An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 03/12/2021, 08:04 - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy 1 _©®Hakkin mallaka nawa ne ni kadai, ban yadda a saffaramin labari ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba a kiyaye⚠_ *FICTION.* FREE PAGE. FALMATA POV. Yola... Tun tana surfen da kuzari har ta kai bata iya daga tabaryar da karfi, babu komai a tare da ita sai tarin yunwa da gajiya ga wani uban ciwon kai da ya saka ta gaba. Cike da dauriya ta karasa surfen sannan ta risina tana kwashewa tana zubawa a kwayar da ke gefen turmen, sai da ta kwashe shi tas sannan ta hade da sauran da ta surfe, mikewa tai tsaye tana rike da surfen ta nufi gurin tukuyar ruwansu. "To mai kunne kashi ban fada miki idan kika yi surfenki ki rika zuwa bohal kina debo ruwanki ba? Ke wai Fulani sau nawa za ayi miki magana ne?" A wahale Falmata ta kalli Tumba wacce ke mata maganar, ta amsa mata tana jin kamar ta fadi a tsakar ranar da ke dukan kanta. "Inna idan na gama zan je na debo wasu sai na cika" "Ban yarda ba, kije ki fara debowa ki yi abunda za ki yi wannan wanda kike debo mana na aiki ne bana wankewa wasu banza surfe ba" Uffan bata sake ce mata ba, sai ta nufi gindin bishiyar dogon yaro ta aje surfen, sannan ta sake komawa ta dauko wani katon bokoti ta riko shi a hannu ta nufi kofar fita jiki ba gwari, tafiya take a hankali kanta a kasa bata kallon kowa sai hanya, gaisuwar girmama ce abunda yake fitowa daga bakinta sa'adda duk tai arba da sa'ar iyayenta. A yayinda ta isa bohal din sai ta nemi guri ta tsaya tana ta kallon yadda fanfon bohal din yake cike da mutane yara da manya. Matsawa ta kara can gefe tana daga zanenta kamar mai kyankyamin ruwan da ke zube a kasa. Kallo daya za ka yi mata ka karancin irin natsuwa da tarbiyar dake tare da ita, sa'aninta na gaban fonfon suna gogoriyon dibar ruwa ita kuma tana tsaye gefe abunta tana kallonsu kamar ba diban ruwan ta zo yi ba. "Falmata kawo na baki bokiti daya" Cewar Khadija kawarta, abun ka da mai nema sai tai saurin cira kafa ta isa gurin da Khadija take tsaye rike da kan fonfon ta mika mata bokitinta. "Na gode kawata" "Karki damu, indai akwai mu ba kya rasa komai kawata" Khadija ta fada tana daga mata gira, murmushi ne ya fadada kansa a fuskar Falmata ya bayyana fararen hakoranta wanda ya karawa bakar fatarta sheki. "Yau ba za ki je gidan Sarki ba? Kin san fa ke ce mai gyara dakin yan uku da kula da su" Khadija ta tambaya tana daga muryar wai dan mutane da ke gurin su san kawarta na aiki a gidan Sarki. Wata irin kunya ce ta rufe Falmata abun ka da bakauyen mutum sai duk ta ji ta muzanta. "Ke Madam ba za ki ba yau?" "Na tafi, har na dawo sai kuma gobe" Ta amsa mata kamar ana matso maganar daga bakinta, gaba daya kunya ta gama rufe ta, kamin bokitin ruwan ya cika duk ta tsawwala, bokitin na cika Khadija ta kama mata ta dora a kai sannan ita ma ta dora nata suka kamo hanya tare. "Mtswwwww Wallahi Falmata ba ki hadu ba, wai ina son ayi kurin nan ke kuma kin wani noke ba ki ma son amsawa" Abun nan dai da ya zame mata al'ada ta yabawa fuskarta, wato murmushi sannan ta soma magana da muryarta mai taushi da dadin sauraro. "Khadija kunya na ke ji" Wani banzan kallo Khadija tai mata. "Kunyar me? Aikin a gidan sarki? Allah ya kai Khadija Wallahi har tafiya sai na sauya" Wannan karon dariyar marar sauti Falmata tai, tana jinjina lamarin kawarta, daman can indai kaudi ne da iyayi da ba ni na iya ba dai Khadija ba. "To ai na ga ni ban wani dade da fara aikin ba, da har za a ce na fara kuri wannan zuwan da nai dazun fa shi ne zuwana na uku, kuma ni na ga..... " Sai kuma yai shiru bata karasa ba, sai dai karara yanayinta ya nuna akwai damuwa a tare da ita kamar yadda fuskarta ta nuna akwai tarin maganganu a kasan halshenta. "Miya faru?" Tsayawa tai tana kallon Khadija kamar yadda Khadijar ma ta tsaya tana kallonta. "Sai na ke ganin kamar ba su yarda da ni ba...." Fuskar Mamaki Khadija tai. "Ban gane ba?" "Kin ga tun da aka dauke ni aikin, har yanzu ban ga yaran ba, sai dai na gyara dakinsu, kuma idan zan gyara sai a saka dogari ko wata baiwa sun tsayaa dakin har nai na gama" "Suna da wulakanci ne?" "Aa har yanzu ba a taba min ba, ban ga alamun hakan a iyalan gidanba, sai dai da alama suna da wuyar aminta da mutum" Hannu daya Khadija ta saka ta daga kafadarta. "Karki damu, daman su yan sarauta basa saurin aminta da mutun, amman dai da sannu za su fahimci kawata mutuniyar kirkice su aminta da ita" Ta karasa tana dariya tare da rika fuskarta. "To Allah yasa" "Amin, kuma bari na fada miki ba wai saboda wannan bakar Tumba ta tura ki aiki dan ki samo mata kudi ba, ba wai duk abunda aka ba ki za ki bata ba, albashin ma rabi za ki bata ki boye rabi, dan alherin idan kin samo karki kuskura ki bari ta gani, ke abinci wannan ma da ki kawo mata Wallahi kara ki ɓarar dashi a akwata" Har wani yatsine fuska Khadija take tana jin kamar ace ita ce a matakin Falmata take da step mother kamar Tumba da Allah kadai ya san irin sherin da zata kulla mata. "Mahaifina yace idan ban mata biyayah ba be yafe min ba, ko da ace bata san yawan kudin aikin ba zan bata dika balle kuma ta riga ta sani, idan ma na hana ta zata iya duka ko taja Baba da kansa ya doke ni, ba ni da wani yanci a gidan nan Khadija kin sani" "Hmm ai har da ke Wallahi da kike biye mata, ke ko yar ketar nan ba ki iya ba, Wallahi da ni ce da sai ta sha wuya, shiyasa na tsani shegiyar matar nan bakar Tumba kawai" Falmata da dai bata ce mata komai ba, ta cigaba da tafiyarta, sanin kanta ne idan zata ce Khadija ta daina kiran Step mom dinta gatsasa sau hansin sai Khadija ta aikata sau dari biyu. "Ki duba ki ga fa saboda ki Wahala ta tura ki aiki a gidan, ga yayanta, muna wai dan tsabar zalinci tace ita zata karbe albashin, bayan babu abunda take tsinana miki" Tafiya suke Khadija na jifar Tumba da kalamai marasa dadi, Falmata dai bata ce mata uffan ba har suka raba hanya, kowa ya dauki hanyar gidansu. Da sallama ta shigo cikin gidan amman aka rasa mai amsa mata kamar masu gaba da ita ko kuma wadanda ba su ji sallamar ba. Ko kadan hakan be dame ta ba, inda da sabo kusan ta saba da wannan rayuwar. Kallo daya tai ma Naja ta dauke kai ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi, yar gata kenan masu yin yadda suke so a gida ba kamar ita ba, wacce aka hana wanke surfen da ruwan da ita da kanta tai aikin jigilar debo su da safe, an bar yar gaban goshi tana wanki da su. Sai da ta sauke ruwan sannan ta nufi gurin da surfen yake ta dauko ta wanke, ragowar ruwan ta juye a karamin bokiti ta shiga bandaki tai wanka, dakinsu ta nufa ta shafa mai abun ka da mai son kwaliya sai ta dauko ragaggin kayan kwaliyarta ta tai kwaliya har da su jan baki. Ta yi kyau sosai duk kuwa da kasancewar ta baka sai dai bakin be rage ta da komai ba daga kyaun sura kwarjini ta halitta da kuma cikar sura da zati irin na ya mace. Baka ce amman ba mummuna ba, baka ce kyakkyawa irin kyau ne mai shining. Bakinta mai kyau ne wanda ya kara fito da manyan idonta kuma farare tas, sai dai bayan ido da hakora da tafin hannunta da na kafa babu sauran wani gurin da fari ya bayyana a jikinta. Yana daya daga cikin dalilin da ya saka Falmata bata sha'awar saka bakin kaya, domin ganin take ita da tufafin za su saje ne. Bayan ta gama shiryawa ta mike tsaye tana cigaba da kallon kanta a madubi kamin ta maida dan karamin madubin a mazauninsa da ke cikin kayan kwaliyarta. Tsakar gidan ta fito ta nufi kitchen dinsu ta dauko abinci da ke rufe a langa (Kwano) ta zauna jikin kitchen din ta soma ci tana ta kallon awakin gidan da ke ta aikin kuka suna fada da junansu, sun ɓata turkensu sun masa kacha-kacha kamar ba dazun ta gama gyara shi ba. Can kuma ta maida dubanta gurin mayan shanun da ke daure guda biyu a gafen garken awakin. "Idan kin gama ki taso ga surfen masarar nan ki surfa ko tiya daya ne" Kam ta gama cin abinci Tumba tai mata furucin, a take yanayinta ya canja tai narai narai da fuska kamar ta fasa kuka. "Inna ba kin ce sai gobe ba" "To masu masarar yau suke son abunsu, kuma da safe ai sai dabobi su samu abunda za su ci" Kalma daya idan ta kara fitowa daga bakinta ta san ba tasha ji da dadi daga bakin Tumba. Bata da wani zabi da ya wuce ta gama cin abinci ta taje tai surfen kamar yadda ta umarce ta. A hankali tai ta cin tuwon marar har ta gama ta tashi ta nufi gurin butarda ke gindin ice ta wanke hannunta sannan ta nufi gurin da masarar take ta dauka ta bude turmi ta fara surfawa. Tsakanin fara surfen da sallamar Maman Baby makociyarsu ba zaka iya tantance wanda ya riga wani ba. Tumba da ke tsakar gidan ta amsa sallamar tare da kallon Falmata da sauri. "Kina da son wahalar da kai Fulani, ina ke ina surfe da tsakar ranar nan? Dan Allah ki aje har zuwa anjima ko kuma idan Naja ta gama wanki sai ta surfa" Kallonta kawai Falmata tai ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfen. "Aa zan iya" Sai kuma ta fada kasa-kasa idanuwanta na cika da kwalla, haka take mata a duk lokacin da wani a shigo gidan ko kuma idan a gaban mahaifinta ne. Kowa a unguwar ya shaidi Tumba akan kaunar da take nunawa Falmata agaban idanuwansu, wani lokacin har da ita ake bada kwacen matar uba wacce ta rike yar kishiya da amana. "Oh Tumba ikon Allah, ke dai ba ki kaunar ganin Falmata tana aiki" Cewar Maman Baby tana dariya. "Mahaifiyarta amana ta bar min ita, idan ina ganin tana wata wahalar sai na rika ganin kamar na ci amanar mahaifiyarta" Daga inda Falmata take tsaye tana surfen ta dago manyan idanuwanta masu kamar madara ta kalli Tumba wacce ta shantake da makociyarta suna fira ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfe idonta tab da kwalla...! FADIME POV. Katsina State... Shanun na gaba ita kuma tana biye da su a baya tare da karenta, hannunta rike da yar karamar sandarta ta dukan shanun, tana sanye da tufafin riga da zane na fulani gashin kanta a cinkushe. Sosai hankalinta yake akan ko wace shanuwa da ke gabanta, zuciyarta cike da fargaba da zullumi irin wanda ya saba ziyartar a duk sa'in da ta fita da shanun. Ba ta natsu ba har sai da ta isa da shanun a gurin da ta saba tsayawa da su, sannan ta nemi guri ta zauna saman wani karamin dutse ta zuba musu ido. Haka take wuni a cikin tashin hankali da fargaba a duk lokacin da mahaifinta ya tura kiwo, ba tsoron kiwon take ba, ba dan bata saba ba, sai dan fargabar abunda zai samu shanu a duk lokacin da ta fita da su. Ba kasafai take zuwa kiwo ta dawo da shanun lafiya ba, wani lokacin a hanyar tafiya wata zata mutu, wani a hanyar dawowa wani sa'in ma har sai ta iso gida. Tun shanun suna arba'in da uku har sun dawo sauran goma sha bakwai.    Mikewa tai tsaye tana kallon wata bakar mage mai jajayen indanuwa, wacce ke tsaye saman dutsen da ke gabanta, ba yau ta saba ganin magen ba, kusan kullum idan ta fita kiwo sai ta ganta, tun tana tsorota har ta daina, sai dai su yi ta kallon kallo ita da magen, sai dai a duk lokacin da tai arba da magen sai tsigar jikinta ta tashi, tsakanin ita da magen aka raba mai daukewa wani ido, ba m kamar magen da ke kyakar hakora.   Can dai Fadime ta nemi guri ta zauna ta dauke kanta daga kallon magane da take, ta maida hankalinta gurin shanunta. WASIN RAU POV. As usual, yau ma sai da hasken rana ya fara haska kyakkyawar fuskarsa sannan ya bude idonshi a hankali yana kallon birds din dake saman icen suna rera masa waka kamar yadda suka saba a ko wace safiya. Lumshe ido yayi sai kuma murmushi ya biyo baya mafarkin da yai yake kokarin tunawa, jinke hannunsa yai gam yana maida numfashi a hankali tare da dantse hakoransa. Kamar an tsikareshi sai kuma yai saurin bude idon yai hanzarin saukowa daga kan icen ya doro kasa, jikinsa ya girgiza har sai da kowace gaɓa ta jikinsa ta motsa. Babu riga a jikinsa sai dai hakan be hana shi jin zafi ba, duk kuwa da irin tsananin sanyin da ake kasancewar yanayin safiyar yau a akwai hadari da ya karade ko'ina a sararin samaniya. For the first time a yau yaji a kasa yake sha'awar yin busar sarewa abunda be taba ba, a kowace safiya a saman dutse yake yin busarsa mai dadi saurare da kawarda duk wata damuwa. Jingina yai jikin icen ya ciro sarewarsa ya kafa bakinsa ya soma busar cikin kwarewa da shauki, a take duk dajin ya dauka, yanayin haduwar hadarin da kuma busar sarewar, da iskar da ke kadawa sai ya bada wani kalar yanayi na musamman wanda ko wace irin halitta zata so kasancewa a ciki. Sai da yai busar ya gama sannan ya kai hannunsa a gefen walkin da ke jikinsa ya kwance wata yar karamar jakar tsaba ya bude bakinta ya zubo hatsin da ke cikin jakar a hannunsa ya watsawa tsuntsaye a kasa, a take suka sauko kasa suka baibaye gurin suna ta cin tsabar har wasu na hawa kan wasu, kallomsu yake suna cin abinci har sai da idonsa ya gundura da abincinsa sannan ya juya ya kama hanyar shiga cikin burninsu.    Safiya ce amman kowa hada hadarsa yake, kai tsaye ya wuce cikin fadarsu, gaba dayan mutane da suke cikin fadar babu mai tufafi kowa walki ne a jikinsu, fuskarsu babu annuri kamar sun yi arba da mutuwa.   Kafarsa ya kai kasa dayar kuma ya gurfana da ita ya sirinar da kansa ya gaishe da mahaifinsa. Da mafecin da ke hannunsa ya daga ya dora masa a kai alamar ya amsa gaisuwar sannan ya mike tsaye ya nufi cikin gidan sarautar mai kamar wani karamin burni.   Ta wani bangaren ruwan korama ne ke da guduna ga shukoki a gefenta daga can nesa da shukokin kuma wasu manyan itatuwan ayaba ne, idan ka tada kanka ka kalli gabanka kuma ginar kasa ta zakanin da irinnta kaka da kakkanin, wacce aka kawata ta da fatar damisa wani gurin kuma an kawata shi da gashin tsuntsaye kalakala da suke cikin dajin.   Masarautar GARUK babban masaurata ce mai karfi tsafi, tun daga kakannin har jikoki su ba su yarda da cigaban zamani ba, a duk inda za su je a duniyar nan sai dai su taka a kasa ko su yi tsafi ko su hau wani abun hawa daga dabbobinsu ya kaisu, fita su bar garin ma abu me mai wahala, ba kasafai yam garin ke nesa da garin ba saboda yanayin rayuwarsu da kuma suturarsu, kamar yadda ganganci ne wanda ba dan garin ba ya kawo ziyara a garin ba tare da sanin wani a garin ba. Yawancin abincin mutanen garin yayan itatuwa ne sai alkama danyar kwakwa. ZAINAB POV. Yola... Kadan ta kurba tea da ke gabanta ta aje karamin kofi a hankali sannan ta tattara dukannin hankalinta da natsuwarta ta maida akan laptop din dake gabanta. Hotunan da ta dauka jiya take kokarin gyarawa, tunanin yadda zata banbanta su da sauran take, domin a halin yanzu bata da wani buri da tunani da ya wuce ganinta a matakin da kowa be taba kaiwa ba, tana bukatar sabuwar idea. Tunani take tana wani tsuke karamin bakinta, tare da dora kafa daya saman daya. Wayarta ta dauko  ta kunna data, ba da niya ba ta shiga whatsapp, da gangan ta duba sakonin da ake aiko mata na dan ta bada amsa ba, ta saba halinta sai ta bude sako ta bar shi a bude ba tare da ta mayar da amsa ba, ji take ta isa da hakan, kuma ra'ayinta ne dole kowa ya bi.   Kai tsaye ta nufi status, sai da ta fara duba adadin mutane da suka duba nata status din wanda ta saka sannan ta fara duba na mutane. “Wow.......” Ta furta tana kara zooming wani hoto na wani namiji tare da matarsa da yayansa biyu. “Amman mijin nan na ki ya hadu fa” Ta kara duba hoton da kyau da sauran hotunan da suke biye da shi duka na miji wani guri da yaran wani gurin ita da shi wani gurin kuma shi kadai, sai a lokacin ta lura da matar ta goge hoton ma, sai ita a gurinta be gogu ba saboda tana using GB whatsapp. “Happy anniversary dear zan zo cin cake” Ta rubuta mata sannan ta shiga wani sashen tai saving hoton. Wata Dattijuwar mace ce ta shigo dakin tana daure da zane kanta kuma ya yafin atamfa kalar zanen da ke jikinta.   Ganin matar yasa Zainab kara relaxing akan kujerar tana wani lankwafar da kai. “Iya..... ” “Kyakkyawa, kowa yana can yana karyawa ke kina nan” “Iya inata tunanin abunda zan yi this week na haska duniya, kuma na amsa sunana na photographer, ina da mabiya miliyan uku da rabi a media, ina yan hamayya ya kamata ace na hara kura na daga musu hankali, kin san mu photographers kullum burinmu mu dara kowa” Ta karasa tana kai kafarta ta tana wata karamar camera dake gabanta da kafartata. Iya ta yi murmushi irin nasu na manya, sannan ta lasa bakinta ta dan daga jajayen idanuwanta kadan tana kallon Zainab tace. “Na fada kullum idan kina bukatar wani abun, ki rika kiran yayanki, shawara kike bukata ko wani taimako ki rika fada masa” “Iya kin san baya son waya mai tsaye ne, kuma baya gari balle na same shi mu yi magana” “Yana gari be dai shigo gidannan ba” Da sauri ta tashi zaune tana kallon mummunar fuskar Iya. “Ya akai kika sani?” Iya ta yi dariya. “Kina wasa Zainab, sirrin masarautar nan a hannuna yake, sai ki rika abu kamar a nan aka haife ki ba, ni na fada miki Omar yana cikin garin Yola” “Idan hakan ne, ba shi da amfani tun da baya bukatar shigowa cikin gidan nan....” “Kira shi ki fada masa dansa Labib, be da lafiya” “Ba zai jidadi ba idan nai masa karya” Ta fada tana dan turo baki tare da komawa jikin kujerar ta kwanta. “Ni kuma mahaifiyarki sai nace ki yi karya? Da gaske ne dan sa be da Lafiya, bari na dauko miki shi yanzu nan” Iya na fadar hakan ta juya ta fice daga dakin, sauka tai kasa gaba daya downstairs, ta nufi wani bangare na masarautar, a tsakanin bangaren da ta nufa da kuma wanda ta baro yayi nisa wata karamar unguwa zuwa wata.   Da kanta take tafiya hadiman gidan nata aika mata gaisuwa ita ko tana amsa musu baki har kunne, haka take da kowa fatfat kusan ta fi kowa far'a gidan.   Sai da ta fakaici idon mutane sannan ta shiga garken dawakai tana tambayar mai gadinsu. “Yau ka duba su kuwa?” “Ranki ya dade duba su kuma ai dole ne tunda shine aikina” Ta yi murmushi. “Hakan na da kyau bari na duba dokin Babban mutum.... ” Haka take kullum sai ta fake da sai ita da kanta zata duba dokin ba dan komai ba sai dan ta samu damar shiga ciki, cikin gurin ta shiga tana takawa ahankali tana duba dokuna kamar mai duba lafiyarsu, har ta isa gaban wani farin doki wanda ake kebe can shi kadai aka zagaye shi da katako, bude gurin tai ta shiga, ta kai hannu ta shafa dokin wanda kusan ya saba da ita, sannan ta duka kusa da shi ta fara tonon kasa, wasu abubuwa da fiddo guda uku dane a cikin zare, na tsakiyar ta matsa sai kuma taja zaren da karfi.   Daga inda take ta jiyo kukan Labib a kunnuwanta, da kuma maganar Nana wace ta tsorota da yadda yai kyalowa ta nufo shi tana ambaton Allah. Cikin saurin ta mayarda kulolan ta rufe ramen ta nade hannunta cikin zanenta gudun kar a ganshi da kasa sannan ta fito daga gurin. OMAR.... YOLA... Kofin tsamiya ne a hannunsa, dayan hannunsa kuma rike da lemun tsami yana matsawa a karamin kofin, farar singilat ce jikinsa sai farin tawul din da ke daure a ƙwugunsa, kafafaren kafafuwansa kuma sanye da takalminsa na bedroom. Sai da ya gama matsa lemun sannan ya saka tea spoon ya garwaye lemun tsamin da tsamiyar suka hade jikinsu, a take ya daga kansa sama ya hanye, a gurin ya dire kofin ya mike tsaye ya nufi bathroom, he spent more than thirty minutes a bathroom din yana jika kansa da ruwa sannan ya fito rike da wani karamin tawul yana goge kyakkawan jikinsa, gaban madubi ya tsaya yana goge gashin kansa. Fari ne kyakkyawan gaske, irin kyau nan mai daukar hankali, bafulatani gaba da baya amman idan ba sani kai ba sai ka rantse da Allah baasbine ne ko shuwa, ko'ina na jikinsa yana amsa sunansa na namiji kamar yadda muryarsa da siffar zatinsa take haska surarsa. Wani farin mai, mai sanyi ya dauka ya shafa a hannunsa ya murza sannan ya shafa shi a jikinsa, kana ya ware hannayensa yai mika, wacce ta sanarwa dukan jikinsa.   Wayarsa da ke kan gado ce tai ringing, sai da ya kwance tawul din jikinsa sannan ya nufi wayar ya dauka. “Nana” “Na'am Labib ba Lafiya yana ta ihu” “Waya taba shi?” Ya tambaya sanin cewar daman can ba lafiya ta isheshi ba. “Babu ina ma dakin, sai kawai na ji yayi kyalowa ya fashe da kuka, jikinsa ma duk yayi zafi” “Ku kira Doc” “Ammy ta kira shi” “Gani nan zuwa” Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa, kiran Nana na sauka na Muhseen ya shigo wayarsa, da murmushi Omar yai picking call din. “Omar kana gurin Ammy? Ko kana sokoto” “Ka shigo gari ne?” “Yeah ina Yola yanzu haka” “Wow gani zan je fada yanzu” “Okay mu hadu a can” Daga haka ya sauke wayar yana murmushi he can't remember when last ya ga Muhseen mutanen Abuja.   Daukar tawul din yai yaaje shi a muhallinsa sannan ya bude wardrobe ya dauko farin jean and blue t-shirt ya saka, a gagauce ya shirya ya saka agogon hannunsa ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin.   “Baba Adamu.... A tashi mota yanzu nn zamu je fada Labib ba lafiya” Tun kan ya sauko ya fara kwalawa Baba Adamu kira, abunka da mai jira jikin na rawa Baba Adamu ya nufi motar yai mata key sannan ya fito ya budewa Omar. Tun kan su shiga motar mai gadi ya bude gate Omar na shiga Baba Adamu ya fisgi motar kamar ba Dattijo ba. “Ahaaa haka nake so, a dinga taka mota kamar mu kadai ne a garin nan” Omar ya fada yana jindadim yadda Baba Adamu ke gudu da motar kamar dominsu kawai akai titi. ________________________ Did i ever write something about witch? (Mayu) Do you remember other family Mama Fulani da suke Yola? The story is about them now 🤗 03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: I just published "Free Page -2" of my story "FULANI". https://www.wattpad.com/1104521181?utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_source=android&utm_content=share_published *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *Free Page -2* Police din da suke gadin Masarautar ne suka bude masu gate, suna dagowa Shattima hannun duk kuwa da kasancewar ba su da tabbacin yana ganinsu domin bakin gilashin motar ba zai basu damar ganin ya karbi gausuwarta su ba ko akasin haka “Fada za mu biya ranka ya dade?” “A a sai na fara duba Labib” Kai tsaye Baba Adamu ya nitsa da motar cikin harabar Masarautar kamin ya dauki wani bangare da zai sadashi da bangaren Momy. Kamin su karasa wayar Shattima ta sake ringing cirota yai daga aljihunsa yana dubawa Hajiya Karama ce rubuce a gaban wayar, sai da tai ringing kamar ba zai daga ba sai kuma yai picking. “Shattima, Labib ba lafiya” “I know na shigo cikin Masarautar ai” Mikewa tai tsaye daga saman kujerar da take zaune ta fito daga dakinta ta zagayo ta fito backyard ta tsaya tana hango motarsa. “Okay” Ta sauke wayar da already ya kashe kiran tun da ya bata amsa. A gaban wata katuwar kofa wacce ta sha ado kamar ba za a mutu ba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito da sauri ya budewa Shattima. Cikin wata irin isa da kasaita Shattima ya sako da kafafuwansa waje ya fito daga cikin motar yana wata irin tafiya ta takama kamar wanda baya son taka kasa, a zahirin takamarce da isa da kuma kasaita a tare da shi kamar yadda idon kowa na cikin Masarautar ke gani, sai dai a badini sam babu hakan a tare da shi ko da rana daya be tana jin ya fi wani ba dan yana dan sarauta, be taba jin wani ba sa'ansa ba ne dan yana da dukiya da ilmi, ba zaka taba fahimtar hakan ba har sai idan ka zauna da shi ka fahimce shi sosai da sosai.   Fadawan da ke gadin kofar ne suka bude masa da sauri suna risinawa tare da zuba gaisuwa, dayan kuma nata aikin isar da kirari, ko kallonsu be yi ba balle ya amsa musu gaba daya hankalinsa yana gun dansa kiran da Zainab tai masa bayan na Nana yasa hankalinsa ya kara tashi. Cikin tafiyarsa ta kasaita ya natsa kafarsa cikin wani babban guri. Wani irin katon falo ne mai dauke da Turkish furnitures tun daga kan kujeru har carpet da center table, da kuma side table dake kowace kusurwa ta kujerun, ga katon Hoton mai Matarba, sai kuma hoton Ammy sai na Hajiya daga gefe na mai Martaba a tsakiya sai hotunna wasu muhimman mutane na Masarautar dake tsaye a falo, idan ka cire farin fentin da ya kawata falon komai na cikinsa ja ne gwanin sha'awa, falon ya sha ado sai dai ba ado irin na komai a zuba ba, a a adon yan zamani wanda za a kawata falon da abu kadan amman masu kyau da tsada ta yadda duk wanda ya shiga ciki sai ya manta a wace duniyar yake, idan kana a cikin falon za kayi zaton akwai hadari a waje ne ko kuma yamma ta yi ko ma kai zaton farkon budewar safiya ne sakamaon hasken da aka kawata falon da shi kadan ne, mai daukar hankali, sanyin ac ta ko'ina, ga wasu manyan kyandira irin na zamani masu aiki da wutar lantarki suna bada haske a falon gwanin burgewa, ta dayan bangaren kuma wani irin kamshi ne ke tashi a cikin falon kashin da ba zaka iya tantance wane irin kalar turarene ba. Wata babbar kofa ya nufa mai kyau da kyalle kamar an am mata ado da zinari, ya kai farin hannunsa ya tura kofar ya shiga, sai ya tsinci kansa a wani matsakaicin corridor mai kama da karamin falo an cika ko'ina da na gurin da manyan fulawoyin na kasko da jan carpet. Mikewa yai straight zuwa katon stairs din da ke gabansa, gabansa kawai yake kallo har ya haye sama, kofar farko ya fara turawa tun kan ta karasa budewa ya jiyo kukan dansa, hakan yasa shi hanzarin cira kafa ya shiga cikin falon mai kama da da wata karamar fadar turawa, a wannan falon kam komai na cikinsa blue ne idan ka cire farin fentin mai kawata ko'ina na gidan, ta bangare daya kuma wani gini ne akai a cikin gurin mai kamar swimming pool sai dai wannan anyi shi da dan yi tsayi, an masa kwalliya da kwaryar da kuma rudayi sai dawusu a samansu yana furzo ruwa gwanin sha'awa, a iya cikin gilashin ruwan ke tsawa ko kadan basa digowa kasa balle har su sauka.   Falo ne mai dauke da set din kujeru uku kujerun farko kanana ne an jerasu kamar kujerun dinning wato a zagaye, sai dan karamin tebur a tsakiya da kuma wani karamin carpet blue, na biyun su kuma manyan turkish ne masu daukar hankali, sai  wasu daga can karshen falon su ma blue kamar dai sauran an zagaye gefen da su, su ma kuma suna da karamin carpet da center table. A gaban falon kuma wani katon kirsten tv stand ne fari mai gloss fronts da haske blue, left and right na tv stand din matsakaicin show glass ne mai haske a ciki blue color an masa kwaliya da turaruka na alfarma masu kyau da tsada gwanin burgewa. Ga wani katon plasma da aka kawata tv stand da shi kamar matanen ciki za su fito waje. A dayan gefen kuma wani karamin madubi ne na aka manna mai dauke da gurin wanke hannu, yamma da falon kuma matattarar cin abinci ce mai zamam kanta wacce aka ware mata kofarta dabam kusa da wani katon freezer mai kofa biyu, a dinning area din ma akwai madaidaicin plasma wanda zai bawa duk wanda yake zaune a dinning din damar kallo. Kofar da Umar ya shigo ce kawai gini a cikin falon sauran duka glass ne gwanin burgewa.   A dayan bangaren kusa da dinning akwai wata karamar kofar glass, shiga cikinta na sadarda mutum da wani kebantaccen guri mai dauke da set din karamin dinning har biyar an rarrabasu an jera ko wane set dabam da wani. Ta backyard din mutum zai iya hango wanda ke tafe da kuma abunda ke gudana a harabar Masarautar sai dai ba zai bawa mutum damar hango bangaren mai Martaba ba, dama da shi kuma wanda ke tsaye a gurin zai iya hangon garden din dake bangaren Momy, shi ma kuma ganin mai shiga ko mai fitowa ne kawai mutum ke da damar yi ba wai komai da komai na cikin ba kasancewar garden din na da manyan itatuwa da katon Swimming pool a gafe na dutse..... Nana na ganinsa ta mike tsaye rike da Labib da tana jijjigashi ta nufi gurinsa. Cike da kulawa da tausayi da kuma kaunar dansa ya sa hannu biyu ya karbe sa. “What happened?” “Ba wanda zai fada maka ga abunda ya faru fa, ina dakin kawai yai kyalowa” “No karya kike na fada muku a daina barinsu su kadai” Bata sake unkurin cewa komai ba ta koma ta zauna tana kallonsa. A kafadarsa ya dorashi yana jijjigashi tare da karanta masa ayatul kursiyu ya tofa masa sannan ya nufi hanyar dake kusa da dinning da kansa ya bude kofar ya shiga, yana shafa bayan Labib a hankali yana kallon abunda ke gudana a kasa. Ta kofar farko Hajiya Karama ya fito ta nufo inda yake tsaye. “Har ka iso, ya jikin na shi?” “Da sauki” Ya amsa mata domin ya daina kukan da yake. “Me ke damunshi” “Ban sani ba” “Kawo shi” Ta karbe shi tana jijjigashi cike da kulawa domin ita ma kanta tana kaunar yaran. “Nana tace kyallowa yai, na fada musu a daina bar min yara su kadai, if not zan dauke su daga gidan nan” Ya fada yana juyawa ya kalli wata harabar dabam kana ya aje numfashin da sautin da ke nuna ba da wasa yake ba, biyoshi tai tana girgiza kai. “Nono Ammy ba zata jidadi ba, am samu mai kula da dakinsu fa, na ce a barta ta kula da su Iya tace bata yarda da ita ba” “Wacece?” Ya juyo yana tambaya. “Wata ce ba zata wuce 16-17 years ba” “Miyasa ba ta yarda da ita ba?” “I don't know ko maybe saboda ta yi kankanta ne” Kare mata kallo yai ya dauke kai “Ji dress dinki, na sha fada miki ki daina irin shigar nan” Ya karasa yana takawa a hankali zuwa gurin karfen dake gabansa. Sai ta kalli jikinta. “What's wrong with my dress?” Be amsa ta ba ya juya ya fice daga gurin ya barta rike da Labib din a kafadarta. Murmushi tai tana kara kallon kanta, dogon wando ne da wata riga mai guntun hannu wacce ta tsaya iya kwankwasonta, ba laifi kayan sun matse ta sai dai ba irin matsuwa can can sosai ba, a gurinta hakan normal ne ko ba komai tana jindadin yadda hankalin maza yake tashi idan sun yi arba da irin halittar da Allah yai mata, hakan na mata dadi sosai wai sai dai a gani a hade yawu babu yadda za'ayi da ita. Bin bayansa tai ta kofar da ya shiga tana cigaba da murmushi, a kujerar da ke kusa da kofar ta zauna ta sa dayan hannunta tana gyara yar karamar jar hular da ke kanta. “Yayi shiru?” Nana ta tambaya tana nufo inda Zainab din take zaune. “Yeah i think yayi bachi” Ta taba jikinsa sai ta ji shi da dan zafi za tai magana Zainab ta mike tsaye tana kallon Doc Deen wanda ya shigo rike da dan karamin akwatin magani, fuskarsa sanye da farin gilashi. “Sannu da zuwa Doctor” “Hajiya Karama” Ya amsa mata yana murmushi tare da kallon Shattima wanda ke tsaye jikin window ya rumgume hannayensa ta baya yana kallon harabar gidan. Har Doc ya zauna Zainab ta mika masa Labib ya fara duba shi Shattima be juyo ba. “Miya same shi?” “Ba komai haka kawai yai ihu” Nana ta amsa shi tana zaunawa kusa da Doc kamar ita ce zata duba yaron, Doc Deen yayi murmushi yana kallonta. “Ko na baki ki duba shi?” Dariya tai mai sauti ta make kafada tana girgiza masa kai. Zainab ta yi murmushi ta nufi gurin da Shattima yake tsaye ta tsaya ta jera tare da shi tana kallon dokin da yake kallo wanda ake yi wa ado irin na sarakuna. “Yaushe ka dawo?” “Jiya....” Ya amsa mata a takaice duk kuwa da kasancewar yana a cikin yanayin da baya son magana, amman ba zai iya kin amsa ta ba, babu abunda Zainab zata bukata ya kasa mata, bayan girman da tai a kusa da shi ta bude ido, kusan ta fi shakuwa da shi fiye da kowa, tana jin maganarsa kamar yadda shi ma yake saurarenta yana girmamata a ciki har da sunan mahaifiyarsa da ta ci, wanda hakan yasa ake mata lakabi da Hajiya Karama, gashi tana da sirri idan ya fada mata A babu mai ji sai idan shi ya umarce ta data fada, babu abunda za tai ba da saninsa ba, babu abunda take boye masa ita da shi abokai ne kuma shakikai. “Wannan shi ne karo na biyu da ka sauka wani guri ba Masarautar nan ba, and i don't think hakan zai mana dadi” A hankali ya busar da iskar bakinsa ya zuba hannyensa aljihu yana cigaba da kallon dokin ta cikin gilashin falon ya ce. “Abubuwan gidan nan basa min dadi” “Yeah amman some time muna bukatar shawararka, ko bukatar wani abu kusan kai ne Sarki a gidanan tun da Mai Martaba bashi da Lafiya, be kamata ace kana nisa da gida ba, and the way you act Ammy ba zata jidadi ba” Murmushin gafen baki yai ya kalleta. “Zan gyara Hajiya Karama” “Good” Ta fada with smile on her face, sannan ita ma ta saka hannunta aljihu tana wasa da dayar kafarta, shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi “This time around ina son nai wani abun da zai bawa kowa mamaki as a photographer i want to do something differently like..... ” Sai kuma ta kasa karasawa ta ware hannayenta kamar mai tunanin abunda zata fada. Kallonta yai kadan ya dauke kai. “Well i think ki shiga kauye, ki duba wata culture ko yare ki duba wasu addinai na wasu da suke wanda ya sha banban da wanda ake gani sai ki dauka” Ta wara idonta tana murmushin jindadi. “Wow shiyasa bana son kai nisa da ni, a duk lokacin da na nemi shawara sai ka sama min mafita” Murmushi yai mata kamin ya juyo da sauri jin muryar Muhseen. “Wow wow wow..... Longest time Dude” Tsakanin shi da Muhseen aka rasa wanda ya fi wani sauri, a tsakiyar falon suka hadu suka rumgume junansu ko wanensu fuskarsa dauke da dariya da farincikin arba da dan'uwansa. Nana ta taso da sauri ta rumgume Muhseen. “Ya Muhseen oyoyo” “Hey Little One” Zainab ma side hug tai masa tana welcoming dinsa, sai da ya kai wa Doc Yazeed hannu suka gaisa sannan ya zauna kusa da Zainab. “Hajiya Karama how far?” “Fine ya Abuja?” “Kalau” “Ina Aliyu and Mama Fulani?” “Yana nan kalau Mama kuma tana kasa tare da Mai Martaba” Shattima ya karbi Labib dake bachi a hannun Doc Deen yana fadin. “Doc me ke sa su yawan zaburar nan ne wai?” “To Wallahi ba zan iya fada ba, adai rika yi ana hada musu da addu'a especially idan za su kwanta bachi ko idan sun farka, and a daina barinsu a duhu ko barinsu su kadai” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya rufe akwatinsa yana musu sallama, sai Nana ta mike tsaye ta bi bayansa suka fita falon tare, yana saukowa stairs din ta ce. “Doc yaushe zaka kai ni gurin wannan sister taka wace kace tana kama da ni” Kallonta kawai yai ya dauke kai yana murmushi be ce mata komai ba har ya sauka ita kuma bata fasa tambayarsa tana masa magiya ba har ya isa gurin motarsa. “You know what? Sometimes dabi'unku daya da Ya Shattima, sai ku rika yi ma mutum wulakanci idan kun ga yana son abu” Sai da ya bude motarsa ya saka akwatin sannan ya juyo ya kalleta daga sama har kasa, green lace ne jikinta kanta ba dankwali ta kulle gashin kanta, babu yan yankunne a kunnenta babu makeup a fuskarta amman hakan be hana kyauta fita ba, kallo daya zaka mata ka san cewar jini daya ce ita da Shattima domin kamarsu ta bace kamar an tsaga kara. “Ba a nan take ba” Ya amsa mata with smile. “A ina take?” “Abuja” “Abuja ai gurin zuwan mu ne zan iya binka na kaini na ganta, tun ranar da ka fada min nake son na ganta har yau” Ya zaro ido “Ki bini? So kike ace na sace ki?” “A a zamu je da sanin Ammy da kuma Hajiya kuma zan fada musu ba za su hana ba” “Ba za su bari ba” “To mu tsere idan mun dawo sai mu fada musu” Wannan karon dariya yai sosai. “Nana ba ki da wayo” “Ina da wayo mana, amman ai ina da hankali” Ta fada ita ma tana dariya kamar shi. “Fine, zan san abun yi ko dai na dauko miki ita na kawo ko kuma na baki address dinta idan kin shiga Abuja ki je ki ganta” “Okay” Ta fada tana daka tsalle, kamar ance ta daga kai ta gani, sai ta hango Sirleem a sama daga can bangarensu yana kallonsu. “Idan kai tunani ka kira Ya Shattima ka fada masa sai ya fada min ka ji?” Tun kamin ya amsa mata tai saurin barin wajen ta koma sashensu. Kai Doc Deen ya daga ya kalli Sirleem wanda ke watsa masa wani irin kallo na rashin kima, murmushi Deen yai ya bude motarsa ya shiga. Daga backyard din da yake tsaye zuciyarsa take wani irin tafarfasa ganin Nana da Yazeed da yai, ba tun yau ya lura a duk lokacin da Deen ya shigo  Masarautar sai ya tsaya yayi magana da Nana yake tafiya. A fusace ya nufi bangaren Ammy zuciyarsa kamar zata fito tsabar kishi, cikin fusata ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Shattima da Muhseen Zainab da Nana zaune a falon, dukan su kallonsa sukai ban da Shattima da yai kamar be san da shi a duniya ba, be damu ba ya soma gabatar da abunda ya kawo shi. “Ke me kike yi waje da Deen?” “Ina ruwanka?” Ta amsa masa ita ma tana turo baki gaba kamar za tai kuka sannan ta mike tsaye rike wayarta ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta. Zainab ta daga kai tana masa wani shegen kallo. “Look at you Sirleem sai ka rika yin abu kamar wani fool ya zaka shigo a gaban mutane kana tambayarta miye take a waje? Kamar wani ubanta” Runtse ido yai ya bude cikin bacin rai ya ce “Hajiya Karama babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan ina magana da Nana ki daina saka min baki” “Oh really? To ko dukana zaka yi?” Ta fada tana mikewa tsaye, daman can ita da shi ba sa shan inuwa daya. Sai a lokacin ne Shattima ya daga ido ya kalleshi ya kalli Zainab. “Please Hajiya Karama tafi dakinki” “Amman....” Bata karasa ba maganar ta makale sakamakon kallon umarni da Shattima yai mata sai ta duka ta dauki wayarta ta fice daga falon. Shattima ya kalli Muhseen yana murmushi kamar ba shi ba yace. “Muje sashena ka huta na san yanzu za a fara jera maka abinci dan gidan Mai Martaba” A tare suka fice da Muhseen din aka bar Salim tsaye a falon kamar wani wawa. FADIME POV. Busar sarewar nan da take yawan ji a mafarki ta soma jiyowa tana tashi a hankali. Kwantar da kanta tai jikin kafafuwanta tana sauraren yadda busar ke ratsa kunnuwanta tana saukar da nishadi a zuciyarta busa ce mai ban tausayi mai saka shauki da dadin saurare, a iya lissafinta tana tuna mafarkinta ne shiyasa take jiyo busar, hakan yasa ta rufe idonta tana ta ganin mutumen nan mai busar sarewa na mafarkinta, a kullum idan tai mafarkinsa baya yake bata bata taba ganin fuskarsa ba, yana daure da walki jikinsa babu riga. Jin kamar a zahiri ake busar yasa ta bude idonta ta mike tsaye ta saki sandar korar shannun da ke hannunta, sai ta ji karar busar sarewar yana karuwa kamar ana kusantota, waige waige ta fara yi sai kuma ta juya da sauri ta nufi gurin itatuwan masara ta kusa kai ciki domin a ciki take jin kamar busar na fitowa, tana tafiya tana juyawo tana ratsa shukar masara ta ko'ina, can kuma ta juyo sautin kamar a inda ta baro ta juyo a guje ta dawo gaba daya hankalinta ya tashi domin bata taba jin busar a zahiri ba sai a yau, saman katon dutsen dake gaban shanunta ta haye tana hawaye tana waige waige ko zata hango mai busar ko kuma tabbatar da inda sautin busar ke fitowa amman sai ta ji abun ya karade ilahirin dajin gaba daya, faduwa tai a gurin ta dafe kanta tana kuka domin a yanzu ta fara tunanin ba azahiri take jin busar ba a cikin kwakwalwarta ne. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ta furta tana kara runtse ido tana girgiza kai domin har lokacin bata daina jin busar sarewar ba, ta dade a gurin tsugune, sai da ta daina jin busar sannan ta mike tsaye tana kallon shanunta da ke kasa, a take saniya daya ta yanke jiki ta fadi a gurin tana shure shuren mutuwa, Fadime na ganin haka ta sauko da mugun gudu ta nufi hanyar gida tana wani irin kuka na tashin hankali, @250 ta isa gida kamar wata mahaukaciya ta fada cikin gidan tana kururuwa. “Inna Inna yau ma nagge guda ta fwadi, gata can tana shure shure Inna mutuwa za tai” Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata. “Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa” Ta amsa masa ta yaren da suka fi gwarewa, a take Fadime ta tashi da gudu ya fice daga gidan zuwa gonar mahaifinta, Inna Amo ce ta fito daga bandakin lullube da bakin gane ta nufo tsakar gidan tana. “Inna Fadime lafiya kike?” “Nagge ce ta sake faduwa da sannu naggen Malam sai karewa suke Amo” “Allah ya kyauta” Shine abunda ta fada ta nufi bukkatarta tana koda tsatsagar hakora.   Ko da Fadime ta isa ta fadawa Mahaifinta ya tafi tare da mutunensa da suke aiki tare sun isa a kuraren lokaci domin kuwa tuni saniyar ta mutu sauran kuma na tsaye suna kiwonsu. Faduwa Fadime tai ta dafe kai tana kuka, har sai da Mahaifinta ya tasheta tsaye. “Haba Fulani komai ai na Allah ne? Ki daina wannan kukan” “Bappa kullum fa idan na fita kiwo sai Nagge ta mutu, ni kadai take ma haka” “A a daman can haka Allah ya rubutu” Ya amsa mata cike da karfin hali, sai daya daga cikin mutanen da suka zo tare da shi dayan ya ce. “Malam da dai ka daina barinta tana fita kiwo da su” Malam Jauro yayi murmushi yana girgiza kai. “A a babu abunda za a fasa, idan mutanen gari sun canfa ta ni ai be kamata na yarda a matsayi ne na mahaifinta, idan Fulani bata ji dadi a gurin iyayenta ba a gurin wa zata ji? Ko da duka sanu na za su kare ba Fulani ba zata daina zuwa da su kiwo ba” “To Allah Hukkumo sa'a” Dayan ya fada cikin jin haushin be dauki shawararsa ba. Malam ya dafa kan Fulani ya ce. “Ki cigaba da kiwon idan yamma ta yi sai ki dawo da su gida, annani?” “Iyyiye” Ta amsa masa tana gyara kai har lokacin bata daina hawaye ba, kuma bata san ranar dainawar ba domin wannan matsalar ta shiga cikin jininta ta zauna ta hanata sukuni da walwala duk kuwa da irin ficen da tai a cikin kauye na amsa sunan yarinya daya tilo wacce ta iya turanci kuma ta iya rubutu da karatu a kauyen. Sai dai wannan abun yasa mutane na tsoronta ga rashin farin jinin da yake damun mahaifiyarta, tun tasowarta har ta girma ta kawo yanzu babu namijin da ya taba nuna yana ra'ayinta balle har ya furta yana sonta, ko irin zuwa dandalin da take sai dai taje wani lokacin dan ta kai sana'arta wani lokacin kuma dan tai kallo, domin ko da ta shiga tai rawa babu namijin da zai mata kari, sai dai tai wasa da yan 'uwanta mata duk kuwa da irin kyau da Fadime take da shi. Haka ta zauna a gurin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba. Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wanne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen. Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito tsakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na biyu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi. Haka ta debi ruwan ta rika watsa musu suka fara gudu banda daya wanda ya tsaya yana kallonta sai wani rausayarda kai yake. Hakan yasa ta tsorata ta fara ja da baya tana cigaba da watsa masa ruwa, aiko kamar jira yake sai ya sauko da sauri yai cikinta, tsakanin ihunta da fallawa da gudu da kuma sakin robar ruwan ba a san wanda ya riga wani ba, kamar bera haka ta shige bukkarsu har wani tsale take sama tsabar gudu da tsoro. “Inna Kadangare ne ya bijoni” “Ba dai zaki daina watsa musu ruwa ba ko? Wata rana sai kin watsawa aljani” “Inna wannan ma da gudu yake, ba zan iya wanka a ciki ba” Duk maganar da take da Inna ba ta dago ta kalleta ba sai aikin auna giɗa take a kwarya, sai da ta mike tsaye sannan tai arba da yarta. “Innalillahi Fulani a tsirara kike fa, zindir Subhanallahi” “To Inna kadangaren ne ya biyo ni ai ba zan iya tsayawa daura zane ba” Ta fada tana turo baki tare da sa hannu ta kare kirjinta wanda da shi da babu duk daya kamin ta nufi inda zane yake ta dauka ta daura. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fito sannan ita ma ta fito waje tana labe bayanta kamar wacce zata sake arba da shi. “Ni ban ga komai a bandakin ba” “To Inna ki tsaya na gama wanka tukuna sai ki tafi” A bakin kofar bandakin Inna ta tsaya Fadime ta dauki robar taje ta debo wani ruwan ta tsaya daga baki-baki tai wankan ta fito da sauri... *FULANI -it's not free, if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* 03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *-3* FALMATA POV. Bayan gama sallah isha'i Baba ya shigo gidan rike da yar ledarsa, da sauri ta karasa ta karba tana masa sannu da zuwa, ya amsa mata can ciki yana dauke fuska kamar wanda baya kaunar ganinta. Dakin Tumba ya nufa tana biye da shi a baya rike da ledar sai da ya shiga sannan ita ma tai sallama ta shiga ta aje ledar ta juyo ta fito kamshin tsire na dukan hancinta, guri ta samu a saman tabarmar dake shimfide tsakar gidan ta zauna tana ta bitar karatunta na iziya. Hango mahaifinta ya fito daga dakin Tumba zai kama ruwa yasa tai sauri tashi ta karasa ta dauki butarsa ta zuba masa ruwa ta mika masa tana sirinawa kamar yadda ta saba. Sai da ya shige bandakin sannan Tumba ta fito ta rike kofar dakinta tai tsaye tana watsa mata harara. “Fulani dauki bokiti kije ke samo mana ruwa” Juyowa Falmata tai ta kalleta da fuskar tausayi tana jin kamar tace ta dauki bokiti taje ta debo wuta, har ga Allah bayan surfe deban ruwa ne abu na biyu data tsana, sai dai babu yadda za tai kullum sai ta yi surfen sai kuma ta yi deban ruwan abu ne da ya zame mata dole ko a ciwo ko da lafiya dole ne tai. “Umma na debo ruwa dazun da safe fa sai da na cika komai” Ta fada da muryar dake nuna rokon take a tausaya mata. “Ba gabanki Naja tai wanki ba? Ruwan ya kare ko so kike mu tashi da safe babu ko na alwala?” Umma na kai aya Abba ya dauka yana daka mata tsawa. “Dauki kije debo ruwa aka ce sha-sha -sha kawai” Ya karasa yana daure zariyar wandonsa karen sigari a bakinsa. Kamar wacce tai arba da mutuwarta haka ta nufi inda bokin ruwan yake ta dauka da sauri jikinta har rawa yake ta shiga dakin da suke kwana ita da naja ta dauko hijabinta ta saka ta dauki bokintin ta fice daga gidan tana ala ala kar ma tai numfashi da karfi mahaifinta ya ji. Sai ta fito daga cikin gidan sannan ta shara hawaye, ina zata je debo ruwa yanzu cikin dare? Ta san ko wane gida a yanzu sun rufe rijiyarsu, gashi babu wuta balle taje bohol domin idan babu wuta to bohol din baya aiki. Hanya ta mike tana tunanin wace rigiyar zata dosa, hawaye na ziryo mata, da karfi da yaji dazun Umma ta hana ta deban ruwan ta wanke mata surfe amman ta bar Naja yar gata tai wanki da ruwan yanzu kuma sai ace ita ce zata je ta debo wasu. Hawayen idonta ta share ta nufi gidansu kawarta Khadija, tun a bakin kofar gida take sallama amman babu wanda ya amsa ta sakamakon kure volume da sukai da wakar fitattacen mawakin nan da Falmata tafi kauna fiye da komai da kowa a duniyar nan, wato Sirleem M2. A take ita ma ta bi sahu cikin yaran makota da suke zaune bakin kofar dakin Maman Khadija suna kallo, ba ta ko bi ta kan neman Khadija ba ta zauna saman bokitin ta fara bawa idanuwanta abinci, a take murmushin ya gauraye fuskarta ranta yai fes kamar ba ita ba, daman can haka take indai tai arba da wakarsa ko hotonsa wani irin dadi take ji saboda burgeta yake kaf a mawakan duniya babu wanda take so irin Sirleem har wani shauki take ji idan ta tuno wakarsa. “Ke” Khadija ta dafa ta aje butar hannunta da ke nuna cewar daga bandaki ta fito. “Ina kika fito da bokita da daren nan?” Falmata bata kula ta ba sai da wakar Sirleem ta kai karshe kaf sannan ta juyo tana kallon kawar tata kamar wacce ta dawo daga hayyacinta. “Me kike cewa?” “Oh na shiga uku ni Khadija wato tsabar son wakar M2 har baki ji abunda nake fada ba” Dariya Falmata tai. “Wallahi ina son M2 sosai Khadija ya iya waka sosai yai ta hausa yai ta turanci har kasashen waje ance yana zuwa yai waka kuma kin ga dan Yola ne ai dole mu so shi ko?” “Ke dai kike sani, dan yana dan Yola aka ce miki zama suke a garinsu ne, yawanci kasashen turawa suke zuwa ko Abuja su zauna” “Khadija kin san me? Da ace na yi boko na iya rubutawa da karanatawa ko? Da nima na rika koyon wakokinsa ina yi” Cewar Falmata tana dariya har kyakyatawa. “Lallai Falmata abun na ki babba ne, ina zaki je da dare ke da ba a barin kina fita?” A take yanayinta ya canja murmushi da far'ar dake fuskarsa ta gushe tunawa da duniyar kuncinta, cikin rashin kuzari ta labartawa Khadija abunda ya faru sannan ta dora da. “Dan Allah muje ki kara ni idansu Binta tun da kawarki ce kila Mamanta zata yarda na debi ruwan ko maya biyu ce dan Allah” “Gaskiya dai tsakani da Allah Falmata Umma tana cutarki, shi kuma Baba ya zama wani iri duk abunda tace shi yake amfani da shi, yadda fa iyaye suke da hakki akan yayansu su ma yayansu suna da hakki akansu, ni kam da ma ke aka kai kauye aka bar kanenki nan wannan wahala ta miki yawa Falmata” Ta zaro ido. “A a ke idan su Aisha n suke nan ai wahala za su sha sosai tun da su kanana ne, kara dai ni da nake da girma yanzu ni dai muje ki rakani” “Ga ruwa can a jarka je ki deba ki yi uku da bokitin ki” Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace. “Ga ruwan nan na debo” “To Allah yai miki albarka Fulani ya baki miji na gari” Tumba ta fada da far'arta, Falmata dai bata ce komai ba dan tasan ba da zuciya daya tai mata addu'ar ba sai dan ganin mahaifinta yana nan, daman can haka take mata a gaban idon jama'a ko kuma a gaban mahaifinta. Dukawa tai ta dauki takardar tsiren ta nufi hanyar dakinsu tana lasar yajin dake jiki, hakan be gamsar da ita ba sai da ta cire wani sashe a takardar dake da mai da yaji ta saka a baki ta tauna ta tsotse ruwan tass sannan ta jefar ta shige dakinsu.   Wani tsohon zanen gado ta dauka ta shinfida saman gadon karar da take bachi sannan ta kashe kyandir din ta kwanta tana karanto addu'o'i kamar yadda ta saba, Naja kam tuni tai nisa da bachin.   Asubar fari Falmata ta fito daga dakin ta dora alwala ta shiga ta fara nafila kamin ta gabatar da sallah Asuba, ta saba da wannan dabi'ar ta yin nafila kamin asuba da kuma addu'o'in safe da maraice da na bachi tun tana karama, duk da kasancewar tana da kananan shekaru hakan be saka ta watsar da koyarwar mahaifiyarta ba, ko kadan Falmata bata wasa da addu'a da kuma sallah akan lokacin komai take zata aje taje tai sallah, idan kuma lokacin addu'ar yamma yayi ko aiki take haka zata rika karanta addu'inta, abun har ya zame mata jiki idan ba tai ba sai ta ji bata cikin natsuwa. Sai da rana ta fito sannan ta fito daga dakin ta fito harabar gidan ta tattara kayan wanke wanke ta wanke komai tas ta share gidan sannan ta cika karamin bokiti da ruwa ta nufi bandaki, sai ta ta tube tufafin jikinta sannan ta daga wani karamin dutse ta dauko ragowar amon da tai wanka jiya ta saka a soson ta soma wankanta. Bayan ta gama ta fito tana ta tsanda domin ban dakin a kasa kasa ce ba suminti ba idan kana wanka ruwan dake sauka yana tartsatsin yana sa kafar bandakin ta watso maka a kafafuwa.   Gindin biyar ta nufa ta zauna ta saka dutsen gugar kafafuwa ta goge kafafuwanta tas ta sake wanke su sannan ta shiga dakinsu, bata ɓata lokaci ba gurin shiryawa sanin inda zata je gashi rana ya soma takewa.   Duk da irin saurin da take hakan be hana ta kwaliya ba sannan ta saka atamfa tare da Hijab ta fito cikin sauri tana saka talkaminta na roba. “Fulani zo ga abincin ki” Cewar Umma daga gindin murhu da take zaune tana kallon Falmata, abun ka da mai neman sai ga Falmata ta karaso cikin sauri ta cire hijab dinta ta rataya a igiya sannan ta tsuguna taja kwanon da Umma ke nuna mata mai dauke da dumamen tuwo masara. “Fara shan wannan tukuna” Umma ta mika mata wani ruwan rubutu dake karamin kofi, jiki a sanyaye Falmata ta mika hannu ta karba tai Bismillah da muryar da tasan Umma ba ta ji ba ta shanye, inda sabo da saba da shan magani daga hannun Umma wani lokacin ma a cikin kunu ko madara take kada mata ta mika mata kuma ta karba ta sha, sai dai bata taba mantawa da Bismillah idan zata ci abunda yafi komai batawa Umma rai kenan wani lokacin har hana ta take idan ta ji. MASARAUTA.... Kowa a dinning din fuskarsa a sake take ana fira ban da Nana wace ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa sai wasa take da abincin da ke gabanta. “Hakan dai be hana ki zuwa makaranta, da ki ci abinci da karki ci duk uwar su daya ubansu daya a gurina, kullum cikin latti kike shiyasa suka aiko suka ce baki zuwa makaranta” Mama Fulani dake kokarin daukar cup din tea ta kalleta. “Nana ba ki son makaranta why?” “Ba makaranta ne bana so ba Mama Fulani auren Sirleem ne bana so” Murmushi Mama Fulani tai. “To miya hada aurenki da Sirleem da kuma zancen karatu?” Ta bata fuska kamar zata fasa kuka bata dai ce komai ba. Shattima ya kalleta kadan ya dauke kai yana kai plantain baki ya ce. “Gaskiya ne yarinya Wallahi ba ki cancanci auren mawaki ba, yar Sarki Abdallah Umar Jari ace ta auri mawaka ki, abun ai be yi ba” “Miye matsalar mawaki ne Shattima? Waka ba a sana'a ba ce? Bayan waka kuma ai yana aiki da Unicef ko duk shi din ba aiki bane? He is graduated kasan gaba ina Allah zai kai shi ne? After that yana da restaurant yana da katon Boutique, yana da shagon siyarsa phones and what else kake son ya mallaka kamin a aura masa Nana?” Ammy na kai aya, Mama Fulani ta wara ido. “Aa ba laifi gaskiya kuma kin ga yadda yai popular din nan kudi suke samu sosai indai yana da rufin asiri ai ba laifi ta auri abunta” Nana ta kara bata fuska tana kallon Mama Fulani. “Mama ni dai bana son shi yanzu” Sai kuma ta kalli Shattima “No ki daina kallona kar ace ni nake kitsa miki komai” Ammy ta tabe baki tana fadin. “Ko dai minene kyaji da shi ba abunda za a fasa idan ka ga an fasa auren nan sai idan shi ne da kansa yace ya janye ba zai aureta ba” “Haba Ammy sai kace na yi alo ace sai idan shi ne ya fasa Fisabilillahi” Ta fada tana kara bata fuska. Zainab dake aikin chakuda wainar kwan da ke ba gabanta da fork ta yamutsa fuska tana fadin. “Matsalar ba wai ta aikinsa ko kudinsa ba ne, matsalar wakar da yake ne be dace ace zuri'ar gidan nan ta auri mawaki ba” “Daga ke har Shattima wayayyen mutane ne, kin san miye waka ai kina tare da masu yinta, ba photographer ba ce ke miyasa mazan da suke zuwa neman aurenki ba su ce ai ba zasu aureki ba saboda yanayin sana'arki, kuma yarinyar a gaban kowa Mai Martaba ya tsayar da ita ya tambaye ta tana son shi ko irin kunyar da yan mata ke yi ita ba tai ba, tace tana son shi kuma aurenshi za tai, to sai yanzu dan Mai Martaba bashi da lafiya sai ku kitsa mata magana ku ss ta tsane shi ace ni na hana aure? Daman ance ni da yaya mu ke mulki Masarauta, ku dai kawai saboda ba kya son M2 shiyasa kuke wannan abu ita kuma yarinya ce karama duk inda kuka a zata dauka hawa za tai” “No No Ammy i'm out of this” Shattima ya fada yana mikewa tsaye tare da ware hannayensa alamar babu ruwansa a ciki ya fita daga dinning are din, Hajiya Karama ma mikewa tai tsaye daman can bata saka komai a bakinta ba tun zamanta gurin. “Ina da inda zanje ne, ayi breakfast Lafiya” Daga haka ta bar wajen, sai ya rage daga Nana Sai Ammy da Mama Fulani ne kadai a dinning din. “Zaki tashi ki wuce makaranta ko sai na bata miki rai? 9:14 ace baki shiga school ba, anya wai makaranta ma kike zuwa Nana” Ta mike tsaye tana kuka har da tara hannu a fuska ta fice rike da jakar makarantarta, kofar falon ta bude ta fara sauka saman stairs din kadan kadan har ta sauka gaba daya, sannan ta bude kofar corridor ta fice, ta sani sarai Ammy bata son ana bi ta fadarta idan za a fita amman ita da dan'uwanta abun ya zame musu al'ada ala dole sai ta nan za su fita ko su shiga bangaren Ammy.   Kwankwasa kofar tai fadawam dake can ta gaba suka bude mata da sauri suna gaisheta, ban da turo baki gaba babu abunda take har ta isa gurin direbanta wanda aja tanadar dan kaita school kadai ya faka motarsa, tun kan ta karaso ya fito ya bude mata mazaunin baya ta shiga ya rufe sannan ya shiga ya tashi motar suka fice. “Hajiya har da yau ma can zamu je?” “Eh kullum ma” Ta fada tana ta kara turo baki gaba. “Amman Hajiya idan aka gane ina cikin matsala” “To wa zai gane? Kai zaka fada?” “A a ni na isa ki sa amin daurin rai da rai, Wallahi ba zan taba fada ba” Ta yi yar dariya tare ta bude school bag din ta dauko 3k ta bashi, haka take masa kullum na rufe baki dan kar ya fada cewar ba makaranta take zuwa ba, a kullum X&Z Restaurant take zuwa tai zamanta sai idan direban ya auna lokacin komawarta gida yai sannan ya zo ya dauke ta.   UNCLE AA POV. “Sai sardaunan samarin Yola” “Yes amman na marasa galihu, komai kuke so za ayi da yardar Allah” Ya fada yana dagawa Wanda yai masa kirarin hannu, bayan ya gama ajewa na kusa da teburin Nana abinci ya kalleta, bachi take hankalinta kwance ta dunkule kanta yadda ba za a gane ko wacece ba. Ba yau ce ranar farko yana fara ganin yarinyar nan ba, yau kusan sati biyu kenan tana zuwa nan, kulluk kuma idan ta zo ruwa kawai rake order ta yi zaman awanin sannan ta tafi kuma kullum da uniform take zuwa, tunani kawai yake anya ba wani rashin gaskiya take tana gudo nan ba? “Ke Ke” Ya daki teburin, sai ta farka a firgice. “Na'am Na'am Na'am” Suna hada ta watsa masa harara ta turo baki gaba. “Miye bashi ko tara?” Ya dan wara ido sannan ya risino yadda babu wanda zai ji ya hade rai. “Me kike zuwa yi nan?” “Ina ruwanka ai na biya kudin ruwa” “Ruwa kawai suke kawo ki a nan? Daga gani wani laifin kika yi shiyasa kike zuwa ki boya or maybe kina gudun makaranta ne ko?” Ta yi saurin rufe baki tana zaro ido. “Karya kake ni bana aikata komai kuma bana gudun makaranta, yayana ne yace na rika zuwa nan ina jiranshi kullum” “Kullum yau kusan two weeks kenan!” “To wai ina ruwanka wai? Ba na biya kudin ruwa ba” “Ba kudin ruwa kawai ake biya ba sai kin biya kudin zaman da kika nai awoyi, dan mu nan karanci mutum yai zaman 2 hour ya tafi amman ke har bachi kike, ki biya kudin bachi da na zaman awoyi da kika yi” Ta bata fuska. “Wallahi ni ba zan biya ba haka kawai” “To ko zan saka security can ya fitar da ke waje kin ga dai akwai mutane ko za ki sha kunya” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya juya, sai ta ka karewa kowa kallo tana ayyana yadda zata sha kunya idan yai mata korar wulakanci a gurin wata kila ma akwai wadanda suka santa ita bata san shi ba. “Baka ji ba” Ya juyo ya dawo daman Kadan-kadan yake tafiyar yana jiran ta kira shi. “Nawa ne kudin bachin da kudin zaman?” Yayi wani shegen murmushi yana shafa kansa. “5k” Ya bude school bag dinta ta ciro kudin da zai kai 50k ta kirga 5k ta mika masa. “Gashi nan” Karba yai a ransa yana. ‘Shegiyar yarinyar ta gani diyar yar masara tausayin kasar ne bata san zafin kudi ba’ Aljihunsa ya saka kudin daman aljihunsa babu ko sisi, sannan ya juya ya bar gurin mutane da ke vip din suna ta kallonsa shi kam a jikinsa. FALMATA POV. Daga unguwarsu zuwa unguwar da take aiki akwai yar tafiya mai nisa sai dai ba sosai ba, wata kila kuma ita din ce bata ganin nisan unguwar sosai kasancewar ta saba da tafiyar kasa daga wata unguwar zuwa wata a cikin garin Yola tun mahaifiyarta na a raye balle yanzu da Umma bata tausaya mata bata isa ko wani garin tace zata aikata da kafa ta ki ba. Bata sha wahala gurin masu gadin masarautar da kuma polisawan da suke gurin ba kamar kwana biyu da suka wuce yanzu kam sun wayance ta ganin wannan shine zuwanta na uku bayan gabatar musu da ita da akai, sai dai a duk lokacin da zata shiga Masarautar ko ta fita sai ta rika jin tsoron dogarawan da kuma police din da suke gurin, domin Allah ya dora mata tsoron yan sanda sosai da sosai. Ko'ina na masarautar mutane ne wasu da uniform wasu kuma babu kasancewar safiyata ko wa sai aikin gabansa yake.   Ta kofar data saba ni ta bi ta dauki doguwar hanyar da ke sada mutum da bangaren Uwargidan Mai Martaba, tafiya ta wata karamar unguwar tsakanin Gate din karamar kofar gate din Ammy. Ta kofofin da ta saba shiga ta fi tana tafiya sai kara karewa gidan kallo take tana ganin kamar ba a duniya take ba, saboda yadda aka tsara gidan da kuma kwalliyar da aka masa, ta bangare daya kuma tana mamakin irin girman gidan wai ace duk ba mutum daya ne, bayan bangaren Ammy ga wani bangare can ta hango wanda aka ce na Amaryar sarki ce can nesa da shi wasu gine ginen  na da ta mutane na fitowa ko na miye oho ita dai kallo kawai take, ga wasu manya manyan motoci na alfarma an faka a harabar space din Ammy, wata kila can bangaren Amaryar ma akwai motocin ko ina ma bangaren sarkin yake oho. Ta fada a zuciyarta tana cigaba da tafiya tare da daga kanta sama tana kallon yadda aka jera windows din dakunan gwanin burgewa.   Sai ta isa bakin karamin gate din mai gadin gurin dake rike da bulalarsa ya dakatar da ita. “Ke ina zuwa?” “Ni ce Falmata wacce take gyara dakin yan uku” Ya mata wani kallo daga sama har kasa ya santa tun da wannan shine zuwanta na uku amman kullum ta zo sai ya mata tambaya, da gangan ya bata mata lokaci sannan ya bata hanya ta wuce. Da sauri ta raba ta wuce daman tsayar da ita da yai a gurin cikinta ya duri ruwa abun ka da mai tsoro, kamin ta karasa kofar shiga tsakar gidan dan ita ba ta falo take bi ba sai dai ta zagaya ta can baya kamar yadda aka nuna mata ta shiga ta inda mutane suke shiga haka ma idan zata fito. “Ke.....” Iya dake tsaye lullube da zane ta kwala mata fira fuska a murtuke kamar bata taba dariya ba daman kuma fuskar ba ta dariya ba ce. Suna hada ido Falmata ta fara karanto addu'o'i ta nufe ta sam hankalinta ba kwanta da matar da duk kuwa da bata san aikinta ko matsayinta ko alakarta da yan gidan ba, sai dai ta lura kamar batsa shan inuwa daya domin ko ranar da aka kawota sai da tace ba a dauke ta ba dan kawai Ammy na gurin ne tace a dauke ta, kusan kullum idan ta zo aiki gidan sukai arba sai ta ji gabanta ya fadi ga wani kallo tsana da iya take mata, sannan ta hana ta ganin yaran kullum idan zata fara aikin sai tace a dauke yaran kuma sai ta saka dogari ya tsare ta har tai ta gama. “Tafi tafi tafi tafi karki karaso nan” Iya ta fada yana runtse ido, ba karamin dadi Falmata ta ji ba, sai ta juya ta nufi hanyar shiga cikin gidan, sai da ta gaisa da mutane da yawa kamin ta samu isa bakin kofar farko ta falon Ammy. Haka ta ratsa falo kusan uku sannan ta isa gaban wata haraba tana kallon Hajiya karama dake tsaye a backyard tana kallon wani gurin dabam, Falmata ta kasa dauke mata ido, domin ta hadu iya haduwa tana da kyau sosai irin kyaun nan mai daukar hankali ga mayan ido sai dai ba manya can sosai ba, bayan tufafin jikinta mai kamada na turawa da ta saka wato English wears ta saki gashin kanta ya sauko sai tai kamar wata baturiya abun ka da Fulani. Ba karamin burge Falmata Hajiya Karama tai ba, domin fari na daga cikin abunda Falmata ta rasa kuma yake burgeta iya burgewa idan ta ga wani da fari sai ta ji kamar ta cire ta sakawa kanta, ba dan tana da siffar Fulani ba da kuma yaren da take ji ba zaka ka taba kallonta kace ita Fulani ce saboda bakinta. “Ko wacece? wata kila yar sarkin ce?” Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa a gurinta. Wani abun mamaki tana kwankwasa kofar corridor Iya ta bude mata tana watsa mata wani kallo mai kama da harara. Falmata ta bata yarda ta yi ido hudu da ita ba ta sanda kai kasa ta shiga. Kato falo ne mai cike da kayan alatu ga sanyin ac da katon plasma, an jera wasu ɗakunan daga gafe, kai tsaye stairs din ta nufa ta fara takawa a hankali saboda tana gudun kar tsantsin gurin yaja ta ta zame kasa, sai da ta waiga taga babu kowa bayanta sannan ta risina kasa ta shafa tile din, sai a lokacin ta tabbatar ba ruwa ba ne kuma ba mai ba, a iya tunaninta yadda take jin tsantsin gurin da yadda take ganin yana shining a zatonta ruwa ne ko mai duk kuwa da kasancewar bata jin ta taka abu makamancin haka.   Dan abun da aka nuna mata na jikin kofar ta danna wato door bell sannan ta ja ta tsaya sai rabon ido take, sai da ta danna shi sau kusan uku sannan aka bude mata kofar. Har kasa ta risina tana gaishe da Muhseen. “Ina kwana?” “Lafiya kalau” Bayan ya amsa ya juya yana kallon Momy wacce ke tambayar waye a kofar. “Wata ce ban santa ba dai shigo” Ya matsa daga kofar wanda hakan ya bawa Falmata damar shigo cikin falon mai kama da aljannar duniya. Da sauri ta fadi ta kasa tana gaisar da Ammy, Ammy ta amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta cigaba da danna wayar da take. “Ranki ya dade zan gyara dakinsu Yan uku ne” Ta fada muryarta kana ji kasan tsoro ne ya cika mata ciki fal, tsoron irin amsar da za a bata tsoron kallon matar sarki tsoron mutane da suke falon duka suka taru sukai mata tsaye a kai, kamin Ammy ta bata amsa har idonta ya soma cika da kwalla cikinta har murdawa yake kamar wacce tai wani laifi. “To ai kin san inda dakin yake” Ta yi saurin mikewa tsaye ta nufi corridor da zai sadata da dakin yaran, a nan ma wasu hadiman ne suke ta aikinsu, Falmata sai gaishe su take kowa ta gani sai tace nasa ina kwana da wanda ya kamata da wanda be kamata ba, ta kasa daga ido ta kalli kowa. Sai da tai Bismillah sannan ta kai hannu ta tura kofar dakin ta shiga har lokacin gabanta be daina faduwa ba, tsoron da take ji be gushe ba, haka take samun kanta a duk lokacin data shigo Masarautar, abun ka da wanda be saba shiga mutane sosai ba balle kuma manya kamar gidan Mai Martaba.   Wannan karon ba tai mamakin ganin Iya a dakin ba, daman ta saba ganinta a kullum idan ta shigo sai dai wani abun da yake bata mamaki yau kusan kwananta uku da fara aiki a gidan amman bata taba ganin yaran ba ko hotuna, a kullum kuma sai ta tararda Iya a dakin, haka ma a kullum sai Iya ta saka dogari yai mata gadin dakin har Falmata ta gama gyaranta ta fita.   “Ka sa ido, irin wadannan yaran ba abun yarda ba ne” Iya da fadawa dogarin tana wani yawo da manyan idonta akan Falmata kamar zata ciro su. “To ranki ya dade” Ya amsa mata yana risinawa sannan ta fice tana ta wani shinshine². Falmata dai bata ce komai ba bayan gaisuwar da ta mikawa dogarin har da risina masa, sannan ta hau gyare gyaren dakin tana yi tana satar kallonsa domin gani take kamar wani abu zai mata. Muhseen ne kadai zaune a dinning domin kowa ya karya a kama gabansa, wayar makkale a kunnensa yana ta fira da matarsa sai faman zuba murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin nishadi. Sai da ya gama breakfast din sannan ya yanke wayar ta taso ya nufo gurin Ammy yana fadin. “Wai har sun wuce ne?” Da kallo Ammy ta bishi tana murmushi har ya karaso kusa da ita ya zauna a kasa. “Ka dade kana bachi ne shiyasa” “Gajiyar jiya ce, gashi kuma yau zan kama hanya shiyasa na tsaya hutawa” Shiru tai na yan mintuna kamin ta kalleshi ta ce. “Yau zaka koma kenan?” “Eh daman Mama Fulani kawai na kawo, ba dan ma yamma yayi ba ai da tun jiya zan koma dan ina da aiki yau” “Ai ka kyauta shi Aliyu ya dauke mana kafa ko?” Muhseen yayi murmushi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa ya ce. “Shi ma zai zo soon da Matarsa” Ammy ta tabe baki. “Shi dai ya sani, babu ruwansa da dangi daga Momy sai Fulani su kawai ya sani a rayuwarsa, ko da yakeba laifinsa ba ne laifin Fulani ne da bata nuna masa ba” Ammy ta karasa maganar tana aje wayar hannunsa. “Ko da yake ga Shattima ne nan muna fama da shi, idan na ce yaje gurin yan'uwa kamar na kira masa mutuwa, sai dai azo a iske shi, wani irin jin kansu suke kamar wasu Sarakuna” “Ammy ai kara ma Shattima da Aliyu, tun da shi zai zauna ayi fira da shi kuma zai sakewa kanensa Fuska, Aliyu kuwa idan kika ga yana fira to da Mama Fulani ne ko matarsa ko Momy sai kuma Abba” Ammy ta tabe baki. “Uhm Abunda yai Aliyu shi yai Shattima idan ya ganka ne yake nuna shi na kwarai ne” Har Muhseen ya bude baki zai yi magana sai ga Iya ta shigo falon fuska daure. “Ranki ya dade wai yarinyar nan za a bari tai ta kula da dakin yan uku?” Ammy ta mata wani kallo cike da kasaita. “Akwai wata matsala ne?” “Ranki ya dade ni kam sam ban yarda da ita ba, kuma yarinya ce karama ina zata iya wani abun kirki, yanzu ga masu aiki bila'adadin a gida amman ace sai an dauko wata daga can waje ta zo gyara dakin jikokin Mai Martaba?” Kallonta kawai Ammy take na wasu yan dakiku kamin ya bude bakinta cike da kasaita ta ce. “To yanzu challenge dina kike yi Iya? Ko umarni kike ba ni?” Da sauri iya ta risinar da kai. “Ba ko daya ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya, shawara ce kawai ni kaina idan aka bar ni zan iya kula da su” “To Mahaifinsu yace baya bukatar kowa ya kula masa da su a nan sai daga waje, kuma shi yace baya son tsohuwa ko mai ƴaƴa, sai ki same shi ki bashi shawara” Kasa kasa Iya ta watsawa Ammy harara tana wani kashe ido. “Rana na zuwa Zainabu” Ta fada a ransa sannan ta juya ta fice bayan ta bawa Ammy hakuri. Sai da Iya ta fice sannan Ammy ta daga kai ta kalli Katuwar kofar ta dauke kai ta mike ta nufi hanyar dakinta. Tsab Falmata ta gyara dakin yaran daman can ba datti yai ba sai dai kullum sai ta tisa gyaran ne ta goge ta saka turare ta canja sanin gadon yaran, tana gamawa ta fice ba tare da ta yi ma kowa sallama ba. Sai da ta fito daga Masarautar gaba daya sannan ta samu sallama da natsuwar zuciya domin a yanzu har numfashinta take jin ya daidaita tsabanin idan tana gida bata son yin numfashi da karfi wai kar su ji ace ta yi laifi. Ta mika kafa sai tafiya take ita kadai a titin da babu mutane sosai, idan ka cire kofar Masarautar da a kullum take cike da mutane sauran makotansa kowa yana cikin gidansa sai idan fitar ta kama, unguwar manyan mutane ce mai kama da GRA, ko'ina manyan gidaje ne gwanin sha'awa.    Sai da ta shigo cikin gari sannan natsuwarta ta kara daidaita domin ta fi son unguwarsu fiye da wacan da take ganin kamar wata rana za a iya sace ta a can, da ganganta ta rage tafiyar da take ta soma tafiya kadakadan tana saurarin wakar Sirleem dake tashi a shagon wani mai charji, cikin zuciyarta take bin baitin wakar tana jin muryarsa na shiga har cikin kanta. 03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *Fadime dabam ta kauyen Katsina ita ce take jin busar sarewa. Falmata dabam ita ce ta Yola mai aikin raino a gidan Sarki, sai dai dukansu ana musu inkiya da Fulani. Fatar kun gane za ku daina rudewa 😀* *4* SIRLEEM POV. “Hajiya ina jin kamar ba zan iya jira har Nana ta kare Karatu na aureta ba....!” Ba Hajiya kadai ba gaba daya kanensa kallonshi su kai. Da Mamaki Hajiya tace. “Ban gane ba?” Ya cika ma bakinsa iska ya busar sannan ya shiga murza hannunsa kamar mai shafa mai. “Kawai dai bana iya jira, tana kula wasu bayan kuma kowa a Masarautar nan ya san ni zata aura, sannan ina ganin kamar yan gidansu basa son hadin nan nawa da ita idan abun ya kai wani lokacin za su iya lalata shi” Ajiyar Hajiya ta sauke. “Gaskiya ne, za su iya lalatawa amman zancen tana kula wasu kar ya dame ka kai auren a haka ai zata daina kuma idan ka gani ka rika magana” “Na ganta da Deen din nan da yake zuwa duba yaran Shattima, na je har Part din su na yi magana babu wance komai karshe ma Hajiya Karama ta taso tana fada ni wai ina takurawa Nana kamar wani ubanta” Hajiya ta yi murmushi mai kama da dariya. “Kar hakan ya dame ka Sirleem kai dai ka aureta kawai komai zai wuce” Ya kalleta cike da gajiyar jin abunda take yawan nanata masa idan yai mata complain akan Nana. “But Hajiya miyasa dole sai Nana? Tsakanin da Allah neman auren nan na saka kaina ne kawai saboda kin tirsasa ni amman ni kaina yarinyar nan bata kwanta min ba, ni kuma na fara gajiya gaskiya ba zan jure daukar wulakanci a gurin kowa ba na fi karfi haka, dan kawai tana yar sarauta ubanta yana sarki mahaifiyarta tana matar sarki yayanta yana dan sarki ba zan dauki wannan wulakanci ba na fi karfin wulakanci a gurin kowa ni” Ya fada yana daga kafadunsa, Rima ta tabe baki tana ture kofin tea dake gabanta tare da kallon yayan nata. “Ni kaina ba son auren nan nake ba, dan dai kawai Hajiya ta matsa ne akan ayi, amman miye amfanin hada alaka da makiyi alakar ma ta aure haba dai...” Murmushi Hajiya tai ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo bayan Sirleem ta tsaya. “M2 ba haka duniya ta sanka ba? Kai a yadda kake Celebrity sai kaje ka auri wacce bata kai ba? Ga yar sarauta yar masu naira kuma kyakkyawa yarinya mai kurciya a gidanku? Ba ka lura ba? Maran manyan mutane suna auren yar manyan mutane? A yadda kake sannen a duniya ai kamata yai ace ka auri yarinyar da ta isa gaba da baya, taya za a tashi maganar da kasan zata iya saka Mai Martaba a cikin wani hali bayan gashi kwance ba lafiya? Baka tunani ya takama mu sakawa Mai Martaba da irin hallacin da yai mana? Idan mahaifiyarta matar sarki ce kai ma taka uwar matar sarki ni da Zainabun Jirgi daya ya dauko mu domin dukanmu Mai Martaba muke aure. Ke kuma Rima da kike fadar hakan ai kyautatawa ce wanda yai maka sheri sai ka saka masa da alheri, ba ni da burin da ya wuce na ga Sirleem ya auri Nana a yanzu ku karfafawa dan'uwanku guiwa ba wai ku sare ba” Ta karasa tana kallon Rima. Sirleem ya juyo yana kallon mahaifiyarsa tasa. “Amman Hajiya ai ba Nana ce kadai yar sarauta ko yar masu arziki ba, akwai da yawa mi yasa ba zaki bar ni naje da kaina na zabi wacce tai min ba?” “idan zaka auro yar sarkin Makka, dan arzikinsu da Sarauta ba ka cika min burina ba matukar baka auri Nana ba, idan kuma zaka auri yar sarkin talauci na duk duniya bayan ka auri Nana to ba zai tana damuna ba, ni dai burina Nana ta zama uwargidanka” A hankali ya aje numfashi yana kallon kanensa wanda shi ma kallonsa yake suna mamakin furucin mahaifiyar tasu. Talba ya ce. “Amman Hajiya miyasa?” “Saboda ta wannan hanyar ce kawai zan iya sakawa mahaifinka da abunda yai mana” Gaba daya kanensa mata su uku tashi sukai daga dinning, kaf a duniya basa da makiyiya irin Ammy wato uwargidan Mai Martaba, su kam ba su da dalilin na cewa ala dole sai yayansu Sirleem ya auri Nana ba bayan shi kansa ba sonta yake ba. Da kallo ta bisu tana murmushi kamin ta kalli Talba ta ce. “Raheen a kira min Kulu” Tana fadar hakan ta nufi hanyar dakinta cikin wani irin taku kamar wacce ba zata mutu a saka a kasar ba, tsadadar shaddar dake jikinta sai motsi take tana wani maiko. Tashi Talba yai ya fita domin zuwa kiran Kulu kamar yadda ta Umarta, Sirleem kuma ya ciro wayarsa daga aljihu yana kallon kiran Mansura da ke shigowa wayarsa. Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuska babu annuri kamar ba ita ce dazun ta gama dariya ba, a zahirin sarkar gold din dake wuyanta wacce ta sauko har saman kirjinta take kallo a badini kuma zuciyarta na can wani gurin tana wani tunani na dabam,  stool din madubin ta ja ta zauna tana cigaba da kallon kanta abubuwan da suka faru a baya take tunawa, ta dayan bangaren kuma tana kitsa yadda wasu abubuwa za su tafi a nan gaba. Yanayin yadda take motsa bakinta kadai ya isa ya sanar da cewar zance zuci take. “Shigo” Ta fada tana dauke kai bayan an kwankwasa dakin minti uku da suka wuce. Kulu ce ta shigo dakin tana sanye da doguwar riga ta atamfa an mata irin dinkinsu na tsohu kanta lullube da mayafi, gaban Hajiya Bilki taje ta zauna tana mika mata gaisuwa. “Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya, Sardauna yace kina nemana” Tashi Hajiya tai daga kan Stool din ta koma saman shimfidarta da ke gefen gado ta kishingida tana kallon Jekadiyar ta ta. “Kulu wane Likita ne yake zuwa duba yaran Shattima?” “Wallahi ban san shi ba ranki ya dade” Wani kallo Hajiya tai mata. “Taya za'ayi kina cikin masarautar ace baki san masu shiga da fita a ciki ba?” “Ranki ya dade na ga kamar bangaren Ammy ne, ni kuma na fi kula da abunda ya shafi bangarenki ne Allah kara miki lafiya” “This is nonsense, Ammy da bangarenta ba a cikin masarautar nan suke ba?” Hajiya ta fada a tsawace har tana tashi zaune fuska babu annuri. “Ciki suke Allah ya baki yawan rai, tuba nake” Cewar Kulu tana kara noce kai kasa. “Kina da matsala Kulu, duk abunda ya kamata ki saka ido akai ba kya yi” “Zan bincika ko waye shi Allah ya huci zuciyar ki ya kara miki lafiya” “Kira min Jarma” “An gama ranki ya dade” Kulu ta mike da sauri ta fice daga dakin ganin yadda Hajiya ta hade rai kamar bata taba dariya ba. Ba a dauki dogon lokaci ba Jarma ya shigo dakin yana sanye da babban riga ga wani uban rawani a kansa, inda Kulu ta zauna ya zauna tana kallonta hankalinsa kwance sai dai har ya zauna ta kira shi ya amsa ta kora masa bayani bata kalleshi ba. “Jarma” “Hajiya” “Akwai wanda ke son shiga tsakanin Sirleem da Nana” “A cikin masarautar nan yake?” Jarma ya tambaya cike da mamaki, sai a lokacin ta kalleshi. “Bare ne, yaron da yake zuwa duba yaran Shattima” Jarma yayi murmushi. “Doc Deen? Kar hakan ya damu Salim, wayayyace kawai irin ta yan zamani ke kinsan ai ba zan bari wani ya dauki hankalin Nana ba” “Idan ma ka ga zai kawo mana matsala ko wasa, aka yi masa sanadi da gidan nan” “Baki da matsala da wannan Hajiya Salim ya cigaba da neman yarinya babu abunda za a fasa” Ta dan yi murmushi tana kallon wata doguwar Fulawa dake gabanta. UNCLE A A POV. Ya yamutsa shinkafa da waken dake gabansa a kwano yana bata fuska. “Anti Rabi sai ayi ta mana wake da shimkafa ba wani canji” Anti Rabi dake aikin damawa dabbobinta kasari ta yi dariya. “Hmm Unclen dinsu wani lokacin iskancin ka yawa yake, wani na can be samu kamar wannan ba amman kai ka raina, da alama dai kana da kudin cin wani abinci shiyasa” Ya shafa kansa yana yar dariya. “Wallahi kuwa wata yar marasa sanin darajar naira na samu nai mata na yan talakawa na ci kudinta” “Ban gane yar marasa sanin darajar naira ba” Yayi dariya a karo na biyu sannan ya labartawa Antinsa yadda ya yaudareta. “Amman dai Uncle din yara baka da tausayi” “Wane irin tausayi kina ganin yarinyar nan kin san yar masu abunce ce karamar yarinyar yar secondary school ta ciro kudi sun kusan 50k ta bani 5k ya maida saura, uwayensu ne barayin Jihar mu ai” Ya mike tsaye yana ciro kudi, 2k ya cire a ciki ya mikawa Yayar tasa sannan ya maida sauran aljihu. “Ni bari naje waje na ci abu mai kyau” “Ni wannan aikin na ku yana bani mamaki kuma aiki a restaurant amman ba zaku iya cin abinci a ciki ba?” “Ai wannan mutumen be da kirki ko ruwansa ka sha sai ka biya shi, zaka ci idan kana so amman zai cire a cikin albashinka” “Allah dai kyauta ni kam ban taba gani ba” “Ai ina samun wani aikin zan bar na shi Wallahi” “Allah dai ya kawo rabo mai amfani” Da amin ya amsa sannan ya fice daga gidan. Abun ka da unguwar mai mutane yana fita abokasa suka fara dago masa hannu. “Sai Sardaunan samarin Yola” Ya nufe su yana dariya. “Amman na talakawa” Ya karasa ya basu hannu suka gaisa sannan ya kara gaba ya siye alalen gwangwani gurin wata ya cika cikinsa a titi. Washe gari ma fa yaje restaurant din sai da ya sake tararda Nana a inda ta saba zama, wannan karon ba bachi take ba idonta biyu suna hada ido ta watsa masa harara ta kawardar da kai, a iya ganinta da yake yi a yanzu kam ya tabbatar karya take da tace yayanta ne yake cewa ta jira a nan, ya lura idan ta ga mutane sai ta boye fuskarta kar a ganta haka yai ta aikin raba ma jama'ar da suke shigowa abinci yana kallonta zuciyarsa na karantarta tana tsara masa yadda zai sake samun wasu kudin a gurinta.   Sai da ya koma gurin zamansa ya zauna sannan ya dauki biro da takaradar yai rubutu a kai ya dauki bottle water ya nufi inda take ya aje mata takardar a saman tebur din tare da ruwan ya koma ya zauna yana kallonta. Tun da ya nufota take turo baki tana harararsa har ya karaso ya aje mata ruwan da takardar ya koma, a zatonta zai ce yau ma sai ta biya kudin zaman dana bachi amman bata ji yace mata komai ba, sai dai ta lura duk abunda yake idonsa na kanta. “Ni nace ka kawo min ruwa ne” Ya fada tana turo baki cikin sautin da ita kadai zata iya jin kanta, na kusa da ita ko kuma mai kallonta sai dai yaga bakinta na motsi sai hararar da take watsa masa ta isa ta sanar masa cewar da shi take. Hannu ta kai ta dauki takardar ta jefar a kasa tana cigaba da turo baki ita ala dole ga shagwa6a66iya. “Ba za a karanta ba” Daga can inda yake zaune ya gwalo mata ido ya hade rai yana mata alamu da ta dauki takardar ta karanta ko ya daketa, sai ta make masa kafada tana murguda masa baki, sai da ya unkura kamar zai taso ta karaso inda take sannan tai saurin kai hannu ta dauki takardar ta bude. “Idan kina so zan iya kai ki wani guri inda zaki rika boyewa ba tare da kowa ya sani ba, amman nan ai public place ne kowa zai iya ganinki, idan kin aminta fita waje mu yi magana” Da sauri ta dago ta kalleshi tana gyada masa kai alamar eh ta amince din, da ido yai mata alama da waje sai ta dauki school bag dinta ta nufi hanyar fita tana waigensa. Sai da tai kusan minti biyar da ita sannan Sardauna ya fakaici idon mutane ya tashi ya fita. Can gefe ya hangota ta juya baya dan kar a ganta sai boye boyen fuska take. “Ke” “Ni ba ke ba ni Nana Aisha” “To ina ruwana da wani sunanki” “To nima ina ruwana da kai” Ita ta amsa masa ta shigar da yai mata maganar wato da fada fada, sai yai kwafa ya juya alamar zai tafi ya barta, da sauri ta riko hannun rigarsa. “To akwai ruwana” Ya sake yin kwafa sannan ya kalli security camera dake gurin ya kalleta. “Idan kina so zan iya kai ki gidan ku sai ki boya a can idan lokacin da direban ki zai dauke ki yayi sai na dawo da ke” “Ina zuwa” Ta fada kai tsaye cike da jindadi, kallonta ya tsaya yi a ransa yana ayyana cewar idan shi barawo ne sai ya sace ta salon alon. “To ai zamu aro babur da zamu je can unguwar” “To aro” “Zaki hau?” Ya tambaya da mamaki dan be dauka zata yarda ba. “Eh” “To ai kudi ake biya kamin a bamu aron babur din” “Nawa?” Tunani ya tsaya yi kamin ya ce. “2k kuma a can gidan da zaki zauna sai kin biya kudin zama” Ta dan bata fuska. “Nawa?” “3k” “Toh, ai dai ba zaka sace ni ba ko?” “Eh shekararki nawa?” “16” “Amman dai ke wawuya ce” Ya fada yana dariya a ransa sannan ya juya ta nufi cikin restaurant din, abokinsa Mu'az yai ma magana ya karbi makulin mashin dinsa sannan ya fito ya same ta a inda ya barta. “Ki fita can titi sai na zo na dauke ki” Ba musu ta kama hanya a ranta tana jin zafin wawuyar daya kira ta dazun, karasa yai gurin da suke aje abun hawan a gurin ya bude mashin din sannan yasa masa key yai tashi mashin din sannan ya fara tukawa ya fito da shi bakin titi can ya hangota ta boya a kusa da wani shago, karasa yai gurim ya faka mata ta hau yana fara tafiya ta rirrike shi gam ta boye fuskarta a bayansa, kusan sai ta rantse a rayuwarta bata taba hawan achaba ba, iyakarta keke shi ma tana yin wayo Ammy ta hana ta hawa saboda tana mace. “Ke dallah sake ni kin wani rike ni kamar yar iska haka zan shiga da ke a unguwar mu kina tabani, ni ba dan iska ba ne ba a saba ganina da mace ba balle kuma ta rike ni” “To ni ba tsoro nake ji ba ko kuma ni aka ce masa yar iska ce, ni yar iska ce kai ne dai dan iska mai sato yarinyar mutane kaje ka kaita wani guri ta boya” Ta fada tana turo baki har lokacin bata yarda ta dago kanta ba. Tafiyar ba tai nisa ba ya faka mashin din gefen titi ya sauko ya fuskance. “Ni ne ma dan iska mai sace yaran mutane? Ai ke ce stupid girl mai guduwa daga makaranta kina boya a wani guri, kuma ba zan kai ki din ba na fasa” Ya karasa yana dangwararta da yatsansa. “Ai Wallahi ba zan sauka ba, zan maka ihun ka yi satar mace” Yadda ta daddage kan mashin din kamar na gidansu tana watsa masa wani kallo ya sani sarai zata iya iya masa ihun abunda ba halinsa ba, kwadayi yaja masa bala'i, ya san ma it's risk tsayinsu a gefen hanyar dan wani wanda ya santa zai iya ganinta da shi, ba shi da wani option da ya wuce kaita gidansu din ko kuma maidata inda ya daukota. Da farko yayi kudirin maidata inda ya daukota sai dai zuciyarsa na son kudin nata da yake gani kamar na banza a dole ya daure ya cije ya cigaba da tafiyar idan ta riko shi ya buge hannunta har suka kusa isa unguwar sannan yai mata dabara da ta rike karfen mashin din ta sake shi. Bata yarda ta dago fuskarta ba sai da ya faka mashin din kofar gidansu ya sauka sannan ita ma ta sauka tana wani kyankyamin unguwar balle kuma da aka shiga cikin gida har wani dage kafa take sama sama kar ta taka kasa. Shi yai sallama Anti Rabi dake aikin hada kwado ta amsa masa, ita kam banda aikin bata fuska da karema gidan kallo babu abunda take. Anti Rabi ta bishi da kallo har ya shiga dakinsa Nana na biye da shi ya dauko tabarma ya shimfida mata bakin kofar Anti Rabi. “Zauna a nan” Ta karewa tabarma kallo tana kyankyami. “Wallahi ba zan zauna ba, wannan gida duk kazanta ni ba na son nan” Ya zaro ido “Kan uban gidan na mu ne duk kazanta? Idan ba ki zauna ba zan bata miki rai” Ya fada a tsawace amaimakon ta ji tsoro kamar yadda yaran Anti Rabi suke idan yana musu fada ita sai ta make kafada. “Wallahi ba zan zauna ba, gida duk datti gidan dokin mu yafi wannan” “Zan zane ki zan miki bulala” Ya fada yana nuna mata icen dogon yaron dake gidan, sai ta sake make kafada. “Wallahi ba zan zauna ba, kuma ba zan koma can ba, kuma ba zan biya kudin ba” “Na rantse da Allah karya kika sha” Ya fada yana buga kafa a kasa dan kudin sune damuwarsa. Anti Rabi ta tashi ta shiga dakinta jikinta na bari ta kwalowa kanen nata kira. “AA...” “Tsaya nan sai na fito” Ya fada mata bayan ya amsa kiran Anti Rabi, sannan ya nufi dakin ya cire takalminsa ya shiga cikin rada Anti Rabi ta fara masa magana har lokacin jikinta rawa yake dan tsoro ya gama kamata. “Ina ka dauko wannan yarinyar?” “Ita ce wanda na baki labari jiya” “To miyasa zaka dauko ta ka kawo nan? Kidnapped dinta zaka yi?” “A'uzubillahi haba Anti kamar dai baki san ni ba? Ce mata zan kaita inda zata boya sai ta biya kudin” Hannu biyu Anti Rabi ta hada tana rokonsa. “Dan Allah dan Annabi ka rufa min asiri ka maida yar mutane, karka jamin masifa ka jawa kanta, daga ganin yarinyar nan yar manyan mutane ce, ka duba kaga irin kallo da ake mana a unguwar nan na masu rufin asiri amman ita kallon kazamai ma take mana har da cewa gidan dokinsu ya fi gidan nan kyau ka rufa min asiri ka maida ta karka sake kallonta ma kar sheidan ya sake raya maka wani abun” “Anti Rabi.... ” “A a bana son jin komai indai kana jin maganata ka maida yarinyar nan inda ka dauko ta dan Allah” Juyawa yai ya fito daga dakin, sa cin karo yai da Nana tsaye a kofar dakin da alama labe tai musu. “Wallahi ba zan koma ba, sai direbana ya zo kuma ba zan zauna a nan ba” Anti Rabi ta fito da sauri ta hade hannayenta ta risina har kasa tana rokonta. “Dan Allah dan ma'aiki ki rufa mana asiri yarinyar nan ki koma inda ya dauko ki” Ta make kafada daya lallai ita ba zata koma ba. “Sai idan direbana ya zo” “Haba Anti ya zaki duka kina rokon yarinya kamar wannan dan Allah tashi” AA ya fada cike da jin haushin yadda yayar tasa ta risina tana rokon Nana, wanda hakan ba karamin dadi yai ma Nana ba domin ko a gidansu aka risina mata dadi take ji tana ganin an bata girma yadda ya kamata tun da Mai Martaba ba ma haka ake masa. Anti rabi bata bi ta kansa ba ta ce. “Yanzu ya kike so a yi?” “Sai ya duka ya roke ni yadda kikai” “Ni din? Ashe ko zaki tsufa a tsaye” AA ya tambaya yana kallonta da mamaki ganin take kokarin zame masa kashin wuya. “Ba zan zauna akan wannan ba” Ta nuna tabarma sai Anti tace. “Idan na dauko miki katifa na shimfida miki a waje zaki zauna?” Tayi wani abu da kai kamar mai yanga sannan ta amsa da eh. Abun ka da mai nema cikin sauri da kuzari Anti Rabi ta dauko katifar dake kan gadonta ta aje a waje ta dauko zanin gadon data wanke ta ninke ta shimfida mata har da su filo. Sai da Nana ta karewa katifar kallo sannan ta cire takalminta ta hau ta zauna tana kara karewa gidan kallo. Anti Rabi ta kuma ta cigaba da hada kwadon da take cikin rashin natsuwa dan ita tsoro ma take kar wani wanda ya santa ko ya san yan gidansu ya shigo ya ganta a gidanta. Bayan ta gama ta zubawa AA ko da wasa batai ma Nana ta yi ba dan ta san ba zata ci ba, ita dai tana zaune tana kallon yadda AA yake aikin auna kwadon a bakinsa kana gani kasan yunwa yake ji. “Gashi nan ba kiba sai mugun ci” Ta fada a ransa, kamar ya san ta yi maganar sai ya juyo ya kalleta. “Za ki ci?” “Allah ya tsare ni da cin ragin abincinka kazami da kai ma” Ta fada tana dauke kai, har cikin ransa ya ji zafi ya kalli Anti sai tai masa alama da yai shiru, a iya tunanin Anti Rabi yarinyar tana neman rigima ne ayi mata wani abu taje tace an taba ta babanta yasa a dauresu ita da AA duk kuwa da kasancewar bata san waye uban nata ba. Sai karfe daya da yan mintuna direbanta ya kirata ya fada mata cewar zai zo ya dauke ta yanzu, sannan ta tashi wanda yai daidai ta dawowar yaran Anti daga makaranta. “Ki ce masa ya maida ni” Ta fada ta sigar Umarni kamar yadda take wa bayin gidansu. Anti  Rabi ta kalli AA dake aikin danna karamar touching dinsa tace. “A-A tashi ka kaita” Ba musu ya mike tsaye ya saka wayar aljihu. “Ina kudin zaman da kika yi dana katifar duk sai kin biya” Ta bude jakarta ta kirga kudin da za su yi 8k ya mikawa Anti. “Gashi na zaman da nai da na katifarki, ai ba gidanshi ba ne ba katifarshi ba ce” AA ya saki baki yana kallonta. “To waya kawo ki gidan? Ki bani kudina malama” Ta maida ragowar kudin. “Wallahi ba zan bayar ba, kai da kace min ma kai dan iska” Anti ta zaro ido. “Subhanallahi AA” “Na rantse da Allah karya take wannan yarinyar munafuka ce” Ya karasa yana kara dangwararta a karo na biyu bayan wanda yai mata a titi. “Kin gani ko haka dazun yai min a titi dan yace na taba shi na ki wai sai dai na rika taba shi idan muna kan babur din hadda cewa yai zai sace ni” Bayan kallon Anti Babu abunda AA yake, gaba daya kunya ta gama rufe shi shi da ko budurwa be taba yi ba yau ace wai yana neman mace ta taba shi, ji yai kamar kasa ta rabi biyu ya shige ciki, Anti ta kasa cewa komai sai kalloshi take da mugun mamaki. “Kaje ka aje ta inda ka dauko ta” Ta masa maganar da sigar da shi kansa ya san ba da wasa take ba. “To” Ya juya sululu ya fice, Nana ta risina ta aje kudin da Anti ta ki karba saman katifar sannan tai mata sallama ta fice. Ko da ta fita har ya tashi babur din ita kawai yake jira, kamar dazun yanzun ma tana hawa ta sake rike shi sai da ya buge mata hannu sannan ta maida kan karfen baya ta boye fuskarta a bayansa. Tun da suka kama hanyar bata ji yace mata komai ba, a tunaninta zai mata magana ko yai mata fadan karyar da tai masa a gurin yar'uwarsa amman sai taji shiru. “Ni ba zan sake biyoka ba” “Ki ga ma Uban da zai sake zuwa da ke, ko a restaurant din nan na sake ganinki sai na fadawa shugaban mu yasa an koreki” Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba. “Ka yi hakuri ba zan sake ba” Be ce mata komai ba har suka kusa isa, sannan ya faka gefen hanya ya sauka kan babur din ya kalleta. “Ba ni 5k dina, kin ga dai taimakonki nai ko? Dan Allah ki bani kudina dan Allah” Bata ce komai ba sai kallonshi take. Hakan yasa ya koma rokonta ta sigar tausayi yana mata magiya a iya ganinsa idan ta tafi ba ta bashi kudin nan a yayi aikin banza kenan. “Haba baiwar Allah, ki ji tausayina kin ga nan ni maraya ne ba uba ba uwa komai ni nake yi ma kaina kuma gashi ba wani aiki sai na restaurant dan Allah ki ba ni kudin kinji?” “Ba kace ba zaka sake kawoni ba” “Zan sake kawoki, mota ma zan aro ba babur ba kin san ya fi sirri” Ya amsa mata da sauri. “Ka iya mota?” “Eh” “Idan kana zo zan iya maida kai direbana sai ka rika kawo ni nan kullum idan lokacin tashina yayi sai ka maida ni gida” “Da gaske?” Ya kara masowa kusa da ita. “Eh yau zan ce ma Ammy bana son driver din ta canja min wani” “Kuma zata amince?” “Eh” “To kawo wayarki na saka miki number ta idan ta amince sai ki kirani” Ta bude jakarta ta dauko iPhone yar yayi ta kunna sannan ta mika masa. “To sa min a nan” Da mugun mamaki da kuma dan tsoro ya karbi wayar, how yarinya karama kamar ita ace tana rike irin wannan wayar? Lallai babanta ba karamin barawon kasa ba ne. “Waya saya miki wayar?” Ya tambaya bayan ya saka mata number. “Ammy na ce ta siya min bata siya min ba, Ya Shattima idan na masa maganar baya sai ya ce sai na gama makaranta, Hajiya Karama ce ta siya min?” “Wacece Hajiya Karama?” “Yayata ce” “Waye mahaifinki Nana?” Ya tambaya mamaki na kara bayyana a fuskarsa, har ta bude baki ta bashi amsa sai kuma ta fasa bata son ya san asalinta gudun kar ya tona mata asiri ko kuma ya sace ta. “Wani ne ba shi da lafiya ma, baya son mutane idan an yi taro da yawa sai ya rika jin tsoro shiyasa baya fita muma ba kullum ake bari muna shiga ba, ance wai sammu ne wasu kuma su ce jiface amman dai Ammy tace mu daina cewa haka mu rika cewa be da lafiya kawai” Ya maida wayar a jakarta bayan ta kashe, wannan karon kallon tsoro yake mata sai a yanzu yake fahimtar yaren da Anti Rabi take masa, wata nawa yana kokarin ganin ya canja wayar hannunsa ya siye ko ta 50k amman abun ya gagara, yau sai gashi yaga karamar yarinya da wayar 500k lallai mayan kasar nan ba karamin dadin rayuwa suke ji ba, ya raya a zuciyarsa a take sai yaji ya ba kansa tausayi matuka. “How babur na maida ke” Bata ce komai ba ta bude jakarta ta ciro 7k ya mika masa. “Gashi” Ya kalli kudin be karba ya ce. “Wa yake ba ki wadannan kudin?” “Hajiya Babba” “Mahaifiyarki?” “A a Step mother dinta, wani lokacin kuma Hajiya Karama ma tana ni kudi sosai idan ta samu Ya Shattima ma yana bani amman ba sosai ba, sai Ya Sirleem shi ma yana ba ni sosai, ka karba” Ya kara mika masa, ya dade yana kallon kudin da mugun mamaki sannan ya karba yana tunanin anya ma mutum ce? Ko dai garin shegen son kudinsa ya kwaso aljana? Yanzu akwai yarinya karama mai rabon kudi haka dan bata san zafin su ba? Ya hau babur din ita ma ta hau baya suka cigaba da tafiya, be yarda ya isa har cikin restaurant ba ya sauke ta a titi ya shiga ciki, ita kam bata ma shigo ciki ba sai ga direbanta ya zo daukarta sai kawai ta shige mota suka kama hanyar gida. 03/12/2021, 08:07 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *5* HAJIYA KARAMA (Zainab) POV. Ta bude motar ta fito tana karewa gidan kallon kamar wani bakonta, ko da yake kusan gidan bakonta ne domin tun zuwanta na farko ba ta sake ba sai yau, Zainab irin matan nan ne da basa bin kawaye sai dai kawaye su bi su dan suna jin sun isa, tana ji da Sarautar da ba ta jininta ba tana jin naira ga kuma daukaka da ta samu sakamakon aikinta na daukar hoto wanda ba kasafai kake mace bahaushiya kuma musulma tana yi ba, bayan daukar hoto Zainab fitattaciyar yar daukar wanka ce  Instagram hakan yasa hotunanta suka yawo a duniya kamar wata yar film ko mawakiya ga kuma kyau da Allah ya hore mata da cikar sura irin ta ya mace.   Katon bakin gilashin idonta ta cire tana kara kallon mijin kawarta da kyau, sai ta ga yafi kyau a fili ma fiye da hoton da Humaira ta dora lokacin anniversary su. Daga inda take tsaye sanye da dogon wando na jean da half gown ta atamfa kanta da jar hulla waccw ta bayyana rabin gashin kanta daya sha gyara, ta daga masa hannu alamar HI tana wani yauki da fingers dinta kamar ba farata ba sai wani murmushi take masa na daukar hankali. Da mugun mamaki ya dago mata hannun shi ma wai celebrity ta dago masa hannu da kanta ya santa dan yana daya daga cikin followers dinta na instagram, secondly kuma Humaira na yawan ba shi labarinta ta nuna masa hotonta ya fi a kirga third kyauta ya wuce yadda yake ganinta a hoto domin a fili farinta har wani haske yake kana ganinta ka ga yar fulanin asali kuma wayayyiyar mace. “Ba laifi bayan kyau kana da naira” Ta fada a ranta tana karewa tsaddadiyar motar da yake kokarin hawa kallo, sannan ta doshi cikin gidan tana wani irin taku na daukar hankali, murmushi ya cika kyakkawar fuskarta ko ba komai zuwan da tai yau saboda mijin kawarta ne domin tun a lokacin fa Humaira ta saka shi a status dinta na happy anniversary ta ji ranta ya biya, kuma bukatarta ta biya tun da ta yi arba da shi. Door bell din ta danna in few minutes house help din Humaira ta bude mata kofar, sai ta nasa kafarta a katon falon tana kare masa kallo, a ranta ta raya ba laifi ita kam ta ga gurin zama. Cike da far'ah da jindadin ziyarar Humaira ta fito ta rumgume ta. “Oyoyo manyan kasa yau ke da kanki Hajiya Karama” “To ya za'ayi muna so ne ai dole mu biyo, ykk” “Lafiya kalau ya gida ya su Hajiya da Ammy” “Suna nan kalau ina yaranki?” “Suna makaranta” Ba laifi Hajiya Karama ta saki jiki suka sha fira da Humaira har abun ya bawa Humaira mamaki domin ba kasafai Hajiya Karama take sakewa tai fira da kawaye haka ba no matter how close they are, ita din tana da wani irin jin da kai da isa idan ana fira sai dai ta rika jefo zance can sama-sama, hakan kuma be hana kawaye binta domin tana kashe musu kudi kamar bata san zafinsu ba, ga kyauta da alheri ga kowa. “Bude min wayar na ga hotunan anniversary tun da ba a fada mana ba” Ba musu Humaira ta cire mata password tana dariya tare da fadin. “Ba mu gayyaci kowa ba fa daga ni sai yara mu kai sai uban gayyar” Cikin hotuna Hajiya Karama ta shiga tana dubawa, sai da ta bari Humaira ta tashi sannan ta shiga long calls dinta tana bin numbers din da kallo, number da aka sakawa Alone da hoton heart ta bude tayi copying digit din ta shiga message ta saka number ta ta aika ma kanta da number sannan ta goge sakon ta aje wayar tana murmushi. “Humi zan wuce daman na biyo ne kawai na gaishe ki” Har gurin motarta Humaira ta rakota tana ta mata godiya domin ba karamin dadin ziyarar taji ba, ba ta bar Hajiya Karama ta wuce ba sai da su kai hoto. Cikin farinciki ta dawo Masarautar ranta fes domin ta samu abunda take so, part din Ammy tai parking sannan ta fito tana wani irin taku na kasaita kamar wata yar sarki ta shiga cikin gidan. Ko kallon mutane dake gaisheta ba su isheta ba, balle har ta amsa gaisuwar da suke miko mata, yadda take lumshe ido ta bude ma kadai wani abun kallo ne. A natse ta shiga katon falon na Ammy, babu kowa a ciki sai plasma da Ac dake ta aiki bada sanyi, ta kalli farantin dake cike da sweet an dora shi saman kujera, ko ba a fada ba ta san aikin Nana ne ko Yusra. Kusa da farantin ta zauna ta bude wayarta ta soma dannawa, can kuma ta kai hannu ta dauki sweet din ta bude ta fara sha. After like 30 minutes Ammy ta fito daga dakin sanye Holland Nana na rike da gyalen nata tana kuka kamar wata yar 6 years. “Baby what happened?” Hajiya Karama ta tambaya tana kallonta cike da kulawa. Nana kamar mai jira ta saki hannunta ta dawo gurin Hajiya Karama ta zauna tana kukan da ba hawaye. “Ammy ce Hajiya” Hajiya Karama ta kalli dake kokarin zama a dinning. “Ammy me aka mata?” “Iskancinta ne ya motsa” Ammy ta fada ba tare da ta kalli inda suke ba. Hajiya Karama ta kamata ta dawo da ita saman kujera ta zaunar da ita. “Fada min me kike so baby?” “Wai na ce ma Ammy bana son driver dake kai ni school a canja min shine tace wai ba za a canja ba” Ta karasa tana rushewa da kuka kamar gaske alhalin idon nata ko hawaye babu. Hajiya Karama ta kalli Ammy. “Haba Ammy dan wannan dai?” “Ki tambaye ta me direban yai mata da za a canja shi? Tsabar iskaci da jindadi? Wata na can kullum a kafa zata je makaranta ta dawo a tsakar rana ke dan kin samu ana kai ki a dauko ki a mota da ac da komai ki dawo mana wani zance na banza yanzu” Hajiya Karama ta kalli Nana. “Mi driver yayi miki?” “Hajiya Tsoho ne fa, kan shi har da hurhura ni bana son gani” Ta karasa da kukan da ba hawaye tana buga kafa kasa, Hajiya Karama ta mike tsaye ta nufi dinning room taja kujera ta zauna tana kallon Ammy. “Haba Ammy idan ba yi ma Nana abunda take so ba wa za ayi ba? Canja driver ba wani abu ba ne fa, ita yake kai wa kuma ya dauko idan bata ra'ayinsa ba dole” Ammy ta tsayar da cin abincin da take ta kalli Hajiya Karama. “Nana da ban isa na saka ta aiki ba, ko kofi na ce ta dauko yanzu zata ce min ta gaji jikin ta ciwo yake bla bla bla iskanci kala kala, tun dazu na ce yarinyar nan ta dauko min abin ci na ci a daki ta ce min kafarta ce ciwo, na ce taje waje ta kira min wani daga masu aikin gidan nan a kawo kin abinci a daki na ci tace kafartana ciwo ba zata iya sauka kasa ba, and now kina tunanin tace na canja mata driver saboda wani selfish interested na ta kuma na yi saboda ita ta haife mu” Shiru Hajiya Karama tai, ita kanta ta sani idan halin Nana za ayi mata abu to ba za a mata ba, domin ko ita da take mata gata bata isa ta saka ta aiki ba, wani lokacin ko cewa tai ta dauko mata abu sai tace kaza nata ke ciwo bata iya tashi. “Gurin Mai Martaba janye na fada masa, ai Wallahi shi komai na ce ina so yi min yake, yana so na” Nana ta fada cikin daga murya dan Ammy ta jiyota domin akwai tazara sosai tsakanin falon da dinning room di. Ammy ta juyo daga inda take zaune tana nuna Nana da yatsa da fuskar dake nuna babu wasa a tare da ita. “Kin fi kowa sanin halin da Mai Martaba yake ciki, Wallahi ko da wasa kika kuskura taba kofar dakinsa da sunan kai masa complain sai na baki mugun mamaki Nana kuma ki gwada” Tashi tai ta fice tana kuka kamar gaske. “Zainab ki daina biye Nana kuna kara lalata, duk abunda take da gangan take dadi ne yake mata yawa” Ammy ta fada ba tare da ta kalleta ba, domin har cikin ranta bata jindadin yadda Hajiya Karama, Shattima da Hajiya Babba suke yi ma Nana. Hajiya Karama ta yi murmushi tana mikewa tsaye. “Ai mun kusa bar miki gidanki Ammy, ina yin aure zan dauke Nana mu tare a can” “Auren da babu rana” Ammy ta fada tana tabe baki, sai Hajiya Karama tasa dariya. “No very soon Ammy, domin na samu wanda na ke so” Ammy ta kalleta. “Da gaske?” “Wallahi Ammy, yana da mata daya yara uku ban dai san real name dinsa ba amman dai ya min, ban fada masa ba but very soon zan sanar da shi ina son shi kuma zan aure shi da gaske” Magana Zainab take kamar abunda take fada ba komai ba ne. Ammy ta kalleta irin kallon nan na mamaki da tunani. “Ke za ki ce kina son shi? Ban gane ba” “Yeah normal ne ai Ammy” Tana fadar hakan ta nufi hanyar sauka downstairs dake dinning, bata son tsayawa kar Ammy ta fara karanta mata wasu haruffan da ba zata iya hadasu ta tada ba. Tana saukowa, ta nufi dayan stairs din da zai sadata da bangarenta ita da mahaifiyarta, kamar ta wuce dakinta sai kuma ta nufi dakin mahaifiyar ta ta. Zaune ta same ta hannunta rike da wuri, sai dai ganin Zainab din yasa tai yi saurin boye wurin a bayanta ta kalli yarta ta manya idanuwanta da suka rine su kai ja kamar barkono. “Na fada miki ki daina shigo min daki babu sallama” “Na manta ne” Ta fadi hakan bayan ta zauna kusa da ita, sannan ta bude wayarta ta shiga gallery ta kamo hoton mijin kawarta ta nuna mata. “Iya kin ga surukinki” A razane Iya ta kalleta kamin dubanta ya kai gurin hotonta sai da ta kare masa kallo sannan ta dauke kai ta hade rai. “Shi kika zabo bana?” “Yes kuma wannan karon da gaske aurenshi zan yi, mijin kawata ne, thought dai ban fada masa ina son sa ba amman zan fada masa soon” “Zainab kenan, kin san miyasa ake kira da Hajiya?” Iya ta tambaya tana kare mata kallo, kamin Zainab tace komai Iya ta bata amsa. “Saboda ina son ki zama isashiya, tun da aka haife ki na saka mahaifinki da kansa ya rada miki sunan Zainab uwargidan Mai Martaba, ni da kaina nai miki lakani da Hajiya sai dai ganin akwai wata Hajiyar matar Mai Martaba ta biyu yasa ake kiranki da Hajiya Karama, so a komai ki isa, kuma ki amsa sunanki yadda Mahaifiyar Shattima take matar Sarki kuma uwar Yarima da Gimbiya ke ma ki taka wannan matsayin” Zainab ta tsotsa mintin dake bakinta tana jin maganar Iya na wuce mata ta bayan kunne. “Iya ba mu da gadon Sarautar nan fa karki manta, kuma ni bana son wani an mutu an dawo, finally dai na samu miji kuma shi zan aura that's all” Tana gama fadar hakan ta mike tsaye ta fice daga dakin dan ba gane yaren mahaifiyarta take ba. Iya ta bita da kallo har ta fice sannan tai murmushi ta fiddo wurin dake boye a bayanta. “Ba ki da miji a waje Zainab, mijinki a cikin masarautar nan yake, idan ba mu da gadon sarauta to ya kamata jikokin mu su gaji sarauta.....” Ta karasa tana daga wani bakin kullin da aka nade da zare kamar laya ta matsashi. “Mai Martaba ko kuma Labib?” Ta tambayi kanta tambayar da ita kadai ta san amsarta tana lasar bakinta. FALMATA POV. “Sallamu Alaikum wai an ce ana sallama da Falmata a waje” Almajirin ya fada yana tsaye daga bakin kofar gidan. “Falmata aka ce ko dai Naja?” “Falmata” Ya amsa mata, sai da tai kamar tace aje ace tace ba zata zo ba, sai kuma ta tuna da yan kudin da take shigo mata da su na zance. “Tashi ki tafi” Falmata kamar tana jira ana fadar hakam tai saurin mikewa ta saka Hijabinta ta fice, Tumba taja tsaki. “Ni wannan abun mamaki yake ba ni, kamar a kasa nake zubarwa, a maimakon abu ya ragu sai karuwa yake na Naja na raguwa?” Ta fada slowly tana mamakin lamarin Falmata. Da mugun far'a Falmata ta fito dan ta san mai kiran nata Maniru ne, har zumudin zuwansa take saboda yana kunna mata wakar Sirleem M2 audio da video, wannan ya saka duk a cikin samarinta ta fi kaunarsa. Sai da ta fara masa sallama ya amsa mata da murmushi suka gaisa sannan ya zauna a dakalin dake kofar gidan suka dasa hira, can kuma ya kunna mata wani sabon video da M2 ya fitar, tsabar zumudi da farinciki sai ta ji kamar ta rumgume shi. Bayan sun gama zance ne ya bada dari uku da lemun yanka a leda, cikin kunya ta karba domim har ga Allah bata son karbar abu a hannun wani sai dai ta sani idan ya koma cikin gidan ba tare da komai baa Tumba za ta iya mata fada ko ma ta doke ta. Cikin natsuwa ta shigo cikin gidan ta nufi inda Tumba take ta aje mata ledar lemun a gabanta sannan ta mike mata kudin da hannu biyu. “Gashi ya ba ni” Kallonta kawai Tumba take irin kallon na mamakin yadda take tsallake duk wani abu da take mata. “Umma” Falmata ta kira sunanta ganin kamar bata san ma tana mika mata kudin ba, sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya sannan ta karbi kudin ta kuma kalli Ledar. “Dauki daya” Cikin ladabi Falmata ta saka hannu ta dauki lemun daya kamar yadda ta bata umarni ta nufi dakinsu, tana shiga tai shirin bachi babu komai a fuskarta sai murmushi yau kam ranta fes ta ga sabon video M2, har ta kwanta sai kuma ta tashi tana rare wakarsa a hankali tana rawa tana kallon inuwarta wacce kyandir ya haska, sai ka rantse da Allah ba Falmata bace yarinyar da ko a hanya ka hadu da ita ba zaka taba saka ran tana magana ba. Sai da taji motsin shigowar Naja sannan ta yi addu'ar bachi ta kwanta. Washe gari ma kamar ko yaushe, sai da ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta saka wasu tufafin ta fito ta sha kokon da Tumba ta dama, kamin ta sake mika mata wani rubutun ta karba ta sha da Bismillah. Sannan ta fito ta kama hanyar zuwa gurin aikinta tana tafiya a natse, kana kallonta ka ga natsantsiyar yarinya mai kamala da tarbiya. Ba ta yi mamakin sake karo da Iya a Harabar gidan ba, domin kusan kullum sai ta ganta a gidan duk da bata san aikinta ko alakarta da masarautar ba, amman ta tabbatar da ita din wata babba ce a ciki. Ta gaishe ta kamar yadda ta saba sai dai Iya bata amsa mata ba yau kam ko kallon inda Falmata take Iya bata son yi. Sai dai gaishe da kowa sannan ta wuce cikin gidan, a tsanake ta hau stairs din ke sada mutum da falon Ammy sannan ta danna door bell. after like 5 minutes Shattima ya bude mata kofar, wani irin jan numfashin Falmata tai ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallon Shattima idonta a waje kamar irin ka ga wanda ka dade ba ka hadu da shi ba ko kuma kake mafarkin gani, ba ido kadai ba har bakinta a bude yake a wannan lokacin. Shattima kan sakin kofar yai ya dawo falo ya zauna yana taba wayarsa daman indai shi zai ce mata ta shigo ko ya tambaye abunda take so sai dai ta shekara a gurin, budewar ma ta yi sa'a yana tsaye jikin kofar ne. Na so kafarta tai ta shigo cikin falon tana cigaba da kallonsa kamin idonta ya sauka a gurin Hajiya Karama wacce ke kallonta, wani irin kallonsu take kamar bata taba ganin mutane ba, ita a rayuwarta bata tana ganin fararen mutane da farinsu ke haskawa sosai kamar Shattima ba, gaba daya kallon Balarabe take masa sam bata yarda bafullanin mutum ne take kallo ba, ta kallin fatar jikinta da take baka ta sake kallon Shattima, ba farin ba ko gashin kansa da ke a gyare abun kallo ne, ga wani dogon hanci kamar biro kai ko cikin larabawan wannan na musamman ne. Shi ne abunda zuciyarta take raya mata. “Me kike so?” Hajiya Karama ta tambaya, a lokacin ne Falmata ta kara rikicewa, ta sara abunda zata ce, gaishe su zata fara yi ko fada musu aikin da ya kawo ta, tun da take zuwa gidan bata saba karo da daya daga cikinsu ba sai yau, sai dai jiya ta hango Zainab a stairs sai dai bata dauka a kusa kyauta yayi haka ba sai yau. “Me kike so?” Zainab ta daka mata tsawa, a take jikim Falmata ya hau rawa sai ta fashe da kuka domin ba karamin tsorata tai ba. “Easy mana” Shattima ya fada yana kallon Hajiya Karama. “To ana mata magana sai tai ma mutane shiru, kuma sai kallonmu take kamar mayya i hate nonsense” Ta karasa tana mikewa tsaye ta fice daga falon tana wani yatsinar fuska kamar ta ga abun kazanta. “Baaba ware” Shattima ya kira taohuwar yana kallon inda take tsaye rike da turaren wuta, sai a lokacin Falmata ta lura da ita da wasu masu aikin da ke can gaban Plasma suna gogewa. Da gudu Baaba ta karaso gabansa. “Allah ya kara maka lafiya” “A tambaye ta me take so” Ya fada kamar baya son magana. Baaba ta kalli Falmata da har lokacin kuka take tana shasshekar kuka ta ce. “Ke yar talakawa fadi ki yi kwashi gaisuwa kuma ki bude baki ki fadi abunda kike so” Falmata na jin haka ta fadi kwance a gurin rib kamar an jefar da ita cikin muryar kuka ta ce. “Ina kwana” Da ace shi kadai ne adakin da Allah kadai yasan kalar dariyar da zai yi, domin ba karamar dariya ta ba shi ba, sai dai ko da wasa be nuna hakan ba sabanin hakan ma sai ya kara hade rai. “Wacece ita?” “Allah ya baka yawan rai ita ce mai gyara dakin yan uku” Baaba ta fada tana daga masa hannun kamar mai gaisuwa, ya kalli Falmata daga inda take kwance ya kare mata kallo sannan yai mata alama da ta mike tsaye da hannunsa, da sauri ta tashi ta share hawayen idonta tana jiran wani umarnin. Da ido yai mata alama da ta wuce dakin tai aikinta, da sauri ta wuce, cikin rashin natsuwa tai aikin ta fito kamar wacce ta saci wani abu haka ta rika leken falon da babu kowa sannan ta fice. AA POV. Be yarda ya fadawa Anti Rabi cewar bayan kudin da Nana ta bata ba ta sake ba shi wasu, sai dai ya sha fada kuma ya sha gargadi akan cewar kar ya sake kula ta. “Kai ko kallon inda take kar ka sake yi” “To ai ba za a koma ba” Ya fada ne kawai amman wani bangare na zuciyarsa na kara raya masa yadda zai sake samun wasu kudin haduwarsu ta gaba, tun da ta karbi lambarsa yake jiran kiranta. “Wallahi Allah ne ya ji tausayi na ya kawo min yarinyar nan, Allah kadai ya san me babanta ke yi” Ya fada a ranshi yana aikin saka talkaminsa, sai da yai ma Anti sallama sannan ya fice daga gidan, kamin ya isa gurin aikin nasa har addu'a yake Allah yasa yau ma ta zo, ya kuwa taki sa'a domin ya tarrarda ita zaune a gurin tana ta boye fuskarta kamar yadda ta saba, wannan karon be tsaya komai ba ya nufi inda take, Nana na ganinshi ta fara dariya. “Tun dazun na zo” “Muje waje mu yi magana” Ya fada yana kallon daidaikun mutanen da ke wajen, domin safiya ce ba kamar da rana ba ko dare da ake taruwa sosai a restaurant din. Mikewa tai tsaye ta riga shi fita sannan ya fito ya same ta tsaye a inda ta tsaya jiya. “Kin samo min aikin driver?” Ta bata fuska kamar za ta yi kuka. “A a ta hana” “Daman karya kike yi” “Da gaske ne mana” Shiru ne ya biyo baya na tsawon lokaci, sannan ya sake kallonta ya ce. “Yau ma kina son na kai ki wani guri ki boya?” Da sauri ta daga kai. “Eh Eh” “To kawo kudi na karbo babur din, amman yau ya ce sai an bashi 4k” Bata tsaya komai ba ta bude jakar ta dauko kudin ta mika masa. “Na je can waje na jira ka kamar jiya?” “Eh” Ta nufi hanyar fita shi kuma ya koma ciki gurin abokinsa Bashi, ba laifi yau ya manna masa 500 sannan ya karbi key babur din ya fito ya kunna ya hau ya fito da shi waje, yana isowa bata tsaya komai ba ta hau ya boye fuskarta, sai da ya su kai nisa sannan ya fara tunanin inda zai kai ta, ya san zai ba zai sake kaita gidan Anti Rabi ba, bayan dazun da safen nan ma sai da tai masa gargadi, to ina zan kaita? Ko ya kaita gidan Gwaggonshi? Ko gidan Kawu Bala? Kuma idan na kaita suka gano abunda cewar boyeta na yi za su min fada? Sai tambayar kansa yake yana neman mafita, be an karo ba yaji kamar an bugu babur din da suke kai yana kokarin saita babur din suka fadi kasa daga shi har ita, babur din ya haye shi ita kuma ta mulmula ta fada kwalbati. Kamar ita ta fi kowa ihu a duniya haka ta kwala ihu ta fashe kuka na gaske tana duba hannunta da yaji rauni da kafarta, daman can ko allura aka ce za a mata sai anyi da gaske take tsayawa balle kuma wannan da ta gurje a hannu da kafa da gefen fuska. “Wayyo Allah Wallahi sai na fadawa kowa, sai an kashe ka yau Wallahi kai ne ka ji min rauni kai ne ka fadar da ni da babur, sai na fadawa kowa yau sai an kashe ka” Cikin wani irin kuka da tsoro take fadar hakan tana kallon jikinta, AA na jin haka ya manta da nasa ciwon ya taso ya nufo ta ya daga ta, mutane sai sannu suke musu, ganin yana jan kafar wani yace “Zaka iya jan babur din kuwa” “Eh zan iya ku taimaka ku dora min ita dan Allah” Sai da ya hau sannan suka dora masa Nana dake ta ihu tana fadin sai ta fada a gidansu. A hankali ya fara tafiya gabansa na mugun bugawa kamar zai fito, sai da ya samu wani mai chemist sannan ya faka babur dinsa a gurin ya sauko ya rikota ta sauko ya shiga da ita cikin chemist din, zaunar da ita yai sannan ya ce. “Bari na gyara fakin din babur di na” Bata ko kula shi ba tana ta kuka da duba kafarta domin har a cinya ta ji ciwo. AA na isa ya haye babur din ya auna a guje be be nufi ko'ina ba sai unguwarsu, kamin ya isa har wani zazzabi ya rufe shi babu muryar da yake ji sai ta Nana tana fadin sai ta fadawa yan gidansu yau ko sai an kashe shi, laifi goma da ashiri, ga boyon da yake mata ga na fadar da ita akan babur dinsa dan ya san yarinyar yar masu abu ce wata kila ma ita kadai iyayenta suka haifa ya san kuma ba za su kyale ba. Kamar wani mahaukaci haka ya shigo gida hannunsa na ta jini sai dingishi yake. Anti na ganinshi gabanta ya fadi. “Lafiya AA” Kasa ce mata komai yai ya zauna bakin kofar dakinta ya dafe kanshi. “Lafiya hadari kai?” “Eh yarinyar ce ta roki na kawo ta nan shine na sake aro babur, muna tahowa sai wani mai Napep ya kade ni muka fadi ta ji ciwo ni ma na ji” Anti Rabi ta daki kirji. “Me? La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam” AA ya kalleta a tsora ce ya soma magana gumi na karyo masa. “Kuma Wallahi na ji tana cewa sai ta fadawa duk yan gidansu, wai yau sai an kashe ni tun da na fadar da ita akan babur” A take cikin Anti Rabi ya murda, ta dora hannu aka ta fashe da kuka. “Ka gani ko? Sai da na gargade ka amman baka ji ba, Allah kadai ya san waye ubanta mun shiga uku, ina yarinyar take?” “Na barta a can wani chemist na gudo” “Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mun shiga shida” Ta fada tana nufar butar da ke tsakar gida ta dauka ta nufi bandaki. Mikewa tsaye AA yai ya fice daga gidan, chemist din unguwarsu ya nufa yana isa be ko tsaya gaisawa da abokin nasa ba ya ce. “Dan Allah Ilya kai min treatment din ciwon nan kuma ka min allurar malaria, ina jin zazzabin malaria na ta so min” _________________ Waye zai zo ya cece AA 🤣😂 Me iya take kullawa? 🤔 Anya dai Hajiya Karama mace ta tana neman miji da kanta kamar yadda kike?😥 Wai me Falmata ta tarewa Tumba ne?😭🤧 03/12/2021, 08:07 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *6* HAJIYA BABBA POV. “Jarma har yanzu ban ga komai ba” Ta fada tana karewa Jarma dake zaune a gabanta sanye da babbar riga, kansa kuma da rawani. “Kina gaggawa ne kawai Hajiya, ba gashi mun fara ganin haske ba? Komai a sannu ake binsa” Ya dauke kai tana kallon wani bangare na dakin. “Ba Mai Martaba nake magana ba, Shattima shine matsalata a yanzu” “Da Shattiman za mu fara kamin Mai Martaba ya biyo shi, idan mu ka yi gaggawa to kamar muna fallasa sirrinmu ne, ya kamata mu bi komai a sannu” “A sannu na ke bin komai Jarma, domin burina dole ne ya tabbata, Talba kadai na ke son ya yi mulkin garin nan, so na ke na ga Ammy na zubar da hawayen bakinciki, shekarun da ta saka na yi a damuwa so na ke ta ninka a cikin bakinciki, na san a yanzu tana farinciki da ciwon Mai Martaba saboda tana ganin Shattima ne zai gaje shi ko? Hmmmm” Ta karasa tana murmushin gefen baki. Jarma ma murmushin yake yana kallonta zuciyarsa na saka masa burinsa. ‘Za mu kawar da Shattima da Mai Martaba, amman dan ki ba zai yi milkim garin nan ba, indai ina raye’ A zahiri kuma sai ya gyara babbar rigarsa ya ce. “Da sannu komai zai wuce Hajiya, kuma kar Salim ya fasa neman Nana” Sai a lokacin Hajiya ta dawo da kallonta a gurinsa. “Ai dole ya neme ta, tun da har Mai Martaba ya sallama masa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu, dole ne Ammy da zuri'ar ta su dawo karkashin kulawata, duk abun da tai min a shekarun baya sai na maimaita mata shi” Ta karasa zancen fuskarta na sauyawa alamar bata son tuna bayan. “Komai zai wuce Hajiya komai zai zama tarihi da yardar Allah” Ya daga masa kai tana sauke wani dogon numfashi. “Haka ne, tashi ka je kar a fara yi mana zargi” “Zargi kuma na nawa? Sai dai kar a koma” Ya fada yana mikewa tsaye da murmushi a fuskarsa, sannan ya dan risina mata. “Na bar ki lafiya” Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta mike tsaye ta nufi gaban drawer ta dauki wayarta ta aikawa Hajiya Talatu kira bugu daya ta daga tana jerowa Hajiya Balki wani irin kirari da ke kasa kan Hajiya fashewa. “An gaishe da Talatu Uwargidan Waziri” Talatu ta risina kamar Hajiyar ce a gabanta. “Allah ya kara miki lafiya da imani, Surukar Ammy kuma Uwar Sarkin gobe, a ganki a bar ki kuma a bi ki a dole” Hajiya Bilki ta yi wani irin kasaitaccen murmushi. “Yanzu Jarma ya fita daga nan” “Tsohon makiri, Allah yasa dai ba ki masa zan ce na ba, domin tsab zai labartawa Waziri komai ya kashe mim aure a asirance” “Taya za ayi na bar shi ya san shirin mu Talatu? Bayan na san shi akwai kwadayin masarautar nan a ransa? Ubansa daya fa da Mai Martaba kuma babu yadda be yi ba Mai Taba ya bashi Babbar masauta ya ki, yanzu kuma kike tunanin baya sha'awar wannan?” Hajiya ta dan yi jimm tana murmushi mai sauti “Mu dai gama da bangaren sauran ne sannan mu dawo kansa, na kira ki na ji yadda ake ciki” “Zan shigo da kaina ranki ya dade, domin maganar ba ta waya ba ce” “Ina jiranki” “To ranki ya dade” Daga haka ta aje wayar ta juya ta fice daga dakin, kofar dakin bata kara idam an bude ko an rufe gashi akwai yar tazara sosai tsakanin dakunan da inda aka jera kujerun falon, hakan ne yasa Sirleem be ji motsin mahaifiyar tasa take tsaye a bayansa tana kallon Mansura wace ke a fuskar Laptop dinsa yana video chat da ita ba. Har sai da ya ga Mansurar ta kasa karasa maganar da take tana kallon gafensa, sannan ya juya sai yai arba da mahaifiyarsa. Da sauri na rufe laptop din. “Hajiya Barka da fitowa” “Ban maka iyaka da yarinyar nan ba?” Ya sinne kai kasa, ya kasa cewa komai gabansa sai bugawa yake da karfi. Wata irin tsawa ta daka masa rai bace “Waye miye hadin Bayarabiya da bafullatani ne Sirleem? Me ta baka ka sha da baka iya rabuwa da ita? Ni uwarka ban isa na ce ka fita hanyar Mansura ka fita ba? Me yake damunka ne?” Dagowa yai ya kalleta cike da ladabi ya ce. “Hajiya ba fa cewa nai zan auri Mansura ba, Mansura kawata ce kawai, i think Nana kike so na aura ai” “Yes wannan kuma dole ne, auren Nana ya zame maka wajibi matukar ina raye, yaushe rabon da ka je ka dauki Nana ku fita ko na kira a waya? Amman ka zauna kana video call da wata yar iskar yarinya marar tarbiya, kuma a cikin falona” Cikin wata kalar murya dake nuna bacin ranta ta karashe maganar tana nuna shi da yatsanta da ke rawa kamar zata doke shi. “I'm sorry” Shine abunda ya fada ya mike tsaye ya dauki system dinsa ya fice daga falon. Zaunawa tai saman kujerar tana kokarin daidaita fushinta. AMMY POV. Bayan Waziri ya gama zayyana mata komai, sai ta amsa masa da. “Okay babu wata matsalar zan saka Shattima ko Jarma ya wakilce shi tun da kai ba zaka samu zuwa ba” “Jarman ma yafi dacewa tun da shine Dattijo kuma kin ga abu ne na manyan mutane” “To sai a yi ma Jarma magana da wuri ya shirya komai kamin lokacin” “Zan sanar da shi” Waziri ya fada yana karantar yanayin matar dan'uwan nasa. Har ya mike tsaye da zimmar yai mata sallama ya fice sai kuma ya koma ya zauna ya kalleta. “Hajiya ko dai akwai wata matsalar ne?” Ammy ta sauke ajiyar zuciya, daga inda take zaune ta saka hannunta na dama ta rike kanta, a take idonta ya cika da hawaye abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa. “Ina cikin damuwa Waziri, na rasa da wanne zan ji, matsalar Nana ko ta Mai Martaba ko kuma ta maganganun da suke tasowa a masautar nan?” “Matsalar Mai Martaba tana damun kowa, addu'a yake bukata da kuma kulawa, gulma kuma ta daina damunki daman duk daukaka ta gaji haka, za ka samu akwai hassada da kiyayya da kananan maganganu, sai dai Nana nake son na ji abunda ya same ta?” “Abubuwan da take min bana jindadinsu, tun jiya take damuna da zancen sai an canja mata driver yau da safe har tsawa ta daka min akan haka, taya yarinyar da ke neman albarka za ta yi ma mahaifiyarta haka? Yanzu kuma na duba drawer dubu dari uku da saba'in na aje a ciki yanzu na duba na ga babu kudin sai dubu talatin da biyu suka rage, abubuwan da Nana take suna tsorata, kuma suna damuna, ba a nan kadai ba Nana ko dakin Mai Martaba ta shiga indai idonta ya ga kudi sai ta saka yadda tai ta dauke su, ina tsoron kar wannan abun ya zame mata hali, ga shi bata da natsuwa duk wani abu na masu hankali Nana ba ta yinsa....” Ta karasa hawaye na sauko mata, ba dan komai ta tsaya ta fada ma Waziri damuwarta akan Nana ba sai dan sanin shi ne kadai mutumen da zai tsawatarwa Nana ta ji kuma shine mutumen da idan ta fada masa damuwarta ko damuwar Masarautar nan yake fadi tashin ganin ya same mata mafita. Waziri ya kankance ido irin na su na manya yana mamaki. “Me take yi da kudin da take dauka?” “Wallahi ban sani ba, amman kai kanka kasan babu abunda Nana ta nema ta rasa” “Zan daukar mata mataki kuwa, amman duk da haka ki rika gamawa da addu'a ta tsari da kuma ta shiriya” Sosai Ammy ta jidadin maganar Waziri domin tana ji a ranta kamar ba zata iya da Nana ita kadai ba. Har ta bude baki ta yi magana sai ta Yusra ta shigo dakin da gudu har tana haki. “Ammy Nana ta fadi ta ji ciwo gata can an kawo ta....” Tun kan ta karasa Ammy ta mike tsaye hankalinta a tashe ita da Waziri suka fita daga dakin. A kwance suka samu Nana saman gadonta an saka mata bandeji a kanta da kafarta da hannu, Shattima na tsaye tare da Hajiya Karama, Driver ba kuma yana daga bayansu jikinsa sai rawa yake. Da sauri Ammy ta zauna saman gadon ta taba jikinta. “Me ya same ki Nana?” Ta kalli Shattima da Hajiya Karama, sannan ta kalli Ammy, ko da wasa bata kalli Waziri ba domin yadda take tsoronsa ko mutuwarta albarka. “Mai Babur ya kade ni, na fito daga school ina jiran Driver ya zo ya dauke ni be zo ba har babur ya kade ni, sai wani ya kai ni asibiti aka saka min wannan shi ne ya kawo ni nan ma da motarsa” Nana na fadar hakan driver ya risina kasa yana rokon Ammy. “Hajiya dan Allah dan Annabi amin afuwa, uzuri ne ya rike ni shiyasa ban samu isa da wuri ba” Ammy bata ce komai ba sai duba jikin yarta take cike da damuwa. “You fired, saboda ita aka dauke ka aiki, then why all this? Har mai babur ya kade ta ta ji ciwo wani dabam ya kawo ta gida” Zainab ta fadawa driver, a take ya fara magiya yana kallon Ammy. “An kore ka aka ce fita ka bar dakin nan” Ganin Ammy za ta yi magana yasa Shattima ya nanata masa abunda Zainab ta fada domin abunda yake da niyar yi kenan, cikin rashin dadin rai driver ya fice daga dakin fuskarsa kamar zai fashe da kuka. “Me kike son ki ci? I will cook for you” Ammy ta tambaye ta cike da kulawa, sai Nana ta kawardar fuska ita aka dole har yanzu fushi take da Ammy. “Bana son komai” Ammy ta hade abu da karfi sannan ta mike tsaye ta nufi kofar fita sai kuma ta juyo ta kalleta fuskarta da mamaki. “Amman ya akao kika fito ba lokacin tashi daga school ba? Ya akai suka bar ki kika fito? Yanzu fa karfe 11:40am how?” Shattima ya kalleta. “Ammy za mu yi wannan maganar daga baya yanzu dai ta samu lafiya” Ammy bata sake cewa komai ba ta juya ta fice. Sai a lokacin ne Waziri yai magana. “An kori direban ko? To kin samu abunda kike so idan ma ke kika tsara haka saboda a kore shi burinki ya cika, amman bari na fada miki daga yau school bus ce zata rika kai ki makaranta tana dauko ki, ba ki wayar ki” Ya mika mata hannunsa sai tai saurin kallon Shattima tana son saka kuka, kai ya gyada mata alamar ta ba shi din, sannan ta kai hannu ta bude school bag dinta ta dauko wayar ta mika masa tana hawaye. Shattima ya zauna kusa da ita kenan Waziri ya ce. “Daga yau kar wanda ya sake daukar kudi ya bata ko ya siya mata waya, daga kai har Zainab shi ma Sirleem zan masa magana” Da mamaki Zainab ta kalleshi sai dai babu damar tambayarsa dalilin hakan dan ta fi kowa sanin waye Waziri. “Zainab je ki kira Baaba ta zo ta bincike dakin nan duk inda kudi suke ta fito min da su, kuma ta kwashe kayan kallon nan da system din nan bana son ganinsu a nan” Ta amsa masa ta to, sai da ta kalli Shattima sannan ta fice zuciyarta cike da tambayoyi. Waziri ya kalli Nana. “Da kin ji sauki ke za ki fara gyara dakinki da kanki, ba za a sake miki ba, ko tufafin da ke saka miki a wardrobe daga yau ke zaki saka idan sun yi datti ki wanke da kanki” Ta kankame Shattima tana fashewa da kuka. “Wayyo Yaya mutuwa zan yi” “Kin dade baki mutu ba” Waziri ya daka mata tsawa yana matsowa kamar zai doke ta, da sauri Shattima ya mike tsaye ya tare ta. “Ayi hakuri Baba zan mata magana” Shi kan shi Shattima sai da Waziri ya watsa masa harara sannan ya fice daga dakin, wanda hakan yayi daidai da shigowar Baaba, a take ta hau aikinta sai da ta bincike dakin tsab ta fiddo kudi ba kanana ba har da dollars din da Nana take daukowa dakin Mai Martaba ta fito falo ta kawowa Waziri sannan ta kira Sarkin Dogarai ya cire tv da decoder da system din dake dakin. Nana na ji na gani aka kwashe kayan aka bar mata daki wayan daga gadonta sai wardrobe da dan karamin dinning dinta na karatu domin har hotunan artists da saka sai da Waziri ya saka aka cire su a lokacin da ya sake dawowa dakin dan ganin idan an yi yadda ya ce. “Yaya Wallahi Baba Waziri da Ammy basa so na” “Shiiiiiiiiii kar na sake jin wannan kwanta ki yi bachi idan kin tashi zan kira Doc Deen ya duba ki Okay” Ya daga masa kai sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin. Tai saman gadon ta fara kuka na gasken gaske tana jin kewar mhaifinta domin ta tabbatar da yana raye babu wanda ya isa ya mata haka har shi Baba Wazirin da kansa. Can kuma ta fara murmushi mai sauti tunawa da yadda AA ya rude a lokacin da suka fadi din, sai a lokacin ta soma dariyar abunda ya faru tsakaninsu tun haduwar farko har zuwa yau. FALMATA POV. Cikin rashin jindadin ta isa gida tana jin ina ma ace tana da wata dama da zata hana kanta aiki a gidan da ta huta, domin abunda Zainab tai mata a yau be mata dadi ba ga Iya data saka ta gaba ga wahalar tafiya kasa kullum kuma ta dawo. Sai dai babu yadda ta iya idan tace zata bar aikin ta san sakamakonta a gurin Umma wacce tai ruwa da tsaki ta sama mata aikin saboda ta rika bata albashin. Kamin ta isa gidan sai da ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta su kai yar fira har ma ta kunan wakar Sirleem M2 a wayar Khadija ta kalli video wakar sannan ta wuce gida. Tana isa bata ko tsaya hutawa ba, ta dauki bokitin diban ruwa ta nufi bohol daman diban ruwa ne abu na farko da take idan ta dawo daga aikin, sannan tai surfe. Haka ta cika komai na gidan sannan ta zuba surfe ta surfe iya wanda zata iya ta wanke ta bawa dabbobi kasarin, ita kuma ta debi ruwa tai wanka ta shirya cikin uniform dinta na islamiya wanda ya gama kodewa har ya fara yagewa a wani gurin ma. Ta dauki jakarta ta makaranta ta nufo dakin Iya. “Umma makaranta zan je” Iya ta hankada fillonta ta dauko naira talatin ta jefo mata. “Kwadon da mu kai be ishemu ba, ga talatin nan ki siye awara ko dankali” “To na gode” Ta saka hannu biyu ta dauka sannan ta juyo ta fito daga dakinta idonta cike da kwalla. Idan zalinci da danne mata hakki ko kuma sakata aikin wahala ba yau Tumba ta saba ba, amman ta kasa sabawa a kullum idan akai mata sai ta yi kuka, cikin damuwa taje makarantar sai dai a yadda suke cikin ajin da dalibai ana wasa da dariya yasa ta waye kamar ba ita ba. Kwalama ta siya da kudin a lokacin da suka tashi daga makarantar, bata ci abincin kirki ba sai da dare da aka sauke tuwo. A yau ma sai da wani ya sallamo mata wani dabam ba na jiya ba, shi ma ya mata siyaya kuma ya bata kudi after ya kunna mata wakar Sirleem M2 ta kalla a wayarsa. Yau kam kamin ta kwanta iya ta bata rubutun ta sha, hakan yasa da safe ba ta bata ba. Sai a kullum Falmata bata fashin bismillah idan zata sha addu'ar safe da yamma kuma ta zame mata jikin duk da karancin shekarunta. Cikin tsoro da tunanin abunda akai mata a jiya ta shiga masarautar ga kuma tunanin haduwa da Iya. Sai dai har ta isa bakin kofar falon Ammy bata hadu da ita ba sai dai hakan be saka ta fidda ran haduwa da ita a dakin yaran ba ko a falon. Sai da ta karanta addu'ar neman tsari sannan ta danna door bell din, ba dadewa Nana ta bude mata kofar sai ta tsaya kallonta. “Me aka yi?” Har kasa Falmata ta sirina ta gaishe ta sannan ta ce. “Zan gyara dakin yan uku ne” “To shigo” Nana ta matsa daga jikin kofar tana dingishi ta koma a set din kujerun farko da suke falon ta zauna ta cigaba da cin plantain chips. Da sauri Falmata ta shiga dakin ga mamakin yau kam sai ta samu Luma a kan gadon jarirai ta mike tsaye tana ta ihu sai zabura take kamar ana tsikararta. Da sauri Falmata ta karasa inda take tana kallonta. “Laaaaaaaaaaa” Ta fada tana kallonta cike da burgewa sai dai ganin yadda take zabura kamar mai tsoro yasa ta karanta ayatul kursiyu ta tofa mata a kai sannan tai bismilla ta kai hannu ta dauke ta tana mata wasa. Tana juyowa ta yi arba da Shattima tsaye bakin kofar yana kallonta fuska a hade. A rude ta aje yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri tana girgiza masa kai alamar ita ba ta yi komai ba. “Wallahi Wallahi.... Wallahi ganin nai tana kuka tana zabura shiyasa nai mata addu'a kuma na dauke ta, Dan Allah kai hakuri na shiga uku” Ta fashe da kuka ta duka har kasa tana rokonsa kamar ance mata dukanta zai yi. Be ce mata komai ba ya karaso cikin dakin ya dauki yarsa wacce ke faman kuka tun da Falmata ta maida ita cikin gadon, be ce mata komai ba ya fice. Ita kuma bata fasa kuka tana nadamar abunda tai ba har ta yi aikin ta gama ta fito, ba karamin dadi ta ji ganin babu kowa a falon ta fice da sauri har lokacin hawaye take. Sai da ta fito daga habarar Ammy sannan ta ji kamar ana binta a baya, da sauri ta juya suna yin arba da Iya gabanta ya buga da karfi. “Shattima ya ce a fada miki karki sake dawowa daga yau” Kasa cewa komai Falmata tai Iya kuma ta juya ta koma ciki tana rumgume da hannayenta a baya. Babu wacce ta fado mata a rai sai Tumba, ta san idan ta fada mata abunda tai aka kore ta zata kara mata da nata ne. Sai dai ya zame mata dole ta fadi gaskiya dole ne ta fada mata gaskiya. A kullum idan zata je gida tana ganin tafiyar tana mata nisa amman ban da yau da take cikin tashin hankali sai ta ga kamar an ragewa hanyar tsawo. 03/12/2021, 08:09 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *7* Dogon wando ne da da yellow t-shirt a jikinta, kanta ba dankwali gashin kanta na dunkule guri daya da ribbon, se kai tana ganinsa ka san ya kwana biyu ba a taba shi ba. Tana tafe tana dingishi har ta shigo cikin falon, Rima na kallonta ta dauke kai ta cigaba da damna wayarta, hakan yasa Nana ta ja mata tsaki kamar ba yayarta ba. Ta kalli Juwairiya wacce ke tambayarta abunda ya same ta. “Anty Jurry ima Hajiya?” “Tana dakinta, Nana me ya same ki?” “Hadari na yi” “Garin ya?” Nana ba ta ce mata komai ba ta nufi hanyar dakin Hajiya, bata ko yi knocked ba ta tura kofar dakin ta shiga tana kiran Hajiya wacce take ganin har ta fi mata Ammy. Hajiya da ke makale da waya a kunne tana ganinta ta sauke wayar da sauri tana fadin. “Subhanallahi Daughter me ya same ki?” “Hadari na yi” Nana ta fada kamar zata fashe da kuka, da sauri Hajiya ta mika mata hannu alamar ta karaso fuskarta na nuna tsantsan damuwa. Nana ta karasa kusa da ita ta zauna bakin gadon sai Hajiya ta kwantar da ita jikinta. “Garin ya hakan ya faru daughter?” Irin karyar da tai ma su Ammy ita tai ma Hajiya. “Amman an kore shi ko?” “Yes Ya Shattima ya kore shi” “Da ba a sallame shi ba, da sai na saka an hukunta shi sannan na masa korar wulakanci” Hajiya ta fada cikin bacin rai, wanda hakan ba karamin dadin yai ma Nana ba. Babu abunda ta rage bata fada mata ba akan abunda Baba Waziri yai mata jiya har da hawayenta. Hajiya ta shafa kanta tana murmushi “Haba daughter kar hakan ya dame ki, ba dai ina raye ba babu wanda ya isa ya taba ki, nan da kwana biyu zan maida miki duk wani abu da Waziri ya cire a dakinki, ni kaina ya min magana wai ni da Sirleem mu daina ba ki kudi ko siya miki wani abu, amman kin san ba zan yi haka ba ko? Domin ni ina kaunarki sosai” Nana ta rumgume ta. “Na gode Hajiya, za ki rika ba ni kudi?” “Sosai ma, duk lokacin da kike bukatar kudi ki zo ki min magana, amman fada min me kika masa?” “Ni ban masa komai ba, ban san miyasa yai min haka ba daman can shi baya so na ai” “Mu ai muna sonki, bari na kira Sirleem ya zo ya kai ki wata asibitin a duba ki” “A a Ya Shattima ya Kora Doc Deen ya duba ni jiya” Ta mike tsaye jin maganar asibiti, domin zuwa asibiti da allura sune manyan makiyanta a duniya. Hajiya ta mike tsaye ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko kudin da za su kai 20k ta juyo ta dawo kusa da Nana ta mika mata kudin. “Karbi wannan ki siye wani abu” Da sauri Nana ta saka hannu ta karba tana murmushi. “Na gode” Murmushi Hajiya tai mata a respond ita kuma ta saka kudin cikin aljihun wandonta ta juya tana dingishin ta fita daga dakin, Hajiya ta bita da kallo tana murmushi. Hakan da Hajiya tai mata ba karamin dadi yai mata ba, daman can ta san babu mai sonta sai Hajiya domin ta fi kowa sakar mata kudi ita da Hajiya Karama. Sai da ta fito daga bangaren Hajiya gaba daya sannan ta fiddo kudin ta karga 20k ne cif ta maida a inda ta saka dazun sannan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarensu. “Imagine Muhseen ya tafi be min sallama ba” Cewar Zainab tana mamakin tafiyarsa ba tare da saninta ba. “Yana busy daman Mama Fulani kawai ya kawo, any problem?” Shattima ya fada ba tare da ya kalleta ba. “No kawai na ji tafiyar ta sa a ba za ta ne, ita ma Mama Fulani ban ganta ba ai ko tare suka tafi?” “Tana cikin garin gurin yan'uwa” Ya bata amsar still be kalleta ba sai aikin taba System dinsa yake, ita kuma tana shafa wani mai a fuskarta jikinta sanye da sleeping dress wando da riga. Suna haka Nana ta shigo falon ta nufo inda suke tun kamin ta zauna Zainab ta ce. “Ammy na nemanki” “Me nai?” Zainab tai murmushi “Sai kin yi wani abu Ammy zata nemeki? Haba Baby ta shiga dakinki bata ganki ba na fada mata kin tafi bangaren Hajiya, tace idan kin dawo na turo ki” Ta juya ba dan ranta ya so ba ta nufi dakin Ammy, a kasan carpet ta samu Ammy zaune rike sanye da hijab hannunta rike da carbi. Ta karasa ta sauna bakin gadon tana turo baki tana kin kallon mahaifiyarta. Ammy ba ta bi ta kanta ba ta kalleta a natse ta ce “Ya jikin na ki?” “Da sauki” “Na shiga dakinki ban same ki ba, Zainab tace kin je bangaren Hajiya Balki me kika je yi?” “Naje na fada mata duk abunda Baba Waziri yai min” “Da kika fada mata sai ta miki maganin me?” Turo baki tai ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sai da Ammy ta daka mata tsawa. “Nana....! Ina magana zaki tashi ki fita?” Ta juyo tana turo baki amman bata dawo ta zauna ba. “Daman ai na san ba so na kike ba, gidan nan daga Ya Shattima sai Hajiya Karama sai Hajiya Babba kadai ke so na, sai Mai Martaba....” Mikewa tsaye Ammy tai ta karasa inda Nana take ta fisgeta iya karfinta ta jefar kasa sai da kanta ya bugi gadon dakin. A take Nana ta bude baki ta fara ihu daman kukanta na kusa, da gudu Zainab da Shattima suka shigo dakin, Zainab ta nufe ta da sauri ta rika ta. “Ban mata komai ba ta jefar da ni kasa” Ta fada cikin kuka tun kan Zainab ta tambayeta. “Okay tashi muje room dinki” Da taimakon Zainab ta mike tsaye suka fice daga dakin. Shattima ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana karantar yanayinta. “Ammy ki rika dagawa Nana kafa she is still young, ba isa tai irin wayon da kike so tai ba” Ammy ta kalleshi. “Wata yarinya kamar ta tana da hankali da tunani, wata yarinya kamarta ta san ciwon kanta, Nana ban isa na ce kar ki yi ba ta bi umarnina, ban isa na hana ta ba ta hanu, bata san komai ba sai a bata kudi ayi mata kaza, abunta ya fara yawa ace Nana idan ta ga kudi sai ta saka hannu ta sata?” “Nonono Nana ba zata taba haka ba In-Sha-Allah, Ammy ki daina mata wannan fatan, tana dauka ne saboda tana ganin a gidansu ne, kuma wannan halin da ta yi wayo zata daina” Ammy bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya. Jin muryar Hajiya Babba yasa Shattima mikewa tsaye ya fito falo. Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa mishi da far'arta kamar ko yaushe tana kare masa kallo. “Hajiya Zainab tana ciki?” “Eh tana ciki” Binsa tai da kallo sai da ya isa gurin system dinsa sannan ta dauke kai ta tura kofar dakin Ammy ta shiga. Daga bakin kofar dakin ta tsaya tana kallon Ammy. “Hajiya Zainab kin kyauta kenan?” Ammy ta mata kallon rashin fahimta. “Me ya faru? Karaso mana kika tsaya daga bakin kofa” “A a bar ni a nan da ina da muhimmaci a gareki ai da kanki zaki aika min abunda ya samu Nana, ko ba komai Nana yata ce kuma surukata ina hakkin sani” Surukata yafi komai yi ma Ammy za fi domin har ga Allah bata son hadin nan na Sirleem da Nana, sai dai babu yadda ta iya tun da sai da aka tambayi Nana da kanta tace tana son shi sannan akai musu baiko. Murmushi karfin hali Ammy tai tana kokarin maida abun ba komai ba. “Haba dai, dan ɗan wannan sai ace sai an tashi hankalinki, garin shiritarta ne taje ta ji ciwo kuma ba wani rauni ne sosai ba, kin dai san halin Nana da raki shi ne kawai” “Uhmm ko da ace ba ni na haifi mijin da Nana zata aura ba, na ga dai nima uwa ce a cikin gidan nan, ko ciwon kai Nana take ya kamata a fada min, abunda kike yi sam ba yi ba ne, yau idan Mai Martaba ya fadi ya mutu haka zamu tai zama cikin rashin hadin kai? Idan yau kika fadi kika mutu ni zan rika Nana ya kamata dai a gyara...” Tana fadar hakan ta juya ta fice daga dakin rai a bace sai dai bacin ran na iya fuska ne be kai zuci ba. Ammy kuma ta ja dogon numfashi ta sauke ta lumshe ido. Ba tun yau indai ta hadu da abokiyar zamanta sai ta fada mata wata maganar marar dadi, me ya kawo maganar mutuwar Mai Martaba ko nata a nan? Kan abunda be kai ya kawo ba? Sai da ta fice daga bangarensu sannan Shattima ya mike tsaye ya rufe system dinsa ya dauke ta ya nufi dakin Nana. Zaune ya same su ita da Zainab suna ta kyalkyalar dariya bakin kofar ya tsaya yana kallonta yana murmushi. “Ya Shattima zo nan” Ya karasa ya zauna dayan side dinta da ta nuna masa da hannunta. “Me kuke kallo?” “Comedy” Ta amsa masa tana karbar wayar daga hannun Zainab ta mika masa. Kadan ya kalla ya mike tsaye. “A sha kallo lafiya” Ya juya ya fice, ita ma Zainab din ta mike tsaye. “Bari naje mai wanka kamin na shirya kin gama” “Okay” Ta cigaba da kallon hankalinta kwance bayan Zainab ta fice. Shattima na fita daga dakin Nana ya nufi dakin da ya aje yaransa ya dauko su ya dawo da su dakinsu wanda Falmata tai masa tas sai kamshi yake. FALMATA POV. Kamar wacce zata sanarda mutuwar wani haka ta shiga cikin gidan cikin tashin hankali da fargaba ga tsoron da ya cika mata zuciya har ya bayyana a fuskarta. Tun daga sallamarta zaka fahimci akwai damuwa da tashin hankali a tare da ita balle kuma idan kai arba da fuskarka. Kamar mai koyon tafiya haka ta karasa kusa da Tumba da ke aikin tsintar shinkafa ta risina kan ta ce komai hawaye ya fara isar da sakon abunda zata sanar. “Umma dan Allah ki yi hakuri” Umma ta aje tray shinkafar tana mata kallon uku saura kwata. “Ban gane na yi hakuri ba, me kika min macuciya?” Ta fara yarfar da hannu. “Sun kore ni daga aikin” A take Umma ta saka, sam bata kawo kora daga aiki Falmata zata fada ba, a daukarta wani laifin tai mata na dabam. “Amman wannan Ya kin iya bakinciki, dan kudin da zan samu kike wa Hassada? Ni zaki yi ma cuta?” Da sauri Falmata ta girgiza kai tana wani irin kuka mai ban tausayi. “A a Wallahi ba dan shi ba ne” “To me kika yi ma wai suka koreki? Taya za su kore ki haka nan kawai ba tare da kin musu komai ba?” Bata boye komai daga abunda ta aikata ba wanda take kyautata zaton hakan ne yasa aka koreta, wato tofawa Luma Addu'a har mahaifinta ya gani. “To uban waye ya kai ki yi musu addu'a ke ashibi yar neman yabo ko? Makira shegiya yar iskanka, ni za ki yi wa bakinciki? Bari Babanki ya dawo sai na miki wanda ya fi wannan” Tana fadar hakan ta mike tsaye ta kai hannunta a kirjin Falmata ta fara murzar kirjinta iya karfinta. Wani irin kuka Falmata ta saka tana rike hannun Umma. “Umma ciwo mutuwa dan Allah ki yi hakuri” Bata saurareta ba har sai da ta murja iya yadda take cin zata cutarta da ita, tun da ta san idan aka murza kirjin burduwa mai tasowa ciwo take ji sosai. A rana Falmata ta wuni da kirjin nata kamar dutse yana ta mata ciwo bayan nauyin da yai mata. Bayan sallah isha'i tana zaune saman tabarma ita da Naja sai dariya take mata, ita kuma ta takure guri daya tana ta tunanin abunda Umma zata saka Baba yai mata sai ta ji sallamarsa, wani irin tashin hankali ta ji kamar ance mata ga mutuwarta nan. A yau Naja ce ta amsa sallamarsa taje ta karbo ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa sai far'a take. “Baba sannu da zuwa” Falmata ta fada muryarta na rawa tana masa wani irin kallon tsoro dan ji take kamar ma Umma ta mata sherin ne. Sai akai sa'a yana kawowa daidai inda take tsaye Tumba ta fito daga dakinta tana fadin. “To Malam sai ka san abun yi, Fulani dai so take ta lalace, kama ta nai a kofar gida ita da wani da ban san ko waye ba yana taba mata kirji” A bala'in firgice Falmata ta mike tsaye tana kallon tana kallon Umma, a take Umma ta zaro mata ido. “Ko karya na ke?” Falmata ta girgiza kai da sauri. “A a ba karya kike ba Umma amman Wallahi ba zan kara ba dan Allah kui hakuri....” Tun kan ta karasa Baba ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, yasa kafarsa ya shure kafafuwanta ta fadi kasa tana jin kamar babu naman fuska a fuskarta, ga kunnenta yayi wani dummmm jin tai yai dogon zango, kamar an aiko shi haka ya hau dukanta yana fadin shi zata kawa abun kunya, gaba daya ta kasa kuka komai ya zo mata kamar a mafarki ga shi bata jin komai daga cikin abunda Baba yake fada kamar mai dukan Namiji haka Baba ya rika shurin Falmata yana dukanta har da saka kafarsa ya danne mata ruwan ciki sai da tai amai sannan Umma ta rugo da gudu ta rike shi tana kuka. “Haba Malam daga fada maka abun dan ka mata fada sai ka hau yi mata wannan dukan, idan ka kashe ta fa, yarinya marainiya zaka mata wannan dukan” Kuka take riri tana fadin haka iya karfinta wanda hakan yasa makonta su shigowa suna tambayar ba'asi, babu abunda ta rage sai ma kari da tai cewar wani ta gani yana taba kirjin Falmata. A lokacin ne Falmata ta ji wani irin kuka ya zo mata da karfi ta shiga ambaton Allah tana kiran mahaifiyarta da bata raye. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Mama Mama Mama Mama Mama, na shiga uku mutuwa zan yi, Bana jin komai Mama Baba Baba” Ta unkura zata tashi ta ji ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ta kwanta a kasan ta rike kunnuwanta tana wani irin kuka mai shiga zuciya. Tumba ta nufi inda take ta rika tana kuka kamar ba ita ta kitsa komai ba, kokarin dagata take amman Falmata ta kasa tashi sai kuka take. Mutane wasu na bata hakuri sai dai mafi yawa sun girgiza da jin dalilin dukan da mahaifinta yai mata, domin Falmata yarinya ce mai natsuwa da kamun kai wacce ake ganin kamar wata yarinyar matashi irinta a unguwar, wasu cewa suke sai dai idan saurayin ne yake son lalata amman Falmata ba halinta ba ne, wasu kuma sun yarda wanda hakan bacin suna a gareta da kuma tarbiyarta, a yadda kowa yakr ganin Tumba tana rikon Falmata tana mata gatan da bata yi wa Naja ma da take yarta sai suka yarda da abunda ta fada a ganinsu ba zata mata sheri ba. Har aka ci aka shude Falmata na kwance a gurin tana kuka, bata jin abunda mutanen suke fada har sai idan sun yi da karfi, fuskarta ya kumbura sosai kafarta sai ciwo yake kamar an cire mata shi, sai da dare ya raba sannan ta rarafa daker ta shige dakinsu bata ko karasa kan shimfidarta ba ta kwanta a gurin a kasa tana kuka a hankali, babu komai a ranta sai kewar mahaifiyar ta kalaman da tai mata na bankwana. “Zan tafi na barki ciki taradadi Fulani, Allah ya zama gatanki, na san za ki sha wahala kuma za ki ga banbanci da kiyayya, amman ki rike Allah shi sai miki gata, kuma kar ki yi wasa da addu'a” Mama..... Ta kiran sunan mahaifiyarta a hankali tana jin kamar ace tana kusa da ita, sai kuma ta fashe da matsanaicin kuka. __________ Falmata baiwar Allah Iya ta ja miki wahala yau 😭 Nana yar...... 🤔 03/12/2021, 08:09 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *8* Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi. Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai. Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo. “Ba za ki tashi ki je gurin aikin ba?” Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi. “Ban ji komai ba Umma” Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata. “Ni za ki fara yi wani sabon siyasa?” Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada. “Wallahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai” Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta. Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura. “Cewar nai ki tashi ki tafi aikin” Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa. “Ba za ki je, ki ba su hakuri ba?” Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar. “To” Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya. Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa. “Kar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....” Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali. “Haba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro” “Ni dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba” Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya. “Wallahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu” Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta. Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin. “Innalillahi ke lafiya me ya same ki?” Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan. “Khadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku” Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta aka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye. “Wai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?” “Allah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki” Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawar tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta. “Kullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum” Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai. “Na gode” “Babu komai ai yiwa kaine, wannan rashin imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?” “Allah zai saka mata In-Sha-Allah” Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gidansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba. AA POV. Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da accident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA. “Babu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki” Kallon Anty Rabi yai yana murmushi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa. “Babu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanzu ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai” “Hmm ka sani ko ana can ana nemanka?” “Idan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki” Ya fada har lokacin murmushi yake. “Maybe yar farin ce tana da wauta sosai” Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba. Gaba daya sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci komai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito. “Anti bari na leka nan waje” “To Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah” “Okay In-Sha-Allah” Sai da yai addu'ar fita daga gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa. SHATTIMA POV. Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, but wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa. A falo ya tararda yaransa, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi. “Babban Mutum an shigo?” Iya ta fada baki har kunne. “Eh Iya ya gidan?” Ya amsa mata yana leka yaransa. “Gashi nan fa sun sha ado, yanzu na gama gyara dakinsu” Da mamaki ya kalleta. “Mai gyaran bata zo ba ne?” Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye. “Wannan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi” Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a ne yasa ta ji tsoro ta ki dawowa. “Karka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu” Dan murmushi yai. “Haba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata” Iya ta yi murmushi tana kallonsa. “Haka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu” “Amman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai” “An gama Babban Mutum” Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannunta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi. “Lafiya Kalau Shattima” “Ammy ina tunanin gobe zan koma” Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa. “Amman ba zan yi dadewar wacan lokacin ba zan dawo” “Ya dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki” Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da take. “Ya gida ya aiki?” “Alhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident” “Eh amman da sauki sosai” “Allah ya tsare gaba” “Amin” After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama. “Shattima ba ku gaisa ba” Daga shi har Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba. “Shattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu” Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kawai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokacin da Sirleem ya mika masa hannun. Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna masa isa tana takama. Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi. “Ya Sirleem” Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake. “Ya jikin na ki?” “Na ji sauki, Ya Sirleem ban karya ba” “Why?” Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce. “Dan Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?” Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalleta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi. “Alright muje” “Kaje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina” Har ta juya sai ya kira ta ta juyo. “Nana... An hana ki fita da ni ne ko me?” “Zan fada maka a mota kaje can ka jira ni” Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji haka ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem. Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri. “X&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please” Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara tafiya. “Waya hana ki fita da ni hala?” “Babu” Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan. 03/12/2021, 08:22 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *10* FALMATA POV. Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba. “Karki sallah bari ki yi wanka” Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wutar da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi. “Zo dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne” Tana maganar tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannunta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta. “To je ki yi sallah ma” Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta saka ta saka hijabinta ta fara sallah. Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya. Tana tafe tana nemawa kanta mafita, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata samu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota. Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa. “Ko na zuba miki a leda?” “Idan ta gani zata iya min fada” Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki. “Ashe idan an tura ki aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani” Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa. “Dan Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri” Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun ssn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka. Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara. “Gata nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi” Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske. “Wato Falmata duk abun da za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?” Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana. “Zo nan....” “Baba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsoron komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je” Ta fada cikin kuka. “Zo na ce....” Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa. “Wayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah” Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har gurin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa. “Dan Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba” Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kukan yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai ta hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai. Ba tai wani bachi kirki ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta. “Na gode” Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta yi zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma. “Tashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin” “To” Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale ta gaishe da mahaifinta. “Baba ina kwana?” Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce. “Babu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita” “To Baba” Ta amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yadda Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta. Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin sa'a ta hango Iya tsaye ita da wasu matan gidan tana magana, a take jikinta yai sanyi, ta san ko kowa zai ji rokonta ya karbi uzurinta ban da Iya, duk da baya san wacece ita ba amman ta lura da bata son ta tun farkon zuwanta gidan, bayan Iya akwai Zainab da Shattima su ma tana tsironsu ba ma kamar Shattima da shi ya kamata da kansa tana taba masa ya.   Ji tai ba zata iya karasawa ciki ba ba kuma zata iya komawa gida ba, sai kawai ta koma gurin kofar babban gate na uku ta zauna tana ta kukanta marar sauti. *****      *****       *****      ***** “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Shi ne abun da kowa yake fada, Ammy ta karbe ta daga hannun Baaba tana jirgizawa, amman babu alamar rai a tare da ita “Hajiya a kira likita” “Ko kuma a je asibiti kai tsaye ba” Ammy ta hada hankalinta a tashe, Iya ce ta karaso gurin tana tambayar abun da ya faru. “Wallahi Luna ce, ta buga kwallowa, tana ta ihu ko da muka daukota jikin yayi zafi kamar wuta, daga nan bata sake motsi ba” “Innalillahi” Iya ta fada tana karbarta daga hannun Ammy. “Ayi sauri a tafi asibiti ai ba tsayawa za ayi ba” Ammy da kanta ta shiga ta dauko mayafinta ita da Baaba da Iya suka nufi asbitin. A lokacin ne labarin ya karade Masarautar kowa ya san abun da ake ciki ban da Nana da hankalinta be kai can ba, domin tana bangaren Hajiya kuma Hajiya ba ta yi magana a gabanta ba ita kadai ce a falon tana ta kallon Tv duk da hankalinta baya wajen. Ta kusan minti talatin a falon sannan ta taso ta dawo bangarensu, ta tararda manyan masu hidimar gidan zaune a falon cikin har da wasu kanen mahaifinta mata da suke zaune cikin masarautar, amman Nana bata tsaya ta kula kowa ba balle ma ta tambayi abun da yake faruwa. Kai tsaye ta wuce dakinta ta shige da rufo kofar ta hau saman gado ta kwanta, jikinta na bata ba lafiya ba amman ba zata iya tambaya ba. Sai da ta ji hayaniyar na so ma yawa har da masu kuka sannan ta fito ta tsaya jikin kofar dakinta tana kallon Hajiya Karama dake kuka sosai ita da sauran matan, Shattima na zaune kan cushion kansa a kasa Iya kuma na zaune kasa tana kusar kuka kamar ba gobe. Sai a lokacin gabanta ya so ma faduwa, kar dai Mai Martaba ya rasu? Da sauri ta karasa fitowa ta nufo gurin da Shattima yake zaune ta zauna tana tambayarsa. “Ya miya faru why kowa yake kuka?” “We lost Luna” Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. A take ita ma ta fashe da kuka ta riko shi. “Ya How?” Dagowa yai ya kalleta da idonsa da suka rine su kai ja, kana ganin kasan ransa a bace yake. “Lokacinta ne yai” “Ita take?” “Tana ciki za a mata sutura” Ya fada bayan ya nuna mata kofar da bakinsa, kallon kofar tai sai ta kwantar da kanta jikin yayanta ta fashe da kuka sosai. Kusan a falon Shattima ne kawai be yi kuka ba, sauran daga masu kuka suna ihu sai masu hawaye domin ko ba ka yi niyar kuka ba ganin yadda Iya da Nana da Zainab suke kuka dole ya baka tausayi ga kuma Shattima da ya kasa kallon kowa ya kasa tashi daga gurin. Sai da ana daf da za a fara mata sallah sannan Hajiya Balki ta shigo falon da Hijabinta da carbi a hannun tana kuka. Sai da aka fara shigowa gaisuwa sannan yaranta suka shigo suka zaune a falon Ammy ana amsar gaisuwa da su. Da dare Waziri ya tara kowa na gadan ya fada musu kar wanda ya sanarwa Mai Martaba da maganar mutuwar Luna. Kuma wannan zaman gaisuwar shi ne na karshe duk wanda ya zo sai dai yai musu ya tafi. A cikin daren Mama Fulani ta dawo daga kauyen da tafi sakamakon wayar da aka buga mata aka labarta mata abunda ya faru. Misalin ten Shattima ya shigo falon tare da wasu friends dinsa su kai ma Ammy gaisuwa sannan ya wuce da su bangaren Hajiya Balki su kai mata gaisuwa ita ma.   Bayan sun fita Mama Fulani take cewa. “Ni wannan abun har mamaki yake bani Wallahi, abu kamar ba banza ba” Ammy ta kalleta. “Wani lokacin ana munana zato, saboda an san akwai makiya kuma babu abunda basa iyawa, haka Waziri yake yawan fada wai yana ganin kamar da sa hannun wani a lamarin gidan nan” “Ya Waziri yana da gaskiya, ni kaina sai da mu kai maganar da shi, kuma maganarsa abun dubawa ce, tsakani da Allah da can ba haka ake ba, ki duba ki ga yadda suka mai da Mai Martaba ace kana sarki babban sarki amman an maida ke a daki zaune komai sai dai a labarta maka iyalinka ma ba kowa ke shiga ya ganka ba?” “To wa za ka yi zargi Fulani? Wasu dabam ko kuma a cikin masarautar ko a tsakaninmu, kanensa ko yan'uwa ko kuma matansa? Yanzu abunda ake ta yayatawa a gidan nan wai har da sa hannu a cikin ciwonsa saboda ina son da na ya gaji mulki” Mama Fulani ta rike baki. “Iko sai Allah ke kuma” “Wallahi hake ake fada ance na mallake masarauta ni na ke da ikon kowa sai yadda na yi, in ban da rashin tunani taya macen da zata auri mutumen tun tsufansa har kawo yanzu da yara suka girma sai kuma na ce wai ina son ya mutu a dora dana? Wallahi ni ban taba yi ma Shattima kwadayin sarautar nan ba, Shattima da be cika son damuwa ba ina ma zai iya da sarauta? Yau ko babu ran Mai Martaba akwai kanensa masu so na nesa da na kusa, kuma sarautar yanzu ai ta sama waka sani waya sanka me ka tara me kake da shi, ni ban taba masa fatan hawan wannan sarautar ba ko can da balle kuma yanzu” “Wallahi Hajiya karki ce dan muna uwa daya uba daya nake wani zargi, Wallahi har ga Allah ba dan muna uba daya da jarma ba wallahi sai nake ganin kamar har da sa hannunsa a lamarin nan, saboda kwadayenyen mutum ne, kuma ya so a bashi sarautar nan tun tuni” Ammy ta sauke ajiyar zuciya. “Wani lokacin sai ka yi zaton da ba haka yake ba, mu dai mun bar wa Allah komai yai mana magani” “Amman gaskiya a tashi tsaye nema masa na hausa” “Ai an gwada, idan aka masa na hausar sai ki ga kullum abun na kara gaba har tsoro yake ba mu, kuma kin ga idan an karbo ta nan ita ma Hajiya Balki ta gurinta tana karbowa sai ka rasa wanene na kwarai wanene mugun, shiyasa aka ce adaina ba shi gaba daya a cigaba da masa addua kawai” “Allah ya kyauta” “Amin” Ammy ta amsa, sannan ta kai hannunta ya janyo cooler abincin da ke gefen gadonta sai ga Nana ta shigo sanye da kayan bachi, ta zauna kusa da Ammy kanta a kasa. “Ya akai?” “Ba komai Ammy nan zan kwana” “To sai ki kwanta tare da Gwaggonki, ni kin san dakin Mai Martaba zan kwana” “Ni dai da ke nake son na kwana please” “No ba zai yiyu ba Nana tsoro kike ji?” Ta gyada kai. “To kije dakin Zainab ki kwana ya miki” Ta gyada kai sai kuma ya kwantar da kanta jikin Ammy. Ammy ta shafa kanta zuwa kafadarta. “Kin ci abinci?” “Aa bana so” “Gobe dai za ki koma school” Ta dago kanta da sauri ta kalli Ammy. “An samu sabon driver ne?” “No School bus za ta zo ta dauke ki” Ta bata fuska har ga Allah ita dai bata son zuwa makaranta. “Ammy no please” “Ba ni na saka ba Waziri ne, kamin ya bar nan ma sai da ya fada min zaki koma gidansa da zama idan an gama gaisuwa” Da sauri Nana ta bar jikin Ammy ta koma jikin kanwar mahaifinta wato Mama Fulani. “Mama Fulani dan Allah ki saka baki bana son zama gidan Baba Waziri Wallahi” “Ya Waziri ai daman ba shi da dadin zama da yara ba ke kadai ba duk yara ba son zama gurinsa, zan masa magana ya bar ki zauna nan sai ki cigaba da karatunki” “Eh dan Allah” Nana ta fada cikin kuka tana daga mata kai. A dakin ta kwanta duk firar da Mama Fulani da Ammy suke tana ji ta labe sosai kamar mai bachi alhalin idonta a bude yake. Misalin sha biyu Ammy tai ma Mama Fulani sallama ta sannan ta leka Nana. “Nana...” “Na'am” “Ba ki bachi ba? Tashi ki je dakin Zainab ki kwanta, ko nan kike so?” “A a zan je can” “Goodnight” Ammy ta fada tana shafa bayanta, har cikin ranta take kaunar yarta, sai dai dabi'un da Nana take yasa basa jituwa da Ammy har Nana take ganin kamar Hajiya ta fi Ammy son ta. Sai da Ammy ta fice sannan Mama Fulani ta fashi ta shiga bandaki, da sauri Nana ta mike tsaye ta bude wardrobe Ammy ta inda ta san tana aje kudi ta fara mata bincike, tana yi tana kallon kofar bathroom bata samu komai ba yasa tai saurin rufewa ta fice daga dakin da sauri. Zainab na zaune gaban system dinta tana duba wani aiki Nana ta kwankwaso kofar dakin. “Waye?” “Hajiya Karama ni ce” Jin muryar Nana yasa ta tashi taje ta bude mata kofar. “Baby” Ta kirata da sunan da take kiranta da shi. “Na'am nan zan kwana” “Tos shigo” Ya matsa nata daga jikin kofar, sai da Nana ta shig sannan Zainab ta rufe dakin ta dawo ta zauna a inda take tana hamma. Nana ta cire talkamin kafarta ta kwanata saman gadon tana ta kallon zoben zinarin da Zainab da aje kan bed side drawer.           Washe gari aka tashi gidan kowa shiru shiru ba ma kamar Ammy da Zainab, Ammy ta tsorota da mutuwar Luna ne sai take ganin kamar so min tabi ne zata iya rasa mijinta, gashi kwana biyun nan sai mafarke take da bata gane kansu. Zainab kuma ta damu da mutuwar kuma ta damu da halin da Shattima zai shiga duk da ta san ba zai nuna ba amman abun yana nan cikin zuciyarsa. Kowa yana falon suna karyawa ban da Ammy dake kitchen tana hadawa Mai Martaba nasa abun karyarwa dabam. Kadan kadan Nana take cin abincin tana sanye da uniform dinta sai satar kallon Shattima take da ya ke ta kurba tea shi a hankali. Sirleem ne ya shigo falon be yi sallama ba sai da ya iso dinning room din, Shattima ne kadai ya amsa masa Zainab kam tai kamar bata gan shi ba. “I'm sorry for your lost Allah ya yasa masu ceto ne my condolences please” Ya mikawa Shattima hannu, Shattima ma ya miko masa nasa suka gaisa. “Thanks” Shattima ya fada yana kallon Ammy wacce ta fito daga kitchen din tana murmushi. “Sirleem” “Na'am Ammy barka da tashi ya hakuri?” “Al-hamdulillah” “Allah masu rahama” “Amin Thank U” Yana kokarin juyawa Nana ta mike tsaye da sauri ta ce. “Ya Sirleem dan Allah zaka sauke ni makaranta?” “No School bus zata zo ta dauke ki” Ammy ta amsa mata, Nana ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Sirleem be ce komai ba ya juya ya fice daga bangaren gaba daya, daman saboda yai ma Shattima gaisuwa ya shigo, saboda jiya be masa gaisuwar saboda baya son fitowa cikin mutane. Daga bangaren Ammy ya koma bangarensu, sai ya tararsa falon ba kowa tsabanin dazun da ya bar kanensa suna karyawa. Kai tsaye yai nufi bangaren corridor da zai sadashi da dakin Hajiya. A hankali yake takawa har ya isa kofar dakin, yana kokarin kai hannunsa ya tura sai ya ji shi a rufe. “Hmmm ai na jidadi Wallahi an rage mugun iri, sauran su bi baya mu huta, da sannu mugun abun su zai koma musu ai, kin ga idon shi wai? Da wannan makirar sai kuka take kamar yarta” Shiru yai yana sauraren muryar mahaifiyarsa. Can kuma ya ji ta ce. “To shikenan bari na duba yanzu” Fasa kwankwasa kofar yai ya juyo zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala. Da wa Hajiya take? A waya take magana ko da wani? Be shiga dakinsa ba ya sauka downstairs. Ya nufi gurin motarsa tun kan ya karasa ya danna key hannunsa, yana isa ya bude motar ya shiga, be san inda zai je ba at this early morning, but haka nan dai ya tashi jikin nasa ba dadi yau, haka yasa kowa ya karya shi yana gefen falon zaune. 03/12/2021, 08:22 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *11* A hankali ya fara driving din da dayan hannunsa dayan kuma yana shafa fuskarta da ke annuri kamar wani sabon ango. Tun ka ya karasa babban gate din ya hango wata duke ta rufe kanta wanda hakan ke muna alamar kuka take. Very slowly ya karasa kusa da gate din, ya mika hannunsa ya dauko facing cap dinsa ya saka ya dauki bakin gilashinsa dake cikin motar ya saka, sannan ya sauke gilashin motar yana kallonta, kuka take a hankali wanda in baka saurara sosai ba zaka iya ji ba. “Ke...” Ya kirata da muryarsa mai dadi sauraro, sai dai yanayin da yai mata kiran ba zata iya ji ba, saboda ita din ba ta da lafiyar kunne a yanzu. “Hey....” Still bata dago ba dan bata san ma yanayi ba. Be sake na uku ba ya data gilashin motarsa ya cigaba da driving dinsa sanyin ac motar na ratsa ko'ina na jikinsa. Kamin ya karasa babban gate din wayarsa tai ring, cikin very low volume, hannunsa ya sa ya ciro wayar daga aljihunsa yana dubawa yai arba da Mansura. Murmushi yai kamin yai picking call din da Bluetooth din dake kunnesa. “Hey Baby” “Baby kana ina?” “Gani zan fito daga gida” “Ina zaka je?” “I don't know kawai na ji bana son zaman gidan ne” “Baby i miss you” “Miss you too, on wednesday zan dawo Kaduna” “I can't wait ina jin kamar na biyoka yanzu, i miss everything about you, your smell, your hug, your smile and everything, ina jin kamar idan ka auri wata ba ni ba zan iya mutuwa” Ya karshe maganar da muryar da ke nuna tana daf da fashewa da kuka, sai tausayinta ya kara shiga zuciyarsa. “Even if na auri Nana still zan aure ki, Hajiya ta yarda na auri Nana first then na auri duk wacce nake son aure daga baya, and i promise you....” Sai kuma ya kasa karasawa what if yai mata alkawari kuma ya tsaba? What if Hajiya ta hana shi aurenta gaba daya? “I know lokaci zai zo da zaka kasa daga kirana ma, but no matter what ina son kasan cewa ina kaunarka Sirleem, Hajiya tana son ka auri Nana ne saboda Nana ta fi ni kyau, ta fini kurciya ta fini asali ta fini komai, na san idan ka aureta za ka manta da ni ne” “C-omon kin san kyau ba ya rudata, da dan kyau ne da Allah kadai ya san matan da zan so, ke kanki da ba mu kawo yanzu ba, kyau be cikin tsarina hasalima na tsani mace mai kyau sosai that's why nake son black girl very dark, but ever since i found you bana bukatar komai” Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba. “Na rabu da kowa saboda kai Sirleem pls karka juya min baya” “Ba zai taba faruwa ba kin san ina son ki ai” “I love you too” He kiss her on the phone, sannan su kai sallama ya aje wayar a saman cinyarsa, ya cigaba da driving dinsa hankali kwance ba dan ya san inda zai je ba, shi din ba kamar sauran mutane ba ne da zai iya fita any how ko zuwa ko'ina at any time, wani gurin yana zuwa za a fara masa ihu ana cewa za ayi hoto da shi ko a fara masa video ko tambayoyi, shi kuma abun da ya tsana kenan a rayuwarsa, that's why be cika son zama ko'ina ba sai a family house dinsu indai yana cikin garin Yola. Wayarsa ce ta sake ring for the second time but this time around Hajiya ce, hannunsa na dama ya kai ya danna Bluetooth din kunnensa. “Hello Good morning” “Kana ina?” “Na fita” “Ai na san ka fita ba na aika kiranka ba babu kai a dakin kana ina?” “Wani abu kike so ne Hajiya?” “Ban isa na tambayi inda kake ba?” “Ina son na karya ne a waje” “Ka dawo yanzu gida zaka karya” “Amman Hajiya har na iso fa” “Umarni na baka” Tana fadar hakan ta kashe wayar, runtse idonsa yai for one second ya bude, ya juya motarsa ya dauki hanyar gida. Inda ya bar yarinyar dazun a nan ya sake tararda ita, sai dai wannan karon ba kuka take ba, zane zane take da yatsanta a interlock din dake gidan.   Ya dan sauke gilashin motarsa kadan ya leko kansa. “Ke me kike nan wai?” Bata ji me yace ba balle ta dago ta kalleshi, kana bata ji karar mota ba balle hankalinta ya bata an tsaya kusa da ita ne. Yanzu kam he realized bata ji domin ya daga muryarsa fiye da dazun da yai mata magana. Horn din motarsa ya danna sai ta dago da sauri ta kalli motar. Marar mota ce fes mai bakin gilashi, an sauke gilashin motar a amman kadan mutumen ciki na sanye da facing cap da katon bakin gilashin ido wanda ya boye fuskarsa. Directions dinta yake kallo tana gani ta san ko dai magana yake mata ko kuma kallonta yake. Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta tana kallonsa hawayen da ya bushe ya bata mata fuskarta. Hannunsa ya leko kadan yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, jikinta be bata cewar mutumen da ya kore ta ba ne, domin wacan ya fi wannan fari, idan ma shi din ya za'ayi ya kira ta? And wannan din da ke kiranta waye? Wat if marinta zai yi? Ita dai jikinta be bata mutumen arziki ba ne domin ya ki sauke gilashin motar gaba daya balle a iya tantance ko waye ne, gashi ya saka gilas da facing cap. Sirleem be sake kokarin ce mata komai ba ya ja motarsa zuwa gate din bangarensu, haka ta bi motar da kallo har ya shige sannan ta mike tsaye ta fara tafiya tana dingishi har ta isa gate din farko, sai da ta fara lekawa ta gani idan Iya na nan, ganin babu kowa yasa ta jidadi kuma ta ji kuzarin cira kafarta ta karasa har harabar gidan. Bata kai karamin gate ba school bus ta shigo harabar tsayawa tai kallon daliban da ke ciki ba karamin burge ta su kai ba, a rayuwarta tana sha'awar ace mace tana karatu, abun yana burgeta ace wannan yar makaranta ce, tsabanin ita da bata iya karanta komai a cikin boko. Nana ce ta fito ta kofar gaba tana ta turo baki ta shiga motar sannan driver motar yaja motar suka fita daga gurin. Bin motar tai da kallo tana tuna lokacin da Yayanta Fadil ke zuwa makaranta a lokacin tana karama sosai, yana yawan fada mata abun da ake makarantar, yana yawan ce mata ita ma idan ta kara wayo Baba zai saka ta kamar yadda ya saka shi, amman yanzu komai ya gushe, ta rasa mahaifiyarta Babanta kuma ya tsaneta, yayanta kuma ya tafi ya barsu, kanenta uku kuma suna kauye ita kadai take rayuwa cikin wahala. “Ko ina Yaya Fadil yake yanzu?” Ta tambayi kanta idonta na cika da hawaye, a hankali ta fara taka stairs  din tana jin yadda kafarta take diban tsantsin gurin kamar ta fadi. Cikin wani irin tsoro ta danna door bell din dake gefem kofar lake, sai ta koma gefe ta labe jikin fulawoyin kasko dake gurin tana leken ta ga wanda zai bude kofar. Daya daga cikin tsofin dake aikin a gidan ce ta leko tana tambayar waye, Falmata bata ji abunda tace ba sai dai ganin tana waige waige yasa ta fito daga inda take boye tana kallon matar. “Ke kika kwankwasa kofar?” Falmata ta daga kai alamar Eh ba dan tana jin abun da tace ba sai dan nuna da tai. Matar ta koma ta sanar sannan ta sake dawowa tai ma Falmata alama da ta shigo da hannu kamar ta san idan ta fada ba zata ji ba. Babu kalar addu'ar da Falmata bata karanta ba kamin ta saka kafarta cikin falon, tana shiga sai ta tsaya daga jikin kofar ta rakube ta kasa kallon kowa balle ta tantance waye da waye a ke cikin falo. “Me ya hana ki zuwa kwana biyu?” Bata daga kai balle ta gane tambayar da Ammy take mata, gashi ba ji take ba sosai ba a yanzu. “Ke yar talakawa ba magana ake miki ba...” Wannan kam ta ji sarai, domin tsawa ce Baaba ta katsa mata, a take jikinta ya hau rawa hawaye suka ce sallamu alaikum. “Ba kuka za ki yi ba bude baki ki yi magana....” A nan ma ta ji domin ba da wasa Baaba take daka mata tsawar ba. A lokacin da ta dago kanta sai ta rasa kan waye zata sauke su, Shattima ko Zainab ko Ammy ko Wasu bakin fuska da bata sani ba? “Idan ba za tai magana ba ta fice ta ba mu guri mana” Zainab ta fada cike da kufula, da sauri Falmata ta girgiza kai kamar ta san abunda Zainab ta fada. “Dan Allah ku yi hakuri, bana iya jin komai idan ba a fada da karfi ba, ko kuma kusa da kunnena” Gaba daya kallonta suke, ba maganarta kadai ba, hawayen da ke fita daga idonta ma da yadda numfashunta ke shudewa ya isa ya sanar da irin tsoron da take ji. “Baaba matsa kusa da ita ki tambayeta abun da take so” Shattima ya fada a hankali yana kallonta. “To Ranka ya dade” Baaba ta matsa kusa da Falmata wacce tak take jiran a sake ce mata ta juya ta zura a guje, daf da kunneta Baaba ta rada mata. “Me kike so?” A lokacin ne Falmata ta duka kasa ta hade hannayenta tana kallon Shattima hantar cikinta na mugun kadawa. “Hakuri na ke son na bashi, Dan Allah yai hakuri ya maida ni aikin, na san na yi kuskuren taba masa ya amman ba da wata manufa nai ba, dan Allah ka yi hakuri ka kyale ni na cigaba da aikina, idan baka hakura ba ban san yadda zan yi ba” Shattima kallonta kawai yake ba dan ya fahimcin inda ta dosa ba, domin be san ya koreta ba, sai dai idan ita ta kori kanta saboda ta kasa natsuwa da abun da tai. Ta share hawayen idonta tana hade yawu daker. “Sanadin korar da ka min yasa Babana ya mare ni kunnuwana suka rufe, har Ban iya ji sosai, idan baka maida ni ba zai iya kashe ni” Wani irin jan numfashi take tana maidawa, daker ta maganar ga kukan tsoron kar su ki karbarta ga kuma na kallonsu da take a gabanta. Ammy ta kalli Shattima. “Ta maka wani abun ne?” Ya girgiza kai ya dan tabe baki alamar no. “Waya kore ki?” Ammy ta tambaya sai matar ta rada mata a kunne. “Wannan matar wacce take nan gidan ita ta fada min cewar ka koreni, kar na sake dawowa” “Wace mata?” Ammy ta sake tambaya tana son tantance gaskiyarta. Sai Baaba ta rada nata a kunne. “Wannan wacce take saka zane da mayafi kala daya, wata Dattijiwa ban san sunanta ba” “Idan kika ganta za ki gane ta?” Falmata ta gyada kai bayan Baaba ta rada mata. Duk abunda ake Zainab bata ce komai ba Shattima ma be sake cewa komai ba kallonta kawai yake, ba wai tausayi ta bashi ba, kawai kallon mamakin wanda ya koreta da sunanshi yake, shi dai ya san be koreta ba, waya ce ya koreta? Bayan be yi magana da kowa akan haka ba.   “Me kika aikata ne?” Ammy ce ta sake tambayar, Baaba tai isar da sakonta a kunnen Falmata, sai Falmata tai kasa da kanta ta kasa cewa komai sai hawaye take tana yarfar da hannunta. Dawowar da za tai sai tai arba da Iya wacce shigowarta kenan a falon ko karasowa inda suke ba tai ba. “Gata nan ita ce” Falmata ta fada da sauri tana nuna ta, gabanta sai ya ninka na dazun bugawa, tsoronta ma ya ninka na dazun kamar wace ta ga wani horo, gashi Iya ta sako mata jajanyen idonta tana kallon komai na jiki da jininta.     A lokacin ne kallo ya koma gurin Iya wace ta karaso kusa da su ta yi wani tsayi hannayenta a baya. “Ya akai?” “Yarinyar nan ta ce kin ce Shattima ya koreta daga aiki” Iya ta juya sake kallon Falmata bayan Ammy ta fada mata haka, sai ta nuna kanta. “Ni na fada miki haka?” A zaton Iya Falmata ba za ta iya cewa komai ba, musamman irin yadda ta ga ta tsaya kallonta kamin Baaba ta rada mata. “Eh ke kika ce Wallahi ba karya na ke miki ba” “Okay Iya ita za tai karya kenan? How are you da kika iya munafurci?” Zainab ta nufo ta tana fadin haka, Falmata dai sai kallonta take irin na kurma, sai dai tana gani ta san fada take mata. Iya ta yi saurin riketa. “A a karki dake ta wata kila dai wata tai mata haka amman ba ni ba” “Ta rasa wanda za ta lakawa sai ke? Ke kadai ce a gidan nan ne?” Wannan karon Falmata ta ji abun da Zainab ta fada saboda ta fada ne cikin tsawa tana hararta. Sai Falmata ta girgiza mata kai. “Idan bata ce ba ba zan mata karya ba, Wallahi Allah yana shaidata ta fada min haka” Shattima ya mike tsaye yana fadin. “Ko ma dai minene ya wuce je ki yi aikinki” Shattima ya fada bayan ya mike tsaye, yan'uwan Ammy da suke falon dai ba su ce komai ba na su ido ne kawai. Zainab ta juyo ta kalleshi. “Kamar ya ya wuce? How yarinya za tai wa Iya kazafi ba ayi komai ba and you are telling us ya wuce like how? Har umarnin taje ta cigaba da aikinta kake ba ta” Wani wawan kallo mai kamar harara Shattima ya watsa mata, kamin Iya ta wanke mata fuska da mari, da sauri Zainab ta dafe kunci tana kallon Iya. Falmata kuma da bata gama fahimtar abun da ke faruwa a tsakaninsu ba tai kara shan jinin jikinta tana jin kamar ita aka mara. “Har abada karki sake, taya Babban Mutum zai ba da umarni ke ki ce ba haka ba? Har kin isa? Waye ke da za ki fada masa abun da zai yi?” Zainab ba ta ce komai ba ta bayan hawayen da suka wanke mata fuska wanda ta manta rabon da hawaye ko wani abu damuwa ya rabeta, sai da ta kalli Shattima da ke tsaye yana kallonsu sannan ta kalli Ammy, har lokacin tana rike da kuncinta da ke ta mata zafi, da sauri ta fice daga falon tana jin wani irin fusata marar misaltuwa. Sai da ta fice sannan Ammy ta ce. “Iya da ba ki mareta ba ai” “Sam ba zan lamunci kowa yai ma dan cikinki maganar banza ba, balle har ya musa masa, ban yarda wani yai masa ba ina ga yata? Na sani Zainab kadai ta rage min a duniyar amman Wallahi da zata cigaba da musa miki ko Babban Mutum sai na yafe ta gaba daya a duniyar nan” Kowa na cikin falon jinjina kai yake yana ganin ta girmama Ammy da Shattima, ban da Ammy da take ganin kamar da biyu tai haka, ko dai tana jin kunyar abun da Falmata ta fada ne tana son kare kanta ne, ko kuma da wata manufar tai. Shattima be ce komai ba ya fice daga falon. Kallo Falmata kawai Iya tai ta dauke kai ta fice ita ma daga falon. Da kai Ammy ta nunawa Falmata dakin yan uku, sai ta tashi jiki ba kwari ta nufi dakin, yau biyu ne sabanin waca zuwan nata na karshe da ta tararda da daya, sai dai yau ko da wasa ba ta kalli inda yaran suke ba, har tai abunda zata yi ta gama bata kula yaranba, tana daf da gamawa Shattima ya shigo dakin ransa a bace cikin tsawa ya ce. “Ya za ki yi shara da yara a cikin daki? Baki da hankali ne?” Da sauri ta juyo ta kalleshi ta girgiza masa kai. “Idan na taba su zan iya yin laifi, dan Allah kai hakuri” Ta duka har kasa ta hade hannayenta tana bashi hakuri, wani dogon tsaki yaja ya karasa cikin dakin ya kai hannunsa ya dauki dayan ya dora a wuyansa dayan kuma a dauke ta da hannunsa. Kamin ya fice Falmata ta karasa aikinta duk ta tsawwala. Tana gamawa ta fice da sauri kamar wacce aka kora. WASIN POV. Yana daga saman icen guava zaune yana kallon yadda mawakan cikin gidan sarautar suke busa suna rawa daga su sai walki a jikinsu, ga wuta kara a tsakiya sai tashi take a tsakiyarsu, mahaifinsa kuma yana zaune a saman wata kujerar ice wacce aka mata kwaliya da fatar damisa, sai kallon masu wasan yake yana murmushi cike da jindadin, kusan rabin garin duk suna tsaye a gurin suna kallon yadda ake wasar, mazajen da suke tsaye kuma jikinsu sai rawa yake suna jin kamar su fada ayi da su. A cikin masu wasan har da Liya wacce ke sanye da rigar fatu, ta sako gashin kanta har baya, sai tai masa kwalliya da gashin tantaba yai mata kyau kamar wani ribbbon, hannunta sanye da wuri kamar yadda duka kafafuwanta suke sanye da su, duk wani motsi nata sai sun motsa, wuyanta sanye da kokon kan mujiya wanda ya bushe aka yi mata tsarka da shi. Wasa take sosai kamar wata yar buri, yadda take wankwasa hannunta da jikinta sai ka dauka wata macijiya ce. Mikewa tsaye Wasin yai ya fara busa sarewarsa sai gurin ya dauki wani kalar sauti mai dadi ga iska na kadawa yana daukar busar tana karade ko'ina na gurin. Wani irin kuzari ne ya kara shigar Liya sai ta ji kamar dominta kadai yake busar, a lokacin ne ta fara kada kafafuwanta da kunkurunta wurin da ke jikinta yana ta kara, sauran yan rawan kuma sai suka rika buga kafarsu a kasa su ma wurin da ke daure a kafarsu ya rika kara. Duk abunda ake ran Sarkin cike yake da farinciki da annushuwa, domin wasan ba karamin kayatarwa tai ba, kuma wasa ce wacce ya samu asali tun kaka da kakanin. Bayan ya gama rawar aka shigo da gassashen naman kuraye, yanka daya ake yankawa kowa ya dauka ya ci, haka ake a duk lokacin da akai wami wasa, ta nan suke iya gane wanda ba jininsu ba kuma ba dan garin ba, idan kai ba dan garin ba ne ka ci naman kurar a take makoshinka zai fara kaikaiyi, domin naman tsafafen nama ne. Sai da aka gama komai sannan Wasin ya saka daga kan bishiyar, ya isa gaban mahaifinsa ya kwashi gaisuwa, sannan ya fara tafiya barin garin, daman shi be saba kwana a cikin garinsu ba. Yana tafiya yaji ana binsa a baya, tsayawa yai cak ya duba tafin hannunsa, sai sunan liya ya fito rubuce a cikin manyan baki. Juyawa yai ya kalleta sai ta sakar masa murmushi ta biye hannayenta a baya tana wasa da su. “Ya akai?” Ta girgiza masa kai alamar babu komai, sai kawai ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai ya sake jinta a bayansa, sake juyowa yai ya kalleta nan ma kan ta girgiza masa, sai ya nuna mata bayanta, tana juya bata ga komai ba ko da ta juya har ya bace. Dariya yai ta kwala masa kira da iyakar muryarta. “Wasin.......” Manyan duwatsun da suke gaban garin ta fara kallon duk da kasancewar dare ne, sai dai akwai hasken farin wata da zai iya bata damar ganin duwatsun ban da abun da yake kansu domin sun mata nisa sosai. A saman icen da ya saba kwana ya hau ya kwanta yana ta kallon manyan taurarin da suka haska samaniya su kai mata ado, ga iska mai sanyi sai kadawa yake. FADIME POV. _A yau ba mafarki nai ba a fili na ji busar, amman ban ga kowa ba_ Bayan ta rubuta wannan ta sake buge wani fegin ta rubuta. _Kuma yau ma naggen Bappa ta mutu, kuma kadangaren dake bandaki ya biyo ni_ Bayan ta rubuta ta rufe littafin ta aje a inda ta saba ajeshi tare da biron, haka take duk abunda ya faru a wunin ranar sai ta fada, idan tai mafarkin busar sarewar nan ko mutumen nan da yake bayanta ma rubutawa take, ita ala dole ga yar boko. “Fulani” “Inna” “Warre” Ta mike tsaye ta fito daga dakin zuwa inda mahaifiyarta take zaune tana kiranta. “Gashi nan an gama dauki ki je” Sai ta gama kirga gidar ko ta nawa ce sannan ta dauka ta dora saman kai, ta koma can kusa da dakinta ta dauki wani karen zana ta fice daga gidan. Dandali ta nufa tana tafe tana rera wakar da ake a dandalin ta Fulatanci, tun kan ta isa ta hango yadda dandali ya cika da mutane masu sana'a sun baza, masu samari kowa ya ja tashi gefe suna fira, masu rawa da wasar dandali na yi. An kunna wutar kara ta kama sosai ta haske ko'ina na gurin. A gurin da ta saba zama ta zauna ta aje gidar dake kanta a gabanta tana bawa idonta abinci. Sai kusan sha daya sannan kowa ya watse wadanda sukai ciniki sun yi, masu samari kuma akai sallama kowa ya nufi gidansu. Ita ma kanta a gajiye ta dawo gida tana hamma, ko da ta iso Inna ta gyara mata gurin kwanciyarta sai kawai ta shige dakinta ta kwanta. Misalin karfe biyu suka fara jin tafiyar jakuna a rufin dakin na zana, can kuma ta fara kukan mage, kamin ta koma kiran sunanyen mutanen gidan. A take Fadime ta tashi zaune ta kwala wani uban ihu tana kiran sunan Babanta. “Bappa Bappa Bapppa.......” Kamar jira ake sai ta fara jin kokan magen a bakin bukkatar tana koyonta da sautin kukan magen. “Bapkwau Bapkwau” Sai kuma ta ji tafiyar dakuna a tsakar gidan, har da wani tuma suke suna direwa, sai kuma ta ji kamar kukan kare, a lokacin ne tai ihun na gaske wanda ya farkar da Bappa daga bachin da yake domin shi idan sabo ya saba da irin wannan abun, dan haka baya hana shi bachi ita din dai ce da ta kasa sabawa kuma a duk lokacin da ta ji sai ta yi ihu ta kirashi. Da sauri ya budewa zagen da suka sako wanda shi ne murfin bukkar ya fito, sai yai arba da bakar mage tsaye a kofar bukkar Fadime, cikin kuzari ya nufi inda tabaryar gidanta take ya dauk ya jefeta da ita da sauri tai tsalle ta haye saman bukkar tana masa kuka sannan ta sauka da can baya. “Bappa....” “Kone Fulani addu'a akai idan kajji haka haba, kai kullum in zaka kwanta baka addu'a Fulani” “Ni addu'ar wuya take ba ni” Ta fada bayan ta ga mahaifinta a cikin bukkatar yana lalaben inda take ya riko hannunta suka fito, komawa yai da ita dakinsu ya saka ta a ta su bukkar, ya kunna ashana ya lika a kyandir yai mata shimfida a kasa, shi kuma ya hau saman gadon karan ya kwanta, mahaifiyarta na daga gefe kwance sai kwasar bachinta take. 03/12/2021, 08:22 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *12* SIRLEEM POV. “Tun kwanan baya nai maka maganar, ya kamata mu fara hada lefe ba ka ce min komai ba” Ya daga kansa ya kalli Mahaifiyarsa, kamin ya sake kallon Jarma wanda tun da suka gaisa be sake ce masa komai ba, sai kuma ya sake kallon mahaifiyarsa. “Yarinyar da aka ce sai ta gama makaranta, idan mu ka ce za mu hada lefe yanzu ai mun yi sauri” “Ba dole sai ta gama makaranta za ayi auren ba, ba zan iya jira har lokacin ba, idan muka hada komai mu kai musu su ce ba za su karba ba” “Amman already an yi wannan alkawarin ai, be kamata mu tayar ba” “To ni na tayar sai ya? Malam ka fara bada kudin da za a hada maka lefe kaji” “To In-Sha-Allah” Ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fice daga dakin. Da wani kallo mai kamar harara ta bishi har ya fice, sannan ta kalli Jarma. “Yaron nan idan ba mu yi da gaske ba, zai iya ba mu kunya” Jarma yayi murmushi. “Karki ji komai Hajiya, ai yana da biyayya ba zai tsaba miki ba, yanzu matsalarmu guda biyu ce, Mai Martaba da kuma Shattima, kuma na sama mana mafita” Hajiya ta mike tsaye duk da isar da take ji da kasaitarta ta isa bakin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta zauna. “Wace mafita ce?” Jarma yayi murmushi a karo na biyu sannan ya ce. “Akwai wani gari can yamma da Katsina, garin wasu matsafa manyan arna, ance aikinsu kamar yanka wuka yake” Hajiya ta dauke kai cike da kasaita. “Na saba jin irin wannan daga bakinka, sai mun gwada kuma mu ga ribar yar adan ce, ni yanzu masu yi da gaske na ke nema” “Wannan karon masu yin da gaske ne Hajiya, domin su ba a musu aike sai dai mai sako ya isa da kansa, bari ki ji na fada miki a yadda aka ba ni tarihin garin basa bako, sai da sanin manyan gari gudun kar rayuwar bakon ta shiga hadari, wanda ba jinin garin ba baya zama garin. Sannan aikinsu kamar yankam wuka ne, sha yanzu magani yanzu, tun kan ki fadi bukatarki za su sanardar ke dalilin zuwanki da inda mafita take, ke bari na baki wani labari gaba daya jama'ar garin ba su yarda da wani abu wai cigaba ba, na zamani ko mai moriyarsa, in yanzu kika ce a kashe miki Shattima take za su masa harbin kasko su aika shi lahira, mayan yan siyasa da masu kudin garin nan ance can suke yada zango dan biyan bukatunsu” Cike da gamsuwa Hajiya take kallon Jarma, yadda ya koda mata mutane da ace ba a gaske haka suke ba, zata iya yarda domin ta ji abunda ta dade tana nema. “A ina ka san su Jarma” “Wani abokina Malam sa'idu ne ya fada min su, shi mutumen Bandalo ne wani kauye da ke Katsina, sai dai cirani yake a garin nan sai dai shi din amintaccen na ne” “Mutumen da zai iya rike mana sirrinmu ne?” “Idan ma zai tona mana asiri, sai dai ya fadi cewar ina nemawa yata maganin aure ne, domin na fada masa yata Nafisa ce take fama da bakaken aljannu da suka hana ta lafiya kuma suka hana ta, sai ya bani shawarar cewar da zan iya da naje can zan samu gani a take” Murmushi mai kyau Hajiya tai tana kallon tv dakinta kamar da gaske hankalinta yana can. “Jarma sarki wayau” “Hajiya kenan, wani ai be isa ya san sirrin mu ba, sai dai zuwan ne da kamar wuya a yanzu” “Zuwa ba shi da wahala duk inda samu yake zan iya kai kaina, ba ni da kowa a katsina amman zan iya karyar zuwa wani gurin sai mu je can, matukar zan samu biyan bukatata Jarma, bana tsoron ratsa ko'ina zuciyata a bushe take” “Zan neman takamaimen inda garin yake, da inda ya kamata mu sauka da kuma wanda zai magana jagora a cikin garin” “Ka nemo Jarma amman ka tabbatar idan muka tafi ba zuwan banza za mu yi ba, za mu samo maganin ciwon mu” “In-Sha-Allah” Daga haka yai mata sallama ya fice daga dakin, ita kuma ta mike tsaye ta isa gaban windows dakinta tana kallon bayan gidan, ji take kamar ta runtse ido ta ganta a garin. FADIME POV. A yau ma sai da ta rubuta domin ta yi mafarkinsu, sai dai a yau mutum biyu tai mafarki da nai busar sarewar nan da kuma dayan da yake tsaye a gefensa dukansu sun bata baya ne. Daga bukkatarta ta fito ta nufo inda Inna da Amo suke zaune suna maganar sarautar garin. “Ni ina ganin kamar abun nan zai zama rigima ne, tun da duka yayan suna son sarautar fa” Amo ta lashi baki da wata uwar tsaga da ta bata mata fuska tace. “Mu dai na mu ido, ban da rashin hadin kai, yayan uku ba za su hakura su bar wa daya ba? Wannan ai ba burgewa ba ce” “Ni ma dai haka na ce” Fadime na zuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta ta kwanta jikinta. “To mage sarkin son jiki daga ni” Da sauri Fadime ta dago ta kalli Inna wacce tai mata maganar. “Inna jiya ma sai da mage ta zo” Hanzarin tashi tsaye Amo tai ta dauki kwayar danyen manshanunta ta dora saman kai. “To muka zamu bunni sai wada hali yai” Bata ko tsaya jiran abunda Inna zata ce mata ba ta saka kai ta fice daga gidan da saurinta, har kusan karo su kai da wata makociyarsu wacce ta kunno kai cikin gidan rike da takarda hannunta. “Maraba da Nene” “Na yalle dam Inna Fadime” “Janfelen” “Na sukkaɓe?” “Janfelen, na wurinde?” “Janfelen” Ta zauna inda Amo ta tashi tana mikawa Fadime takardar hannunta. “Fadime karanta mini injiya minana Mai samari yak aiko min” Fadime ta karbi takardar ta bude tana karanatawa, gaisuwa ce farko sai tambayar lafiyar mahaifiyarsa sannan ya sanar da ita sakon kudin da ya aiko mata dubu bakwai ta hanyar abokinsa, dan rani. “Munafwuki amman be ba ni komai ba, sai wasika, yalla ya aza babu me karanta min ita, bari naje yanzu na iske shi, mugun ba'adare” Inna ta saka dariya ita da Fadime dan sun san halin Nene da kudi bata jin has. Nene ta fita daga gidan sai fada take ko sallama bata tsaya yi ma Inna ba. “Fadime tashi ki tahi rahe ki samo mana diyam” A take ta bata fuska ta fara shura kafafuwanta. “Inna ko hutawa ban yi ba, yanzu na farka daga bachi ai” “Wallahi ina sa miki sanda yanzu, wa zai dauko ruwan ni?” Ta tashi tana zabure zabure ta dauki tulun ruwa ta fice daga gidan, tana sanye da kayan fulani riga da zane cigiyarta a sake kanta kuma babu dankwali sai dan xaren kwaliya da suke daurawa akai ta raba gashinta gida biyu ko wane tsoro ya sauko bayanta. A maimakon ta taje zafin da ta saba diban ruwa sai ta nufi babban gulbi garin da ba kowa yake zuwa can ba, saboda nisansa da kuma girman da gurbi yake da shi domin gulbi ne da ya hada mayan jihohin yanki. Baki baki ya tsaya ta saka tulunta cikin ruwan ya cika ta cire ta aje, tana waige waige ko zata samu wanda zai dorata kasancewar safiya masu kamun kifi sun gama sun tafi sauran mutane kuma ba su fara hada hada a gurin ba. “Kai kado, ware” Ta kwalawa wani bahaushen mutum da ta hango can nesa da ita. Amman ko kula ta be yi ba. Zaune tai a gurin tana ta wasa da ruwa da kafafuwanta, kamar ance saurara ki ji sai ta fara jiyo busar sarewar nan can nesa da manyan duwatsun da suke gefen gulbi, da sauri ta mike tsaye, ta fara waige waige sai kuma ta fara gudu tana nufar inda duwatsun suke, gudu take sosai kafafuwanta babu talkami domin a can ta baro su gurin da ta cika tulun, manyan duwatsu ne wanda hanyewa samannsu ma wani sabon aiki ne amman a haka ta rika dafa tana rarrafe kamar dole har ta haye sama, mikewa tai tsaye tana kallon mutumen da take hange a saman wani dutsen da ke can nesa da ita yana busar, jikinaa babu riga sai walki sanye a kugunsa, ba zata iya tantance fuskarsa ba domin baya ya bata kamar yadda ta saba mafarkinsa, wani irin gwalo ido tai waje ta hangame baki tana kallonsa, ya mata nisa sosai bare ta jira shi ya jita ko kuma ta jarasa kusa da shi, sai dai busar da yake ya karade ko'ina saboda yau a saman dutsen yai ta sabanin a da fa yake yinta a kasa ko a saman ice. Sai da ya gama busar sannan ya juyo ya fuskanci inda ya bawa baya, sai ya hango wata yarinyar da be tana gani ba ba kuma zai iya tantancewa ba tana kallon inda yake. Gangarawa yai ya sauka daga saman dutsen yana kallonsa tun tana hangoshi har ta daina ganinsa, a lokacin ne ita ma ta sauko da wani irin gudu kamar sabuwar mahaukaciya, tana isa gurin tulunta ta zubar da rabin ruwan ta dauki tulun ta dora a kai ta saka talkaminta ta nufi gida da sassafar zuciyarta na bugawa da karfi kamar zata fito daga kirjinta, numfashin ma daker take yinsa. Ta kasa yarda cewar abunda take gani a mafarki shi ta gani a zahiri, mutum ne ko aljanani? Miyasa yake zo mata a mafarkinta? Kuma a irin busar da ta ji yana yi a yau? Why ba shi da tufafi a jikinsa? Why yake busar a kusa da inda zata iya jinsa? Wanene shi? Duk tana bukatar wadannan amsoshin a yanzu. A bakin bukkar Inna ta aje tulun ta shige bukkarta, ta dauko littafinta ta fara rubutawa abun ya zame mata kamar wajibi. AA POV. Ba karamin dadi ya ji ba kudin da Nana ta saka masa a account, sai dai ko kadan hakan be bashi natsuwar ya cigaba da zama a unguwar ba, domin a ganinsa kamar ana dana masa tarko ne, line ma cire shi yai ya aje ya daina kira da shi ya dauko wani tsohon line sa ya saka a wayar. Baya tafiyar da zai yi nisa da gidansu, ba dan komai ab sai dan ganin yake kamar idan ya bar unguwar za a iya kama shi, ita kanta Anti Rabi ta lura da rashin natsuwarsa har take ganin kamar ma ya fita tsoro. “Idan kana jin zaman ka a nan ba zai yi ba, ka koma cikin gari gurin Kawo ka zauna na kwana biyu tukuna, duk da dai na ga kamar ba za a maka komai ba” Ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta. “Anti bayan faduwar da mu kai yarinyar ta sake ba ni kudi fa” Anti ta zaro ido. “Yaushe ka hadu da ita har ta baka kudi” A dolen dolensa ya labarta mata yadda komai ya gudana da kuma irin tsoron da yake ji da kuma zargin an dana masa tarko da yake. “Ai Allah ya kara maka, AA wani irin mayen kudi ne kai? Sai ka jawa kanka fitina ko? So kake azo a kulle mu gaba daya kuma kasan ba mu da gata sai Allah, idan ma ba tarko ne ta dana maka ba, wata kila yarinyar sato kudin take ko kuma tana samo su ta hanyar da be dace ba, duk ranar da dubunta ya cika kai zata nuna” A take AA ya ji kamar ya saki fitsari domin shi be kawowa kansa tunanin tana samun kudin ta hanyar da be kamata ba ne, sai yanzu da Anti ta fada. “Anty yanzu ya za ayi?” “Ina na sanar maka? Ai kara ka koma can unguwar Waziri gurin Kawo Bala, idan ma wani abun za maka kara ace kana kusa da wani babba namiji” Shiri yai ba dan yana so zai bi shawarar tata ba sai dan be da yadda zai yi, idan har sata take tabbas zata jefashi a cikin matsala kara ma ya koma unguwar da bata sani ba ko da ta zo gidan ta tararda baya nan. A take ya shiga cikin dakinsa ya hada kala biyar ya saka a jakarsa ya fito. “AA ka rika hakuri da rayuwa, rashi ba hauka ba ne, kai maraya ne kana ta neman jefa kanka a cikin matsala, kai kawarda idonka daga neman kudin nan dan Allah, idan kai hakuri sai ka same su cikin sauki, amman wannan bude idon da kake sai ka ga ka samu kudin ta hanyar da be dace ba, idan kai hakuri zaka samu duk abunda Allah ya rubuta maka cikin sauki” Anti ta fada cike da damuwa, ta san kanenta ba irin yan iskan samarin nan ba ne, ba zai aikata wani abu dan neman kudin ba, amman tana tsoron shedan da zuciya, domin son kudin AA ba na wasa ba ne ita kanta ta sani. “Shi ma wannan yana cikin rabo na ne Anti, yarinyar Allah ya kawo ta ne dan na yagi rabona” “Ko kuma ka yagi rabon wahala ba, gashi nan ai ka fara boye boye ka kasa komawa aikinka, ka kasa natsuwa” “Ke dai ke yi ta min addu'a kawai, Allah ya sa kar ta tona mana asiri, amman fa ko gobe ta bani sai na amsa” “Idan an kama ka kar ma ka fadi sunana Wallahi” Ta fada a fusace sannan ta shige dakinta, shi kuma yai murmushi ya fice daga gidan. HAJIYA KARAMA POV. “Abun da kike yi be dace ba Zainab, taya Shattima zai yi magana ki musa masa, a iya tunani Shattima ko cewa yai ki dauki wuka ki yanka ni za ki iya” Da mugun mamaki Zainab ta kalli Iya. “Iya kin san abunda kike fada kuwa?” “Na sani, biyaya ya kama ace kina musu ta kowane hali kamin ki gina kanki” “Ba ki wulakanci da akai miki ba ne” “Wannan duk mai wucewa ne, ki koyo juriya da hakuri Zainab ki koyi kaskantarda kai sannan za ki samu nasara a komai, shakarata talatin a gidan nan na san ko waye Shattima kuma na san waye Ammy” “Ba fa siyasa na ke ba, balle ace na nemi soyayyar wasu, abun da akai miki be kamata ba sam” “Idan har kin ji zafin abun da aka min ya kamata ki fara kishin mahaifiyarki ki taya ta yakin da take, har mu ci nasara, kuma ki fara tunanin gina kanki, ban yarda ki yi ma Shattima rashin kunya ba domin shi din wata rana shugabanki ne” “Na fara tunanin gina kai na Iya, tabbas zan yi aure na bar gidan nan” Ta karasa tana kara zare manyan idanuwanta, Iya ta girgiza kai domin ba haka take son ji ba. Zainab ta mike tsaye ta isa gaban madubi inda wayarta take aje tana ringing ta dauka ta kai kunne. “Hello Ra'ees” “Na'am Hajiya ya kike?” “Lafiya Kalau ya ake ciki?” “Komai kalau, MBS ne suka shigar da gasa, suna son hoto da zai dace da kamfaninsu a week din nan” “Miye hadina da kamfanin MBS?” “Sun bada damar photographers su turo hoton da suke ganin ya dace ya hau, idan kai nasara kai za su bawa ambassador na kamfanin na shekararar na kuam kin san ba kana nan kudi za a samu ba” “Zan yi tunani a kai” “Na turo miki komai ta whatsapp idan kin hau za ki gani” “Okay” Cike da gadara ta aje wayar ta ja stool din madubin ta zauna tana kallon kanta. Iya ce ta zo bayanta ta tsaya tana kallon irin kyau da yarta take da shi. “A yadda kike da kyau nan, kamata yai ace Sarki ne ya auri ki, ba mijin kawa ba” “Mijin kawar nake so Iya, ba zan iya auren tsoho ba” “Ni ma ban ce ki auri tsoho ba, amman kina iya auren mutumen da za ku tsufa kuna cin moriyarku” “Shiyasa na ke son na auri Auwal ai....” “Kashiiiii kin kasa ganewa” “Babu fa abun da zan gane Iya, ni shi nake so kuma aurensa zan yi” “Allah ya taimaka ya kai mu lokacin” Iya ta fada fuskarta ba yabo ba fallasa, sai Zainab ta juyo ta kalleta tana murmushin jindadi. “Yauwa yanzu na ji magana, Amin thank you” Dan murmushi kadan Iya tai mata sannan ta ce. “An jima ki samu Shattima ki ba shi hakuri” “Zan yi hakan In-Sha-Allah” Iya ta gyada mata kai sannan ta juya ta fice daga dakin. NANA POV. Tun da ta dawo school tana cikin dakinta bata fito ba sai la'asar, duk mutanen da ke zuwa gaisuwa sai dai su lekota ko kuma su tambayi lafiyarta Ammy tace musu tana ciki. Tana fitowa daga dakinta ta nufi dakin Ammy, kai tsaye ta tura dakin ta shiga babu ko sallama, Shattima na zauna saman kujera Zainab na gefensa ita ma zaune, shigowarta yasa ya dago ya kalleta Zainab ta miko mata hannu. “Hey Baby zo nan...” Nana ta karasa kusa da ita ta tsaya, dan ba zaman take son yi ba, Ammy dake bandaki take jiran ta fito. “Waya taba ki?” “Ni bana son School bus tana kai ni makaranta” Ta fada a shagwabe, tana dan satar kallon Shattima da yaki ya sake kallonta. Kamin Zainab tace komai Ammy ta fito daba bathroom din fuskarta jike da ruwa. Kallo daya tai ma Nana ta dauke kai ta karasa bakin gadonta ta zauna, sai Nana ta matsa kusa da gadon tana turo baki domin kwata kwata yau bata jidadin yadda aka kaita makarantar ba aka dawo da ita. “Ammy ni bana son school bus tana kai ni makaranta” Kallonta kawai Ammy take. “Nana wai me yake damunki, tunanin ki dabam, ki duba yarinyar da take zuwa gyara dakin yaran can ba ta wuce warinki ba, amman aiki take zuwa nan, kina tunanin ita bata son gata nan? Ko bata son karatu? Me kika nema kika rasa ne? Tun da kika dawo school kika shige daki kika zauna duk masu shigowa sai tambayarki ake amman kin zauna a can kamar ba ki san rashi mu kai ba? Abinci ma ba ki fito kin ci ba, what is wrong with you?” Ta yi shiru bata ce komai ba, domin bata da abun cewa ita dai karatun ne bata so. “Driver na ke son a daukar min” “To ba za a dauka ba, kuma dole ki je makaranta, Islamiya ma yaushe rabonki da zuwa?” Ammy ta amsa mata kai tsaye. Sai ta kara bata fuska. “Wallahi ba zan karatun ba, indai ba a daukar min driver ba ba zan sake zuwa makaranta ba” “Idan kin yi karatun ni zan karu ko ke? Shashasha, ba ki son a fada miki gaskiya, kin fi son a barki ki yi ta hauka, kuma Wallahi kika ki zuwa makaranta sai na sa sarkin bulala ya zane miki jiki” “Ai daman ba so na kike ba, shiyasa kika saka Baba Waziri ya kwashe komai na dakina....” “Eh bana son ki, je ki nemi wata uwar da take son ki, idan ba ki bata min rai ba hankalinki ba zai kwanta ba, idan so kike na miki ba ki wata rana zan miki, duk ranar da bana raye sai ki nemi mai fada miki gaskiya ki rasa, sakaryar kawai nai kukan ciwon Mahaifinki na yi na ki...” Ammy ta karasa cikin fada hawaye na sauko mata, da sauri ta tashi ta koma bandakin. Nana na juyowa Shattima ya wanke mata fuska da mari. “Stupid girl, wuce ki je ki hada kayanki yanzu nan driver zai kai ki gidan Baba Waziri” Fashewa tai da kuka ta fice dakin da gudu. Zainab ta mike tsaye tana kallon yadda ran Shattima ya bace. “Shattima ka rika daga mata kafa yarinya ce” “Ta fara wuce gona da iri, abun ta gaba yake ba baya, i hate nonsense” Ya amsa a fusace sannan shi ma ya fice daga dakin. Ko kadan Zainab bata jidadin abunda ya faru ba, amman ita tana kallon Nana da kurciya ne da kuma shagwaba, a gurin ta aje wayarta ta fice zuwa dakin Nana. 03/12/2021, 08:22 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *13* Tun ranar da Fadime ta ji ga mutumen nan mai busa bata sake ganinsa ba, hakan kuma be saka ta fasa zuwa gurin manyan duwatsun ba a kullum tana leka ko zata ganshi. Kuma tun ranar bata sake jin busar ba, bata sake mafarkinsa ba, a lokacin ne ta fara rayawa a ranta cewar aljani ta gani kuma shi take mafarki. Kasancewar yau friday da safe ta fito da shanun kiwo, daman duk Friday da safe take kiwon kasancewar jumma'a kurarren lokaci ne. Shanunta na gaba tana biye da su, kanta sanye da malfar saƙa, ta daura zare a wuyanta da gaban goshinta, dan karamin kare na binta hannunta rike da sandar korar shanu bata fasa wakewaken da Inna take hanata ba. Sai da suka isa bankin rafi sai ta nufi inda ta saba zama, ta zauna tana hango wasu shannun da wani bafullatani dake can nesa da ita yake kiwo. Kanne ido daya tai ta fara kirga masa shanu daga inda take zaune, sannan ta dawo kirga nata. “Nawa sauran 37, idan wata ta sake mutuwa yau sauran 36 idan wata ta kara mutuwa sauran 35...” Bata karasa kirgen ba ta soma jiyo busar sarewar tana karade dajin. Bude baki tai ta zaro ido ta fara dukuduku ta ratsa cikin marar sannan ta mike tsaye tana leken inda ta fi jin busar na fitowa, sai kuma tai dukuduku ta dawo ta haye saman dutsen ta mike tsaye. Hangoshi da tai a saman wani dutsen zaune yasa ta kara gwale idon. “Kai...........” Sai ta ji muryarta ta amsa duka dajin da kiran da tai masa. “Laaaaaaa” Ta yi dariya, wani dadi taji yadda ta ji muryarta ya gwauraye dajin, a yanzu ta gano dajin ne ke da daukar sauti. Saukowa tai saman dutsen da sauri ta fara gudu tana daga kanta sama tana hango dutsen da yake zaune, kamar wacce aka koro haka take yankan dajin tana gudu har ta isa gaban katon dutsen a lokacin ne ta ji sautin busar sarewar sosai a kunnenta, labewa tai jikin dutsen tana dariya marar sauti tana kara zaro ido. Gaba daya ta manta da wani zancen aljani ne ko mutum, sai ta dan lekesa ta sake boyewa tana dariya har da su kyakyatawa kadan ta rufe bakinta.        Zaune tai a gurin tana ta sauraren fusar sarewar dake shiga kunneta, har da wani lumshe ido take tana budewa. Lokaci daya ta daina jin busar saurara tai na dan lokaci ta ji ko za a cigaba, shirun da ta ji ne yasa ta tashi ta leka sai ta ga babu shi a gurin, hakan yasa ta fito gaba daya tana kallon dutsen. “Ina yaje?” Ta tambayi kanta tana tare hasken ranar dake haskata da hannunta, domin malfar dake kanta ta fado bayanta igiyar malfar ce kawai a wuyanta, kara natsawa tai tana rabon ido, sai ta hangoshi yana saukowa saman dutsen. Saurin komawa tai ta boye tana yarfar da hannunta tana dariya da jindadin ganinsa da tai. Amman da yake saukowa ina zai je? Gurinta ko wani guri? Ta dan zaro ido kamin ta kara shan jinin jikinta jikin dutsen tana saurare ko zata ji takun tafiyarsa ko motsin wani abu, amman sai ta ji shiru hakan yasa ta fara takawa kadan kadan ta leka sai ta ganshi tsaye yana kallon inda take kamar daman can jiran yake ta leko ya ganta, da sauri ta koma sai a lokacin ne tsoro ya fara kamata. “Wayyo Bapppa.....” Ihun da tai ne yasa ya karaso kusa da ita yana kallonta, hannunsa rike da sarewa, sai dan walkin dake daure a kugunsa, fari ne sol kuma kyakkyawa gashin kansa ya kwanta luf kamar bafulatani idonsa ma fari kal kamar madara ga dogon hancin daya kara kawata fuskarsa. Dukewa Fadime tai kasa ta rufe ido tana kuka. “Bapppa.....” Bappan kawai take kira kamar ance mata zai ji ta daga inda take, tasa hannayenta ta rufe fuskarta sai rusar kuka take kukan da ba hawaye. Shi dai kallonta kawai yake cike da burgewa ba yau ya fara ganinta ba, kusan a duk lokacin da ya bar gulbin dake kusa da garinsu ya iso wannan dan yi wwanka ko yin wani abu sai ya ganta ta zo kiwo ko deban ruwa, sai dai ita bata taba kula da shi ba sai a yanzu da yake busar kusa da inda take ji. Jin be mata komai ba yasa ta dago ta kalleshi kadan ta runtse ido, gabanta sai dukan tara tara yake. “Bapppa” Ta kira sunan Babanta da kuka, sai kuma ta sake bude ido ta kalleshi yanzu kuma so take ta tantace mutum ne ko aljani. “Ban maka komai ba, ni ban maka komai ba, ni mutum ce ni ka yi hakuri ba zan sake ba” Bayan kallonta babu abun da yake, matsawa tai baya tana yi tana kallon gefensa inda hanya take sai kuma ta kallesa, cikin wayo ta zo da mugun gudu ta taba shi da yatsanta ta daka wani uban tsalle tana son ta ranta a na kare, sai yai hanzare cafko hannun nata ya rike gam. Wani irin shidewa tai ta dawo ta bude ido sosai tana kallon hannunsa da ya rike ta da shi tana bude baki kamar zata kwala ihu kuma ba tai ihun ba, sai ta sulele kasa tana wani jan numfashi, so take ta suma kuma suman be zo mata ba. Dayan hannunsa yasa ya rikota ya jinginar da ita jikin dutsen tana kallonta. “Bapppa...” Ta sake kwala masa kira. Uffan be ce mata ba sai kallonta yake duk ganinta da yake bata taba burge shi ba irin yau, he never thought haka take da wauta sai yau and he like it. “Bapppaa Na...... ” “Wuta na binki ba ki gani ba....?” Ya fada cikin siriyar muryarsa mai dadin sauraro yana daga mata kai alamar ta duba. Cikin wani irin tsoro marar misaltuwa Fadime ta waiga kasanta. “Ba wuta dutse ne” Ta fada numfashinta na rawa domin a yanzu kam da gaske tsoro take ji. Matsowa da ita yai kusa da shi kamar zai rumgume ta dan filin dake tsakanin bayanta da dutsen yai wani abu da hannunsa kamar zai kama abu ya cafke hannunsa ya jimke sai ga wutar tana ci a cikin hannunsa. Kadan Fadime ta juya ta ga wutar sai ta kara bude ido ta kwala ihu. Shi kam kallonta kawai yake har tai ta gama sannan ya juya ya fara tafiya. “Kai a aljanine?” Ya girgiza mata kai alamar a'a. “Kai ka saka min wutar?” Nan ma kan ya girgiza. “Ya akai ka ga wutar waya saka min wutar?” Daga inda take tsaye take aiko masa tambayoyin cikin daga murya ta yadda zai ji ta, sai a lokacin ya juyo ya kalleta sai tai saurin rufe fuskarta da hannayenta. “Wutar maita ce, mayu suke sakawa mutun ita, idan mutum yana da baiwa sai su kwashe ta su saka masa wuta, komai ya rika ko ya taba ba zai yi albarka ba, ba zai amfane shi ba, idan suka kasa cin kurwarsa sai su daddanketa mutum ya koma wawa ko mahaukaci ko musaki, akwai wanda ke bibiyarki” Yana fada mata haka ya juya ya cigaba da tafiyarsa yana murmushi, fitowa tai tana kallonsa har ya haye saman dutsen yai tsaye yana kallonta, daga inda take tsaye ta daga masa hannu shi ma ya dago mata sannan ya gangara ya sauka ta arewa da dutsen. A lokacin ne ta samu kafafuwan gudu ta dawo gurin kiwon shanunta ta zauna tana ta tunanin abunda ya fada mata. Har ta gama kiwonta nagge ko daya bata mutu ba, cikin jindadi ta kora shannun suka nufi gida, kamin su isa gida duk ta matsu, suna isa bata ko tsaya saka hannun ciki gida ba, ta shige Bukkarta ta dauko littafinta ta fara rubuta abun da ya faru, sai da ta rubuce komai tsaf sannan ta fito waje tana neman Inna ta labarta mata. FALMATA POV. Tana cikin wanke wanke ta ji Tumba a bayanta tsaye, juyawa tai da sauri ta kalleta, sai Tumba ta risino daidai kunnenta tana fadin “Wai ke Falmata ba ki da irin samarin nan masu yi ma budurwa anko? Kullum suka zo ba su da abun yi sai kawo miki abu a leda ko su baki yan kudi a hannu, haba Falmata ki rika sakin jiki mana” Cike da damuwa Falmata ta sanda kanta kasa, ta fahimci inda Tumba da dosa a yanzu. “Ke baki ga sauran yan mata yadda suke ba? Ki rika sake musu jiki da fuska kinji kina far'a samari suna son mace mai far'a” “To” “Yauwa yau duk wanda ya zo ki ce ya baki dubu uku ko biyar, in dai kina kawo min kudi haka zan rika miki komai” “To” Ta sake amsawa a ranta tana mamakin yadda Tumba take son ta zama, ta rasa me ta tare mata a dubiyar da bata son farincikinta, yau kwana uku kullum sai dare ya raba take satar kafa ta fita taje shago ta ci bashin garin kwaki ta saka a cikinta, sakamakon abincin da ba a bata a gidan. Yanzu kuma tana nuna mata wani mugun hali wanda ba halinta ba. Tana wanke wanke tana hawaye, sai ta share ba tare da ta bari Tumba ta gani ba, haka tai aikin cikin rashin kuzari sannan ta fara shara, ta bi ko'ina na gidan ta masa tas, ta dawo ta zuba ruwa a bokiti ta shiga bandaki, ta nan ta samu damar kuka iya son ranta tana tuna irin gargadin da Mama ta yi mata kamin rasuwarta. “Wannan farin jinin na ki kar ya kai ki ga halaka Fulani, tun kina yar jaririya Allah ya saka miki farin jinin jama'a yanzu kuma kin tasa samari sun fara miki sallama, bana son zuwa firar nan karki sake fita duk wanda ke son ki da gaske ya aiko gurin mahaifinki, kuma kin ga kin fara al'ada ko hannunki kika bari namiji ya rike za ki iya samun ciki, dan zai ja a wuce guri, karki kuskura bari a rike hannunki” Fashewa tai da kuka ta rufe bakinta dan kar kukan ya fito, farar fita zance da samari da take, bayan mutuwar mahafiyarta ne, wanda Tumba take bata umarni, tun tana jin kunya tana boya tana rasa abun fada har ta waye, ta iya magana da tarbar wanda ya zo gurinta. Yanzu kuma tana nuna mata hanyar da ba mai bullewa ba ce, taya za ta ce a bata kudi mai yawa haka? Cikin rashin kuzari ta gama wankan ta fito ta shiga dakinsu ta shirya cikin wani farin yadi ta saka hijabinta ta fito tsakar gida. “Na tafi” “To Allah ya tsare yar albarka” Tumba ta fada cikin daga muryar tana washe mata hakora, Falmata ta dauke kai ta fara tafiya kamar bata son zuwan ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta. “Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan, komai nai mata kamar ban yi ba, kowa nai ma ya kama ban da ita, ban san me shegiyar uwar nan ta bata ba, kudi kawai na ke kashi a banza” Tumba ta fada tana rafka uban tagumi, tana tuna abunda Malam na zaure ya fada mata game da Falmata. “Idan ba ki yi da gaske ba, yarinyar sai ta gawurta, ina ji miki tsoron abun da zata zama nan gaba” Wani dogon ajiyar zuciya ta ja ta sauke. “Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan idan nai wannan a banza, wacan a banza” Ta furta cike da jin zafin irin kudin da ta kashe akan Falmata amman har yanzu shiru, farinjinin da take son ya gushe ba daina ba, abu ma kamar ƙaruwa yake. Falmata na tafe tana tunanin maganganun Tumba, wace karya zata mata ta tsira? Idan ma bata kawo mata kudin ba zata iya dukanta ko ta mata wani sharin. Bata hankara ta ji an taka burki da karfi wani abu ya bugeta ta fada can gafe, da sauri ta rike kafarta da bata warke daga daurin da Baba tai mata ba, yau kuma ta sake jin ciwo a kafar, da sauri Sirleem ya fito daga motar ya karaso inda take. “Ba ki ji ciwo ba? Ina ta horn ba ki lura ba” Baki sake take kallonsa idonta kamar za su fito gaba daya ta manta da wani ciwo a kafa, ta masa yardar Sirleem take gani da gaske shi? Ko mai kama da shi. “Sannu ba ki ji ciwo ba?” Yana tambayarta ta kuma ta kasa amsawa sai kallonshi take tana ganin abun kamar a mafarki, daman kuma ba jinsa take ba tun sai an yi da karfi take iya ji. “Hey” Ya kada mata hannunsa a fuska sai a lokacin ne ta dawo hayyacinta, a lokacin ne mutane suka fara taruwa kallonsa da kuma ganin abun da ya faru. Rawa jikinta ya fara yi idonta ya cika da kwalla bata san lokacin da ta riko hannunsa da sauri ba. “Dan Allah kai ne Sirleem M2 ko kama ce kawai” Kallonta yake for few seconds sannan ya ce. “Ni ne” Tana kallon yadda bakinsa ke motsi da yadda ya nuna kansa ta san magana yai, amman bata ji komai ba saboda be yi da karfi ba, gashi kuma tana son jin muryarsa. “Bana ji sosai sai ka fada da karfi, dan Allah kai da karfi na ji muryarka kanji” Ta sakin hannunsa tai ta rike kafafunsa ta fashe da kuka. “Ni ne” Ya amsa mata da karfi yadda zata ji, ta ji muryarsa sai dai akwai banbanci a tsakanin muryarsa ta cikin waka da kuma ta zahiri, amman tabbas kamaninsa da wacan Sirleem din ba su da banbanci tun daga kan sajen har farin da tsaye da iya wanka. “Wallahi ina matukar son ka, ni masoyiyarka ce sosai, ina kaunar wakokinka, ban tunanin Allah zai hada ni da kai cikin sauki haka ba, na gode na gode da ka kade na yafe maka na yafe maka Wallahi ina kaunar sosai” Jikinta har rawa yake sanadin kallonsa da take, hawaye kuma suna ta aikinsu a fuskarta, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba. “Ko dai mafarki na ke yi” Ta tambayi kanta tana taba fuskarta, sai yai murmushi ya cire facing cap din dake kansa ya saka mata akai saman Hijabinta, yana girgiza mata kai alamar a'a ba mafarkin take ba fuskarsa da murmushi. Hannunta ta kai ta cire hular daya saka mata ta rumgune hular tana kuka, a nan wasu suka fara tsaki suna fadin wai abun ta yayi yawa sai kace wacce ta ga wani sahabi ko Annabi, ita kam ta san me take ji a kan Sirleem kuma ganinsa da tai a yau yasa ta kasa yadda ma a duniya take. Hannu yasa aljihunsa ya ciro wallet dinsa ya ciro kudin da za su kai 5k ya mika mata, sai tai saurin girgiza kai. “A a ni bana son kudi, na gode da ka kide ni, na gode na yafe maka” Kai kawai ya kada mata daman kuma be jin zai iya kara ce mata wani abu tun da sai an yi magana da karfi zata ji, sai ya sara mata ya nufi motarsa ya bude ya shiga masu aikin daukarsa a hoto suna ta yi, da kallo ta bishi har ya tashi motar ya hau titi. Sannan ta mike tsaye ta saka hullar cikin hijabinta tana jin wani irin farinciki a ranta marar misaltuwa. Gaba daya ta manta da wani tunani da bacin rai, sai laleben hular dake kamshin turarensa take tana jan numfashi tana saukewa, yadda zata labartawa yan islamiyarsu da kawarta labarin yadda ta ga Sirleem yau kawai take tunani, har ta isa masarautar murmushi be gushe daga fuskarta ba, ji take kamar yanzu komai ya faru. Zancen wani haduwa da Iya da fargaban da take samunta idan zata shigo gidan duk ta manta sai murmushi kawai take tana jindadi a ranta. Door bell ta danna sannan ta samu guri ta zauna a gurin tana jiran a bude mata kofar, after like ten minutes aka bude kofar. Mikewa tai tsaye sai tai arba da Iya hakan kuma ba karamin fadar mata da gaba yai ba, a take murmushin fuskarta ya gushe, Iya sai kallonta take irin kallon nan da ke nuna mata komai na jikinta har yadda jini yake gudana a jijiyarta, Falmata ta yi kasa da kanta ta saka cewa Iya ina kwana balle tace ta bata hanya ta wuce. Ba kallon bakinciki abun da ya faru kawai take mata ba har da na kurwarka dake ta yawa a saman kanta kamar fara, irin ta ce mai wuyar kamu, kurwar da ke yin kasa mai kamar hawainiya ita tafi saukin kamu sai kuma wacce take yawo a kasan kafafuwan mutum, wanda wani lokacin kasan kafafuwan mayu suke kallo su kama kurwar mutum. Akwai wance take kamar tantabara ita ma tana da wuyar kamu sai dai bata kai mai kamar fara ba wacce ke fira. A take jikin Falmata ya fara wani tsamtsamtsam wanda hakan ke bata cewar ba mutumen arziki bace, a take ta fara karanta addu'o'in da ta iya, sai iya ta kauce mata da sauri tana mata alama da ta shigo da hannunta. Ita kuma tai saurin ficewa daga falon, sai da Falmata ta juya ta kalli ficewarta sannan ta juyo ta nufi hanyar dakinsu yan uku, tana ta mamakin yadda Iya ta rikirice saboda Addu'ar da tai. ‘Idan zan sake zuwa sai na samu furen tumfafiya na hada da goro na zauna’ Ta fada a ranta dan ta taba jin Tumba na fadar indai mutum yai haka yai arba da maye ba zai iya kallonsa ba. Yau ma bata tararda yaran ba, daman haka ya fi mata dan bata son tai wani abu ace ta yi ba daidai ba. For the first time yau tana ta ji tana sha'awar yin shara tana kirar suratul Baqara, surar da idan ka karanta shaidane sai yayi wata daya kamin ya sake shigowa gidanka, idan kuma ka karanta ayoyi goma na farkon surar a kullum, to kana cikin tsaron Allah babu wani abun da zai same ka, maita ko aljani ko wani shari kuma zaka wuni cikin nishadi. Daga alif lam min ta fara karatun cikin muryarsa mai dadi da kwantar da hankali ga saukarda natsuwa kasancewar qur'ane take karatu, a yanayin yadda ta kare a kirar ma sai ka dauka wata balarabiya ce ba fulani ba. Har ta yi aikin ta gama karatunta take sai da ta gyara komai tsaf sannan ta fito ta janyo dakin ta rufe ta fito daga corridor, bata wani tsaya kula wadanda suke falon ba ta sa kai zata fice, sai Ammy ta kira wata mata dake zaune kasa tana kallon tv. “Salamatu kira yarinyar can” Jikin Salamatu na rawa ta kwalawa Falmata kira tana mikewa tsaye ta nufi inda take. “Ke... Falmata ta juyo a tsorace gabanta na faduwa, ita dai tsoron ta kar ace ta yi wani abu. “Na'am” Ta taho da sauri ta zube kasa ta gaishe da Ammy kamar yadda ta lura da mutanen gidan na yi, ko daga kai ta kalli Ammy bata yi saboda tsoron irin an talaka a gaban sarki. Sai ta karaso sannan Ammy ta yi murmushi kadan tana kallonta cike da burgewa, yadda ta ji tana karatun ya matukar burgeta ga natsuwa da kuzari aiki da take ganin kamar yarinyar tana da shi, ina ma ace Nanarta ce a haka. “Duk abun da na ce ki rada mata a kunne” “To ran ki ya dade” Salamatu ta amsa, sai Ammy ta maida dubanta gurin tv kamar ba zata ce komai ba, ba dan komai ba sai dan isa da kasaita irin ta matan sarakuna musamman idan suna cikin talakawa. Falmata kan cikinta sai kadawa yake tana ta tunanin abun da tai ba daidai ba. “Ya sunanki?” Salamatu ta rada mata, sai Falmata tai saurin amsawa muryarta har rawa take kana jinta kasan tana daf da fashewa da kuka. “Falmata” “Shekarunki nawa?” “Cikin ta sha bakwai” “Kina zuwa makaranta?” “Eh islamiya, bana boko” “Saboda me?” “Ba a saka mu ba” Ko wace tambaya sai Ammy ta bada tazara take yinta kamar mai tunanin wace tambaya zata mata ko kuma mai hutawa sannan yai wata tambayar. Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, daman can Falmata shi take jira sai ta tashi da sauri ta fice daga katon falon jikinta har rawa yake. Sai da ta fice sannan Ammy ta kalli Salamatu. “Tashi ki nemo min Gambo” “To ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya da imani” Da sauri Salamatu ta fice daga falon, ba a dauki lokaci ba sai ga Gambo ta shigo ta zube kasa ta kwashi gaisuwa. “Gambo yarinyar nan da kika kawo tana da halin kwarai ko?” “Wallahi ranki ya dade ba zan dauko sheri na kawo a cikin iyalanki ba, ina wace ni, Wallahi sai da na duba na dubo na zabo sannan na dauko ta, kaf a unguwar nan ba yarinya matashi kamar ita wacce tai kunya da tarbiyar Falmata, Allah ya mata natsuwa da kamala, ga ilmin kamar ruwa, sai dai ace ba tai boko ba amman na muhammadiya kam babu abun da bata sani ba” Ammy ta yi shiru har na wani lokaci sannan ta ce. “Ma-sha-Allah, ina son ki fadawa iyayenta za ta rika wuni nan tana rainon su Labib” “To ranki ya dade, yadda kika ce haka za ayi, yanzu ma daga nan can zanje na isar musu da sakon Hajiya, Allah ya kara miki imani” Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, sai ta mike da sauri ta fice. ***  ***   *** Hajiya ta sauke ajiyar zuciya bayan Jarma ya gama yi mata bayanin salin inda garin yake, da kuma abokinsa da zai musu jaroganci. “Jarma ina tunanin kai ya kamata ka fara zuwa, domin kai ka fada masa matsalar ta yarka ce, ganina zai iya gano wani abu, sannan ba zai yiyu na shirya tafiya a yanzu ba, kai ma kuma a nemeka a rasa cikin masarautar nan, za a fara zarginmu” Jarma ya jinjina kai. “Na yi wannan tunanin Hajiya, sai dai jin cewar ba a musu sako sai dai mutum yaje da kansa yasa dole ne mu yi tafiyar a tare” Hajiya ta yi shiru na wani lokaci kamin ta kalleshi ta ce. “Zuwana kamar zuwanka ne Jarma, domin bukatar da nake da ita ita ce a kanka, idan ka je ka ga guri sai mu shirya wata tafiyar daga ni sai kai mu tafi ba tare da abokin ka ba” “Abokina amintaccena ne Hajiya karki samu damuwa da shi” “Bana saurin yarda da mutane kai ma ka sani, kuma ka san Shattima a can yake aiki, zai iya ganinmu” “Haba Hajiya ya za ayi mu yi saken da Shattima zai gan mu sai kace wasu yara dai?” “Baka san gayyadar da Zainabu ta tara ba ne, shi kanshi ba dan sa ido ne lamurran gidan nan” “Zan fara zuwan kamar yadda kika bukata, daman can na yi tunanin fara zuwa ni kadai” “Haka yayi, ka karanta musu komai idan ka je, idan zai yiyu ka shirya tafiyar nan a cikin satin nan” “Assabar din nan zan tafi In-Sha-Allah, Allah dai ya bamu nasara” “Amin” Hajiya ta amsa tana kashe ido daya. Hannunta ta kai ta dauko wayarta ta soma neman number Talba, ta san ko yana a gari ba saba shigowa ya gaishe ta ba kamar Sirleem amman rashin ganinsa kwana biyu yasa ta damu. Ring biyu ya daga, sai da suka gaisa sannan ta ce. “Talba ina ka shiga kwana biyu?” “Ina nan” “Kwana biyu baka saka mahaifiyarka a ido ba, kuma hankalinka kwance” “Hajiya idan wani abu ya same ki ai dole a sanar da ni, na san lafiyarki kalau ai” “Kana da labarin dai za a daura auren Teema ko?” “Yeah na sani” “To kai nake son ka wakilci mai martaba” Ya zare ido kamar tana gansa. “Wane irin ni kuma Hajiya, kin san ban saba shiga irin abubuwan nan ba, kuma dai ga Baba Waziri ga Baba Jarma ga Shattima sai ace sai ni?” “Yanzu ina son ka fara shiga, duniya ta san da kai, wannan umarni ne ba shawara ba, idan ka shigo zan mu tattauna akai ya kamata ka fara mika hannu ana yin komai da kai” “Gaskiya Hajiya ba zan iya ba Wallahi ban saba wannan ba” “Shiyasa na ke son ka saba din ai” Ta kashe wayar bata ma tsaya jiran abunda zai fada ba. Idan ba tai da karfi ba, ba zata samu abun da take so ba, a komai sai Ammy ta tura danta ko'ina shi ake gani ita ba a san da nata dan ba, tana ganin yanzu ya kamata ta zage dange tai da gaske kar a mata yar gidan jiya. 03/12/2021, 08:32 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *14* Gaba daya ta koma kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da suka zo gidan Waziri haka take zama wata saliha, bata sakewa har sai sun bar gida, wannan karon kuma zuwan gaba daya tai dan bata san ranar komawarta ba. Gashi nan tana jinta kamar tana gidan yari, domin yaran Baba Waziri basa fita ko'ina daga makaranta sai gida sai kuma wata hidimar idan ta tashi, gara ma a can masarautar tana iya yin karyar zuwa wani guri Ammy ta barta ko ta samu Sirleem ya fita da ita ko Hajiya Karama, nan fa? Gaba ta kasa sakewa ko breakfast bata fitowa ayi da ita kamar yadda aka saba yi tare da kowa sai ta shige cikin daki ta zauna ita kadai sai idan an kawo mata nata abun karyarwa haka ma da rana, gashi nan dole ne taje makaranta kuma school bus din da bata so ce take kai ta kullum ta dauko ta. Gaba daya ta rasa yadda za tai, wata zuciyar na raya mata ta ari wayar wani ta kira Hajiya Babba ta fada mata dan ita kadai ta ke da tabbacin zata taimaka mata ta cireta daga wannan kangin. Misalin karfe biyu da yan mintuna Motar Hajiya Karama ta shigo gidan, ta window Nana ta leka tana hangota ta sauka saman gadon da sauri ta fita a guje har tile din na kokarin zameta ta fadi. Zainab na kokari rufe motarta sai ga Nana ta fito da gudu ta zo ta rumgume ta, Zainab ta saka dariya tana cire gilashin idonta. “You miss us right” “Yes Hajiya Karama ki ce Ya Shattima am sorry kuma zan ce ma Ammy sorry pls ya maida ni gida” Zainab ta taba kumatunta tana mata dariya. “Shattima ma baya garin nan, ya koma aiki” “Ni bana son nan Hajiya dan Allah” “Dukanki suke?” “No” “Tau why? Kanen mahaifinki ne Nana yayansa kuma yan'uwanki ne, ni kaina idan na gaji da zaman gidan can wani lokacin a nan nake zuwa na kwana biyu sannan na koma, a gida nan ma ina da gata komai kike so za ayi miki, komai kike so shi zaki ci to miye matsalar ki Nana?” “Ba a zuwa ko'ina kuma dole sai an je school both islamiya and boko” Zainab ta rika fuskarta. “Can baya na san kina son makaranta yanzu miyasa ba ki so?” “Ni dai bana so kuma, kuma.... Ni bana son na gama bokon saboda kar na auri Sirleem” Kyalkyalewa Zainab tai da dariya. “Saboda ba ki son Sirleem sai ki lalata karatunki? To idan ba ki son zuwa makaranta ai sai ya ce ayi muku auren da wuri, Nana ki kwantar da hankalinki idan ba ki son babu dole ki bada lokaci kawai zan yi supporting din ki na hana auren Sirleem” Nana ta zare ido. “Har da Hajiya Babba ma za ta goya min baya ko? Shikenan ma na huta” “Ya za ayi Hajiya ta goyi bayanki, ki ki auren danta na cikinta? Ke har yanzu ba ki da wayo?” “Ai tana so na” “Amman ta fi son danta dake, ki daina wannan tunanin, yanzu dai zuwa nai na ganki kuma na dauke ki muje mu sha ice cream dan san kina so” “Yes yes, amman kina shiga cikin gidan nan Hajiya Maryam ba zata bari ba, zata ce Baba Waziri yace kar na je ko'ina” “Okay je ki dauko veil ko hula mu je” Da gudu Nana ta juya ta koma dakinta dake cikin gidan ta dauko wani karamin veil ta saka a kanta, ko da ta fito har Zainab ta yi reverse ta bude nata front seat. Da sauri ta shiga Zainab ta fara tukin tana kai hannunta ta dauki kwakwarda ke gefenta ta ci sai kuma ta dauko wata ta mikawa Nana, ita kuma ta karba ta fara ci, tafiyar ta su ba tai nisa ba Nana ta hango AA tsaye kusa da wani gida mai karamar kofa yana waya. “Hajiya tsaya tsaya tsaya....” Da sauri Zainab ta taka burki ganin yadda Nana ke kokarin tsayar da ita kamar ta ga wani abu. Sai da Zainab ta faka motar sannan ta bude ta fita, AA na hangota ya yanke wayar da yake tana kallonta gabansa sai faduwa yake, wata zuciyar na raya masa cewar ya gudu, ko kuma ya shige cikin gidan ya boya. Wata kuma na ce masa ya daure, dan murmushi da Shaukin da ya hango a fuskar Nana yasa ya dan ji kwarin guiwar tsayawar. “AA AA” Ta fada tana jin kamar ta rumgume shi. Shi kuma ya kasa amsawa sai kallon motar da ta fito yake, sai da Zainab ta sauke gilashin motar ya ga macece sannan hankalinsa ya dan kwanta. “Me kika zo yi nan? Waya ce miki ina nan? Biyoni kika yi?” “A a ba mu fita ni da Hajiya Karama shine na hango ka na ce ta tsaya” Ta fada tana kara matsawa kusa da shi kamar ta rumgume shi wani irin shauki take ji idan ta ganshi. “Nan ne unguwar ku?” Ya tambaya yana zaro ido wata zuciyar na ce masa ashe baka tsira ba. “A a nan gidan aka kawo nan dai, wai bana jin magana shine za min horo” “Kamar ya?” “Wai saboda gidan ba a zuwa ko'ina kuma dole aje school, shiyasa aka kawo nan” “Wane gida?” “Wacan gidan mai Ash da white paint” Kai tsaye ya san gidan Waziri take nufi, baki sake ya ce. “Gidan Waziri?” Ta gyada masa kai. “Ya kike da shi?” Shiru tai tana kallonsa sai kuma ta fara dariya. “Ina ruwanka kai me kake a unguwar?” Ya dan shafa kansa yana tunanin karyar da zai mata. “Na zo gaishe su ne, ko zan dan samu wani abu kudi na ke nema, ba ki da wani abu nan ki ba ni?” “Ba ni da kudi amman bari na ce Hajiya.... ” Yayi saurin dakatar da ita. “No no no tsoro nake kar a kama ni, na sani ko kin fadi cewar ni kika bawa 20k din ki kuma ni na jefar da ke akan babur” Ta fara dariya. “Wallahi ban fada ba, ai idan na fada Ammy zata min fada ne tace ashe bana zuwa school, cewa nai driver na ne” A nan ta fada mishi karyar da tai musu da kuma yadda ta isa gida a ranar. Sosai AA ya jidadin haka ta rufa mishi asiri yanzu kan hankalinsa ya kwanta. “Bari na karbo maka kudin” Ta juya ta koma gurin Motar Zainab ta lekar da kanta. “Hajiya kina da 10k ko 20k ki ara min, ko ma dai ki ba ni” “Me za ki yi? ” “Shi zan bawa” “Waye shi?” “Malamin mu ne na makarantar islamiya, na masa alkawarin ne shiyasa” “Karbo account dinsa a tura bani da cash” Ta juyo da sauri ta zo ta fada masa, sai ya rubuta mata account din a wayarsa ya mika mata yana fadin. “Gt bank” Sai da Zainab ta kare masa kallo sannan tai masa transfer 10k ta mika mata wayar. “Yi sauri mu je” “A a na fasa zuwan ki tafi kawai” “Saboda?” “Ni dai na fasa dan Allah ki tafi, Wallahi ba guduwa zan yi ba, zan yi magana da shi kawai na koma gida you have my word” “Promise?” “I promise” Ta fada tana daga hannu alamar ta dauki alkawarin. “Okay take care of yourself, kuma kin san kika dade har aka fito aka ganki babu ruwana zan ce ni ban ma zo gidan ba” “Na zan yi haka ba i love you” Zainab ta yi murmushi tana daga gilashin motarta, sai da ta wuce sannan Nana ta dawo inda yake ta mika masa wayar. “Ban san ko nawa ta saka maka ba” Ya karbi wayar ya duba alert din da ya shigo na 10k. “Dubu goma ne thank you so much Allah ya biyaki” “To zaka ara min na kira Hajiyata?” “Yes ba dai tona min asiri zaki yi ba ai” “Aa” Ta karba wayar ta saka number Hajiya Babba ta aika mata kira, sai da ta jera mata miss calls kusan uku a ana hudu aka daga cikin tsawa. “Waye wannan?” “Hajiya ni ce fa Nana” Hajiya ta sake fuska jin Nana. “Daughter da sabowar number?” “Eh to ba Baba Waziri ya karbe min waya ba, kuma gashi nan Ya Shattima ya dawo da ni gidan wai bana jin magana, Hajiya dan Allah ki zo ki dauke ni yau yanzu” Ta fashe da kuka. “Wai me yake damun mutanen nan ne? Gani nan zuwa yanzu” “To sai kin zo Hajiya yanzu pls ko minti biyu kar ayi” “Yanzu daughter” Ta katse wayar ta mikawa AA. “Wa kika kira?” “Step mom dina ce ita ai tana so na, yanzu za ka ga ta zo ta dauke ni” Ya saka wayar aljihu yana kallonta. “Kin rame” “To ina ruwanka?” Ta watsa mishi harara sai kuma tai yar dariya. “Yanzu tana zuwa zan ce ina son ta daukar min kai driver” Ya kalleta da sauri. “Kuma zata yarda?” “Eh so na take sosai” “Bari na koma kar ta zo ta gan ni a hanya” Ta daga mishi hannu. “Bye” “Bye” Ya amsata yana binta da kallo har ta isa gaban gate din gidan Waziri ta shige. Ba tai minti talatin da shiga gidan ba sai ga Hajiya Babba ta iso tare da driver ta furka a murtuke kamar da gaske ranta a bacen yake. Nana na hangota ta windows ta fara tsalle tana rawa tana jindadi. Kai tsaye ta wuce bangaren Uwargidan bata biya inda kawarta kuma amiyarta Talatu ba, amasama ta gaisa da matar kanen mijin nata Hajiya Maryam daman can ba sa shan inuwa daya sannan tace. “Zuwa nai na tafi da Nana” Hajiya Maryam ta kalleta. “Nana kuma? Shattima ne ya kawo ta nan ta kwana biyu” Hajiya Balki ta yi mata wani kallo. “Ikon Allah kina nuna min ban isa da Nana ba kenan? Ko kuma kina nuna min ita din ba yata ba ce? Ban gane ba?” “A a Wallahi ba wannan, kawai dai ance ana son ta kwana biyu nan ne shiyasa na fada miki” “To bata kwana biyu ba, Nana ba ta kusa sati a gidan nan ba?” “Ba wai ana nufi kwan nan biyu ba, kwana biyu na malam bahaushe ake magana Hajiya” “Wai wacece ke da kike fada min wannan maganar? Banza a banza kashi a masai? Shattima ya fi ni iko da Nana ne ko kuma me? Ke kina kara nunawa Ammy wannan bakin abun na ki na wani yan uba, mu yaran gidan mu ba su san wannan ba, kowata da yai nan ma ai bata mata tarbiya za ayi” Hajiya Maryam ta yi dariya “Hajiya kenan, ke kuma abun da kike gyara mata tarbiya ne? Shattima ai ya san da ke a gidan amman ya dauke ta ya kawo ta gurin kanen ubanta kuma be ce a kawo ta ko'ina ba sai a nan bangarena, har waya sai da ya daga ya kirani yace na kula masa da Nana, kin ga kuwa dan gyara aka kawo ta ba baci ba” “Eh Lallai Hajiya Maryam, ni kike fadawa magana haka? Yanzu da Ammy ce za ki mata haka? A a sai ni da nake kishiyarta ko? Ba komai komai yana da lokaci ai wata rana sai labari, Ke Zarah tashi ki kira min Nana” Hajiya Balki ta karasa tana kallon karamar yar Hajiya Maryam. Zarah ta tashi ta fita daga falon zuwa bangaren da dakunansu suke, ta kira Nana suka fito tare, Hajiya na ganinta ta mike tsaye. “Idan Waziri ya zo ki ce masa na dauki yata, idan kuma ban isa da ita ba, sai ya zo ya dauko ta” Haka ta saka Nana na gaba suka fice daga falon, tun kan su karaso driver ya bude musu baya, Hajiya ta shiga Nana ma ta zagaya ta shiga ko tsinke bata dauka ba a gidan. Sai da direban yaja motar suka fita daga gidan sannan Nana ta rungume Hajiya a cikin motar. “Na gode Hajiya” Hajiya ta yi murmushi. “Anything for my daughter” “Ke ba kamar Ammy kike ba kina so na sosai kuma kina min duk abunda nake so i love you so much Hajiya” “I love you too Daughter” “Kuma Hajiya ina son sabon driver, bana son school bus tana kai ni makaranta, shi zai rika kai ni islamiya da boko ma, tun da can na fadawa Ammy ta dauka min sabon driver ta ki” “Karki damu zan daukar miki sabon driver, duk abunda kike so shi zan miki daughter zan saka a samo sabon driver ya rika kai duk inda kike so” Ta dago da sauri tana kallon Hajiya cikin wani irin jindadi marar misaltuwa. “Akwai wanda yai min magana Hajiya, yace zai iya kuma yana so” “To ki nemo shi daga gobe zai fara tukaki ki bashi keys din motar kuma ki fada masa yadda ake biyan wacan driver ni zan din ga biyansa every month” Da sauri Nana ta kara rumgume ta ta kwanta jikinta tana jin wani son ta fiye da Ammy. *** *** *** Kofar wani gidan ta kwankwasa aka bude mata, matashiyar matar ta leko. “Hajiya kuna siyen danyen man shanu?” “A a muna da Allah bada sa'a” “To amin” Ta amsa tana lasar bakinta, a nan ta janyo kurwarta ta warware zanenta ta saka yar tsokar ta kulle, ta maida zanen ta daure ta yi saurin bari wajen har da hadawa da gudun, duk da bata matsi kurwar ba ta ta ga matar tana da aljanu kuma za su iya tashi, ko da yake na Amo sun fi na matar karfi. Cikin unguwar Nasara ta shigo gidan data saba kawo musu danyen manshanu suna siye, tana buga gate din mai gadin ya bude mata, ta gaishe shi da far'arta tana kallon kurwarsa dake kasan kafafuwansa. Nisa kai tai cikin gidan har ta isa bakin kofar falon da ke bude ta zauna kasa tana sauraren hirar da Hajiyar ke yi da kanenta yaranta su ka zo da gudu suka rumgume Amo. “Oyoyo Amo ta zo Oyoyo” Ta muku ya zaunar da su saman kafafuwanta tana dariya tana musu wasa. “Shi fa be ma san da maganar ba, kuma ita Ammy tace kar na bari ya ji sai komai ya kama” “To sai matsalar wannan abun da ke tare da shi” “To ai ni ma shine, kar a aura masa yar mutane ta mutu, shi kansa yanzu abun da yake tsoro kenan shiyasa ya cire ransa daga auren ma” “Sai dai idan ba za a fada ba” “Idan kuma ba a fada ba, ai an cutar da yar mutane, kuma ita yanzu Ammy tace ta damka min ragamar komai, wai ko a nan Katsina din ne su zauna tukunan” “Ai kam samun mata yanzu ga Shattima aiki ne, ga kudi ga kyau ga ilmi ga sarauta amman fa ana tsoron mutuwa” Ra'ees ya shafa kansa cike da damuwa dan wannan aikin da Ammy ta bashi ba karamin aiki ba ne. Karamar yar Hajiyar ta shigo tana tsalle. “Momy ga Amo can ta zo” “To yar gidan Amo” Ta fada tana dariya sannan ta mike tsaye ta fito waje suka gaisa da Amo. Sai da ta bude manshanun suka fara ciki ta siye wanda zata siye sannan Amo tace. “Hajiya na ji kuna neman mata” Hajiya ta yi dariya. “Muna nema kan amman ai shi mai son matar ne da matsala” A nan Hajiya ta labarta mata waye Shattima. Sai Amo tace. “Kai duk canfi ne Hajiya, ku bar wannan maganar ma, karku sake fadin haka abun da Allah ya kawo ai shi yake kasancewa, ni da za ku yi shiru da bakinku akwai yar da nake riko sai a bashi ita, indai za a saka ni gaba ayi komai” “Aiko da kin kyauta mana, zancen fadin haka daga yanxu ma mun daina” Amo ta yi dariya tana kallon sabon cikin Hajiya take dauke da shi, da be wuce sati biyu ba, amman ita tana ganinsa da idonta hudu na maita. A nan ta fada musu addirenshi da wanda za a nema idan aje. “Indai da gaske suke suka je Malam zai bashi aurenta, dan shi kanshi neman mijin da zai aureta yake, shekara goma sha 16 babu wanda ya taba tambayar amrenta” Har lokacin tana kallon cikin, wata zuciyar na ce mata ta taba wata na cewa ta bari sai ya kara kwari. Bayan sun gama yanke komai ta siye manshanun ta sallame ta taso tana ta jindadin indai ta zama jagaba ita ce zata samu kudin komai ai. FADIME POV. A yadda ta kabartawa Inna labarin cewa tai wani ta ji a jikinta akwai wata wuta tana binta kuma wutar maita ce, bata son ta fadawa Inna gaskiya dan kar ta mata fada ko kuma ta hana ta zuwa gurin kiwon. “Dubi kike ne da kika fara ne Fulani?” “Minene Dubi Inna?” “Bokaye suke yinsa su duba hannun mutu ko idonsa su fada masa abu, ana basu kudi” Gyada kai Fulani tai tana dariya a ranta tana tunanin ta samu sana'a. “To yanzu idan nai miki Inna za ki ba ni kudi ko?” Inna ta watsa mata harara. “Bari Malam ya ji da wannan dabi'ar sai ya zaneki kin san dai babanki malami ne ko?” ‘To ni ina ruwana da wata malantarshi’ Ta fada a ranta tana turo baki gaba, a dayan bangaren kuma tana ayyana irin kudin da zata samu idan tai wannan sana'ar. Waya sani ma ko aljani ne ya zo ya taimaka mata? Bayan kwana biyu Inna da Fadime na zauna waje, Amo ta fito daga bukkatar tana fadin. “Inna Fadime na yi ma Fadime miji” Kamin Inna tace komai Fadime ta nufe ta da far'a tana dariya, kwatakwata a rayuwarta babu wanda ya taba zuwa yace yana sonta sai yau. “Da gaske? Ina miji?” “Ke arrr Fulani babu kunya” Inna ta fada cike da jin haushin yadda Fadime take rawar jiki. Fadime ta rufe ido ta dawo da gudu ta rufe kanta jikin Inna sai a lokacin take jin kunya wai. Amo ta zauna tana dariya ta labartawa Inna. “A can bunni inda nake kai mansanu, samarayin gidan abokaine yake neman mata nace ga Fadime nan tun ita yar boko ce kuma tana da kyau ba kamar hajjo ba” Inna ta jidadi sosai cikin ranta duk da tasan Amo ba zata kawo mata abun alheri ba, amman jin yau ana son yarta yasa ta jidadi abun da ba a taba ba ko da wasa. “Ai na ce su zo su yi magana da Malam indai da gaske suke.” Amo ta fada sai Fadime ta ce “Allah yasa su zo Allah ya kawo su lafiya, yana da kyau?” Inna ta rafka uban tagumi tana kallonta, Amo kuma ta saka dariya domin ita dadin rashin kunyar da Fadime take, take ji domin ba al'adar fulani ba ce. Ganin yadda Inna take hararta yasa ta fita daga gidan da gudu tana dariya, kai tsaye ta nufi gidansu Ma'u ta fada labari, tana isa ta tarardar Ma'u na yi ma wasu mutane kwatancen wani gari da ke yamma da su. Mutum uku ne da wata dalleliyar mota daya na tuki daya a baya daya kuma a mazaunin gaba. Gurin madubin motar Fadime ta je tana duba fuskarta kamin ta fara shafa motar, wanda hakan ya ba Jarma tsoro yana ganin kamar lekensa take ta ga ko waye ne, kamin a gama musu kwatance su kama hanya duk ya takura. “Kiyaye....” Ta fada tana daga musu hannu kamar ta san su, ta bi motar da kallo sai da ta daina hangota sannan ta talkamo kawarta ta fara bata labari. *** *** *** Jarma yaja tsaki cike da jin haushi. “Wai yanzu kai Saminu ka san baka san gari ba kasa mu ka kamo hanya haka? Saminu dake gaban mota ya juyo yana kallon abokinsa. “A a fa na san hanya, garin da shi jafaru yake zuwa ci rani ne ban sani ba, amman muna isa muka ce gidan liman ance babu wanda be san shi ba a garin, ka ga sai mu tambayi Jafarun sai ya shige mana gaba mu shiga cikin garin tun da shi ya san yan garin da yawa kuma yana yi wa mutane jagoranci amman mu kai tsaye ai ba za mu shiga garin ba” Jarma be koma cewa komai ba, har suka isa garin Dan burki, suna tambayar gidan liman aka nuna musu, a gidansa suka sauka yai musu tarbar ban girma duk da be san su sai dan karamci irin na mutanen kauye. Sai da suka huta sannan aka kira musu Jafaru suka kama hanyar garin, ba Saminu ba ko Jafaru da ya saba zuwa garin sai da tsorata da suka kusa isa balle kuma Jarma danke jin kamar fitsari za su zubo masa ganin yadda ake ta yankan daji kamar ba a dubiya ba. “Ai dai ba za su mana komai ba ko Jafaru?” “Babu abun da za su mana tun da ina tare da ku, amman ba za mu shiga garin da motar nan ba” Cikin manyan duwatsu suka ratsa har suka isa bakin kofar gate din garin da ba zaka iya fadar da me kai ta ba, itace ko katakaye ko kafara katuwar kofa ce mai tsayi sosai ga masu gadin kofar sanye da warki sai kallon su motar su Jarma suke. Jafaru ne ya fita yaje yai magana da su sannan ta dago musu hannu suka fito suka karasa inda yake. Shine gaba suna biye har suka shiga cikin magarin, sannan aka kawo musu motar jaki suka hau aka nisa cikin garin da su. Sai da aka isar da su gurin sarki suka gaishe shi ya san da zuwansu sannan aka wuce da su gurin boka, duk abunda ake Jarma be wani motsin kirki ko kallonsu be son yi gudun kar yai laifi, shi a rayuwarsa be tana ganin mutane haka ba sai yau, you ashe akwai irin mutanen nan har yanzu. Amman kam garin akwai kyau ga manyan duwatsu da itatuwa ga kuma ruwa ta ko'ina gwanin burgewa kowa sai hada hadarsa yake. A nan ma sai da Jafaru ya shiga yai magana da su sannan akai musu iso, sun san Jafaru sosai dan ya saba kawo musu mutane kala kala kuma yana cikin irin mutane da suke bawa kudi ayi musu sako a burni ko daga wani gari zuwa wani gari. A saman agalami suka samu mutanen mai kama da munanan tsofi kansa da aski an masa tas idonsa kamar garwashin wuta, kana ganinsa ka san aka gawurtaccin ifiritai a tare da shi, yawanci mutane garin suna jin yaren hausa da fulatanci duk da kasancewar ba su cika mu'amala da kowa ba, sai wanda suka yarda da shi, amman ban da wannan baya jin ko wane yare sai na su. Sai dai a kusa da shi akwai mai fassara musu komai. Suna zama ya fara karaton musu abun da ya kawo su. “Ka zo nan saboda a kawarda dan'uwanka, da matarsa da dansa ka hau sarauta, kana son a kashe Shattima da Talba da sannan a nakkasa Zainabu da Balki” “Wallahi haka ne” Jarma ya fada yana kara gyara zamansa mamaki duk ya cika shi, ta dayan bangaren kuma yana jin kunyar jin sirrinsa da abokinsa Saminu yai. “To ga tafiya nan da ba dawowa, ga Fadime nan ga Falmata, ga Sardauna su za su lalata muku shiri” Jarma ya nisa a cikin tunani yana ta neman gano waye Fadime waye Falmata? Kuma waye Sardauna? Sardauna na na Yola ko kuma wani sardauna nan dabam? Wata kwarya ya dauko mai ruwa ta aje gaban Jarma, ya fara karanta wasu abubuwa sai ga Mai Martaba ya bayyana a cikin ruwa, wani irin zabura Jarma yai ya matsa baya. “A harbe maka shi? Yanzu nan za mu yi masa harbin kanko” Jikin Jarma sai rawa yake yayi sauri cewa. “Aa shi ai mun samu nasarar kwantar da shi, yanzu Shattima muke son a fara harbewa tukuna” Mutumen ya fara karance karance yana kiran sunan Shatttima amman ya ki ya bayyana a cikin ruwan. Tun yana daukar abun da wasa har ya fara yi da gaske Shattima ya ki bayyana a cikin ruwan sai sunansa. “Akwai abun da ke kare shi, lallai shi ma be tsaya haka nan ba” “Yanzu ba a iya harbe shi kenan?” “Za a iya amman idan akai be same shi ba, zai dawo gurinka” Jarma ya mike tsaye yana lalaba jikinsa. “A a bari dai sai mun yi shawara tukuna” “Ba a shawara a nan ku tafi can gari” Jarma ya mike tsaye da sauri ta ciro kudin da za su kai dubu 30k ya aje musu, sai ya girgiza masa kai mutumen ya fassara masa. “Kudin siyen dabba ake ba mu” Jarma ya karo 50k ya aje musu sannan suka juya jikinsa sai rawa yake. Duk shige shigensa be tana shiga irin wannan gurin ba, ba tana ganin tsafi kararsa irin yau ba. _________ Sauran page daya mu gama free pages. 03/12/2021, 08:32 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄* By Khadeeja Candy *15 -Last Free Page* Fadime ta kara lakkamo Ma'u tana dariya “Wallahi kuwa” Ma'u da rufe baki tana zaro ido. “Kuma Wallahi da gaske koko na sa da safen nan, Fulani da gaske kin iya” Wani kalar dadi ya kara rufe Fadime jin ta canki abun da Ma'u ta karya da shi yau, bayan ta gama fada mata ita tana da aljannu kuma suna sa ta gane komai na mutum. “Yanzu kenan za ki iya fadawa mutum abun da zai same shi” “Eh amman sai na yi bachi, amman dan Allah Ma'u karki fadawa ko sai wanda kika yarda da shi, idan Bappa ya ji zai min fada ko ya doke ni ma” “Ba zan fada ba” Fadime ta yi dariya. “Inna tace masu irin wannan abun kudi ake ba su, idan kina ga wani na son a masa ya bada kudi ki kawo shi zan masa amman a boye” “Aiko zan ta kawo miki mutane Wallahi, sai ki sammin wani abu ni ma” Sai da hantsi ya bude sosai sannan Fadime ta bar kofar gidansu Ma'u ta dawo gida. Kai tsaye ta nufi bukkatarta ta dauko biro da littafinta ta fara rubuta hau Amo tace zata kawo mata miji, kuma ta fadawa kawarta Ma'u cewar tana dubi. Gaba daya wunin ranar wuni tai cikin farinciki da jindadi kana ganinta kasan dadi take ji tana murna wai Amo ta mata miji kuma a bunni. Amo dai sai kallonta take a ranta tana fadin ‘Zaka si ubanka idan ka aureshi mutuwa za kai, idan ka gagaran ci ai ba ka gagari wani ba’ Ta fada tana dan murmushi sai da Fadime ta mike tsaye tana kora shanu zuwa daji Amo ta lura yau wutar nan bata biye da ita, a razane ta mike tsaye tana bin bayanta da kallo. Inna ma ta mike tsaye daga can cikin bukkar da take zaune tana kallon Amo, wacce razanar ta bayyana, Inna daman can ta dade tana zargin Amo da maita ba tun yau ba, tun daga lokacin da ta bata labarin cewar suna da maitar gado wacce ake bawa yara tun suna kanana amman ita Allah ya tsareta ba a bata ba, ga yayan wabin da Inna tai ta yi a duk inda take neman magani sai ace manya ce take cinye mata yaya, wani cikin ma tun kan ya zo duniya zata yi barinsa, Fadime ce kawai ta rayu ita ma daker dan babu kalar ciwon da ba tai ba, Allah ne dai ya rata ta da kuma addu'oin da take yawan yi mata, Bappa ma yana mata sosai har rubutu yake mata ya bata ta sha, tun a wacan lokacin idan Inna ta fada masa tana zargin Amo sai ya karyarta yace baya son tashin hankalin, har yake ganin kamar kamar Inna tana haka ne saboda Amo kishi, bayan kuma ita ta zo ta tararda Amo. Sunsunsun Amo ta shige bukkarta da mugun mamaki, ta sani wani sa'in ana samun akasin abun da tai mata, sai dai ba ko yaushe ba, domin Fadime babu ruwanta da addu'a sai dai idan yi mata akai, kuma wannan wutar ta dade da saka mata ita tun Fadime na karama, taya yau rana daya za a wayi gari babu ta? Ko dai Inna ta karbo mata wani maganin ne? Idan ba haka ba gaya wutar ta bar binta? Adakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya. A kullum idan Fadime zata je kiwo sai ta saka shanun gaba tana binsu a baya, ban da kwana biyun nan da take son sake ganin Wasim, kullum baya take baro shanun sai idan sun kawo kansu. Tana isa ta haye saman dutsen ta fara kiransa. “Mai busa” Haka take kiransa a duk lokacin da ta iso gaban dutsen, duk kiran da zata masa kuma ba zata ganshi ba, ba zata ji busar ba, bata kuma fasa kiran ba. Sai dai shi yana saukowa kasa ne ya boya jikin dutsen yana kallonta har tai abunda za tai ta gama. Sai da ta sauko saman dutsin sannan ta ganshi kasa tsaye ta inda zata ganshi yana kallonta fuskarsa da murmushi, dan tsoro ta ji. “Kenan shi aljanin dutse ne?” Ta raya a ranta, a fili kuma sai ya kara hayewa saman dutson alamar ba zata sauko ba. Ganin hakan yasa ya fara haurowa saman dutsen still yana mata murmushi. “Ka yi hakuri ni ba dan wani abu na kira ka ba” Ta fada tana kokarin sauka ta dayan bangaren, ganin hakan yasa shi ma ya juya ya sauka. Sai suka koma kallo kallo ita da shi, ta kira shi ne kawai ba dan tana da abun cewa ba, kuma bata san zai ji ta ba, tun da ta saba kiransa kwana biyu bata ji shi ba. Da hannu yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, ta girgiza masa kai. Zaunawa yai a gurin ta dauke kai daga barin kallonta. Hakan yasa zuciyarta ta raya mata cewar ko aljani ne shi ba zai cutar da ita ba tun da har mafarkinsa take. A da idan Inna tace mata tai addu'a sai tace mata wuya take ji, amman a yau da take son zuwa kusa da shi sai da ta tsaya ta karanta addu'oin data iya sannan ta tunkareshi tana takawa kadankadan kamar mai tsoron ya ji takunta, kansa na kasa har ta kawo kusa da shi ta risina ta leki fuskarsa, sai ya sakar mata murmushi ita kuma tai masa dariya irin dariyar nan ta dole kuma ta tsoro wacce mutum ke yi a rikice. “Kai aljani ne?” “Aa” Ya amsa mata yana dagowa ya kalleta da kyau. “To miyasa na ke mafarkinka?” Kallonta kawai yake irin kallon nan na son tantace gaskiyarta. Kamar tasan irin kallon da yake mata sai tace. “Wallahi ba karya na ke ba, ina mafarkin, da wani mutum kuma da wani kana rike da wannan abun busar kana busa amman kullum baya kake bani, shiyasa lokacin da na ji busarka na zo har nan dan gani idan da gaske ne, kuma busar iri daya ce” “Ni ba aljani ne bane” Ya fada cike da mamakin mafarkinsa da tace tana yi. “Kuma tun lokacin nan nagge bata sake mutuwa ba, miyasa kake saka wannan abun” Ta nuna warkin dake kugunsa, sai yai murmushi. “Haka muke, kayan garin mu” “Ina ne garin ku?” “Garuk” Ta gwala ido tana matsowa kusa da shi, sai a lokacin ta tuna da taba jin labarin garin ance mutanen ciki basa saka tufafi kuma matsafa ne. Ta zauna a kasa tana kara kallonsa. “Kai kake min tsafi nake mafarkinka kenan?” “Aa” “Ya za'ayi na tabbatar da kai mutum ne?” “Idan kika taba jikina za ki ji shi kamar na ki, idan na aljanine za ki jishi da sanyi ko taushi ko gashi ko kiji kamar ba hannun mutum ba” Dan matsawa tai kusa da shi, sai ya miko mata hannunsa ta taba sannan ta taba nata, sai ta ji shi normal kamar ita. Amman hakan be sa ta gansu ba. “Ka yanke kanka na ga jini sai na yarda” Wannan karon dariya yake, a ransa yana mamakin wauta irin nata taya zata ce ya yanka jikinsa. “Samo min kare ko dutse mai tsine” Ba musu ta tashi taje ta samo masa, ta kawo ta zauna kusa da dan tabbatarwa idan da gaske yankawan zai yi ko a'a. “Miye sunanki?” “Fadime” Ta amsa mashi tana kallonsa da manyan idonta masu haske da daukar hankali. Murmushi yai ya mike hannun na dama ya saka hannunsa na hadu ya karkari hannunsa na dama kadan jini ya dan fito. Da sauri ta rufe ido tsigar jikinta na tashi. “Innalillahi, da gaske ka yanka ni wasa nake maka fa” “Ba hakan zai sa ki yarda da ni ba” Ya fada yana kallon gashin kanta. “Na yarda” Ta fada bayan ta bude idon. “Miye sunanka?” “Wasim” Haka ta fara masa tambayoyi kala kala yana bata amsa, duk abun da ta tambaya sai ya bata amsa, tun tana da sauran tsoron har ta sake jiki da shi. Har da karbar sarewarsa ta busa, sai nata busar bata fita saboda bata iya ba. Har sai da ya karba da kansa ya fara busar tana ta kallonsa cike da burgewa. “Waya koya maka?” “Wani tsoho” “A ina yake?” “Garinmu” Ya amsa yana kallonta, mugun burgeshi take, ko wane motsi nata the way da take tambayarsa yadda take sake jiki da shi far'arta kyauta and everything. Ta gyada kai tana murmushi, da yamma lis ta koro shannun ta sako su a gaba ta jeru ita ta shi suna tafiya, sai ya rakota har kusa da hanyar gidansu sannan ya tsaya ita kuma ta daga masa hannu, shi ma ya dago mata sai ta juya ta cigaba da tafiya sai kwasar dariya take. Daman tun dazun take jin dariyar take son ta yi ta kasa, wai basa saka rika kuma basa son shiga cikin mutanen da na nasu ba, gaba daya kallon mahaukata take musu. Sai ta kai shannun gida ta shigarda da su gurin da aka saba ajesu, sannan ta sunsuda ta fita, sai da ta kama hanya sannan ta hango Bappa tafe tare da wani makocinsu, da sauri ta boya bayan wata bishiyar dogon yaro. Kasancewar bishiyar katuwa yasa Bappa da mutunen ba su lura da ita ba, domin gaba daya hankalinsu baya gurin yana kan abunda suke tattaunawa ne. “Gaskiya ina baka shawarar ka kara aure kawai” Shine kawai abun da ta ji, duk da bata san abunda ake tattaunawa akai ba, amman tabbas ta ji Bappa na ce masa ya kara aure, a gurin tai ta tsayi har sai da suka karyar kwana sannan ta fito yana girgiza kai tana dariya. Juyawa tai ta canja hanya zuwa gidansu Ma'u, ko da ta shiga ta samu Ma'u na alwala sallah magariba, sai ta risino kusa da ita. “Ma'u nan da kwana biyu mijin Ande Hanne zai fara maganar aure ce ni na fada miki” Ma'u ta kalleta da sauri. “Aljanin ne ya fada miki?” “Eh, yau da naje kiwo ma a fili ya ganshi yace zan rika ba da magani zan rika fadawa mutane komai” Ma'u ta kara zaro ido gaba daya ma sai ta ji tsoron Fadime ya fara kamata. “Da gaske?” “Allah amman karki fadawa kowa” “Ba zan fada ba” Gaba daya tsoro ya gama kama Ma'u, Fadime ma ta lura da hakan kuma ta jidadi, ita gaba daya tun da Inna ta fada mata masu magani kudi ake ba su su fadawa mutum matsalarsa ta ji tana sha'awar abun. Haka ta kwana da tunani kala kala na irin karyar da za ta yi ma Inna ta yarda ta fara bada maganin. Sai da Fadime ta gama karyawa da fura mai tsami sannan ta zauna saman tabarmar da Inna ke zaune tana gyaran gida. “Inna na sake mafarkin aljanun nan sun ce zan bada magani fa” Inna ta daka mata tsawa. “Fulani kar na sakd jin maganar nan a bakin ki, da kin sake maganar nan sai na fadawa Malam” Da sauri tace. “Na bari” “Gashi kije ki debo ruwa” Ta tashi da sauri ta nufi inda tulun daukar ruwan yake ta dauka ta fice da sauri ta nufi gurin deban ruwa, tasan Bappa sarai be son irin abubuwan nan. Tana tafe tana wakewaken har ta isa, sai da ta duka ta fara cikon ruwa sai ta ji a na kirata. “Fadime” Da sauri ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake mata murmushi. Tsaye yake nesa da ita. “Ashe kana zuwa nan da safe” Ya gyada mata kai yana karasowa kusa da ita, har yanzu bata daina jin tsoro ba sai dai ba kamar na da ba. “Ruwa kike deba?” “Eh” Ta fada tana dariya sannan ta duka ta cigaba da cikon, sai kuma ta juyo ta kalleshi. “Dan Allah ka taimaka min ka min wani abu” “Minene” “So na ke idan na cika tulun nan, ka masa tsafi tun da ku matsafa ne ai zaka iya ko?” “Saboda me?” “Saboda Inna ta yarda cewar ina mafarkin aljanun, so na ke ka masa tsafi sai na je gida na aje tulun sai ruwan su zama maciji” “Ba ki jin tsoro?” “Ai ba anan ba sai na je gida, amman ka min alkawarin ba za ka cutar da ni ba” “Ko wani ba zan bari ya cutar da ke ba” “To ka min ka ji” Ya daga mata kai. Sai da ta cika tulun dam sannan ta matsa tace yai mata ita dai burinta kar Inna ta karyartata, burinta Inna ta bata hadin kai ba sai Bappa yaji ba. Matsawa yai kusa da tulun ya saka hannunta yana ta kallonta be wani dade ba ya cire sai ta zaro ido. “Yanzu shikenan da naje gida zan ga ruwan ya zama maciji?” Ya daga mata kai alamar Eh yana ta kallonta, sannan ya tallaba tulun ya dora mata saman kai, tsakanin dora mata tulun da fara jin motsin abu mai rai a cikin tulun be yi minti 1 ba. Yana kallonta sai ta fashe da kuka. “Ba yanzu na ce ba, Wayyo Bappa wayyo Bappa wayyo Bapppa” Sai fitsari, ta fara kukan da gaske gasken hawaye kamar ruwa. “Idan kika sauke tulun macijin ciki zai cijeki, karki sauke sai kin isa gida” Ya fada yana dariya. Gaba daya jikin Fadime rawa yake kafafuwanta sai lankwashewa suke kamar zata fadi, numfashinta ya fara sama sama, faduwa tai kasa ta fara rarrafe dan bata ma iya tafiya, haka nan ta isa gari duk da bata zanenta da zawo sai kuka take tana kiran Bapppaa, ga tulun saman kanta. Duk wanda ya kalleta sai ya ganta da tulu saman kai ga kan maciji ya leko, mutane sai gudu suke, kamin ta isa gida har ta canja kammani. “Bappppa wayyo Inna na bani na taro aljalina” Ta kasa tashi tsaye gani ba take idan ta mike macijin zai iya saukowa, mutane aka fara taruwa ana kallonta tai zaure a kasa sai rusar kuka take fuska duk da bace da majina da hawaye zuciya kuma kamar ta fashe dan tsoro, ita gaba daya bata dauka ma da gaske yana iya yin tsafi ba sai yanzu. “Mike tsaye ki zafar da tulun” Kowa abun da yake fada kenan, ita kuma babu kuzarin mikewar tsaye gashi yace mata idan bata isa gida bata sauke zai cijeta. “Yace sai na kai shi gida, ku dauke ni ku kai ni gida, wayyo Bapppaa na wayyo Bapppaa” Ta fada tana ta yarfe hannu, idonta har ya kumbura saboda kuka. FALMATA POV. Da tunani kala biyu Falmata ta isa gida, tunanin saukin kai da jindadin kadeta da M2 yai ga kuma kiranta da Ammy tai ta mata tambayoyi, ko miyasa tai mata haka oho. Sosai ta so ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta labarta mata yadda ta ga M2 sai ta tuna da Baba ya mata iyaka da gidan. Hakan yasa tai hanzarin cira kafa ta isa gida, da zimmar ta gama aikinta dan ta samu isa Islamiya da wuri ta labarta musu. Ko da ta isa gida har Gambo ta sanar da sakon Ammy ta bar gidan dan ita abun hawa ta hau ba kamar Falmata ba da take tafiya a kafa. Falmata na isa ta manta da wani kunci da tsoron fada ko wani abu, ta hau bawa Naja labarin yadda ta ga M2. “Dan Allah matsa can mahaukaciya, hala M2 ne banza da zaki ganshi a bagas, sannu kakar farin jini, dan kin ji ana cewa kina da farinjini shine kike wani karya kin ga M2 mahaukaciya” Ko kadan bata ji abun da Naja ta fada ba, amman a yanayin yadda take harararta take jan tsaki tasan karyarta tayi, hakan yasa Falmata ta kara boye hular da ya bata a cikin jikinta ta mike tsaye cikin rashin jindadi ta nufi dakinsu. Tumba dake zaune bakin kofar dakinta ta bushe da dariya. “Wallahi yarinyar can ta fara haukacewa, mugun son M2 da take ne yasa ta fara ganin mutane na zame mata haka” Naja ta ja tsaki. “Ko mai wankewa M2 takalmi ta isa ta gani balle M2, ita fa yadda ake fadar tana da farin jinin nan wani jin kanta take” “Kira min ita” Tumba ta fada tana dariya, daga inda Naja take zaune ta kwala mata kira. “Ke kurma zo ana kiranki” Falmata har cikin ranta ta ji sunan, wani abu na rashin jindadi ya ratsa zuciyarta, ta saka hular M2 can ciki bakkon kayanta sannan ta fito ta tsaya bakin kofa jiki ba gwari tun da babu wani abincin kirki a ciki. “Ke yar kurma, dazun Gambo ta zo tace zaki rika wuni can kina rainon yara” Tumba ta fada mata tana mata alama irin na kurame. Naja ta saka dariya. “Ban cin kurmanta har da hauka na son kamaki, kin fara ganin mutane kina ce musu M2 ko?” A nan ma Tumba ta saka mata dariya, a gurin Falmata ta duka ta fashe da kuka, ba karyatata da suke take ji ma ciwo ba, kiran da kurma da suke a yanzu. “Ji munafuka salon a shigo ace wani abu Umma tai miki kike kuka mu kuke dariya ko? Da shegen baki kamar zunubi” Naja ta fada cikin tsawa, sai Falmata ta mike tsaye ta shige dakinsu ta cigaba da kuka tana rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito. Sai da tai mai isarta sannan ta fito ta zuba surfe ta fara, sai da ta surfe tiya da rabi sannan ta shiga tai wanka ta saka uniform dinta na Islamiya ta dauko qur'ane ta da littafai ta fice. Kusan kullum cikin rashin jindadi taje zuwa makaranta, saboda rashin jin da take a yanzu, idan akai karatu sai Khadija ko wata ta rada mata abun da Malam ya fada a kunne sannan ta ji, sai kuma idan Malamin yayi da karfi, Falmata ba yarinya ce mai yawan surutu ba, amman hakan be hanata fadawa yan ajin su cewar ta hadu da M2 ba, most of them sun karyatata wasu na fadin dan dai tana son shi sosai ne yasa ta ga mai kama da shi. Haka dai ta bar Islamiya cikin rashin jindadin yadda suka karyarta daman ta san ba za su yarda ba, ita ma dai a lokacin ta fara kwankwanto da gaske M2 ta gani ko mai kama da shi? Ko da ta iso gida sai ta tararda wani tashin hankali, yaron da aka aiko yana tsaye yana jiran dawowarta Tumba kuma ta yi wani shegen zama tana rawa da kafa. Ta shigo da sallama Tumba ta hau ta da matsifa. “Ashe Falmata zuwa kike kina cin bashin garin kwaki a shago da sunana?” Dakan shida-shida gabana yai, ta sani yau asirinta ya tonu, tabbas tana zuwa karba kuma idan ta je Tumba take cewa saboda tana jin kunyar tace ita zai bawa bashin gari. “Saboda asan ba a baki abinci ko kuma dan ki bata min suna ni da ubanki? To ya aiko yace a bashi kudinshi bari ubanki ya dawo sai kin fadi dalilinki na bata min suna” Kamar an tureta haka ta fadi gaban Tumba kamar mai neman gafara hawaye sai sallama suke a fuskarta. “Dan Allah dan darajar Annabi karki fadawa Baba Umma, ki rufa min asiri, zan samu kudinsa yanzu na bashi, ki yi hakuri Umma ba zan, idan na sake ki kashe ni, Umma wallahi yunwa take damuna shiyasa na ci bashin amman daga yanzu ko zan mutu ba zan sake ba, na rantse da Allah Umma, dan manzon Rahama ki rufa min asiri Umma ba zan sake ba har abada” Tumba ta fisge kafarta tana kallon. “Tafi idan Babanta ya dawo za a fada masa” Yaron ya juya ya fice, sai Falmata ta mike tsaye da sauri. “Na bani na lalace na shiga uku wayyo ni Allah na Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ta furta ta karfi kuka na subuce mata, sai ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinta, da gudu ta shiga dakinsu ta fada kan shimfidar da take kwana. “Wayyo ni Allah na yau asiri na ya bonu, wayyo Mama Mama ina ma ni na mutu ba ke ba, Allah ka karbi raina kamin Baba ya dawo Allah na shiga uku” Ta fada tana yarfe hannunta hawaye sai zubo mata suke kamar ba gobe. ZAINAB POV. Ta dan yi shiru sannan tace. “Na ce mishi ya bari har na dawo daga tafiyar da zan yi” Ammy ta kalleta. “Ni fa ina tsoron lafiyar nan Zainab, kin san kasar ba wani tsoro kuma ki ce za ki je garin cikin mutanen da ake fadar basa saka tufafi? Kina ganin ma za su aminta ki dauke su hoto ne?” “No ba wai kai tsaye zanje can ba, zan sauka garin dake kusa da su ne, nai magana da mutanen tukuna sai na isa garin, kuma ko ban samu zuwa can ba ai ance akwai manyan duwatsu a kusa da su da ruwa, kuma ance akwai Fulani irin masu yin bukka da gidan zana su zauna a kusa da su, ko da ban samu isa can ba na san ba zan sara abun dauka ba” “To Allah dai ya tsare” “Amin, Ammy dan Allah ki mata magana, ban zan abun da mutunen nan yai mata ba, ta ki ta saurare ni, ni kuma ina son shi, shi yanzu yace yana son ya turo kuma ya sanar a gidansu amman sai ya samu tabbaci daga gareni” Ammy ta yi murmushi. “Karki samu damuwa, zan yi magana da ita, idan ta aminta sai a sanarwa yan'uwan mahaifinki” “Na gode Ammy” Mikewa tai tsaye tana sanye da riga da wando English wears, kanta sanye da dankwalin nan da ake yayi blue. “Bari na duba dakinta idan tana nan sai na turo miki ita” Kai kawai Ammy ta daga mata, ta maida dubanta gurin tv dake dakinta, kallon kawai take amman hankalinta baya can, bata da damuwar da ta wuce ta Mai Martaba a yanzu, a iya tunaninta ta rasa gane abun da yake damunsa, gashi idan an gwada yi masa na hausa sai abu ya karu a maimakon raguwa. Kiran wayarta nd ya katse mata tunanin da take, sai ta mika hannu ta dauka. “Assalamu Alaikum” Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren. “Wa'alaiki-Assalam, Ammy barka da yamma” “Yauwa Ra'ees ya gida” Ta fada cike da kasaitar da ta zame mata jiki. “Al-hamdulillah Ammy an samu wata, amman dai ba mu je, sai dai marikiyar yarinyar tace zata iya aura masa ita” “Ka fada mata matsalar sa ne?” “Eh ta ji komai, firar ma ta ji muna yi shine tace tana da ƴa zata ba shi, amman dai ba mu je ba tukuna” “To yayi kyau, amman fa ba sai kun bayyana dan wane ba, kuma ka yi duk abun da ya dace, karka bari Shattima ya ji komai, sai an kammala yadda ba zai iya ce mana aa ba” “In-Sha-Allah Ammy” “Na gode Allah ya maka albarka” “Ameen” Tana kokarin aje wayar aka kwankwaso kofar dakin kamin a turo a shigo. Hajiya Balki ce Nana na biye da ita a baya, a baki kofa ta tsaya tana kallon Ammy sai cika take tana batsewa. “Yanzu an kyauta kenan? Sai a dauke yarinya akaita gurin Waziri bayan kin san ita da Waziri ba jituwa suke ba?” Ammy ta kalleta da mamaki kamar ba zata ce komai ba. “An kaita gidan Waziri kamar wacce aka kai gidan yari? Kanen ubanta ne fa” “Na san kanen ubanta ne ai, amman tun da bata son zuwa ai sai a kyaleta” Ammy ta dauke kai bata sake ce mata komai ba. Ganin hakan yasa ta juya ta fita Nana kuma ta zauna saman kujera tana matsar yatsun hannunta tana kallon Ammy. Ko da wasa Ammy bata kalle inda take ba har ta gaji dan kanta tace. “I'm sorry” Ammy ta watsa mata wani mugun harara. “Dakinki dai kike so ko? To gashi can idan kin mutu a haka rame a saka ki a ciki, tashi ki fata” “Ammy ki yi hakuri....” Bata karasa ba Ammy ta daka mata tsawa. “Get out” Ba shiri ta mike tsaye jikinta na rawa ta fice daga dakin tana fashewa da kuka. _________________ Al-hamdulillah, a nan na kawo karshen free pages, duk mai son cigaban wannan labarin ya biya 300. Pages din da za su biyo bayan wannan na kudi ne ba kyauta ba, ko kun ganshi a waje na sata ne. Patronize me if ku masoyana ne na gaskiya, show me that love. Son so Fisabilillah. *FULANI -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 ƴan nijar za ku tura 500cf to +22790165991* Wadanda ba su account za su iya turo mtn card ta 08036126660 bana karbar transfer. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels