An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BA MAHAUKACI BANE! NA BINTA UMAR ABBALE Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Ubangiji mad'aukakin sarki. Tsira da aminci su 'kara tabbata ga fiyayyan hallita Annabi Muhammadu S.A.W 'Kir'kirarran labari ne wanda ba'ayi don a ci zarafin wani ko wata ba. duk wanda ya ga ya yi dai-dai da rayuwarsa to a rashin sani ne. TSOKACI: Kasancewar Ubangiji ya halliceka da ji da ga ni tare da wadatacciyar lafiya, to kada hakan ya sanya ka d'auki kanka daban da sauran wanda aka hallita da wata larura makamanciyar wannan, Ubangiji ba yanda baya zartar da ikonsa, kuma yanda ya so haka shi yake faruwa. tabbas bawa baya shiryawa kansa rayuwa face wacce ya riski kansa a ciki. 1 KANO STATE GADAR SALGA Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar KANO Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da alamar sauri a tare da ita. Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."? Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda kunnuwanki a toshe! suke." Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake gabanta. A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki. Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko." Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da take miki ba." A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya. Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi tace."Baba gani Saliha tace kina kira na." Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai. Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba." Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci." Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a kwance da waya a hannunta tana game. Girgiza kanta kawai tayi ta bude ma'ajiyar kayanta ta dau'ko hijabi tasa a wuyanta ta fito falon. Ta kalleta da fadin."Dubu arba'in da hud'u ne man gyada galan d'aya manja ma galan d'aya kafin ki isa zan kira Garba a waya na sheda masa zuwanki ya tari a daidaita sahu ya sanya komai a ciki. Tace."To shikkenan Baba sai na dawo." Tace." Ki kula sosai da kudin hannunki yau Juma'a akwai turmutsutsu na jama'a." Kud'in ta ri'ke da kyau da fadin." Zan kula insha Allah. Cikin nutsuwa take tafiya har ta fito bakin titi can tsallake ta hango mutumin ta zaune a 'karkashin tsohuwar motar da yake zama tare da tarkacen kayansa na mahaukata! Girgiza kai tayi tana me tsira masa ido yana kwance kan wani tattararran buhu ya takure jikinsa guri daya jikinsa duk yayi fururu! kasancewar lokacin sanyi ne shiyasa al'amarin ya tu'azzura. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tana sake jin tausayinsa na bin ilahirin jikinta, hakika da tana da yadda za tayi da ta taimaka masa ya daina kwana 'kar:kashin mota duk yanayin da ake ciki na ruwa da iska anan yake wanzuwa tsayin watannin da yayi a cikin unguwar tasu. Cike da tsantsar tausayinsa ta d'auke kanta daga inda yake ta fara laluben abun hawa Juma'a ce shiyasa abubuwan hawa sukayi k'aranci a kan titin. Ihu! da hargowar yara ya sanya da sauri ta mai da kanta gurin, nan taga yara masu yawa sunyi masa rumfa suna tsokanarsa sai ihu! suke tare da fad'in "Baban- baba kazami! Baban -baba mai annakiya Baban-baba mai kashi a wando."! Shi kuma Yana zaune yana kallonsu fuskarsa a sake kamar koda yaushe idan yara suna tsokanarsa sai ya yi ta murmushi koda kuwa cikinsu za'a samu masu jifansa da duwatsu! ba zai yi 'ko'karin 'kare kansa ba. Ranta ya 'baci mutuk'a ganin yanda manya mutane ke wucewa wasu a kasa wasu abubuwan hawansu amma a cikinsu an rasa wanda zai tsawatarwa da yaran akan abinda suke. Ba tare da tayi tunanin komai ba ta tsallaka titin kai tsaye gurin ta nufa. Tana zuwa cikin 'bacin rai irin na kurame take musu fad'a tana korarsu........Sai suka kwashe mata da dariya suna nuna ta da hannu da fadin." Mu bama jin abinda kika cewa ke din kurma ce ko kuma bebiya?" Abun yayi mata ciwo sosai ta sake d'aga muryarta cikin yanayin saurin maganarta da yanayin hallitarta take gargadinsu da fadin." Ita din kurma ce kuma haka Allah ya halliceta idan da wanda ya isa ya sauya mata hallita a cikinsu sai ya d'aura aniya. Suka dinga kyalkyala mata dariya sunayi mata ihu! kawai sai ta durk'ushe a gurin ta fashe da kukan 'bakin ciki a wannan lokacin ledar kudin dake hannunta ta fad'i ba tare da 'bata lokaci ba wani matashi dake can tsallake yazo ya d'auke yayi gaggawar watsa yaran ya gudu da kudin a daure a leda. Ido kawai ya tsira mata tana tsugune a kusa da shi kanta a tsakanin kafafunta sai kuka take. Sosai yake jin zafin kukanta a cikin zuciyarsa to amma 'kudirin dake cikin zuciyarsa shi ya hana shi rarrashinta tun ba yau ba ya san da yarinyar a duk sanda zata gan shi a hanya ko a gurin zamanshi yana hankalce da irin kallon da take masa 'kwayar idonta kadai ita ke nuna masa da cewar ta damu da shi, duk da cewa wata magana bata ta'ba had'asu ba to amma ya yi imani da cewa ita d'in mai 'kaunarsa ce, Abinda tayi a yanzu shine ya tabbatar masa da zarginsa. A nutse yace."Ki yi hakuri kinji ko." Shiru bata d'ago kanta ba, jim yayi yana nazari wani 'karamin icce ya d'auka ya zungureta dashi. a firgice ta d'ago kanta idanuwanta sunyi fululu fuskarta har ta kumbura! Tsigar jikinshi ce tashi ya mayar da kanshi kasa yana wasa da icce hannunsa. Tsaye ta mike tana karkad'e jikinta gabanta sai dukan uku-uku! yake! Ta kalli gabas ta kalli yamma kudu arewa sai kawai ta d'ora hannu a ka ta kurma ihu! tare da fadin." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una! Ya mike tsaye da sauri yana kallonta so yake yayi magana amma jama'ar da suka fara taruwa a gurin suka hana shi idanuwanshi kawai ya zuba mata. Haladu wanda ya kasance ma'kocinsu ya 'karaso gurin da fadin."Ke Shahida menene? me kike a gurin wannan mahaukacin."? Cikin kuka tace." Zuwa nayi na kori yaran da suke tsokanarsa shine suka sace kudin kuma Baba Asabe ce ta aike ni bakin asibiti na saro mata man gyada." Yace."In ban da shashanci irin naki da hauka yaushe zaki iya watsa yaran da suka dad'e suna tsokanar wannan shashashan mutumin nan wanda bai san ciwon kansa ba, shashahar banza kawai gashinan garin hauka kin janyowa mutane asara to kada kiji da wai sai na fad'a mata yanda akayi komai ya faru." Tana kuka take fadin." Don Allah kayi hakuri kada ka fada mata ." Tsaki yaja ya gyara zaman daddumar dake kafad'arsa ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Ganin haka yasa mutanan dake gurin suka watse. Komawa yayi ya zauna tare da rungume hannuwansa a kirji, Ta kalleshi da fadin." Baban- Baba Don Allah baka ga wanda ya daukar min kudi ba?" Girgiza kansa yayi alamun bai gani ba, hawaye suka sake zubo mata tace."To ko zaka duba min cikin takarcen kayanka ko Allah zai sanya suna ciki." Beyi mata jayayya ba ya fara dudduba tsummokaran dake gurin yana musu filla-filla babu komai sai tarin ledoji na pure water da sauran robobin lemo da yake tarawa. Ba tare da tsoron komai ba tazo ta tsuguna daf dashi tana sake hargitsa ledojin babban burinta ace taga ledar dake d'aure da kudin Baba Asabe. Sosai yake mamakin rashin tsoron yarinyar da yawa yara duk fitsararsu daga nesa suke tsayawa su tsokane shi, basa iya kusantar gurin da yake duk da cewa baya doke-doke amma hatta da manya basa iya zuwa inda yake amma abun mamaki ita ba taji tsoronshi ba tazo ta tsuguna kusa dashi duk da ta san cewa shi din ba mai cikakken hankali bane. Gabadaya jikinsa ya mutu wata iriyar kasala da kaunar yarinyar suka sanya shi kasa dauke idonsa daga kanta. Ta kalleshi da jajayen idanuwanta da karfi tace."Babu kudin sun sace ban san wane irin hukunci Baba Asabe za tayi min ba." Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda alamun yana bata hakuri. Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya. Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa! Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a. Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu. Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa. Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta. Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?" Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake kansa. Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?" Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi." Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai! Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru. Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga ne?" Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba. Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada mata. Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace." Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau." Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san kansa ba." Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina. Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali. Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da kaina na duba kudina yau koni ko shi duk haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai " Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.'' Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da mayafi. Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin neman gira a rasa ido ni dai na fada miki. "Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana 'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare a tare. Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai tayi har ta k'araso inda take, "Don ubanki abinda ki kayi min kenan? ta fad'a tana kokarin kai mata duka! tasa hannu ta kare tana kallonta da idanuwanta da suka taru da ruwan hawaye. cikin masifa ta ce."Tashi muje gurin mahaukacin daya sace min kudina." Cikin k'okarin kare kanta ta bude baki za tayi magana.......ta buga mata tsawa! wacce ta sanya babu shiri ta mike tabi bayanta tana me cigaba da aibata ubanta wanda bai san abinda yake faruwa ba. Har suka isa bakin titin tana surutai! jama'arta sai tambayarta suke abinda ke faruwa tana tafe tana basu amsa wasu dariya kawai suke su wuce wasu kuwa bin bayanta suke domin kashe kwarkwatar idonsu. Yana tsaye da wata jarka a hannunsa da alama gurin yake so ya bari, katamau! ta rike hannunta suka 'karasa gurin da yake. Tsira musu ido yayi yana kallo. ta kalleshi da niyyar yi masa tijara! dafin idanuwansa ya sanya jikinta mutuwa sai ta gaza furta komai kawai tayi 'kasa da kanta. Kallon yarinyar ya yi suka hada ido da ido, sai tayi gaggawar saukar da nata idon sakamakon mutuwa da jikinta ya yi a cikin k'wayar idonshi akwai wani sirri wanda shi kanshi bai san yana dashi ba. Can 'kasan ma'koshi ya ce." Menene ko za ku duba kudin ne?" Kai kawai ta iya d'agawa har yanzu kanta na kasa ta kasa kallonshi, Baba Asabe tayi namijin kokari gurin Fad'in." Kaga Malam dakata! ba mu yarda da cewa kai mahaukaci bane kazo cikin wannan unguwa ne da mummunar manufa don haka kud'ina dubu arba'in da hudu daka sace wallahi sai ka fito dasu ko kuma ka kwana a police station." Ya zuba mata kyawawan idanuwansa masu cike da kwarjini. Dalladi dake bayansu a tsaye yace."Uwar towo wannan magana ki barta kawai ko kin ta'ba ganin anyi sharia da mahaukaci ni na tabbata da cewa Baban-baba ba zai sace miki kudi ba, to yayi me da su? mutumin da ba shi da hankali idan kuma baki yarda ba sai ki dauki mataki amma ina mai tabbatar miki da cewa wahala zaki sha domin kuwa duk inda za ki je babu wanda zai saurareki. Ta girgiza kai nifa ba zan yarda ba wallahi." Yace."Shikkenan sai kiyi abinda za kiyi." Gurin ya bari bayan ya gama maganarsa, sai kawai ta hankad'a yarinyar kusa dashi da fad'in "Maza shiga k'arkashin motar ki duba min kud'ina idan zai kashe ki da duka bai dameni ba." Ba tare da wata fargaba ba ta shige k'arkashin motar ta fara dube-dube duk da tasan kudin basa gurin. Kallonsa tayi da fad'in." 'Yan sanda zan dauko maka yanzu ai gamu ga police station haukanka na 'karya ne" Cikin sauri ta bar gurin. Yana tsaye ya rungume kirjinsa da hannuwansa idanuwansa a kanta a lokacin da take karkashin tsohowar motar tana dube-dube. Jikinta ya jik'e da gumi ta fito daga 'kasan motar da 'karfi tace."Baba banga 'kudin b........Had'a ido sukayi yana kallonta jiki a sanyaye tace."Babu kudin a gurin." Kai ya gyad'a mata. sai ta matsa ta bashi guri ganin yana kokarin ture ta, ya shiga ya zauna tare da rungume gwiwarsa still idanuwansa na tsaye a kanta. Baba Asabe Cike da kwarin gwiwa ta isa station din duk ta zayyane musu abinda yake faruwa. Koda sukaji abinda take tafe dashi sai suka shashantar da maganar saboda sun riga sun san sharia da mahaukaci sai wanda ya shirya bayan haka kuma duk tsayin watannin da mahaukacin yayi a unguwar ba'a ta'ba kawo musu shi da sunan ya aikata mummunan aiki ba. saboda haka sai suka sallameta tare da kafa mata hujja da cewa ko don gaba ta daina cewa za ta yi sharia da mahaukaci domin kuwa al'kalami ya sauka daga kan duk wani mai matsalar k'wakwalwa. Jiki a sanyaye ta fito daga station din ranta duk a bace! tana tafe tana zancan zucci da irin hukuncin da za tayi wa yarinyar. Ita kuwa Shahida tana nan tsaye a gurin gabanta sai faduwa yake ta san halin Baba Asabe akan kudi babu shakka yau sai buzunta. A jikinta take jin yana kallonta amma tsabar fargaba ta kasa juyawa ta kalleshi ta fahimci a cikin haukan nasa harda kallo a ciki to idan ba haka ba menene abin kallo a tare da ita. Ya jima yana kallonta kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya hannunshi yasa ya ja gefan hijab dinta. Cikin wani irin yanayi ta juya suka hada ido. muryarsa ya daga sosai da fadin." Wacece ita?" Zuciyarta ta karye hawayen da take ta tattalinsu suka su'bce. A raunane tace."Kakata ce." "Ina iyayenki?" ya fad'a still idonsa na kanta, kai ta sunkuyar jin tana shirin fashewa da kuka, ya sake maimaita maganarsa. Murya na rawa ta ce." Mahaifiyata ta mutu Babana kuma yana can unguwar Ja'in da matarsa da sauran 'yan uwana." Zama ya yi ba tare da ya sake magana ba. A sace ta d'an Kalleshi da gefen idonta, al'amarinshi akwai abun mamaki a ciki maganarsa cikin nutsuwa babu alamun ta'bin hankali a ciki ko dai akwai wani abu da yake 'boyewa ne? gashi ba yaro bane da shekarunsa yanda take ganinsa ma kamar zai yi shekarun mahaifinta, Kallonsa ta sake yi taga ya rungume gwiwarsa da hannuwa biyu yana girgiza kansa can kuma sai taga yana 'yar dariya. Cikin faduwar gaba Ta ce." Baban-Baba kana jin yunwa ko?" Ba tare da ya kalleta ba ya daga kanshi. Ta ce." Yanzu a ina zaka samu abinci?" Ya kalleta na second biyu kafin ya kauda kansa. Wata maganar take shirin yi masa ta hango Baba Asabe ta tsallaka titi, ya kalleta cikin tsawa yace."Ki tafi ki bani guri." da sauri taja gefe tana kallonsa, ya dauki iccen dake gabansa yana nuna ta dashi. "Na ce dake ki tafi ki bani guri ko ba kya ji ne? Saurin barin gurin tayi tana waiwayensa. Sai girgiza kansa yake tare da wasa da iccen dake hannunsa, Hawayen tausayinsa ta goge tana tunanin a inda zai samu abinci ya ci watakila kan bola zai je ya yi tone-tone ya samu lalataccen abinci ya ci tunda mafi akasari da haka mahaukata 'yan uwansa suke kawar da yunwar da ta damesu. A soran gidan ta samu ghana masgo kayanta kaf a ciki. Ta dinga jin masifarta daga gidan Saliha na taya ta. Jiki a sanyaye ta shiga da sallama a bakinta, ta kalleta da fadin." Na gama zama dake ki tafi duk inda za kije mara mutunci." "Baba kiyi hakuri tsautsayine kin san dai tunda kike aike na banta'ba zubar miki da kudi ba wannan ma kaddara ce." Tace." Ban san kaddara ba na fada miki na gama zama dake ki tafi can gidan Ubanki duk abinda za su yi miki dama tausayi yasa nake rike dake to tunda kin zama munafuka zama na dake ya 'kare Kije duk abinda Talatu za tayi miki ba zai dameni ba. Ta durkushe a gurin tana kuka da rokonta tayi hakuri tayi kunnan uwar shegu da ita kicin ta shige ta barta a gurin, ta kalli Saliha da fadin." Ki sanya baki tayi hakuri kinji." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da abinda take, A fusace! ta fito daga kicin din ta nufi dakin sai gata ta fito da bulala a hannunta ta riga ta san idan tazo babu abinda zai hana ta doke ta. dan haka da gudu ta ruga a guje ta fita daga gidan tana jin lokacin da ta sanya sakata ta koma ciki tana surutai. Babu yanda ta iya haka ta kama hanya domin tafiya gidan mahaifinta dake can Ja'in Tafiyar 'kafa za ta yi tunda babu kud'i a hannunta gashi akwai tazara mai tsayi tsakanin Gadar salga da Ja'in. Koda ta fito bakin titin hankalinta na gurin zamansa, babu shi a gurin sai tarin tarkacensa , sai ta tsinci kainta da kasa tafiya har sai da ya dawo da ledar biredi a hannunsa taga ya shige karkashin motar ya zauna. Ajiyar zuciya ta sauke cikin zuciyata Tace."Watakila wani ne ya tausaya masa ya siya masa biredin. Sai da taje Sabon titi na gidan 'kankara a kasa kafin ta samu wani d'an kirki ya taimaka mata ya rage mata hanya. [4/16, 3:47 PM] Bintu: Ta zo shiga gidan kenan ta yi karo da 'karamar k'anwarsu Walida tana d'auke da markad'an awara a kanta. kallon juna su ka yi sai kawai yarinyar taja tsaki ta wuce ba tare da tayi mata magana ba. Idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan wulakanci da 'kas'kancin da 'yan uwanta suke mata duk da cewa itace babba a cikinsu amma mutum d'aya ce take ganin girmanta. Gabanta na fad'uwa tayi sallama cikin gidan. Talatu tana kicin ta baza kwanuka tana rabon abinci yayin da Hadiza babbar 'yarta ke yanka musu salak da tumatur. ita kuma Jamila tana shanya kayan makarantarta akan igiya. Itace ta amsa sallamar fuska a sake tace."Auntymu kece ki ke tafe da wannan ranar.?" Hadiza ta kalleta a watse ta mayar da kanta kasa tana cigaba da gyara salak din dake gabanta. Jamila tace."Talatu ga fa Aunty Shahida tazo." Ba tare da ta juyo ba tace."To Ubanta zan yi mata kome?" Jamila ta girgiza kanta ba tace komai ba taja hannunta suka shiga daki tana 'kokarin kawar da 'bacin ran dake damunta, ta tsani halin ko in kulan da mahaifiyarsu take mata a ganinta Shahida abar tausayi ce duba da maraicin da take ciki bayan haka kuma akwai nakasu na rashin ji a tattare da ita, babban damuwa yanda mahaifinsu yayi shakulatun 'bangaro da lamarinta da kuma lalurarta a matsayinsa na mahaifinta baya taimaka mata da komai gabad'aya ya sakarwa kakarta wacce ta haifi uwarta ragamar rayuwarta, bai san ci da sha da sutturarta ba, Uwa uba karatunta duk be san wannan ba, ta wannan fanni dole a jinjinawa Baba Asabe domin ita d'in maca ce mai kamar maza duk da nauyin ba akanta yake ba amma ta d'auka tana iyakacin 'bakin 'ko:karinta akan yarinyar. Tsaf Talatu ta gama rabon abinci amma babu rabon Shahida a ciki duk da cewar lokacin da ta zo gidan bata gama rabon abincin ba idan da ta yi niyyar sanya mata kwano zata san yanda tayi ta fitar mata da rabonta amma k'emagadas! tayi mirsisi ta rabe abincin kaf ta kira kowa ya d'auki nasa. Jamila a sanyaye ta nufi dakin da nata kason a hannunta. Kamar ta san niyyarta sai ta kira sunanta, taja ta tsaya tana kallonta, fuska a tsuke tace." Ki ka shiga da abincin nan ku ka ci tare sai na tsine miki albarka." Dama sarar ta kenan daga zarar 'ya'yanta sunyi mata laifi sai tace zata tsine musu. A marairaice tace."To yanzu ita Shahidan haka zata zauna Talatu kada fa ki manta itama tana da hakki a gidan nan tunda duk ubanmu d'aya." Ta ciko hannu da shinkafa 'yar manja wacce taji salak da yaji ta watsa a bakinta tana taunawa ta ce." Kafin ki san haka na rigaki sani ban yi niyyar bata abincin ba shiyasa nayi rabo babu ita idan kuma ki kayi wasa wannan na hannun naki zan k'wace na bawa almajirai kema kiyi asara." Hadiza ta kalleta da fadin." Banza mara kishin uwarta shin har kin manta labarin da Talatu ta ba mu a lokacin da suka zauna tare da mahaifiyarta yanda ta azabtar da ita amma shine saboda rashin kamun kai kike tausayin abinda ta tafi ta bari ai wallahi ni da wannan kurmar yarinyar har abadah." Jamila ta girgiza kanta da fadin." Ke Hadiza jahilci ne yake damunki wallahi ni ina ruwana da irin zaman da su ka yi kawai 'yar uwata na sani saboda duk rintsi ba'a sanjawa towo suna Shahida 'yar uwarmu ce dole ko mun 'ki ko mun so." Hadiza ta fusata! ta hau d'ura mata ashar wai ta kira ta da jahila. 'Kokarin tashi take taje inda take tsaye ta doke ta uwar ta hana ta. Sallama ya yi cikin gidan yana sanye da manya kaya sabuwar shadda mai uban surfani, kansa sanye da hula zanna bukar idan ka ganshi sai ka dau'ka wani hamsha'kin mai kud'i ne nan kuwa tsabar 'karya ce da fafar tsiya Jamilu kenan wanda abokansa suke kiransa da Ya hajuj! tsabar 'karya da nuna shi wani ne. ya sanya sunanshi ya 'bata a ko'ina ake kiransa da Hujaj! Ya kallesu da fuskar shannu "Menene na ganku a tsaye ke Jamila ya akayi?" Da sauri tace." Baba ka ga Aunty Shahida ce tazo shine Talatu ta raba abinci babu ita wai don na d'auki nawa zamu ci tare shine fa suka had'u suke zagina. Ya gyara zaman babbar rigarshi da fadin." Ina Shahidan take? Tace."Tana daki a zaune.'' Tsaki yaja da fadin." Shige ki je kuci abincin tare." da sauri ta shige dakin. Talatu ta kalleshi da fadin.'' Yau kuma? ba tare da yace mata komai ba ya bude dakinsa ya shiga ya turo k'ofa. Kasan kafet ya zauna ya cire babbar rigar jikinsa, hannu yasa cikin aljihu ya shiga fito da kudi daure da kyaure bandir biyar ne ya zube a gabansa yana wani irin murmushi babu shakka yau kura tayi nama ya tashi da Sa'a ko da yake dama sana'ar tasu ta gaji haka yau kai gobe wanin ka da yake shi akwai nasibi duk ranar da suka buga wasa baya fad'uwa, wasan yau yafi na kullum domin ya samu kudi masu yawa, burinsa a yanzu bai wuce siyan babur ba, zai sayi vespa d'an 'kasa irin wanda manya alhazawa suke hawa a duk lokacin da ba suyi ra'ayin hawa mota ba. Tura kofar dakin tayi sai yayi saurin boye kudin a bayansa. Tayi sallama tare da tsayawa 'kerere a gabanshi, yace."Kefa dadina dake rashin ladabi meye haka kin shigo ba tare dana nemeki ba kin tsaya min 'kerere a ka." Ta gyara daurin zaninta da fadin." Ka san kwanan zance ai bana so muyi hayaniya da kai a gaban yara saboda haka ka bani kudin dana ranta maka." Yaja tsaki da fadin." Wai shin har nawa ne kudin naki?" "Dubu biyu da dari hudu ne kada ka manta yau kwananka uku baka ba da ko kwabo ba tun daga safe har dare ni nake d'awaniya da gida to tunda Allah yasa yau ne cikar alkawarin da kayi min ba zan fita ba sai ki biya ni kud'ina." Kashingid'a yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa. Tace."Jamilu meye haka zaka dinga yi min murmushi kada fa kayi min wata magana don wallahi baza mu wanye lafiya ba." Ya sosa gemunsa da fadin." Ki je yanzu zan fito zan baki kud'inki ina jin shikkenan ko?" Kai ta girgiza da fadin." Ba fa zan fita ba sai da kud'ina a hannu. Ya mike zaune da fadin." Idan kika matsanta min wallahi zan ha naki ni nace kije zan baki idan na fito sanin kanki ne bana san takurawa." Ta yi jim tana kallonsa kafin ta gyada kai da fadin." Na kawo maka abincinka ne.? Sai da ya mula tukkuna ya ce."Aa ki bawa Jamila da Shahida suka 'kara ni na koshi." Ba tare da tace komai ba ta juya ta fita, koda ta fito daga dakin a maimakon tayi abinda yace kai tsaye kicin din ta nufa ta dauko abincin nasa tasa a gabanta ta dinga ci sai kace jaka, Walida dake sud'e hannu tace."Talatu d'an k'ara min wallahi ban koshi ba." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kai loma bakinta, yarinyar dake mara kunya ce ta yatsine fuska da fadin." Talatu ki dai ci a hankali kada ki 'kware wannan loma haka." Bud'e baki tayi za tayi magana aikuwa ta shaki shinkafa ta hanci tari ya sar'ke ta ta dinga yi hawaye na zuba, yarinyar ta tashi ta bar gurin ba tare data debo mata ruwa ba. Shahida da Jamila haka sukaci abincin ba tare da sun 'koshi ba, suka fito domin wanke hannu nan suka ga Talatu tayi wurjajan ido yayi jawur har yanzu da sauran tarin amma saboda zulama bata daina cin abincin ba. Shahida ta banka mata harara ta wuce dama duk sanda tazo gidan abinda ke shiga tsakaninsu kenan harar juna, sai taso take gaishe da ita, Hadiza ta fito daga d'aki Talatu tace."Kinga 'yar iskar yarinyar nan saboda ban zuba mata abinci ba take hararata. Hadiza tace."Take harararki kamar sa'arki." Tace."Au! keda baki ta'ba gani ba? ai a duk san da zata zo gidan nan hararace take shiga tsakaninmu." Bagazan! bagazan ta nufi inda take ta juyo da ita suka fuskanci juna, murya ta d'aga da fadin." Don Uwarki mahaifiyarmu sa'arki ce?" Jamila tace."Hadiza neman fitina bashi da amfani me kuma tayi miki? Ta juya tana yi mata bayani yayin da ita kuma Shahida ta juya inda Talatu ke zaune ta dinga watsa mata muguwar harara tunda ta lura da abinda bata so to ta daura d'amarar 'bata mata rai. Talatu ta rike ha'ba da fad'in.'' Ni kike harara don Ubanki! ta dauke kanta tana jan tsaki tare da niyyar barin gurin. Hadiza ta fizgo kafad'arta tana nema ta kai mata duka, sai ta rike mata hannu cikin yanayin maganarta tace."Hadiza ki kiyaye ni wallahi ni nafi karfin ki dake ni." Ta fizge hannunta tana d'ura mata ashar!! Ya fito d'aga daki da yanayin bacci a tare dashi ya ce." Baku da hankali ne? sukayi shuru ya kalli Shahida da fadin." Me yasa duk lokacin da ki kazo gidan nan sai anyi rigima dake? Ido ta zuba masa, yaja tsaki da fadin." Ana magana kin tsare mutune da ido kizo ki tafi inda ki kafi wayo." Da yake da 'karfi yake maganar duk taji komai sai tace." Ai na dawo gidan ubana da zama." Talatu ta zabura! ta mike tsaye da fadin." A'ina.? Babu tsoro tace." A nan." Jikinsa ya mutu ya ce."Kinyi mata laifi ko?Fashewa tayi da kuka ta durkushe a gurin!. Talatu cikin masifa ta ce."Wallahi ko kukan jini za kiyi baki da gurin kwanciya a gidan nan aikin banza kawai." Ya kalleta da fadin." Kin san dai 'yata ce ko?" A fusace! Tace."Na sani amma wallahi ba zan zauna da ita ba." Ya girgiza kai da fadin.'' Duk lokacin da nayi ra'ayi 'yata zata dawo hannuna da zama." Tana numfarfashi! tace."Ni kuma a ranar zan tattara kayana na bar maka gidanka domin kuwa ba zanyi kishi da uwarta nazo nayi da ita ba. Murya ya d'aga gurin kiran sunanta, ta d'ago kai tana kallonsa fuskarta gaje-gaje da hawaye, Ya ce."Tashi muje ki fad'a min laifin da ki kayi mata." Ta mike tana share hawaye tabi bayansa zuwa dakinsa, kallon banza Talatu ta bisu dashi tayi k'wafa tana girgiza kanta. Duk abinda ya faru ta sheda masa tana kuka, ya ce."Kiyi hakuri kinyi sara a bakin ga'ba matsalar Baba Asabe kudi za'a biyata kud'inta" Cikin izzah! da nuna isa yayi maganar kamar wanda yake da burin biyanta kud'in dawainiyar da tayi masa daga farko har 'karshe. Yasa babbar rigarsa da fadin." Tashi mu tafi." Ta mike da sauri ta fito, shima ya fito yana kokarin kulle kofa tazo ta ta rike k'ugu tare da jan tunga a gabansa. Hannu yasa cikin aljihu ya zaro sabbin 'yan dubu-dubu uku ya watsa mata. Ta tsuguna tana tsincewa da fad'in." A banza dai duk abinda za kayi ni na rufa maka asiri." Ya gyara zaman hularsa ya kama hanyar fita ba tare da ya tanka mata ba. Ta kalli Jamila dake kan rijiya a zaune ta ce." 'Yar uwata na tafi na gode da zumunci." Jamila tana murmushi tace."To Aunty Shahida ki gaishe da Baba Asabe da kyau." Tace." Za taji da kyau." Hadiza tace."Banzaye kawai wannan munafurcin naku babu inda zashi." babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Shahida tabi bayan mahaifinsu ita kuma Jamila ta shige daki tana jiyo irin zagin da sukewa Shahida tamkar maguzawa! Jamilu Ya hujaj! mutum ne mai fara'a da wasa da dariya shiyasa yake da jama'a yara da manya duk inda ya gifta za ka ji ana fadin "Ya Hujaj! Shi kuma ya dinga washe baki kenan yana dariya idan da kudi a jikinsa ko nawa ne sai sun k'are domin bai iya gwaninta ba kyautar dubu biyar a gurinsa ba abu ne mai wahala ba, mutuk'ar yana da kudi to na bajinta ne amma fa gidanshi sai godiyar Allah domin da k'yar! yake bayar da kudin awo watarana matar gidan itace take cefane da yake tana awarar siyarwa shiyasa suke raba daidai. Da yawa mutane suna mamakin yanda yake sanya manyan sutturu da bajinta a waje amma 'ya'yanshi suna yawo babu sutturar arziki babu makaranta mai kyau, uwa uba kuma matarsa na sana'ar siyar da awara wannan dalilin ya sanya wasu ke zaginsa suna ganin arzikinsa ya tashi a banza tunda ya kasa sauke nauyin iyalinsa sai dai ya fita yana neman suna a gurin jama'ar gari. A zahiri sana'ar sa wacce kowa ya san shi ida ita sayar da takalma a cikin kasuwar wambai shago guda ne dashi yake bada sarin takalma na roba dana fata amma irin wanda akeyi a cikin kasuwar bayan wannan sana'ar tashi akwai wata wacce ya jima yanayi a 'boye kuma itace take kawo masa ma'kudan kudin da yake facaka dasu. Yau zaka gan shi da sabuwar mota amma idan aka kwana biyu sai gan shi cikin a daidaita sahu ko kuma a kafa yana tafiya idan ka tambayeshi sai kawai yace motarsa tana gareji ta samu matsala 'karya kamar kudin guzuri a gurinsa, wannan dalilin ya sanya jama'a suke d'aukarsa a matsayin mai rariyar hannu ko kuma d'an bariki har yanzu babu wanda ya hasaso irin sana'ar dake sanya abubuwan hannunsa suke salwancewa. Ko a cikin a daidaita sahun ma sai jan 'yar tashi yake da wasa yana tsokanarta wai lallai sai ta fada masa sunan saurayinta. Ita dai Shahida murmushi kawai take tana mamakin halayyar mahaifin nata, kwata-kwata baya jin nauyi da kunya idan yana wasu abubuwan. Da yake yamma tayi ya sanya titin ya cunkushe da ababan hawa bayan jama'ar dake kai kawo a gurin. Duk wanda yake cikin garin KANO ya san cewa titin JAKARA yana bukatar gyara daga mahukunta, amma anyi shakulatun 'bangaro dashi duk da irin gudumawar da matasan unguwar ke bayarwa a lokocin za'be amma ko wane d'an takara daga zarar ya samu abunda yake so sai ya manta da wad'anda suka sha masa wahala. mai adaidaita sahun yace."Alhaji ko zaku sauka anan ne yamma tayi gashi gowslow nan yaki sauki. Yace."Aa akwai sauran tafiya kayi hakuri ka shiga damu ciki, Yace."To shikkenan amma zaka 'kara min wani abu." Yace."Babu damuwa." Da karfi! tace."Subahanallahi." hankalinsu ya dawo kanta kokarin fita take daga babur din ya rike hannunta yana tambayarta, ta nu na masa shi wanda yake can tsallaken titi wani mai babur ya kusa buge shi jama'a har sun taru a kansa. Hawaye ta share tana fadin." Allah ya kiyaye da tuni mai babur ya buge shi Allah sarki Baban- baba." Yace."Ke wai baki da hankali ne kike magana ke kadai. Mai babur din yace."Alhaji baka lura bane ai mummanan al'amari ne ya kusa faruwa akan wancan mahaukacin dake tsallaken titin can.'' Yaja tsaki da fadin." Ni ai ban lura wallahi ba kaji yanda hankalina ya tashi ba ke ina ruwanki da mahaukaci Shahida." Yana kallonta yake maganar. Hawaye ta share da fadin." Haka kawai nake tausayinsa." Tsuke fuska yayi da fadin." Malama shige mota mu tafi bana son shashancin banza a garin tausayi ake cutarku wancan mutumin da ka gani ba mahaukaci bane akwai manufarsa. Ta share hawaye da fadin." Eh Baba nima bana masa daukar mahaukaci tunda wani sa'in duk abu na masu hankali yana aikatawa rashin galihun da yake cike ne yake damuna, da za'a samu wasu masu imani da tausayi su taimaka masa da abin yi Abbah ka duba fa kaga kayan jikinsa duk daud'a duk sun yage fuskarsa bakikirin takalmin kafarsa ya sud'e ya tsinke kullum karkashin mota yake kwana rana zafi iska ruwa babu wanda ya damu dashi da ci da shan sa." Yace."Shahida Irin wad'annan mutanan da kike gani basu da gaskiya shiyasa Allah yake mayar dasu haka watakila akwai wani mugun abun da ya tafka wanda yasa Allah ya nuna masa kuskuransa saboda haka idan za ki yi tausayi da imani ki tausayawa 'kananun yara ko kuma marayu ko nakasassu irinki amma ba irin wad'annan mutanan ba." Direba yace."Gaskiya ne Alhaji nima na jima ina mamakin mutumin nan da yake ina yawan shigowa unguwar nan ina ganinsa sai nayi ta mamakin yanda akayi rayuwarsa ta lalace haka koda yake duk mutumin da bashi da gaskiya yakan 'kare rayuwarsa a firgice ba tare da ya san ina ya dosa ba." Hawaye ta share tana jin zafin magangansu tace."Abbah ku dai kuyi masa Addua dashi da masu lalura irin tashi watakila kuma babu d'aya daga cikin abunda kuke zargi mybe jarabtace daga Ubangiji." Murmushi yayi ya dauko tafkekiyar wayarsa yana dubawa yace." Shahida irin halinku daya da mahaifiyarki Allah ya gafarta mata." Ta amsa da ameen tana goge fuskarta. Suna zaune a tsakar gida ita da Saliha suna gyaran kayan miya suka shiga gidan. Koda ta amsa sallamarsu sai kawai ta mayar da kanta kasa ta cigaba da abinda takeyi tai bala'in shan kunu! Da yake ya iya Siyasa sai ya cire takalmansa cikin ladabi da 'yar dariya a tare dashi yace."Baba sannu da aiki." Ciki-ciki ta amsa ita kuwa Saliha ko kallonsa ba tayi ba ballanatanta ta gaisheshi hakan ya 'bata mata rai sosai sai itama ta kudiri aniya a zuciyarta kan cewa duk sanda babanta yazo gidan ta daina gaishe shi. Da fara'a a tare dashi yace."Ai dawowata kenan na samu yarinyar nan a gidan shine take sheda min abunda ya faru har kika kore ta daga gidanki haba Baba ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar." Hannu ta d'aga masa da fadin." Dakata! Jamilu kazo ne kayi min dadin baki ko kuma kud'ina kazo ka biya ni bana son neman gidin zama ko kuma dama can hakkin rike yarinyar nan a hannuna yake?" Maganar ta 'bata masa rai amma sai ya basar yace."Haba Baba ki kwantar da hankalinki muyi magana ta fahinta mana ake rasa mutum ma ballanatana kudi." Tsaki! taja tana cizge alayyahun dake gabanta ta ce." Mutuwa dole ce amma da gangan yarinyar nan tayi min wasarere! da kudi har 'barawo ya sace saboda haka ka tashi ka bani guri bana bukatar tsari da dadin baki mutukar ba biya na kudi za kayi ba." Ya girgiza kai har ila yau da murmushi a fuskarsa yace."Wai shin ma nawa ne kudin naki.?" Ta kalleshi she'ke'ke! kafin tace."Kaji fa! kamar gaske har wani tambaya kake kamar wanda zai iya biya." Dariya yasa baka ta'ba ganin 'bacin ransa saboda ya iya siyasa yace."Ko ba zan iya biya ba ai yana da kyau na sani." Ta'be baki tayi da fadin." Babu amfanin na fad'a maka tunda ba iya biya za kayi ba." Ya gyad'a kanshi yana kallonta minti biyu ya giciye yana gyara babbar rigarsa ta zuba masa ido tana kallonsa ya zaro yan dubu-dubu sabbi kar dasu har wasu na zubewa a kasan gurin. Cike da mamaki take kallonsa yana irgawa cas ya cake mata dubu hamsin a gabanta ya gyara zaman babbar rigarsa da fadin." Gashinan duk da na san ban isa na biya kudin hidimar da akayi min ba ayi hakuri da ni da hali na na san anyi min kokari." Kunya ce ta rufe ta sai ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai ba har ya gama maganarsa ya fita daga gidan. Ganin haka yasa Shahida shiga daki ta kwanta kan gado abu biyu suka dame ta irin rayuwar k'as'kancin da take a tsakanin 'bangare biyu da kuma al'amarin *Baban- baba* daya tsaya mata a cikin rai. Hawaye masu zafi suka dinga karakaina a saman fuskarta hakika maraici bala'i ne tabbas da uwarta tana raye a duniya ta san ba za tayi irin wannan rayuwar ba, Baba Asabe itace ta haifi mamanta itace kuma ta haifi Kawu Musa mahaifin Saliha kenan amma ba tasan me yasa take fifita Saliha a kanta ba, Gashi dai duk ita ta haifi iyayensu amma tafi son Saliha a kanta duk abinda Saliha za tayi daidai ne a gurinta amma ita abu kad'an idan tayi sai ya zama laifi. Ta shigo dakin ta sameta tana kuka, sai jikinta ya kara sanyi murya ta d'aga da karfi ta ce."Kukan me kuma kike bayan ubanki yazo ya fanshe ki ashe dama yana da kudi mugunta ce take sa baya zuwa ya bani wani abu duba da irin dawainiyar da nake dake ko tausayin tsufa na ba ya ji." Ta mi'ke zaune cikin 'bacin rai da masifa irin ta kurame! tace."Wai shin Baba ni d'in bare ce a gurinki? ko kuwa bake kika haifi uwata ba?" Ta rike baki tana kallonta da fadin." Ni kike wa tsawa yau kuma tambotsan naki a kaina zaki sauke shi?" Tace"Ni tambayarki nake ina so ki bani amsa? Tace."Ni ce na haifi Uwarki na kuma Haifi Musa su biyu kacal Allah ya ba ni sai me kike so kiji.? Tace."To me yasa kike 'bakin ciki don kin kula dani kin ciyar dani kin tufarta dani don kinyi min d'awainiya shine kike gorantawa ubana ai sai yana dashi zai zo ya baki." Cike da dumbun mamaki tace."Shahida yau ubanki kike fifitawa a kaina.? Tace."Kada kiyi min mummunar fahinta Baba ina so na nuna miki Kuskuran da kike aikatawa kada ki d'auka bana fahimtar komai duk abinda kike ina lure dake kin fi k'aunar Saliha a kaina meye dalili? ko don ita ubanta yana baki kudi ni kuwa uwata ta mutu bata raye babu abunda take tsinana miki shine kike gallaza min saboda kawai tsautsayi ya ratsa an sace kud'inki shine har zaki tattara min kayana ki watsa waje wai kin kore ni Haba Baba ke baki ji kunya ba." Baba Asabe bakinta ya mutu kallonta kawai take ta cigaba da cewa." Tunda kika dasa sayar da man gyada a gidan nan ni nake zuwa na saro miki kuma bant'ba zubar miki da kudi ba sai wannan karon amma saboda rashin tawakkali kika fita duniya kina zage-zage kowa yana kallonki ai wannan abun kunya ne." Baba Asabe ta fashe da kuka tasa gefen zaninta ta fyace hanci ta ce."Lallai Shahida wuyanki ya isa yanka ni kikewa rashin kunya ko kuma dai Jamilu da Talatu sunyi miki hud'uba akaina." Tace."Ni ina ruwana da Talatu itama ai ba k'aunata take ba kuma Abbanmu ba zai zuga ni nayi miki rashin kunya ba." Ta goge fuska da fadin." To babu laifi tunda a karan kanki ki kaga dacewar hakan na gode." Tana 'kare maganarta sai ta kama hanyar fita tana goge fuskarta. Komawa tayi ta kwanta tana jin wasai a cikin ranta dama abubuwan da ake mata a gidan yana damunta yau dai ta amayar da abunda yake cikinta ta samu sa'ida. Ta shigo d'akin ta tsaya a kanta cike da tsageranci ta d'aga murya da fadin." Shahida ke marakunyar ina ce da zaki dinga farfad'awa Baba magana kamar wata sa'arki." Dama a ciki take da ita sai ta zabura! ta mike tsaye jikinta har tsuma! yake cikin yanayin maganarta tace."Mara kunyar gidanku ce! nace mara kunyar gidanku ce idan kina da mataki ki dauka." Saliha ta tsorata domin ta san halinta idan tana cikin bacin rai! bata lank'wasuwa kuma idan fada ya ratsa a tsakaninsu da wuya take kai labari domin lilis! take mata. Sai taja baya, bata daddara ba tace."To mara kunya Da kika mike tsaye kina wani zabura! duka na za kiyi ne kin san dai ni ba sa'arki bace." Tace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganinki ni duk wanda ba zai ja girmanshi ba to zan hau kai na taka kuma ke baki cancanci na baki girma ba saboda kema baki da ladabi." Tace."Don Ubanki ni ce mara dalabi.'' Tace."Ubanki dai domin uba bai fi uba ba ehe.! Saliha ranta ya 'baci kawai sai ta fitar da hannu ta kai mata duka, ai kafin kice me! ta cukumeta ta matseta jikin bango! tana dukanta ta ko'ina." Saliha ta dinga ihu! tana kakari tare da kiran sunan Baba wai tazo ta ceceta. Ita kuwa Shahida dukanta kawai take sai kace wata mai iskokai. Hankali a tashe ta shigo dakin tana fadin." Sai da nace ki kyaleta saboda kinfi kowa sanin halinta idan tana irin wannan halin babu maganar wanda ta ke ji kuma 'karfi ku ba daya bane kin girmeta amma ta fiki 'karfi duka take miki." Saliha na ihu! take fadin." Ki janyeta ni ba surutu za ki yi ba ta matse min wuya zata kashe ni." Cikin rarrashi da kwantar da kai tace." Yarinyar kirki yi hakuri ki saketa ai ta daku kada kiji mata ciwo kinga k'arfinku ba daya bane kiyi hakuri ta daina yi miki katsalandan a cikin al'amuranki." Banza tayi mata ta cigaba da dukanta tana mintsininta! Baba ta cigaba da banbanki tana kwantar da kai da 'yar murya tace."Shahida kinga bani da lafiya kada wannan 'bacin ran yasa ciwona ya tashi yau da 'kyar zan iya bacci sakamakon wannan al'amari banji dadin maganganun da ki ka fad'a min ba." Ta fashe da kuka tana cigaba da maganar daso ta tabbatar mata da cewa abun yana ci mata towo a kwarya. Ganin yanda take kuka ne yasa ta saketa ta koma gefe tana mayar da numfashi, Saliha data samu kanta sai ta wawuri! wani gwangwani da Baba ke ajiye-ajiye a ciki ta kai mata duka dashi da fadin." Shegiya mayya 'yar mai dattin hula." Da yake 'kasa-'kasa tayi maganar yasa ba taji ba, Baba ta buga mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita, tana numfarfashin wahala ta fita d'aga dakin. Baba ta rufa mata baya ba tare da ta sake wata magana ba. [4/19, 10:24 AM] Bintu: Ya hujaj! bayan ya rabu da amaryarsa da wata uku sai ya hango wata 'yar dumur-dumur! mai cikar kirji fara tas da ita amma ba ta cika kyau a fuska ba dan Mariya ma ta fita kyawun fuska, to da yake yana da kudi a hannu bai sha wahala gurin siye zuciyar Talatu ba, dama ubanta talaka ne basu da komai koda yaje neman auranta basu wani tsananta binkice ba suka dauki 'yarsu suka bashi. Wannan karon ba'kin cikin da Mariya ta had'iya yafi wanda ta had'iya a lokacin da ya auri Hafsatu, Talatu fitinanniya ce ta ajin karshe gabad'aya ta kanainaiye shi ta hanashi gane fari da baki ita kadai yake gani a gabansa, iskanci iri - iri suke a gidan, Sai ya kasance Mariya ta zama 'yar kallo domin tunda Talatu ta shigo gidan shikkenan ta kar'be girki da mijin gabadaya tsayin wata shida itake juya gidan sai abinda take so za'ayi. Sai dai abinda Talatu bata sani ba shine duk ranar da ta tafi Unguwa shi kuma a lokacin yake samun damar shiga dakin Mariya yayi abinda yake bukata domin duk gigin da yake akanta ba wani cikakkiyar gamsuwa yake samu da ita ba, Yafi samun gamsuwar da yake bukata da Mariya. Cikin ikon Allah ciki ya samu kuma bai bayyana kanshi ba sai da yayi wata biyar, ita Mariyar ta san da zaman cikin a jikinta. kawai tayi masa shuru ne saboda tana gudun ta fada masa ya zubar dashi tunda tana ganin irin k'wayoyin da yake dubgawa matayensa. Aikuwa bala'i ne ya tashi a lokacin da Talatu ta farga da cikin tana kuka tana fadin." Ashe dama yaudararta yake yana kusantar Mariya gashinan har yayi mata ciki amma ita saboda mugunta duk sanda ta samu ciki sai ya bata magani cikin ya zube to dan haka wallahi ba zata yarda ba sai an zubar da cikin Mariya. Budar bakinsa sai yace."Ta kwantar da hankalinta shi wannan ciki ba nasa bane domin shi rabon da ya hada shimfida da Mariya har ya manta. Mariya tana share hawaye ta fito daga dakinta tana kallonsu a tsaye a tsakar gidan sai rarrashinta yake, Tace."Jamilu kaji tsoron Allah kaji tsoron ranar haduwar ka dashi, kai ka san wannan cikin na jikina kai ne ubansa amma ka ke shegenta shi. Ya nuna ta da yatsa da fadin." Rufe min baki munafurka Allah ta'ala har yaushe na kwanta dake da zanyi miki ciki ban yarda ba tun wuri kije ki nemi uban danki." Wani irin hawaye masu tsananin zafi suka shiga zuba a saman fuskata, ta dinga kokarin magana amma tsabar bacin rai ya hanata furta komai, a daddafe ta shiga dakinta, tasa hijabi ta fito. Ya kalleta ya watsar da fadin." Duk in da zaki tafi kije domin kuwa ba zan yarda da wannan cikin ba. Talatu zuciyarta tayi wasai dama babban burinta Mariya ta fita ta bar mata gidan ita kad'ai. Tsakanin Baba Asabe da Hujaj! rigima aka tafka ba kad'an ba! domin kuwa Baba Asabe cewa ita ba zata yarda da wannan 'kazafin ba sai ta maka! shi a kotu a maimako ya risina ya bata hakuri domin su samu daidaito a tsakaninsu, sai ya k'ara fusata yace idan kotun k'oli zata kai k'ararsa taje ta kai babu abunda ya dame shi. Baba Asabe kai tsaye kotun musulunci ta nufa ta d'auki lauya ya tsaya mata suka fara bugawa, da yake ita gaskiya duk inda take sai ta nuna kanta a take asirin Hujaj! ya tonu domin kuwa duk wanda zai bud'i baki a gurin ba zai fadi alkairinsa ba sai sharrinsa. Alk'ali ya tabbatar da shedu daga bakunan jama'a a take ya yanke hukunci kan cewa dole Hujaj! ya amince da wannan ciki domin addinin musulunci ne ya amince da hakan, koda bashi yayi cikin ba tunda har ya kasance a gidanshi a ka sameshi dole ya dauki d'an da za'a haifa a matsayin d'ansa, bayan haka kuma dole ya cigaba da kula da matarsa da cikin da take dauke dashi, Ci da sha da kula da lafiyarsu duk yana rataye a wuyansa. Mai sharia ya gama yanke hukunci ya buga katako alamun hukuncin ya tabbata, ya mi'ke. kotu ta tashi kowa na fadin albarkacin bakinsa. Bayan kwana uku ya samu takarda da biro ba tare da tunani da tsinkaye ba ya rubuta saki har uku da kansa yaje ya har gidan ya bada takadar ya futo abunsa. Baba Asabe ba ta iya karatun hausa ba, ita Mariyar ita ta karanta takardar a take a lokacin ta fadi a gurin, hankalin Baba Asabe ya tashi a wahalce aka kaita asibiti taimakon gaggawa akayi a kanta domin kuwa jininta ya kai k'ololowa gurin hawa. Haka Baba Asabe ta dinga kai kawo ita kad'ai dan ma dai tana da kudi a ajiye shiyasa ta samu saukin wasu al'amuran. A takaice sai da Mariya tayi sati uku a kwance a asibiti ta samu sauki likita ya dora ta akan magani tare da sharad'ai masu tsauri domin kuwa. hawan jini ga mace mai ciki babban matsala ne. Baba Asabe ta sake yun'kurin shigar da kara kotu domin tun sanda alkali ya yanke hukunci Hujaj! bai ta'ba zuwa ya kawo naira biyar a cikin abunda alkali ya yanke masa ba. Kawu Musa d'anta shine ya hanata yace ta bar maganar kawai su barshi da Allah domun duk yanda take tunanin Hujaj! ya wuce haka shaid'anin mutum ne, Sharia dashi bata da amfani. Baba Asabe ta hakura ta bar maganar suka kyaleshi da mugun halinsa, Bangaran Mariya kuwa sai addua domin ita kadai ta san irin kuncin da take ciki bata ta'ba tsammanin Jamilu zai tozartata irin hakaba. Allah al-musauwiru wanda bashi da tamka, ya fara saukar da ishara akan Hujaj! kasuwancinsa ya tsaya duk abinda ya ta'ba sai ya lalace ta kai ta kawo idan ya fita kasuwa haka zai wuni babu wanda zai zo gurinsa da niyyar sayan kayansa, Idan zai tafi gida sai ya ci bashi domin kuwa idan yaje gida babu kudi a jikinsa zasu kwana suna tafka rigima da Talatu. Wani abokinsa ya jashi gurin wani malami domin yayi masa duba acikin al'amuransa yaga abunda yake kai kawo. Kai tsaye malamin yace."Matarsa da ya rabu da ita itace mahad'in arzikinsa saboda haka idan yana so arzikinsa ya dawo tilas yaje ya dawo da ita gidansa. Jin wannan magana sai hankalinsa ya tashi ya dinga share zufa yana tunanin yanda za'ayi ya cigaba da zaman aure da Mariya bayan yayi mata saki uku. A hanyarsu ta dawowa gida Alhaji Shu'aibu ya kalleshi da fadin." Ya hujaj! naga duk ka tashi hankalinka wannan al'amarin fa duk mai sauki ne." Ya kalleshi cikin damuwa yace."Alhaji Sha'aibu ya kake kiran wannan al'amari me sauki saki uku fa nayi mata ta yaya zan aureta dole sai ta auri wani sannan zata hallata a gareni." Alhaji Sha'aibu yayi murmushi da fadin." Yanzu dai mu bari ta haihu akwai shawarar da zan baka." Yace." Alhaji zama cikin kuncin talaucin nan ya isheni wallahi." Yace."To ya za kayi kaine kayi ganganci ai irin wannan ba'a yanke hukunci kai tsaye sai mahukunta sun duba maka abunda ya dace da rayuwarka gashinan ka saketa ba tare da ka san itace abokiyar arzikinka ba." Hujaj! ya girgiza kai da fadin." Wallahi sharrin zuciya ne amma nan gaba dole na kiyaye a yanzu dai burina ta dawo hannuna ko arzikina ya dawo." Yace."Ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauki insha Allah. ***** Alhaji Sha'aibu shi ya cigaba da kwantar masa da hankali, amma duk da haka kullum cikin lissafin wattanin cikin yake sai da ta haihu sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu shi ya bashi bashin kudi wanda yayi wa 'yar da aka haifa siyayya, sannan kuma shine ya jagorance shi zuwan gidan, kunyar duniya ta isheshi sai sunkuyar da kai yake, Alhaji Sha'aibun ne mai k'ok'arin magana Baba ta kalleshi da fadin." Da dai banyi niyyar yi maka magana ba amma ta kama dole sai nayi inaso ka bude idonka sosai ka kalli wannan 'yar dake hannunka." Yayi ta maza ya daga kai ya kalleta da fadin." Ai tunda na kalli yarinyar nan na tabbatar da cewa ni ne ubanta saboda haka don Allah Baba ayi hakuri kada ayi tone-tone duk abubuwan da suka faru a baya tsautsayi ne amma na san ban kyauta ba. Ta girgiza kai da fadin." To naji maganarka wane suna kake ganin za'a sanyawa yarinyar ."? Da murmushi a fuskarsa yace."Sunan mahaifiyata nake da niyyar sanya mata Maryama kenan." Tace."Shikkenan Allah ya raya ta yasa cikon addinin musulunci ce." gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah." Da zasu tafi ya ajiye mata dubu biyar da fadin duk hidimar da ta tashi tayi da kudin kafin ranar suna." Ba tace komai ba har suka fita daga gidan, Ta girgiza kai da fadin." Kullum yana fama da malin-malin(babbar riga) sai kace limami amma shaid'ancisa yafi karfinsa. Itama Mariya dake uwar dakin maganar da take kenan, idan yana magana kamar mutumin kirki amma mugun halinsa yafi dubu! gabad'aya yanzu bata kaunar ta bude ido ta ganshi ta tsaneshi don dai kawai kaddarar aure ta ratsa a tsakaninta dashi babu yanda za tayi tunda ya kasance uban 'yarta dole tayi hakuri ta manta da abubuwan da suka faru a baya. Ashe rigima ce take jiransa a can gidansa. Ya shiga gidan cikin nishadi da walwala domin kuwa gani yake kamar Mariya ta dawo gidansa ta gama tunda Alhaji Sha'aibu ya fada masa shawarar da ya yanke kan cewa shi din ya amince zai yi (Auran kisan wuta) da ita zai saketa idan tayi wata daya ko biyu a gidansa, To tunda ya fada masa wannan magana yake farin ciki tabbas ya san Alhaji Sha'aibu ba zai cutar dashi ba. A tsaye ya sameta a tsakiyar tsakar gidan sai kace wacce aka dasa! tsoro ta bashi da sauri ya kira sunan Allah kafin ya fuskanci itace yaja mummunan tsaki da fadin." Talatu ke wace irin jahila ce zaki tsaya tsakiyar tsakar gida sai kace aljana ko wani siddabarun kike min a gida."? Ta fusata! dama a wuya take ta hayayya'ko! masa tana kumfar baki tace." Rufe min baki algungumi! munafiki duk halin da kake ciki na sani tsohuwar matarka daka saki ta haihu har kana siyayya kana kai wa jaririyar data haifa bayan da bakinka ka furta cewa ba kaine ubanta ba." Ya daga mata hannu da fadin." Kinga saurara min! idan kuma kin 'kiya zanyi maganinki ni ba shashashan namiji bane da zaki titsiye da maganganun banza ni ne nan Uban yarinyar da Mariya ta haifa kuma a yau nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyata Maryama saboda haka ki hadiyi zuciya ki mutu." Ihu! ta kurma! taje ta cikwikwiye masa riga tana zaginsa da fadin." Ya cuceta wallahi ba zata yarda ba sai ya sake ta. Ya fizgeta daga jikinsa ya yar! a gurin yana fadin." Dama ai ke din baki dace dani ba saboda tunda na aureki komai nawa ya lalace baki da amfani a gurina a halin yanzu, Mariya ce mahad'in arzikina kuma zata dawo gidana babu gudu babu ja da baya, sannan wannan maganar da nake miki itace ta farko kuma itace ta karshe duk sanda kika sake cewa na sake ki to wallahi na gama auranki har abadah ni ba'a haka dani mace tamkar riga take a gurina.'' Yana maganar yana buge! babbar rigar dake jikinsa. Tsallake ta yayi yaje ya bude dakinsa ya shiga ya barta a gurin cikin wani irin hali mai wuyar fassara! babu abunda ya dameta a halin yanzu sai ganin ta samu haihuwa dole ta dauki mataki akan irin cutar da yake mata ta daina yarda yana dubga mata kwayoyi kuma ba zata sake yarda yasa condem (kwaroron roba) idan yazo auratayya da ita ba, dole itama ta haihu tunda har ya amince da 'yar da Mariya ta haifa a matsayin 'yarsa. Hujaj gabadaya hankali da tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin Mariya ta dawo gidanshi, domin shi kansa yanzu ya kara tabbatar da maganar malaminsa Mariya itace taurarinsu suka daidaita domin tunda ya aureta k'ofofin samunsa suka bude, ko wace harka ya buga yana samun nasara amma tun sa'ilin da ya rabu da ita komai nasa ya lalace ya rasa gane kan al'amuransa, saboda haka shawarar abokinsa Alhaji Sha'abu itace dai-dai da abinda yake zuciyarsa ya tabbatar da cewa abokin nasa ba zai cutar dashi ba. To cikin ikon Allah akayi suna yarinya taci sunan mahaifiyarsa Wato Maryama kamar yanda ya fad'awa Talatu, sosai yayi bajinta Alhaji Sha'aibu ya bashi aron kudi yayi duk abinda ake bukata na haihuwa dan ragon suna manya guda biyu ya sayawa maijego bayan uban naman 'kaurin daya siya mata, duk wannan facakar da yake Talatu tana da labari, hankalinta ya tashi ainun! lokacin ta shiga sauke samirun dake kan kwabarta ta kulle a dankwali ta nufi kasuwar bakin asibiti. Talatu na siyar da Samirun ta hada kan kudin tsaf ta nufi gurin malaminta domin ya taimaka mata akan al'amuran da suke faruwa. Yamma likis ta dawo cikin tarin gajiya da yunwa ta kwanta a tsakar gidan tana tunanin abinda za taci domin kwayar shinkafa basu da ita, gashi tayi ragwan azanci gabadaya kudin dake hannnta ta tattare ta bawa Malamin babban burinta ace Mariya ta lalace ta kuma yi nesa da ita. Sallamarsa ce ta dawo da ita hayyacinta. Ko kallonta bai yi ba ya kama hanyar dakinsa yana baza babbar rigar sabuwar shaddar dake jikinsa, tunda ya shigo gidan ya game da Kamshin turaransa, a zahiri ka ganshi zaka dauka wani babban hamshaki ne wanda yaci ya tada kai saboda yanayin sutturun da yake tu'ammali. Ta hadiye kakkauran yawun dake bakinta gatsal ta ambaci sunansa."Jamilu." Ya juyo yana kallonta fuskarsa a murtuke! mugun haushinta yake ji yana ganin duk ita ta janyo masa shiga talauci dan dai kawai Malaminsa yace kada ya sake ta amma da tuni ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda." "Kasan tun safe haka nake zaune banci abinci shin baka tsoron hakkina ya kama ka." Cikin taushin harshe tayi maganar. Yaja tsaki da fadin." Talatu ashe kin iya kwantar da murya ai na d'auka karfinki ne zai kwatar miki." Murmushin takaici tayi tace." Jamilu kenan ai ni yanzu na daina kishi da Mariya babban burina ka dawo da ita mu zauna tare tunda na fahimci cewa itace farin cikinka. Murmushi yayi yace." Kin ci albarkacin Mariya." Hannu ya zura cikin aljihu ya dauko kudi duba daya ya zara a ciki ya cilla mata da fadin." Gashinan da yau da gobe kici abinci, sannan magana ta karshe da zanyi miki shine ki iya bakinki akan zama na da Mariya kuma ki zauna lafiya da ita domin itace mahadin arziki na." Ba tace komai ba tasa hannu ta dauki kudin da ya jefa mata tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta. Bai bi ta tanka ba ballanantana ya duba halin da take ciki dakinsa ya shiga ya sayo k'ofar ya kashingida yana hutawa kafin dare yayi ya nufi in da yafi wayo. **** Hujaj shige da fice ya cigaba dayi tsakanin gidansu Mariya da kuma zauran malaminsa wanda yake sake tabbatar masa da cewa lallai yayi kokarin ganin Mariya ta dawo gidanshi mutukar yana so arzikinsa ya yalwata, aikuwa ya tashi hankalinsa, sai da yaga tabbutuwar auran kisan wutan da abokinsa sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu yayi murmushi tare da godewa Allah, babu shakka dami ya tsinta a kala, babu yanda za'ayi Allah ya azurta shi da mace kamar Mariya ya rabu da ita, auransa da ita mutuwa ce kawai zata raba, dama can yana jin abokin nasa ne, bai auri Mariya dan ya sake ta ba. 'Bangaran Mariya kuwa hankalinta ya kwanta, a yanzu ne ta san tayi aure domin kulawar duniya Alhaji Sha'aibu nayi mata tare da 'yarta wacce suke kira da Shahida, ita kanta Baba Asabe sai yanzu hankalinta ya kwanta ganin yanda Alhaji Sha'aibun yake kulawa da 'yarta wannan shine babban burinta ace 'yarta tayi dace da miji nagari. Mariya tayi shar abunta tayi kyau da kiba haka nan Shahida tayi wayo rayuwarsu sukeyi mai tsafta dukkaninsu sun amince da juna babu nufin auran kisan wuta a zuciyarsu. Yana can sake da baki yana ta lissafin wa'adi (kwanaki) ya cika Abokin nasa ya cika masa alkawari kamar yanda yayi daukar masa. Bonono rufe kofa da barawo kenan. Lokacin da Hujaj ke lissafin wa'adi ita kuma Mariya ta samu ciki da Alhaji Sha'aibu. Shahida nada wata takwas a duniya Ganin yanda cikin yake wahalar da ita ne yasa Baba Asabe tazo ta dauki Shahidan ta tafi da ita can gidanta domin kula da ita, aikuwa cikin ikon Allah yarinyar tayi lafiya ta manta da nono, Baba Asabe ta cigaba da kula da ita tare da bata magungunan gargajiya. *** Sau uku kenan yana masa maganar cikar wa'adin amma yana shakulatun 'bangaro dashi, yau ne karshe dole ne ya saki Mariya ko yaso ko yaki. Koda ya isa kasuwar bai zauna a shagonsa ba, kai tsaye shagon abokin nasa ya nufa, fuskar nan tasa a murtuke. Alhaji Sha'aibu na ganinsa sai gabansa ya fadi, ya san dai labarin gizo baya wuce na koki. Babu walwala suka gaisa da juna. Ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu ban ta'ba tsammanin cewa za kaci amanata ba wallahi yanzu haka mu kayi da kai? wata biyar fa mukayi da kai cewa za ka sakar min matata amma duba wata takwas kullum idan nayi maka magana sai kayi shuru ko kuma ka dinga raragefe, Alhaji Sha'aibu kai kanka kasan cewar yarinyar nan itace kashin arziki na mai zai sanya kayi min haka."? Hular dake saman kansa ya cire ya ajiye gefensa ya kalleshi da fadin." Alhaji Jamilu ni fa ba jahili bane ina da ilimin addini daidai gwargwado dama can ban auri Mariya dan na sake ta ba, kuma duk kudin da na baka kayi mata hidima wallahi saboda tsananin son da nake mata ne, bana bukatar komai a gurinka, 'Yarka Shahida kuma zan cigaba da daukar nauyin ta domin duk abinda Mariya ta haifa ina sonsa, babban Albishir din da zanyi maka shine Mariya na dauke da juna biyu ni ne kuma ubansa." Wani irin gumi ya dinga yanko masa! a take wuyan rigarsa ya jike jagab! bakinsa yana rawa yace." Alhaji Sha'aibu cin amanar da za kayi min kenan? sharadi mukayi da kai cewa babu mu'amular aure a tsakaninka da ita, amma me yasa za kayi min haka." Shuru yayi masa domin duk maganar da zai fada masa ya riga yayi masa bayani duk abinda zai biyo baya mai sauk'i ne. Ya girgiza kai bala'in bakin ciki kamar ya kasheshi ido jawur! ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu idan ka san wata baka san wata ba ka mance waye Jamilu ko."? Murmushi yayi da fadin." Alhaji Jamilu duk in da zamuje fa nafika gaskiya idan hukuma za kaje ka sanar dasu, to kanka zaka tonawa asiri watakila ma alkali ya daure ka, saboda haka hakuri kawai da dangana za kayi." Yaji kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu! saboda takaici babu shakka Alhaji Sha'aibu yayi masa bazata. 'Kwafa yayi tare da girgiza kansa ya kama hanya ya fita daga shagon yana sa'be babbar riga, duk ya zauce ya fice daga hayyacinsa, kasa zaman kasuwar yayi ya nufi zauran malaminsa duk ya zube masa abinda ya faru, Arrama ya buga kasa ya zana ya kuma zanawa ya kalleshi da fadin." Ka rabu dashi kawai na duba naga zamansa da yarinyar na 'kan'kanin lokaci ne, yanzu ka kwantar da bankalinka ka zuba masa ido kawai ka cigaba da harkokinka, akwai wasu layu da zan baka wanda zaka samu kwalba mai murfi kasa a ciki, ka jefa cikin tsohowar rijiya, sannan akwai turaran da zan baka kullum kafin ka turara jikinka sai ka kalli gabas yamma kudu arewa ka kira Arziki har abadah! talauci kada yazo inda kake." sai ka turara jikinka da hannayenka, ina mai tabbatar maka da cewar kai da talauci har abadah." Hujaj yayi farin ciki sosai da irin taimakon da yake samu daga gurin malaminsa, sosai yayi masa alkairi kana sukayi sallama, ya nufi gida hankalinsa a kwance yana da tabbacin cewa duk abinda malaminsa ya fada masa zai tabbata. Wannan shine abinda ya faru. Hujaj ya dauke hankalinsa gabadaya daka kan Mariya ya cigaba da fagauniyar yawan malamai domin samun sa'a ta duniya arziki kawai ko ta halin yaya. Bangaran Talatu kuwa kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki dama babban burin ta Mariya tayi nesa da ita, duk abinda yake faruwa tana da labari kuma idan taje gurin malaminta yana sake tabbatar mata da magana, wannan dalilin yasa ta kara gazgata al'amirin malamin nata, ya iya aiki kamar yankan wuka. Cikin wannan halin ta samu ciki domin sai da ta shiga ta fita ta janyo da hankalinsa kanta, kuma bata yarda ya kusance ta da k'waroron roba(conderm) **** Mariya na cigaba da samun kulawa da mijinta da kuma mahaifiyarta, cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwarsa, sai kuma lalura tayi yawa , yau da lafiya gobe babu, ta kai ta kawo har sai asibiti suka bata gado domin kula da ita da abinda ke cikinta, Allahu akbar ashe abokin tafiya ne, daran juma'a nakuda ta tashi, kafin asubah, ta haihu 'ya mace sai da babu rai! mahaifa kuma tayi gardama likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta, duk abinda Allah ya kaddara babu makawa, suna tsaka da taimaka mata mahaifar tayi sama, a take ta dinga wani irin nishi! idonta na rufewa da wata irin jijjiga, da kalmar shahada Allah ya dauki rayuwarta. Sun shiga rudu mai tsanani mussaman mijinta da mahaifiyarta, bangaran Jamilu kuwa ko a jikinsa domin yanayin sa ma ya nuna kamar yana farin ciki da mutuwarta, domin koda yazo gaisuwa babu alhini a tattare dashi, kwalliya yayi sosai yana uban kamshin turare kamar sabon ango! komai na jikinsa mai tsada ne. Wannan shine abunda ya faru a baya, Shahida ta cigaba da zama gurin Baba Asabe tana kula da ita ci da sha suttura harkar karatu da kula da lafiyarta duk Baba Asabe ta dauka. sana'a take sosai domin macace mai kamar maza. Hujaj mantawa ma yake yana da wata 'ya a wani guri mutukar ya tuna da ita to yaje gidansu ne, mahaifiyarsa tayi masa maganarta, anan zai girba 'karya yace ai yana zuwa ya duba yarinyar har kudin abinci yana kaiwa, alhalin tun bayan haihuwarta bai sake zuwa gidan ba. gabadaya ya manta da ita, domin ko lokacin da Kawu Musa yaje kasuwa ya sameshi domin ya sheda masa lalurar yarinyar, sai da ya gama sauraransa tsaf sannan yasa hannu a aljihu ya dauko dubu daya ya bashi da fadin." Suyi hakuri insha Allahu zai zo ya dubata.'' Takaici yasa Kawu Musa ya fita daga shagon ba tare da ya karbi kudin ba. Tun daga ranar Baba Asabe tayi al'kwarin cewa ta daina neman komai a hannunsa, za ta cigaba da kula da yarinyar da ikon Allah babu abinda zai gagare ta. [4/19, 10:25 AM] Bintu: AIRPORT babban filin tashi da saukan jirage na Malam Aminu dake Kano. A hankali nake bin su da kallo sun jeru tsaf dasu cikin uniform gefen maza daban na mata daban, suna tsaye kowanne da 'yar jakarsa a hannu da alama screening ake musu kafin shiga cikin jirgin. Na dinga ayyanawa a raina cewa wata shekarar insha Allahu dani cikin masu hauke farali. Ajiyar zuciya na sauke a hankali na gyara takardar da biron dake hannuna nayi saurin matsawa gefe jin horn na mota a dab dani. Motar na zubawa ido tare da ayyana wani abu a raina. Da sauri na kalli jiragen dake daukar fasinja. sunan mutumin dake bayan motar irinsa ne a jikin jiragen dake d'aukar fasinjan domin zuwa kasa mai tsarki. 'DANGASKE AIR LINE sunan dake tambare a jikin jiragen kenan. 'DANGASKE41 shine a rubuce a jikin hamshakiyar motar da tayi parking gefan da nake tsaye. Ido na zura akan motar domin ganin wanda yake kokarin fitowa. kafarsa sanye cikin brown din takalmi mai gidan yatsa da kafar da takalmi duk abin kallo ne. Ya fito bakinshi na dan motsi yanda na fahinta kamar addua yake. direban ya mayar da murfin motar ya rufe ya dan bashi hanya, kira kuma sai ya shigo wayarshi dake rike a hannunsa. A sace nake kallonsa ina sake nazari a kansa. babu shakka shine hamshakin attajirin mutumin nan da sunansa ya mamaye ko'ina a fadin Najeria da ma kewayenta. Yana sanye da milk din shadda 'yar gasken dinki tazarce rigar har kasa da aikin rumi a wuyan rigar kanshi sanye da brown din hula (dara) ya nad'e hular da farin hirami, hannunshi daure da wani irin agogon sarka white colour, a irin kallon kurrula irin nawa na fahimci cewa shi din ba yaro bane kamar dai yanda jama'ar gari suke maganarsa, babban mutum ne kamili mai shekarun da suka wuce arba'in, a kalla dai shekarunsa na haihuwa zasu kai hamsin da biyu zuwa da uku. da akwai tsalli-tsallin furfura a kwantaccen gashin da yake zagaye da bakinsa. Yana wayar ina kallonshi tare da nazartarsa tabbas ya cika cikakken mutum mai kima da mutunci gami da daraja dan adam ko ga yanayin kalamansa a waya, a nutse babu baragada da hayaniya. Escort dinshi uku suna tsaye a kusa dashi, sai kuma wata matashiyar budurwa dake d'an kama dashi kad'an a gefensa a tsaye sai zumbura baki take tana dauke kai tana sanye da jallabiya baka mai duwatsu tayi roling da pink din gale hannunta rike da wayoyinta da kuma handbang dinta. Murmushi yayi ya dan gyara zaman gilashin dake sakaye da idonshi yace." Yanzu dai ni already ina airport tare da Shukura da Hajiya bana tsammanin kan wannan dalilin zan janye abinda nayi niyya saboda haka duk abinda ya dace ayi ina gari ko bana gari duk abinda kayi dai-dai ne Sule a cigaba da duk abinda aka saba kada a sauke min tukunya a gida " Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Okey to hakan yayi Allah yasa albarka a ciki sai mun dawo." daga haka bai sake wata magana ba ya kashe wayar ya mayar da ita gaban aljihun rigar dake jikinsa. Ya juya yana kallonsu a nutse yace."Ina Hajiya.? Shukuran ce tayi magana. "Tana cikin mota wai kafafunta ke ciwo." Girgiza kai yayi ya san za'a rina dama ko a gida ma kuka take da kafafun amma saboda rigima tace lallai sai taje aikin hajji tunda da iko to duk shekara ba za tayi fashin zuwa ba. Hannu yasa ya bude motar gyangyadi take. sai abin ya bashi dariya yayi kadan kafin ya fara kiran sunanta. Firgigit ta bude idonta tana kallonsa, da sauri tace." Wane irin baccin asara ne yake nema ya kwasheni a mota nida nake da niyyar zuwa gaban ma'aiki SAW." 'Kokarin fitowa take tana cigaba da surutai." Wannan kafa ita kadai ce damuwata a duniya amma Allah yayi min komai saboda haka babu abinda zan fasa na ibadah." Duk wani bayani da k'auli da zai kawo mata ba zata yarda ba, shiyasa yaja bakinsa yayi shuru kawai yabi ra'ayin ta akan duk abinda takeso babban burinsa su rabu lafiya. Yace." Ki zauna kada ki fama kafafun bari akawo keke a sanya ki a ciki. "Wa za'asa a keke?" a tur'bune tayi maganar tana hararsa." Shima ya gyara fuska babu wasa yace." Ke mana ko kin dauka idan mun isa can ma zaki iya d'awafi da kanki.? Shuru tayi tana tunani. da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa domin wani irin ciwo kafafun nata ke mata. Ya d'an juya tare da kiran daya daga cikin Escort dinsa. Ya risina cike da ladabi yana sauraransa. "Adamu kaje ciki ka fito da keke za'a dora Hajia a kai." Ya amsa da sauri cike da bin umarni ya bar gurin. Ina nan tsaye a raka'be kamar wacce tayi wa sarki k'arya har wanda aka tura ya dauko keken ya dawo suka dora ta akan idona suka shige Ban samu damar bin bayansu ba saboda akwai securities (masu tsaro) sai na dinga leken su ta tsakanin 'karafuna anan ne naga yanda ma'aikata da jama'a fasinjojin dake gurin ke bashi girma, fuskarsa ba 'boyayya bace idan akayi duba da yanda jaridu da gidajan television media ke nuna hotonanshi. Yanzu ma dai tunda ya shiga gurin masu daukar labarai sai d'aukar hotonshi suke da duk wani motsinsa. Cikin kamala da dattako yake dagawa jama'ar dake gurin hannu yana amsa gaisuwarsu fuskarsa a sake saboda daraja dan Adam har sai da ya cire farin gilashin dake sakaye da idonsa. wannan ya bawa gidan television din NTA dama daukar vedio sa lokacin ya juya da niyyar shiga wani kebantaccan jirgin da ya kasance na mussaman dashi da iyalinsa. Kamar yanda mane ma labarai ke bin diddinginsa nima haka ban dauke idona ba har sai dana tabbatar da cewa sun shiga jirgin sannan na janye idona, gumin dake goshina na sharce kafin na sauke wata irin ajiyar zuciya, gaskiya na jinjinawa wannan mutumin da ace duk haka masu hali suke da sun ji dadi, ya zama koda yaushe a fadi alkairinka kafin a fadi sharrinka. Wannan kenan ***** Takwas na dare suka kawo wutar nepa cikin unguwar wanda jama'ar dake zaune a cikinta suka cire tsammanin samun wutar sakamakon faruwar matsalar data janyo shud'ewar wattani rabonsu da samun wutar lantarki. Unguwar ta rikice da ihu! ba yara ba manya mata na cikin gida ma ihu! suke kananun yara sun fito waje sai ihu suke da fadin." NEPA!!. Baba Asabe dake zaune a tsakiyar rumfa tana daura man gyada irin wanda take siyarwa, tafi kowa farin ciki da samuwar wutar dalilin sana'ar ta, bata samun lokacin daure-daure sai da daddare, fuskarta da fara'a tace." Allah ya taimake mu, jama'a mai za'ayi da duhu ko a kabari Allah yayi mana tsari dashi." Saliha data fito daga uwar daki tace." Ameen dai ai Baba na fi kowa farin ciki kinga na huta wahalar kai waya ta gurin chaji." Tana maganar tana kokarin sanya wayar hannunta a chaji. Tace." Aikuwa ai yaran nan sun cutar damu wallahi ace saboda tsabar mugunta da bushewar zuciya mutum abu ba shi ya aje ba kayan gwamnati amma sai abi dare a sace ko tsoro ba sayi watarana injin wutar ya tashi dasu, kai Allah dai ya shiryi yaran yanzu." Ta amsa da "Ameen tana kokarin kunna Tv tace." Baba kin manta ai ba wannan ne na farko ba kusan sau uku 'barayi na bin dare su sace abubuwan dake da muhimmanci a transformer amma dai wannan karan naji ana cewa anyi kwamiti akwai kuma 'yan bijilanti da zasu sanya ido sosai." Tana cigaba da abinda yake gabanta tace." Ai hakan shine abinda ya dace suyi dama can rashin hadin kai ne na cikin unguwa." Shahida ce ta katse maganar da suke. rumfar ta shigo hannunta rike da plate da abinci a ciki. Can gefe ta zauna babu walwala a fuskarta, kallo guda kayi mata zaka fahimci cewar akwai abinda ke damunta. Ta kalleta da fadin." Akwai miya amma me yasa zaki sanya manja a cikin abinci, kina so wani ya shigo yaga kina cin fara da manja ya fita ya zage ni ko? dama kwana biyu naga sai nukufurci kike wai shin me akayi miki ne."? Hawaye suka fara gudana a saman fuskarta. kawai sai ta ajiye cokalin ta kifa kanta tsakanin gwiwarta tana rusa kuka." Ta bude baki kawai tana kallonta gabanta in banda faduwa babu abinda yake, rikon maraya akwai matsala babba. Saliha taja tsaki da fadin." Baba don Allah ki kyaleta ke kike rarrashinta shiyasa ai take duk iskancin da takeso idan bata bukatar zama a gidan ba sai ta hada kayanta ta tafi gidan ubanta ba." Duk da tana da matsalar kunne hakan bai hana ta jin irin kausasan maganganun da Salihan keyi a kanta ba, ta rasa me yasa Saliha bata kaunarta, tun suna yara take nuna mata kiyayya, bayan mahaifinta shine yasha nono ya bawa mahaifiyarta, amma kiyayya karara take nuna mata. Baban tace." Saliha wace irin magana ce wannan? ba na san tashin hankali da neman fitina, saboda kina ganin tana da matsalar kunne shine kike cin mutumcinta a fakaice, kin fi kowa sanin halinta, duk sanda kike kure hakurinta to zan kyaleki da it........Ta katse ta da fadin." Ki kyaleta Baba ta cigaba da maganganu a kaina jikinta ne zai yi tsami yanzu yanzu." cikin dashewar murya take magana. Baban tace." Magana dai ta wuce ke Saliha babu ruwanki da ita ki kama girmanki." Tsaki taja ta gyara wayar ta dake chaji ta tashi ta bar gurin tana kunkuni." Duk suka bi ta da kallon mamaki, Saliha sam bata da tarbiya wai a hakan ma gwara Shahidan tunda ita duk rintsi tana jin maganar kakar tasu. Gurin yayi shuru sai tv dake aiki. Kallonta tayi tana juya abincin har yanzu ta gagara saka loma daya a bakinta, da d'an 'karfi tayi maganar." Shahida sanja min tasha ki kai NTA KANO na saurari labarai." Ajiyar zuciya ta sauke ta rarrafa ta isa gurin Tv fa fara kokarin sanja tashar Tv ce irin ta da sai shuuuuuu! take mutane ma basa fita sosai, a haka suke kallon. Dai-dai lokacin da ta kai tashar NTA din yayi daidai da lokacin da aka haskoshi a filin jirgi yana gaisawa da mutane tare da cikakken bayani a kansa amma kuma da turaci ne. Murya ta karo ita da Baba Asaben suka kurawa Tv ido suna ganinshi haza-haza domin tv ba clear saboda rashin Area mai kyau. Baba Asabe tace." Shahida wannan mutumin ne mai taimakon mutane ko.? A sanyaye ta daga kai da fadin." Shine wai suna bayani a kanshi zai je aikin hajji da tare kakarsa da kuma 'yarsa tilo guda daya." Karaf tace." To bashi da mata aure ne.? Itama tace." To ina zan sani Baba nima na dan tsinci wasu abubuwan ne ba komai na fahimta a kanshi ba, amma dai gaskiya ba zai rasa matar aure ba tunda ga budurwar 'yarsa nan." Tace." Eh gaskiya kam amma kuma surutai marasa kyau suna yawo a kanshi jama'a da bin diddigi da ganin kwaf da yawa mutane nayi masa zargin auri saki wai a kalla ya auri mata sama da goma ya saki saboda yana da kudi." Ta kalleta da fadin." Baba ki iya bakinki wallahi, na lura mutane ke kawo miki gulma iri-iri kada aji wannan maganar daga bakinki babu ruwanki." 'Yar dariya tayi tace." Yo 'yar nan ai maganar duniya bata 'buya, ko na fada ko ban fada ba, idan halinsa ne, Allah zai tona masa asiri watarana." Tace." Eh duk da haka dai babu ruwanki wannan al'amari domin na san ki da magana watakila wasu na iya zuwa siyan abinci ki basu labarin da baki da tabbas akai, daga haka kuma sai al'amari ya lalace! sunanki yayi ta yawo gari." Uffan ba tace ba, saboda ta san duk maganganun Shahidan akan hanya suke, sai kawai ta cigaba da abinda ke gabanta. abincin take cusawa a bakinta tana had'iye wa da 'kyar! ita kadai ta san abinda ke damun ranta, kwana uku bata sanya shi a idonta ba, taje bakin kasuwar ya kai sau biyar bata ganin gilmawarsa, sai dai tarin tarkacensa a karkashin tsohowar motar da yake kwana, ko yana ina oho! wasu zafafan hawaye suka zubo mata a kumatu, tayi saurin gogewa! tana satar kallon in da take zaune, hada ido sukayi sai tayi saurin sunkuyar da kanta tana juya sauran abincin da ya rage da cokalin hannunta. Ta ture bokitin man gyadan da ta gama daurawa, a nutse take kallonta kafin ta d'an bud'e murya yanda za taji tace." Shahida idan baki fada min damuwarki ba waye zaki fad'awa? duk halin da kike ciki na fahimta kwana biyu kamar baki da lafiya, shin ko dai wani abu yana damunki ne."? Tasa hannu ta goge hawaye dake ta gudana a saman fuskarta, murya na rawa tace." Baba zuciya tana tausayin wannan mutumin na bakin kasuwa wallahi haka kawai nake tausaya masa, kullum dashi nake kwana dashi nake tashi a raina yau kwana uku kenan babu labarinsa sai dai tarkacensa a karkashin motar da yake kwanciya.'' Baba Asabe ta tsira mata ido cike da tsantsar mamaki tace." Baban- baba kike nufi.? Kai ta daga. Mamaki ya cika ta tace." Ke kuma meye damuwarki da mahaukaci Shahida kada fa garin tausayinki ki jefa kanki a wata musifa watakila ma ba mutum bane, aljani ne domun babu wanda ya san daga wace duniya ya fito." Gabanta na faduwa tace." Wallahi mutum ne kamar kowa kuma ba mahaukaci bane, tunda yana sallah kuma baya doke-doke watakila damuwa ce ta mayar dashi haka." Baba tace." To ai shikkenan yanzu wane irin taimako za'ayi masa." Wani dadi ya ratsa zuciyarta, cike da farin ciki tace." Ki sanya masa kwano na abinci tun daga safe har dare, tunda Allah ya baki yanda za kiyi wallahi zaki samu lada." Tace." To shikkenan zanyi yanda kikeso amma kada na kara ganin kin shiga damuwa a kansa, kuma kiyi kaffa-kaffa dashi tunda na lura baki da hankali." Tana 'yar dariya tace." Baba kenan, Baban-baba ba zai cutar dani ba nayi imani da hakan, tunda na jima ina bashi sadaka kuma bai ta'ba yunkurin kawo min duka ba, sai dai yace ya gode." Shuru kawai tayi mata ba wai dan bata da abun cewa ba, tsabar takaici ne ya isheta, yanzu yarinyar ta zama hukuma sai da rarrashi! za tayi kokarin ganin tayi mata duk abinda ta ke so. Duk da Baba Asabe ta amince da abinda ta ke so hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, don ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta gan shi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake k'ar'kashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a 'karkashinta. Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa. Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kad'ai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati." Tabe bakinta tayi ta ce." Yanzu ta fita." Cike da mamaki ta ce." Ta fita kamar yaya ina taje?" Ta ce." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita." Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data d'auki son duniya ta d'ora masa. A fili ta ce." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne." Ta d'aga labulan d'aki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta. Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa. Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan. Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa! "Insha Allahu bai mutu ba." Ta furta hakan a fili. Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta. Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani." A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama?" Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba?" Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar." Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi ya ce." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta. Ba ta ha'kura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nu na ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba? Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin k'okarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta. Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali ba to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba. Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta saya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da 'ko'karin faranta ran jikokinta dake gabanta. Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga d'aki da hijab dinta a hannuta. Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan? ai da nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta, sannan kuma da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko. Baban ta ce." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda ta ce." Babu damuwa a tare da ita ta ce." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo." Ta ce." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa." Bata tsaya taji 'karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta. Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta samesu suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin. Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi suke a gurin da wari mara dadi. Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana biyu kina raina." Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan." Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun ji." Babu wani 'kulli a cikin ranta ta ce."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya? A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar tsokar naman dake cike da kaskon suya. Jamila ta shimfid'a mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune! kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan. Gabad'aya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bud'e d'akinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! da ka gani yana da damuwa. Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa gurin da nake?" Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce ba kya so na yi miki shiyasa ki ka d'auke k'afarki daga gidan nan ko?" Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata shida bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema?" Tana shashshekar kuka ta ce." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so na yi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na." Ya girgiza kai da fad'in.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake buk'ata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba." Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fad'a masa ba zai yarda ba, bahaushe ya ce." Mai d'aki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta. Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba." "Zan tafi Baba." tafad'a tana k'okarin tashi. ya ce."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki." Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba ta ce."Baba ina ka samu kudi ka yanka SAH! har da Rago?" Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki." Ya fada yana zazzare mata ido! A sanyaye! ta ce." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri." Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta da burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne. Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi SAH! da Ragon a gurinsa. Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba. Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka 'kwamushe haka ya dawo gida a motar haya. Kwabo yanzu babu a cikin asusunsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa. Talatu ta shiga d'akin tana gyara d'aurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko. 'Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada." A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin." Ta juya ta fita bagazan-bagazan! Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu. Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma?" Bai saurareta ba ya cigaba da loda zallar tsoka da k'ashi cikin buhu yana fad'in gidajan da za'a kai musu. Talatu kamar ta dora hannu ka ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma?" Ya ce." Na bayar sadaka dama haka Allah ya ce ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku." Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba. Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan k'aunar da mahaifin nasu ya yi musu. Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bu'kata ta siyan icce ko man gyad'a da makamantansu. [4/19, 10:26 AM] Bintu: Talatu tare da su Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar da su, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwad'ayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige d'aki tana matsar hawayen ba'kin ciki, tunanin hanyar da zata k'untata masa take. 'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka ya yi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa. Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa. Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Walida kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana 'kunk'uni! d'aki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo 'katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi. *** Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya ya yi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharad'in daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure. Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wad'anda su ka yi layya sun cinye naman su, har sun fara sayan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye. Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da d'aurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki. Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta 'boye a k'arkashin gado. Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne." Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi 'karfin ki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na." Saliha ta fusata! "Ni ce mayya." Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa." Tace." Don Uwarki sharri za ki yi mini naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar ta ce." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku." Cikin yanayin maganar ta ta ce." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya." Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma.?" Ta ce." Wanda ki ka bani ne na b'oye abina." Ta ce." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina." Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa." Gabad'aya suka zuba mata ido. Baban ta sake maimaita maganar." Ki ka ce Baban-Baba ki ka ajiye wa?" Ta gyad'a kai alamun "E." Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta. ABUJA Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da su ka ci. Gida d'aya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci. Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali. Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali. Suna tsaye sanye da bak'aken kaya a bakin k'ofar suna dakon fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi. Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira." Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kad'ai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta. "Hajiya lokaci na tafiya." Ya fad'a yana duba tsadaddan agogon dake d'aure a hannunsa. Ta kalleshi babu fara'a a fuskarta ta ce." Alhaji Habu." ita kad'ai ce take kiransa da wannan suna HABU tun yana yaro, Asalin sunansa Abubakar-Assadiq mahaifinsa ne kadai ke kiransa da Saddiku sai kuma abokan karatunsa, amma da yawa daga cikin 'yan uwan mamansa kuwa suna kiransa da 'DANGASKE wanda mahaifiyarsa ta sanya masa dalilin yaci sunan mahaifinta da kuma alkunya irin ta dan fari, wannan dalilin yasa 'yan uwanta suka 'boye sunan domin daraja sunan mahaifinsu, sunansa ya 'bace gabadaya a famliy idan zaka kwana kana kiran ainihin sunansa babu wanda zai gane wanda kake nufi mutukar baka kira DANGASKE! ba. Ta cigaba da cewa." Na ce wai kai ina zaka kai kudi ne? kullum baka gajiya, kai ne can kai ne nan, a duniyar nan babu 'kasar da baka taka ba, wannan kud'i dai haka zaka tafi ka bar su, ka na ji kana gani Shukura ta zama magajiya tun da ita kadai ka ajiye gemai-gemai da kai da gemu da furfura kana zaune babu aure." Sai ta fashe da kukan b'akin ciki ta cigaba da cewa." Ya jama'a ba zasu zarge ka ba, Habu nima na fara zarginka kana neman matan banza a waje." Ya sunkuyar da kansa yana sauraran kukanta dake mutukar tafarfasa masa zuciya! zubar hawayenta yana nufin abubuwa da yawa a tare dashi, dole ya rarrasheta domin duk irin bayanin da zai mata ba zata yarda ba bahaushe yace (mai daki shi ya san in da yake masa yoyo) duk ta san gwagwarmayar da ya sha a baya, ya tabbatar da cewar ba za tayi masa uzuri ba tunda kullum fadi take ai matan ba duka suka taru su ka zama daya ba." "Ki kwantar da hankalinki Insha Allahu zanyi aure very soon." Hanci ta ja kamar wata k'aramar yarinya murya na rawa tace." Alhaji Habu ni na fi so ka dawo da Fatima Uwar Shukura domin matar fari itace rufin asiri." Lokaci guda fuskarsa ta sauya! idonsa yayi jah! kansa ya girgiza da fadin." Hajia kada ki sake min maganar Fatimah idan kina so mu shirya.'' Ta kalle shi ganin yanda kwayar idonsa ta sauya yasa taji tsoro kada ciwonsa ya tashi dama can Fatiman ce SILA ta ce." To yanzu ka samu wacce zaka aura din kuma 'yar wane gari ce? domin wannan karon ba na so ka auro 'yar wata k'asar." A cunkushe ya ce." Ina dubawa tukkuna tunda na ce miki na kusa aure to kisa al'amarin a cikin ranki kuma ki taya ni da addua." A sanyaye ta ce ." Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen hankalinsa na kan agogon dake daure a hannunsa. Tsaye ya mike wanda yayi dai-dai fa fitowar Shukura daga dakinta. "Daddy yau fa duka kwananmu biyar da dawowa ba zaka zauna ka huta a gida ba." Hannunta ya ri'ke da fadin.'' Shukura ku kwantar da Hankalinku ba nisa zanyi ba KANO na nufa insha Allah zan duba ma'aikatu na (company's) domin ganin abinda yake gudana." Ita da Hajiyan suka sauke ajiyar zuciya domin duk a tunaninsu sun d'auka zai bar 'kasar ne kamar yanda ya saba tafiye-tafiye. Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidansa wanda ke unguwar giginyu, cikin kamala ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai k'aramin hannu kansa sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi. Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu. Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku." Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar. Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye." Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali." Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria. Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban?" Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne." Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida. Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai. Shi da abokansa suka rasa bakin godiya. To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu. **** Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take. Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci. Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji." Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata. Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma. Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai." Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri. Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci. Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba. Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba. Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta. Bakinta na rawa ta kirayi sunansa. Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake k'asan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu. Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki. Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.'' Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take. Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda take da 'kyankyami Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau. Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta sayi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba. daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, ta ce." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar. Ta fara k'ok'arin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi ka ci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a." Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba. Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka ta ce." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.'' Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne. Hannu yasa ya 'karbi wainar a takaice ya ce." Na gode." A hankali ya yi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata. Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo." Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta. Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu. Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko?" Ta ce." Eh saura naki a kadai gashi can a jug." Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.' Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya." Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi." Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita. Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa ba sai wannan mahaukacin.' Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar." Tana 'yar dariya ta ce." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa." Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri. "Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci." Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bud'e kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai k'amshi yake. Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba. Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba. A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?" Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.? Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka." Shuru yayi bai ce komai ba. Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu." Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin. Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya. 'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata! Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka! Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.? Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta. **** "Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj. Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa." Ta ce." To za'a fada masa. Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya. Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar. [4/19, 10:26 AM] Bintu: Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu. Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo. Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi." Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan." "Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne?" Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje." Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni. Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka." Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa. Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji." Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri." Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai. Jallabiya yasa ya fita. Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne. Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo." Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba." Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka." Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin." Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa. 'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka." Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah." Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul sai uban 'kyalli yake. Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa. **** Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya. Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara." "Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci." Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane." Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi." Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina." Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake." Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba. Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin." Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta. Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado. Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu. Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba. Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa. Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar. **** Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye. Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa. Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa. Ha'ki'ka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwad'ayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sa ni, Hujaj cikin rashin k'ima da rashin arziki ya nufi gidansa da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an k'wamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin 'kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne su ka yi arangama da mak'ocinsa mai suna Malam Habu yana nannad'e tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, ya yi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai. Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da ma'kocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya d'auke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari ma'kocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu. Fitowar ta kenan daga d'aki da buta a hannunta za ta kama ruwa. ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba. Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu?" Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa. Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata. Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita. "Wai ana sallama da mai gidan." Wani ne yaro ne yake magana a gidan. Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne? Luf yayi a d'akin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadi'n." Ka ce gashi nan zuwa." Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin. Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko?" Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi." Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta. Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya samu Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah." Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ?" Yayi shuru bai ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana hura 'katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni." Cike da burga da rashin gaskiya ya d'aga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi k'arfin haka." Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na mai'ko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi idan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali." Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa mak'ocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj d'aya na k'okarin d'aura masa ankwa a hannu. "Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.'' Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun mak'aryaci ne, saboda haka hukuma ce zata raba ni dashi." Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba. Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da k'ima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari. Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis da shi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya." Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba. Wai a kace labarin duniya ba ya 'buya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar. Shahida kam d'aki ta shiga ta ci kukanta ta k'oshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani. *** "Ranka ya dad'e iyakar ha'kuri nayi kawai abinda na ke so ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani." Officer ya ce." Saminu kaje ku yi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto." Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure na ke so nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin ma'karyaci ne na daina yarda da maganarsa." Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu." Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana." Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa." Yayi jim yana nazari wannan maganar kawai dai ya shata ne ya fad'a amma babu wani dilalli da su ka yi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fad'o kansa a gurin sana'ar tasu. Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa." Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa k'aton ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne sheda." Ya kar'bi zungureriyar takardar ya yi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba. Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana. Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai." Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar maca ce san kowa k'in wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu." Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake buk'ata daga jikin mace falillahil hamdu.'' Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta." Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata." Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za ta yi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin. [4/19, 10:27 AM] Bintu: "Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar. Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita. "Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa! Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan! Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali. Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse? Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata k'arfin iko na a kan 'ya ta." Ta ce." Me take nufi to? Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana." Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke." Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa. Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa. Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya." Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!" Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki." Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan." Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta." Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi." Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.'' Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa. Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata. Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici! Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba." Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu." Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba. Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa. Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba. Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta." Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu. Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.'' Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?" Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku! "Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun. 'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?" Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.? Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci." Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau." Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa. Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu. Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke...... ***** "Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa. Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.?" Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a." Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa. Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune. "Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba." Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa." Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe. Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa. Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake. Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira masa Shahida maza su zo tare yana nemanta. Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana zan can zucci. Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya tsami banza." Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau kwanansa hudu a jikinki." Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."? Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake. Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya rike ta ba nima naji da nawa." Tsakaninta da Allah take maganar. Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki." Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari." Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne. Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa. Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan. Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka. Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta. Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su ka ji sautin muryarsa. "Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."? Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba." Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."? Kai tsaye ta ce." Babu kowa." Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar daku a lokaci guda." Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso." Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa." Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so ya gan ka a hakan ne. Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke. A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta. Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake sanya ta zubda hawaye. Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi ta cigaba da aikin gabanta. Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi miki." Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin." Wai aure zai yi min ." Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar "Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani. Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi. Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba." Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba. Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar." Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu." Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba." Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so." Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake. A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana! Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa." Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan." Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa. A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci! Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata. Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani! Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido. Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta. Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin. Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin. ''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."? Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka." Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."? Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci. Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."? Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa." Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza! Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin." Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi." Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin. Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya. Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin...... [4/19, 10:28 AM] Bintu: Unguwar giginyu. Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take. Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai! Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje. Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko? A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah." Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida." Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar. Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba. Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara." Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka! Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar dalili ita kad'ai ce babu wasu. shiyasa take lallabata. ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba. Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa. Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu." Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu." Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana." Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare su ka yi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita." Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar fige ta da karfin gaske ta fita daga gidan, kai tsaye rijiyar zaki ta nufa gidan Hajiya Zaliha domin sunyi waya da Mamanta ta ce ta sameta a gidan domin itama ba ta jima da sauka a garin ba. **** Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa. Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri. Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru." Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.'' Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .'' Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa. **** "Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba." Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka." Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.'' "Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi. Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri. Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka." Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi. Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ." Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata." Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ." Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi. A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya. **** Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin. Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin. Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi. Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu. A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri. 'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Lurwanu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa. Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita. Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin ya yi shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun. Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu?" Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku." Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi." Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.?' A sanyaye ta ce." Ki yi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta ya ge kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a b'ace ta yi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau. Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben. Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya. Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole. Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar." Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari." Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta. A gaggauce ya shigo gidan. sai kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo. A tsaye ba tare da ya risina ba ya gaishe ta. itama fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa sai ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa. Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba." Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa?" Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba." Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi. Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta" Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga. Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta. Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da ya ji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu ya fi su rinjaye da yarinyar. Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta. Ta fito da hijabi a wuyan ta. Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta. Zum'bura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa." Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.? Murmushi tayi tana kawar da fuskarta. Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin SO! dole tayi wa yarinyar uzuri. Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami! **** Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a. Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar. Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa. Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni." 'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci wani abu a tare dashi, sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannnunta. Ba zato ta tsinkayi maganarsa." Kin tafi kin barni da tunaninki." Kallonshi tayi tana so ta tabbatar da maganarsa. Ya lumshe ido tare da daga mata kai "Nayi kewar ki My dear." Gabanta ya fad'i ta dinga kallonsa tana mamakin kalaman dake fitowa daga bakinsa kamar ba wannan mai tabin hankalin ba. A sanyaye Ta ce." Ga abinci nan kayi hakuri nima kwana biyu bani da lafiya shiyasa ban zo ba." "A jiki na naji hakan domin tare muka kwanta ciwo nima bani da lafiya my dear amma ganinki a yanzu ciwon ya tafi." A d'an tsorace ta ce ." Don Allah waye kai nifa har yanzu zuciyata bata amince min da cewa kana da tabin hankali ba, haka kawai nake tausayinka. Shuru yayi bai ce mata komai ba. A lokacin ta fahimci sauyawa daga gare shi, sai ma ya shige 'kasan motar ya bar ta a tsugune a gurin. Ta mike tsaye tana 'karkade jikinta tana juyawa taga yara sun fara taruwa a gurin, da sauri ta tsallaka titi ta shiga layinsu cikin sassarfa. Washe gari ma da safe ita ce ta kai masa abin kari, sai dai lokacin da ita isa bakin titin baya nan, sai dabbobi a kwance akan buhun da yake kwanciya duk sunyi kashi da fitsari! gurin sai wari yake ga shara nan birjik da bawon lemo da sauran tarkace! Tsigar jikinta ta tashi! ta tsani ganin kazanta a rayuwarta, wai yanzu a ce mutum mai rai! wanda Allah ya daraja shike kwanciya a gurin, ta girgiza kai tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata, kofin kunun ta ajiye a can gefe in da babu k'azanta! ta juya gaba da baya tana duba gurin, da yake yanzu garin ya waye babu mutane sosai amma dai wandanda ke sana'a a bakin kasuwar sun fara fitowa yara 'yan makaranta da wanda ke cikin ababan hawa suna ta wuce wa suna kallonta lokacin da take kokarin korar dabbobin dake kwance a kan shimfidar buhun nasa. Wani almajiri ya zo ya tsaya da roba a hannunsa. Kallonsa tayi idonsa cike da 'kwansa da alama tashinsa kenan daga bacci ya fito neman abinda zai sa a bakinsa. Cikin yanayin da Allah ya halliceta take masa magana." Ya ce." A she baki sani ba ai jiya da daddare wani mutumi ya zo wai ashe shine mai wannan motar." Ya fada yana nuna katuwar akori kurar da ta jima a gurin. ya cigaba da cewa." Ya gargadi Baban-Baba cewa lallai ya kwashe tarkacensa daga gurin zai turo kanikawa su kwance motar ya siyar da ita. Gabanta ya dinga dukan uku-uku! baki na rawa." Ta ce.'' Yanzu ina yake."? Cike da rashin fahimta ya ce." Waye? Murya a sama ta ce." Baban-Baba." Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa." A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata. A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji." Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan." Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba." Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko?" Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin. Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka. Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida." Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka. Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels