An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [08/10, 2:50 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                    💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*             *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._              *NO_1 & 2*              *RIYADH NORTH*          Hannun ta riƙe da bairo tana juya wa a kan book ɗin but ta kasa rubuta komi, tunani ne sosai a ranta wanda ya hana ta saƙat, shin yaushe ne zata kasance cikin farin ciki? Har yaushe ne komi zai wuce a rayuwar ta? Komi ya koma mata kamar baya? Idan ta zauna tana irin waɗannan tunanin sai taji da ace ba'a haife ta ba...             Faɗin da bairon nata yayi ne ya sanya ta dawo cikin hayyacin ta, idanun ta a kan bairon amma ba ta da alamun ɗauka, sai ta tsira mishi Sexy eyes ɗin ta a ɗan soconni kafin ta janye su tana jan ajiyan zuciya, lumshe idanun tayi a lokaci ɗaya tana buɗe su, ko kaɗan fuskar ta babu ɗigon fara'a wanda dama ta jima rabon da ta ganta cikin farin ciki, idan kuwa ka ga tayi murmushi sai dai tana gaban Abee ɗin ta ne, wannan kuma domin farin cikin shi take yi, ba ya ga haka babu wanda ke ganin dariyan ta bare murmushin ta a yanzu, ko yaushe a yanayi ɗaya take, walau farin ciki ko baƙin ciki, abin har ya zame mata jiki Tashi tayi tana saka room silifers ɗin ta da ta zame su daga ƙafafun ta, sai ta taka a hankali ta nufi bakin windown ɗakin ta, hannayen ta ta sanya ta zuge cootin ɗin wanda haske ya bayyana a cikin ɗakin da ada babu, kanannaɗe hannayen ta tayi a ƙirji tana bin wajen da kallo, yayinda ta faɗa duniyar tunanin da ya zame mata jiki ko yaushe, tana tuna abubuwan dake faruwa a rayuwar ta Daga ita sai guntun riga me ruwan Powder, dressed sleeping ne, sai gashin ta da ta ɗaure shi a ƙasan ƙeyanta ta sanya baƙin hula me kauri wanda ya fito mata da tuntun gashin nata, har kunnen ta ta rufe a cikin hulan wanda da alamu garin da akwai sanyi ne, duk da haka be sa ta sanya kayan sanyi ba, illa hulan dake kanta na sanyin, kuma ba wai don ba ta jin sanyin ba, sai dai ta saba da yanayin ne.           Ta jima a nan a tsaye kafin ta janye idanun ta tana wuce wa cikin Toilet, wanka tayi ta fito ɗaure da Towel a jikin ta, a lokacin ne ake mata Nocking a bakin ƙofar ta "Na'am". Tace tana me zama gaban dressing mirror Buɗe ƙofan aka yi wata budurwa ta shigo da uniform a jikin ta, da alamun ƴar aiki ne don sai da ta duƙa ta gaishe ta kafin cikin harshen larabci tace, "ji'itu liru'uyatiki, li'annani ƙultu laki lah takruj". ( "dama na zo duba ki ne saboda naji ki shiru baki fito ba".) Bata kalle ta ba ta bata iznin tafiya Sai ta tashi ta fice Ita kuma lotion ta shafa a jikin ta tare da Powder, sai ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta, buɗe wa tayi ta ciro kayan da zata saka, ta shirya cikin riga da wando masu taushi brown color, sai ta ɗaura after dress baƙi sannan ta yane kanta da gyalen shi, flet shoes ta saka a ƙafafuwan ta sannan ta ɗauki handbag ɗin ta ta fito. Steps ta taka ta sauka ƙasa ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan Bata kai da shiga ba wata mata ta fito tana sanye da fararen kaya, da alamu Nurse CE ita Sai ta kalle ta tace, "Abee". Murmushi matar tayi mata tace, "jasadahu khafifun jiddan, wal'aán huwa naà'im". ("jikin shi da sauƙi sosai, yanzu haka ya samu barci ne".) Bata ce komi ba ta ɗago hannun ta tana duba wrist watch ɗin ta, sai kuma ta juya ta nufi kan dainning, zama tayi tana ajiye handbag ɗin ta saman dainning ɗin, sai ta saka hannu ta janyo Cup ta haɗa tea rabin Cup, ta soma sha a hankali duk da akwai zafi, sai dai hakan be dame ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tana miƙe wa tsaye A lokacin ne Nurse ɗin nan ta fito daga kichen riƙe da faɗeɗen bowl a hannun ta Fuska ba walwala kamar ko yaushe tace da ita, "a'atani bihi jiddan min fadlik". ("ki kula dashi Please".) Bata jira cewar ta ba ta juya tayi hanyar fita, tana fita compound ɗin gidan ta shiga motan ta ta fice. Tafiyan mintuna goma ya kaita cikin school ɗin su, kai tsaye department ɗin su ta wuce, tana yin parking ta fito ta wuce class ɗin su A lokacin babu wasu mutane a ciki sosai, sai ta samu wuri ta zauna a gaba ta ciro wani book tana duba wa Har Malamin ya shigo ya soma musu karatu babu wasu mutane sosai Hankalin ta na kan malamin har ya gama ya fita Time ɗin ne waɗanda ke gefen ta suka samu damar mata magana, Esha ce tace, "Hello, my beauty, are you already here today?" Ta ƙare maganar tana murmushi Ɗago kai tayi ta kalle su, memakon ta bata amsar sai tace, "where is Zamiya?" "Today she will not come". Cewar Ummu Hani "Why? But she didn't inform me?" Ummu Hani Said, "you know the pain she is going through, today she is suffering." "Let's go check on her before the teacher comes in." "Ok". Suka tashi su ukun suka fice, kai tsaye Hostel ɗin makarantan suka wuce, room ɗin da Zamiya take suka nufa, until they were Nocking before she opened it for them Seeing them, she jumped up and hugged them happily Esha na dariya tace, "Oh are you okay? Let's go back". Hararan ta Zamiya tayi tana turo baki tace, "wlh I don't feel comfortable, glad to see you". Duk dariya suka yi ban da Meema dake bin su da kallo, duk da a ranta tana jin farin ciki, amma kuma baza ta iya nuna shi a fuska ba "Let's come in". Tace dasu tana yin gaba Zama suka yi a kan sofa, inda Zamiya ta dubi Meema tace, "My Beauty What about Abee's Body?" "Alhmadulillah easily". Ummu Hani Said, "By the way, we forgot we didn't hurt him. Please I'm sorry." "It's alright". Cewar Meema tana duba wayan ta, sai kuma ta ɗago tana kallon Zamiya tace, "what about your body?" "Alhmadulillah, I was relieved. I wanted to go to school but I didn't get a chance." Esha said, "Did you hear anything. You don't care about your body, do you?" Tana dariya Zamiya tace, "Allah has made it easy for me. Let's get ready and go together." "You are not enough wlh, you will not follow us". Esha tace hakan tana hararan ta Ummu Hani na dariya tace, "where is your water? It's easy for her, please let her go." "is what I see like her body". Zamiya tafaɗa tana dariyan itama "Get up and let's go". Cewar Meema "No there is still time for us Meema, sorry stay please?" Tayi maganar da marairaice fuska Kallon ta Meema tayi tace, "We're going to be late for class. It's too late for us to leave, but we'll be back soon, God willing." "Yeah then, but what can I cook for you?" Esha tayi tsagal tace, "How are you Can you cook for us? "No, we forgive you." "I can wlh". Zamiya Tayi maganar cikin shagwaɓa Dariya Ummu Hani tayi tace, "The king of racism is not in front of Ummee you are". Cike da gajiya wa Meema dake kallon su suna dariya tace, "let's go please". Sallama suka yi mata suka bi bayan Meema da har ta fice ma, ita kuma Zamiya ta rako su har bakin ƙofan ɗakin ta sannan ta koma Suna fita wayan Meema ta soma ringing, ɗago wa tayi tana kallo sai taja tsaki tana sauke hannun ta ƙasa suka ci gaba da tafiya Esha da ba ta iya shiru tace, "Is that Ishaq?" Meema bata kalle ta ba bare ta tanka ta Sai ita kuma ta sake cewa, "but why do you want to change him? Please don't let your worries affect your love, you are suffering a lot from it, Please do peacking you see he calls again". "Hmm". Kawai Meema tace bata kula ta ba Ummu Hani Said, "here he is". Duk ɗaga kai suka yi suna kallon inda Ummu Hani take kallo Wani kyakykyawar Balaraben saurayi ne tafe zuwa wajen su, fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi ya iso wajen su Daga Ummu Hani har Esha tsaya wa suka yi wajen sa suna amsa sallaman da yayi musu Ita kuwa Meema har ta yi gaba zata wuce, sai Esha ta janyo ta baya tana cewa, "Please O'o Meema". Hararan ta Meema tayi bayan ta dakata daga inda take Shi kuwa kallon ta kawai yake yi yana doka murmushi Esha says, "we'll pass the class, when you're done find us in class". Daga haka suka yi gaba ita da Ummu Hani Kanta a ƙasa bata kalli inda yake ba Hakan yasa ya ƙarisa kusa da ita ya tsaya yana faman kallon ta, sun ci mintuna biyu babu wanda ya furta komi Sai ta ɗago kanta ta zuba masa idanun ta, ganin kallon da yake yi mata sai ta balla masa harara tana cewa, "Please I will be late for class. " Cikin sanyin muryan sa yace, "why Beauty did you change me? Wlh I really love you! Why do you want to part with me?" Cikin ido take kallon shi yayinda ta sake ɗaure kyakykyawar fuskar ta tamau kafin tace, "please let's stop saying that now, let's do it later". "No, I do not agree. I cannot leave here unless you answer my questions. You know that I love you and this decision you have taken has made me very sad. How do you think I can part with you after tasting your honey love? Wlh I love you Meema, if you want I will kneel in front of you because I will apologize". Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka Itama fuskar ta da alamun gajiya wa in a calm voice she said, "I told you we will talk later. Please let Me go". "Ok When?" Dafe goshi tayi tana kallon sa tace, "Ishaq problems". Dariya yayi yace, "on your love I am crazy". Taɓe baki tayi kafin tace dashi, "by tomorrow insha Allah". Tana gama faɗar haka ta wuce ta bar shi nan. Kai tsaye aji ta wuce, tana zama malamin da suke dashi ya shigo class ɗin.               Zuwa ɗaya suka sami break, sai suka wuce Hostel wajen Zamiya, a can suka yi sallah suka ci abincin da ta girka musu, sai faman hira suke yi suna dariya amma banda Meema da sai jefi-jefi take saka musu baki.               Three O.clock suka koma class suka yi lecture ɗaya, sannan kowa ya wuce gida.                Meema na koma wa gida tayi parcking ta fito tayi cikin gidan, gaba ɗaya a gajiye take amma hakan be sa da ta shiga ta wuce ɗakin ta ba, ɗakin Abee ta wuce ta shiga da sallama Nurse ɗin dake kula dashi ta amsa mata sallaman tana faɗaɗa fara'an ta tare da mata maraba Da kallo kawai ta bi su daga ita har Abee ɗin nata ta kasa amsa wa, sai dai gaba ɗaya fuskar ta ta sake haɗe wa ganin ta da poo a hannun ta, "taya ma za'a ce wata ce zata riƙa kula da mahaifin ta a irin wannan yanayin?.." Muryan Abee ɗin ta da ya ratsa mata kunnuwa yasa ta ƙifta idanun ta da suka kawo ruwan hawaye, cike da ƙunci a zuciyar ta ta ƙarisa wajen sa While Nurse Zara tuni ta shige Toilet don plushing kashin da yayi A gaban gadon ta durƙusa tana kallon sa, sai ta saka hannayen ta ta kamo nashi hannun guda ɗaya, cikin rawan murya tace, "Abee.." Murmushi ya sakar mata a hankali yace, "Ummy why are you crying?" "Nothing Abee, I'm not crying". Ta ƙare maganar hawayen ta na silalo mata saman kunci Girgiza mata kansa yake yi, cike da raunin murya na wanda ciwo yaci sosai yace, "Please Ummy I beg you to stop crying ok? I'm not happy to see your tears." Tamke bakin ta tayi tana saka hannu biyu ta share hawayen tana faɗin, "ok Abee I'm stop, you see?" Sai ta ƙare maganar da sakin murmushin da ya bayyana jerin ƙananun fararen haƙoran ta, wanda har dumples ɗin ta suka samu damar fito wa "Ok, did you go to school today?" "Na'am Abee, I went to school, but I'm sorry I didn't come in to check on you. " Murmushi yayi yana gyaɗa kansa yace, "don't worries, go eat and rest ok?" Amsa mishi tayi kafin ta ɗago hannun nasa a hankali ta sumbace sa, sannan ta tashi daga durƙuson da tayi, a time ɗin ne Nurse Zara ta fito daga Toilet ɗin, kallo ɗaya Meema tayi mata ta ɗauke kai tana fice wa Ita kuma Nurse Zara ta gyara mishi pilown da ya sauke kansa, sannan ta tambaye sa "ko da abinda yake buƙata kuma?" Girgiza mata kai kawai yayi Sai ta juya ta ɗauko airfreshna ta fesa a ko ina sabida warin kashin da ya ɗuma ɗakin ya fice, bayan ta gama ta fice a ɗakin.                   ******                Da kuka Meema ta koma ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gado tana ci gaba da rera kukan nata, wanda inda da sabo ya rigada ya zame mata jiki, a kullum tausayin Mahaifin nata ƙara yawa yake yi a zuciyar ta, ta kasa saba wa da wannan ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa, kullum gani take yi tamkar zai tashi ya koma kamar da, ya riƙa mata wasa kamar yanda ya saba yin mata, su riƙa cin abinci tare suna wasa da dariya tare, amma kuma ciwo ya yanke mata wannan ƙauna da jin daɗin, wanda tana ganin babu ranan da zata sake shiga cikin farin ciki idan har ba mahaifin ta bane ya warke ya koma kamar da ba, ba ta ganin akwai ranan da walwala da jin daɗin ta zai dawo Hawayen ta ta saka hannu tana share wa yayinda wasu suke sake ɓullo mata, babu abinda ke sake bata haushi illa yanda mahaifiyar ta ta kasa kula da Abee ɗin ta, sai wata ce take iya cin kashin sa taci fitsarin sa, sannan kuma ta ƙetara muhallin da ba nata ba, a kullum sake jin tsanar mahaifiyar ta take yi, tana ganin kamar har da baƙin cikin ta Abee ɗin ta ya kasa samun lafiya, ko da be faɗa mata ba ta san yanda yake jin ƙuna da azaban tafiyan ta, ta zaɓi son duniya da son zuciya ta rabu da su, a kan abinda be taka kara ya karya ba, ita a ganin ta babu mahaifiyar da zata tafi ta bar ɗiyar ta da mijin ta a halin ƙunci da neman taimako, mahaifiyar ta ba mutum bace, kuma bata da zuciyar imani Fashewa tayi da wani sabon kukan, cikin tsananin ƙunan zuciya tace, "I hate you so much Ummee! I hate you!! I hate youuuu". Hannu ta sa ta rufe fuskar ta, in slow voice tace, "Why Ummee? Why did you leave us?". Ta jima tana kukan wanda har kanta ya ɗau zugin zafi, sannan ta dakata tana tashi ta zame kayan ta ta shiga Toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallan Asar bayan ta saka shimi iya gwiwa da dogon Hijab, tana idar wa ta ɗaga hannu ta soma kwararo addu'o'i tana kuka, gaba ɗaya duk wani addu'ar ta yanzu nema wa Abee ɗin ta lafiya take yi, domin shi ne farin cikin ta a yanzu, idan har babu shi haƙiƙa ba ta ba sake farin ciki a duniya.             House girl ɗin su ne ta shigo da sallama Hakan yasa ta dakatar da addu'ar nata tana shafa wa a fuskar ta, sannan ta sauke kumburarrun idanun ta a kan ta ba tare da tace mata komi ba illa amsa sallaman da tayi a ranta "Sayyadaty, hunaki duyuufu fiis saàlun, jaà'uu ila Abee". ("Ma'am akwai baƙi a Parlour, sun zo wajen Abee ne".) Jimm MEEMA tayi har a lokacin tana kallon ta, sai kuma tace, "izhab wa'as'al man hum?" ("Je ki tambaya su wane ne?") "Ok Ma'am". Ta miƙe da nufin fice wa Sai kuma ta dakatar da ita tana ce mata, "Ƙaàlat lahum an yaruûhaà huna". ("tace musu ga ta nan.") Bayan ta fita sai ta tashi ta zare Hijab ɗin jikin ta, daga ita sai shimin jikin ta sannan ta zira room slippers a ƙafafuwan ta ta fice, tana sauka downstairs ta hange su su biyu a cikin parlour'n, bata gane ko su wane ne ba sai da ta iso gab da su sannan fuskokin su suka yi mata maraba, baza ta taɓa manta waɗannan mutanen ba, duk da kusan shekaru shida kenan rabon su da tako wannan ƙasan, yayyin mahaifin ta ne dake zaune a Nigeria da suka haɗa uba ɗaya, waɗanda suka watsar da su suka raba hanya da su, saboda tsantsan tsanar da suka yiwa mahaifin ta, shiyasa ma ko zuwa nan ɗin ba sa yi.              Tana isowa tabi su da kallo hannayen ta a ƙugu, ko ba'a faɗa mata ba ta san ba arziƙi ya kawo su ba kamar yanda suka saba zuwa a shekarun baya, tunda su ko kaɗan basu da mutunci, shiyasa itama yanda take ji a ranta duk abinda suka zo dashi tana dai-dai dasu, zuciyar ta sosai take mata ƙunci baza ta taɓa raga musu ba idan har za su taɓa mata Abee Wanda yake shi ne Babba ya soma magana da faɗin, "ke baki da kunya ne zaki zo ki tsaya mana akai dan uban ki?" Sai ɗayan yace, "taya zaka tambayi kunya a nan Yaya bayan ka ga yanda tazo mana a tsatstsaye tana turo mana ƙirji? Ai daga gani ka san babu kunya domin Faruk be koya mata ba, shiyasa yaƙi yarda ya koma ƙasar sa tunda ya san abinda yake faman yi a nan. Yanzu dan ubanki ke da kika zo gaban mu kika yi ƙere-ƙere rashin kunya zaki yi mana ko me? Uban naki shi ne dai-dai damu ba ke ba". Duk maganganun da suke faɗa ko ɗaya MEEMA bata ji su ba domin ba ta jin Hausa. kuma su ma sun san da hakan; amma dayake tsiya yaci ransu shiyasa suke ta maganar ba tare da sun tuna ba She then said to them, "what are you saying I do not hear you". Tsaki Yaya Ali yaja yana cewa, "matsiyaciya ubanki muka ce shegiya.." sai kuma ya juya harshe cikin turanci yace, "ina shi uban naki muka ce?" Wani kallon banza ta watsa musu kafin tace, "He is not here, what you want?" Salati suka saki lokaci ɗaya suna kallon ta "Yanzu Zulaiha mu kike faɗa wa wannan maganar? Yanzu har idanun ki sun buɗe da zaki yi mana rashin kunya a matsayin mu na Yayyin ubanki? Tirƙashi.." cewar Yaya Ali cikin harshen turanci Ita kuwa bata ma tsaya sake jin ta bakin su ba ta juya zata wuce Sai Zubairu ya kwaɗa mata kira, "Zulaiha.. Zulaiha". Amma ko juyo wa bata yi ba ta haye Steps da gudu tayi ɗakin ta, kan gadon ta ta haye tana ɗaukan wayan ta ta soma Game cikin sauri-sauri, sosai ranta ke a matuƙar ɓace shiyasa ta kasa controling kanta tsaban yanda ranta ke ƙuna, sai kuma ta jefar da wayan a saman gadon tana miƙe wa da sauri, fita tayi da gudu ta nufi downstairs, ganin babu su a parlour'n sai ta nufi ɗakin Mahaifin ta da sauri ta bankaɗa ƙofan da ƙarfi Yaya Ali da Zubairu dake gaban gadon da Abee yake kwance sun tasa shi gaba suna ta tsitsiye shi da bala'i duk da kuwa sun ga mawuyacin halin da yake ciki, hakan be sa sun dakata daga amayar masa da tijaran da suka ɗibo ba, ko tausayi babu a lamarin su. Buɗe ƙofan da MEEMA tayi ne sai duk suka tsaya suna mayar da kallon su kan ƙofan, inda suka sauke idanuwan su kanta da itama take bin su da kallo idanuwan ta sun kaɗa sun yi jawur tsaban ɓacin rai. [08/10, 2:51 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*           *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                  *NO_ 3 & 4*      Gaba ɗaya idanuwan ta sun rufe ta manta da cewa su ɗin ƴan uwan mahaifin ta ne, ta nufi ciki a zuciye tana cewa, "what are you doing here What brings you to my Abee room? Get out .. get out..." Zubairu ne ya dage ya falla mata marin da sai da yasa ta duƙe a wajen tana tsandara ihu Daga Nurse Zara da House girl ɗin su dake Parlour sun yi cirko-cirko sai da suka tsorata saboda ihun MEEMA da suka ji, musamman ma Nurse Zara tunda bata san su ba sai House girl ɗin ne tayi mata bayani da suka nemi shiga ɗakin Abee zata hana su, dayake ita ta san su tun shekarun baya da suke zuwa.         Yanda MEEMA take ihu zaka ce an yanka ta ne saboda abinda bata taɓa ji bane ya faru a rayuwar ta, tunda uwar ta ta zuƙuna ta haife ta ba'a taɓa marin ta ba, shiyasa duk ta gama gigicewa ta rasa gabas da yamma Abee kuwa tuni ya soma kuka saboda ganin abin da Zubairu ya yiwa ɗiyar sa, idan da ace yana da ƙafafun tashi wlh babu abinda zai hana shi be rama mata ba saboda yanda zuciyar sa take tafarfasa, cikin rawan murya da kuka daƙyar ya soma maganar cikin gurɓataccen hausan sa yace, "Yaya Zubairu meyasa ka maran min Ummy? Meyasa.. meyasa? Me tayi muku? Don Allah kar ku kashe min ita na roƙe ku". Yanda Abee ke yi ne sai duk suka saki baki suna kallon shi "Ikon Allah yanzu kai Faruk don an yi mata wannan ɗan marin shi ne kake kuka ka tayar da hankalin ka haka? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. tabbas  maganar da ake faɗa ya tabbata, ashe bayan rashin auren da ka ƙi kay mata take yawon karuwanci kai ma bin ta kake yi wato? Ita shafaffiya da mai baza a taɓa ta ba tunda kana samun abinda kake so ko?..." "Enough Yaya... Enough...?" Yayi maganar cikin rawan baki sosai wanda daƙyar ya iya faɗi tsaban tashin hankalin dake cin sa da jin abinda ɗan uwansa yake faɗa Yaya Ali da yayi maganar sai ya sake cewa, "dalla rufe mana baki ko zaka ce ƙarya ne bayan ga shi mun gani? Shiyasa Allah ya kama ka ga ka nan a kwance babu ƙafafu ciwon Cancer ya kama ka, to, wlh kaɗan ma ka gani muddin baka canza alƙibla ba, ka gudu ka bar ƙasan ka ka zo nan ka ɗauki al'adun wasu, sannan ka koya wa ɗiyar ka karuwanci ga ta nan taƙi aure ganɗamemiya da ita, ƙannin ƙannin bayan ta mun aurar da su amma kai kaƙi, shiyasa ma matar ka ta gudu ta barka tunda muna da labarin komi, abin ma da yasa ka gan mu a nan don mun ji labarin ciwon ka ne, kar duniya ta tsine mana a matsayin mu na ƴan uwan ka muka zo mu taimake ka, zaka bamu wannan mara kunyan yarinyan taka mu je can mu aurar da ita ko ka rage nauyi a kanka". Duk maganganun nan da Yaya Ali yake yi gaba ɗaya Abee ya tsaya yana sauraron sa inda hawayen fuskar sa ke sake kwaranya kamar an kunna famfo, domin ya ma kasa magana MEEMA da sai yanzu ta gama dawowa hayyacin ta, sai ta tashi da gudu ta faɗa jikin Abee ɗin ta ta sake sakin kuka me tsuma rai, sosai take kuka tana kiran sunan sa, so take yi ta ce mishi ya dena kuka amma bakin ta ya ƙi furta wa illa kukan da take yi Shi kuwa sosai jikin sa ke rawa yana hawaye babu daman taɓa ta, domin gaba ɗaya jikin sa ba ya aiki Zubairu yace, "ka gani ko Yaya Ali, tun bamu je ko ina ba suna son su nuna mana halin karuwancin". Sai ya kalli MEEMA ya daka mata tsawa da cewa, "tashi ki je ki haɗo kayan ki mu tafi". Ita duk bama tasan me suke magana a kai ba, ko kaɗan taƙi ɗagowa a jikin Abee illa kukan ta dake ƙara yawaita Abee daƙyar yace dasu, "babu inda ɗiya ta zata bi ku wlh, na gode da taimakon naku Yaya zaku iya tafiya". A zuciye Yaya Ali yace, "haka kace ko? Mu yi tattaki tun daga uwa duniya amma kaƙi bin umarnin mu? To shikenan Allah ya gani mun sauke haƙƙin ka tunda haka ka zaɓa. Taho mu je Zubairu yau zamu koma gida". Haka suka fice gaba ɗayan su a fusace.         Sai lokacin MEEMA ta ɗago kai tana kallon Abee ɗin da idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jazur tace, "What are they saying Abee? Please tell me." "No Ummy stop talking ok?" Gyaɗa masa kanta tayi inda sosai hawayen ta suke tsiyaya Girgiza mata kai yayi yana cewa, "Stop crying please I don't want to see your tears flow. Please Ummy". Hannayen ta ta saka tana share hawayen, sai kuma ta saka hannun tana shafa inda Zubairu ya mare ta, wurin sosai ya kumbura yayi ja har yatsun sa sun fito, sai ta sake shigewa jikin Abee ɗin tana ɓoye fuskar ta jin wasu sabbin hawayen sun sake zubo mata Be ce mata komi ba illa a haka suka ci gaba da zama, yana jin yanda take fitar da numfashi da shashsheƙa na tsawon lokaci kafin kuma yaji fitar numfashin nata ya sauya, hakan yasa ya gane ta samu barci, shima lumshe idanun sa yayi yana me jin hawaye sun cika mishi ido, ba komi ya tuna ba sai rayuwar su na baya, da yanda ada suke tsantsan cikin farin ciki ako da yaushe, sai dai kuma lokaci ɗaya Allah ya jarabbe shi da wahalhalun ciwukan nan, Cancer da ciwon sugar, yayi jinya na ɗan wasu watanni a asibiti inda lokaci ɗaya kuma side ɗin jikin sa ya dena aiki gaba ɗaya, mafarin kenan da suka sake rasa gaba ɗaya farin cikin su Daga baya likitocin sun sallame shi domin sun ce, "jinyan sa sai dai a gida, saboda zai daɗe be warke ba, kuma hakan zai cinye musu kuɗi sosai ga wahalhalun zirga-zirga na asibiti," dole aka mayar dashi gida likita na kula da shi Tashi ɗaya mahaifiyar MEEMA ta nuna gajiyawar ta da mishi hidima na yau da kullum a matsayin shi na majinyaci wanda be iya taɓuka wa kansa komi A wani ranan da baza su taɓa manta wa ba MEEMA ta tafi school, sai dawowa tayi ta tarar da Ummeen ta ta tafi. Wanda sanadiyar tafiyan nata ne ciwo ya sake yin tsanani ga Mahaifin ta, domin ada yana iya magana sosai amma daga baya ya dena magana gaba ɗaya MEEMA ta sha kuka wanda hakan ya saka har sai da tayi jinya tsaban ruɗu da tashin hankalin da take ciki, tana ganin lokaci ɗaya Allah ya jarabbe su da matsaloli kala-kala har hakan yayi sanadin tafiyan mahaifiyar ta, ta kasa yarda mahaifiyar ta zata yi musu haka ita da mahaifin ta, duk rayuwar da suka gina tsawon shekaru amma lokaci ɗaya ta rushe musu, meyasa baza tayi haƙuri na ɗan lokaci Abee ya samu lafiya ba? Meyasa zata nuna gajiyawa da laluran Abee ɗin ta? Ashe dama ba son su take yi ba da har zata iya tsallake su tabar su a wannan duniyar? Haƙiƙa abin ya taɓa ta wanda lokaci ɗaya gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta sauya mata, wanda tana ji kamar gwara mutuwar ta da wannan rayuwar, sai lokaci ɗaya MEEMA ta sauya sabida ƙunci da raɗaɗin da Ummeen ta ta sanya mata, ga kuma uwa uba wanda tafi ƙauna yana kwance tamkar matacce, hakan na nufin ta rasa kowa nata kenan? Ada ita me son fara'a ce matuƙa, ga surutu kamar aku don idan ta soma zuba ba ta jin bari, shiyasa wannan halin nata sai ya zamana kowa nata ne, idan har ta zauna a wuri dole sai ka santa, mahaifin ta ya koya mata sangarta da shagwaɓa domin ita bata san bari ba, hakan yasa ta taso yarinya me kazar-kazar da son Wasa har girman ta, tana jin ta tamkar dai yarinya ƙarama ce, ga dolanci irin na ƴan fari kuma gata Auta. Ga kuma yanda iyayen ta suka ɓata ta da gata. Lokaci ɗaya sai kuma komi ya juya mata baya, ta dawo tamkar Miskila.. ba ta dariya bare murmushi kullum gani take yi rayuwar ta mafarki ne akwai ranan da zata farka shiyasa ko yaushe cikin tunani take da damuwa, idan ka ganta tana murmushi to tabbas tana gaban Abee ɗin ta ne domin saka shi farin ciki.        Shima da yaci gaba da samun kulawa domin tuni an kawo Nurse tana kula dashi ita take mishi komi, sai kuma likitan dake duba shi. a sannu a sannu ga shi har yana iya yin magana, shima daƙyar domin wani lokacin ba ya iya yi duk da yana son Yi Babu abinda ya fi komi saka MEEMA farin ciki illa ganin Mahaifin nata ya soma magana, hakan na nufin wata rana zai warke ya tashi kamar yanda yake a baya. Kuma za su ci gaba da rayuwar su ta farin ciki ko da babu Mahaifiyar ta a tare da su. Idan ta tuna hakan shi ne take jin salama a rayuwar ta Da farko ta dena zuwa school, sai da mahaifin ta ya soma samun sauƙi sannan ya matsa mata a kan, "ta koma". Yanzu haka tana degree ɗin ta ne a fannin Mas.Com. kuma tana zangon ƙarshe domin watanni ya rage mata. She's 26years all.          Abee shi ɗaya ne wajen mahaifiyar sa, asalin su ƴan Yola ne Fulanin can. Mahaifiyar shi ita ce ta farko wajen mahaifin su Alh. Ahmad Riskuwa. Matan sa biyu da Maman Faruk sunan ta Zulaiha da kuma Jammatu, amma suna kiran ta da Jamma Bayan Shekaru me tsawo da Zulaiha bata haihu ba sai iyayen Ahmad suka sanya shi ya ƙaro aure ya auri Jamma, ita kuma daga zuwan ta ta haifi Yaya Ali, bayan shi ta jima kafin ta sake haihuwa, inda ta sami cikin Zubairu Ashe itama Zulaiha tana da cikin amma babu wanda ya sani. Sai da Jamma ta haifi Zubairu kafin cikin Zulaiha ya bayyana. Aikuwa ta sha habaici wajen su Jamma da ƴan uwan Ahmad, sai dai bata biye musu ba tunda Allah ya bata nata ba juya bace ita kamar yanda suka ce ɗin Zubairu na da watanni huɗu aka haifi Faruk Zo ku ga murna wajen Ahmad domin ji yake yi kamar ba'a taɓa haihuwar masa ba sai yanzu, domin ƙaunar da yake yiwa Zulaiha ya wuce kwatance, shiyasa dangin shi suke jin haushin ta sosai, sai kuma suka sami dama wajen rashin haihuwar ta suka saka shi ya ƙaro aure.      Tun tasowan yaran Ahmad ya rigada ya bambanta su, domin ba ya iya ɓoye soyayyar shi ga Faruk. Wannan dalilin ne Jamma da yaran ta suka tsani Faruk sosai, ko kaɗan ba ya jin daɗin zama dasu illa wajen mahaifin sa da Mahaifiyar sa Ana haka Jamma ta soma biye-biye wajen bokaye domin ta raba Faruk da soyayyar mahaifin shi, inda kuma ta sanya wa Zulaiha ciwo lokaci ɗaya ta mutu Mutuwar nata shi ya jawo Ahmad ya samu ciwon zuciya, inda yayi jinya me tsayi kafin ya rasu.      Faruk ya taso cikin maraici da uƙuban rayuwa, wanda ya gummaci mutuwar sa da rayuwar sa. Sai dai Allah shi ne me rayawa shiyasa har ya kai girman sa. A lokacin da mahaifin sa ya rasu ya gama secondary School ɗin sa, koda ya mutu kuma an ƙi ba shi gadon shi bare yaci gaba da karatu, sai ya koma aikin ƙarfi tare da taimakon dangin mahaifiyar shi da suka rage mishi, a haka yake rayuwa yake samun abin saka wa a bakin sa, domin be da wani amfani a gidan su tunda har koran sa ma sun yi, sai daga baya ne da ƴan uwan Maman shi suka nema masa ƴancin sa shi ne suka bar shi yana kwana a zauren gidan Rayuwa taci gaba inda har su Yaya Ali suka gama karatun su suka sami aikin yi A lokacin ne Allah ya taimaki Faruk ya haɗu da wani uban gida me kuɗin gaske yana mishi gadi, tsawon lokacin da ya ɗauka yana mishi aiki wanda ya yaba da hankalin sa, sai ya ɗauke sa ya tafi dashi can Riyadh kasancewar a can matar sa da ɗiyar sa ɗaya suke zaune, a nan kuma Nigeria kasuwanci yake yi yana da Company, nan Faruk yake mishi gadi. Ya mayar dashi can ne sabida ya riƙa taimaka mishi a can tunda ya yaba da hankalin sa, ga kuma tausayi da yake ba shi domin ya san komi cikin rayuwar sa tunda ya taɓa tambayar shi, shiyasa ya yanke shawaran kai shi can Riyadh ya kula masa da dukiyar sa sannan kuma ya saka shi makaranta, tunda yayi alƙawarin sai ƴan uwan sa sun yi alfahari dashi, sai sun dawo suna dana-sanin koran sa da suka yi.       Wannan ne mafarin da yasa Faruk ya dawo Riyadh da zama har yayi karatu ya sami aikin yi, inda lokaci ɗaya Allah ya buɗa mishi yayi kudin kanshi, a lokacin har ya auri ɗiyar uban gidan nasa tunda soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai dai Allah be taɓa basu haihuwa ba shekara da shekaru     Shekara goma suna zaune da Abiha kafin Allah ya ɗauki ranta, inda ta rasu har lokacin bata taɓa ko da ɓarin wata bane, shi kuma Faruk yaƙi yin aure domin kawai farin cikin ta, yana ganin be kyauta ba muddin yayi mata kishiya saboda gudummawar da mahaifin ta ya ba shi a rayuwa, domin a lokacin ma Mahaifin nata tuni ya daɗe da rasuwa sai mahaifiyar ta, ita kuma ta koma can dangin ta har ta sake aure.         Mutuwar Abiha ya taɓa Faruk sosai, inda ya jima be sake aure ba, a lokacin ne ya yanke shawaran zuwa Nigeria neman ƴan uwan sa tunda ya rasa kowa nasa a nan, zuwan sa ya tarar da su ma su Yaya Ali sun sami ci gaba sosai, tunda duk kansu suna aiki da albashi me tsoka, inda suka rushe gidan su suka yi na zamani ko wanne da nashi part ɗin tare da matan su da yaran su Abubuwa da dama sun sauya mishi domin an yi rashi kala-kala, inda Jamma tuni ta daɗe da rasuwa itama, sai kuma wasu daga cikin dangin Maman shi na kusa.     Su Yaya Ali sun yi matuƙar mamakin ganin Faruk ya sauya yayi kuɗi sosai, domin ko hausan ma tuni ya ɓace a bakin sa sai ɗaiɗai. Sai hassada ya cika zuciyar su ganin ya fi su Sai dai shi be duba wannan ba illa alkhairin da yake ta musu. Duk yabi ya zagaye dangi ya gaishe su. Inda da ya tashi tafiya sai su Yaya Ali suka ce basu san zancen ba, wai, "a dole sai ya dawo Nigeria ya zauna da su". Shi kuma yace musu, "bazai iya ba tunda ya baro dukiyan sa da komi nashi a can," domin a lokacin har Company biyu ne dashi a can. Haka suna ji suna gani ya tafi ya bar su domin a tunanin su za su iya juya shi, sai dai yayi musu alƙawarin zai riƙa dawowa yana ganin su.      Allah da ikon sa a faɗi tashin nan da yake yi na ziryan zuwa Nigeria duba ƴan uwan sa sai suka ci karo da mahaifiyar MEEMA, sunan ta Zulaiha ƴar Kaduna ce. Inda lokaci ɗaya soyayyar ta ta shiga Abee kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar mata, duk da a lokacin yana da shekaru sosai ba kamar ita yarinya jagal ba, amma kuma kasancewar sa me kuɗi yana samun jin daɗi sai girman nasa ya ɓoye, tamkar yaro ɗan shekara 35.     Babu abinda ya ƙara faranta mishi rai jin sunan ta Zulaiha sunan mahaifiyar shi, shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata, inda suka yi soyayya na ɗan ƙanƙanin lokaci domin shi yace, "ba wasa ne ya kawo shi ba, Auren yake so da sauri".      An so ayi fitina sanda ya kai labarin wajen ƴan uwan sa, domin su a lokacin har sun yanke shawaran za su zaɓa mishi mata, sam suka ce, "basu yarda ya auri Zulaiha ba". Amma shi kuma yace, "atabam ita yake so". Dole ba don sun so ba suka bar shi ya aure ta.     An yi auren lafiya an gama lafiya inda ya ajiye ta a gidan sa na can Riyadh, kamar jira ake yi tana shiga ta samu cikin MEEMA, zo ku ga murna wajen Faruk, tun a ciki ya ɗauki son duniya ya ɗaurawa ɗiyar sa.            Bayan wasu watanni aka haifi MEEMA kyakykyawa ƙin kowa ƙin wanda ya rasa, sak mahaifin ta bafulanan usuli don basu da maraba, inda ya mayar mata da sunan mahaifiyar sa Zulaiha, sannan kuma sunan Ummeen ta itama. Shiyasa suke kiran ta da MEEMA tun tasowar ta, kuma da haka take amfani dashi a school wato *MEEMA FAROUK.*         Ta taso cikin gata sosai fiye da tunanin mutum, bata san babu ba ko hantara har sai sanda ta soma girma ta fara gane ƴan uwan Abee ɗin ta dake zuwa gidan sun takurawa iyayen ta, har ita kanta basu bari ba domin sun dinga dungure mata kai kenan, kuma duk idan sun zo sai sun saka iyayen ta kuka saboda baƙaƙen maganganun su, shiyasa tuni Abee ya dena zuwa Nigeria gaba ɗaya Inda akwai wani lokacin da suka yi faɗa baram-baram yace, "kar su sake zuwa mishi gida". Wannan dalilin ne yasa suka dena zuwa gaba ɗaya, sai dai idan suna neman kuɗi me yawa a wurin sa sai su zo dole sai ya basu. Idan ba kuɗi ba kuwa babu abinda ke kawo su. Da haka suka sami salama.      Duk da iyayen MEEMA ƴan Nigeria ne amma bata taɓa koyan Hausa ba, ba wai don sun ƙi koya mata bane, a'a sai dai don ba ya birge ta Yaren, bata damu ko kaɗan ta koya ba, kuma su ma basu cika yi ba tunda shi Abee har hausan ma ya ɓace a bakin sa sai kaɗan, idan kuma yana yi tamkar yana yare, ba kowa ke iya ganewa ba. Iyakan Turanci da Larabci suke yi.      Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin su.                      ✳️✳️✳️✳️✳️         Shigowar Nurse Zara ne ya sanya Abee ya buɗe idanun sa da suka kaɗa suka yi jazur Da sauri ta ƙarisa wajen sa tana mishi sannu Be iya amsa wa ba sai da ya ja lokaci kafin a hankali yace da ita cikin larabci, "ko zata iya ɗaukar MEEMA ta kaita ɗaki ba tare da ta tashi ba?" Dariya ma maganar taso bata, taya zata iya ɗaukar ganɗamemiyar budurwan da ta girme ta ta kai ta ɗaki kuma ba tare da ta tashi ba? Duk da dai ta fi ta jiki amma dai ta san MEEMA ta girme ta. Sai tayi saurin girgiza mishi kai itama ta mayar masa cikin harshen larabcin, "baza ta iya ba". Sai yace mata, "ta tafi". Haka ta fice tana rufo musu ɗakin.        Dole ya bar MEEMA a kan jikin sa taci gaba da barcin ta yana faman kallon kyakykyawar fuskar ta wanda ya kasance irin nasa sak. Murmushi ne tare da hawaye ya saki lokaci ɗaya. Babu abinda yake ƙauna sama da MEEMA a duniyar nan, ba don haka ba da tuni ya roƙi Allah ya ɗauki ransa saboda ƙuncin da ke cikin ransa, amma kuma tunawa da ita a rayuwar sa yana saka shi jin sanyi a ransa, wanda yake fatan samun lafiya nan gaba domin yaci gaba da rayuwa da ita a duniyar sa. Duk da ya san dole wata rana zata yi aure ta bar shi, kuma har a zuciyar sa yana son ganin kafin ya mutu ya danƙa ta wajen wanda zai zame mata jigo a rayuwar ta, ma'ana mijin ta, ba ya fata ya mutu ya bar ta hannun ƴan uwan sa, tun yanzu ma sun zo amsar ta wanda ya san duk saboda kuɗin sa ne, suna ga kamar zai mutu a yanzu shiyasa za su ɗauke ta don su mallaki komi nata. Ba ya fatan hakan ya faru dole ne yayi wani abu a kai, amma taya? Ta ina zai faro wajen samar mata abokin Rayuwa? Ta ina zai saka ta ta yarda tayi aure bayan tace, "muddin yana numfashi a duniya to babu ita babu aure a rayuwar ta! Baza ta taɓa tafiya ta bar shi ba har sai idan ya samu lafiya ne". A koda yaushe wannan kalaman nata take yawan sanar masa. Be san ta ina zai fara shawo kanta ta amince da ƙudirin sa ba.         Lumshe idanun sa kawai yayi yana haɗiyar wani yawu me ɗaci. [08/10, 2:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                    💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *SAKAMAKON SALLAH 1*           _Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas'ud ya ce, "Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?" Sai Annabi ya ce, "sallah". Na sake cewa, "daga ita fa?" Sai Annabi ya ce, "kyautata wa iyaye". Na sake cewa, "daga wannan fa?" Sai ya ce, "sai jihadi."_        _Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, "in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace," Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba'iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba'ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._           _Abu Sa'id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, "ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: "ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta." Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._         _Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._         _Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa'danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._ _Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha'i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha'in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha'i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, "ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku." Allah yasa mu dace duniya lahira._                     *NO_ 5 & 6*              Sanda MEEMA ta farka ta ganta jikin Abee ɗin ta sai ta ɗago kai tana kallon sa Idanun su ne ya haɗu da juna, ya sakar mata murmushi yana ce mata, "You woke-up?" Bata iya magana ba illa gyaɗa mishi kai da tayi Still murmushin ya sake Yi Yana lumshe ido tare da buɗe wa yace da ita, "Okay, go pray and eat. I know you haven't eaten yet." "Ok Abee". Tayi maganar tana sauka daga kan gadon, sai ta wuce ta shiga Toilet ɗin sa ta ɗauro alwala. Tana fito wa ta duba wardrobe ɗin sa ta cira Hijab, dayake akwai kayan ta a ciki tunda ko yaushe tana ɗakin sa, idan har ba karatu zata yi ba, to, bata cika zuwa ɗakin ta ba, ta fi son zama kusa dashi.           Har ta gama sallan yana kallon ta yana faman murmushi kaɗan Bayan ta gama dawowa tayi ta zauna gefen gadon tana riƙo hannun sa, "Abee, you are doing to pray?". Gyaɗa mata kai yayi makes her smile "Ok let me Call Nurse". Tayi maganar tana tashi ta fice.            A Parlour ta tarar da su zaune suna hira, sai ta kalle su fuska ba fara'a tace, "Abee will pray". "Ok". Cewar Nurse Zara tana tashi da sauri tayi ɗakin.              Direct MEEMA Kan dainning ta nufa, sosai take jin yunwa tunda rabon ta da abinci tun wanda suka ci ɗazu da Zamiya ta girka musu, shiyasa sai da ta cika cikin ta sosai kafin ta tashi tayi ɗakin Abee ɗin ta, sai da safe tayi masa sannan ta wuce nata ɗakin Ta san ko ta kwanta baza ta iya barci ba, shiyasa ta ɗauki school bag ɗin ta ta haye hill chair ɗin da take karatu a kai me haɗe da table, ta soma duba karatun da aka yi musu tana revision, bayan ta gama sai ta ɗauko assignment ɗin da aka basu tun last week, tamkar project ne suna bincike akai, taci gaba da binciken ta cikin ɗan ƙaramin Laptop ɗin ta tana yi tana rubutu. Sai 01:30am da taji barcin yazo mata kafin ta kwanta, babu daɗe wa kuwa ya sure ta cike da mafarkai kala-kala da ta saba yi ko yaushe.                 Washe gari zuwa ƙarfe 08:00am. Ta gama shirin ta, kamar yanda ta saba shigan ƙananan kaya sai ta ɗaura Abaya a kai me bottles a gaban, wannan karon Abayan brown color ne sai mayafin shi fari da Flower's kalan brown, flet shoes ta saka fari sannan ta ɗauki School bag ɗin ta ta rataya a kafaɗa ta fito, a hankali take sauka a kan Steps ɗin har ta dira ƙasa House girl ɗin su dake gyara parlor'n, ganin ta yasa ta dakata tana gaishe ta Kallo ɗaya tayi mata ta amsa a taƙaice tana shigewa ɗakin Abee ɗin ta Nurse Zara da fitowar ta kenan daga Toilet ta gaishe ta cike da fara'a Kamar kullum ta amsa mata a daƙile tana wuce wa kusa da mahaifin ta, ganin sa yana barci sai ta kalli Nurse Zaran tace, "He still hasn't woken up?" "Yes". Numfashi taja tana mayar da idanun ta kan shi While Nurse Zara ita kuma tayi ficewar ta Sai da ta shafa fuskar sa zuciyar ta na cike da damuwa, kafin kuma ta tashi ta fice, yau bata tsaya breakfast ba tayi ficewar ta, motan ta ta hau ta wuce school.               Lokacin da ta shiga class su Ummu Hani duk sun zo, yau har da Zamiya saboda jikin nata da sauƙi. Suna cikin gaisawa ne Malamin su ya shigo, sai suka nutsu suka mayar da hankalin su kan darasin da yake musu.               Sun sami break lokacin suna duba karatun su sai wayan MEEMA tayi ƙara, ɗauka tayi ta duba sai taga sunan Ishaq ne, tsaki taja ta ajiye tana ci gaba da duba book ɗin dake hannun ta Esha Sarkin shaƙiyanci dariya ta saki tana kallon ta tare da ɗage mata gira tace, "Is that Ishaq?" Ɗago kai MEEMA tayi tana hararan ta bata ce komi ba ta sake ɗauke kai daga kallon ta Sai tace, "Please go if he is, don't get tired of waiting for you, you know his condition is persistent". Sai duk suka saki dariya har Eshan da tayi maganar While MEEMA ta sake kicin-kicin da fuska still taƙi magana Sun san halin ta shiyasa suka yi gum da bakin su suka ci gaba da karatun su A lokacin ne kiran nashi ya sake shigo mata, bata sake bi ta kai ba har sanda yayi mata three Miss calls, ganin ya dame ta sai ta ɗauki wayan a daƙile tana amsa mishi sallaman nashi Sanar mata yayi, "he came outside where they used to meet". Sai ta tashi kawai ta fice Su kuma sai suka koma hira memakon karatun da suke yi, har wasu daga cikin mate ɗin nasu suka zauna cikin su ana yi da su.                   ********                  MEEMA da fitar ta Direct inda zata ganshi ta nufa, tana zuwa ta hange shi a cikin rumfar da yawancin ɗalibai suke zuwa su zauna don shaƙatawa, babban rumfa ne da kujeru a wajen da aka jera su gunun sha'awa da tables ɗin su Ƙarisawa tayi taja kujera ta zauna bayan tayi sallama a ciki-ciki Shi kuma tuni ya mayar da idon sa kanta yana faman doka mata murmushi tare da amsa mata sallaman yana cewa, "My Baby". Kallon sa tayi tana ɗan sakin fuska kaɗan tace, "how far?" "I'm not Fine Baby". Ɗan ɗage gira tayi tana kallon sa alamun tambaya Sai yayi murmushi kana yace, "Have a drinks before we start talking". Yayi maganar yana nuna mata drinks ɗin wajen "Laa. shukran". "Baby you can not drink?" Gyaɗa masa kai kawai tayi Sai yaja numfashi yace, "We should stop talking now. I want to send to your house to have a wedding day," Ƙura masa ido tayi har ya dira aya, sai ta fuske tare da kini-kini da fuska tace, "Ishaq now there is no word between us, I can tell you now I will not marry". "Why MEEMA? Why do you want to humiliate my life?" "No. I will not humiliate your life, I will not marry if Abee is in his condition, I will never marry until he is fine". "Ok, baby, I agree to marry you, so bring him to my home and take care of him." "No Ishaq". Sai ta tashi tsaye tana kallon shi tace, "please don't come out to me again, i will never get married now". Ta juya tayi wuceWar ta Yana kiran ta amma ko juyo wa bata yi ba.            Sanda ta koma class sai su Ummu Hani duk suka tambaye ta ganin ta dawo da wuri But bata ce komi ba ta zauna taci gaba da karatun ta Su ma ganin bata tanka su ba sai duk suka fita harkanta domin sun saba da halin ta yanzu, so hakan ba ya basu haushi tunda sun san ba haka take ba a baya.              Three O'Clock yau suka gama lectures, suka yi sallama da juna Esha said, "MEEMA dropped her off at home because she didn't bring her own car today." Shiyasa suka tafi tare, dayake duk wajen anguwan su ɗaya ne, sai da ta sauke ta kafin ta ƙarisa gida, tana sauka ta rufe motan ta taka tayi ciki a gajiye, tana shiga da sallama Me aikin su ta amsa mata tana mata sannu da zuwa Da kai ta amsa mata kafin ta wuce ɗakin Abee Shi kaɗai ne a ɗakin idanun shi a lumshe, sallaman ta ne yasa ya buɗe idon yana kallon ta da yalwataccen murmushi a kyakykyawar fuskar sa na asalin bafulatani, wadda ta ƙara zabge wa tayi siriri da ita tsaban zaman jinya "Abee". Tafaɗa sanda ta zauna a gefen gadon tana riƙo mishi hannu "Ummy". Shima ya faɗa still yana mata murmushi, sai kuma yace, "uridu an ata haddas". ("ina son muyi magana ne".) "Ok Abee, lakin jasadak sahl?" (amma jikin ka da sauƙi ko?") "Na'am Ummy alhmadulillah. Al'aàn karajal mahaàmil kassi biî wa natahaddasa ma'ahu". ("Yanzu Lauya na ya fita mun yi magana dashi".) "Abee maàzaà hadasa?" ("Me ya faru?") Sai da yaja numfashi daƙyar kafin yace, "Ummy, nothing, but now I have decided to return everything to you." "Why?" Tafaɗa da wani irin murya me kama da son kuka Murmushi yayi yace, "nothing Daughter. I am not comfortable with the arrival of my brothers. That is why I have made this decision. I want everything to return to your name so that you can own it or after my life is yours. I own everything for you." Kuka ta fashe da shi tana sake damƙe hannun shi, cikin kukan take cewa, "No Abee, You will be cured by God's will, nothing will happen to you ok?" Sai ta ɗaura kanta kuma a jikin shi taci gaba da kuka, domin ji take yi kamar wani abu ne zai sami Abee ɗin nata, don me zai mata irin wannan zancen? Me kuma yasa zai yanke wannan hukuncin? Shafa kanta yake yi cike da rarrashi yana ce mata, "enough". Daƙyar ya samu tayi shiru sannan yace mata, "She went to rest". Tashi tayi ta fita, kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta kwanta ta hau faman tunanin da ya zame mata jiki, ga shi yanzu lokaci na ta ƙure mata karatun su ya zo ƙarshe, amma kuma ba ta iya yin karatun sosai sabida hankalin ta ba a kwance yake ba. Lumshe idanuwan ta tayi hawayen ciki na sake zubo mata a kunci, ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallah, sannan ta wuce downstairs ta zauna a kan dainning ta soma cin abinci, gaba ɗaya a tunani ta gama yi kafin ta wuce ta koma ɗakin Abee ɗin ta Lokacin yayi barci Sai ta haye kan gadon ta kwanta a gefen shi tana ta faman kallon shi, babu abinda ke dawo mata sai rayuwar su na baya sanda suke tsananin farin ciki, amma ƙaddara ta zo ta ɗauke musu wannan jin daɗin, sanadiyar haka Ummeen ta ta tafi ta bar su, bata san har yaushe za su kasance a haka ba, duk da ta yarda da ƙaddara kuma ta san komi zai wuce, komi zai koma musu dai-dai kamar baya, tana fatan hakan a koda yaushe, shi ne burin ta Mahaifin ta ya samu lafiya hakan ne kaɗai zai dawo da daidaiton walwala a tsakanin su Idanun ta ta rufe da suke tsiyayar da hawaye wanda ko kaɗan ba sa gajiya, tana jin zuciyar ta na sake ƙunci a duk sakonnin da zata tuna da mahaifiyar ta.              Ta jima a haka kafin ta buɗe rinannun idanuwan ta a kan fuskar Abee ɗin ta, kallon sa kawai take yi kamar wanda bata taɓa ganin sa ba, ko kaɗan ta kasa ƙifta idanu a kan sa, Every second his sympathy deepened into her heart, numfashi taja kafin ta kai fuskar ta dai-dai nasa she kissed him on the forehead and then pressed him to his lips, sannan ta tashi ta fito. Direct waje ta nufa, a hankali take taka wa hannayen ta soke a ɗan guntun jeans trouser ɗin da ta sanya, while fuskar ta babu alamun walwala a cikin ta, gaba ɗaya damuwa ne ya sake mamaye ɗan kyakykyawar cuty face ɗin nata, duk da hakan be hana fito da zallan kyawun ta ba, domin ta kasance kyakykyawa ce MEEMA, bata da bambanci da mahaifin ta sak shi, a kallon farko idan kayi mata zaka tantance ita ɗin asalin bafulatana ce domin zaka yi tunanin ma tana jin yaren, nan kuwa bata iya komi ba a ciki, daga turanci sai larabci shi ne abinda ta iya, sai kuma kaɗan-kaɗan tana jin yaren talegu kasancewar Zamiya na koya musu, asalin ta ƴar India ce ta zo nan Riyadh karatu shi ne take zaune a Hostel.            Babu inda ta tsaya sai wajen swimming pool ɗin da ke mamaye a bayan gidan, wanda yake cikin ɗan ƙaramin garden me ban sha'awa da birge wa, Everything is green and very beautiful. Tana tsaye ta kafe idanunta waje ɗaya hannayen ta a ƙirji, sosai ta faɗa duniyar tunani, tunanin da ta saba a koda yaushe, bata san cewa hawaye na tsiyaya a kuncin ta ba har sanda taji muryan ƴar aikin su kusa da ita, sai tayi firgigit ta dawo cikin hayyacin ta tana juyo da kallon ta gare ta "Afwan ya Sayyadaty! Anti gariîb fiî intizaàraki". "(Kiyi haƙuri Madam! Kin yi baƙo yana jiran ki)". Gyaɗa mata kai kawai tayi Ita kuma ta tafi Numfashi ta ja tana saka bayan hannun ta ta share hawayen fuskar ta kafin ta taka tabi bayan ta a hankali cikin tafiyan ta na salo. [08/10, 2:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                    💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*              *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                    *NO_7&8*                 Da shigan ta cikin parlour'n su ta sauke idanun ta a kan Ishaq dake zaune yana shan drink a cikin Glass Cup. Da kallon mamaki kawai take bin sa tana tako wa a hankali Shi kuma ganin ta yasa ya ajiye Cup ɗin saman Centre table yana me miƙe wa tsaye tare da yalwata fuskar sa da murmushi, ƙyam ya ajiye idanun sa a kanta ya kasa ɗauke wa illa bin ta da yake yi da wani irin kallo me wuyan fassara Ita kuma ganin haka yasa ta sake tamke fuskar ta bayan ta ƙariso wajen sa idanun ta a kan sa tace, "What are you going to do in our house? What brought you here? " Sai da yayi murmushi yana shafa suman kansa kafin yace, "Oh Baby, you know there is no way I can get rid of you so easily. Please, I have come to talk to you." Naman goshin ta ta tattare waje ɗaya tana me runtse idanu, sai kuma ta ware su a kansa murya a hassale tace, "What do you want from me?" "I want to get married MEEMA, I love you so much I can't divorce you. Please accept my request. I may die if I don't marry you." Sai kuma ya duƙa ya saka gwiwowin sa a ƙasa tare da haɗe hannayen sa waje ɗaya yace, "please help Me MEEMA I can't live without you, I love you so much! I may lose my life for you". Sosai a wannan karon ta fusata da kalaman sa, meyasa ba ya gane wa ne yake son takura mata a rayuwa? Lokaci ɗaya ta daka masa tsawa da faɗin, "I also do not love you Ishaq, go out in my life and leave my life alone, I will never marry you and then leave this house Now". Ta ƙare maganar da nuna masa hanya, "I say Out". Tashi yayi tsaye yana bin ta da kallo, har gaban ta ya tako still idanun sa a kanta. Kallon kallo kawai suke yi ido cikin ido na tsawon daƙiƙu ba tare da ko wannen su ya ɗauke ba, sai ya ci je leɓe yana me ɗauke kansa a kanta ya sauke a ƙasa, hannun sa ya saka na dama ya sosa goshin sa kafin ya sake duban ta kana kuma ya taka ya bar parlour'n Har ya fice tana tsaye a wajen ta kasa motsin kirki, zuciyar ta sosai take tafarfasa wanda ita kanta bata san dalili ba, sai kawai ta juya tayi kan Steps da gudun ta ta shige ɗakin ta tare da faɗa wa kan gadon ta, wani irin kuka me tsuma rai ta saki wanda har jijjiga gadon take yi tsaban kuka, da hannun ta take tattaro zanin gadon tana yamutsa wa still tana ci gaba da kukan ta me tsuma rai wanda ke fito wa daga can ƙasan zuciyan ta. Sai da ta ɗauki like two minutes kafin ta shanye kukan a lokaci ɗaya tana me tashi zaune, hannayen ta ta saka ta soma share hawayen duk da wasu suna sake kwaranyowa, "I will not cry again. From today on, I promise. From today on I will remove you from my life Ishaq. I will never marry." Sai kuma ta sake fashe wa da wani sabon kukan, cikin kukan take cewa, "I love You Ishaq, i really Love you, you are the only one i ever wanted you are still in my soul, i will never forget you, i love you, i hope one day we will get married, I'm sorry ok?" Sai ta lumshe idanun ta tana me jan numfarfashi, a haka har ta kafar da hawayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka yi jazur suka kumbura, tashi tayi ta wuce Toilet ta wanke fuskar kafin ta fito ta zauna a kan table ɗin karatun ta, School Bag ɗin ta dake saman table ɗin ta janyo tare da buɗe wa ta zaro Text book ta soma karatu, duk da zuciyar ta babu daɗi amma haka ta daure tana ta karatun domin sama ma kanta nutsuwa, ta san idan ta biye wa damuwar ta zata iya rasa chance ɗin ta, dole ne a wannan gaɓar ta mayar da hankalin ta a kan karatun ta.            Shiyasa tun daga ranan ta hana zuciyar ta sukuni bare ta bata damar yin wani tunani me zurfi, kullum tana cikin karatu ko da tana wajen Abee ɗin ta ne da books ɗin ta take zuwa, bata da lokacin kanta a yanzu saboda ganin time ɗin exams ɗin su ya gabato, idan tayi wasa zata iya Field.             Da sannu da sannu ga shi har time yayi sun soma zana jarabawan su, wanda shi ne na ƙarshe sun haɗa degree ɗin su a fannin Mascom.                Gefe ɗaya kuma bata sake ganin Ishaq ya zo wurin ta ba, ko me kama da shi bata sake gani ba, duk da a wani ɓangare na zuciyar ta tana matuƙar kewan sa amma babu yanda zata yi, hakan ma ya fi mata shi zai bata daman nutsuwa ta manta komi, duk da ta san da cewa cire soyayyar sa a zuciyarta gaba ɗaya ba ƙaramin jan aiki bane a gare ta, ada sun so juna matuƙa ita da shi wanda basu yi tunanin ƙaddara zata zo ta raba su ba, First love yana da matuƙar wahala a zuciyar ɗan Adam, haka MEEMA take ji a yanzu, sai dai ƙauna da tausayin Mahaifin ta ya sa ta jure duk wani baƙin ciki da ƙuncin dake zuciyar ta, ta rabu da shi a kan rayuwa da mahaifin ta na har abada, wannan hukuncin ta yanke shi ne ba tare da tunanin me zai je ya dawo ba.               Alhmadulillah komi aka ce yana da farko kuma yana da ƙarshe, kamar yau ne su MEEMA suka soma zana jarabawan su sai ga shi har sun kammala. Inda makarantan tasu ta shirya musu gagarumin waliman yaye ɗalibai Sun shirya taron ne a ranan Saturday, inda aka gayyato manya-manyan ƙusoshi na ƙasar Riyadh ɗin, kama daga kan ƴan siyasa da masu kuɗi har da ƴan maƙotan ƙasan duk sun hallara, wanda dama an saba yin babban taron nan a duk shekara.            Mahaifin MEEMA na gaban talabijin kamar yanda ya buƙata a kunna masa don ganin taron waliman ɗiyar sa mafi soyuwa a birnin zuciyar sa.            Bazan iya misalta muku tsantsan kyawun da MEEMA tayi a wannan lokacin ba, duk da ko kaɗan fuskar ta babu walwala bare kwalliya, but tayi kyau sosai kasancewar ta me kwarjini ga duk wanda ya kalle ta, kyawun ta shi ke hana a gane tayi murmushi ko bata yi ba, domin ko ya tayi a hakan kyau take ma Mutane, tana zaune ne a sahun gaba-gaba kasancewar tana ɗaya daga cikin manya-manyan Ɗalibai, tayi shiga irin na larabawa babu abun da ake gani nata sai kyakykyawar fuskarta da tafukan hannayen ta. Inda a lokacin aka sanar ana buƙatar *MEEMA FAROUK* ta fito tayi jawabin buɗe taro. A cikin sanyin ta da tafiyan ta me matuƙar birge wa wanda kamar ba taka ƙasan take yi ba ta isa ga mumbarin tare da amsan speakern ta soma buɗe taro da addu'a cikin harshen larabci, wanda tsaban ƙwarewan ta da iya Yaren zaka yi tunanin ita ɗin asalin Balarabiya ce. Bayan ta ida addu'an ne ta juya harshe zuwa Turanci domin kowa ya ji, kasancewar ba kowa ne ke iya jin larabcin ba, godiya da ban girma tayi ma malaman makarantan tare da baƙin wajen, kana ta koma ta zauna While mutanen wajen sai tafi suke mata.             Daga nan aka soma gudanar da abubuwan da ya tara su har zuwa kan kyaututtuka da ɗalibai haziƙai suka samu. MEEMA na ɗaya daga cikin waɗanda suke amsar kyaututtuka masu yawan gaske, kowa sai jinjina mata yake yi sabida yanda aka nuna hazaƙan ta Yayinda Abee na kwance a ɗakin sa yana kallon komi yana hawaye, da ace lafiyan sa lau da ya fi kowa nuna murnan sa ga ɗiyan sa a wannan ranan, tabbas da a yanzu ya kasance a wurin tare da ɗiyar sa yana Alfaharin kasancewan sa uba a wajen ta, sai dai babu hali, but duk da haka babu wanda ya kai sa murna ɗin, tsaban murna har kuka yayi Itama tana can tana share nata hawayen tuna mahaifin ta da tayi, tabbas da yanzu yana tare da ita suna farin ciki tare, tuna hakan ne ya saka ta zubar da hawaye, ko babu komi tana matuƙar kewan mahaifin ta a irin wannan yanayin, ta tuna sanda ta gama secondary School ɗin ta irin farin cikin da ya nuna sakamakon kasancewar ta gwarzuwa a shekaran, Allah ya yi MEEMA me ƙaunar karatu ne sosai shiyasa zai yi wuya ace ba ita ce ta wuce ko wani ɗalibi a class ɗin su ba, idan kuwa bata zo na farko ba dole a na biyu zata zo. Ta tuna sanda ta gama karatun ta before ta ɗaura Degree ɗin ta, irin Big partyn da ya shirya mata da irin celebrate ɗin da suka yi, amma kuma wannan karon babu ko ɗaya, babu damar da zai shirya mata partyn da zai kasance abinda baza ta taɓa manta wa da shi ba.            Lumshe idanuwan ta kawai tayi a sanda ta kawo nan a tunanin ta, yayinda hawayen ciki suka zubo a saman dandamalin fuskar ta Su Esha suka rungume ta suna me taya ta kukan kasancewar sun san lokacin rabuwan su ne yayi, duk da suna gari ɗaya amma kuma rayuwan school daban ne, Zamiya ce kaɗai ta fi shiga tashin hankali tunda ita tazaran su da yawa, sake haɗuwan su zai yi wuya, shiyasa take kuka sosai Yayinda suka haɗu suka rungume ta suna me sake fashe wa da wani sabon kukan.               Sanda za su rabu kamar kar su rabu, amma babu hali haka kowa ya wuce tare da ƴan uwan sa, while MEEMA ita kaɗai ta nufi gida, a lokacin kuka sosai take yi tunawa da Ummeen ta da kuma Abee ɗin ta dake kwance a can gida babu halin fito wa. Bata iya fitowa a motan ba sanda tayi parcking a cikin haraban gidan, sai ta kifa kanta a saman sitiyarin ɗin tana ci gaba da tsiyayar da hawaye, ta jima a haka ko motsi ta gaza yi before ta ɗago fuskar ta da yayi jawur idanun suka sake kumbura, handkerchief ta saka ta share fuskar tare da daidaita ta kafin ta buɗe motan ta fito hannun ta rike da wayan ta da keey ɗin mota kaɗai domin baza ta iya ɗauko kyaututtukan ba dole ta bar su a cikin mota tayi cikin gidan.               Babu kowa a parlour'n sai ta wuce kanta tsaye ɗakin Abee Yana kwance kamar ko yaushe, sai dai yanzu an rigada an kashe masa t.v'n idanun sa a lumshe suke. Muryan ta da ya ji yasa ya buɗe idanun yana sauke wa a kanta, yalwataccen murmushi ya sakar mata yana mata alama da ido a kan, "tazo gare shi". Da sauri ta iso tana me duƙa wa a gaban gadon tare da sanya hannayen ta biyu ta riƙo nashi duka, da raunanniyar fuska take kallon shi kamar wacce zata saki kuka Sai ya janye hannun sa ɗaya ya shafa kanta still Yana murmushi yace, "Alfu mabruùkin ya Ummy, Baárakil lahu fií hayaátiki, jazaákumul lahu aksara min zaliki watamjudniy". ("ina taya ki murna Ummy, Allah yayi ma rayuwar ki albarka, Allah yasa ki fi haka ya ɗaukaka min ke".) "Amin Abee". Tafaɗa tana me kwantar da kanta saman ƙirjin sa zuciyar ta na farin cikin addu'ar da yayi mata wanda har sai da hawaye suka watso a saman kuncin ta Shafa kanta kawai yake yi yana murmushi ba tare da ya sake cewa komi ba. Sun ɗau lokaci a haka kafin ya kira sunan ta, "Ummy". "Na'am Abee". Ta amsa mishi ba tare da ta ɗago ba "Al'aán ba'ada an tahaƙƙaƙu hilmaki fiì tusbiha suhfiìyan, kana haáza hilmaki daá'iman, al'aàn ba'adi inyihaá'i baƙiìyatiz zawaáj, uriduki an tatazauji hatta yahda'a ƙalbiì fiì kulli marrati azhaba fiìhaá ilal firaásh, uriduki an tahdira khaɗììbaki watatawaƙƙafu anil tahaddas ila waálidihi". ("Yanzu burin ki ya cika kin zama Ƴar jarida, mafarkin ki kenan a koda yaushe. Yanzu saura aure ya rage zaki yi, ina son inga kin Yi aure domin zuciya ta zata fi kwanciya a duk sanda na tafi na barki, ina son ki fito da wanda zaki aura mu tsayar da magana da iyayen shi".) Saurin ɗago da kai tayi tana kallon sa, nan da nan hawayen ta suka ci gaba da kwaranya, cikin amon muryan ta dake fita da rawa tace, "Laá Abee, la astaɗiìu an atazauja wa'azhaba wa'aƙuùla wadaá'an, laá yumkinuniìl zahaábu li'aƙuùla wadaá'an fiì haálatil mardi haázihi, laƙad saámahtu zawaáji Abee, lan atazauja hatta tatahassana". ("A'a Abee. Bazan aure in tafi in barka ba, bazan iya tafiya in barka a wannan halin na rashin lafiya ba, na yafe aure Abee, bazan yi aure ba har sai sanda ka samu lafiya".) Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana me riƙo hannun sa sosai tace, "Abee Ummee... She's going.. and..." harshen ta kawai ke motsi ta gaza furta abin da take son furta wa saboda yanda wani abu me ƙunci ya tokare mata maƙogwaro Shima Abee tuni ya soma zubar da hawaye, ya saka hannu ya kwantar mata da kanta a saman jikin sa yana rarrashin ta, "Aásifa". Kawai yake iya furta wa shima a laɓɓan sa zuciyar sa na masa ƙuna, shi kaɗai ya san me yake ji a wannan lokacin daure wa kawai yake yi A haka suka kasance har barci ya ɗauki MEEMA a wurin Numfashi yaja yana me lumshe idanuwan sa, jikin sa rawa yake masa ga azaban zafi da yake ji, gaba ɗaya yau ba ya jin daɗin jikin sa, daure wa kawai yake yi saboda yau ranan murna ce ga Ɗiyar sa, ba ya son ko kaɗan ya ya ɓata mata wannan ranan me muhimmanci.             Nurse Zara ce ta shigo tace masa, "time to take his medicine". Haka ta ba shi maganin ta fice Dayake akwai na barci sai ya samu barcin ya sure sa.            Sanda MEEMA ta farka ana kiran magriba ne, ganin Abee na barci sai ta miƙe ta wuce ɗakin ta, sallah ta gabatar kafin tayi wanka ta shirya cikin kayan barcin ta, riga da wando masu ruwan Powder and dressed less, ta sauko ƙasa ta zauna a kan dainning, sosai take jin yunwa shiyasa taci abincin da yawa, ta miƙe ta nufi ɗakin Abee Har a lokacin be tashi ba domin a time ɗin jikin sa ya yi zafi zau, shiyasa Nurse Zara take gasa mishi jikin a time ɗin domin ta shafa masa magani Da kallo MEEMA take bin ta dashi tana sake tamke fuska, ko sannun da tayi mata bata amsa ba sai ta jeho mata tambayar, "He hasn't gotten up yet?" "Yes, he don't get up". Tsaya wa tayi kawai a wurin tana naɗe hannayen ta a ƙirji ta kafe su da idanu, bata jirga a wajen ba har sanda Nurse Zara ta gama duk abinda zata yi masa kafin ta fice, sai ta taka a hankali ta isa bakin gadon ta zauna, hannu tasa a hankali ta kamo nashi tana tamke wa a cikin nata, shiru tayi tana bin sa da kallo zuciyar ta a raunane, sai kuma ta matsa setting kanshi ta saka hannu tana shafa mishi gashin kanshi, nan taji kamar da zafi jikin sa, taɓa wuyan sa tayi taji da ɗumi sosai, lokaci ɗaya ta lumshe idanu hawaye na saukar mata a fuska, sai ta buɗe tana bin shi da kallo tana tamke bakin ta don hana bayyanuwar kukan da ya taho mata. Kanta ta ɗaura a ƙirjin sa ta ƙanƙame shi. A haka ta kwana a jikin sa ko runtsa wa bata iya yi ba Ko sanda Nurse Zara ta dawo duba sa a cikin daren, ganin ta yasa ta koma taje tayi barcin ta tunda ta san tana tare da shi.              Sai asuba MEEMA ta tashi ta koma ɗakin ta, lokacin barci sosai ne a idanun ta sakamakon kwana da tayi bata runtsa ba, sallah tayi ta nema wa Abee ɗin ta sauƙi a wurin Allah, kafin ta haye kan gado barci ya sure ta.                Sai 12:30pm. Ta farka, da mafarkin mahaifin ta ta tashi shiyasa duk jikin ta ya mutu, bata iya taɓuka komi ba ta fito ta sauka ƙasa don duba lafiyan sa, tana shirin shiga Likitan sa dake zuwa duba sa ya fito daga ɗakin, hakan yasa gaban ta ya faɗi ta nufe sa da sauri kamar zata faɗa kansa idanun ta ware a kansa tace, "Doctor what's happened?". [08/10, 2:54 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                    💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*               *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                  *NO_9 & 10*                Sai da ya gyara wa eyeglasses ɗin sa zama kafin yace, "calm down please let me explain". "No Doctor what happened to my Dad?" She asked him again with a smirk Numfashi ya ja kafin yace, "Your father is very sick. We have to take him to the hospital because he needs to be examined. He needs special care." Hawaye ne kawai ke zirya a kan fuskar ta ta gaza ma magana Hannu yasa a kafaɗan ta yace, "Calm down MEEMA insha Allahu he will get up he will be fine". Idanun ta kawai ta lumshe still hawayen ciki na tsiyaya, sai kuma ta buɗe su tana shirin wuce sa ta shiga ɗakin Sai ya tsayar da ita yana faɗin, "No, don't come in, let's get an ambulance now and we'll pass, Sorry ok?" Bata bi ta kanshi ba ta buɗe ƙofan ta shige, wajen Abee ɗin ta da idanun sa ke rufe yana fitar da numfashi daƙyar ta nufa, Kasancewar doctor yayi masa alluran barci sabida a samu a kai shi Hospital ba tare da wani problem ba. A hankali ta zame a wajen tana riƙo hannayen sa, cikin kuka daƙyar ta kirayi sunan sa, sai dai ta kasa yin maganar dole tayi shiru tana danne bakin ta, ɗaura kanta tayi a cikin sa tana ta shashsheƙan kuka.               A haka aka zo da ambulance aka ɗauke shi suka wuce Hospital ɗin Gaba ɗaya MEEMA ta gaza nutsuwa sai kuka take yi, duk rarrashin da Doctorn yayi mata kafin su shiga duba Abee amma ina taƙi yin shiru, haka ma Nurse Zara tana tare da ita tana faman rarrashin ta amma ina taƙi shiru, dole ta tafi ta barta a wajen tana ta sintiri duk ta gaza zama, gaba ɗaya idanuwan ta sun yi jawur sun kumbura suntum, kallo ɗaya zaka yi mata ka gane tana a cikin tashin hankali domin hakan ya gaza ɓoyuwa a kyakkyawar fuskar ta Daga baya ne House Girl ɗin su ta zo shi ne suka zauna tare har sanda Doctorn Abee ya fito Da gudu ta isa wurin sa tana kuka tana tambayar shi jikin Abee ɗin Cike da tausayin ta yace, "I'm so sorry MEEMA: Just be patient. As your father is in a difficult situation, we will have to wait and see what the situation will be like." Jiri ne ya kusa kwasar ta sai house Girl ɗin su tayi saurin tare ta ta faɗa jikin ta, kuka sosai take yi tana son tsaya wa da ƙafafuwan ta amma ina ta gaza, dole sai da taimakon House Girl ɗin su dake riƙe da ita ta iya tsayuwa. Cikin kukan take cewa, "Doctor help my father please, I love him I don't want to lose him, please help me don't let him go". Break the words and burst into tears Rarrashin ta kawai yake yi yana bata baki, dole yace wa House Girl ɗin, "she holds her and passes her to his office". Haka suka wuce can ta samu ta zauna Nan yace mata, "Now they put oxygen on him and he is asleep, or later she will check on him. But she calms down and nothing will happen. He will be fine soon." Har ya fice bata iya magana ba, a haka suka zauna a Office ɗin har zuwa yamma babu abinda ke tayar da su sai sallah, gaba ɗaya ita MEEMA ta gaza saka komi a cikin ta illa kai kukan ta wurin Allah da take yi, after dress ɗin ma da ta sanya a jikin ta take sallan House Girl ta koma ta ɗauko mata a gida, don daga ita sai kayan barci ta zo, kuma duk rarrashin da tayi mata taci wani abu ta ƙi magana bare ta kalle ta, duk tayi wani zuru-zuru da ita fargaba da tashin hankali yasa ta fita hayyacin ta, mahaifin ta kawai take burin ta gani yanzu.              Sai bayan magriba ya farka likitan ya zo ya sanar mata don ta je ta duba sa Shima Abee ɗin tunda ya farka ya nemi a kira ta Da gudu tabi bayan Nurse Zara da tayi mata jagora zuwa ɗakin da Abee yake ciki. Tana shiga ta ƙarisa wurin sa da sauri tana me kiran sunan sa a lokaci ɗaya hawaye na kwaranya mata, Abee.." ta sake faɗi bakin ta na rawa Idanun sa ya sauke a kanta yana mata murmushi Hannu tasa ta riƙe nashi tana me sake kiran sunan sa da cewa, "Abee, please recover. Abee I need you in my life. I love you so much. I don't want you to leave me. Please get up." Daƙyar ya iya furta, "Ummy sickness and death all belong to God, I have no power to continue living except the one God has chosen for me". Sai ya tsakaita kafin ya sake sakin murmushi zuciyar sa na ƙuna da ganin tana hawaye be da yanda zai yi ya share mata. Ya fito ta yayi alamun ta matso Da sauri ta matso sosai tana me ɗaura kanta a jikin sa A hankali ya soma raɗa mata magana cike da rauni wanda daƙyar yake furta kalaman Ita kuma sai zubar da hawaye take yi har sanda ta kasa jure wa da kalaman nasa ta hau girgiza masa kai tana cewa, "laà Abee I can't.." abinda take iya furta wa kenan tana kuka sosai Shi kuma lumshe idanun sa yayi while hawaye masu zafi suna sauko masa a kunci. Yana riƙe da hannun ta gam ya ƙi saki Ita kuma sai kuka take faman yi Sai da Nurse Zara ta shigo ta janye ta kafin ta samu ta fita tana me sake ɓarke wa da wani sabon kukan, a jikin ƙofan ta zame tana kuka sosai duk fuskar ta ta sharɓe da hawaye tayi jazur Me aikin su da Nurse Zara suka kama ta suka mayar da ita Office ɗin Doctor.               Daga ranan kullum a cikin ƙunci da kuka take kwana, a kan sallaya take wuni tana sallah da roƙon Allah ya warkar da Abee ɗin ta, ko abinci ta dena ci sai an yi da gaske, a kuma asibitin take kwana ko jirga wa ba ta yi, kuma tun daga ranan ba'a sake barin ta ta duba Abee ba sabida ganin tana ɗaga hankalin ta, ga shi ciwon nasa yanzu yayi tsanani sosai.            Five days after his arrival, he died at the hospital. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un bazan iya misalta muku tashin hankalin da MEEMA ta shiga ba, gau ta sume bata sake sanin inda take ba har sai da aka yi kwana uku da jana'izar shi, a ranan da ta farka ƙaramin hauka tayi musu a kan, "sai sun dawo mata da mahaifin ta," duk ta fita hayyacin ta tamkar mahaukaciya, da farko sun yi tunanin ta haukace ne ashe zafin rabuwa da mahaifin ta ne ya janyo mata rasa tunanin ta gaba ɗaya, sai da aka koma ɗaura ta a kan magani don abubuwan da take yi bata da maraba da mahaukata. Da ban baki da nasiha tare da treating ɗin ta har aka samu ta soma samun sauƙi Likitan mahaifin ta shi ya ɗau ragamar komai na jana'izar Abee har aka yi aka gama lafiya, kuma ya samu mutane ba kaɗan ba sabida babban masallaci na garin Riyadh ɗin aka kai shi aka yi masa Sallah.                Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwan sa kafin aka sallami MEEMA. House girl ɗin su ita ke kula da ita domin tsananin tausayi take bata, ita take ta ɗawainiya da ita a asibitin har suka koma gida, a lokacin sam baza kace MEEMA bace sabida yanda ta sake rame wa tayi fari fat tamkar mara jini a jiki. Ko magana ba ta iya yi kullum sai zubar da hawaye, ta kasa yarda cewa Mahaifin ta ya rasu ya bar ta, har ji take yi a wannan lokacin gwara mutuwar ta da rayuwar ta, ta gummaci ta bi shi a irin wannan Rayuwar, a yanzu tana buƙatar mutuwar ta fiye da rayuwa, ta rasa komi nata, bata da kowa sai ita kaɗai, taya zata iya rayuwa a haka? Komi nata na farin ciki ya wargaje ya barta. Mutuwa shi ne ya fi cancanta a gare ta.               Amma a haka babu gajiya house Girl ɗin ta take bata kulawa. Ita take lallaɓa ta ta samu ta ci abinci, sai ta kwana ta wuni daga ruwa sai ruwa take zuba wa a bakin ta, idan kuma ta matsa mata da cin abinci har marin ta take yi ta daka mata tsawa ta kore ta, amma kuma haka anjima zata sake kawo mata, da haka har ta soma shawo kanta wani lokacin ta ɗan kalle ta taci abincin, wani lokacin kuma idan ta birkice tayi ta zagin ta tana daka mata tsawa a kan, "ta tafi ta barta ko ta kashe ta, tana damun rayuwar ta," duk waɗannan abubuwan haka house Girl ɗin take iya ƙoƙarin ta wajen jure wa.                Da haka kwanaki suka soma shuɗewa haka ma satikai, ga shi yanzu har an yi sati Uku curr da rasuwar Abee.                   A wannan lokacin ne Ishaq ya zo gidan yin mata ta'aziyya, domin sai a lokacin yake jin labarin kasancewar ba ya ƙasar Sanda ya shigo gidan da House girl yaci karo, ita tayi masa jagora har cikin ɗakin MEEMA kamar yanda ya ɓukata yana son ganin ta.               MEEMA na kwance a saman faffaɗan gadon ta while ta tusa kanta a ƙasan pilow. Daga ita sai ƙaramar vest fara da leggings da iyakan sa gwiwowin ta shima fari Ishaq da ya ƙariso ciki a hankali ya isa bakin gadon ya samu wuri ya zauna yana ƙure ta da kallo, shiru yayi na ɗan wani lokaci sai kallon ta yake yi kafin ya sanya hannu a bayan ta yana shafa ta tare da kiran sunan ta Jin muryan sa tamkar a mafarki ya sanya ta ciro kanta da sauri tana ware manyan idanuwan ta da suka sake girma suka yi jawur sabida kukan da take wuni yi ko da yaushe. Kallon sa kawai take yi ba tare da ta iya furta komi ba daga bakin ta Shi kuma sai ya sakar mata murmushi tare da mamakin sauyawan ta lokaci ɗaya haka, ya san tsananin ƙaunar ta da mahaifin ta dole zata shiga wani yanayi da rashin sa, shiyasa ya ji tausayin ta ya tsarga masa zuciya a lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me sake buɗe su a kanta tare da kiran sunan ta Shiru tayi masa sai dai ta kasa ɗauke idanun ta a kansa Hakan yasa yaci gaba da faɗin, "MEEMA sorry with the temptations that God has bound for you, or what life is mortal everyone will leave this world, I offer you my condolences for the loss of your father, may God have mercy on him and forgive him, I left that's why I did not come early I'm sorry". Take ta mayar da idanuwan nata ta rufe su ruf hawaye na wanke mata fuska. Sai ta sanya tafukan hannayen ta ta rufe fuskar ta tana me fashe wa da wani sabon kuka wanda dama shi take jin yi amma ya gaza fito wa, but yanzu jin ana mata ta'aziyya sai kawai zuciyar ta tayi rauni sosai wanda hakan yasa kukan nata fito wa Ishaq hankalin sa ya tashi sosai ganin kukan da take yi sosai, da sauri ya sanya hannayen sa ya cire nata daga fuskar ta yana bata haƙuri Ita kuma idanun ta a rufe suke ruf ta kasa buɗe wa sai kuka take yi Duk rarrashin ta da ya so yi ya kasa, dole ya zuba mata idanu har tayi ta gaji don kanta tayi shiru ta koma shashsheƙan kuka. Sai ya saki ajiyan numfashi yana cewa, "be patient MEEMA so your destiny has come, Abee needs nothing from you but your prayers, please refrain from him and pray for him with the hope of being right with the ya Rabbi". Sai a lokacin ta buɗe idanuwan nata tana kallon sa da jinjina masa kai tana me ƙumshe bakin ta don hana kukan nata fita Shiru ne ya gifta na ɗan wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "Although I know you are now in a state of ecstasy and happiness, and I know my words will upset you but I have to do it, MEEMA a second time I beg you to agree to marry me, I desperately need you in my life, I know Abee's problem is why you abandoned my love but now I'm back I need your answer, I really love you MEEMA, I can't live without you, Abee is gone and you need me in your life, you can't live alone no marriage, think about it". Har ya dire maganar sa bata ɗago ta kalle sa ba bare ya sa ran zata amsa mishi Sai yace, "Please I beg you MEEMA to give me another chance to enter your life, I will give you back the happiness you lost, I will be your mother and father in your life, I will take care of you accordingly, you will be happy in your life insha Allah ok?" Shanyayyun idanuwan ta ta ɗago ta kafa masa su, sai da tayi luu da su kamar zata rufe sai kuma ta sake ware su tana kallon sa, cikin sanyin muryan ta da ya disashe daƙyar yake fita ta soma magana a hankali, "I don't need to get married now in my life Ishaq, in fact I will return to Nigeria..." "What.. What are you saying?" Yayi maganar da sauri yana katse ta Sai da ta sauke ajiyan zuciya kafin tace, "I said I would return to Nigeria." "No MEEMA why would you do that to me? Please don't go and leave me, what will you do in that country after this is your country? Please stay and live happily ever after, how do you think you will go and leave Me when I need you? Or do you just not loving me MEEMA? Tell me, have you ever loved me?" Hannu ta sanya a goshin ta tana rufe idanu, still ta ware su a kansa cikin raunin murya tace, "I love you Ishaq, I personally don't go there because I don't like the people there, but I am going to Nigeria because Abee told me to go," sai ta fashe da kuka tana ƙara faɗin, "Abee told me to go there. He told me to go back and look for my mother. I never thought Abee would remember her again because of what she had done to him. She left us for a long time. she chose her life on her own, but Abee told me to go to her, and I didn't love her and I don't want to go.." "So why don't you stay here and get married, why?" Yayi maganar kamar zai yi kuka yana dafa mata cinyoyi Hannun nasa tabi da kallo sai kuma ta mayar da kallon ta a kan fuskar sa tace, "Ishaq I have to go, Abee says don't stay here and go back there, if I go Ummee doesn't answer Me and ask his relatives to stay there. I have decided not to go to Ummee but to go to my father's family and stay there." Sai ta riƙo hannayen nasa tana kallon ƙwayan idanuwan sa tace, "I love you Ishaq. If you really want me, we will live together. I will be with you wherever I go. We will get married." "How do we get married?" Yayi maganar a hankali shima ya kasa ɗauke nashi idanun a cikin nata "Make sure we are together, going there will not separate us, if you really want me to follow ME there and marry Me". "What are you saying?" Yayi maganar yana me zame hannayen sa a cikin nata. "Ok I know. you want me to let everyone follow you there and get married?"     "No, I want you to go there and ask for my marriage. I don't have anyone here. You must follow me there and ask for my marriage." Shiru yayi yana kallon ta, sai kuma ya tashi ba tare da yace uffan ba ya fice Da kallo ta bi sa itama ta kasa cewa komi, har ya fice tana bin ƙofan da kallo. [08/10, 2:56 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                    💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*               *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                      *NO_11*              A ranan da Abee yayi arba'in su Ummu Hani suka zo wajen MEEMA, dayake sun zo sun mata ta'aziyya tun ranan da yayi kwana ɗaya, a lokacin tana asibiti babu lafiya shi ne suka yi ta zarya ita da Esha har sanda suka zo ta farka suka yi mata ta'aziyya, basu sake zuwa ba sai yau ɗin da Zamiya zata zo tunda ita bata samu ta zo ba sai yau tace zata zo, zata yi kwana biyu before ta koma can Indian.               Duk da MEEMA ba ta cikin walwalan ta amma ta ji daɗin zuwan su saboda sun ɗebe mata kewa sosai Da jirgin Zamiya ya sauka drever MEEMA ta sanya ya ɗauko ta. Koda suka haɗu sai duk suka rungume juna cike da farin cikin sake haɗuwa wuri ɗaya. "I'm so sorry MEEMA for not coming until today, please be patient. May God have mercy on Abee and forgive him". Zamiya tafaɗa idanuwan ta a kan MEEMA da ta riƙe mata hannu Murmushin yaƙe MEEMAN tayi kafin tace, "no problem, thank you very much for your coming". Cike da fuskar tausayi Zamiyan tace, "Are you alright now? But you are not going to be alone in this house, are you? You should go back to Ummee." "We've already told her, if she doesn't come back she will follow ME to our house." Ummu Hani Said Kallon su kawai MEEMAN take yi, sai dai gaba ɗaya a ranta damuwa ne ke damun ta, duk da har yanzu basu san asalin abinda yasa Ummeen ta ta tafi ta bar su ba, ta sanar musu cewa, "Ummee sun rabu da Abee ne". Dalilin da yasa ta tafi ta bar su kenan, domin ba ta fatan su san real labarin, tana ga kowa ya ji dole ne zai yi tirr da mahaifiyar ta, abun kunya ne ma a gare ta ace an san Ummeen ta ta tafi ta bar su. Shiyasa kawai da suka matsanta mata sai tace musu, "dama tana da ninyar zuwa Nigeria wajen ta". A ranan a gidan suka wuni kafin suka wuce suka bar ta da Zamiya don a wajen ta zata zauna. Zaman Zamiyan na kwana biyu yasa ta ɗan sake jikin ta sosai saboda tana jan ta da surutu tare da mata abinda zai ɗebe mata kewa, shiyasa da zata tafi tayi kewar ta sosai har ƙwalla tayi.             Zuwa kwana biyu duk ta gama haɗa kan komi na Abee ɗin ta, lauyan Abee shi yayi mata jagora ta haɗa takardun ƙadarorin shi da ya mayar da sunan ta, dama already duk dukiyan sa ya mayar mata a account ɗin ta kafin ya rasu, lauyan ta saka ya samo masu siyan companies ɗin suka taya, da fari ta so siyar da su duka ne sai kuma ta sauya shawara aka yi cinikin ɗaya, ɗayan kuma ta danƙa shi a wurin Lauyan Abee zai riƙa kula mata dashi sai kuɗaɗen su riƙa shiga account ɗin ta.              A ranan da zata tafi Nigeria kuka sosai ta sha, haka ma house Girl ɗin su da duk masu aikin gidan, babban Trolly ta cika da kayan ta da sauran abubuwan amfanin ta, har computers ɗin ta dana Abee duk ta haɗa ta tarkata, sai kuma ɗan ƙaramin Back Shima da ta cika iyakan abubuwan da ta kwashe a gidan, gidan kuma ta danƙa a hannun su don ta kasa siyarwa, za su ci gaba da kula dashi tana tura musu albashin su ta account Gaba ɗayan su da drever suka raka ta har airport ta hau jirgin da zai wuce Nigeria. Seat ɗin ta na line 3 ne, ita ce a ciki shiyasa tunda ta zauna ta kafa kanta a window ta mayar da idanuwan ta ta rufe. Har jirgin ya cika ana ta maganar a saka belt while bata motsa ba Wanda yake gefen ta da ya gama saka nashi a karo na farko sai ya kalli inda take, kamar bazai yi magana ba domin har ya kawar da kansa sai kuma ya sake kallon ta yace, "excuse me". Bata ji sa ba har sai da ya saka hannu ya buga jikin kujeran nata kafin tayi firgigit tana kallon sa idanun su cikin na juna. Janye nasa yayi yana ɗan lumshe su kafin ya buɗe, ba tare da ya kalle ta ba yace, "put on your belt". Sai a lokacin ta janye nata idanun tana kallon jikin ta, sai kuma ta saka hannayen ta a kasalance ta saka belt ɗin ta sake kafa kanta a window, sai dai a wannan lokacin bata rufe idanuwan ta ba waje kawai take kallo, bata sake motsa wa ba har sanda aka zo tambayar su abinda suke so a kawo musu. Ko juyo wa bata yi ba ta girgiza kanta alamun ba ta son komi Wanda ke gefen ta shima be amshi komi ba, jarida kawai yace, "a kawo masa." ya kara a fuskar sa yana karanta wa. Shima ɗin be sake motsa wa ba har jirgin nasu yayi landing a garin Abuja.               Sai da aka soma fita tukun MEEMA ta ɗago kanta ta kalli wanda ke kusa da ita da yake ƙoƙarin tashi zai ciro jakan sa, murya a matuƙar sanyaye tace, "Afuwan uridu an as aluk". Ɗago idanuwan sa yayi ya zuba mata su ba tare da yayi magana ba Hakan ne yasa ta ɗan dafe goshin ta kuma sai ta maimaita masa da harshen turanci, "Please I want to ask you". Ɗauke kansa kawai yayi ya mayar kan jakan sa, sai da ya sauko kafin yace da ita, "I hear you". Ran MEEMA babu daɗi tace, "We come to Yola?" Be san sanda ya kalle ta ba jin abinda tace, ƙare mata kallo kawai yake yi yana nazartan ta Ita kuma ganin kallon da yake mata sai ta ɓata fuska tana tura baki tare da ɗauke kai Hakan yasa ya waro idanu waje still idanun sa a kanta, be furta komi ba ya ɗauki kayan sa ya wuce Da kallo tabi bayan sa zuciyar ta cike da haushi, sai kawai taja tsaki tana miƙe wa itama ta soma ciro nata kayan ta fita a jirgin. Tun da ta saka ƙafafuwan ta a waje take bin duk inda Allah ya kai idanuwan ta da kallo, wannan shi ne rana ta farko da ta taɓa zuwa Nigeria a rayuwar ta, duk da ta sha jin labarin ƙasar wajen mahaifin ta amma bata taɓa mayar da hankali a kan wai tana son ta ga ya ƙasar take ba koda a hoto ne, ko kuma tazo ta gani a matsayin ƙasar iyayen ta, in fact ma ita ko sau ɗaya bata taɓa jin ƙaunar ƙasar ba, amma yau sai gata a cikin ta, shiyasa ta zama kamar village Girl sabida yanda take kallon mutanen ciki, daƙyar take ma iya tafiya tsaban kalle-kalle har tuntuɓe take ci. Bata san ina zata nufa ba shiyasa ta tsaya a tsakiyar airport ɗin tana ta ganin yanda mutane ke zirga-zirga, duk da dare ne amma gaba ɗaya wajen ya haske da ƙwan fitila. Sai da ta ji ƙafafuwan ta sun soma gajiya kafin ta tasar wa ƙofan da ta ga ana fita. Yawanci ganin mutane take yi sai hawa mota suke yi suna tafiya, sai kuma wasu suna wuce wa wajen ƴan taxi suna hawa, da yanda kuma masu taxi ɗin suke biyo fasinja suna tambayar inda za su je. Hakan yasa itama ta nufi can ɗin kanta tsaye tana jan kayan ta daƙyar Ɗaya na hango ta ya taho da sauri yace da ita, "tafiya zata yi?" Bata san me yace ba shiyasa tace mishi, "I'm going to Yola". "Yola kuma Hajiya? Ai babu inda zaki samu motan Yola a nan, gwara ma ki kama hanya ki san inda dare yayi miki". Ya wuce abin sa yana ci gaba da tare fasinja Tsaye tayi a wurin kawai don bata fahimci inda zancen nasa ya nufa ba Wani yana hango ta shima ya zo ya hau tambayar ta inda zata je The same amsar da ta bawa wancan shi ta ba shi Shi da yake ya iya turanci sai ya sanar mata, "babu motan Yola a nan, saboda yanzu dare yayi baza ta samu ba sai gobe". Jin hakan yasa ta roƙe sa a kan, "Take her to Yola. She will give him whatever it is." Cikin turancin yace mata, "Madam nan fa Abuja kike ba Yola ba, tafiyan da zamu yi awanni taya zan ɗauke ki a wannan tsohon daren? yanzu fa ƙarfe 09:00pm". Bata kai ga yin magana ba mutumin da suka zauna tare a jirgi ya iso wajen. Kallon me motan yayi fuskar shi babu walwala yace, "mu je ka kai Ni barikin sojoji". "Ok to". Me taxi ɗin ya amsa mishi da sauri yana amsar Jakar sa ya wuce mota shi kuma ya bi bayan sa. Bayan ya saka mishi kayan a cikin Boot sai ya dawo wurin MEEMA da ke tsaye kamar status a wurin ta kasa motsa wa yace da ita cikin turanci, "ta faɗa inda zata je ya sauke ta sabida motoci sun ƙare, idan ba haka ba zata sha wahalan samun abun hawa idan ta bar wurin". Hotel kawai ta iya furta wa a laɓɓan ta Shi ne yace, "to su je". Taimaka mata yayi da kayan suka wuce, ya sanya mata a Boot Ita kuma ta wuce ta buɗe baya zata shiga. Ganin mutumin hakimce a bayan motan sai ta ja ta tsaya ta ƙi shiga "Madame, enter. We are in a hurry." Maganar da me taxin yayi ne ya ankarar da shi na cikin motan ma, don a lokacin wayan sa yake duba wa ko ɗago kai be yi ba. Idanu suka haɗa dashi sai yayi saurin ɗauke nasa While itama hakan ne, rufe motan tayi ta koma gaba ta shige Me taxi ya ja motan suka tafi Babu me motsi a cikin motan har sanda suka isa wani kyakykyawan Hotel ya tsayar da motan, sannan ya kalle ta yace, "Madam here is ok?" "Is that Hotel?" Ta tambaye sa tana kallon sa "Yes, it's a hotel. Look at the name there." "Ok" kawai tace tana shirin fita "Your money is two hundred Madam". Shaf ta manta shiyasa ta dakata tana juyo wa ta kalle sa, cikin sanyin murya tace, "give me your account number". "Account number? Two hundred You paid for my account? I don't have it. Just give me Cash." "Sorry I don't know how much money you are using, and I don't have money now in my hand, I will pay you through my account". Zai yi magana suka ji muryan mutumin nan na baya yana cewa, "wai zaman me kake yi ne? Ka sallame ta mu tafi." Dayake ita bata ji me yace ba tunda da Hausa yayi Shi kuma me taxin yace, "kayi haƙuri don Allah haƙƙi na zata bani". "Mu je zan biya". Cewar sa ba tare da ya ɗago kai daga latsa wayan da yake yi ba bcoz hasashen sa ya ba shi kamar ita baƙuwa ce a ƙasar, domin yanayin ta da shigan da tayi ya nuna ba ƴar nan bace "Ok madam let's go take your Trollys off, he said he'll pay your bill". "WHO?" "This is in the car." Kallon sa tayi ta ga hankalin sa na kan waya ne. Bata ce komi ba ta buɗe motan ta fice, Sai da ta fita ne kuma ta leƙo kaɗan tace dashi, "shukran". Be yi ninyan ɗago wa ya kalle ta ba, amma jin yanda sassanyan muryan nata ya daki kunnen sa hakan yasa ya ji kwaɗayin sake tozali da ita Ai kuwa idanuwan nasu suka shige cikin na juna. Ita ta soma janye nata idanun tana juya wa ta tafi domin already shi me taxi ya gama ciro mata kayan ta Shiga motan yayi ya ja suka bar wurin A hankali ta ja kayan nata ta nufi Hotel ɗin. Ta samu masu aikin don basu tashi ba, faɗa musu tayi, "she needs a room". Babu ɓata lokaci suka yi mata bayanin dokokin Hotel ɗin tare da bata takarda ta cike bayan ta biya su kuɗin ta account, sannan suka bata keey ɗin ɗakin bayan ɗaya tayi mata jagora har zuwa bakin ƙofan ɗakin Murɗa ƙofan tayi ta shige ciki, a bakin ƙofan ta tsaya ganin ɗakin da duhu, sai ta laluba jakar ta ta ɗauko wayan ta ta haska, a nan ta samo inda abun kunna glof ɗin ɗakin yake ta kunna, ta mayar da ƙofan ta rufe. A hankali ta taka ta isa kan sofa ta zauna tana me bin ko ina da kallo yayinda fuskar ta take a cikin tsantsan damuwa. Tunda ta zauna bata iya motsa wa a wurin ba domin kwantar da kanta tayi a kan kujeran ta mayar da idanuwan ta ta rufe, a haka ta zauna na tsawon wani lokaci. Daƙyar ta iya tashi ta rage after dress ɗin ta ta koma ta ƙudundune a kan sofa ɗin, yanda take ji gaba ɗaya jikin ta babu daɗi har zazzaɓi yake son kama ta, hakan yasa ta kasa taɓuka komi, ga shi kuma barcin ya ƙi zuwan mata don tsananin damuwa da tunani sun yi mata yawa, gaba ɗaya kewar Abee ɗin ta ya cika mata zuciya har hawaye take tsiyayar wa. Ta raba daren a haka bata iya kataɓus ba kuma ta kasa barci, sai daga baya ta tashi ta shiga Toilet tayi alwala ta soma gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar ta ɗaura da nafila tare da nema wa Abee ɗin ta rahamar Allah. Sai da aka kira sallan subahi kafin ta dakatar da nafilolin da take yi ta gabatar da sallan subahi ɗin. Tana idar wa wani nannauyan barci ya kwashe ta a wurin. Bata farka ba sai taran safe, lokacin daƙyar ta iya tashi a wurin saboda tsaban yanda jikin ta yayi mata nauyi da tsami, daƙyar take iya ɗaga ƙafafuwan ta haka ta isa cikin Toilet ta fito ta zauna a kan kujera, idanuwan ta duk sun gama sauya kala sun kumbura sosai daƙyar take iya buɗe su, da gani ka san damuwa ce da rashin barci ishashshe ya mayar da ita haka. Ta fi mintuna talatin a zaune a kujeran ta kasa motsi.                Sai wajen ƙarfe Goma kafin tayi odan abin da zata ci aka kawo mata. Dama har da yunwa ya galabaitar da ita amma sabida rashin daɗin bakin ta yasa ta kasa saka komi a cikin nata tun jiya. Daƙyar a yanzu ɗin ma tayi Breakfast ɗin, ko kaɗan abincin be mata daɗi ba dole ta koma tayi odan tea ta Sha sosai sannan ta tashi ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito tayi shirin ta, riga da wando ta saka a ciki, sannan ta ɗaura after dress blue color, tayi rolling kanta da ɗankwalin Abayar babu abinda ake gani nata sai kyakykyawar cuty face ɗin ta da ta sake yin haske sosai tayi fayau kamar mara lafiya, komi bata saka a fuskar nata ba ta tattara kayan ta ta fito. Kai tsaye wajen reception ta wuce ta mayar musu da keey ɗin sannan tayi musu sallama ta fice. Har ta fita hotel ɗin baki ɗaya sai kuma ta juya ta dawo ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin tace mata, "She needs to go to Yola, please tell her where to find a car to take her?" "Ok but don't say I'm full of questions, aren't you a native of this country? Because of your temperament and the way you speak English you are not Nigerian." Cewar receptionist ɗin cikin fara'a Gyaɗa mata kai MEEMAN tayi ba tare da ta furta komi ba Murmushi ita kuma tayi tace, "Yes I can understand. You are really beautiful. " "Thank you". Tace da ita itama tana murmusawa "Okay, I'll help you get there Bus Stop and get a car there." "Ok no problem". Ita kuma matar fita tayi ta shiga cikin hotel ɗin, babu jima wa ta dawo ita da wani na miji. Sai ta nuna masa MEEMA tace, "ita zaka kai Tasha, sai ku yi magana da ita zata biya ka". Sannan kuma ta kalli MEEMAN tace, "This will take you". Godiya MEEMAN tayi mata sannan suka fice ita da saurayin. A cikin keke napep ɗin sa suka wuce ya kaita tasha. Shi ta roƙa ya taimake ta ya sama mata motan da zai kaita Yola. Taxi ya samo mata tace, "she will pay in full and be taken alone". Me taxi da ya ji zunzurutun kuɗin da zata biya shiyasa ya amince zai kaita ita kaɗai Haka shima me napep ɗin ta biya sa kuɗi me yawa sannan suka tafi Sai da tace, "It has started to change where it will change Nigeria's Money". Bayan sun je shi ya amsa ya canzo mata kafin suka tasar wa hanyar Yola, tafiya suke sosai don tsula gudu kawai yake yi. Duk da haka sai magriba suka shiga cikin Adamawa Me taxi ɗin tambayar ta yayi, "inda zai wuce da ita ya sauke ta?" A nan ta sanar dashi address ɗin gidan su Abee ɗin ta, da sunan me gidan, kasancewar gidan yayi suna domin Kakan sa Alh. Riskuwa shi ya fara zama a anguwan nasu, shiyasa zai yi wuya idan ka je ɓarayin a kasa gane gidan nasa, kaf anguwan babu wanda be san gidan Alh. Riskuwa bafulatani ba duk da a yanzu ɗin jikokin sa da tattaɓa kunnen sa suke zaune.          Duk da haka me Taxi ɗin ya sha wahala yana tambayar gidan kafin ya samu wanda ya san anguwan ma, dayake ba ta ɓarayin suka sauka ba. Sun kai bakin gidan wajen ƙarfe 09:12pm na dare. A nan ya sauke ta ta biya shi kuɗin sa. Sai godiya yake mata saboda kuɗin da ta ba shi masu yawa ne, haka ya ja motan nasa ya tafi Ita kuma tana tsaye tana bin anguwan da kallo ko ina tsit kake ji babu kowa, don har wasu sun kulle gidajen su, dare yayi sosai sai dai akwai hasken farin wata. MEEMA bata saba tsintan kanta a irin wannan rayuwan ba shiyasa duk ta tsure jikin ta har rawa yake yi, daƙyar ta iya ƙarisa wa bakin Gate ɗin gidan ta hau buga wa tana yi tana kalle-kallen bayan ta.            Ta jima a wurin tana buga wa kafin me gadin ya fito da goran sandan sa yana haske-haske da tocilan hannun sa, a fuskar MEEMA ya sauke yana dalle ta da cewa, "kee lafiya daga ina?" Hannu ta sanya ta rufe fuskar ta tana kau da kai, bata iya magana ba domin bata san ma me yake cewa ba Shi kuma ƙara dage wa yayi yana haska ta don a tsorace yake da ganin ta, musamman kyawun nata da ganin ta fara fatt da yayi. Daure wa yayi kawai yana sake tambayar ta, "daga inda take kuma wa take nema?" "Please remove this item on my face". Tayi maganar tana ɗan goce wa Dayake shi kuma ya iya turancin sai ya kawar yana sauya harshe ya sake tambayar ta, "Where are you from, Ma'am? Please leave there before I hit you." "It was here that I was told the house of Uncle Aliyu my father's Brother to his place I came." She spoke looking at him Me gadin sake haska ta yayi sosai har yana leƙe kafin yace, "You mean you come his home?" "Yes". "So stop here let me go and let them know". Yafaɗa yana garƙame Gate ɗin ya wuce Ita kuma jingina tayi da jikin Gate ɗin tana ta kalle-kalle Har sanda ya dawo shi da Kawu Zubairu yana cewa, "ina take ne?" "Tana waje". Inji me gadin. Da sauri ya buɗe masa Gate ɗin suka fita suna haske ta da tocila "Zulaiha". Cewar Kawu Zubairu yana sake haska ta da kyau don sake gasgata idanun nasa.   _bakwa yin Comments. Gaskiya zan dena tunda ba kwa so._ [08/10, 2:57 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                          💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *KAN MATSALAR KASANCEWA A TSAYE ANA SALLAH*       _Rahamar Allah tana isowa, mun samo labarin wani shahararren mai kawo hadisai da ake kira Abu Ishak Subaihi wanda ya rasu yana da shekara ɗari. A kan ji shi yana cewa, "Kash! Wannan rauni na zurfin shekaru ya hana mini more ma doguwar sallah. Yanzu a raka'o'ina biyu Baƙara da Al-imrana kaɗai nake iya karantawa." Su kuwa surorin nan biyu sun kai kamar ɗaya bisa takwas na Alƙur'anin gaba ɗayan su._ _Shi kuwa Hafiz Ibni Ƙayyam yayi nazarin irin fa'idojin da ake samu daga sallah ne ya jero su da cewa, "sallah tana tabbatar mana da samun abincin yau da kullum, ta kawo lafiya, ta kore cututtuka, ta ƙarfafa zuciya gami da faranta ta, ta kawo haske ga fuska, ta sabunta jiki, ta kawar da lalaci, ta haskaka zuciya, ta daɗaɗa ta, ta rage mata jin nauyi kana ta yiwa mutum albishir da rahmar Allah. Tana kasancewa garkuwa ga azabar Allah, tana tsare mu daga shaiɗan ta kuma kusanta mu da Ubangiji. A taƙaice dai; sallah lamuni ne na duk wani abin so kuma garkuwa ce ga duk wani abin ƙi na zuci ko na jiki a wannan duniya ko lahira." Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin ya Allah._                             *NO_12*               Bata iya magana ba sai kallon sa da take yi "What happened to bring you here? Where is your father?" Ya sake jero mata waɗannan tambayoyin Wannan karon ma bata ba shi amsa ba Dole ya kalli Me gadin yace da shi, "ya ɗauko mata kayan nata ya shigo da su," sannan yace mata, "she follow him". Shiga suka yi gidan suka wuce Part ɗin Kawu Ali. Sai da yayi Nocking kafin ɗiyar sa Murjana da suke zaune da Umma a parlour'n suna kallo ta zo ta buɗe masa jin muryan Kawu Zubairun "Lafiya me ke faruwa? Wace ce wannan kuma?" Inji Umma domin itama ta taso ta biyo Murjanan a baya a tunanin ta ko babu lafiya ne Shi kuma yace mata, "baki gane ta bane? Zulaiha ce ƴar wurin Faruk". "Faruk.. Faruk dai ɗan uwan ku na Riyadh?" Ta ambata tana sake ƙare wa MEEMAN kallo "Eh shi. Kira min Yayan nawa sai ki sanar masa do Allah". "To shikenan bari in shiga in Kira sa". "Ke kuma ki zo ki zauna kin wani tsaya a tsaye". Inji kawu Zubairun yana kallon MEEMAN dake tsaye har yanzu a bakin ƙofa. Ganin bata motsa ba sai ya tuna ai ba ta jin Hausa sai ya kuma maimaita mata da turanci Hakan yasa ta tako a hankali tana bin ko ina da kallo ta zo ta ɗofana mazaunan ta a kujeran Itama Murjana zama tayi tana ƙare mata kallo kafin kuma ta kalli Kawu Zubairun tace, "wai Kawu wannan ɗin ita ce yarinyan Uncle Faruk ɗin?" "Eh ita ce mana baki ga sun yi kama da uban nata bane?" Taɓe baki tayi tana sake ƙare wa MEEMAN kallo don bata taɓa sanin ta ba, a kaf gidan ma babu wanda ya san ta illa labarin ta da suke ji, sai kuma su Kawu Ali da suke zuwa can ɗin shi ne suka santa.               "Ina Zulaihan take?" Inji Kawu Ali da ya fito da sauri daga ɗaki Umma na take masa baya. Ganin ta yasa yace, "ashe dai ba ƙarya Jamila take min ba itan ce da gaske, ikon Allah". Yafaɗa yana zama gefen Kawu Zubairu idanuwan sa a kan MEEMAN, kafin kuma ya juya yana tambayar Kawu Zubairu, "a ina ya samo ta?" "Nima wlh Ina tsaye a bakin ƙofan sashi na na hangi Gali Yana taho wa, shi ne nake tambayar sa lafiya ina zai je? Yake sanar min wai baƙuwa ce ta zo kuma wurin ka ta zo shi ne zai zo ya sanar maka, Ni kuma nace mu je in ganta". Kawu Ali yace, "to ke wa ya nuna miki gidan namu? Waye ma ya kawo ki ƙasar? Ina uban naki?" "Kaima ka san ba ta jin ka tunda ba iya Hausa tayi ba". Cewar Kawu Zubairun Shi shaf ya ma manta sai ya juya harshen yana sake tambayar ta "My Abee is Dead". "He died?" Suka faɗa a tare cikin wani irin farin ciki da ya kasa ɓoyuwa a fuskar su Ita kuwa bata ma fahimci yanayin nasu ba sai gyaɗa kanta da tayi cikin muryan kuka take cewa, "yes he died and left Me". A nan take sanar musu da komi da mutuwar nasa da kuma wasiyyar da ya bata ta dawo Nigeria ta zauna "Ka gani ko Zubairu ai Allah ba azzalumin bawan sa bane, tunda Ni na gansa a haka dama na san zai wula nan ba da jima wa ba, muka so mu taimake shi mu tafi da ita amma ya ƙi furr har shegiyar yarinyan nan tana mana rashin kunya, sai ga shi dai mu ne dolen ta ga shi ta dawo wurin mu, to uban wa yace mishi muna da wurin ajiye ta? Ai a daren nan zamu kaɗa shegiya ta tafi.." Kawu Zubairu yayi saurin taran numfashin sa da cewa, "to gadon mu fa? Haka zata tafi da dukiyan nasa bayan shi muke wa sintiri tun ba yanzu ba?" "Gaskiya nima abun da na gani kenan?" Inji Umma da ta saka musu baki Kawu Ali yace, "to ai dole sai mun amsa kason mu kafin ta bar mana gida". Sai ya juya yana kallon MEEMA da kanta ke saman cinyoyin ta tana ci gaba da kuka yace, "so since he died now where is our inheritance? Where is your father's property then we will share?" Ɗago kai tayi tana kallon su, sai kuma tace, "Abee owned everything for me before he died, and now he has returned all his property to my name." Wani ashar Kawu Ali ya fesar ya buɗe jajayen idanuwan sa zai yi mata magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi "Ka ga Yaya bar ta don Allah, na nemo mana mafita, ai maganar ma gado bata taso ba, kaf dukiyar sa ya zama namu wlh kuma dole sai mun amshe sa, amma yanzu idan kace zaka nuna mata halin da muke ciki zata iya tafiya wajen uwar ta ta bar mu, yanzu samun hanyar da zamu yi mu mallaki komi ya zama namu shi ne mafita, in yaso daga baya sai mu kore ta ta tafi, ka san tayi karatu tana da ilmi dole sai mun nuna mata siyasa komi ya dawo hannun mu". Shiru Kawu Ali yayi yana tunani Umma tace, "Abban Sajjad maganar Zubairu fa a kan gaskiya take, yanzu ai ko kace zaka amshi komi bazai yiwu ba, ta yiwu ma babu komi a hannun ta dole zata zauna damu har sai kun mallaki komi ya zama naku kafin ku kore ta". Sai da Kawu Alin ya kalli Murjana yace, "ke ja ta ɗakin ki ku tafi ki nuna mata komi don a can zata zauna". Tashi tayi tana kallon MEEMAN cikin yatsina tace mata, "she got up and they went". Hakan yasa ta kalli su Kawu Alin ta ƙi ta tashi Shi kuma yace, "she get up and followed her to her room." Sannan ne ta tashi ta ja kayan ta tabi bayan ta suka wuce ɗakin Murjanan "Yauwa to na yarda da shawaran ku hakan za'a yi, yanzu dai dole zamu ja ta a jiki domin mu mayar da duk ƙadarorin ta ya zama namu". "Eh Yaya hakan za'a yi". Inji Kawu Zubairu "To shikenan mu bar maganar yanzu sai zuwa gobe sai mu ci gaba da tattaunawa ko zamu ɓullo hanyar da ya kamata". Da haka suka rufe maganar Kawu Zubairu yayi musu sallama ya tafi. Su kuma suka wuce ɗakin su.                  *WASHE GARI*             Sai tara da rabi MEEMA ta farka daga barcin da ya ɗauke ta tun sallan asuba da tayi ta koma. Ta jima a zaune a saman gadon bata iya tashi ba tana ta faman tunanin da ya zame mata jiki, da kuma yadda Rayuwar ta zata koma a nan gaba a inda bata saba ba. Sai daga baya ta miƙe sabida yunwan dake ƙwaƙulan ta don babu wanda ya zo ya tashe ta, daga ita sai farar riga me tsantsi da guntun wandon sa ta shiga bayi tayi brush sannan ta fita parlour'n ko ɗan kwali, sai dai ta kama gashin nata ta tufke shi a tsakiyar kan.           Babu kowa a parlour'n sai wani kyakykyawar saurayi bafulatani fari sol, don da gani kaf gidan ya fi su kyawu domin shi zak Fulani ne babu silƙi, tamkar dai Mahaifin MEEMA ya haife sa saboda kamanceceniyar da suke yi, don shi ya fi kama dashi a kan su Kawu Ali. Yana zaune ne a kan sofa ya saka ear phone a kunnen sa, daga shi sai gajeren wando ko riga babu, kan nan nasa ya sha askin zamani wanda ƴan iska suke yi, ya bar tulin gashi sosai a tsakiyar kan wanda ko kitso za'a iya yi tsaban tsawon sa, wata macen ma baza ta nuna masa yawan gashi ba. Waƙa yake bi na Turanci duk ya kure parlour'n da muryan sa MEEMA dake tsaye a bakin ƙofan tunda ta fito ta hange shi sai ta tsaya cak tana bin sa da kallo, tayi five minutes a tsaye a wurin tana faman kallon sa kafin kuma a hankali ta tako ta soma dosan cikin parlour'n zata wuce zuwa kan dainning table da ta hango Gab ta iso kusa da wajen nasa ne ya ankare da ita, da sauri ya ɗaga idanu yana kallon ta, be san sanda ya miƙe tsaye a kan ƙafafuwan sa ba yana sake ware ido a kanta Itama idanun ta na a cikin nasa ta kasa ɗauke nata a kanshi, sai dai ko kaɗan fuskar ta babu alamun walwala haka take kallon sa. Sai da ta kusa wuce wa kafin ta janye nata idanun ta nufi saman dainning Har sai da ta zauna before ya kawar da kansa ya nufi ɗakin Umman sa yana kwaɗa mata kira kamar zai tsaga gidan Kafin ya kai har ta fito da sauri tana faɗin, "lafiya Sajjad wannan wani irin kiran mafarauta kake min? Me ya faru ne?" "Umma wace ce wannan? A ina kuka samo ta?" Sai da ta bi inda yake nuna mata da kallo ta hangi MEEMA a zaune har ta soma haɗa tea ko kallon inda suke bata yi ba, sai ta ja tsaki don ta manta da ita a gidan sai yanzu da ta ganta, tace dashi, "jiya ta zo ai lokacin kayi barci, yarinyan Uncle ɗin ku ne na Riyadh". "What..! You mean Zulaiha ce wannan?" Yafaɗa yana sake nuna inda MEEMAN take a zaune "Eh ita ce. Ka bari idan Abban ku ya dawo sai yayi maka bayani Ni yanzu ina aiki". Tafaɗa tana juya wa ciki ta bar sa a wurin Shi kuma juya wa yayi ya isa inda MEEMAN take Sai da ya ja kujera ya zauna kafin ta ɗago tana kallon sa da manyan idanuwan ta Washe baki yayi yana bata hannu yace, "Hi Zulaiha I'm Sajjad your brother". Sai ta bi hannun nasa da kallo tana tsayar da taunan bread ɗin da take yi Murmushi ya sake yi yana tura mata hannun yace, "I'm your brother fa? I was so surprised to see you here, I never thought of that, are you so good. The truth you very beautiful. " Miƙe wa kawai tayi ta juya ta bar wurin Shi kuma sai ya saki baki yana bin ta da kallo kamar zai zubar da yawu, har wani lanɗe baki yake yi. "Wow gaskiya tana da kyau. Wai dama haka take yarinyan? Amma gaskiya an cuce Ni da ba'a nuna min ita ba sai yanzu. Wow.. wow". Yake ta faɗi yana shafa ƙeyan sa, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin Umman nasa, ya same ta tana gyaran gado sai ya zauna a kan drowan gadon yana cewa, "Umma wlh yarinyan kyakykyawa ce sosai har kama take yi dani, amma a nan gidan zata zauna ko?" Ɗago wa tayi tana hararan sa kafin tace, "Ni fa Sajjad ka rabu da Ni da wannan halin naka, ka kiyaye Ni wlh". "Haba Common Momcy yawa ne, ki share kawai Ni fa yarinyan ta shiga raina ne wlh, I like her so much, kuma kin ga ƙanwa ta ce wani abu ne idan nayi tambaya game da ita?" "To ka je ka tambaye ta mana ina ruwa na a ciki?" "To ai Umma ta ƙi kula Ni ne, yarinyan tana da matuƙar class ta haɗu Allah fa ina gaya miki". "Hohoho Sajjad baza ka rabu da Ni ba ko?" "Sorry Momcycy na rabu dake." Ya faɗa yana tashi tsaye tare da sara mata, sai kuma ya matso kusa da ita yana cewa, "but Umma Ina Murjana sai in tambaye ta?" "Ta je school". Ɓata fuska yayi sai kuma ya juya ya fice. Har ya zauna a kan kujeran Parlour'n yana ta kallon ɗakin Murjanan, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin ya tura ƙofa ya shige MEEMA dake ƙoƙarin cire rigan jikin ta zata ɗaura tawul ta shiga wanka, sai ganin sa kawai tayi a tsakiyar ɗakin, ƙara ta saka lokaci ɗaya ta ja rigan tayi sama da shi Shi kuwa daskare wa yayi a wurin tsaban ganin kyakykyawar halittan ta da yayi, idanun sa kawai suke motsi a kanta A lokacin da gudu Umma ta shigo ɗakin tana tambayar, "lafiya?" Saboda ihun da MEEMAN tayi har ɗakin ta. A kan Sajjad ɗin ta sauke ido sai kuma ta kalli MEEMAN, "ke lafiya mene ne?" Ita dai tana tsaye ta maƙure a jikin bango tana kallon su don bata san me tace ba Sai Umman ta ja tsaki tana cewa, "wannan ai shashanci ne kawai ki zo kina cika mana gida da ƙara. Kai kuma uban me kayi mata ne da zata fasa min dodon kunne?" Daƙyar yake iya sauke numfashi, sai da ya ɗan ja fasali kamar ya dawo a cikin hayyacin sa kafin yace, "Babu Umma. Shigo wa ta kenan nima". Dogon tsaki ta ja tana juya wa kawai ta fice Shi kuma sai ya mayar da idanun sa kan ta kafin ya taka izuwa wurin ta Hakan yasa tayi saurin haye wa gadon tana sake ware idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa a kansa, hannayen ta kuma suna a kan ƙirjin ta sai sake matse su take yi tana ƙanƙame jikin ta. Ganin da tayi ya ƙi dakata wa daga inda yake yana neman hayo wa gadon cikin ruɗe wa tace, "what are you doing here? Please get out." Dariya ya saki yana ci je leɓe, sai kuma ya saka hannu zai riƙo ta yace, "Common Babe nayi zaton ke wayayyiya ce, ki riƙa abu kamar na classics big Girls mana, just I will hugg you because I really Love you". [10/10, 3:38 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                          💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*              *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                             *NO_13*                   Da sauri ta sauka daga kan gadon ganin da tayi ya kusa taɓa ta. Fuskar ta babu walwala cikin ruɗu da tashin hankali tace, "what will you do for me? What is my connection with you? Please get rid of Me." Tsaya wa yayi yana kallon ta domin yanda ta buɗe baki ala dole tana masifa sosai ta sake burge sa, ji yake yi kamar ya je ya rungume ta ya tsotse mata bakin da ya fi ɗauke masa hankali, sai kawai ya shafa kansa yana killer smile yace, "Babe I love you so much, I am so impressed by everything you do. Please I want us to be friends..." "No I don't want to. I said go out". Ta katse sa a cikin tsawa "Ok, calm down. I'll be out." Sai ya juya yayi bakin ƙofa har yana waigen ta, yana zuwa dai-dai bakin ƙofan ya dakata yana juya wa sosai ya kafe ta da ido yana haɗiyar yawu, har da wani lanɗe baki sai faman shafa kansa yake yi wanda alamu ya nuna ɗabi'an sa ne hakan. Ya ja wani soconni a wurin kafin ya juya ya fice Wani irin ajiyan zuciya ta sauke har tana dafe ƙirjin ta ta zauna a bakin gadon, sosai zuciyar ta ke gudu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban tsoro, a haƙiƙanin gaskiya ta tsorata da shi sosai domin abun da be taɓa faruwa da ita bane. Zumbur ta tashi kamar ta tuna da wani abu ta nufi ƙofa ta murza keey sannan ta dawo ta sake zama. Ta daɗe a wurin tana faman saƙa da warwara a ranta kafin ta tashi jiki a saɓule ta ci gaba da zame kayan nata, sannan ta ɗaura tawol ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito ta wuce bakin dressing mirror, tsaya wa tayi kawai tana kallon kanta a mirror  har a lokacin fuskar ta babu wani ɗigon walwala, ƙare wa kanta kallo take ta yi har na tsawon lokaci kafin ta ja numfashi tana wuce wa wajen Trolly ɗin ta ta buɗe, kayan da zata saka ta ɗauko, sannan ta ciro cream lotions ɗin ta da take amfani da su ta shafa ta mayar, ta saka kayan riga da skert masu tsananin kyau, rigan me ruwan madara ne me taushi sosai tana da zane-zane a jiki wanda sai ka kula da kyau zaka iya hango wa kasancewar da kalan ruwan madaran aka yi, gajeren hannu ne da ita sai kwalliya da aka yi da zare dack brown color da kuma milk ɗin, sai skert ɗin sa Robber brown color da ta sanya har wajen cikin ta, sai ta ɗaura belt ɗin sa Shima Brown but light, gyara gashin ta tayi ta kama da ribom, bata saka komi a kanta ba ta ɗauki computern Abee da nata ta haye kan gadon, buɗe wa tayi ta soma aiki akai.               Abun da Sajjad yayi mata shiyasa ko kaɗan ba ta sha'awar sake fita, shiyasa tayi zaman ta a nan tana ta faman aiki a computer, sai da aka kira sallan azahar kafin ta tashi ta gabatar sannan ta sake zama ta ci gaba har sanda Murjana ta dawo ta hau buga mata ƙofa. Da sauri ta rufe computern ta mayar a cikin Trolly ɗin ta sannan ta wuce ta buɗe mata. Su biyu ta gani a bakin ƙofan ita da wata sa'ar Murjanan har kayan school ɗin su iri ɗaya ne Ita Murjana tsaki ta banka tana hararan ta ta wuce ciki While ita kuma ɗayan washe baki tayi tsaban farin ciki kawai ta rungume MEEMA, sai kuma ta sake ta tana faɗin, "Oyoyo sister. Ni ƴar uwan ki ce suna na Habibah, Habibah Zubairu, I am your uncle Zubairu's daughter, I am happy to see you". Ta ƙare maganar tana bata hannu MEEMA bata gama fahimtan maganar nata ba sabida kasancewar ta haɗa da Hausa, amma sai ta miƙa mata hannu itama tana ƙirƙirar murmushi tace, "me too". Shigowa ɗakin Habiban tayi tana riƙo hannun MEEMAN ta ja ta suka zauna a kan gado tace, "yanzu da zamu dawo school Murjana take sanar min da zuwan ki, shi ne nace bari in zo in ganki". MEEMA kallon ta kawai take yi, sai kuma ta murmusa tace, "sorry i don't understand, what did you say?" "Oh don't you understand Hausa?" Habiban tayi magana tana ware idanu da mamaki Still MEEMA tana murmushi ta gyaɗa mata kai "Ok sorry I don't know, but do you want to teach you our language?" Shiru MEEMAN tayi bata iya ce mata komi ba Sai ita kuma tayi murmushi tana riƙo hannun ta ta haɗa da nata kafin tace, "I will pass our Part, I will come back to see you later, because even in my soul I like you". "I like you too". Tafaɗa itama sosai a wannan lokacin tana murmusa wa Tashi tayi Habiban ta ɗaga mata hannu ta fice Da kallo ta bi bayan ta har ta ɓace wa ganin ta, a ranta sosai ta ji sanyi haɗuwar ta da Habiba zata samu wacce za suna magana ba kamar Murjana da ko kallon ta ba ta yi, ko magana ta ƙi yin mata Yanzu ma tuni ta fice a ɗakin tunda ta sauya kaya. Tana fita parlor Sajjad ya tare ta da maganar MEEMA, shi ne abin ya bata haushi ta ja tsaki tana cewa, "wai Yaya meye haɗin ka da ita ne da kake son sanin wani abu a kanta? Gaskiya yarinyan bata yi min ba bcoz tana da jijji da kai, ko don ta ga tana da kyau ne?". Dungure mata kai yayi yace, "kina dai baƙin ciki ne bayan haka meye a jikin ta da zaki ce bata miki ba? Ni kuma ina son ta". Tura baki tayi ta wuce ta zauna a saman dainning ta soma haɗa lunch Sai ya biyo ta yana cewa, "Common Sister ki sanar dani abun da na tambaye ki kinji? Haba My sister". Sai da ta taɓe baki kafin tace, "Wai Mahaifin ta ne ya rasu shi ne ta zo nan". "Wow da gaske?" Yafaɗa yana buga tsalle Da kallo ta bi sa kafin tace, "lafiya Yaya meye na murnan?" "Uhmm daɗi nake ji sosai a raina, kenan ta dawo nan da zama? Kin ga shikenan zan same ta". "Wai kana nufin da gaske son ta kake Yi?" "Sosai ma. Kuma auren ta zan yi domin dai-dai kala ta ce ita, macen da nake fatan samu kenan, Abba na dawo wa zan sanar mishi ayi-ayi a aura min ita". Dariya Murjana tayi tace, "daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi Yaya? Tab ɗijim zan ga inda draman nan zata ƙare, akwai kallo a gidan nan wlh". Ta ƙare maganar tana sake fashe wa da dariya "Ke fa baki da kunya na lura, amma bari in je in dawo kafin Abba ya dawo zaki ga me zan yi". Ya tashi ya fice Ita kuma sai dariya take yi, daƙyar ta dakatar da shi ta soma cin abincin.               A lokacin ne MEEMA ta fito ta nufi wajen dainning ɗin Da kallo Murjana take bin ta har ta ƙariso ta ja kujera ta zauna. Sai ta ja tsaki tana ɗauke kai ta ci gaba da cin abincin nata Ita kuma MEEMA kallo ɗaya tayi mata itama ta cire nata idanun a kanta ta soma serving kanta. Duk da tana jin yunwa but daƙyar ta iya yin spoon uku ta ture abincin, hannu ta sanya ta janyo Flaks ɗin dake wurin ta zuba ruwan Lipton ɗin a cikin Cup, ganin babu kayan haɗa tea ɗin a wurin sai ta ɗauka haka nan ta soma sha ko sigar babu a ciki Murjana dake kallon ta ta ƙasan ido sai ta taɓe baki a fili ta furta, "sanabe gai da uwar miji a kasuwa. Zaki saki ciki ki riƙa cin abinci ne tunda nan ba can bane, ƴar wahala". Dayake MEEMAN ba jin ta take yi ba shiyasa ko ɗago wa bata yi ba bare ta kalle ta, har ta kurɓe ruwan lipton ɗin ta tashi zata koma ɗaki A time ɗin ne Habiba ta shigo ita da Inna Mahaifiyar ta, dayake itama ta shigo domin ta ga MEEMAN ce tunda Kawu Zubairu ya sanar mata "Yauwa Inna kin ganta". Cewar Habibah cikin farin ciki tana me ƙarisa wa kusa da MEEMAN ta riƙe mata hannu. Sai kuma ta juya ga MEEMA tana ce mata, "she's her mother". Hakan yasa ta ɗan saki fuska tana gaishe ta Inna kuwa sai ƙare wa MEEMAN kallo take yi tana faman yamutsa fuska da taɓe baki, domin itama irin waɗannan jarababbun matan nan ne, don har ta fi Umma iya shege Sai da Habiba tace mata, "Inna gaishe ki fa take Yi?" "To Ina na sani tunda ba iya Yaren nayi ba?". Sai kuma ta ja tsaki ta wuce tana tambayar Murjana, "Ina Umman ta?" Hango ta da tayi zaune a saman dainning "Tana ɗaki". Ta bata amsa a taƙaice Hakan yasa ta wuce ciki Habiba itama tuni ta bi MEEMA cikin ɗaki.              Inna na shiga ɗakin Umma ta ganta zaune tace, "ashe kina ciki na shigo ban gan ki ba?" "Eh ina ciki Halima. Aiki na gama kuma na zauna ban fita ba". Inna zama tayi a gefen ta kafin suka gaisa kana tace, "Wai Jamila haka zaki zauna da yarinyan nan a gidan ki. Me ya kai ki amsar ta?" "Wace yarinyar?" Umma ta tambaya tana kallon ta "Wannan Yarinyan mana na wajen Faruku". "Ohh wlh Ni manta wa nake yi da ita a gidan, to ya na iya tunda ba dauwama zata yi ba, su ma su Abban Sajjad ɗin ai suna shirin koran ta ne bayan komi ya dawo hannun su". "Ai gwara haka don wlh bata da wurin zama a wannan gidan haka kawai, Ni kinga Habibah ne ma naga tana wani murna da zuwan ta, Ni fa bazan lamun ta hakan ba wlh sai in saɓa mata". Umma tace, "ai Ni dayake Murjana babu ruwan ta kinga ko shiga safgarta bata yi ba". "Na san maganin Habiban ai, bari in je wanki nake yi na taso". Cewar Innar tana tashi tsaye Itama Umman tashi tayi ta bi bayan ta suka fita Parlour suna sake zantawa Innar ta tambayi Murjana dake zaune a kan sofa a yanzu tana latsa waya, "Ina Habiban?" "Ta bi wancan yarinyan ciki". Tayi maganar cikin taɓe baki "Habiba.. Habiba". Inna ta ɗaga murya tana kiran ta Da sauri ta fito tana faɗin, "Inna gani nan fa ba nisa nayi ba". Hararan ta tayi tana cewa, "ai na san ba nisan kika yi ba, uban me kike yi a wurin ta?" "Inna babu komi fa muna hira ne tunda.." Katse ta tayi tana faɗin, "dalla rufe min baki, idan baki yi wasa ba wlh zan saɓa miki a gidan nan, ina ruwan ki da ita daga zuwan ta zaki fara maƙale mata?" "Inna ƴar uwa ta ce fa". Tafaɗa tana zaro idanu "Eh ƴar uwan taki, ba na son alaƙar ku nace, wuce mu je dalla". Habiba cike da rashin jin daɗin abun da uwar nata tayi mata haka ta bi bayan ta suka fice "Nima fa wlh yarinyan ba burge Ni tayi ba Umma, idan ba ma zubar da kai ba na Habibah daga zuwan ta ta wani fara maƙale mata, da can suna son mu ne da zata zo mana gida?" "Nima abun da na gani kenan, ki barta ai mu ma ba dauwama zata yi mana a nan ba, can ta wuce dangin uwar ta ba dai nan ba, don bazan riƙe ɗan riƙo ba wlh". "To Umma amma fa bazai yiwu ta zauna a haka kullum ki girka ki bata ba babu abinda zata rika yi ƙatuwar budurwa kamar ta, nan ba gidan su bane dole ta riƙa yin aikin gida ko nima zan huta wlh, kinga tunda na fita ke baki gyara parlor'n nan ba ita kuma bata zo tayi miki ba." Umma tace, "to dama ai na barta ta ɗan kwana biyu ne kafin ta soma mana aiki, wlh ƴar aiki aka kawo mana don bazai yiwu ta ci ta sha a gidan nan ba ta luƙume a ɗaki, ki bar ta zuwa gobe komi na gidan nan dole tayi shi, wannan sanƙamemiyar budurwan da a yanzu tana gidan miji ina zan iya da ita?".                 ******           MEEMA dake zaune a ɗaki duk maganar da suke yi a kunnen ta ne tun fitan Habibah, sai dai bata fahimci ko eh ba a ciki, tayi jiran ko Habiba zata dawo amma shiru shiyasa ta kwanta tana ɗaukan wayan ta ta soma latsa wa Murjana ce ta shigo ɗakin ta ganta a haka, ta ɗauke kai tana wani ciccin magani ta wuce ta shiga Toilet. Bata jima ba ta fito tana kallon MEEMAN tace, "ke dalla tashi ki fita zan gyara ɗaki na tunda baki san ki gyara min ba". Idanu ta zuba mata tana mamakin yadda take hararan ta tana mata tsawa a kai. Shiru kawai tayi tana sake ƙare wa Murjanan kallo, ko a girme zata bata good 5years ko fiye da haka..         "Keee! Ko ba kya ji ne ki tashi nace ko gadon uban ki ya siya min ne?" A wannan karon ma Murjanan tayi maganar a fusace tana ɗaga murya Tashi zaune MEEMA tayi tana kallon ta sosai kafin tace, "what do you say I don't hear you?" "Uban ki nace banza kawai. I said get up and go out". Ɗauke kai tayi daga kallon ta tana me ɗaukar wayan ta ba tare da ta furta komi ba ta tashi ta fice a ɗakin.. Kai tsaye Parlour ta koma ta zauna tana ɗaura kanta a saman kujeran ta lumshe idanuwan ta Sajjad ne ya buɗe ƙofan ya shigo yana rera waƙa ear phone a kunnen sa. Idanuwan sa suna sauka a kanta yayi saurin zare ear phone ɗin yana bin ta da kallo kamar zai haɗiye ta tsaban kallo while zuciyar sa cike da farin cikin ganin ta Ita kuwa tuni ta ɗago tun sanda ta ji muryan nasa itama tana kallon sa, sai dai ta sake haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. [10/10, 3:39 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                          💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*              *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                             *NO_14*             Ɗauke kai tayi a kansa ganin ya taho wurin ta. Sosai ƙirjin ta ke luguden buga wa saboda tsoron sa amma ko kaɗan bata nuna a fuska ba Har ya zo ya zauna gefen ta yana wani faman shafa kai da kafa mata idanu kamar wanda zai cinye ta. Cikin sanyin murya yace, "Babe why don't you want to take care of Me? I am your brother and I love you so much." Ɗago Kai tayi ta kalle sa, sai dai bata ce komi ba ta sake ɗauke kai a kansa Numfashi ya ja kafin yace, "ok I'm so sorry for what I did to you, I forgot I did not greet your dead father, sorry God bless his grandson". Still dai shiru tayi Sai shima ɗin yayi shiru kawai yana kallon ta Abba ne ya shigo gidan da sallama a bakin sa Sajjad ya amsa mishi yana kallon sa, sai kuma ya miƙe ya nufe sa yana hugg ɗin sa tare da cewa, "Oyoyo Dadyyyy". "My son ya kake?" Abban yafaɗa yana shafa kansa cikin fara'a "I'm fine Abba, sai dai i miss You so Much". Dariya yayi yana bugan kafaɗan sa da cewa, "Oh my son baza ka dena halin ka ba". Cikin shagwaɓa yace, "Allah Dadyyyy da gaske nake yi fa".           Idanu MEEMA ta zuba musu tana faman kallon su, sai kawai Abee ɗin ta ya faɗo mata a rai, lumshe idanu tayi tana me buɗe su a lokaci ɗaya tare da son komar da hawayen da suka taru mata a cikin ido. Mayar da kallon ta tayi a kansu da har sun ƙariso wurin, sai ta tashi cikin girmamawa tace, "Welcome Dad". Yaƙe yayi Kawu Ali yana kallon ta yace, "Ah Zulaiha you are here?" "Na'am Dad". "Okay we have something to talk about, but then your uncle comes and we will discuss". "Nima Abba akwai maganar da zamu yi da kai gaskiya". "Ok my son, ai ko wani time lokacin ka ne faɗa mu ji". Sai da ya bubbuga ƙafafu kafin ya kalli MEEMA da ta saki baki a wannan lokacin tana kallon sa, ya nuna ta da yatsa da cewa, "Abba Gaskiya na kamu da son ta, I really love her Ina son ka aura min ita". "Whattt.. Sajjad what are you saying?" "Ina son in aure ta". Ya sake maimaita wa yana tura baki Umma da ta fito daga ɗaki a yanzu ɗin tace, "uban wa zaka aura ba dai wannan yarinyan ba Sajjad? Kana da hankali kuwa?" "Yes Umma ina da hankali na, Ni dai kawai ita nake so ku aura min ita wlh, idan ba haka ba zan mutu". Ya ƙare maganar da dafe ƙirjin sa yana wani narke fuska "Ai kuwa sai dai ka mutu wlh, ka dena tunanin ma maganar ka zai yiwu, koda yake babu wanda be san halin ka ba". "Umma wlh da gaske nake yi ina son ta da aure ne". Yayi maganar yana ƙarisa wa wajen ta da riƙo hannayen ta "Dalla sake Ni banza kawai, meye abun so a nan?" "Abba baka ce komi ba kana jin ta ko?" Yayi maganar cikin buga ƙafafu "Nima me zance Sajjad? Shirmen ka yana da yawa kai kam, Ni yanzu na dawo a gajiye ka bari na huta". Ya ƙare maganar yana wuce wa ɗakin sa Itama MEEMA tuni ta koma ta zauna tana ta kallon su kamar ta sami t.v, sai dai ko kaɗan bata fahimci inda zancen nasu ya nufa ba illa mamakin abun da Sajjad ɗin yake yi kamar wani yaro. Tana kallon yanda yake ta bin Umman har cikin kichen yana mata shagwaɓa Murjana da ta fito yanzu bin bayan su tayi tana cewa, "wai umma wa ya taɓo Yaya ne yake ta mammanne miki?" "Wai maganar wancan yarinyan yake min auren ta zai yi". Dariya Murjana ta kwashe da shi tana cewa, "ai akwai kallon drema kenan a gidan nan, nima haka yace min ɗazu abun da bazai taɓa yiwuwa bane." Biyo ta yayi yana faɗin, "ina wasa dake?" Da sauri ta gudu suka soma zagaye kichen ɗin suna zagaye Umma dake tsaye a tsakiyar kichen ɗin Sai faɗi take yi, "zaku ka dani fa". Amma ba su ji ta ba sai guje-guje suke yi, daga ƙarshe Parlour suka wuce suka ci gaba da yi Lokacin MEEMA bata a parlour'n ta koma ɗaki Ƙarshe dai ɗakin Abba suka je a can ya raba su faɗan, domin haka suka saba tunda sun zama kamar yara an sangarta su sai abun da suke so suke yi a gidan, sun tashi babu kwaɓa ko kaɗan, ba ma kamar Sajjad da yake ɗan fari, dayake sanda aka haife shi sai da ya jima domin har sun ɗauke tsammanin sake haihuwa, sai kuma daga baya aka haifi Murjana.             Yanzu haka Kawu Zubairu shi kuma yana da yara uku ne, dayake tare suka yi aure da Kawu Ali, Ɗiyar sa ta farko me sunan mahaifiyar su Jammatu suna kiran ta Ummi tayi aure har da yara uku don ita ce sa'ar Sajjad, sai kuma Amina itama tayi aure da yaron ta ɗaya da cikin na biyu, ko MEEMA ta girmi Amina, sannan sai Habibah sa'ar Murjana, yanzu suna S.S 3 ne zangon ƙarshe.                 ✳️✳️✳️            Da aka yi sallan isha'i sai Kawu Ali suka shigo sashin shi da Kawu Zubairu. Sajjad na biye da su a baya Umma ta kawo musu abinci tana cewa, "yau a nan zaka mana hira kenan?" Dariya Kawu Zubairun yayi yace, "a'a yanzun nan zan tafi ai, maganar dai Zulaiha ce muke so muyi yanzu, ina take? Ki kira mana ita don Allah". "To". Tace tana juya wa ta wuce ɗakin Murjana Shi kuma Sajjad dake hakimce a saman kujera yana latsa waya da sauri ya ɗago yace, "Abba to nima ayi maganar mu da ita, wlh da gaske nake yi ina son ta ku aura min ita". "Wace ce yake so ne?" Kawu Zubairu yake tambaya "Wai Zulaiha yake so, idan ba shirmen Sajjad ba ina shi ina yarinyan nan bayan ya san yanda muke da uban ta ƴar tsaman dake tsakanin mu, ai bazai yiwu ma ya kawo ta a matsayin surukata ba wlh, yarinyar da ta gama ɓalɓancewan ta kusan sa'ar shi me zai yi da ita?". Kawu Zubairu yace, "Yaya ni ina da shawaran da zan bayar a game da wannan zancen". A lokacin Umma da MEEMA suka ƙariso wajen Sai Kawu Zubairun yace, "to Sajjad bamu wuri zamu tattauna, kuma kar ka damu idan Zulaiha ce zaka aure ta". "Da gaske Uncle?" Yafaɗa cike da murna "Ƙwarai kuwa, bari zamu yi magana da Abban naka". "To Uncle. Na gode sosai". Ya tashi yana murna, idanun sa a kan MEEMA da ta samu wuri ta zauna bata ce komi ba, killer smile ya saki yana faman ci je baki kafin ya wuce.         Ita Umma itama tuni ta wuce cikin nata ɗakin, dama wanka zata yi ta tsaya ajiye musu abinci tunda sun shigo tare "Wai Zubairu me kake nufi wani shawaran ne zaka bayar? Ba dai a kan auren nasu ba don bazai taɓa yiwuwa ba". "Haba Yaya ka kwantar da hankalin ka mana, Ni ina ga wannan ma yana a cikin tsarin mu idan har hanyar da zamu ɓullo be yiwu ba, to kamata yayi ta auri Sajjad idan ya so ko nan gaba sai mu raba ta da komi ya zama mallakin mu, tana ji tana gani kuma bata da yadda zata yi damu tunda a lokacin mun fi ƙarfin ta, tana ƙarƙashin mu dole Sajjad zai san yanda zai yi ya sauya komi da sunan mu. In yaso ma ko ƙara zata kai mu gaba sai mu iya raba ta da duniyar ma". Waro ido Kawu Ali yayi "Ah to abu me sauƙi, kai kana ganin yarinyan nan ba matsala zata zame mana ba?" Jinjina kai yayi yace, "haka ne kam. Amma yanzu mu fara gwada ta mu gani." Sai ya juya da kallon sa ga MEEMA dake zaune still tana ta faman kallon su kamar wacce take fahimtar maganar nasu, nan kuwa ko eh bata fahimta ba illa bakunan su da take ta ƙare wa kallo. "Zulaiha, this is what we called you about your father's assets, you know it is not possible for us as your father's relatives to leave you with these huge sums of money, even if you say that your father owned everything for you before he died then you must We have a share in the property, but now it is not a matter of what we want to do. You can bring everything so that we can turn it over to you. You feel that we are not advising you. It is an order that you will give us everything to hold in our hands." MEEMA da ta tsare sa da idanu tana sauraron sa har ya dire, Bata manta su waye su ba kuma bata manta dalilin da yasa Abee ɗin ta ya mayar da komi nashi da sunan ta ba, dole yanzun ma akwai abin da suke nufi shiyasa ta gyara zaman ta tana cewa, "Uncle's be patient with what I'm talking about, I've already decided what to do with my money, and Abee's companies are selling them all, and I can keep the documents of his house in my hand. I do not need your help..." Wani irin fusata Kawu Ali yayi saboda zancen nata Zai yi magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi da cewa, "don Allah Yaya ka ƙyale ta, dama nace maka wannan yarinyan shegiya ce mahaifin ta ya rigada ya koya mata yanda zata yi tun kafin ya rasu, kana tunanin bata san manufar mu bane? Ka barta kawai yanzu mu bi ta a sannu idan muka nuna fin ƙarfi zamu iya rasa komi wlh, kuma ka san ba yanda zamu yi mu amshi komi sai da saka hannun ta, takardun filayen kuma ta ce ya mayar da sunan ta ka ga bazai mana amfani ba ko mun ƙwata da ƙarfi". "Haka ne. Amma yanzu ya kake so mu yi? Yanzu kana nufin Mu zuba mata ido da zunzurutun kuɗaɗen nan? Wlh bazai yiwu ba". Kawu Ali yace hakan cikin jin haushi yana sharce zufa "Lallaɓa ta zamu yi mu jawo ta a jiki hakan zai saka ta saki jiki damu, na san zata bamu komi domin mu riƙa juya mata tunda dai ba ita zata kula da wannan dukiyan ba". Sai ya kuma juya wa ya kalli inda MEEMAN take cikin turanci yace, "Zulaiha tunda mu a matsayin mu na Iyayen ki kin ƙi aminta damu kin nuna bamu isa dake ba, shikenan ki ci gaba da riƙe kuɗin idan wani abun ya same ki babu ruwan mu, kin yarda?" Gyaɗa kanta tayi "Ok get and go". Tashi tayi kuwa ta wuce ɗaki "Gaskiya wannan abun be min daɗi ba, yanzu haka zamu zuba idanu sai kace yarinyan ta fi ƙarfin mu?" Kawu Zubairu yace, "Kai yaya ka cika saurin hawa ne, to ya zamu yi kuwa wlh baza mu iya amsar komi ba bare kaf ƙadarorin sa suna wani ƙasa ne, ka ga kuwa ba abu bane me sauƙi ya dawo hannun mu ba, idan baka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama ka, shawaran dai da zamu bi mu haɗa su aure da Sajjad ko tana so ko ba ta so". "Kana ganin hakan zai fi?" "Eh mana hakan zamu yi. Idan ta zama matar sa komi zai fi zuwan mana a hannu babu yanda za'a yi ta tafi tunda da auren ta, shima Sajjad ɗin dole mu sanar masa da komi domin ya san shirin mu, in yaso daga ƙarshe mu raba su ko ya ƙi ko ya so idan mun gama da ita, kana gani fa juya mata dukiyar zamu yi amma ta ƙi amincewa, wannan yarinyan halin su ɗaya da uban ta wlh dole sai mun bi a sannu Ni dai Yaya ina faɗa maka, auren su babu fashi zamu tsayar da time a ɗan ƙanƙanin lokaci, sannan baza mu sanar mata ba har sai a ranan bikin idan an ɗaura, ka ga ba yanda zata yi". Kawu Ali sosai ya amince da wannan shawaran da ya bayar, sai da suka sake tattauna wa sosai kafin ya tafi A lokacin su Umma har sun gaji sun fito suna kan dainning suna cin abincin su "Sajjad kira matar taka mana ku ci abincin, ya naga bata fito ba?" "Wow Abba ka amince zan aure ta?" Murmushi yayi yace, "My son kenan, ka taɓa ganin kun nemi abu kun rasa ne? Ai da yardan Allah Zulaiha matar ka ce, sai dai ban ce ka sanar mata ba har sai an ɗaura auren naku, zamu tsayar da lokaci nan ba da jima wa ba don haka sai ka shirya zama ango nan kusa". Ihu ya saki tsaban murna ya rungume Umma ya haɗa da Murjana ya matse su yana ci gaba da murna "Kai wai lafiyan ka ƙalau kuwa? Dalla sake Ni". Inji Umma tana ɓanɓare shi, sai kuma ta dubi Abban tace, "wai me kake cewa? Ni fa gaskiya ban amince ya auri yarinyan nan ba, haba Abban Sajjad kai ne kuma da faɗan hakan bayan kai zaka fi kowa ƙin auren?" "Jamila zo ki zauna ki zuba min abincin nan, idan muka gama sai muyi magana in fahimtar da ke." Bata ce komi ba dai ta taso ta nufi inda yake ta soma zuba masa abincin Shi kuma Sajjad tuni ya wuce da sauri ya burma ɗakin Murjana don kiran MEEMA, har wani tsalle yake yi tsaban farin ciki.   _Rashin Comments zai saka baza ku riƙa samu kullum ba, ba sai na riƙa maimaita muku ba duk sanda ku kaga new update shikenan._ [10/10, 3:40 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                          💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/              *P.W.A✍️*              *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *KAN MATSALAR KASANCEWA A TSAYE ANA SALLAH*       _Rahamar Allah tana isowa, mun samo labarin wani shahararren mai kawo hadisai da ake kira Abu Ishak Subaihi wanda ya rasu yana da shekara ɗari. A kan ji shi yana cewa, "Kash! Wannan rauni na zurfin shekaru ya hana mini more ma doguwar sallah. Yanzu a raka'o'ina biyu Baƙara da Al-imrana kaɗai nake iya karantawa." Su kuwa surorin nan biyu sun kai kamar ɗaya bisa takwas na Alƙur'anin gaba ɗayan su._ _Shi kuwa Hafiz Ibni Ƙayyam yayi nazarin irin fa'idojin da ake samu daga sallah ne ya jero su da cewa, "sallah tana tabbatar mana da samun abincin yau da kullum, ta kawo lafiya, ta kore cututtuka, ta ƙarfafa zuciya gami da faranta ta, ta kawo haske ga fuska, ta sabunta jiki, ta kawar da lalaci, ta haskaka zuciya, ta daɗaɗa ta, ta rage mata jin nauyi kana ta yiwa mutum albishir da rahmar Allah. Tana kasancewa garkuwa ga azabar Allah, tana tsare mu daga shaiɗan ta kuma kusanta mu da Ubangiji. A taƙaice dai; sallah lamuni ne na duk wani abin so kuma garkuwa ce ga duk wani abin ƙi na zuci ko na jiki a wannan duniya ko lahira." Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin ya Allah._                             *NO_15*             Yana shiga ya hange ta kwance a saman gadon tana latsa waya Bata san da zuwan nasa ba sai da ya zo har gaban ta yana shirin amshe wayan sai tayi saurin firgita tana shirin ƙwalla ƙara Shi kuma ya sanya hannu ya kama bakin nata ya rufe ruf yana dariya Tuni ta yar da wayan tana shirin ƙwace kanta, nan da nan ta ƙwalalo idanu waje domin a tunanin ta wani abun zai mata ta soma Shure-shure zata ƙwace kanta Saurin matse ta gam yayi a jikin sa yana raɗa mata a kunne, "Shiiiiiii! Calm down! I have nothing to do with you." Amma ina bata saurare sa ba sai son ƙwace kanta take Yi tana son buɗe bakin ta da ya ɓame mata ɓam While Iya ƙarfin sa ya riƙe ta ya ƙi saki, musamman yanda ya ji skin ɗin ta kamar ya tamke mage sabida tsaban taushi da yake dashi, har wani santsi yake yi, hakan ya ja hankalin sa da jin wani irin feelings ya sake manna ta a jikin sa yana shinshina mata fuska Nan da nan ta soma kokuwa da shi iya ƙarfin ta har hawaye sun soma wanke mata fuska tsaban yanda ta tsorata ainun To ƙarfin su ba ɗaya ba sosai ya sanya mata ƙarfin sa ya mayar da ita kan gadon ya danne ta yana cewa, "Babe there is nothing I can do for you, I say calm down ok?" Sai numfashi take sauke wa sabida yanda tagalabaita a ɗan kokawan nan da tayi, because kasancewar ta ƴar hutu bata saba wahala ba shiyasa abu kaɗan a wurin ta aiki ne, idanuwan ta kuwa kamar za su fito waje tsaban zaro su da tayi Killer smile ya saki yana sake matse ta sosai har ƙirjin su yana haɗe wa, a hankali ya kai fuskar sa saman nata fuskar yana son kissing ɗin ta a forehead still yana liƙe da bakin ta gudun kar tayi masa ihu. Muryan Abban sa ya ji yana kiran sunan sa. Dalilin da ya sanya ya dakata yana me kallon cikin idanun ta in a cool voice yace, "Babe I'm sorry I didn't do this to spoil you, i love You so Much I will not do it again ok?" Kallon sa kawai take yi idanuwan ta suna zubar da ƙwalla ko ƙyafta su ta kasa A hankali ya janye hannun nasa still idanun sa cikin nata Har ya janye bata sake motsa wa ba illa numfashi da take ta faman sauke wa akai-akai, tana ganin ya sauka daga jikin ta tayi saurin tashi da gudu zata shige Toilet Hannun ta ya riƙe gam yana cewa, "Where are you going again?" "Please let me go, I do not want to". Tafaɗa tana hawaye tana son ɓanɓare hannun nasa "Ok, I'll let you go, but let's go and eat." "No I'm not hungry". Ta sake faɗa tana ƙwaƙule hannun sa da ƙarfi Be ce komi ba ya riƙe ta ya janyo ta suka fice Da kallo su Abba suka bi su baki sake "Kai lafiya me kayi mata Son? Meye haka?" "Abba babu komi wlh, ta ƙi zuwa ne shi ne na janyo ta". Yafaɗa yana isa har wajen dainning ɗin ya ja mata kujera yace, "sit please". MEEMA dake faman zubar da hawaye zama tayi kawai tana bin sa da kallo kamar zata maƙure sa don baƙin ciki Umma tace, "Ni ban san irin ka ba Sajjad, wlh zan saɓa maka idan ka cika shiga shirgin yarinyan nan, ina ruwan ka da ita ne?" "Umma kina so in barta da yunwa ne bayan mata ta ce? Abba kana ji ko?" Yayi maganar kamar zai yi kuka Abba yace, "kyale ta My son, amma ka dena mata abin da bata so kaji tunda ta nuna ba ta son zuwa ka barta mana. Idan ba haka ba zata tsane ka". "To Abba zan dena bazan sake ba". Sai ya kalli MEEMAN da har yanzu take zubar da hawaye yace, "sorry My Angel I will not do it again, let me serve you". Ya ƙare maganar yana rawan jiki wajen serving ɗin ta Murjana dake zaune a kan dainning ɗin tashi tayi tana jan tsaki tace, "amma wlh Yaya kaji kunya na rantse da Allah, ji be yanda kake mata bauta kamar zaka haɗiye ta?" Be kula ta ba shiyasa ta sake jan tsaki ta wuce wajen su Abba dake Parlour'n ta zauna tana cewa, "umma akwai matsala fa, dole sai kin shiga tsakanin Yaya da wannan yarinyan, idan ba haka ba wlh kina gani zai zama mijin tace". Umma da damuwa ta kalli Abba tana cewa, "ka gani ko abinda nake gudu kenan, don Allah ji be yanda yake ɓarin jiki Abban Sajjad?" Abba yace, "ke dai Jamila ki bar wannan zancen duk na ɗan lokaci ne, idan muka cika burin mu komi zai ƙare". "Ta ya ya? Kana ganin hakan me yiwuwa ne? Ni fa kar azo garin cikan burin ku in rasa ɗana". Abban be kai da magana ba Sajjad ya ɗaga murya yana cewa, "Abba ka ga ta ƙi ci". "To ka ƙyale ta mana uwar ka ce?" Umma tayi maganar a fusace "Zulaiha eat the food ok?" Inji Abba cikin kwantar da murya Girgiza masa kai tayi alamun baza ta ci ba "I said eat I don't want to argue." Dole a wannan lokacin ta soma ci ba tare da ta sake cewa uffan ba, dama yunwa take ji kuma abincin ba daɗi yake mata ba, shiyasa idan ta Kai spoon ɗaya sai ta ɗau soconni take sake kai wani Sajjad da ya saka ta a gaba yana kallon ta har da murmushi sai yace, "Babe don't you enjoy the food? What do you want to bring you now?" Bata ɗago kai ba bare ta kalle sa gaba ɗaya zuciyar ta tsanar sa take ji a ranta, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta kula sa shiyasa tayi masa shiru, tana sake kai wani spoon ɗin baki ta tashi ta ture kujeran zata tafi Shima biyo bayan ta yayi kamar jela yana tambayar ta, "did you finish?" Abba ya kira ta yace, "come and sit here, I ask you". Zuwa tayi ta zauna tana sake haɗe rai fuska a kumbure Umma da Murjana sai aikata mata harara suke yi kamar za su make ta Shi kuma Sajjad tuni ya zo ya zauna kusa da ita yana kallon ta Abba murmushi yayi yana kallon ta yace, "Daughter I know our country is very happy for you. Are you happy to be here?" Tura baki tayi gaba bata ce komi ba "Ok, since you refuse to talk, I want you to say what you need, so that tomorrow it will be brought to you". "I don't want anything". Tayi maganar tana tashi tsaye zata wuce, sai kuma ta juyo fuska babu walwala tace, "I need Simcard". Kafin ma Abba yayi magana Sajjad yayi saurin tsagal ɗin cewa, "Abba ina da sabon Simcard a ɗaki na bari in ɗauko in bata". Ya ƙare maganar yana tashi da rawan jiki ya wuce ɗakin sa Shi kansa Abba abubuwan da Sajjad ɗin yake yi ya soma ba shi mamaki da tsoro, sai ya ɗan yi murmushin yaƙe yana kallon MEEMA yace, "Let your brother take it." Koma wa tayi ta zauna ba tare da tace uffan ba Umma tace, "Abban Sajjad wlh abun da Sajjad yake yi ya fara yin yawa". "Jamila Ni kaina na ga hakan, amma ki sani wannan yarinyan bilonia ce shiyasa kika ga nima ban ɗauki mataki a kanta ba, dukiyar ta kawai muke so daga nan mu kore ta". "To ku amshi kuɗin mana meye na tsaya wa lallaɓa ta?" Umma tafaɗa a fusace "To ta ya ya zamu amsa bayan kafin mahaifin ta ya rasu sai da ya mallaka mata komi? Yanzu ko mu kan mu bamu da damar amsar gadon mu, kuma kin ga ba nan Nigeria bane idan muka ce zamu amsa ta tsiya ƙarshe kulle Kan mu zamu yi, can suna da doka ba irin nan bane, duk ƙadarorin sa suna can babu damar mu siyar da su a can sai da saka hannun ta da kuma yardan ta". Sajjad ɗin ne ya ƙariso wurin da sauri ya miƙa mata Simcard ɗin Amsa kawai tayi ta tashi ta wuce Umma tace, "kai Sajjad wai me ka gani a jikin yarinyan nan ne da kake ta rawan ƙafa a kanta?" "Wlh Umma ban taɓa son wata yarinya a duniya kamar Zulaiha ba, ina son ta sosai, don Allah Abba idan za'a tsayar da ranan auren mu a saka nan kusa kafin in koma karatu na na master's sai mu tafi tare". Riƙe baki Umma tayi da cewa, "Iyeeeee Sajjad". "Umma kema kin san halin Sajjad, Ni wlh gaba ɗaya na tsani yarinyan nan gaskiya Abba a hana sa auren ta.." Kafin ta ƙarisa maganar ma Sajjad ya bige mata baki, "ke ki kama kanki Allah zan tattaka ki ina wasa dake ne?" Yayi maganar yana wani zazzare mata idanu Ita kuma kuka ta saka ta hau shura ƙafafu Abba yace, "meye kuma na dukan ta My son?" "Abba baka ji me take cewa bane? Idan ba ta son ta ai Ni ina son ta, Kuma wlh idan ta sake zan fasa bakin ne". Ya ƙare maganar da tashi ya wuce ɗakin sa "Ke ma kiyi hakuri da Allah ba fa wani dukan ki yayi ba kina wani ɓare wa mutane baki". Inji Umma tana kallon ta Tashi Murjanan tayi tana bubbuga ƙafafu ta wuce ɗaki tana cewa, "ai dama kun fi son shi wlh, kuma bazan yarda ba sai na rama". Tana shiga ɗakin MEEMA dake kwance a kan gado tayi saurin ɗago wa saboda a tunanin ta ko Sajjad ne, ganin ba shi bane sai ta mayar da kanta ta ci gaba da waya da Esha da ta kira ta suna gaisa wa Dogon tsaki Murjanan ta ja tana wuce wa Toilet, tana fito wa ta haye saman gadon tana sake jan tsaki kamar wacce tsaka ta haifa, "dole ne ma a raba mana ɗaki don bazai yiwu in riƙa kwana da ita ba, shegiya kawai da wani fuska sai kace na mage". MEEMA na jin ta sai dai dayake bata san me take cewa ba wayan ta kawai take yi, sai da duk ta kira su Ummu Hani da Zamiya suka gaisa kafin ta ajiye wayan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyar ta, rufe idanuwan ta tayi zuciyar ta duk babu daɗi, bata jin ko wani irin farin ciki a cikin ta, tana ji baza ta iya zama a gidan nan ba Sajjad na mata abun da ya ga dama, sosai take jin tsoron kar ya zo yayi mata wani abun, shiyasa take ta saƙa da warwaran hanyar da zata ɓullo, ko kaɗan zaman gidan ba ya mata daɗi tunda ta fahimci kamar ba ƙaunar zaman ta suke yi ba, musamman ma Murjana da Umma da suke mata wani kallo, ga kuma Sajjad dake son takurata, tana ga idan babu hali dole zata koma can Riyadh, gwara ta zauna a can zai fi mata, amma kuma abu ɗaya ke hana ta tafiya saboda wasiyyan mahaifin ta, umarni ya bata ta koma wajen mahaifiyar ta ta zauna da ita, but ko kaɗan ba ta ƙaunar sake tozali da Ummeen ta har ta koma ga mahalicci, ta tsane ta sosai a zuciya shiyasa ta ga gwara ta zo wajen dangin Mahaifin nata ta zauna tunda zaman ta a can ne be son tayi ita kaɗai, sai dai a yanzu ɗin tana ganin dole ta nemi layin Ishaq ta ba shi haƙuri ya taho nan ya aure ta ta bi shi, hakan shi ne maslaha a rayuwar ta don baza ta iya zama a cikin Nigeria ba, har yanzu ƙasan be mata daɗi ba, but idan ta auri Ishaq sun koma can hakan ba yana nufin ta ƙi bin umarnin Abee ɗin ta bane. Share hawayen fuskar ta da tun ɗazu suka soma sintiri tayi tana gyara kwanciyar ta, ƙanƙame jikin ta tayi tana sake jin kewar Abee na ratsa mata zuciya, da ace yana da rai da ba haka ba, komi nata na farin ciki ya ruguje, ba ta tunanin akwai ranan da zata sake farin ciki da walwala babu Abee ɗin ta, Abee shi ne farin cikin ta kuma ya tafi ya barta, rayuwar ta gaba ɗaya ta ruguje tun tafiyan Ummee, shiyasa gaba ɗaya laifin alhakin mutuwar Abee take ɗaura shi a kanta, ita ta kashe mata Abee ɗin ta da a yanzu suna tare cikin ƙaunar junan su, baza ta taɓa yafe mata ba. Daƙyar a daren barci ya ɗauki MEEMA tare da mafarkai kala-kala. [10/10, 3:40 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._             *TUNATAR WA* _Kamar yadda sallah take ibada ce ta ruhu, haka nan muka lura cewa wajen yin ta jikin yakan sami babban ƙarsashi saboda motsa shi da ake yi. Ƙwararrun masana wasannin motsa jiki sun yaba da abubuwan da sallah ta ƙunsa, harkokin nan daban-daban waɗanda ake nanata su a cikin raka'o'in Sallah. Wadannan harkoki ba su barin wata gaɓa a jikin mutum mai Sallah sai sun motsa ta. Watau dai, yadda musulmi suke samun ibada ta ruhu a cikin sallah, haka nan ma suna samun amfani babba na motsa jiki._          _lada da fa'ida da mai yin Sallah zai samu kenan. Ina hukuncin wanda ya yi watsi da ita, ya ƙi bari ta zame masa garkuwa?_          _Duk wanda ya juya wa sallah baya ya guje wa Musulunci, ya saɓi Ubangijin sa. Ya karya dokokin imanin sa, ya kuma kama hanyar halaka. Duk ayyukan sa na ƙwarai sun ɓalɓalce don kuwa ya kauce wa umarnin Ubangiji game da Sallah - duk wanda ya saɓa ma Allah tamkar ya ce ba shi ne ma, domin kuwa ai da ya amsa cewa akwai Allah ai ba shakka da ya bi umarnin sa, kamar dai yadda yace, a cikin Alƙur'ani mai tsarki:_         *"Kuma ku tsayar da Sallah. Lalle sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi"* _Suratul Ankabut, aya ta 45._ Allah yasa mu dace.                              *NO_16*              *WASHE GARI*           MEEMA na cikin barci ta ji ana shafa mata face, tana buɗe idanuwan ta suka faɗa cikin na Sajjad dake durƙushe a gaban gadon ya tsira mata idanu, da sauri ta sake zaro idanun nata don sake gasgata shi ɗin ne a lokaci ɗaya tana me tashi zaune "Good morning my love." Yayi maganar yana mata murmushin sa me kyau Bata iya amsa wa ba kuma bata cire idanun ta a kan sa ba, sai ma tamke kyakykyawar fuskar ta da tayi tana mishi mugun kallo Tashi yayi ya zauna a gefen ta, kana ya saka hannun sa zai riƙe nata Tayi saurin daka masa tsawa tana janye hannayen nata, "don't touch me again". "Why dear?" Yayi maganar kamar zai yi kuka Tashi tayi daga kan gadon tayi hanyar Toilet ta shige Da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta tsaban yanda tayi masa kyau a cikin guntun rigan barcin nata, ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a ƙofan har sanda ta fito Ganin sa a zaune har yanzu sai ta ɗauke kai kawai tana sake haɗe fuska, wajen Trolly ɗin ta ta nufa ta ciro towel da abubuwan da zata buƙata ta sake shige wa Toilet ɗin Sajjad buga tagumi kawai yayi still idanun sa a kan ƙofan ya ƙi ko gezau. A lokacin da ta fito ai sandare wa yayi ganin ta daga ita sai towel, gaba ɗaya santala-santalan cinyoyin ta a waje suke Ita kanta bata yi tunanin zata sake ganin sa ba kasancewar ta ɓata lokaci a cikin Toilet ɗin, da sauri ta ja ta tsaya tana kallon sa cike da haushi, "I will prepare. Please Get out." Numfashi ya sauke sabida jin daddaɗan muryan ta a kunnen sa, yanda yake ji a jikin sa bazai iya magana ba shiyasa a hankali ya taka ya fice a ɗakin har yana sake waigen ta, ji yake yi kamar ya koma ya haɗa jikin su wuri ɗaya tsaban feelings ɗin da yake ji Ita kuma yana fita ta ja dogon tsaki ta nufi kayan ta, gaba ɗaya zuciyar ta ba ta mata daɗi har ta gama shirin ta cikin wata doguwar riga fara ne wuyan love, rigan Robber ce gaba ɗaya ta bi ta lafe mata duk ta fito mata da shafe ɗin jikin ta, dayake akwai ɗan guntun Hijab ɗin sa maroon color da aka yi design da less a ƙasan, shi ta saka ya tsaya mata a iyakan kafaɗa, da agogon ta da flet shoes ɗin da ta sanya duk na kayan ne white color, tayi kyau sosai duk da fuskar ta babu abun da ta sanya, wayan ta dake ajiye ta ɗauka ta fita Parlour Babu kowa sai Sajjad dake zaune. Yana ganin ta ya tashi tsaye idanuwan sa kamar za su faɗo a kanta, tsaban kyan da tayi masa tamkar ya je ya haɗiye ta haka yake ji, sosai MEEMA take da mugun kyau shiyasa gaba ɗaya ta zauta shi ya koma kamar wani soko a kanta, shiyasa ko barcin kirki ba ya iya samu sabida rashin kula sa da take yi, ba zai iya haƙura da ita ba a rayuwar sa, tabbas idan ya rasa ta mutuwa zai yi domin be taɓa ƙaunar wata mace ba sai ita, duk da yana da tarin ƴan mata domin Sajjad na mata ne but sai dai ya gara su be san cewa akwai ranan da wata mace zata shiga zuciyar sa kamar yanda MEEMA tayi ba... Idanuwan sa ya lumshe sanda ta gifta sa ta wuce ƙamshin daddaɗan turaren ta na Arab ya bugi hancin sa. Ya buɗe su yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a saman dainning. Wani irin numfashi ya ja nan da nan idanun sa suka soma kaɗa wa, bazai iya jure wa ba dole ya nufi inda take shima ya ja kujera ya zauna, kamar zai yi kuka tsaban yanda yake kallon ta yace, "Zulaiha". Kallon sa tayi sanda ta kai tea Cup bakin ta, ido cikin ido suke kallon juna sai dai fuskar ta a tamke yake tun zaman sa a wurin ta sake haɗe wa "I love You, why don't you love me?" Kawar da kanta tayi bata iya cewa komi ba taci gaba da shan tea ɗin, sosai yake tururi but haka take kaiwa baki tana kurɓa a hankali Sai shima yayi shirun ya sanya mata idanu zuciyar sa babu daɗi Wayan ta ta ɗauka ta soma latsa wa still tana kurɓan tea ɗin, Numban Ishaq ta rubuta sannan tayi dealing but switch off, tsaki ta ja tana ajiye Cup ɗin ta tashi tsaye ta wuce Har ta kusa shiga ɗaki Umma da ta fito a nata ɗakin ta kwaɗa mata kira Hakan yasa ta tsaya tana kallon ta, sai kuma ta buɗi baki a hankali tace, "Morning Mom". "Kar ki koma ɗakin nan ki zo ki gyara mana parlour, sannan ki shiga kichen ki ɗaura mana girki". Ita dai MEEMA tsaya wa tayi tana kallon ta bata ce uffan ba tunda bata san me tace ba Sajjad da ya taho wurin ya kalli Umman yace, "Umma wani girki kuma? Haba Umma daga zuwan nata tana baƙuwa sai ki saka ta aiki? Ni gaskiya baza a saka min mata aiki ba". "Sajjad ka fita ido na tun kafin in nuna maka fushi na, idan bata yi aikin ba haka zata zauna mana a gida sai dai muyi mu bata taci tayi kashi kamar wata uwar mu?" Sai kuma ta juya ga MEEMAN tace, "ke ko baki ji abinda nace bane kin tsaya kin wani kafa min idanu kamar wacce zata haɗiye Ni?" Sajjad yace, "to ai bata san me kike cewa ba ko kin manta ba ta jin Hausa ne?" "Ohh! To sai ka sanar mata da abun da nace". Juya wa MEEMAN tayi kawai zata shige ɗaki Umman tayi saurin janyo ta tace, "babu inda zaki shiga dan uban ki, na ce ka sanar mata ko?" Ta ƙare maganar da daka wa Sajjad ɗin tsawa "Umma yawa fa kike yi wlh, haba don Allah baki ga yanda take bane taya zata iya wani aiki? Kema daga gani kin san ƴar hutu ce baza ta iya waɗannan aikin ba Gaskiya, don Allah Umma kiyi hakuri ki barta". "Iyeeeee Sajjad Ni kake faɗa wa haka don uban ka? Wato ta zauna sai dai Ni nayi ita tana luƙume a ɗaki saboda ita ƴar hutu? To nan ba gidan uban ta bane wlh idan har tana son zaman ta a gidan nan dole ne sai ta yi min bauta". Ta ƙare maganar tana jan hannun MEEMAN da cewa, "ai dole ki gane idan na tasa ki gaba". Da sauri Sajjad ya riƙe Umman yana cewa, "don Allah Umma ki sake ta wai meye haka ne? Ni zan yi aikin a madadin ta ki sake ta". While MEEMA kallon su kawai take yi zuciyar ta kamar ta fito tsaban baƙin ciki, ganin Umman ta ƙi sakar ta sai ta ƙwace hannun ta idanuwan ta har sun soma cika da hawaye, bata ce komi ba ta juya ta shige ɗakin Nan Umma ta yunƙura zata bi bayan ta tana kiran sunan ta But Sajjad ƙiri-ƙiri ya tare ta ya hana ta wuce wa, "haba Umma haba Umma ki ƙyale ta". A fusace tace, "to bari uban naka ya dawo barin gidan nan zata yi". Sai ta wuce fuuu ta nufi kichen Shi kuma ɗakin Murjanan ya wuce zai shiga, sai dai MEEMAN ta garƙame ƙofan da keey, dole ya haƙura ya wuce nasa ɗakin.                   MEEMA bata buɗe ɗakin ba har sanda ta ji muryan Murjana kafin ta zo ta buɗe mata ta juya ta koma Da kallo Murjana ta bi bayan ta tana ƙare wa rigan jikin ta kallo, har ta shiga ciki ta kasa ɗauke ido a kan rigan domin yanda take matuƙar son irin rigan a rayuwar ta, sai dai har yanzu bata mallake sa ba don har kasuwa suka je a lokacin ita da Habiba but basu samu ba, dole suka haƙura tunda a lokacin sun so suyi ankon ta ne sanda za'a yi auren Amina. Cire kayan ta tayi ta sanya riga da skert na atamfa kafin ta fice ɗakin. Can sai ga ta ta shigo a lokacin MEEMA ta buɗe Trolly ɗin ta ta ciro computern ta ta koma ta zauna. Tsaki ta ja tana ɗauke kai daga kallon ta Ita kuma MEEMAN sai a lokacin ma ta ɗago da idanun ta ta dube ta, kawar da kai tayi ta ci gaba da abin da take yi While Murjana tuni ta sake fice wa tunda dama wayan ta ta dawo ɗauka Fitan ta babu daɗe wa Habibah ta shigo tana kiran sunan MEEMAN fuskar ta ɗauke da fara'a Itama ganin ta yasa ta tsayar da abinda take yi tana murmusawa "Sister I miss you so much, I can't bear to say let me come and see you." Tayi maganar bayan ta zauna a gefen MEEMA ta riƙe hannun ta Sitll da murmushi a fuskar ta tace, "me too". "But your dress looks good on me, and it looks great on you. You are so beautiful." Kallon ta kawai tayi bata ce komi ba illa murmusa wa da take yi "Aren't you working? Because we're going to our Part today stay for us there, I'll be happy with that". Jinjina kanta tayi kafin tace, "ok I will go". Ta ƙare maganar da rufe computern tana ɗauka ta tashi ta mayar a cikin Trolly ɗin ta, sai ta zaro irin rigan dake jikin ta sak sai dai shi blue color ne, ta kalli Habiban dake zaune tace, "take it's for you". "Wow! Thank you so much. Thanks again". Tafaɗa cikin farin ciki bayan da ta taso ta amsa rigan "Don't worry there is no gratitude between us." Itama MEEMAN tafaɗa cikin murmushi kana ta mayar da Trollyn ta rufe sannan ta tashi tana kallon ta tace, "ok let's go".            Suna fita Habibah da ta hangi Murjana zaune a kan dainning, da gudu ta isa wurin ta tana shaida mata kyautar rigan da MEEMA ta bata Yayinda MEEMAN ke tsaye a wurin da ta barta bata motsa ba tana kallon su, sai dai a yanzu ɗin murmushin fuskar ta ya gushe Ita Murjana taɓe baki tayi cike da isa tace, "ai yayi miki kyau tunda kin je kin roƙe ta kin zubar mana da mutunci, ke dai wlh Habibah baki yi ba a rayuwa". Sai ta ja tsaki tana banka mata harara ta mayar da hankalin ta kan abincin ta Habibah da ta saki baki tana kallon ta sai tace, "to fa! Gaskiya Murjana akwai gyara a lamarin ki, har yanzu baza ki dena wannan ɗabi'an naki ba bayan kin san da cewa ita ƴar uwan ki ce, to Ni meye ma a wuri na don na roƙe ta ai kin san Ni ba irin ki bace domin ba Ni da girman kai". "To kar dai ki gaya min magana don Allah ki tashi min akai". Tsaki kawai Habiban ta ja tana juya wa ta wuce wurin MEEMAN da har yanzu idanuwan nata a kan su suke, bata iya mata magana ba sai jan hannun ta da tayi suka fice.            Suna fita Murjanan ta tashi da sauri ta nufi ƙofan ta leƙa su, ganin da tayi sun bi hanyar Part ɗin su Habiban sai ta koma ta rufe ƙofan ta wuce ɗakin ta da sauri, tana shiga ta nufi wajen Trollyn MEEMAN ta saka hannu zata buɗe. [10/10, 3:41 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED ND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_17*                Koda tayi ƙoƙarin buɗe wa ya ƙi buɗuwa dole sai ta saka code, hakan yasa ta saka sunan Zulaiha but ya ƙi buɗe wa, sai da ta tsaya tayi tunani kafin ta tuna sunan da ake kiran MEEMA da shi, shima ta saka ya ƙi, ta saka sunan mahaifin ta Faruk nan ma ya ƙi buɗe wa, ta saka sunan Daddy domin a tunanin ta haka MEEMAN take kiran sunan Mahaifin ta but nan ma ya ƙi. The same ƙaramin jakan shima da akwai code, cike da jin haushi ta tashi ta fice sabida rashin cikan burin ta, amma dai a sannu a sannu zata riƙa sanya mata idanu domin ta gane Numban da take sanya wa. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️              Suna shiga Part ɗin su Habiban babu kowa a parlour'n, sai tace mata, "she just seat there and called her mother." koda ta je tana Toilet tana wanka shiyasa ta dawo tana mata murmushi tace, "Come, let's go to my room." Tashi MEEMAN tayi ta bi bayan ta suka shiga ɗakin Habiban Nuna mata kan gadon ta tayi tace mata, "set". Sannan ta fice ta ɗauko mata Fresh Yo me sanyi ta haɗo da Cup, zuba mata tayi ta miƙa mata tace, "take drink". Murmushi MEEMAN tayi mata ta sanya hannu ta amsa tana me furta, "shukran". Kafin ta sanya a baki ta ɗan kurɓa kaɗan Habibah cike da fara'a tace, "You can also teach me Arabic because I really like it." "Ok insha Allah If you want I will teach you". "Thanks. But I want you to tell me about your country. In the past we wanted to come but Baba refused to bring us." Murmushi kaɗai MEEMAN tayi bata ce komi ba Habiban na shirin magana sai ga Inna ta tura ƙofan ta shigo, kallon su tayi fuska a ɗaure tace, "uban me wannan yarinyan ta zo min a nan? Ke kika kawo ta ko Habibah ban miki kashedi ki fita harkan ta ba?" Tura baki Habiban tayi tace, "kai Inna Wai me tayi muku ne da kuka tsane ta? Ni dai ina son ta tunda ƴar uwata ce kuma idan aka tsaga jini na dole sai an ga nata a ciki.." "Uban ki tayi mana, ki je ki tambayi uban ki sai ya faɗa miki abinda tayi, tun wuri ki sallame ta ta bar min gida tun kafin in saɓa miki wlh, kuma ki zo ki tattara kayan ki ki wuce gidan Amina tunda ke ba kya jin magana, gwara ki je can ki zauna da ita ki riƙa mata aiki. Ki zo ki wuce kar ki sake kuma in dawo in tarar da ita wlh na gaya miki". Bata jira cewar ta ba ta ficewar ta Gaba ɗaya zuciyar Habiba babu daɗi don har ƙwalla ne suka taru mata a idanu, dole ta mayar da su ta saka wa fuskar ta murmushi saboda kallon da MEEMAN take mata tace, "Don't worry. Inna is talking about the job she did for me." Gyaɗa mata kai kawai tayi ba tare da tace uffan ba.            Shiru ne ya ratsa saboda Habibah ta kasa yadda zata yi ta sanar mata, "Let them go". Tun da ita ta kawo ta kuma yanzu idan tace mata, "su tafi." Zata iya gane Innar ta ce ta kore ta Ita kanta MEEMAN duk da bata yarda da abun da Habiban ta sanar mata ba domin a jikin ta ta ji cewa faɗan da Innar ta yiwa Habibah a kanta ne. Shiyasa ta tashi tana kallon ta tace, "I'm leaving because I have a job. " "Ok, let's go with you." Habiban tafaɗa tana mata murmushi Fita suka yi ta kaita har bakin ƙofan su Murjana, bata shiga ba tayi mata sallama ta koma Ita kuma MEEMAN ta buɗe ta shiga Umma da Murjana ce a Parlour'n while Umma tana sanar mata da abun da ya faru ɗazu. Shiyasa yanzu da ganin MEEMAN sai Murjana tace mata, "Zulaiha, come here, Ummah she's calling you. " Tsaya wa tayi tana kallon su, sai kuma ta taka ta isa wurin su ta tsaya ƙiƙam a kansu tana kallon su Murjana tace, "Umma says she will not guarantee that you will stay in this house. You have to go out to work. It is not possible for you to sit on the room of a girl who is being cooked in your mouth and eat and then go back to bed, you have to do the housework since my mother gave it to you." "Work?" According to MEEMAN full of surprise on her face "Yes working or you Don't do it?" "Na'am I can't". Tayi maganar tana juya wa ta wuce ɗaki. Tana jin Murjanan na zagin ta but bata ko juya ba har ta shige Umma tace, "wai me tace ne?" "Cewa tayi wai baza ta iya ba, ki ji fa Umma?" Ƙwafa Umman tayi tace, "bar Ni da ita bari Abban naku ya dawo ai ya kusa zuwa. Je ki kira min Sajjad a ɗaki". Tashi tayi ta wuce ɗakin Sajjad ɗin, koda ta je ta ganshi a kwance a saman gado yana ta sharan barci. Hannu ta sanya ta soma tashin shi tana kiran sunan shi Daƙyar ya buɗe ido ya zuba mata yana kallon ta "Umma na kiran ka". Shiru yayi kawai yana kallon ta Ita kuma ta juya ta fice abin ta, ta koma wajen Umma tana sake zuga ta a kan MEEMAN A lokacin da Sajjad ya fito shima Abban ya dawo Sannu da zuwa suka yi masa Ya amsa yana zama cike da gajiya Umma ta tashi ta kawo masa ruwa kana ta zauna tana kallon sa tace, "dama yanzu jiran ka nake yi Abban Sajjad, a kan wannan yarinyan da ka kawo ta ka ajiye min babu aikin fari bare na baƙi haka zata zauna min a gida wato? Kuma ɗazu na ce tayi min aiki ƙiri-ƙiri Sajjad yace baza ta yi ba, to Ni ban gane abin da ake nufi da ita ba domin wlh baza ta zauna min a sashi ba ta aikin komi ba sai dai ta ci ta sha abun da ta iya kenan, idan haka ne sai dai ta koma sashin Zubairu gaskiya". Sajjad da ya buɗe baki ya soma magana Abba ya katse shi da cewa, "kayi shiru Sajjad ban son jin bakin ka. Ke kuma Jamila meye ne na son takura mata don Allah? Mene ne a kan aiki ca nake yi na ce zan kawo miki me aiki but kika ƙi? To ki barta kawai ta zauna tunda ko kin saka ta na tabbata bata iya ba, ba na son ki takura mata don Allah saboda zaki iya rusa mana shirin mu". "Abba wai meye shirin naku?" Cewar Sajjad "Ka bari zuwa anjima zan sanar maka, sannan zancen auren ku mun tsayar da shi nan da wata ɗaya me zuwa domin so muke yi ayi-ayi". Umma zata yi magana ya katse ta da cewa, "Please Jamila ba na son musu kiyi abin da nace miki kawai, taso mu je ɗaki akwai maganar da zan faɗa miki". Ya ƙare maganar da tashi tsaye Haka ta tashi itama ta bi bayan sa kamar zata fashe Suna shige wa ɗaki Murjana ta bi Sajjad ɗin da kallo dake ta faman farin ciki sai tace, "wai Yaya don Allah me ka gani a wurin yarinyan nan da zaka aure ta? In fact ma su Abba fa so suke yi su amshi kaf dukiyar ta su kora ta ta bar gidan nan". Fara'an fuskar sa ne ta gushe yana kallon ta yace, "whattt Are You saying? Ban fahimta ba?" Sai a lokacin ma ta gane katoɓaran da tayi sai tayi saurin cewa, "suna so ne su amshi dukiyar ta su mallaki komi nata ya dawo hannun su shiyasa ka ga sun bar ta ta zauna, amma na san tunda ka kawo zancen auren ta sabida kai ne fa kawai zasu iya barin ta a gidan nan, kuma na san Abban zai buƙaci ka taimaka musu idan ta zama matar ka tunda ta ƙi yarda da su". Shiru Sajjad ɗin yayi be ce komi ba illa tunani da ya faɗa, sai da Murjanan tayi masa magana kafin ya ɗago ya kalle ta yace, "to Ni ina ruwa na idan har zan aure ta? Su dukiyar ta suke so Ni kuma ita nake so, in dai zasu bar Ni in aure ta wannan me sauƙi ne ai, bari in je wurin Abban." ya tashi ya wuce ɗakin Abban da ya ga sun shiga Itama Murjanan bin Bayan sa tayi da sauri.       ********** *****       MEEMA da ta shiga ɗakin; computern ta ta ɗauko dana Abee ɗin ta ta ci gaba da aiki, sai dai gaba ɗaya fuskar ta babu wani walwala aikin kawai take yi but tana tuna abubuwan da Murjana ta gama sanar mata. Tana ganin zaman ta a gidan ya kusa zuwa ƙarshe idan har zasu takura mata... Shigowar Murjana ya dawo da ita cikin hayyacin ta, da sauri ta rufe computern ganin ta a gaban ta tana kallon cikin computern Wayance wa Murjanan tayi tana sakin guntun murmushi da cewa, "Please barrow me your phone because I don't have a card in my own, I want to make a phone call with my friend's". Mamaki ne ya hana MEEMAN motsi illa kallon ta da take yi. Bata ce komi ba dai ta ɗauki wayan ta miƙa mata Sai da tace, "You did not remove the code." Sannan ne ta tuna ta cire mata ta miƙa mata Murjana ta so ta ga yanda take cirewan ne, but yanayin yanda take sauri wajen danna code ɗin yasa bata fahimci komi ba, dole ta amshi wayan don kar ta gane wani abu, ta samu wuri a gefen gadon ta zauna sannan ta saka Numban Abba ta kira sa. Yana peaking tace dashi, "hello Murjana ce". Shiru tayi tana sauraron sa sai kuma tace, "eh na amsa wayan amma ban ga yadda ta cire ba"... "Ok to". Daga nan sai ta katse wayan ta goge Numban ta miƙa mata tana sakin guntun murmushi da cewa, "thanks". Gyaɗa mata kai kawai tayi ta amshi wayan ta ajiye, sai dai ta kasa ci gaba da abun da take yi domin har yanzu mamakin ta take yi. Ganin ta ƙi tashi a wurin sai ma kwanciya da tayi shiyasa ta kashe computern tare da miƙe wa ta kai ta ajiye a cikin Trolly ɗin ta, sai ta koma can gefen gadon ta soma dealing Numban Ishaq, sai dai har yanzu ba ya shiga that's why ta mayar da akalan kiran ga Esha. Gyara zaman ta tayi jin ta ɗauka ta sauya harshe zuwa larabci suka soma waya, sun jima suna waya duk a kan Ishaq ne da yanda za'a yi Eshan ta je gidan su ta duba mata shi, sai ta samo mata Numban shi Murjana na zaune tana jin ta sai dai ba ta fahimtan komi shiyasa ta tashi ta fice Fitan ta yasa MEEMAN ta tsakaita wayan tare da yin ma Esha sallama sannan ta ajiye wayan. Shiru tayi tana me faɗa wa tunani, a haka har aka kira sallah ta tashi tayi ta koma ta sake kwanciya, ko fita ta ci abinci ta ƙi yi Sai ga Murjanan ta zo kiran ta, "su ci abinci". She looks at her in amazement, sai dai bata ce komi ba and she got up and followed her Suna zaune duk kan su a saman dainning Da sauri Sajjad ya tashi ya ja mata kujeran kusa da shi yana mata murmushi da cewa, "have a seat Baby". Ko kallon sa bata yi ba ta samu wuri ta zauna "Daughter, don't go into the room. You sit here with your siblings, stay in them and talk to them ok?" Inji Abba yana kallon ta da murmushi Jinjina kanta tayi kawai ba tare da tace uffan ba Sajjad da ya ɗauki Plate zai yi serving ɗin ta yace, "What will you eat if I pour it on you?" "Nothing". Abba said, "you mean you don't eat anything?" "I'll have some tea." "Tea is not food Daughter. Carry and eat ok?" Still kanta ta jinjina masa Sai yace, "Sajjad serve her". "Ok Abba". Shi ya zuba mata jollof rice ɗin tare da veggies ya tura mata a gaban ta Bata ce komi ba ta ɗauki spoon ta soma ci kaɗan-kaɗan don ko kwatan cokalin ba ta iya cuko sa Shiru wurin ya ɗauka kowa sai cin abincin sa yake yi, while Sajjad gaba ɗaya hankalin sa na kan MEEMA, sosai yanda take cin abincin nata ya ɗauki hankalin sa har yana manta wa da shima abincin yake ci Sai da Murjana ta bugi cokalin sa sannan ya dawo hayyacin sa, "kai yaya ka mayar da hankali a kan abincin ka ba guduwa zata yi ba kuna tare". Hararan ta yayi yana langaɓe kai ya kalli Umma yace, "Umma ki ce mata ta fita harka ta yarinyan nan". Taɓe baki ita kuma tayi bata ce komi ba illa abincin ta da take kaiwa baki fuska babu walwala Murjana tace, "Yaya ya kamata ka kaimu shopping da ita hakan zai saka mu sake shiga jikin ta, ko ya Abba?" "Yes haka ne Murjana," sai ya kalli MEEMAN yace, "Daughter, are you going shopping with your siblings and seeing the city." MEEMA da ta ɗago kai tana kallon sa kasa cewa komi tayi. Sai da ya sake maimaita mata sannan tace, "ok". Ta mayar da hankalin ta kan abincin da take ta faman cakala. Ita ta soma tashi ta wuce ɗaki Hakan yasa da sauri Murjana ta tashi ta bi bayan ta. Tana shiga ɗakin ta ganta a zaune sai tace, "get ready to go don't Bro Sajjad hear us silently". Bata ce komi ba ta miƙe ta shiga Toilet ɗin, wanka tayi bayan ta fito sai Murjana ta shiga MEEMA tayi shirin ta kamar ko yaushe yanda ta saba, bayan ta saka riga da wando sai ta ɗauki Abaya baƙa me kamar alkyabba ta sanya, ta yane kanta da farin gyale me Stones wanda ya ƙara fito da cuty face ɗin ta sosai ta ƙara yin fayau kasancewar babu abinda ta sanya, babu wani annuri a face ɗin ta haka suka fice a ɗakin ita da Murjana Sajjad dake jiran su a Parlour tun fitowar su ya kasa ɗauke ido a kan MEEMA, gaskiya Allah yayi diri a nan wurin, yana rasa nutsuwar sa a duk sanda yayi tozali da ita ji yake yi kamar ya je ya haɗiye ta tsaban shauƙin da yake ji a kanta, har yana jin kamar bazai iya jure har nan da one month be mallake ta ba, be san ya zai yi da tarin buƙatuwar ta a zuciyar sa ba. Daƙyar ya iya control kansa suka fice a gidan bayan sun yiwa su Abba Good bye Da suka fita MEEMA baya tayi ninyan shige wa sai Sajjad ɗin yace, "ta dawo gaba". Tsaya wa tayi tana kallon sa while tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta Shi kuma murmushi yayi mata yana sake roƙon ta a kan, "She Return the front seat". Kasancewar Murjana tuni ta shige baya shiyasa ta buɗe gidan gaba ta shiga A haka ya ja motan suka fice a gidan Duk inda suka bi idanun MEEMA na kai, sai kallon yanayin garin take yi duk da ba wai farin ciki take ji a zuciyar ta ba Hakan da Sajjad ɗin ya gani ne yasa yake mata bayanin duk inda suka wuce Sai dai bata kula sa ba har suka kai wani ƙaton shop Mall suka fito. Tana biye da su duk inda suka sanya ƙafa har suka shiga ciki. Sai dai duk yanda suka yi da ita, "ta dauki abun da take so." but ta ƙi ɗauka Dole Sajjad da kansa ya dinga jidan mata abubuwan duk da ya ga yayi masa Itama ta fannin Murjana duk abinda ta ɗauka tana daukar mata, domin tana ganin ta hakan ne zata sake shiga jikin ta sosai idan ta bata kayan a matsayin gift ɗin ta.         Har suka gama suka fito suka wuce wajen shan Ice cream, nan ma MEEMA ta ƙi taɓa duk abin da suka bata, ce musu tayi, "she does not want to drink anything." Dole suka kyale ta sabida banza tayi da su daga baya Murjana tace, "gaskiya Yaya kana da jan aiki a gaban ka wajen yarinyan nan, Allah ba na tunanin zata so ka ko kaɗan, kana gani fa abun da take yi ko magana wannan bata taɓa yin maka ba". Sajjad da kamar zai yi kuka yace, "Murjana nima ban san meyasa take min haka ba? Kina ganin akwai makusa a jiki na da har zata ƙi so na?" Murmushin ƙeta tayi kafin tace, "babu Yaya sai dai kawai ina tunanin har yanzu bata saba da mu bane, tabbas akwai abun da ke ranta da har ta ƙi sakin jikin ta da mu, amma ina ga duk sanda ka aure ta sai yanda ka juya ta Yaya, nayi maka alƙawari sai ka juya ta kamar waina domin sai ta koma a tafin hannun ka, kawai ka bari lokaci yayi Yaya kai da kanka zaka sauke mata duk wani abun da ke kanta". Dariya yayi yana ɗan shafa tulin gashin kansa, sai ya kalli MEEMAN da hankalin ta ke kan waya amma tana sauraron abun da suke faɗi, sai dai kasancewar ba ta gane abun da suke cewa shiyasa bata san da ita suke yi ba. "Ƙanwata nima wannan lokacin nake jira, abu ɗaya ne yake hana Ni aikata abin da ke raina a halin yanzu a kanta, sabida kawai ina son mallakan ta that's why komi nake yi a sannu, ai kamar yau ne wata ɗayan zai cika." Sai ya ci je leɓe yana faɗin, "zata san waye Sajjad Aliyu Ahmad Riskuwa". Dariya Murjanan ta sheƙe da shi tana ɗago Glass cup ɗin hannun ta dake cike da Ice cream ta miƙa masa suka haɗa Cup ɗin sannan suka ci gaba da sha suna ci gaba da hiran su. Daga ƙarshe gida suka wuce bayan sun gama zagaye-zagayen su.    [10/10, 3:45 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK* 💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *NO_18* Tun daga ranan MEEMA ta soma ganin canji a gidan, sosai Murjana ta shiga jikin ta duk inda ta sanya ƙafa tana biye da ita, tun ba ta sakar mata fuska har dai itama ta saki jiki da ita sosai tunda har ɗaukar ta take yi su fita wajen friends ɗin ta tare, ko kuma wajen dangin su suyi ta yawo hakan yasa MEEMAN ta sake sakin jiki da ita har suka shaƙu sosai Gefe ɗaya kuma ana ta shirye-shiryen auren ta ita da Sajjad but babu wanda ya sanar mata sai da ana jibi biki Habiba ta dawo gidan saboda bikin, da ɗokin ta ta je wurin MEEMAN tana tsokanar ta da, "Amarya Amarya." A nan ne abun ya bata mamaki take tambayar ta, "Who is the Bride?" "Oh you mean you don't know who bride is? I know everything wlh, I just wish you the best of luck you are lucky you got Bro Sajjad, I congratulate you because you are compatible with each other". MEEMA fa kanta ya ƙulle cike da rashin fahimta tace, "I do not understand you. Please explain to me?" In Surprised Habiba said, "You mean you don't know this week you're going to get married? Are you kidding me?" Quickly MEEMA stood up looking at Habiba but she couldn't say anything While Habiba itama miƙe wa tsaye tayi ta kamo hannun ta ta mayar da ita tana cewa, "What's going on? What's wrong with you?" Idanuwan ta ciko wa suka yi da hawaye still tana kallon Habiban tace, "I don't know what you mean. You said I was going to get married but who am I going to get married without my knowledge?" "You and Sajjad, I think you are in love, and any service you see in this house is for your marriage." "I don't know about it. I don't love Sajjad. In fact I hate him in my heart. I don't love him! How can I trust him to marry me? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ta ƙare maganar tana tashi tsaye da sauri duk ta gama rikice wa. Sai kuma ta juyo a firgice tana kallon Habiban da cewa, "I will not marry him. I hate him! I have to leave this house today. I will not stay." Ta wuce wajen kayan ta cikin ruɗe wa har hawaye sun soma zubo mata Da sauri Habiba ta je ta riƙo ta ta dawo da ita bakin gadon suka zauna, "Calm down Zulaiha, I understand your situation but there is no way you can leave this house now, be patient please stay". "Do you want me to marry him? Do you want me to marry someone I don't like?" Jinjina mata kai tayi tana kallon ta and she Said, "yeah but..." "Noo! it is not possible. I have someone I love, and Sajjad is not one of the few men I can marry. How can they marry me without my knowledge? It is not possible until I leave this house." Sai ta saki kuka tana kifa fuskar ta a tafukan hannayen ta Sosai Habibah ta rikice ganin yanda MEEMAN ke kuka sosai. Duk rarrashin da tayi mata taƙi yin shiru. Buga ƙofan da ake yi yasa Habiban ta sake rikice wa tana kallon MEEMA a firgice tace, "Please Zulaiha be quiet, I will help you to leave this house but be quiet so no one understands". Kallon ta MEEMAN take yi da idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur sai tsiyayar da hawaye take yi Hannu ta saka ta share mata hawayen tana cewa, "Don't let anyone understand what's going on. Please pretend there's nothing ok?" Gyaɗa mata kai tayi itama tana sanya hannun wajen share face ɗin nata tare da gyara wa Ita kuma Habiba zuwa tayi ta buɗe ƙofan. Murjana ta gani a tsaye sai tayi saurin sakin murmushi da cewa, "har kin dawo?" "Yes na dawo, wai me kuke yi ina ta buga ƙofa kun yi banza da Ni?" Tayi maganar tana ƙoƙarin shige wa Jirga mata tayi a hanyar tana me rufo ƙofan da cewa, "babu komi muna hira ne da Zulaiha, dama yanzu nima nake son in tafi". Murjanan da ta shiga ɗakin suna haɗa idanu da MEEMA ta nufe ta da mamaki tana cewa, "Sister, what's wrong with you? I look at you with tears in your eyes". Shiru MEEMA tayi tana kallon ta sai kuma ta mayar da idanun ta ga Habiba, zata buɗe baki tayi magana kenan Sai Habiban tayi saurin zama kusa da ita tana cewa, "wani abu ne ya faɗa mata a idon shiyasa kika ga sun yi ja, yanzu na gama cire mata har kuka tayi min kamar wata Baby". Ta ƙare maganar tana dariya Itama Murjanan dariya ta saki tana cewa, "I'm sorry sister". MEEMAN murmushi kaɗai tayi mata ba tare da tace uffan ba don bata san me Habiban ta faɗa mata ba "Ok yanzu ki tashi mu je Part ɗin ku akwai kayan da na kai can zamu haɗa a can, kin san su Khalid zasu zo min bikin nan, akwai tanadin da nayi musu but ba na son su Umma su gani don ba wanda zan ba shi". Dariya Habibah tayi tace, "to mu je". Har ta tashi sai kuma ta kalli MEEMAN tace, "will you follow us?" Murjana tayi saurin cewa, "No, leave her let's go. We'll be back soon." Har suka fita MEEMA bata ce da su komi ba. Shiru tayi tana lumshe idanun ta tears welled up in her eyes Habiba ce ta dawo ɗakin da sauri tana ce mata, "sorry i'll help you later, but please don't go and stay till i come back ok?" Gyaɗa mata kai tayi tana me aza kanta saman pilow ta mayar da idanun ta ta rufe ruff Ita kuma Habiban ta fita ta barta a ɗakin. Zuwa magriba sai ga ta ta dawo, bata bari kowa ya ga shigowar ta ba har Murjana don a lokacin tana ɗakin Umma, ta shiga da sauri tace ma MEEMAN, "She picked up her Trolley and left". Ita ta taimaka mata da ƙaramin jakar suka fice har wajen gidan. Kasancewar an shiga sallah shiyasa babu wanda ya gansu. Rungume ta tayi tana hawaye tare da kallon ta tace, "Where are you going from now? I don't want you to go because I will miss you!" With tears in her eyes, she said, "I miss you too! but I have no choice but to go back to Riyadh Saudi Arabia." "No, please, I beg you not to go back and live alone like everyone else. If they refuse to hold you honestly they want to marry you. I know your mother will hold you in both hands. Please go back it will be better for you. If you live alone you will not be happy. Stay here in Nigeria or one day we will see each other please." Habiba ta ƙare maganar hawaye sosai a wannan lokacin suna fitar mata a idanu MEEMA kasa magana tayi kasancewar itama shashsheƙan kukan da take yi ya ci ƙarfin ta. Tana shirin zame hannayen ta ba tare da tace da ita uffan ba Sai Habiban ta sake rungume ta kafin ta sake ta tana share hawayen fuskar ta da bayan hannun ta, ta ɗaga mata hannu tana cewa, "Please stay here in Nigeria, hurry up and leave here to let Abba come out to see you". Daga haka ta juya ta shige gida da sauri Itama MEEMAN jan Trolley ɗin ta tayi tana rataye da ƙaramin a hammatar ta taci gaba da tafiya. Har sai da ta fita titi kafin ta tsaya tana faman waige-waige. Bata sha wahala ba ta samu keke napep tace, "he peak her with hotel". Kasancewar ta ga dare yayi baza ta iya zuwa wani wuri da daren nan ba. Kai tsaye ana kaita hotel ɗin ta kama ɗaki ta shiga. Zuwa washe gari zata wuce Kaduna tuna wa da tayi akwai mahaifiyar Ummee ɗin ta da ƙanin ta, ko a wajen su zata iya zama ba sai a wajen Ummeen ta ba, duk da bata so yanke wannan shawaran ba amma tuna wasiyyar mahaifin ta da kuma maganar Habiba yasa taga ya dace ta koma wajen su, bata da kowa a can Riyadh baza ta iya rayuwa ita kaɗai ba. Da safe bayan ta gama shirya wa ta fito ta sami me napep ya kaita tasha inda zata samu motan Kaduna. Wannan karon ma drop ta ɗauka suka wuce Kaduna, wajen goshin magriba suka isa. A cikin G.R.A Ummeen ta take zaune ita da Mahaifiyar ta da ƙanin ta, shi yanzu ƙanin nata ya koma Abuja da zama da shi da Matar sa da ɗan su guda ɗaya, wajen shekaru shidda kenan da aka tura sa yaƙi ya tafi ya bar matar tasa a can Abujan kasancewar tana aiki shiyasa bata dawo nan Kaduna ba, sannan kuma ɗan su na school wannan dalilin ne ya zaunar da su can, sai dai jefi-jefi tana zuwa Kadunan ta gaishe su. Yanzu haka mahaifiyar Ummee me suna Hajiya Halima suna kiran ta da Hajiya, tana cikin halin rashin lafiya na hawan jini wanda yasa har ta rasa ƙafafuwan ta tana zaune a wheelchair ne. Mahaifin su Ummeen shi ya daɗe da rasuwa, su biyu Hajiya ta haifa daga ita sai ƙanin ta Captain Hashim. Kuma mahaifin su dai-dai gwargwado ya bar musu dukiya me ɗumbin yawa, don gidan su babban gida ne me hawa biyu. Part ɗin Hashim da matar sa daban duk a ciki idan ya zo hutu suna sauka a nan, sannan sai na Hajiya sai kuma inda Ummee ke zaune a halin yanzu, tana aiki ne a wani Company tun dawowar ta daga Riyadh. Kwatancen da MEEMA ta yiwa Me motan be sha wahala ba wajen tambayar mutanen garin, tunda sun rigada sun shiga G.R.A ɗin, duk da MEEMA bata taɓa zuwa ba amma ta riƙe sunan gidan su Ummeen nata sosai tunda ba wani ɓoyayye bane, har Numban gidan sai da Abee ya sanar mata da zai rasu hakan yasa nan da nan suka gano gidan. Bayan ta sauka ta sallami me motan ta ɗauki kayan ta ta taka a hankali zuwa bakin Gate ɗin. Ta jima a wurin tana ta kallon ƙofar gidan ta kasa buga wa, lokaci ɗaya idanun ta suka cika da hawaye yayinda zaciyar ta ta soma zugi tsaban ƙuncin da ya ziyarce ta a halin Yanzu ɗin. Ba komi ya haifar mata da hakan ba sai tuna wa da tayi a yau zata haɗu da mahaifiyar ta wacce ta guje su a cikin rayuwar su gaba ɗaya, kuma bata taɓa tunanin ta neme su ba har ga shi Abee ɗin ta ya bar duniya da baƙin cikin ta, ta kasa gane wani irin abu ne Abee ya aikata mata da har ta zaɓi tayi masa wannan mummunan hukuncin? Baƙin ciki da ƙuncin da take ji a wannan lokacin tamkar yanzu ne Ummeen ta tafi ta bar su, sanadin ta sun rasa farin cikin su wanda hakan yasa ta rasa mafi soyuwa a rayuwar ta wato Abee ɗin ta. Sai kawai ta fashe da kuka sosai har bata iya ganin komi tsaban yanda hawayen suke kwaranya a face ɗin ta. Hannu ta sanya ta dinga share wa yayinda wani tuƙuƙin baƙin ciki ke kai komo a maƙogwaron ta. Ta kasa ɗaga ƙafafu ta isa bakin Gate ɗin bare ta buga. Tana nan tsaye wadda ta fi mintuna talatin a wurin har an kira sallan magriba ana shirin shiga A lokacin ne aka buɗe Gate ɗin gidan wanda me gadi ne da shi da masu hidiman gidan su biyu suka fito zasu wuce masallaci. Da kallo suka bi ta ganin ta da suka yi a wannan yanayin kuma a jikin gidan su. Sai dai babu wanda ya samu halin yin magana illa idanu da suke bin ta da shi kamar wacce basu taɓa ganin halitta makamanciyar nata ba, gaba ɗaya a cikin zuciyoyin su mamakin ganin Balarabiya a bakin ƙofar gidan suke yi. A haka har suka wuce ta suna waigen ta While MEEMA tunda tayi musu kallo ɗaya taci gaba da share hawayen ta kafin ta ja ƙafafu a hankali ta isa ƙaramin ƙofan ta tura ta shige. Kallon gidan take faman yi tana tafiya a hankali har ta isa ƙofar da zata shiga gidan, a nan ma ta ɓata lokaci kafin ta sanya hannun ta dake faman rawa ta soma Nocking. Kasancewar a hankali take Nocking ɗin shiyasa sai da ta ɗau lokaci tana yi kafin a zo a buɗe mata Wata mata ce me jiki don a ƙalla zata kai shekaru arba'in, wanda daga gani ƴar aikin gidan ce. Tunda ta ɗaura ido a kan MEEMAN ta tsaya kallon ta, sai da ta gama ƙare mata kallon kafin tace, "baiwar Allah daga ina?" Ita MEEMA yanda bakin ta yayi mata nauyi shiyasa ta kasa yin magana illa zuba mata idon itama da tayi tana bin ta da kallo. Koda tayi mata maganar bata fahimci abun da tace ba amma hakan yasa ta buɗe baki a hankali tace, "May I come in?" Jin tayi turanci kuma bata gane ba kasancewar yanda take furta words ɗin sai Matar ta sake cewa, "to Ni gaskiya ba na jin ki ina zuwa". Sai ta juya ciki tana ce ma Hajiya dake zaune a kan wheelchair ɗin ta, "wata budurwa ce ta zo Hajiya, amma gaskiya ba na jin yaren nata, turanci ne ko wani yaren ne oho don maganar nata wani iri wlh, Idan kika ganta kamar ba ƴar nan bace, sanye da kayan Larabawa ta zo". Hajiya dariya tayi da cewa, "Kai Zabba'u kin cika Zabbo ta, wlh kin ci sunan ki. Idan ban dake memakon ki zauna kina min kwatancen ta ai gwara ki ce mata ta shigo kin bar ta a waje kuma". "To kuma fa haka ne Hajiya, to amma kin san yanda duniya babu gaskiya shiyasa gwara in soma sanar muku don wlh ban yarda da ita ba Ni daga kallon ta, sak bata yi kama da ƴar nan ba, yaren nata ma fa ban fahimci me tace ba don ba turanci bane ai da zan gane ko ya ya ne tunda ina jin kaɗan-kaɗan." "Ki dai zauna kiyi ta rattaba zance da Allah kin bar baiwar Allah a waje". Hajiya tafaɗa tana jan guntun tsaki Hakan yasa Zabba'un ta wuce da sauri bayan ta ce, "to kiyi haƙuri Hajiya kar ranki ya ɓaci, bari in CE ta shigo to". Tana zuwa bakin ƙofan tace da MEEMA, "shigo baiwar Allah". MEEMA da bata fahimci me tace ba ko motsi bata yi ba sai kallon ta da take yi Sai Zabba'un ta sake maimaita mata da gwarancin turancin ta tana sanar mata, "ta shigo ciki". A hankali ta taka ta shiga ciki idanun ta suna faɗa wa kan Hajiya wanda itama ta kafe ƙofar da kallo Da sauri ta furta, "Zulaiha ke ce?" Har gaban ta ta tako ta tsaya ba tare da ta furta komi ba illa son hana fitowar hawayen ta da suke maƙale a kwarmin idanun ta "Ya ki Jika ta, taho.. taho wuri na". Hajiya ta furta cike da rawan baki tsaban murnar ganin MEEMAN Yanda take ya fico ta da hannun ta ne yasa ta isa gare ta a hankali tana duƙa wa a gaban ta Hannayen ta ta kama cike da farin ciki kamar zata yi kuka tace, "Will I ever see you again? How did you get here? Who brought you? Where is your father?" Bata iya amsa mata ko kalma ɗaya ba duk da a ranta ta ɗan ji sanyi da yanayin karɓar da tayi mata, sannan kuma farin cikin da ta ga ya bayyana a fuskar ta yasa ta gane tana murna da zuwan ta. Shiyasa ta matsa sosai ta rungume ta hawayen idanun ta suna sauka kamar an kunna su Sosai itama Hajiyan ta sake ƙanƙame ta a lokacin tana kuka da sambatu Ita dai Zabba'u baki ta kama kawai tana kallon su. A lokaci ɗaya kuma sai ƙwaƙwalwan ta ta bata ƙila yarinyan Ummee ce, domin ta san da cewar tana da ɗiya kasancewar wani lokacin tana yawan jin suna ambatar ta, sai dai a zahiri bata taɓa ganin ta koda a hoto ne duk da ta daɗe a gidan tun kafin Ummee ta dawo Nigeria, shiyasa tayi tunanin ita ce ɗiyar Ummee duk da ba wai kama suke yi ba, amma Idan ka kalle ta tabbas zaka gane jinin ta ne. Sun jima a haka kafin Hajiyan ta sake ɗago ta tana me riƙe mata hannu da cewa, "Zulaiha, will we see you again? Your mother do not came to check on you, and I was sick and had legs, and your uncle was not in the country to go and check on you and your father, I hope he feels better?" Fashe wa tayi da kuka tana girgiza mata kai tace, "My father is dead. He is dead.. He is dead." Yanda kukan ya ci ƙarfin ta ta kasa ƙarisa zancen nata dole tayi shiru tana sake rungume ta a wannan lokacin tana kuka sosai Salati kawai Hajiya take yi tana bubbuga bayan ta. Sun jima a haka kafin ta ɗago ta taci gaba da rarrashin ta, sannan ta kalli Zabba'u da har yanzu tana wurin tana ta kallon su, tace da ita, "ki kawo mata ruwa ta sha sannan ki kira min Zulaiha a ɗaki". "To Hajiya". Ta amsa ta tana wuce wa wurin Fridge ɗin da sauri Ita kuma Hajiya hannu ta sanya tana share mata hawayen fuskar ta tana ci gaba da rarrashin ta, sannan ta ɗago ta ta zaunar da ita kan sofa dake jingine da wheelchair ɗin ta. Da Zabba'u ta kawo ruwan ita da kanta ta amsa ta bata ta sha tana sake shafa mata fuska cike da rarrashi Zabba'u da ta wuce kiran Ummee bata kai ga hawa benen ba ita Ummeen ta fito daga saman zata sauko, kyawu da zubi da tsari gami da haɗuwa da tsaban iya kwalliya shi zaka soma gani a tattare da ita, a kallon farko baza ka taɓa ce mata ta haura shekaru arba'in ba, but tsaban kyawun jikin ta da ɗaukan wanka irin nata sai kayi tunanin ƴar shakara talatin ne, sam bata da jikin manyanta. Tana sanye da lesi me uban tsada da tsantsan kyawu, gaba ɗaya hannayen ta da wuyan ta duk ta zuba sarƙa da awarwaron Gwal sai walwali suke yi, fuskar nan nata ya ɗau Powder duk da ba kwalliya ne a fuskar ba, yanda take tafiya zaka tabbatar da babban mace ce me aji sosai. Tun daga saman benen idanun ta suka sauka a kan MEEMA, sai dai bata gasgata itan bace kasancewar ba ta ganin fuskar ta sosai. Hakan yasa ta ɗan ƙara sauri wajen sauko wa tana son ƙaryata idanun ta. Sai dai bata gama ƙarisowa ba suka haɗa ido da MEEMAN wanda a lokaci ɗaya ta tsaya cak daga inda take tsaye. [10/10, 3:46 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_19*              Wasu sabbin hawaye ne suka wanke mata fuska saboda arba da tayi da fuskar mahaifiyar ta a yau, kimanin shekaru biyar da watanni kenan rabon da ta sake tozali da ita. yanda idanuwan ta suke mata zafi ne yasa ta mayar da idanun nata ta rufe ruf tana sauke numfashi daƙyar While itama Ummee tuni hawayen ne suka cika mata idanu, sai dai ta kasa samun ƙwarin gwiwan da zata iya tunkaran MEEMAN a halin yanzu, gaba ɗaya ta kasa motsa wa a inda take Inda Hajiya tace da ita, "ki ƙariso mana kin tsaya a wurin, ko zuwan nata ma baki yi murna da shi bane?" Girgiza kanta ta soma yi still hawaye na zuba a face ɗin ta, sai a lokacin ta samu damar taka wa ta iso gaban MEEMAN zata sanya hannu ta taɓa ta tare da furta, "My daughter..." Saurin janye jikin ta tayi tana tashi da sauri, ido cikin ido take kallon ta cike da wani irin yanayi da fushi a tattare da ita tace, "Don't touch me again! I am not your daughter because I will never be your daughter." Sai ta juya ga Hajiya cike da rawan murya a wannan lokacin tace, "She is not my mother. If she touches me again I will leave this house. I will enter the world wherever I am and, I will not stay here." Gaba ɗayan su shiru suka yi suna sauraron kukan ta da a yanzu take yi da ƙarfi wanda ke fita da ɓacin rai da tuƙuƙin baƙin cikin da ya kasance da ita tsawon shekaru Hajiya ce tayi ƙarfin halin kiran sunan Zabba'u tana bata umarnin, "ta kai MEEMAN ɗakin kusa da nata". Hakan yasa ta iso da sauri ta ja Trolley ɗin bayan ta ɗauki ƙaramin Hajiya ta yiwa MEEMAN bayanin, "she follow her." Bata ce komi ba ta bi bayan Zabba'un har ɗakin da zata kaita, a downstairs ne ɗakin bayan ka wuce dogon corridor zaka hangi ɗakuna guda biyar a jere, ɗaya daga ciki ta shigar da MEEMAN. Dayake ɗakin babu datti tunda a koda yaushe ana gyara wa, tana ajiye mata jakan ta ta fito ta bar ta.                     ********              "To kin gani abun da nake gudan miki kenan tuntuni Zulaiha, son zuciya da ruɗin ƙawaye yasa kin aikata mummunan aikin da zai ja miki dana-sani a rayuwa, yanzu ke baki ji kunya ba da kiran ta da kika yi a matsayin ɗiyar ki? Kin san kina son ta meyasa kika yanke wannan hukuncin? Dama na sha sanar miki akwai ranan da zaki yi nadama, tunda kika tafi kika bar su baki sake waiwayan su ba, sannan ni ba ƙafa ba bare in je in ga lafiyan su, wanda kuma zai je ɗin yanzu kusan shekaru shida kenan basu dawo ba, bamu da tabbacin yana raye a halin yanzu ko ba ya raye, wata huɗu kenan da wayan Hashim ba ta shiga, ba don haka ba da shi ne zai riƙa zuwa yana duba mana a halin da suke ciki. Ni na tabbata Faruk ya tafi da baƙin cikin ki a zuciya domin kin cutar da shi sosai, ya koma ga Allah ya bar ki a duniyar da kike ganin ya fi miki shi, mutum me ƙaunar ki amma kika kasa zama ki tallafi rayuwar sa da ɗiyar sa, wannan wani irin zuciya ce da ke Zulaiha? Anya kina da ɓurɓushin imani?" "Wlh Hajiya nayi matuƙar nadaman abin da na aikata, na san zuciya ta bata yi min adalci ba da har na yanke hukuncin barin su, amma wlh ina matuƙar nadama da abun da nayi musamman ma a yau..." Kukan da ya ci ƙarfin ta yasa a dole tayi shiru Hajiya tace, "hmm kaɗan ma kika gani, yanzu ga shi kin koya wa ɗiyar ki tsanar ki a zuciya, ba na tunanin a yanzu kina da wani sauran mutunci a idanun ta, wacce ta tafi ta bar ƴar ta tsawon lokaci babu waiwaya ai ba na tunanin akwai wani sauran soyayya, gwara ma ki tashi min a nan tun kafin raina ya ɓaci, kuma ban amince ki takura mata ba domin muddin ta bar gidan nan a sanadin ki wlh sai nayi mummunan saɓa miki Zulaiha". Daga haka Hajiyan ta kwaɗa wa Zabba'u kira. Tana zuwa tace mata, "ta mayar da ita ɗaki." Haka ta ja ta suka wuce ɗakin Hajiyar suka bar Ummee a wurin tana ta faman share hawaye. Zuciyar ta sosai take mata tuƙuƙi da baƙin ciki sabida fama abun da ke cikin ta. Ta jima a wurin ta rasa me ke mata daɗi, daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakin da aka sauke MEEMAN Tunda ta shiga ɗakin MEEMA ta sauke ido a kanta sai tayi saurin kawar da su tana sake haɗe rai sosai Ita kuma a hankali ta taka izuwa bakin gadon da take zaune, kasa zama tayi illa tsaya wa da tayi tana kallon ta yayinda idanuwan ta har yanzu suna da danshin hawaye. A hankali ta soma magana a cikin harshen turanci. "I know I was wrong with you and your father, and I do not know how to apologize to you. I was a mother who loved herself more than anyone else. I followed the deceptions and advice of my friends. I made a big mistake that I now know..." sai tayi shiru sabida kukan da ya taho mata sosai a yanzu ɗin. Daƙyar ta iya buɗe baki da zummar taci gaba Sai MEEMAN ta dakatar da ita wajen ɗaga mata hannu da cewa, "enough..! I do not want to hear your words in my ears, you are a tyrant in my place, you do not love me and you do not love my Abee, if you had faith you would never do that to us, how can I call you mother? Do you think that is appropriate? Tell me, do you think that is appropriate?" Ta ƙare zancen da wani irin ihu tana kuka sosai. Sai kuma ta haɗe hannayen ta wuri ɗaya tana haɗa su da fuskar ta tace, "please leave this place before my heart beats, I do not love you and I don't want to see you around me!" "Daughter..." "Please out". Tafaɗa cikin tsawa yayinda take kallon ta a wannan lokacin ido cikin ido hawaye na zuban mata Shiru Ummeen tayi ta kasa motsa wa, sai kuma a hankali ta juya ta fice har tana sake waigo ta Ita kuwa tuni ta kifa kanta a saman gadon ta soma rusa kuka sosai, ji take yi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu tsaban baƙin ciki, why Ummee zata yi mata haka? Anya ita uwa ce a gare ta da har ta zaɓi rabuwa da su? Ba ta tunanin akwai wata uwa makamanciyar nata uwar, shin wani hujja ne da take da shi da har zata tsallake tabar su alhalin suna matuƙar buƙatar ta? Tana ga rashin lafiyan Abee ɗin ta ba hujja bace da zata aikata musu haka, abun da take gani kawai Ummeen ta bata da imani, rashin imanin ta ne yasa ta aikata musu wannan abun, to, don me itama zata ɗauke ta a matsayin uwa? No hakan bazai taɓa yiwuwa ba domin tun sanda ta tsallake ta bar su itama ta cire ta daga zuciyar ta, a yanzu ita ba mahaifiyar ta bace, bata da kowa a yanzu sai ita kaɗai, a ko yaushe kuma hakan zata riƙa ɗauka... ta jima a nan zaune tana ta sharɓan kuka wanda har kanta ya soma mata zugin ciwo kafin ta shafa wa kanta lafiya ta haƙura, kiran sallan da ta ji ana yi shi ya ankarar da ita bata yi sallolin dake kanta ba, don haka ta tashi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala ta ciri hijabin ta ta soma rama sallolin ta Tana cikin yi ne Zabba'u ta shigo ɗakin, ganin tana sallah sai ta juya, babu jima wa kuma sai ta dawo da ƙaton faranti a hannun ta ta ajiye mata ta fice Ita kuma ta jima tana sallan, sai da ta haɗa da shafa'i da wutri sannan ta sallame sallan, ta zauna yin addu'o'i na tsawon lokaci kafin ta shafa, yunwan dake addabar ta shi ya sanya ta jawo farantin ta zuba abincin dake cikin coolar a cikin ƙaramin Plate, haka tayi ta tusa abincin a baki ba don yana mata daɗi ba, duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana cin abincin ko rabin Plate ɗin bata yi ba ta ture ta tashi tsaye. Wanka ta shiga tayi kafin ta sanya kayan barcin ta tabi lafiyar gado. A lokacin wajen ƙarfe 11:30pm. Na dare ne, sosai tunani suka bijiro mata a zuciya wadda yasa ta kasa barcin sai daƙyar ya sure ta daga baya. Tunda ta tashi da asuba tayi sallah ta sake komawa kasancewar akwai barcin sosai a idanun ta, bata farka ba har sai sha biyu saura domin Hajiya ta hana a taso ta har sai idan ita ce ta tashi, ta san tabbas akwai gajiya a tattare da ita. Koda ta tashi sai da tayi wanka ta shirya a cikin riga da skert na wani jan yadi me flowers da aka yi da kalan maroon color. Rigan tana da igiya ta baya wanda ta ɗaure shi, sai kuma gaban rigan a buɗe yake sai dai an saka raga-raga kalan maroon, shi kuma skert ɗin ya buɗe sosai tun daga saman ƙugun ta har ƙasa, sun mata cif sun fito mata da kyakykyawar surar jikin ta da Allah ya bata, while ta tufke gashin ta a ƙeya ta sanya ɗan kwalin kayan tayi Rolling da shi wanda ya saukar mata iya kafaɗun ta, exactly ta fito a tsantsan Balarabiyar ta. Koda ta gama shirya wa bata fita ba sai tayi zaman ta a kan gado, wayan ta dake kashe tun daren jiya ta ɗauka ta kunna, da saƙonni ta soma cin karo wanda ta fahimci Sajjad ne ya turo mata, domin kasancewar shi ya bata Simcard ɗin that's why ya mallaki Numban, a ko yaushe yana kiran ta but tunda ta san shi ne bata sake ɗauka ba, yanzu ɗin ma bata duba ko ɗaya ba illa zare layin da tayi ta karya shi biyu ta jefar. Miƙe wa tayi ta bar wayan a wurin ta zira room slippers ɗin ta da ta ciro su daga Trolley ɗinta ta fita. Ta cikin corridorn da ta san an biyo da ita ta nan ta fita sai ga ta a tsararren parlour'n gidan A lokacin Hajiya na zaune a Kan wheel chair ɗin ta tana karanta littafin Hisnul Muslim sanye da eyeglasses. Ganin ta yasa ta tsayar da karatun nata tana me yalwata fuskarta da murmushi tare da yiwa MEEMAN alamu da hannun ta alamun ta ƙariso gare ta A hankali ta taka izuwa wurin ta yayinda ta ɗan saki fuskarta kaɗan. Hannun Hajiyan da ta miƙa mata ta kama tare da ɗan ranƙwafa wa kaɗan ta sumbaci hannun cikin sassanyan muryan ta da a yanzu be fita ko kaɗan ta gaishe ta Sai da ta riƙo mata kafaɗun ta ta zaunar da ita a saman kujera kafin ta amsa ta cikin tsantsan fara'an da dole zaka gane tana a cikin farin ciki sosai, kana ta tambaye ta yanda ta kwana? A taƙaice ta bata amsa tana kallon ta Murya Hajiyan ta ɗaga ta kirayi Zabba'u Babu jima wa kuwa sai ga ta ta bayyana a gaban Hajiyan, cikin washe baki ta kalli MEEMAN tace, "Barka da safiya ƴar nan". Kasancewar da hausa tayi bata amsa ta ba Sai Hajiya tace, "ki riƙa mata magana da turanci ne saboda ba ta jin Hausa. Tukunna ki je ki haɗo mata Breakfast ɗin ta ki kawo mata nan sai ku gaisa daga baya". "To Hajiya". Ta amsa cikin sauri tana juya wa Ita kuma Hajiya ta kalli MEEMAN tace, "Now she'll bring you your Breakfast. Hope you stay home?" Guntun murmushi ta saki tana jinjina mata kai "Calm down, ok? Whatever you are want ask me directly, insha'Allah you will never touch Zulaiha. I am always with you." Still kanta ta sake ɗaga mata a lokacin idanun ta suna me ciko wa da hawaye Murmushi Hajiyan tayi mata, kana kuma ta mayar da kallon ta kan Zabba'u da ta kawo Breakfast ɗin a saman faranti. Still she keeps her eyes on MEEMA asking her, "what she wants?" "Tea alone is enough". Tafaɗa a hankali cikin muryan ta da har yanzu be washe ba sakamakon kukan da ta sha jiya Saka Zabba'u tayi ta haɗa mata tea ɗin. Bayan ta gama ta amsa da kanta ta miƙa mata Ita kuma Zabba'un zama tayi kana ta kalli MEEMAN da har ta soma kai Cup tea ɗin bakin ta, cikin turancin ta na ƴan koyo tace, "Good morning and hope you are fine? Hope you enjoyed the stay?" Kasancewar har yanzu Cup ɗin na bakin ta, kallon Zabba'un kawai take yi tare da gyaɗa mata kai kawai ta ci gaba da shan tea ɗin Sai ita Zabba'un ta kalli Hajiya tana muskuta zaman ta tace, "Hajiya wai yanzu ita ɗin dai yarinyan Hajiya Zulaiha ce kenan?" "Ƙwarai kuwa. Baki ga sun yi kama bane?" "Eh na gani wlh, ai ban yi tunanin ta kai girman haka ba, Masha Allah gaskiya tana da kyau matuƙa tamkar dai ƴar can ƙasan wlh". Ta ƙare maganar tana washe baki Ita dai Hajiya bata ce komi ba illa ɗaukan Hisnul Muslim ɗin dake jikin ta taci gaba da karanta wa "Hajiya nace ba. Amma tana da aure ko?" Ɗago wa Hajiyan tayi tana kallon ta da cewa, "ke dai Zabba'u kina da son tsegumi wlh, idan tana da aure ai zaki sani tunda tare muke da ke tsawon shekaru a gidan nan, a baya nasha sanar miki labarin su tun Zulaiha na can, sannan kuma koda ta dawo baki taɓa jin mun ce miki tayi aure ba". "Haka ne Hajiya. To kiyi haƙuri". "Idan ban yi haƙuri da ke ba ya zan yi ne Zabba'u? ki tashi dai yanzu ki je ki ɗaura mana sanwan abinci kina gani rana tayi amma kin zauna tsegumi". Tana washe baki tace, "Hajiya ai na ɗaura miyan har ya kusa soyuwa zan sauke, dama farar shinkafar kaɗai ya rage in girka". Bata ce mata komi ba ta juya ga kallon MEEMA da har yanzu tana kafe da Cup tea ɗin a bakin ta. Tace da ita, "What do you want to eat?" Sai a lokacin ta cire Cup ɗin a lokacin ta shanye tass duk da kuwa zafin shi, domin ita ta fi son ta ji tea da zafi-zafin sa, kuma ta shanye sa a hakan ya fi mata a ko yaushe. Ce mata tayi, "She doesn't need anything, that's enough." "No, Zulaiha, tell me something to be cook for you, because you will not sit still and eat nothing but tea." She Said, "I will eat whatever is prepared." "To maza tashi ki girka ki kawo mata". Inji Hajiyar tana kallon Zabba'un "An gama Hajiya." Ita kuma tafaɗa tana tashi ta wuce Hajia Looking her said, "I am still not tired of being sorry with you for not coming to see you. Please be patient. Your uncle is not in the country that's why he did not come to you, but forgive us." Hannu MEEMAN ta sanya ta riƙo nata, fuskar ta a sake sosai a yanzu ɗin tace, "Don't worry my grandmother because you are not criminal. Ummee is a criminal and I am the only one who is angry with her. " Hajiya tace, "But do not be angry with her because she is your mother, bind yourself to hide what you feel about her in your heart, don't forget she's a mother to you, no matter what she does to you, you should not hate her." Girgiza kanta MEEMA ta soma yi hawayen idanun ta da suka taru suka soma zubo wa, cikin amon muryan ta me kama da ɓacin rai tace, "No, I will never forgive her for taking me not her daughter, I will never see her as my mother, I have long removed her as my mother. Please grandma I don't like talking about her". "Well. Since you said I will never speak to you again." Ta ƙare maganar da shafa mata kai tana mata murmushi.                  Lokacin ne Ummee ta sauko daga sama a cikin shigan ta kamar yanda ta saba, yau ma tayi kwalliya da baƙin less me kyan gaske, duk ta saka sarƙa da awarwaro a hannayen ta, duk da a yanzu ɗin damuwa ce cinkushe a fuskar ta, ga shi idanuwan ta sun yi ja sun kumbura sosai. Koda ta iso gaishe da Hajiya tayi tana samun wuri ta zauna a kan sofan da ke kallon wanda MEEMA ke zaune Hajiya amsa mata tayi tana kallon ta da cewa, "wai yau baza ki je aiki bane sai yanzu kika fito?" "Eh Hajiya yau bazan iya fita ba". "To me ya sami idanun ki suka yi ja haka? Kar dai ace tunanin MEEMA kike yi?" MEEMA da kanta ke sunkuye tun zuwan Ummeen sai ta ɗago kai ta kalli Hajiyan jin ta kira sunan ta, duk da bata fahimci me suke cewa ba ta gane da ita ake yi Ita kuma Hajiya murmushi tayi mata tana dafa hannun ta, sai kuma ta mayar da kallon ta ga Ummee da ta ƙura wa MEEMAN ido, tace da ita, "tun wuri ki dena saka wa kanki damuwa tunda komi da ke faruwa ke kika jawa kanki, son zuciyar ki yasa kika aikata hakan, kin baro Ƴar ki da mijin ki kin taho nan, to, meye na saka wa rai damuwa? Abinda kike so fa kika aikata, kuma duk rarrashi da ban bakin da nayi miki domin ki koma amma kika ƙi bin shawara ta". "Hajiya ba haka bane wlh nayi nadama tun ba yanzu ba, abun da na aikata yana damu na a zuciya na rasa yanda zan yi in koma, ban san ya Faruk zai kalle Ni ba shiyasa na kasa koma wa, baƙin ciki na yanzu ya koma ga mahaliccin mu ban nemi afuwar sa ba Hajiya, ya zan yi da raina?". Ta ƙare maganar cikin muryan kuka Tsam MEEMA ta tashi zata wuce ɗaki Hakan yasa Hajiya ta dakatar da ita tana tambayar ta, "where to go?". "There is something I have to do.". Daga haka ta wuce ba tare da ta jira cewar ta ba "Yanzu ya ya zan yi Hajiya ɗiya ta ta dawo tana ƙauna ta? Bazan iya jure halin da take ciki ba, Ina son ganin farin ciki a fuskar ta, ina son ta ɗauke Ni a matsayin mahaifiyar ta me ƙaunar ta. Nayi kuskure sosai ban san ya zan yi in dawo da farin cikin da ta rasa ba, na san MEEMA ta kasance a cikin baƙin ciki na tsawon lokaci, nayi ƙoƙarin neman ta a waya a baya but wayoyin su duk ba sa shiga." "To ai haƙuri zaki yi tunda ke kika jawa kanki, a sannu wata rana zata gane idan kika fahimtar da ita, Ni dai ban ce ki riƙa damun ta ba na gaya miki domin idan har ta bar gidan nan sai dai ke ma ki bi ta." Shiru kawai Ummee tayi yayinda hawaye ke zuba a saman fuskar ta, hannu ta sanya tana share wa zuciyar ta na mata zafi da raɗaɗi "Ki je ki karya ga Breakfast ɗin ki can a dainning Zabba'u ta shirya miki". Hajiyan tafaɗa tana kallon ta Bata ce komi ba ta tashi ta wuce kan dainning ɗin.                 ******        Shigan MEEMA ɗakin kwanciya tayi a saman gadon tana hawaye, danne kanta tayi a ƙasan pilow ta saki kuka me tsuma rai, ta jima tana kukan kafin ta tsagaita tana tashi zaune ta sanya hannayen ta tana share hawayen. Sai ta miƙe ta nufi jakar ta ta ciro computern ta ta soma aiki a ciki Bata jima da fara wa ba Zabba'u ta shigo ɗakin da sallama A ciki-ciki ta amsa mata bayan ta ɗago ta kalle ta sau ɗaya ta mayar da kanta Cikin washe baki Zabba'u tace, "good job. Hajiya says let me call you cooking is complete." Gyaɗa kanta tayi ba tare da ta furta komi ba ta mayar da hankalin ta ga computern Ita kuma Zabba'u ta fice Kamar mintuna goma kafin ta rufe ta tashi ta fita. *WhatsApp only* 07065334256 [10/10, 3:47 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_20*              Tafiyan MEEMA ya ja tashin hankali matsananciya a wajen su Uncle Ali. Musamman ma Sajjad domin hauka tuburan ya nuna musu a kan, "sai sun nemo mishi ita duk inda ta shiga." Kuka sosai yake yi duk ya hargitsa musu gida, su kansu sun kasa zama suyi tunanin mafita illa rarrashin sa da suke yi a kan, "ya kwantar da hankalin sa zasu nemo ta duk inda ta shiga." Mutanen da suka soma taruwa sai dai suka tafi a washe garin ranan tunda an nemi Amarya an rasa. Wasu har tsegumi suke yi da dalilin tafiyan nata Su kuma tun suna ɗaukan abin da Sajjad yake yi a matsayin na ɗan lokaci dole zai haƙura; sai kawai zazzaɓi ya kama sa, sosai yake jin jiki wanda a koda yaushe sai dai yayi ta musu sambatu, "shi fa a nemo masa Zulaiha, bazai iya rayuwa babu ita ba." Hakan yasa suka wuce da shi asibiti tunda abun nasa sai gaba yake yi.             Uncle Ali da Uncle Zubairu sun rasa inda za su fara zuwa su neme ta, hankalin su a matuƙar tashe yake sabida rashin amsar komi daga wurin ta, tabbas suna tunanin ta gane auren da zasu yi mata ne ta gudu, kuma ko kusa basu yi tunanin zata iya zuwa wajen Ummeen ta ba kasancewar ita Ummee ta bar su tun ba yanzu ba, ba sa tunanin cikin sauƙi zata je can. Shiyasa suka yanke shawarar zuwa Riyadh ɗin su duba ta Umma duk ta tashi hankalin ta itama sai kuka take yi, a yanda ta ga Sajjad ya ƙi haƙura da zancen MEEMAN yasa itama take kuka da faɗin, "a nemo ta duk inda ta shiga don ɗan ta bazai mutu a kanta ba, a nemo ta a ɗaura mishi aure da ita idan har ɗan ta zai samu lafiya." Uncle Zubairu shi ya je har Riyadh ɗin amma masu aikin gidan suka ce, "bata zo ba". Kwanan sa biyu a can yana zaman jiran ko zata zo amma babu ita babu alamar ta, dole ya dawo gida ya sanar wa da Uncle Ali. Hankalin su ya sake tashi sosai, sai dai babu yanda suka iya dole suka mayar da hankali wajen samun lafiyan Sajjad tunda har yanzu ya ƙi dangana shi a dole sai an nemo ta. Har ya samu sauƙi sun koma gida ya tayar da hankalin sa, "shi da kansa zai je neman ta a Riyadh ɗin." Ba don sun so ba suka bar sa ya soma shirye-shiryen tafiya. A ransa ya ƙudura aniyar, "muddin be ganta ba bazai dawo gidan ba, dole tare za su dawo, a ko ina take a faɗin duniyar nan sai ya nemo ta, ba shi da matar aure sama da ita, yana matuƙar ƙaunar ta bazai taɓa barin ta ba". ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️             Zaman da MEEMA tayi a gidan ta samu kwanciyar hankali sosai, duk abin da take so Hajiya tana mata, tare suke zama suyi ta hira har da Zabba'u don yanzu ta saba da ita kasancewar ta akwai surutu da shiga abun da babu ruwan ta, yanda take shige wa MEEMAN ne dole ta saki jiki da ita, sai dai matsalan ko kaɗan ta ƙi bai wa Ummee dama wajen ganin ta wanke kanta daga laifukan da tayi mata, ko magana ba ta mata koda suna zaune wuri ɗaya, tun Ummee na damuwa sosai a yanzu har ta saba da halin MEEMAN, itama a hankali yanzu take ɗan shiga sha'anin ta duk da ba kula ta take yi ba, amma wani abun sai ta riƙa mata ko don ta faranta mata, musamman girkin da ta san tana matuƙar so irin ciman Larabawa, haka zata zaƙe tayi mata but ko kula wa ba tayi, Hajiya ke sanya ta taci wani lokacin shiyasa take ɗan ci idan ta ga dama.            Yau ma suna zaune da Hajiyan, Zabba'u na gefe tana musu surutu Hajiya na amsa ta, ita kuma MEEMAN tana zaune tana kallon su wani lokacin idan suka sako ta a zancen su tana tsulma musu baki Dayake Ummee na wajen aikinta bata dawo ba Duban Zabba'u Hajiya tayi da cewa, "yauwa Zabba'u kira min drever zan aike sa, zai siyo wa MEEMA layin waya ne ta ce min  tana buƙata." "To Hajiya bari in je." Tayi maganar tana tashi da sauri ta fita MEEMA da ke kallon su sai tace, "grandma I also want to learn Hausa because I want to know what you are saying". Dariya Hajiya tayi da cewa, "Are you tired of hearing us talk? Don't you understand?" Ita kuma sai tayi murmushi tana jinjina mata kai, sai kuma ta ƙara da cewa, "yet I want to be able to." "Ai kuwa zaki koya, da sannu ai zaki saba dama". "You say what?" Hajiya smiled and said, "I said you will learn slowly." MEEMA smiled at her looking at her "But I think your stay there makes you very anxious. what i was thinking why not get a job you going out, It will help you a lot and you will forget about any worries." "Na'am grandma. I need a job, I want to start working." She spoke excitedly Hajiya itama murmushi tayi da cewa, "If that makes you happy, you will be offered a job".                Zabba'u da Ummee ne suka shigo a tare Hajiya ta amsa musu sallaman tana kallon su "Sannu da gida Hajiya." Inji Ummeen tana zama a kan sofa "Yauwa an dawo?" "Eh." Zabba'u da itama ta zauna take faɗin, "Hajiya wai ya fita zuwa shago yanzu zai dawo, na bar wa me gadi sallahu idan ya dawo ya faɗa masa kina neman sa." "Tom shikenan." Cewar Hajiyan kafin ta mayar da kallon ta kan Ummee dake yunƙurin tashi tace, "zauna zamu yi magana". Koma wa tayi ta zauna tana kallon ta "MEEMA tace tana son Fara aiki kinga ke ya kamata ki nema mata abun da ya kamata tayi". "To Hajiya sai in nema mata a wurin aikin mu hakan zai fi mu riƙa zuwa tare." Inji Ummeen tana kallon MEEMA da murmushi Hajiyan kallon MEEMA tayi tana sanar mata da abun da Ummee tace Fuskar ta babu walwala ta dubi Hajiyan tace, "Laá. I do not like." They were silent Sai kuma Hajiyan tace, "But you said you needed it, or did you break it?" Kafin tayi magana sai Ummee tace, "a'a Hajiya ina ga ba ta son yi a inda nake yi ne, kuma dama mass.com ta karanta Ni ce dai nake son tayi aiki a companin da nake aiki hakan zai sa ko yaushe muna tare, amma tunda ba ta so sai in Yi ma Idris magana ya samo mata a wajen aikin su na gidan t.v hakan zai fi." Hannun MEEMAN Hajiya ta riƙe tana kallon ta tace, "well. Now you're going to get a job somewhere, did you?" Kanta kawai ta ɗaga har yanzu kyakykyawar fuskar ta a turɓune Ita kuma Ummee tashi tayi ta haura sama While su kuma suka ci gaba da taɓa hira ban da MEEMA da ke latse-latse a cikin wayan ta Nocking ɗin da aka yi ne yasa suka yi shiru suna ba da iznin shigo wa Drever ne ya shigo da sallama a bakin sa, ya isa wajen su ya durƙusa yana cewa, "Hajiya gani an ce kina nema na". "Eh Salihi. Layin waya zaka siyo wa Jika ta." "To Hajiya". "Yauwa Zabba'u ɗauko mishi 2k a ɗaki na ya je da shi." Amsa mata tayi tana tashi ta wuce Drever'n yace, "amma Hajiya wani iri ne zan siyo?" Kallon MEEMA tayi da cewa, "What brand do you want with the Simcard?" Sai a lokacin ta ɗago da idanun ta daga duba wayan da take yi, "MTN." Ta furta a taƙaice "To kaji. Mtn take so ka siyo mata." "To Hajiya." Koda Zabba'u ta kawo kuɗin ta miƙa masa ya fice. Ita kuma tace, "Hajiya bari in shiga kichen in ɗaura mana abinci. Ko zaki taya Ni ne MEEMA?" Ta ƙare maganar da kallon ta tana washe baki Jin ta kira sunan ta yasa MEEMAN ta kalle ta ba tare da ta furta komi ba Hajiya tace, "kin yi mata Hausa taya zata san me kika faɗa mata?" "Oh wlh manta wa nake yi Hajiya." Sai ta maimaita mata da turancin Girgiza kanta MEEMA tayi tace, "laá I can't." "But you should always learn that it will benefit you even at your husband's house." Murmushi kaɗai MEEMA tayi bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta Ita kuma Zabba'un sai da ta gama zuba surutun ta da Hajiya duk dai a kan MEEMAN kafin ta wuce kichen ɗin Hajiya ta kaɗa kai da cewa, "Zabba'u baki da dama ke dai, a nan kika fi auki wajen surutu, ayi mutum kullum ba ya gajiya kin girma baki san kin girma ba." Ɗago kai MEEMA tayi ta kalle ta tace, "grandma you do it for me?" Tace, "No, I'm not doing it. I'm doing Zabba'u. She's worried about you coming. She's going to teach you how to cook." "I can't grandma." She spoke in a calm voice "Then if you want she can teach you, because you should learn. If you get married who will go and teach you?" Shiru MEEMA tayi and she drops head down "If you have time, she will teach you ok?" Gyaɗa kanta tayi kawai. Sai kuma ta miƙe tana kallon Hajiyan da cewa, "I'll go into the room and lie down." Hajiya amsa mata tayi ita kuma ta wuce zuwa ɗaki.         Tafiyan ta babu jima wa wani saurayi wanda bazai fi sa'ar MEEMAN ba ya shigo da sallama ciki Hajiya ta amsa mishi tana masa lale da faɗin, "idon ka kenan Idrisu?" Dariya yake yi ya ƙariso ya zauna yana cewa, "Allah ya bar mu da Hajiyar mu. Kin ci zamanin ki kina cin tamu, tsohuwa me ran ƙarfe an buga an bar ki, na same ki lafiya?." "Ai bazan amsa ba tunda sai yanzu ka san da Ni, gaba ɗaya ka manta da Ni sai yau zan ga ƙafafuwan ka a gida na." "Woo! Hajiya kina da ƙorafi ne na rantse da Allah, ban da abun ki duka-duka yaushe ne na ɗauke ƙafafu na a gidan nan? Kin san kuma aiki na ne ba ya bari na in shigo amma da sai kin gaji da gani na." Yafaɗa still yana dariya Hajiya tace, "babu wani nan, da ace ban san daɗin bakin ka bane." "Tukunna dai Hajiya inyaso daga baya sai mu ci gaba da taƙaddamar tamu, ina Aunty ita take nema na?." "To ka ji batu ashe sai da aka neme ka ka shigo?" Dariya yayi da cewa, "Hajiya tawa ke dai so kike yi ki laƙaba min laifi, kowa ya san ina mugun ƙaunar ki, ko su Umma sun san cewa ina na fito wurin ki ne, ina zan tafi wurin ki ne, amma kike faɗan haka; idan wani ya ji ai sai yayi mana dariya Allah kuwa." "Ni zan fara yin dariyan kuwa. Dama ai ba yau kuka saba ba, sunan dai kuna miji da mata ne." Cewar Zabba'u da fitowar ta kenan daga kichen ta tsinkayi maganar nasa "To kin gani ko Hajiya ta? Ai dama nace miki akwai ƴan saka eyes wlh, kin ga ɗaya ta ɓullo. Bamu san kuma nawa za su ƙaru ba a nan gaba." Dariya suke yi su duka While Zabba'u tana faɗin, "ai yau har gidan su Umman taku sai na je kai gulman ku." "Kin gani ko Hajiya? To ki faɗa mata ba faɗa muka yi ba." "Ƙyale ta Idrisu na, duk wanda yace zai gan mu a rana ai zai ruɓe ne, Ni da miji na ai ba ma ɓaci. Yanzu dai kira Zulaihan a waya tana sama ne." Wayan sa ya ɗauka yana latsa wa yana ci gaba da bai wa Zabba'u amsa wacce ta sako shi a gaba sai ba'a take mishi. Bayan ta ɗau wayan ne ya sanar mata, "ya zo." Ba'a jima ba kuwa sai ga ta ta sauko. Ta zauna a kan sofan tana amsa gaisuwar sa, kana ta ƙara da faɗin, "Idris aiki zaka samo wa yarinya ta MEEMA a wajen aikin ku, Ina fata za'a samu?" "Eh Aunty za'a iya samu insha Allahu, idan ma hakan ya gagara zan yi ƙoƙari ko a ina ne in samo mata, amma Aunty Kar dai ace yarinyan ki ta Riyadh ita ce ta zo?" "Eh ita ce." Ta ba shi amsa tana murmushi "Wow! Gaskiya zan so in ganta, kin san na daɗe da jin labarin ta wajen Hajiya sai dai baki taɓa zuwa da ita nan ba." "To ai yanzu sai ka gaji da ganin ta kuwa Mijin, tunda muna nan da ita ta dawo gaba ɗaya." Cewar Hajiya tana dariya "Allah Hajiya ta?" "Ƙwarai kuwa Mijin. Yanzun nan ma ta tashi ta shiga ɗaki." "To in dai haka ne insha Allahu I will try my best to get her a job. But I need her documents so I can go with them." Ummee da sauri ta kalli Zabba'u tace, "ki kira ta sai ki faɗa mata ta kawo takardun nata." Tashi Zabba'un tayi ta wuce ɗakin MEEMA. Bata jima ba ta dawo ta sanar musu, "ga ta nan zuwa".                   Ba'a jima ba MEEMA ta fito riƙe da documents ɗin a hannun ta ta taka a hankali zuwa wurin su Hajiya na murmusa wa tace, "to ka ganta nan Idris, Jika ta kenan." Idris da ke faman kallon MEEMAN miƙe wa tsaye yayi fuskar sa yalwace da fara'a yace, "gaskiya tana da kyau Hajiya, Allah ya baki jika kyakykyawa. Anya Hajiya ba daga can ƙasar kika sanyo ta da naki ba?" Sai kuma ya kama haɓa yana sake ƙare wa MEEMAN kallo da cewa, "Hajiya Ni fa ban yarda ba, kwata-kwata ban ga tayi kama da ke bane ai." Dariya suke yi duk kan su sabida abin da ya faɗa While Hajiya tace, "ai yaro duk kyawun nan da ka gani kaɗan ne da wanda nayi a zamanin da nayi ƴan matanci na, wannan ai bata kai Ni kyau ba." "Nima haka na gani ki bar sa kawai Hajiya don ya ga kin taƙwarƙwashe ne shiyasa yake faɗan haka." Inji Zabba'u tana dariya They all laughed. while MEEMA na tsaye tana kallon su bata ce uffan ba tunda ba jin su take yi ba Idris yace, "ƴar uwan tawa ba ta magana ne Hajiya naga tayi shiru ko fara'a ba ta yi?" Zabba'u tayi tsagal ɗin cewa, "ba ta jin ka ne shiyasa, baka yi mata da Yaren da zata gane bane." "Kina nufin larabci?" Yafaɗa yana ƙwalalo ido. "To ai Ni ban iya ba." Ummee tace, "kayi mata da turanci." Murmushi yayi ya kalli MEEMAN da cewa, "sorry sister. My name is Idris. Our house is looking at this house, we are staying outside Hajiya, I am happy to meet you." Guntun murmushi tayi masa da cewa, "me too." "Ok Bring the documents." Yafaɗa yana miƙa mata hannu Handing him the fetus without saying anything again she turned and walked away Hajiya tace, "to sai ka ƙoƙarta Idrisu na." "Kar ki damu Hajiya ta baki da matsala. Ni zan tafi don akwai inda Abba ya aike Ni dama. Zuwa gobe ko jibi zaku ji me ke akwai in Allah ya yarda." Daga nan sallama suka yi ya fice ya bar su. Su kuma suka ci gaba da ɗan taɓa hira, inda Zabba'u ta wuce kichen domin ci gaba da aikin ta.               Ba'a rufa kwana biyu ba Idris ya dawo gidan ya shaida musu, "an dace da samun aikin MEEMA".                  Zuwa Monday suka soma fita aikin tunda a wurin aikin su ta samu, tare suke fita da Idris kasancewar sa me son Wasa da barkwanci a cikin ƙanƙanin lokaci suka soma saba wa, idan ya shirya sai ya zo gidan su tafi tare Tunda ta fara fita aikin ta sake sakin jiki sosai, abubuwan da ta gani a wurin aikin nasu da kuma yanda ake gudanar da al'amura gunun sha'awa a wurin ta. Musamman yanda mutane suke son mu'amala da ita domin sosai tayi farin jini a wurin jama'a, kowa MEEMA kowa MEEMA sai hakan yake sanya ta farin ciki da nishaɗi, duk da ba kowa take kula wa ba iyakan gaisuwa sai kuma abun da ya kaita tunda ko yaushe suna tare da Idris, ga kuma cousin ɗin shi Laɗifa komi tare suke yi, ita take jan MEEMA a jiki tana koya mata wasu abubuwan musamman idan bata fahimta ba kasancewar yanayin mu'amalar mu ta nan bata san da su ba, ga kuma rashin iya Hausa da har yanzu ko Eh ta gaza fahimta.           Musamman Ummee ta siyo mata mota sabuwa fil domin ta riƙa zirga-zirga da ita na yau da kullum zuwa wajen aiki, amma ta ƙi amsa Hajiya da kanta ta kira ta, ta miƙa mata keey ɗin motan daƙyar ta amsa. Sai dai bata taɓa hawa ba kullum Idris take bi tunda sun zama tamkar friends ne a cikin ɗan ƙanƙanin lokacin da be gaza wata ɗaya da haɗuwar su ba. Wani lokacin ma har gidan su take shiga wajen Umman sa, kasancewar gidan akwai yara shiyasa zaman gidan yake mata daɗi, kowa so yake yi ya ja ta a jiki saboda farin jinin ta. Shiyasa a ɗan ƙanƙanin lokaci ta saki jikin ta ta soma saba wa da sabon rayuwar ta, a hankali ta soma manta duk wani rayuwar ƙunci da tayi na tsawon shekaru, duk da har yanzu ta kasa manta wa da Abee ɗin ta duk idan ta tuna sa tana zubar da hawaye sosai, sai ta riƙa jin tsanar Ummeen ta yana sake zama sabo a zuciyar ta, tana jin tamkar baza ta taɓa yafe mata ba. Ita ce silan komai. [14/10, 9:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                           💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*              *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._             *FAƊAKARWA* '''Manzon Allah yayi mana bayani cewa, "Bambancin da yake tsakanin mumini da kafiri shi ne rashin yin Sallah." Busaida ya ruwaito wani hadisin mai kama da wannan inda ya ce, "na ji Manzon Allah yana cewa," "haƙƙin da ya bambanta mu da su shi ne salla. Duk wanda yayi watsi da ita ya zama kafiri."       Shi kuwa Abdullahi Ibnu Umar ya ce ne wata rana Annabi yayi magana a kan Sallah yace, "Ga wanda yake tsayar da sallah, takan zame masa haske, shaida da kuma tsira a ranar lahira. Wanda ba ya tsayar da ita kuwa, gare shi babu haske, babu shaida, babu tsira, kuma a ranar lahira za a haɗa shi da Ƙaruna da Fir'auna da Ubayyu ibnu Khalaf."        Da hadisai da ayoyin Alkur'ani duka suna nuna irin munin zunubin da yake rataya da ƙin yin salla, suna kuma nuna matsayin mai yin hakan duniya da lahira. Dokar musulunci dai tana yin gargaɗi ne ga mabiya addinin cewa su riƙe shi da gaskiya ta yin Sallah, babban jigon Islama kuma aikin addini mafi girman daraja. Ashe ba abin mamaki ne ba mu ji cewa duk wanda ya guje mata ya kafirta, ya kauce ma hanya miƙaƙƙiya. Alƙur'ani kam na kiran irin wannan mutum mai zunubi wanda aka tanadar wa wutar jahannama, mai ƙona komai, mai cinye Mutane da tsananin zafin ta. Kyakykyawan sakamako ga wanda ya bijire. Ubangiji ba ya zaluntar kowa. Allah yasa mu dace yasa mu gama da duniya lafiya.'''                      *NO_21*                  Yau ma kamar kullum MEEMA tayi shirin ta kamar yanda ta saba, Abaya ta saka blue color da aka yane shi da kwalliyan Stones daga saman wuya har ƙasa, sai faffaɗan hannu me kamar alkyabba shima an sanya Stones da kuma bakin lessi, tayi Rolling da jan veil sai ta saka cover shoes Shima ja, haka zalika agogon hannun ta. Iyakan Powder da lipstick ta saka sai ta zizara kojol a idanun ta, I can't describe to you how beautiful she is, but her beauty is even more beautiful. Fita tayi Parlour inda Idris ke zaune da Hajiya suna hira yana jiran fitowar ta "You look so cute Zulaiha." Cewar Hajiya kenan sanda ta ƙyalla ido ta ganta Ita kuma murmushi tayi ta isa wurin ta tayi mata peak a goshi tare da faɗin, "thank you Grandma." Idris da ya miƙe tsaye a yanzu ɗin yace, "to Hajiyata mu zamu wuce sai mun dawo." "To Allah ya bada Sa'a Allah ya tsare." Tafaɗa tana murmushi Daga nan sallama suka yi mata suka fice. Sanda suka isa bakin motan Idris ɗin da kanshi ya buɗe wa MEEMA ƙofa yana solute ɗin ta Kyakkyawar murmushinta ta sakar mishi tana ƙarisawa ta shiga ciki Ya rufe shima ya zaga ya shiga ya ja motan zuwa wajen aikin su. A cikin motan sai janta da hira yake yi duk da kasancewar ba amsa mishi take yi ba sai dai tayi masa murmushi kawai, a haka har suka kai suka fito A nan suka haɗu da Laɗifa itama zuwan ta kenan, ta isa wurin su cikin farin ciki suka rungume juna da MEEMA Idris da ke kulle mota yace, "to saura Ni baza ayi hugg ɗina bane?" Hararan sa Laɗifa tayi tana cewa, "haka kawai ƙato da kai ba miji na ba, na ƙi ɗin." Sai kuma ta kalli MEEMA tace, "let's go." Ta riƙo hannun ta suka shige ciki suka bar Idris na kwaɗa mata kira. But ta ƙi tsaya wa suka shige ciki. Dayake Office ɗin su ɗaya ne can suka shiga suka zauna suna ɗan taɓa hira Sai ga Idris ɗin ya shigo yana cewa, "wato ke ina kiran ki kika yi banza da Ni Ko? Kin ganki; ki fa mayar da hankali a kan aikin da oga ya sanya ki don na kula tunda na kawo miki Abokiyar hira kike wasa yanzu." "A'a yaya kai ne dai kake ganin haka but ina aiki na yanda ya kamata wlh." "Ok on that talk of ours we are going to meet the Senator tomorrow, he has given us an appointment tomorrow, but I have a place to go tomorrow, there is work for me to go to Zaria, now you and MEEMA will visit his house tomorrow, I hope you can?" "Don't worry Bro, we'll go together." "Ok let me go I have a job, kiyi sauri da Allah ki gama wancan aikin ki zo mu fara ɗaura videon Nan." Yafaɗa Yana kallon Laɗifan "Ok." Tace da shi tana janyo computern ta gaban ta Shi kuma ya fice ya bar su.             There they were at work and MEEMA raised her head looking at Ladifa and said, "Where are we going tomorrow I don't understand?" Laɗifa tace, "There is someone who is seeking the Senate seat in this city, we have been wanting to interview him on this television station for a long time, but we have not had the opportunity yet until this time, he is a great man because everyone wants to meet him. But now we have a way to go tomorrow. We going to interview him." "Ok God Lead us." Cewar MEEMAN tana mayar da hankalin ta kan abin da take yi.                 By 02:00pm. Suka je suka yi sallah, Idris ya ɗauke su zuwa wani restaurant da babu nisa da wurin suka ci abinci, sai hira suke yi gunun sha'awa suna dariya har suka dawo. Zuwa ƙarfe 03:00pm. Suka tashi, Laɗifa ta sauke MEEMA a gida tunda Idris Yana da aiki ba yanzu zai koma gida ba. Sallama suka yi Bayan ta sauke ta taja motan ta ta tafi Ita kuma MEEMA tayi Nocking aka buɗe mata ta shiga ciki, lokacin da ta isa parlour babu kowa sai Zabba'u wacce ta buɗe mata ƙofa tana mata sannu da aiki "Where is Grandma?" Ta tambaye ta tana kallon ta "She is in her room praying." "Ok." Tace tana wuce wa. Sai da ta shiga ɗaki ta watsa ruwa a jikin ta ta sanya wata ƙaramar riga na shan iska wacce tsawon ta be wuci iya ƙasan gwiwan ta ba, kalan ta kalan ruwan Powder ne, sannan ta fito ta wuce ɗakin Hajiya. Sai dai a lokacin babu ita a ciki shiyasa ta fito Parlour ta tarar da ita tana karatun Hisnul Muslim. Wajen ta ta nufa tayi hugging din ta tana sakar mata kiss a bayan hannun ta tare da faɗin, "Weldon Grandma." Murmushi tayi mata tana shafa kanta da cewa, "it works hope you enjoy the project?" "Alhamdulillah." Tafaɗa itama tana mayar mata murmushin "Ok go eat and come back for a chat." Amsa mata tayi tana miƙe wa ta nufi kichen. Tana shiga ta ga Zabba'u a bakin madafa tana juya miya, ta isa wurin ta tana murmushi tace, "you are always cooking, you are not tired?" Dariya Zabba'u tayi tace, "How can I get tired of cooking after a woman is known for cooking? You too should come in and teach you because cooking is for women. What are you looking for?" Taɓe baki tayi tana sake duban kichen ɗin tace, "nothing. I came to see what you are doing." Murmushi Zabba'un tayi tana ci gaba da juya miyan. Sai kuma tace, "your food is on the dainning table go and get it." Kanta ta gyaɗa tana juya wa bata ce komi ba ta fice. Sai da ta ɗibi abincin sannan ta koma kusa da Hajiya ta zauna tana ci tana kallon ta While ita kuma tana ta karatun ta Bayan ta gama ta ɗauki Plate ɗin zuwa kichen Lokacin Ummee itama ta dawo gidan, gaisa wa da Hajiya tayi ta haye sama.                  The following day. Har gida Laɗifa ta zo ta ɗauke ta suka wuce G.R.A where they will go to the Senator's house to find out about him being that the election is near, they want to post his interview on their television channel Koda suka isa bakin Gate ɗin gidan an hana su shiga Laɗifa ce ta fito a motan ta isa wajen Gate man ɗin tace, "Malam don Allah ka faɗa masa ƴan jarida ne daga Light T.v suke son hira da shi ya san da zuwan mu Please." "Ok sai ku jira in sanar a ciki idan ya san da zuwan naku." "Ok thanks." Tafaɗa tana kallon shi While shi kuma ya shige ciki Shiru-shiru kusan mintuna goma babu me gadi. Laɗifa da ke waje har yanzu sai kai komo take yi tana faman jan tsaki Sai daga baya sai ga shi ya fito yace mata, "su shigo." Hakan yasa ta koma wajen motan ta sanar wa MEEMA da ke zaune a ciki tana latsa wayan ta. Fitowa tayi da Laptop a hannun ta suka jera zuwa cikin gidan Babban gida ne me Part-part da yawa. A can daga nesa akwai wani babban gini don shi kaɗai ne upstairs a gidan. Duk inda ka gifta masu aiki ne suke yawo suna ta faman aikin su, tsarin ginin sosai zai tafi da kai saboda tsantsan haɗuwar shi, daga gani ka san mamallakin gidan me kuɗi ne sosai. Sai da suka zagaya round about da ke tsakiyar gidan kafin suka isa wannan dogon ginin. Dayake suna biye da wani house men ne yana musu jogara zuwa wajen ogan nasu Kafin su kai ga isa ginin ne sai ga wata tsaleleliyar budurwa wacce a ƙalla baza ta fi 24years ba, ta ɗau wanka a cikin ƙananan kaya tamkar baza ta taka ƙasa ba, tana tafe tana amsa call ta fito a ɗaya daga cikin sashin gidan. Tana matsowa wajen su ne while su ma hakan. Sai da suka yo gab da juna sannan ta ɗaga kai ta kalle su. Kallon kallo suka yi gaba ɗayan su yayinda ta ƙi ɗauke nata idanun a kan MEEMA wacce ita tuni ta ɗauke nata tun kallon da tayi mata daga nesa. Har sun gota ta kuma sai ta kira House Men ɗin tana yafico shi da hannu Hakan yasa ya dakata daga yin musu jagoran da yake yi ya nufe ta da sauri ya duƙa a gaban ta Magana take mishi tana nuna su MEEMA da yatsa Shi kuma yana bata amsar tambayar ta. Sai kuma ya tashi a bisa umarnin ta ya nufi su MEEMA ya sanar musu, "kuyi haƙuri Ƙanwar Yallaɓoi tace baza ku samu ganin shi ba." "To saboda mene?" Inji Laɗifa cike da haushi "Haka tace in sanar muku." Kallon inda budurwan ke tsaye tayi. Tana nan har yanzu da waya a kunnen ta idanun ta na kallon wani wurin. Hakan yasa Laɗifa ta kalle shi tace, "kai mu je ka kai mu." "To." Yafaɗa da sauri yana yin gaba MEEMA da bata san ma me suke faɗa ba ganin Laɗifa tayi gaba yasa itama ta bi bayan ta tana jan gajeren tsaki, kasancewar akwai rana sosai duk tafiyan nan da suka yi daga bakin Gate zuwa nan duk ta gama takura, har wani gumi ne yake tsatstsafo mata sabida yanayin shigan kayan ta Budurwan da itama ta biyo bayan su cikin ɗaga murya tace, "Hi.. Hi.." Dole suka ja suka tsaya gaba ɗayan su jin muryan ta a sama wanda yake nuni dasu take yi "Me nace maka? Ina zaka kai su bayan nace maka baza su samu ganin shi ba?" Tayi maganar a ɗaurewar fuska tana kallon House Men ɗin Kafin yayi magana sai Laɗifa ta riga shi da faɗin, "kiyi hakuri ba wajen ki muka zo ba, shi wanda muka zo wajen shi shi ne yace a shigo damu don haka baza mu koma ba." Sai ta ja hannun MEEMA suka yi ciki ba tare da ta sake bi ta kan ɗan rakiyan ba Ita kuma ƙwafa tayi tana bin su da kallo har suka ƙule mata, sannan ta ja dogon tsaki ta wuce zuwa wajen motan ta ta shiga tabar gidan.        A dogon ginin Laɗifa ta ja tunga ta tsaya domin a ranta tana da tabbacin nan ne ya kamata su shiga. Sai ta soma Nocking ƙofan MEEMA da ke kallon ta tace, "but who is that? What is she asking us?" "Forgot her. I think she's also a housewife, or his younger sister oho."Cewar Laɗifa still tana ci gaba da Nocking ɗin Babu jima wa aka buɗe musu. House maid ne ya buɗe yana kallon su da tambayar, "wanda suke nema?" Laɗifa tayi mashi bayanin abin da suka zo yi Yace, "ok ku shigo". Ya shigar da su har cikin ƙaton parlour'n ya basu wurin zama. Sannan ya kawo musu drinks sai ya wuce kiran musu me gidan. Be jima ba ya dawo yace musu, "su biyo shi." Kallon MEEMA Laɗifa tayi tace mata, "let's go." Tashi tayi ta bi bayan ta suka shiga wani ƙayataccen parlour'n sai dai shi be kai wancan girma ba, amma ya fi haɗuwa sosai da sosai Wata matashiyar yarinya wacce a shekaru baza ta fi 8yers ba ke zaune a parlour'n tana buga Game a t.v, Remote ɗin na hannun ta tana sarrafa wa. Daga ita sai siririn wando da vest a jikinta, ganin su yasa ta tsayar da abun da take yi tana faman kallon su Shi kuma house maid ɗin yace musu, "su zauna." Zama suka yi while Laɗifa sai baza idanu take yi a parlour'n kasancewar yayi mugun tafiya da ita, babu shakka kuɗi na inda suke, baza ka taɓa cewa a duniya kake ba idan ka ji ka a cikin parlour'n nan saboda tsantsan tsaruwar shi. Sosai haɗuwar sa ya tafi da ruhin Laɗifa kasancewar bata taɓa tozali da irin tsararren gidan nan ba While MEEMA kuwa kasancewar ta taso a wanda ya fi shi sau miliyan shiyasa bata tsaya kallo ba domin babu abinda ya birge ta sai wani hoto da ta ƙyalla ido ta hanga. Hakan yasa ta sake ɗago kai ta sauke a kan yarinyan da ke zaune tana bin su da kallo sannan ta sake mayar wa a kan hoton. Yarinyar ce a cikin hoton ita da wata wacce bata kai ta Shekaru ba, sun rungume mutumin da ke a cikin hoton duk kan su suna dariya, tsananin kaman da suke yi da shi dole ka gane mahaifin su ne, babban Mutum ne domin ya sha manyan kaya me ruwan madara, riga da wando da malin-malin ɗin shi, a ƙalla bazai wuce shekaru 37years ba, amma tsaban kwarjinin shi da tsantsan kyawun shi dole sai ya cika maka ido. Shiru tayi tana kallon fuskar mutumin tana son zurfafa tunanin ta, sai muryan yarinyar ya dawo da ita a cikin hayyacin ta. Hakan yasa ta mayar da kallon ta wajen ta Faɗa yarinyar take yiwa hause Maid ɗin a kan shigowar su MEEMA cikin parlour'n Shi kuma yake sanar mata, "Mahaifin ta ne yace a kawo su wurin." Sai ta ja dogon tsaki tana ɗaukan Remote ɗin taci gaba da Game ɗin ta bata sake magana ba bare tabi ta kansu While me aikin tuni ya fice Su kuma suka zauna jigum babu wanda ya sake bi ta kansu. Har MEEMA ta gaji ta juyo da kallon ta ga Laɗifa tana cewa, "I'm so tired I'm leaving." Hannu Laɗifa ta saka ta riƙe nata tana marairaice fuska da cewa, "Please let us wait a little longer, since we have come so far we will sit and wait." Bata ce komi ba ta ɗauke kai ta mayar ga T.vn da yarinyar take yin Game. Sai kawai ta shagaltu da kallon Game ɗin domin tunawa tayi da itama sanda take gida, a lokacin da Abee ɗin ta yake lafiya, tare suke buga Game ɗin suna farin ciki da nishaɗi, kasancewar ta me matuƙar son game shiyasa ba sa rabo da buga wa tare, kala-kala take da su domin har ɗakin Games ne da ita... Hawaye ta ji sun cika mata idanu ta kai hannu ta share waɗanda suka silalo mata a kunci tana ɗan jan majina kaɗan. _Barka da wannan rana me albarka. Ina ma ɗaukacin masoya na murna da zagayowar wannan rana ta juma'a. Allah ya sada mu da albarkatun ta yasa mu dace duniya da lahira. Ayi weekends lafiya._ [14/10, 9:54 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_22*                   Yanda aka shanya su a wurin ne yasa ran MEEMA ya ɓaci ta miƙe tana kallon Laɗifa fuska babu walwala tace, "Please get up and go. I'm very tired." Bata kai ga yin magana ba sai wata yarinyar ta fito a guje tana kiran sunan, "Aunty Hafsah.. Aunty Hafsah." Tafaɗa kan kujeran da ƴar uwan ta ke zaune "What's wrong?" Ta tambaye ta tana ajiye Remote ɗin hannun ta Ita yarinyar tuni ta mayar da kallon ta kan su MEEMA tana kallon su. Sai kuma ta nuna su da yatsa tana cewa, "Aunty waɗannan fa su wane ne?" "Oho ki tambaye su ga su nan." "Baby come I want to ask you." Cewar Laɗifa tana ma ƙaramar murmushi Hakan yasa ta taso izuwa wurin ta Sai ta riƙe mata hannu still tana mata murmushi tace, "what's your name?" "My name is Yusra." "Ok Yusra ko zaki kira mana mahaifin ki?" Gyaɗa mata kai tayi kana ta juya da gudu ta hau upstairs Tafiyan ta yasa Laɗifa ta kalli MEEMA tace, "Sister, sit down. Now she will be called for us, Let's wait a little longer." Ɗauke kai tayi bata ce komi ba kuma ta ƙi zama Babu jima wa sai ga Yusran sun fito ita da mahaifin nata. Daga shi sai jallabiya fara sol da waya a kunnen sa yana amsa call Har suka sauko ƙasa Laɗifa idanun ta na kanshi, sosai take tasbihi da tsantsan kyawun da Allah ya yi masa While MEEMA itama tunda ta kalle su sau ɗaya sai ta sami wuri ta zauna Har ya iso wajen hankalin sa be kai ga su Laɗifa ba, sai da ya zauna a ɗaya daga cikin manya-manyan kujerun parlour'n sannan ya sauke fararen idanun sa a kan su Hafsah da Yusra tuni sun haye kan shi While shi kuma yana ci gaba da wayan shi, sai dai tunda ya ɗaura idanun sa a kan MEEMA ya ƙi ɗauke wa. Hannun sa ɗaya na a saman giran sa yana murza wa hakan yasa baza ka gane ita yake kallo ba Ita kuma a jikin ta taji ana kallon ta shiyasa ta sake ɗaga kai a karo na biyu ta kai duban ta gare shi. Hakan yasa idanuwan su suka shige cikin na juna. Ko soconni bata ɗauka ba ta cire nata idanun tana jin gaban ta na faɗuwa matsananciya, tabbas tana ji kamar ta san wannan fuskar, a jikin ta tana jin kamar ta taɓa ganin sa Shima haka a wajen sa. Shiyasa ya kasa cire idon sa a kanta yana son tuna inda ya san fuskar ta. Be ɗauke idanun nasa ba har sanda ya tuno ta kuwa. Ya tuna sanda ya je Umrah ya hayo jirgi daga Riyadh, ita ce wacce suka zauna a jirgi tare zuwa Abuja. A lokacin ya dawo da dare babu wanda ya sani shiyasa ya wuce gidan Abokin shi Hashim a barikin sojoji ya kwana. Tabbas ita ce. Hakan yasa ya lumshe idanuwan sa yana me sake buɗe wa a kanta, sallama yayi da wanda suke wayan ya mayar da kallon shi sosai a kan su har Laɗifa yace, "ku ne kuke nema na?" "Eh ranka ya daɗe!" Inji Laɗifa cike da murmushi a fuskar ta "Ok sorry I settled you, there's something I'm doing what's important in it." Hakan yasa MEEMA ta sake ɗago kai ta kalle shi jin abun da yace, sai suka sake haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta Shima haka janye nashi idon yayi yana kallon yaran nashi da cewa, "ku ɗan bamu wuri zamu yi magana My Babies." "Ok Daddy." Suka faɗa a tare suna tashi da gudu suka yi cikin gidan "Ina sauraron ku. I give you ten minutes to do what brought you here." "Ok Sir." Laɗifa ta faɗa da sauri tana amsar Laptop ɗin hannun MEEMA ta buɗe Ita kuma ido kawai ta zuba mata bata ce komi ba.              Nan ta soma mishi tambayoyi tun daga full name ɗin shi zuwa shigan shi siyasa A taƙaice dai ba wani amsa mata sosai yake yi ba, wasu ataƙaice yake bata amsa. Daga ƙarshe duba agogon sa yayi yace, "lokaci ya cika. Ina da abun yi." Sai ya tashi ya wuce be jira cewar su ba Dole su ma suka tashi suka fice a gidan. Sanda suka hau mota Laɗifa take cewa, "I don't think we will ever see him wlh, he is very well connected and it is beautiful, but I honestly didn't like the way he answered our questions." MEEMA da ta kwantar da kanta a jikin kujeran idanun ta a rufe, tana jin ta but ko magana ta gaza yi sabida ɗan tunanin da ya hau mata kai, so take yi ta tuna inda ta san fuskar nan domin ya tsaya mata a rai. Sai da Laɗifa ta taɓa ta sannan ta ɗago kanta tana kallon ta "I mean you're silent what do you do?" "Nothing." "Ok call Bro Idris and let him know we're done." Laɗifa tafaɗa tana ci gaba da tuƙin MEEMA bata ce komi ba ta ɗauki waya ta soma neman layin Idris. Sai dai a kashe aka ce Laɗifa tace, "maybe it is still not in Zaria. We'll try again later." Da haka suka ƙarisa wajen aikin su.            Zuwa ƙarfe uku Laɗifa tayi dropping ɗin ta a gida. Lokacin da ta shiga Parlour Hajiya da Zabba'u suna zaune sun yi baja-baja da kaya "These are your belongings, come and see if they do it for you." Cewar Hajiya bayan MEEMAN ta zauna Kallon kayan take yi bata ko motsa ba Zabba'u da ke washe baki tace, "These items are all Hajiya's choice for you. In fact, Hausa clothes will look good on you. God willing, they will please you." MEEMA kallon Hajiya tayi tace, "Thanks grandma, I am very happy." "Ok come and see. Look at everything that is not yours and you will be changed." Kanta ta gyaɗa kafin ta tashi ta iso gaban kayan ta durƙusa tana duba wa While Zabba'u tana taya ta ɗauko wa Atamfofi ne da lessi sai materials kala-kala. Sai takalma har da gyale Ɗago kai MEEMAN tayi tana kallon Hajiyan a marairaice tace, "But how can I use them? I can't." Dariya suka yi mata Hajiya tace, "You will learn, no matter what you say you can't. Since you came back to our country you have to learn all our culture." Murmushi kaɗai tayi tana ci gaba da ɗaga kayan, wasu kuma sai ta kara a jikin ta kafin take ajiye wa Hajiya tace, "You go with Zabba'u to take your sewing, then choose the style you want. Go eat and rest later and take it to your sewing shop." "Ok." MEEMA tafaɗa tana tashi ta wuce ɗaki Yayinda Zabba'u kuma ta haɗa kan kayan ta mayar a cikin leda.               Koda MEEMA ta shiga ɗaki wanka tayi ta saka riga da wando masu taushi ta fito Parlour. Abinci ta sawo ta zauna a gefen Hajiya tana ci tana sauraron hiran nasu. Sai da ta gama ta wuce ɗaki ta ɗaura after dress baƙi a saman kayan ta tayi Rolling da ɗan kwalin shi kafin ta fito suka fita. Drever ya ɗauke su suna shirin fita itama Ummee ta dawo gidan.                Koda ta shiga parlour'n ta tarar da Hajiya. Sannu da gida tayi mata kafin ta tambaye ta, "ina su MEEMA zasu je ta gan su a mota?" "Kaya ne na ɗaukar mata wajen Dillaliya, ɗazu nace ta kawo min shi ne zasu kai ɗinki." Gyaɗa kanta tayi, sai kuma tace, "amma Hajiya da kin bari na siyan mata da kai na kar ɗawainiyar yayi miki yawa." Hajiya tace, "yanzu ma ban hana ki siyan mata naki ba, Ni nayi ra'ayi baza ki hana Ni abun da nayi ninya ba." "To Hajiya ai ba na faɗa bane abun." Ummee tafaɗa tana murmushi Shiru Hajiya tayi mata tana mayar da idanun ta kan t.v dake faman aiki shi kaɗai Ita kuma Ummeen sai ta wuce sama inda ɗakin ta yake. Sai da tayi wanka ta sauya kaya kafin ta fito ta zuba abinci ta dawo Parlour. Tana cikin ci ne sai kuma ta kalli Hajiya da cewa, "Hajiya baki yiwa MEEMA magana a kan ƙadaran mahaifin ta ba, ya kamata a san abun yi sabida be kamata a bar su a can ƙasar babu me kula da komi ba, sannan akwai magada a ciki kamata yayi a sauke mishi nauyi tun yanzu." Hajiya da ta dawo da kallon ta kan Ummeen tace, "nayi tunanin hakan, sai dai be kamata mu tayar da maganar yanzu ba, mu bari zuwa nan gaba bayan ta sake sakin jiki sosai damu, har yanzu ina ganin damuwa sosai a tattare da MEEMA, har yanzu ba wai ta manta mutuwar mahaifin ta bane, shiyasa duk wani abun da zai saka ta farin ciki nake iyakan ƙoƙari na wajen naga nayi mata. Tunda ke kin gaza a matsayin mahaifiyar ta ki bar ni Ni inyi mata, Ni kaɗai take kallo take jin daɗi a yanzu." Cike da sanyin jiki Ummee tace, "Amma Hajiya mene ne na gori kuma?" "A'a ba maganar gori bane gaskiya na faɗa. Yarinyar nan tana cikin damuwa tsantsa, ko fuskar ta kika kalla bata cika yin fara'a ba, wani abun ma tana yi ne kawai domin mu, don haka ba na son ma a cika mata maganar da zai riƙa tuna mata da mahaifin ta." "To shikenan." Cewar Ummeen tana ajiye Plate ɗin abincin. Sai kuma ta ɗauka ta kai kichen ta haura sama.             Ba su wani jima ba su MEEMA suka dawo gidan.             Da dare suna cin abinci a dainning Idris ya shigo gidan. Kai tsaye wajen su ya nufa yana jan kujera ya zauna yace, "nima yau da Ni za'a ci abincin duk da na cika ciki na daga gida." Hajiya tace, "dama wa ya isa yace ban da kai za'a ci Mijin?" "A'a gaskiya ban girka da kai ba, ka tashi ka bamu wuri." Inji Zabba'u cike da barkwanci "Wai kin ji Hajiya in tashi?" "A'a zauna ka zuba abun da ranka yayi maka, idan ba ka kawo wa taya za su samu su ci?" "Yauwa Hajjaju na Ni kaɗai, an dai Gwale wasu." Yafaɗa yana dariya Su ma dariyan suke taya shi ban da MEEMA da ido ta zuba musu tunda ba ta fahimta Gaishe da su yayi kafin ya mayar da hankalin sa kan MEEMA yana tsokanar ta Ita dai murmushi kaɗai take mishi har suka gama cin abincin suka koma Parlour A nan ya ɓata lokaci kafin yayi musu sallama ya tafi. Dama ya zo wajen MEEMA amsar Laptop ne kasancewar ita ta taho da shi lokacin da suka tashi daga aiki tunda nashi ne. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️                Horn tayi har kusan biyar kafin me gadi ya buɗe mata ƙofa. Ta shige da motan ta zuwa wajen parcking. Fitowa tayi ta nufi Part ɗin su da ke a cikin gidan Tana shiga parlour'n Momy da Abdul dake magana suka tsayar da maganar suna kallon ta Ita kuma kai tsaye kan kujera ta nufa ta zauna tana ajiye numfashi "Har kin dawo?" Cewar Momyn still tana kallon ta "Eh." Ta bata amsa a taƙaice. Sai kuma tace, "Momy da zan fita naga wasu ƴan jarida sun shigo nan gidan." "Nan gidan kuma?" Tafaɗa Momy mamaki cike a fuskar ta Shima Abdul ya ƙara da cewa, "kina nufin ƴan jarida suka shigo gidan nan? To waye ya gayyato su?" Tsaki ta ja da cewa, "waye kuwa ban da Yaya Umar. Wajen shi suka ce sun zo." Momy tace, "Mata ne ko maza?" "Mata ne su biyu suka zo, Ni ban ma ga sun yi kama da ƴan jarida ba gaskiya." Momy tace, "ba na tunanin Umar Faruk zai gayyato su nan gidan duk da dai ban sani ba, amma kin san zaɓe ya kusa nan da kwana huɗu dole dama zasu takura masa, but mun yi maganar da shi kuma na san bazai ƙetare magana ta ba, babu wani amfanin yin hira da ƴan jarida bare har su tako wannan gidan." "Gaskiya ne Momy, Ni ina ga wankin hula yana so ya kai mu ga dare." Abdul yafaɗa fuskar sa babu walwala ko ɗigo. "Momy i hate this Guy wlh! na gaji na gaji da ganin shi kiyi wani abu don Allah, Nima fa Ina so na fara watayawa a ƙasar, don Allah jibe yanda ya jajibo wani siyasa saboda iyayi don ya ga uban shi yayi, so nake yi Ni in gan Ni a matsayin sa Momy amma ba shi ba, Ni ya kamata nayi suna ba shi ba Momy. Sannan a kan wannan siyasan kowa zai san waye shi and kowa zai san arziƙi mu muke ci a gidan nan. Wannan ai tonon asiri ne." Ajiyan zuciya Momy ta sauke tana kallon shi tace, "kayi haƙuri Abdul da sannu burin mu zai cika, da sannu komi zai kasance namu, Ni fata na ba na so muyi wani abun da zai ja hankalin police a gidan nan, ka san yanda muka kashe Nusaiba a gidan nan, mun bata guba ta ci daƙyar muka samu muka tsallake zargin ta, ba don mun biya ASP kuɗi me yawa ba ba na tunanin zai goge hujjojin da ya samu a kan gaskiyar guban da aka bata, so dole sai da dabara burin mu zai cika a kan Umar Faruk, muna da sauran lokaci da zamu aiwatar da shirin mu, yau saura kwana huɗu ayi zaɓe, kafin lokacin dole zamu cika burin mu a kan shi, sai dai wani ba shi ba." Duk kan su murmushi ne ya suɓuce a fuskar su Yayinda Luwaira wacce fuskar ta babu walwala ta buɗe baki da ninyan yin magana sai suka ji Nocking a bakin ƙofa Shiru duk suka yi ko wanne yana kallon ƙofan. Sai da aka sake Nocking ɗin ne kafin a tare Momy da Abdul suka amsa, "yes. Waye ya shigo." Hafsah da Yusra ne suka fara shigo wa kafin shi ya biyo bayan su. Kamar yanda ya saba yayi shigan shi na manyan kaya, farar shadda wacce sai maiƙo take yi tsaban sabunta da ɗaukan guga, tamkar wani ango sabida kyawun da yayi, gaba ɗaya turaren sa ya cika parlour'n da ƙamshi. Da gudu yaran suka isa wurin Momy suna rungume ta. Yayinda shi kuma ya taho a cikin ƙasaitan sa ya sami wuri a kan kujera ya zauna Momy sai rungume yaran take yi tana musu maraba da zuwa fuska a washe While Abdul yace, "to ku taho nan mana yara na, Momy kaɗai kuka sani ne?" Da gudu suka dawo jikin shi suna kiran sunan shi da, "Uncle Abdul." Ya rungume su yana cewa, "yauwa babies ɗina." Umar Faruk da ke murmushi sabida yanda suke nuna wa yaran shi ƙauna sai ya mayar da idon shi kan Momy yace, "dama zan fita ne ina da meeting sai zuwa dare zan dawo, kuma ba na so su zauna su kaɗai, idan na dawo komin dare zan zo in ɗauke su." Momy cike da fara'a tace, "ok babu damuwa my son. Ka kula da hanya ka san zaɓe ya kusa, kar ka soma ka fita kai kaɗai ka je da masu tsaron ka Please my son. Allah ya kiyaye ya dawo min da kai gida lafiya, Allah ya bada sa'ar abun da aka je nema kaji ko?" Cike da jin daɗi wanda ya nuna a fuskar shi yace, "Amin Momy. Sai na dawo." Ya ƙare maganar da tashi tsaye. Idanun sa a kan Luwaira yace, "Luwaira babu addu'a kamar muna faɗa?" Murmushi tayi tace, "haba yaya ko zan yi faɗa da kowa ai bazan yi da kai ba. Ina jiran Momy ta gama nata ne Nima inyi maka nawa special." Murmushi yayi da cewa, "no ba na tunanin naki ne special ke dai kar ki ɓige da daɗin baki. Na Momy na ne special. Yanzu dai yi min naki in tafi." Daga Momy har ita dariya suka yi Momy tace, "yauwa ɗan albarka ashe dai ka gano ta." Murmushi yayi kaɗai Luwaira tace, "to Yaya Allah ya tsare ya kare hanya." "Amin my dear sister. Ban manta da maganar ki ba idan na dawo zamu tattauna ko zuwa gobe." Washe baki tayi tace, "to Yaya." Daga nan fita yayi bayan ya sake yiwa yaran shi Ba-bye.                  Yana fita Momy ta kira Talatu me aikin ta tace, "kwashe su ki wuce da su ɗakin ki ku zauna tare." "To Hajiya." Tafaɗa tana jan hannun yaran Sai Hafsah ta ɓata fuska tace, "Ni bazan je ba wajen Uncle Abdul zan zauna, ai yace zai kai mu shan Ice cream." "No Hafsa ki je wajen ta ai ba yanzu zan fita ba, yanzu akwai abin da zan yi zuwa anjima sai mu je ko?" Yafaɗa hakan da murmushi a fuskar sa yana riƙe da kumatun ta da hannayen sa biyu Murmushi tayi masa sannan ta bi bayan Talatun da ke riƙe da Yusra suka wuce Tafiyan su Luwaira ta ja dogon tsaki tace, "wlh Momy na tsani yaran nan sosai kamar yanda na tsani uwar su. Ni ban ga amfanin su ba, kamata yayi su ma a aika su inda uwar su ta tafi." "To abin hauka ne ashe? Ki bar maganar yaran nan ƙananan alhaki, idan mun gama da uban su zamu dawo kan su. Shirin mu kawai na plan A. Yanzu zamu mayar da hankali, idan haƙan mu be cidda ruwa ba zamu sauya wani shawaran. Abdul kai yanzu ya kamata ka samo mana waɗanda zasu yi aikin nan, in two days komi zai kammala ba na son a wuce wannan ranan." "An gama Momy. Bari in je akwai inda zan je yanzu. Idan na dawo zamu yi magana." "To." Daga haka ya tashi ya fice Luwaira kuma ta dawo kusa da Momyn tana ɓata fuska da cewa. "Ni Momy meyasa baza ku amince da nawa plan ɗin bane? Gaskiya ba na jin zan haƙura da shi cikin sauƙi haka. Ku taimaka min Momy." "Ban san shirmen banza ke Luwaira. Wai meyasa kike haka ne sai mun kai magana ki dawo damu baya? Gwara ma idan zaki cire wannan shirmen naki a zuciya ki cire shi tun wuri, baza ki taɓa auren Umar Faruk ba, ke ma kin san da haka kar ki sake zuwar min da wannan maganar. Dalla tashi ki ban wuri." Zumɓura baki tayi tana ƙunƙunai kafin ta tashi ta wuce Ita kuma ta ja dogon tsaki tana bin ta da mugun kallo. "Idan ba iskanci irin naki ba ko mu mun amince shi zai amince ne? Ba na tunanin zai taɓa auren ki tunda yana kallon ki a matsayin ƙanwar shi ce. Kina so ki mayar da mu baya naga alama zamu dena saka ki a aikin mu, duk wannan abin da nake yi ina yi ne duk don ku amma ke ta banzan shirmen ki kike yi, to sai dai ki mutu kuwa don baza ki taɓa auren shi ba." Haka Momyn ta ci gaba da faɗa ita kaɗai duk da ita Luwaira tuni ta wuce ɗaki abun ta. [14/10, 9:55 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_23*           Yau SATURDAY ranan da aka tashi da zaɓe na senetoci shiyasa ko ina ana hutu makarantu da wajen aiki. Su MEEMA ma yau suna gida suna hutu, shiyasa bata tashi barci ba sai ƙarfe 11:09am. Ta farka. Wanka ta soma yi ta saka doguwar riga fara me taushi da zanen followers a jiki. Ta fito Parlour ta sami su Hajiya zaune har da Ummee suna taɓa hira. Zama tayi a gefen Hajiya bayan tayi kissing ɗin hannun ta kamar yanda ɗabi'ar ta kenan gaisuwar ta Hajiya tace, "Hope you are well?" "Alhamdulillah." Ta amsa ta tana kallon ta Zabba'u tace, "Weldon you slept. Today is a holiday." Murmushi tayi mata "Go to Breakfast there and lie down." According to Hajiya Hakan yasa ta tashi ta wuce kan dainning ɗin Ummee da ke aiki a computer ta ɗago tana kallon Hajiya tace, "Hajiya zamu fita da MEEMA zuwa kasuwa, kiyi mata magana sai mu je tayi shopping abun da take so, and Ina so in je gidan Hajja Salma sai mu je tare su gaisa, dama tayi min complain bata san ta ba." "To ke meyasa baza ki faɗa mata ba sai Ni? Ki sanar mata idan zata bi ki sai ku je." Ummee tace, "ok." Sannan ta ci gaba da aikin ta.               Bayan MEEMA ta gama Breakfast ɗin ne ta dawo parlour'n ta zauna Ummee looked at her and said, "We are going to go shopping. If there is anything you need, we will go and buy it." "No I don't need anything." Tafaɗa ba tare da ta kalli Ummeen ba "Why do you say that? I know you need MEEMA, you will follow me to go because I want to go to my friend's house and greeting". Shiru MEEMAN tayi bata ce komi ba Hakan yasa Ummee tayi tunanin ko ta amince ne, sai ta ci gaba da aikin gaban ta Hajiya tana ji bata tanka ba hiran su suke yi ita da Zabba'u While MEEMA tana latsa wayan ta Can Ummee bayan ta gama abin da take yi ta tashi tana kallon MEEMAN tace, "Go get ready and we'll go out." "I will not go anywhere." Tafaɗa a wannan lokacin tana kallon ta Shiru Ummeen tayi kamar zata yi magana kuma sai ta juya ta haye sama Hajiya kallon MEEMAN tayi tace, "Why are you like that?" Da ido ta bi ta ba tare da ta fahimce ta ba "Don't do that to your mother. She's your mother. You shouldn't argue with her. Get up and follow her." Girgiza kanta ta soma yi har hawaye sun cika mata ido. "No, I'm not going. I'm not happy if I follow her." Tafaɗa tana miƙe wa ta wuce ɗaki da sauri Da kallo suka bi ta har ta ƙule Zabba'u tace, "wai Ni Hajiya mene ne ya haɗa su ne take yiwa Hajiya ƙarama haka? Kawai fitan da zasu yi ne tare shi ne take cewa baza ta je ba hakan be dace ba." "To ai duk yanda kika gani da laifin Zulaiha. Sannan kinga rayuwar su da na nan ba ɗaya bane. Dole sai kin taimaka min wajen mun fahimtar da ita muhimmancin uwa, yanzu tana kallon mahaifiyar ta ce a maƙiyiyar ta kuma kin san hakan be dace ba tunda uwa uwa ce. Ni kaina ba na so ta ci gaba da nuna wa mahaifiyar ta tsana." "To Allah ya kyauta Hajiya, ai a sannu zata saba komi zai wuce tunda yanzu suna tare a gida ɗaya". Cewar Zabba'un tana tashi tsaye zata wuce kichen. Sai kuma suka ji Nocking hakan yasa ta wuce bakin ƙofan ta buɗe. Zaro ido tayi tana kallon Matar da ke tsaye riƙe da hannun ƙaramin yaro da bazai gaza shekaru bakwai ba. Washe baki tayi tana kiran sunan ta. Sai kuma ta juya tana cewa, "Hajiya Jalila ce ita da Habeeb." Jalila murmushi tayi ta shigo tana cewa, "ina Hajiyar tawa? Yau na kawo miki Mijin ki." Dariya Hajiya tayi da cewa, "maraba lale yau dai muna da babban baƙi kenan?" "Ai ba mu kaɗai bane har da Abban shi." Inji Jalilan tana zama Kafin ma suyi magana sai ga shi ya shigo Hajiya bata san sanda tayi yunƙurin tashi daga kujeran da take zaune ba. Sai dai kasancewar ta kasa dole ta zauna tana bin ɗan nata da kallo Shi kuma da sauri ya iso yana kiran sunan ta. Ai rungume ta yayi tsaban murna sai ga hawaye Itama haka hawayen ta fara bakin ta na rawa tace, "Hashimu ashe zan sake ganin ka? Kai ne dai ka dawo?" Ɗago kansa yayi yana murmushi da hawaye a tare yace, "Hajiya Allah yayi mun dawo. Yau dai gani ga Hajiyata." Sai ya sake rungume ta Zabba'u kuwa baki har kunne, ai sai ta ruga zuwa sama don sanar wa da Ummee. A tare suka dawo Ummee kamar zata kifa tsaban sauri Shi kuma yana ganin ta sai ya tashi ya nufe ta yana faɗin, "Aunty." Hannayen sa ta riƙe cike da tsantsan farin ciki tace, "na kasa yarda da aka ce min kai ne ashe dai kai ɗin ne? Gaba ɗaya ka manta damu?" "Haba Aunty Kar ki CE haka, kin san aiki. Inda muka je gaba ɗaya babu network muna daji, jiya na sauka muka taho yau." Yafaɗa yana koma wa ya zauna Itama zama tayi sannan aka sake gaisa wa Zabba'u tuni ta cika musu gaba da drinks Hayaniyan su ne ya fito da MEEMA dake ɗaki Uncle Hashim shi ya fara hango ta, sai ya waro ido yana faɗin, "wa nake gani kamar MEEMA?" Sai kuma ya kira sunan ta Hakan yasa ta dawo da idon ta kanshi. Sai kuma ta nufe shi itama tana kiran sunan shi Cike da farin ciki ya tashi ya rungume ta yana cewa, "When did you come back here? Are you already here?" Hajiya ce ta ba shi amsa tana faɗa mishi dalilin dawowar ta Hannun ta ya riƙe suka koma suka zauna. Cike da tausayin ta yayi mata ta'aziyyar mahaifin ta Kasa magana tayi saboda yanda idanuwan ta suka cika da hawaye Yace, "Be patient my daughter. Pray for him because he is the only one who needs it. May God forgive us for his loss." Duk suka amsa da, "Amin." Ban da MEEMAN da har yanzu ta kasa magana Hajiya kallon Habeeb tayi da ya maƙale a jikin mahaifiyar shi tace, "kai kuma baza kazo bane mu gaisa? Ko har ka manta da Ni ne tunda dama ka rabu da zuwa gaishe Ni?" Tashi yayi ya iso wurin ta Ta kama shi tana shafa kanshi tace, "Miji na yau dai ga ka a gida, ga kuma Baba ya dawo ko sai murna?" Murmushi yayi yana gyaɗa mata kai "Ai yau tunda muka tashi da safe yake murna zai zo wajen Kaka, dayake ya tashi da zazzaɓi a jikin sa amma hakan be hana shi murna ba, zaman mota ne yasa duk yayi yaushi kafin mu zo amma da kuzarin shi muka zo don ya dame Ni har yanzu ba'a kawo ba?" Cewar Jalila tana murmushi Dariya duk suka yi Hajiya tace, "ayya ashe mijin nawa babu lafiya ne? Ai ko be kamata a bar shi haka ba. Zabba'u ki samo mishi magani sai a ba shi, amma kafin nan ki dama mishi ko Custard ne sai a ba shi kafin a gama girki." "To Hajiya." Tafaɗa tana yinƙura wa ta tashi Su kuma hira suka ɗan fara taɓa wa While Uncle Hashim kallon MEEMA yayi suka sakar wa juna murmushi. Sai ya saka hannu ya riƙe nata hannun yana cewa, "My baby has grown, how did you grow up so much? I miss you so much." Dariyan farin ciki ta saki wanda zai tabbatar maka da cewa tabbas tana a cikin farin ciki sosai. Dayake sun saba da shi, a lokacin da tana yarinya kusan ko yaushe yana yawan ziyartan su can Riyadh musamman domin ta, tunda dai aka ƙara mishi matsayi a wurin aiki ne ya dena zuwa amma duk da haka suna waya sosai, sai kuma tafiyan nan da yayi ya jima dole ta dena jin wayan shi, duk da bata yi tunanin ko aiki ne yasa ta dena samun shi a waya ba sai dawowar ta da Hajiya ta sanar mata. Kanta ta ɗaura a saman kafaɗan shi tace, "I miss you so much, Uncle!" "Now I know you graduated?" Gyaɗa masa kai tayi "Now you are getting married. However I thought I would come back and find out you are married and I will see your children walking." Ya ƙare maganar yana kwatanta wa da hannun sa Duk dariya suka yi har su Hajiya da suke hiran su daban Yayinda ita kuma ta shagwaɓe fuska da cewa. "Uncle I am still a young girl." "Really?" Tura masa baki tayi Murmushi yayi yana sanya hannu ya ɗan bugi goshin ta Tace, "oshhh! Uncle it's hot." "You still don't change my daughter." "I also see that she is still unchanged." Cewar Jalila tana murmushi Hajiya tace, "Now that you're back, you're going to get marry her." "No. I'm not going to get married now. I haven't finished my studies yet. I'm just starting to work and I'll be long before I get married." Tafaɗa tana kallon shi "Well daughter no matter what you say, what you want is what I want too." Shima yayi maganar idanun shi a kanta yana mata murmushi Itama murmushin tayi tana sake mayar da kanta a jikin shi Jalila tashi tayi tana cewa, "Hajiya bari in Kai kayan mu ɗaki." Ta wuce ta ja Trollyn tayi sama A lokacin ne Zabba'u ta dawo da Custard ɗin ta gama dama mishi. Ta zauna tana cewa, "to zo ga shi na gama dama maka ka sha." Taso wa Habeeb ɗin yayi daga jikin Hajiya ya taho wurin ta. Ita take ba shi da kanta bayan ta zaunar da shi a cinyan ta.                 Da haka dai suka kasance a ranan suna tare suna ta hira. Sallah kaɗai ke tayar da su a wurin. Sai da aka gama abinci suka haɗu gaba ɗaya suka ci a saman dainning sannan suka dawo Parlour suka dasa hira. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️           "Har yanzu Allah be bamu Sa'a a kan wannan yaron ba, na rasa meyasa har yanzu yake tsallake shirin mu. Yanzu wai ya zamu yi ne?" "Momy ba fa matsalar mu bane, kin san kwana biyun nan ba ya zama dole baza mu samu damar aiwatar da komi ba, kuma kinga yau gidan cike da jama'a duk masu taya shi murnar samun kujeran nan ne, dole mu jira har sanda komi zai yi sauƙi." Tsaki ta ja tana tashi ta soma zagaye. Can kuma ta juyo tana kallon Abdul tace, "yanzu ina Umar Faruk ɗin?" "Na bar shi da wasu Mutane a waje, ya ce yanzu zai shigo idan suka gama." "To ka tashi ka je kar yazo ya tarar da mu a nan." Tashi yayi ya fice.           Babu jima wa sai ga Umar Faruk ya shigo parlour'n da sallama Momy saurin sauya fuskar ta tayi tana murmushi tace, "ah ah my son ƙariko mana ka zauna." Taho wa yayi ya zauna a kujeran da ke facing ɗin nata "Yanzu Abdul ya fita yake sanar min da daddaɗan labari. Ashe har an sanar da zaɓen ne?" Murmushi yayi da cewa, "A'a Momy akwai saura, mu namu ba'a tabbatar ba dai. Zuwa anjima muke tunanin komi zai kammala." "To ai dai tunda kaji haka insha Allahu kai ne da Nasara, na san yaro na bazai wuce shi ne da Nasara ba da yardan Allah. Kai na Mutane ne kamar yanda mahaifin ka shima na Mutane ne, ina da tabbacin kai ne zaka lashe zaɓen nan." "Amin Momy." Yafaɗa cike da jin daɗi Gyara zaman ta tayi tace, "ya maganar mu da muka yi da kai a kan neman matar aure? Kar ka manta fa yanzu kowa idon shi na kanka, kana da wannan babban matsayin amma ace baka da mata wannan be dace ba, dole ka nema wa su Hafsah mahaifiya ko su ma zasu ji daɗin uwa a halin yanzu, Nusaiba ta rigada ta tafi inda kowa zai je baza ta taɓa dawowa ba. Ba na so Mutane suna ma yaro na kallon ƙaramin mutum wanda zai gaza musu. A kullum da wannan batun nake kwana nake tashi kullum ina cikin zullumi da tunani." Ta ƙare maganar nata fuskar ta cike da damuwa Shiru yayi kansa a ƙasa ya gaza cewa komi "Umar ka duba magana ta komi ina yi ne domin ka, bazan so ace yau duniya tana zagin min ɗa ba, kai ɗana ne wanda nake ji kamar Ni na zuƙuna na haife ka. Mahaifiyar ka ta haife ka ne kawai amma Ni nafi kowa ƙaunar ka. Ina son ka ba na son abinda zai same ka, ba na iya barci a ɗan kwanakin nan tunda ka kama siyasan nan." Ta ƙare maganar da fashe wa da kuka Da sauri ya ɗago yana kallon ta jin muryan kukan ta. Sai kuma ya tashi izuwa gaban ta jikin sa har rawa yake yi ya riƙo hannayen ta. "haba don Allah Momy mene ne na kuka kuma? Don Allah ki dena. Duk abun nan da kika ga ina yi; wa nake da shi da zan yi dan shi idan ba ku ba? Bani da kowa sai ku, na rasa kowa nawa amma kun zauna da ni, kin zame min mahaifiya sannan ga ɗan uwa na samu ga kuma ƙanwa duk kin maishe su nawa. Kina nuna min duk ƙaunar da uwa zata nuna wa ƴaƴan ta. Don Allah ki dena kuka na yarda zan yi aure ko domin farin cikin ki ne Momy." Sai yayi shiru saboda jin hawaye sun cika mishi ido. Daƙyar ya furta. "Zan yi auren Momy." Murmushi tayi tana saka hannu ta riƙe nashi hannayen tace, "Allah ya maka albarka my son, Ni dama buri na inga kana farin ciki ne a rayuwa, tunda Matar ka ta mutu ka gaza yin aure wanda hakan be dace ba, kowa yana maka kallon Mutumin kirki ba na son a soma maka akasin haka tunda yanzu ka ga idanun duniya a kanka suke, kana da babban matsayi a duniya, ina son aci gaba da kallon ka a haka. Tashi ka je Allah yayi maka albarka." Amsa mata yayi yana miƙe wa tsaye cike da sanyin jiki ya fice. Kai tsaye Part ɗin shi ya wuce ya shiga. Ɗakin yaran shi ya wuce ya duba ya ga suna barci sai ya haye sama inda ɗakin shi yake. Ya shiga ya yiwa kansa masauki a gaban gadon shi. Shiru yayi yana me kama kanshi da hannayen shi biyu. Shi Mutum ne me sanyin hali da rashin son hayaniya, shiyasa ko ya ya ne aka yi wani abu ko ya ɗan samu damuwa a ranshi yanzu sai duk ya rasa kuzarin shi, sai nan da nan kanshi ya soma ciwo har ya rasa sukunin shi, yana da matuƙar sanyin hali da tausayi sosai, abu kaɗan ke ɗaga mishi hankali shiyasa a sanda ya rasa Matar shi tashin hankalin da ya shiga ne ya haddasa mishi ciwon zuciya. Wanda har yanzu fama yake yi da kanshi kullum cikin magani. Ba ya son abubuwan da za suna tuno mishi da matar shi a koda yaushe shiyasa ya kasa ƙara aure yau kimanin shekaru shida kenan. Ta haifi Yusra da kwana ɗaya Allah ya ɗauki ranta sakamakon guban da ta ci a cikin abinci wanda su Momy suka sanya mata.              Nusaiba ta kasance ɗaliban likitanci yarinya ɗaya tilo a wurin mahaifan ta da suka kasance Malamai, a nan Kaduna suke zaune kuma ba wasu masu kuɗi bane, sai dai suna da rufin asiri sosai. Tun Umar Faruk yana karatu a ƙasar Amurka lokacin ya dawo hutu suka haɗu da ita sanda ya kai ziyara wajen wani abokin shi a makarantar su. Kamun kanta da tsantsan tarbiyyar ta yasa Umar Faruk ya faɗa soyayyar ta, domin Nusaiba ba wata kyakkyawar yarinya bace amma akwai ta da tarbiyya sosai, tun tana ƴar shekara goma tayi saukar alƙur'ani me girma. Kuma a sanda ta girma tana koyar da ɗaliban mahaifin ta a makarantar da ya buɗe. Binciken farko da Umar Faruk yayi a kanta wajen abokin shi wanda ya santa sosai. Shi ya tabbatar mishi da Malama ce ita sosai da kuma ƙoƙarin ta. Hakan yasa ya faɗa soyayyar ta kafin komawar shi ƙasar waje. Be yi ƙasa a gwiwa ba da taimakon abokin nashi ya bayyana mata soyayyar shi. Inda cikin ƙanƙanin lokaci suka gina soyayyar su me tsafta har zuwa sanda ya gama karatun shi ya dawo ya aure ta. A lokacin ya rasa iyayen shi domin tun yana yaro mahaifiyar shi ta rasu, shi kuma mahaifin shi ya auri Hajiya Salamatu wacce ita ce Momy, ta zo da yaran ta biyu gidan kuma tayi zama da mahaifin shi na shekara ɗaya kafin Allah ya ɗauki ranshi sakamakon ciwo da yayi. A lokacin Umar Faruk ya sake zama Maraya babu uwa babu uba bare ƴan uwa, sai Momy da ƴaƴan ta da suka nuna mishi ƙauna bisa son mallakar dukiyar shi da suke son yi, ya ɗauke su tamkar jinin shi be taɓa tunanin ba da zuciya ɗaya suke ƙaunar shi ba, be da wasu dangi da suka fi mishi su, duk abinda suke so yana musu kuma yana tsananin yiwa Momy biyayya tunda ya ɗauke ta kamar ita ta haife shi, yana ji a ranshi ya rasa uwa ce amma ita ce ta maye mishi gurbin ta. Sai dai shigowar Nusaiba cikin rayuwar shi sai ta fara fahimtar zagon ƙasar da suke yi mishi, wanda ta so ta fahimtar da shi ba ƙaunar shi ta Allah da Annabi Momy take yi ba amma ina bata ci galaba ba. Lokacin ta haifi Hafsah da shekara biyu ta samu cikin Yusra. Tun lokacin suke tagen yanda za ayi su kashe ta domin ba sa son tazo ta haihu ta sama mishi Magaji na miji, domin shi kanshi so suke yi su kawar da shi a doron duniya su mallaki komi da kuma dukiyar shi, basu ci Nasara ba sai da ta haihu a lokacin tana fama da rashin lafiya sakamakon haihuwar ya zo mata da tangarɗa, suka saka mata guba a cikin abinci ta ci ta mutu wanda ya ja cece kuce a tsakanin likitocin asibiti da ƴan sanda sakamakon a asibiti ta mutu, an gane cewa guba taci sai dai maganar be kai ga kunnen Umar Faruk ba suka san yanda suka yi suka siye ɗan sandan aka binne maganar.         Mutuwar Nusaiba ya taɓa Umar Faruk sosai domin Allah ya ɗaura mishi ƙaunar ta a zuciya, yana matuƙar son ta kuma yana jin ta a zuciya matuƙa. Mace ce me shiga zuciya bata da hayaniya ko kaɗan, tana da kirki da halin ƙwarai wanda idan har ka zauna da ita dole ne sai ka so ta. Mutuwar ta ya taɓa shi hakan yasa har yayi jinya sabida damuwar da ya saka a zuciya, wanda yanzu ya haifar mishi da ciwon zuciya.              Har yanzu burin su Momy su ga bayan shi amma sun kasa cin Nasara, yanzu haka suna ta shirin yanda zasu kashe shi ne ba tare da an yi zargin kisa bane domin su mallaki komi, mahaifin Umar Faruk wato Alh. Aliyu Bature ya rasu ya bar mishi ɗumbin dukiya har da gidajen mai guda uku wanda ake ji da su a nan Kaduna. Yanzu haka shi Umar Faruk ɗin ya gina babban Company na sarrafa shinkafa wanda shi ke kula da shi tare da Abdul. Sanadin shigan shi siyasa kuma mutanen mahaifin shi ne suka saka shi, tun ba ya sha'awa sai dai ya basu gudummawa domin ya san manyan mutane sosai, har dai a yanzu sun ci galaba inda kai tsaye suka nema mishi kujeran Senata kuma ga shi Allah ya ba shi.                        *****        Ajiyan numfashi ya sauke yana miƙe wa tsaye tare da nufan drowan mirror ya buɗe, maganin shi ya ciro ya buɗe ya ɗauki wanda zai sha sannan ya wuce bakin Fridge, buɗe wa yayi ya ɗauki faro ya sha maganin dashi sannan ya wuce bakin gadon shi ya soma cire kayan jikin shi. Wanka ya shiga ya fito yana tsane jikin shi da towel bayan wanda ya ɗaura a ƙugun shi. Wayan shi da ta fara ƙara ya nufa ya ɗauka yana zama a gefen gadon, peacking yayi yana kara wa a kunne. Congratulations ɗin da ake masa yasa ya saki murmushin shi me kyau yana amsa wa cike da farin ciki. Koda ya gama amsa call ɗin sai wasu kuma suka ci gaba da kiran shi dole ya ɓata lokaci yana amsa calls kafin ya tashi ya shirya a cikin sauri, wani farin tissue ya saka wanda har farin Singlet ɗin da yayi using dashi ana gani. Kayan sun yi masa kyau sabida ƴan dai-dai ne iya jikin sa, sai ya murza hula baƙi ya nufi gaban mirror yayi amfani da turarukan shi wajen feshe ko ina na jikin sa da turare, nan da nan ɗakin ya sake tashi da ƙamshi sosai. Bayan ya gama jerin takalman sa ya nufa ya zari ɗaya wanda ya kasance baƙi ne ya zura ya ɗauki keey ɗin mota da wayan shi ya fito Fitan shi sai ga motoci sun fara shigowa gidan. Sun yi kusan goma haka suke ta tururuwan shigowa, Mutane ne cike a cikin su suka firfito suka nufe shi ko wanne yana mishi congrats Hannu yake basu fuskar sa a washe yana amsa musu Abdul ne ya iso wajen yana son mishi magana Dole ya ɗau excuse a wajen su ya matsa zuwa wurin shi Nan Abdul ɗin ya sanar mishi, "Momy ce tace a sanar mishi akwai girkin da ta shirya musu shi da abokan shi zuwa bayan sallan isha'i." Murmushi yayi cike da farin ciki ya gyaɗa mishi kai kana yace, "ok insha Allahu zamu yi ƙoƙarin zuwa, ka sanar mata zuwa ƙarfe goma zamu zo." Abdul ɗin amsa mishi yayi ya juya ya tafi     Shi kuma ya koma cikin mutanen suka ci gaba da gaisawa. Kana kuma suka ɗunguma gaba ɗaya suka fice a motocin su, while Umar Faruk Yana a cikin nashi tare da securities ɗin shi da suka bi su a baya. [14/10, 9:56 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK* 💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *NO_24* *WASHE GARI* "I want you to tell me about your country, because I also want to go abroad, especially to the Arabian Peninsula." Cewar Laɗifa tana murmushi MEEMA wacce take latsa Laptop, ɗago Kai tayi ta kalle ta da murmushi a fuskar ta, a ranta Habibah kawai ta faɗo mata a rai. "Ok, I'll tell you, but not now. We have a lot of work to do now." Ɓata fuska Laɗifa tayi tana miƙa tare da kwantar da kanta a saman kujeran da take zaune, sai kuma tace, "I'm very tired too, and I'm hungry so we should go and get something to eat." Hannun ta MEEMA ta ɗago tana duban agogo sai ta mayar da idanuwan ta a a kanta tace, "It's 12:40 pm. Stay tuned." "No now we're going. I'm tired of work." Ta sake faɗa tana miƙe wa. Sai ta saka hannu ta rufe Laptop ɗin gaban MEEMAN tana cewa, "Get up and let's go please. I'm very hungry." Shigowar Idris yasa MEEMA tayi shiru bata ce komi ba Shi kuma kallon su yayi, sai kuma ya kama haɓa yana mayar da idon sa kan Laɗifa yace, "ke kuma fa? Where are you going when you get up?" "Wlh Brother na gaji yau yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba." Hararan ta yayi yace, "kin gan ki? Na kula ke acici ne wlh. Ok, let's get up and eat now." Washe baki Laɗifa tayi tace, "yauwa ko kai fa Yayan mu." MEEMA tashi tayi itama ta bi bayan su suka fice. A motan Idris ɗin suka ƙarisa restaurant da suke shiga cin abinci. Kowa yayi odan abinda zai ci suka zauna suna ci suna hira. Ƙarfin hiran duk Idris ne yana basu labari suna dariya, kasancewar sa me son Wasa da dariya shiyasa ko baka yi ninya ba sai kayi dariya idan har yana baka labari. Da suka gama suka koma wajen aiki. Sai three O'Clock suka tashi kamar ko yaushe, Idris ya ɗauki MEEMA suka wuce gida Suna zuwa layin gidan su suka ga motoci kusan biyar a jere, sai wasu masu baƙaƙen kaya da alamu securities ne "It looks like something is being done here." Cewar Idris yana faka motan shi daga bakin Gate ɗin su MEEMA bata ce komi ba illa kallon wajen da take yi, sai kuma ta juyo da kallon ta gare shi tace, "And who are these people?" "I don't know MEEMA, but I think someone came here." "Ok." Tace tana ɗaukar jakar ta. Sai da tayi masa godiya sannan ta buɗe motan ta fice Shi kuma ya danna horn me gadin su ya buɗe mishi ya shige MEEMA da ƙafa ta taka zuwa bakin Gate ɗin su ta shige ciki. Tana isa bakin ƙofan parlour zata buɗe sai Uncle Hashim ya buɗe suka fito shi da Umar Faruk. Da kallo ta bi su tana ɗan matsa wa baya While they are also watching her "My daughter are you back?" According to Uncle Hashim he was smiling at her Itama murmushin tayi tana gyaɗa masa kai don she could not speak Uncle Hashim kallon Umar Faruk wanda idanun sa ke kan MEEMA yayi yace, "this is MEEMA, the Aunty's girl." "Really?" He asked looking at him "Yes. She is back here to stay." Sai kuma ya kalli MEEMAN yace, "My daughter this is my friend, my best friend, his name is Umar Faruk." MEEMA kallon shi tayi ta ɗan yi murmushi kaɗan tare da cewa, "Hello Uncle." "How far?" Yafaɗa shima yana kallon ta "I'm fine." Sai kuma ta kalli Uncle Hashim tace, "Uncle I'll go inside." "Ok daughter. Let me accompany him outside." Kanta kawai ta jinjina mishi tana wuce wa ta shige ciki Su kuma suka taka suka nufi waje. Sai da suka fita suka tsaya a bakin Gate ɗin Umar Faruk yace, "but I know this girl, kwanaki ta zo gida na." "Haba dai? To wa ta sani a gidan?" Uncle Hashim yafaɗa da mamaki "Sun zo ne ita da wata, amm.. ina ga From t.v I see they come." "Ok I understand. Tana aiki ne a gidan t.v ai, but Dude I'm wondering if I'll give it to you? Don kallon da kake mata I think kana ciki ne." Yafaɗa yana dariya Shi kuma murmushi yayi da cewa, "kai halin ka na nan ko? Baza ka sauya ba, dama aka ce idan ka rabu da ganin mutum kar ka tambayi idan ya canza, domin halin shi na nan." Murmushi Uncle Hashim yayi yace, "Allah da gaske nake yi, ka san daughter na ce kuma wlh kun dace sosai. Tunda naga ka ƙi sake aure tun tafiya na ga shi har yanzu kana nan a haka, na san yanzu ai Yusra ta girma sosai tunda tana shan nono muka rabu." "She's grown up, now she's in school too." "Allah Sarki Yusra da Hafsah, insha Allahu I will come in and see them later, zamu gaisa da Momy ai". "Allah ya kai mu." Sai ya ba shi hannu suka gaisa suna wuce wa wurin motan. "But will you stay here for two days?" Uncle Hashim yace, "insha Allahu. Zan yi two weeks ni gaskiya, sai dai Jalila za su koma tunda akwai school ɗin Habeeb." Daga nan sallama suka yi ya shiga motan da ɗaya daga cikin securities ɗin ya buɗe mishi Har sai da motocin suka tafi kafin Uncle Hashim ya shige gida. A haraban gidan ya tsaya yana amsa call, yana nan tsaye ne ya hangi wani guy yana shigo wa ciki, ganin ya dumfaro wurin shi sai ya katse kiran yana mayar da hankalin sa a kan shi, kallon sani yake mishi sai dai be ce komi ba har ya iso wurin shi, ya ba shi hannu suka gaisa kafin ya tambaye shi, "wane yake nema?" Murmushi Sajjad yayi yana ɗan shafa kanshi kamar yanda ya saba yace, "suna na Sajjad Aliyu, ni ɗa ne wajen Kawu Faruk surukin nan gidan." Tabbas sai a yanzu ya gane fuskar MEEMA yake gani a tare dashi, sai ya washe baki yace, "ah kace daga Yola kake? You Are welcome, let's go inside." Sajjad bin Bayan shi yayi har cikin gidan Sai dai babu kowa a Parlour, sai yace mishi, "ya zauna bari ya kira mutanen gidan." Ya wuce ciki. MEEMA ya fara kira sannan ya kira Ummee, ya shiga ɗakin Hajiya ya gunguro ta suka fito Tunda MEEMA suka yi ido huɗu da Sajjad ai sai ta ja ta tsaya daga inda take ta kasa ƙarisowa Shima haka yana ganin ta ya miƙe tsaya idanun sa ƙyam a kanta nan da nan farin ciki ya cika shi da ganin ta Fitowar Uncle Hashim tare da Hajiya ya kalle ta yace, "let's go daughter." Sannan ya wuce Ummee itama sai a lokacin ta fito suka zauna a kan sofa "Ka zauna mana." Uncle Hashim yafaɗa yana kallon Sajjad ɗin Babu musu ya zauna. Sai kuma ya fara gaishe da su Ummee da ke mishi kallon sani tace, "kamar na so in Gane ka? Sajjad ko?" Murmushi yayi yace, "Yes Ummee Ni ne." "Ikon Allah kai ne a nan? Kai da wa kazo?" Tafaɗa da mamaki "Ni kaɗai." Murmushi tayi sai kuma ta kalli Hajiya tace, "Hajiya wannan ɗa ne wurin miji na, mahaifin shi Yayan Faruk ne ai." "To Masha Allah, sannu da zuwa, ki ce ɗan uwan MEEMA ne ai, Ga kamanni wlh." Tafaɗa cike da fara'a Uncle Hashim yace, "to ai ga daughtern can ta ƙi ƙariso wa." Sai ya ɗaga murya ya kira ta Dole a yanzu ta iso wurin sai dai fuskar ta a ɗaure tamau tana kallon Sajjad ɗin "Daughter do you recognize him? This is your cousin". Cewar Uncle Hashim Yana murmushi "Na'am. I recognize him Uncle, But what did he come to do here? I don't want to see him." Mamaki duk kan su suka yi da maganar ta Musamman Ummee da ta san zai yi wuya MEEMA ta gane Sajjad, kasa shiru tayi tace, "How come you know him after you've never seen him?" Cikin muryan kuka da ya ƙwace mata tace, "When I landed here country I went to their house and stayed. They wanted to marry me without my knowledge. One day before we were to get married I knew. That's why I came here. And I don't want him, I hate him so much." "Subhanallah.. married again? Don't you know?" Hajiya tafaɗa da tsantsan mamaki Itama Ummee kalman auren ta sake maimaita wa fuskar ta cike da damuwa Sajjad da kanshi ke ƙasa ya kasa cewa uffan Sai Uncle Hashim da ya tashi a zuciye yace, "kai tashi ka kama hanya ka bar mana gida, nan ba wajen zaman ka bane..." Hajiya ce ta katse shi da cewa, "a'a Hashim ai baka san me ya kawo shi ba, kuma kana da tabbacin da laifin shi ne?" "Da laifin shi mana Hajiya, ba shi ne wanda za'a ɗaura mishi aure da ita ba ba bare da amincewar ta ba? Don kawai zalunci, dama ai ba ƙaunar ta suke yi ba kuma mun san da haka, tabbas akwai abinda yasa suke son yi mata aure ba tare da amincewar ta ba, wato auren dole suka so suyi mata?" Yafaɗa a fusace Da gudu MEEMAN ta isa wurin Uncle ɗin ta rungume shi tana kuka Hakan ya ƙara hassala shi yana kallon Sajjad ɗin da cewa, "kai baka ji me nace maka bane? Ka tashi ka bamu wuri ka koma inda ka fito tunda baku da mutunci." Cikin hawayen da suka kufce mishi Sajjad ɗin ya zube a kan gwiwowin shi yana roƙon su da Allah, "su bar shi a nan ya zauna, wlh yana tsananin ƙaunar MEEMA bazai iya rabuwa da ita ba..." Katse shi yayi da cewa, "tashi nace, wlh ka bari na sake maka magana sai dai uwar ka ta haifi wani a gidan nan." Su Hajiya sun san halin Uncle Hashim akwai zuciya ba ya son raini, dama dalilin da yasa ya shiga aikin soja kenan domin akwai shi da zuciya sosai idan ranshi ya ɓaci. Dole Hajiya ta soma rarrashin sa da cewa, "ka ga Hashimu kayi haƙuri ya fita a hankali kar kayi masa wani abun kaji ko?" "To Hajiya uwar me yake jira da bazai fita ba?" Duk hayaniyar Uncle Hashim ɗin ne ya fito da su Jalila da Zabba'u suka zo suka tsaitsaya suna kallon ikon Allah Sajjad ba don ya so ba ya tashi ya fice yana sharan hawaye Zabba'u da ita ce bakin ta ke ƙaiƙayi take bin ba'asin me ya faru. Sai da aka sanar mata sannan hankalin ta ya kwanta. Sai kuma ta koma tana faɗan albarkacin bakin ta, sai tsiya take yi tana faɗin, "ai wannan mugunta ne ace zasu yiwa yarinya aure ba da amincewar ta ba, haka ake yi ne?".. Shi kuwa Uncle Hashim tuni ya ja hannun MEEMA zuwa ɗakin ta, a can ya rarrashe ta domin kuka take ta yi sosai ta kasa yin shiru. Sai da ya kwantar mata da hankali kafin ya fito ya yiwa su Hajiya sallama a kan, "zai je gidan abokin shi." Ya fice Su kuma sai mayar da zacen suke yi, daga ƙarshe kuma suka koma hira. The following day. Lokacin Hajiya na zaune a ɗaki tana lazimi Uncle Hashim ya shigo ɗakin duk a rikice. Kallon sa tayi tana tambayar sa, "lafiya Hashimu wani abun ne ya faru?" Sai da ya zauna a kan sofa ya gaishe ta kafin yace, "wlh Hajiya babu lafiya, ina zaune a ɗaki aka kira Ni ake sanar min Umar Faruk yayi hatsari jiya da dare." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. a garin ya ya? Da sauƙi dai ko?" Tafaɗa itama a rikice "To Hajiya ban sani ba wlh, sai dai idan na je yanzu zan gani." "Subhanallah.. ai ba kai kaɗai zaka je ba, mu tafi gaba ɗaya, Allah sarki jiyan nan fa ya zo gidan nan, yanzu da ace mutuwa ce sai dai mu ji an ce ya mutu, oh Allah! Allah yasa dai ba magauta bane domin dama duk wanda ya shiga siyasa ai baza a raba shi da su ba." "Haka ne Hajiya. Nima wlh Ina tunanin haka." Yafaɗa fuskar shi duk a dame "To ka jira Ni bari in Yi wanka. Ka turo min Zabba'u da Allah." Yace, "to." Yana miƙe wa ya fice. Sai da ya je ya sanar wa Zabba'u wacce take kichen tana haɗa kumallo kafin ya nufi Steps zai haye A lokacin ne MEEMA ta fito daga ɗaki a cikin shirin ta na zuwa Office. Ganin shi yasa tayi saurin ɗaga murya da cewa, "Uncle good morning." Tsaya wa yayi ya juyo. "Ah ah my daughter. You wake up?" "Na'am Uncle." Tafaɗa tana Isa wurin shi. Ta kama hannun shi tayi masa kiss tana kallon shi Shi kuma ya shafa kanta yana murmushi da cewa, "Do you go to work?" Jinjina masa kai tayi tana mayar mishi da martanin murmushin "Ok. Let's go out together I'll drop you off at work. We're going to greet my friend who came here yesterday. It had an accident last night." Waro ido waje tayi da cewa, "This one we greeted yesterday?" "Yes daughter." Fuskar tausayi tayi tace, "eyya. God forbid. He don't hurt?" Sai da ya riƙe hannun ta da alamun rarrashi yace, "insha Allah It's easy for him, will you go and greet him?" Gyaɗa kanta tayi don ta kasa magana, haka kawai taji gaban ta na faɗuwa while idanun ta sun cika da hawaye Ganin yanda ta koma sai yayi murmushi yana cewa, "You Care about him?" Still gyaɗa mishi kai tayi don ta kasa yin magana, sosai bakin ta yayi mata nauyi "Ok let's go to my room, don't worry ok? Insha Allah he will be fine." Hannun su a saƙale da juna suka wuce sama. Ɗakin Ummee yayi Nocking still Yana riƙe da hannun MEEMA Tana buɗe wa suka haɗa ido da MEEMA Ita kuma tayi saurin ɗauke kanta tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta Ummee yanda ta ga MEEMAN ne yasa ta tambayi Uncle Hashim bayan ta amsa gaisuwar shi. "Me ya sami MEEMA kamar akwai wani abun da ke damun ta?" Sai da ya ɗan kalli fuskar ta kafin yace, "eh Aunty, na sanar mata da hatsarin da Dude yayi ne shi ne duk ta shiga damuwa. Dama shi na zo faɗa miki Umar yayi hatsari jiya da dare." "Subhanallah.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. da sauƙi ko?" "I don't know aunty, Amma Hajiya tace mu shirya gaba ɗaya sai mu je mu duba shi." "Ok to bari in shirya." Tafaɗa tana koma wa cikin ɗakin Shi kuma ya ja hannun MEEMAN suka wuce nasu ɗakin Shigan su ɗakin Jalila ganin su tare yasa ta washe baki tace, "oh yau tare kake da daughtern taka har nan?" Murmushi yayi yana zama a gefen Habeeb While MEEMA na tsaye. Sai ta gaishe da Jalilan tana ɗan sakin fuskar ta Habeeb da sauri ya taso ya rungume ta yana kiran ta da, "Aunty." Hakan yasa ta saka hannu ta sake rungume shi tana mishi magana While Uncle Hashim kuma yana sanar da Jalila abun da ke faruwa. Sannan ya sanar mata, "ta shirya su je duba shi". MEEMA tana tare da su har suka shirya sannan suka sauko ƙasa. Tun suna yin Breakfast gaba ɗaya ta sauya, abincin kawai take ci hankalin ta ba ya jikin ta, haka kawai a zuciyar ta ta ƙosa ta je ta ganshi, duk ta damu fatan ta Allah yasa yana ƙoshin lafiya. Babu abinda ke mata gizau sai kyakykyawar fuskar shi, ita kanta mamakin yanda ya tsaya mata a rai take yi, amma kuma gani take yi tausayin sa ne ya shige ta kasancewar hatsari yayi, Allah-Allah take yi su tafi Da suka tashi tafiya mota biyu suka cika suka tafi asibitin da aka ce yana can. [14/10, 9:58 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                 *NASIHA* _Duk wanda ya karya ginshiƙin addinin sa, duk wanda ya bijire wa umurnin mahaliccin sa, duk wanda ya saɓa wa koyarwar Annabin sa wanda aka aiko shi ya kasance jagora ga al'umma, duk wanda ya ji kalmomin Ubangiji da suke gaya masa me ya kamata yayi ya kuma fahimce su amma duk da haka ya dage a kan hanyar tsageranci da hamɓare su, duk wanda yake fankamar shi ya fi ƙarfin ya bauta wa Allah Ubangijin sa, to, duk wani horon da ya same shi bai yi yawa ba. In ya tsaya tsaf ya ƙi yin Sallah lalle ya fita daga daular Islama kuma ba shi da damar ya kuka da hukunci da ya dace da shi Kamar dai yadda Alƙur'ani yayi bayani. Allah yasa mu dace._                              *NO_25*                 A haraban Hospital ɗin suka tsayar da motocin kafin suka fito. Uncle Hashim ya fito da Hajiya ya zaunar da ita a wheelchair ɗin ta, sannan sai Zabba'u ta tura ta suka yi cikin asibitin. Tun kafin ma su tambayi ɗakin da aka kwantar da shi suka hango securities a gaban wani ɗaki. Hakan ya tabbatar wa da Uncle Hashim nan ne ɗakin da Abokin shi yake. Can ya nufa suka take mishi baya Securities ɗin tsayar da su suka yi suna tambayar, "ina zasu je?" Uncle Hashim ne yayi musu bayani Kasancewar sun gane shi yasa suka bar su suka shiga A ɗakin daga Momy sai Abdul ne zaune sun tasa Umar Faruk a gaba gunun tausayi, kai kace sun damu da shi ne a yanda suka nuna, musamman ma Momy wacce gaba ɗaya idanun ta sun jiƙe da ruwan hawaye sai kai gyalen ta take yi tana kwashe su Yayinda shi kuma yana kwance a saman gado idanuwan sa a rufe, da alamu ba wasu rauni ya ji ba sai dai a kansa da aka naɗe mishi da bandage, sai kuma ƙafar shi ɗaya ta dama da itama duk an saka mishi bandage a ciwukan da ya ji, sai kuma ƙaramar yatsar shi itama ta hannun dama wacce aka saka mishi drip Shigowar su yasa su Momy suka bi su da kallo suna amsa sallaman nasu. Kasancewar Momy ta gane su musamman ma ganin Uncle Hashim da tayi yasa ta washe baki tana tashi tsaye tare da musu lale marhaban Shima Abdul tashi yayi ya bai wa Ummee kujeran sa Sannan aka gaisa cike da mutunci. Su Hajiya suka yi musu, "ya me jiki?" Momy ta amsa da faɗin, "alhmadulillah. Ya samu barci ne  mu ma tunda muka zo be farka ba." "Allah Sarki! Allah ya ba shi lafiya. Wlh hankali na ya tashi da jin labarin hatsarin shiyasa muka taho gaba ɗaya." Cewar Hajiya cike da damuwa Momy tace, "wlh kuwa. Ai abun ne da tashin hankali. Nima ya zo ya gaishe Ni a jiyan yake ce min zai fita meeting, wlh a Raina sai da naji ban amince da fitar nashi ba, amma kuma tunda ya zama dole babu yanda zan yi, be fi mintuna goma ba aka kira mu aka sanar mana yayi hatsari, kuma motar tashi ce kaɗai ta kwace ma drever'n, Allah yasa akwai mutane tare dashi aka yi saurin taimakon shi tunda hatsarin ba sosai bane, ai mun auna arziƙi." Ta ƙare maganar tana sake share hawayen fuskar ta Haƙuri duk suke bata. Hajiya na sake tausan ta Sai kuma ɗakin ya ɗan yi jugum A lokacin ne Umar Faruk ya buɗe idanun sa Hakan yasa Uncle Hashim da ke tsaye ya koma gefen gadon ya zauna yana kallon shi A hankali yake bin mutanen ɗakin da kallo yana yi yana ɗan lumshe idanun sa Uncle Hashim ya soma mishi sannu kafin sauran su soma gaishe shi da jiki Kanshi kaɗai yake ɗaga musu yayinda ya sauke idon shi a kan MEEMA wacce ta tsaya a can baya ta zuba mishi ido But yana kallon ta sai ta ɗauke nata idon daga kallon shi tana ɗan gyara tsayuwar ta kasancewar ta soma gajiya, ɗan ɗago kai ta sake yi ta sauke a kanshi ta ga har yanzu ya kasa ɗauke ido a kanta, sai ta janye nata tana sauke kai ƙasa tare da wasa da yatsun hannayen ta. Ta kula yana da yawan kallo a yanda ta fahimta, kaifin idanun shi yake sa take gane ita yake kallo, hakan ke haifar mata da faɗuwar gaba me tsanani, sosai gaban ta ke bugawa wanda yasa ta kasa tsayuwa wuri ɗaya tana ɗan jujjuya jiki Momy wacce ta lura da kallon da yake yiwa MEEMA yasa ta mayar da kallon ta gare ta, sai yanzu tayi mata kallon ƙurilla domin tun shigowar ta baza tace akwai ta a cikin ɗakin ba ma, duba da yanda ta ja can baya ta tsaya. Hakan yasa ta ɗan washe baki tana cewa, "ita kuma wannan kyakykyawar yarinyar fa daga ina?" Zabba'u tayi saurin bata amsa da faɗin, "ai ɗiyar Hajiya ƙarama ce, sunan ta MEEMA." "Allah Sarki! Masha Allah yarinyar kyakykyawa da ita." Duk murmushi suka yi While Abdul da shima sai yanzu ya kula da ita, tunda ya kafa mata ido ya kasa ɗauke wa, sai ƙare wa halittan ta kallo yake yi daga sama har ƙasa tamkar idanun sa za su fito waje har buɗe baki yayi Uncle Hashim da shima yana kula da kallon da Umar Faruk yake bin MEEMA da shi, sai yayi murmushi yana matso da fuskar sa gefen sa, ya ɗan raɗa masa maganar, "sai na tsole idon idan baka dena kallon ta ba, ko dama ba jinya kake yi ba?" Hakan yasa ya saki kyakykyawar murmushin sa yana ɗan lumshe idanun kamar zai rufe su sai ya juyo su ga kallon Uncle Hashim ɗin, be ce komi ba illa murmushin da yake saki, sai kuma ya ɗan karkata kai ya kalli Habeeb da ke jikin Jalila ya yafico shi da hannu Hakan yasa yaron ya iso wurin shi Yayi mishi murmushi da cewa, "har da kai kaima ka zo duba ni?" "Eh Uncle. Ya jikin ka?." "Alhamdulillah my boy. Kai ma ya naka jikin?" "Ai naji sauƙi." Yafaɗa yana ɗaura hannun sa a kai Zabba'u tace, "ai ya ji sauƙi sosai in dai Habeeb ne." "Eyya shima be da lafiya ne ashe? Allah ya sawwaka ɗan yaro na, taho mu gaisa ko." Cewar Momy fuskar ta cike da fara'a Daga Hajiya har su Ummee amsa mata suka yi da, "Ameen Ameen." Iso wa yayi wajen ta, ta ɗaura shi a cinyan ta tana tambayar shi Daga haka ɗakin yayi shiru illa sauraron surutun da Habeeb yake yi tare da Momy.              Ita kuwa MEEMA duk ta gama gajiya, gaba ɗaya fuskar ta ta sauya tamkar zata yi kuka sabida rashin sabo Ta gefen ido duk Umar Faruk yana kallon ta, a ransa kuwa dariya ta ba shi yana mamakin sangarta irin nata domin ya kula tsayuwar nata ne ya dame ta take shirin kuka. Sai dai ya kasa yanda zai yi yayi mata magana bare yace, "ta zauna." Wanda hakan ne a cikin zuciyar sa Shima Abdul ya kula da yanayin ta hakan yasa ya buɗe baki da ninyan yin mata magana Sai Uncle Hashim yace, "Daughter, you are tired? Come here and sit down and let me out." Murmushin yaƙe ta ɗan saki sai dai bata ce komi ba ganin inda yake nuna mata ta zauna ɗin, ma'ana a saman gadon shiyasa ta kasa motsa wa Hajiya tace, "ai mu ma ba daɗe wa zamu yi ba, But before we leave, go and sit down since you are tired." Kanta ta ɗan gyaɗa ta nufi wajen ta ɗofana mazaunan ta a inda Uncle Hashim ya matsa mata, hakan yasa har jikin ta ke gogan juna da cinyan Umar Faruk. A tare suka lumshe idanun su ko wanne yana jin wani abu ya tsirga mishi; wanda ita ta kasa jure wa dole ta sake jan jikin ta ta matsa gefe sosai ta yanda baza su haɗe ba.            A haka dai suka zauna jigum sai su Hajiya da suke ɗan taɓa hira. Sai da wasu mutane da suka zo gaishe da Umar Faruk ɗin suka shigo sannan su Hajiya suka yi musu sallama suka fice a ɗakin. Manyan Mutane ne kusan su goma ƴan siyasa suka zo gaishe da shi.           Uncle Hashim da MEEMA a mota ɗaya suka koma. Dayake zai sauke ta a wajen aiki. Yana zuwa ya sauke ta ya wuce tunda akwai inda zai je Tunda ta shiga ciki suka gaisa da waɗanda ta ci karo da su ta wuce Office ɗin su. Sai dai tana shiga babu kowa sai ta tsaya ba tare da ta zauna ba. Tana shirin juya wa zuwa Office ɗin Idris sai wata me suna A'isha wacce itama aiki take yi a gidan t.vn, ita ta hange ta ta ƙariso wurin ta tana cewa, "Hi MEEMA". "Hi." Ta amsa mata tana kallon ta Murmushi A'isha tayi tace, "Today I thought you would not come, and Laɗifa did not come, and you is ok?" "Fine. I went somewhere." Isowar Idris wajen shi yasa A'isha ta yiwa MEEMA sallama ta wuce Yana isowa suka gaisa yake tambayar ta, "Where are you going? I've just come to pick you up but your gate Man says you're all out." "We went to the hospital." "Subhanallah.. Who is sick?" Shiru tayi, sai kuma tace, "This man we went to his house me and Laɗifa and interviewed, amm... Senate." "Ok Senator Umar Faruk Aliyu, You went to him?" Gyaɗa masa kai tayi da faɗin, "na'am." "Ok I heard, right now I want to go and talk to him about the accident, now go to the office and rest when I finish my work so we can go together and talk to him. From there we go to greet Laɗifa and She is not feeling well." Fuskar ta ne ya sauya tana ɗan sake buɗe manyan idanuwan ta tace, "really? I don't know, i didn't call her, easily her body?" Ɗan numfashi ya ja kafin yace, "Calm down, insha'Allah. Her body is fine, but I just called her and she couldn't pick up the phone. Her mother informed me of her condition. Go inside and finish your work and we'll go." Ɓata fuska tayi hawaye na ciko mata a idanu tace, "I can't work now until I see her condition. I'm scared." Murmushi yayi a ransa yace, "MEEMA rigima! tana jin ta kamar wata yarinya ce." Sosai ya kula akwai dolanci da sangarta irin na ƴaƴan masu kuɗi a tattare da ita, irin waɗan da aka shagwaɓa ɗin nan sosai. komi nata tana yin sa ne tamkar wata ƙaramar yarinya, ba ta kunyar ta yiwa ko waye taɓara ko kuma tayi masa kuka, bata da wahalan kuka ko a gaban waye ne. "Fine. Let's go to my office and pass from there." Kanta ta ɗaga mishi tana bin Bayan shi. Daga can bayan ya gama abinda zai yi suka fito suka wuce asibitin da aka kwantar da Senator Umar Faruk. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️           A can kuwa gida lokacin da su Hajiya suka koma. Me gadi na buɗe musu ƙofa Ummee ta tura hancin motan ciki. Tunda suka shiga suka ga wata jan mota wanda sun tabbatar ba na gidan bane Me gadi na rufe Gate ɗin ya iso wurin su da gudu. A lokacin duk sun fito suna ƙoƙarin fito da Hajiya. Ya gaishe su yana cewa, "Hajiya dama baƙi ne suka zo nan gidan. Ga su can a cikin mota." "Baƙi kuma?" Da Hajiya da Ummee suka haɗa baki wajen faɗa "Eh wlh. Nayi yunƙurin tsayar da su daga waje amma sun ƙi tsaya wa, dole suka saka Ni na buɗe musu ƙofa suka shigo. Bari inyi musu magana sai su zo." Ya ƙare maganar yana wuce wa wajen motan da hanzari Bayan yayi musu magana ne sai suka fito daga motan Ai Ummee na ganin su ta gane su, Kawu Ali ne da Kawu Zubairu Hajiya kuma sai da suka iso gab da ita itama ta shaida fuskar su Su suka fara gaishe da Hajiya kafin itama ta saki fuska ta amsa su tana musu lale marhaban Ita Ummee ta kasa musu magana sai kallon su da take yi, domin ta san halin su tunda ta gansu a nan ba alheri ne ya kawo su ba, baza ta manta sanda suke zuwa can Riyadh suke cin musu mutunci ba ita da Faruk da ɗiyar su. Sanadi har da rashin ƙaunar da suke nuna mata yasa ta bi ruɗin ƙawaye ta bar mijin ta a halin laluran da yake tsananin buƙatar ta ta taho nan. Daƙyar ta buɗe baki a yanzu ɗin ta gaishe su Duk amsa wa suka yi fuska a ɗaure suna wani ciccin magani Ita dai taɓe baki kawai tayi tayi gaba abin ta  Hajiya ce ta ce musu, "su shiga ciki." Sannan ne suka bi bayan su suka shiga Parlour. Sai da suka zauna aka ƙara gaisa wa Kafin Kawu Ali ya soma magana da faɗin, "ba wani abu ya kawo mu nan ba sai maganar Zulaiha. To mu mun zo ne mu tafi da ita kawai babu wani kace nace duk da dai wulaƙancin da ɗana ya fuskanta zuwan shi nan, yarinyar nan ta ci mana mutunci ba kaɗan ba amma duk da haka muka biyo baya saboda a matsayin mu na dolen ta, ba don haka ba wlh babu yanda za'a yi mu tako ƙafar mu mu taho nan. Don haka sai ku bamu ita mu tafi da ita abun da ya kawo mu kenan." Hajiya da ta zuba musu ido tana kallon su jin yayi shiru sai tace, "to Aliyu kake ko wa? Zancen gaskiya baku yiwa yarinyar nan adalci ba, ita a yanda ta faɗa mana so Kuka yi kuyi mata aure ba tare da amincewar ta ba, hasali ma bata san da zancen ba sai da biki ya zo. Hakan ai ba kyautuwa bane..." Bata ajiye numfashi ba Kawu Zubairu ya tada jijiyan wuya da cewa, "to ke a ganin ki Hajiya har sai an tambaye ta sannan zamu iya mata aure? Muna da ƴancin da zamu iya aurar da ita ga duk wanda muke so, sannan shi wannan yaron ɗan mu ne haka itama ƴar mu ce, ganin babu ran mahaifin ta yasa muke so mu rufa mata asiri mu aurar da ita ga ɗan mu kamar yanda ya ce yana so, amma mu ma ba'a son ran mu bane tunda babu yanda za'a yi muna ji muna gani mu ɗaura wa ɗan mu yarinyar da ta gama gantale wa ta kasa auruwa, yarinyar da kaɗan ya girme mata don mun yanke wannan hukuncin shi ne zai zama abun magana? Ai idan ba'a gode mana ba baza ayi Allah wadai da mu ba." Sosai maganganun Kawu Zubairu ya ɓata wa Hajiya rai Ba ita kaɗai ba har Ummee wacce tana ji tana gani ana son aibata mata ɗiya. Shiyasa tayi saurin cewa, "maganar gaskiya Yaya bazai yiwu ace ku zo har cikin gidan mu kuna gaya wa Mahaifiya ta da ɗiya ta magana ba, idan na jure a baya wancan nayi shiru ne domin ɗan uwan ku, amma yanzu babu wanda zai zo har gidan mu ya ci mana fuska, ita MEEMA ai ɗiya ta ce kuma ta dawo hannu na baku da halin amsar ta, ita da kanta ta zaɓi nan don haka babu wanda a cikin ku zai tafi min da yarinya wani wuri." "Auu iyeeeee! Wuyan ki ya isa yanka Zulai mu kike faɗa wa haka?" Cewar Kawu Ali a zafafe Hajiya tace, "gaskiya ce ta faɗa, babu inda zaku je mata da ɗiya tunda ba arziki ne da ku ba." Kawu Ali yace, "to wlh baku isa ba, dole sai mun tafi da ita tunda mu ne ya zama wajibi ta zauna da mu, idan ba haka ba wlh babu inda zamu je ƙafar mu ƙafar ta, har ku kun isa? Matsiyatan banza matsiyatan hofi! ɗan uwan mu ya bar dukiya dole ai ku ɗauke ta, meye bamu da labari a kai, nan ita uwar ta ta tafi ta bar su sai yanzu da kuka san ya mutu shi ne kuke da bakin cewa zaku riƙe ta, to zan gani, wlh tallahi sai dai kotu ta raba mu da ku." "Yo kuce kuɗi kuka biyo ba yarinya ba? Akwai wasu matsiyata ne bayan ku? Tunda ba mutunci ne daku ba ku fice min a gida tun kafin ku ga abin da zai faru da ku, ƴan iska mara sa mutunci." Inji Hajiya itama a zafafe kamar zata tashi tsaban rigima Nan fa sai cacan baki ya kaure wanda dole su Jalila ita da Zabba'u suka fito tunda su basu a wurin Yanda suka taru suke ta cin ma ƴar tsohuwa mutunci ne yasa Ummee itama take tare mata Jikin Jalila na rawa ta nufi ɗaki ɗauko waya ta kira Uncle Hashim ganin abun nasu ba na ƙare bane. Tana kiran shi ya ɗauka ta sanar mishi da halin da ake ciki Kankace me ya kashe wayan da faɗin, "ga yi nan zuwa yanzu-yanzu." ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️             Idris na Isa hospital ɗin ya faka motan suka fito suka shiga ciki. Sai dai koda suka je shiga ɗakin securities ɗin shi sun hana su shiga duk da Idris ya nuna I.D card ɗin shi Da ya dame su da naci ne sai ɗaya security ɗin ya shiga ya sanar wa da Umar Faruk ɗin. Babu jima wa ya dawo ya sanar musu, "ba ya buƙatar hira da su." Fitowar security ɗin ne ya bar ƙofan a buɗe wanda ya bai wa Umar Faruk damar hango kayan MEEMA, baƙin Abayar da ta sanya tabbas shi ne ya hango tunda dashi ta zo ɗazu. Sai leƙa kai yake yi sai dai ya kasa yin magana domin ya san ko ya ɗaga murya baza su ji ba, bare shi ba me son hayaniya bane. Yana kallo har suka tafi sai ya ɗan yarfa kai gefe yana mayar da idanun sa ya lumshe su. Allah yasa sai ga security ɗin ya shigo da sauri ya buɗe ido yana kallon sa ya sanar mishi, "yayi maza ya kira mishi Macen tazo." Hakan yasa ya fita da sauri ya isa haraban Hospital ɗin A lokacin har sun shiga mota Idris na ƙoƙarin tayar wa Sai ya isa wurin da sauri. Ya tsayar da shi yana faɗa mishi saƙon Umar Faruk ɗin. Ganin Idris ɗin zai fito sai yace dashi, "ita kaɗai yake buƙata." Koma wa yayi ya zauna Idris ɗin yana duban MEEMA wacce take zaune a cikin motan. Bata ma san me suke cewa ba tunda hankalin ta na kan waya tana latsawa. Yace da ita, "MEEMA come out and join Senator Umar Faruk he wants to talk to you." Duban sa take yi da mamaki but taƙi yin magana sai ɗan ƙara buɗe kyawawan idanuwan ta da tayi "Yes. He said he should be called you. I think you will talk together." Sai ya miƙa mata recorder ɗin hannun shi yace, "Go with this and discuss." Ɗan jim.. tayi tana kallon shi, sai kuma ta saka fararen hannayen ta ta amshi recordern ta fice. Bayan security ɗin tabi har zuwa ɗakin da yake ciki. Shi security ɗin ya tsaya a waje ita kuma ta tura ƙofan ta shige a hankali kamar wacce take tsoron shiga. [14/10, 10:01 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                      💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                       *NO_26* Tunda ta turo ƙofan ta shigo idanun sa na kanta ya kasa ɗauke su Ita kuma ganin kallon da yake mata yasa ta kawar da kai tana takowa a hankali zuwa cikin ɗakin, tsayawa tayi ta kasa ƙarisawa illa sauraron bugun zuciyarta da ke ƙara hauhawa take yi Shi ne yace mata, "Come and sit down here." Ya nuna mata kujeran da ke bakin gadon nashi Hakan yasa ta ɗan kalle shi sai kuma ta taka izuwa kujeran ta zauna a hankali. Kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa Sai ɗakin yayi shiru illa shi da yake faman kallon ta ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a kanta, be san meyasa ba tunda ya fara ganinta ta tsaya mishi a rai, ba ya gajiya da kallon kyakykyawar fuskar ta hakan yasa be iya control kansa, wani lokacin be ma san yana kallon ta ɗin ba sai daga baya yayi ta mamakin kansa. Yanzun ma daƙyar ya iya buɗe baki yace, "Do you need anything from my place?" Kanta ta ɗago ta kalle shi a wannan lokacin sosai sai dai fuskar ta babu walwala. Bata iya ce mishi komi ba illa kallon shi da take yi Shima sai ya tsira mata ido yana kallon cikin idanun ta yayinda yake jin tamkar wani abubuwa suna jansa izuwa cikin nata idanun Ta kasa jure wa ta ɗauke idanuwan ta tana mayar da su ƙasa. Sai kuma a hankali ta furta, "how your body?" Yanda muryan ta ya bugi kunnen sa yasa ya lumshe idanun sa sabida daɗin sanyin muryan ta. Ya ɗau lokaci a haka kafin ya ware idon a kanta yana furta, "alhmadulillah. How did you get home?" "Fine." Tafaɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ɗago ta dube shi da cewa, "We want to talk about your accident. If you don't mind I'd like to talk to you?" Idanun sa cikin nata yace, "I don't want to talk to journalists. I have nothing to tell you. And I see that you want to restrict me." Jin maganar nasa yasa ta tashi tsaye still tana kallon shi, sai dai bata ce komi ba ta juya ta fice tana mamakin, "to meyasa ya kira ta idan babu abinda zai ce da su?" Shi kuma ya kasa tsayar da ita yana kallo ta fice domin be san me zai ce mata ba, shi dai ya bi umarnin zuciyar sa ne wacce ta saka shi ya kira ta ba shi da abun ce mata. Tana isa wajen motan ta buɗe ta shiga Idris da ke faman jiran ta kallon ta yayi ya tambaye ta, "Did you interview him?" Girgiza masa kai tayi kamar baza tayi magana ba sai kuma ta kalle shi tace, "He says he doesn't need to talk to us." Mamaki ne bayyane a fuskar sa, sai yace, "But why does he need to see you if not the interview would bother us?" "I don't know." Tafaɗa a hankali tana kawar da kanta gefe Shima be ce komi ba ya ja motan suka fice. Sai da ya cilla motan a kan titi kafin ya sanar mata, "their house Laɗifa will pass." Bata ce masa komi ba har suka kai bakin gidan Ya taka birki suka fito suka shiga cikin gidan su Laɗifa. Da Umman ta suka soma cin karo a tsakar gida don haka Idris ya gaishe ta. Itama MEEMA ta gaishe ta da Hausan jin Idris ya gaishe ta Cike da fara'a ta amsa musu tana musu lale marhaban. Kana kuma tayi musu jagora zuwa ɗakin nasu Suna shiga suka ga Laɗifan a kwance a saman kujera Ganin su yasa ta tashi zaune da murnan ta tana washe baki, duk da kana kallon ta zaka fahimci tana jin jiki amma hakan be sa ta ƙi nuna farin cikin ta da ganin su ba Idris da ya ƙware wajen tsokana sai ya kama haɓa yana cewa, "Umma anya yarinyar nan ba ciwon aure ne ke damun ta ba? Dama na faɗa miki ki gaggauta aurar da ita kin ƙi, kullum ita ciwo ba ta shafe sati bata yi ciwo ba." Dariya Umma tayi While ita kuma Laɗifa hararan shi tayi tace, "masharranci kawai, kai me ya hana ka auren sai Ni zaka ce nayi? Idan ka gaji da gani na ka aurar da Ni mana." Sai kuma ta kalli MEEMA tace, "Sister come here and sit." Zama MEEMAN tayi a gefen Laɗifan Idris da shima ya sami wuri ya zauna sai ya taɓe baki yace, "ai Ni bani da kuɗin miki aure, amma zan sanar wa Baba tunda naga alamu aike na kike yi. Wlh ina faɗa miki yarinya gwara kiyi auren ki kar ki biye ta tawa, Ni yaro ne har yanzu ban isa aure ba idan kika ce sai kin jira Ni ai kuwa zaki yi kwantai a gida don Ni ba take nake yi ba, bar gani na haka na san abun da yake zuciyar ki." Ɓare baki tayi kamar zata yi kuka tace, "Umma kin gansa ko ki ce ya dena ba na so, nima me zan yi da kai ai kayi min ƙanƙanta." Zaro ido waje yayi, zai yi magana kuma sai suka haɗa ido da Umman, sai ya kwashe da dariya yace, "Allah arziƙin ki ɗaya akwai Umma da sai na faɗa miki magana Al'ƙur'an." Umma tace, "ai Ni Idris ba kunyata kake ji ba da kayi maganar ka ma. Hmm Allah ya shirye ka baza ka sauya hali ba wlh." Dariya kawai yake yi Laɗifa kuma bata kula shi ba illa riƙe hannun MEEMA da tayi tana kallon Umman nata tace, "Umma wannan ita ce MEEMA wacce nake baki labari ƙawata." Murmushi tayi Umman tace, "Masha Allah ga ta kyakykyawa, Ashe Zulaiha tana da yarinya kamar ta ban taɓa sani ba wlh. Sannu ƴar nan ga shi ko ruwa ban kawo miki ba, na zauna ina jin shirmen Idris." Dariya yayi yace, "ai Umma bata san me kike cewa ba. Bari Ni in taimaka in ɗauko mata ruwan." Ya tashi izuwa wurin Fridge ɗin Ita kuma Umma tace, "au ba ta jin Hausa ne?" Laɗifa tace, "eh Umma, har yanzu ta kasa koya wlh, kuma kwanaki har na fara koya mata amma ko tunawa ba tayi." Ta ƙare maganar tana dariya "Allah Sarki." Cewar Umman. "Da sannu zata iya tunda tana tare da mu Hausawa." Ruwan da Idris ya kawo mata MEEMAN ta amsa ta kurɓa kafin ta ajiye. Cike da sanyin murya tace da Laɗifan, "I'm worried about you, but I'm glad to see you. God get well soon." Murmushi Laɗifa tayi tace, "Ameen thanks MEEMA." Idris yace, ,"ai ta warke sosai. Get up and let's go since her body is fine." Murguɗa masa baki Laɗifan tayi da cewa, "baza ta tashi ba, a nan zata zauna, kai ka tafi kai kaɗai." "Kina ji ko Umma? Yarinyar nan naki ta raina Ni wlh zan fasa mata baki." Umma tace, "ai kun fi kusa wlh babu ruwana." Hakan yasa Laɗifa tayi masa gwalo Yayi ƙwafa shi kuma yana kaɗa mata yatsa alamun, "zai riƙe ta." Da haka dai suka zauna suna ta shirmen su, duk da Laɗifa ba ta jin daɗin jikin ta sai da ta biye mishi don Idris akwai wasa, ko ba ka so idan ya saka ka a gaba sai ka biye mishi Daga baya ya tashi yace, "za su tafi." Suka yi musu sallama suka fice. Kai tsaye wajen aiki suka koma. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️ Zuwan Uncle Hashim da ya tarar da yanda suke ta cin ma Hajiya mutunci ai sai ya hau su da faɗa. Dama ga shi akwai fushi nan da nan ya zuciya yace Jalila, "ta ɗauko mishi bindigan shi duk sai ya harbe su." Yanda suka ga Uncle Hashim ɗin yake yi ne tamkar be da Kai, sun san tsab zai iya harbe su kamar yanda yace, hakan yasa suka ɗibi jiki suka fice daga waje suna ta zage-zage a kan, "sai an basu gadon su." Daƙyar suka bar gidan Hajiya tace, "ku ne matsiyata, gado ne za'a raba a kawo muku naku har inda kuke, MEEMA kuma babu inda zata koma a nan zata zauna." Nan ta saka Uncle Hashim ɗin da zancen, "idan MEEMA ta dawo yayi magana da ita a kan dukiyar Mahaifin nata". "Ai Hajiya ki bar zancen waɗannan matsiyatan, gadon ne baza a raba ba inga wanda zai sake tako mana gida yace zai ci mana mutunci, ƴan iska matsiyata." Hajiya tace, "a'a dole ne a raba ko don mamacin, kana ganin yanda suke tada jijiyan wuya duk wannan fitinan a kan Faruk zai ƙare, gwara a raba ko zai samu salama a cikin ƙabarin shi, inyaso ko can Riyadh ɗin ne sai ku je tare a san abun yi." Kansa kawai ya gyaɗa ya haura sama da sauri domin har yanzu a cikin fushi yake, bindigan na hannun shi tunda Jalilan ta kawo mishi, Da da farko ta ƙi kawo wa ne tana tsoron abun da zai biyo baya, sai da ya hau ta da faɗa sannan ta kawo a lokacin su kuma su Kawu Ali tuni sun fice a gidan. Su Hajiya suna falo suna mayar da zancen duk kan su sai cece kuce suke yi suna tsine wa su Kawu Ali musamman yanda Ummee take ta faɗar mugun halin su, abubuwan da suke musu tun Faruk yana da rai, dama ba shi suke ƙauna ba dukiyar shi suke so, ga shi kuma yanzu sun biyo sahu har suna iƙirarin zasu aurawa ɗan su MEEMA ne. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️ *TWO DAYS AGO* "Ke ɗaga kanki mana, wai lafiyan ki ƙalau? Na kula tunda muka zo school ɗin nan kike cikin damuwa karatun ma be dame ki ba yau". Cewar Abida wacce ke zaune a kan deks tana taunan chewing gum idanun ta a kan Luwaira. Ganin ta ƙi ɗago kai yasa ta bugi bayan ta tana cewa, "wai Ni kike wa wulaƙanci Luwaira? Ina magana kin yi banza da Ni." Sai a lokacin ta ɗago kan nata ta zuba wa Abidan idanu. Fuskar ta babu walwala tace, "me kike so in CE miki? Abida ba na son takura don Allah ki bar Ni in huta." Taɓe baki tayi tana wani yatsina da taunan chewing gum ɗin bakin ta, sai da ta dage ta ɗirka ƙwai ta fasa shi tuss a kusa da fuskar Luwairan kafin tace, "kin san hali na, idan har baki kula Ni ba wlh na dinga damun ki kenan, bazai yiwu ace tun ɗazu muna tare dake kin bar Ni ina ta zuba Ni kaɗai ba, sannan kin wani luƙume kai a benci kamar wata kunkuru ki ce bazan tanka ba. Dalla ki faɗa min damuwar ki Ni fa ƙawar ki ce." Tsaki Luwaira ta ja, ta san halin Abida shiyasa ta buɗi baki tace, "baza ki gane ba koda nayi miki bayani Abida..." Katse ta tayi da faɗin, "ba dai ki fahimtar da Ni bane ta yanda zan gane, idan kika faɗa min damuwar ki ai zan gane." "Hmm matsala ce ta soyayya Abida. Ban taɓa sanar da ke ba amma tunda kin matsa zan sanar miki, na san zaki kalle Ni da wani irin kallo sabida abinda zaki ji ya fito a baki na. Soyayyar Umar Faruk ne yake son kashe Ni, duk yanda na so na jure amma abin ya faskara na kasa." "To ban gane ba. Wani Umar Faruk ɗin? Ko kin yi sabon saurayi ne?" Abidan ta tambaye ta tana tsare ta da ido Ita kuma sai ta girgiza mata kai, sai da ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kafin tace, "Yayana Umar Faruk wanda kika sani, wanda muke gida ɗaya da shi; shi nake nufi." "Kutmar..." Ta saki wani zagi tana duro wa daga saman deks ɗin da take, sai kuma ta koma ta zauna a kan kujera tana facing ɗin Luwairan tace, "ke kar ki haukata Ni mana da yawa, yayan ki dai Yayan ki wanda na sani? Senator Umar Faruk na gidan ku; shi kike so? To ta ya hakan zai yiwu bayan na san Yayan ki ne?" Kanta Luwaira ta sauke ƙasa tace, "Ba Yayana bane, Umar Faruk ba Momy ta haife shi ba, hasali ma Momyn mu ita ce take auran mahaifin shi ta zo da mu gidan nan, sannan bayan ya rasu mahaifin shi sai ta riƙe Umar Faruk a wurin ta tamkar ɗan da ta haifa, bamu da wani alaƙa da Umar Faruk bayan wannan da nake faɗa miki." "Tab ɗijam... Gaskiya ban taɓa tunanin ba Momy bane ta haife shi duba da yanda take tsananin ƙaunar sa da nuna masa kulawa, duk da a yawancin lokuta ina mamakin yanda shi ya fita daban da ku, sai dai kasancewar na ga hoton Mahaifin shi shiyasa naga kamanceceniyar su tare, hakan yasa nayi tunanin shi ɗin ya biyo Mahaifin ku ne, ashe duk wannan abun shi ba ɗan Momy bane?" Gyaɗa mata kai tayi ta ƙara da cewa, "haka ne. Amma kuma maganar gaskiya sai dai Momy ba ta ƙaunar na aure shi." "To a kan me? Meyasa hakan bayan duk abinda na miji me ji da kanshi ya kai har ya zarta a so shi? A ko yaushe ina ma kaina kallon ban kai ajin da Umar Faruk zai so ni ba, bayan haka da tuni na afka a ƙaunar shi, sai dai ina ganin tabbas zan sha wahala duba da yanda rayuwar shi take, ba na tunanin zai iya so na domin babu ƙofan bayyana hakan, amma ke kuna gida ɗaya da shi kuma kin fi kowa sanin yanda yake ji da ke amma ki kasa sanar mishi, tun yaushe ma kike fama da dakon son shi?" Luwaira tace, "tun da muka dawo gidan su da zama, kamar yanda nace miki Momy ba ta ƙaunata da shi saboda wani dalili wanda sirrin mu ne bazan iya faɗa miki ba." Shiru ne ya biyo bayan zancen nata, yayinda Abidan ta kafe ta da idanu tana tunani a ranta. Sai can kuma ta ja numfashi da cewa, "to yanzu ya zaki yi? Idan har kin amince Ni zan taimaka miki, ya kamata ace ke ce kika mallaki babban ƙadaran nan ba wata ba, dama ce a gare ki, Umar Faruk ya wuce duk yanda kike zato, idan da zaki san yanda ƴan mata suke rushing a kanshi zaki sha mamaki tunda na san ke kanki sheda ce, amma babu inda zancen shi be zagaya ba a duk faɗin garin nan, ba na son kiyi rashin shi ƙawata, duk yanda za'a yi ki mallake shi domin kun dace wlh, idan ba haka ba zaki mutu a ƙaunar shi, ke ya kamata ki fahimtar da shi halin da kike ciki, kar ki wani biye ta Momy duk da ban san dalilan ta ba, amma ina mamakin ta ya ya take son hana auren ku duk da tarin ƙaunar da take nuna mishi." Shiru Luwaira tayi, a zuciyar ta tana son ta bayyana mata sirrin su na son ganin bayan Umar Faruk domin su mallake komi nashi, amma kuma tana tsoro, shiyasa ta sauke numfashi tace, "zan faɗa miki dalili amma ba yanzu ba." Gyaɗa kanta kawai tayi kafin tace, "fine. Allah ya Kaimu lokacin, yanzu tashi mu je mu samu wani abu mu ci yunwa nake ji, duk chewing gum ɗin nan ya gama ƙwaƙwule min ɗan hanji." Tashi Luwaira tayi ta ɗauki jakan ta suka fice. Sai da suka je suka ci abinci sannan suka dawo aji, dayake lecture ɗaya suke dashi ana gamawa suka yi gida. Kowa drever'n gidan su ya zo ya ɗauke ta. Luwaira na koma wa gida ta shiga Parlour ta tarar da Momy zaune ita da su Hafsah. Da gudu yaran suka isa wajen ta suka rungume ta suna mata Oyoyo Murmushin ƙarfin hali ta sakar musu tana rungume su duka. Daga nan ta ja su zuwa kan sofa ta zauna ta ɗaura Yusra a jikin ta Cikin murna Hafsah tace, "Aunty Dadyn mu ya dawo, an dawo da shi daga asibiti yanzu." "Da gaske?" Tafaɗa cike da farin ciki a zuciyar ta jin abinda Hafsan tace "Eh Aunty. Amma bamu je mun gan shi ba har yanzu." "Ok ku tashi mu je yanzu sai in Kai ku wurin shi." Yanda Luwairan take rawan jiki ne yasa Momy ta bi ta da harara. Sai dai kasancewar bata kalle ta ba bata san ma tana yi ba. Har suka fice sannan tayi ƙwafa tana ɗauke kai daga kallon bakin ƙofan da suka fice. Kai tsaye Part ɗin Umar Faruk suka wuce. Babu kowa a babban parlour'n don haka suka wuce ƙaramin parlour'n Ai kuwa yana zaune a saman sofa daga shi sai baƙar Singlet a jikin sa da dogon wando Robber kamar na sanyi itama baƙa, ƙasan wandon da mazugi wanda ya bai wa wandon damar tsuke masa ƙafa. Gaban sa kuma computer ne yana dannawa a hankali idanun sa ƙirr a kai. Jin motsin su yasa ya ɗaga kai ya dube su, ganin su yasa ya saki yalwataccen murmushi wanda ke ƙara fito da zallan kyawun sa da kamalan sa. Nan da nan ya buɗe hannayen sa suka zo suka faɗa jikin sa ko wannen su na kiran sunan, "Dadyyyy." Ita kuma Luwaira hannayenta ta naɗe a ƙirji tana bin su da kallo tare da sakin murmushin da be kai har zuci ba, domin a zuciyar ta ji take yi kamar ta je ta ture su ita ta shiga faffaɗan ƙirjin sa da koda yaushe yake mata gizau a cikin mafarkin ta, bata da wani buri sama da ace an wayi gari ta mallaki wannan basaraken namijin me tsananin haiba da kwarjini gami da nagarta. Tabbas duk wanda ya sami Umar Faruk ya gama dace da duniya domin duk inda na miji ya kai da ji da kanshi ya kai, kyawu nasaba gami da kuɗi duk ya haɗa, ga uwa uba tsantsan ilmi da tawali'u da son ibada. Shiyasa sosai take baƙin ciki da kishi da yaran shi duk idan ta gansu maƙale dashi, ko kaɗan ba ta iya sukunin zuciya sai dai dauriya da take azawa kanta wajen ta ga ta ɓoye abin da ke cin ranta... Maganar da yayi mata shi ya dawo da ita dogon tunanin da ta afka wanda yasa har guntun murmushin da ke fuskar ta ya gushe bata sani ba, da sauri ta gyara kanta tana sake yalwata fuskar ta da wani ƙirƙirarren murmushin tace, "na'am Yaya." "Ya naga kin tsaya a nan? Come and sit." Zuwa tayi ta zauna a kan sofa wanda ke kallon nashi still tana murmushi Sai ya ɗan ƙura mata ido tare da cewa, "me ke damun ki naga kamar kina da damuwa ko? Please faɗa min abinda ke damun ki domin ba na son ganin ki a cikin damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi." "Oh Yaya babu komi wlh, babu abinda ke damuwa." Tafaɗa maganar tana sosa kai tare da sake faɗaɗa fuskarta da fara'a Numfashi ya ja tunda shi dama ba Mutum bane me son takurawa makusantan shi. "Well. But kiyi haƙuri har yanzu ban cika miki alƙawarin ki ba. Ki ƙara haƙuri da Ni kinga yanzu nauyi ya hau kaina Ni kaina yanzu bani da lokacin kai na, amma insha Allahu i promise you wannan week ɗin motan ki zata shigo." "Allah yaya babu komi na san ai baka manta da Ni ba, Allah ya kai mu rai da lafiya." Murmushi yayi yace, "Amin." Sai kuma ya mayar da kallon sa kan Yusra wacce ta langaɓe masa a jiki yace, "Ya dai my Baby?" Tura baki tayi gaba tace, "Dady yunwa." "Yunwa kuma Baby?" Yafaɗa yana ware ido Ta gyaɗa mishi kai "To baku ci abinci bane? Hafsah baku ci komi bane da kuka dawo school ɗin?" Hafsah tace, "mun ci Dady, Momy ta saka Talatu ta girka mana kus-kus amma ita bata ci ba." Fuskarsa ne ta nuna alamun damuwa, sai dai yayi shiru be ce komi ba Hakan da Luwaira ta gani ne sai tayi saurin cewa, "Yaya bari in dafa mata a nan tunda yunwa take ji. Me zaki ci in dafa miki?" Ta ƙare maganar da kallon Yusran tana mata murmushi "Indomie zan ci." "Nima zan ci Dady ta dafa har da Ni." Cewar Hafsah cikin sauri "To kuna so ku mayar da ƙanwata kukun ku ne? Basu takura miki ba ko sister?" Yayi maganar yana kallon fuskar ta Murmushi ita kuma tayi tace, "haba dai a'a wlh, ai babu damuwa, bari in je in dafa musu." "Ok thanks my Sister. Nima ban san meyasa Kukun su har yanzu be dawo bane, ina tunanin zan sama musu wani." Luwaira ita dai tuni ta tashi ta nufi kichen. Hakan yasa Hafsa ta bi ta tana tsalle-tsalle While Yusra ita kuma ƙara maƙalewa a jikin sa tayi Shafa kanta yayi kafin ya ci gaba da latsa computern shi, jefi-jefi yana ɗago kai yana mata magana yana hura mata iska a fuska ganin tana wani lumshe idanu Hakan yasa ta ɗan dawo da kuzarinta ta saki jiki har tana dariya. Ta soma tsalle a jikin sa kamar yanda ta saba Ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke ganin ta saki jikin ta sosai. Ya san duk da yunwa ya mayar da ita haka, ko daga kallon ta zaka gane ƙarfin hali kawai take yi saboda Yusra akwai ci ba ta wasa da cikin ta, abu kaɗan ke saka tayi wani yaushi da ita tunda ta kasance me son gazar-gazar. Shiyasa yake matuƙar ƙaunar yarinyan saboda sak mahaifiyar ta ne, har lukutin jikin ta na Nusaiba ne. *Nayi iya yi na wajen sanar muku ina buƙatar more comments but har yanzu You don't changes, I'm very tired! from today insha Allah I will not posted again. Nima ina bukatar Comments ɗinku domin shi ke saka Ni naji daɗi a raina har na tabbatar da cewa ana karantawa, ko Thanks ka rubuta min zai tabbatar min kana karantawa, amma yanzu na gane babu masu bukata insha Allahu na dakata daga yau sai kuma sanda Allah ya waiwayo Ni. Bissalam 🙏🏻 Ina ma Real masoyana Barka.* [14/10, 10:03 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_27*              Bayan Luwaira ta gama dafa musu indomien sai ta zubo ta kawo musu parlour'n. Sannan tayi masa sallama ta fice Shi kuma yana ta faman aikin shi har suka gama cin abincin suka koma wasa da juna. Daga ƙarshe kuma barci ne ya ɗauki Yusra. Hakan yasa ya tashi ya wuce sama inda ɗakin shi yake ya bar Hafsah tana kallon cartoon. Da shigan shi ɗakin inda yake ajiye towul ɗin shi ya nufa ya zari ɗaya ya wuce cikin Toilet. Wanka yayi ya fito sanye da towul ɗin a jikin sa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa ya gyara suman kanshi kana ya wuce wajen sif ɗin kayan shi ya zaro wani farin yadi me tsananin haske da taushi, kayan dai-dai jikin sa suke sun masa kyau ainun tare da ƙara haskaka skin ɗin shi, sai yayi amfani da baƙar hula tare da cover shoes su ma baƙi, sannan ya wuce gaban mirror ya feshe ko ina na jikin shi da turaruka masu tsananin ƙamshi da shiga rai, agogo ya ɗauka ya ɗaura a tsintsiyan hannun sa kafin ya zari wayoyin sa guda biyu ya zuba a aljihun wandon sa ya fice da keey ɗin mota a hannu.           A lokacin da ya fita falo ya tarar da Hafsah itama tana gyangyaɗi, kai tsaye wajen ta ya nufa ya kira sunan ta. "Baby na KE ma barci kike ji?" Kanta ta gyaɗa mishi ba tare da tayi magana ba "To Ni kuma ga shi zan fita. Amma tashi mu je wajen Momy sai ku kwanta a can." Tashi tayi shi kuma sai ya nufi wajen Yusra ya ɗauke ta ya aza ta a kafaɗan shi, tare da riƙe hannun Hafsan suka fice. Part ɗin Momy ya nufa yayi Nocking a bakin ƙofan kafin ya tura da sallama a bakin sa ya shiga. Babu kowa a parlour'n don haka ya sauke Yusra a saman kujera ya shimfiɗa ta Yana cikin gyara mata kwanciya ne sai ga Talatu me aikin Momy ta fito daga kichen. Wajen shi ta nufa tana gaishe shi tare da mishi, "ya jiki?" Murmushi yayi mata kamar yanda ya saba ya amsa ta cikin mutuntawa. Kana ya tambaye ta, "ina Momy?" "Tana ɗaki bari in Kira maka ita." "A'a ba sai kin kira ta ba, ga su Hafsah nan ki shiga da su ciki suna jin barci ne, idan Momy ta fito ki sanar mata na fita." "To ranka ya daɗe!" Tafaɗa cikin girmamawa kana ta matso da zummar ɗaukar Yusran Shi kuma ya shafa kan Hafsah kafin ya juya ya fice. Kai tsaye haraban gidan ya nufa nan da nan securities ɗin sa suka nufo sa suna kai gaisuwa gare shi. Tsayar da su yayi da hannu kana ya wuce gaban wata farar mota ƙirar jib zai buɗe da kanshi, amma sai ɗaya daga cikin security ɗin ya zo da gudu ya buɗe masa. Sai da ya shiga ciki kafin ya kalle shi fuskar sa a sake yace, "ba na son ku biyo baya na." "Amma ranka ya daɗe!..." Katse shi yayi da cewa, "ya isa. Haka nake buƙata ba na son ku biyo NI zan iya da kai na ok?" "Ok Sir. Allah ya tsare." Yafaɗa yana sara mishi. Sannan ya mayar da ƙofan motan ya rufe mishi Shi kuma ya ja motan a hankali ya fice a gidan.                        ******           Momy da ke tsaye a bakin windown ɗakin ta tana kallon duk abin da ke faruwa. Bata saki labulen ba har sanda ta ga fitar Umar Faruk sannan ta ja dogon tsaki tana yarfe labulen. Sai ta koma zagaye ɗakin hannayen ta a goye a baya, gaba ɗaya damuwa ta nuna a fuskar ta kasancewar gani take yi wankin hula na son Kai su ga dare, har yanzu sun kasa cin nasara a kan shi, ga shi abinda suka shirya domin ganin bayan shi hakan be kasance ba, ya tsallake hatsarin da suka shirya mishi yanzu basu san kuma abinda zasu yi ba next? Tunanin Momy duk ya tafi ga matakin da zata ɗauka a kanshi. Ya zata yi? Zuciyar ta tana bijiro mata abubuwa da dama a ranta wanda har yanzu ta kasa yanke ƙwaƙwƙwaran makaman abin da zasu yi. Maganar Abdul ne ya faɗo mata a rai sai ta saki dogon numfashi tana komawa bakin gado ta zauna tare da tsirawa waje ɗaya ido. ita yanzu abinda ke damun ta kar yace zai auro wata ya kawo ta cikin gidan nan kamar yanda take buƙata, duk da ba har zuci take mishi maganar ba amma ba ta son ya sake aure, gaskiya akwai matsala dole ta samo mafita, amma kuma ba ta so ɗiyarta ta aure shi domin dole nan gaba zata rasa shi, "amma kuma idan dogon burin ki zai cika fa?" Wata zuciyar ta tambaye ta haka. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️            A hankali yake tuƙin motan cikin ƙware wa, duk da tuƙin yake yi but hankalin shi gaba ɗaya ya tafi ga tunanin abun da ke zuciyar sa, shiyasa lokaci-lokaci yake fuszar da iskan bakin shi yana ɗan dukan sitiyarin motan kaɗan-kaɗan a haka har ya kai gidan Hajiya. Ya danna horn me gadi ya fito Ganin da yayi Umar Faruk ne sai ya koma ya buɗe mishi Gate ɗin ya shiga da motan Parking space ya nufa ya faka motan Da gudu me gadin ya taho ya buɗe mishi ƙofan yana washe baki da faɗin, "Barka da zuwa ranka ya daɗe!" Murmushi yayi mishi yace, "Yauwa. Kana Lafiya?" "Alhamdulillah ranka ya daɗe!" Yafaɗa cike da fara'a kamar zai duƙa mishi Shi kuma fitowa yayi a motan kafin yace, "Allah yasa Captain yana nan?" "Eh yana nan don yanzu ya dawo gidan ma." "Ok." Yace dashi sannan ya saka hannu a cikin aljihu ya zaro sabbin kuɗi ƴan dubu ɗaya ya ba shi Nan ya soma mishi godiya kamar zai je ƙasa don duƙa masa Shi kuma murmushi yayi yace, "kar ka damu ka dena min godiya." "Ai ranka ya daɗe! Dole ne. Allah ya ƙara buɗi yasa kafi haka, Allah ya tsare ka da duk kan sharrin maƙiya." "Amin Amin." Ya amsa shi cike da jin daɗi kana ya wuce ya tafi. Kai tsaye ƙofan shiga parlour'n ya nufa yayi Nocking Babu jima wa sai ga Uncle Hashim ya fito yana waya. Ganin shi yasa ya waro ido waje yana kashe wayan kana ya ba shi hannu tare da cewa. "ah ah patient ɗin mu ne a nan? Ya aka yi haka?" Murmushi yayi ya miƙa mishi hannun suka cafke kana yace, "Ai naji sauƙi Malam." Matsa mishi yayi ya shigo sannan ya rufe ƙofan suka shiga Parlour Zabba'u da Jalila ne zaune a parlour'n. Don haka suka soma gaishe shi Zabba'u na faɗin, "ikon Allah har ka samu sauki da zaka fara yawo Umaru?" Murmushi yayi yana zama Shi kuma Uncle Hashim yace, "nima abun da na gani kenan. Yau fa aka sallame ka? Gaskiya zan ɗau mataki a kan masu tsaron ka da har suka bar ka ka fito, i know Momy bata san ka fito ba?" "Haka ne. "But I'm relieved. I came to greet Hajiya." "A'a ai baka kyauta ba kuwa. Ina kai ina zuwa gaishe da Hajiya baka da lafiya, itama baza taji daɗi ba, bari in Kira ta." Cewar Zabba'u tana tashi ta wuce Ita kuma Jalila tuni ta tashi ta kawo mishi drinks ta ajiye mishi Godiya yayi mata sannan ya tambaye ta, "ina Habeeb?" "Yana tare da Ummee a ɗakin ta".            Fitowar Hajiya itama sai da tayi mishi faɗan zuwan nashi Shi kuma yace, "ya zo gaishe ta ne kawai." Tace, "haba dai Umar. Kana wasa da lafiyan ka dai, amma mene ne na zuwa gaishe Ni bayan yau aka sallamo ka?" Uncle Hashim yace, "hm Hajiya bar shi kawai." Tace, "duk da haka dai mun gode, sai dai ka riƙa kula da lafiyan ka. Ya jikin naka Yanzu?" "Alhamdulillah Hajiya." "Masha Allah haka ake so ai. Allah ya daɗa tsare ku ya taimaki rayuwar ku." "Amin Hajiya." Shi da Uncle Hashim suka amsa A lokacin Ummee itama ta fito suka gaisa take tambayar shi itama jikin nashi? Yace, "da sauƙi Aunty." "To Masha Allah mun ji daɗi Allah ya tsare gaba." Daga nan ɗan hira suka taɓa kafin suka fita da shi da Uncle Hashim zuwa waje. Sai da suka kai baƙin motan shi sannan ya kalle shi yace, "Your daughter is not here?" "Oh ko dai wurinta ka zo ne? Tell me the truth?" Murmushi yayi yace, "No Ina tambaya ne saboda ban ganta ba." Uncle Hashim yace, "bata dawo daga wajen aiki ba, amma na san yanzu zata shigo tunda three ya kusa." "Ok." Yace yana ɗan kaɗa keeys ɗin hannun sa "I still don't trust you Dude, tell me the truth you come to her?" "Yes. I think about your talk, I want to marry her if there is no problem, because.." sai ya ɗan ja numfashi kafin yace, "because she entered my soul. I love her!" Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Uncle Hashim, cike da tsantsan farin ciki yace, "da gaske kake yi Aboki na?" "Yes." Yafaɗa yana gyaɗa mishi kai "Oh I can't tell you how happy I feel in my heart, naji daɗin abun da ka faɗa, insha Allahu zan shige maka gaba a kan samun ta, ina bayan ka dude because you fit so well." Murmushi kaɗai Umar Faruk yake yi be sake cewa komi ba, shi kansa a zuciyar sa farin ciki ne yake ɗawainiya da shi, yana ga hukuncin da ya yanke hakan shi ne dai-dai, zuciyar sa zata fi aminta da ita a kan ta zame mishi Abokiyar rayuwa, ya san hakan zai faranta ran Momy idan yau aka ce ya je mata da zancen ya samu matar aure duk da be da tabbacin ita MEEMAN zata amince, but yana sa ran hakan Uncle Hashim yace, "Let's go back inside and wait for her to come back sai ku gaisa." Daga nan gidan suka koma. A nan Uncle Hashim yake sanar wa su Hajiya abun da ke faruwa Babu wanda be nuna murnan sa ba musamman ma Ummee da ta fi kowa farin ciki, tabbas ta ga dacewar ɗiyarta da Umar Faruk saboda shi Mutum ne me matuƙar kirki, ko ba komi hakan zai kusanta ta da ɗiyarta tunda zata yi aure a nan, kuma tana fatan ta ga auren ta yanzu tunda ta kai girman da ya kamata tayi aure domin rayuwar mu a nan daban da can inda ta tashi, 26/27years ai ya wuce ace har yanzu tana zaune babu aure.                ******        Koda MEEMA ta dawo babu wanda yayi mata maganar sai Uncle Hashim, sai yace mata, "she prepares and eat and a visitor comes to her." Dayake lokacin yana parlour'n sama an kai shi ya zauna zaman jiran ta "A visitor came over me?" She asked in surprise "Yes daughter. Get ready and go find him." Ɓata fuska tayi tace, "then Uncle why did you come of me?" Dafe goshin sa yayi kafin ya kalle ta yace, "daughter please leave your questions and go to him, he will tell you what he has come to do." Daƙyar ya shawo kanta da tambayoyin da ta tsare shi da su. Ta ci abinci sannan tayi wanka ta saka doguwar riga kamar yadda ya zame mata jiki, Abaya ce ja da kwalliyan Stones a gaban. Sai tayi Rolling da mayafin Har zata fita sai Jalila ta shigo ɗakin ta ganta, tace, "Where are you going to go without a make up?" Ido ta zuba mata fuskar ta da mamaki Sai ta kamo hannunta ta zaunar da ita a gaban mirror ta soma mata shafe-shafe Bata ce mata komi ba illa bin ta da take yi da ido. Sai da taga abun ya wuce gona da iri domin ita ta tsani kwalliya sosai a fuskar ta, "no Aunt I don't want. Leave me alone." Murmushi ita kuma tayi tana kallon ta tace, "You're so beautiful." Ɗan tura baki tayi tana kawar da kai Ita kuma dariya tayi mata ta kamo hannun ta suka fice. Sai da suka fito ta saki hannun nata tace, "Go upstairs he waiting for you". Daga haka ta juya ta wuce Parlour inda su Hajiya ke zaune Ita kuma kamar baza ta tafi ba sai kuma ta taka a hankali ta soma hawa matattaƙalan benen, tana zuwa bakin ƙofan da zata shiga parlour'n ta ja ta tsaya, tunani kawai take yi, "Then who came to her?" Bata da me amsa mata tambayar ta hakan yasa ta tura ƙofan ta shige. Sosai gaban ta ya faɗi kawai arba da shi da tayi zaune a saman kujera. Sai ta sake waro ido tana sake duban shi kamar wata status a wurin Haka zalika shima kallon ta yake yi yana aiyana tsantsan kyawun da Allah ya bata, musamman yanzu da ya ganta da Powder a fuska ta saka kwalli a fararen manyan idanun ta, hakan ya ƙara fito da zallan kyan ta domin be taɓa ganin fuskar ta da kwalliya ba. Yanda ya ga ta tsaya ta ƙi takowa ne sai ya tashi tsam ya isa gaban ta Idanun ta ƙirr a kanshi har yanzu tana mamakin ganin shi kuma tana son tabbatar da cewa, "Is he her guest?" "Why did you stop here?" He spoke slowly looking at her Hakan yasa ta ɗan ƙyafta idanuwan ta tana kawar da su, sai kuma ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin sun haɗa ido ta sake ɗauke kai Shi kuma murmushi yayi yace, "Let's go and sit down." Sannan yayi gaba Hakan yasa ta taka tabi bayan shi kamar an tsamo ta a ruwa coz yanda take tafiyar. Slowly she sat down in the chair looking at him, sai ta haɗa hannayen ta a saman cinyoyin ta ta dunƙule su wuri ɗaya tana sauraron bugun zuciyar ta da sauyin yanayin da ke baƙuntan ta Shiru ne ya biyo bayan zaman nata. Shi kansa be san ta ina zai fara ba shiyasa kawai ya kafa mata ido yana kallon ta, sai da ya ɗau kamar mintuna biyar yana mulmula baki da tunanin ta inda zai fara kafin ya ɗan ja numfashi yana sake tsayar da idanun sa ƙyam a kanta ya soma kiran sunan ta Hakan yasa ta ɗago dara-daran idanuwan ta ta sauke a kanshi wanda fuskar ta har ta soma tsatstsafo da zufa sakamakon halin da take a ciki "I know you will be surprised to come to your place even though I know your Uncle has informed you." Sai ya sake jan numfashi ya ci gaba da faɗin, "MEEMA is nothing come to you but a word of love. I am currently in love with you That's why I let you know. I hope you will be the mother of my children if you don't mind." Still sai ya kira sunan ta Kiran sunan ta da yayi a ƙarshen maganar nasa yasa ta lumshe idanuwan ta tana sake tamke hannun ta sosai "I love you MEEMA! please trust me As your beloved please." Sosai maganar nasa ya shige ta har cikin zuciya, sai dai ta kasa ko motsin kirki domin har zuciyar ta ta dena aiki a halin yanzu, maganganun nasa kaɗai ke kai kawo a cikin kunnuwan ta suna sake mata yawo tamkar yana sake maimaita mata. Bata san sanda ya iso gaban ta ba sai kawai ganin shi tayi durƙushe a gefen ta. Da sauri ta ɗaga kai ta zuba masa idanun ta wanda hakan yasa suka shige cikin nashi. Kasa ɗauke kai tayi domin yanda take jin wani baƙon yanayi na shigan ta sabida haɗa idanun da suka yi Karantan yanayin ta yake yi na ɗan soconni kafin yace, "I want to hear your answer if there is no concern please." Tsit tayi ta ƙi yin magana domin bata san me zata ce ba "Okay I'll give you time to think, but you know I'm a big man I need your answer in a little while because I hope soon we will be husband and wife." Sai ya tashi tsaye yana tusa hannayen shi a aljihun wandon shi. Kamar zai yi magana a yanda ya kafa mata idanun shi, sai kuma ya fuszar da iska ya juya ya ɗan yi taku biyu kafin ya kalle ta yace, "I will go, good bye." Sannan ya juya ya fice.                 Ta kasa motsa wa a wurin tun fitan nashi. Idanun ta kawai ke motsi a jikin ta, sosai ta shiga wani yanayi da bayyana mata kalaman soyayya da yayi, ba wai don bata saba ji ba, hasali ma baza ta iya cewa kai tsaye ba ta ƙaunar shi ba sabida abubuwan da take ji a game dashi, amma kuma tana da wanda zuciyar ta take ƙauna har yanzu, "ISHAQ." zuciyarta ta furta mata. Har yanzu shi ne a zuciyar ta, tana son shi matuƙa kuma shi take da burin ta aura, but bata san meyasa ba tana jin wani irin shauƙi tare da marari a zuciyar ta wanda take ji tamkar shi ne ya fi dacewa da ita, bata san meyasa ya tsaya mata a rai ba musamman yanzu da ya gama bayyana mata abun da take ji kamar tana buƙatar jin sa a bakin sa. Yanda zuciyar ta take bugawa a halin yanzu sabida tunanin da suka cinkushe mata yasa ta tashi da sauri ta nufi ƙasa ta shige ɗakin ta. Kan gado ta faɗa tana mayar da idanun ta ruf ta rufe. Ta jima a haka bata sake yin motsi ba kuma bata ba wa zuciyar ta damar yin wani tunani ba, har sanda Uncle Hashim ya shigo ɗakin bayan Nocking ɗin da yayi mata. Tashi tayi zaune tana kallon sa Shi kuma ya zo ya zauna a gefen ta kana yace, "MEEMA I want to talk about something understands." Sai ya saka hannu ya kamo hannayen ta biyu ya haɗa da nashi. Cikin ido yake kallon ta yace, "I know you heard what my friend brought to you. He loves you very much and wants to marry you. What did you say?" Shiru tayi tana sauke kai ƙasa Sai ya saka hannu ya kamo fuskar nata ta yanda zata sake facing ɗin shi yace, "Tell me. Do you like him? I want an answer from your mouth." Nan ma she kept quiet because she had nothing to say Sai yace, "MEEMA let me know what's on your mind, no one will restrict you ok? Do you like my Friend?" "Uncle, I have the one I want.." she said calmly. "Who is he?" Ya katse mata maganar yana kallon ta "ISHAQ. I still love Ishaq very much. But I still haven't got his phone, every time I call But his phone did not ring." Sai ga hawaye sun soma zubowa a fuskar ta, nan da nan ta soma shashsheƙan kuka Mamaki ne ya kama shi, sai ya riƙo kafaɗun ta yace, "Why you crying Daughter? What happened to you? Or because you can't find him on the phone?" Girgiza kanta tayi, sai kuma ta kwanto da kanta a jikin sa cikin shashsheƙan kukan da a yanzu ya ƙaru tace, "Uncle I love him but I know he broke up with me." Kasa magana yayi illa shafa mata kafaɗa da yake yi alamun rarrashi. Can sai ya ɗago kanta yana kallon ta yace, "Now you don't like my friend but Ishaq?" Shiru tayi tana runtse idanun ta Shi kuma sai ya bi cuty face ɗin ta da kallo a ransa yana nazartan yanayin ta, tabbas idan ba hasashe yake ba he sees his friend's love in her eyes amma kuma tana son dannewa sabida wani. Don haka dole ya san abun yi bazai bari abokin shi ya rasa ta ba, sun fi dace wa da juna koda be san wancan ba. Hannayen ta da ya saki ya sake riƙo wa yanzu tare da kiran sunan ta Sai ta buɗe idanun ta da suka soma sanja kala ta zuba mishi "Tell me about your boyfriend. What do you have in common? Did you fight?" Sai da ta ja majina kafin ta buɗe baki a cikin raunin murya tace, "I started to break up with him, but when I came to this country I told him to follow me and ask to marry me, but since I came I have not got his number again, I informed my friend to go home and check on him.." sai ta tsagaita sabida yanda muryan ta ya harɗe sakamakon shashsheƙan da take yi. Kana taci gaba da faɗin, "but he refused to listen to her. He refused to let them speak." "MEEMA raise your head and look at me". Babu musu ta ɗago kanta tana kallon shi "I will tell you the truth now that he is separated from you, he cannot follow you here and marry you, you also know the truth, forget him. keep my friend as your life partner, he loves you. Umar Farouk is very kind has a good attitude, He was once married but his wife died, and she bore him two children Hafsah and Yusra, he loved them very much, and now he lives with his father's wife and children in their house. I promise you you will be happy, he will take care of you." Sai ya sake kiran sunan ta a hankali, be bari ta amsa ba yaci gaba da cewa, "my daughter. Please accept my friend's love. Please allow him to show you his love for you. If you do not like him you may part with him in the future, but now I beg you give him a chance ok?"   Kanta ta jinjina mishi a hankali hawayen cikin idanun ta suna sake zubo wa     Sai ya saka hannu ya ɗauke mata yana murmushi yace, "Why are you crying Daughter? Because my friend told you he loves you is because you're all in trouble?" Fuskar ta ta kwaɓe a yanzu ɗin tana shirin yin kuka tace, "laà Uncle." "To what's wrong?" Shiru tayi masa tana sauke kai ƙasa Sai ya ɗaura hannun sa ɗaya a kanta yace, "I give him your Number you will always look for him. Let me go." Sai ya mike ya fice ya barta a wurin ko motsin kirki ta gaza yi. [14/10, 10:04 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                         💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️*                  *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._                              *NO_28*                  Ya fi mintuna biyar a cikin motan be fito ba koda yayi parcking ɗin motan a cikin gida Securities ɗin sa duk sun zo sun mamaye wurin har ɗaya ya buɗe masa ƙofan motan suna miƙa mishi gaisuwa Sai dai ya ɗaga musu hannu be ce komi ba. Ɗan numfashi ya ja kafin ya ziro dogayen ƙafafuwan sa ya fito a motan, sannan ya taka ya wuce ya nufi Part ɗin Momy. Nocking yayi da sallama ya shiga ciki Da gudu Hafsah da Yusra suka yo kanshi ganin mahaifin nasu suna murna Nan da nan ya haɗa su ya rungume cike da fara'a yana ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye wa. Kana kuma ya riƙe musu hannu zuwa kan kujeran yana tambayar su Momy Kafin ma su ba shi amsar sai ga ta ta fito a ɗaki tana washe baki tace, "ah ah my son ka dawo?" "Wlh kuwa Momy. Ina wuni?" "Lafiya lau. Nayi mamaki da aka ce min ka fita, kuma ga shi har yammaci tayi baka dawo ba duk hankali na ya tashi, yanzu nake cewa Luwaira ta kira min kai a wayanta tunda nawa ya ƙi shiga." Murmusawa yayi yace, "ayya Momy kiyi haƙuri na tayar miki da hankali. It's something I do and it's important that I go out." "Masha Allah tunda Babu abunda ya same ka ka dawo gida Lafiya, abun da nake ji dama kenan shiyasa duk na tashi hankali na." Sai kuma ta kalli su Yusra tace, "an ga Dady ana ta murna ko?" "Momy dama akwai maganar da zamu yi. Maganar aure na insha Allahu yanzu na samu wacce nake so zan aura." Sosai maganar ta zo wa Momy a bazata, wani irin sarawa ƙirjin ta yayi wanda ya hana ta magana, sai da ta ɗan ja seconni kafin ta buɗe baki cike da murnan da iyakan shi fuska tace, "Masha Allah Son, yau ka faranta min abun da na jima ina fatan ji daga bakin ka, ai hakan ya fi shi ne zai ƙara kankaro maka mutunci ka zama babban mutum. Aina yarinyar take?" Yana murmushi yace, "yarinyar Aunty ce ai, ƴar Yayar Hashim Aboki na." "Oh ko wannan yarinyar wacce muka haɗu a asibiti?" "Eh ita Momy." Murmushin yaƙe tayi tace, "Masha Allah sosai kuka dace kuma, ai yarinyan naga kamar babu ruwan ta, yanzu kuma zumunci zai ƙara ƙulluwa kenan kai da Hashim? Abun gunun sha'awa wlh tunda zai baka yar shi ai haka ake so." Shi dai murmushi kaɗai yayi Tace, "alhmadulillah ai komi yanzu ya zo da sauƙi tunda ka samu Matar Aure, ko su Hafsa zasu ji daɗi ai idan aka ce sun sami Mahaifiya. Allah yasa ayi damu." "Amin Momy. Abdul be shigo nan bane?" "Eh ina tunanin ma ba ya gidan, amma na san bazai jima ba zai shigo tunda dare ya fara." Miƙe wa yayi yace, "zai tafi." Sannan yayi mata sallama suka fice da yaran.               Kai tsaye Part ɗin shi ya nufa, ya saka yaran suyi alwala sannan shima yayi, sai da ya tabbatar sun tayar da Sallan ya bar su a nan falo ya wuce masjid ɗin da ke a cikin gidan.                  *******           Momy kasa motsa wa tayi a wurin tun fitan shi gaba ɗaya hankalin ta ya tashi Fitowar Luwaira daga ɗaki ne ta zauna tana tambayar ta da cewa, "Momy kamar na ji muryan Yaya Umar a nan ina Toilet. Ya dawo ne?" Kallon ta Momyn tayi bata iya ce mata komi ba domin hankalin ta ya fita a jikin ta tunani ya sha mata kai Sai da ta sake magana ne tana tambayar ta, "Wai Momy lafiya kika yi shiru?" "Babu lafiya Luwaira. Ina Abdul kira min wayan shi yayi maza-maza ya zo?" Yanda ta ga hankalin ta ya tashi ne yasa ta tashi da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauko wayan nata ba tare da ta sake furta komi ba, sai da ta kira shi kafin ta sake kallon ta tace, "Momy wai lafiya ki sanar min don Allah?" "Ki bari Abdul ya zo".              Babu jima wa sai ga Abdul ɗin ya shigo tunda dama ya iso gida. Koda ya shigo ya gansu a haka shima tambyar ya soma jeho wa A nan Momy ta sanar musu da zancen da Umar Faruk ya faɗa mata Luwaira kasa cewa komi tayi saboda tashin hankali "Momy wacce yarinyar kika ce zai aura?" "Wannan yarinyar da suka zo gaishe shi a asibiti da su Hajiyan Hashim." Saurin tashi tsaye yayi ya furta, "Whattt..?" Kallon sa Momy tayi tana karantan yanayin sa ganin yanda gaba ɗaya tsananin tashin hankali ya nuna a fuskar sa. Kafin ma tayi magana sai ji suka yi Luwaira ta faɗi ƙasa a sume. Tuni Momy tayi kanta ita da Talatu wacce ta fito daga ɗakin ta ta hangi me ke faruwa Shi kuwa Abdul a halin da yake ciki yana ga ya fi ta shiga tashin hankali, shiyasa be bi ta kansu ba ya juya ya fice da sauri ya nufi Part ɗin shi. Yana shiga ya faɗa kan kujera yana mayar da numfashi, sai kuma ya kama kanshi zuciyar sa tana tafarfasa kamar zata faso ƙirjin sa, kawai maganar Momyn ne ke dawo mishi a kwanya, taya zai bari ya rasa yarinyan nan bayan ya rigada ya kamu da ƙaunar ta? Ya za'a yi ma ace Umar Faruk ne zai aure ta? Haba bazai yiwu ba.. sai kuma ya tashi tsaye ya nufi cikin bedroom ɗin shi kamar zai tashi sama.                Ruwa talatu ta ɗibo aka zuba mata kafin ta farfaɗo Ganin sambatun da take yi ne sai Momy ta kalli Talatu tace, "je ki kiyi aikin ki." Hakan yasa ta tashi ta wuce har tana jiyowa tana kallon su, sai kuma ta taɓe baki a ranta tace, "babban magana. Akwai tashin hankali kenan." Momy kuwa tana ganin Talatu ta shige sai ta kalli Luwairan tace, "ke ki yiwa mutane shiru kina hauka ne zaki tona mana Asiri?" Kuka ta fashe da shi tana cewa, "Haba Momy ke kin san a halin da nake ciki ne? Wlh ji nake yi kamar zuciyata zata faso ƙirji na saboda zancen ki, bazan iya jure wa ba wlh, bazan iya bari wata ta shigo gidan nan a matsayin Matar Umar Faruk ba, Ni ce zan aure shi, idan har ban aure shi ba to babu shi babu wani auren, sai dai duk abinda za'a yi ayi bazan bari ba." Sai ta sake kece wa da kuka Dole Momy ta koma rarrashin ta tace, "ki tashi ki wuce ɗaki kiyi sallah, zamu yi maganar daga baya domin nima bazan bari wata ta shigo gidan nan ba gwara ke ki aure shi." "Da gaske Momy?" Tafaɗa da sauri jin abinda Momyn tace "Ki tashi nace ki wuce ban son iskanci." Dole ta tashi tana faman hawaye ta wuce ɗakin ta Ita kuma Momy kasa tashi tayi saboda ruɗu da tashin hankalin da yake cin ranta, duk ta rasa abun yi, daga baya kuma ta miƙe ta wuce ɗakin ta.                 ✳️✳️✳️✳️✳️                Sai da aka yi sallan isha'i sannan ya dawo gida. Da ya shiga parlour'n su Hafsah suna zaune suna kallo. Yana shigowa suka zo suka ƙanƙame shi suna kiran sunan shi. Ya kama su suka zauna yana cewa, "My babies har Kun idar da sallan?" "Eh Dady." Suka haɗa baki wajen faɗa Shafa kansu yayi ya dubi wajen dainning. Sai kuma yace, "ok to ku tashi mu je ku ci abinci." Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin. Bayan sun zauna ya zuba wa kowa abinda yake so kafin suka soma ci Shima abincin yake ci amma hankalin shi na kan wayan shi, laluba Numban MEEMA da Uncle Hashim ya turo mishi yayi, sai da yayi saving kafin ya danna kira. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe sanda ya ji wayan ta soma Ring, sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba sai ya sake kira, nan ma shiru dole ya haƙura ya mayar da hankalin sa kan abincin sa. But ko kaɗan ya gaza ci sosai saboda tunanuka da suka yi masa yawa, surutun da su Hafsah suke mishi ma kaɗan-kaɗan yake amsa musu tunda hankalin shi ba ya wurin. Sai da suka gama yace, "su wuce ɗaki yana zuwa." Daga baya ya bi bayan su ya ciro musu kayan barci suka saka sannan yace, "su hau gadon su kwanta." Yayi musu addu'a ya fice ya koma ɗakin sa Shima sai da ya shiga yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya hau kan gadon shi. Kansa ya ɗaura a dantsen hannun shi yayi shiru, ya jima a haka sai kuma ya ja numfashi ya karkace kai ya ƙura wa wayan sa ido da ke ajiye a saman gadon. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya saka hannun sa ya ɗauka ya sake laluba Numban MEEMA ya kira ta. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️               A lokacin shigowar MEEMA kenan ɗaki, ta gama shirin ta tana ƙoƙarin kwanciya ta ji Ring ɗin wayan ta da ta ajiye a saman mirror tun kafin fitan ta. Zuwa tayi ta ɗauka sai kiran ya tsinke, nan ta ga an yi mata three missed calls, ɗan jim tayi bata kai ga yin wani tunani ba wani kiran ya sake shigo wa. Sai ta nufi bakin gadon  ta zauna kana ta latsa wayan tayi peacking ta saka a kunne.              Wani ajiyan zuciya me ƙarfi ya saki jin anyi peacking call ɗin. Sai da ya ɗan gyara kwanciyar sa kafin ya kai wayan kunne yana sallama Sassanyan muryan sa da ta bugi kunnen ta ne yasa ta ɗan lumshe idanu tana buɗe su. Sai da ta ja seconni kafin ta amsa sallaman in a very low voice Shiru ne ya gifta na ɗan wani lokaci Kasancewar MEEMA bata san shi bane; ko kaɗan bata kawo shi ne ya kira ta ba duk da muryan nasa yayi mata kama da wanda ta taɓa ji, jin shiru sai ta ciro wayan ta duba ta ga yana tafiya sannan ta mayar ta sake faɗin, "hello who's online?" Lumshe idanu yayi saboda jin yanda muryan nata ya ratsa shi har cikin jiki da ɓargon shi, sai da ya gyara kwanciyar sa daƙyar ya buɗe baki wanda muryan nasa har shaƙewa tayi ya kirayi sunan ta Hakan yasa tayi shiru tana tunani a ranta, a nan ne tunanin sa ya faɗo mata wadda ta tabbatar da tabbas shi ne. Bata amsa ba illa shirun da taci gaba da yi Sai yace, "Weldon, I hope I didn't bother you calling you last night?" Duk da ta gane shi but hakan be sa tace, "But to whom am I talking?" Shafa kansa yayi a hankali ya furta, "Are you talking to Umar Faruk, hope now you understand Me?" Still shiru tayi Sai yace, "Do you still understand MEEMA?" Jin yanda ya kira sunan ta yasa ta lumshe idanuwan ta tana zamewa a kan gadon ta kwanta, still she's silent Hakan sai ya saka jikinsa yayi sanyi sosai, a hankali ya sake furta sunan ta "Na'am." She answered him briefly "I don't know why you don't want to talk to me. Does that mean you don't need me in your life? Tell me the truth." Shiru ta sake yi tana jin zuciyar ta na bugawa sosai fiye da sanda ta gane shi ne "I know I'm restricting you but I'm sorry please, Don't say I'm bothering you That's not my nature, but I'm in a political situation. But I have nothing to worry about, I look forward to seeing you whenever you want to let me know."   MEEMA rufe idanun ta kawai tayi tana sauraron muryan nashi wanda ke ratsa mata can cikin kunnuwa yana saukar mata da kasala da wani irin yanayi a jiki "MEEMA." Ya kira sunan ta in a slowly Buɗe ido tayi a hankali tana amsa mishi "I restrict you with my words?" "Laà." Sai ya ja numfashi yace, "ok but did you allow me to call you? I don't want to restrict you because I am a person who does not want to restricted." Shiru tayi kamar baza tayi magana ba sai tace, "Na'am." "Ok thanks. I will let you rest until tomorrow. Sleep well, dream of me please." Wani abu ne ta ji ya tsarga mata, tayi saurin mayar da idanun ta tana sauke numfashi Shi kuma jin tayi shiru sai yayi mata sallama ya kashe wayan. Ajiye wa yayi yana saka hannu a fuskar sa ya shafo sajen sa yana me lumshe idanu, kyakykyawar fuskar ta kawai yake hango wa hakan yasa ya saki murmushi a hankali, sai ya gyara kwanciyar sa yana buɗe idanun sa ya kafa wa wuri ɗaya ido. Tunani yayi masa yawa dole ya miƙe zaune ya buga tagumi, sai kuma can ya koma ya kwanta yana mayar da idanun sa ya rufe still haka ya ci gaba da tunanin ta a ranshi.                    "*****            MEEMA kuma tunda ya kashe wayan itama ta kasa motsi, idanun ta a rufe har sai da ta ɗauki kusan mintuna ashirin a haka kafin ta tashi ta gyara kwanciyar ta sosai ta haye kan gadon, duk yanda ta so ta cire tunanin sa tayi barcin ta but ta kasa. Sai dai ɓarawo barci daga baya ya zo ya sure ta cike da mafarkin Umar Faruk. [14/10, 10:05 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK* 💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *NO_29* *THE FOLLOWING DAY* MEEMA tana tashi da safe da text ɗin Umar Faruk ta soma cin karo, haka kawai sai ta ji farin ciki ya ziyarci zuciyar ta, ta karanta text ɗin ya fi sau uku, yanda ya nuna kulawar sa a kanta da yanda ya damu da ita sosai ya saka ta farin ciki, shiyasa gaba ɗaya a lokacin ta ji ta a wani irin yanayi na nishaɗi wadda ta kasa gane meye ya saka ta wannan farin cikin sosai haka, duk da gefe ɗaya kuma tana jin wani irin faɗuwar gaba. shirin ta take yi but tunanin ta na a kanshi, har ta gama shiryawa yau ta sanja shiga, haka kawai yau take son saka kayan hausawa kasancewar tunda aka ɗinko mata bata taɓa amfani da ko ɗaya ba, atamfa ce kalan ruwan madara sai aka yi amfani da ja da baƙi wajen design ɗin flower, ɗinkin riga da skert ne da suka kama ta cif kasancewar ta me diri tubarakalla, sosai kayan suka yi mata kyau suka sake haska skin ɗin ta, ita kanta ta kasa ɗauke kai daga kallon surar jikin ta sabida yanda kayan suka yi mata kyau, sai juyi take yi a gaban mirror tana ƙara kallon kanta, murmushin kan fuskar ta ya kasa gushe wa still sai juyi take yi, sai da ta gaji don kanta kana ta ɗauki ɗankwalin da ninyan ɗaurawa, sai dai duk yanda ta so ta ɗaura ɗin ta kasa, sai cikuikuiye shi take yi tana ɗaura wa tana kwance wa but ya ƙi mata yanda take so, dole ta haƙura ta gyara gashin ta ta tufke shi a ƙeyan ta, kana ta ɗauki veil ja tayi Rolling da shi ya saukar mata a iya kafaɗa, sai tayi using da black flat shoes da saman ya kasance ja, yanda ta ga kayan sun yi mata ne yasa ta ɗauki after dress tana shirin saka wa, sai kuma tayi shiru tana ɗan tunani idanun ta a kan mirror tana kallon kanta, sai kuma ta mayar ta ajiye ba tare da ta saka ba sannan ta ɗauki Handbag ɗinta ta fice ba tare da ta shafa komi a face ɗin ta ba Babu kowa a parlour'n kasancewar safiya ne, sai Zabba'u wacce take ta ƙoƙarin shirya Breakfast a saman table. Ganin ta yasa ta washe baki tana cewa, "wow MEEMA, you look so good, the stuff looks so good to you." Ita kanta murmushi take zuba wa har ta iso kusa da ita tace, "thanks. Good morning." "Hope you are feeling well?" "Alhamdulillah." Tafaɗa tana jan ɗaya daga cikin kujerun dainning ɗin ta zauna. Sannan ta soma haɗa tea Ita kuma Zabba'u surutu ta soma jan ta dashi a haka har ta gama shirya komi a inda ya dace. Kana ta juya ta koma kichen While MEEMA sipping tea ɗin take yi a hankali tana ɗan lumshe idanuwan ta, tunani ne a ranta har ta gama shanye tea ɗin ta ajiye sannan ta tashi ta wuce ɗakin Hajiya Lokacin Hajiya na zaune a saman sallaya tana ta lazimin safe Da shigar ta ta nufi wajenta tare da kiran sunan ta Hakan yasa Hajiyan ta sakar mata murmushi tana kallon ta har ta iso ta duƙa a gaban ta As usuals hannun ta ta kama ta sumbata tana kallon fuskar ta cike da murmushi a face ɗin ta tace, "Grandma good morning." Sai da ta shafa addu'ar nata kafin tace da ita, "Morning my dear. Today you have done very well, Masha Allah you look so cute." "Thanks Grandma." Tafaɗa itama tana murmusawa "You eat breakfast?" "Na'am grandma. I'm go". "Ok God help give Luck. Take care of yourself?" Amsa mata tayi tana sake mata peak a hannun ta kana ta tashi ta fice While Hajiya ta raka ta da kallo. Sama ta nufa sabida su gaisa da Uncle Hashim. Kafin ta sauko ne Idris ya shigo gidan, yana zaune a Parlour suna surutu da Zabba'u ta sauko ƙasa Shima yana ganin ta ya miƙe yana murza idanu, sai ya ɗan soma ɗaga kai Like yana leƙen bayan ta Ita kuma tsayawa tayi tana kallon sa da mamaki, sai tace, "what you look?" Waro ido yayi da cewa, "wai You mean like you? A mean MEEMA?" Murmushi tayi coz ta gane tsokanar sa ne ta motsa Itama Zabba'u da ke jin su dariya tayi tace, "Today you see her has changed a lot, she has joined us Hausa, she is very beautiful." Tafa hannayen sa yayi yana matsowa kusa da ita, fuskar sa cike da fara'a yace, "wow my cuty friend! I never thought you were so beautiful until today, have you seen? You've done very very well, You look so cute." Ya ƙare maganar da ɗaura hannun sa a baki ya huro mata kiss 😘 Sosai take dariya a lokacin nan wanda hakan ya bai wa dimples ɗin ta damar fito wa sosai "I've never seen you laugh beauty. Laughter is so good for you. Please do it ok?" Yafaɗa still yana kallon ta yana murmushi Bata ce komi ba illa sake ƙawata fuskar ta da smile da tayi Shi kuma juyawa yayi ga Zabba'u yace, "to ranki ya daɗe! Yau dai bazan ci abincin ki ba sauri muke yi, idan Hajiya ta fito kice ina gaishe ta mu mun tafi." Tana dariya tace, "kace yau abinci na ya huta da tsegumi? yau babu sharhi. To a dawo lafiya Allah ya tsare." "Ai kar ki damu yau zan ci na rana a nan don haka ki girka da Ni, ki gode wa Allah ma yau ina sauri but anjima dai zamu haɗe ɗin." Yafaɗa yana yin gaba ya bi MEEMA wacce har ta fice ma. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️ Gaba ɗaya yau tunda Luwaira ta tashi babu walwala a tattare da ita, idanunta duk sun kaɗa sun yi jawur sabida kukan da ta sha a daren jiya, ga rashin barci da bata samu tayi ba. Shirin ta na school tayi saboda tana son ta je ta rubuta test, ba don haka ba ba ta tunanin zata iya zuwa ko ina a halin da take jin kanta. Koda ta fita Parlour ɗakin Momy ta shiga, ta sanar mata, "zata wuce school". Kallon ta Momy tayi tace, "ba dai kuka kika yi ba Luwaira?" Shiru tayi tana ɗauke kanta gefe Tsira mata idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta kaɗa kai da cewa, "kin yi Breakfast ne da zaki tafi?" "Ba na jin yunwa Momy." Sai ta juya ta fice bata jira cewar ta ba Ita kuma Momy ta raka ta da kallo har ta fice. A yanda take jin baƙin ciki a zuciyar ta da zata iya cire soyayyar Umar Faruk a zuciyar ƴar ta da tuni ta cire, sosai take baƙin ciki da hakan sai dai babu yanda zata yi, tabbas koda ta saka auren su ya yiwu ba ta jin zata kasa cika burin ta a kansa, dole ne sai ta mallaki komi nashi kafin hankalin ta zai kwanta, dukiyan sa da ƙadarorin sa duk mallakin su ne, ta san ita kanta Luwaira baza ta gane abinda take guje mata ba sai nan gaba. Amma kuma yanzu ta yanke shawaran barin ta ta auri Umar Faruk domin hakan shi ne maslaha a wajen su a kan ya auro wata ya kawo ta cikin gidan nan, inyaso daga baya bayan Luwaira ta haihu da shi sai su kashe shi su mallake komi ya dawo hannun su, a lokacin kuma zata san duk hanyar da zata bi domin fahimtar da Luwaira sannan ta mantar da ita shi a gaba ɗaya rayuwar ta, a lokacin zata auri wanda ya fi shi ta sake sabuwar rayuwa, su kuma burin su ya cika. Numfashi ta ja tana yalwata fuskarta da murmushi, tabbas ta san Umar Faruk yana jin maganar ta idan har ta ba shi umarnin auren Luwaira zai amince, amma ta ina zata bi ta fahimtar da shi ba tare da ya ɗarsa wani abu a cikin zuciyar sa ba? ******** Tana fita mota ta shiga drever ya ja ta zuwa school ɗin su. Koda ta shiga aji ta tarar da Abida tana zaune, sai dai kasancewar tayi latti a lokacin Malamin su ya shigo shiyasa basu yi wani magana ba suka natsu suka mayar da hankalin su kan karatun. Bayan ya fita ne wani ya shigo daga nan ne suka sami break Abida wacce ta lura da yanayin Luwairan ita ta soma mata magana da tambayar abinda ke damun ta ganin halin da take ciki Sai kawai Luwaira ta fashe mata da kuka saboda tsananin ƙuncin da ke damun ta Da sauri ita kuma ta sanya hannu ta kama ta tana faɗin, "Haba Luwaira zaki tara mana mutane ne? Me ke damun ki meye ya saka ki kuka? Please kiyi shiru haka nan ki sanar min." Daƙyar ta iya tsakaita wa da kukan duk da bata yi shiru duka ba, daƙyar ta buɗe baki take sanar mata da zancen auren Umar Faruk, kana ta ƙara da cewa, "ban san ya zan yi ba Abida, ban san ya zan yi ba muddin ya ƙara aure, wlh ji nake yi kamar zan kashe kai na tsaban ƙunan da nake ji a raina, ina matuƙar ƙaunar sa amma be san ina yi ba, ya zan yi ne?" Tausayin ta ne sosai ya kama Abida, tabbas so da zafi musamman idan kana yin shi a inda ba'a san ma kana yi ba, hakan ya fi komi ɗaci da tada hankali. Rarrashinta ta soma yi kafin tace, "Ni a nawa shawaran Luwaira ki fito fili ki sanar mishi kina ƙaunar shi, that is the only solution. Idan kika bar abun a ranki be san ma kina yi ba, idan da tun farko kin sanar mishi maybe da tuni be ga wancan ya ce yana so ba, kina fa da duk abinda ɗa namiji zai so ki, Ni a tsari na ba na barin abu ya cutar da Ni don haka dole ke ma ki samu hanya mafi sauƙi ki sanar mishi, sai ki ga me zai ce, idan ya amshi soyayyar ki Fine, Idan kuma be amsa ba dole mu san abin yi, ko ta wani hanya ne zamu bi domin ki samu zuciyar shi, ke ƙawata ce Luwaira zan taimaka miki a duk sanda kike neman taimako, ai yanzu kai ya waye sai mutum ya so yake barin damuwa ta karshi." Kallon ta Luwaira tayi yayinda idanun ta suke ci gaba da zubar da hawaye tace, "Abida wlh hanya ɗaya ce na san zan samu Umar Faruk cikin sauƙi, muddin Momy ta amince da auren mu na san shima zai amince ko ba ya so na, but She is still silent and refuses to tell me anything and yesterday she told me we would talk." "To meyasa baza ki same ta kuyi maganar ba? Inaga idan kun zauna kika sanar mata da halin da kike ciki zata fahimce ki, Ni abun yana ɗaure min kai meyasa ba ta son ki da shi ne?" "Uhmm baza ki gane bane Abida." Sai kuma tayi shiru tana ɗaura kanta a kan deks Itama Abidan shiru tayi tana kallon ta, sai kuma tace, "idan har baza ki iya zuwa wajen ta kuyi magana ba ni zan je, Let's go together sai in faɗa mata halin da kike ciki." Ɗago kai Luwaira tayi ta kalle ta, ba dai tace komi ba illa ɗauke kai da tayi tana saka hannu ta soma share hawayen ta Sai Abidan ta dafa ta tace, "don Allah ki kwantar da hankalin ki, ki bi shawara nan yau ɗin nan ba sai gobe ba ki same shi ki sanar mishi, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa kina jina?" "Abida faɗan ba sauƙi ne da shi ba, da ace zan iya tunkaran shi da wannan kalman ai da tuni na daɗe da furta mishi, Umar Faruk ya wuce yanda kike zato, yana da wani irin kwarjini da kamalan da bazan iya tunkaran shi da zancen nan ba, sannan a yanda ya ɗauke Ni yana matuƙar girmama Ni a matsayin ƙanwar sa hakan ke saka wa nake kasa yin komi." "Haka nan zaki daure ƙawata". Abida tafaɗa tana sake dafa ta, "na tabbata zaki iya, idan ba haka ba wankin hula ne zai kai ki ga dare, shawaran da zan baki kina da Numban shi ki tura mishi a text message, na tabbata zai fahimce ki idan har yana ƙaunar ki, do that please." Shiru tayi Luwairan tana kallon ta, sai kuma ta gyaɗa kanta tace, "insha Allahu I will try my best. Zan tura mishi zuwa anjima, amma kina ganin zai amince bayan ya sami wacce zai aura?" Murmushi Abida tayi tace, "ba na tunanin zai ƙi amince wa sabida dole zai fahimci a halin da kike ciki, idan har bazai fasa wancan auren ba sai dai ya haɗa ku duka amma ba na tunanin zai ƙi amince miki, ko don halaccin da Momy tayi masa, ko domin kunyan ta bazai ƙi son ɗiyar ta ba." Daga haka shawara Abidan ta ci gaba da bata. Har sanda lecturer ya shigo sannan suka dakata suna gyara zaman su tare da ba shi attention ɗin su. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️ Dariya sosai Laɗifa take sha saboda yanda MEEMA ta dage wajen furta yaren Hausa, tana koya mata ne amma duk kalma ɗaya idan ta faɗa sai ta tuntsire mata da dariya har da riƙe ciki Tun MEEMAN ba ta kula ta itama tana tayata dariyan har dai ta gaji ta koma hararan ta, ganin ta ƙi denawa sai ta ɓata fuska kamar zata yi kuka tace, "Since you're laughing at me I've stopped learning." Cikin dariyan Laɗifa tace, "I'm so sorry my dear. Wlh dariyan ne refused to stop, but..." Sai ta kama bakin ta sabida wani sabon dariyan da ya taho mata, daƙyar ta riƙe shi tana murmusawa tace, "But I'm sorry again." Still fuskarta a turɓune ta balla mata harara tana cewa, "I will not ask you to teach me again since you will laugh at me. I will go to Idris and he will teach me." Laɗifa bata kai ga yin magana ba wani saurayi yayi Nocking Yana turo ƙofan. Shima ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ne And they all followed him, watching him He smiled and said, "Hi how far?" Laɗifa ta amsa mishi tana cewa, "Brother Idris ya turo ka waje na? I have not finished but I will finish now." "Eh shi ya turo Ni, amma duk da haka there are strangers who come to MEEMA." Ya ƙare maganar da kallon MEEMAN wacce ta mayar da hankalin ta kan computer tana latsawa Hakan yasa ta ɗago kai tana kallon sa sai dai bata furta komi ba Laɗifa tace, "And strangers? Who are they?" "I don't know wlh, they were outside in the car, they demanded that I call MEEMA saying they would miss a message being sent." "Ok to zata zo". Daga haka shi kuma ya fice Sai Laɗifan ta kalli MEEMA wacce itama ta zuba mata ido tace, "Is there anyone you expect to come to you?" Girgiza kanta tayi sai kuma tace, "No, no one." "Ok get up let's go check." Tashi tayi suka fice tare. Suna fita bakin Gate ɗin suka hangi baƙar mota ƙirar jip a fake, kasancewar glasses ɗin tited ne ba a ganin kowa daga ciki. Kai tsaye wajen motan suka nufa Sun kusa isa sai wayan Laɗifa tayi Ring, tsayawa tayi a wajen tana peaking call ɗin Hakan ya bai wa MEEMA damar karisa wa wajen motan tana bin ta da kallo Sai kawai aka zuge ƙofa wani mutum ya fito da sauri, kafin ƙiftawar minti ɗaya har ya tura MEEMA a cikin motan ya rufe an ja motan a tsiyace Laɗifa wacce take waya a kan idanun ta komi ya faru, sai dai kasancewar ta shiga shock ko motsi ta kasa sai da suka tafi ne sai ta kwatsa ihu tana bin Bayan motan, tuni ta jefar da wayan hannun ta sai zuba ihu take yi, ganin sun yi mata nisa da gaske ai sai ta zube a wurin tana ɗaura hannaye a kai tana ihun kiran sunan MEEMA Kankace kobo har tsirarun mutanen da ke wajen sun nufo inda take don a zaton su wani abun ne ya same ta, kasancewar basu san me ta biyo ba shiyasa suke tambayar ta ba'asi? Hannu kawai take nuna wa ta inda motan ta bi bakin ta na rawa tana kiran sunan MEEMA but sai dai gaba ɗaya muryan ta ba ya fita sabida tsaban ruɗu da tashin hankali. [14/10, 10:07 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎 *MEEMA FAROUK*                      💎💎💎 *NA_NAFISA ISMA'IL* *WATTPAD_UMMUDAHIRAH* *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                    *P.W.A✍️*                *SADAUKARWA* _Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._ *SAKAMAKON SALLAH 1* _Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas'ud ya ce, "Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?" Sai Annabi ya ce, "sallah". Na sake cewa, "daga ita fa?" Sai Annabi ya ce, "kyautata wa iyaye". Na sake cewa, "daga wannan fa?" Sai ya ce, "sai jihadi."_ _Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, "in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace," Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba'iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba'ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._ _Abu Sa'id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, "ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: "ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta." Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._ _Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._ _Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa'danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._ _Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha'i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha'in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha'i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, "ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku." Allah yasa mu dace duniya lahira._                       *NO_30*              *IN TWO HOURS*                Idan ka shiga gidan Hajiya tamkar an yi mutuwa saboda tsaban tashin hankalin da suke ciki. Tunda labarin ɗauke MEEMA ya iso gare su suka shiga tashin hankali, masu kuka nayi masu salati nayi, Ummee har wannan lokacin ta kasa yin shiru sai kuka take yi saboda ta fi su shiga tashin hankali gaba ɗayan su. A yanzun ma suna zaune gaba ɗaya a Parlour sun Yi cirko-cirko suna jiran dawowar Uncle Hashim Wanda ya fita tun ɗazu shi da Idris da masu aikin gidan sun tafi kai rahoto wajen ƴan sanda A lokacin ne motocin Umar Faruk suka shigo gidan kusan su huɗu, da shi da Momy tare da Abdul suka taho. Bayan an buɗe musu kofofin motan suka fito gaba ɗayan su Bazan iya misalta muku a halin da Umar Faruk yake ciki ba, duk da yana iya ƙoƙarin sa wajen ɓoye tashin hankalin sa da halin da yake ciki but kyakykyawar fuskar sa sai da ya bayyana damuwar da yake ciki Haka ma Abdul domin shima zan iya ce muku ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tashin hankali da jin an rasa Masoyiyar sa, sosai yake jin ƙaunar ta a zuciyar sa wanda gaba ɗaya ta mamaye masa zuciya ta hana sa saƙat, duk da har yanzu be taɓa tunkarar ta da zancen soyayyar sa ba, kuma tun ganin ta sau ɗaya be sake ba bare ya bayyana mata halin da yake ciki a ƙaunar ta, babu abun da ya fi ɗaga masa hankali jin cewa Umar Faruk zai aure ta, shiyasa gaba ɗaya a kwana ɗayan nan yake cikin tashin hankali, sai ga shi kuma abun ya daɗu saboda ɓacewar ta Momy kuwa babu wanda ya fi ta shiga farin ciki da jin wannan labarin, sai dai ko kaɗan bata nuna a fuska ba sai alhini da tashin hankali da ya bayyana a fuskar ta, wanda har ƙwalla sai da ta fitar a gaban Umar Faruk a sanda ya je musu da zancen. Ita da Luwaira tamkar zasu zuba ruwa a ƙasa su sha tsaban farin ciki Yanzun ma da suka shiga ciki. Umar Farouk shi be iya zama ba tunda ya gaishe su yayi musu jaje ya tambayi Uncle Hashim? Shi ne Jalila ta sanar mishi a halin da ake ciki Hakan yasa ya fice ya koma haraban gidan yana riƙe da wayan sa a hannu yana laluba Numban Uncle Hashim ɗin don jin inda yake ya biyo bayan sa Sai yace mishi, "ga shi nan ma a hanya suna dawo wa." Hakan yasa ya dakata daga bakin motan sa ya harɗe hannayen sa a ƙirji yayi shiru, idanun sa har kaɗa wa suka yi saboda tsaban tunani, abin da kawai ya zo masa a zuciya kidnapper ne suka sace ta, kuma zai iya kashe ko nawa ne koda dukiyar shi zai ƙare domin a amso ta, yana matuƙar ƙaunar ta sosai a ransa. Soyayyarta ta rigada ta kama mishi zuciya wanda yana jin bazai iya koda kwana ɗaya ne be sake sanya ta a idanu ba Abdul shima fitowan yayi ya zo ya tsaya a wajen sa fuskar sa duk a dame duk da babu wanda ya san a kan me ya shiga tashin hankali haka Ita kanta Momy sosai take mamakin yanda ya nuna damuwarsa har ya buƙaci zai biyo su.                 Sanda su Uncle Hashim suka dawo gidan a lokacin ne Umman Laɗifa da ita Laɗifan suka zo gidan su ma, sai da suka gaisa kafin suka shige ciki Uncle Hashim da Umar Faruk suna tsaye bakin motan shi suna zantawa, inda Uncle Hashim ɗin yake faɗa mishi a halin da ake ciki yanzu Jan numfashi yayi shi kuma yana kallon sa da cewa, "I think it was the kidnappers who took her. Abin da nake tunani kenan." "Nima haka nake tunani, duk yanda aka yi su ne suka ɗauke ta, sai dai mu jira har sanda zasu kira mu tunda abun ya faskara, Numban ta ba ta shiga har yanzu da alamu sun salwantar da wayan nata ne." Uncle Hashim Yafaɗa fuska babu fara'a zuciyar sa na suya Dafa kafaɗan sa yayi yana kallon sa yace, "haka ne. But we must do our best to answer her, bazai yiwu mu bar ta a can ba, bamu san me zai same ta ba".                  Har aka kira sallan magriba Umar Faruk suna tare da Uncle Hashim Momy da Abdul tuni sun koma gida tunda suka yi musu jaje Har zuwa dare babu labari daga wajen ƴan sanda duk da kuwa suna iya bakin kokarin su wajen sun ga sun nemo ta, bare akwai hannun manya musamman da suka ga Umar Faruk ya sake zuwa da kansa, haka sukai ta zirya babu inda basu duba ba har a gidan talabijin ɗin da take aiki an yi sanarwa duk da ba'a saka hoton ta ba, haka ma gidan rediyo duk an kai rahoto Yanzu kawai jira suke yi su ji an kira su an buƙaci kuɗi tunda sun bar zancen a kan duk yanda aka yi ƴan kidnapped ne suka ɗauke ta. ✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️                 Idanuwan ta ne suke buɗe wa suke rufe wa, dishi-dishi sosai take gani wanda hakan yasa ta ɗau lokaci tana rufe idanun ta mayar da su har sanda ta buɗe su tarwai tana kallon cilling ɗin ɗakin. Yanda komi ke juya mata ne ta kasa gane a inda take yanzu ɗin, a hankali komi ya soma dawo mata daga sanda suka fito ita da Laɗifa har sanda wani Mutum ya tura ta a cikin mota, sai kuma sanda ta ji numfashin ta ya ɗauke sakamakon toshe mata hanci da aka yi da handkerchief. Daga nan ne bata sake sanin me ke wakana a duniyar ba sai yanzu da ta farka ta tsinci kanta a wannan ɗakin. Zumbur ta tashi zaune tana ƙara ware manyan idanuwan ta da suka sake shanyewa suna buɗe wa daƙyar a cikin ɗakin da babu komi sai katifan da take kwance a kai, sosai take bin ko ina da kallo tana son ganin ta farka a wannan mummunan mafarkin da take hasashen tabbas mafarki ne, tabbas ba da gaske ne ba. Sai da ta fi mintuna goma a haka tana ƙare wa ɗakin kallo da son ganin ta farka, sai zare idanun ta take yi ko ta ina, sai kuma daga baya ta saka hannu ta soma mitstsike su domin ta kasa yarda har yanzu ɗin ba mafarki bane. Ta shafe fiye da mintuna talatin a wurin bata gasgata kanta ba, sai kuma daga baya da ta gane tabbas gaske ne ba mafarki ba, sace ta aka yi sannan aka kawo ta nan inda babu kowa aka ajiye ta. Sai kawai ta fashe da kuka a lokaci ɗaya tana tashi tsaye da mugun sauri, tsaban tashin hankali jikin ta har rawa yake yi domin ƙafafuwan ta ma sun kasa riƙe ta, inda ta ga ƙofa ta nufa da gudun gaske zuciyar ta na wani irin bugawa tamkar zata tsago ƙirjinta ta fito, fatan ta kawai idan ta taɓa ƙofan ta ganta a waje a bainar jama'a. Tana taɓa ƙofan ya buɗe sai dai ganin ta tayi a wani babban parlour da shima babu komi a ciki sai wani ƙofa da ya kasance kichen ne. Tsoro ne ya sake tabaibaye mata zuciya while idanuwan ta suna tsiyayar da hawaye domin a lokacin kukan nata ya tsaya cak sai hawayen da ke zuba tsaban kiɗima. Da gudu ta isa ɗaya ƙofan da ta tabbatar daga shi sai waje ta fincika da ƙarfi domin ganin ta buɗe, sai dai a rufe ruf ko motsi ba ya yi. Wani irin jijjiga ƙofan ta soma yi a lokaci ɗaya tana sakin wani irin ihu me uban ƙara, sosai ta ɓare bakin ta tana kuka da neman ceto da amon muryan ta da be fita sosai tsaban tashin hankalin da take ciki. Duk yanda ta so ta buɗe ƙofan ta fice ta kasa sai kuka take yi tana neman ceto. Daga ƙarshe kuma sai ta koma bin parlour'n da kallo tana tunanin har yanzu mafarki ne, tabbas zata farka, taya za'a ce ita ce a nan? Ita ce aka kama? To a kan me? Sai kuma ta koma bin ɗayar ƙofan da ta gani ta murɗa ta shige, kichen ne da windown sa a can sama wanda ko tayi ƙoƙarin ficewa ta nan babu hali. Dole ta sake koma wa inda ta fito a cikin ɗakin da ta ganta, can ma windown a sama yake, tana kallo sai ta zame a ƙasa ta kurma ihu tana kiran sunan Uncle Hashim, Hajiya, Ummee.. babu wanda bata kira ba a wanda ta sani but babu wanda ke jin ta. Sai ta faɗa kan katifan ta dinga rera kuka, tun tana yi da ƙarfin ta har ta gaji ta koma zubar da hawaye kaɗai, ta sadakar sace ta aka yi, amma su wane ne? Me tayi musu?. Tsawon lokaci tana a yanda take babu wanda ya zo wajen ta, har duhun magriba ya soma gabato wa yayinda ɗakin ya soma duhu. A lokacin ne ta ji kamar an buɗe Gate an shigo da mota. Sai ta tashi a firgice tana fice wa tayi ƙofan parlour. Jira kawai take yi ta ga wanda zai shigo da readyn da zaran ya shigo ta samu hanyar tsere wa. Wuri-wuri tayi tana neman inda zata samu abun bugu, sai dai a kaf gidan bayan ita babu komi a ciki, da alamu gidan sabo ne domin ko penti babu a cikin gidan. Jin an fara taɓa ƙofan sai gaban ta ya sake tsananta da wani irin bugawa saboda bata san wa zata gani ba, da sauri tayi bayan ƙofan da zaran an buɗe ƙofan hakan zai saka me shigowar bazai ganta ba, idanuwan ta sai tsiyayar da hawaye suke yi sun kasa tsayawa. Shiru taji an dakata ba'a buɗe ba, a hankali take jiyo murya ƙasa-ƙasa domin da alamu kamar mutane biyu ne a wajen, lumshe idanun ta tayi tana ɗaura hannun ta ɗaya a ƙirji saboda wani irin kyarma da jikin ta yake yi ga zuciyar ta da ke ƙara hauhawa tsaban buga wa, komi nata rawa yake yi sosai har hannayen ta, daƙyar take iya riƙe kanta a wurin domin ƙiris take jira ta faɗi ƙasa, tsoro da fargaba sun hana ta tsayawa ƙyam, sai ta sake manne wa a jikin bango saboda jin an sake taɓa ƙofan tare da murɗa wa za'a shigo. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels