An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH FCW 🅿️1️⃣ Gabaɗaya ta jibge kayan cikin wardrobe ɗinta a kan gado, sai zuba wa take a cikin wata babbar bakkon kai da gani tamkar ƙaura za ta yi, sai da ta kwashi son ranta ta maida sauran. Akwatin ƙarfe ta ɗakko irin tasu ta mutanen da, kayanta ne na fita unguwa ƴan atamfofinta sabbi. Sai zuba kayan take tana ta faman murmushi gabaɗaya wani irin daɗi take ji a ranta "Yau sai kwanan binni" Inna Azimi ta faɗa tana ƙoƙarin zige zip ɗin bakkon nata, hango sallayarta ya sanya ta dakata da zige zip ɗin ta ɗakko abin sallar tana cewa "Kar in je in ke cewa a bani abin sallah dan ni bana son yin sallah sai a kan sallaya ta bare ma su yara da kunya kake bani-bani in da abinka kwa sai dai a ga ka ɗakko" Ta ce tana sanya sallayar ta dannata daƙer ta samu ta shiga saboda cika da bakkon ta yi. Wanka ta shiga abin ta, tana ta sauri ta fito, kallon ɗakin kishiyarta ta yi ta yatsina fuska a ranta ta ce " Humm ba zan faɗa miki ba jikata na naƙuda, ba sai dai ki ganni da kayana zan tafi birni in yaso baƙinciki ya kasheki, tun da ke baki da dangi a birni" Ta faɗa har da wani gatsine kamar wata ƙaramar yarinya.Ɗakinta ta shiga sai da ta shafa mai tsaf, ta sanya kwalli sai wani kallon ƙaramin mudubi take tana wani gyagygyara fuska tamkar wata ƴar budurwa. Sai da ta gama tsaf ta ɗakko atamfarta batik a linke a kan gado daman takanas ta fitar da ita saboda ta sanya idan za ta tafi. Sanyawa ta yi a jikinta ta ɗakko ɗankwalinta irin na tsaffin nan ɗan kantu mai santsi ta ɗaura har da yi gwaggwaro a gaban goshi, ƙasan gado ta sunkuya ta ɗakko takalminta ɗan madina domin shi ne wanda take sanyawa in za ta gidan biki dan shi ne na ganin sarki, ta fiddo shi ƙofar ɗaki ta ajiye, ta ɗauki silifas ɗinta wanda ta cire duk ya wani tsufa ya katale, ta shiga da shi ɗakin ta sanya a ƙasan gado, madarar turarenta ta ɗakko ta shafa abinta, sai ta kwalbar turaren a ƙaramin aljihun bakkon tana cewa. "Wannan sai ranar suna kuma zan shaga abuna, yo a kan me zan ke wari ranar suna a raina min hankali ganin daga ƙauye nake" Ta faɗa tana taɓe baki. Sauran goranta ta ɗauko ta ɓantala tana ci ta ƙulle sauran ta saka a ƙaramar jakarta ƴar pos wacce jikarta Sadiya ta bata. "Yauwa na gama komai bari in je in tambayo Malam, dan ma kar ya ji ya wai dan wallahi tafiya babu fashi" Ta faɗa tana fitowa ta nufi turakar mijin nasu da ke can wajen hanyar zauren gidan. Kai da tsaye ta danna kai turakar Malam tana mai cewa "Gafaranmu dai" "Allah mana gafara" Cewar Malam yana kallonta mamaki bisa fuskarsa ganinta da shirin fita dan ya san biki ma sai na wanda yake da kusanci da ita take saka atamfofinta na adakar ƙarfe, hakan na nufin biki za ta ko sanar masa bata yi b ya faɗa a ransa. Inna Azumi kwa sai da ta gama shigowa ɗakin ta lura da Tasalla da ke zaune a ɗakin sai lokacin ma ta tuna Tasallar ce da girki. Wani kallo ta yiwa Tasallar ta ce "Umm in ji mai ciwon haƙori" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Shi dai Malam har lokacin kallonta yake da mamaki, sai da ta zauna ta ce. "Sannu Malam" Kallonta ya yi tare da gimtse fuska sannan ya ce "Yawwa sai ina, dan na san dai zancen gizo bai wuce na ƙoƙi tun da na ganki da shirin fita" "Haba Malam, dama magana ce nake so mu yi" Ta faɗa tana kallon Tasalla dan so take Malam ya ce Tasalla ta fita dan bata so Tasallar ta san da tafiyar tafi so sai ta fiddo jakarta ta mata bazata. "Ki faɗi abin da ya kawo ki" Cewar Malam yana kallonta har lokacin babu fara'a a fuskarsa. Washe haƙuranta ta yi wanda har lokacin da ɗan sauran goron da ta tauna a bakin ta ce "Dama Halima ce ƴar wajen wannan yaro zan je yiwa zaman wanka sai... "Zaman wanka kuma Yaushe Halimar ta haihu da har za ki tafi zaman wanka ko faɗa min baki yi ba sai da kika shirya? Shin ma me za ki je ki yi da girmanki da komai?" Malam ya faɗa rai ɓace dan abin ya bashi mamaki bai zaci ma garin za ta bari ba duj tunanisa biki ne za ta je a cikin garin ko wani ƙauyen da ke maƙotaka da su. Tasalla da farko wani haushi ta ji jin kishiyarta za ta tafi birni, dan duk da sun tsufa amma kishin nan yana nan sabo dal a zukatansu. Amma ganin Malam ɗin ya haƙiƙice sai ta faki idonsa ta yiwa Inna Azumi gwalo. Inna Azumi wani ƙululun baƙinciki ne ya tokareta ganin kishiyarta tana mata gwalo har da ƙunshe dariya. "In kin san wata baki san wata ba wallahi sai na yi kissar da sai ya barni na tafi, shegiya ƴar baƙimciki da bata da kowa a birni bare tasa rai wataran za ta je ta sha miyar ɗanyen kaya (jar miya). "Bata haihu ba fa fama... "Ban gane bata haihu ba wato shi zaman wankan ma tun kan a haihu ake zuwa yinsa?" Malam ya katse ta da tambaya cikin nuna tsantsar mamaki a fuskarsa. "Yau za ta haihu" "Ikon Allah wato dai har ɗan adam ya san ranar da wani zai haihu in ce dai wannan ilimin ubangiji ne, ko su turawan da suka fito da yin hoton ciki (Scanning) Dan a san watanninsa da ranar haihuwar ai ko sun faɗi ranar ba a ita ake haihuwa ba ko dai mace ta rage kwanankin ko kuma ta haura ma amma ke har kin ware ranar da za ta haihu, wallahi Azumi ki fita idona ba na son fitina" Malam ya faɗa yana nunata da yatsansa. Sosai abin ya yiwa Tasalla daɗi, sai ƙunshe dariya taje tana yiwa Azumi kallon ƙasan ido, wannan abu shi ya ƙara ɓatawa Azumi rai sosai take jin kamar ta fashe da kuka. "Haba Malam ai ka bari na mutu kafin ka binne ni" Cewar Azumi a ɗan fusace. "To uwata yi min faɗa ko ki haɗa da duka tun da ke ce mai gidan, kuma ma da kin san ke ce mai gidan ai da baki zo nan neman izini ba da sai ki yi tafiyarki" Malam ya faɗa yana gyara zamansa ya lanƙwashe ƙafafunsa wanda suke a miƙe. Sai sannan Azumi ta gane katoɓarar da ta yi aikuwa da sauri ta ɗan karyar da kai tare da sanyaya murya ta ce "Haba Malamin Malamai, Malamin da ƙauye da rigagen yankin nan ke ji da shi suna alfahri da shi, ni na isa in ja da Malamin da kowa ke girmama shi saboda ilimi da ɗaukakar da Allah ya masa" Aikuwa Azumi ta harbo jirgi tuni Malam ya washe jajayen haƙoransa, cikin jin daɗi ya ce "To ai ke ɗin ce Azumi sai kike abu kamar dai ke ce sama da ni amma ai sai ki yi bayani tin farko" Tasalla wani irin takaici ne ya mamaye dukkan zuciyarta dan bata so Malam ɗin ya sakko ba ta so ayi ta gumurzu, har ayi faɗan da Malam ɗin zai hana zuwa birnin duk da ta san har yanzu bata ji an yi haihuwar ba, ta san kawai riɗin abincin birni ne ya sa ta zazzoɗin son tafiya. Wani kallo mai haɗe da hara Inna Azumin ta yiwa Tasalla kafin ta juya wajen Malam ɗin ta yi murmushin jin faɗi ta ce. "Wallahi dama ɗazu ne na kira lambar Babar Halimar dan in ji ya suke, to shi ne fa na ji tana ta sheshshekar kuka tana cewa "Inna ki taho idan da hali muna asibiti an kawo Sa'adiyya tana naƙuda idan ya so sai ki nemo izini agun Malam ki mata zaman wanka, kin san dai bata da wata kakar da za ta mata zaman wanka sai ke kaɗai a duniya" Inna Azumi ta faɗi maganad tana share ƙwallar ƙaryar da ta mammatso daga idanun nata. "Wato da gasken dai bata haihun ba?" "Haba Malam wai ya kake maida hannun agogo baya ne, na faɗa maka naƙudar take amma kaƙi yarda sai wasu tambayoyi kake min mau kamar tuhuma, ko dan ka ga yarinyar ba jikar ka bace, amma tabbas ka zama mai manta alheri lokacin yaron nan na da rai haka zai kwaso goma ta arziƙi ya zo ya gaisheka duk da ba kai ka haifesa ba amma shi ne yanzu dan ƴarsa za ta haihu zan je zaman wanka kake nuna mata wariyar launin fata?" Ka san dai shi kaɗai na haifa a duniya, shi ma su biyu ya haifa daga ita sai ƙanwarta, kuma wannan ne karo na farko da jikata za ta haihu amma kana ta yalbatsani a gaban kishiya salon wataran a min gori" Ta ce tana fashewa da kukan makirci har da su fatar majina ita ala dole ta tuno da ɗan mata da ya mutu. Baki sake Malam ɗin ya ke kallonta, ganin dai ta daddage sai zuba kuka take ya ce "Ku dama mata kowa ya sanku da goranta abin da kuka yiwa mutum, ko goranta masa a kan abin da wani naku ya masa, da zarar abu ya haɗoku sai ku yiwa mutum gori. In ba haka ba daga magana sai ki fara lissafo abubuwan da ɗanki ya mini saboda ba ni na haifesa ba, to indai tafiya birni ne ki je Allah kiyaye Allah ya sauketa lafiya. "Haba Malam ba haka nake nufi ba na ga ma har ranka ya ɓaci, kawai ma na fasa tafiya da in tafi kana fushi da ni" Ta ƙara faɗa cikin kissa da kisisina. "Lah babu komai wallahi, ai mu ma maza wani lokacin da namu laifin sai mu hana mace zuwa abin da bai dace mu hana ba, kin ga wannan ai bai dace ko kusa na hanaki ba, wallahi na aminci Allah kiyaye hanya" Ya faɗa yana sanya hannu a aljihu ya fiddo dubu biyu ya miƙa mata. Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ta rafka godiya "Yaushe zan dawo kuma?" "Kamar ya yaushe za ki dawo ba zaman wanka za ki mata ba ai zan ce kwana arba'in ne ake zaman wanka ko an canja shi daga haka ne?" "A'a ba a canja ba sai dai da yake haihuwar fari ce ana iya ƙarawa ma a yi arba'in biyu wani sa'in ma in mijin mai sakin fuska ne bai nuna alamar gajiyawa ba har arba'in uku ana yi" Ta ce tana ƴar dariya. "Inyeee to abin ya zama hauka kuma ba zaman wanka ba, ke yanzu sai ki yi sama da watanni uku a gidan mutane yo ai har yaron ya fara zama ma, amma ana yiwa uwarsa zaman wankan haihuwarsa ai da kunya ma gote-gote da ke ki zauna a gidan yara har arba'in uku" "Ni fa ba wai cewa na yi zan yi arba'in uku ba kawai dai ina faɗa maka ne abin da ake yi, amma ni kwana hamsin zan yi, sannan jar miya da naman kaza sun ratsa ni" Ta faɗa tana lashe leɓenta dan har yawunta ya tsinke. "Ko da na ji, Allah kiyaye" "Amin, amin Malam" Ta ce tana kallon Tasalla da ta cika ta yi fam kaɗan ya rage ta yi bindiga dan baƙinciki. "To Tasallele, mu zamu tafi birni sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, kike sana'ar man ƙuli na da nake yi dan kar kasuwar ta yi ƙasa ganin ana zuwa nema babu sai mutane su ɗauka na daina yi ne kwata-kwata amma in kina yi da na dawo sai in ɗora daga inda kika tsaya, kuma kowa ya tambaye ni ki ce masa na tafi Kano ta dabo tunbin giwa jikata ta haihuwa zan mata ZAMAN WANKA" Ta faɗa tana dariya, Malam dai kaibya girgiza a ransa yana tunanin ranar da matan nasa za su girma gashi dai sun tsufa amma in suka yi wani abin kamar yaran mata. Haushi ne ya ƙara cika Tasalla wato bayan sana'arta ta waina, hallaw take sana'ar mai da ƙarago ita tana can tana cin shinkafa da miya da nama, har wata ƙwallar takaici ce ta kawo a idonta. Ganin Malam ya kalleta ta daddage ta danne ta ce mata "Sauka lfy" "Sana'ar man ƙulin fa?" Ta tambaya da sheƙiyanci. "Ba zan yi ba" Ta bata amsa a takaice. "Kin huta" Ta faɗa tana dariya dan ta lura Tasallar ta shaƙa sosai. "Amma kin san dai yanzu motar kasuwa ta tafi, sai dai ki hau machine ki je Garki ki hau motar Kanon a can ko?" Malam ya katse musu maganar dan ya lura abin na neman zama fitina gwara a rabu lafiya. "Eh dama yanzu mota ai ta tafi dan rana ta yi sosai dan azzahar ma ta kusa hantsi ya dubu luday" "Yawwa a gaishe su" "Za su ji" Ta faɗa tana tashi daga zaunen da take ta buɗe labulen ta fito daga turakar Malam ɗin. Ɗakinta ta koma ta ɗakko lalle ta sanya a bakkon (Ghana mostgo) Ta ɗaga dakyar ta fito da ita daga ɗakin ta ajiye a ƙofar ɗakin ta ɗakko kwaɗo ta kulle ɗakinta ta sanya mukullan a cikin pos ɗinta. Ƙofar gida ta fita ta sanya Lawwali almajirin Malam ya samo mata mai machine, aka ɗakko jakar za a fice da ita dai dai nan Malam ya fito daga ɗakinsa ya ga Lawwali ɗauke da jakar. "Azumi lafiyarki kuwa?" Ya tambaya da mamaki. "Me ka gani Malam" Ta faɗa cikin nuna rashin fahimtar inda tambayarsa ta dosa. "Wannan jakar ce za ki yi tafiyar da ita, kin shaƙeta da kaya kamar wanda za ki ƙaura can" "Ba fa kaya bane kaɗai Malam har da bargona a ciki ka san lokacin sanyin nan kar inje ina bani-bani a gidan yara gwara na tafi da abuna" Ta faɗa tana murmusawa. "To ai shikenan" Ya faɗa, suka fito tare ta hau machine almajiran Malam na ta ɗaga mata hannu, ta tsakiyar ƙauyen suka bi duk inda suka wuce ana ɗaga mata hannu alamar Allah kiyaye dan an ganta da jaka a gaban machine kuma duk yawanci an san tana da ƴan uwa a birni da yake ma ƙaramin ƙauye ne, tun da a can ne ma ta fara aurenta na fara har ta haifi ɗanta ɗaya tilo kafin ta auri Malam ɗin, da har yau basu taɓa haihuwa da shi ba. Duk inda suka gifta sai hannu ita ma take ɗagawa alamar ta tafi har sai da suka hau hanyar da za ta sada su da garin Garki L.G sanna ta sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ranta fari ƙal tana jin wani nishaɗi dan babu abin da ya fi faranta mata sama da yadda Tasalla ta shaƙa, da kuma yadda jama'a ke ta ɗaga mata hannu lallai zuwa birni da daɗi.Gabanta ne ya bada wani rass tuno da halin mijin Halimar sam bashi da sakin fuska ga rashin ta ido, tunaninta ma yadda zaman zai kasance... To fa dandandan dan dan dan dan, ku biyo ni dan jin wannan labari mai cike da barkwanci, shin ya zaman zai kasance tsakanin masu gida da kuma ƳAR ZAMAN WANKA 🥰😘😍 Mai son cigaban labarin ya mn mgn 09030283375 wtsapp only 👩‍🍼ƳAR ZAMAN WANKA🤱 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️2️⃣ Tun da ɗan acaɓan ya kaita tasha, ta biya shi kuɗinsa har gaban mota ya ajiye mata jakarta tana ta zabga masa godiya kamar wanda ya kawo ta kyauta. Mota na cika suka kama hanyar Kano, Inna Azumi ta samu wata tsohuwa mai shegen surutu irinta aikuwa suka rinƙa zuba kamar daman sun san juna, tafiya ta yi tafiya Inna Azumi ta fara gyangyaɗi a haka suka ƙaraso Tashar ƴan kaba ɗan sahu ta samu unguwa uku zai kai ta, suna cikin tafiya ta tuna cewa bata sanar da Mamar Halima ba dan dama ƙarya ta yiwa Malam a kan cewa ta ce ta taho, kawai dai Inna Azumi ta kira su gaisa sai take ce mata suna asibiti Sadiya na naƙuda shi ne fa ta shiryo ta taho ba tare da ta sanar da ita ba. Ganin wayar babu caji ta mutu ta taɓe baki a zuciyarta ta ce "Yo ya za a yi da ni, ni da gidan ɗana duk da dai ya mutu amma ai babu mai korata daga gidan jikokina, dole na je na tabbatar kar na fara zuwa gidan Halima(Sadiya) Na tarar an bar ta a gidansu saboda wankan jego, ko da kuwa ma hakan ta kasance dole na mayar da yarinyar ɗakinta na mata zaman wanka dan ba kasafai wasu mazan ke son matansu su je gidan iyayensu wankan jego ba" Tana cikin saƙar zucin ta lura sun kusa layin da za a ajiyeta, dan haka ta shiga nunawa ɗan sahun inda zai bi har dai suka ƙaraso ƙofar gidan, idanu ta ƙwalalo lokacin da ta yi tozali da danƙareran kwaɗo a ƙofar gidan ɗan sahu bai ankara ba ya ji ta ce "Na shigenge ni Azumi" "Lafiya dai Baaba" Ya faɗa yana kallonta da mamaki, ganin ta dage sai zabga salati take kamar an ce wani ya mutu. "Yo ba dole ba na yi salallami ɗan nan ka ga gidan da na zo a rufe" "Haba Baaba ya za a yi da ki taho baki sanar da mutanen gidan ba, gudun haka ne ya sa ake faɗa, gashi na ga da alama ma kamar ba a gari kike ba dan na ga lokacin da kika sauka daga mota" "Wallahi kuwa ɗan nan ba a gari nake ba daga wani garin nake, amma na san inda zan same su, mu je tarauni" "To Baaba" Haka ya juya kan napep ɗin suna tafiya tana ta faman surutu har suka kawo ƙofar gidan da ta nuno masa zai ajiyeta tun kan su ƙaraso. "La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W, yau dai na ga ta kaina wannan wane irin abu ne kamar an haɗa baki" Ta ƙarasa faɗa tana tafa hannuwa. Ɗaga ido ɗan sahun ya yi aikuwa ya sauke a kan ƙofar gidan ashe nan ɗin ma a kulle. "Gakiya Baaba kin taka fawul a ce ko ina babu kowa kamar basa son zuwanki" Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya. "Kai ɗan nan ka kiyayeni ni nan da kake gani can gidan ɗana ne nan kuma gidan jikata kuma na san inda suke suna asibiti jikartawa za ta haihu zatona duk sun dawo shi ya sa" "To ki musu waya mana" Bani sa caji kai bari dai ka ga" Ta faɗa tana fitowa daga napep ɗin ta lissafa kuɗinsa ta biyashi kamar yadda ya faɗa, ya fito mata da jakar kayanta kamar yadda ta buƙata. "Baaba ziyara kika zo ko ƙaurowa kika yi?" Ya faɗa cike da sheƙiyanci lokacin da ya ɗaga bakkon ya ji wani uban nauyi. "Ka ji ni da ja'irin yaro to ina ruwanka" Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan da ke maƙotaka da gidan Sadiyar, shi kuma ya ja ya tafi yana ta dariya dan hatta yadda take magana dariya yake bashi, ga wani uban gwaggwaronta kamar bututun zuba kalanzir. Tana shiga suka gaisa da matar ta sanar da ita gidan Sadiya ta zo a rufe, nan matar ta ce suna asibiti tun da sassafe. Matar ta ce ta zauna kafin su dawo dan ta gane kakar Sadiya ce ta taɓa zuwa gidan sun haɗu lokacin ita Inna Azumin ta zo, cewa ta yi bari ta samu ko almajiri ne ya ɗakko mata jakarta. Imran ne tafe a kan machine ɗinsa roba -roba matashi ne matashi ne dan ba zai haura shekara 26 ba ɗan gayu ne dan yanzu ma yana tafe a machine ɗin sai wani dube -duben jiki yake, lokaci zuwa lokaci yana sanya hannu ya karkaɗe rigarsa duk da ba komai a jiki amma saboda kawai tsabar tsafta da ƙyanƙyami yake karkaɗewa. Imran bashi da son mutane gashi da ƙyamatar ya ga an kusanci inda yake sai wanda ya yi niyya sai kuma wanda jininsa ya haɗu da nasa. Ba ya son duk wani abu da zai shiga tsakaninsa da farincikinsa wato matarsa Sadiya yana son ta sosai saboda auren soyayya suka yi hakan ya sanya ba ya son duk wani abu da zai sa ya yi nesa da ita ko ya nesanta shi da abar ƙaunar tasa. Ya fi so koyaushe idan yana gida ya kasance tare da matarsa, gashi mutum mai yawan buƙata, shi ya sa ko yaya ba ya son wani abu ya haɗashi da Sadiya bare ta yi fushi, idan kuwa hakan ta kasance to ya kan yi iya ƙoƙarinsa ya shawo kan ta dan kar ya rasa biyan buƙatarsa dan bashi da haƙuri ko kaɗan a wannan harkar, sai ya samu matar tasa ita ma mai burin faranta masa bata so ko kaɗan ta hana shi kan ta. Ya kusa ƙarasowa gidansa ya hango wata ƙatuwar jakar bakko a ƙofar gidan, cikin mamaki yake kallon jakar da kuma neman dalilin ajiyeta a ƙofar gidansa. Cikin sauri da azama ya ƙaraso har yana neman faɗuwa a machine ɗin dan ba ya ƙaunar abin da zai haɗa shi da kayan wasu, dan shi akwai tsare gidan ko maƙota iyakarsu gaisuwa tsakaninsa da su dama shi ba wani yawan magana yake ba bare zaman majalissa in har ba wurin aiki ya tafi ba to yana gida tare da iyalansa, sai ko idan ya je gaishe da Hajiyarsa. Yana faka machine ɗin ya ƙanƙance idanu yana kallon jakar, kallon da ya mata ma sai ya ji yana tsantsaninta dan sai ya ga duk ta yi wani ƙura, ko kuwa dan bai yarda da jakar bane oho ya ɗago kai yana son gano yadda aka yi jakar ta zo ƙofar gidansa sai ya ji wata murya tamkar daga sama an ce. "Shikenan ma na huta ga Imirana nan" Shiru ya yi tare da runtse idanunsa da ƙarfi, jin an kirashi da sunan da ba ya so kwata-kwata, kuma ma duk duniya ya san babu mai kiransa da sunan nan sai kakar Sadiya wato Inna Azumi ita kaɗai ke kiransa, kuma ya shaida muryarta dan ko daga bacci ya tashi ba zai kasa shaida muryarta ba. Shi ya rasa me yasa matar nan take son takurawa rayuwarsa, sam ba ya son wannan nuna ƙoƙon usulin da take nuna masa dan yana auren jikarta, shi ko ƴarta yake aure ba ya son takurawa amma ita ta kasa ganewa, sannan duk miskilancinsa na ƙin son magana da mutane sai da ya daure ya faɗa mata cewa Imran ake kiransa dan idan ta kirasahi da Imirana nan ji yake kamar ta kwaɗa masa gudum a kan sa. "Ashe ma kana kusa har nake bin gidan maƙotanku ka ganni nan saukar yanzu tsal ɗin nan" Ta ƙara faɗa tana ƙarasowa wajensa ba tare da ta jira ya ce wani abu ba, cije gefen lips ɗinsa ya yi yana ji da a ce wani ne da ban ba tsohuwa ba yake damunsa kamar yadda tsohuwar nan ke damunsa da sai ya ɗau mummunan mataki. "Eh" Kawai ya ce hakan ma dan ta kasa kunne ne ta gane me ya ce amma da gungune ya yi maganar. "Allahu akbar Imirana har yanzu dai kana nan da wannan mugun halin naka, kai wane irin mutum ne da baka sakewa da mutane ku yi magana ma ta fatar baki kawai ni fa kakar ka ce ba sirikar ka ba" Ta faɗa tana kallon fuskarsa da ya haɗe ta murtuk kamar zai saki kuka. "Sauri nake" Shi ne kawai abin da ya ce, shi ma dai da ƙunƙunen ya faɗa. "Oh Allah na shiga aljanna na maƙale, yanzu baka ce min Inna ina wuni an zo lafiya ba sai ka zauna kana min magana kamar mai ciwon haƙori, ko kallon arziƙi na kasa samu daga wajenka" Banza ya mata ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan. Inna Azumi kuwa baki ta taɓe, dan ta lura in ta ce za ta ga yadda take so to zuciyarta sai ta yi bindiga bata samu yadda take son ba, gwara ta lallaɓashi a rabu lafiya, bare ita da ta zo dandalar arziƙi. "Sa'adiyyar ta sauka ne?" Ta faɗa tana kallonsa yana cire kwaɗo daga jikin ƙofar gidan. Bai bata amsa ba a take ta tuna da katoɓarar da ta yu, dan dama Sa'adiyya take kiran Sadiya amma saboda kwainane irin nasa ya ce wai ta fiya ɓatawa mutane suna ganin baya iya faɗar Sadiya sai Sa'adiyya sai take cewa Halima saboda jarabar Imran ɗin dan duk ranar da ta zo gidansa haka zai yi ta mita a ƙunƙunen nan har dai ta ɗan canja sannan ta samu salama. "Na ce Halimar bata sauka bane?" Ta gyara sunan dan ta matsu ta ji halin da jikarta ke ciki. " Ta sauka" Ya faɗa a takaice yana tura ƙofar gidan ya shige ya bar Inna Azumi a tsaye baki sake, da ya shige ma sai da ya ɗan turo ƙofar. "Yau na ga abin da ya isheni, a haka zan yi har kwana hamsin ɗin, ana wannan zaman doya da manjan, taɓɗi aikiwa duk abin amarya sai an sha manta wallahi ko me za ka yi sai na zaina ZAMAN WANKAN nan dan ban ga abin da zai sanya na fasa ba dan kana wannan fisfigar" Ta faɗa a ranta tana tura ƙofar ita ma ta shiga gidan tare da jan jakarta ta shigar da ita dakyar saboda nauyi, Imran da ya dawo domin ya ɗakkowa Sadiya zani saboda zannuwan sun yi kaɗan yana cikin sanya zanin a leda ya jiyo ƙaran jakar Inna Azumi tana janta ƙiiiii. "Me yasa matar nan ta shigo min da ƙazamar jakarta gidana" Ya faɗa a ransa, ya yi sauri ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya sanya hannu ya fusgi labule da ƙarfi ya fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar dan ma kar ta yi gigin shigar masa da jakarta ɗaki dan ba ya jin zai iya bacci ma idan jakar tana ɗakin saboda ƙyanƙyami. Baki sake Inna Azumi ke kallonsa har ya gama kulle falon, yana wani ɗaɗɗaga kai kamar ya ga kashi ya ce. "Asibiti zan koma" Sai da Inna Azumi ta saurara da kyau sannan ta gane me ya ce. "Yo ni ma ina na ga ta zama, ai ba zama wai an ɗaurawa karya zani, mu tafi sabitin in je in gan su dan can ma gidansu na fara zuwa a rufe, na zo nan ɗin ma ashe dai basu dawo daga asibitin ba" "Eh" Kawai ya ce dan shi kamar mai ciwon baki haka yake ba ya son magana ko Sadiya sai ita ta yi ta masa hira shi dai sai umm da um, um kawai ko da zai yi maganar ma to ba wata mai yawa ba sai dai kuma ranar da ya ga dama sai ya yi maganar amma ba sosai ba. Yana fitowa ita ma ta fito ya rufe gidan, aikuwa sai ga wani mai napep zai wuce ya tsayar da shi ya ce ya ɗauketa sai ya biyo bayansa. "Wannan yaro da mugun hali yake" Ta faɗa tana taɓe baki ta shiga napep ɗin suka bi bayansa. Maƙociyar Sadiya kuwa da ta leƙo ganin Innar bata dawo ba, ganin Imran ya sa ta juya ta koma gidanta dan ita ko gaishe shi ta yi banza yake yi in ma yana amsawa to ita bata ji, sai ma ta daina gaishe da shi ganin rainin wayo da rainin hankalinsa dan ita tana mamakin yadda Sadiya take zaune da mutum kamar gunki. Tun da suka fara bin Imran yake zabga uban gudu kamar zai tashi sama, da yake kuma unguwar kwana -kwana ta yi yawa ga ƙurunƙusai sai ya zama na Inna Azumi tana ta tangal-tangal a cikin napep ɗin saboda yadda ɗan sahun shi ma ke zuga gudu abinsa. Inna Azumi hannu ta sanya ta kama ƙarfen napep hagu da dama ta ƙanƙame dan ji take gabaɗaya kamar juyata ma ake yi. Idanu ta ɗaga ta sauke a kan me napep ɗin fa bai wuce shekaru sha tara zuwa ashirin ba, ga wani uwar suma a kan gashin ya yi cibir-cibir har da matajin kai a soke a jikin gashi, ga wani uban kiɗa da ke tashi a napep ɗin tamkar ma kiɗan jijjiga napep ɗin yake. "Wai ni kai kwa yaro bahaushe ne?" Inna Azumi da bakinta baya shiru ta tambaya tana mai ƙuga maganar da ƙarfi yadda zai ji.. "Ke tsohuwa da wane yare na miki kama"?" Ya faɗa yana sakin wani uban fito da duk ƙaran kiɗan amma bai hana fitowar fiton ba. "Ai tambayrka na yi dan na ga alama hausa bara ganka ba" "Inyamuri ne ni, ko na miki ne, kina ciki" "Amma wannan yaro an yi shegen yaro yanzu ka dubeni tsofe-tsofe da ni ka ce ina sonka? Amma gidanku ba manya" "Sun ƙare" Ya bata amsar yana sanya hannu ya ciro matajin ya ɗan taza kan ya mayar ya soke. "Baby kin yi shiru" "Uwarka ce baby, wallahi tsakani na da kai Allah ya isa, ni Azumi na ga ta kaina. "Ba dai shaƙa kika yi ba Hajiya, ban da ƙauyanci dan na ce baby ba wai yarinya nake nufi ba, wasan kaka da jika ne fa" "Ƙauyancin uban wa? Na ce ƙauyancin uban wa, to tun kafin a haifi uwar mai sabulu farfela take da farinta" Ta faɗa tana jin kamar ta saki fitsari dan gabaɗaya an dagula mata lissafi ga yunwa ga wani fitsari da ya cika mata mara ga wannan jijjigar da napep ɗin ke yi sai ta ji a ranta ta fara ɗan da na sani kaɗan ba da yawa ba na tahowa ZAMAN WANKA, da tana gidanta da yanzu ta ci ta ƙoshi tana bacci ko kuma tana kama ƴan kuɗaɗenta daga masu zuwa siyan mai da ƙuli amma wani ɓangaren na zuciyarta sai ya bata ƙwarin gwiwa. "Kar ki karaya bayan wuya sai daɗi, daga yau ne fa wahala ta ƙare za ki fara cin kayan daɗi" Wani murmushi ne ya suɓuce mata har sai da ta ɗan rausaya kai. "Ka daina zabga wutar nan haka gudun ya yi yawa" "Bakya ganin yadda wanda muke bi yake gudu kamar zai tashi sama. "Rabu da Imirana mugun hali ne da shi ka yi tafiyarka a hankali ka ji" "In ya ɓace mana ke zaki kaimu wajen da za ku je?" Shiru ta yi bata ƙara magana ba, wata kwana Imran ya shiga dai dai wani gida ya faka machine ɗin ya sauka ya faka machine ɗin ko kallon su Inna bai yi ba ya tura gidan ya shiga. "To ki fito mana tun da mun zo ashe ma babu wani nisa sosai" "Nan ne asibitin?" "Asibiti kum?" "Eh mana asibiti za mu je" "Haba Hajiya nan ya miki kama da asibiti nan ai gida ne" "Gida kuma, wai ni me ya sa Imirana ya raina mutane ne haka, ya za a yi ya shige wani gida ya bar ni ko bayani ba zai mini ba" Ta faɗa tana saurin sakkowa daga napep ɗin ta ce mai napep ɗin ya jira ta, a fusace ta tura ƙofar ita ma ta shige tana shiga ta ga wani ɗaki da ke a farkon shiga gidan, bata yi wata- wata ba ta bankaɗa labulen kawai sai ganinta suka yi bakam ta shigo kamar an jefo ta. Wani kallo da Imran ya jefawa Inna Azumi shi ya sanya ta wayance ta ce "Ikon Allah ashe ba mu zo asibitin ba, wallahi duk zatona ɗakim haihuwar ne nan" Ta faɗa tana saurin juyawa ta fito da sauri dan shi da wani da alama abokinsa ne ya miƙo wa Imran ɗin zamzam a robar zamzam. Abokin kuwa yadda Inna ta yi ya matuƙar bashi dariya, Imran kwa tsaki ya yi ya fito ya hau machine ɗin. Inna kuwa mai napep ganin ta fito da sauri sai abin ya bashi mamaki har ya so bashi dariya. "Kin masa magana?" Ya tambayeta lokacin da ta fito ta shiga napep ɗin. Inna da gabaɗaya take a ruɗe ba wai kallon da Imran bane ya sa ta gigice ba, abokin nasa ne babu kaya a jikinsa daga shi sai ƙaramin wando wanda ake kira inpant, to har ga Allah bai san ya yi wawan zama ba ashe Inna ta hango abu ya leƙo ta ƙafar wandon wannan ne abin da ya ruɗa ta dan ita yaushe rabonta da ta yi ido huɗu da bananar ma ta manta, dan su yanzu an tsufa, ganin bananar abokin Imran ne ya ruɗa ta, hakan ne ya ruɗa ta ta dawo da sauri har tana neman yin tuntuɓe. Dan da alama ɓa abokin nasa gwauro ne dan ɗakin nasa a bakin ƙofar gidan ne daga ciki kuma tana jiyo hayaniyr mutane daga cikin gidan. " Ashe ruwa zai kama" Ta faɗa dan ta waske amma a ranta sai salati take ko idanu ta rufe sai ta ga abu kawai. Da haka dai har suka iso asibitin bayan sun sha uban gosulo. A wurin da aka tanada dan ajiye napep a nan ya sauke Inna haka ya yanka mata uban kuɗi ta bashi, dan Imran ko tsayawa bai yi ba bare ta sa rai zai biya kuɗin napep ɗin. Tana bawa mai napep ɗin kuɗi ta fara sauri-sauri gudu-gudu dan ta tarar da Imran dan machine ana iya zuwa da shi har ƙofar ɗakin da mutum zai je da ke asibitin na gwabnati ne, ashe da ɗan tazara zuwa ɗakin haihuwar dan haka kafin Inna ta kawo ta gama jigata dan ma tana iya hango Imran ɗin da yake wurin babu kwana bare ya ɓace mata. "Oh ni da bani da kuɗi yau da na tagayyara, wannan yaro ko kaɗan bai san mutunci ba, uwarsa kwa ba haka take ba lallai albasa bata yi halin ruwa ba, na ɗauka shi zai biya min kuɗin tun da shi ya tsare ɗan sahun amma sai ni na biya, ko ma ya tsaya idan ma ba zai biya ba, sai ya ce Inna ki biya kuɗin amma shiru maƙatau babu niyya wai ango ya kwana da wando" Take ta zancen zuci har ta ƙaraso wurin ɗakin haihuwar. 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️3️⃣ Ƙarƙashin bishiyar da aka tanada dan zaman masu zaman jinya can ta nufa inda ta hango Imran ya yi, dakyar take iya ɗaga ƙafarta dan lokacin har an yi sallar la'asar amma Inna ba azahar ba la'asar dan wajen sha biyu ta baro ƙauyensu. Da jan ƙafa ta ƙaraso wajen da suke zaune a tabarma, dan tun daga nesa ta hango Hajiya Amina mahifiyar Imran, Ashrof ƙanwar Sadiya, sai kuma Ruƙayya mahaifiyar Sadiya, sai Imran da ke gefen mahifiyarsa da alama magana yake mata "Wash Allah nah" Cewar Inna kamar an shaƙe mata wuya tana neman kan tabarmar ta zauna daɓas. Da mamaki suke kallonta su duka, Inna Azumi kwa saboda wahala ta ma manta da cewar ba a san da zuwanta ba. "Inna!" Ashrof da Mama Ruƙayya suka faɗa da mamaki. "Rakiya dan Allah ku taimaka min da ruwa wallahi maƙoshina duk ya bushe ƙamas ko yawu na haɗiye sai na ji wucewarsa wani garrrr yana cin birki saboda bushewar maƙoshin a maimakon na ji wucewarsa midik" "Humm ai bari ba shegiya bace da ubanta" Cewar Imran a zuciyarsa dan yadda idanun Innar suka koma sun wani ƙanƙance kaɗai ya isa ya sanya ka dariya duk ta fita hayyacinta, ga gwaggwaron gaban goshin ya koma gefe har ɓangaren hagun ɗin ɗankwalin ya zamo ya ɗan rufe gefen idonta amma duk bata kawo a ka ba. "Inna wai kin ganki kwa kamar wata maroƙiyar" Ashrof ta faɗa tana tuntsurewa da dariya. Inna ji ta yi ba za ta iya magana ba, amma da sai ta ji amsa dai dai da tambayarta, amma ina! Babu hali. Hatta Mama Ruƙayya da Hajiya Amina dariyar suka ƙunshe ganin Innar a birkice sai wani faman nishi take kamar ta yi tseren gudu. "Gashi Inna" Mama ta faɗa tana miƙa mata pure water guda ɗaya da ta ɗakko a cikin leda. "Haba Rakiya kamar wata almajira, za ki bani ruwa ƙwalli ɗaya" Ta faɗa a fusace dan ita ba ma ruwan ɗaya bane ya ɓata mata rai, so ta yi Mamar ta ce mata ga abinci dan ta tabbatar yanzu idan ta sha ruwan nan cikinta ƙullewa zai yi. Mama kwa faranti ta ɗauka ta ɗora ruwan har huɗu ta miƙa Innar, har lokacin tana mamakin zuwan na Inna Kano da ma yadda aka yi ta gane asibitin da suke. Ruwan ta kalla guda huɗu ga cikon na biyar ɗin a hannunta,ta ce. "Kai Allah na tuba wannan ruwa kamar wata saniya ina zan kai shi ma son in sha ya ƙulle min ƴaƴan hanji, mu wallahi zamanin da ba haka muke yiwa baƙo ba sai mun fara gabatarwa baƙo sanwa (Abinci) Kafin mu kai ga bashi ruwa, amma yanzu zamani ya banbanta halayya wani wurin ma sai ka je baƙunta ka tafi amma ko ruwan ma ba zaka samu ba to amma ke kin yi ƙoƙari ma da kika bada ruwa har biyar da babu gwara ba daɗi amma da ace ko kaɗan kuna haɗawa baƙi da abinci duk ƙanƙantarsa ai da hanau ƙwara mannau" Ta faɗa tana sauke idanunta a kan wasu food flaks har guda uku da ke ajiye a gefe. "Wai Inna dai ko yunwa kike ji?" Ashrof ta tambaya tana kallon Inna da sheƙiyanci ganin duk idanunta ya faɗa bakin nan a bushe kamar mai azumin nafila. "Yo Allah na tuba yunwa sai ta karni za a san ina jinta, cikin nan nawa kaɓar an yi shara ko motsin ɗiyan hanjina bana iya jiyowa duk sun yi likimo ko kuwa suma suka yi" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce. "Asharofa kar fa ki min fassara ato, ni ba wai ina roƙon a bani abinci bani kawai dai ina koyawa uwarki abinda ya dace ta yi ne, idan ta yi baƙi amma ba wai kaina nake yiwa tanadi ba" "Wannan tsohuwa da shegen ɓatawa mutane suna take, wai asharofa sai ka ce wata tinkiya, ni ta ce min Imirana kamar wani gatari, sannan ko Sadiya ma Sa'adiyya ko kaɗan bata iya seta bakinta kamar wacce aka gutsirewa gefan harshe" Imran ya faɗa a ransa yana aika mata da harara a ɓoye. Kunya ce ta rufe Mamar Sadiyar jin furucin da Innar ta yi, ga sirikinta ga Babar sirikin amma ko kaɗan Innar bata san kunya ba. " To da yaushe ma ta zo, ko gaisawa fa ba a yi ba amma har ta ɗora min laifin rowa, ni ban taɓa ganin tsohuwa mai rangwangwan irinta ba" Mama ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce. "Inna wallahi ina shirin baki abinci ne ka wai dai wani lokacin an fi fara gabatar da ruwa kafin abincin ne" "A'a Rakiya a lokacin zafi ba amma a lokacin sanyin nan ai an fi jin yunwa a kan ƙishirwa, amma ba wai ina nufin ina cewa yunwa nake ji a bani abinci ba, kawai da ku ɗauka hira ne muke kowa yake faɗar abinda ya dace a yiwa baƙo idan ya kai ziyara " Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba. "Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi. "Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina. "Da me ya kai ki bin Imran yaron da ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku da ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce." Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba. "Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi. "Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina. " Humm Inna kenan, a nunawa na rigingine farin wata, ai ni sai dai na bada labarin Imran, dan ma ni yana raga min kasantuwata mahaifyarsa, kema da gangan ne ai, duk wanda ya sayi rariya ai ya san za ta zubda ruwa, me ya kai ki bin Imran yaron da, ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku daga ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce. "Sannu Inna gaskiya kin yi ƙoƙari, wallahi kai kuma Imran ka kiyayeni a kan me za kake gudu baka ganin tsohuwa ce?" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Imran da ke wani haɗe rai yana kauda kai gefe irin bai yi laifin ba ma. "Hajiya baki san yadda tsohuwar nan ta takura min bane, ta kasa fahimtar ni ko ganinta ban son yi" Cewar Imran a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce. "Sorry Hajiya" Ya faɗa yana sosa ƙeya. "Au Allah, wato sorre, a soron gidanku na kwana, kai kenan taƙidarancin naka har uwarka bai baka bari ba to Allah wadaran naka ya lalace wallahi" Cewar Inna tana jijjiga kai irin na ga abinda ya fi ƙarfina. Mama kanta ta kawar gefe tana jin wata irin kunya ganin gabaɗaya Inna tana kwance musu zani a kasuwa. "Ina za a kai wannan abin kunyar? Ta faɗa a ranta. "Haba Inna ki yi shiru dan Allah" Ashrof ta faɗa jin ɓaran-ɓaramar Inna ta yi yawa. "Ashrof miƙo mata abincin" Mama ta faɗa dan ta kawo ƙarshen maganar. Idanun Inna a kan kwanukan abincin wani mai jan murfi da ratsin yellow shi ya fi tafiya da hankalinta dan tana tunanin wataƙila a samu abinci mai daɗi a ciki, cikin ikon Allah kwa sai Ashrof ta miƙo mata shi, hannunta har karkarwa yake wajen karɓar tana washe baki. "Yawwa Asharofa kamar kin san shi nake hari shi ne a raina" Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta kama kwanan da hannu biyu ta buɗe. Fuskar Inna ce ta sauya har suka lura da hakan, ba komai ya sanya fuskar Inna sauyawa ba sai arba da ta yi da wake da shinkafa. "Ni da na sanya ran wankin ciki, in samu jar miya idan hali har da naman kaza amma in ga wake da shinkafa da mai da yaji, to Allah suturibuƙui inji kishiyar mai doro" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi saurin gyara fuskar ganin kowa ya lura da ɓata ran da ta yi ta sanya hannu ta kai kyawawan lomomin guda biyu, hakan ya yi dai dai da buɗewar da Ashrof ta yiwa ɗaya daga cikin flask ɗin aikuwa Inna ta yi ido biyu da shinkafa da miya ga wani uban namomi a saman. Tufff Inna ta tofa da duka lomar abincin da ta take bakinta taf da shi ta ce. "Amma Asharofa baki da imani wallahi, akwai wannan abincin mai rai da lafiya amma kika bani wannan ci ka mutun?" Ta kai ƙarshen maganar tana ture flask ɗin gaban nata. Gabaɗaya suka saki baki suna bin Inna da kallon mamaki. "Inna abincin Aunty Sadiya ne fa da za ta ci idan ta falka" "Ka ji ni da yarinya mai shegen iyayin tsiya yo Allah na tuba meye marabar dambe da faɗa? Abinda ya yi ni ai shi ya yi yarinyar nan, in kuma kin manta ne in tuna miki" Ta faɗa tana janyo kwanan gabanta. "Ikon Allah na zaune ya faɗi, lallai in da rai da rabo" Cewar Inna lokacin da ta luntuma hannu cikin abincin ta cika hannu ta kai bakinta ko bismillah babu. Mama dai kan ta na ƙasa dan ta rasa bakin magana, dama abincin Sadiya ne Hajiya Amina ta girka mata takanas ta koma gida ta iyo girki dan ta samu ta ci idan ta falka. "Ya rabb, matar nan ta addabemu" Cewar Imran a zuciyarsa yana dafe goshinsa da hannu. Loma ɗaya biyu, a ta uku sai kawa Inna ta saki kuka, kukan da ya sanya duk waɗanda ke kusa da su suka waigo suna kallonta, dan wasu ma zatonsu ko mutuwa aka yi. "Inna lafiya?" Mama ta tambaya da mamaki. "Haba Rakiya ba dole in yi kuka ba, yanzu a ce kuna cikin irin daular nan amma ko ki ce in zo in yi ko da shekara ne a marmarce ni ma in yi wankin ciki amma kika barni ina fama da karta kafura (Miyar kuka) Da tuwon masara wanda in Tasalla ta tuƙa da yake bata iya ba kana ci yana maka dariya" Ta faɗa tana ɗaukan cinyar kaza ta yagi tsokar har wani lumshe ido take. "Na shiga aljanna na maƙale" Cewar Ashrof da bata san ma maganar ta fito ba. "Yo waye zai shiga aljanna ya fito ɗiyar nan kowa ya shiga ai ya ga wajen zama" Ta faɗa tana suɗar hannunta da take jin daɗin miyar har tsakar kan ta. Gabaɗaya mutanen wurin dariya suka saka, wani saurayi da ke tsaye yana kallon Inna daga can gefensu a ransa cewa yake. "Tsohuwar nan da za ta yarda in ɗauketa vedeo in sanya a status na san duk wda ya gani sai ya ci dariya kamar me sannan na san kowa ya gani sai ya yi replay har na rasa saƙon wanda zan duba, wallahi za ta yi kyau da comedy sosai ma" Ya faɗa a ransa yana kallon Inna daga can inda yake yana ta dariya. Imran kwa ganin hankulan mutane duk ya dawo kan su hakan ya sanya a fusace ya bar wurin. Sai da ta cinye abincin tas duk da yawansa ta suɗe kwanan ta maida murfin ta rufe, ta ɗauki pure water biyu ta kora ta ce "Kai garin daɗi ba kusa ba, Allah sarki Malam da ƴar Tasallar sa suna can ana fama da dambu ni kwa nan na samu abinci na ci na yi nak" Ta faɗa tana miƙa hannunta can gefen tabarmar ta tilla wani pure water ɗin ta wanke hannunta. "Jama'a ina wuninku" Ta faɗa tana kallon Hajiya Amina da Mama. Dariya Hajiya Amina ta yi dan wallahi sosai Inna ta bata dariya wato sai da ta ƙoshi ne ma za a gaisa, ita mamakinta ɗaya ma da Inna bata tambayi mai haihuwar ba bare ma abinda aka samu ba, sai ta abinci ma take. "Lafiya ƙalaw Inna, kin zo lafiya" Ta faɗa har lokacin tana ƴar dariya dan wallahi ta kasa riƙe dariyar. "Lafiya ƙalaw, wallahi" Ta faɗa tana maida kallonta kan Mama ta ce. "Kin ji Rakiya yaushe kika koyi mugun hali ne, ace ke baki gaisheni ba ni na gaisheki amma kuma kin kasa amsawa sai ɓata rai kike kamar na miki mugun abu, yo in shinkafar da na ci da nama ne ai rabona ne ya tsaga, ita kuma wake da shinkafar shi ne rabon Halima haka Allah ya tsara tun fil azal ni Hajiya Amina ta girkawa abincin tun da rabona ya rantse sai na ci kin san rabon kwaɗo ba ya hawa sama" "Ina wuni Inna" Mama ta faɗa kamar ta yi kuka dan wallahi yau dai Inna ta gama zubar musu da kima da mutuncin a idon siriki da uwar sirikin ma baki ɗaya. "Yawwa ko ke fa, lafiya ƙalaw ya abin da aka samu, mai ta haifa Halimar?" "Ƴan biyu ne duka maza?" Salati Inna ta ɗauka tamkar an yi wani abu, sai da ta gama salallamewa ta ce. "Amma wallahi kin cuceni Rakiya, yanzu a ce jikartawa ta haifi tagwaye duka maza amma tun zuwana wajen nan kika kasa faɗa min har sai da na ci na gwatse?" Ta faɗa tana sakin wata gyatsa. "Ki yi haƙuri Inna dama jira nake na faɗa miki to kuma na ga kina ta ƙoƙarin ki ci abinci" "A'a babu niyya ango ya kwana da wando, yo bana ci abinci ba, lafiya ce ta kawo haka, yanzu da za ki bi ɗakunan marassa lafiyar asibitin nan, za ki tarar ana ta fama da su a kan su ci abinci, to duk dan basu da lafiya mu kuma da muke da lafiya ai sai mu ci ba sai an faɗa mana ba" "Allah bar mana Inna" Cewar Ashrof tana dariya dan ta m daina jin haushin abin da Innar ke yi kuma dama inda sabo sun saba da halinta kuma mai hali ai baya canjawa. "Amin ƴar nan, in da gaske kike, dan na san wani so yake ma ka mutu y bar ganinka saboda ba ya son ganinka amma babu yadda zai yi da kai sai kallo" Ta faɗa tana kallon inda Imran yake amma sai ta ga wayam ba ya nan, baki ta taɓe ta kalli Mama ta ce. "Wai ina mazajen nawa ne, ko sai na roƙa za a bani in gan su, kuma ita Halima da ake ta faman cewa bata falka ba, ragwanta ta yi a haihuwar har ta suma ake jiran falkowarta?" "A'a allurar bacci suka mata, saboda tana buƙatar hutu" Cewar Mama tana miƙa mata yaron hannunta. "Kai duniya inda ranka ka sha kallo, wato yaron ma yana hannunki amma baki bani ba, ni kuma ban lura ba ko dan an ce hankali ke gani ba ido" Ta faɗa tana karɓa yaron ta buɗe shi tana ta yaba kyansa.Babu wanda ya ce wani abu, sai da ta gama ganinsa ta ce "Wai ina ɗayan ko ba za a bani su lokaci ɗaya ba dan kuna tsoron in gudu da su?" Ta faɗa tana kallonsu. "Wannan tsohuwa da ɗaukan ƙafa take" Cewar Hajiya a ranta a fili kuma sai ta ce ."Kin ga ɗayan Inna, wannan Husaini ne, shi ne ƙaramin wannan kuma shi ne Hassan ɗin, an haifeshi da wata baiwa ne" Ta faɗa tana ɗorawa Inna a cinyarta daga gefe sai ya zamana gefe ɗaya Hassan ɗaya gefen Husaini. "Allah sarki bawan Allah, ashe da baiwa aka haifeshi, yo banda abinki ai an fi son ƴan baiwa" Ta faɗa tana buɗe fuskarsa tana ta sakin murmushin farinciki. Ashrof kwa dariya take dannewa dan ta san yanzun nan Inna za ta tsorata in ta ji baiwar da ke tare da yaron. "Ai gabaɗaya fatar bayan Hassan ɗin ce kamar jikin miciji, kin san wasu ƴan biyun ma ana haifar ɗaya mutum ɗaya miciji saboda baiwa ce id... "Jikin miciji fa kika ce Amina?" Inna Azumi ta faɗa tana zaro idanu jikinta gabaɗaga ya ɗauki karkarwa dan tsoro... Next page.😂😂😂 Yanzu fa aka fara wasan 🤣🤣🤣 Masu son grp ɗin ƴar zaman wanka 09030283375 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️4️⃣ "Kai jama'a shi kuma irin tasa baiwar kenan?" Inna ta faɗa gabaɗaya jikinta ya ɗauki karkarwa, musamman da ta ji Hajiya Amina ta ce wai wasu maciji ake haifa ɗayan kuma mutum. "Wallahi sai ma kin buɗe kin gani da idaonki kin san an ce gani ya kori ji" Cewar Hajiya Amina. Daidai nan Imran ya dawo riƙe da ledoji a hannunsa amma Inna ba wai ta ledojin take ba duk kwaɗayinta da son abin duniya sai ta ji duk bata cikin nutsuwarta. "Ni Azumi barni in mutu maza su kai ni ba mata ba, ai in kin ganni a lahira kaini aka yi" Ta faɗa tana ɗaukan Husainin ta miƙawa Mama ta ɗauki Hassan ɗin hannunta na karkarwa har yaron ya so kuɓucewa ya faɗi. "Haba Inna ya za kike garaje a kan jaririn da aka haifa yanzu" Imran ya faɗa a fusace dan yanayin da Innar ta miƙo yaron tamkar wacce ta riƙo kashi. "Jakar uban nan kayya, ɗan malafar uba ka ce fa, ashe dai kana magana rainin hankali ne yasa kake maƙe murya kamar ka haɗiyi rariyar tankaɗe, to dukana za kayi fa da hayayyaƙo min, yo wa ma ya sani ko haka bayanka yake irin na miciji abu a duhu, wa ma ya sani ko kai yaron ya gado na san ko haka naka bayan yake wannan yarinya Halima ba faɗa za ta yi ba, dan mu kaf danginmu babu masu fatar macizai" "Me kika ce" Imran ya tambaya yana kafeta da idanunsa da suka masa jajir dan da ace matar nan bata da haɗi da matarsa wallahi sai ya shuka mata tsiya tunda ita bata san annabi ya faku ba. "Yo ni kwa mai na ce, abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro" Cewar Inna tana kawar da kai gefe. Hajiya kwa ta kasa furta komai dan yadda Innar ta jangwaɓar da yaron tamkar ɗan mutuntumi ba ɗan mutum ba. "Ina ƴan uwan Sadiya Abdussamad wacce ta haifi ƴan biyu ɗazu?" Wata nurse da ke tsaye ta faɗa tana daga tsaye kan barandar ɗakin haihuwar sai wani yatsina take tana taɓe baki. "Gamu nan" Cewar Ashrof tana miƙewa tsaye. "Haba Asharofa bakya barin in bata amsa dai dai da ita, to in banda raini ta kallemu duk mun haifi uwarta ma mun yi jika da ita ta wani mere baki, ina ƴan uwan Sa'adiyya" Inna ta faɗa tana gwada maganar matashiyar. Wani kallo nurse ɗin ta watsawa Inna, ta ce "Ta falka ana buƙatar mutum ɗaya ya zo, dan sallamarta ma za a yi dan babu matsala" Ta faɗa tana gyara hijabinta da yake iya kafaɗarta. "Bismillahi ku bari ni in je tun da ni kaɗaice banganta ba, ku duk a nan na sameku" Inna ta faɗa tana miƙewa ta gyara ɗaurin zaninta tare da ɗankwali, ta daidaita mayafinta. "Haba tsohuwa ya ana neman masu ɗan gwaɓi -gwaɓi za ki taso bayan ke ma da za a taimaka miki kina buƙatar taimakon, ta ya za ki taimakawa wani?" Ta faɗa tana kama tsantsa. "Ke ki kiyayeni da ganinki ko auren fari baki da shi amma sai a ɗaukeku aiki saboda kun yi karatun masu jajayen kunne, ku ke karɓar haihuwa kafin ku je gidan miji kun gama haddace komai, kun san ta yaya ake haihuwa har kun ɗinkesu tamkar wata ƙwarya, to ni nan har gozomanci na yi a ƙauyenmu" Ta faɗa tana hawa kan barandar da za ta sadata da ɗakin haihuwar. "Inna dan Allah ki bari ko Mama ko Hajiya su je mana ke fa ko ɗakin baki sani ba" Ashrof ta faɗa tana marairaicewa. "Ke rufe min baki matambayi ai baya ɓata, zan tambaya kuma ma Allah na tuba ko daga bacci na tashi ai bazan kasa shaida Halima ba, duddubawa zan yi har in ganta, ke ɗin da gulma ajali in ba a yi ba a mutu" Ta faɗa tana wani gatsinen gefen hanci. "Ki bari Mama ta je" Cewar Imran lokacin da ya ajiye ledojin hannunsa ya nufo wajen Innar dan ya ɗan bata baki, dan shi a kan matarsa zai iya yin komai ko da ba ya so. Mama kuwa ranta in ya yi dubu ya ɓaci ji take dama bata sanar da Inna Sadiya na naƙuda ba da yanzu duk haka bata faru ba ta rasa bakin magana tana da kara, bare kuma ƴar fari ce Sadiya a wajenta, kuma Inna sirika ce a wajenta ko da kuwa ɗanta baya raye uwa ce a wurinta. Bare kuma Hajiya ita mai za ta ce tun da ba daga ɓangarenta Inna take ba. "Lallai Imirana to wallahi in kuma ganin bakinka a ƙunshe kamar wani balangu a takarda, tun da har kana magana, kai da kake da aiki jajawur a gabanka, wato an haifa maka ƴaƴa biyu ai yanzu kamata ya yi ace kana kasuwa siyo sadakin gado (Raguna) Sai ka tsaya kana shiga shari ba shanu" Ta faɗa tana yin gaba ta barshi tsaye baki sake, tana shigewa ɗakin nurse ɗin ta ce "Mutum ɗaya ta taho dan wannan babu abin da za ta yi in ba surutu ba" "To mun gode ki yi haƙuri kin san tsofaffin nan sai a hankali" Hajiya da ta baiwa Ashrof Hassan ta faɗa tana tahowa dan zuwa wajen Sadiya ganin Mama tana yiwa Inna kara ba za ta bita ba. Ashe Inna tsayawa ta yi bata tafi ba, dan haka nurse ɗin na shiga ɗakin ta ganta a tsaye a hanyar shiba ɗakin dan akwai ɗan tazarar zuwa inda masu haihuwad suke. "Ƴar nan an buga an barmu" Inna ta faɗa tana ƴar dariya. ."Nonsense" Cewar matashiyar tana jan tsaki ta juya abinta. "Uwaki ce nosi wallahi ba dai ni ba, ƴar kare kawai da kai tun na haihuwa, ai duk da ban san abin da kika faɗa ba yanayin yadda kika yi maganar da kuma yadda kika yi tsaki na san ba abin arziƙi bane, to aniyarki ta biki" Ganin Hajiya ta taho ya sa ta yi shiru, haka ta bi bayan Hajiyar suka tafi har suka je ɗakin. Suna shiga ɗakin gadaje ne sun kai talatin da yake ɗakin hutu ne inda ake ajiye masu haihuwa bayan sun haihu shi asalin cikin ɗakin da ake haihuwar yana daga ciki amma ana iya jiyo ihun masu haihuwar da ke naƙuda saboda kusa ne ƙofa ce ta raba. "Ke rufewa mutane baki, lokacin da kika je kika karɓo cikin wa ya raka ki wajen mijin, to yanzu ma haka zaki sha wahalarki ke kaɗai" Cewar Inna cikin ɗaga murya, jin wata mai naƙuda ta daddage tana ihu tana cewa a kawo mata agaji. Kowa bin ta yake da kallo kawai wasu na dariya. "Sannunku kun ji, sannunku da ƙoƙari yau kowa ta san yadda ta zo duniya da irin rigiji gabjin da uwarta ta yi lokacin haihuwarta, da wanɗanda yau ne suka yi ta fari da kuma wanɗanda sakewa suka yi, sai a wasa haƙora kuma domin cin sadakin gado "Ragon suna" Cewar Inna da ta buɗe muryar tana ta faɗa wa matan da ke wurin su kwa mai za su yi in ba dariya ba. Hajiya kwa gadon Sadiya ta wuce, ta bar Inna tana ta yawan yi, kallon nurse ɗin nan Inna ta yi ta ɗazu ganin tana darawa kan maganar da Innar ta yi Inna ta mere baki ta ce "To fa harda su kaza a cin danƙo?' Bata jira cewar nurse ɗin ba ta wuce gadon Sadiyar tun kafin ta ƙarasa ta fara rafka uban salati tana cewa. "Wayyo Allah sannu Halimatus Sa'adiyya, sannu kin ji" Wani uban bugawa kirji Sadiya ya yi da ta ga Inna. "Na shigesu mai Inna ta zo yi kuma daga haihuwar ba dai ta zo bane har suna, in kwa haka ne to tabbas akwai matsala dan ta san kafin ranar sunan nan sai ta ginshi kowa" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce. "Yawwa Inna" Ta faɗa a hankali kamar bata so. "Ikon Allah ya wuce mamaki sai kallo, yanzu ke ma Halima halin mijin naki kika koya? Magana kamar mutum baya so ni na kasa ganewa gayu ne hakan ko kuwa rainin hankali ne, ace Allah ya tsaga maka baki dan kake magana amma kake tauyewa baki haƙƙinsa" Cewar Inna lokacin da ta ƙaraso ta samu gefen gadon ta zauna da yake Halimar ma a zaune take ta jingina da filo. Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba. "To ni in baki so zuwana ba in tashi baki alekum in koma inda na fito, dama dan ke zan yi, dan ɗana kuma marigayi, ai dai yau kin ɗanɗana haihuwar kin ji kin banbance tsakanin aya da tsakuwa kin kuma ƙara sanin muhimmancin ƴaƴa a wajen iyayensu da na iyaye a wajen ƴaƴan ma baki ɗaya. " Ni ban ce ba Inna" "A'a to in ma bakya so ai ba faɗa za ki yi ba, dama abu ɗaya ya kawoni amma kuma yanzu ya zama biyu, zuwa na yi in miki barka in miki jaje duk a tare" "Jaje kuma Inna?" "Yo jaje mana, barkar Hussaini zan miki, sai kuma in miki jajen Hassa... Ai Inna bata ƙarasa ba sai Sadiya ta fashe da wani kuka mai cin rai, dan ita zaton ta Hassan ɗin mutuwa ya yi. "Haba Inna ya zaki sakata kuka?" Hajiya Amina da take haɗawa Sadiya shayi dan ta sha ta ji ƙarfin jikinta ta faɗa cikin fusata dan abin na Inna ya fara wuce gona da iri. "Yo ba dole ba in mata jaje ba wannan yaro da fatar bayansa take ta miciji ai abin a jajanta ne, ko ba haka ba bayin Allah?" Ta faɗa tana kallon mutanen ɗakin da wasu hankakinsu ke kan su babu wanda ya ce wani abu wanda ta basu dariya dai sun ɗan dara a ɓoye wanda kuma ta basu haushi sun ji haushi. Dafe kai Sadiya ta yi tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin ba mutuwa ya yi ba dan ita sosai take jin son Hassan ɗin har ya fi na Hussainin saboda baiwar da ke tare da shi. "Shi yasa aka hanaki shigowa amma kika shigo dama na san in banda surutu babu abin da za ki zo ki yi" Nurse ɗin nan da ta taso daga kujerarta da aka tanada domin su ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajen gadon domin yiwa Sadiya allura. Hajiya kwa jin abin da Inna ta ce sai ta ce " Allah kyauta" Tana ga shan shayin, aka mata allurar, Inna dai bata ƙara yin magana ba har Sadiyar ta tashi suka je wurin nurse ɗin ta rubuta musu sallama tare da magungunan da za a siya. Da yake basu da kaya a ɗakin sai kawai kayan shayin Hajiya ta ɗakko suka taho Inna na yiwa ƴan ɗakin sallama tana ɗaɗɗaga hannu masu dariya suna yi ita kwa ko a jikinta dan ita iya gaskiyarta take komai ba dan wani abu ba. Tafiyar da Sadiyar ke yi ce Inna da ke bin su a baya ta lura da hakan ya sa ta ce. "Halima wannan tafiyar tantatan da kike yi fa sai kace wata wacce aka yiwa shayi?" "Haba Inna yo wanda ya haihu har a haɗashi da ɗan shayi, ai haihuwa tafi gaban wasa, bare ita da ta haifi tagwaye kuma ɗinki uku aka mata a waje daga ciki kuwa huɗu aka mata dan bayan an ƙarata ta sake ƙaruwa da kan ta shi ya sa take tafiya... "Halima ɗinki bakwai kenan aka miki sai ka ce wata ƙwarya? Yo ki ce min Sa'adiyya babu bayani yanzu Imirana zai daina wannan rawar kan da rawar ƙafar, tun da duk an miki faci a mafitar ɗa, shi kwa namiji dama wannan wurin yake wa da an ce babu to ke kuwa mace kin kaɗe a wurinsa har ganyenki dan wata zai nema ya aura" "Faci fa Inna sai kace wata tayar keke?" Hajiya Amina da ta dakata da tafiya ta faɗa tana kallon Inna. "Yo meye marabar dambe da faɗa Amina? Da bakinki fa kika ce ɗinki har bakwai to aikuwa bagaruwa ma bata yi wannan aikin ba" Kunya ce da haushi duk suka kama Sadiya abin da Inna ke mata a gaban sirikarta idanunta har ƙwalla suka kawo. Har suka fito babu wanda ya ƙara magana Inna kwa sai taɓe baki take yi abinta. Suna fitowa suka samu an sanya komai a motar abokin Imran da Imran ɗin ya kira domin ya maida su gida, Inna tana hango Imran a zuciyarta ta ce "Wannan ai shi ne sauna kira mana shasha sha in ka ga sakarai ku taho tare, wato dai har yanzu bai tafi neman sadakin gado ba (Raguna) Kar dai a ce ba zai yiwa yaran nan yanka ba amma kwa in haka ne da Imirana ya cuceni ya jayo min abin faɗa a ƙauyenmu, dan yo mai zan ce idan na gama zaman wanka zan koma ƙauye ne babu naman suna son ayi dani cewar ba a yiwa jikata yanka ba, ni da nufi na in a ban kashina in sanya a cikin mai (Kakide) Dan kar ya lalace amma ni ban ga yaron nan yana da niyya ba" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da suka ƙaraso wajen motar. Mama riƙe da Husaini, a baya, da Sadiya, sai Hajiya riƙe da Hassan wanda ta karɓa yanzu a hannun Ashrof, suka shiga gaba ita da Ashrof ɗin, Imran kwa dama a machine ɗinsa zai tafi. "Inna can zaki shiga fa" Hajiya ta faɗa ganin Inna tana wani kalle-kalle ."Haba Amina ai ban ce miki ban sani ba, ko kina nufin a ɗan sahu zan koma ai wallahi ko babu wuri sai dai ɗaya daga cikinku ta haƙura ni in shiga" Ta faɗa tana shiga bayan Imran ya rufe musu ƙofar yana jin haushin Inna. Abid kuwa abokin Imran sai dariya yake abinsa dan sosai yadda Inna ke magana ya bashi dariya ya daɗe yana jin labarinta wajen Imran idan ta zo gidansa wai baya son matar takura masa take sai kuma ɗazu da yake bashi labarin zuwanta a waya, sai yau dai Allah ya sa ya ga Inna da idonsa. Tun da suka hau kan titi take ta kalle -kalle abinta babu wanda ya ce wani abu, zuwa can ta ce "Oh yau ai na ga ta kaina da na biyo Imirana, ko kallon titi ban samu na yi ba, yo ni da lokacin ma ina zaman garin nan ko unguwa zani in ba wani nisan azo a gani gareta ba bana hawa abin hawa da ƙafata nake yawo, yo in a ƙafa ne sai ka gama kallon gidaje masu kyau da abubuwa a hanya amma in a abin hawa ne sai dai ka ke ganin wulgawarsu wul-wul" Ta faɗa tana taɓe baki babu wanda ya tanka ta sai Abid da ke tuƙi yana darawa abinsa. " Ka ji yaro ya sunanka?" Ta tambaya tana ɗan ɗaga murya yadda zai ji ta. "Abid" Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa yana kuma jiran mai zai biyo baya dan ya tabbata sai ta masa ƙwasƙwarima a sunan kamar yadda Imran ya ce ta jagwalgwala masa suna wai Imirana. "Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Abid kuma ka dai ce Abida wato sunan mata ma kai aka saka maka" Sosai Abid yake dariya. "Ka yi dariya man ɗan nan a rasa sunan da za a saka maka sai sunan mata" Har lokacin dariya yake. A haka suka gangara hanyar da za ta sada su da gidan Sadiya, a cikin tafiya aka zo gidan da Imran ya shiga wajen abokinsa, aikuwa idanun Inna suka sauka a kan abokin Imran da ke tsaye yana latsa waya lokacin sanye yake da riga da wanda na yadi. "Abida ka ga wancan wanda ya ɗago maka hannu?" "Na ganshi Inna kin san shi ne?" "Yo ina fa na san shi ɗazu ne dai abokin ka kurma Imirana ya shiga gidan karɓar zaitun ni duk tunanina asibitin ne, ka san shi ba bayani zai yiwa mutane ba, aikuwa na bi bayansa, na shiga ɗakin, ka ga wannan kana ganinsa dai yanzu cikin shigar kamala ko to wallahi in ka ganshi a cikin gidan wasarere yake zama jiki babu kintsi" "Ƙazami ne kenan Inna" "Ashsha wane irin ƙazanta haka dai yake zama jiki babu kintsi ni na san abin da na gani ɗazu" Ta faɗa tana jan bakinta ta yi shiru ganin bai harbo jirginta ba ita kuma ba ta so ta yi ɓaranɓarama shi sa ta yi shiru. A dai dai ƙofar gidan ya tsayar da motar, kowa ya fito Ashrof da Imran ya baiwa mukullin gidan ta buɗe suka fara fito da kayan ita da Abid, haka ta kwasa Abid ya ɗauki wasu kowa ya fara shigowa gidan, da mamaki kowa ke kallon ƙatuwar bakkon da ke shaƙe da kaya sai suka fara tunanin ko Imran ne ya siyo kayan jarirai amma ban da Sadiya da ta san cewa sun sayi komai na haihuwa dan dama tun lokacin da aka mata scanning aka sanar da su ƴan biyu ne. "Allah darki jakata ki yafe mini, wallahi abubuwa sun sha kaina na barki duk kin sha sanyi a wofi, kuma ma dai da laifin wannan ja'irin yaro Imirana yana jin sanda na janyoki amma dan mugun hali ya rufe ƙofar ɗakin ban samu na shiga da ke ba" Inna ta faɗa tana kama makamar da ke jikin jakar. Abid kwa mai zai yi in ba dariya ba wai jaka ake cewa tana shan sanyi. "Inna wai kina nufin jakarki ce wannan?" Ashrof ta jefawa Inna tambayar da mamaki, Sadiya kwa tuni ta buɗe ɗakin da ta karɓi mukulli wurin Ashrof ta shige ɗaki, Mama da Hajiya ma baya suka mara musu. "To ta uwaki ce in ba tawa bace, wato ku kun raina mutanen ƙauye gani kuke mu ba za mu iya siyen jakar nan ba, to tawa je na siya tun lokaxin tana jaka shida da rabi(1300) Ba yanzu da farashinta ya faɗi ba. "Ni fa ina nufin kayan da kika kwaso a cikinta ba wai tsadar jakar ba mai za ki yu da kaya har cikin jakar nan" Tunanin Ashrof kar Inna ta ce sati guda za ta yi sai an yi suna da kuwa sun banu. "Ikon Allah haka fa Malam ya titsiyeni wai ina zani da kaya haka kamar wanda zan ƙaura, yo Allah na tuba kwana arba'in nan ne? Ga lokacin sanyin nan hatta bargona sai da na ɗakko saboda Imirana mai mugun halin nan" Ta faɗa tana zige zip ɗin aikuwa ta yi ido huɗu da abin sallarta. Wani salati ta rafka. "Ni Azumi zuwa birni yau bai min rana ba, yo ina daɗi an manta da faɗar ubangiji, ashe duk abin nan da ake banyi sallah ba, ba azahar ba la'asar ga magriba ta kawo kai" Ta faɗa tana janyo abin sallar daga ciki. "Wai Inna kwana arba'in ɗin me za ka yi da kaya niƙi -niƙi haka har da su bargo?" Cewar Ashrof tana kallon Inna Abid kuwa har riƙe ciki yake dan tuni ya harbo jirgin Inna "Lallai akwai dirama a gidan nan" Ya faɗa a ransa yana ƙara darawa. Ashrof dai baki sake take kallon Inna dan ita ta gane manufarta kawai dai so take Innar ta amsa da bakinta dan ta ƙara tabbatarwa. "Ka ji yarinya da tambayar ƙwaƙwa yo meye baƙo a nan da baki fahimta ba, ZAMAN WANKA na zo in yiwa jikata mana" Inna ta faɗa, hakan hankalinta kwance, hakan ya yi dai dai da shigowar Imran da ya ji maganar Inna tamkar saukar aradu a kunnuwansa, har wani amsa kuwwa maganar ta masa a kunnu, sakin ledar maganin hannunsa ya yi wacce ya biya wani kemis ya siyo... Next page 😂😂😂 Ba a fara ba zaman wanka🤣🤣🤣 Masu son grp na ƴar zaman wanka 09030283375 .......😂😂😂 Mai son shiga grp ɗin dan samun cigaban buk ɗin ya mn mgn 09030283375 Wtsapp only 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️5️⃣ "Zaman wanka?" Imra ya tambaya a fusace. "Eh zaman wanka mana ko a kan ka zan zauna da ka wani hayayyaƙo min kamar wani ubana, ko da dai da duka zaka hauni Imirana" Inna da ta miƙe tsaye daga durƙuson da ta yi tana riƙe da sallayarta. "Haba Inna wai mai yasa kike haka ne, Yaya Imran fa kamar siriki yake a wajenki" Cewar Ashrof kamar ta saki kuka ganin abin da take yiwa Imran ɗin a gaban abokinsa gashi mahaifiyarsa a gidan amma Inna duk bata gansu ba. "Ashrofa, Ashrofa, Ashrofa, kin ji na kiraki sau uku to wallahi ki fita daga sabgata ko ke ce uwata mai daddawa da zaki takura min ko uwaki Rakiya ta yi kaɗan ta ce za ta sani abin da ban yi niyya ba" Wani takaici ne ya sanya Ashrof juyawa da sauri ta shige ɗaki, Imran kuwa juyawa ya yi ya fice daga gidan, Abid da ya juya yana ƙunshe dariyarsa zai marawa Imran baya. "Kai yaka ɗan nan, yo kai sunan naka ne wahalar faɗa gereshi, ka ce ba Abida ba, to koma dai menene zo ɗauka min jakar nan ka shigar da ita ɗaki, dan babu dalilin da zai sa ta ƙara zama a waje sanyin duniya ya ƙare a kan ta" Ta faɗa tana haɗa mayafinta da abin sallar ta rataye a kan igiya. "To Inna" Abid da bashi da zaɓi sai bin umarninta dan haka ya ɗauki jakar ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Hajiya ce ta amsa masa, shi ma gani duk sun yi jingum-jingum sai bai ce komai ba ya ajiye jakar ya fita, su duka suka bi jakar da kallo, suna jinjina ƙoƙari irin na Inna dan basa ce wauta ba a shiga uku. Banɗaki ta wuce ta ɗauro alwala ta shimfiɗa sallayarta a waje ta shiga gabatar da sallolin da ake bin ta, tana sallar amma kunneta a ɗaki. A can cikin ɗaki kuwa Hajiya ce ta katse shirun da cewa "An kawo tukunyar dafa ruwan wanka babba irin wacce ake dafa abincin gidan suna gata can a waje da kuma itace duk suna nan, dama yadda muka tsara da Imran cewa tun da gidana babu nisa da sassafe zan ke zuwa ina ɗora ruwan wanka in wanki jarirai, ita kuma Ashrof take zuwa tana wuni shi ya ce zai ke kwana da su, amma yanzu tunda Inna ta zo ZAMAN WANKA sai a ruguje wannan tsarin" Ta faɗa tana kallon Mama da gabaɗaya damuwarta ta bayyana a fili ƙarara. "Haba Hajiya ya zaki ce haka bayan ga tsarin da aka yi kin san dai gidan nan ciki da falo ne kawai to shin a ina Inna za ta zauna?" Cewar Ashrof cikin sanyin murya. "A gidan uwaki zan kwana, na ce a cinyar uwaki zan kwana Asharofa, wato ma saboda rashin ta ido har zama kuke ku yi da ni, Allah na tuba nawa ne kwana arba'in kwanci tashi asarar mai rai kamar yau ne fa za su ƙare, ban da abinku ma yarinyar da ta haifi ƴaƴa biyu ai kamata ya yi a yiwa Hassan arba'in ɗinsa da ban ta Hussainin ma da ban. Amma shi ne kuka zauna kuna ɗaya biyu, to ni nan gani nan bari farar tunfafiya ko sama da ƙasa za su haɗu babu yadda za a yi in fasa ZAMAN WANKAN NAN" Inna da idar da sallarta kenan ta faɗa tana tsaye a bakin ƙofa dama tana sallar amma kunnuwanta a wajen su Hajiya dan ta ji waye mai son ta zauna waye kuma wanda bai goyon bayan zamanta a gidan. "Allah baki haƙuri Inna wannan fa tsari ne da aka yi tun kafin a san da zuwanki ne aka yanke wannan maganar" "In ma ba a san da zuwana ba ai yanzu an sani, kuma ita Asharofa da take cewa ciki da falo ne a gidan menene aibu tun da har ciki biyu ne wato ɗakuna biyu, shi Imirana ya ɗauki ɗaya mu ma mu ɗauki ɗaya ni da mai jego da jarirai, ke ko ma ciki ɗaya ne a gidan nan sai dai muke yin kai da ƙafa da Imirana ehe" Sadiya jin maganganun Inna suka tuna mata da maganar Imran lokacin tana da tsohon ciki. "Ni fa wallahi ban son wannan al'adar da ake yiwa mace idan ta haihu ta ZAMAN WANKA saboda bana son abin da zai rabani da ke ko na second guda ne da, bare ma ba mu da wadatattun ɗakunan da za a zo gidan nan a zauna, ni zan ke muku komai ke da jariri daga magriba zuwa wayewar gari da safe Hajiya tun da kusa muke sai ta zo ta musu wanka ta miki abin da ya dace in ya so Ashrof sai take zuwa tana wuni tana yin girki" Halima kin ci wake da shinkafar ki" Ta katsewa Sadiya tunani tana ƙarasowa kusa da ita ta zauna wani takaici ne ya tare mata a zuciya.Ganin Sadiya ta ƙyaleta ta ce "Oh ni Azumi na ji na gani an kashe tsohuwa da ranta, ke ma bakya son zaman nawa ko me? Lallai in da ranka kasha kallo, yanzu ke Halima ZAMAN WANKAN ne bakya so a miki saboda ke mahaukaciya ce ke, kin manta gabaɗaya jikin ki faci ne sai fa da aka ɓarka ki kamar wata takarda aka maida aka ɗinke kamar wata ƙwarya, sai da aka miki ɗinki bakwai. So kike a barki daga ke sai wannan kurman yaro a gida cikin dare ya haike miki ya ƙara ɓarka ki, gabaɗaya ki tashi a aiki, dan da ganinsa fitinanne ne ido fici-fici yawa na ƴan cena (China) To wallahi kika sake aka barku ya nemi ya shiga rijiyar jikin ki kika bashi dama wallahi sai dai ke ba wata dan wallahi ko likitoci basa iya ɗinke ki ba tun da wurin ɗanye ne sharaf kuma wani cikin ne zai shiga nan da wata shekarar in dawo suna haɗe da ZAMAN WANKA amma in ina nan aradu ko hannunki bai isa ya kama ba bare ya shiga jiriyar ma, amma dai bari in yi shiru ciki ba dan tuwo kaɗai aka yi shi ba" Ta faɗa tana tashi ta nufi kan frige ɗin falon ta shiga bubbuɗe ledojin da Imran ya kai asibiti. "Kai kurma ma ya san dai dai wallahi ashe siyayya ya iyo mana ta pan zaman jinya ɗan arziƙi, kun ga fa ta faɗa tana nuno musu hanta ce da kayan marmari (Fruit)" Da soyayyiyar doya, da ƙwai cikin ƙwai sai kuma maltina guda biyu masu sanyi" "Ku ɗaɗɗauka " Ta faɗa lokacin da ta ɗauki hanta ta sanya a baki, shi ne ta miƙa musu takarda.Gabaɗaya babu wanda ya karɓa. "Kun huta wallahi ni gaba ta kaini gobarar titi, tabbas idan na yi ZaMAN WANKAN nan na koma Malam ba zai shaidani ba dan ɓulɓul zan yi, taɓɗi Tasalla kwa har baƙinciki ya so kashe ta" Ta faɗa tana neman wuri ta zauna tana cin hantar sai kuma maltina da ta ɗakko ta ajiye a gabanta. "Ke ma Halima bakya ci kenan ai na ga alama ƙam baki kike na masu haihuwa da basa cin komai sai sun ɗan ware" Babu wanda ya tanka ta can ta ce "Asharofa ɗauki maltinar nam ki buɗe min in ke yi ima korawa kai ai wallahi kuna jin daɗin ku ƴan birni, gaskiya na yi wauta da bayan mutuwar kakanku na yi aure a ƙauye, gaskiya Malam ya tsinci dami a kale, yo in ba dan ƙaddara ba ina wanda ke zaune birni, birnin ma kamar Kano zai koma ƙauye da zama, wallahi ko kallon motoci kaɗai kake da dogayen gidaje (Gidan bene) Kaɗai ya isa ya sanya idanunka su yi ƙwari, amma a can ban da dai daga ka tashi karatun almajiran Malam ya hanaka sakat ka koma bacci, ga ka rinƙa haɗa ido da wasu alluna na Malam sai ko kake ganin shanaye da dabbobi in kwa kin ga mota to motar kasuwa ce ta Alhaji Tukur da take cika mutane wani kan wani idan za a tafi cin kasuwa yo Allah na tuba ganin motacin Alhaji tukur duk sun yi tsatsa wallahi ganinsu kaɗai ya isa ya kashe maka ido" "Inna wannan fa kayan Aunty Sadiya aka siyo wa amma kin zo kina ci" Cewar Ashrof tana wani harar Inna. "Oh wallahi ke dai ƴar nan bakya mutuwar tsakar ɗakin ki sai dai ta wani, to tun da na Halima ne kuma na ci to in ji didim" Ta faɗa tana juya wa Ashrof baya. "Ni ban ce zan da ke ki ba Inna amma kike yin abin da ya dace " "Yo ai gwara dai ki dake ni ɗin, ban da ma neman magana ina ma mai ɗanyen jiki (Mai haihuwa) Da shan kayan sanyi ai sai dai ake bata ruwan zafi yanzu babu ita babu shan kayan sanyi sai jikinta ya yi ƙwari nan da watanni masu yawa" "Ɗauki ni ki buɗe min in sha sanyin ya ratsa ni, kar ya huce" "To" Ashrof ta ce ta ɗauka ta buɗe mata. "Da dai da ya fi miki, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki" Ta faɗa lokacin da ta karɓi kwalbar ta kafa kai ta shiga kwankwaɗa har wani lumshe ido take. "Oh Allah mai yadda ya so tabbas rabon kwaɗo bai hawa sama, ai gaskiya in dai zan ke samun haka to babu abin da zai hana ni yin arba'in uku cikakku, kowane yaro a masa kwana murtala uku (60) Wai fa a hakan ma babu madara a ciki, humm yo mu a can daga shekara sai shekara wato da azumi muke shan lemomo dan bana ce lemo ba yo gasarar koko ce ake zuba mata ruwa zuba mata ɗan zaƙi (Sweetner) Shi Malam bai iya siyen lemon takarda (Vevi mis) Haka za a haɗa mu da almajira mu yi kamfata muna kwankwaɗa kamar wasu shanaye, yo ya ka iya da abin da ya fi ƙarfinka ai ko dan ƙishirwar azumi ma ka sha" "Ashrof fita ki samo min ɗan sahu kin ga har an fara kiran sallar magriba" Cewar Hajiya jin ta gaji da sauraren Inna ko gajiya ma bakinta bai yi da yawan magana. "Amina yaushe kuka tashi daga gidan da na sanku" Cewar Inna tana kama haɓa. "Ba mu tashi ba" Hajiya Amina ta bata ansa a takaice. "Wai kina nufin kuna can ɗin har yanzu, kuma nan da nan ɗin ne sai kin hau abin hawa? Tafiyar bata kai ta kawo ba, in ce dai kwana uku za a yi daga nan layin a je gidan naki?" "Eh" "Tabɗi jam" Ta ce tana jijjiga kai. "To wai Inna meye naki a ciki? Sadiya da Ashrof suka haɗa baki wajen faɗa. "Ikon lillahi ai kwa bari in mutu, kafin ku binne ni, ni fa wallahi na fi son tafiyar ƙafa, saboda kallon ababen hawa da gidaje masu kyau, ina tafiya gidan da na ga ya birgeni sai in tsaya in shashshafa shi, ko da dai bani da rabon shiga irinsa a duniya ai na taɓa da hannu na, akwai wani lokaci fa ina tafiya na a ɗan sahu na ga wani gida gabaɗaya an baibayeshi da fulawoyi gwanin sha'awa, da hanzari na cewa ɗan sahun a nan zan sauka hakanya sauke ni, yana tafiya na juya abuna na je jikin gidan na rinƙa shafa fulawoyin, sai ga wani matashi ina cikin shafawa ya ce menene kike yi hakan, na ce a'a ɗannan, ba abin da zan yi taɓawa kawai zan yi in bar muku kayanku ai ya kama dariya, wai ina da barkwanci da na tashi tafiya har tsinka min ya yi wai in ke shafasun, wannan ya sa ba na son hawa abin hawa, yo hawa abin hawa ko asarar kuɗi an wuce da kai baka ga komai ba komai yana wulgawa wul-wul... "Ashrof yi sauri ki kirawo mini tafiya nake son yi" Cewar Hajiya ganin gabaɗaya su Ashrof suna dariya, ita kuma ranta duk ya dagule saboda ta san zaman Inna a gidan zia takura mata ɗanta kasancewar Imran ɗin nata mai yawan buƙata yana da ƙarfin sha'awa ne kuma mahaifinsa ya biyo dan ko da ba za su samu biyan buƙata ba in ma mace tana priod to suna son koyaushe su kasance a jikin matarsu dan su rage damuwarsu haka Allah ya halicce su. "To Hajiya" Ta faɗa tana fita daga falon dan gabaɗaya har lokacin maganat Inna dariya take bata wai ta tsaya shafa gidaje kai wani kaya sai amale gaskiya Innarsu da ban take. ~IMRAN~ Tun da ya fita daga gidan ya je jikin machine ɗinsa ya tsaya ya ɗora hannunsa ɗaya a jikin machine ɗin ɗayan kuma ya dafe kansa da shi, ji yake kamar ya fashe da kuka dan takaici saboda ya san dole sai Hajiya ta ce a bar Inna ZAMAN WANKA amma ta ina zai fara rayuwa da wannan matar a gida ɗaya a ɗaki ɗaya, shi ba ma wannan bane damuwarsa, damuwarsa ɗaya yadda zai kwanta ba tare da matarsa a kusa da shi ba, dan ya san ko giyar wake ta sha idan ta gan su kwance a gado ɗaya sai ta musu ɗiban albarka shi ya zai yi. Zuwan Abid wurin ne ya dawo da shi daga tunanin da yake. "Haba abokina ya za ka sanya kan ka a damuwa haka, tun ɗazu fa na zo kira uku na maka amma baka ji ba har sai da na dafa ka, mai ya yi zafi haka?" Imran ji ya yi kamar ya rungume Abid ya saki kuka ko ya ɗan samu sassauci. "Haba Abid ya kake so in yi to matar nan fa tana son kashe ni ne kai kan ka ka san saboda ina da yawan sha'awa na yi aure a yanzu, kuma ka san yanzu matar nan idan tana nan ko yatsan matata ba za ta bari ma taɓa ba, ni kuma ka san halina ba manemin mata bane, ko da a ce ta haihu ba zan kusance ta ba ai dai zan so na kwanta a kusa da ita saboda yadda Allah ya halicce ni" "Haƙuri za ka yi, i kaina ban ji daɗin hakan ba amma kawai ka kyaleta" "Wallahi idan matar nan ta sake Hajiya ta bata dama ta zauna sai ta gwammace kiɗa da karatu wallahi sai ta yi da na sanin zuwanta gidana ZAMAN WANKA dan ba zan raga mata ba sai na mata abin da za ta bar gidan da ƙafafunta... Ƙaran wayarsa ne ya dakatar da shi daga maganar da yake, ganin sunan Hajiya ya marairaice fuska kamar ya saki kuka har kiran ya katse bai ɗauka ba, sai da wani ya shigo ya ɗauka dan ya san zancen gizo bai wuce na ƙoƙi. 'Ka zo ina son ganinka "Hajiyar ta faɗa tana kashe wayar ba tare da ta jira cewarsa ba. Sallama Abid ya masa tare da fatan Allah ya raya ya shiga motarsa ya tafi dan ya san yadda abokin nasa ya zuciya da kuma yadda yake da kafiya duk abin da zai faɗa masa ba yarda zai yi ba. Yana ƙoƙarin shiga gidan suka yi kiciɓis da Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa , ratse masa ta yi ya wuce ta ita ma ganinsa rai ɓace ya taho a fusace kamar kumurcin maciji sai ba ta ce masa komai ba, dan ban da ma haihuwar nan da aka yi bakinta da shi gaisuwa ce kaɗai to ga kuma Inna ta zo ta hargitsa murnar haihuwar ta damawa kowa lissafi. "Jama'a duk kun yi shirun kun yi jigum-jigum kamar masu zaman makoki, yo Allah na tuba ko gidan makoki yanzu an daina zama jigum-jigum kowa hirarsa yake da an binne mamaci, bare ku da aka muku haihuwa har biyu duk da ɗayan na ɗauke da lalura dan ba na ce baiwa ba" Imran da ke ƙoƙorin shigowa ya jiyo muryar Inna tana ta zuba. Da sallama ya shigo falon yana shigowa ya yi tozali da takardar hantar da ya siyo da maltina a gabanta. Kallonta yake baki sake. "Imirana ya kake kallona ko so kake ka ci, zo ɗauki hantar yanka ɗaya ka maida mugun yawu. " Ta faɗa tana ɗauko yanka ɗaya ta miƙa masa. Takaici ne ma ya sa ya ɗauke kansa ya maida kan Hajiya. "Hajiya gani" "Ka huta ka je can da mugun halinka, kake haɗiye yawu midik, aikin banza harara a duhu, da kuwa a asibiti ware murya ka yi kake magana, amma yanzu ka dawo kurmanka na asali to in hakan kake so Allah maida ƙoƙo masaki" Ta ce tana kai hantar bakinta. ""Imran ni zan tafi, ga Inna nan za ta yi ZAMAN WANKA kar in ji kar in gani" Ta faɗa tana miƙawa Sadiya Hassan da ke hannunta. "Hajiya a ciki da falon?" "Kai bari ka ji in fito maka a mutum, ba ciki da falo ba idan ciki ɗaya ne Imiran sai na zauna sai dai muke kwanciya kai da ƙafa da kai, in kuma ka ga ba zaka zauna ba ka bi Amina gidanta ka koma ɗakinka na da na gwauro, yo dama meye marabar dambe da faɗa yanzu ma gwauron kake tun da matarka ta haihu, in kuma ba zaka gidan Aminar ba sai ka kama shago na samari kake kwana" Cewar Inna har da tafa hannuwa. "Tashi mu je ka raka ni na ji ƙaran napep ɗin a waje ina ga Ashrof har ta kira shi, mu kwana lafiya Mamar Sadiya " "To Hajiya Allah tashemu lafiya ya huta gajiya mu ma yanzu za mu tafi ai" Cewar Mama. Haka suka fita ita da Imran ɗin... Masu son shiga grp na zaman wanka MMN AFRAH 09030283375. Beelal dai yana nan yana sauka da zafinsa ki nema ki karanta labari a kan nakasashshen yaron da wani bahagon gidan da aka rasa alƙiblarsu Alƙalamin mmn afrah ba ya rubuta shirme😍 *🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝* *MTN* . *Airtel* 1GB = ₦300. 1GB = ₦300 2GB = ₦600. 2GB = ₦600 3GB = ₦900. 3GB = ₦900 4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200 5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500 *GLO* . *9MOBILE* 1GB = ₦350. 500Mb ₦500 2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100 3GB = ₦1050. 2GB ₦1600 4GB = ₦1400. 3GB ₦2000 5GB = ₦1750. 4GB ₦2500 *VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 *🪀08066268951* A sayi data mai rahusa masoya😍💃💃💃 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH Na gode sosai da addu'o in ku gareni, da wanda suka min a grp da na pc har masu kirana ana tare masoya son so fisabilillah😍😍🙏 🅿️6️⃣ *Hajiya Amina* Tun da suka fito daga cikin gidan take ta yiwa Imran nasiha, a kan zaman Inna a gidan duk da dai an takureshi amma bata nuna masa hakan ba. "Haba Hajiya kin dai san halin tsohuwar nan, tana zuwa ta tafi ma ya aka ƙare bare kuma a ce za a zauna da ita na wani lokaci" Ya faɗa yana kauda kai gefe dan maganar da yake ma ji yake kamar ya saki kuka saboda yadda yake ji, ba komai yake ɗaga masa hankali ba illa nesanta gangar jikinsa da ruhinsa wato Sadiyarsa. "Duk da hakan da ma a lokuta da dama muna haƙuri da wasu mutanen wanda hakan ne kawai mafita, akwai mutane da dama wanda idan da ana biye halinsu ba za a zauna da su ba. Ka ga Inna tsohuwa ce, kuma ma a al'adance wankan jego ba wani sabon abu bane tun da ana yinsa bare kuma ita da ta haifi yara biyu dole tana buƙatar a taimaka mata musamman da haihuwar ta zama haihuwar fari ce" "Yanzu ki ga fa abubuwan da Inna take yi tun a asibiti zuwa gida, a haka za ta taimaka mata kin gani dai hatta abincin mai jego ita ke cinyewa to ta yaya za ta bata kulawar da ta dace" "To ko ma menene kai dai ka ja bakinka ka yi shiru kuma dai ai ba za ta iya cinye ko ma menene ba, dole akwai saura, sannan tun da kai kana nan yanzu hutu ake baka zuwa wajen aiki(School teacher ne) Sai kake yiwa Sadiyar wani abun" "To" Ya faɗa kamar ba ya so. "Imran kar fa in ji na san halinka, yanzu magriba ta yi ba wanka za su yi dukan su yaran an goge musu jiki da zaitun, ita kuma da yake jininta ya hau ɗazu da za a sallame ta nurse ɗin ta ce kar ta yi wanka, sai zuwa gobe, duk da dai jinin nata ya sauka amma dai har yanzu akwai kumburi a jikinta, bari in je" Ta ce ganin mai napep ɗin sai horn yake mata. "Sauka lafiya ni ma masallaci zan shiga in yi sallah" Haka Hajiya ta tafi tana ɗan jin ba daɗi a ranta saboda tausayin ɗan nata da yanayin da ta ga fuskarsa tabbas ta san akwai damuwa a ransa duk da bai fito ya nuna hakan ba. Sai da ya je masallacin ma ya yi alwalar da aka idar da sallar magarubar ma sai ya zauna a masallacin ya ƙi tahowa gidan. ```MAMA``` Bayan fitar Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce. "Inna mu ma gida za mu tafi, tun da gaki, sai dai fa kin ga Sadiya babu abin da ta ci sai ruwan shayi dan haka yanzu abinci za a bata" "Haba Rakiya in ban da dai kina so ki ɗauki alhakina ya za ki ce haka, ni da na zo na tarar da ku a asibitin shin duk baku gabatar mata da abinci ba sai yanzu kike neman ɗora laifin a kaina saboda ga Inna kuka mai daɗin hawa ko?" "Ba haka nake nufi ba Inna, kin san lokacin da kika zo ai tana bacci to tun da ta haihu ai bata sanya komai a cikinta ba, sai shayin da Hajiya ta bata" "Amma kuwa yaran nan kun cika sakarkaru, wai dama kina nufin Sadiya babu abin da ta ci? Lallai in da ranka ka sha kallo, wallahi ya za a yi yarinya ta yi naƙuda da sunkuto ƴaƴa har biyu amma a barta da yunwa, ni duk zatona sai da ta ci wani abu sannan ta koma baccin, kuma da na ga ma ina tambayarta ta ci wake da shinkafar nan da na ga bata yi magana ba tunani na ƙam baki take irin na masu haihuwa kin san wasu basa iya cin komai idan suka haihu, yo da na san bata ci komai ba tun zuwanmu da na ɗora tukunya na tuƙa mata tuwo tun da shi ne zai fi riƙe mata cikin kin san cikin jego sai abu mai nauyi" Ta faɗa tana kallon Mama. "Hakane kam" Mama ta faɗa ba dan ta so ba sai dan son a zauna lafiya. "To laifin waye tsakanin ni da ku?" "Namu ne" Cewar Mama. "Aunty Sadiya mai za ki ci?" Ashrof ta tambaya. "Komai ma" Cewar Sadiya da ke ƙarewa Hassan kallo. "Kai amma wannan yarinyar da nunkufurci kike wallahi yanzu dama kina jin yunwar amma kika yi shiru dan ki ƙwari kan ki? Kika bari na ci hantar nan har ta so ta min karo, ai wannan abin kunya ne wai uwa ta cinye siriki ranar aure da ba san kina so da na rage miki amma yanzu ai ga doya can da ƙwai a cikin ƙwai har ma da kayan marmari bari in baki ki ci yo ai hakan ya zama min farilla tusa a masallaci" Ta faɗa tana tashi ta zubo mata doyar da ƙwan, sai kuma Ashrof ta haɗa mata wani shayin ta karɓi Hassan ɗin ta ci ta ƙoshi, tana gamawa ta gi gyatsa. "Ko da na ji, yo yanzu ba gashi har da gyatsarki ba, amma a ce mutum ya zauna da yunwa ai mai jego da MAI ZAMAN WANKA sai suna cika cikinsu za su iya rainon abin da aka haifa, shi yasa kika ga ni ba na ƙwarar kaina a yunwa babu yadda zan yi in zauna cikina na kiran ciroma yunwa tana ƙwaƙulata" Ashrof wancan zamzam ɗin na fida ɗakko a baiwa Husaini kin ga ya tashi" Cewar Mama tana mata nuni da fidar. "Mama wacce ce tashi daga ciki" "Farar ita ce tashi, jar kuma ita ce ta Hassan" " Kuma dai da ɗaurewa ƙarya tsantsa kuke, yanzu bulunbotin ma sai an rabawa yaran nan, baku ga Allah ma a ciki ɗaya ya haɗa su ba tsawon wata tara da kwanaki suka rayu a cikin amma saboda sanabe ace kun ware musu bulumboti (Fida) dan san ku raba kawunansu, ai kamata ya yi komai a haɗe musu ya zama guda ɗaya kokwa" Inna da ke ƙoƙarin kunna soket ta faɗa tana kallon Mama da ta ɗagawa Husainin fidar tana bashi zamzam ɗin. Ashe soket ɗin yana ja Inna da ta maida hankali kam Mama hannunta a jikin soket bata ɗauke ba sai jin wani garrrr ta yi wuta ta ja ta, da sauri ta janye hannun ta bar wurin tana rafka salati, sai da ta koma ta zauna tana maida numfashin tsoratar da ta yi ta kalli Ashrof da Sadiya da ke ta dariya ta ce. "Haba Halima kin san sokat (soket) Ɗin yana jan mutane amma baki faɗa min ba kika barni zai shanye min jinin jikina, dama abu ba abu ba duk tsufa ya gama tafoya min da jinin jiki, ban da ma Allah ya sa ɗazu na sha kwalbar maltina guda da yanzu sai dai a nemo manyan ita ce a ɓanɓareni daga jikin dan na san mutuwa zan yi ni ban yi ZAMAN WANKAN BA an wanke ni, shikenan na tafi na barwa Tasalla Malam sai yadda ta yi" Ta faɗa tana share hawaye dan sosai yadda wutar ta jata abin ya firgita ta. "Sannu Inna" Cewar Mama tana ɗan ƙunshe dariyarta. "Yawwa sannu Rakiya, ai yau dai na leƙo barzahu, wai da kallo zan kunna kin san ni da son kallo kamar me" "Hakane Allah tsare" "Amin" "Wai Inna ya kika ji ne, ni fa ban ankara ba sai kawai na ga kin zauna a kan kujera kamar an jefo ki, har kina neman yin tuntuɓe da ƙafar Aunty Sadiya" Ashrof ta faɗa har ƙyaƙyataww take. " Aniyarki ta biki Asharofa, masu irin halinki ko a lahira wutarsu da ban ce amma ba na miki fatan shiga wuta ni nan Azumi wallahi na ci dubu sai ceto kuma ina nan har sai kin tsufa ni ban mutu ba in ma so kike in mutu " Ta ce tana goge hawaye. "Sorry Inna ke yanzu sai ki bari har in tsuga kin raye ai ba za ki kyan gani ba" "Soriyo, na ce soriyo ban... Sallamar Imran ce ta katse maganar da suke, shigowa ya yi. "Mama ta ce. "Ta tafi Hajiyar" "Eh tun daɗewa ma" "Imirana ashe dai sokat ɗin gidan ka jan mutane yake, daga taɓawa wuta ta jani ji kake wani girrrrr duk jikina ya ɗauki rawa baka ji ba yadda ta jijjigani, amma Asharofa da matarka har da dariya" "Daman ma sumar da ke ta yi a kai ki asibiti mu ga ta yadda za ki yi ZAMAN WANKAN" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce. "Eh za a gyara ne" "Ai gwara a gyara amma ni yanzu ai ina ga sai ka samo min madarar ruwa gwangwani uku na sha" "To" Kawai ya ce ita ma kuma sai ta ja bakinta ta yi shiru. "Hajiya ta ce sai gobe za ta yi wanka sbd kumburin jikinta in ji likitoci" Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. "Eh sai gobe har yaran ma ai sai goben tun da an goge musu jiki da zautun kuma saboda mura kuma yanzu ai dare ya yi" Mama ta bashi amsa. "Allah kaimu" Cewar Imran kuma dama ya yi hakan ne dan Inna ta ji kar ta je ta tarki yiwa yaran wanka. "Halima ki sa yaron nan a nono mana tun da ya tashi ko babu ruwan nonon in yana tsotsa zai zo" Inna ta faɗa tana kallon Sadiyar. "To" Ta ce Mama ta miƙa mata Hussainin ta sanya shi a nono. "N a dama za ki fara bashi, kuma koyaushe za ki bashi kike fara yin bismillah kafin ki bashi, sannan kike lura wajen bashi nonon dan kar ya danne masa hanci in yana sha, kuma sai kin tiƙe nonon a hannunki in zaki basu kin san nauyi yake musu idan aka bar musu ba a riƙe ba" Cewar Mama tana ɗan nuna mata yadda za ta yi. "To Mama" "Wayyo Allah na wallahi ciwo" "Haka za ki daure"Cewar Mama. "Ke ma Rakiya da wani abu yo wane haka za ta daure, bada nono ai ya zama wajibi ciwo ko dole ne, Allah na tuba kika haihu ma, ai fitowar ɗa shi ne babban abu" Cewar Inna. Babu wanda ya tanka, Sadiya kwa sai rurruntse ido take jin zafin da nonon ke mata da yaron ya kama kan. "Ashrof ba Inna Hassan ɗin mu tafi kin ga har an yi ishsha'i" Cewar Mama. Gaban Inna ne ya bada wani diririmdim, jin wai an ce a bata Hassan. "Ni har ga Allah tun da aka ce yaron yana da fatar miciji a bayansa nake jin tsoronsa gashi ni ce MAI ZAMAN WANKA dole dai ni zan wankeshi, wayyo Allah na shigenge" Inna ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce. "Yo ku bari mana a ɗan jima muna hirarmu ai kwa rage dare, ko kuma in Halima ta gama shayar da Husainin sai in karɓeshi ki bata Hassan ɗin shi ma ta bashi nonon. "Haba Inna tun jiya da dare fa muka baro gida muka zo nan kwanan zaune muka yi, tana naƙuda da sassafe muka tafi asibiti dama mun je asibitin a daren suka ce da saura mu koma gida kuma yanzu har an yi ishsh'i bamu tafi ba tun da dai Allah ya sauketa lafiya yaran ma suna cikin ƙoshin lafiya kuma gaki ai sai mu je gida sai kuma gobe in muna raye" Cewar Mama cikin sanyin murya dan ta harbo jirgin Inna kawai dai Hassan ne bata son karɓa. "Ni Azumi na ɗakko ruwan dafa kaina" Ta ce a ranta a fili kuma ta yi dariyar yaƙe ta ce. "Kayya Rakiya, ai ban sani ba, to, to, babu komai ai, da yanzun da anjiman duk ɗaya ne Allah bamu alheri" "A gaba ma wallahi sai kin gwammace ko Kano baki zo ba bare gidan Imran" Cewar Imran a ransa.Ya tashi ya fita. "Amin Inna" Cewar Mama. "Inna ga mijinki Hassan" Ashrof ta faɗa tana dariyar ƙeta a ranta, a fili kuma tana danne dariyar yadda ta ga Inna na wulwulga idanu. "Ba dai wannan rabi da rabin ba, rabi mutum rabi maciji, mijina Malam yana can a ƙauye" Ta ce a ranta a fili kuma ta ce. "To ai ni Husainin ne mijin Hassan ɗin na sake shi" "A'a Inna ai aure da ke babu saki, ke da shi mutuƙaraba" Ashrof ta faɗa tana ɗorawa Inna Hassan a cinya, Inna ji ta yi kamar Ashrof ta ɗora mata miciji a cinya haka dai ta daure ta riƙe yaron gabanta na duka uku-uku.Sallama suka musu suka tafi, Inna dai ko sallamar tasu bata karɓa ba. "Halima kar fa a shiga haƙƙin yaron nan ki karɓeshi shi ma ko bashi nonon" Inna da ta sanya hannu ta ɗan jijjiga yaron ya buɗe ido dama da niyya ta yi hakan. "Inna shi ma fa wannan ɗin ba sha yake ba, kawai dai ciwo nake ji" "Yo ai dai shi ma ko fatar ce ya tsotsa dan kar Allah ya kama ki kin nuna musu banbanci" Ta faɗa tana ta Allah -Allah Sadiya ta karɓi Hassan, Haka ta zarewa Hussaini nono, aikuwa ya tsallara ihu, a hakan Inna ta miƙa mata Hassan ɗin take lallashin Hussainin. Bayan sun yi bacci yaran Sadiya ta sanya kowanne a gadonsa ta kwantar tare da sanya bargo ta lulluɓesu. Zuwa can Imran ya dawo gidan dan dama yana waje a zaune takaici ya hanashi shigowa gidan, dan shi bai saba zuwa yawo ba. Da dai ya gaji da shaƙar sanyin sai ya kulle gidan ya shigo, lokacin Inna jakarta na gabanta ta fito da bargwanta tana maida kayan. Yana shigowa bayan ya yi sallama Sadiya ta amsa sai ya wuce bedroom Sadiya ta tashi ta bi bayansa. "Ba ni da raƙumi da akala ba" Cewar Inna lokacin da Sadiya ta bi bayan Imran. Tambayarsa ta yi abin da zai ci, dakyar dai ta lallaɓashi ya amince zai sha fura, Inna da ke falo ta ce. "Wa ankarahu ake ankara dai, ana yi dai ana zaman ƙuda da buzuzu, wato zaman doya da manja" Ta faɗa cikin ɗaga murya. Suna jin ta babu wanda ya yi magana, har Sadiya ta fito ta ɗauki furar a falo, da yake a cikin kwanon sha take haar luday akwai a cikin hannun frige ɗin haka ta ɗauka ta koma cikin bedroom ɗin Inna dai sai taɓe baki take. "Bari dai in cire atamfar nan ta akwatin ƙarfe kar in kwanta da ita alharamun giya a gidan liman" Ta faɗa tana ɗakko wata doguwar riga marar nauyi a jakarta ta sanya ta linke atamfar ta sanya a jakat ta rufe ta ajiyeta gefe. Bayan ta koma ta kwanta jin tsit babu motsin su ta tashi cikin sanɗa ta je baki ƙofar bedroom ɗin ta tsaya ba tare da sun sani ba, ta kama labule a hankali ta ɗan leƙa. Imran ta gani zaune a bakin gado sai Sadiya da ke zaune kan bed side drower tana bashi fura a baki. Da sauri Inna ta saki labulen ta dawo ta zauna daɓas dan ita hankalinta bai kwanta ba da kasancewarsu su kaɗai a cikin ɗaki. "Ni Azumi ba da ni ba wai gyaɗa a kabari, ya za a yi ina gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA in bari a yi aika-aika ai yadda na gan su ɗin nan kusa da juna a zaune shi a bakin gado ana jimawa sai dai in ji sun rufo ƙofa" Ta faɗa a zuciyarta, sai kuma ta ce. "Halima, Halim, Halima" Har sau uku amma bata fito ba kuma bata amsa ba Sadiya kwa ta tashi za ta fito sai Imran ya riƙe hannunta ya marairaice mata, hakan ya sa bata fito ba shi kuma da gangan ya yi hakan dan kawai ya ga abin da Innar za ta yi. "Sa'adiyya, Sadiyya, Imirana, wai bakwa ji na ne" Ta faɗa tana tashi tsaye daga zaunen da take. " Ko dai basa cikin hayyacinsu ma dai, kar fa kudirarren yaron nan ya je ya ɓarkewa yarinyar nan ɗinkin da aka mata, ita ban da ma shashanci jiki duk faci amma za ta biye wa namiji" Ta faɗa tana tafa hannuwa, jin shirun ya yi yawa sai ta nufi ƙofar ta kusa zuwa jikin labulen sai ga Sadiyar ta fito da sauri ta koma ta zauna a kan kujerar kusa da hanyar bedroom ɗin ta wayance dan da a kan kujerar wajen bakin ƙofar falo take a zaune. "Inna gani" Sadiya ta faɗa tana haɗe rai. "Dama na ji shiru ne nake kiranki" "Haba Inna shirun me kuma me zan miki to" "Babu komai ɗiyar nan taimakon ki zan yi dan kar ki hau dokin zuciya yaron nan ya kai ki ya baro ki" "Haba Inna wai wacs magana kike haka ne, kar fa ki manta mata da miji muke fa" "Yo dan an ce mata da miji kuke sai me to, ai yanzu kin haramta a gareshi" "In ji wa" "To halasta masa kan ki wallahi kika sake ya janyo ruwa a rijiyar nan Allah sai kin ɗauka a injin markaɗe aka saka ki" Takaici ne ya sanya Sadiya ta juya ta koma ta bar Inna tana sababi ita kaɗai. Masu son grp zaman wanka 09030283375 Masu tambayar Beelal ina baku haƙuri sai ranar monday in sha Allah za a posting. 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️7️⃣ Inna na nan zaune abin duniya ya ishe ta, jin sun yi ɗif basu da alamar fitowa, wajen gadajen yaran ta nufa sai da ta ƙare musu kallo ta gane Husainin dan bata so ta taɓa Hassan, hannu ta sanya ta ɗan jijjigashi aikuwa ya ɗan motsa ya yi ɗan kuka kaɗan. "Ka yafe min ɗan nan ba da niyya zan yi ba ban son na ɗauki alhakinka, jihadi zan yi in ƙwato waccen shakatafin gyatumar taka, da babanka ke neman wuce gona da iri" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Halima zo ɗan nan ya motsa" Sadiya da dama ta ji ɗan kukan da Hussainin ya yi, hakan ya sanya ta ɗakko kwanon furar da Imran ya sha dan ta fito da shi, tana zuwa idanunta suka sauka a kan Inna da ke ƙoƙarin ƙara taɓa Hussainin da zuwa lokacin tuni bacci ya ƙara surarsa ya yi awon gaba da shi. "Dama na yi zaton hakan, haba Inna yanzu meye amfanin tashin yaron nan" "Ya koma bacci abinsa fa Halima, tashin sa ya yi amfani mana, tun da gaki kin fito dama kuma burina kenan" Da ido kawai Sadiya ta bi Inna ta fice daga ɗakin domin kai kwanon kicin.Tana dawo wa falon ta samu Inna ta rafka uban tagumi, ji ta yi wani tausayin Innar ya kamata hakan yasa ta ce. "Inna ko bacci kike ji ne a ɗakko miki katifa, akwai ƙaramar katifa sai a sanya miki a nan ɗin ko?" Ta faɗa tana kafe Inna Azumi da ido ganin ta yi saurin ɗauke hannunta daga tagumin. ta saki baki ya layar mai tafiya tana kallon Sadiya. "Ko da wani abun ne Inna?" "Yo Allah na tuba ba dole ki ga na saki baki ba Halima, yanzu ni har lokacin bacci gareni a gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA?" "Kwanan zaune za kike yi?" "Yo ba gwara kwanan zaune ba ka san a zaune kake, ai bakam zan ke yi saboda tsaro ba wai dan tsoro ba, yo idan na kwanta na saki jiki ina bacci ai sai dai kuma a saka ki a kogin bagaruwa" "Wai Inna bakya jin kunya Imran ya ji abubuwan da kike faɗa? Wai shin ma kin manta mace tana yin jinin biƙi idan ta haihu kurum ki ɗorawa kan ki, ki hana mutane sakat da zancen abu ɗaya?" "Kunyar me zan ji? Na ce kunyar me zan ji Sa'adiyya, ai kunyar marar kunya tsoro ne, kuma ma da kike maganar jinin biƙi shi shaiɗan ina ruwansa da wani jinin biƙi lokacin da zai ɗau hankalinku ma kina ina, sai dai bayan komai ya lafa ku yi istigfari, kuma wallahi ni nan Azumi ƙafata ƙafarki, babu yadda za a yi in kwanta a falo sai dai mu kwanta da ke da yaran a cikin ɗakin, shi Imirana ki saka masa ƙaramar katifa a falo ya kwanta" "Haba Inna mai gidan ne za a sakawa katifa a falo?" "Eh mana, wato kina nufin in barku a ciki ni a nan ban san me za ku yi ba gwara dai idona idonki Sa'adiyya hankalina zai fi kwanciya kuma in san ZAMAN WANKA na zo" Imran da ke ciki wani baƙinciki da takaici ne ya lulluɓeshi, ga kan sa da ke matuƙar masa ciwo sanadin wannan hayaniyar da Inna ke ta faman yi bakin ta ko gajiya ba ya yi. Tuno wa da maganar mahaifiyarsa ya sanya ya miƙe zaune daga kwancen da yake a kan gadon , ya tashi dafe da kan sa yana ciccije leɓe, yana raya wa a ransa sai ya rama abin da tsohuwar nan ta masa. Sadiya ya ƙwalawa kira, da sauri ta shige ɗakin. "Oh ni yarinyar nan ta rako mata, ji yadda take sauri kamar za ta tashi sama, ko dan tsoronsa ma take kamar wani mala'ikan mutuwa" "Ɗakko yaran ki maido su nan, ki kai min katifar falo, ku kwanta a nan ɗin" Ya faɗa fuskarsa cike da damuwa. Shiru Sadiyar ta yi tana ɗan jin babu daɗi amma dai ta san hakan shi ne mafita a wurinsu dan tsohuwar nan sai ta sa a maimaita yaƙin badar dan kaɗan daga aikinta ta tada tarzoma. Cikin sanyin jiki ta amsa masa, haka ta ɗakko yaran Inna tana kallonta ta shiga da su, tana kai su ɗakin duk ya ɗaukesu ya ƙara ganinsu yana jin wani farinciki na maye gurbin baƙincikin, da yake ciki ya so ace, yau su kaɗai za su kwana a gidansu da ya nuna musu kulawa su da mahaifiyarsu fiye da kima, to amma Inna ta warware komai addu'a ta riga fata. Katifar ta ɗauka ta kawo falon ta shinfiɗa zanin gado, ta ɗora filo tsaf. Inna dai tana kallonta bata ce mata komai ba, ta koma ta ɗakko bargo ta ajiye masa, ganin Sadiya ta ce masa za ta shiga banɗaki ya kwantar da yaran yana jin ƙaran rufe ƙofar banɗakin da Sadiya ta yi aikuwa ya tashi cikin hanzari ya cire kayan jikinsa, sai da ya tuɓe tsaf daga shi sai singlet da gajeran wando gadan -gadan ya nufo falon Inna da ta hangame baki tana hamma bata ankara ba sai ganin mutum ta yi ya fito, ai bata san lokacin da ta katse hammar da take ba ta fara jero salati tana, sanya hannu a fuska tana cewa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ni Azumi na ga abin da ya fi ƙarfin gani, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani, haba Imirana ka manta cewa ba ku kaɗai bane a gidanku akwai ƴar ZAMAN WANKA?" Inna ta faɗa har lokacin idanunta a rufe da hannunta, a duniya ta tsani ta ga namiji haka a tuɓe. Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan katifarsa ya kwanta ya ja bargo ya rufa. Cikin. Sauri Inna ta tashi ta shige bedroom ɗin tana neman faɗuwa a ranta tana cewa. "Oh yaron nan bashi da kunya ko kaɗan, ko dan dama hausawa sun ce abokin damo guza, ashe dai shi ma halinsu ɗaya da abokinsa da na iske a wannan gida ya yi wasarere, gabaɗaya halittar jikinsa na leƙowa waje" Tana nan zaune sai ga Sadiya ta shigo ɗakin, dan ita Sadiya da farko ma ta ɗauka Innar ce ta kwanta a falon da yake Imran har kan sa ya rufa da bargon sai da t shigo ne ya buɗe ya mata magana cewar ta miƙo masa wayarsa a kan mudubi. "Halima ashe dai mijinki bashi da kunya?" "Me kuma ya yi Inna kin ce ya koma falo ya koma to me kuma kike so ya miki?. "Ana ga yaƙi kina ga ƙura yo ai na ga yana so ya min kora da hali, in ba kora da hali ba ya za a yi ya san ba ku kaɗai bane a gidan, kawai ina zaune sai ganin mutum na yi sangamgam ya shigo falon babu neman izini gandaƙai-gandaƙai ko suturar kirki babu, da da sanyin nan ma amma ya zauna da kayan banza" Sai lokacin Sadiya ta gane abin da Innar take nufi, ba tare da ta tanka ta ba ta ɗauki wayar Imran tanjuya za ta fita Inna ta ce. "Ki taho min da bargona a kan kujera, ki haɗo min da wannan sauran maltinar guda ɗaya ta ɗazu" Tafiya Sadiya ta yi ba tare da ta ce komai ba, tana fita daga ɗakin Inna ta rafka uban tagumi, idanunta a kan gadon Hassan. "Ni Azumi da zan yi kwana Hamsin amma tun ban kwana ɗaya ba na fara fuskantar abubuwa, ga yaro mai bayan miciji ga ubansa yana yawo da jiki babu maraba fa tsirara, haka kawai lokacin fatarar nan fa ake rashin kuɗi ya je ya sa in gamo da ganin al'aurarsa, ni Azumi in shiga uku in ma ban makance ba" Ta faɗa a zuciyarta dai dai nan Sadiya ta dawo ɗauke da bargon da maltinar, ta miƙa mata dama ta buɗe mata kwalbar maltinar. Haka ta kafa kai ta shanye tas ta miƙa kwalbar kan mudubi ta ajiye, lokacin Sadiya tana shan magungunanta. "Ni da nake ta shan maltina kayan ruwa, ko ya zanyi da fitsari, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, ni mai yawan fita fitsari cikin dare, bare na cika cikina da kayan ruwa, wannan kurman mutumi falo" Ta faɗa tana kallon Sadiya. "Shi da yake gefe ɗaya a kwance kuma ina ke ina shi" "A'a Halima nake ƙetara mutum ina fita wa ya san fita nawa zan yi" Sadiya dai bata kulata ba ta yi shirin kwanciya ta hau gadon ta kwanta. "Inna ki kwanta mana, na ga dai gani gaki gani kuma menene zai hanaki kwanciya?" "Hankalina a kwance yake, kawai dai ina jin kunyar gadon ne, yo na kwanta a gadon yara" "Sai ki kwanta mana, ai babu komai ke da jikokin ki" Wannan kalaman da Sadiya ta mata yasa ta ji ƙwarin gwaiwa ta kwanta ta rufa da bargonta, ita ma Sadiya gadon yaran ta tashi ta maido gefen gadonta kusa da ita dan ma haɗe yake da net ɗinsa sauro ba zai cije yaran ba. ~DARE~ Wajen ƙarfe biyu na dare Imran ya tashi zaune, dan dama ya ji tashin Sadiya wajen ɗaya saura yaran sun motsa, ya basu ruwansu yana dai ji har ta kwantar da su, bai sani ba ko sun sha nono ko kuma nonon bai zo ba, sa'a ma aka yi yaran ba wasu masu rigima bane. Ɗakin tsit baka jin komai sai ƙaran minsharin Inna tun da ta kwanta bata motsa ba, haka ya tashi cikin sanɗa ya leƙa bedroom ɗin sai da ta tabbatar bacci suke sannan cikin sanɗa ya shiga ɗakin drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko farar jallabiyarsa, tare da wata farar rigar sanyi mai haɗe da hula, haka ya lallaɓa ya rufe drower ya fita ba tare da sanin su ba, dan Inna kamar wata gawa haka kawai sai sakin munshari take. A ransa ya ce "Kina wannan munsharin koma me mutum zai yi da matarsa sai ya yi baki sani ba, ya faɗa yana jan tsaki tare da yin ƙwafar ganin Inna ta maye gurbin makwancinsa. Jallabiyar ya sanya sannan ya ɗora rigar sanyi a ka sai ya bar zip ɗin a buɗe, haka ya fita ya je bayin nasu ya cire ƙwan fitilar ya dawo ya kwanta.Zuwa can ya ji motsin Inna ta tashi tana cewa. "Dama na san dole na tashi fitsarin nan duk ya cika min mara" Da hanzari ya ɗakko filillikan kujera, ya jera a kan katifarsa ya dai daita su kamar mutum ya rufe da bargo, yana gamawa ya lallaɓa ba takalmi ya tafi banɗakin. _INNA_ Haka ta tashi ta kunna fitilar ɗakin, ta kalli Sadiya da ke baccinta cikin kwanciyar hankali ta ce a fili. "Allah da hikima yake, shi yasa ya sanya mata ke zubar da jini bayan sun haihu (Jinin haihuwa) Amma ba dan haka ba Allah kaɗai ya san yawan matan da matansu za su ke maida musu mahaifa nan da nan (Su yi tarayya da su) Musamman in aka samu kudurarru masu jaraba, tuni za su haƙƙewa mai jegon saboda basu san wahalar naƙuda ba, shikenan mata su ringa haihuwar kwenika" Ta faɗa tana gyaran ɗaurin ɗankwalinta ta taso ta fito. A hankali ta leƙa falon dan tabbatar da Imran ɗin yana bacci, ganin filon da ya jera sai ta ɗauka shi ne ke bacci da yake ma fitilar falon ma a kashe take bata kunna ba dan bata so ma ya tashi. Haka ta nufi bayin gadan-gadan har tana haɗawa da sauri jin fitsarin ya matseta. Imran da ke cikin bayin jin takun Inna yasa ya ƙara jingina a jikin bangon da ke kallon ƙofar bayin ya baza hannu ya sanya hular sai ya sunkuyar da kai. Inna jin fitsarin na nema zubo mata ganin fitilar a kashe sai bata kunna ba kawai ta shige bayin. Sai da ta je tsakiyar bayin kawai sai ganin abu ta yi fari ƙal,kallon abun ta yi da kyau ta ga mutum ne a take ta ji ƙafafunta sun fara karkarwa, hannu ta miƙa ta dafe jikin bango tana cewa. "Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahim, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba" Ta faɗa har lokacin tana karkarwa, so take ta gudu amma ƙafafunta sun ƙi bata dama, ji take kamar a wurin aka dasa ta. Imran ganin tarkonsa ya kama tsuntsu ya ce a ransa. "Mu zuba ni da ke mu gani, ba dai kin ce ke ZAMAN WANKA za ki yi ba ai ga wurin nan" A hankali ya fara takowa yana nufota, dama ƙafarsa ko takalmi babu, Inna ganin aljani ya doso ta a nata tunanin kenan, sai haƙoranta suka fara haɗuwa da juna kafkafkaf, gaba ɗaya ta tsure ji take aljanin nan yana dafa ta mutuwa za ta yi, ji ta yi kawai fitsarin nan ya ƙwace mata, yana bin ƙafafunta, aljanin na matsowa a hankali ita kuma faɗuwar gabanta na tsananta. Imran kwa duk nufotan da yake bai ɗago kan sa ba, jib Inna ta zame ta zauna ƙafafunta sun kasa ɗaukanta, ganin dai da gaske aljanin na miƙo hannu hakan yasa ta fara rarrafe domin ƙwatar kan ta, tana rarrafawa yana ƙara matsota har suka fito daga bayin, dan Imran rage tsawo ya yi sai ta ga ɗan guduldili ne aljanin, tana rarrafe tana salati dan so take ta yi ihu amma ta kasa gabaɗaya bata da karazana. Ta fito daga bayin yana biye da ita tana rarrafawa duk ta zubar da takalmanta, suna fitowa ta juya tana rarrafe dan rarrfenma dakyar take yi sai Imran ya yi saurin juyawa cikin sanɗa ya koma cikin bayin, Inna sai da ta kusa shiga falon da rarrafe ta waiga aikuwa sai ta ga babu aljanin hakan ya sa ta ɗauka ɓacewa ya yi. Hakan ya sanya ta cigaba da rarrafen duk da tana jin kamar aljanin zai rafkota ya maidata bayin. A haka ta shigo falon, kallon katifar Imran ta yi ganinsa lulluɓe yasa ta cigaba da rarrafe dan ba za ta tsaya a falo ba tashinsa sosai take jin tsoro, haka ta wuce cikin ɗakin tana jin rigarta jigif da lemar fitsarin da ta saki. ```Imran``` Tun da ta waiwaya ta ga baya nan, sai ya laɓe daga bayin ya cire kayana ya bar singlet da gajeran wandonsa, sai da ya dai dai ci Inna ta kai bedroom cikin sanɗa ya dawo falo ya ɗauke filillikan ya mayar da su mazauninsu ya sanya kayan da ya cire a ƙasan filo ya koma ya kwanta ya rufa. ```INNA``` Gadon ta kama hannunta nankarkarwa so take ta hau amma ta kasa hawa ga bakinta ya kasa magana, hannu ta kai ta kamo ƙafar Sadiya ta kama babban yatsan Sadiya take ja, dan bakinta ba zai iya kiran sunan Sadiyar ba. Sadiya da gabaɗaya ta yi nisa da bacci bata san Inna na jan yatsanta ba. Imran ya tabbatar yanzu Inna taa cikin halin ƙaƙanika yi dan haka ya miƙa ƙafarsa ya bugi jikin kujera, ai Inna na jin ƙaran sai ta ɗauka aljanin ne ya biyo ta, ganin Sadiya ko motsi bata yi kamar gawa hakan ya sanya Inna ta lallaɓa ta shige ƙasan gado... Masu son shiga grp zaman wanka 09030283375 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️8️⃣ Inna sai numfarfashi take, nishinta na fita ta kwanta lifet da ribda ciki, kawai jiran tsammani take, dan duk tunaninta aljanin ne ya shigo kawai neman inda take yake yi. "Allah ka gani ZAMAN WANKA na zo, hanyar zumunci ne, idan kuma ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne Allah ka yafe min kura-kuraina, ka haɗa mu a aljanna da Malam, ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Cewar Inna a zuciyarta. Gabaɗaya ta sanya hannunta ta riƙe ƙafar gadon, duka hannayenta a jikin katakon suke, dan gudun kar aljanin ya ɓanɓarota daga ƙasan gadon. Har aka fara kiran assalatu Inna tana ƙasan gado Sadiya kwa bata falka ba, saboda kwana da ta yi ta waye tana gwagwarmayar naƙuda hakan ya sanya ta gaji bare haka nan ma nauyin bacci gareta. ```IMRAN``` Tun da ya buga ƙafarsa a jikin kujera ya ƙara razana Inna, jin ɗif a ɗakin babu motsinta hakan ya sanya ya gane ta mugun tsorata dan haka bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba. Sai dai lokacin sallah ya yi alerm ɗin wayarsa ya fara masa sallama, tashi ya yi ya kunna fitalar falon ya fara kiran Sadiya sau boyu kawai ya kirata dama ba dan ya tasheta ya yi kiran ba dan Inna ta jiyo muryarsa ya san tana nan har lokacin a tsorace dan haka ɗakin ya nufo ya zo ɗaukan kayansa dan ya yi shirin tafoya masallaci. Daga setin da Inna take a ƙasan gado daga nan drower kayansa take, haka ya buɗe ya sanya kayan da ya yi amfani da su wajen tsorata Inna ya ɗora musu wasu kayan ya ɓoye su yadda ba za a gani ba ya ɗakko wami yadi riga da wando, ya juyo ya fito daga ɗakin sai dai ya yi matuƙar mamaki da Inna ta ji shigowarsa amma bata fito ba, kuma ya tabbatar idonta biyu, dan babu yadda za a yi bacci ya ɗauketa dan bata cikin kwanciyar hankalin da bacci zai ɗauketa.Sosai abin ma ɗaure masa kai da ya ga bata kan gadon, yana tunanin inda za ta ɓuya a ɗakin sai da ya je zai buɗe drower ne ya hangi rigarta a ƙasan gadon aikuwa kamar dai ya yi ta ƙyaƙyata dariya. "Ashe ma abin naki tsoro ne ba dai ke MAI ZAMAN WANKAN da za ta addabi mutane ba ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta" Ya faɗa a zuciyarsa ya fito falo ya sanya yadin da ya ɗakko ya fita domin yin alwala ya tadi masallaci. ```INNA``` Tun da Inna ta hangi hasken fitilar falo gabanta ya shiga faɗuwa dan duk tunaninta aljanin ne. "Ya Allah ka makantar da aljanin nan kar ya ganni, idan kuma shi ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne ka sa in cika da imani, ka haɗa ni a aljanna da Malam Allah ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Ta faɗa hawaye na gangarowa daga idanunta. Har sai da ta ji Imran ɗin yana ƙwalawa Sadiya kira hakan ya tabbatar mata ba aljanin bane Imran ne ya tashi. Ta san jin Sadiya bata amsa ane ya taho ɗakin. Amma sai ta ƙyaleshi har ya gama uzurinsa ya fice. "Babu abin da zai sa na faɗa maka akwai aljani a bayi, sai ka je kaima kun yi ido huɗu da shi ka gan shi ra'ayal aini, sannan in ga ƙarshen kurmanci dan na san yau in ka rinƙa ƙwanzama uban ihu sai duk maƙota sun ji ka sai ka gwammace kiɗa da karatu, dan yaro bai san wuta ba sai ya taka, yau za mu ga ƙaryar rainin wayo" Inna ta faɗa a ranta tana hasashen yadda Imran ɗin zai yi idan ya ga aljanin. Shiru -shiru bata ji ihun Imran ba, abin ya bata mamaki dan ita mugunta ce ta sa ba za ta faɗa ba ma bare ya fs zuwa bayin, tana a haka sai ƙaran buɗe ƙofar gida ta ji ya fita masallaci, sosai ta girgiza da hakan. "To ko dai aljanun gidan ne basa yiwa masu gidan komai si baƙi, ko dai tun da ya ɓace lokacin da na waiwaya bai ƙara fitowa ba shi sa Imran ɗin bai ganshi ba?" Ta rinƙa saƙa-da warwara zuciyarta. Har sai da gari ya ɗan fara haske sannan ta ji ƙaran ƙofar gida alamar Imran ya dawo daga masallaci, kamar jiran dawowarsa yaran ke yi, uka tashi suka fara kuka a tare. Hakan ma ya yi dai dai da shigowarsa ɗakin ya fara tashin Sadiya daga bacci, haka ta tashi tana ɗan yatsina fuska tare sa murza idanu irin na wanda ya tashi daga bacci.Haka ta ɗauki Hassan ta yi bismillah ta sanya shi a nono, shi kuma Imran ya ɗauki Husainin yana jijjigashi a kafaɗarsa. Sai bayan yaran sun ɗan yi shiru ta lura Inna bata kan gadon. "Inna har ta tashi sallah kenan" Ta tambaya tana kallon Imran. "Sa'adiyya, Sa'adiyya" Inna da ke ƙasan gado ta shiga kiran sunan Sadiya. "Ikon Allah daga ina nake jiyo muryar Innar ne?" Ta faɗa tana ɗan waiwaye -waiwayen ɗakin dan ta ni muryar a ɗakin ne. "Halima kin ganni nan" Cewar Inn jin bayanta ya tokare da jikin katako ta ma kasa ko da yinƙurin fitowa daga ƙasan gadon dan ta san dai yanzu aljanin ko yana nan dai, ba zai zo a tun ba ga masu gidan a nan kuma gari ya waye shi kuma zuwan dare ya yi jiya. "Ina kike Inna?" "Ko a cikin drower take" Cewar Imran a fili a ransa kuwa sai dariyar ƙeta yake yiwa Inna. Hannu Inna ta ɗauke daga riƙon da ta yiwa katakon, ta sanya a jikin filankin gadon ta shiga bugawa da hannunta. "Ƙasan gado kuma, Inna?" Sadiya ta faɗa da mamaki, ta miƙa Hassan kan gadonsa ta kwantar dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi. "Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?" Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki. Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su. "Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike" Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa. "Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga" Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa. "Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba" Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce. "Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau" dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi. "Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?" Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki. Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su. "Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike" Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa. "Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga" Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa. "Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba" Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce. "Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau. " Imran ganin Sadiya ta kamo hannunta tana janyowa amma ta kasa taimakawa Innar, hakan ya sanya ya kwantar da Husainin jin ya yi shiru ya nufi wurin ya durƙusa ya leƙa, da idanun Inna ya ci karo sun yi wani ƙwala -ƙwala, ga bayanta tokare da saman jikin ƙasan gadon. "Wa ya ga ido ya ƙwallin wake, sai rarraba ido take ya na mujiya" Ya faɗa a ransa yana dariyar zuci. Hannu ya sanya ya kamo ƙafar Inna ya riƙe wajen idon sawun ya ja. "Haba Imirana, baka ganin yadda ka riƙe min ƙafar da ƙarfi kamar ka riƙe ƙafar raƙumi, son dai ka karya min ƙwauri ko ka girɗa ni" Cewar Inna tana sauke numfashi dan da ɗan ƙarfi ya janyo ƙarfar. Ai jin ta kira shi da Imirana nan da take kiransa hajan ya sa wani haushi ya ƙara turnuƙeshi, a haɗa ƙafar duka biyu ya shiga janyosu. "Wayyo Allah, ashe Halima kina ganin rashin imanin da mijinki ke min sai ja min ƙafafu yake kamar mai ɗakko ruwa a rijiya, ni ba guga mai igiya ba a ce ana jana ta ƙarfin tsiya" "Bari in ɗauke katifar sai a ɗauke filanki sai ta fito" Cewar Sadiya dan ita ma ta tausayawa Innar amma har yanzu tana mamakin dalilin shigar Inna ƙasan gadon. Jin abinda Sadiya ta faɗa yasa Imran sakin ƙafar Innar amma ba a hankali ya saki ba jaɓas ya yiwa ƙafafun. "Ta Allah ba taka ba Imirana, in Allah ya yarda da ƙafafuna zan mutu, in ma taƙamarka ka gurgunta ni" "Ga aljani nan mai fararen kaya, na ciki bayi yana tsaye a samanki" Imran ya faɗa a ransa. Sai da aka fitar da duka filanki Inna Azumi ta lallaɓa ta fito tana jin jikinta gabaɗaya yana mata ciwo kamar wanda aka mata dukan tsiya. "Ubangijn mutane da aljannu, Allah saka m..."Inna da ta fara ƙoƙarin neman sakayya ta ja bakinta ta yi shirun gudu ko aljanin na wurin ma dan su b ganinsu ake ba. Sharaf ta zauna a tsakiyar ɗakin tana sauke numfashi. "Inna wai mai ya kai ki shiga surƙuƙin ƙasan gadon nan, ko duk kunyar gadon ce ta sa kika ƙi kwana a ka, kuma sai ki shiga ƙasan gado san ki jiwa kan ki ciwo" Sadiya ta faɗa cikin jin tausayin Innar ganin ta yi wujig-wujiga, ji yadda rigarki ta jiƙe jigif" "Haba Halima yo in har kunyar gado nake ai bana shiga ƙasan sa ba, sai in kwanta a tsakiyar ɗaki" "To mai ya ki ki shiga ƙasan gadon?" Imran jin an jefowa Inna wannan tambaya sai ya yi saurin barin ɗakin ya koma falo dan ya yi dariyarsa ta ishe shi. "Wai na ce Halima bayi nawa gareku a gidan nan?" "Inna ana ga yaƙi kina ga ƙura, bayin me kuma amma dai na ga ba yau kika fara zuwa gidan nan ba bare ki ce baki sani ba" "Ke kar fa ki min rashin kunya ki bani amsa kawai" "Guda ɗaya ne" "Mara ta gabaɗaya a cike take ina zuwa" Ta faɗa tana miƙewa ta fito daga ɗakin, gabanta na ɗan faɗuwa, tana zuwa falo ta ga Imran zaune a kujera ya ɗora ɗaya kan ɗaya baki ta taɓe ta ce "To Allah ya yi dare gari ya waye" Ta faɗa tana yin gaba ta fita daga falon. "Gata nan aljani" Cewar Imran zuciyarsa ya fara dariya har da riƙe ciki yana mamakin ƙarfin hali irin na tsohuwar nan wai ita ala dole ba za ta nuna karayarta ba. " Amma dai mu je zuwa" Ya faɗa yana sake sakin wata dariyar. Dai dai nan Sadiya ta leƙo, ganin Imran na dariya sai abin ya bata mamaki mutumin da ganin dariyarsa m aiki ne sai ya ga dama amma yake dariya haka har da riƙe ciki amma dariyar ba mai sauti ba. "Inna a ƙasan gado" Ya yi saurin faɗa dan Sadiya ta ɗauka ganin Inna a ƙasan gado ne ya sanya shi dariya, dan kar ta yi zaton akwai wani abu a ƙasa ta yi saurin harbo jirginsa. "Haba kuma menene abin dariyar ni wallahi tausayi ta bani na san haka kawai ba za ta shiga ƙarƙashin gado ba" "Hakane amma ki tuntuɓeta" "To" Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin ɗakin. ```INNA``` Tana fitowa gabanta na daɗa tsananta bugu, gani take kamar za ta sake ganin aljanin nan, hango takalmanta a wajen hanyar bayin kowanne ya kama gabansa, hakan ya sa ta nufesu ta ɗakko ta sanya a tsorace dan gani take kamar aljanin ya sa takalmin. "Wallahi dama da ba takalmina bane na ado, da ba zan ɗauka ba in je in saka kofato ya fito min" Haka dai a tsorace ta sanya takalmin ta je wurin wanke -wanke ta kunna famfo ta yi fitsarinta ta yi tsarki, ta wanke cinyoyinta zuwa ƙafafunta da fitsarin daren na ganin aljani ya ɓata mata, haka ta ɗaura alwala cikin sauri ta baro tsakar gidan, sai gata bidik ta faɗo falon kamar an jefo ta, duk da Imran ya san dalilin saurin nata sai da ya kalleta da mamaki. Amma Inna ta wayance ta fara tafiya a hankaliyadda take tafiyarta, ta buɗe jakarta ta ɗauki abin sallah da wasu kayana ta wuce bedroo. Sadiya na kallonta ta ce "Inna akwai ruwan ɗumi fa kika yi dana sanyi" Banza Innar ta mata har ta gama canja kayan ta tada sallah ita kuma lokacin tana baiwa Husaini ruwam zam-zam ɗinsa. Sai da ta idar ta kalli Sadiya ta ce "Ni Halima baku da mansileta ko roob, ko ma aboniki ne ki bani" "Me kuma za ki yi da su Inna "Ni na ji yarinya da neman dalili in da akwai ki bani mana , yo ni da na ƙarasa kwana na a ƙasan gado tamkar wacce take a ƙasan gadar legos har a tambayeni mai zan yi da man zafi, jikin nan nawa ban da ciwo babu abin da yake, ga wani wurin ma duk na kuje wallahi, kai in da ranka ka sha kallo" "Akwai kin gan su can a kan mudubi, amma Inna wai dan Allah me ya kai ki kika shiga ƙasan gado?" Har za ta faɗawa Sadiya abin da ya faru sao kuma wata zuciyar ta ce mata "Kar fa ki bada labari yana jinki ke da ba ganinsa kike ba, ya ke ya ƙara tsorataki cikin dare in har yana zuwa ita ma za ta gan shi wata rana" "Yo me zai sa kwa na shiga ƙarƙashin gado in ba sanyi ba, kin san ɗakinmu na ƙasa da banbanci da na siminti sanyi ne kawai ya sanya na shiga ƙasan gadon haba ina zan iya da sanyin nan naku na birni mutum ya rasa inda zai sa ransa, yake jinsa kamar a cikin ruwa" Ta faɗa tana shafa aboniki a jikinta. Shiru Safiya ta yi tana sauraron Inna tana ammaki wane irin sanyi Inna ta ji da har ta shiga ƙasan gado. "Allah kyauta"Cewar Sadiya. "Ina kwana Inna, ba mu gaisa ba" "Lafiya lau, ya kwanan ƴan samarin?" "Lafiya ƙalau" "To madalla bari in tashi in ɗora ruwan wanka tun da gashi har gari ya waye tangararau" Cewar Inna ta tashi ta fita. "To"Inna Haka ta fito ta ga Imran yana kan katifar ya sanya filo ya jingina da jikin kujera yana latsa waya. Ko kallonsa bata sake yi ba ta fita , wajen da aka tanada tukunya da ita ce ta nufa ga wani ƙaton murhu wanda zai ɗauke tukunyar.Kallon tukunyar kaɗai ya sanya Inna zaro idanu tana tunanin ta yadda za ta ɗor tukunyar haka ta sassaka itacen a murhun ta hura wutar tana ta ɗari-ɗari da tsakar gidan sai take ganin kamar aljanin nan zai fito, har dai ta kammala ta shiga kokawa da ƙatuwar tukunyar dakyar ta ɗorata a kan murhun sannan fa ta je take ɗakko ruwa tana zubawa a ciki sai da ta cika sannan ta rufe ta dawo ɗaki. "Ina kwana Imirana"Inna ta gaishe da shi jin bai gaishe da ita ba. "Lafiya ƙalaw" Ya faɗa idanunsa na kan wayarsa. "Idonka da kunya nangaisheka ka amsa Imirana, dan rashin kunya in zo gidankanZAMAN WANKA in kwana amma a ce ni zan gaisheka?" Shi dai bai ƙara cewa wani abu ba.Haka ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya yi zafi, ta kwalfa ta kai bayin tana ta addu'a ba dan Sadiya ba za ta iya kai ruwan ba da a ƙofar bayin za ta ajiye. Haka ta yiwa Sadiya wankan nan da ruwa mai zafin tsiya sii tururi yake amma haka ta laflafta mana da tawul, sai da ta gama sannan ta haɗa mata ruwan da za ta shiga ciki wanda aka zuba dettol a ciki, dakyar Sadiyar ta yarda ta zauna. "Yo wannan har wankan jego ne Halima wanka da tsumman tawul, mu lokacin mu da runhu ake yin wankan ruwan kan tafasa har sai ya yi ja, sannan a sanya ka tsugunna a kan garwashi" "Garwashi fa Inna" "Eh mana a sanya turaren gabgab a ciki har sai ya ƙone za ka tashi, amma ke yanzu da wannan jikin duk faci wa zai sanyaki tsugunna ɗinkin naki ya farke bayan ruwan da za a shiga ma cewa suka yi marar zafi sosai" Haka dai ta fito ta bar Sadiya a zaune a cikin ruwan ta zo ta haɗa wanda za ta wanki Hussaini dan bata ma san yadda za ta wanki Hassan ba dan bata so ma ta ga bayansa bare har ta masa wanka, dan duk maganar nan da ake fa bata yi ido biyu da bayan Hasan ɗin ba.Husssimin ta wanka ta gasa wa cibiya ta shirya shi tsaf, haka dai ta zubar da ruwan ta ƙara haɗo wani na Hassan ɗin danbata so ma dai amma haka za ta daure saboda ita ta ce ta ji ta gani za ta yi ZAMAN WANKA. Bayan ta ajiye ruwan dama Hussainin Imran ta baiwa da yake a bedoom ɗin take musu wankan.Har lokacin Sadiya bata fito daga bayi ba.Inna hannu na karkarwa ta ɗakko Hassan da ke ta bacci haka ta shiga rabashi da kayansa zuciyarta na lugude, shi kwa ya shiga yantsara kuka jin an tashe shi daga baccinsa.Sai da ta tuɓe shi tana ɗauke idanunta sannan ta kalli yaron wani irin zabura ta yi ganin yadda bayansa yake. "Lahaula wala ƙuwwata illah billahi aliyal azim" Ta faɗa hankali tashe. "Imirana! Imirana!Imirana!!" Ta shiga zabga masa kira hannunta riƙe da yaron jikinta sai rawa yake... Masu son grp na zaman wanka 09030283375.🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️9️⃣ ```TASALLAH``` Tun da Inna Azumi ta fito daga turakar Malam ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, hankalinta ya tashi, ji take tamkar ta je ta dokewa Inna Azumi ƙafa ta karyata katsak ta ga da ƙafar da za ta tafi birnin, ta san dai duk nacin son tafiyarta ba ta tafi da ƙafa a karye ba.Ta so ta nemi alfarmar Inna Azumi a kan ta tafi da ita ko ta ga yadda birni yake amma kuma girman kai rawanin tsiya ba zai barta ta aiwatar da hakan ba, ko ma an yi hakan to kuwa ta san ba za ta tsallake zunɗen mutanen gari ba, a kan cewa ta tafi dangin kishiya shishshigi da neman ɗuwawun zama, bayan nan ta san duk sanda suka dawo ta jawa kanta gori har da gore-gore daga Inna Azumi wanda babu ranar ƙarewarsa . Takaicin kishiyar tata take ta ƙoƙarin dannewa, wai har da cewa ta riƙa mata sana'ar ƙuli-ƙuli, wannan abu ya mugun tsaya mata a rai. Wato saboda ita basu da kowa a birni hasali ma bata san hanyar da ake bi aje birnin ba, shi ne Malam zai bata izinin tafiya ZAMAN WANKA har kwanaki hamsin saboda yana tsoronta. "Tasalla ki cigaba da bani labarin mana ke d kike bani labari amma kin yi shiru kamar ruwa ya cinyeki" Cewar Malam ganin tun fitar Azumi Tasalla ta sunkuyar da kai ƙasa ita ba mai zaman makoki ba ita ba mai lazimi ba, gata nan dai kamar an dasa ta. Dakyar ta danne wani wahaye da yake ƙoƙarin fin ƙarfinta, ta yi dariyar yaƙe ta ce. "Ai a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa kan nata dai a sunkuye dan tana ɗagowa hawaye ne zasu malalo mata. "Ikon Allah ke fa kika ce mahaukacin ya biyosu suna ta shirgar gudu a titi ana ƙafa mai na ci ban baki ba, ai labarin daga ji ba a kai ƙatshensa ba amma kuma ki ce ya ƙare" Malam ya tambaya mamaki fal fuskarsa. "Na ce maka a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa ƙwalla na cika idanunta daf take da gangarowa amma ta hanasu fitowa dan kissa da kisisina, dan kar Malam ya ce dan Inna Azumi za ta je birni take yin kuka dan tun da ta share hawayen farko a ɓoye bata bari wasu sun biyo bayansu ba. "To ai shikenan, bari na fita na ga tafiyar Azumi kar ta ɗauki ƙafa cewar ko tafiyarta ban gani ba, haka ya ɗora babbar rigarsa a kan kayan jikinsa ya fito ya barta, dai dai an ɗakkowa Inna Azumi kayanta. Tasalla kwa na ganin fitar Malam sai ta fashe da kuka tana jin ina ma ita ke ƴan uwa a birni ta zo tafiya Malam zai rakata ya ga tafiyarta a bi da ita ta tsakiyar gari tana washe baki. Amma ina gabaɗaya danginta a ƙauye suke, Malam tana jin lokacin da Malam ke cewa Inna Azumi jakar nan kamar wanda za ta ƙaura hakan ya sanya ta tashi ta leƙo ta tagar ɗakin Malam ɗin aikuwa ta yi ido biyu da jakar Inna Azumi da ke shaƙe da kaya almajiri na riƙe da ita. "Wayyo ni dama ban haɗa kishi da wacce take da dangi a birni ba da na huta da baƙincikin tafiyar Azumi" Ta faɗa a ranta tana sharar hawaye. Tun da Malam ya fita bai dawo ba har ta gaji da zaman ɗakin masa ta fito ta koma ɗakinta, dan lokacin da ta fito ma da ta yi tozali da ɗakin Inna Azumi rufe da kwaɗo sai da ta ji kamar ta yi ta zabga ihu da kururuwa mutane su kawo mata ɗauki, dan halin da ta tsinci kanta a ciki. Tana shiga ɗakin ta zauna a ƙasa ta shiga rasga kuka kamar wata ƙaramar yarinya kowacce aka ce ubanta ya mutu, sai da ta yi mai isarta ta nemi wuri ta kwanta tana ta saƙar jaki, ta saƙa ta kwance, addu'a take ta yi a zuciyarta Allah ya sa Inna Azumi su faɗi a machine ta ji ciwon da zai hanata tafiya birni ZAMAN WANKA. Jin shiru-shiru bata dawo ba kuma ba a kawo mata wani labari ba ta san cewar Inna Azumi ta tsallake.Haka ta tashi tana ta ƙuncin rai ta ɗora tukunyar danbun rana tana jin a ranta cewar yanzu kenan ita za ta ke ta ɗorawa da sauke wa tun da Azumi birni ta ɗauka. A haka ta kammala danbun ta raba ta baiwa kowa nasa, Malam kuwa saƙon tafiyarsa wani ƙauye kusa da su ɗaurin aure ya aiko mata, hakan ya sanya ta zuba danbun nata ta shiga ɗaki, zaune take a ɗakin nata ta sanya danbun a gaba amma saboda tsabar kishi da baƙinciki ta kasa cin ko da loma ɗaya ne. "Ni da cin danbu yana shaƙe min wuya ina korawa da baƙin ruwa ita kuma tana can za ta ke cin shinkafa da miyar ɗanyen kaya ta kora da lemon kwalba ta yi kuɓulɓul da ita" Ta faɗa tana jin wani takaici. Haushi ne ya sa ta sanya ƙafa ta hankaɗe kwanon danbun ba tare da ta ci ko da loma ɗaya ba. Bayan ta kammala tuwo dab da magariba, lokacin Malam yana waje wurin almajirai ana karatun yamma. Ɗaki ta koma har lokacin ranta ba daɗi a kan tafiyar Inma Azumi birni dan wunin yunwa ma ta yi saboda baƙinciki. Tana ɗakin ta tsinkayi sallaɓar Tsahare aminiyar Inna Azumi, duk a tunanin Tasalla Inna Azumi sun faɗi a machine ne Tsahare ta samu labari ta taho dubiya. "Wataƙila tana asibitin bayan gari" Ta faɗa tana tashi har da taka rawarta ita ala dole Inna Azumi bata samu tafiya birni ba, sai da ta gama taka rawarta ta ɗaga murya ta amsa sallamar Tsaharen, ta fito baki a washe tana ta fara'a kamar ranar salla. Mamaki ne ya kama Tsahare ita dai ta san duk ranar da ta zo gidan nan konda Tasalla tana tsakar gida Inna Azumi na ɗaki to kuwa Tasalla ba za ta amsa sallamarta ba sai dai Inna Azumi ta amsa mata, amma sai gashi yau wai ita ce har da washe mata baki. Gaisawa suka yi cikin mutunci Tasalla tana jira ta ji ta ce mata ya mai jikin amma sai ta ji ta ce. "Ikon Allah ashe dai da gaske ne?" "Hatsarin wai?" "Subhanallahi! Su waye kuma suka yi hatsari?" "A'a ba hatsari aka yi ba, kawai dai na faɗa ne" Cewar Tasalla cikin wayancewa ganin babu alamar Inma Azumi ta yi hatsari dan ga mamaki nan ƙarara a fuskar aminiyarta. "To da mai kike tambaya da gaske ne?" Tasalla ta faɗa tana tana wani haɗe rai tamkar ba ita ce ke washe haƙora ba yanzu, jin haƙarta bata cimma ruwa ba. "Ni fa mai machine ne ya je gidana ya xe min wai Azumi ta ce ya faɗa min ta tafi birni ZAMAN WANKA babu ma ranar dawowarta, wai tafiyar ce ta zo mata a bazata, shi yasa bata je min sallama ba, wai in shirya in je ranar suna, to shi ne fa na ce bari in je gidan in tabbatar to kuma ina shigowa kwaɗon ƙofarta ya tabbatar min da gaskiyar al'amarin" Cewar Tsahare tana washe baki. Wani haushi ne ya turnuƙe Tasalla kawai sai cewa ta yi. "Wai sun isa Garkin lafiya kenan?" "Lafiya ƙalaw dan mai machine ɗin da ya kaita ma ya ce sai da motarsu ta Kano ta tashi ya kamo hanyar dawo wa" "To ai shikenan, kuma za ki je sunan?" Tasalla ta tambaya tana kafe Tsahare da ido. "Zuwa kamar da ƙasa ma kuwa, kin san ko bikin jikar tata Sadiya wacce ta haihun yanzu mun je bikin kwanana uku, bare kuma samun ƙaruwa ai mu dole ne ma birni ta ɗauka" Ta faɗa tana washe baki dan ta turawa Tasalla haushi, tun da ba wani zama lafiya suke ba da Inna Azumi dan haka ko lokacin bikin ma bata gayyaci Tasallar ba. Taɓe baki Tasalla ta yi ta juya ta shige ɗaki abinta, ita kuma Tsahare ta fita daga gidan tana jin daɗi cewar gaske ne Inna Azumi ta tafi birni ashe wannan karon ma akwai wankin ciki da na baki. Tasalla na shiga ɗaki ta rinƙa gewaye -gewaye ta rasa abin da yake mata daɗi, dan haka ta ci alwashin da Tsahare za su je sunan nan sai dai ta fanjama fanjam ta san abin da za ta faɗawa Malam ya barta su je birnin. ```MAMA``` Tun a napep ɗin suke ta jajanta halin da zaman Inna zai kasance a gidan Sadiya yadda Imran yake da faɗin rai ga girman kai rawanin tsiya, bugu da ƙari ma baya ƙaunar mutane su raɓeshi, ga Inna kuma da ɓaranɓarama, kwata -kwata bata yin abin da ya dace sai ta saki baki ya layar mai tafiya ta rinƙa zuba kamar lalataccen famfo babu ruwanta da mijin Sadiyar bare kuma mahaifiyarsa, tabbas dai akwai gwarama dan Imran ba ƙyalewa zai ba ita ma kwa Innar bata tsoron ta mutu bare ta yi rai kawai komai ta fanjama fanjam. "Amma Mama bakya gani tsofa ne ke sanya Inna waɗannan abubuwan?" Ashrof ta tambaya tana kallon Mama. " Haba Ashrof ko ma da tsufa ai da sha'anin Inna wani abin ai dole take kauda kai, ki ga fa daga cewa Sadiya tana naƙuda shikenan ta haɗo kaya shimili guda ta taho ZAMAN WANKA, ba tare da ta sanar da kowa ba" "Kuma haka ne, amma gaskiya ya kamata ta canja halinta Mama ko dan take ja mana girman mu a wajen Hajiya da kuma Imran ɗin ma dan irin wannan ai sai ya ta ja mana raini" "Yo na nawa kuma an ce da kuturu a gama lafiya, ai sai dai kar a ƙara kuma in da sabo ai su ma zuwa yanzu sun san wacece Inna" "To Allah kyauta" "Amin" A haka dai har suka isa gida suna fitowa daga napep ɗin Mama ta buɗe musu gidan suka shiga. Bayan sun ɗan huta suka rama sallolin da ake binsu, sai Ashrof ta fita ta siyo musu awara suka ci suka kwanta suna ƴar hira. "Wai Mama baki lura da yadda idon Inna suka firfito ba lokacin da zan miƙa mata hassan, bakinta sai mutsi yake kamar mai zikirin safiya da maraice" Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya. " Yo tsoronsa fa take, dan ta ji an ce fatar bayansa irin ta miciji, ban da Inna menene na tsoro ita da za ta yi ZAMAN WANKA, wankansu fa da shirya su har ma da goyo da raino duk ita fa za take yi" Mama ta faɗa tana ƴar dariya hasasho yadda za ta kaya tsakanin Innar da Hassan da ma ubansa Imran. "Allah Mama ni fa tausayi take bani, yanzu wanann ƙatuwar tukunyar ta yaya za take ɗorawa a murhu da ruwa ai ba za ta iya ba ma, idan kwa ta tarka wallahi wataran sai dai ta tumbulu cikin ruwa dan hantsilawa ciki za ta yi" Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya. "Baki da dama Ashrof wato dan kin ga Inna bata nan ko, shi sa kike faɗar hakan amma da tana nan si ta baki amsa dai dai da ke" "Mama har hango Inn fa na yi ta faɗa ruwan tana iyo kamar kwaɗo tana neman ɗauki, Yaya Imran yaƙi fiddota, tana cewa Imirana ka ji tsoron Allah ka fiddoni, idan na mutu nauyi ya rataya a wuyanka, shi kuma ya ce mata in kin mutu dama kwananki ne ya ƙare" Ta ƙarasa faɗa tana dariya har da riƙe ciki hango yadda za a yi diramar kawai take. "Ke ki kiyayeni, in ke kakarki ce ai ni uwa ce a wurina" Mama ta faɗa tana dariyar ita ma, dan ta san tabbas da ace hakan za ta faru Imran ba zai fito da Innar ba musamman in aka ce Sadiya bata kusa ko da zai fito da Innar daga tukunyar to sai ta sha wahala ita ma kuma idan ta fito sai ta rama ta wata hanyar dan bashi ya ci daga haka suka kwanta abinsu. ```HAJIYA``` Tun da ta sauka a napep ɗin ta shiga gidan nata jiki sanyi ƙalaw dan kwata -kwata haɗin Inna da Imran bai yi ba musamman da ya kasance za ta shiga haƙƙinsa na rabashi da kwana wuri ɗaya da masoyiyarsa dan ta san Inna ko giyar wake ta sha ba za ta bari su kwana ɗaki ɗaya ba ma bare kuma wuri ɗaya sai dai ta san Imran dai dai yake d Inna duk ta yadda ta ɓullo masa sai ya zame duk da dai ta gargaɗeshi a kan zaman Innar a gidan. ```INNA``` "Imirana kar ka jinkirta wajen amsa kirana dan Allah ina cikin halin ƙaƙanika yi" Cewar Inna har lokacin hannunta da gabaɗaya jikinta ma tsuma suke suna karkarwa kamar an jona jikinta a wutar nepa ko transpomer. Imran kuwa yana jinta banza kawai ya mata dan ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, tabbas ya riga da ya san cewa arba kawai ta yi da bayan Hassan. Jin kiran nata ya cika masa kunne tare da karaɗe gabaɗaya gidan hakan ya sanya ya kwantar da Husaini a kan kujerar ya tashi a hankali ya leƙa ta jikin labule ba tare da ta sani ba. Hangota ya yi a zaune magashiyan ga uban baho ɗauke da ruwa, sannan ga Hassan ɗin a hannunta sai jijjiga hannunta ke yi. "To fa ga zara ga wata" Ya faɗa yana komawa ya zauna a kujera yana dariya ƙasa -ƙasa yadda ba za ta jiyo ba. "Imirana wallahi ina cikin matsala dumu-dumu, ka zo kar yaron nan ya koma maciji gabaki ɗaya, in shaga uku, dan idan na ganni da riƙe da miciji muraran babu shamaki suman da zan yi sai ya fi cikin carbi idan ba dakyar ba ma na ƙarasa ƙiyama a haka" Inna ta faɗa tana sakin kuka. Jin shiru dai babu alamar motsin Imran gashi ta san ko ta kira Sadiya ba jinta za ta yi ba dan tana can a bayi, kuma bayin a rufe, sannan ma ita kawai so take a taimaketa a rabata sa yaron a karɓeshi daga hannunta dan ta ma kasa jajiyeshi. "Imirana wallahi mutsu-mutsun da yake a hannu na yana motsi ji nake kamar maciji na riƙe, yo ina daɗi ace ina riƙe da ajalina, yo maciji ai mutuwa ne, wannan ai mutuwa kusa ne" Ta faɗa tana ɗaga muryarta dan Imran ya kawo mata ɗauki. "Wannan tsohuwa da zan san inda MALAM Abubakar bilhaƙƙi mai magununan nan da ake tallarsa a tv wallahi da na ce masa ya zo ga wacce za take masa talla ba sai ya sha wahala ba dan tsaf za ta ke karaɗe gidan talabijin da wannan shegen surutun nata marar kan gado marar kai da ƙafa.Ya faɗa yana tasowa daga kan kujerar ua nufi ɗakin. "Yawwa ɗan albarka ai gwara da ka tausaya min ka zo" "To wai meye kika dameni da kira kamar wata makauniya" Ya faɗa yana kallonta. "Haba Imirana da rashin kira karen bebe ya ɓata" "To gani ai" "Riƙa nan riƙa Imirana" Ta faɗa tana ɗago Hassan ɗin. "Kamar ya na riƙa Inna, ni zan masa wankan ne?" "Haba Imirana shin kusan haka jikin yaron nan yake amma aka bari na tuɓeshi tsirara na yi mugun gani" "To menene a ciki" "A'a sa komai a ciki mana, kasan kowa da kiwon da ya karɓesa wai maƙocin mai akuya ya sayi kura" "Ki masa wankan mana" "To inda riƙeshi in dubo Halima a bayi" "Haba Inna in mafaɗin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce. "Bari na dubo miki ita da a kan dubo Sadiyar ne kike ta wahalar da kan ki har da kuka Inna" "Ka karɓesan dai ni na dubo ta, ka san mutum baya ƙin ta mutane wai an ce ɓarawo ya gudu" "Inna magana fa zarar bunu ce, ke kika ce mun san jikin yaron nan haka yake kika tuɓeshi yanzu kuma kin canja maganar kenan" "Bari dai in fito maka a mutum Imirana, karɓi yaron nan dan ba zan iya tashi in ɗorashi a gadonsa ba saboda yadda jikina ke tsuma ga arangamar da na yi jiya da dare duk jikina ciwo yake, ka karɓeshi kar in je in luntumashi a ruwa, dan ni ban ma yarda ɗan mutuma bane wannan" "Ɗan nawa ne ba ɗan mutum ba, to wallahi kika saka shi a ciki sai mun yi shari'a" "Yo in ba ɗan aljan...Shiru ta yi da faɗar aljannun tunowa da ta yi da yadda suka kwashe da aljani da dare har ta ƙarasa kwananta a ƙasan gado hakan ya sa ta saki akalar maganar ta kama wata. "Da za ka yarda ku kai shi bakin ruwa a gani indai ya gangara ya shige ruwa to dama ɗan ruwa ne, in ba haka ba tayaya zai yi rabi mutum rabi miciji" Kan ta kai ƙarshen maganar Imran ya sanya hannu ya karɓe ɗansa cikin zafin nama da jin haushin Inna yana raya wani abin da zai mata dan bashi ta ɗauka cewa ɗansa ɗan ruwa da ta yi. "Wash Allah, ai gwada da ka karɓeshi, ai dama kowa da kiwon da ya karɓeshi wai maƙocin mai akuya ya sayi kura, wato ga Inna ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, kamar ni a ce a sanya min linzami a baki yo da bakina wa zai hanani magana, aikin banza harara a duhu" Ta faɗa lokacin da ta sauke wata ajiyar zuciya ta tashi ta zauna a bakin gadon tana sakin maganganu. Wani kallo Imran ya watsa mata yana ji kamar ya shaƙeta. "Aikin banza harara a duhu, ni ban san harara ba sai ido ya faɗo" Ta faɗa tana tana gyatsinan gefen hanci.Imran da ke ƙoƙarin fita daga ɗakin sai kawai ganin kan Hassan ya yi yana wani kamar lanƙwasa kawai sai ya koma kamar yadda kan maciji yake lokacin da ya fasa kai, sai ganin fatar cikin yaron ma ta fara komawa irin fatar bayan, Inna bata lura da abin da ya gani ba dan haka cikin sauri ya kalli ƙasa inda shawul ɗin Hassan da Inna ta ajiye ya ɗorashi a hankali, cikin hanzari ya fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar ɗakin ya sanya mukulli. Inna da ta lura da fitarsa bata san ya ajiye Hassan ɗin ba sai ƙaran rufe ƙofar kawai ta ji, Ta zabura za ta tashi sai ji ta yi Imran ya ce "Inna kalli Hassan ki gani gashi nan na ajiye miki shi" Idanu Inna ta zaro ganin fatar cikin yaron ta rikiɗe zuwa irin fatar bayansa, wani uban ƙara ta ƙwalla, dan yaron a setin hanyar da za ta sada ta da ƙofa yake gashi ma ta ji Imran ya rufe ƙofar tare da sanya mukulli... Masu son grp na zaman wanka MMN AFRAH 09030283375 🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼 (KWANA ARBA'IN) NA MAMAN AFRAH 🅿️1️⃣0️⃣ Last 🆓 page Wannan littafin kuɗi ne 300 Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134 ```MALAM``` Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya shigo gidan dan tuwansa ma ƙofar gidan aka kai masa inda suke cin abinci shi da abokansa. Cikin gidan ya nufo bayan almajirai sun shigo masa da tabarma da butarsa cikin gidan dan dama yanzu basu da wasu yara a gidan sai almajirai. Duk an aurar da matan suna gidajensu haka ma mazan babu wani ƙaramin yaro yanzu. Sallama ya rinƙa kwalawa daga tsakar gidan Tasalla da ke cikin ɗakinta ta amsa masa dan yanzu dakyar ta daure ta ci tuwo kaɗan shi ma dan tana jin yunwa na neman kwantar da ita shi ne ta daure ta ci, amma ko tuwon ta ɗauka za ta sa a baki sai ta ji wani ƙululun takaici a zuciyarta dan tana tunanin Inna Azumi na can birni tana asuwaki da kaza. Malam kuwa turakarsa ya sanya kai bayan ya ƙwalawa Tasalla kira kyawawa guda uku, haka ta tashi ta nufi ɗakin nasa tana kitsa yadda za ta yi kisisinar da zai barta zuwa birni dan ko sau ɗaya ne dai a rayuwarta ya kamata ta je birni ko da kuwa kwa Inna Azumi za ta tsireta idan ta je. Da sallama t shiga ɗakin ya amsa mata tana shiga ya ce. "Wai ni Tasalla me yake damunki ne, ya za a yi ki bar ɗakin nan babu garwashi kin san dai ja fi so a kawu wuta ɗaki kafin in shigo gida ɗakin ya ɗau ɗimi" Ya faɗa yana kallonta. Shiru Tasalla ta yi dan ita gabaɗaya ma yau ta manta da zancen kaiwa wutar ɗakin na Malam. "Wallahi Malam sha'afa na yi ka san yau da gobe sai Allah" "To sai ki je ki ɗakko yanzu idan baki kashe wutar ba in kuma kin kashe sai ki hura ko dai ki tafi maƙota ki samo" Ya faɗa yana ajiye hiraminsa da ya cire. " A'a ban kashe ba ma dai cire itacen ne kawai amma akwai garwashi bari in ɗakko maka" Ta faɗa tana ɗaukan ƙaton kaskon wutar Malam ɗin. Sai da ta ciko shi da garwashi sannan ta dawo ɗakin ta maida ƙofar ta rufe dan dama al'adar Malam ce daga isha'i ta yi yake shigowa gida ya rufe sai kuma gobe in Allah ya sa ana raye. Sai da ya yi shirin kwanciya ya kwanta amma Tasalla tana gaban kaskon nan tana kara hannayenta a jiki tana jin ɗumin wutar. "Wai kam Tasalla yau duk wani iri nake ganinki ko baki so Azumi ta tafi ba?" "kai, kai kai, Malam bar faɗa dan Allah, ni da ƴar uwata Azumi abokiyar zamana mai zai sanya na ƙi son tafiyarta" "Yau ɗin kuma Azumi ce ƴar uwarki Tasalla ko dai kin yi makuwa ne?". "Ras nake wallahi, dama ai an ce zo mu zauna zo mu saɓa, amma ai ina ƙaunar Azumi" Zaune Malam ya tashi da sauri yana ƙarewa Tasalla kallo dan bai taɓa jin hakan ba daga bakinta ko a mafarki. "Allah sarki ashe akwai ranar da Allah zai nuna min irin hakan nan ɗaya tana yabon ƴar uwarta ku da bakwa jituwa ko da wasa tun daga girmanku har tsufanku amma kuna faɗa sai gashi yau komai zai zama tarihi" "Yoa ai ka san duk irin makaman yaƙin da mutum ya ɗauka idan ya ajiye nasa kaima ajiyewa kake, wai ɗazu baka ga shigowar Tsahare gidan nan ba?" "Ni kwa na ga shigowarta dan har gaisawa mun yi" "Wayyo ashe sai haƙata ba za ta cimma ruwa ba ashe sun gaisa ta faɗa masa me ke tafe da ita" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce. "Ashe ma ta faɗa maka saƙon" "Wane saƙo ai gaisawa kawai muka yi da yake da mutane sai kawai ta shigo ciki" Wata ɓoyayyar ajiyae zuciya ta sauke jin bata faɗa masa ba dan hakan zai bata dama ta sheƙa ƙaryarta son ranta. "Saƙon meye?" "Malam kenan" Ta faɗa tana ɗan sunkuyar da kai alamar tana jin nauyinsa da kunyarsa.. "Dan Allah ki faɗa min Tasallata daga ke ba ƙari" "Yo na nawa kuma an ce da gwauro ya iyali, Azumin kuma fa da ka ƙaromin ko ka ɗauka na manta to ai in maye ya manta uwar ɗa ba zai yu ta manta ba" "Ni ba na son tone-tone kawai ki faɗa min ko da na ƙaro Azumi ma ai kece babba kuma matsayinki da ban yake a wurina" Wani irin washe baki Tasalla ta yi daɗi fal ranta masoyinta a yabe ta tare da jaddada yadda take a wurinsa. "Dama Azumi ce ta baiwa ɗan machine ɗin saƙo ya je gidan Tsahare ya faɗa mata ta je birni sunan jikarta Sadiya, kuma ta zo har gida ta faɗa min mu tafi tare a sha shagali" Ta faɗa tana kallonsa. Wani irin kallon mamaki yake mata wanda har ya so ya bata tsoro. "Haba Malam kamar an faɗa maka wani mugun abu" "Yo ba gwara mugun abu ba da wannan kk ma in ce meye marabar dambe da faɗa, Azumin da za ta tafi ya kuka kwashe da ke a ɗakin nan nawa, me yasa bata gayyaceki ba da bakinta sai bayan ta tafi za ta bada saƙo?" "Malam kenan kai baka san sauyi ya kan zuwa wa mutuɓ lokaci guda ba, ina ga bayan tafiyarta ta ga dacewar hakan" "Ko jikina kunne ne ai ba zan yarda ba cewa Azumi za ta gayyaceki sunan jikarta ba" "To ai gashi nan yanzu ka gani ta aiko har gida ka san dai ba zan zauna in shirga ƙarya ba dan kawai ina so in je birni" Ta faɗa tana sanya hannu ta share hawayen kissar da ta ƙwaƙwulo. Hakan ya sanya jimkinsa yin sanyi, ya ce. "Ban ƙi taki ba Tasalla kawai dai abin ne da mamaki wai kiɗa a gidan makoki, amma tun da har ta faɗa babu dalilin da zai sanya na hanaki zuwa ai hakan kamar kawo gyara ne a zamantakewar ku Allah nuna mana" Wani daɗi ne ya baibaye Tasalla har tana rasa inda za ta sa ranta dan daɗi, cikin murna ta yi kan Malam ta ƙamƙameshi tana ta dariya. "Wayyo kin cukuikuye min wuyan riga Tasalla duk kin shaƙe min wuya, yashe rabon duniya da ayyaraye" "Wallahi Malam duk daɗi ne ya cika min ciki" "Daɗin daidaituwarki da sobar zamanki?" "Daɗin zuwa birni dai" Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ce. "Wallahi kuwa Malam zama lafiya ai ya fi zama ɗan sarki" "Allah ƙara haɗa kawunanku" "Amin Malam" Haka suka kwanta Tasalla ko baccin kirki bata yi ba tana ta tsara yadda komai zai kasance Allah-Allah take gari ya waye ta je ta san ƙaryar da za ta yiwa Tsahare dan ta tafi da ita ranar sunan. Da gari ya waye Tasalla bayan ta gama komai ta tafi gidan Tsahare ta same ta tana tuyar ƙosan siyarwa nan suka gaisa ta faɗa mata abin da ke tafe da ita kan cewa Malam ya tilasta mata zuwa sunan Sadiya dan a samu maslaha tsakaninsu, duk da Tsahare ta yi mamakin amma sai ta ce mata babu koɓai Allah ya nuna mana ranar, tun da dai ta san da kuɗinta za ta yi kuɗin mota kuma sauran diramar ta sha kallo tsakaninta da Azumi dan ta san ba za a kwashe ƙalaw ba muddin Azumi ta ga Tasalla a gidan sunan da ba ta gayyaceta ba dan lo lokacin bikin Sadiyar cewa ta yi babu inda Tasalla za ta je bare kuma suna.Haka ta baro gidan Tsahare ranta fari ƙal. Wannna kenan. ```MAMA``` Da asuba bayan sun idar da sallah sun yi azkar sai Ashrof ta shiga gyara gidan da yake yanzu bata zuwa makaranta sai islamiya da yake ta kammala secondry school kuma bata cigaba ba da karatu da yake ƙa'idar babansu ce tun kan ya rasu cewar babu wacce za ta cigaba da karatun sai dai in ta yi aure ta cigaba a ɗakin mijinta. Ko Sadiya ma tana kamamala secondry school aka mata aure. Bayan ta kammala komai suka karya ta yi wanka ta shirya sai Mama ta ce ta bari sai kamar ƙarfe tara sai ta tafi dan kar ta yi musu sakko. ```Hajiya``` Tana idar da sallah ita ma ta shiga hada hadar gyara gidanta da yake wuni biyu kennan bata zauna ba dan haka gidan yana buƙatar gyara sosai dan haka ta shiga gyarawa a ranta tana ta tunanin yadda Imran da Inna suka kwana ko ya aka ƙarshe. ```INNA``` Rawar sanyi ta fara tamkar wacce masassara ta yiwa mugun kamu, ta shiga wani irin tashin hankali da ya sanya ta kasa gane ina mafitarsa take, so take ta je ta buga ƙofar tare da roƙon Imran ya fiddota dan ta san matsawar ta ƙara wasu lokuta tare da Hassan a ɗakin to tabbas babu abin da zai hana ta suma in ma bata yi gawa ba. A tsaye take amma kuma ƙafafunta sai rawa suke kallon Hassan take da ke kwance kan shawul gaba ɗaya ya gama sawaya daga mutum zuwa miciji kan sa ne kaɗai na mutum amma dai yana a inda aka ajiye shi ko yunƙurin motsawa bai yi ba. Ganin yadda Hassan ya mata shamaki da zuwa wurin ƙofa hakan ya sanya ta yanke shawarar neman ɗaukin Imran duk da ta san da gayya ya rufe ta amma ya zame mata farilla tusa a masallaci ta nemi ya buɗe ta. "Imirana, Imirana, dan Allah ka taimaka ka buɗe ni kai ma da ɗan nan ya zame maka dole ka gudu daga ɗakin bare ni ɗorin ɗosano kakar uwarsa" Ta faɗa tana magiya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa ko motsin Imran ɗin ma bata ji. Amma hakan bai sa ta saduda da neman ɗaukin daga gareshi ba dan haka sai ta ƙara ware murya ta ce. "Imirana indai mutuwa kake so in yi billahillazi ba sai ka rufe ni da Hassan a ɗakin nan ba lokaci na ma yana tafe zan mutu ba sai ka haɗani da wannan abun ba" "Inna in kin ga na buɗeki to tabbas sai kin wanki yaron nan, ya zaki yi ki wanki ɗan uwansa amma shi kiƙi masa wanka, sannan bayan haka ma har ki ce wai shi ɗan ruwa ne bayan kin san baiwa ce Allah ya masa, ba ke ce jiya kika ce kar ake raba kan su ba, tun da har Allah ya halicce su a ciki ɗaya? Amma shi ne ke kika fara nuna musu banbanci, baki san ba a yiwa tagwaye haka ba ransu ɓaci yake" "Haba Imirana ya za ka faɗi haka da bakin ka, son dai ka sanya Hassan ɗin ya min wani abu, ni ban nuna musu banbanci ba, kuma da kake batun ba a nuna musu banbanci ni dai na san ba a ɓata musu rai in ransu ya ɓaci suna ɓatawa mutane abinci ko ayi ta dafa abinci yaƙi dahuwa amma tun da uwata mai daddawa ta haifeni ban taɓa jin inda aka yiwa ɗan mutum baiwar komawa miciji ba" "Wai wa ya ce miki miciji ne bayansa ne fa kawai fatar ta miciji" "Ƙur'ani miciji ne, dan baka ga yadda ya koma ba yanzu wallahi kan sa ne kawai na mutum" Inna ta faɗa idanunta a kan Hassan tana sakin kuka dan sai ta ga girman macijin ya yi yawa. "Ki wankesa sai na buɗeki" "Wallahi ba zan wankeshi ba, ta ina zan fara wanka wannan abu himili guda wallahi da in wankesa gwara ya kasheni in san mutuwar shahada na yi, ai da uwaka Amina ce ba za ka rufeta a ɗaki ɗaya da maciji ba" "To zage ni Inna sai in buɗe miki" "Ni shegiya in ji ɗan daudu ba zan fara ba ma ina so ka buɗe ni ta ina zan fara zaginka ai ko banza ba zan ce maka ba" "Gashi kwa kin faɗa kn ce banza" "Sa'adiyya, Sa'adiyya, dan Allah ki fito daga bayin nan, ima dalili kamar wacce za ta koma budurwa in kin yi zaman ruwan zafin, bayan har ƴaƴa biyu sun keto ta gabanki ba yadda za a yi ki koma kamar da, in kuma wanka kike in ba fatar za ki canja ba dan Allah ki zo ki ga halin da Innarki Azumimi take ciki duk na fita hayyaci na... "Sadiya fa bata jinki kawai ki min abu ɗaya in buɗe ki ya katse mata magiyar da take yiwa Sadiya. "Me kake so, ko goyaka ka ce in yi Imirana zan goya ka in dai ka fito dani" "Kin ji matsalar ai, so nake ki kirani da suna na, na asali wato ki ce IMRAN inda kin faɗa to zan buɗeki" "I,Imir, Imirana" Ta faɗa dakyar dan ta kasa faɗar yadda yake so. "IMRAN kawai nake so ki ce" "Haba wnnnn rashin imani har ina tayaya bakin tsohuwa zai iya faɗar wannan abu ban da ɗaukan alhaki wallahi Imirana duk ranar da na fito za ka san ka min wannan wulaƙanci" Ta faɗa tana rushewa da kuka. "Sai ki bari sai kin fito ɗin, ke ba matar malam bace ki yi addu,a kawai ki kuɓuta" "To ai mutum ba ya ƙin ta mutane" Cewar Inna.Jin abin da Imran ya ce sai ta tarki yin addu'ar amma ruɗani ya sa ta manta komai, tunani ta shiga yi can sai kawai ta ji wani karatu ya faɗo mata a baki. "Alif, am baki, waw, zal, ba, alif, baƙi, lallam, hakuri" Ta faɗa da ɗaɗɗaya kamar yadda ta ji almajiran Malam na biyawa da allo. Imran yana kwance rigingine tsabar dariya yana tunani wai dama matar nan akwai maganinta aka bari ta addabi mutane, dariya yake tun ƙarfi can ya ce. "Am, baki," Sai Inna ta karɓa da cewa 'Waw zal" Ƙaran dariyar Imran kawai Inna ke ji, hakan ya sanya ta fara neman yadda za ta samu mafita dan ta ga bashi da niyyar taimakonta. Idanunta ta mayar inda Hassan ke kwance aikuwa ta yi arba da gabaɗaya ya koma maciji har kan, idanunta ta zaro ta ce. "Hassan kai ne ka koma haka,duk da hausawa sun ce kaƙi naka duniya ta so shi, ka so shi duniya ta ƙi shi, to yau dai ga ranar, ni dai na ƙika dama ba wani haɗi garemu ba,Allah tsari gatari da saran shuka, uban gyatumarka kawai na haifa, ni ma ban da shishshigi shiga dangin miji da ganamasgo me ya kaini zuwa ZAMAN WANKA, ya Allah ka raba bawa da wahala gwauro a teburin mai shayi" Tana faɗar haka ya fara ja baya har sai da ta ji ta tokare da jikin drower waigen mafaka ta fara amma bata gani ba, idanunta ne suka sauka a ƙasan gado inda ta kwana jiya kawai sai fashewa da kuka ta yi ta ce. "Ni Azumi na ga takaina, tun da na zo birnin nan nake yin angamo da abubuwa, na yi angamo da mazaƙutar (Al'aura) abokin Imirana, na yi gamo da aljani cikin dare lokacin da ake cewa mahutar bawa amma haka na kwana a tsakanin katakwaye, sauron duniyar nan ya gama cinye min ƙauri, ga riga a jiƙe duk sanyin nan amma rigar tana naniƙe dani da lema da komai haka na jure na kwanta, yanzu hallaw daga garin Allah ya waye a rufe ni da miciji a ɗaki" Ta faɗa tana jin haushin kan ta da bata fito daga ɗakin ba lokacin da Imran ya karɓi Hassan. Da sauri ta nufi akwatunan Sadiya da aka musu ɗaya kan ɗaya, guda huɗu ne, hakan ya sa ta hau kan su amma tana iya hango jelar Hassan na kaɗawa tana motsi, da sauri ta diro daga kan akwatuna ta taka gado, ta buɗe drower step ɗin wardrobe ɗin ta kalla ta ce. "In ka ji mutum na cewa ba zan iya ba to bai kama shi bane, ƙafafunta ta ɗora a kan step ɗin cikin drower ta ƙanƙanme a haka ta yi matakala da step ɗin sai gata ta haye saman drower can saman ta hau kan ta na gab da silin. "Taimakona ɗaya da Allah ya yi lokacin sanyi ne da ace zafi ake fanka a kunne ai da an yi gudun gara an tadda zago, da fil fanka za ta ɗauke min kai" Ta faɗa tana kallon ƙasa inda Hassan yake har lokacin yana nan a micijinsa. Sai da ta ji ta zaune dandam, ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce. "Allah raba bawa da wahala, na san dai komin nisan dare gari zai waye, amma ban da dai matar mutum kabarinsa babu yadda za a yi Halima ta auri wannan yaron marar imani" Ta faɗa tana rafka uban tagumi. Ƙaran buɗe ƙofar bayi ne ya sanya Imran daina dariyar da yake ya tashi zaune sa sauri ya koma kan kujera ya zauna ya ɗauki Husaini ya riƙe dan ba ya so ko Sadiya ta san gashin ƙumar da zai ke yiwa Inna a gidan dan ya san ko ba komai kakarta ce kuma ba za ta ji daɗi ba. Da sallama Sadiya ta shigo falon, amsa mata Imran ya yi mamaki ta yi da ta ganshi ɗam a zaune fuskarsa fes da alamar yana cikin nishaɗi, mamaki take yi daga jiya zuwa yau Imran ya sauya ya zama mai yawan fara'a kumai magana ba ta masa wahala yanzu, danganta hakan ta yi da ƙaruwar da aka samu. "Ina Innar?" Tambaya tana kallonsa. "Tana ciki Hassan take yiwa wanka" "Ikon Allah shi ne har da rufo ƙofa" Ta faɗa tana sanya hannunta ta tura ƙofar, ashe kafin ta shigo falon Imran ya buɗe mukullin da ya sanya, dan haka ƙofar kawai ta tura ta shiga. Inna da ke saman drower tana jin duk abin da suke cewa, a ranta ta ce "Lallai Imirana ya cika maƙaryaci, kuma maƙetaci wallahi yau duk abin da za a yi sai na yi jarumta na yi ta maza na rama abin da ya mini" Ta faɗa tana jijjiga kai. Sadiya da ta shigo idanunta suka sauka a kan Hassan da ke kwance a siffar miciji ya fasa kai kamar zai sara, idanu ta zaro cikin kiɗima ta fara waiwayen inda za da ga Inna dan bata ganta ba kuma tana tunanin kar dai saran Innar ya yi. "Sa'adiyya kin ganni nan" Inna ta faɗa cikin raɗa-raɗa, ta shaƙe murya kamar wanda aka riƙe mata maƙoshi sai da ta faɗa sai biyu sannan Sadiya ta tsinkayo muryarta ɗaga idanu ta yi ta sauke su a kan Inna da ke kan drower ɗare-ɗare kamar biri ya samu saman bashiya. "Inna" Ta faɗa tana kallon Innar yadda ta yi wani wujiga-wujiga ta yi sharkaf da gumi kamar wacce ta fito daga filin restiling, sai ka ce ba sanyi ake ba. Amma kuma sai ta ga Inna tana sanya hannu a baki alamar ta yi shiru mamaki ya kama Sadiya sai kuma ta yi tunanin tsabar tsoro ne ya sanya Inna bata so a ɓuga magana saboda micijin, tana ƙoƙarin juyawa ta kira Imran ya zo ya ga abin al'ajabi dan ta lura da yanayinsa bai san abinda ke faruwa ba dan cewa ya yi Innar wanka take yiwa Hassan. Inna ta gani ta ƙanƙame drower ta sanyo ƙafarta cikin drower ta ya fara taka step ɗin drower da ke drower a buɗe take kawai sai gani ta yi Inna ta dirƙo a kan gado da ta faɗo gadon ma har da wata adungure ta yi alkafira sannna ta sauke idanunta a kan micijin nan wani yawu ta haɗiye midik amma duk da hakan bata karaya ba a kan abin da ta yi niyyar yiwa Imran. Tsaye ta miƙe a kan gadon sai da ta saita yadda za ta tsallake micijin sai kawai ta yi wani tsalle sai gata ta tsallake miciji ta zo kusa da Sadiya da ke bakin ƙofa, tana zuwa bata yi wata -wata ba ta riƙe Sadiya ta ce mata a kunnenta "Ƙwalawa Imran kira ki ce ya ajiye Husaini ya zo amma kar ki faɗa masa Hassan ya zama maciji dan kar ya razana" Inna ta faɗawa Sadiya hakan cikin raɗa a kunne. Sadiya kuwa da bata gane menene ba sai ta shiga kiran Imran da cewa ya ajiye Husaini sai da ya yi dariya sosai sannan ta taso dan shi duk tunaninsa fatar miciji Inna ke yiwa rangwangwan ɗin wannan. Yana dai dai shigowa ɗakin Inna ta riƙe hannun Sadiya gam, yana gama shigowa ɗakin kafin idanunsa su kai kan Hassan Inna ta ja Sadiya ta shammaceshi sun fita daga ɗakin, suna fita ta banke ƙofar ta cire mukullin ta sanya a aljihun ɗan tofinta (Siket ɗin da ake ɗinkawa tsoffi suka sanyawa cikin kayan jikinsu) Ta ja zip ɗin ta zige hakan ya yi dai dai da saukar idanun Imran a kan danƙareran miciji da ya fasa kai yana ciccira ido. Wani uban juyawa ya yi tare da yin kukan kura zai gudu yana taɓa ƙofa a jita a rufe. Sadiya kuwa da bata gane abin da Inna ta yi ba sai ta shiga tambayarta dalili nan Inna ta kwashe komai ta faɗa mata. "Saboda Imirana ya raina ni dan rashin Imani har da cewa in ke addu'a tun da ni matar Malam ce, yo ɗiyar nan ina ma na tuno da wata addu'a kawai dai na ji ina karanto alif, am baki ,waw zal, yo banda ruɗewa da gigicewa ina waɗannan baƙaƴe zansu zama addu'a kai Allah raba bawa da wahala, ji yadda na koma yau ne kika shiga wanka amma azabar da na sha wallahi kamar wata na yi a cikin ɗakin, yadda kika san a cikin rijiyar macizai aka saka ni haka na tsinci kaina cikin fargaba amma Imirana bai tausaya min ba bai dubi tsufana ba ai yau ko sama da ƙasa za su haɗe sai ya ɗanɗani abin da na ɗanɗana dan wallahi ba zan buɗe ba gwara ma ki ja bakin ki ki yi shiru ki toshe kunnuwanki dan ba magiyarki ba zan ji". "Sadiya miciji ne fa, Sadiya da ke za a haɗa baki a sanya ni a ɗaki a rufe da miciji" "Babu mai buɗe ka sai ka masa wanka tas ka shirya shi, ni ma da yake ɗan jikata muka zauna bare kai da ka yi fush ya fito duniya" Inna ta faɗa tana zaunawa a kan kujera Sadiya kuw sai magiya take Inna ta bada mukulli ko ta buɗeshi amma taƙi. Kuka Imran ya saki ganin micijin ya fara gangarowa daga kan shawul ɗin kamar ma wajensa zai zo. Ya dadage cikin ihu da ɗaga murya yana kuka ya ce. "Inna dan Allah ki min rai wallahi ban san ya zama miciji ba da na buɗeki duk tunani na a yadda yake a haka yake". "Sai ka lissafo min sunayen limaman da suka yi limanci a masallacin makka da madina tun daga wanda suka fara har zuwa na yanzu" "Haba Inna ya za a yi in iya wannan aiki" "Ni kuwa ka ce sai na faɗi sunanka ba wanda nake faɗa ba bayan ni ma ba iya na yi ba. Sai da ya shafe sama da awa guda a ɗakin nan yana kuka da magiya amma Inna bata buɗe ba, sai da ta ga Sadiya na kuka sannan ta haƙura ta buɗe tana buɗewa ta ga Imran a jingine a jikin bango ya yi sharkaf da gumi har da fitsari ma ya yi a wurin, ga macijin ya fasa masa kai a daf a daf suke da shi. "Imran haka kake manne da bango kamar wani ƙadangare" Inna ta faɗa tana dariya, da gudu ya miƙe har yana neman hankaɗe Inna da ke bakin ƙofa, Inna ta juya ta bishi tana dariya har lokacin yana share hawaye dan bai taɓa shiga mawuyacin hali irin haka ba. "Imran ka ganka kamar wanda ya fito daga rijiyar maciji" Banza ya mata , Sadiya kuwa ta ɗanta take ɗakin ta nufa tana zuwa cikin jin tausayin Hassan ɗin ta sanya hannu ta ɗan dungureshi, cikin tsoro dan ta san ko zai cutar da kowa ita ya ɗaga mata ƙafa ko dan kasancewarta mahaifiya a wajensa.Tana dungurinsa kuwa ya kanannaɗe jikinsa sai kuwa ya koma jariri tare da tsallara uban kuka, da sauri ta miƙa hannu ta ɗaukesa tana jijjigashi, ta zauna tana share hawaye ta sanya shi a nono tinɓir da shi ko wando babu da Inna ta masa tsirara za ta masa wanka. Inna ce fa shigo ganin tana bashi nono ta kama haɓa ta ce "Lallai uwa da ɗa sai Allah yanzu nono kike baiwa miciji Halima" "Haba Inna dan yana zama miciji sai na hana shi nono bayan na san ɗan mutum ne, kakarmu ta wajen uwa ta taɓa bamu labarin wacce ta haifi ɗaya mutum ɗaya miciji, kuma ta taɓa cewa wata maƙociyarta ta haifi yan biyu in aka kwamtarsu idan aka zo ɗaukansu sai a ga wani ya zama miciji kuma ta ce da za ave za a cillar da su to sao su koma mutum kuma za a ga sun ji ciwo" Taɓe baki Inna ta yi ta ce "Sai ki ajiyewa Amina ko Rakiya in sun zo su masa wankan. Ta faɗa tana fitowa daga ɗakin, tana fita tsakar gida suka yi ido huɗu da Imran yana wani muzurai. Haka dai Ashrof ta zo ta girka abinci da yin ayyukan gidan, Hajiya ma ta zo Mama kuma sai yamma ta zo. Ƴan uwa da abokan arziƙi da maƙota suka ringa shigowa suna yin barka. ```DARE``` Kowa ya yi bacci amma Inna idanunta biyu dan gani take kamar aljanin nan ma jiya zai kawo mata ziyara, haka ta matse fitsarinta, can cikin dare ta tashi Sadiya ta ce su yi macanjan bargo ita dai Sadiya bata ce komai ba, dan bata son rikicin Inna kuma ga bacci a idanunta, Inna kuwa ta yi haka ne dan idan aljani ya zo nemanta sai ya ga bargonta a jikin Sadiya wataƙila ba zai yiwa Sadiya komai ba dan ita ƴar gidan ce, ca haka bacci ya yi awon gaba da Inna, da goronta da ta ɓalgata ta gama taunewa ma bata haɗiye ba. ```IMRAN``` Gabaɗaya ya kasa bacci burinsa kawai ya ji shi a jikin Sadiya, zuwa can ya yanke shawarar zuwa ya shiga bargon Sadiya ya ɗan sanyata a jikinsa ko ya rage zafi tun da Inna nauyin bacci gareta. Cikin sanɗa ya shigo ɗakin, da wayarsa ya haska ya gansu suna ta bacci, haka ya kashe wayar ya ajiye akan mudubi yana mamakin yau Inna bata munshari. Bargon Sadiya ya ɗaga a hankali ya shige ciki, ya sanya hannu ya rungumota jikinsa, dan bai san Inna bace kawai ya yi amfani da bargo ne dan bai san sun yi canjan bargo ba, bakinsa ya sanya ya haɗe da na Inna da bai san ita bace Inna kuma jin an ruƙunƙumeta da ta falka sai ta yi zaton aljani ne hakan ya sanya ta fara kiciniyar ƙwatar kan ta, Imran bai ankara ba ya ji wani goro a bakinsa mai uban ɗaci, da sauri ya ɗauke bakinsa yana zaro idanu Inna sakin uban ihu ta yi da ta tashi zaune wanda ihun nata ya sanya Sadiya miƙewa zaune , Imran kuwa gefen gado ya samu wani ɗan sukurutu ya laɓe dan ya ana yau ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai fidsa kan sa ba ga goron da ya gogo garin yin kiss ya haɗe masa baki... 😂😂😂😂😂 To fa readers dandandan dan dan dan dan, ga akuya ga kura dan jin yadda za ta kaya ki siya ki karanta dan nishaɗinki ki sha walwala da dariyarki, labarin ZAMAN WANKA yanzu aka fara. Ku nuna soyayyarku ga marubuciya mmn afrah ta hanyar siyan littafin mai zaman wanka ngd Dan ƙarin bayani 09030283375 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels