Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan nasa aka nemo mini masu tsaran zahrah saboda ita kadai nake tausayi a cikin 'ya'yana kasancewa itace mai karamin shekaru, sati daya muka kara a Nigeria muka wuce kasar saudiyya, saboda badda sawu da mukayi, kawanan mu biyu a saudiya muka wuce Dubai(Abu Dhabi), wanda Already Rulwan ya shirya mini komai acan , daga gida , mota da aikin da ya saman mini a wani company jallabiya.


Zaman mu a Abu dabhi, zamane na kwanciyar hankali tare da freedom, babu mai damunka balle sa ido, sai dai rashin kwanciyar hankali daga Ni'eema wanda a kullum sai ta yi mini kuka akan tana son ta koma Nigeria, sai dai inta lallashinta da bata baki, sannan a bangaren ku duk ina samun rahotanni daga wurinki lawyer, sannan ina turo ma Zahrah da text message a kullun safiya, wanda hakan na sani in samu kaina cikin kwanciyar hankali, a lokacinne na umurci lawyer a raba dukiya a matsayin gado, sai dai kar a raba da gidana danake zaune nace masa ya fadi haka a matsayin wasiyya ta, hakan ko ya faru, sannan na fara tura masa kudi don ci gaba da ginin Asibitin Zahrah da na fara gina mata wanda daga ni sai Lawyer muka san da haka.


Watan mu tara acan Allah yayi ma rulwanu rasuwa sakamakon Hatsarin mota da yayi, hakika naji rasuwar rulwanu, wanda sai dai muce Allah ya jikanshi.


Watan mu goma Ni'eema ta haihu inda muka sa ma yaron sunan Baffa, sai dai abun mamaki a lokacin kwata kwata bama sha'awar dawowa gida, don wani zubin mantawa mukeyi da Nigeria sai dai duk jumma'a bana fashin tura ma zahrah text message haka kuma duk karshen wata ina tura mata kudi ita da lawyer.


Haka rayuwarmu ta ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da nishadi, har Zahrah ta gama karatu tayi workmanship dinta, sannan na umurci Lawyer da ya danka mata asibitinta, sannan alokacin na umurce shi da yayi mata dabara ta yanda za'a saka mata security locks a kofofin gida dana office dinta don ganin dana yi kamar an fara bibiyarta kasancewa na fada muku duk abunda ke faruwa ina da masaniya, ranar da Zahra ta zo wurina a Dubai bayan Rasuwar Lawyer ba karamin kaduwa nayi ba, saboda nasan ana bibiyenta zai yi wuya bada su ta tawo ba, wannan dalilinne yasa ban tsaya sauraronta muka hada kayanmu muka bar gidan, muka koma hotel da zama har sai danayi bincike na tabbatar ba wanda ya biyota sannan muka koma gidanmu, a wanna shekaranne ni'ima ta haifi 'yarta wacce na saka mata Aisha.


Ranar naje daukar karatu a masallaci, wani cikin dalibai yayi ma malamin tambaya akan yana taso ya koma garinsu amma da zaran ya kawo tunanin a ranshi sai yaji wani matsananci ciwon kai ya taso masa, idan ya kwanta yayi bacci shikenan ya manta, nan dai malam ya sanar dashi sihirine yazo zai bashi magani, jin haka yasa da aka tashi karatun nabi malamin inda nima na masa bayanin nawa matsalar, nan dai ya bani magani wanda nida Ni'eema muka yi amfani dashi, bayan wata uku kuwa muka jimu sakayau tare da son komawa Nigerian, take ko muka fara shiri, muka taho yayin dana sauka a Taheer Guest lounge a kano, kwananmu biyu da sauka aka fara case din zahrah, wanda raina ba karamin baci yayi ba da jin abunda ake zarginta akai, hakan na fara bincike har na samu wacce ta aikata mata haka, kuma ni nake kiran zahrah a waya ina sanar da ita idan an fara problem dinnan, wanda nake haka don in tungurata in ta kalla taje ta wanke kanta a median, wanda hakan da tayi yasa na samu peace of mind, jiya muka baro kano zuwa kaduna, direct gidana na wuce don na samu labarin sunyo nan ta bangaren Baba maigadi wanda shima yana cikin masu kirana don information, daga nan na kira Abdul yazo ya sameni yau da safe, wannan ne abunda ya faru.


Gaba dayansu jikinsu yayi sanyi, yayin da suka kasa magana, mazan ne kawai masu dauriya, matanko hawaye suke tayi, don duk zuciyarsu tayi rauni.

Baba usman ne ya tsinke shirun tare da cewa" yaya Ali ka muni mummunar fahimta akan abunda ya faru, wanda yanxu zan warware muku gaskia".

"Bayan mun gaisa da kai,sai na shige cikin barrack saboda zan gana da ogana, ko da naje sai aka sanar dani akan ya dan fita, hakanne yasa na samu wani suckway na zauna wanda yake kusa da Windows na office din ogan ka, anan naji yana magana kasa², wanda na kasa kunne inajin sakon da yake bayarwa ta waya akan a bika hanya a kashe ka dakai da matarka sannan a kona gawarku tare da motar yanda za a ce Accident ne kukayi, a lokacin na shiga rudani, wanda har sai dana zubar da hawaye, hakan ne yasa na ari bike na biyoka hanya, wanda is too late ko da nazo sun rigani isowa, wallahi banzo da niyyar kasheka ba, nazo da niyyar taimakonka ne, kasancewarka dan uwana ta yaya zan kasheka, kuma na rufe fuskana ne saboda tsaro a matsayina na karamin soja, wannan dalilin yasa da nazo na tasar ma wancan wanda har Allah ya bani galaba akansa, sai dai kuma sai naji ka kwala mini bindiga akai" ya karashe magana yana mai zubar da kwalla.


Kallonshi daddy yayi cikin sanyin murya yace" kana so in yadda da wannan zancen naka ne Usman, wanda inada tabbacin zaka aikata don tun da muka tashi ba kaunata kake ba, har yazo kan matata da 'ya'yana, especially Zahrah wanda duk abunda kake mata inada labari, idan baka acikin makasan me yasa ko da rulwanu yazo bai same ka a wurin ba?"


Idonshi na zubar da hawaye yace" saboda tsoro na gudu don nasan idan aka kamani a wurin ba makawa sai an kasheni, shi yasa ina farfadowa naja jiki nabar wurin, don a yanda na ganka na dauka ka rasu, kuma kaima kasan in aka kamani za a daura min alhakin kashe ka ne, shiyasa nabar wurin, wanda a lokacin naga Ni'eema tana waya, wannan dalilin yasa da akace motarku ta kama da wuta kun mutu a ciki naja bakina nayi shiru, don na tabbata karasa ku sukayi saboda dama irin mutuwar da oga yake so kuyi kenan".


Zahrah ce tayi karaf tace" to me yasa ka tsanemu especially ni, wanda a iya sanina ban maka komai ba"

Murmushi yayi mai kama da yake sannan yace" ba tsanar ku nayi ba, hassada ce, wanda aka dasa mun ita a zuciya, tun muna kanana Yaya Ali ya fini ci gaba, duk da tsakaninmu ba nisa, amma komai sai ya fini, hakan yasa nake tsananin jin haushinshi tare da tunzurani da Dada take yi, a lokacin da ka tafi jami'a har ciwo nayi, saboda sai da ka tafi na fara cizon yatsa tare da dana sani na tsaya nayi karatu, ashe lokacin dana sani bata kare mun ba sai da akace za a saman maka aikin soja, wannan yasa na shige daki na ringa yima Dada kuka akan ni ya kamata in tafi ba kai ba, wannan dalilin yasa tayi ta bore har sai da aka hada dani, a lokacin da ka auro Aisha naji kamar zan mutu saboda aganina da ni ta dace ba da kai ba saboda kyanta, wannan dalilin yasa na sa mata kahon zuka a cikin gidan nan idan nazo, don jin nake kamar ka saketa na aure don haukata, sai dai sanda Baffa ya baka Auren Ni'eema, anan na tabbatar wa kaina Hassada ce nake maka, saboda ka fini komai , babban gida, mata kyawawa, sannna da 'ya'ya kyawawa, wannna ne yasa na saka ma 'ya'yanka karan tsana Especially Zahrah wacce a kullun na kalleta nake ji dama ni na haifeta duba da daukakar da take samu a rayuwarta, wannan dalilin yasa duk sanda muka hadu da zahrah na tuna bani na haifeta ba nake jin zuciyata tayi baki, wanda ayau na gasgata hassada da mai rabo takice, amma wallahi nayi nadama abunda na aikata abaya wanda sai yanxu nake girban shukata, wacce ga daya nan a gabanka, don Allah Ina neman Yafiyarku gaba daya 'yan uwana sannan ku saka baki Yaya Ali da Ahalinsa su yafemin" ya karshe magana yana mai gurzar kuka.


Cikin kuka Dada Ladiyo tace" ba laifinka bane Manu leifina ne, ni na daura ka akan turbar haka, dama malam na fadamin kafin ya rasu, akwai ranar da zanyi kuka da idanuna akan tarbiyyar da na baku, sai dai su yayyinka tunda suka fara tara iyali suka yi hankali suka dena biyemin, don Allah duk ku yafeni, don duk ni naja wannan matsalolin da suke ta faruwa".


Tashi daddy yayi ya rikota tare da rungumeta shima yana mai zubar da hawaye, gaba dayansu dake wurin kuka suka kece dashi babu mai rarrashin wani, hatta huwailat da Mama Asabe jikinsu yayi sanyi.

Bugo kofar da aka yine yasa dukkansu suka maida Hankalinsu wurin, hajiya sailuba ce ta shigo tana ihu tana fadin" wallahi baku isa ku ja dani ba, shekara kusan arba'in kenan ina abunda naso, don haka ba wanda ya isa ya zarta mini layi" ta karasa magana tana mai bugun kirji.


Gaba daya mikewa suka yi suna mata kallon zautacciya yayin da Najib idonshi ya cika da kwalla saboda bakin cikin abunda yaga mahifiyarshi ke aikatawa.


Wani ihu zulai('yar Baba Mahmood) ta saki tana fadin "wallahi mayya ce, muguwace ita ta cinye Aunty Aisha, wai baku gani bane ga idonta nan jajawur tana ta lashe halshe". dajin haka fa take mata suka cukwuikwuye hajiya Sailuba suna duka, yayin da su Baba Mahmood suke kokarin kwatarta, wanda dakyar suka kwaceta a lokacin sun sumar da ita, ganin haka fa Baffa yace a kira masa Alaramma, nan Baba Usman ya fita cikin sauri, gaba dayansu sun yi cirko cirko akan hajiya sailuba, babu wanda yayi tunanin yayyafa mata ruwa a cikinsu, ganin hakane yasa Najib yana zubar da hawaye ya nufi rigiya ya jawo ruwa, ya zo ya watsa mata firgigif ta bude idanuwanta wanda yayi dai² da shigowar Alaramma, sai dai take gidan ya dauki duhu har baka ganin na kusa dakai, ganin haka fa yasa Alaramma dasu Baffa fara karanto addu'oi da karfinsu, inda gaba daya jama'ar dake gidan kowa ya dauka, cikin ikon Allah a hankali duhun ya fara washewa, nan suka ci gaba da yi, take ko komai ya dawo dai², sai dai mugun gamo da suka yi da gajiya Sailuba dake zaune kusa da wani katon oganta yana mai bude halshe yayin da isonshi ya zama baki kirin.


Gaba dayansu sun tsorata hakan yasa Alaramma cikin dauriya ya debi wani magani a kwalba ya watsa masu, take suka saki wata gagarumar kara, nan danan wata guguwa ta turnike wurin, nan fa Alaramma ya numurcesu da su fara karatu tare da Addu'oi........



*Kash wallahi nagaji nasi gama littafin nan yau, amma kuma kaina ya fara ciwo, ku daga mun kafa zan gobe, da izinin Allah zan gama shi.*



*Comment*
*Vote*
*Share*



*_Fateeyzah_*✍


HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*


*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*




*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________

*_Page 121 to End_*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
A hankali guguwar nan ta laba, sai dai take oga ya bace bat! a wurin, hakan yasa fa matan wurinnan kwalla ihu tare da neman masala, wata irin tsawa Alaramma ya daka musu tare da cewa " kar wanda ya bar wurinnan".


Gaba dayansu sun yi tsuru² a wajen da suke tsaye, yayin da su Alaramma da Baffa suka ci gaba da karanto Addu'a, can sai ga Hajiya Sailuba nata Atishawa, hakan yasa suka dakata, tunda Atishawar nan ta laba ta fashe da wani marayan kuka, haka tayi² babu mai lallashi don ko Najib da yaga Abunda ya faru, wani tsorontane ya shige shi lokaci daya.




Sai da taci kukanta ta goge hawayenta sannan ta fara cewa" Nasan kwanana yasa kusa ya kare duk da ban taba kawo hakan a raina nan kusa ba, hakika na tafka babban kuskure wanda nasan ko mutuwa nayi wuta za a sakani, na zalunci mutane, na raba uwa da 'ya'yanta, uba da 'ya'yanshi, na raba dan'uwa da 'yan uwa,sannan na dilmiyyar da mutane, wanda ko wadanna zunubai da na kwasan ma kaina bazai taba bari inyi kyakyawan karshe ba".

Gaba dayansu da idanuwa suke binta ba wanda yace mata ci kanki.

Ci gaba tayi da cewa" Na kasance daya daga cikin member na kungiya *BLACK MAFIAANS* , wacce har na kai matsayin mataimakiya shugaba, yayin da General Phillips Okonko Iweala ya ke matsayin shugaban kungiya, nayi sacrificing da yawa, wanda cikin na jikina na bada Mamata, mijina, Babana da kuma dan mijina, bacin sauran jama'ar da basu jiba, basi gani ba. A lokacin da Najib yazo mun da maganar aurensa da Basma, take naki amincewa saboda ina ganin class dinsu na aure ba daya ba, anan na fada masa ko zao yi aure sai dai 'yar governor ko 'yar sanata, sai dai kuma bayan kwana biyu da mukaje taro, sai oga yake fada mini nayi kuskure saboda shigata wannan family shi zai bani damar gajen kujerarshi nan gaba kasancewa kuna dauke da baiwa da albarkar ubangiji a tare daku, wanda sai dai kuma duk abunda zanyi in yishi a sannun saboda kuna da tsari mai karfi a jikinku, wannan dalilinne yasa na amince da auren Najib da Basma, sai dai bincikena ya tabbatar mini da zahrah zata kawo min matsala, hakan yasa nayi amfani da hajiya Asabe ta bani 'yarta huwailat na tura ta makaranta tayi kusanci da zahrah Saboda in ringa samun information, Aikin farko dana fara shine lokacin da Maman Basma bata da lafiya, a lokacin aka bani Assignment akan in nemo jinin mai dauke da ciwon zuciya tare da zuciyar, ban wani daga hankalina ba saboda nasan inda zan samu, wannan dalilinne yasa naje kasar Egypt dubata, wanda ban wani sha wahala na zuke mata jinin jikinta, sannan na cire zuciyarta, kasancewar ba kowa a dakin, sai dai ko da nakai oga yayi mini jan kunne akan zahrah saboda acewarshi ta riga tasaka ayar tambaya akaina, haka na ci gaba da aiwatar da sacrifices din da aka bani, bayan shekara daya na fito ina neman mataimakiyar shugaban kungiya, sai dai an bani sacrificing da yawa, ciki zan bada jikokina uku, da kuma mahaifar 'yan mata biyar wanda sai nayi lesbianism dasu,sannan in saka handkerchief in goge gabansu dasu, ta haka nake cire mahaifarsu, yayin da duk 'ya'yan Najib da suke mutuwa ranar cika shekara biyu da haihuwarsu ni nake kashe su tare da zuke jinins" ta karasa magana tana shoshe².


Cikin tashin hankali Najib ya mike tsaye yana mai zubar da hawaye yana karkada kai, cikin murya shi da take rawa yace" Ashe ina zama da azzaluma ce ban sani ba, mashirkiya, annamimiya, macuciya mai zaluntar mutane, anya kuwa ke kika haifeni, wannan wace irin rayuwace, tir da halinki, wallahi nayi nadamar kasancewarki uwa a garen.........." saurin rufe mai baki Yaya Abdul yayi tare da girgiza masa kai, sannan ya zaunar dashi.


Duk wanda ka kalli fuskarshi a wurinnan zaka ci karo da irin bacin ran da ke kwance a fuskar, yayinda ko wanne yake mamaki da tu'ajjabin labarin da hajiya sailuba ta bayar, wanda ita kuma a lokacin sai waige² ta ke yi, tare da soshe², sannan ta kwala ihu tana fadin" haba oga kar kumin haka, wayyo Allah na, ku yi mini hakuri ganinan zuwa yanxu ²", wuf tayi ta tashi, kafin a ankara ta bace daga wurin.


Ganin sallar Azahar ta gabato yasa Baffa ya umurci kowannen su da suje suyi sallah, nan mazan suka wuce masallaci, yayin da matan jikinsu a sanyaye suka mike don zuwa gabatar da alwala.


Bayan Awa daya, zaune suke gaba dayansu, wanda a wannan lokacin sun yi sallah tare da cin abinci, Nan aka kuma sako zancen Baba usman da Daddy, wanda nan suka tabbatar mawa da 'yan uwansu ogan hajiya sailuba General Phillips shine ogan su daddy a waje'aiki, nan dai aka yi ma juna Allah kyauta tare da yafewa juna.


Nan Baffa ya koma kan Najeeb tare da mai nasiha sosai, sannan da nuna masa duk aibun iyayenka ba a canza ma tuwo suna, ba karamin samun natsuwa da nasihar Baffa yayi ba, yayin da take nan ya maida aurensa da Aunty Basma, duk da Daddy da Basma basu so ba, hakan nan dai suka hakura tare da yin fatan Alkhairi Saboda Baffa ya yanke hukunci, nan dai yayi sallam ya tafi yayin da ya ba ma Aunty Basma sati biyu don ta samu ta kintsa don barin kasar zawuyi.



Bayan tafiyar shine aka kawo case dunsu Huwailat, wanda Daddy ba karamin kaduwa yayi ba da jin zancen, sai dai gaba daya sun dauki kaddarar haka, yayin da nan matar Baba Usman ta tada bala'i akn baza tayi accepting din huwailat ba anan gidan, nan dai ta dauki lullubinta ta daka yaji, ganin haka ne yasa Daddy cewa Huwailat zata koma wurinsa da zama kasancewa Mama Asabe ta ce kauyensu zata koma.


Bayan sallar isha'i suka rankayo, yaya Abdul, Aunty Basma, Aunty Naina, Zahrah, Daddy da su little,wanda suka bar Aunty Ni'eema acan ta dan kwana biyu.

*A gurguje*


A yanxu wata biyu kenan da faruwar lamarin, inda yanxu suke zaman su cikin kwanciyar Hankali da kaunar juna, tsakanin Zahrah da Huwailat sai dai son barka don duk sun zubar da makamansu sun rungume junansu, yayin da Aunty Basma da Najib suka daga zuwa Paris, can ya samu canjin wurin aiki, Hajiyar sailuba ko tsintar gawarta akayi a wani incomplete building an kwakwule mata idanu tare da yanke harshenta, wanda ba aikin kowa bane sai na oga, acewarsa Madam Sailuba ya kamata ta mutu saboda suyi sacrificing da a idonta da halshe don su kara ma kansu power kasancewa a artabon su da Alaramma sunyi masa babban illa.


A yau suka tashi da shirin Tarbar manemin Aunty Naina, wanda suka hadu a wani shopping mall, gaba dayansu sun hadu a kitchen sai aiki suke yi harda Aunty Ni'eema, cikin raha da natsuwa suke aiwatar da aikinsu har suka gama, sannan suka gyara wurin tare da wanke kayayyakin da suka bata, sannan kowaccensu tayi wanka ta shiri irin na alfarma.


Karfe uku na rana suka karaso dashi da a kanninsa, an tarbesu cikin mutunci da girmamawa, sannan aka musu jagora suka gaida Daddy daga nana aka gabatar musu da abinci da soye soye.


Habeeb Sardauna da Ibrahim Sardauna(ib), su biyu iyayensu suka haifa wato Alh Ado Sardauna da Hajiya Maryam, kafin rasuwarsu yayin da sun bar musu makudan kudi, kasancewar Babansu ficeccen dan siyasa ne kuma dan kasuwa, sunyi hatsari a jirgin sama a hanyar dawowarsu saga umara, wanne dalilin yasa rikon ib ya koma wurin Yayansa habeeb wanda ya zame masa uwa da uba kasancewar ya bashi kusada shekara 14, ammaa Habeeb bai da wani aboki da ya wuce kanninsa ib, wanda shima hakan ne a wurin ib.


Habeeb yayi aurensa na fari da matarsa habeeba shekara biyar da suka wuce, wanda har suka samu rabon 'ya'ya biyu, yayin da a last year aka yi Appointing dinshi a matsayin Ambassador na kasar Turkey, wanda yanxu ma hutu yazo y hadu da Naina a Super market har suka fara soyayya, kuma sukayi amanna da auren juna.


Zahrah ce ta shigo parlourn tare da Aunty Naina, tun shigowarta yake binta da wani kallo kasa² wanda in ba lura kayi ba, baza kace kallonta yake ba, ganin sun karaso cikin parlourn yasa ya dauke kansa tare da maida hanakalinsa ga wayar da yake dannawa, sai dai kunnan sa ana wurinsu.

Gaisuwar mutunci sukayi, yayin da Habeeb ya ringa jan Zahrah da hira, ita kuwa sai sunne kai take yi sai kace wata Amarya, Haka kawai ta samu kanta da kunyarsa, jiyowa Ib yayi garesu yana mai fadain "Aunty Naina barka da rana", cike da jin kunyar yanda kato dashi ya kirata da Aunty ta amsa da" Barkanmu dai, ya Gida, ya yara?" Ta na mai tambayarsa .


Dariya Habeeb ya kwashe da shi tare da fadin" yara kuma, ai wannna duk girmansa da kike gani tuzuru ne, shi wai yaki aure sai ya samu mata Doctor, shi yasa nake kiransa da Mijin Doctor ai" ya karasa magana yana mai kara kwashewa da dariya, yayin da Ib ya hade rai yace" ka gani ko yaya, wallahi saboda Halinka yasa bansan fita dakai wallahi, duk inda muka je sai ka kirani da tuzuru, ai da bari kayi na amsamata, inta shigo gidanmu sai ta tabbatar ma idonta, amma yanxu ka bata min shiri, ni bazan ma jiraka ba, jibi zan wuce America, dama zaman nan danayi na sati biyu a kasarnan a daddafe nayi" ya ja wannna dogon zance cike da shagwaba da yatsine yatsinenn fuska, yayin da zahrah ta tsaya tana kallonshi ko ita data ke mace bata iya shagwabar da yayi baa.


Sai dai gaba daya ya tafi da ita, wannan shine first namijin da ya taba burgeta in ka cire yaya Abdul da Daddy, kare mai kallo take, kyakkyawan gaskene sai dai ba fari bane, chocolate colour ne, wanda babbancinsa kenan da yayansa, kasancewa shi farine, fuskarshi na dauke da lumshashen idanuwa kamar mai jin bacci a ko da yaushe, dogon hanci da dan karamin baki, sai saje da ya zagaye masa fuska tare da matsakaicin gemunsa, daga zaunan zaka ga alama yana da tsayi amma ba sosai ba, yayin da jikinsa yake a murje shi ba kato ba, shi ba siriri ba, ganin irin kallon da take binsa da shi yasa ya karkada mukullin motar hannunsa a saman fuskarta, cike da jin kunya ta janye idonta tana mai murmushi, ganin babu su Aunty Naina a parlourn yasa ta yi saurin mikewa tana mai kokarin barin gurin, wata dariya ya saki tare da cewa" wallahi kedai matsoraciya ce, ina kuma zaki,ke da aka bar mun ke ki taya ni hira,don Allah dawo nan madama".


Ji tayi kamar an daure ta a wurin, ba yanda ta iya haka ta janyo kafa cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna tana mai dukar da kai, domin ya cika mata ido, saboda kwarjininsa.


"Meye sunanki,which school are u" ya jefe ta wannan tambaya.

Lumshe idanu tayi cikin sanyin murya tace" sunana Zahrah, kuma baana school".


Da mamaki ya kalleta yace" bakya school, why?".

Murmushi tayi tace" bcos I am a medical doctor".


Wani kallo ya jefe ta dashi mai cike da ma'anoni yace" u are a doctor, wani hospital kike aiki".


" I am the owner of A.A.Rahman Specialist Hospital" ta fadi so proud.


Zamowa yayi da ga kan kujera, ba zato ba tsammani taji ya rike hannunta tare da fadin" Haba Doctor, ashe kina kusa kike ta wahalar dani, shi yasa tun da kika shigo naji a jikina u are my wife, please will u marry me?".ya fadi yana mai kwabe fuska.


Kasa magana tayi ta bisa da kallon mamaki tare da tambayar kanta wani irin mutum ne wannan, saurin katse mata tunani yana cewa" haba baby, answer me, will u marry me, wlh first sight sonki ya shige ni, I really love you my zahrah anda I really want you as a wife".


Yanda yayi magana ya saukar mata da kasala a jikinta, saurin janye hannunta tayi daga nasa tare da mikewa cikin sanyin jiki tabi hanyar kofar fita parlourn, sai da taje dai² kofar ta juyo ta sakin masa murmushi tare da cewa" l love u too" sannan ta fice, da gudu ya bi bayanta yana kiranta yana mai fadin "I love u too my Doctor".

_(Hmm, Abunka da soyayyar dan America da 'yar Indian, karshen soyayya kenan ba kunya😎😎)_

A takaice ranar zahrah ta fada soyayyat Ib, yayin da shima haka, kafin ya bar gidan sai da ya tursasa Habeeb yaje ya neman masa izinin wurin Daddy, wanda Daddy yayi farin ciki tare data bashi auren zahrah, saboda akwai kyakyawan alaka tsakaninsa da mahaifinsu Alhaji Sardauna kafin ya rasu, kuma kasancewa garin su daya da Mummy wato *Garzarma*.


Wata zafaffiyar soyayya suke nuna ma junansu,

Please Login or Register in order to submit comment