Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us kundun hikima* *writers* *association@facebook*






*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩‍⚕️💉_*



*_Written by fateeyzah_* 😍😍
*Follow me on wattpad@Fateeyzah*


*_Dedicated to Hauwa . A . Abba and Sophie H Muhammad❤_*

_Assalamu alaikum fans, da fatan an gama azumi lafiya, Allah ya karbi ibadunmu, na dawo da sabon novel dina mai suna *DOCTOR* *ZAHRAH* , ina rokon Allah yasa na fara a sa'a, sannan ina godiya gareku da irin kaunar da kuka nuna ma novel dina *GIDAN* *NAGOGGO* , naji dadin comment dinku ,Allah ya saka da Alkhairi yabar kauna._

_Wannan labarin nawa kirkirarren labari ne, ban yadda a juya min shi ta wata hanyar ko ayi editing ba sai da izinina._



_Wannan page din_ _nakune_ *HIKIMA WRITERS,* _da fatan anyi_ _sallah lafiya,Allah ya kara basira da zakin hanna._

*Doctor Zahra kirkirarren labarine dayake magana akan zumunci, daukar fansa, cin amana, rikici tsakanin 'yan uwa, karku bari a baku labari, just follow me from first page to last page.*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_01 to 05_*

Da gudu motar kirar Mercedes Benz ta shigo harabar Asibitin, wanda hakan yaja hankulan mutanen dake wurin, direct parking space motar ta nufa wanda ke dauke da allon da aka rubuta *SENIOR* *CONSULTANT* da manyan baki tayi parking a wurin, saida aka dauki kamar minti biyar tukunnan tabude kofar motar, kyakkyawa ce fara sol da ita, wanda kallo daya zaka mata kasan Allah yayi halitta a wurin ,zan iya cewa komai nata is perfect baiyi yawa ba sannan bai yi kadan ba, daka ganta kasan tahada dangi da shuwa arabs, *DOCTOR ZAHRA* Aliyu AbdulRahman kenan, wadda akema lakani da young doctor, shekarunta ashirin da hudu a duniya, itace mamallakiyar Asibitin A.A. Rahman memorial hospital, asibitin dayayi fice a fadin kasarnan, wanda sukayi specializing akan abunda ya shafi zuciya.

sanye take da wata baby pink gown wanda tadaura labcoat a sama, sannan tayi rolling da wani pink squeeze veil, wanda Hannunta na dama take dauke da wata baby pink cingum bag, hannun hagunta kuma dauke da jakar laptop, kafarta sanye take da wani pink toms me dauke da touch din white, cikin hanzari ta rufe motar tare da jefa key din cikin bag dinta sannan ta nufi upstairs building din wurin tana takunta cikin kasaita, upstairs ne hawa uku wanda aka masa painting green and white, duk inda ta gifta mutane ne ke kawo gaisuwa wanda ita kuma take amsawa cikin kulawa hade da murmushi kwance a fuskarta.

Daidai zata shiga lifter, wani tsoho dake sanye da wani army green din yadi wanda dakaga yanayin dinkin kasan uniform ne na security ya tawo cikin hanzari tare da fadin "barka da zuwa diyar albarka, an tashi lafiya".

Nan danan fara'ar fuskarta ta karu, cikin sweet voice dinta tace "lafiya lau babana ya iyali".

Fuskarshi dauke da mirmushi yace "suna lafiya diyar albarka, yau dai kin kusa latti, don tun dazu nake ta jiranki" ya karashe magana cikin kulawa.

Sai da tayi mirmushi sannan tace "wallahi kuwa babana, jiya ban kwanta da wuri bane saboda dan wani research danakeyi, dafatan dai ba matsala" ta karashe magana tare da jefomai tambaya.

"Ba wata matsala diyata, dama maganar Doctor sulaim ne don jiya da daddare sunzo wurina shida mahaifinshi akan inbaki hakuri ki dawo dashi bakin aiki, bazai sake aikata abunda ya aikata ba" yayi magana fuskarshi dauke da damuwa.

Nan danan ta hade fuska kamar ba ita yanxu ta gama murmushiba tace" babana ka fita daga wannan batun don gaskiya inajin kunyarka, girman laifin da Doctor Sulaim ya aikata yasa bazan iya dawo dashi bakin aikiba, asibitina na gina shine don taimako, wannan dalilin yasa bana so ana nuna banbanci tsakanin masu kudi da talakawa, amma duk da haka Doctor Sulaim yasan haka ya karya dokata, baba bari kaji abinda ya faru, wata yarinya aka kawo bata da lafiya,sai ya zamana tana bukatar jini,hakan yasa aka diba jinin babanta dayayi dai² danata za a kara mata,kafin a karan ne Doctor Sulaim ya dauki jinin ya kara ma 'yar chairman na local government, saboda mahaifiyarta ta kawota kuma aka rasa jinin daza a samata, shinefa aka kira babanta dake London aka sanar dashi, shikuma ya turama Doctor Sulaim 200k yace yanemi jini ko a inane a sama yarinyar, wannan dalilin ne yasa yaje ya dauki jikin daza a sama waccan ya gwada yaga yayi dai² da jinin 'yar chairman yasa mata, wanda da abun yazo da karar kwana yarinyar ta rasa ranta, baba wannan ba zalinci bane, salary danake basa ne bai isheshiba harsai ya hada da cin hanci wanda yayi sanadiyar rai" ta karshe magana cikin bacin rai.

Cikin sanyin jiki yace" hakane diyar albarka, wallahi ni bansan abunda ya faruba kenan, daban shiga wannan magana ba, amma don Allah kiyi hakuri"

Sai da ta goge zufar data feso mata a fuska tace" babana ya wuce, amma don Allah karka kuma zo mun da magana irin wannan don ba karamin miki take tadomin ba" ta karashe magana tana kokarin danna mabudin lifter.

Cikin rawar baki ya amsa da" insha Allahu hakan bazai kara faruwa ba"

Nan ta shige tabarshi a tsaye.

Direct office ta nufa wanda daga samanshi aka rubuta *SENIOR* *CONSULTANT* *OFFICE*, danna wata na'ura tayi mai kama da calculator a jikin wata kofa, sannan ta saka wasu numbers sai ga kofar ta bude, cikin takunta na kasaita ta shiga office din,sannan kofar ta rufe batare da ta tabata ba, babban office ne wanda aka shirayashi da ingatattun furnitures, tsaya wa badin haduwarsa bata lokacinne, direct side din dake dauke da tables da chair ta nufa.

Dandano sai zuwa bayan sallah.

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us@facebook, kundin hikima writers association*


*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩‍⚕️💉_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*follow me on wattpad@Fateeyzah*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad_* ❤




_Wannan page din nawane fateema zahrah Muhammad sani(fateeyzah)_

_I am +1, happy birthday to me, Allah ya biyamini bukatuna na Alkhairi, ya bani abunda nake nema duniya da lahira, ya tabbatar mun da Alkhairi acikin rayuwata, ya kara shiryatar dani hanya madaidaiciya, ameen._


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_Page 06 to 10_*


Ajiye bag dinta tayi da jakar laptop dinta akan table din, sannan ta cire labcoat dinta tare da rataye ta a jikin hanger, tukunna ta nufi kujerar dake gaban table din ta zauna tare da jawo jakar laptop dinta, hakan yayi dai² da karar telephone din dake kan table din, sai da taja tsaki tukunnan ta yi receiving tare da sawa a speaker, daga cikin telephone dinne wata murya mai taushi tace "good morning Doctor, you are speaking with sister Ganiyat, (ina kwana likita, kina magana ne da sister Ganiyat)".

Cikin zakakkiyar muryar ta ta amsa da "morning, how can i help u?, ( lafiya, dame zan iya taimakonki?)"

"Please Doctor we need you urgent in emergency ward, one of our patient is in crital condition, (don Allah likita muna bukatanki da sauri a emergency ward, daya daga cikin majinyacinmu ne yake cikin matsala)" Ganiyat ta amsa ta cikin muryarta mai taushi.

Cikin alamun damuwar wanda fuskarta ta nuna tace" when is he admitted?,(yaushe aka kwantar dashi?)".

"He was admitted last night (an kwantar dashi jiya da daddare)"

"I am coming, give me few minutes,(ina zuwa, ki bani dan mintoci)" tana gama fadin haka ta katse kiran batare da ta jira amsawar Sister Ganiyat ba.

Nan danan ta mike ta fara hada wasu kayayyaki sannan ta saka labcoat ta fice daga office.

Emergency ward ta nufa, inda tana shiga ta nufi gadon da ta hango nurses hudu a tsaye suna kokarin ba ma mara lafiya kulawa, ganin tawowarta dasuka yi yasa suka matsa daga jikin gadon don bata space.

Kallon majinyancin datayi yasa fuskarta ta sauya cikin bacin rai, sannan ta fara magana cikin sassarfa"who admitted this bloody idiot into my hospital(waya kwantar da wannan dan iskar a cikin asibitina)?" .

Cikin sauri tare da hada baki sukace "sorry doctor,he was admitted by Doctor Kamal(kiyi hakuri likita, Doctor kamal ne ya kwantar dashi)".

Cikin tsananin bacin rai ta nuna wani cleaner da yatsa tare da fadin"go and call 3 securities for me, i don't want to see him here( je ka kiramin masu tsaro guda uku, bansan ganinshi a wurinan)"

Haka suka tsaya jiran securities wanda baka jin motsin kowa sai na patient din dake ta sauke numfashin wahala.

Kusan minti uku sai gasu sun shigo su uku, cikin tamkewar fuska doctor Zahra ta nuna musu patient din da hannu tare da fadin"please take this man out of my hospital quickly( don Allah ku fitar da mutumin nan daga asibitina da sauri)".

Jin wannan umurnin nata yasa gaba daya wadanda ke ward din daga nurses, securities, har patients jikkunansu suka yi sanyi, don duk wanda ya kalli mutuminnan yasan yana bukatar taimakon gaggawa.

Cikin tsananin fushi da hargagi ta kuma kallon securities din tare da fadin "you are wasting my time( kuna bata min lokaci)".

Wannan yasa suka yunkura don daukar shi, wanda yayi dai² da shigowar wani magidanci wanda bazai wuce shekara talatin da biyu ba, cikin tashin hankali yace" where are u taking my dad, or are going to change room for him?(ina zaku kaimin dad dina, ko zaku canza mai daki ne?)".wannan yasa securities suka dakata da daukar patient din daza suyi.

Jin maganarsa yasa doctor zahrah ta juyo da fuskarta gare shi tare da tambayarsa" are you doctor shareef son?( kai dan doctor shareef ne?)"
Muryar shi cikin sauri ya amsa mata da "yes i am his son(eh ni dansa ne)".

Wani shu'umin murmushi ta saki wanda kana gani kasan iyakarshi fuska sannan tace"thank God because you are here on time, if not, you will meet your father laying outside the hospital , I want you to quickly take your father and leave my hospital because even if he is dying I will not check him talkmore of given him prescription.( ka gode ma Allah daya kawoka cikin sauri, don inba haka ba da ka sami babanka kwance a bakin Asibitinnan, inaso ka tattara babanka ku barmun Asibiti don ko zai mutu baza a dubashi a Asibitina ba ballantana har a bashi magani)".

Cikin marairacewa yace " oh doctor,why are you doing such things to my father, we came all the way from kano just to bring him to this hospital because people says you are the best for curing heart problems(haba likita mai yasa kike ma babana wadannan abubuwan, mun zo ne tun daga kano, don kawai mu kawo shi Asibitinnan don ance kunyi fice wurin magance matsalar zuciya)"


Cikin karaji tace" I said u should take your father away, saboda asibitin nan ba na mutane irinsa bane, shawarar dazan taimaka maka dashi shine ka kaishi new delhi specialized hospital dake kasar india, sannan in Allah yaba doctor shareef sauki kayi masa narrating abunda ya faru ayau ,sannan ka fada masa fateema zahrah Aliyu Abdulrahman tace kadan ma ya gani akan rayuwar da zaiyi nan gaba"ta karashe magana hawaye ya na zubo wa daga idan ta.

Cikin sauri ta fita daga ward din tana kuka, ba tare data saurari abunda wani daga cikinsu zaice ba, direct office dinta ta nufa, wanda tana shiga ta kifa kanta a table ta saki wani gigittacen kuka mai karyar da zuciyar, hakika duk wanda yaga Doctor zahrah a wannan lokacin sai ya tausaya mata, don kuka takeyi hani'an sai kace wata karamar yarinya.

A can ward kuma, hakanan mutumin nan ya tattara mahaifinsa da Doctor Zahrah ta kira da Doctor Shareef suka bar wurin, inda nan kuma hayaniya ta tashi a ward din, wasu patients na ganin rashin kyautawar abunda Doctor tayi, yayin da wasu suka mata uzuri kasancewa mace ce mai kima da mutunci wanda a koda yaushe zaka sameta mai tausayinta talakawa, don so da yawa wasu insuka kawo mara lafiya Asibitin kuma ya zamana sun kasa biyan bill, ita take basu kudi a aljihunta domin su biya.

yayin da bangaren nurses din wurin kuma suke ganin abunda tayi kamar creating ma kai enemies ne, amma duk da haka sun mata uzuri saboda wannan shine karin farko da suka ga tayin ma patient haka, indai da wani ma'aikacin Asibitin ne tayi ma haka, zasuce ta saba saboda bata daukar mistake, kuskure kadan ne zakayi ta sallameka ko ta rage albashinka, don bata daukan wargi, wannan dalilinne yasa kowannansu yake taka tsantsan da ita, don kamar hawainiya take a ko da yaushe cikin canza kala take, inko kabi dokokin data shimfida sai ku zauna lafiya.


_Nidai fateeyzah nace akwai rina a kaba_


A can office kuma haka Doctor Zahrah ta wuni tana kuka,don da ta share hawaye wasu kuma zasu kuma sauka, wayarta ko da telephone haka sukayi ta ringing amma ko kallon bangaren dasuke batayiba ballantana tayi yunkurin dauka.

Wurin karfe daya da rabi na rana ta dakatar da kukan da take gami da shiga toilet tayo alwala tazo ta shimfida sallaya ta tada kabbarar sallar azahar.

Cikin minti 10 ta idar tare da daga hannunta sama tana addu'a hawaye na zubo mata, nan ma sai da ta dau mintoci sannan ta shafa tare da ninke sallayarta da hijab, ta maidasu karamar cabinet din da ta dauko ta ajiye.

Bag kawai ta dauka da phone dinta ta fice daga office din,direct parking space ta nufa, ta dauki motarta ta fice a guje, haka ta ringa shimfida gudu a titi, tanayi tana share hawaye.

Cikin 30minutes ta iso gidanta dake G.R.A Anguwan rimi, wani mahaukacin horn ta danna wanda hakan ya razanar da baba maigadi, da gudu ya ajiye tsintsiyar dake hannunshi ya nufi gate da gudu, nan danan ya kwaye mata gate din, da gudu ta shigo da motar ko kallon baba da yake mata sannu da zuwa batayi ba, tanayin parking ko cire key din motar batayiba ta dauki bag dinta ta bude mota ta futo, ko tsaya rufe motar batayiba ta tunkari main door din shiga gidan, nan ma wasu numbobi ta yi pressing tukunna ta bude kofar ta shiga.

Makeken parlour ne da aka cikashi da kayan alatu, an gyarashi ko ina tsaf², da kyar take jan kafarta har ta hau stairs,dakin dake bangaren dama ta bude ta shiga, wani katon royal bed ne pink and gold da ya malale rabin dakin,sai wardrop da su mirrow, bangare daya kuma studying table ne da computer a saman table.

Cilla bag dinta tayi da wayarta akan gado, sannan ta nufi wardrop ta fito da wani katon kwali, zama tayi dirshan a gaban kwallin sannan ta fara budewa, kwalabene aciki na codien dau totaline, nan ta fara, idan ta kafa kwalba a baki sai ta shanye, sai ta jefar ta kuma daukar wata, sai da tasha kwalba hudu,nan danan idonta ya kada tayi ja, take ta fara lumshe ido tana ta jijjiga kai, nan ta kuma daukar kwalba daya ta bude ta kai baki, banko kofar da aka yine ya dakatar da ita daga kaiwa baki, cikin yanayin maaye ta dago kai ta kalli kofar, saurin yadda Kwalbar hannunta tayi tare da fadin " wallaaaahi bazaaaaan" bata karasa ba taji saukar mari wanda sanadiyar haka sai data kwanta, nan bacci ya kwasheta.



*Tofa🤔likita da shaye²*



*Shin fans menene alakar Doctor Zahrah da Doctor Shareef?.*

*Shin Doctor Sulaim ya hakura da korar da Doctor Zahrah ta masa ne?.*

*Waye ya mari Doctor Zahrah a cikin Bedroom din ta?.*

*Meye dalilin dayasa office din Doctor Zahrah da Gidanta ke dauke da wannan numbobin na tsaro.*


_Duk ku bini daki², kar kuyi missing din ko one page._



_More comment, more typing_



*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*


*_Fateeyzah_*✍




*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us@facebook, kundin hikima writers association*


*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩‍⚕️💉_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍
*follow me on wattpad@Fateeyzah*



*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad_* ❤




_Wannan page dinkune_ *Fateeyzah novel fans* , _da fatan anyi sallah lafiya, Allah ya karfi ibadunmu._


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_Page 10 to 15_*

Kallo daya zaka masa ka gano tsantsar kaman dasuke yi da doctor, kakkaura ne, giant sanye yake da wandonsa na kakin soja,sai wata army green silk shirt, wadda ta matse masa kirji duk ta fito da da cikakkiyar kirar shi ta da namiji.

Daukar ta yayi kamar jaririya ya shimfideta a saman gado, sannan ya fara tattara kwalaben dake wajan, haka yabi sako² na dakin duk kwalbar da ya gani yana hadasu wuri daya, hatta kwayar maganin da bai yadda da ingancinta ba sai da ya daukota, sannan yazo ya ringa iban su yana fitar dasu.

Bata farkaba sai misalin karfe shidda na yamma, mika tayi hade da karanto addu'ar tashi daga bacci, wanda a dai² lokacin wayarta dake yashe akan gado ta fara ringing, cikin mutuwar jiki ta dauko wayar tare da receiving din call din sannan ta danna speaker, daga cikin wayar wata zakakkiyar murya tace" hello habibty"

Cikin sanyin murya ta amsa da" na'am Aunty Basma, ina wuni"

"Lafiya habibty, kar kicemin wannan birthday ma bazaki yi attending ba,don muryarki ta nuna
min kamar ma daga bacci kika tashi" Aunty basma tayi magana cikin sanyin murya.

"Don Allah Aunty kiyi hakuri, tunda na dawo wurin karfe biyu daga Asibiti nake bacci sai yanxu ma na farka"

"Cikin kakkausar murya Aunty basma tace"wai har yanxu Habibty baza kiyi ma kanki fada ba, ki rungumi maraicinki, kinje kinyi shaye shayanki ba dole kiyi ta bacci ba"


"Aunty nakasa controlling din kaina ne, abubuwan dasuka faru a baya, su suka dawo mun ayau, Aunty Doctor Shareef fa aka kawo Asibitina yana fama da heart problem"

Muryarta dauke da mamaki da bacin rai tace" Doctor Shareef kuma a Asibitinki, Kai zahrah anya ko shi kika gani, mutumin da ya koma kasar Egypt mai zai kawo shi Nigerian, yana ciwo bama yazo ziyara ba"

"Wallahi Aunty shine, saboda da danshi ma suka zo, kuma dan ya tabbatar mun dashine".

"To wani hukuncin kika yanke masa?, karki cemin kin masa treatment, don in haka ta faru sai nayi takakkiya nazo na shemeki wallahi"tayi magana cikin zakuwa da bacin rai.

"Haba Aunty, aini nafiku kullatan shi, ni da komai ya faru a gabana, ai korar kare na masa shi da dansa, kuma wallahi inkika gansa yana jin jiki" ta fadi so proud.

Cikin murya mai cike da jin dadi tace"ai kin min dai² habibty ,Allah ya biyaki".

Ta amsa da" Amin, wai ina Aunty Naina ne, ko bata karaso bane?".

Tana can garden tana gyara decorations, wallahi habibty ni ji nake kamar kar ayi birthday dinnan, sai inga kamar abunda ya faru a baya zai faru da fawas shima" tayi magana cikin karayar zuciya.

"Haba Aunty ki kwantar da hankalinki, duk abunda kikaga ya faru yana cikin kaddarar mutum, kinga tunda mummy ta nace sai anyi, ki saki ranki kawai, kuma kafin ki fita ki tofe shi da ayatul kursiyyu, da qul'a'uzai".


Sai da ta saukar da nannauyar ajiyar zuciya sannan tace" nagode da tunatarwar nan habibty, insha Allahu zanyi kamar yanda kikace"

Ta amsa da" Amin Aunty, a shafa min kan celebrant, happy birthday to him, sannan ki gaida Aunty Naina, ayi celebration lafiya"

"Zasu ji Insha Allahu, bye" .

Nan tayi cutting din call din hade da sauke nannauyar Ajiyar Zuciya.


Mikewa tayi ta nufi toilet tayi wanka hade da dauro alwala, cikin kankanin lokaci ta gama shiryawa cikin farin three quarter da farar body hug, sannan ta feshe jikinta da storm body spray, sannan ta shimfida sallaya ta tada sallah.

Sai da tayi sallar isha'i tukunna ta sauko kasa kasa domin samun abunda zata sama cikinta.


Zaune yake a 2seater ya daura kafa daya kan daya, hannusa rike da remote, gaba daya hankalinsa ya koma ga kallon kwallon daya keyi, karar tafiyar ta yaja hankalinsa kanta, wani harara ya wurga mata, wanda yasata rufe ido da sauri.

Cikin husky voice dinsa yace" meye na rufe ido, ai bani ya kamata kiji kunya ba, mahalliccinki ya kamata kiji kunya, wai ke habibty wace irin yarinya ce mai kunnan kashi, kina Sane da side effects din shaye² amma kikeyi, ke ba abun kunya bane a gareki kina Doctor, Doctorn ma mace kina shaye², ko da kikeji ana fadin wasu Doctors suna shan giya ai mazane, amma ke kina 'yar musulmi, jikar musulmi a sameki da aikata haka, tir da rayuwarki wallahi kina sani ina ganin laifina, sai inga kamar ban rike amanar da iyayenmu suka barmini ba" ya karashe magana yana sharce zufar data tsatsafo a goshinsa.

Fuskarta taf da hawaye, don tun daya fara magana suke zuba a idonta, ta karaso tare da zubewa a gabansa hade da ruko kafarsa tace "yaya Abdul don Allah kayi hakuri bazan sakeba, wallahi bazan sakeba, na kasa controlling din anger nane, shiyasa ka sameni inasha, amma insha Allahu bazan kuma ba, ka yafemun yaya, ayanxu kaine uwata kaine ubana, bani da wani gata da ya wuce kai dasu Aunty Basma"

Cikin karayar zuciya kamar ba soja ba yace" habibty haka kullun kike cewa bazaki karaba, amma ba ki keeping promise dinki, na fada miki

Please Login or Register in order to submit comment