cireta cikin 'ya'yanta.




Shi kuwa sarki jin abunda ladiyo ta fadi yasa yace usman ya kawo takardarshi na secondary a saman masa ko recruitment ne, duk da dai takardun nasa basuyi kyau ba haka aka hada data Daddy aka kai.




Cikin hukuncin Allah suka

Please Login or Register in order to submit comment