An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIRI. By Mrsjmoon. Adabi Writer's Association (AWA) https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 (Hatsabibin tsibiri kagaggen labari ne, ba'ayi shi dan wani ko wata ba in anci karo da abinda ya yi daidai da rayuwarka/ki alkalami ne ya zo da salon. Labarin zaiyi nutso ne cikin wata rayuwa mai ban al'ajabi na matsafa tare da wata ƙasaitacciyar masarauta da magajinsu ya shigo da salon da tun ginuwarta tayi hannun riga da lamarin. Duhu, Haske, Ƙarya,Gaskiya, Zalinci, Tausayi, Halarci,Butulci, Sadaukarwa, son mulki bakin rai bakin fama gami da tasirin riƙo da Addini duk na ƙunshe cikin tafiyar Mrsjmoon a cikin wannan labarin na Hatsabibin tsiri. Ya Allah ka lamuncemin na rubuta abinda zai amfani al'umma. Allahumma Amin. *Littafin baki dayansa sadaukarwa ce ga aminaina masu dubun karamci a gareni wato Khadija Candy da Rahma Kabir, Allahu ya ja wannan zumunta har zuwa gidan Aljanna mu zamo makwaftan juna Alfarman sayyidul sadati Manzon Allah S.A.W. Amin.* Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ka karo dubun salatai marasa irga ga masoyinnan naka, shugaban Halittu baki ɗaya abin alfaharin salihan bayi, jagoran mabudin alkhairai, Abul Fad'imatul Zahra'u Sayyiduna Muhammadur Rasulullah S.A.W. Page 01 Tekun Kabobo. Teku ne mai faɗi da tsawo wanda ya ke cikin k'ungurmin dajin da ke yammacin Hatsabibin tsiri kuma gabashi da Masarautan birnin Mungaye. Ruwan Tekun na da abin al'ajabi domin da safe zuwa rana kalansa blue ne amma idan marece ya shiga sai ya koma fari k'al wanda mai gani kan iya hango halittun da ke rayuwa a ƙasanshi na shawagi dan k'asansa na dauke da halittun da ke rayuwa a ruwa nau'ika daban daban, kama daga Kadoji, Kifaye da sauransu haka yashi da tsirrai koraye duk suna bayyana a fili ga duk wanda ke iya kawo ziyara da yamamcin. Duk wannan girma da Tekun ke da shi gami da yawan ni'ima ya zamo hange daga nesa ga Fulani makiyaya domin basa iya isa gab'an shi balle tsautsayi ya kai dabbobinsu su shan ruwansa, hasalima basa biyo hanyar sai bisa makuwa inda suna farga da dimuwan da sukayi zasu sanja hanya tare da kare hanyar da dabbobin zasu isa zuwa gab'an Tekun domin jugewa samun asara dan duk wanda ya yi kuren isar bisashensa bakin Tekun zasu afka ciki tamkar waɗan da aka tura. Hatta da mafarauta ba kowa ke shiga dajin Tekun ya dawo lafiya ba sai in har ya kai kwaro wurin tsafi tamkar irin tsirarun jama'ar Hatsabibin Tsibiri. Sai kusan shekaru biyu da ya gabata Gimbiya Lina d'iya ga Sarki mai mulkin Hatsabiban Tsibiri ta maida Tekun muhallinta shi ya janyo matsafan sukayi nesa da Tekun domin girmama muradin mafi soyuwar Gimbiyarsu. *** Guguwar iska ce ta turnik'e sararin samaniya dajin ya koma bak'ink'irin tamkar ruwan sama na daf da sauka domin ba sautin da ke tashi sai gunjin fitar iska wanda guguwar ta ke kad'awa da mugun k'arfi gami da tashin duk abin da taci karo da shi zuwa sararin samaniya, abin mamaki har da ƙananun duwatsu iskan sama ta ke yi da su tamkar ledoji. Ƙara gami da rugugi kawai ke tashi abinda ya haddasa rud'ewar tsun-tsayen da ke saman bishiyoyin da suka kewaye Tekun soma neman wurin tsira. A daidai wannan lokacin Gimbiya Lina na zaune a saman ruwan Tekun Kabobo ta hard'e kafafunta saman kujera mai ruwan zuma tamkar ta hau saman dutse kamar yarda wurin da ta ke zaunen ya nuna babu alamun ruwa mai motsi balle igiyarshi ya wuce da ita ta zamo abin kalacin halittun ruwan. Ga dai shi ruwan Tekun na tsiri gami da kumfa na gudu cikin murd'ewar igiyoyi sai dai kafin ya iso inda ta ke zaune ya ke sanja hanya ya zagayeta ya nausa gaba inda ke isa tsakiyar Tekun ya rufe dutsen da ke tsakiyarshi ruf zuwa wasu sakonni dutsen ya bayyana tamkar ruwan bai tab'eshi ba. Murmushi ta saki cike da nishad'in ganin yarda ruwan Tekun ke wasanninsa, jin rugugin ya ƙi ƙararewa sai ta d'aga kai ta tsirawa sararin samaniyar ido na tsawon sekon goma sannan ta sauke kallonta kan fatar jikinta da ya ke bud'e ba sutura sai walwali ya ke yi cikin d'aukan ido tamkar jikin tarwad'a, sake kallon giragizan ta yi da suke k'ara yin duhu sai ta shafi fatar dantsen hannunta na hagu tare da kallon halittan k'irjinta masu ban sha'awa da cika domin ita kanta in ta kallesu suna burgeta saboda zubin da Allah ya yi musu na kyawu gami da jan hankalin duk wanda ya yi arba da su. Shafosu ta yi da hannun dama idanunta lumshe sumar idanunta na d'igar da ruwa na bin saman kuncinta. Girgiza kai ta yi sumar kanta ya yi tsiri sama ya fesar da ruwa sannan ya dawo ya rufe mata fuska zuwa saman k'irjin, ta yaye sumar da hannunta na hagu tare da sake kallon sararin samaniya a tak'aice ta kauda kai gefe cikin had'e fuska. "Lima kenan, tabbas neman maganarki ya yi yawa, sam bakya son a zauna lafiya, kin addabi'a al'umma tsibiri kin kuma hanani watayawa a can, to ai shi kenan mu zuba mugani, domin jiya ba yau ba, Gimbiya Lina ta tumbatsa matuk'a, zata baki mamaki dan haka bari in nuna miki kaɗan ya ke Gimbiyar da bata kai a ambata mata sunar ba." Ta furta a hankali tare da jan tsaki mai sauti ta nuna guguwan da tafin hannunta wani haske ya soma fita daga tsakiyar hannunta na nufar iskan, aikam tamkar kiftarwar ido sai ga sararin samaniyar ya washe tangaras, ta sauke numfashi tare da share gumin da ya tsats-tsafo mata a saman goshi sai ta mike a saman ruwar ta yi nutso cikin Tekun, kujerar da take zaune ya zama walk'iya ya b'ace haka ruwan da ke sanja hanya a inda take zaune ya samu damar biyowa na kai da kawon shi. Bak'ar tsun-tsuwa ce mai yarfin ja a fuska-fuskanta ta baiyana gefen Tekun zuwa can ta bud'e fuka-fukan ta soma shawagi a saman Tekun zuwa kimanin 'yan mintoci sai ta zama bak'in hayak'i ta b'ace. Gimbiya Lina da ta nutse cikin kogin sai da ta sami kimanin mintoci goma sha biyar sannan ta taso sama ta soma tafiya tamkar tana taka turb'aya dan yarda k'ura ke bin bayan takalmi idan ana tafiya a kan sa to haka ruwan ke tartsi na bin diga-digan Gimbiya Lina, wanda suke farare sol tamkar yarda fatar jikinta ya ke. Tafiya ta keyi tamkar wacce ke filin gasar sarauniyar kyau dan cikin k'asaita ta ke takun abin da ya bawa mazaunanta da ke cikin siririn pant damar motsawa tamkar ba ita ce mamallakinsu ba dubi da yarda take mara k'iba su kuma gasu da fad'i gami da cika tare da fitar da shape na musanman tamkar wacce aka zana su a jikinta. Ta yi tafiya har zuwa tsakiyar Tekun sannan ta tsaya jikin k'aton dutsen ta bud'e hannayenta tamkar walk'iya ta rikid'a zuwa balbela fara sol ta tashi sama zuwa wani tsauni da ke kusa da Tekun tana sauka ta yi girgiza ta dawo halittarta na Bil'adam ta yarfe yatsunta biyu saiga sutura ya baiyana a jikinta cikin shigar doguwar rigan yadin karan miski fari da ratsin ja tare da takalmin fata half cover mai launin Sarauta shima fari ta mik'a hannu jan gyale mai yarfin fari ya baiyana saman tafin hannunta ta nad'e kanta da shi ya zauna d'as, ta sake mik'a hannu kwalban turaren Company mai daraja mai suna LOST IN YOU ya baiyana ta fesa tare cilli da shi sama ya b'ace wani kwalban turare fari sol tamkar ruwa ya bayyana ta kai bakinta ta b'alle murfin ta kafa a bakinta ta shanye tas tare da cilli da kwalban ya zama walk'iya ya b'ace ta had'a hannayenta wuri d'aya ta manna a saman goshinta tare da kulle ido tana wani surutai saiga wata budurwa mai kama da ita sak tamkar an tsaga kara ta baiyana cikin shiga mai kamanni da nata, suka tsirawa juna ido kowa da karatun da ruhinsa ke kitsawa masa. Gimbiya Lina ce ta kawo k'arshen shirun da cewa "Ba kya jin magana ko Lima? Shin wai har sai yaushe zan daina yi miki gargad'i akan shigomin yanki batare da neman izininta ba?" "Baki isa ba Lina kuma bazaki tab'a isar ba, yankinki ko yankina? Ko kin manta ne in tuna miki? Ni ce mai k'arfin iko sama da ke dan haka kada ki sake yimin tsaurin ido domin zan hukuntaki tamkar uwar gijiya da baiwarta, dafatan kin tuna tazararmu da juna na sanin alkaliman sihiri." "Oh rigimar na ki ta nan ya b'ullo? To zan barmiki nan amma ki sani duk ranar da kika k'ara binciko inda na ke sai kin raina kanki domin yanzu ba da ba ne, na ga ba ya yi ga ba na baya kam sai tsintar hula sannan ina baki shawara ki koyi yarda ake magana da shugaba kada ki sami matsala nan ba da jimawa ba domin Gimbiya Lina ce gabanki sarauniyar Hatsabibin Tsibiri lokaci kaɗan mai zuwa." "Haka zalika nima Gimbiya Lima ce a gabanki wacce kowa na tsibiri ke tsoron karo da ita domin bata san wargiba aiki da cika ne takenta ko da kuwa ga jininta ne sannan magajiyar karagar Hatsabibin Tsibiri batare da wasi-wasi ba." "Na yaro kyau take bata karko amma bari in barki ki gama cika bakin naki sai 'yar nanuniya ta nuna shugaban wani a tsakaninmu ba da jimawa." Dogon tsaki Lima ta ja tare da kaiwa kafadar Lina duka cikin cewa "Ke dalla ni rufemin baki ki zauna ki sanarmin da inda kikayi b'atan dabo na tsawon shekara d'aya da rabi, kika barni da jidalin rabuwa biyu duk in Abun ya nemi ganinmu a lokaci d'aya domin bana son b'acin ranshi idan ya gano bakya Tsibiri zai iya sauke fushin a kaina." "Binciken ki ya bayyana miki inda na je tunda bazaki fita sabgata ba kamar yarda ba ruwana da naki sannan baruwana da fushin Abun dama Mah kika ce to na duba lamarin." "Idan kin isa ki cire hijabin da kika sanya a tafiyar naki kisha kallon tonon silili kamar yarda na tabbatar cikin jikinki da kika tafi da shi d'an kwanaki talatin da bakwai wanda kika b'oye haihuwarsa kuma fushin Abun ya dad'e bai dameki ba idan kinso kice ba shi ne makyen-kyashinki ba daga sama kika fad'o." Jim Lina ta yi tana kallon 'yar uwarta zuwa can ta motsa labba ta ce "Lima sharrin da zakiyimin kena, na Haihuwa? A she tsanar naki har ya kai haka? Ni ce fa Linar da ta tsani ak'idarki na bilayi a gidan hutu, shin me yasa zaki jefeni da lamarin da kika san ban taɓa sha'awar aikatawa ba?" Kinfi kowa sanin ban iya sharri ba domin abin da nake da tabbacin shi na kanyi zantuka a kansu sannan kin fi kowa sanin ina kan gaskiya, tabbas kin bar Tsibiri da ciki dan haka maza sanarmin ko ranki ya b'aci, yanzu na aikaki gaban Abun ba sutura ki fuskanci hukunci." "Zama bak'ar guguwar da kika zo a cikinsa ki b'acemin da gani ko in illataki sannan ki sani na wuce gaban barazanarki, jiya ba yau ba ce Lima na sake sanar da ke wannan kalman kuma ki saita harshenki kada ki fusatani na aikata miki abinda zai taɓa min domana ( rai)." "Kome zakiyimin bazan kauce ba sai na san gaskiyan da kika b'oye kuma shi ne dalilin da yasa na rufa miki asiri ban sanarwa Abun labarin bakya cikin Tsibiri ba domin ina son na soma hukuntaki kafin ya yi miki nashi." "Saboda na zama karyan maza irinki ba, mara yiwa kanta amfani?" "Lina in magana kike son faɗamin kin makaro domin kaf sirrikanki a tafin hannuna suke dan haka ki biyoni mu koma tsibiri ko infasa kwai kowa ya san halin da kika kasance na yin cikin da baida sahihin uba sannan da ƙarfi akayi miki kika b'oye wanda yayi saboda kina yiwa jama'a bakin cikin samun ganimar jinin shi." "Ko yanzu lokaci bai k'ure miki ba maza tafi ki tona asirin domin ban shirya komawa Tsibiri yanzu ba ko wannan ganin da kikayimin wani dalili ya sanyani fitowa duniyar tsirrai dan haka yanzu zan koma dausayin sanyi na cigaba da rayuwa tare da hallitun ruwa masu amana." "Aikam kin gama komawa k'asan Tekun Kabobo Lina tunda ke ba aljanar ruwa bace haka ban san ta inda kika haɗa dangi da 'yan ruwa ba." Dariya Lina ta bushe da shi tare da zama a saman wata kujera mai haske da ta bayya gabanta tamkar kiftarwar ido wanda haskenta ya kashewa Lima ido ta k'are da tafin hannunta tana ja baya, hannu Lina ta kai ta rik'o hasken tamkar igiya haka ya shige tafin hannunta sannan Lima ta samu damar dauke hannayenta daga saman fuskanta ta zubawa Lina ido wacce ke cin kayan lambu da suka bayya gareta cikin wani container mai d'aukan ido shima. "Lina banda tsafi da muka gada kin koma ruwa biyu ce?" Bata amsa ba illa murmushi da take dokawa cikin jijjiga kai. "Wani Aljani kika samu ya baki sa'a irin wannan? Ko shi ne wanda ya yi miki cikin?" "Lima idan baki daina ambatar cikin nan ba zan sab'a miki." "Zamu sab'awa juna dai Lina domin baki isa b'oyemin halin da kika fad'a ba kuma duk takunki ban k'yaleki sai kinyimin bayanin inda kika b'oye ko rayuka su b'aci." Kayan marmarin ta watso mata cikin fushi Lima ta yi sauri daga hannu suka tsaya cak batare da sun iso inda ta ke ba haka basu sauka k'asa ba. Numfashi su sauke a tare sannan suka ja baya ko wacce rai a haɗe zuwa can suka juya baya sannan suka juyo da makamai rik'e a hannunsu cikin gaggawa ko wacce ta nufi 'yar uwanta da nufin halakawa. A ta ke k'azamin fad'a ya b'arke tsakaninsu, guguwa ya turnik'e ya rufesu ruf baka ganin kowa cikinsu sai fitar sautin takubba tare da walk'iyar hasken sukan da suke kaiwa juna. Bayan wucewar mintoci goma sha biyar sautin ya d'auke gami da washewar guguwar, wurin ya koma babu su sama ko ƙasa. Takun ingarman doki ne ya ratso saman tsaunin da ya sanya itatuwar tsaunin soma fad'uwa ƙasa zuwa can wani gabjejen Sadauki ya bayya zaune a saman dokin ya iso ya tsaya a daidai wurin da Lina ta zauna yana bud'e k'ofofin hansa sai kuma ya diro ya shafi dutsen gefen da ta jingina da shi ya sunsuna ya soma waige-waige sai ya juya da hanzari sai ya kaiwa inda Lima ta tsaya duka sauti ya fita dum! Ya ja tsaki sai kuma ya zabura ya hau saman dokinsa ya nausa cikin tsaunin da mahaukacin gudu dokin na sakin haniniya wanda ya hargitsa k'ananun haluttun tsun-tsaye. *** Lima ce ta soma bayyana jini na zuba a gefen kanta zuwa can itama Lina ta bayya dafe da kafad'arta jini na bin hannunta, a tare suka kalli juna ko wacce ta shafi inda taji ciwo a take ya koma babu alamun rauni suka sake kallon juna ko wacce taja tsaki tare da sauyawa zuwa halittar tsun-tsaye suka sula sararin samaniya. Lina ta nufi kudu, Lima ta nufi yamma sai dai bayan wucewar mintoci uku Lima ta dawo saman tsaunin ta talli wata bishiya take ta tsage ta rabe biyu, ta bushe da dariya cikin cewa "Na san zaki dawo wurin nan Lina ni kuma na yi alk'awarin gano sirrinki tare da gano uban da yayi miki ciki kika b'oye bayyanarshi balle Kadojin kogin sihiri su sami abin kalaci kud'in shigar Tsibiri ya bunk'asa dan ina jiyowa da karfi ya ketaki sannan na yi alk'awarin bawa Kadoji jinin wannan mutumin domin barinsa a raye barazana ce ga lafiyar tsibirinmu mai dogon tarihi da ya barranta ga haik'ewa mata da ƙarfi." Tana ambatar hakan ta yi girgiza ta dawo yarinya karama cikin takun hawainiya ta isa gaban bishiyar da ta tsage ta shige ta koma ta kulle tamkar wani abu bai faru ba. Daga can saman girgije Lina ta huro iskan bakinta zuwa kan bishiyar take kuwa ta b'ace b'at sannan ta sakko ta tsaya tare da kama k'ugu ta ce "Ni walkice daidai k'ugun kowa Lima, ki farka barci lafiya tare da mance kin ganni a zahiri domin nuna miki na wuce da saninki, yanzu ba da ba ce da kike shugabana a sanin alk'aluman sirihi da mugunta, ni yanzu shugabar kowa da ke HATSABIBIN TSIBIBI ne hatta kuwa da mahaifanmu nasha gabansu balle wancan basamuden banzan Buda wanda ke kan wahalar da kanshi, burina na daf da cika domin ba da jimawa ba zan kawo sauyi a tsibirinmu, Gimbiya Lina nan ta fe gareku ya ku jama'ar Hatsabibin tsibiri da samuwar cikar 'yancin da kuke burin wanzuwar shi." Tana ambatar haka ta lula cikin girgije tamkar walk'iya bata sauka a ko ina ba sai saman Tekun Kabobo. "Lina!" Sautin kiran sunarta ya karad'e yankin bata waiwayo ba saboda ta gano muryan mai kiran nata sai kawai ta yi girgiza ta zama babban kifi ta yi nutso cikin Tekun daga can saman tsaunin Buda ya zaburi sihirtacce dokinsa ya daka tsalle zuwa cikin Tekun wanda yana fad'awa ruwan Tekun ya sanja kala zuwa launin yellow a maimakon fari k'al. Faruwar haka da seconds halittun cikin Tekun irin kifaye da kadoji suka soma fitowa suna yada zango a gefen Tekun wasu kuma na tseren hawa saman dutsen da ke tsakiyar Tekun. A take kuwa Ruwan Tekun ya soma maik'o yana taruwa wuri d'aya tare da yin tsiri na feshi zuwa jikin bishiyoyin da ke kewaye da shi. Mrsjmoon ce. Ku daure ku buɗe Arewabooks👇 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI BY MRSJMOON ADABI WRITER'S ASSOCIATION. https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕 *Shafin sadaukarwa ce ga kafatanin member na Adabi Writer's Association (AWA) Allah ya ƙara dankon kauna mara algus, Amin.* Page 02 Juyi Lima ta yi cike da jin daɗin barcin sai ta jita a k'asa tim! daga saman gadon da ya ke da wani launi na daban da sauran gadajen da jama'a suka saba gani. A razane ta tashi zaune tana sosa bayanta cikin son tuno abin da ya faru amma ta kasa kamo komi tsaki taja ta dubi bangon d'akin tare da hura iskan bakinta sai ga Lina ta bayyana tana zabga murmushi yamutsa fuska ta yi tare da mik'ewa ta ja hannunta tana cewa "Nagaji da wannan wahalar narantse duk inda kike sai na nemoki domin hakan ya tauyemin jin dad'in rayuwata na tabbata Lina kin aikata min hakan ne dan murgunamin tare da hanani fita holewata amma duk ranar da na yi ido biyu da ke bazakiji da daɗi ba." Duk yarda taso jin basaja fushin da ke fuskanta ya koma irin murmushi fuskan fake Lina ta kasa saboda yau ta fusata sama da kullum, ga shi Abun bai nemeta ba taji son zuwa gareshi. Wani tsakin ta kuma ja tana dokawa dake Lima harara ita kam sai murmushi dake dokawa abinta. "Wallahi ba dan rabi ruhina da ke nanne jikinki ba da yau na kasheki na huta." Gurnani tajiyo a bayanta ta juyo cike da masifa amma bataga komi sai sake jan tsaki zuciyarta na ƙara shiga ƙunci. Fadar mahaifinsu ta nufa kai tsaye, tana shiga fadawan suka soma mik'o gaisuwa cike da tsoro ba wanda ta kula ganin haka suka watse aka barta da mai Tsibiri. Ta iso ta sunkuya gabanshi ya mik'a hannu zai dafata ta tashi da sauri tana dariya fake Lina da ke bayanta duk'e itama ta tashi tana dariyar girgiza kai Dattijon ya yi tare da kaiwa wani tulu duka a ta ke dake Lina ta nufi jikin Lima ta shige suka zama a bu d'aya, ya kalleta ta sunkuyar da kai ya nuna mata hanyar fita cikin fushi sai ta iso gabanshi ta zauna tare da kamo hannunshi. "Kada kice komi Lima na jima da gano Lina bata wannan tsibirin sai dai tsawon lokacin na kasa gano inda ta b'oye duk da bincikena yana nunamin tana rayuwa cikin walwala da 'yanci amma na kasa samun natsuwar ruhi akan inda ta ke da dalilin aikata mana wannan munafuncin sannan ina hango wani haske mai son maidani makaho a tare da ita amma a yau Buda ya gano mab'oyarta a k'asan Tekun Kabobo kamar yarda bincike ya bayyanarmin mintoci biyu kafin shigowarki, yanzu haka ina dakon isowarsu ne duk da ina shakkar isowar sa tare da ita." "Saboda me Abun kake shakka?" "Lina ta soma bani tsoro da gaske ba wasi-wasi." "Abun me ya razanaka da ita haka, alhalin ko tsun-tsun Tsibiri bata iya kamawa saboda sokancinta da rashin amfani?" "Kayya Lima, ki bi a sannu domin wannan sabuwar Lina ce mai cike da sadaukantaka ta fannoni da dama haka bincikena ya haskomi halin nan nata na tausayi shi ne zaiyi sanadin kawo k'arshen Hatsabibin Tsibiri mai dogon tarihi domin ba'a gina shi dan adalci da tausayi ga bak'i ba amma ita ce ta farko da zata shigo mana da sauyin da dole mu amsa kamar yarda taso yin nasara a baya." "Ta ina hakan zai sake faru Abun?" "Ban sani ba Lima amma ina lalibo hakan a lokuta da dama tun kuwa kuna tsumman goyo shi Kaka Gunu ya keb'eki ya rik'a nuna miki sanin ilimin tsafi fiye da ita ya kuma raini ruhinki da rashin tausayi wanda kika rik'a wahalar da ita mahaifiyarku na yi miki kashedi kina watsi da kamarin saidai a yau na hango alamun ta samo sanin alk'aluman tsafi fiye da wanda kike tare da shi dan na kalli artabunku na d'azun duk da ta yi dubarar b'oyewa cikin iskan guguwa dan ta san zan gani sai amma ta makaro dan komi ya bayyana gareni tamkar kuna gabana." "Abun dama ba mafarki na yi na had'u da Lina ba har muka goge raini?" "Eh ba mafarki ba ne, tabbaas kin had'u da Lina wanda hakan ya bawa Buda damar gano inda ta ke ta bayan b'atan dabon da ta yi na tsawon shekara d'aya da watanni ta hanyar jiyo k'amshinta wanda ta nan mafi akasarin jama'ar Tsibiri ke ganeku.." "Abun me kake son sanar dani akan 'yar uwata Lina?" "Babu komi 'yata illa hatsarin da Lina zata zame mana musanman ke domin zuciyarta ya ginu da tausayi ne ya yin da na ki ya ginu da tsabar mugunta, Kaka Gunu ya sanarmin d'abi'unki na kamanni da kakan-kakanninmu wanda shi ne silar samuwar Tsibirin nan wato Sarki Goma na farko." "Abun rabani da wannan zantukar gaibun na Kaka Gunu yanzu babban damuwata shi ne sanin gaskiyan abin da Lina ke b'oyewa." "Nafiki son gano lamarin da ta birne wanda bokayenmu suka kasa gano shi hatta kuwa da ni sarkinsu kuma jagorar wannan tsibiri." "Abun, shin yanzu Lina tafika k'arfin tsafi kenan?" "Bata isa ba Lima." "To meye yasa ka kasa gyara Mata zama?" "Har abada bazan tab'a fito na fito da ita ba saboda ina son 'yata haka itama bazata tab'a yin gaba da gaba da ni ba domin girman da ta ke ganina da shi ya wuce tunaninki tana kawai nuna miki tafi damuwa da mahaifiyarku ce kamar yarda kika fi nuna damuwa da ni sannan zan baki aiki wanda na san akanshi kike wato na son gano lamarin Lima baki dayanshi na tsawon tafiyar da ta yi." "Ina saurarenka Abun." " 'Yata Lima a yanzu nake son ki shiga bukkan Kaka Gunu kiyi wannan binciken." "Abun yau da kanka ka amince in shiga taskan sirrin Kaka Gunu wanda ya ke kulle tun bayan mutuwarshi?" "Eh na baki damar shiga ya ke 'yata, dama can gadonki ne dan ya tabbatar min ke kad'ai ya mincewa shiga bukkar amma bisa babban bincike shi yasa na baki umurnin shiga dan gano mana abin da Lina ta b'oye da kuma wanda ya koyar da ita dabarun ilimin sihirin da ya ke son doke wanda muka gada Kaka da kakanni." "To Abun kasan da wannan wasiccin ka barni ina ta wahala tsawon shekara d'aya da rabi akan wancan sokuwar yarinyar?." "Akul Lima! 'yar uwarki ce bana son wannan tsanar da kike nuna mata wanda na yi imani shi ne silar b'oye miki sirrikanta ga shinan zai wahalar da ke a banza." "Abun bana sonta tunda Mah ta nuna da ita take yi ba ni ba." "Lima kin sanfa an raba ne ke ce nawa ita kuma na Mah ɗin ku." "Na barka lafiya Abun gobe da safe zan taho maka da bayanai wanda na amince tono sirrin Lina ce kaf d'inshi." Ta ambata tare da mik'ewa bayan ta subbaci bayan hannunshi. "Baburdo ya taimakeki 'yata." "A'a Abun ruhin Kaka Gunu ya bani sa'a zakace domin Baburdo Dodon gadin Tsibiri ne bai isa bani taimakon komi ba saima ni ce keyi masa alfarma na shaƙar ni'imar Tsibirin." "Haka ne Lima to ki fito lafiya cikin kiyayewar Ruhin Kaka Gunu." "Amin." Ta fice cikin sauri tana yarfe hannaye cikin salon mugunta inda yarfin ke fitar da iska na watsar da mutanen da duk ta ci karo da su a kan hanya wasu tsoffi ne da yara k'anana ya yin da masu ƙarfin tsafin ke kare kansu tun kafin ya iso inda suke, ganin jama'a na neman wurin buya saboda giftowarta sai tayi amfani da wuta da kunna a tsakiyar Tsibirin a take mutane suka soma kulle gidajensu masu sana'a suka tsere wutar ta soma bin kayansu tana lashewa, sai hakan ya wadata k'irjinta da nishad'i tayi ta zabga murmushi, batare da ta kula da illar da wutar takeyiwa jama'ar ba tayi gaba abinta tana dariya. Ruwan ƙanƙara ne ya sauko a cikin minti ɗaya ya kashe wutar tare da ɗaukewa batare da sanin Lima ba hakan ya afku, jama'a suka dawo bakin kayansu suna tsinewa Lima a cikin zukatansu. Tafiya mai tsayi Lima ta yi kafin ta isa bakin bukkan da ke cikin kogon wani dutse duk a saman Tsibirin. WAIWAYE A DON TAFIYA. *Asalin Tsibirin da mutanen da ke rayuwa a cikinsa.* Hatsabibin Tsibiri, Tsibiri ne mai dogon tarihi domin sarakuna masu dama ne suka shud'e a cikinsa kuma dukkannunsu abisa turba d'aya suka ginu wato tsafi da kafurci domin basa da abin bauta balle wurin bauta, gasu nan dai kara zube domin ko Dodo Burda da ke TSIBIRIN basa bauta masa dan a mai gadi suka ajiyeshi ta hanyar yin bishara idan bak'o ya shigo ko samun wanda ya karya doka na yiwa mata fyad'e dan duk da wannan duhun da suke ciki suna kyamatar ketawa mata haddi. Mafarin TSIBIRIN ya samu ne bisa jagorancin sarkin farko mai suna GOMA wanda aka ci shi da ya k'i inda ke mulkin al'uma masu yawa, sakamakon rashin nasarar da ya yi ne ya yi hijira da iyalansa ya yada zango a Tsibirin lokacin wurin sansanin miyagun namun daji ne da suka kashe dajin mafarauta da makiyaya suke tsoron haurowa samansa,. Saukan sarki Goma ya sa suka koma gefen TSIBIRIN suka kewayeshi cikin yi masa mubaya'a domin k'arfin tsafinsa kad'ai ya isa zamowa bara zana ga rayukansu. Sarki GOMA ya yi nasarasar k'awata TSIBIRIN cikin alk'aluman sihiri yarda kowa ya keto cikinta sai ya burgeshi kuma ya zamo ganimansa in ya so ya maidashi bawa in kuma ya so ya kasheshi musanman idan ya bincika yaga mai addini ne. A haka ya cigaba da shimfid'a mulkinsa tamkar yarda ya keyi a birninsa da yayo hijira sai dai ya k'ir-k'iro wasu ababe ya sanya su doka mai zaman kansa wanda d'aya da ga ciki shi ne sanadin yo hijiransa wato dokar ita ce ta hana mazaje haik'ewa Mataye wato yi musu fyad'e amma bai hana zinace-zinace ba abisa ra'ayin juna amma ayiwa mace da k'arfi wannan babban laifi ne domin duk wanda ya aikata hakan kafin macen ta kawo k'ararsa fadar Sarki Dodon Burda zai yi kuwwa mai razanarwa kuma a take kowa zai halarta gaban faɗar Sarki inda wanda ya aikata laifin zai fito da kansa tsirara mahunta lamarin su sanya takofi mai kaifi su datse masa al'aura tare da d'aukansa zuwa wata muguwar k'orama da Sarki GOMA ya k'irk'ireta na musaman domin hukunta masu laifi mai suna k'oranar sihiri, su jefashi ciki, wacce ba komi cikinta sai ruwa mai rai da lafiya tare da manyan Kadoji wanda abincinsu ya zamo manyan namun daji da mutane masu laifin aikata fyad'e da masu hayowa tsibirin dan ganin k'wam. Haka duk sarkin da ya hau sai ya k'ara inganta wurin da salon muguntarshi na daban inda kudin shigarshi zai sake ninka na sarkin da ya gabata. Wannan doka na hana fyad'e Sarki Goma ya aiwatar da ita ce saboda 'yarsa d'aya tilo wacce ya ke tsananin so da k'auna Gimbiya Aya da wani cikin jama'arsa ya yi.mata fyad'e lokacin da tafita shak'atawa bayan gari a sanadin ta rasa ranta sai gawarta aka kawo masa cikin jini babu kyan gani hankalinsa ya tashi ya bazama duban wanda ya aikata laifin sai ya baiyana d'an sarkin yak'insa ne ya aikata a ta ke ya sanya aka kamosa ya datse masa kai da hannunsa a bainar jam'a lamarin da ya haifar da k'azamin fad'a tsakaninsa da rundunar Sarkin yak'i inda Sarakunan da suke yammaci da na kudanci suka taho suka marawa Sarkin yak'in baya suka rufuma rundunar Sarki GOMA inda suka sami nasara akansa tunda ya fahimci kutunguilar da suka shirya na su sami nasara akansa su maidashi bawa sai ya silale da kafatanin ilalansa wanda suka had'a shi da matansa biyu da 'yayansa biyar dukansu maza dama Aya ce d'iya mace tilo cikinsu. 'Yayan ba wanda ya yi aure sai mutum d'aya wanda matarsa ke goyon jariran 'yan biyu suma maza. Cikin mabiyansa an sami wasu sun rufa masa baya sai ya sami nasarar tafiya da jama'a masu d'an yawa. Dukkan kulawan Sarki Goma akan 'yan biyun nan ne har suka samu isowa HATSABIBIN TSIBIRIN da yaga dacewar ya zamo fadarsa amma akan hanya ya yo fashin zuk'a-zuk'an 'yan mata guda biyar wanda suma sukayo gudun hijira bisa jagorancin wani Sadaukin mayak'i inda ya amince zai tserar da su amma bisa sharad'in zasu zama matarsa a take kuwa suka amince shi ne ya biyo hanya da su bisa gudunmowar alk'aluman tsafi sai kuma ya yi rashin sa'a ya gamu da tawagar Sarkin GOMA ya ritsashi ya kasheshi ya kwashe 'yan matan inda ya mallakawa 'yayansa suka angwance a lokaci d'aya bayan kammaluwar gyaran Tsibirin wanda ya bashi suna da HATSABIBIN TSIBIBI domin bak'o bai tab'a shigowa TSIBIRIN ya fita ba fa ce wannan Dodon ya kamoshi ya bawa wad'an nan Kadoji sunyi watanda da Naman shi ko a maidashi bawa daga bisani ya zamo dan Tsibirin na har abada ya manta da Asalinsa balle burin komawa garesu. Wannan zalincin yasa mafarauta da sauran ma'abota shiga daji basa bin ko gefen TSIBIRIN duk kuwa sonsu da yankin saboda ababen tsoratarwa dake kewaye da Tsibirin yafi ƙarfin ji da ganinsu har gara kafin bayyanar Sarki Goma sukanyi shiri na musanman su hau, yanzu kam ba wanda ya san yarda TSIBIRIN ya koma balle ya bada labari dan duk wanda zai bada labarin an halakashi ko ya zama ganimar Tsibiri. Mrsjmoon ce🥰 Ku daure ku buɗe Arewabooks👇 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon ADABI WRITER'S ASSOCIATION. https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕 *Shafin na Mum twins ce Kawalliyata Billy Galadanchi, Allah ya bar kaunar ta har abada mara algus, Amin ya rabbi.* Page 03 Wad'annan manya dokoki sunyi matuƙar tasiri wurin d'aukaka darajar TSIBIRIN ta inda mutanen cikinta ke alfahari da kansu domin sukan sakko yin farauta inda suke razana makiyaya su d'auka wasu halittu ne na daban ko aljannu ne suka bayya garesu inda zasu gudu subar dukiyarsu sai su kame shanye tarw da tarkacensu ciki har da yaransu maza da mata wanda basa iya gudu ceton rai, su dawo kan TSIBIRIN su sadaukarwa Sarki shi kuma ya d'iba ya bar musu sauran su raba tsakaninsu domin lokacin basu da yawa sosai kome suka samo na wadatarsu. Yara da suke rabosu da iyayensu kuwa suna zuwa Sarki ke tsaface zukatansu su manta da danginsu su saje da jama'ar Tsibirin in suna da addini su koma marasa shi. Shi yasa babban yare a Tsibirin Fulatanci ne sai yarensu na gado wato Dusanci sai ko tsillin yaren Hausa domin cikin mafarautan da tsau-tsayi ya kan ritsa da su zuwa farauta yankin an taɓa kamo Bahaushe inda ya zauna a fadar Sarkin zamanin tare da miƙami mai girma wanda yanzu a cikin tsatsonsa ne Sarkin yaƙi ya fito wato mahaifin Jarumi Buda. Jama'ar Tsibiri mafi aka sarinsu suna da hasken fata mai daukan ido musanamam matansu shi yasa suke da kyau na ban mamaki ko da kuwa baƙin fata garesu to zaka gansu masu cika idanun mai kallonsu ne dan haka maza da matansu masu d'aukan hankali ne ainun sakamakon gauraya da jinin Fulanin usul da sukayi. Suna da zumunci na ban mamaki tare da rufawa juna asiri, jimlatan sun kasance masu amfana da kayan juna ne sam basu san k'eta da mugunta ga junarsu ba shi yasa suke zaune tamkar Uwa ɗaya Uba ɗaya. Tafiya ya yi nisa inda TSIBIRIN ya cika da 'ya'ya da jikoki inda duk a tsarin da Sarki GOMA ya ginasu suke wato tsafi da kwace wanda tuni ya mutu shekaru masu yawa da ya shudewa, sai babban d'ansa ya gajesa bayan ya rasu shima d'ansa ya gajeshi, haka dai suka cigaba da rayuwa bisa gadon-gado tare da cigaba da gina mulkin zaluncin na fashi da makami gami da sace 'yan matan Fulani su zamo uwayen ƴaƴansu sai dai ba wacce ake haikewa sai tare da son ranta domin a zamanin wani sarki mai suna Numan babban bafadensa ya taɓa haikewa ɗaya daga cikin wanda sukayo fashin dan nuna isarshi a fadar tunaninsa ya wuce ayi masa hukunci, aikam yana gamawa Dodo ya kwalla ihu kafin ace kwabo jama'a sun taru gaban fadar Sarki, ana haka cikin dakon jawabin da za a yi masu saiga Bafaden nan ya bayyana tsirara, batare da duba girmansa gami da mikaminsa ba aka datseshi tare da jefashi a kogin sihiri tun daga ranar jama'ar suka sake shiga taitayinsu suke gujewa aikata wannan zunubi. A wannan karnin Sarki Barde ke mulkin TSIBIRIN wanda ya kasance jika ga sarki Gunu wanda ya sauka mulki batare da ya mutu ba dalilin mutuwar magajinsa wato mahaifin Barde dan haka ya nad'a jikinshi Barde dan shima ya kasance yana da halin zalinci amma yana kawo tsari mai b'ullewa ga masarautar tamkar yarda Sarki na farko ya ke yi dan ba'a tab'a sarki mai kawo mafita ga Tsibirin ba irin Sarki Goma sai kuwa yanzu da sarki Barde ke kamantawa amma duk da haka suna da bambanci mai tazara domin shi Sarki Barde wani lokacin yana kamanta adalci sab'anin Sarki Goma da zaluncin kawai ya sanyawa gaba tare da wad'anda suka biyo bayanshi ciki har Kaka Gunu. A kawo sauyi ga Jama'ar Tsibiri Sarki Barde ya sanya mutanensa sun soma Noma da kiwo a gefen Tsibirin inda duk wani makiyaya da suka jiyo k'amshinsa zasu bi bayansa su yake shi su mamaye dajin baki ɗaya. Da yaga sun tara abin duniya sai ya hanasu fashi da makami sai bisa lalura ta rashin abinci sannan ya nad'a mutum uku da zasu rik'a kaikawo a tsakanin jam'ar TSIBIRIN. Sai ya killace TSIBIRIN ta inda ba mai iya fita gefenta da zarrar sun cire amfanin gona face mutum uku sun amince masa, kome mutum ya keso a nan TSIBIRIN zai samesa domin ya bud'e musu kasuwa na cinikayyan kayan abinci da sutura dan yanzu suna saka kaya sab'anin a baya da suke saka ganye da fatu. Na mijin da ke da aure zai saka dogon wanda da rigar 'yar shara mara aure kuwa gajeren wando zai saka da rigar sak'i na Fulani, mata kuwa da mai aure da mara aure zani da riga na sak'i suke sakawa su nad'e kansu da bak'in sak'i sai dai 'yan matan sunfi saka godayen riguna na farin yadin karen miski da ratsin ja. Su wad'annan mutum ukun da Sarki Barde (Mai Tsibiri) ya wakilta sun had'a da Sarkin Noma wanda alhakin kula da kayan amfanin gona ke hannunshi shi ne ke fitarwa da Sarki kasonshi kafin mamoni ya soma amfana da kwayar hatsin da ya noma haka shi ke hada-hadar sai da musu da kayan ya kawo musu kudinsu ba cuta ba cutarwa. Sai na biyu shi ne mai dawa wato sarkin mafarauta wanda shi ne ke kula da abu-buwan da ke faruwa a dajin da kewayen Tsibirin gudun samun tangarda mahara su kawo samame duk da Tsibirin na kewaye da alk'aluman tsafi. Sai mutum na ƙarshe shi ne Sarkin yak'i wanda shi ke sanya ido a kai da kawon kowa dake cikin Tsibirin da shirin ko ta kwana idan mai dawa ya yi nisan zango zuwa farauta. Musanman Sarki Barde yasa aka farauto driver da motarsa, ya sami wata biyar yana ko yawa mutane uku nan mota bayan sun kware ya korashi daji inda Namun daji sukayi watanden namansa bayan ya turawa 'yan matan Tsibirin sun gama zuk'e masa ruwan jiki da jarabarsu daga nan labarinsa ya zamo tarihi. Sarkin ya sama musu motoci uku lafiyayyu inda suka soma shiga cikin gari suna mu'amala da su ta hanyar fitar da amfanin gonansu su siyar su siyo wanda basa shukawa tare da sutura irin tasu sai dai duk in zasu shiga gari sukanyi shiga irin na makiyayan usul wani zubin kuma suyi irin na kabilun da suke hurd'a da su shi yasa abokan huld'an kasuwancin nasu basu gano daga inda suke fitowa ba balle su zama abin tsoro. Duk wannan lamari da ake ciki Tsibirin baida magaji domin matar Sarki Barde bata taɓa yin bari ba, ganin haka sai ya dukufa yin tsafi akan ya samu haihuwa inda kakanshi Gunu ke tausarshi da cewa zai haihu da zarar lokaci ya yi. Kwatsam bayan shudewar wasu shekaru matar sarki ta sami rabo inda ta haifi 'yan biyu dukansu mata masu kama d'aya tamkar an tsaga kara, ranar suna anyi bidiri na gaban kwatance daga bisani aka sanya musu suna Lina da Lima inda suka ci gaba da girma bisa kulawan mahaifansu da kakan mahaifinsu wato tsoho kaka Gunu. Sai dai tun suna tsumman goyon suka taso da bambancin ra'ayi inda Lina mai tausayi ce Lima kuma muguwa, hakan yasa basa ga maciji da juna. Lima ta soma cutar da 'yar uwanta Lina tun kafin su san kansu sai Mahaifiyarsu wanda suke kira da Mah ta maida kulawarta ga Lina shi kuma Abun ya maida nasa kulawan kan Lima inda Tsoho Guna ya mara mashi baya. Sadda suka soma tasawa sai Kaka Gunu ya killace Lima ya soma koya mata dabarun tsafi da yak'i ya yin da itama Lina ke amsar horon wurin d'an sarkin yak'i Buda a b'oye batare da sanin kowa ba wanda ya kamu da sonta batare da ta san yanayi ba, dalilin da ya k'udiri aniyar horar da ita kenan domin yana sane da wariyar da Kaka Gunu ke nunawa tsakaninta da yar uwanta sai dai abinda bai sani ba horarwan baiyiwa Lina amfanin komi saboda kafin ta dawo gida Kaka Gunu zai lalatashi idan ta dawo nanma mahaifiyarta kan cigaba da koya mata tsafi domin tasan ilimin sosai wanda shi ne ke amfanarta domin Kaka Gunu bai lalatashi bisa wani dalili nashi na daban. Ganin sun soma taka makakin girma sai burin Sarki Barde ya koma kan tagwayen 'ya'yan dan yana aiyana wata rana d'aya daga cikinsu zata jagoranci jama'an Tsibirin domin su kad'ai ya mallaka saidai burinshi yafi karkata akan Lima saboda muguntarta da k'arfinta tamkar babban sadaukiya sabanin Lina da ke da sanyi tare da gudun zalinci dan lokacin suka shiga shekaru goma sha ɗaya a duniya amma a haka Lima ke iya dambe da manyan sadaukai kuma ta samu nasara akansu. Tunanin mai Tsibiri daya dana Kaka Gunu duk da a tarihin Tsibirin mace bata taɓa jagorantar su ba. Lokacin da suka taka matakin cikakkun 'yan mata sai rashin jituwar su ya k'ara tsanani sakamakon ganowa da Lima ta yi Sadauki Buda na son Lina wanda ta ke ganin bata isa kaiwa matsayin ba alhalin gata wacce ta tara abin so fiye da ita kamar k'arfi da tarin ilimin tsafi, wannan dalili ya tunzurata ta ƙara k'aimi wurin murguna mata ya zamo bata jin dadin zaman Tsibirin kwata-kwata, sai ta soma keb'e kanta tana rayuwa ita d'aya inda Lima zata binciko wurin taje ta mallake a cewar ita ce ke da ikon mallakan wurin hutawa sama da Lina. Tsananin Lima ya soma kai Lina bango gashi bata son suna fada da juna, sai kawai ta koma duk in ta fita rangadi sai ta ajiye kuyanginta a bayan gari ta zama tsun-tsuwa mafi gudu cikin tsin-tsaye ta nufi biranen da ke da nisa da su inda zatayi ta ganin ababen al'ajabi musanman bauta da taga jama'a na yi a killatattun d'akuna masu kyau abin da yafi bata mamaki shi ne ganin yarda suke gudu idan ana magana a abin fitar sauti (Kiran sallah kenan) sai ta lalace wurin kallonsu gami da sauraren muryan da ke fitowa (Karatun Qur'ani kenan) ta kan b'ata lokacin tana saurare tare da son shiga wurin amma sai ta riƙa jin hucin zafi na dawo da ita baya inda zatabar wurin a d'imauce amma idan ta nemi shiga dayan ginin da ake kida da rawa gami da wak'a sam bata jin hucin zafi sai tafi maida hankali a wurin inda zatayi ta binsu suna tikan rawa batare da ta bayyana masu fili ba balle su koreta har ta soma ƙaunar yaren da suke magana da shi ta soma fahimta kaɗan-kaɗan. Wani zubin kuma in ta shigo birnin sai ta tare a makarantun boko inda wannan ya bata damar jin yaren turanci managarci har take fahimtar abinda ake koyarwa a d'akin da ake yin rawa da wak'a. Sosai ta sami ilimin boko batare da sanin kowa ba sai mahaifiyarta wacce bata boye mata duk abin da ta aikata, sannan tana halarta Masarautu kala-kala tana naɗo salon mulkinsu domin wata rana ta shimfida a Tsibirin su da take da burin mulkansa ko da hakan zaizamo ajalinta ne. A kwana a tashi Lina na nad'o labarai na samun 'yanci sai watsam ta soma aiwatar da manufarta cikin dibara inda ta kawo sauyi a tafiyar mulkin Tsibiri inda ta soke tsarin hana jama'ar Tsibirin fita lamarin gabansu sai da izini wanda ba dan mahaifin nata ya so ba ya amince rok'onta sai dan manufar da ta gina maganar akai mai amfani ne na abar kowa na fita shan iska duk inda suka so da harkan cinikaiya da kansu saboda ta nan zasu kara wayewa na daga abin da basu sani ba sannan tanan za su iya ƙarowa Tsibirin sanin da bata da shi ta fannoni da dama. Ganin ta samu nasara a nan bayan wani lokaci ta sake wargaza wani tsarin inda nanma ta sauya musu shigar sutura ta kawo tsarin 'yan gidan sarauta dole su bambanta da jama'ar da basu da sarauta inda ta ce suna da damar saka suturun da suka so a duk sadda suka ga dama kuma mai tsada da burgewa irin wanda yayi daidai da ra'ayinsu musanman ga 'ya'ya mata ababen ado da kwalliya su kuma jama'ar gari ta ce suna da damar saka sutura masu rufe jiki duk kalan da suka so amma banda irin na gidan Sarauta. A nan gefen ne tasha wuyar janyo hankalinsa har ya amince da tsarin inda Lima ta yi ta fushi wai Lina na son juya kan mahaifinsu son da keyi mata ya dawo kanta sai da kyar ya iya shawo kanta ta janye ik'irarin sai ta yi yaƙi da Lina. Jama'ar Tsibiri kam sun ji dad'in wannan sauyi dan a take suka soma bata girma sama da wanda suke bawa Lima dan killace su a wuri ɗaya yayi mugun takurasu basa da bakin magana ne kawai ya sa dole sukayi biyayya ga abin da iyaye da kakanninsu suka wanzu a cikin shi. Mrsjmoon ce🥰 Ku daure ku buɗe Arewabooks👇 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon. ADABI WRITER'S ASSOCIATION. https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕 Page 04. Sai dai abin da basu sani ba Lina ta yi yaƙin k'wato masu 'yanci ne domin kanta saboda gudun kada mahaifinsu ya gano tanayin nisan zango zuwa wani yanki batare da saninsa ba haka tana da burin shiga ta alfarma kamar yarda take ganin a masarautun da take zagayawa da ke birane daban daban sannan tana da burin samo ilimin tsafin da zai bata kariya daga zalinci Lima tare da samun damar shiga fadar da jama'a ke turu-ruwan shiga musaman ranar juma'a suma taga wani kalan bauta sukeyi tare da iya yarensu mai ratsa zuciya. (Masallacin Juma'a da karatun Alqur'ani Lina take magana) Burinta ya cika inda ta cigaba da fita yawo duk inda taga dama a kuma sadda ta so dan har ta kan kwana a can amma bata wuce kwana ɗaya zuwa biyu duk tanayin tafiyar ne bisa amincewar Abun tare da neman albarkan Mah. Lima hankalinta ya tashi sadda ta fahimci yawon da Lina ke fita wani sabon ilimi take samowa wanda nan gaba zai iya zama bara zama a gareta, sai itama ta soma yin nisan zango saidai ita ilimin zalunci take sake koyowa inda zata dawo tayi ta azabtar da bayi tare da jama'ar gari hakan kuwa na faranta ran Kaka Gunu domin alamomin gadar karagar mulki na ta ƙara bayyana a gareta, sai ya ƙara mara mata baya tana cigaba da zalintar wanda basu ji ba basu gani ba, har saida Abun ya tsawatar mata tare da nunawa Kaka Gunu illar hakan ya ce a bari ta hau mulkin zaifi wannan kalamin nasa ya fusata Kaka Gunu har ya ce ba wanda ta gaji ruwan tulun albarkansa sai Lima sai Abun ya rokeshi da ya b'oye zancen zai cika masa wannan wasiccin. A cikin wannan tsakani Kaka Gunu ya mutu, Abun ya tafi dan mallakan Ruwan Tulun da sauran sirrikan tsafi amma ifritan da ke gadin Bukkan suka hana shi da ya matsa sai suka nemi halakashi kan dole ya hak'ura amma yana cike da burin mallakan wannan ruwa na albarka. Bayan wasu shekaru burrin Lina ya cika domin ta samo ilimin da take burin mallaka wato tsafin da ya doke na Lima wanda yanzu take shirya fito na fito da wanda ya nemi kawo mata cikas a cikin manufarta na zamowa magajiyar karagar kujerar HATSABIBIN TSIBIBI domin shimfid'a mulkin adalci gami da samar masu da abin bauta su daina zama kara zube, su sami ilmomi mabambanta haka tana burin ganin wayewar su ya zarta na biranen da take shiga tana ganin cigaba da suke tare da shi mai burgewa haka babban burinta shi ne su sakko daga kan Tsibirin (Tsauni) su gyara dajin ya zamo birni mai zaman kan shi tare da kayan more rayuwa in yaso saman tsibirin ayi masa gyara ya zamo wurin shakatawa na musamman da jama'a daga birane daban-daban zasu riƙa zuwa yawon buɗe ido kuɗin shiga na halal na samuwa ga Tsibirin daga nan ƙarshen zalincinsu ya zo su kowa rayuwar 'yanci mai cike da farin ciki tare da zumuncin ga kowa, baƙi su zamo abar karramawa a tsibirin. Tarihin Hatsabiban Tsibiri da Sarki Goma ya gina ya zamo ya tarwatse sai wanda ta ingana da kanta, sunarta ya zagaye Duniya da tambarin Adalci. Saidai a gefen Lima duk kishiyar burin Lina shi ne nata wanda a kullum da shi take kwana da tashi. *Wannan shi ne asalin labarin Tsibirin da rayuwar jama'ar cikinsa gami da burikan tagwayen Gimbiyoyin.* Cigaban labari. *** Lima a Bukkan Kaka Gunu. Ta tura kai cikin Bukkan bayan ta yi amfani da alkaliman sihiri k'ofar bukkan ya buɗe, cikinsa katon wuri ne da ya cika da k'okunar kan namun daji kala daban-daban a can daga nesa wani kilisa ne mai daukan ido samansa da kujerar na alfarma ce, wurin Lima ta nufa ta hau saman kujeran ta zauna tana fesar da iska cikin nuna izzar jinin sarauta. "Barka da isowa uwar gijiyata, me ke tafe da ke?" Kallon tsamurmurin tsohon ta yi cike da mamakin bayyanarshi ba neman iso daga gareta. "Affuwan uwar gijiyata na kasance zaune a wannan bigire shekaru masu yawa domin tun sarki na biyu nake a matsayin hadimisa sannan nine sirrin dukkanin sarakunan da suka shude dan haka kema nine idonki akan komi umurninki kawai nake jira yanzu kiga aiki da cikawa." "Me ye sunarka?" "Tsidau uban yan binciken wannan fada." "Madallah, yanzu na zo ne domin sanin abin da 'yar uwata Lina ke boyemin game da tafiyarta da duk abin da ya faru gareta tun kafin tafiyar har zuwa yanzu." "Kwanta ki huta uwar gijiyata kina tashi na yi alkawarin bayyana miki duk abin da ya shige miki duhu akan Gimbiya Lina." "Tsidau bana jin barci domin bashi na zo yi ba." "Dole kiyi shi uwar gijiyana." "Kada ka kawomin wargi na hukunta ka y kai Tsohon wofi." "Tuba nake Sarauniyar Gobe, fushinki kukan yaro." Tana shirin sake magana ya hura mata iskan bakinsa a take ta zame daga kujerar kanta langabe alamun barci ya ɗauke ta, da yatsarshi ya nunata sai gata kwance saman kilisar ta yi matashin kai da wani filo mai zanen fatar jakin daji. "Shin ta ina zan soma boye miki sirrin abin da kika zo bincike?" "Bar wurin don ka gama aikinka kafin ta farka na nade sirrin da aka barmata gado." Muryan Lina ya ratso. "Na barki lafiya Gimbiya mai jiran gado." "Ko da yake kafin nan zauna da ita ya kai amintaccen hadimin Sadauki Gauɗu bari in koma na sallami wancan lalataccen kada maikon kogin da ya yi jagorar samar da shi ya halaka shi." "A dawo lafiya ya ke adalar Sarauniyar Duniya." Murmushi ta yi tare da b'acewa shi kuma ya gyara zama gaban Lima ya tsirawa hawa da saukan numfashita ido tamkar mai irgawa. Rugigi ya ji a bayanshi kafin ya tantance dalilin afkuwan lamarin Bukkan ya ɗauki rawa wani gaton dutse ya d'ago daga ƙasa inda ke zaune ya nufo inda ya ke yana fesar da koren wuta, tamkar walkiya Tsidau ya b'ace a daidai lokacin Lima ta farka a firgice sai dutsen ya koma mazauninshi tamkar bashi ba. Abun ne ya shigo a rikice ta tashi da hanzari ta isa gabanshi ya rik'o hannayenta ya soma magana. "Ya ke farin cikina wannan binciken yafi karfinki dan haka ki lamuncemin amsar gadonki domin na samu damar taimakonki." "Abun zan iya, kabarni da kayana." "Bazaki iya ba tunda ga shinan an sakaki barci bisa hila wanda saninki da ilimin tsafi bai amfana miki komi ba a wannan gab'an." "Abun waye Tsidau?" "Hadimin ne ga 'yar uwanki Lina." Ware ido ta yi cikin cewa "Lallai Lina ta shiryawa taran aradu." "Biyoni kawai domin sanin ta inda zaki bullowa lamarin." Biyo bayanshi ta yi cike da zantukan zuccin wanda ta sanyawa ranta sai ta nemo sanadin afkuwansu dan hatta Abun ta soma wasi-wasin a kansa. *** Lina ce tsaye a saman ruwan Tekun Kabobo fuska a haɗe ta watsa wani haske da ya fito daga babban yatsar hannunta na dama,a take maikon da ya b'ata ruwan ya soma tafiya har ya b'ace amma launinsa na yellow bai sanja ba. Ta sake tsuke fuska tana fitar da huci zuwa can ta yi gunji ta soma tafiya a saman ruwan a hanzarce har ta isa tsakiyarshi kujerarta ga gold ya baiyana a saman dutsen da ke tsakiyar Tekun inda wasu halittun ruwan sukayi dandazo domin gudun hijira daga halaka, ta zauna tare da tsirawa ruwan Tekun ido da ya ke sake komawa yallow mai duhu, zuwa can dokin Buda ya taso sama ruwa ya yi tartsi tare da fitar haniniyarshi mai firgitarwa inda halittu suka sake rudewa da neman mafaka sai kuma ya koma ciki tsundum! Tamkar an janyoshi, kimanin mintoci biya ya sake tasowa sama wannan karan Buda na kwance saman bayarshi tamkar Gawa, tafiya yasomayi a saman ruwan cikin jan ƙafa saidai kafin ya kai bakin gab'a wani igiya daga kasan ruwan ya fito kamar walk'iya ya maidashi ciki sai ruwan ya sake rukid'ewa zuwa bak'in-k'irin tare fitar k'ugi tamkar rugugin hadarin damina. Lina da ke kallon komi ta mik'e tsaye da sauri tare da kulle ido ta nuna ruwan a ta ke dokin da Buda suka taso sama ta tura hannunta gaba suka tafi a guje tamkar tsintsaye suka zube a saman yashi da ke gefen Tekun. Ta sauke numfashi ta re bud'e hannayenta ta nuna ruwan ya dawo launin shi fari k'al yana murdewa yarda ya keyi a tun farko, ai kafin kwabo Halittun nan sun soma rige-rigen komawa muhallinsu, ido ta zuba musu tana sakin murmushi ta sunkuya tamkar zata fad'a cikin ruwan sai kuma ta tashi tsaye tana mai shafan gefen fuskanta cikin cewa "Na sami cikar burina na taimakon dabbobin ruwa tare da sokon can Buda, mulkin Adalci ya soma sauka daga hannuna, godiya gareka Sadauki Gaud'u da kayimin komi na ganin na mallaki ilimin tsafin da ya zarce na ko wani matsafi dake nahiyar nan harma da waje ta, hak'ik'a zanyi aiki da Adalci tamkar yarda hakan shi ne cikar burinsa, ganinan tafe zuwa mik'o gaisuwa ga ruhinka abar girmamawata, tabbas idan na zama Sarauniyar Tsibiri kogon da kabarinka ya ke nan ne wurin bautarmu." Tana kulle baki ta rikid'a zuwa k'aramar tsuntsuwa mai shegen gudu ta lula sararin samaniya ta ɓace tamkar kibiya sai dai tana sauka a cikin kogon dutsen da kabarin Sadauki Gauɗu yake idonta ya sauka kan Hadimi Tsidau kansa sunkuye cikin tsantsar ladabi ya soma magana. "Uwar gijiyana ayimin gafara lamarin ne ya sha gabana domin na kusa halaka kuma a faruwa hakan na gano ma'adanar tulun sirrin da kike burin mallaka sai dai zamowa mallakinki da kamar wuya saboda manyan iffiritai ne ke gadinsa kuma mahaifinku shima na burin mallakan tulun ya tura 'yar uwanki ne domin ta binciko Tulun sai ya tabbatar ta nemo sai ya taho ya amshe cikin hikima saboda ya san iffiritan da ke gadin Tulun ruwan albarkan baza su yi mata komi ba sabanin da in shi ne zai iya rasa ranshi dan ya taɓa jaraba mallakansa ya sha da k'yar." Numfashi Lina ta sauke tare da buɗe idanunta da suke kulle tun soma maganar Hadimi Tsidau ta kalleshi na sakonni ta jinjina kai batare da ta furta kalmar ba ta matsa gaban Kabarin Sadauki Gauɗu ta russuna gabansa ta miƙa hannunnta na dama ta ɗora saman Kabarin kanta sunkuye, ganin haka sai shima Hadimi Tsidau ya taho da sarsarfa ya russuna a bayan Lina tare da sauke kansa ƙasa, ta sami mintoci goma sha biyar a haka sannan ta mike tsaye shi kuma Hadimi Tsidau na nan sunkuye cikin girmamawa. Murmushi ta yi kana ta soma magana cikin tsantsar isa da mulki inda kallaman ke fita ɗaya bayan ɗaya. "Tsidau zanyi aikin da kaina domin ina tare da Zobben sihiri na Sadauki Gauɗu duk da saka Zoben tamkar na yafa mayafin mutuwana ce ga rayuwata amma akan cikan burina zanyi wannan kasadan saboda da in mutu a hannun Lima gara na ƙare rayuwa a matsayin baiwa a masarautar Sarki Gamji ko ba komi shi ɗin mahaifi ne ga shugabana Sadauki Gaud'u." "A'a Uwar gajiyana banayi miki fatar shiga hannun azzalimin Sarkin nan wanda har 'ƴa'ƴan cikinsa bai bari ba saidai kafin ina baki labarin hatsarinsa zanso sanin sirrin da Zoben ke tare da shi da na kasa ganowa tun sadda mai gidana Gaud'u ke sanye da shi." "Tsidau bana buƙatar jin komi daga masarautar Sarki Gamji domin Sadauki ya sanarmin da komai sannan Zoben da zan fito da shi yana ƙasan Tekun Kabobo sirrinshi mai faɗi ne domin duk wanda ke tare da shi a cikin yatsarshi yafi ƙarfin duk wani matsafi haka duk abin da ya tunk'ara sai ya samu nasara komin wuyar lamarin, in barka haka." "Tafdijan amma Shugabana yana da wannan Zoben ya yi sake mugun nufin mahaifinsa ya yi nasara akanshi?" "Ya sanarmin ya wuce shekaru bakwai da cire ainihin Zoben a yatsarshi jabun ke sanye da shi tare da boyewa mahara Zoben gano jabun ne ke yatsarsni cikinsu har da mahaifinsa domin burinsa ya mallakamin." "Shugaba ya sanki da jimawa kenan?" Jim ta yi domin bata son ambatar ƙaddarar da ya taɓa afka mata wanda ya kasa b'acewa a ranta haka ta kasa maida hankali akan gano dalilin faruwar lamarin kamar yarda tak'i amincewa ruhinta a hukunta mai laifin duk da tarin damar da take da shi na aikata masa komeye da ta so amma ganin Tsidau na dakon amsarta sai ta amsa a takaictda " Eh." "Affuwan Uwar gijiyana, ban gamsu da amsar nan ba a matsayinsa na sirrintaccen Hadiminki bai kamata ki riƙa bani bayani a dunkele ba dukda ina aljani zan iya gano kome kika boye saidai alkawari nayiwa Shugabana cewa bazan taɓa binciko sirrinki ba kamar yarda ban taɓa gigin binciko nashi ba bisa alkawarin da na daukan masa wanda wannan lamarin yasa aka kawo masa hari batare da na nasan meke faruwa ba dan haka a yau ina neman alfarman ki amince alkawarin da na ɗaukawa Shugabana ya zamo tarihi inda zan riƙa sanin abin da zai sameki na kangin rayuwa kafin ya iso na tareshi na maidawa wanda yayo aiken." "Godiya nake ya kai Tsidau amma ban amince ka zamo cikin marasa cika alkawari ba, ina son ka yarda komi nawa kada ka binciko sai wanda na baka dama, ka dauwamma a aikinka na ɗan aike tare da rakiya zuwa inda nake da muradin tafiya da kai." "Angama ya ke Uwar gijiyana, Gimbiyan gobe bisa amincin mahaliccin tsuntsaye da tsirrai." "Tsidau ina yawan jin kalaman nan a bakin Sadauki Gauɗu sannan duk in ya furta na kanji kaina ya yi girma basirana ya toshe inda nake hango kaina cikin wani duhu tare da haske daga nesa can, shin me hakan ke nufi? "Uwar gijiyata rayuwar Shugaba na tarin ababen al'ajabi domin duk nacina akan ya bayyamin sirrin da ke cikin kalaman nan ya k'i dan haka ban san komi akai ba domin harshesa nake kwaikwayo har na ambata miki hakan sai dai ina ta tabbacin wani abin bautane mai girma da ƙarfin mulkin da ya doke wanda su Sarki Gamji ke bautamawa." "Zanzo sanin shi ko da kuwa hakan zai iya zamowa ajalina ne." "Uwar Gijiyata kidaina ambatar mutuwa baki zamo Shugaban Tsibiri ba wacce adalcinta zai kewaye Duniya." Murmushi ya kubce mata sannan ta fuskanci Tsidau tana mai cewa "Ya kai amintaccen Hadimina hakika mun kusa rabuwa domin da zarar na sanya Zoben, zan bacewa ganinka na har abada kai kuma zaka tsinci kanka cikin jinsinka cike da yanci daga nan kazamo yantacce daga bawa ni kuma zan mallaki Tulun ruwan albarka saidai ba zan jima ba akan karagar mulki Tsibiri Sarki Gamji sai aikomin da sako walau irin wanda ya aikowa Sadauki Gauɗu ya halaka ko ya ɗaukeni daga yankin zuwa kurkukunsa na karkashun ƙasa na tabbata a can har zuwa sadda mutuwa zai riskeni dan haka yanzu zan koma Tekun Kabobo in d'auko Zoben, ina godiya da taimakon da ka riƙa bani na duk abin da nake son ci da sha tare da sutura, gaisuwata mai yawa zuwa ga iyalenka, sai wata rana." Momyn Haske ce 🥰 [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri By mrsjmoon ADABI WRITER'S ASSOCIATION. https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks.🖕 06 Tafiya na ƙara nisa inda zuwa lokacin Aliyu Malle ya tara iyali mai yawa dan ya auri bafullatanan da ta yi makuwa mai suna Mero haka ya nemi aure a wurin wani Buzu shima da ya fito ci rani yaga dajin Mungaye ya zama maraya sai ya zauna da iyalinsa, sannan ya koma Asalinsa ya auro 'yar uwarshi Kanuri inda ya auro har guda biyu, a lokacin danginsa suka soma nuna masa ƙauna tunda suka gansa cikin rufin asiri musamman sarautan da yake da shi yanzu na matsayin Sarkin Birnin Mungaye. A wannan komawa danginsa da yayi wasu daga ciki suka biyoshi tare da iyalansu sai Masarautan Mungaye ya sake cika da al'umma. Daga nan auratayya ya cigaba da kulluwa tatsakanin kabilun uku wato Barebari, Fulani da Buzaye. Wannan auratayya da ya kullu tsakaninsu sai ya tsakud'a ya fitar da wata kalan al'umma masu kyawun sifa gami da kyawun launin fata, fuska dana sura. Kowa ka gani a cikin birnin Mungaye mai kyawu ne musanman 'ya'yan gidan sarauta domin Sarki da matarsa masu tsan-tsar kyau ne, wasu masu hasken, wasu mai sirki da ja da kuma masu haɗi da duhu kaɗan amma duk wanda ka kalla mai kyau ne a Masarautan dan har akanyi masu kirari da Birnin Mungaye mai kyawawan Mata. Birnin ta sami wayewa bisa ziyartan turawa inda suka gina makarantun Boko tare da kawo malamai suka riƙa koyar da su ilimin zamani duk dama can akwai masu Ilimin daidai misali musanman Sarki Aliyu Malle tare da danginsa, sai dai hak'ar Turawa bai cimma ruwa ba na samun nasarar rabasu da addinin da suka samesu akai wato Musulunci wanda burin sanja masu tunani ne su koma bin addininsu ya sanya suka shigo birnin sai suka samu Sarki Aliyu Mallae ya yi namijin kokari akan al'umman shi na ganin sun ginu akan turban gaskiya na kaɗaita Allah Subbahanatu Wa Ta'alah gami da riƙo ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shi yasa har izuwa yanzu Birnin Mungaye cike ya ke da musulmai, malamai gami da tsirarun mabiya addinin Yahudu da Nasara wanda suke zaman lafiya da juna domin tun tarihin kafuwar Birnin babu abin tashin hankali da ya taɓa kawo matshi ziyara ko riciki a bisa bambancin Addini ko wani tarzoma na daban sai dai su jiyoshi a makwaftansu saboda sunyi imani da Allah ɗaya ne kuma suna masu jajircewa wurin zaman addu'o'in samun kariya ga Birnin tare da zaman lafiya tsakaninsu suma sauran k'abilun nayin irin tasu addu'ar awurin bautarsu. Wannan tsarin ginin tubalin zaman lafiyar duk ya samune bisa jajircewar mai Mungaye wato Malami, Sarki kuma Limamin Birnin Aliyu Malle wanda ya rasu shekaru masu yawa sai tsa-tsonshi sukayi ta gadan Sarautar har zuwa kan sarki na yanzu Sarki Abdul Hakam. A dalin jagora tamkar 'yan uwanshi da suka gabata sai dai shi ne Sarki mafi wayewa domin dan Boko ne na gaske wanda ya taka har zuwa matakin Professor, shi yasa hawa karagar mulkinsa ya zo da sauyi wurin shigo da abubuwan Zamani fiye da sarakunar da suka gabace shi. Abin burgewa ga wannan ƙasaitacciyar masarauta shi ne riƙon Addininsu domin har zuwa yanzu sarakunarsu sune Limamai kuma masu gabatar da tafsirai a lokacin Azumin Ramadan dan haka babban masallacin Juma'a na garin a kofar Fada take kamar yarda mafi yawan masarauta aka sani da gina Masallatai da ake sallar Juma'a a Fadar su, saidai wannan a cikinta ake sallar Idi dan takasance mai girma tamkar wata Masarautan kaso sake ginawa haka a gefen Masallacin wani daji ne da aka killace shi aka cika shi da shuke-shuken kayan marmari wanda ina mutum ya shiga zai dauka a wani yanki na daban ya ke saboda yalwar bishiyoyi tare nisan tafiya kafin a isa k'arshenta, aka ba wurin suna da Mungaye Garden. Wannan ak'idar da Masarautar ta ginu da shi na son Musulunci da Musulmi shi yasa jama'anta suka kasance masu karamci ga bak'i masu zuwa fatauci da zama na mundun rai. Dan ƙasar Mungaye Allah ya hore mata kyawun fitar tsirrai (Amfanin gona) shi yasa Manoma suka cika garin ta ko wani sassa da ke makwaftaka da ita, lamarin da ya kara daga darajar Birnin ta zamo abar yabo ta ko ina haka duk inda ɗan Masarautar ya shiga yana da alfarma. Mai martaba Abdul Hakam na da Matan Aure biyu. Uwar gida Hajiya Hafsatu (Umma Babba) da Amarya Hajiya Murjanatu (Mami Fulani) da yara maza da mata sai dai 'ya'ya matan ne manya domin wasu sunyi aure tare da albarka zuri'a. A yanzu Mai martaba girma ya soma kamashi, babban burinshi ya yi murabus ya dank'a mulkin hannun ɗaya daga cikin zaratan matasan 'ya'yanshi wato Ahmad (Sardauna) da Aliyu (Saudauki) Sai dai ƙurar da ke hangowa ya sa ya tsuke bakinsa akan ayyana wanda zai zamo magajinsa cikinsu, ya zuba masu ido yana sake lak'antar halayyan kowa tare da wanda Jama'a sukafi nuna k'aunarsu da ya zamo jagoransu makar yarda mahaifinsa ya yi sadda aka bashi mulkin duk da baida ra'ayi amma jama'ar gari suka nuna shi ne zaɓinsu kuma ba jayayya 'yan uwansa sukayi masa mubaya'a sai dai a wannan lokacin baijin shi zai sami sauk'in dank'a mulki da ɗaya daga cikin 'ya'yan nasa ba saboda kowa yana nuna mulkin ya ke so bakin rai bakin fama. A fannin Yarimomin Mungaye kuwa duk sun can-canci hawa karagar mulkin sai dai jama'ar gari sunfi nuna ra'ayinsu akan Sadauki sama da Sardauna duk kuwa da matsalar da ke ga Sadaukin na auri saki domin a shekaran da ya gabata sukayi auren fari amma zuwa yanzu ya mata huɗu ya aura ya saki batare da sanin laifin da suke aikata masa ba domin ya k'i yin bayanin da yasa ke aikata sakin haka suma matayen idan an tambayesu amsar ɗaya ce suke bayarwa ita ce basuyi masa laifin komi ba ya sallamesu ba tare da ya haɗa shimfida da su ba. Cikin matar na ya saka akwai ta farko 'yar kanwar Sarki mai suna Mubina wacce aka aura masa tana da k'arancin shekaru domin kammala secondary dinta kenan a ka yi mata aure cikin rashin son ranta inda shi kuma Sardauna aka aura masa 'yar Waziri wanda shima ya ke kani ga sarki kuma har wayau k'anwa ce ga aminin Sadauki wato Abubakar ana yi masa alkunya da Imam, wacce ta kasance babba mai yalwar komi na cikar halittar mace sama da Mubina, wannan bambancin da ke tsakanin matan nasu yasa sadda Sadauki ya saki Mubina a washegarin kaita gidanshi yasa hankali bai wani tashi ba musamman da ita Mubinar ta yi ta murna har aka ɗora laifin akanta ganin yarda ta yi ta boren bata son auren sai ake zargin ita ce ta nemi sakin da kanta. Matarsa ta biyu 'yar Aminin Sarki ne wacce ta zamo mai wayewa domin ita tana da degree har biyu amma kwanarta uku a gidanshi ya saketa hankali ya tashi a wannan karon amma Sadauki ya nuna ko a jikinsa, akan haka Mai Martaba ya ce ya gama samo masa matar aure. Bayan watanni Mamie Fulani ta matsa sai ya amince da auren 'yar aminiyarta inda ya amince bisa takurashi da tayi saidai shima auren kwanarshi daya ya bata sallama inda kafin ta isa cikin Masarautar da labarin ya tsere gidanshi da ya gina a b'oye da ke dajin Tekun Kabobo wurin da ba wanda ya sani sai amininsa Imam da turawan da sukayi aikin. Bayan wasu watanni ya dawo ya sha faɗa tamkar Sarki zai dukeshi ya yi ta basu hak'uri, anan suka rutsashi sai ya sanar masu da matsalarshi Amma yak'i magana akan dole suka rabu da shi, daga nan bai sake aure ba sai wata ɗaya da ya wuce inda Na'ibin Sarki ya bashi sadakar d'iyarshi mai wadataccen ilimin addini sai dai yana jin labarin ya hankalinsa ya tashi inda Mami Fulani ta rufe shi da faɗa tare da gargadi akan kada ta sami labarin ya saki yarinyar inko ya kuskura ya aikata mai rabata da shi sai Allah wannan kalma ya hura wutar jin rabuwa da Sakina wacce a ranar da aka kawo mashi ita ya bata saki wanda faruwar haka ya saka Masarauta shirya taron zama na musamman akanshi a karan farko tun soma wasa da auren da keyi gami da son zubar da Martaban Masarautar su domin lamarin na taɓa ran manyan masarautar musanman Baba Chiroma da yafi kowa zafi haka ansha mamaki da har zuwa lokacin bai nemi ganawa da Sadauki ba shi yasa yanajin sakon kiran da yafito daga bakin sa sai ya gudu mab'oyarshi tare da gargadin Imam akan kada ya sake ya tona inda ya ke. Sai da ya sami wata ɗaya da kwana biyar wato sati biyar kenan sannan ya dawo inda ya ke kan fuskantar fushi daga mahaifanshi ya yin da dan uwanshi Sardauna ke yi masa shagub'e na kiranshi da kalman mai auri saki mara godiyar Allah, duk da kalaman nayi masa ciwo amma ko kallo bai isheshi ba balle ya tsaya bashi amsa wanda ke kallo a matsayin bata lokaci sannan duk da hakan kauanrshi ga Jama'ar gari bai rage komi ba wannan lamari ya rage masa damuwar da ke ciki na fushi da mahaifanka keyi da shi. Duk da b'oye halin da ke ciki da ya keyi amma kallo ɗaya zakayi masa ka gano yana cikin matsanancin damuwa wanda Amininsa Imam ke aikin bashi baki. *** Aliyu Sadauki. Tsaye ya ke a bakin window dake bedroom dinsa inda ke kallon kai da kawon hadimai bisa alamu manyan baƙi ne zasu halarci Masarautan. Bushe-bushen da aka soma ne ya sashi barin wurin ya koma saman sofa ya kwanta idanunsa na kallon sama zuwa can ya tashi zaune ya furzar da iska mai huci tare da kaiwa k'irjinsa duka ya rintse ido da hanzari jin yarda zafi ya ziyarci wurin da ya duka. Ya juya kai cikin furta "Why ta zamemin masifa a rayuwa? Shin aina zan sake ganta? Shin ita din mutum ce ko aljana? Me yasa na aikata mata haka? Shin har sai yaushe zan fita daga wannan rayuwar na fitinuwa da son kasancewa mace amma ko ta zo gareni sai naji banda mak'iya irinta?" Kwalla ne ya taru a kwarmin idanunsa ya kai hannu ya goge tare da tsirawa ruwan hawayen ido da ya shafo. "Narantse duk ranar da na sake ganinta sai na wulak'antata fiye da yarda take kan wulak'antani yarda zatayi jinya tare da shiga damuwa sama da wanda ta jefani ciki." "Wacece ita Aliyu?" Kallon Imam ya yi wanda bisa alamu ya jima tsaye bai sani ba. Ganin da Imam ya yi ba zai sami amsar tambaya ba sai ya tako ya zauna gefenshi ya kamo hannunsa cikin sanyin murya ya soma magana "Please Sarkin gobe ka daure kayimin bayani yarda zan fahimta wanda zai fitar da su Mamie Fulani daga zargin sihiri akayi maka wanda ba dare ba rana suke mik'a kukansu ga mai warware k'ulli batare da gajiyawa ba akan abinda ke jikinta ya fita ka yi aure ko saga jininka kafin su koma ga mahalicci su." Shiru bai tanka ba saima kwanciya da ya yi yana jin mararsa na kartawa tamkar yarda ya saba ji duk in ya shiga tunanin sanin wacce ke alak'anta silar rashin zamanshi da matarsa na aure. "Yar gidan waye? Me ta ke tak'ama da shi? Shin zan iya samun wadannan tambayoyin daga bakin Aliyu Abdul Hakam?" "No." "Why?" "Imam ban santa ba haka ban san me zance maka akanta ba." "Ikon Allah, wato ta tabbata Aljana dai kenan?" "Ina tunanin hakan." "To aina ka gamu da ita?" "A Barci." Ya samu kanshi da ambatar hakan alhalin ya san ba hakan ba ne. Shiru Imam ya yi na kallonshi ya yin da shi kuma ya kauda kai gefe,murmushi ce ta kufcewa Imam har da zarcewa da guntun dariya lamarin da ya fusata Sadauki ya mik'e ya nuna masa kofar fita sai kawai ya kulle bakinsa da tafin hannunshi ya cigaba da dariya har da fitar kwalla. "Na haukace ko Imam?" "No Brother kawai dariya k'aryar da ka yanko ne ya bani domin k'arara ka tona kanka ba gaskiya ka ambatamin ba." "Me kake nufi da kalamanka?" "Nothing, but sit and tell me the truth, dan wallahi ba zanyi kaffara ba, ba gaskiyan kenan ba." "Nagode da maidani mak'aryaci da kayi kuma ka fice alamarina, bana son sake ganinka kusa da ni, yes na amince na rayu cikin kaɗaici kamar yarda Mamie ta furtamin, Abba ya bawa sokon danshi mulkin Mungaye, Umma ta cigaba da kirana mara amfani." "Innalillahi! Sadauki yaushe Umma ta ambata maka wannan mugun kalman?" "I said get out! Malam." Ya ambata tare da jan hannun Imam ya mik'ar ya soma ja har zuwa bakin falonshi sannan ya sakeshi ya koma saman Cushing ya zauna ya rik'e kanshi gam wanda ke jin tamkar zai fice daga muhallinsu. "Affuwan A... Hannun da ya daga masa yasa Imam gintse ban hak'urin da ke nufin bashi. Tsawon mintoci uku ba wanda ya yi magana sannan Sadauki ya mik'e ya doshi hanyar bedroom saida ya tura kofar sannan ya yi magana cike da izza ya ce "Ka shirya idan anyi sallah zaka rakani sake bawa su Abba hak'uri a turakarshi dan yau Mamie ke da girki kamar yarda Lailah ta sanarmin." "Ok Allah ya kaimu." "Amin." Ya amsa can ƙasar mak'oshi wanda ko Imam bai jiyoshi ba. *** Durk'ushe suke gaban Mai Martaba Abdul Hakam da Mamie Fulani. Imam ne ke ta ban hak'uri ya yin da Sadauki yake ciccira hawaye nayi masa zarya na bak'in cikin jin kalaman da Mamie Fulani ta ambata sadda ta ganshi gabanta. 'Ban son sake ganin fuskanka Babana domin k'unci nake shiga a duk sadda ka ziyarceni dan haka kada ka sake zuwa inda nake na rok'eka.' Toshe kunnuwansa ya yi tuno kalaman, ya d'ago kanshi hawaye wani na bin wani duk da zamowarshi mara saurin kuka amma kalaman Mami ya sakashi kasa jurewa. Ya sarrafa cikin sarsarfa ya isa bagan Mamie Fulani ya sauke kanshi a saman k'afafunta yana furta "Ki yafemin Mamiena wallahi ina cikin iftila'in rayuwa ne domin fushinki guba ne gareni dan ba zan tab'a sake yin tasiri ba har abada." Sai ya fashe da kuka mai sauti wanda rabon da ya yi irinsa ba zai tuna ba. Ganin haka sai Imam ya tashi ya fice da sauri yana goge hawayen tausayin Amininsa. Momyn Haske ce🥰 [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsiri By Mrsjmoon. ADABI WRITER'S ASSOCIATION (AWA) https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕 Page 5. Kuka Tsidau ya fashe da shi abin da ya sanya Lina dakatawa daga rikiɗan da ta so yi zuwa tsun-tsuwa domin komawa inda ta fito, ta zuba masa idanu shi kuma bai saurara da kukan ba lamarin da ya karya mata zuciya taji kwalla ma ciko mata ido sai ta lumshe idanu gami da ware hannayenta zuwa can ta nuna Tsidau haske ya sauka saman kansa tamkar walkiya sai gasu a wani fada mai cike da shimbud'u na alfarma ta dubi Tsidau da ya ɗauke kukan ta ce "Samo mana abinci mai rai da lafiya kana na saurari matsalarka da ya sanyaka kuka daga jin ka kusa samun 'yanci zuwa ga iyalenka." Motsa kai yayi ta murmusa cike da Izza tana mai fesar da iska daga bakinta, kafin kiftawar ido Tsidau ya bacewa ganinta, gyara zama ta yi a saman kilisan ta ɗauki kwalban turare ta ɓalle murfunsa ta kafa a bakinta, tas ta shanye tamkar ta sami ruwan roba, ta cillar da kwalban tare da tsirawa gefen hagunta ido zuwa can ta mik'e da sauri ta kaiwa iska cafka saiga wata budurwa riƙe ba hannunta, suka zubawa juna ido kafin Lina ta furta kalma budurwan ta zama ƙatuwar Kura ta ja baya tana sakin haniniya, ita kam ko motsi ba tayi ba illa zubawa Kuran ido da tayi tana mai nazarin abinda take nema a gareta da take bibiyan duk takun sawayenta tsawon lokaci. Tsidau ne ya bayya dauke da abinci mai rai da lafiya kafin kwabo Kuran ta ɓace. 'A sannu zan gano abinda kike nema a gareni.' Ta ambata cikin ranta tana mai wadata fuskanta da murmushi. *** Abun da Lima. Sunyi tafiya mai tsayi sannan Abun ya kalleta yaga hankalinta baya kanshi sai ya daga dafadarta ta saki ajiyar zuciya gami da kafeshi da ido. "Ya ke 'yata mafi soyuwar gareni, hak'ik'a ina sonki so matsananci shi yasa na ke son taimakonki domin kina fita na shiga taskan bincikena aikam na ci karo da isowar yar uwanki Lina tare da binciko manufar zuwar Tsidau shi ne na taho a hanzarce na tasheki domin inda ban iso ba a haka zaki wanzu cikin barci tsawon lokaci ko sadda zaki farka Lina ta gama mallake gadonki domin a yanzu shi ne babban burinta." "Abun zan kashe Lina!." Ta mabata bakinta na fesar da hayak'i saboda ɓacin rai. "Kul! Na sake jin wannan kalami mai cike da abin kunya na fita a bakinki." "To ka dakatar da ita daga shigamin gona." "Zanyi wannan domin idan mukayi sake ta mallaki Tulun ruwan albarkan to ba ke ba har ni zan fuskanci matsala ta hanyar mallake min Tsibiri duk da ina hango wani babban kalubale da zata fuskanta bayan ta samu cikan burinta lamarin da nake jin ban son ya afku gareta." "Me ye shi Abun?" "Binciken da zan shiga kenan na tsawon kwanaki uku dan haka ina baki umurni da kada ki sake komawa Bukkan Kaka Gunu har sai na fito." "To Abun amma ina son ka bani dama na tafi Tekun Kabobo na dakaceta zuwa sadda zaka fito." "Na yarje miki wannan ya ke yata mafi soyuwa gareni." "Godiya nake Abun." "Kafin ki tafi ki shiga wurin Mah domin tana bukatar sanyaki a ido." "To." Ta amsa da sauri. Kanta ya shafa tare da shigewa turakanshi tana ganin shigewarshi ta rikida zuwa bak'ar tsun-tsuwa ta tashi sama da gudu ta nufi inda Abun ya ce kada ta koma sai ya fito daga bincikesa. Lima na isa bakin Bukkan Kaka Gunu ta samu yana ta cike hanyar shiga ta ja da baya cike da fushi ta watso wuta sai dai yana sauka ruwa ya taho da mugun gudu ya kasheshi, iska mai ƙarfi ta turo daga bakinta shima yana isa guguwa ya maida iskan baya ya tafi da ita gefe ta zube ƙasa, numfashi ta sauke da karfi ta mike ta tunkari bukkan da dukkan ƙarfin sihirinta sai dai bisa mamakinta sai ta ga Lina Zauna a saman kujera bata sama bata ƙasa ta kare hanyar shiga Bukkan, kallon kallo suka yiwa juna na sokonni sannan Lina ta sakar mata murmushi tare da mik'a hannu container ya bayyana cike da farfesun kayan ciki sai fitar da turiri keyi, ta kalli Lima cikin izza tare da sake sauke mata murmushi tamkar zata furta kalma sai kuma ta gintse ta maida hankali wurin cin farfesun hankali kwance. Iya fusata Lima ta yi sai kawai ta ja baya ta dunk'ule ta zama k'aton dutse mai fitar da hayaki ta nufo Lina gadan gadan saidai kafin ta isa Jarumi Buda ya bayya cikin gaggawa ya ture dutsen tare da kai masa naushi a take Lima dawo sufarta ta tashi tsaye tana murmula goshinta da ya kumbura sakamakon naushin da ta sha, kalonsa ta yi cikin mugun fushi kafin ta furta kalla ya iso gabanta shima a fusace ya kwasheta da mari yana mai cewa "Me yasa baki san ciwon kanki ba ne? Shin idan kika shiga Bukkan a wannan yanayin kin san kalan barnan da zakiyi? Ko ance miki fadar kaka Gunu wurin wargi ne? To maza ki bar wurin nan har sai Abun ya fito daga bincikensa kamar yarda ya bani umurnin zuwa dakatar da ke daga aikata barna wanda zai iya zanyowa Tsibiri nak'asu." "Ka bani hanya Buda na illata Lina domin gata nan tanayimin dariya dan ita nake son kaudawa a doron ƙasa dan ta gane bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne haka faɗa da Giwa bana 'yan kuikuyo ba ne, burina ta gane ni babban goro ne mai taɓani ya kwana lafiya sai wanda ke neman turb'aya ta kulle maganenshi na har abada." "Karya kike Lina bata zo nan ba sai dai in gizo idanunki keyi miki dan haka ki ɓacemin da gani tun ban aikata miki mugun aiki ba." "Buda na rantse da kabarin Kaka Gunu Lina na tare da mu dan haka ka kaucemin a gaba ko in sauke fushin a kanka wanda ya wuce naka fushin da kake karad'in cika baki a kai." "To nunamin ita domin na hukuntata akan wani rainin hankali da ta yimin wanda ya janyomin rasa sihirtaccen Dokina Mardu." Da hanzari ta tureshi daga bakin Bukkan sai dai abin mamaki ta nemi Lina ƙasa ko sama ta rasa alhalin ko sadda take maganar ta ganta zaune bayan Buda. "Tabbas Lina ta koma Aljana." Ta ambata da fushi hucin hayaki na fita daga bakinta saboda tsabar masifa. "Tare kuka zama ai." "Buda!." Ta kira sunarshi da ƙaraji. "Lima!." Shima ya maida mata martani. Sunkuyar da kai ta yi tana hasko wani lamari da ke yi mata wasi-wasi akan sabon halayyar Buda wanda sam a da bai daga mata murya hasalima miskili ne mai takama da Izza a kan Lina kawai ke zamowa soko saboda kaunar da keyi mata. "Maza wuce muje ki huta, tunaninta da kikeyi ne ya ke son maida ki sokuwa har ta soma yi miki gizo." "Kaine Babban soko amma bani Gimbiya Lima ba." 'Lallab'ata ta wuce tun kafin ta hargo jirgin.' Murmushi ya sakar mata jiyo abinda Lina ta ambata masa a kunni. Ya gyara tsayuwa cikin tsare gira ya ce "Biyoni kawai ta salama Basarakiyar gobe." Bata musaba ta rufa masa baya cike da sake nazartan halayyar da ya aro da rana tsaka sannan a gefe kuma ta ci alwashin hukunta shi haka komin rintsi da sa idonshi kafin mahaifinta ya fito daga dakin bincike sai ta mallaki Tulun gadonta domin batajin zata raba gadon da kowa hatta kuwa da shi Abun. *** Suna barin wurin Lina ta bayyana gaban Bukkan ita da Hadimi Tsidau inda keyi mata fifita da fatar kunnin Giwa fuskansu dauke da murmushi. "Uwargijiyata kina da kaifin basira duba yarda na koma Jarimi Buda na tasa miki keyarta cikin lumana sai dai marin da naushin danayi mata zai bar baya da k'ura domin ta rikeshi hanyar fansa akan Jarumi Buda kuma kinsan shi ɗin ba kyalle ba ne barinma da yanzu ke cike da haushin ajalin dokinsa da kikayi sanadi." "Bar soko ai da gangar nayiwa dokin illa saboda na gano shi ke hasko masa lamuran dana boye." Shugabana kina ƙara kutsa kanki cikin ayyuka masu hatsari domin kin haɗa Lima faɗa da Buda lamarin da zai iya haifar da ɗa mara ido a Tsibiri bayan burinki zaman lafiya ya wataci yankin naku." "Bana dana sanin komi akan hakan dan kome zatayi matsalarta ce haka zalika Buda ya wuce da saninta hasalima baida lokacinta na tabbata kome zatayi mashi ba zai daga kai ya kalleta ba ko ni da nayi masa babban laifi ba zai kulani ba dan na tabbata ita ba za tayi masa mai munin wanda na aikata mashi ba." "Haka ne Shugabana, kin gini hango gaskiya." "Mu bar zancen haka Tsidau, yanzu zan tafi domin dauko Zobe na." "Uwar gijiyata mu bar yankin nan na baki shawara mai b'ullewa domin na jiyo kamshin tahowar dan leken ashirin tsibirin na tinkaro inda muke cikin alk'aluman sihiri bisa umurnin Lima domin ta gano makircinmu." Yana rufe baki suka b'ace b'at inda suka sauka a saman Dutsen dake tsakiyar Tekun Kabobo suka shige wani rami inda cikinsa ruwa ne ke kwaranya fari k'al, duwatsune masu suffar kujeru sun zagaye ruwan akan ɗaya daga cikinsu Tsidau ya zauna ita kuwa Lina kujerarta ya bayyana na zauna cikin mulki ta kalli Tsidau ya sunkuyar da kai tare da soma magana "Shugabata bana son ki d'auko ajalinki da hannunki domin ina jiyo amon sautin fitar ruhinki daga muhallisa shi ne d'azun ya sakani zub da jirwaye(hawaye), wannan hatsarin ya sanya Shugaba Gauɗu ya birne shi a ƙasan Teku dan haka kema ki barshi a inda yake inma da hali ki fita sabgarshi har abada dan bala'in da ke cikinsa yafi nasarar da kike hange." Shiru ya ratsa wurin na tsawon mintoci goma sannan Lina ta sauko saman dutsen kujerar da take zaune ya b'ace ta tsomo kafafunta cikin ruwar dake da mugun sanyi ta lumshe ido kana ta bud'esu tar akan Tsidau da ya sake sunkuyar da kai ƙasa cike da ladabi. "Ya Amintaccen Hadimina na fahimceka amma in kaga ban sanya Zoben nan ba to numfashina na ne ya bar jikina sannan kada kayi kuskuren boyemin ganinsa domin na gano kana shirin aikata hakan sannan ka sani son mulki a jinana yake dan ko da zan hau karaga da dak'ik'a ɗaya ne numfashina ya bar jikina sai na hau a sanya lissafin sunana cikin Sarakunan da suka mulka Hatsabibin Tsibiri." "Allah huci zuciyar Shugabata, nasara naki ce nabarki lafiya zan tafi hutu amma ki sani ban shirya komawa ga Iyalaina ba." "Sauka lafiya hadimin gaskiya, ka huta sosai bana tare da matsala." Motsa kai yayi tare da komawa jemake ya fice daga kogon dutsen a guje. Tsirawa hanyar da ya fice ido tayi zuwa can sai ta murmusa tare da cewa "Hadimi Tsidau mai amana ne, kada ka yarda wani ya yi nasarar rabaka da halin kirkin nan." Ta jima zaune tana hasko abinda ke taɓa mata zuciya wanda batajin zai bar ruhinta ya huta domin a duk sadda ta kaɗai ce lamarin ne k yae mamaye zuciyarta. Numfashi ta ja idanunta ya kad'a ya koma jajur da sauri ta sunkuya ta tura hannu a cikin ruwan dake gangara, aikam take duwatsun wurin suka b'ace sai wata kofa babba ta bude ruwa na tartsi daga cikinsa, ta fadawa cikin ruwan kofar ta kulle duwatsun da suka b'ace suka dawo muhallinsu. *** "Affuwan Shugabata ba zan taɓa tafiya na barci cikin tarin hatsari ba ina tare da ke bakin rai bakin fama indai Zobe ne a jalinki ba zan taɓa bari ki sanyashi a yatsarki ba ko da kin d'aukoshi." Tsidau ya ambata bayan ya sauka a wani Tsibiri domin ganawan sirri da wani gawurtaccen Ifiritun Bil'adam, shi ɗin masanin warwaran lamura ne shi yasa ya taho gareshi duk da yasan rashin imaninsa amma haka ya yi kasadan zuwa saboda bawa Lina kariya. *** Lima na tura ɗan sak'o dan ya nad'o mata abinda su Lina ke tattaunawa sai ta zarce gidan shak'atawar jama'ar Tsibiri inda suke cin karensu ba babbaka tunda suna gudanar da lamarin bisa son zuciyoyinsu ne shi yasa doka bata hawa kan Mazajen dake tayasu watsewar. Tana shigowa hargowa da kid'an da ke tashi ya ɗauke, hatta da wanda suka killace kansu suna aikata shed'anci sai da suka yatsa cak, haka maja'ar wurin suka riƙa mik'o gaisuwa bata kula kowa ba ta sami wuri na musamman ta zauna wanda tana shigowa aka tanadar mata, saida ta ɗauki tsawon mintoci goma da zama sannan ta bada umurnin a cigaba da abinda a keyi wato kid'a da rawa tare da fasik'ancin da suke aikatawa a gaban kowa batare da alkunya ba domin wurin daki ɗaya ne a gefe wanda shima Lima ce ta bada umurnin gina mata tun sadda ta soma kawo ziyara wurin dan more k'uruciyarta. Wasu samari ne kyawawa guda biyu ba kaya jikinsu sai gajerun wando suka taho gabanta suka zube, ta fesar da iska cikin Izza sannan ta yi masu nuni da kafad'arta suka tashi da hanzari suka soma matsa mata zuwa hantsen hannayenta, sai miƙa take saki cikin 'lumshe idanu cike da jaraba bajimawa wasu 'yan mata suma kyawawa suka zauna gabanta ta ɗora kafafunta a saman cinyoyinsu suka soma matsawa suna ja mata yatsu ta tana lumshe ido cike da jin daɗin yanayin abinda ya gusar mata da kaso mai yawa na damuwar da ta iso wurin da shi. Sun sami kusan awa ɗaya suna aikin yi mata tausa sannan ta dakatar da su ta mike zuwa dakin da yake tilo a wurin samarin suka rufa mata baya suna masu zame gajerun wandunarsu tun kafin su shiga d'akin yayin da 'yan matan kowa ta kama gabanta, sautin kid'a da ihun banza ya sake hautsina wurin ganin Lima ta basu wuri su baje hajarsu son rai saboda duk wanda ke wurin a buge ya ke domin antanadi giya na musamman domin nishad'i a wurin kowa zuwa yake ya sha yarda ya so ba mai yi masa iyaka, sai hauka sukeyi suna shiga jikin juna tamkar dabbobi. *** Abun kuwa duk abin da ya faru yana kallo a madubin tsafinsa illa shigar su Lina cikin kogon dutsen ne lamarin ya b'oye masa sai halin da Lima ke ciki a wurin shak'atawa ya baiyana a madubin, cikin fushi ya mike tsaye sannan akaran farko kunyar abin kunyar da Saurauniyar Gobe keyi a gaban jama'ar da zata mulka ya k'ona masa rai, ya ja tsaki yafi sau shurin masak'i a ƙarshe ya koma zaune ya tsirawa allon tsafinsa cike da burin son gano abinda Lina ke b'oye masa musamman bayani akan Zoben sihiri. Hankalinsa ya kasu biyu ya rasa da wanne zai soma. "Hak'ik'a yanzu nafi ku son dauwama a karagar mulki Tsibiri, zan jajirce dan ganin nayi tsawon rayuwa fiye da na Kaka Gunu yarda zanga mutuwarku batare da kunga nawa ba." Ya furta cikin kaiwa wata batta duka a take ta fashe wani bakin ruwa ya malale ƙasa ya kai hannu ya kwalfe ya shanye sai ga kamanninsa ya sauya sai ya bushe da dariya na kaiwa k'irjinsa duka cike da gadara. *** BIRNIN MUNGAYE. Masarauta ce da ta kafu shekaru aru-aru wacce ta fara daga daji zuwa yanzu da take a matsayin babbar birni mai yalwan al'umman Barebari, Fulani da Buzaye, su ne manyan yarukan da suka kafa Masarautar domin Aliyu Malle da ya zamo tushen kafuwar Birnin babarbare ne, shi ne ya soma yada zango a dajin saka makon matsin 'yan uba da suke son ganin bayanshi sai ya baro garinsu ya dawo cikin dajin , ya cigaba da rayuwar kadaici, abokanansa su ne namun daji inda ke farauto na halal ya samu abinci. Yana a wannan rayuwa ce wata raba ya haɗu da 'yar Fulani da ta yi makuwa ya fitar da ita hanya daga nan fa ya sami wurin zuwa hira rigarsu har ya zama tamkar d'an gida, suka shaƙu da Fulanin matuƙa inda in ya kwana biyu bai zo ba zasu biyo sahun shi zuwa dajin Mungaye wanda a da yake gagaran su shiga kiwo saboda miyagun namun dajin dake halakasu. A hankali Fulanin suka soma yo hijira suna dawowa sansanin Aliyu Malle inda suka nadashi Limaminsu domin shi ne silar musuluntarsu dan ya samesu kara zube ne basu san abin bautawa da gaskiya ba. Zamowarshi mai tarin ilimin addini sai ya riƙa fad'akar da su a ilmance har mafi akasarinsu suka amshi gaskiya, suka gane Allah subhanahu wata'ala ɗaya ne tilo baida abokin tarayya. Momyn Haske ce🥰 [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon AWA. Page 07 "Is ok my son, stop crying, mun huce Allah ya tsare gaba." Mai martaba ya ambata cikin taping bayarshi ammsa sai ya girgiza kai ya sake dank'e k'afar Mamie Fulani yana sake fitar da sautin kukanshi tamkar ƙaramin yaro. "My Fulani say something please, bana son jin sautin kukan nan." Mai Martaba ya sake ambata cikin sigan rarrashi. Itama girgiza kai tayi cikin b'oye fuskanta a lafayar da yazame daga kafadarta sakamakon jijjiga k'afarta da Sadauki keyi wacce itama kukan takeyi cikin b'oye fitar saurinsa hakan yasa ta kasa furta kalma. A fusace mai martaba ya janyo Sadauki ya jefashi cikin k'irjinsa ya matse ya soma magana a kausashe. "Me ye haka Aliyu? Shin a haka kake son zama sarkin Mungaye? To maza ka dawo natsuwarka bisa wannan sokanci dan baka gajeshi ga kowa ba, kai jarumi ne, Sadaukin babban Masarauta irin Mungaye domin tun kana yaro ka ci sunar Sadaukantaka dan haka ganinka cikin wannan raunin sunar zai iya b'atan dabo daga kanka zuwa wurin autar my Fulani Mu'allim." Ya ƙarasa maganar cikin raha irin ta uba mai son farin cikin 'ya'yansa. D'ago kanshi ya yi mai martaba ya jinjina masa kai sai ya maida yana mai goga tsinin hancinsa a k'irjin mahaifin nasa cike da jin natsuwar ruhi domin alamun hucewa ne hakan da ya yi masa. "Abba fushinku ne ke son mai dani ragon maza, dan Allah a gafarceni na tuba ba zan sake maimaita kuren ba." "Tuni ya wuce a gareni Aliyu domin ko wani bawa da kalan zanen ƙaddarar shi, to kai naka a auri saki ya fad'o." "Godiya na ke Abbana." Ya ambata cikin sake kafewa a k'irjin Mai martaba." "Sake ni kada ka kadawa My Fulani miji." Da sauri Sadauki ya janye jikinsa yana murmushi cike da farin cikin sakewar da Mai Martaba ya yi masa, ya dawo gaban Mamie ya langabe kai, tsare gira ta yi ya kalli mai Martaba cikin alamun ya sa baki sai ya zunkud'a kafada tare da kauda kai gefe sai ya tura baki tare da maido hankalinsa kan Mamie ya kamo hannunta ta janye cikin cewa "Kalli idon mai kuka kamar na ɗan yaye." Murshi ya saki tare da saukewa bayan hannunta sumba ya furta "Nagode sosai Mamiena." Shafo kansa tayi cike da kulawa, sai yaji malolon da ya tsaya masa a kak'oshi da faɗa ciki a fili ya furta "Ya Rabbi Alhamdulillah." Ya mik'e dan nufin ficewa Mamie tayi masa nuni da ya koma ya zauna, lankwashe ƙafafu ya yi gami da tsira mata ido cikin neman sassauci, hancinsa ta ja ya saki numfashi tare da sake narkewa zuwa kalan tausayi. "Yallab'ai a kira mai rukiyya ayima yaronka domin lamarinsa yayi kama da mai shafan shed'anun junnu." "Aikam hakan za'ayi My Fulani domin nima mafarkaina na haskomin yana da Junnu." "Wallahi bana da komi, ku yarda ina cikin azal ɗin ƙaddara ce." Ya ambata cikin hanzari yana sake kama hannun Mamie Fulani. "Babana ta ya zamu gamsu da hakan? Alhali ka bijirewa raya sunnar Manzon rahma, bayan kaima ta nan ka zo duniya." "Zanyi aure Mamie, wallahi zanyi, kudai cigaba da yimin addu'ar had'uwa da zab'in ruhina." Had'a idanu Fulani da Mai martaba sukayi suka jingina kai domin hasashensu ya tabbata kenan Sadauki bai son auren had'i kamar yarda suka ruk'a yi masa. "Har zuwa yaushe zamu ga zab'in naka Babana?" Shiru ya yi tsawon lokaci baida niyyar amsawa. "Ok tashi ka tafi gobe da safe ka zo ina son ganinka nasan zuwa lokacin ka samo amsar tambayar Fulani dan nima ina dakon jin lokacin bayyanar zab'in ruhin naka Aliyu." Godiya ya yi masu tare da mikewa natse ya fice sai dai kallo ɗaya zakayi masa ka hango jikinsa a sanyaye ya ke. Karo sukayi da juna kowa ya dafe goshi inda suka bugu, suka zubawa juna manyan idanunsu da suka gada wurin Mai martaba Sarki Abdul Hakam. "Kai makahon inane da kake tafiya baka kallon gaba ka?" Sardauna ya ambata cikin kaushin murya domin jin labarin zuwar Sadauki turakar mai martaba ya daga hankalinsa dan burinsa su cigaba da fushi da shi abinda zai bashi damar hawa karagar mulkin Mungaye hankali kwance domin ya gama cika sharudd'an zama Sarki tunda nada aure da albarka auren wato haihuwa, yayin da Sadauki yake fanko a wannan fannin. Rab'e shi Sadauki ya yi ya wuce batare da ya tanka masa ba domin tankawarshi naushi ne lamarin da ke gujemawa faruwarsa dan in har ya sakawa Sardauna hannu sai ya suma wannan lamarin ya samo asali ne tun suna yara duk in faɗa ya haɗasu to Sadauki sai ya sumar da Sardauna da zarar ya kai mashi duka. "Mara amfani mai auri saki kawai, mijin Aljana!." Kalaman sun k'ona ran Sadauki amma duk da hakan bai sa ya waiwayo ba. "Kai! ne mara amfani, wawa mai fuska biyu kawai." "Kai! Imam ka taka a sannu ko in antayo k'anwarka gida a satin nan na angwance da mata huɗu a lokaci ɗaya." "Wanda ya fasa antayota ya raina kanshi da mai dattin d'ankwalinsa." "Umman kake zagi saboda baka da hankali?" "Gaka nan babban mara hankali, gab'on banza mara amfani." Sardauna ya nufo Imam a fusace shi kam ya gyara tsayuwa na jiran ya shigo shi ganin haka sai Sardauna ya ja baya ya juya ya nufi sashin Umma na aiki bambamin faɗa. Dariya Imam ya kwashe da shi ya furta "Matsoraci kawai kuma ka sani lusari irinka ba zai tab'a zama jagorar babban Masarauta irin ta Mungaye ba." Jiyowa ya yi cike da baƙin ciki aikam Imam ya yi masa gwalo sai ya watso masa dak'uwa, Imam ya zabura kamar zai biyoshi, Sardauna ya kwasa da gudu ya b'ace. Dariya Imam ya sake kwashe da shi har da tafawa, Sadauki dake hangen abin da ya faru shima murmushi ya yi yana Allah wadai da sokancin d'an uwanshi Sardauna. "Ga daishi a fuska da cikar zati kamar jarumi amma saidai ko wata macen tafishi k'wanjin iya kare kai." "Ka bari kawai Sarkin gobe, shi yasa na ke bak'in cikin bashi auren Khadija da akayi domin tafishi komi na jarumta, ni dai Allah yasa kada yaransu suyi gadon mugun abu na zamowa sokaye a cikin tsararrakinsu kamar yarda ubansu ya kasance." Duka Sadauki ya kawo ma Imam cikin cewa "Baka da dama fa Brother." "Uhm ba za ka gane haushin da nake ji ba ne na wannan had'in auren da akayi da sokon can." "Kaganka da neman magana, nikam taho muje nayowa su Mamie siyayya." "Da kyau mutumina bisa alamu an karb'i tubanka." Murmushi kawai Sadauki ya yi mai nuni da bashi tabbacin hasashen shi, aikam cikin jin daɗi Imam ya rungumeshi daga bisani ya sake shi suka jera zuwa inda ake ajiye motoci cikin nishad'i. Sai da suka hau kan titi sannan Sadauki ya kalli Imam cikin rashin wasa ya ce "Ya kamata zuwa yanzu kai da Sardauna ku dawo natsuwarku kudaina abu kamar yara dan kun zama iyaye ko ba ma haka ba sirukan juna kuke tunda kamar yarda ke auren k'anwarka haka kaima kake auren k'anwarshi to Please Aminina kadaina biye masa kuna raba hali ka zamo tamkar ni yarda sam baya gabana kome zaiyimin ban tankashi dan bai kai matsayin na tsaya b'ata lokaci da shi ba, haka ka rik'a duba girman dangartakanku da juna na zamowa daga tsa-tso ɗaya." "Ok in sha Allah zan jaraba d'auke kai amma fa Aliyu ka sani yayanka baida tunani dazunfa cemin yayi wai zai antayo Khadija gida ya angonce da mata huɗu rana ɗaya." Karya ya keyi domin na sami labarin ko Khadija hak'uri takeyi da ragwantarshi kawai ya ambata ne dan ya b'ata maka rai kuma yayi nasarar hakan tunda gashi nan ka biye masa kunyi shiririta." "Kai Yarima yaushe ka sami labarin Sardauna rago ne a turaka?" "Kai dai zauna nan ana batun arziki kana can kana shiririta." "Ban son rainin hankali fa Sadauki, shin kai da ba mata ba gareka ba ta ina aka zauna tattauna lamarin masu iyali da kai?" "Zancen kake so na bar maka to." "Allah baka isa ba sai ka fitar da ni duhu nan." "To tafi ka tambayi Mamie gaskiyan zancen domin a bakinta naji in shima musamin zakayi to bissimillah." Idanu waye Imam ke kallon Sadauki yayin da shi kam ya tsare gira ya cigaba da tuk'insa hankali kwance. "Shin kana nufin ita Khadijan ta iya zuwa gaban Mamie da zancen bata gamsuwa da mijinta?" "Kai kada fa ka dameni da zancen banza tam na kwanciya tam." "Ai wallahi baka isa ba tunda ka takalo zance baka isa ka waskewa ba sai ka fed'emin biri har wutsiya." "Ai zaka iya shak'eni in na jiyo k'amshin barzahu na ambata maka gulman da kake son ji." "Kaga malam dawo hankalinka ina saurarenka." "Kaga Imam zan ci maka mutunci, sannan in kaima ragon ne ai sai ka sanarmin mu tafi neman magani kafin matarka ta raina ka." "Allah ya tsareni mugunji da gani." "Ina tayaka murna da ka tsalle sharrin basir." "Sadauki da magana a bakinka Please tell me." Banza Sadauki ya yi masa har suka isa babban mall din dake dauke da tambarin Fulani store wanda wurin ya zamo mallakin Mamie Fulani. Duk nacin Imam akan sanin gaskiyan labarin Sadauki ya yi kunnen shegu da shi. Suna shiga ya juyo ya aunama Imam mugun kallo a take ya tsuke bakinsa domin jinin sarautan ya motsa kan dole ya yi mubaya'a duk da shima ba baya bane wurin nuna mulkin sai dai Toron Giwa ya take na Rak'umi. Turaruka masu tsada ya daukan musu kowa set huɗu sannan ya zarce wurin lafaya ya zab'ama Mamie Fulani masu kyau kana ya dawo wurin takalma ya daukanma Mai martaba kalan na sarakuna itama Fulani ya siya mata daga nan ya soma zab'ama k'anninsa duk abinda kowa ya fi so suka fito tare da barin kayan a kai mashi gida. Yawo Sadauki yasomayi da su a birnin baiko duba dare sakamakon birnin ya cika da hasken Soler ta ko ina, sannan duk inda suka ratsa sai masoya sunyi masa kirarin da Sarkin Gobe mai Mungaye da yardan Allah, inda Imam zai fito ya yi masu yayyafin kuɗi sannan su wuce, a k'arshe suka dawo Masarauta da misalin k'arfe ɗaya da rabi na dare, har bakin gidan Imam ya kaishi yaga shigarshi ciki sannan ya nufo sashinsa cike da jin barci, a gajiye ya faɗa saman kushin yana maida numfashi zuwa can ya kai hannu saman maranshi idanunsa lumshe yana yamutsa fuska dan hakan ya gujemawa shi yasa ya yi ta gara-ranba da su har dare ya tsala a she a banza ya yi fitinar na nan mak'ale da shi, tsaki ya ja yana mai tausayin kansa. Tamkar ko yaushe ta bayyana cikin shigar daukan hankali ta zauna gabanshi tana jifarshi da shu'umin murmushi. Motsawa ya yi ya tashi zaune da kyau ya tsira mata ido cike da buk'atuwar ka sancewa da ita duk da a ƙasan ranshi baya maraba da lamarin amma gangar jikinsa ya kasa bashi haɗin kai. "Who are you?" Ya furta cikin shak'ewar murya gami da matse cinyoyinta. "Your wife." Ware idanu ya yi ta kyalkyale da dariya gami da huro masa iskan bakinta wanda ke dauke da wani k'anshi na musanman, shi ne ke kuma haukatashi matuk'a. A gigice ya nufeta hankalinsa a tashe cikin son kasancewa da ita ko ta halin k'ak'a. Ta shi ta yi ta soma ja da baya ya kai mata cafkota ta zama haske ta b'ace tana cigaba da yi masa dariya wanda ke sake hautsina masa lissafi, toshe kunnuwansa ya yi amma sai yaji dariya makar sake ƙaruwa ya keyi sai ya cire hannun cikin furzar da iska mai huci ya ce "Na rantse idan kika sake shigowa hannuna a karo na biyu sai na illata miki rayuwa ba aljana kike ba ko ifritiya ce ke sai na gana miki a zaba mai rad'ad'i fiye da wanda kike kan ganamin." Ya k'are furucin cikin kaiwa iska naushi, ta saka ihu cike da tantiranci, ya ja tsaki mai ƙarfi ya nufi bathroom tamkar zaki ya sakarwa kansa ruwan sanyi, ya ɗauki mintoci ashirin tsaye ruwan da dukanshi sannan ya fito jikinsa na digan ruwa dan ko kayan jikinsa bai cire ba ya nufi firij ya zuba ruwa a cup ya ciko k'aramin spoon da gishiri ya juya a ruwan ya matse lemon tsami a kai ya daga ya shanye domin ko yasha tablet ya kan jima kafin ya dawo dai-dai amma wannan had'in take yanke ke samun natsuwa, yana jin kak'oshinsa tamkar zai tsage amma haka nan ya jure. 'Wata rana zaka sami matsala game da lafiyarka Aliyu.' Jinjina kai yayi alamun ya sanda da hakan ta hanyar bawa zuciyarsa amsa. *** Sardauna da Sadauki tagwayen ne ga mai martaba Professor Abdul Hakam duk kuwa da ba d'umin ciki ɗaya suka sha ba dan an haifi Sardauna da hantsi da marece kuma aka haifi Sadauki wanda faruwar haka ya so tada k'ura inda Umma ta ce Sadauki shegene girkinta Mamie Fulani ta ci dan haka bashi da gadon sarauta domin a wanna lokacin Mai martaba ya soma samun haihuwar 'ya'ya maza. Hajiya mai babban zaure ce ta tsawatar wato mahaifiyar mai martaba sannan ta kafa dokar duk ranar da Umma ta sake ambatar wannan kalman a k'arshen zamanta a matsayin matar d'anta, aikam ta shiga hankalinta inda ta kame bakinta har zuwa yau bata sake furta kalmar ba amma ta raini zuciyar Sardauna akan son mulki bakin rai bakin fama dan ta kance da shi ko zai hau karagar mulkin da second ne ya koma ga Allah sai ya hau kujerar sarautan Mungaye. Umma irin matar nan ne masu fuska biyu inda cikin dubara take cutar da duk wanda ta tsanani ganin warwalanshi batare da makusantarshi sun gano ba. Momyn Haske ce 🥰 [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon. AWA. Page 8 Umma ta wargaza zaman lafiya tsakaninta da Mamie Fulani cikin salonta mai wuyar ganewa, duk da ita Fulanin bata kulata tana bata girmanta amma hakan baisa ta kame kanta ba wurin maida k'aramin abu zuwa babba a tsakaninsu ta hanyar makirci kala-kala wanda kafin mai martaba ya farga Mamie Fulani ta k'unsa bak'in ciki har ya kaita ga kamuwa da hawan jini sai dai bisa amincin Allah Mai martaba ya gano tungun Umma batare da ita Umman ta san hakan ba wanda shima mahaifiyarsa ce Hajiya babban ta haska mashi fitila a take kuwa ya warke makanta da ke ciki ya yiwa lamarin tubkan hanci ta siyaya ba tare da nuna fifikon da zai janyo tashin hankali ba inda maimakon Umma ta gyara sai ta sake k'aimi cikin fito da sabon salo. Hassada gami da kishin Umma ga Mamie Fulani ya samo asali ne akan tazararsu da juna tun daga kan Ilimin addini dana boko zuwa dukiya wanda idan bata zarta mai martaba ba to zasu iya zuwa kunnen doki dan mahaifinta mai tarin arziki ne wanda kowa ya shaida a cikin birnin Mungaye da wajenta, ya rasu ya bar musu gado wanda ita da yayanta na miji ɗaya da k'anwarka suka gada sannan tun kafin ta auri mai martaba tana kasuwanci wanda ke kawo mata kuɗi domin tun kafin ta shiga Jami'a ta mallaki restaurant na kanta wanda a yanzu shi ne wurin cin abinci mafi girma da k'ayatuwa a cikin birnin Mungaye. Wannan ya tsole idon Ummu duk kuwa da tana amfana da shi ita da 'ya'yanta dan Mamie Fulani mai kyauta ce bata taɓa nuna bambanci tsakanin 'ya'yan Umma da nata, ko me suke so ta kanyi musu domin kusan ita ta raini Sardauna da Sadauki tare da Imam shi yasa duk fitsarar Sardauna baiyi mata sai dai ya k'are a kan Sadauki marainin wayonshi wanda ke d'aga masa ƙafa ba dan tsoro ba sai dan koyi da halin fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam inda ya ce da mu zamo masu yawan hak'uri. Har izuwa yanzu Umma tana kan sanya rashin jituwa tsakanin 'ya'yanta dana Mamie sai dai ba dukansu ne suke bayanta ba, tafi samun kan Sardauna sama da kowa, shi yasa take ji da shi tamkar kwai duk da shima Sardaunan a cikin Masarauta ne ke nuna mugun halin da tsanarshi ga Sadauki amma da zarar sun fita wajenta tamkar babu komi tsakaninsu ke nunawa wannan halin ya aroshi ne dole ya yafa saboda gargadin mai martaba dan ya tabbatar masa duk ranar da labari ya zo masa ya wulak'an 'yan uwarshi a bainar jama'a to ya tabbatar da ya bar masa Masarauta bari na har abada, ba Sardauna ba hatta da Umma gargad'in ya ratsa kwa-kwalwanta sai ta d'orashi a tsarin fitowa a mai fuska biyu irin yarda take yin takonka shi ne dalilin da Imam kan ambata masa kalman a wasu lokuta in har ya taɓa Sadauki sai ya zamo Imam ne abokin karawarshi amai makon Sadauki. Kaunanr Sadauki da Imam ya samo asali ne tun yarinta inda aka kawoma Mamaie Fulani yayen Imam ta haɗashi da su Sardauna ta raina har zuwa sadda sukayi hankali kowa ya koma gaban mahaifiyarshi sai dai har kwanan gobe Imam yana yiwa Mamie Fulani daukan uwa tamkar wacce ta tsuguna ta haifeshi shi yasa ba'a yi masa shamaki da shiga shashin mai martaba a duk sadda ya nemi hakan. A b'angaren 'ya'yan Mamie Fulani kuwa ba ruwansu da rashin d'a'a ga Umma domin Mami Fulani ta horesu da kada su sake su shiga faɗar da babu ruwansu ciki. Sai dai duk wannan zaman lafiyar da Mamaie Fulani keyi ga kowa a masarautar hakan bai hanata gamuwa da mak'iya ba wand'anda suke takewa Umma baya irin matar Sarkin Fada dama wasu kamar dai yarda mafi akasarin gidan Sarauta aka sanshi bai rasa 'yan bani na iya, ma hassada da 'yan birne-birne asirai duk dan ganin bayan wanda ya fi su samun Ni'imomin rayuwa har da wurin Mahalicci domin duk wanda yafika tawakkali na yarda da ƙaddara khairan ko kishiyarta to ya fika samun duk kan Ni'imomi wurin Ubangiji Allah Subhanahu wata'ala. (Allah ka ƙara cire mana tsa-tsa a zukata domin alfarman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Amin). *** Washe gari a makare Sadauki ya tashi dan ko masjid bai sami zuwa ba lamarin da ya bak'anta masa rai ya k'arajin tsanar budurwan Aljanar domin ita ce silar makarar shi dan bai samu barci ba sai wuraren ƙarfe uku na dare wanda ya yisa cike da mafarkan daji mai duhu yanata neman hanyar fita ya rasa a ƙarshe ita ce ta bayyana cikin guguwa ta d'aukeshi sukayi sama. Lamarin da ya kasa b'acewa a kwakwalwar shi ganin taimakon da ta yi masa alhalin ita d'in azzaluma ce. "Mitcheww! Hak'ik'a ina cikin damuwa matsananci, shin aina zan sake gamuwa da ita?" 'Aliyu ko dai fansa take ɗauka?' "No! Banyi mata komi ba sai bisa tsautsayi wanda ita ta janyo afkuwanshi." Ya ambata cikin bawa zuciyarshi tabbacin shi mara laifin ne duk da wani shashi na zuciyarsa na ƙaryata hakan amma kaso mafi rinjaye bashi gaskiya keyi. Wanka ga gabatar sannan ya yi sallah ya koma saman gado ya kwanta dafe da k'irjinsa ya fad'a kogin karatun wasik'ar jaki wanda bai amfanarsa da komi sai sake shiga damuwa. Babban damuwarsa yarda yake kasa neman tsari da yarinyar haka yanzu bai iya tashi raya dare da nafil-fili kamar yarda ya horu da yin hakan a baya, jin bak'on lamarin na son sake ziyartanshi sai ya soma hailalah zuwa can ya tashi ya shirya cikin shigar sarauta har da yin rawani wanda ya k'ayata fuskanshi ya fito a Mai Martaba sak. Siyayyar da yiyowa su mai martaba ya ɗauka ya bar na k'anninsa. Yana fitowa da Saudauna ya haɗa idanu yana zaune a daf da shiga babban falon sashin Mai martaba, cikin nuna kulawa ya karasa gabanshi ya miƙa mashi hannu tare da ambatar sallama, k'eme-me Sardauna ya k'i amasawa balle bashi hannun dan musabaha, shanye ɓacin ransa Sadauki ya yi ya doshi shiga falon Sardauna ya kara masa ƙafa ya daka tsalle gefe k'iris ya rage bai faɗi ba, kallonsa ya yi tamkar zaiyi magana sai kuma ya gintse ya shige falon cikin sar-sarfa. "Sarauta dai sai gani ga masu gani" Sadauki na jiyo kalamamshi wanda ya soki zuciyarshi domin yana son Sarauta tamkar rai da ajali, a hasashenma ya fi Sardauna kaunar zamowa magajin mahaifinsu. Mai martaba ya samu yana ƙaryawa ya tako a sannu ya russuna ya kwashi gaisuwa sannnan ya zauna sosai cike da ladabi kansa ƙasa yana wasa da yatsun hannunsa. "Aliyu Saudauki Baban My Fulani, ina godiya." Mai martaba ya furta yana janyo jakan da Sadauki ya ajiye a gefenshi. Motsa kai Sadauki ya yi yana murmushi domin lamarin mahaifin nasu game da ambatawa Mahaifiyarsu kalma mai nuni da tsan-tsar kaunarsa gareta ya daina bawa kowa na gidan kunya domin a gaban kowa ambatarta ya ke da My Fulani ko my Queen. Gyaran murya Mai martaba ya yi yasa Sadauki maida hankalinsa kanshi tare da gyara zama ya tsira masa ido. "Aliyu ina da magana da kai mai mahummanci a game da abin kunyar da kake aikatawa wanda lamari ne da ya taɓa martaban Masarautarmu domin auri saki babban zunubi ne a tarihin kafuwar Masarautan Mungaye dama cikin addinin musulinci. Domin ba'a taɓa samun wanda ya taɓa sakin matarsa ba har sai mutuwa ce ta rabasu sai yanzu akanka dan haka ina mai sanar da kai hukuncina na ƙarshe akan lamarin shi ne duk ranar da ka sake sakin matarkata ta sunnah wallahi kaji na rantse bani ba ... "Na tuba Abbana, ku yafemin dan girman Allah, na rok'eka kada ka furta kalman da zai iya zamemin matsala ko ya zamo ajalina." Ya katse Mai martaba da sauri yana mai d'aga hannayensa sama alamun ban hak'uri. Shiru Mai martaba ya yi yana kallonsa wanda har lokacin ke saman guiwoyinsa. "Zauna da kyau ga kayan karin kumallo nan kayi." "Na k'oshi Abba." "Na soma wasa da kai ne?" Girgiza kai ya yi tare da ɗaukan kofi ya zuba kunun alkama ya soma kurb'a a hankali yana jin gard'in Nono tare da madara da aka wadata kunun da shi na ratsa harshensa sai ya lumshe ido zamowarshi masoyin duk abinda ke da alak'a da Nonon shanu. Bayan ya kammala hira mai cike da fahimta suka b'alle da Mai martaba wanda a cikin dibara ke tunasar da Sadauki mahimmancin aure ga baligi musamman wanda ke burin zama jagorar al'umma. Sadauki na amsar nasihohin cike da alfahari da samuwar mahaifinasu a matsayin uba mai tarin nagarta. Suna tsaka da hirar Sardauna ya nemi izinin shigowa Mai Martaba ya dama ya shigo cikin ladabi ya zauna tare da mik'o gaisuwa ga Mai martaba da Sadauki suka amsa daga nan aka ɗora hirar da shi har zuwa lokacin fita fadar Mai martaba ya yi ya sallamesu Mamie Fulani ta shigo ta taimaka masa ya shirya ya fice ta rakoshi har daf da k'ofar shiga fada da ke k'ofar sirri wanda Sarki ne kaɗai ke shiga ta nan duk ranakun girkin Mamie Fulani domin tana yi mara rakiya yayin da Umma ba ruwanta da bashi wannan kulawar dan tana kiranshi da munafunci ne k'anin karuwanci. Hak'ik'a a wurin kula da Mai martaba tundaga kula da cikinsa zuwa walwalanshi ya fi samunsa a wurin Mamie Fulani dan ko ba ranar girkinta ba ne ya kan sanya ta yi masa girki tun Umma na masifa har ta gaji ta bari domin mai martaba Abdul Hakam tsayayye ne akan iyalinsa yarda ya ke shugaban al'umma haka ya ke shugaba a wurin iyalinsa sam bai ɗaukan rainin hankali akan abin da yake ikonsa. Shi yasa yake girmama duk abin da Mamie Fulani tazo masa da shi ko da kuwa bai cikin tsarinsa zai amsa da hannu biyu ballema bata fiye zuwa masa da abin da bai zamowa dai-dai da ra'ayinsa ba. Soyayyarsa gareta ya samo asaline na kaunar da sukeyiwa juna tun kafin a aura mashi Umma wacce ta zamo k'anwa gareshi domin da maifinsa da na Umma ubansu ɗaya, ya ci burin soma aure Mamaie Fulani a farko amma mahaifinsa ya ce a'a ga zaɓinsa da yake mai biyayya ne ya amsa baki alaikum, shi yasa ko haihuwar fari Umma batayi ba ya auro Mamie Fulani sai dai bata sami haihuwa ba har saida Umma ta haihu uku duka mata sannan Allah ya bata kyautar 'yan biyu suma duk Mata, a haihuwar Umma na biyar ne Mamie Fulani ta yiwa 'yan biyunta gambo inda ta sami Aliyu, bayan shi ta sake haihuwar 'yan biyu maza Junaid da Jabir. Yanzu haka Mamie Fulani na da set din 'yan biyu uku, mata uku maza uku saboda a set na uku mace da namiji tayo, Saifullah da Lailah sai ta yi auta takwarar mai martaba suna kiranshi Mu'allim. 'Ya'yanta bakwai kenan, mata uku maza huɗu yayin da Umma ke da goma, mata takwas maza biyu. A nanma Umma na cike da hassadar Mamie Fulani akan finta da 'ya'ya maza da ta yi, sam ba ta gode Allah ba da ya albarkaceta itama da samun 'ya'ya mata jigon ginuwar al'umma. *** Sardauna "Umma dan Allah ki bar batun nan ban son jinsa, matata ta isheni rayuwa, ni bana cikin maza masu ra'ayin tara mata duk da ina son mulki amma banjin zan iya ajiye mace sama da ɗaya ba." "Saboda kana ragon maza ba." "Umma kema kin bi hanyar kirana da sunar da na tsana ko?" "Eh nabi d'in kuma ba k'arya akayi ba, rago ne kai ta ko wani fuska, izzar mulkin kawai ka ajiye gami da bak'ar zuciya amma a nuna k'wanji ko sakaryan mace ta fika katab'us." "Umma wallahi zan bar miki falonki tunda hakan kike so." "Gaskiya ne baka son a fad'a kuma sai na faɗa, sai dai kafi ruwa gudu. Wallahi ina kam takaicin zamowarka mai tarin rauni a cikin 'ya'ya mafi soyuwa gareni, in dama a ce ana canji da bilahil azim dana canjaka da autana Sayyid ya dawo kai ka koma shi ko burina ya cika na zamowa uwa ga Sarkin Mungaye." A fusace ya juya zai fice ta daka masa tsawa ya dawo ya zauna jikinsa na rawa saboda ɓacin rai. "Aifa kam a fushi nan kafi auki kamar wani jarumi." "Umma Please stop saying such kind of things dan wallahi suna k'omanin rai, ina jin tamkar zuciyata zatayi bindiga tayo waje ta tarwatse." "Natsu! Sardauna, ka samu bani hankalinka nan." Ta ambata cikin daka masa tsawa cike da takaici. Idanu ya tsirawa Umma fuska a haɗe, murmusawa ta yi tare da cewa "Kaga Sarkin birnin Mungaye ba, ta kawarka lafiya dan Sarki jikan sarki magajin Mai Martaba Abdul Hakam Hashim Malle." Murmushi ya yi tare kare fuskanshi da tafin hannunsa na dama cike da jin daɗin kirarin da ta yi masa kuma a take fushin da ya ke ciki ya sauka. "Ko kai fa Yarima, yanzu buɗe kunnuwanka ka saurari labarin fitar da na yi daren jiya cikin b'adda kama." "Duk kan natsuwata na tare da ke ya ke Ummata." Muskutawa ta yi daga kishingid'en da ta ke ta soma magana cike da walwala bisa alamu bayanin na faranta mata rai sai dai ga Sardauna abin bai yi masa daɗi ba domin sai tab'e baki ya keyi tare da girgiza kai tana dasa aya kuwa ya mik'e tsaye rai a b'ace ya soma magana. "No Umma bana son jin irin wannan shirmen na bokaye, shin in banda ya rainawa mutane hankali ta ya zaici miliyan biyu da rabi ya tsaya yiwa Aljanu karyan wai suna bibiyan Sadauki dan daukan fansa, k'ila Ubanshi ya turosu daukan fansa! To wallahi tun wuri ya dawo hayyacinsa dan baici bulus ba dole sai yayo kashin kud'ad'en nan tunda ba da Kakan Uban Ubanshi muka nemosu ba." "Sardauna koma ka zauna ko ranka yafi nawa ɓaci kuma kada na sake jin ka zagi Malam Sile dan ba sa'arka ba ne sannan duk wanda ya ce zai taimakeka ai fi gaban wulak'antawa." "Nifa Ummu bai taimakeni ba ya dai taimaki kansa dan haka sai ya biyani dukiyana." "Na ce ka zauna muyi maganar." "Affuwan Ummu sai anjima zan dawo jin tatsuniyar rainin hankalin da sile ya yi miki domin na gama kiransa da Malam daga yau." Baki buɗe Ummu ta raka bayansa da kallo har ya fice falon, tashi zaune ta yi daga kishingid'en ta dauko wayarta ta latsa kira ana dauka ta ce "Hajiya Kilishi maza ki zo in ban takuraki ba." "Lafiya kuwa Hajiya Umma?" "Ba lafiya Hajiya Kilishi." "Innalillahi! To gani nan zuwa ta k'ofar baya ki fito ki buɗe min a sirrance kinsan munafukai sun soma saka mana ido." Momyn Haske ce 🥰 *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon. AWA. Page 9. Bata amsa ba ta cire wayar a kunninta ta mik'e da kyar tana rangaji cike da izzar mulki gami da tarin damuwa. Falo na musanman da suka saba sirri Umma tayiwa Mama Kilishi jagora suka zauna a saman manyan kujerun alfarma da suka k'awata matdakaicin falon, bayan sun kulle k'ofa, Mama Kilishi ta dubi Umma cikin son jin k'arin bayani domin ta zak'u taji abinda ke faruwa. *** Sadauki Motsawa ya keyi a saman lilon a hankali idanunsa lumshe, hannayensa zube saman goshinsa, sanye yake cikin kayan motsa jiki sky-blue sun manne da farar fatar shi, iskan da ke busowa daga bishiyon lambun ya taimaka wurin ƙara nutsawarshi cikin zurfin tunani, inda ya ke hango kyaky-kyawar fuskanta da surarta tana jifarshi da shu'umin murmushin da ta saba amfani da shi wurin birkita masa lissafi yaji kamar zai haukace a cikin buk'atuwa. Daga nesa take hangoshi ta dauki mintoci biyar bata dauke idanunta akanshi ba zuwa can ta ja siririn tsaki tare da watsa masa mugun harara wanda baisan tanayi ba, har ta zauna a inda ta saba zama domin yin nazarin akan abinda ya shafi aikinta na kiyon lafiya sai kuma ta mik'e ta nufo inda ya ke nan ma ta dauki mintoci uku tana kallonsa batare da ya sani ba, nazartowa da tayi ya yi zurfi cikin tunani wanda tabbas zai iya zamowa barazana ga lafiyar yasa ta matsa gabansa ta motsa yatsunta biyu suka bada sauti mai ƙara ya motsa cikin kamewa duk da ya tsorata da jin sautin amma jarumta irin nasa ya hana tsoron baiyana a fuskanshi. Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da jan ƙaramin tsaki yana maijin tamkar ya rufeta da duka saboda katse masa yanayin da ke ciki na shagaltuwa da kallon Aljana domin bad'ini da zahiri sunar dake ambata mata kenan Aljana dan ta can-canci sunar dubi da yarda shi kaɗai ke iya ganinta. Nuna halin ko ina kula da yayi mata ya tunzura Dr. Muneera inda ta yi nufin barin wurin cikin zafin nama ya fizgota ta dawo gabanshi tamkar zata faɗa jikinsa ta yi nufin ja baya cikin ambaton a'uziyya ya sake janyota gabansa yana auna mata harara. Murmusawa ta yi domin ta gano abinda ya keson ji daga bakinta wato ban hak'uri dan zuwarta wurin har ya zamo abin laifi. "I'm sorry Yaya YS (Yarima Sadauki)." Sakinta ya yi ya koma yarda ya ke ya cigaba da motsa lilon. Kasa tafiya Dr Neera tayi ta gyara tsayuwa ta kafeshi da manyan idunta na gado domin zuri'ar Masarautan k'alilan ne basa da manya idanu masu burgewa. "Kina son ranki ya b'aci ko Doctor N?" "No." "To b'ace a wurin nan." "Saboda me?" Buɗe idanu yayi ta rausayar da kai ya tsare gira tare da cewa "Ina buk'atar kaɗaici, zaki iya tafiya domin ban nemeki ba, shin ko nazo ganin likita ne?" Bata amsa ba illa takowa da tayi ta zauna gefensa ta rike ƙarfen lilon da kyau saboda zamowarka mai tsoron hawa Lilo tun tana ƙarama. Ta soma motsa lilon a hankali kamar yarda ya keyi, sake lumshe ido Sadauki ya yi yana jin wani yanayi na ziyartanshi zamowar kusancin da sukayi da juna dan jikinta na gogan dantsen hannunsa da ya ke abude ga kuma k'amshin turarenta mai tada hankali da ya fahimci ya kame jikinta. "Yaya YS ka natsu ka san cewa rayuwarka ba kai kaɗai take amfanarwa ba har da dubban jama'a daga cikin Masarauta zuwa wajenta dan haka ka kori damuwa ka maye gurbinta da nishad'i sannan ka k'ok'arta wurin cikawa su Mai martaba burinsu na zama da mata bisa igiyar aure mai tsauri kada ka sake aikata laifin da ka aikata a baya domin hakan zai taimaka ka samawa su Mamie sanyin idaniyarsu kafin ƙasa ya rufe idanuwarsu wato abin cikin kwai." Shiru ta yi tana murmushi cike da tsokana, ganin baida niyyar magana saita sauka akan lilon ta yi dan taku biyu zuwa uku sannan ta juya ta fuskanceshi duk da tana da tabbacin ba kallonta ya keyi ba ta ce "Karfin sha'awarka na son kaiwa matakin da zaka kasa mallakan kanka har sai ka fitar da shi wanda bana fatar ka haik'ewa kuyangi ko k'adangarun bariki ka goga mana bak'in fenti, laifin da bamusan yarda aka aikatashi ba ya bibiyemu mu shiga uku." Tar ya buɗe idanunsa amma sai ya ci karo da bayanta domin tana gama ambata ta juya ta nufi wurin zamanta da sar-sarfa. Bai daina kallon bayanta ba har saida yaga ta zauna tana shirin d'agowa sai ya maida idanunsa lumshe amma yana hangota dishi-dishi. "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, ai na gamu da wahala kam." Ta ambata a saman lips dinta. "Amma me ye damuwarshi? Yana da lafiya irin haka ya ke sakin matarshi sannan duk ba wacce ya aikata sunna da ita, kai anya ba Aljana ta aureshi ba? A'a Wanda Aljana ta aura baya jin feeling kamar yarda yaya YS ke ji, wallahi da lauje cikin nad'i a game da rayuwarsa, shin ta ina zan san bakin zaren? Murmusawa ta yi tare da murza goshinta ta furta wata kalma a can k'asan mak'oshinta wanda ita kaɗai taji kayanta. *** "Ina jin damuwa da lamura ki Dr. Muneera tun kuwa baki san kanki ba." Sadauki ya furta a hankali yana mai jin yanayin da ke ciki na ƙara tsananta gare shi. Sauka ya yi ya nufi k'oramar da ke ƙarshen lambun ya shiga ya nutse cikin ruwan tsawon mintoci biyar sannan ya taso yana girgiza sumarsa ruwa na tartsi,ya sake komawa ƙasan ruwan wannan karan ya shafi mintoci ashirin sannan ya d'ago rik'e da kan narkeken kifi yana zile-zillen son kufcewa. Bakin k'oramar ya fito ya zauna saman kujerar roba ya tsirawa cikin ruwan ido abin mamaki ita ce take nink'aya cikin sutura masu bayyana halittanta fili, ware idanu yayi tare da sakin kifin ya koma cikin ruwa aikam ta cafeshi ta cillo masa ya fad'o jikinsa lamarin da ya shi sakin siririn ƙara cikin fitar sauti saboda ya dukar masa cinya da ya yi, aikam ƙaran sai a kunnin Neera ta nufo hanyar da zai sadata da wurin a guje, jin takunta yasa Sadauki komawa ruwan tare da kifin domin baya son ta ganshi a yanayin bayyanar halittunsa fili dan shiga ruwar da yayi ya sanya kayan sun mamme a jikinsa surarsa ya fito fili. Zama tayi ta kafe ruwan da ido tana mamakin yarda ke iya jimawa a ƙasan ruwa kuma yafito lafiyalau. Takalmansa ta dauka tana juyawa dan ta soma gajiya da zaman jiran fitowar na shi. Ruwan ya motsa da ƙarfi, ta kalli cikin k'oramar gami da ware ido saboda hango k'atuwar Kada na shawagi alhalin ta san babu ko kadangare a cikin tsafta-tacciyar k'oramar, murmushi ta yi tare da jifarta da takalmin hannunta aikam take ta ɓace. Tafi ta yi tana furta "Haba yaya YS ba twins yayan gambo zaka gwadawa Ofi ba balle ka bani tsoro, wallah sai dai ni na baka tsoro da macizai." Tana rufe baki babban kifin nan ta fado kusa da ƙafarta ta daka tsalle tare da kwalla ihu, kafin kobo ta bar wurin a guje domin Allah ya jarabceta da tsoron manyan kifaye shiya ko su Lailah na kallon chennel ɗinsu bata zama a wurin. Fitowa ya yi yana murmushi ya zauna saman dutsen gefen k'oramar na sharce ruwan gashin kansa. "Doctor Muneerat manya aida kin tsaya kin nunamin ke 'yan biyu ce da ni kuwa na gwada miki Gambo sha gaban 'yan biyu ne a Ofi." Ya jima zaune a bakin k'oramar yana wasa da kifin inda ke kiranshi sai ya taho a juye idan zai kashi sai ya zille ya daka tsalle ya koma ruwa inda zai watso a fuskanshi, da ya gaji ya dawo saman kujera ya zauna ya daga kai sama yana kallon tsuntsaye da ke ta shawagi a saman bishiyar mango zuwa lokacin har kayan jikinsa sun bushe sakamakon iskan da ke kad'awa, yana ta mamakin yarda akayi Aljanan ke son yi masa wasa da hankali. Kiran sallar a Zuhur yasa ya mik'e ya nufi filin motsa jiki ya ɗauki jallabiyasa ya saka ya fito cikin takun k'asaida wanda ke ƙara fito da kwarjininsa a fili. Bayan an fito sallah suka hadu da Imam suka nufi cikin Masarauta gidan su Imam suka nufa suna shiga Neera na fitowa da gudu Maryam biye da ita, tsak suka tsaya kafin Neera ta yi magana Sadauki ya tareta cikin cewa "Kun girma ba kusan kun girma ba to aure za'ayi muku ku tafi can suyi ta haukan da mazajenku." "Aikam da ka kyauta mana dan naga kamar an manta da mu ne gashi mun balaga da jimawa." Kallon Neera ya yi idanu waje yana lek'en bayanta sai yaga bakowa a wurin sai shi da ita dan Imam wucewa ya yi ciki. "Kin rainani ko?" "A'a kawai banji daɗin kalman haukan da ka kiramu da shi bane kuma ina son magana da kai." "Banda lokaci." "Zakayi ne idan ciwonka ya sha k'arfinka." "Neerah!" Ya ambata da sauti. "Yaya YS me nayi kuma?" Ta furta a shagwab'e. Sauke numfashi ya yi ganin Momy ta fito ya russuna ya gaisheta tare da juyawa ya fice. "Muneera me yasa kika raina Sadauki ne?" "Momy wallahi ban rainashi ba." "Shi ne zai ambaci sunarki cikin fushi." Sosa tsinin hancinta ta yi ta furta "Mahaukaciya ya cemin na ce masa aljanin ruwa domin wallahi d'azun a Garding ya dauki kusan awa ɗaya a cikin ruwa bai fito ba kuma har da bani tsoro ya yi." Girgiza kai Momy ta yi tana murmushi, bayanta Neera tabi tana cewa "Hajiya Momy bani sakwarar in kaiwa Ammina." "Ita dama zan haɗa miki da kaina dan nasan Hajiya Safiyya tunda ta ce inyi mata kowa ya saka hannu zata iya ganewa na k'i ci." "Ai Momy lamarin Ammie mamaki ke bani ita ba twins ba amma tafi twins tsirfa da gano abin da aka b'oye mata." "K'ila ke da Sadauki kuka sammata Ofi." "Nikam Momy ban da komi sai dai ko shi." "Baki da shi kike hukunta duk wanda ya dukeki da macizai sadda kuke yara?" "To ai Momy lokacin muna yara ne yanzu kuwa girma ya zo dole na watsar da shiriritan nan." "Uhm Allah yasa haka ne kuma ki rage biyewa Sadauki dan tsaf Hajiya Safiyya zata hukunta ki inta gano kin raina mata shalele." "Uhm nikam Momy ban raina shi ba kawai ina son ganin yana magana ne kamar kowa sam ban son ganinsa cikin shiru domin yin maganar zai taimaka wurin rage masa damuwa." "Shi ya sanar miki yana cikin damuwa?" "A'a Momy amma a kallo ɗaya zakayima yaya YS ka gano na tare da damuwa duk da b'oyewar da ya keyi." "Oh ni Hauwa kulu ina ganin wani salo a wurin Likita alhalin ita ba karatun sanin halayyan d'an Adam ta yi ba." "Kai Momy, kawai damuwana da lamuransa ne yasa nake saurin ganowa in har yana cikin yanayi mara daɗi." Dariyar da Momy ta sanya ne yasa Neera sunkuyar da kai ƙasa, sai kuma ta juya ta fice da sauri. "Ja'ira bisa alamu iska na wahalar da mai kayan kara." Momy ta furta tana jinjina kai fuskanta ɗauke da murmushi. Suna hira da Maryam Momy ta fito da kwando da sauri Neerah ta mik'e ta amsa tana mai furta "Allah ya rubu ce Momy." "Amin Doctor." Har Neera ta kai bakin k'ofar falo ta tsinkayi magana Momy inda take kiranta tazo suyi lunch. "Momy zan shiga Asibiti nan da awa ɗaya amma a haɗa dinner da ni dan anan zan kwana saboda haka Maryam ki dafamin abinda na fi so dafatan kin gane." " 'Yar rainin hankali sai dai ki kwana da yunwa domin jirgi ɗaya ya kwasomu kinfi kowa sani ba son shiga kitcken nakeyi ba" "Kinji Momyna ki dafamin abu mai daɗi kuma Allah ba wanda zaici." "Ko yaya Saudauki ne?" Maryam ta ambata tana kallon idanun Neerah. Ficewa falon ta yi da sauri Maryam ta kwashe da dariya, Momy ta yi mata dak'uwa ta gintse dariyar. "Aikam gara da kika ambata mata haka yaya Maryam domin daga ke sai shi Yaya Neera ke sakemawa in ancire mahaifanmu nasha jin ana gulmanta domin har 'yar k'waya naji ana ambata mata." "Ke Baby Nanah ban son k'arya." "Allah kuwa yaya Maryam, naji yaya Sardauna na faɗawa abokinsa wai k'waya yaya Neerah take sha shi yasa bata ganin kowa da gashi dan kawai ta dawo a gajiya ta wucesu yana yi mata magana bata kulashi ba sai hannu ta d'aga mashi." "Autana taho muci abinci kuma ban son na sake jin kin bada wannan labarin gudun haɗa fitina." "To Momy amma dai zan sanar da yaya Neera saboda ta dauki mataki kada jama'a su soma yi mata wak'ar 'yar maye." "Autana kada ki sanar da ita sannan 'yar k'waya da Sardauna ya ambatawa Muneera ba nufinsa tana shaye-shaye ba, nufinsa tafiye rashin son magana da kuma takawa ko waye burki in ya tab'ota." "Oh Momy na gane yanzu amma ba kowa ne zai fahimci haka ba." "Haka ne kam Autana mai kaifin basira." Murmushi Nana ta yi cike da jin daɗin yabon da a kayi mata alhalin kashe bakin bada labarin Momy tayi zamowarta mai gudun fitina. Bayan sun gana cin abinci Momy ta kira Maryam suka shiga bedroom d'inta ta dubeta ta ce "Me ke tsakanin Muneera d Sadauki?" "Wallahi ban sani ba." "Ban son wasa Maryam sanar da ni abinda na ke zargi." "Momy a gaskiya Neera na son yaya Sadauki tun kafin ya soma auri saki karatun da takeyi yasa bata nuna masa alamu ba har zuwa yanzu tana son shi duk da hatsarin da ke cikin aurensa baisa ta sadduda ba sai dai in banda ni ba wanda ya sani hatta kuwa Lailah da Zuhrah ba wanda ya gano k'aunarta gareshi jama'a na ɗauka ƙarfin zumuntar da ke tsakanin su ne ya janyo suke shiri da juna dan kema sheda ce kaf 'yan matan Masarauta ba wanda yaya Sadauki ke sakewa fuska har ta gaya masa maganar da taga dama sai Neerah." Numfashi Momy ta ja tare da cewa "Zanso Sadauki ya furta yana sonta." "Saboda ne Momy?" "Saboda duk wanda ya aura ya saki haɗa su akayi wata k'ila nuna ra'ayinsa akan auren wacce ya ke so zai kawo ƙarshen auri sakin." "Momy yaya Sadauki na da matsala a fara neman masa magani kafin a sake yi mashi aure." "Kema kinyi magana anan domin muna tattauna maganar neman masa magani da Mamie Fulani " "Yawwa hakan dai yafi." Sai abu na gaba shi ne maganar fitar da miji, shin wa kika tsayar cikin namemanki?." "Miji fa Momy?" "Eh Dadynku ya umurceni da in tambayeki saboda ya daina yarda da auren had'i sannan Mai martaba ya soke auren had'i amma in kun haɗa kanku ba ruwansu zasu sanya albarka." "Momy wani abu na faruwa ne wanda bamu sani ba har akan ya faru?" "Ko ɗaya kawai Mai martaba ne da kansa kwanaki ya tarasu ya sanar da su soke auren had'i amma ina jin bai rasa nasaba da abin kunyar da Sadauki keyi na sakin matar da ake bashi." "Momy bana da gwani saboda ina tsoron abin da ya sami yaya Khadijah ya sameni domin har yau tana begen Mahmud bayarda zatayi ne dole ta karb'i yaya Sardauna duk kuwa da yana kan cutar da ita." "Ban tambayeki wannan labarin ba sannan tunda baki da gwani sai Dadynku ya zab'a miki ko cikin dogarai ne." "Momy dogarai kuma?" "Eh tunda na zama abokiyar wasanki ba." "Sorry Mum zamuyi shawara da su Neera." "Ke dai kika sani kuma ina baki shawara da kiyi nazari banda biyewa shawarar zuciya wanda ke haifar da dana sani." Ganin ta faɗa tunani Momy ta fice daga d'akin cikin yi mata addu'ar samun k'warin zuciya akan duk abinda ta sanya a gaba. Maryam ta kwanta a saman gado, matsanancin damuwa kwance a fuskanta. "Yaya Sadauki." Ta furta a saman lips d'inta tana mai lumshe ido tare da nazarin kalaman Momy na ƙarshe. Zuwa can ta zabura tamkar wacce a sokawa Allura ta fito, ganin ba kowa a falon sai ta dauki hijabin sallah ta fice da sauri, Hadiman da ke kai kawo a tsakanin sassan Masarautar suka soma jero mata gaisuwa amma ba wanda ta sami zarafin amsawa. Momyn Haske ce 🥰 *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon Adabi Writer's Association (AWA) https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 🖕 *Ayimin Affuwa kwana biyu ina cikin hidima ce shi yasa ku ka jini shiru.* Page 10. Part d'in Mamie Fulani ta nufa ta shiga k'aton falon da sallama, Lailah ce ta amsa cikin dishewar murya wacce ke zaune gaban Sadauki bisa alamu laifi tayi masa. Da sauri Maryam tayi nufin juyawa ya daka mata tsawa. "Ke!" Tsak ta tsaya batare da ta juyo ba. "Zo nan dama ina shirin kiranki." 'Nashiga uku Allah yasa dai ba masifa Lailah ta janyomin ba.' Ta ambata a ranta ya yin da a fili ta juyo jikinta na rawa tare da furta "Ni?" Shiru shi ne amsar da ta samu sai tasami kanta da ƙare masa kallo sanye yake cikin kayan sarauta wanda yafi ta'amali da su domin kafin ka gansa da ƙananan kaya aiki ne sai ko suit wanda da an gansa cikin shigar ke nuni da zaiyi tafiya ne sai kuma a filin motsa jiki inda ke shigar sport wear. "Please Maryam ki zo kiyi masa bayani wallahi ba ruwana da Muhib, shi ne ke takurani ke biyoni gida." "Keep quiet!" Ya ambata a fusace. "Sorry Yaya, dan Allah ka taimakeni ka saurari bayanin bakin Maryam domin ita, Neera, da Zuhra ne shaiduna akan bayanin da nake yi maka, wallahi Allah ba ruwana da Muhib." Kallo kin rainani ya auna mata sai ta fashe da kuka ta kama k'afarshi janye ƙafar ya yi tare da mik'ewa ya nufo k'ofar fita saboda kukanta ya karya masa zuciya kuma a take ya yarda da gaskiya take sanar da shi. Maryam na ganin tasowarshi ta runtuma da gudu tamkar zata kifa sai lamarin ya bashi dariya ya murmusa tare da juyowa ya ce da Lailah "Ki fita sabgar mara natsuwar yaron nan idan kuma kina son mu sa k'afar wondo ɗaya da ke ne to in sake ganin ƙafarsa a cikin Masarautar nan sannan in har kin san kin kamu da son shi to kiyi gaggawan cireshi a ruhinki domin kinfi ƙarfinsa ta ko wani fuskan kuma ke mai tsarki ce dan haka ba zan bari ki auri mai cike da dattin najasa ba, a bisa umurnina ki koreshi koro na har abada." Ya kai ƙarshen maganar na runtse ido domin yanajin tamkar bayyiwa masoyan adalci ba. Gyada kai ta yi tana share hawayen da ke zubo mata, ganin na kallonta sai ta motsa baki a hankali ta ce "Nayi maka alk'awarin dakatar da shi daga zuwa Masarauta tare da nesantarshi na har abada duk da dama shi ke haukansa ni bai isheni kallo ba." "Da kyau." Murmushi tayi ya maida mata da martani ya juya, har ya fice ya dawo ya ce "Saura ki haɗa baki da wancan mara kunyar ku turomin macizai saman gadona kamar yarda kuka saba aikatawa idan anyi maku faɗa." "Allah yaya ba ruwana Neerah ce da aikin kasan bana yin Ofi sai da babban dalili." "Nadai sanar dake kada inga maciji a muhallina." Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi domin tsayawa zancen nan na nufin ya huce kenan. "Humm zan gyara maku zama ne musanman ita da ta rainani." Ya ambata yana barin wurin. "Ka soma gyara kanka Babana domin kai da su duk kanwar ja ce wani fanninma kafisu tsorata mutane da Macizai wai lamarin har kan Mai Martaba dan ya sanar da kai gaskiya." Da sauri ya dawo falon ya rik'o hannun Mamie yana k'ifta mata ido, alamun tayi shiru. "Yes, ka soma gyarawa kanka zama kafin ta zo kan wasu wanda basuyi kwatan-kwacin laifin da kake kan aikatawa ba." "Wayyo Mamiena me na yi kuma?" "Babban zunubi na auri saki da kuma tsoratar da Musulmi ta hanyar fito da macizai su razanasu akan laifin da baikai ya kawo ba, kwanaki Mai Martaba har kusan fad'uwa ƙasa ya yi dan tsoro, tabbaas da ba dan ina kusa ba da anji mugun labari sakamakon macizai da suka cika turakanshi marasa kyan gani sannan tamkar almara suka b'ace, ganin anyi binkice ba agano komi ba sai na tabbatar kaine ta turosu, anya Babana hakan ya kamace kuwa?" "Mamie ya wuce fa." Ya furta cikin tsare gira ganin Lailah na k'unshe dariya. "Bai wuce ba, mai jin magana kawai kada a fad'i ɗayan." "Please Mamie ki manta da lamarin, ai natuba da jimawa." "Anya Babana kai kaɗai ne kuwa?" "Me nayi kuma Mamiena?" "Watsi da cikar kamala wato aure sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. "Ayya Mamie ki bar maganar auri sakin nan domin yana daga cikin zanen ƙaddarar shi wanda bawa bai isa kufce masa ba saboda rubutacce ne daga Allah." Duk kallon bakin falon sukayi a tare, Dr. Muneerah ce tsaye idanu jajur bisa alamu kuka tayi. "A'a Likita bokon turai, lamarin Babana ko da ƙaddara to son zuciya ya soma yi masa jagora domin ba sau ɗaya ko biyu ya aikata laifin ba har fa sau hu... "Mamiena ya tuba ai ba zai sake komawa ga zunubin ba ko yaya Yarima?" Kafeta da idanu ya yi batare da ya amsa ba. "Yes Neerah yaya ya yi tuba na gaskiya da yardan Allah ba zai sake komawa ga wannan laifin ba, zaiyi aure ya zauna lafiya da iyalinsa wannan a rubuce yake." Lailah ta amshe da sauri tana kallon idanun Sadauki. "Au, in na fahimta kuna bayan iya shegen da yarik'a aikatawa kenan?" "A'a fa Mamie amma dai tunda ya wuce to abar d'aga zancen gudun ɓacin rai kinsan abu kaɗan ke sanyashi cikin tunani ya soma wasan b'uya da kowa kuma hakan kan jefashi cikin kaɗaici sannan hakan bai kamata ba yana Sarkin Gobe na fuskantan matsin rayuwa." "Muneera wai nawa Babana ya biyaki ne?" "Na me fa Mamie?" "Na campaign mana." Ware ido ta yi Sadauki ya murmusa tare da russunawa gaban Mamie ya yi mata rad'a wanda ita kaɗai tajiyo abinda ya ambata aikam ta sauke masa dundu tana furta "Allah ya tsare, ya kare, can ga su gada wai Zomo yaji kid'an farauta, wallahi a kul ɗin ka da wannan lamarin kadaiji na sanar maka in ba so kake mu koma gidan jiya ba." "Allah Mamie na zama kurna akan lamarin sam banji me kike cewa ba." "Amsa naka Sadauki, Allah kada naji ko na gani kuma nan da sati biyu ka kawo mana matar aure ko ranka yafi dare duhu da fatan katuna maganar Mai Martaba." "Mamiena dan Allah ki ami... "Nagama magana Babana sannan kada na sake ganin ka tasa k'anninka a gaba da zancen baka son suna zance tunda ba jik'asu zamuyi mu sha ba." "Mamie da dare zan dawo muyi maganar a gaban Abba domin a wannan gab'an banjin zan ja da baya ba." "Na zama abokiyar wasarka ko Baba Ali?" "Tuba na ke Fulanin Mai mar... "Gidanku na ce Sadauki." Girgiza kai yayi tare da sumbatar hannunta da ke riƙe da shi tun dazun kana ya saki ya iso daf da Neerah ya rage murya ya ce "Iyayi kawai to ban gode ba." "Gobe ma rana ce da Muneerah kake zancen ɗan Samari." "Mamie 'yarki ta rainani fa." Ya ambata cikin kawo mata duka ta gofce. Banza Mamie ta yi masa sai ya fice yana cije lips gami da nuno Neerah da yatsa cikin salon wasa ya yin da ita kuma keyi masa gwalo. Murmusawa Mamie Fulani tayi domin abinda ke saurin sakata farin ciki shi ne ganin walwala a fuskan Sadauki Aliyu. "Ke kuma taho naji damuwarki da kika tahomin da idanu kamar jan nama." "Ciwo sukemin Mamiena." "Kika sake ambatarmin k'aryan nan sai na saɓa miki." "Affuwan Mamie kaina ke ciwo kuma kin san ban da juriyan ciwo ko kaɗan, shi ne nayi kuka Ammi ta koroni wai na dameta da jan hanci kada in saka masu mura ita da yaranta." "Ayya sannu, kyale Nana ai ciwo na kan kowa, taho kisha magani domin na san halinki na gaba da magani wai kina Likita amma kina gudun magani, Allah ya kyauta kam." Cikin murmushi ta iso ta zauna gefen Mamie tare da manno jikinta da ƙafarta, sai ta dafa kanta cike da kulawa take yi mata sannu kana daga bisani ta bawa Lailah umurnin ɗauko mata maganin ciwon kai a d'akin barcinta, cikin dibara Neerah ta gudu kafin Lailah ta dawo ta nunawa Mami a biyota da shi dakin Lailah saboda abinda Neerah ta tsani shansa shi ne magani. *** Hajiya Umma ta ya kika yi wannan waftar na fed'ewa Sardauna biri har wutsiya shin kin manta waye shi akan gaba da bin bokaye? To wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki ki sanja dabara domin ina da tabbacin bazamu taɓa samun haɗin kansa ba tunda kinayi waftar sanar da shi gaskiyan lamarin da muke kai." "Ki bari kawai Hajiya Kilishi wai a zatona in yaji Aljana na tare da Sadauki zaifi yin farin ciki tare da bamu haɗin kai har mu kai ga nasara." "Kin manta har kwanar gobe suna fita rangadi tare domin ginuwar ƙaunarsu kuma ƙaunar da mai Martaba ya dasa a zukatansu bai taɓa gogewa sai dai zan sanar da ke hanyar gaskiya domin kawo nak'asu a ƙaunarsu shi ne sai mun tashi tsaye mun sa an raunatashi yarda zasu zamo basa ga maciji ko kaɗan shi ne zamuyi nasarar ɗora shi akan turban da muke so haka game da son kud'insa sai anyi mana aiki ta yarda kome kika nema ya baki batare da kai ruwa rana ba tunda yana da dukiya kuma ba mai amfana da shi sai makirar matarshi da uwarta ke kuwa sai hange daga nesa to sam hakan ba mai yiwuwa ba ne, yarda kika sha wahalar haihuwar sa gami da rainon sa dole ya zamo ke ce ta farko da zaki mori dukiyarsa tare da sanin duk kan bayanen ƙaddarorinsa." "Tabbas kinyi gaskiya Hajiya Kilishi, zantukanki masu amincewa ne gareni, yanzu zan baki wuk'a da nama ki zamo idanuna na kai da kawo tsakanin lamarin saboda yawan fitana a b'oye nada hatsari dan idan Mai Martaba ya sani kashina ya bushe wata k'ilama aurena ya sami tangarda tunda angama da shi bai kallona da daraja sai muguwar Fulanin can wacce ba zata gama lafiya ba." "Kibari kawai, gata bata jin Asiri." "Kin manta waye Uwarta kenan? Ai Hajiya Dada cikakkiyar matsafiya ce domin maganar Malam Sale kenan duk in ya buga ƙasa Uwarta na tsaye kanta shi yasa sai yarda tayi da Mai Martaba." "Aikam na yarda Hajiya Dada na tsafi domin dubi zafin Chiroma amma a gaban Nana Safiyya sai ya koma fulawa saboda laushi." "Uhm ai ƙarshen su ba zaiyi kyau ba in sha Allah." Allah ya amsa." "Amin Aminiyata." Murmushi Hajiya Kilishi tayi sannan ta maida hiran kan abinda suka zauna a kai, inda cike da kisisina take cewa "Dama ina shirin yi miki wannan maganar fitar da kanki sai nayi nazarin a wakilta Hud yana amsowa tare da sanya Sardauna amfani shi wanda ba sai ya zo hannunki ba kinsan Hud da iya kalaman makirci na tabbata cikin sauk'i zai sakashi yin amfani da maganin hankali kwance, kinga ko wanda zaici a abinci ne duk Hud zai bashi saboda in muna son ya sami farin jinin jama'a sama da wanda Sadauki ke da shi dole sai mun hada na ci a abinci da sha da wanka har da hayak'i." "To ba matsala hakan za'a yi, zan turo maki sak'o anjima amma kada a amso na hayak'in nan saboda zai harbo jirjinmu." "To madallah, bari in koma kada mai gidan ya neme ni." "Yau ke ce da turakar kenan." "Eh fa." "Ok tafi nima ina da baƙi anjima kaɗan." "To na wuce, Allah bamu yinin lafiya." Motsa kai Ummu tayi cikin lumshe ido dan kanta taji na ciwo, harara Hajiya Kilishi ta zabga mata ta gefen ido tana zund'enta a fakaice sannan ta buɗe k'ofar ta fice cike sak'e-sak'en yarda tsarinta zai tafi batare da samun tangarda ba na ganin d'anta Hud ya haye karagar mulkin Mungaye tunda shima Babansa ɗan Sarki ne yana da sarautar da zai iya Mulki ba sai lallai 'ya'yan Sarkin dake kan karagar mulki ba "Wallahi bana son Sadauki domin tuni na kamla rabashi da Masarautar baki ɗaya lokaci nake dakon ya yi a nemeshi a rasa daga ganan Hud ya zamo Sarki mai iko domin bazan bari Sardauna ya zame masa matsala ba a tafiyar ba." "A'a Mamma ina mutuwar son Yaya Sadauki kuma shi nake burin gabatarwa Abba a matsayin zab'ina kamar yarda kuke dakon jin gwanina sannan ina tare da ke kan zamowar yaya Hud Sarki saboda lokaci ya yi da za a kawo sauyi ba lallai sai 'ya'yan Sarkin dake mulki ne zasuyi ta gadon sarautan ba, duk da a gefe ɗaya ina jin kamar ba zai iya ba dan ban taɓa jin mashayi ya hau karagar mulkin Mungaye ba." A razane Hajiya kilishi ta dubi inda mafi soyuwar 'yar nata ɗaya tilo mace cikin 'ya'yanta maza huɗu. Gyara tsayuwa ta yi tare da jinjinawa mahaifiyar nata kai alamun bata tabbacin furucinta tare da cigaba da cewa "Yes Mamma ina yin Yaya Sadauki kuma shi ne mijina da yardan Allah dan na k'udiri aniyar d'aura d'amarar jure zama da shi a duk yarda ya ke, ni ce zan kawo ƙarshen auri sakinsa insha Allah" 'Wata sabuwa inji 'yan ca-ca, hak'ik'a aiki ya sameni ni jikan Magaji.' "Momma muje nasan baki rasa shawarar da zaki bani akan auren sannan kada ki kushemin zab'i a kan abinda ya ke zanen ƙaddararshi ne wato auri saki." Dafe kai Hajiya Kilishi ta yi tana jin wani mak'ak'in d'aci na sauka saman harshenta. 'Tirk'a haka zakiyimin Zuhra? To wallahi ko zaki mutu ne ba ki isa hanani kora Sadauki duniyar da bazai kuma waiwayen Masarauta ba.' Ta sake ambata cikin ranta tana dallawa bayan Zuhra harara wacce take shirin shiga d'akin barcinta. *** "Hey Doctor Neerah, me ke faru ne har ya sakaki kuka?" Motsa yatsunta Neerah ta yi tamkar zata furta kalma sai kuma ta tsuke bakinta tare da hayewa saman gado ta juyawa Lailah baya. "Dan Allah Muneera sanar dani damuwarki ko in had'a ki da Mamie nasan ita zaki sanar da ita." "A'a Lailah kada kiyimin haka, yanzu taso muje ki rakani gidan Hajiya Dada." "Asibitin da kikace zaki shiga fa?" "Na fasa." "No ki muje na rakaki domin ba kyau saɓa alƙawari." "Na tura masu Dr. Hassana harma ta isa kinga sak'on da ta turomin yanzu." "Ok amma gaskiya kada ki sake irin haka tunda kin san ke suka fi buƙata." "In sha Allah." Suka fito bayan Neerah ta gyara fuskanta ya yi kyau suka sami Mamie zaune hadimai kewaye da ita suna yi mata hira cike da sakewa zamowarta mara girman kai irin na mafi akasarin matar sarakuna. Bayan sun amsa gaisuwar hadimai sai suka sanar da ita inda suka nufa ta tsare gira kafin tayi maga Neera ta rigata da cewa "Please Mamina gidanmu na biyu zan kai ziyara fa Allah daga nan ba inda zamu wuce kinsan halinmu.." "Muneera bana son yawo ne alhalin kuna 'yan manyan gida musanman yanzu da ake maganar aurenmu" "Mamie dubo fa sanyin idaniyarki zamuyi ba yawo ba sannan baza mu wuce awa biyu ba zamu dawo in sha Allah." "Ok to shiga kitchen ki wuce mata sak'onta dama Junaid yanzu zai kai mata kun hutash-sheshi kam." "A'a Mamie suyi tafiyarsu inyi tawa da Maryam dama na ce ta shirya zamuje gidan tsohuwar Mamie ziyara. "Mun huta kam." Lailah ta ambata cikin murgud'awa Junaid baki, ya kawo mata duka ta koma bayan Mamie tana dariya. "Affuwa dai Yarima Junaid." Kuyangi suka ambata cikin girmamawa kansu sunkuye. Hannu Mamie ta d'awa su Neerah suka fice sunayi mata godiya yayin da Junaid ya dubi wata kunyanga ya bata umurnin da ta d'auko masa sak'on a kitchen, ta wuce da sauri tamkar zata kifa. "Bi a hankali Dudu." Mamie Fulani ta furta cikin kulawa saboda yarda ta ke daraja d'an Adam, ko zaman kuyangi a sashinta na dole ne dan zamowarta matar sarki amma tafi son ta kasance daga ita sai 'ya'yan dana al'umma sosai take tausayawa bayi shi yasa wad'anda ke sashinta suke jin daɗi fiye da wanda ke sashin Umma da sauran matan masarautar kuma hakan ya ƙara mata k'ima a idanunsu da zuri'arta dama duk wanda ya ziyarci sashin to zaka samu kuyangin na karrama duk bukatun sa. Momyn Haske ce 🥰 *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI. By Mrsjmoon. Adabi Writer's Association (AWA) https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 🖕 Page 11. Su Lailah na fita wajen Masarauta Neerah ta doshin Mungaye Garding maimakon gidan Dada da ta ce zasu. "Dr. Ya dai?" "Nafasa zuwa can muje Lambu saman Lilo." "Lilo kuma? Yau ke ce ki ke ambatar hawa Lilo?" "Eh Ina son tuno da wani yanayi ne da ya wuce." "Ikon Allah, anya ba soyayya kika faɗa a gofce ba Sister?" Bata amsa ba ta tura hancin motar cikin garding dogarawa masu gadin gate ɗin suka soma mik'o gaisuwa hannu suka d'aga masu kawai suka wuce. Can kusa da filin motsa jiki ta yi parking suka fito zuwa wurin Lilo sula hau suna motsawa a hankali. Neerah ta yi lum idanu lumshe fuskanta cike da murmushi, ita dai Lailah da kallo take binta cike da mamakin sauyin yanayinta daga mara walwala zuwa mai walwala daga hawa saman Lilo. "Uhm in tayi wari maji." "Me ne?" "Komi da kike b'oyemin." Wani murmushin ta sake cika fuskanta da shi, Lailah ta kaiwa cinyarta duka ta buɗe ido da sauri tana shafa wurin batare da tayi yink'urin ramawa ba, cike da mamakin hakan Lailah ta kamo hannunta tana cewa "Me ke faruwa Neerah da za a yi miki abu ki hak'ura batare da kin rama fiye da yarda akayi miki ba?" Bata kula ta ba illa ta sake lumshe ido tana motsa Lilon da ɗan sauri *** "Imam ina cikin damuwa domin a yau ina jin k'aunar d'iya mace sama da komi sai dai k'alubalen da na ke hangowa na son dakushemin k'warin guiwar da nake da shi na tunk'arar yarinyar." "Buɗe min lamarin bana son wannan kwane-kwanen Malam." Rintse ido Sadauki ya yi tamkar ba zaiyi magana ba zuwa can ya buɗe ido yana fuskantar Imam cikin serious tare da yin ƙasa da voice kana ya ce "Ita ce nake hangowa zata iya hak'uri da lalurata, ita ce zata b'oyemin sirri, ita ce jinin jikina gaba da baya dan haka ina jin k'aunarta domin zamowarta mai bani kariya tun sadda na fuskanci ina da lalurar haka ita ce ta fi kowa fahimtar lamuran da na aikata ƙaddarata ce ba son zuciyata ba, shin me wannan karamcin gareni da me ta dace a wurina?" Shiru Imam ya yi domin bai ɗauka jiran amsarshi Sadauki ke yi ba. Duka Sadauki ya sauke mashi a arm ya kalle shi da sauri yana shafa wurin. "Uhm answer please." "Au wai tambayata kakeyi daman? Ai nazaci duk cikin tsarin salon labarin ne." "Wato ka maidani mai zancen kihayoyi ko? Thank you." Yana ambatar haka ya mik'e ya shige bedroom ya bar Imam da baki buɗe. "Anya Sadauki baida shafan aljannu kuwa?" Imam ya furta cikin tsirawa k'ofar d'akin da Sadauki ya shiga ido. Ba jimawa ya fito cikin sport ware ya d'ora alkyebba saman su ya wuce ta gaban Imam cikin takun k'asaita. "Uhm sarauta ba k'arya ba magajin Gobe." Jiyowa ya yi cikin tsare gida ya motsa lips a hankali ya ce "Mu haɗu a filin motsa jiki inkaga dama." "In kuma ban gani ba fa?" Cije lips Sadauki ya yi kamar zaiyi magana sai kuma ya fice da sauri. "Aliyu rigima, ai sai ka sanar da ni abin da ke damunka tunda A har zuwa Z, ina sane nake nuna ban gane yarenka ba, fatana Maryam ce kakeyiwa wannan k'aunar tabbas dana tayata murnan na dakon k'aunarka da tayi tsawon lokaci." Mik'ewa yayi zuwa dakin barcin Sadauki ya sanja kaya zuwa na motsa jiki kalan da Sadauki ya saka wato white da rashin red, ya sako jallabiya mai hula akai ya fito sai ya sami Sadauki tsaye a bakin k'ofa yana jiranshi dukan wasa ya sauke masa a kafad'a ya dalla masa harara aikam ya kawo hannu kamar zai tsole idon ya yi saurin kauda kai. "Au ashe Sadaukantakar na bogi ne tunda har d'iya mace ta iya raunata hamshak'in basarake kamar Aliyu Baban Mamie Fulani shalelen Mai Martaba Professor Ab... "Malam ya isheka wannan shiriritan in zaka zo muje, kaji damuwata kazo in kuma neman magana zaka tsaya sai ka sami wurin zama ga guzirin paper can a saman bola ka d'auka kayi ta rubutu." "Wato na zama mahaukaci kenan?" "Kusan haka." "Ni dalla muje kada Matana ta nemeni." Wani mugun kallo Saduaki ya wurga masa ya ko kwashe da dariya domin ya rama mai dashi mara aikinyi da ya yi cikin sauk'i. "Inaga zanyi hijira daga Masarauta domin samo mafita da kaina batare da masu mata sun tsomamin baki ba." "Sorry Aliyu muje naji damuwarka da fatan ina da mafita." "Malam na fasa sanar da kai zan nemi mafita da akai ko wurin Muneerah." "Haba Yallab'ai yaushe kafara shawara da k'annenka kuma mata?" "Tun sadda ka zama mai iyali." "Oh ya rabbi affuwan Sadauki kafahimceni ba da wata manufa na ambata maka hakan ba sai dan in rama abin... "Is ok nasani wasace, oya wuce muje Aminin sirri tun yarinta." "Nagode Sarkin Gobe." "Allah ya amince hakan ɗan uwa." "Amin." "Mubi ta baya bana son bi ta babban gate su dameni da kirari." "Ok amma ka sani matsayinka ne ya kai." Bai kula ba uka jera Imam natayi masa magana cikin rad'a shi kuma na gyad'a kai tare da murmusawa, zuwa can Sadauki ya kawo masa naushi ya yi saurin tarewa, jinjina Sadauki ya yi masa cikin sake faɗad'a murmushinsa. "Yes jiya ba yau ba boss, ko ka manta mun halarci makarantar koyon dambe a b'oye da muke Japan?." "Imam ina jin wata rata sai kayi sub'ul da baka ka tona mana asiri a Fada, mu shiga uku da masifar Abba Chiroma." "Kai Allah ya tsare wannan rana na shigarmu karejin haƙoran Abba Chiroma." "To Amin dai." Suka murmusa tare da shigewa garding, batare da b'ata lokaci ba suka yi shirin soma buga wasan basketball. "Za'a ga wanda yafi zira k'wallaye araga, idan har ka wuce ni ko da tazarar ɗaya ce to ka can-canci sauraren damuwata inko na wuceka da good 5 goal to Muneerah ce zataji damuwata, do you agree?" "Yes." "Ok let start." Ya cillawa Imam ball ɗin, ya ko cafe suka soma wasan cike da k'warewa. A cikin mintoci k'alilan Sadauki ya yiwa Imam 5 one. Cikim dariya ya dakata yana cewa "Ina baka tazarar biyar ka tashi daga aminin sirrina Dr Neerah zata maye gurbinka, right?." "No Aliyu mu bar wasan da ba zai fish-shemu ba, taho muje bakin k'orama ka sanar dani damuwarka kuma na yi alk'awarin fitar da kai hanya mai b'ullewa tamkar dai yarda na saba." "A'a taho mu cigaba da wasa ina jin nishad'in buga kwallon." "To ni na gaji sai kayi kai kad'ai ko ka kira Doctor Neerah sabuwar Aminiyarka." "Eh gani a kusa ai zan tayashi tafi kayi hutawarka Yaya Imam." Neerah ta ambata tana mai buge ball d'in a hannun Sadauki ta rungume. Idanu suka zuba mata ta rausayar da kai tare da zare ƙaramin hijab ta cillawa Lailah sannan ta b'alle abayarta, ta bayyana cikin best iyaka cibiya da gajeren wando da ya matseta wanda ya tsaya iya guiwarta, ta ajiye ball ɗin ta tubke gashinta sai reto yakeyi saboda tsayinsa sai ta fito tamkar yar wasan na zahiri. "Oya taho mu soma na baka tazara fiye da wanda ka bawa Yaya Imam." Ta ambata cikin ja da baya ta soma buga ball d'in cike da k'warewa. Kallon Imam ya yi yaga ya tsira mata ido, wani harbawa k'irjinsa ya yi ya zabura yayo kanta a fusace, aikam sai ta zille da ball ɗin kafin ya kamota ta daka tsalle ta cilla sama ya zabura ya buge balla din tare da hannayenta tayi baya zata fad'i ya tarota ya jefa a cikin k'irjinsa ya matseta da k'arfi, ihunta ya fito tare da nashi inda shi ya furta "Bani rigarta Lailah!" Kafin Lailah ta d'auko Imam ya miƙa masa ya fizga tare da rufa mata sannan ya sake ta ya juya baya ya kare ta yana mai bata umurnin ta suturce jikinta. Jikinta a sake ta sanya sannan ta iso gefensa ta tsaya ya kalleta idanu jajur lumshe nata ta yi sannan ta juya ta soma tafiya ya riko hannuta ya matse ta kallo ƙara ya kalleta cikin kaushin murya ya ce "Wannan shi ne karo na farko da zan sake ganin kina bayyana tsiraicinki tunda baki da tunani sokuwa kawai." Ya cillar da hannun ya nufi inda alkyabbarsa ya ke ya saka ya nufi bakin k'orama ya faɗa ciki tunjim!!. Duk suka zabura saboda sautin ya razanasu. "Nima abinda zan sanar da ke kenan dan Allah kada ki sake aikata hakan Neera, ko ba komi ki tuna matsayinki na 'yar Masarauta kuma mai tarin sani ga addini." "Baza ta sake ba Yaya Imam." Lailah ta ambata a hankali. Motsa kai ya yi ya nufi bakin k'oraman cike da tarin tambayoyi game da abinda Sadauki yayi wanda bai taɓa aikata kwatan-kwacinsa ga d'iya mace ba wato rungumarta cikin nuna tsan-tsan kishi. *** "Muje ko?" Girgiza kai ta yi. "To me zaki tsaya yi tunda giyan k'aunar ya kaiki aikata abinda baki taɓa yi ba." "Me na yi Lailah" Neerah ta furta cikin rawar murya mai nuni da tana daf da fashewa da kuka. "Ni taho muje kada ki sake bada kanki har ki shafamin." "Ya gane ina son shi wai?" Tafi Laila ta sanya gami da fashewa da dariya lamarin da ya dawo da Neerah hayyacinta ta dafe goshinta cike da takaicin fallasar karatun ruhinta. "Nagano karatun ruhinki Sister sai dai abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa haka fagen da 'yan hamayya sai kin nemi makaman ya k'i domin Zuhra da Maryam na cikin filin dagan." "Maryam? Wacce Maryam?" "Maryam tamu k'anwar yaya Imam d'iyar Momy da Abba Sarkin Fada." Wani dum taji, jiri ya ziyarceta tayi baya zata fad'i, daidai Hud ya iso wurin sai ya tareta da sauri yana ambatar sunan Allah, lumshe ido tayi tana nanata sunar Maryam aminiyarta itama na son Sadauki domin sam jin Zuhrah na ciki bai d'aga mata hankali ba. Ruwar da taji an fesa mata a fuskan yasa ta buɗe ido tana sakin ajiyar zuciya, tundaga saman sumar kansa ta soma kallonsa har ta dire a fuskanshi wanda ke d'igan ruwa. "Yaya Yarima." Ta furta a saman lips d'inta tana sake lumshe idanu. Harara ya zabga mata tare da fizganta daga hannun Hud ya nuna mata hanyar waje "Maza ku b'ace min dagani tun ban karya ku ba kuma daga yau na haramta muku sake shigowa lambun nan sai da izinina, idan kuma kun isa in sake ganin sillayen ƙafafunku cikinsa." Da sauri Lailah ta ja hannun Neerah suka fice, wacce jikinta yayi mugun sanyi. "Malam ba da haka ake nuna k'auna ba ka natsu mu buga game d'in duk da ba ni kad'ai ke cikin 'yan wasan ba, Ni, kai, Sardauna wata k'ila har da d'an korenka Imam na ciki ko da yake na san kai baza ka haye ba saboda warin kashin kajin dake manne da kai na auri sa... "Ya isheka Hud bama son rashin tunani, dan haka ka kiyaye kalaman da zai sake fitowa a harshenka." "In ank'i fa?" Kafin Imam ya bashi amsa Sadauki ya janyo hannunsa na girgiza masa kai alamun kada ya sake magana, tsaki ja tare da nuna Hud da yatsa alamun gargad'i sannan ya biyo Sadauki na bambamin faɗar bai son hanashi gogewa masu kawo masa raini hadda da keyi. *** "Aikin banza da wofi wallahi sai na zama sarkin Mungaye ko da hakan zai zamo fansa ne ga ruhina." "A she muna da yawa masu fansar da ruhunan namu akan hawa karagar mulkin Masarauta Mungaye." A razane Hud ya kalli inda maganar ya fito ya yi raba da Salis d'an Babban Dogari kuma d'a ga Jakadiyan sirri. "Ai wai cin dank'o har da su Kaza?" "Eh sai dai na wuce Kaza sai Jimina." "To mu zuba shege ka fasa." "Tam zaka sha mamaki kuwa." Saboda takaici Hud bai sake magana ba ya bar wurin, Salis ya rakashi da harara daga bisani ya ɗauki Basketball d'in ya soka bugawa shi kaɗai cike da nishad'i. *** Nagaji Imam! Nagaji na ce! Wallahi zanyi hijira, zan tafi inda ba wanda zai sake jifana da kalman auri saki sannan auren ma na fasa yinsa, ka zamo shidata insha Allah ni da aure har aba... "Kul! Baban Mamie, kada ka sake ka shiga hurimin Ubangiji, auri saki na cikin zanen ƙaddarar ka dan haka kada ka yanke k'auna daga samun rahamar Ubangiji, ka sama ranka zakayi aure kuma zaka rayu da matarka batare da saki ya shiga cakaninku ba." "Banjin hakan zai tabbata gareni ba Imam." "Na ce ka saka a ranka zakayi aure ka yi rayuwa tamkar yarda kowa keyi." "Ta yaya hakan zai faru, alhalin wancan shed'aniyar na bibiyan bad'ini da zahiri na, shi yasa zan koma inda babu mutane na k'arasa rayuwata hankali kwance." "Aliyu ka dawo hankalinka, wai me ke damunka ne?" "Damuwa mai tsanani." "Nasar da ni Please." "Not now Imam domin baka da abin magancemin shi." Yana ambata ya mik'e ya shige dakin barcinsa ya murza key. Cike da tarin damuwa Imam ya fice domin tunda yaga Saudauki ya kulle kansa ya tabbatar ba zai taɓa saurarensa yanzu ba dan haka cikin Masarauta ya nufa, direct turakar Mai Martaba ya nufa yana addu'ar samun nasara a k'udirinsa wanda ke hasko samun yayewar damuwa ne ga Amininsa. 'Tuni na jima da sanin kana tare da aljannu, In banda aljana ta aureka taya zaka riƙa zancen ganinta a zahiri d bad'ini, kai wallahi da sake ba wanda ya isa taɓamin amini ya kwana lafiya ko da kuwa Aljan ne.' Shigowar sak'o a wayarshi yasa ya katse masa zantukan zuccin da keyi ganin daga Sadauki ne sai ya waigo ya kalli volcany ya hangoshi tsaye hannaye rungume a k'irji sai ya maida kallonsa ga sak'on. "Ban amince ka sanar da Abba komi ba domin baza su fahimta ba, ka tafi wurin iyalinka zaifi maka." Kallon inda Sadauki ya ke ya sakeyi har lokacin na nan tsaye sai ya girgiza masa kai tare hawa barandar sashin Mai Martaba, wayarshi ya soma ringing sai ya maidata silent ganin Sadauki ne ke kiranshi, yana zama gaban Mai Martaba ko gaisar da shi baiyi ba sallamam Sadauki ya doki kunninsa waigowa ya yi a razane domin bai isa ya iso da hanzari haka ba duk kuwa saurinsa. 'Anya aljannu ba su maidamin da Amini jinsin su ba?' "Imamundeen ya dai kake kallon k'ofa?" Murza idanunsa ya yi babu Sadauki tamkar yarda ya gansa cikin 'yan sakonni da suka wuce. "Uhm kana lafiya kuwa?" Ya katse masa tunani. Maido kallonsa kan Mai Martaba ya yi kafin ya furta kalma ya jiyo Muryan Sadauki na gaisar da Mai Martaba. "Au ka ce tare kuke shi ne ina magana kana kallon k'ofa tamkar warkewar makanta." "Abba anyi lafiya?" Ya sami kansa da furtawa. "Alhamdulillah Imam." Ya amsa tare da mik'ewa ya nufi d'akin barcinsa ganin su Imam nata mazurai ya ce idan sun shirya magana da shi su sameshi a ciki dan bai shirya kallon shirmensu na fama ba. "Kai Sadauki ban son iskanci wato Ofin naka har kanka amininka zai sauka?" Imam ya ambata cikin fushi. "Tashi muje ko ranka ya b'aci." "Ban zuwa sai na bada labarinka da Aljannu." "Zakuwa ka zama bebe nan bada jimawa ba, tunda baka ji magana." "Aliyu me kake aikatawa a b'oye? tsafi ko me?" "Amsa wannan mara jin magana kawai." Aikam kafin ya ankara wani dum ya shiga kanshi ya tafi luw zai fad'i Sadauki ya tare shi zuwa jikinsa tamkar walk'iya suka suka b'ace daga falon. Tun Mai Martaba na dakon shigowarsu har ya gaji ya tashi ya shiga toilet ya d'auro alwalla ya zauna gabatar da azkar d'in marece cikin rashin damuwa da lamuran shiri-ritansu domin sunar da ya bawa lamarin kenan. *** TSIBIRI. Tsidau ya sauka a wani tsauni mai yalwan bishiyoyi wanda suka taimaka wurin ƙara duhun da tsauni ke da shi, amfani ya yi da haskensu na junnu ya cike tsaunin da haske sannan ya samu hango Tsibirin da ke nema wato fadar Ifritu Baushe wanda ya zamo Bil'adam amma yafi Aljani shed'anci ta ko wani fuska shi yasa ake yi masa lak'abi da sunan mugayen Aljannu wato Ifritu. Tsibirin sai fitar da bak'in hayak'i keyi hakan ya ƙara munana dutsen da ya zamo fadar Baushe, ƙasan dutsen kuwa wuta ne ke ci cikin fitar koren harshe, da ganin wurin zuwarsa sai an shirya baga Bil'adam ko Ajani ba. "Lallai ka ci sunarka Baushe domin ko a itatuwan daji, itacen Baushe ba mai saukin k'onawa ba ne kamar yarda na ke hango shiga fadarka ba mai sauk'i ba ne." Tsidau ya ambata yana nazarto yarda zai shiga fadar domin ganawan sirri da Ifritu Baushe akan uwar gijiyarshi Lina. Bai samo mafita ba ya jiyo ruguji a bayanshi bai waiwayo ba ya buɗe zafin hannunshi domin sanin me ke faruwa, wani dutse ne ke fitar da wuta ya nufoshi irin dai wanda ya so halakashi a fadar Kaka Gunu kwanakin baya. A gigice ya juyo tare da neman hanyan tsira sai dai ya makaro domin dutsen ya cimmasa ya bangajeshi a take ya cillashi ƙasan tsaunin inda ke kai inda farin hayak'i ke fitowa mai kama da tafiyar giragizai a sararin samaniya. Kafin ya sauka ƙasa yaji anyo sama da shi wani iska mai ƙarfi ya nashe idanunsa. Bayan wuce mintinan da basu wuce biyu zuwa uku ba ya ji an saukeshi ya zabura sai ya yi ido biyu da Ifritu Baushe, ya bushe da dariya mai fitar amo tamkar cidan hadari ya jima yanayi kafin ya dakata ya soma yiwa kan sa kirata... "Sai ni Baushe mugun itace, Baushe mai hayak'in masifu, Baushe bai san na gida ba tunda ya zamo ajalin ubanshi mahaifi, Baushe k'i sabo dan ko hadimansa bai d'awa ƙafa ba, ko ank'i ko amso sai nayi mulkin sarkin sakakunar Aljanu da Mutane." Ya dakata yana kallo Tsidau da ya koma tamkar d'an tsako a gaban giwa. Momyn Haske ce 🥰 Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon. Adabi Writer's Association. 12. " Ya kai Tsidau amintaccen bawan Sadauki Gauɗu da Gimbiya Lina ni Baushe k'i sabo na san buk'atarka sai dai ka makaro domin nima hanyar nake nema tsawon shekaru tun kafin a haifi Uban mahaifin Gauɗu domin Zoben na Kakan Uba na ne aminci yasa ya sadaukarwa Kakan Sadauki Gauɗu na huɗu, Ubana, ya yi bakin iyawarshi yaga ya mallako Zoben ya dawo a halinmu saboda shi ne yafi k'ulafucin mallakan Zoben tun sadda ya sami labari a wurin aminin mahaifinsa amma ya kasa hasalima ya kasa tun k'arar inda Zoben yake ajiye, da wannan baƙin cikin ya rayuwa to bayan na girma na fahimci burin Ubana sai dai bincikena ya tabbatarmin sai na kashe shi na sha jininsa sannan zan soma taka k'amshin mallakan sihirtaccen Zoben sai na aikata hakan a wani dare da muka fita na koyar da ni sanin alk'alaman tsafi sai nayi amfani da dmar na halakashi na shanye jininsa tare da nad'e duk alk'aliman tsafinsa. Dama ni kad'ai na rayuwa cikin 'ya'yansa, Uwata ta mutu bisa cin amanarta da yayi inda ya sadaukar da ita duk bisa neman hanyar Mallakan Zoben. Daga nan ban koma gida ba na nausa cikin daji na yi ta neman ilmomin sihiri kuma duk wanda na k'aru da shi to nine a jalinsa a haka na haɗu da gawurtaccen matsafi wanda ya haskamin amfanin da Zoben sihirin zaiyimin kana ya riƙe ni tsawon shekaru har zuwa sadda aka haifi uban Sadauki Gauɗu daga nan ya mallakin duk kan tsafinsa tare da hadimansa dangin hatsabiban aljannu da mutane wanda suka maidani Ifritu na zamo k'wan jimina gagara ɗaukan Shaho, na gagari har da su kansu hatsabiban shed'anun alhjannu da mutane na zamo tamkar ba zan mutu ba domin bana jin zan bar Duniya sai an hura k'aho tamkar yarda aka halicci aljanu haka nake jin kaina domin naga zamanai na matsafa daban-daban, ni kuma an kasa ganin nawa " Ya bushe da dariya wacce bishiyoyi suka soma rangaji suna busar da iska mai ƙarfi. 'Hak'ik'a Baushe yafi ƙarfin hilata dole na samo mafita domin tsira da rayuwata kada na ƙare a yi masa bauta.' "Tabbas Tsidau daga yau kazama hadimina, dole kayimin bauta tamkar yarda wanda suka fika komi suke k'asan ikona in kuma ba haka ba dole ka amince da sharad'ina akan shugabanka Gimbiya Lina." "Sanarmin inji me ye sharad'in? Dan ba a yoni domin bautawa azzalimi irinka ba." Wani dariya ya sake bushewa da shi domin abu mafi yi masa daɗi shi ne a ambata masa kalman zalinci. 'Duk da nayi biyayya ga zantukanki Gimbiya da ban kasance a wannan wuri mai cike da hatsari ba.' "Ka natsu Tsidau domin zantukan zuccinka ba zai amfaneka da komi ba." "Ina sauraren sharad'in naka." "Idan na ambata dole sai ka amince da shi, kai ko ban ambata ba amincewarka wajibi ne." "Ina sauraronka ya Sarkin Sarakunar Aljannu da Matsafa." Ya ambata cikin ladabi. "Hilarka ba zaiyi tasiri a wannan Fadar ba ya kai Tsidau garama ka ajiye kalaman yaudararka wata k'ila gaba za suyima amfani." "Sanar dani buk'atarka ya Ifritu Baushe." Wannan karan cikin rashin tsoro ya ambata. "Da kyau Sadauki Tsidau, to maza buɗe masu jinka ka saurari bayanina wato kawomin Lina fadana tare da Zoben sihirin dake tare da ita, a daidai lokacin da ta sanya ya zamo nine mutum na farko da zanyi ido biyu da ita bayan kai." "Ko zan san dalilinka na neman hakan?" "Cikar ikona ba zai samu ba sai Gimbiya Lina ta zamo ɗaya daga cikin Matana ta haifamin yarinya mai kama da ita na sha jininsa to daga ranar burina zai zamo tabbatacce ita kuma zan kasheta da hannuna bayan na sha jinin 'yarta a gaban idonta." "Ba zan yarda a kashemin uwar d'aki a irin wannan kisan wukak'ancin ba domin nayiwa Jarumi Gauɗu alk'awarin kula da ita har ƙarshen rayuwata, dalilin da yasa kenan na zo Fadarka samun wani ilimi da zai bani damar hanata saka Zoben sihiri saboda sakashi mutuwarta ne ya kusanto." "Tabbas ni ne ajalinta kuma wannan bayanin shi ne ya buɗe maka kake hango mutuwarta sannan tunda ka saurari manufata cikamin aiki dole ne ko in ɗauko iyalanta na halakasu a gaban idonka, in na ce iyalanka ina nufi kaf zuri'arka zan tiso k'yeyarsu." 'Tirk'ashi na kawo kaina gidan jafa'i da masifa." "Ko baka kawo kanka ba za'a kawomin kai domin na soma gadinka tun sadda Sadauki Gauɗu suka soma faɗa da Ubanshi akan Zoben." "Ko zan san abinda yasa tun a lokacin baka nemo Gimbiya Lina ba?" "Bata da abin so ne sai sadda Sadauki Gauɗu ya sadaukar mata da tsafinsa to a lokacin ta shigo cikin k'omata dama ina jiran zuwar ranar domin tun kafin a haifeta nake da tabbacin a hannunta zan sami cikar burinsa." "Shugabata ba zata zo fadarka ba domin nasha jin tana ambatar tsanar azzalimi, tana adawa da mulki irin naka hatta kuwa da irin mulkin Babanta, tabbaas tana da burin kawo ƙarshen irinku a doron ƙasa dan haka ban san ta yarda zan faɗa mata ta zo gareka ba." "Dole ka zamo maci amana idan zaka yimin aiki dan bana harka da masu gaskiya gami da tausayi ko Lina domin zan amfana da ita ne amma da yaƙi ne zai rabani da ita duk da ina hango wani al'amari na tun ƙarota wanda ya b'oyu gareni dan haka zan barka ka huta ga abin more rayuwa nan sai wanda kaga damar amfani da shi zan dawo gareka bayan kwanaki biyu sannan a lokacin zaka tafi kazomin da Gimbiya Lina ko ta wani hali sai ka wanzu cikin nemo mafita ina sake sanar da kai cin amana shi ne matakin tsirarka daga hannuna." Daga haka ya b'ace Tsidau ya fad'a kogin tunani daga haka wani barci ya sureshi wanda rabonsa da yin barci har ya manta domin baya cikin jinsin aljannu masu barci. *** Lima ta fito daga gidan shak'atawa bayan ta halaka samarin da suka d'ebe mata kewa ta kuma b'atar da su tare mantar da jama'ar mashaya lamarin wanda ta saba aikata hakan duk wanda ya kusanceta to bai kai labari sannan ba wanda zai sake neman d'ansa wannan sa'ar ta sameshi ne daga Kaka Gunu domin duk wanda ta b'atar yana zamowa arzikin Masarautar ne inda kuɗi zai ƙara taruwa a baitul mali sannan mafi ƙarancin mutanen da ta ke halakawa a duk sadda ta ziyarci mashaya to mutum biyu zuwa uku ne saboda zamowarta mai ƙarfi sha'awa, wannan hali nata na ciwa Gaimbiya Lina tuwo a k'warya har da shi ya zabura da ita ta fita nemo ilimin tsafi domin kawo ƙarshen k'adarin 'yar uwan nata. Cikin Izza Lima ta cigaba da tafiya tana fatahi da duk wanda taci karo da shi a hanya, kafin ta isa gida ta raunata jama'a masu yawa ciki harda tsoffi, shi yasa ba wanda ke son yin karo da ita, ƙaunarsu naga Gimbiya Lina. Muhallin Mahaifiyarsu ta nufa tana ƙara haɗe rai. Ta sami Mah zaune gaban bangon ɗakin tana hira da Gimbiya Lina wacce ke kwance saman ruwan Tekun Kabobo, jikinta babu kayan kirki, fatarta sai ɗaukan ido keyi mai nuni da hutu ya gama ratsata. Mah na ganin Lima ta shigo ta kirawota da hannu ta iso gabanta tana gabgowa Lina harara yayin da ita ke murmushi cike da nishad'i. "Lina ga Lima ku sasanta bana son rabuwar kanku kunji 'yan biyuna, farin cikina?" "Ni kam Mah ina sonta ita ce bata sona." Lina ta ambata a hankali. "Eh bazan taɓa sonki ba, munafuka kawai, mai fuska biyu." "Kin jita ko Mah?" "Kiyi hak'uri Lina, 'yar uwanki mai zafi ce komi zai wuce zanyi magana da ita domin yaɗuwar kanku nake buƙata sama da komi yanzu." "To Mah ni na wuce zan tafi ceton rai a wani kogi, ga jirjin ruwa can na shirin faɗi da mutane ciki." "Nasara na tare da ke ya ke 'yata." "Godiya nake Uwa abin farin 'ya'yanta. Daga haka ta b'ace daga jikin bangon Mah ta fuskanci Lima cikin tsuke fusaka ta ce "Daga yau ban son nasake jin kin ambaci tsana ga 'yar uwanki idan kuma kika sake zan nunamiki wacece ni sannan bana son zuwa mashaya da kikeyi shi ke janyo miki tsana ga Jama'ar Tsibiri domin hatta da mahaifinku baya son abinda kike aikatawa, kiyo koyi da 'yar uwanki zaifi miki khairan ko kya samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri wanda ya ke babban burinki." Sai a nan ta saki rai jin ta ambaci hawa mulkin Tsibiri ta dawo gaban Mah ta zauna tana wani langab'ewa kana ta ce "In har kina sona da mulkin Tsibiri to kije d'akin Abun ki tsareshi kada ya biyoni domin mallakan gadona na wurin Kaka Gunu." "Kunfi kusa Lima ki rok'eshi ya bar maki kayanki." "Ba zai bari ba Mah domin shima na burin mallakan Ruwan Albarkan." "To ki gyara mu'amalanki da Lina na san zata taimakeki ki mallaka." "Idan itama burinta na ta mallaki Ruwan ne fa?" "Zata bar miki domin adala ce kinfi kowa sanin hakan." "To zan nemeta mu sasanta." "Haka na ke son ji 'yata." Juya kai gefe Lima ta yi tana haskowa ruhinta wani mugun nufi akan Lina sai ta saki murmushi tare da hayewa gadon Mah ta kulle ido ganin haka yasa Mah ta fice zuwa turakar mijinta wannan damar Lima ta samu ta mik'e ta shafi bangon da Mah ke hira da Lina sai kuwa ga Lina ta bayyana saman dutsen kogin Babobo iska na kad'a gashinta na rufe mata fuska tana yayewa. "Ya akayi Lima? Na san zaki nemeni shi yasa na tura Tsidau ya taimaki mutanen girjin na dakata jiranki, ina saurarenki." "Ki zo ki taimakeni na ɗauko gadona a Bukkan Kaka Gunu." "Zan zo amma ba yanzu ba sai Abun ya taho nemana dan haka ki nuna mashi kin hak'ura da gadon hakan zai bashi damar barin Tsibiri a sirrance domin yanzu yafi buƙatar mallakan Zoben dake gareni akan ruwan albarkan." "To sai kinzo ina da abinyi." Murmushi Lina ta yi tare da mik'ewa ta kalli Lima ta ce "Zan zo mu kwana tare yau sannan zan baki labarin da kike nema na cikin jikina da wanda yayimin." Cike da zumud'i Lima ta buɗe baki zatayi magana Lina ta d'aga mata hannu tare da b'acewa a take bangon ya dawo yarda ya ke. Dafe kanta ta yi cike da takaicin b'acewar Lina. Ta fito zuwa d'akinsu dake saman wani dutse daga gefen turakar Mahaifinsu. *** Mah na shiga turkan mijinta ta fahimci yana d'akin sirri sai ta sami wuri ta zauna ta tsirawa wani taswira ido wanda sai a yau ta ganshi a turakan sai ta shiga mamakin lamarin abinda ya ɗauki hankalinta har ta shagala da kallonsa sai ta soma ganin tamkar ta koma wani wurin ba turakan take ciki ba, mik'ewa tayi dan isa gaban Taswiran sai taga haske na fitowa daga cikinsa da ta matsa sosai sai taga hanyace ta buɗe daga cikin Taswiran sai taja da baya cike da tsoro amma sai taji ana janyota sai ta soma tattaro tsafintata dan amfani da shi sai dai ya kasa tsiri wurin bata kariya, ihu ta soma dan neman taimako amma sai muryanta ya daina fita illa ita ɗaya takejin fitar kayanta, tsawon lokaci ana son jefata cikin Taswira ita kuma tak'i shiga duk da tsafinta ya k'i aiki sai dai tun can ita ɗin mai ƙarfi dantsen ne. Mah ta jigata iya jigata har ta sare, ƙafarta na hagu ya soma shiga hanyar inda takejin hucin zafin wuta na dokar ƙafar. Sauka wani abu taji dif!! Kafin ta tantance meye iskan guguwa ya nad'eta ya jangota. A take Taswiran ya nad'e kansa ya b'ace b'at, bangon ya koma tamkar wani abu bai taɓa zama ba. " 'Yata Lina." "Na'am Mah, kwanta ki huta nadawo Tsibiri bazan sake barinki ba ko da hakan na nufin ajalina ne." "Me ke faruwa Lina?" "Mah cin amana yayi yawa, zalunci ya kewaye duniya ya zamo har da na jikinka za'a cuceka." "Waye ya so aikatamin mugun abun nan?" "Mah saninsa tarin damuwa ce gareki amma da sannu zaki san ko waye ke farautan rayuwarki domin ya sami cikan burinsa na samun Duniya." "Lina taho na runguneki." Ba musu ta iso gaban mahaifiyar nata suka rungume juna, hawaye na zubowa daga ida uwarsu na sauka a gadon bayan junarsu. "Zan sanja miki wurin zama mai cike da tsaro Mah." "A'a Lina ki barni a nan mahaifinku garkuwa ne gareni." "Idan shi ne ke son halakaki fa?" "Ba zai taɓa faruwa ba Lina, duk tarin zalunci mahaifinku ba zai taɓa sadaukar da abinda yafi so sama da komi ba dan haka ki barni tare da shi tunda kin dawo ba abinda zai sameni." Janye jikinsa Lina ta yi batare da ta sake furta kalma ba, ta soma zagaye d'akin zuwa can ta tsaya ta dubi Mah ta ce "Ina da aiyuka a gabana wanda ban san adadinsu ba kuma ban san mai taimakamin ba haka ban san ranar kammalasu ba." "Ki sassautama kanki lamaura ya ke 'yata kada na rasaki." "Mah banzo duniya dan samun hutu ba, ina cikin matsala tunda nace zan saka Zoben can mai makon naga lamura nayimin sauk'i sai sake rikicewa sukeyi shi yasa nake neman amincewarki da ki yarda na nesantaki da Tsibiri na wani lokaci in komi ya daidaita sai na dawo da ke saboda zamanki anan barazana ne a gareni domin za'a taɓamin ke dan a sami galaba a kaina, Mah ki amince na maidake saman Tekun Kabobo na killaceki ko kogon da gangan jikin Sadauki Gauɗu ke ciki nayi miki alk'awarin zuwa ganinki kullum dan ɗebe miki kewa haka komi kike so na dangin abinci da bin sha zaki samesu." "Lina kincemin fa kin dawo Tsibiri to me yasa zaki ɗaukeni a cikinsa ke ki zauna." "Na sanar miki da hakan ne dan hankalinki ya kwanta amma ban dawo ba." "Lina ba inda zanje." Tamkar zata fashe da kuka take duban Mah sai kuma ta zabura ta nufi k'ofar fita tana cewa "Mah zan dawo anjima kada ki sanar da kowa zantukanmu ko da kuwa Abun ne ko Lima." Kafin Mah ta yi magana ta fice a gaggauce, hawaye ne suka zubowa Mah na tausayin rayuwar da 'yarta ke ciki domin tana burin rayuwa da 'yarta a kusa da ita tamkar yarda takeyi da Lima. "Lina dole ki janye son hawa karagar mulkin nan ko na samu kusanci da ke kamar can baya." Mah ta ambata cike da tarin damuwa. "Mah." Da sauri ta waigo Lima ce tsaye. "Kin haɗu da 'yar uwanki Lima?" "A'a, shin ta zo ne?" "Eh." "Me ta sanar da ke?" Batare da tuno gargadin Lina ba ta sanar da Lima duk abinda ya faru tundaga zuwarta turakan Abun har tafiyar Lina. "Ina zuwa." Itama ta fice da sauri tana fita ta yi girgiza sai ga Abun ya bayyana fuska a murtuke. "Hak'ik'a Lina kina da wayau dole na san waye Sadauki Gauɗu kafin na mallaki Zoben sirihin hannunki ta wannan hanyar na basaja tabbas yanzu zanyi fito na fito da ke duk da ba hakan raina ya so ba." Ya ambata cike da ɓacin rai. Ba jimawa Buda ya isa saman ingarman dokinsa Abun ya hau ya zabura cikin takon dake motsa ƙasa zuwa can ya d'aga sama tamkar tsuntsu ya b'ace cikin gajimare. Lima da duk abinda da ya afku akan idonta ta shiga mamakin lamarin sai kuma ta saki murmushi tare da shigewa d'akin Mah ta isa gaban bangon da Mah ke hira da Lina ta shafa take kuwa Lina ta bayyana cikin shigar yak'i fuskanta babu d'igon annuri lamarin da ya razana Lima domin bata taɓa ganinta cikin ɓacin rai irin wannan ba tun tasowarsu. "Me ke faruwa 'yar uwa?" Lima ta jefo mata tambayar a rikice. "Ya wuce ɗaukan tunaninki Lima, ni dai ina son ki kulamin da Mah, kada sakacinki na yawon zuwa mashaya ya janyo na rasa Mah, domin in hakan ya faru na rantse da ruhin Sadauki Gauɗu sai na illata rayuwarki ki zamo baki da mamora balle ki sami damar zuwa timb'ele a mashaya." "Kada kiyimin barazanar da har abada nafi ƙarfin sa kawai ki sanar dani abinda ke faruwa ko ina da halin taimakawa akai." "Ki kula da Mah shi ne kaɗai taimakon da zaki iyayi." "Kin san shirin Abun kenan?" "Eh wanda hakan na nuni da rayuwarsa na daf da zuwa ƙarshe." "Me kike nufi?" "Zan tafi idan na dawo zan sanar da ke komi batare da kin tambayeni ba." Sai kin dawo amma ki sani ba zan zauna gadin Mah ba tunda ba dan shi na zo duniya ba." "Shi kenan na barki lafiya amma ki kwana da sanin rasa Mah tamkar nak'asarki ce, wata ƙila makanta, kurumta ko gurgwanta sai kiyi nazarin abinda zai fish-sheki domin tabbas sakacinki yasa na rasa farin cikina wallahi kema kinyi ban kwana da naki farin cikin. Ki kula da Mah shi ne ƙarshen umurnina gareki Lima." Kafin Lima ta yi magana bangon ya dawo yarda yake tamkar komi bai wanzu ba a mugun fusace ta fice batare da ta kula kiran da Mah ke yi mata na kula da ita ba dan ta shiga rud'anin kalaman Lina har tayi da ta sanin k'in binta da tayi. Bukkan Kaka Gunu Lima ta nufa ta shige batare da samun tangarda ba. "Zannuna miki ni ce shugabanki Lina kuma magajiyar karagar Tsibiri, a yanzu banjin ko Abun zaifini ƙarfin iko balle ke 'yar tsako abar tausayi." Ta na rufe baki dutsen dake Bukkan ya dare biyu wata gawurtacce mikiya ta bayya ta iso gabanta ta zube tare da rikida zuwa mutum maiji da Sadaukantaka ya russuna cikin cewa "Barka da zuwa magajiyar Tsibiri shalelen mai gida Gunu, raina fansa ne gareki ya ke uwar gijiyata." "Waye kai?" Ta ambata cike da izza duk da tana kokwanto ko Tsidau ne ya sanja salon yaudara. "Ki kwnatar da hankalinki ba mayaudari Tsidau ba ne a gabanki wannan amintaccen Hadimi ne sunana Mutuwa babban hadimin Kaka Gu... Ai kafin ya k'arasa zancensa Lima ta fice Bukkan a guje lamarin da ya janyo Mutuwa ya bushe da dariya a take Bukkan ya soma motsi tuno illar da dariyarsa zai iya haifarwa ga Tsibirin sai yayi gaggawan tsuke bakinsa amma duk da haka saida wata dunk'ulalliyar Guguwa ta fice ta rufawa Lima baya ya so bin guguwan ya dawo da ita amma ya kasa saboda aikinsa iyaka kula da cikin Bukkan ne da kuma tulun ruwan albarka. *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* Momyn Haske ne 🥰 [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI By Mrsjmoon Adabi Writer's Association. 13 Guguwar ta wuce Lima ta nausa cikin Tsibirin inda ta soma b'arna domin duk wanda taci karo da shi nad'eshi takeyi ta yi yaga-yaga da namansa ta watsar. Kafin 'yan mintoci tayi mugun b'arna musanman ga tsoffi da ƙarfinsu ya ƙare. Kuru-ruwan da ke tashi ya cika ko ina a Tsibirin yasa Mah fitowa domin ganin abinda ke faruwa saidai bisa tsau-tsayi Guguwan ta yi karo da ita wacce ta juyo domin komawa inda ta fito bisa arangamar da tayi da matsafan Tsibiri suka haɗu suka dakushe tasirinta shi ne ta juyo a fusace sai Mah ta faɗa komarta. Cikin kiftawar ido tayi awon gaba da Mah, ganin haka ya sanya Lima kwalla ƙara da ya haddasa zubowar ganyan-yaki daga jikin bishiyoyi, a take suma suka rikid'e zuwa guguwa mai karfi wanda ya doke wacce tayi barna, suka watsu cikin al'umma suka soma illata ganinsu. *** MUNGAYE. "Sadauki banda Ofi da ka gada zamowarka Gambon 'yan biyu har da tsafi kake haɗawa?" "Imam tafi wurin iyalinka am not in good mood gobe zamuyi magana." "Kasan Allah ban wucewa sai ka amsamin tambayata." "Nacinka yayi yawa Imam." "Naji kome zaka kirani, ina dai jiran amsarka." Tsaki Sadauki ya ja tare da dukan goshin Imam da ƙarfi aikam ya sunkuya ƙasa da sauri dafe da wurin yana sakin ihu mara sauti. "Ragon maza kawai kana ambatar Brother Sardauna da rago a she kaima layin kake." "Sadauki tafi kawai nafasa jin amsar." Yana ambatar haka ya nufi Part dinsa da sauri har da haɗawa da gudu, dariya mara sauti Sadauki ya raka bayarsa da shi yana mai furta "Bana tsafi aminina amma ina iya yin wasu ababe tamkar mai sihiri duk a sanadin zamowana Gombon 'yan biyu kamar yarda ka ambata sannan tare da taimakon Aljanar can mara mutunci." Yana ambatar haka ya tsare giran sama da ƙasa ya doshi part d'insa rai b'ace tamkar bashi ne ke nishad'i yanzu ba. *** "Neerah idan muka tafi gidan Dadah kafin mu dawo dare yayi kinga Mami b'ata son tukin dare ga su yaya balle garemu mata, haka Abba zai hukuntamu domin kinfi kowa sanin dokarsa a kan 'yan matan Masarauta." "Kaini gate din gidan ki juyo kawai Sister." "Kina son janyowa kanki magana ko Doctor?" "Gidan Dadah zan kwana ba wani wurin da banba Malama." "Umurnin Abba ne dole kowa ya kwana gida in har ba gari mutum ya bari ba ko aiki irin naki ya riƙe mutum." "Idan an tambayeki kice ina asibiti ina da tiyatan dare." "Ba zanyi ƙarya ba." "Shi kenan bani motar ki tari napep ki koma." "Wannan isar ne kuma bakiyi ba sai dai ke ki hau Napep ɗin." "Lailah ke ɗin ciwon kai ce wallahi, dan Allah ki barni na huta badan na isa ba." "Bakiga hutu ba tunda kika bari ƙaunar abinda zai iya tarwatsa rayuwarki yayi miki kamun kazar muku." "Kina cikin yan adawa kenan." "No, but ina takaicin lamarin." "Why?" Sai da ta fesar da iskan bakinta sannan ta amsa "Yaya Sadauki nawa ne zanfi kowa murna da aurenku amma ɓacin ran da zai biyo baya shi ne bana son ji da ganinsa dan haka ki hak'ura da yaya ki kama na gaske mai yi miki ƙauna mara algus." Lafewa Neerah tayi a seat tamkar mai barci, batare da Lailah ta kula da hakan ba ta cigaba da cewa "Mami zata shiga damuwa sannan Abba zaiyi fushi da yaya in har ya aureki ya saki kamar yarda yayiwa su Mubina kuma mu... "Ina sonshi a hakan, in yaso ranar da aka daura mana aure ya sakeni, ni kuma zan nuna masa zama da shi yanzu na soma aurenmu mutu ka raba takalmin kaza." Ta katse Lailah cikin ɓacin rai. "Neerah ki dawo hankalinki kada so ya rufe miki ido ki kasa gano aibun lamarin, wallahi nafi ki son aurenku amma su... "Da kata da motar Malama!" Gefen hanya Lailah ta gangara ta tsaya, Neerah ta nemi ficewa ta yi saurin kulle motar baki ɗaya. "Buɗe ni ko ranki yafi nawa ɓaci." "Ina dakon duka tunda daga faɗar gaskiya sai ya zamo aibu." "Lailah rayuwarki ko nawa?" "Yours." "To ki zuba ido zaifi miki." "Ank'i zuba idon wallahi ko kina so ki ba kya so sai na sanar da ke illar zawarci dan haka bazaki auri yaya Sadauki ba ga yaya Najib nan ya mutu a da ƙaunarki dan haka shi ne zaɓinmu domin munga abinda zai iya ba dan mutuwa tayi masa yankan ƙauna ba da yanzu suna da albarkan aure." "To Ammi sai ki ɗaukeni ki kaini dakinsa da wannan zantukan banzan kuma ki fita harkata tun raina bai ɓaci ba." "Macizai ne turosu muga wanda zai afka ɓacin rai ni da ke domin kinfi kowa sani a fannin tankasar muke." Shiru Neerah tayi tana sauke murmushin yak'e. 'Kai wallahi Lailah fitina ce bata tsoron a mutu.' "Yes bana tsoron a mutu domin mai tsoron a mutu shege ne." Idanu waje Neerah ke kallonta jin ta bata amsar zancen da tayi a zuci. Harara ta zabga mata tare da tada motar da juya zuwa Masarauta, Neerah na kallonta bata tanka mata ba saboda duk tarin rigimanta Lailah ta damata ta shanye. Suna isowa bakin gate Sadauki na fitowa zuwa masjid, tsayawa Lailah tayi tana hararan Neerah dake doka murmushi. "Daga ina Sisters?" Ya ambata idanunsa na kan Neerah ba yabo ba fallasa. "Hanyar gidan Dadah wannan yar rainin hankalin ta juyo bisa dalili mara tushe." Neerah ta amsa a shagwabe. Hancinta ya ja cikin sake d'aure fuska, ta saki ƙara ya janye hannunsa yana zabgawa Lailah harara ganin ta yi kamar bata a motar. "Sorry Yaya bana jin daɗi ne." Ta ambata da sauri. "Saboda kina cikin 'yan adawa ba, kin san Allah kada inji kada in gani idan kuma kince wasa ni da ke ne mara kishin d'an uwanta kawai." Idanu waje suke kallonshi ya ja siririn tsaki ya wuce da kallo suka raka shi har ya haye stairs na masallacin. A tare suka sauke ajiyar zuciya gami da tsirawa juna ido. "Doctor ke ce kika bashi labari ko?" "Tunda gani aljana ba." "Be serious dear Neerah me yasa zakiyimin haka?" Tsaki ta ja tare da bude kofar ta fice da sauri Lailah ta kunna motar ta zo ta wuceta zuwa ma'adanar motoci ta ajiye ta fito ta cimma Neerah dake daf da shiga falon Momy, hannunta ta fizgo suka kafe juna da ido. "Sakeni to Uwata." "Neerah me yasa kika bashi labari?" "Kin san wallahi zan shuka miki rashin mutunci in kika ƙara zargina da gulma alhalin tare muke ko kira ban amsa ba balle tura sako." "To ya akayi ya gane ina adawa da ƙaunarku?" "Ki tambaye shi zaifi da wannan ihu cikin dokar dajin da ba bil'adam balle dabbobi, sannan bai san ina sonshi ba." "Haka ne kuma fa amma anya yaya baida aljannu?" "Layinku ɗaya tunda kema kina jiyo zancen zucci." Hannunta ta matse ta ko kwalla ƙara bashiri ta saketa tana dariya tare da cewa "Ke dallah d'azun zancen zuccinki ne ya fito fili batare da kin sani ba." "Kanki akeji dai, ni kinga tafiyata inyi dinner da Momy ." "Uhm da kuma kishiyarki ba, 'yan wahala kawai." A fusace Neerah tayo kanta ta kwasa da gudu zuwa Part din Ammi tana kyal-kyala dariya. Fasa shiga part din Momy ta yi sai ta sami kanta da nufar Part din Imam kirjinta na harbawa da sauri da sauri. Da Imam taci karo ya fito a gaggauce zai tafi masallaci, koda ta gaisheshi a hanzarce ya amsa ya wuce bayansa tabi da kallo tana son aminta da karatun da ruhinta ke biya mata na fallasa sirrin ruhinta gareshi ko tasamu ya yi mata jagora wurin mallakan Sadauki cikin sauk'i. 'Ki kame kanki Muneerah, namiji baida tabbas.' "No, daina sanarmin da wannan zancen domin Yaya Yarima mai tabbaci ne." Ta bawa zuciyarta amsa tare da turo k'ofar falon, Hafsat ta samu na shirya Mimi ganinta yasa ta tsaya tsak ta zuba mata ido cike da mamakin ganinta a sashinta domin shigowar Neerah na biyu kenan tun aurensu, na farko barkan Mimi tazo sai kuwa yau. "Aunty Hafsat ya da kallo kamar na sanja miki?" "Borin kunya ko Dr. Neerah?" "No Aunty nidai bana son kallo ne sai duk naji na muzanta." "Uhm to sannu da zuwa mai zumuntar ganin dama domin ba zance ni kaɗai kike yiwa haka ba dan har da su Aunty Hassana saboda nasha jin korafinsu akan rashin zumuncinki." "Ayimin affuwa daga yau zan gyara shi yasa na soma da ke wacce ke kusa da Masarauta." "To Allah ya nufa hakan." "Amin." Ta ɗauki Mimi da ke ta mik'o hannu saboda bata da k'yuya. Cillata sama tayi tako kyal-kyale da dariya sai lamarin ya taimaka wurin sanya Neerah nishad'i ta biye mata sukayi ta wasa, sosai ta yabawa Hafsat wurin tsafta ganin yarda gidanta ke ta k'amshin tare adana komi a muhallin da ya dace ga diyarta mai kyau cikin kamhi mai daɗin shak'a. "Kawota kije ki ci abinci gashi can na shirya miki." "Sallah zanyi Aunty." "Ok shiga bedroom kiyo alwallah, ga k'ibla can." Motsa kai tayi tana mai bin inda ta nuna mata da kallo. Bayan ta idar da sallah saita dawo cikin falon ta zauna saman Cushing ta lafe tare da lumshe idanu tamkar mai barci. "Kina tare da damuwa ko Doctor?" Zubawa Hafsat manyan idanunta tayi fuska kwab'e, mai nuni da k'iris take jira ta fashe da kuka. "Don't cry Sister, oya sanar dani damuwarki, it may be I have the solution." "Aunty laifi ne idan ruhi ya samu abincinsa a lokacin da ya ke cike da yunwa?" "Ba laifi ba ne Doctor domin samun cikar buri kenan." "To me ya kamata a faɗa masa lokacin da yake burin cika tumbinsa da wannan abincin?" "Abu biyu a lokaci ɗaya su ne Ci a hankali domin kada ayi karo da tsakuwa wanda zai saka abincin ya fita a ruhin ko kafin a Ci ɗin a tabbatar da an duba babu wannan tsakuwa da zai iya kawo cikas yayin kaishi ma'adanarsa." "Karin bayani Aunty domin na kasa gano inda kika dosa." "Manufata shi ne idan ruhi ya samu abincinsa to kada ya sake ya bawa abincin damar shiga ma'adanarsa har sai ya tantance, wata kila zai iya illata shi dan haka ya san me ye nagartan abincin tare da manufar cinsa gami da amfanin da zai samu idan ya ci domin gamsuwar ruhin shi ne dace da abinci mai kyau da ɗanɗano da zai taimaka wurin tafiyar da lafiyar ruhin tare da gangar jiki harma jama'a suyi alfahari da samuwarshi gareka ta hanyar yiwa ruhin fatan dauwama tare da wannan abincin na har abada." Shiru Neerah tayi tana nazarin zantukan kafin ta dawo tunanin ta tsinkayi muryan Hafsat na ambatar "Allah yasa k'anwata ba soyayya ta faɗa a makance ba?" Maimakon amsawa sai ta mike tana gyara zaman hijab d'inta tare da jan hancin Mimi wacce ke lumshe ido tana son yin barci ta furta "Good night takwarar Mamina." "Me kenan?" "Zan wuce ai nayi miki hira insha Allah zan riƙa shigowa ko da a ƙarshen sati ne ina wasa da diyata mai kama da Yaya Imam sak dan tafiki kyau da iya ado." Yar dariya Hafsat tayi kana ta ja hannun Neerah zuwa dining tana cewa "Sai kinci abinci zaki tafi." Kan dole ta zuba ferfesun kayan ciki ɗan dai-dai ta soma ci a hankali nata nazarin zantukan Hafsa mai cike da fikrah. 'Lallai yaya Imam yayi dace da mata mai hangen nesa.' "Hey Dr. Maida hankali ki daina karatun wasikar jaki wanda ba mai ganin ya rubutun ya ke sai ruhi kaɗai." Murmusawa tayi tana mai sosa tsinin hancinta tare da gyaɗa kai. Taji daɗin ferfesun duk da baya cikin abinci ta, ta kora da Apple juice zamowarta mara son drinks masu gas, sannan tayi mata sallama ta rakota har bakin fita Part ɗinta tana ta son jin gwaninta amma fir Neerah tak'i bata haske sai zillewa zancen takeyi. "Ai zanga Lailah ko Maryam nasan su zasu sanar da ni komi idan ke kin k'i buɗemin nayi fatan khairan tunda kun sami yancin zaban abokanan rayuwarku da kanku ba irinmu ba da ko ka zaba b'atawa kai lokaci kayi." "Uhm nikam Aunty ban tashi yin aure ba yanzu dan haka bana da gwani." "Samun wuri wato kunga an barku kun balaga kun balallage shi ne har da samun bakin salo? Mu yaushe muka samu gatan nan, lallai Masarauta ta sami canji." "Kai Aunty kuma fa saida kuka gama jami'a sanan kukayi aure dama dai su Aunty Hassana kika ce su da secondary ma d'akinsu suka kammala." "Eh da wannan kam amma dai kun fi... "Good night Aunty yar jarida." Ta katse Hafsat domin samun damar kufcewa zantukanta da ta lura basa da ranar k'arewa, dukan wasa ta sauke mata a baya ta saki ƙara cike da shagwaba'a zata sake kai mata duka tayi saurin ficewa da dan gudu tanajiyo dariyarta itama dariyar takeyi saboda ta sami nishad'i shigarta sashin. Tafiya ta cigaba dayi a hankali tana kallon taurari da suka k'awata sararin samaniya lamarin da yasa bata ganin abinda ke gabanta domin kanta a amsa take tafiyar hasken taurarin na sake haska ruhinta tana hasko kanta tare da Sadauki suna nishad'i cike da tarin ƙauna. Karo da juna sukayi wanda sam bai lura da ita ba yayin da itama bata san da zuwarshi ba. A tare suka sunkuya ita cike da tsoro shi kuma tunaninsa yaji mata raunine domin kafadarsa ne ya doki kirjinta, gano bataji ciwo ba yasa ya tsare gira yana kallon cikin idonta ya furta "Sannu amm me yasa bakya lura da abinda ke gabanki?" "Haka ake bada hak'uri tare da tuhuma?" Itama ta furta fuska a haɗe. Kunninta ya ja ta saki ƙara ya saketa da sauri tare da mik'ewa ya nufi hanyar Part din Mami Fulani yana cewa "Kingama rainani amma da Ammi zan haɗaki kuma kika turomin macizai Allah sai na tsoma kanki cikin k'oramar Mungaye Garding kifin nan ya tsole idanun rashin kunya." Lumshe idanu tayi cike da jin madarar ƙaunarsa na kuma cika ruhinta, bata furta masa kalma ba har ya b'acewa ganinta shima ya cika da mamaki jin bata tankashi ba alhalin yasan bata barin ta kwana komin k'araminsa sai ta maida martani musanman idan akansa ne domin ya gano tana d'agawa kowa ƙafa ban da shi marainin wayonta. Zubkud'a shoulder yayi dai-dai sadda ya sanya kai a falon yana cewa "Nayi sake ta san gadon barcinsa amma zan gyara kurena dana bud'e mata sirrina da ko Imam bai sani ba." "Waye ita Babana? Kuma meye damuwarka da ka kasa sanar da Amininka amma ka sanar da mace?" "Mamina Funanin mai mar... "Amsa naka Babana, wai me yasa ka mai dani kamar Hajiya Dadah ce?" "Allah sarki grandma na kwana biyu ban lek'ata ba amma in sha Allah gobe zan d'auki mara kunyar can tayimin jagora dan ban iyawa da sababin Hajiya Dadah, Neerah ce dai-dai da ita." "Allah Babana zan saɓa maka idan baka kiyayarmin tsohuwa ba." "Kaina bisa wuya Mamina." "Amsamin tambayana, wacce ita?." "Mami yawan bincike fa baida kyau, dan Allah ki bari dan ba hurimin kiji sa ba ne." Idanu ta tsira masa cike da zargi ganin haka ya kariso ya russuna ya gaisar da ita bata amsa ba sai binsa da ido takeyi ya ba'ata rai tare da nufar kujera ya zauna ya tallabe kumatunsa. "Babana kada ka sake mace ta zamo abokiyar sirrinka idan har ba matar aurenka ba ce." "To Mami." "Ina saurarenka ka ce zamuyi magana akan Companies." Gyara zama yayi cike da natsuwa ya soma koro mata bayanen cigaban da Companies d'in suke kan samu sai motsa kai takeyi cike da alfahari da ɗan nata, a ƙarshe ta sanya albarka tare da bashi shawarwari da zasu sake bunk'asa kasuwancin nasu zamowarta wacce ta sami ilimi akan kasuwanci. Gyaran murya Mami tayi ya kalleta da sauri ta jinjina masa kai tare da soma magana "Babana kai ne tamkar Uba ga k'annenka a d'akin nan to ina baka shawara da ka guje aikin da mutuncinka zai zube kar wata rana su k'i yi maka biyayya, kaga yanzu Junaid da Jabir sun taso har sun kai minzalin aure domin a wannan lokacin Mai Martaba ya ce zasu fitar da mata, nan da lokaci kaɗan Allah zai basu rabo ya zamo 'ya'yansu ne manya a maimakon naka, dan Allah ba dan ni ba ka fitar da matan aure kayi tare da zama da su bisa igiyoyin shi tun ƙasa bai rufe idanuna ba, kaji Babana domin aure shi ne matakin cikar kalama." Ta kai ƙarshen maganar idanunta na cikowa da ruwa. "Zanyi aure Ammi dan Allah kada kiyimin kuka, wallahi zanyi a cikin tsakanin nan, ni dai fatana ki duba lamarin kada ki juyamin baya kinji Ammina." "Ka sanja magana Babana domin ba zan amince da wannan maganar ba." "Ammina na tuba, wallahi ba zan baki kunya ba." Banza tayi da shi ya cigaba da yi mata magiya tamkar zaiyi kuka. *** Neerah kam ta sami lokaci mai tsawo duk'e a inda Sadauki ya barta sai doka murmushi takeyi tare da bitan karatun ruhinta tana ƙara dilmiya cikin kogin ƙaunarsa. "Hey Sis Neerah dama ina nemanki ido rufe." Kallonta ta sauke kan Zuhrah wacce taci uban kwalliya tamkar zata party. Numfashi ta sauke tare da kauda kai gefe tana jin haushin ganinta saboda tunowa da tayi itama na son abinda take so. "Please Sister zaki iya taimakona?" "Me ke damunki?" Ta ambata tare da mik'ewa tsaye fuska a haɗe. "Makahon so." "Me kike nufi?" "Ciwon so ya kamani kuma ke ce hanyar samun maganinsa." "Like how?" "Ki taimakeni badan na isa ba sai dan shaƙuwar da ke tsakaninku da wanda kaf yaran Masarauta ba wanda ke sakewa da shi sai ke kaɗai shi ne nake neman tallafinki da ki sanar da shi sak'on karatun ruhina wato Yaya Sadauki cewa shi ne zaɓin ruhin Zuhrah mai cike da burin mallakanshi ita kaɗai dan har na sanar da Mamma shi ne zaɓina dan haka idan ya sami labarin ya amince na zamo abokiyar rayuwarshi ko da bai shirya sake yin aure yanzu ba nayi masa alk'awarin zama da shi har ƙarshen rayuwata domin da sonshi na rayu, zamowarshi auri saki bai dameni ba dan shi ɗin nake muradin ganin na amsa sunar mijin Zuhrah." Da taimakon a'uziyya da Neerah ta riƙa ja tun soma maganar Zuhrah a cikin ranta yasa shedanin dake buga gangar kishin hauka a zukatan mata yasa bai rabeta ba, badan haka ba tabbaas da ba abinda zai hana bata kwashe Zuhrah da maruka marasa irga ba. Momyn Haske ne.🥰 *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri By Mrsjmoon. Adabi Writer's Association. 14. "Dan Allah Dr. Neerah ki taimakeni na sami amincewar yaya Sadauki domin shi ne muradina mahad'an ruhina a bisa igiyar aure." Sabbin zantukan Zuhrah suka dawo da Neerah hayyacinta, sai da ta saita kanta kafin ta soma magana cike da kamewa "Kiyi hak'uri, Muneerah bata cikin sokayen matan da so ke kaisu aikin zubar da k'ima dan haka kai tsaye bazan iya taimakonki ba, hausawa suka ce iya ruwa fidda kai, tunda kin iya kamuwa da ƙaunarsa ai banjin tunk'ararsa domin fayyace masa karatun ruhinki zai zamowa abin wahalarwa ba da har sai kin kama ƙafa da ni saboda tsaban kin rainamin hankali, foolish girl, mitcheww!." Ta kai ƙarshen maganar ranta a mugun b'ace tana maijin tamkar zuciyarta zata faso k'irjinta saboda zugi da takeyi maka. "Hey Malama me ye na b'ata rai har da zagin cin mutunci daga neman alfarma." "Kanki a jeji sokuwa kawai kuma wallahi kada ki sake tarana da wannan maganar banzan idan kuma kina son ranki ya ɓaci ne to ki sake jaraba tarana da maganar." Daga haka tayi gaba, duk da Part dinsu taso tafiya amma sai ta nufi Part din Mami Fulani tama haɗa hanya domin bata ganin gabanta sosai. Ita kanta mamakin zafin da ta ɗauka akan maganar Zuhrah takeyi, anan ta sake gasgata ƙaunar da takeyiwa Sadauki. Tana shiga suka d'ago suka zuba mata ido da sauri ta sauke kai ƙasa ta iso gaban Mami ta zauna gefen ƙafanta ta riƙo hannunta tana sauke numfashi da sauri da sauri. "Lafiya kike kuwa Muneerah?" "Mami ina s... Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin Lailah, ta faɗa saman gado tana cigaba da rera kuka tamkar wacce akayiwa dukan tsiya domin tanajin idan batayi kukan ba jininta zai iya hawa. "Babana jimin wani shiri-rita dai." Shafo sajensa yayi cikin jin rashin daɗin ganinta a damuwa, ganin Mami na dakon cewarsa sai ya saita kanshi ya tab'e baki ya ce "Ita ta sani ai, tunda ita ba yarinya ba ce sannan tafi kowa sanin illar jefa kai a damuwa dan haka ki barta har sai ta sakko da kanta tanemi kiji damuwarta amma dan Allah kada ki saka kanki a sokancinta hawan jininki ya motsa." " A she baka da imani Babana?" Da sauri ya kalleta ta zabga masa harara zaiyi magana ta d'aga masa hannu "Gara da hakan ya faru na gane waye kai, daga yau Jabir ko Junaid zan soma kira baya goya marayu, Ubannin k'annensu ba kai ba." "Mami wai me na... "Sai da safe Babana zan tafi jin damuwar d'iyata yanzu bazan fahimci tatsuniyar nan naka ba." "Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai me nayi da zafi ne haka Mami?" Tashi ta yi ta barshi da baki buɗe. Sosa goshinsa yayi cike da mamakin zafin da Mami ta ɗauka akan abinda bai kai ya kawo ba. Maimakon ya tashi sai ya gyara zama ya jingina da Cushing d'in da ta tashi sautin kukan Neerah nayi masa amsa amsa kuwa a cikin kunni hakan ya ƙara dagula masa lissafi inda ya tashi da sauri ya nufi wurin da zuciyarsa keyi masa jagora, tura k'ofar yayi a hankali idanunsu ya sarke da juna wacce take lafe a kafad'ar Mami na taping bayarta da ido yake tambayarka me ke damunta tura baki tayi tare da lumshe ido, k'ofar ya ɗan buga saboda ya lura Mami b'ata san da shigowarshi ba dan ta bama k'ofar baya. "Babana ko maciji ka zama ka shigo a silale kana tunanin ba zan san da isowarka wuri ba ne?" "Mami affuwan na janye kalamaina." "Ya wuce Babana amma ga kanwarka nan ka tabbatar da ta sanar da kai abinda ya sakata kuka." Daga haka ta fice, da ido suka raka bayanta sannan suka kalli juna na seconds, Sadauki ne ya d'age mata hira cikin tambayar kurame na meye damuwarta. Harara ta cilla mashi tare da hayewa saman gado ta rufe jikinta da bargo har saman kanta. "Kin hutar da ni yanzu zan tafi in sanar da Mami kishin wanda baisan kina dakon son shi ba kikeyi." Ai kafin ya rufe baki ta diro daga gadon ta cukumeshi ta baya tare da fashewa da sabon kuka mai sauti wanda ya janyo hankali Mami ta shigo a hanzarce ganinsu haka sai ta nuna Sadauki da yatsa cikin gargad'i batare da ta furta kalma ba. Murmusawa yayi ya janyo Neerah ta dawo gabanshi ya kalli Mami dake cillo masa harara ya kauda kai tare da cewa "Kiji tsoron Allah Doctor N ki sanarmin da gaskiyan damuwarki in har ba akan kishi ba ne" Duka ta soma kai masa a k'irji ya kalli Mami ta watso masa dak'uwa tare da barin wurin ganin Neerah bata lura da wucewar Mami ba sai ya saki Murmushi mai sauti tare da janyota ya jefa cikin k'irjinsa ya matse da ƙarfi dan ji yake tamkar ya tsaga k'irjinsa ya tura ta cikin zuciyarsa. "Wash! my boobs." Ta ambata tana mai son kubcewa. Sassauta riƙon yayi mata ta zame ƙasa ya bita suka zauna saman rug, ta tura kanta tsakanin cinyoyinta sai lamarin ya bashi dariya, ya kai bakinsa daf da kunninta ya hura mata iska ta zabura ta mike tsaye ya nunata da yatsa nayin dariya mara sauti mai bayyana cikar kamalarshi a fili. "Yaya Yarima me ye haka? Allah bana so." "I love you so much Dr. N, do you love me?" Idanu waje take kallonsa ya tsare gira tamkar bai taɓa dariya ba ya sake maimaita tambayeshi cikin dakon jin amsarta, tayi tsit kanta sunkuye tana miƙa godiya ga Allah na jin furucin bakinsa. "Baki so na saboda na zamo mai sauri saki ko?" Da sauri ta d'ago ta zuba masa idanunta har lokacin ta kasa furta kalma, girgiza kai yayi cike da damuwa kana ya mik'e da sauri ya fice tare da bugo k'ofar da ƙarfi. "Your are stupid Neerah." Ta ambatawa kanta hakan tare marin fuskanta cike da takaicin barin damar da ta samu ya kufce mata. "Amma ai kunyarshi naji." "Kunyar Babana ko saurayin da kike kishi?" A firgice ta kalli Mami ta gyaɗa mata kai cikin rashin walwala tare da shigowa d'akin ta kamo hannunta suka fito ta nufi ɗaya daga cikin d'akunar barcinta. "Shiga kiyi wanka ki fito mu kawo ƙarshen maganar munafuncin nan taku." "Kaina ciwo Mami kuma barci nake ji kuma walalhi bamuyi munafuncin komi ba ki yarda dani Mamina." "To kwanta zuwa gobe mayi maganar kuma ki tabbatar da gaskiyan ruhinki zaki sanarmin domin ta nan ne zan gane abinda ya kamata inyi akai duk da ba'a son raina lamarin ya zo a haka ba." Kai ta motsa tana kulle ido sanyin ac na son saukar mata da zazzaɓi sannan ruhinta cike yake da tambayoyin inda zantukan Mamu Fulani suka dosa na abinda take ambata da ba a son ranta zai faru ba. Ac Mami ta kashe tare da rage mata hasken wutan dakin ta fice, ajiyar zuciya ta sauke natsuwar ruhi na rab'arta saboda yarda kalaman ina sonki sosai Dr N, shin kina so na? Ke amsa kuwwan a cikin kunnuwarta, juyi tayi tare da furta "I love you too Yaya Yarima." Tana rufe baki taji motsin tafiyar wani abu a jikinta daidai saitin zuciyarta ta lalibo da sauri sai ga ƙatuwar kunama jajur da ita, ta tsira mata ido sai kai da kawo takeyi tsakanin tafin hannunta zuwa tsin-tsiyar hannunta ba tare da tayi mata illar komi ba, murmushi ta yi tare da matseta da ƙarfi tana jin yarda bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe ido tana mai furta "Where are you Yaya Yarima? Dan nasan kana kusa da ni tunda ga kayanka a hannuna." "Yes I'm here my Doctor." Da sauri ta kalli bakin k'ofan cikin hasken da bai wadaci d'akin ba, shi ne tsaye yana kallonta fuskansa ba d'igon annuri, murza idanu tayi dan tabbatarwa sai taga wayam ba kowa komawa kwance ta yi ta tsirawa kunaman nan ido da ta koma jikin bango tana ta shawagi sai sanja color takeyi from black to red, yellow, blue, brown and so on dan wani color d'in bata taɓa ganinsa ba tsawon rayuwarta. Murmushi kawai take binta da shi, har bata san sadda barci ya ɗauketa ba ta kife ruf da ciki barcin da su Mami ke yak'in ta daina yi saboda rashin alfanunsa ga Bil'adam. *** 'Na yarda da zancen Bokanki Mamma hak'ik'a ya sanar da ke gaskiya cewa ina da kishiya a kusa da ni, in ko haka ne wallahi sai dai kowa ya rasa Yaya Sadauki domin bazanyi kishi da ke Neerah ba kamar yarda nasan kema bazakiyi da ni ba saboda girman zumuntarmu ya wuce wasa, kai bama zai yiwu hakan ya kasance ba, tabbaas kai nawa ne Yarima Aliyu, ruwa da iska banga mai yimin shamaki da aurenka ba, Neerah wahalar banza kikeyi, ke da Yaya Sadauki sai zumunci na yan uwantaka da Allah ya haɗamu.' Duk cikin zucci Zuhrah keyin zantukan idanunta na kan sashin Mami Fulani tana auna masa mugun kallo tamkar shi ne Dr. Neerah. Cin tayar mota da akayi yasa ta kalli wurin a hanzarce hango Ƴaƴanta Hud cikin maye yasa ta buɗe robar ruwar hannunta wanda ke da sanyi ta nufeshi a fusace ta watsa masa ya saki a jiyar zuciya yana kallonta idanu jajur sake juye masa ragowar ruwan tayi a fuska aikam ya rarumota ta kwasa da gudu ya rufa mata baya yana huci. "Mamma kizo danki mara amfani zai illata miki ni." Abinda take ambata kenan tana maimaitawa sadda tayi nasarar shiga falonsu, Mamma ta fito zani na kufcewa dan tunda tajiyo kalaman Zuhrah ta san ita da Hud ne wanda tayi imani ya koma ruwane na shigowa Masarauta cikin maye lamarin da Zuhrah ke adawa shi kuma hakanne yasa tayi mugun rainashi duk da ba ita ce sak'onshi ba domin a kwai mutum biyu tsakaninsu kafin ita. "Me yasa ne Hud? kamanta tijarar Abbanku Chiroma ko? Shin kana ganin wannan gaulancin zai kaika zuwa ga hawa karagar Sarautar Birnin Mungaye?" Da sauri Zuhrah ta anshe da "Ina kuwa domin wallahi ko ni sai na yi sanadin rashin hawarsa domin mu ba 'yan maye ba ne balle ya hau ya maida giya ruwan fanfommu duk mu lalace, kanmu ya kwance kamar yarda nasa yake a kwance." Tama rufe baki ta k'wallah ihu domin a fusace ya jefota da zobbesa mai kama da k'ashi, ya ko sameta a goshi a take jini ya wanke mata fuska, Mamma ta yi kanta tana rafka salati fadi take "Hud kiramin Dr Neerah ta bata taimakon gaggawa domin ban son Masarauta susan wannan abin kunyar da ka aikata." "Sai dai ta mutu wallahi Mamma indai sai na kira an bata taimako ne." Ya ambata cikin rabewar murya irin na 'yan maye. Wani a shar Mamma ta mulmulo ta antaya masa ko ajikinsa sai ma ya kwashe da dariya ya tura kai d'akin Zuhrah ya faɗa saman Cushing yana sunbatun sai ya illata rayuwar Zuhrah tunda ta rainashi, daga haka barci yayi gaba da shi. "Mamma jijiyar idanu zasu tsinke kiyi wani abu kada na rasa idanun gani, wayyo! Na shiga uku na lalace, walalhi ba zan yafewa ɗanki mara amfanin can ba." A gigice Mamma ta kamota tare da tara d'ankwalinta a goshin tana zabga salati gami da toshe mata baki dan ta daina aibata ɗan uwanta tare da gudun kada wani ya jiyo. "Mamma kaini Mungaye Clinic kada in rasa idanu cikar ado da k'walliyar duk kan mutane musanman mata." Bata da zaɓi zai fito da ita zuwa Clinic duk da bata so hakan ba saboda bata son labari ya fito cewa Hud ne ya jima shalelenta ciwo domin a bayyane nakasu ne gareshi akan burinta na ganin ya haye karagar mulkin Mungaye. *** Tsibiri. Iskan bai tsaya a ɗauke masu gani ba har da halaka jama'a, a cikin abinda bai wuce mintoci biyar ba ya halaka mutane masu yawa. Tsibiri ya hautsine da iface-iface na neman dauki, cikin fushi Sarkin yaƙi wato mahaifin Buda ya aika sak'o cikin aikin alk'aliman sihiri zuwa ga Abun akan su dawo Tsibiri zai kama da wuta sannan ya soma ƙoƙarin tsaida guguwan cikin kwarewar tsafi sai dai lamarin ya sha ƙarfinsa, suka taru suka haɗa ƙarfi kamar yarda sukayima na farko nanma bata sanja zani ba sai kawai suka soma neman matseta tare da bawa jama'a taimakon wurin b'uya. Rugugi ne ya doso Tsibirin abinda ya sanya iskan nan lafawa, tamkar k'iftawar ido iskan ta ɓace, zuwa can Lina ta bayyana fuska a daure, kafin su ankara ta soma huro sanyi wanda ke fitowa daga bakinta na shiga jikkunar Jama'a inda ke warkar masu da raunin da suka ji tare da tashin wanda suka jikkata, ta ɗauki tsawon mintoci goma tana huro iskan kafin ta dakata tana kallon al'umman da duk suka samu natsuwa suka sakata a tsakiya suna yi mata kirari da Gimbiyarsu mai tausayi. "Kuyi hak'uri da matsalar da 'yar uwana ta janyo muku, yanzu ku tafi ku kauda wanda suka mutu tare da cigaba da harkokinku zanyi bakin iyawata wurin kare lafiyarku domin wannan shi ne burina kuyi rayuwar 'yanci wata rana." "Mungode shugaban gobe, Sarautar Tsibiri naki ne Gimbiya Lina." Suka ambata a tare cikin daga murya. Jinjina kai tayi ciki da alfahari da su. Suna watsewa Abun ya bayya tare da Buda, Lina na jin alamun takunsu ta ɓace ta bayyana cikin Bukkan Kaka Gunu inda ta sami Lima sunkuye kan Mah tana aikin ceto ranta. "Sakacinki ya janyo Mah zata mutu, wannan bak'ar ranar nake jiye mana har na umurceki da ki kula da ita amma saboda son zuciya irin naki kin kasa zama da ita kin taho neman cikar burinki, to ki zauna a nan tare da ita domin fitowarki kiran ajalinki ne domin Jama'an Tsibiri sun fusata da kashe masu dangi da kikayi sanadi sannan Abun yana farautanki kamar yarda yake faraunata da Mah." "Me kike nufi da Abun na farautanmu? Alhalin mu ne kaɗai sanyin idanunsa." "Lima yanzu Abun ya sanja dan shi ne ke wasa da rayuwar Mah domin ya samu hankalina ya dawo kanta inda zai hilace ni ya mallaki Zoben da ke hannuna wand zai bashi damar samun ƙarfin tsafin da ya zarce na kowa dake zamanin nan haka ya fiki burin son mallakan Ruwan Albarkan Kaka Gunu domin shima na ɗauke da sirrika masu girma akan tsafi da cikar mulki, ki sani a yanzu mu ne damuwarshi akan haka ya kudiri halakamu baki ɗaya indai zamu kawo masa tangarda a samun tsawon rayuwa akan mulki." "Ta ya zan yarda da gaskiya kike sanarmin ba yaudarar da kika saba yimin ba ne? " "Ifritu Mutuwa zai gasgatani." "Tabbas zantukan yar uwanki Lina ba ƙarya duk da itama tana son shan ruwan albarkan domin ta sake finki komi dan hawa karagar mulki, ko ba haka ne manufarki ba ya ke Gimbiya Lina?" "Tabbaas haka ne kuma har a yanzu ina cikin muradin rigaki mallakan ruwan albarkan sai dai ba yanzu shi ne a gabana ba domin haka kaima Mutuwa dole ka dakata da taimakonta na mallakan Ruwan har sai na kammala da abinda ke gaba in yaso sai kayi mana k'uri'a duk wanda ya ci shine mai mallakin gadon Kaka Gunu." "Baki isa ba Lina, ni ce ke da gadon Ruwan Albarkan Kaka Gunu dan haka ki fitar da ranki akansa." Murmusawa Lina ta yi batare da ta furta kalma ba ta isa gaban Mah da ke shimfida tamkar gawa ta sunkuya ta shafi fuskanta wani haske ya sauka a fuskan zuwa ilahirin jikinta aikam sai ta soma tari tana kiran sunar Abun da ya zo ya taimaketa. "Mah kina tare da 'yan biyunki kuma bisa kulawarsu kika tsira daga baƙin iskan da Lima ta yi jagoran shigowarsa cikin al'umma, yanzu zan barki a wannan Bukar ta Kaka Gunu Lima zata kula da ke zuwa sadda zan dawo na maidaki inda duk ƙarfin tsafin matsafi yayi kaɗan ya iya zuwa wurin." "Ki dawo lafiya Ruhin Sarki Goma ya baki kariya." Motsa kai tayi tare da mik'e ta kalli Lima da ta tsare giran sama da ƙasa ta hurama fuskanta iska kan dole ta murmusa saboda tunowa da lokacin baya da take azabtar da Lina da iskan bakinta. "Yawwa kin tuna muguntarki na baya ko? To ki natsu kiji me zan sanar da ke, ki zauna a nan kamar yarda na sanar da ke a farko, ki kulamin da Mah, Ifritu Mutuwa zai kula da ku sannan zan batar da Bukkan Kaka Gunu a idanun Abun wanda ke nufin isowa bada jimawa ba." Lima zatayi magana Lina ta daga mata hannu tare da cewa "Kada kiyi yunkurin barin Bukkan nan dan zuwa watsewarki domin yin hakan wasa da rayuwarki ne domin kina fita zaki tsinci kanki a akurkin sihiri ko na Abun ko na Ifritu Baushe kuma ki sani bana da lokacin taimakonki saboda lamarin Mah d'ita ya fiyemin komi, in kinji gargad'i ruwanki, ni zan wuce ba zan jima ba zan dawo dan bana son na wuce kwanaki biyu rak ban kammala abinda naje yi ba." Kafin Lima ta furta kalma Lina ta zama farin hayaki ta b'ace kallonta ta sauke kan Ifritu Mutuwa sai ya jijjiga kai tare da bude tafin hannunsa saiga wurin ya sanja, ya dawo dauke da kilisai masu laushi da makeken gadon alfarma, jinjina tayi masa ya gyaɗa kai tare da b'acewa, ta doshi gadon ta hau ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa cike da burin sai ta fita wurin nan taga abinda zai faru. Mah itama gadon ta hau cike da tarin damuwa. Lina na fitowa ta jiyo takun Dokin Buda sai ta zama balbela ta haye saman bishiya suna wucewa ta sakko ta watsa haske a baki ɗaya Bukkan ta lula sararin samaniya. *** Abun tsaye a turakansa yana kai da kawo cikin tarin damuwa zuwa can ya ja iska ya fesar tare da zama akan k'ok'on kan Giwa ya na cije lebe, ya sharce Gumin da ya feso masa a goshi tare da mikewa a fusace ya kaiwa bango duka cikin ambatar "Ƙarya ne, saina Mallaki Zoben hannunki Lina sannan yar uwanki zata kasheki a gaban mahaifiyarki, a yanzu bana da abokiyar gaba sama da ke, zan nuna miki ta yaro kyau take amma bata k'arko, ki sani ba zan barki ki Mulke ni ba alhali ina rayuwa, tabbaas a yau na musanta kalman cewa bazanyi fito na fito da ke ba haka na gasgata kalamin Kaka Gunu da ya ce samuwarki cikinmu masifa ce domin zaki karya k'adarinmu ki sanja tarihinmu ki watsa mana Martaban Tsibiri hak'ik'a dana sani na bashi dama a can baya ya sanya kinbi rariya ya zamo Lima kawai zata zo duniyarmu." Momyn Haske ne 🥰 *Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.* [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsibiri By Mrsjmoon Adabi Writer's Association. https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕 15 Ya kai ƙarshen zance cikin ɓacin rai, yana jin tamkar ya dawo da baya ya goge samuwar Lina a cikin zuri'arshi. "Da girman mulkinka ya mai Tsibiri, ya kamata ka fito dan jajantawa Jama'a masifar da ta afku wanda Gimbiya Lima ta janyo faruwarshi." Sarkin yaƙi ya ambata daga bakin kofa kansa sunkuye. Cikin ɓacin rai ya nuna Sarkin yaƙi bakinsa na fitar da tiririn masifa ya ce "Yau she mulkin Tsibiri ya kai ga lalacewar da Sarki mai ikon juya kowa da ke Tsibirin nan zai fito bawa Talakawa hak'uri abisa afkuwan lamarin da ya zamo cigaban Mulkinsa ne, to ka tuna idan ka manta ne Tsibirin nan bai ginu bisa Tausayi ba haka ba zai taɓa haɗa hanya da shi ba, ka ƙara sani, nai alfahari da afkuwan masifar nan domin samun cikar burina na mallakan ababen da ke hannun 'ya'yana sai da zubda jini k irin wannan, lallai aikikinki na kyau Gimbiya Lima, a kullum ina alfahari da zamowarki gudan Jinina tabbaas ke ce magajiyar Tsibiri na sake gas-gata kalaman Kaka Gunu na cewa nasaranmu naga hawa karagar mulkinki ne duk da ina da wani buri akanki amma ba zan k'i yaba miki." "Ya shugabana ka natsu mu fuskancin masifar da wannan zubda jinin zai haifar domin Dodo yayi fushi ya bar Tsibirin domin Guguwan ta rainata masa mata yanzu haka ya killace kansa a Kogo yana shirin yak'ar Lima shin idan baka fito ka jajantawa Jama'a ba me kake tunanin yi wanda zai sakko da Dodo akan dokin nakin na ya hau?" "Sarkin yaƙi ka rufemin baki tun fushina bai sauka kanka ba sannan Dodo zai dawo bakin aikinsa kuma fushin-shi na rashin samun damar san Jinin jama'ar da baiyi ba ne, ba wai na nak'asar matarsa ba, shin ko ka manta bata da lafiya a cikin ko wani lokaci zata iya samun rauni, tunda ta saci jiki taje ta sha Jinin wani dan Fulani shi kuma ya soma bin hakkin jinin Ɗansa lamarin da yaso shafar ƙarfin ikon Tsibiri, shin ko mutuwa tayi ai bamu da asara." "Haka ne ya mai Tsibiri, tabbas na tuna da wannan masifar da muka kasa samun maganinsa sai da k'yar." "To Dodo fushin karya ya keyi sai dai bazank'i ta bakinka ba zamu ɗauki matakin kare kai kada ya kawo mana matsala saboda ya soma nuna rashin amana wanda hakan zai haifar masa da rasa rayuwarshi ba damuwata ba ne." "Me zamuyi masa?" "Cin amanar tun kafin ya samu nasarar cin tamu, wato samo hanyar halakasu cikin dibara." "Ya mai Tsibiri Dodo ya wuce da saninmu domin ya rayu tun farkon Sarkin da ya raya wannan Tsibirin, yana da nindarai kala kala sama da dubbunnai dan haka shawara mafi samun mafita shi ne anjima da dare zanzo mu tafi wurinsa mu rarrasheshi ya dawo mu cigaba da zaman amana amma ka janye batun halakashi saboda gudun matsala." Jim Abun yayi daga bisani ya gyada kai alamun aminta da zancen, Sarkin yaƙi za ku saka magana Abun ya d'aga mashi hannu tare da nuna kofar fita, ya ko juya da hanzari ya fice yana mai cike da farin cikin hayewa matakin farko daga cikar burinsa. Abun d'akin bincikensa ya shige yana mai jin rashin yarda da zantukan Sarkin yaƙi na zuwa muhallin Dodo sai dai burin son nemo hanyar da zai ladaftar da Lina har ya mallaki Zoben hannunta ya shafe binciko abinda Sarkin yaƙin ke shiryawa, sai ma watsar da lamarin da yayi saboda zuciyarsa na bashi tabbacin aminci dake tsakaninsu da juna. A gafen Sarki yaƙi kuwa gidansa ya nufa inda ya sami ɗansa Jarumi Buda zaine na dakon isowarshi. Yana isa ya rungume Buda yana kyal-kyalan dariya sai da yayi mai isarshi sannan ya tsagaita ya doki kafadan ɗan nasa yana mai koro masa yarda sukayi da Abun, yana dasa aya Buda ya amshe da cewa" Ya Baba ina guje mana afkawa tarkon Lina dan zuwa yanzu na soma tsorata da lamarinta kada garin halaka mahaifinta mu ɗin mu halaka a banza saboda bata bari kayi nasarar halaka mahaifinta ba, ni dai da zakaji shawarata da mun hak'ura da son mulkin nan mu kare namu da muke da shi na Sarkin mayak'a." Yana rufe baki wani taurari suka gifta a maganansa sakamakon marin da Sarkin yaƙi ya zabga mashi. A gigice ya durk'ushe gami da kwalla ihu wanda yayi amsa kuwwa a Tsibirin lamarin da ya sake gigita Al'umma suka soma fadawa mahallinsu suna kare kai ta hanyar tsaface kansu da 'ya'yansu domin tunaninsu wata masifar ce ta dawo. Ihun Buda ya sauka a kunnin Abun dake tsaka da bincike, tsak ya tsaya yana nazarin abinda ke shirin faruwa sai dai jin takun isowar Lina Tsibirin yasa shi barin komi ya soma shirin tunkararta tun kafin ta hayo, burinsa ya halakata kowa ya huta da ganinta. Sarki yaƙi yaji rashin jin daɗin abinda ya aikatawa ɗan nasa sai yayi ƙasa da murya yana mai cewa "Kayi hak'uri ya kai ɗana amma ka sani burin mahaifina kenan mu gaji mulkin Tsibiri hakan bai samu ba saboda Kaka Gunu ya katange hanyar shi yasa na rayuwa da burin kawo karshen mai Tsibiri ko da hakan na nufin rasa raina zanyi dan haka kada ka sake ambatamin na ja da baya tunda kai baka son hawa mulki to ni zan hau duk da na soma tsufa." "Zan hau Babana domin nima ina da burin mulkan jama'armu." "Da kyau ɗana, ina alfahari da kai." Kauda kai Buda ya yi yana mai buɗe k'ofofin hancinsa sai kuma ya mik'e a hanyarca, Sarkin yaƙi ya rik'oshi cikin alamun tambayar inda zaije. "Babana Gimbiya Lina na daf da shigowa Tsibiri kuma ina jiyo alamun zata gamu da matsala dan haka zan kai mata ɗauki." "Ta mutu mana ina ruwanmu." "Ina sonta Babana, ka amincemin na kai mata ɗauki saboda sai da ƙarfinta zan samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri." "Kana hauka ne Buda? Lina tafi kowa son mulkan Tsibiri dan haka zan amince maka kaje gareta bisa aniyar kasheta ka riga mai Tsibiri mallakan Zoben da naji yana magana akai wanda ke hannunta." "In haka ne Baba kaga kenan taimakonta zansoma akan duk abinda ta sanya gaba idan ta aminta da ni cewa masoyinta na gaskiya ne sai na yaudareta na amshe Zoben daga nan sai mu fito mata da manufarmu na yak'arta mu kaudata cikin sauk'i." "Da kyau fasihin ɗana Buda, tafi gareta da albarka Takobin yaƙina, kai ne ke da nasara kan Gimbiya Lina." "Godiya nake Babana." Daga haka Buda ya fice ya doshi inda yake jiyo K'amshin Lina wanda ya kaishi ga fita yankin Tsibirin baki ɗaya. Shima Abun ya nausa wajen Tsibirin inda ke jiyo takon Lina har lokacin kuma ya kasa cimma ta sai ya ƙara k'aimi domin riskanta akan lokaci. Sai dai abinda ba su sani ba shi ne duk kansu bayan Lima suka biyo wacce ta fice ta bar Mah na barci, lokacin da zata fita Ifritu Mutuwa ya so hanata amma tuno zaman cika umurninta yakeyi sai ya kyaleta ta fice cike da muradin son ganin abinda zai faru akan fitar nata, mutuwa ce ko rayuwa, nasara ce ko rashin nasara, ita dai burinta yin ido biyu da kalaman Lina domin ji take idan bata fito wajen Tsibiri ba to Lina ta gama samun nasara akanta na zamowa shugabanta tunda gashi nan ta bata umurni kuma ta bi. Abun, Buda tare da Lima sunata yin nisa da Tsibiri a bisa hanya ɗaya batare da sun gano hakan ba domin Ifritu Baushe ne ya shiryo musu sihirin ficewa daga Tsibirin ta hanyar kusanto masu da takun Lima gami da k'amshinta da ya sauya da irin na Lina sak, saboda Hadimi Tsidau ya sanar masa indai suna cikin Tsibirin to ba zaiyi nasarar shigowa ya ɗauke Mah ba wacce ke son yin garkuwa da ita domin Lina tazo yankinsa da kanta inda zai mallaketa tare da Zoben sihirin hannunta daga bisa ya sadaukarwa da Dodonsa jinin Mah a gaban idanunta, kana yayi mata ciki ta haifa masa d'iyar da zai sha jininta duk akan idonta ya tabbatar da ganan labarinta ya zo ƙarshe dan ko bai halakata da hannunsa ba ya san bak'in ciki zaisa ta had'iye ranta. Tunda Tsidau ya farka da barcin da ya kwashe shi sai ifrutu Baushe ya adana shi yana gana masa azaba kala daban daban domin ya fahimci makirci ke son shirya masa ya gudu dan ba zai taɓa kawo mashi Lina Fadar sa ba, yanzu haka yana can kurkukun tsafinsa da ke k'ark'ashin ƙasa cikin tsaron wasu bak'ak'en rindunar Aljannu suna aikin azabtar da shi, wuya yasa shi sanar da Baushe hanyar da zaibi domin samun nasarar shiga cikin Tsibirin har ya samu cikar burinaa wato sai ya kora su Abun sunyi nesa da Tsibiri domin yawan yin nisansu da Tsibiri shi kuma yawan kusanci ga nasararshi na shiga cikin Tsibiri. Yanzu haka Ifritun Baushe ya sami kusanci da Hatsabibin Tsiri saura samun nasarar shiga cikinsa tunda ga su Lima can na cigaba da lulawa cikin duniya ba tare da sun gano sihiri ke d'awainiya da su ba. *** Masarautar Mungaye. Cikin ikon Allah su Zuhrah har suka isa Clinic ba wanda ya gansu sai hadimai dake ta mik'o masu gaisuwa. An wanke mata ciwon inda anan aka gano ƙarami ne tsabar rakine ke damunta ta cika masu kunnuwa da ihu, a hanyarsu na dawo ne suka haɗu da Jabir inda ya gaisar da Mamma cikin girmamawa ta amsa tare da yin gaba ta barshi da Zuhrah, shi kuwa ya tsareta da tambayoyi akan sanadin raunin fuskanta batare da jin ko ɗarba ta koro masa bayanin abinda ya faru sai dai ganin ɓacin ran da ya nuna har saida tayi da ta sanin faɗan domin yarda ya rufeta da masifa sai da tayi zaton dukanta zaiyi, ta ja da baya ya fizgo hannunta suka isa sashin Mamma ya turata tare da rufa mata baya. Mamma dake zaune riƙe da robar ruwa tana sha ta mik'e a firgice tana tambayar abinda ke faruwa. "Mamma ki gyarawa Zuhrah tarbiyya saboda yaya Hud ba sa'arta ba ne, shin taya za'a ce kina kallo ta gama rainashi? A gaskiya da sake, in sha Allah gobe zan sanar da Mai Martaba domin a dauki mataki dan ko me yakeyi ya fi gaban raini a wurin k'aninsa sannan rayuwar dake ciki ƙaddara ce wata rana zai zamo labari dan haka dole Zuhrah ta girmama shi a matsayinsa na babban yaya a d'akinsu." Ya sauke dubansa kan Zuhrah dake risgan kukan baƙin cikin anayi mata faɗa alhalin ita aka zalunta. Ya nunata da yatsa cikin kaushin murya wanda ya koma irin na Sadauki sak ya ce "Wannan shi ne rana ta ƙarshe da zan ji kin sake aibata yayanki mai ɗauke da matakin uba, idan kuma kince wasa nakeyi to ga fili nan ga mai doki, kin sanni dai sarai magajin Abba Chiroma ne, so be carefull kuma ki hanzarta bashi hak'uri, zan tambayeshi idan naji saɓanin haka na lahira sai ya fiki jin daɗi." Sai ya russuna gaban Mamma yayi mata sai da safe ta amsa jiki a mace, saida ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara tsirawa hanyar da ya bi da idanu saboda zantukansa sun nusar da ita wani kuskure da take aikatawa na sangarta Zuhrah ya zamo kaf yayunta bata ganin girmansu saɓanin sauran yaran dake kan girmama yayunsu, ta dubi Zuhrah kafin ta furta kalma ta buga ƙafa tare da fashewa kuka mai sauti, Mamma ta nufota ta zille ta fice da gudu tana gunjin kuka, komawa Mamma tayi ta zauna ta dafe kanta cikin sake tsunduma nazarin kalaman Jabir inda take hango cikakken gazawarta wurin tarbiyyan yaranta. "Ƴaƴan Fulani dai masu hangen nesa ne, komin hassadan mutum ya zauna da su sai sun shiga ranshi tare da ƙaruwa da su, Jabir nagode da tunatarwa amma duk da haka bashi ne zaisa na janye ga son Hud ya zama Sarkin birnin Mungaye ba, ina nan akan bakana sai na salwartan da Sadauki daga wannan nahiyar." Tana ambatar haka ta mik'e da sauri ta shirya ta fice zuwa sashin Umma domin kamma aikin da suka soma na birne layun da Mai Martaba zai ambaci sunar Hud a matsayin magajinsa domin Mamma mutum biyu take aikin a kansu wato Sadauki da Sardauna, ta kora Sadauki ya b'ace a duniya shi kuma Sardauna ya nak'asa yarda mulki zaifi ƙarfin shi,a wannan gaɓar mai martaba zai ayyana Hud, duk ta manta idan ba Sadauki da Sardauna a kwai wasu zaratan samarin Junaid da Jabir. *** Washe gari. Neerah ce zaune gaban Mami Fulani, tambayar duniya tayi mata akan sanin gaskiyan ra'ayinta akan Sadauki sannan ta umurceta da kada ta b'oye mata komi dake ranta, amma taki yin motsin kirki sai shafar yatsun ƙafarta takeyi. Murmushi Mami tayi tare da umurtanta da ta tashi taje ta karya tunda tak'i yin magana. "Ina Azumi." Ta ambata a hankali kuma cike da shagwaba'a. "Masha Allah, ai namanta yau Alhamis, to Allah ya karb'a ya bada lada." "Amin." Shiru ya sake ratsa wurin zuwa can Mami ta kalleta a natse ta gano da maganar da take son furtawa, kiran sunarta tayi "Muneerah." "Na'am Mamina." "Sanarmin da zancen dake ruhinki kada kiji komi, nayi miki alkawari kome ye shi ina tare da ke sannan ki haɗa da bani amsar tambayar da nayi miki, shin kina son Babana ko takuraki yayi?" Tafi mintoci biyar bata ce komi ba har sai da Mami ta dafa kanta cikin cewa "Sarauta gadonsa kikayi ba haye ba d'iyata, idan baki zamo mai nazari kafin bada amsa ba tabbas baki cika d'iya ga Sarki Abdul Hakim ba." Dagowa tayi tana murje ido cikin turo baki ta ce "Mami kiran sunar Abbanmu tsirara fa kikayi." "To Abban su Doctor Neerah, shi kenan na lullub'e?" Dariya ne ya kufce mata domin bata taɓa jin Mami ta kirata da sunar irin haka ba. "Tubarkallah, masha Allah, Allah Alhamdulillah da ya azurtani da d'iya mai kyau koda kuwa kuka takeyi." Kafad'ar Mami ta kife fuskanta tana cigaba da dariyan mara sauti. "Tashi mugama magana domin yau yau ake da zama na musamman akan zaɓinku daga nan sai a tsaida lokacin biki." "Mami nifa ba zan ƙaryata yaya Yarima ba kawai duk abinda ya sanar da ke hakan ne, dama shi ne abinda zan faɗa miki tun d'azun nake jin nauyi." Tana gama ambata ta mik'e da sauri ta fice domin gujewa tambayoyin Mami wanda amsasu zasu bata kunya matuk'a. Bayanta Mami tabi da kallo baki buɗe sai kuma ta tsare gira tamkar an aiko mata da sakon mutuwa. "Da sake bazan yarda da wannan gangancin ba na aurawa Babana jinin k'anwata ya ƙarasa kunyatani cikin dangi." "Mamina kada kiyimin haka, tunda dai kinji gaskiya to ki kai maganar ga Abba tare da sanya mana albarka." Tsirawa k'ofar shigowa falon tayi ido ba kiftawa har Sadauki ya iso gabanta ya zauna tare da riƙe ƙafarta muryansa cike da rauni ya ce "Natuba Mamina, bazan sake aikata zunubin da ya gabata ba, zan zauna da Muneerah har ƙarshen rayuwata domin ita ce sirrina, tasan waye Aliyu sama da ku mahaifana sannan bazan taɓa baki kunya ba nayi miki wannan alkawarin, dan Allah ki yarda da Babanki Mamina." "Babana wannan daɗin bakin naka bai karɓu ba dan haka tashi ka bani wuri domin bazan taɓa amincewa da wannan auren ba dan kafi kowa sanin wacece Nana Safiyya gareni, ni ce na saki Nono ta kama to ba zan amince da wannan lamarin ba." "Please Mamina am begin you, kada ki rabani da Muneerah domin ita ce zaɓin ruhina." "Babana idan ka sake ambatar kalma ɗaya tak a wurin nan sai ranka yafi dare duhu, oya! Maza ka b'ace min da gani " Maimakon ya tashi sai kawai ya kife fuskanshi a ƙafarta, tana jiyo saukan d'umin ruwa wanda hakan ya tabbatar mata da kuka ya keyi amma hakan baisa ta janye daga dokin nak'in data hau ba saima janye ƙafarta da tayi ta mik'e ta shige bedroom d'inta ta kulle k'ofa. Dafe goshinsa yayi cikin jin kansa na sarawa yanayin da baya so na son kawo mashi ziyara, a hankali ya mik'e ya shige dakin Lailah inda ya sami Neerah daren jiya, ya zauna a saman Cushing tare da d'an zamewa ya kwnta ya d'aga kansa sama ya tsirawa ceilling ido, abin mamaki sai ya ji barci na ziyartansa amma idonsa yaƙi kullewa. Fitinannen k'amshinta ya jiyo yasa ya sake ware idonu na kallon fuskanta da ya bayyana a saman fankan da ke juyawa, hannu ya daga ya nunata cikin cewa "Har a sashin mahaifiyata sai kinzo kin tozartani?" D'age masa gira tayi cikin jifarsa da shu'umin murmushi sai kuma ta bayyana zaune gefenshi, ƙafa yasa ya hankad'ata sakamakon tuno makarkin da yayi jiya tamkar a irin haka abin ya soma kafin ta rikid'e masa zuwa sifar Neerah, ya haik'e mata ba d'igon imani. K'irjinsa ne ya harba tuno baya, a mugun fusace ya mik'e ya nunata da yatsa cikin amo mai amsa kuwa ya ce "Kina taɓani na rantse sai na kasheki!" "Ka taɓa ganin inda Aljani ya mutu?" "Za a fara akanki, azzaliman banza kawai,mara addini!!." Ya kai ƙarshen maganar cikin buɗe murya bai ko tunanin Mami zata iya jiyo shi. "Kai ka koyamin zalincin ya kai Yarima Aliyu Sadauki takwarar mafarin Mungaye Malam Aliyu Malle kuma takwarar Baffan mahaifiyar shi Fulanin Sarki Abdul Hakim." "Ya isheni haka nan ya ke banziya!." "To nayi shiru amma in kamanta zauna in tuna maka zalincin da ka aikata wanda ya janyoni bibiyan farin cikinka." Kafin yayi yunkurin magana ta turashi zaune ta hanyar hura masa iskan bakinta ya lumshe ido ya bude cikin jin mutuwar jiki, ta nuna bango da yatsa sai ga gidansa na dajin Tekun Kabobo ya bayyana, ya ware idonu ta gyaɗa masa kai cikin cewa "Ka tuna zalincin da kayi a wannan gidan?" Bai amsaba illa kallon gidan dakeyi cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa. "Nayi alkawarin sai ka ambatawa Masarauta aika-aikan da kayi da bakinka a gaban dubban Jama'a kuma a yau ɗin nan saboda aikina na daf da zuwa ƙarshe." Lumshe ido yayi yarda lamarin ya kasance ya soma dawo masa a idanu tiryan-tiryan, kafin kwabo yaji tamkar gashi a bakin Tekun Kabobo da mafarin lamarin ya soma, wani iziyar ruwa ya zashi zuwa cikin Tekun duk yarda ya so kufcewa halaka ya kasa sai ya hango Neerah a tsakiyar Tekun na d'ago masa hannu ya zabura da ƙarfi, Mami ta zabga salati sai ya kalleta a razane, idanunsa sun sanja kala zuwa jajur, cigaba da karanto addu'a tayi tana tofa mashi ya ritse ido na jiyo amsa kuwwan ihunta, da hanzari ya toshe kunnuwanshi, Mami ta sake zabga salati, muryanta na rawa take cewa "Kada kayimin haka Babana indai akan aurenku da Muneerah ce kake son haukacewa walalhi na amince, Allah ya tsare afkuwan abinda nake tsoro, ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka." Komawa kwance yayi najiyo dariyarta a daf da kunninsa kana daga bisani tace "Na tayaka yaƙin samun cikar burinka na auren masoyiyarka saura samuwar nawa wanda ya ke nak'asu ne ga ci gabanka domin Birnin Mungaye baza su amshi azzalimi matsayin jagoransu ba, na tafi kada mamanka ta ƙarasa konani da gatan addinku wanda kake da sani akansa amma na haka su amfane ka." Yanajin iskan tafiyarta ya juyo ya tsirawa Mami ido sai a lokacin yaga a she harda Abba, da Neerah a d'akin, bai lura ba sai yanzu. Runtse ido yayi tare da tura hannayensa a cikin sumarshi. Jan hannun Mami mai martaba yayi suka fice batare da Sadauki ya sani ba saboda ya amincewa kansa Sadauki na tare da shafan Junnu. "Yaya Yarima." Kollonta yayi ta sakar masa murmushi tare da matsowar ta zauna a hannun kujeran da ya ke kwance ta soma bashi labarin abinda ya faru cikin natsuwa. "Ina fitowa daga falon Mami na hango zaka shigo sai na b'oye sai da ka shige sai na samu kaina da biyo bayanka, na jiyo duk yarda kukayi da Mami shi ne na biyo bayanka domin sake samun tabbacin kalaminka na cewa ni ɗin sirrinka ce sai na samu kana ta magana kai kaɗai, sam na kasa fahimtar abinda kake faɗa ga daishi da yaren da nasani kake maganar amma harshenta yana sark'ewa ta yarda maganar bai fitan da za'a fahimta, ganin kamar baka hayyacinka shi ne na kira Mami, tana zuwa ta soma tofa maka addu'a ganin abin na son fin ƙarfinta sai ta kira Abba inda yana shigowa ka dawo hayyacinka lamarin kamar shafan Aljannu." 'Innalillahi wa inna ilaihin raji'un.' Ya ambata cikin rashi yana maijin harbawan halittarshi da ƙarfi wanda ya haddasa masa zabura tare da kai hannu gabanshi cikin dibara gudun kada Neerah ta gani saidai ita sam bata lura da sanjinsa ba, saima tambaya da ta jefo masa. "Yaya Yarima wasu kalan mafarkai kakeyi? In da hali ka sanar da ni irin wanda kayi jiya tunda na zama sirrinka kuma zan cigaba da kasancewa sirrinka na har abada." Kallonta yakeyi cikin jin wani kalan sha'awa na taso masa na daban da yarda ya saba shiga, sam bai fahimtar zantukan da takeyi. Jin bai amsa ba sai ta kalleshi, mik'ewa tsaye tayi jikinta na rawa dan a take ta tuno mafarkinta na jiya mai wuyar sha'ani, ware idanu tayi a kansa tare da tsirawa inda hannayensa suke ido, ya cire hannun cikin dibara, suka tsirawa juna ido ba k'iftatawa, a take Neerah ta gano halin da yake ciki wanda a irinsa ta ganshi a barcinta na daren jiya, sai dai tuno abinda ya faru tsakaninsu yasa ta nemi barin wurin saidai ta makaro dan a zafafe ya damki dantsen hannunta ya jefata a k'irjinsa ya matse, yana sauke numfashi da sauri da sauri tare da jin harbawan halittarshi cikin salon da bai taɓa samun kansa ciki ba, sai ya sami kansa da ware ƙafa ya matse guk'unta gam. "Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, na mutu Mamina, dan Allah Yaya Yarima karufamin Asiri." Abinda Neerah ta iya furtawa kenan cikin ƙaramar murya saboda tana gudan kada tayi ihu su Abba su dawo su gansu a haka Sadauki ya kunyata lamarin da zai iya kawo nak'asu ga samun damar mallakan junarsu a matsayin ma'aurata tare da hawa karagar mulkin Birnin Mungaye. Jikinta ne ya soma rawa cikin jin shiga matakin da bata san ta inda ya afku ba wato feeling da take cikawa su Lailah bakin bata cikin mata masu motsawar sha'awa, duk in suka nutsa cikin hiransu na 'yamma, inda zasuyi ta tsokanar da cewa bata cika mace ba ne shi yasa. Juyatan da Sadauki yayi zuwa ƙasan shi cikin fita hayyaci yasa ta dawo ɗan tunanin da ta afka, sai dai ta makaro wurin kwatar kanta domin ya saka mata ƙarfi yana kaimata summba a zafafe a duk inda bakinsa ya sauka. *Alhamdulillah.* This is the end of free pages.🤩 Affuwan idan na b'atawa masu jiran shi a kyauta, hakan ya faru ne saboda wahalar da rubutu ke da shi gami da kashe lokacin ayyuka. Pay 300 only to 0468069082, Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence via 08132166848. *Yanzu labari ya soma.* *Ga dai Sadauki da Dr. Neerah, shin ko ya zasu ƙare? Wani Zalinci Sadauki ya aikata da ya zamo kalubale a rayuwarshi? Wacce Aljana ce wannan? Shin burinta na wulakanta Sadauki a cikin fadar birnin Mungaye na samuwa kuwa? Waye Sarkin Mungaye cikin Sadauki, Hud, Sardauna da ɗan dogarai Salis? Burin Mamma da Umma na samuwa kuwa? Sannan ga Tsibiri can na shirin kamawa da wuta. Wa zai kawo masu ɗauki? Shin ta ina Gimbiya Lina zata soma? Burinta na hayewa karagar mulkin Hatsabibin Tsibiri tare da kawo canjin mulkin Aldalci na cika kuwa? Shin itama Lima na samun damar mulkan Tsibirin? Me ye sirrin da Lina take b'oyewa? Shin ta yaya Hadimi Tsidau ke kub'uta? Waye Sadauki Gauɗu da dalilin mallakawa Gimbiya Lina sirrukanshi na tsafi? Shin Ifritu Baushe na yin nasarar ɗauke Mah tare da mallakan Gimbiya Lina kuwa? Buda na samun cikar burinsa na auran Lina da hawa kan mulkin? Ya Abun zai ƙare? Shin na mallakan tulun ruwan albarka da Zoben sihiri kuwa?* Waɗannan dama wasu bayanen duk suna tafe cikin cigaban labarin HATSABIBIN TSIBIBI( labari mai ɗauke da sashi biyu) A cikin farashi mai sauk'i #300 kacal. A turo ta asusun banki kamar haka 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, sai a turo shaidan biya ta wannan layin wayar: 08132166848. Thank you so much my fans. I said kada ku bani kunya dai.😊 Momyn Haske ne🥰 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels