An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍) ❤️🔥Romantic love story❤️🔥 Written by QueenMarh Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai. Alhamdulillah Alhamdulillah….my previous book was a great journey to endeavor… Ina godiya ga Allah daya bani ikon dawowa da sabon littafina mai suna MATAR TAJ, ina mai rokon Allah ya bani ikon kammalawa Ameen. Special appreciation to my loyal AKK fans, and my supporters i can’t be bold enough without you guys😘 Boss bature M shakur Thank you guys for your endless help and support❤️ Special thanks to My arewa book readers, thank you for sticking around (Halima arewabook)😆 i’m sorry for saving your contact as halima arewabook but this lady right here is a great person, (my Siyam, aisha , susu, my nanasko, my ruks and aysha) and my vvips thank you for supporting me and the words of encouragement guys, mummy ammi na❤️❤️❤️ ban manta dake ba I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya. The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃 Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. Enjoy!!!!! Free page Chapter 1-2 Wata katuwar bus ce mai dauke da mutane ta shigo harabar jirgin sama dake garin abuja. Matuqin motar ne ya taka burki da karfi wanda yasa mutanen cikin bus din doka salati. ‘’haba malam ka dunga bi ahankali mana, rayuka fa ka kwaso ba dabbobi ba, wannan tukin gangancin bashi da wani amfani’’ daya daga cinkin matan dake zaune tayi Magana. A zafafe matuqin ya juyo, bakinshi har yana kunfar masifa ya soma Magana ‘’malama dan allah ku min uzuri haka nake tukina, in badan nayi sauri ba ay da kun rasa jirgin naku’’ Shuru matar tayi don da gani drivern bazaiyi mutunci ba, shiko yana bata amsa ya juya wajen wanda ya shawo gabanshi. Cikin masifa irin tasu ta yan tasha ya soma zagin matuqin motar kafin ya juya ya soma neman wajen parking. ‘’wash allah na’’ budurwa dake zaune chan saqon acikin bus din ta dago kanta data chusa tsakanin gwiwoyinta saboda burkin da drivern bus din ya taka, wanda yayi daidai da buga kanta datayi da karfen bayan kujerar dake gabanta, sanye take da koren hijab kamar kowa dake cikin bus din sai face mask data saka a fuskan nata.. Bazan iya tatance tsarin hallittar fuskarta ba saboda mask din saidai kwayar idanunta data bude su da sukayi jaa sosai suna da masifar daukan hankali don kwayar cikin idanun nata yana da haske kamar gajimare, irin su ne ake kira da hazel eyes. Tana da cikar gira wanda ya tabbatar min zata yi suman kai sosai, matar dake gefenta sai kallonta takeyi tana mamakin kukan data dunga yi tun shugowarsu cikin bus din. Allah kadai yasan meke cikin zuciyar yarinyar saboda yanda take kukan kasa kasa kamar ranta zai fita. Zuciyarta ta zama kamar dutse tayi mata nauyi, rayuwarta ta kara dusashewa, emotions dinta baya responding komai saboda yanda takeji a cikin zuciyarta. Idan ta tuna da wasu abubuwa saitaji hawayen dake saukowa daga idanunta sun kasa tsagaitawa, babu abunda takeyi ayanxu sai tausayin kanta, karfin imanin da take dashi ne kawai ke sata hadiye duk wani kunci dake danqare a bangon zuciyarta. Tambayoyin da take ma kanta tsakanin jiya da yau suna da yawa sosai gashi kuma babu wanda zai bata amsa, abunda yafi tsaya mata arai shine kodai tana da wani aibu ne? to kodai ita yar tsintuwa ce? haka ta dunga tambayar kanta countless of times, saidai sanin cewa bata san menene enci ba yasa ta zama confuse akan abubuwan da suke faruwa a rayuwarta ayanxu da shekarun baya ma lokacin data fara mallakar hankalinta. Driver nayin parking ya fito tare da bude kofofin bus din, daya bayan daya, mazan cikin bus din suka fara sauko kafin matan, kowannensu tana sanye da koren hijabi kamar uniform, da jakar goyo a bayansu, yanda suke futowa ajere kamar bazasu kare ba don sunkai su kusan goma sha biyar. Layi sukayi a jere kowacce idanunta zuru zuru, yan matan duk sunfi yawa don zasu kai wajen su goma sannan kana ganin wasun su zaka san daga kauye aka kwaso su, sai wasu manyan mata da bazasu wuce su uku ba sai maza biyar. Yanda sukayi layi ya bama daya daga cikin mazan damar soma Magana kamar haka ‘’yauwa masha allahu, zan baku passport dinku yanxu, kamar yanda nasha fada maku, wannan passport din shine ticket dinku a ko’ina, idan har kuka batar kuyi kuka da kanku ba wannan agency din ba, sannan jirginku zai sauka a jidda, duk wadda ta gudu daga nan idan aka kamata kartayi tunanin agency zata dauki nauyin consequences din laifukanta don komai a rubuce yake,’’ Yana kaiwa karshe ya fiddo da passport dinsu kowacce da ticket dinta, daya bayan daya ya soma kiran sunayen su yana basu. ‘’sabeeha dalhatu, wacece sabeeha dalhatu’’ jin shuru ya sashi doka tsaki har zai wuce sunan yarinyar ta daga hannunta ‘muryarta na seizing tace ‘’ni.. ce’’ Kallonta yayi daga sama har qasa kana ganinta kasan a tsorace take da al’amarin, ‘’malama kinaji ina kiran sunanki kinyi shuru baki san sauri muke ba’’ Saurin sauke kanta tayi tana rarraba idanuwa saboda tsoro, kafin ta nufi inda yake ta karba passport din, kallon hannunta yayi da yake kyarma zufa ta gama wanke hannun, ganin hakan ya sashi cewa ‘’wannan kuma ko daga wani kauyen aka dauko ta oho kibi a hankali dai kar ki jawo ma kanki a kamaki’’ Jin abunda yace yasa cikin ta yin wani irin qugi har saida gabanta ya fadi da furucin shi, ayanxun ne ta kara tabbatar da rayuwar kuma bata da wani sauran amfani. Yau ga mahaifiyarta wadda ta tsugunna ta haifeta wadda duk duniya bata da kowa sama da ita ta saidata,don kwata kwata batasan dalilin hado ta da mutanen nan da mahaifiyarta tayi ba, ta tashi ne kawai da asuba tana shirin hada masu abunci Karin kumallo wanda kawu zaikai asibiti don duk suna asibiti saboda kwantar da inna da akayi, ita ke zaune a gida don ko zuren gidan bata futa, wata uku kenan rabonta data taka kofar gidan saboda wani dalilin mamanta da bata sani ba, innalillahi ta soma furtawa idanunta na kawo ruwa. * Mutumin ne ya jagorancesu zuwa cikin airport din, suna biye dashi, saida akayi checking dinsu daya bayan daya kafin su shiga wajen waiting room don jirgin nasu na gab da tashi. Yarinyar nan dai tana biye da kungiyar tasu da suka taho tare, bata yarda sun daukema ganinta ba har suka zazzauna a waiting room na lower economy. Gefenta kuwa matar nan ce wadda suka zauna kusa da juna a cikin bus. Miqewa matar tayi ta sayo meat pie da ruwa kafin ta dawo, gaba daya mutanen wajen binta suke da kallo musamman yan matan nan, don kana ganinta kasan ta san yanda yanayin wajen yake don hidimarta take hankali kwance, ita kuwa daman ba wannan ne zuwan ta na farko ba, tasha zuwa saudiyya aikatau, tun tana kamar su . Matar tasha adan bula a fuskanta inda tayi bular hanci har guda biyu ga hakoran Makkah data saka a hakoranta har kusan guda hudu. Kana ganinta kaga asalin takarin saudiyya wanda idanunsu ya bude sosai. Zama tayi kusa da yarinyar nan inda yarinyar ta hade jikinta waje guda saboda fargaba, gashi bata iya communicating da mutane ba don kwata kwata tun tasowarta ba a bata damar mu’amala da mutane ba, daga mamanta sai innarta da kawu shikenan, gaba daya rayuwar ta is just around them su uku. Meat pie dinta ta fara ci hankali kwance ta kora da ruwa, saida ta cinye tas ta ajiye dayan daman guda biyu ta sayo, kallon gefen yarinyar tayi, haka kawai taji yarinyar ta bata tausayi, don itama lokacin da aka tura ta aiki lokacin bata wuce shekarunta ba, ita tundaga kauyen gezawa dake garin kano aka daukota aka kawota saboda talauci. Kallon meat pie din da matar ke miqo mata yarinyar tayi kafin ‘’karbi mana’’ matar ta fada tana mai sake miqa mata. Hannu biyu yarinyar ta saka ta karba, har lokacin hannunta karkarwa yake saboda tsoro, sai alokacin ta bude baki tace ‘’nago..de’’ Murmushi matar tayi mata tana mai kokarin tura sauran yan chanji ta cikin Jakarta ‘’sunanki sabeeha ko? Kema aiki zakije yi?’’ Dago da jajayen idanunta tayi ta kalli matar don bata ma san taqamaiman dalilin kawo ta nan da akayi ba, kawai dai ta amsa ta da ‘’eh’’, Wata tambayar ta sake jefo mata ‘’wannan agency dinne suka dauke ki?’’ A tsorace dai yarinyar take amsa matar, da eh, gaba daya ma she’s confuse ita kuwa matar babu abunda take mata sai murmushi kafin tace ‘’ki cire tsoro kinji, wannan tsoron zai iya jawo maki matsala, don mutanen kasar basu da yarda musamman idan sukaga mutun baki ne,’’ ‘’toh nagode’’ yarinyar ta amsata sai alokcin ta danji dama dama datayi Magana da matar. Meat pie din ta soma turawa a bakinta badan dadi take ci ba sai don yunwar dake nuqurqusarta daman bataci komai ba don bata gama sauke tukunyar dumamen data daura masu ba mama ta tasota gaba tun da asuba, babu ko tausayawa. Suna nan zaune aka kira jirginsu, gaba daya suka mike suka shiga cikin jirgi,jirgin nasu dan karami ne bashi da wani girma sosai, daga gani dai irin kananun jiragen nan ne waenda kudadensu ke da sauqi. Koda suka shiga da taimakon matar nan ta samu wajen zamanta, cikinta ya gama durar ruwa sosai, sai a lokacin ta tabbatar wata duniyar za a kaita, inda bata san kowa ba batasan me zata tarar achan ba, karshen zance ma bata san me zai kaita chan ba. * **Saudi Arabia Tahlia street** Tahlia district na cikin garin jedda a kasar saudia, wannan anguwa ta kasance anguwace ta wane da wane manya manya masu kudin dake kasar saudia masu mulki da masu mukami, yawanci da kaji an anbaci tahlia street to ana nufin zuciyar jedda don shine top wealthiest district a kasar saudi arabia. Duk wani mazaunin wajen yana ji da kudi da arziki tun lokacin da aka kafa ma anguwar tambarin zuciyar jedda don ba kowa ke iya zama anan ba, gashi gaba daya anguwar ansan juna don yawanci manyan masu kudi da suka zauna a anguwar bayan sun mutu yayansu ne suke gadar wajen don zama a anguwar babban assets ne. Tahlia district kamar gari guda take don babu abunda babu a cikin district din, daga kan manya manyan branded shopping malls zuwa ga manyan companys da top class hotels da restaurant wanda yawanci na mazauna wajen ne, don kamar competition sukeyi tsakanin junan su. TAHEEL Groups. Taheel groups yana daya daga cikin manyan companies dake cikin tahlia district, an kafa taheel group tun shekaru da suka shude wanda ayanxu yayan masu shares din company din ne suke running companyn. Major holders na group din taheel group sune the taheel family,don mahaifinsu (Taheel Abdullah Tajuddeen) shine founder na TG wato taheel group,kuma suke da 75% share na company din. Taheel groups suke providing gaba daya malls dake cikin tahlia district harma da wasu garuruwan daban a cikin kasar saudi kamar su riyadh da Dammam, suna da collaboration da manyan manyan shop irinsu Gucci, dolce gabbana, ralph lauren, Giorgio Amani da dai sauransu inda suke sayan product dinsu harda tag dinsu su kuma saisu saka masu a shopping mall market dinsu, bayan wannan sune masu babban bankin da ya zamanto yana cikin top 5 best banking service (TG BANKS). The Taheels Residence……. Wani tamfatsetsen modern gida ne a cikin tahlia street, gidan ya gaji da haduwa gashi da dan banzan girma sosai don zaikai gidaje biyu da suke jere a street din don kamarma yafi sauran gidajen kyau da haduwa, daga wajen gate din farko ma abun kallo ne don an qawatashi da karafuna mai adon royal gold dogaye duk sun zagaye da gidan. Street din,kwata kwata babu hayaniya kamar babu mutane, ko’ina tsaf tsaf so organised, babu karikicen gidaje masu hayani, kowane gida is bulid with luxury and class don dole arziki yayi kuka a wajen nan don an kashe kudi sosai. Tsirarrun jigaggun motoci ne ke shige da fuce a street din inda Wata mota mai nunfashi kirar audi r8 baka wuluk ta shigo street din, bata tsaya ko’ina ba sai gaban taheel residence, motar ta dan dauki minti biyu kafin electric gate din ya fara sliding ba tare da an taba shi ba, gate din na wangalewa motar ta kutsa cikin gidan, haka motar ta mike babban compound din dayasha duwatsu farare tass sai bishiyoyi daga gefe koraye tarr, matuqin bai tsaya ko’ina ba wajen parking lots inda motoci ke jere kusan guda goma, brands daban daban abun dai ba a cewa komai, wajen parking dinma abun kallo ne. An dauka kusan minti biyar kafin a bude kofar motar, kafarsa ya fara fiddowa wandda ke cikin wani loafters cover shoe baki kafin ya fito gaba daya, kyakyawan magidanci ne fari tass, yana da farin saje wanda ya fidda girmansa da haibarsa, sanye yake da suit baki wanda tayi mashi kyau sosai, idanunshi na cikin wani farin glass. Rufe motar yayi kafin ya nufi hanyar shiga cikin gidan, anatse yake tafiya har yazo gaban wata katuwar security door mai kalar gold, kamar an kerata da gold. Door bell ya danna anatse kafin ya dan jinkirta for a second. Karar door creak dayaji ne yasa ya sanya hannu ya tura kofar… Maids din dake ta faman shige da fuce suna hidima a sitting room dinne suka soma gaishesa sanin koshi waye, hannu kawai ya iya daga masu kafin ya wuce sitting room din baqi inda shine face of the house don nan ne babban parlorn gidan, gida dai ya tsaru karshe haduwa basai na tsaya baku rahoto ba, abunda zan iya cewa kawai shine gidan nan aljannar duniya ne, komai na daban ne a cikin gidan don an narkar da kudade masu daraja anan.. * Bude kofar dakinta da akayi ne yasa ta dagowa don ganin wanda zai shigo mata daki kai tsaye haka. Wani irin kallo ta watsa ma wadda ta shugo bedroom din tayi kafin ta danyi tsuka ta maida hankalinta kan wayarta kirar latest Samsung ultra,kwance take kan wani makeken gado na alfarma dayasha beddings mai kyan gaske cikin wani kayataccen daki daya sha kayan alatu, hannayenta duka biyu data rike wayar tata yasha manya manyan zobunan daham da awarwaro gefenta kuwa surface laptop ne kalar wayar nata black color, farace saidai ba tass dinnan ba sannan siririya ce don bata da qiba kwata kwata amma akwai kyau masha allah, sanye take da wata baqar riga ta zaman gida. For the second time ta sake dagowa ta kalli wadda ta shugo ganin ta tsaya bakin kofar kuma tayi shuru tana kallonta ‘’babu salam?’’ Rufo kofar wadda ta shigo tayi, itama kyakyawa ce ajin farko saidai ita tafi wanda ke kwance kan gadon haske sosai kuma suna kama sosai, hannunta na rike da hand dryer da alamu gyaran gashinta tayi daya sauko har wajen mazaunen ta yana sheki, gaba dayansu kana kallonsu kasan larabawa ne kuma jinin larabawan asali, ga hancin ga idanu kamar sun qera kansu. Wadda ta shugo sai kamshin bakoor take,ita kuma tana sanye da riga da wando wanda suka dan kamata sai yar jellabiya data daura akai baqa kuma transparent, fuskanta adan hade ta karaso inda yar uwar tata take zaune kafin ta zauna gefen gado ta soma Magana cikin harshen larabci da turanci ‘’kedai wallahi idan kika maqale a daki bakyasa futowa kamar wadda ke boye boyen wani abu, marasa gaskia ne ke kulle kansu waje daya, ni bama wannan ba kinsan waye yazo kuwa fadwa?Guess who?’’ Wadda ta kira da fadwa bata dago ba hankalinta nakan wayar dake hannunta tace ‘’who?’’ ‘’khaal’’( meaning uncle) yar uwar ta bata amsa Cikin hanzari ta ajiye wayar tata ta zauna tana mai kallon ta tace ‘’khaal kuma afiya? meyazo yi kuma na dauka ay ya daina zuwa gidan nan tun bayan abunda ya faru last zuwan nashi?’’ fadwa ta tambayi yar uwar tata tana mai sauraronta don tasan ba haka kawai zaizo ba don it’s been a while rabonshi da yazo don kwata kwata zuwanshi rikici yake kawowa. Kallonta wadda ta kira da afiya tayi kafin tace ‘’its obvious mana yazo duba wannan mara hankalin ne gashi ukty bata nan, hmm I don’t even know what’s going to happen today’’ Fadwa ce tayi saurin cewa ‘’uktyn bata dawo daga office din bane? Naga yanxu it’s almost 5?’’ ‘’nop not yet but I’m sure zaman jiranta zaiyi,saita dawo tukunna ni karma ya fara min maganar aure cause….’’ Dan jinkirtawa tayi da Magana kafin ta tabe baki ta cigaba da cewa ‘’anyways muje dai kasan mu gaisa dashi muji dame yazo yau kuma, I don’t understand why he’s wasting his energy akan wanda baima san ina kanshi yake ba’’ tana kai aya ta mike tsaye ta nufi wajen dresser ta ajiye handryer din. Afiya ce ta fara fita kafin fadwa tabiyo bayanta. * Atare suka sauko daga stairs din mai shegen tsayi dayasha floor carpet, saida suka fito ne na masu kallo tass, gaskia suna da kyau, masha allah ga gashi tabarakallah,bazasu wuce shekaru from 31, 33 ba, kamannin su daya kana ganinsu kasan siblings ne, hannayensu dasuke rike da manya manyan wayoyi sanye da zobunan gold haka zalika kana ganinsu kasan kudi ya zauna a jikinsu saboda yanda skin dinsu ke sheqi, saidai kuma jikin ne dan kiff dan sirara ne basuda girman jiki. Kwata kwata babu alamun girma na shekaru a tattare dasu saboda arziki ya danne tsufan sai ya zamana kamar yan 20s. Yanda suke saukowa cikin aji kamar bazasu sauko ba, sama sama suke hira suna dariya, Wato gidan ma ya gama gajiya da haduwa, daga waje ma ba komai bane ba don saika shugo daga ciki zaka tabbatar da haka don yasha kayan alatu na zamani, duk inda suka gifta ma’aikata ne suna ta hidima kowannen su sanye da uniform daban daban, gidan dai kamar gidan sarauta don yana da girma sosai ga kofofi da yawa alamun parts parts ne. Ko’wanne lungu da sako shaqe yake da kayan zamani, ga luxurious interiors ta ko’ina. Hanyar second sitting dake cikin gidan suka fara wucewa kafin su karasa first sitting room wanda shine face of the house. Da sallama suka shiga parlorn afiya na gaba fadwa na biye da ita abaya saboda tana receiving call din daya shugo mata saida suka zauna tayi sallama da wanda take wayan dashi inda tace ‘’bye qalb’’ kafin ta sauke wayan daga kunnenta. Azaune suka taddashi idanunshi nakan news saidai kwata kwata hankalin shi ba’akan news din yake ba,babu abunda yake mashi yawo akai sai tunanin last zuwanshi da yayi cikin gidan, ba da karamin bacin rai yabar gidan ba saboda y’ay’an dan uwan nashi musamman hidaya, kwata kwata bata ganin girmashi, tafi karfinshi ma, don sai abunda tace za ayi, darajar alqawari da kuma mahaifinsu ne kawai ke sashi zuwa gidan badan haka ba da bazai sake saka kafafunshi cikin gidan ba, bayan wannan akoda yaushe idan ya zauna babu abunda yake dana sani akai sai tilasta dawowar taj da yayi, dukda ya yarda komai muqaddari ne daga allah saidai deep down yana regretting dawowarshi don shine ya tsaya tsayin daka akan dole saiya dawo, sai yake jin kamar ta dalilin nan ne abunda ya faru wata uku da suka wuce ya faru.’…… Muryoyin su da ya soma jiyowa ne ya sashi fargawa daga tunanin daya fada, duban tafkeken wall clock din da akayi ado dashi a parlon yayi, karfe 5 da rabi Kenan na yamma, sallamarsu ya sanya shi dagowa ya kallesu daya bayan daya, zaman half an hour yayi a wajen sai aynxu suke saukowa, shidai yana mamaki hali irin nasu koda yake baa abun mamaki bane don yanxu kam ya saba da halayensu, . kauda kanshi gefe yayi daga garesu ya maida kan tv, kowannen su sanye take da kayan zaman gida gashin nan a bude don ko rufewa basuyi ba,bayan wannan yasan su da practicing rayuwar turawa so su hakan ba komai ne a wajen su ba dukda shi dai hakan a wajenshi ba wayewa bace da girmansu kuma da shekarunsu, shigar fadwa ne ma yafi tsaya mashi arai don ita tana da aure ba kamar afiya ba amma idan ka gansu zaka dauka gaba dayan su basu da auren . Karasowa sukayi inda yake zaune dan nesa dashi, kan kujerun single chairs dake facing nashikafin su zauna, fadwa ne tayi saurin cewa ‘’marhaban khaal’’ Ba tare da ya kalleta ba fuskanshi adan hade yace ‘’shukran fadwa,’’ Afiya ce ta dan tabe baki don daman itace tafi rashin kunya kuma yawanci yafi sa ido akan ta musamman rashin auren da bata dashi. ‘’Marhaban khaal’’ ‘’shukran’’ ya amsata kai tsaye ba tare da ya sake kallon inda suke ba. Takun sahun kafafun da sukaji ne yasa duk suka dago, wani dan yaro ne ya shugo kyakyawan gaske bul bul dashi, bazai wuce 12years ba, yana sanye da kayan paw patrol sai wata yar cute jaka a bayanshi, hannunshi rike da pack of doritos chips da nintendo switch gaming pad, sai faman cin doritos din yake. Cikin sitting room din ya karaso aguje yana washe hakora ‘’Jadd’’ (meaning grandpa) Inda dattijon yake zaune yaron ya nufa cikin farin ciki da jin dadi, farin ciki ya gama lullubeshi, Hannu dattijon ya bude mashi ya taho a guje ya shige jikinsa kafin ya rungumeshi shima dadi duk ya gama lullube shi sosai, ‘’Barad’’ Dattijon ya kira sunan yaron bayan ya fiddoshi daga kirjinshi, murmushi yaron ya soma mashi kafin ya soma gaishesa, kumatun shi dattijon ya kama irin yanda ya saba yi mashi koda yaushe‘’I missed this cute baby face’’ Turo baki yaron yayi kamar zaiyi kuka yace ‘’jadd I’m not a baby anymore, I’m turning 13 next month’’ Shafa kanshi dattijon yayi kafin ya sumbaci kumatunsa yace ‘’kaje school yau?’’ ‘’yes jadd’’ yaron ya amsa dattijon. Wani irin kamshi ne ya danno cikin parlorn mai tsada don lokaci guda ya bade parlor kamar anyi ruwan turare, takun tafiyar ta ne ya biyo baya ‘’qwas qwas qwas’’wanda yasa duk suka juyo suna kallonta banda dattijon da yayi mata kallo daya ya dauke fuska sai yanayin fuskanshi ya chanza gaba daya kamar bashine ya gama yima yaron nan dariya ba. Nima dai kallota na soma yi, kasa dauke idanuna nayi akanta, wato wata irin classy matace a tsaye, daganin fuskanta kasan ta soma manyanta saidai tsufan ya boye sosai don kwata kwata bazaka iya tantance shekarunta ba dukda tana early 40s, farace tass kamar a bula fatarta jini ya futo,ya allahu, tana da kyau sosai don doguwace, sanye take da wata azababbiyar abaya baqa wadda ta haskata sosai tayi mata kyau don ta haska fuskanta data dan hade girar sama da kasa, gaba daya zubinta irin na matan nan ne da basa daukan nonsense, ga jii da kai da kudi da aji, waya ce kawai a hannunta kirar iphone 15 pro max latest, gefenta kuwa wata maid ce rike da Jakarta da wasu document tana biye da ita a baya don kusan taku uku ne tsakaninsu saboda ita ba a jerawa da ita. Idanun matar sunsha kohl baki wuluk tayi lining idanun nata sai bakinta dayasha jan matte lips stain. Kamaninta sun fito sosai da su fadwa saidai kamannin nata yafi zama visible da afiya don tama fi yanayi da afiya akan fadwa dukda kamanninsu ta jini itama ta fito. Saida ta gitto parlorn ta hango dattijon sai kuma maganganunsa da barad data jiyo. Chak ta tsaya tana kallonshi kafin ta tako cikin kasaita ta karaso parlorn, fadwa ce tayi saurin miqewa tana mata sannu da zuwa kafin ta bata inda ta zauna ta koma gefe. Kamar an mata dole haka ta dago ta kalli maid din kafin ta bata umarnin wucewa da Jakarta zuwa sama, kallon barad tayi kafin ta mashi nuni da hanyar stairs ba tare da tace uppan ba, miqewa yayi yana ma dattijon murmushi kafin ya fuce daga parlor. Gyaran murya tayi kafin tayi relaxing bayanta akan kujerar ta daura kafa daya kan daya duk akan idanun dattijon yana kallon ikon allah, saida ta dan dauka yan few seconds kafin ta soma Magana anatse with class ‘’marhaban khaal’’ ‘’shukran Hidaya fatan na sameku lafiya’’ A gatsale ta yatsine fuska tace ‘’alhamdulillah’’ Shuru ne ya biyo baya, su fadwa dai kallonsu suke daga shi har ita, yanda kasan maqiya sun hadu. A duniyar nan hidaya bata kaunar ganin mutumin nan agidannan,a yanu tana mashi kallon kamar maqiyinta dukda yana matsayin qanin mahaifinta marigayi Taheel, duk yanda taso akan ganin ya raba hanya da gidan abun yaci tura don ita gani take yana son ya shiga tsakaninta da big baby dinta ne to wama ya isa? Babu shi a doran kasa. Bata qaunar kowa ya rabe shi kwata kwata,wannan yasa duk yanda zatayi saitayi don ganin tayi pushing uncle away. Ganin shurun yayi yawa ne yasa hidaya cewa ‘’ko zan iya sanin dame kake tafe?’’ Mamakin jin tambayarta yayi da yanda tayi mashi tambayar saidai saninta da halinta yasashi dannewa kawai ya gyara zama don idan har zai bi abunda zuciyarshi ke raya mashi akan yayan dan uwan nashi marigayi Taheel to fah bazai kara waiwayar su ba, gyara zama kawai yayi ya danyi relaxing bayanshi kafin ya soma magana. ‘’ba komai ne ke tafe dani ba sai maganar Tajudeen,’’ Saurin rintse idanu tayi kafin ta budesu ta sauke akanshi, Ganin haka yasa shi cigaba da cewa ‘’yanxu wata uku Kenan babu wani progress akan condition dinshi, shine nace ko zamuyi trying wasu expert health organization da suka kware sosai ta wannan fannin na wasu kasashen daban ko za a samu dacewa’’ Tsagaitawa yayi kafin ya nunfasa ya cigaba da Magana cikin kamala ‘’ ni ina ganin idan muka dage sosai akanshi za a samu cigaba akan matsalar tashi’’ Wani irin kallo take mashi mai wuyar fassara wanda yana hango tsantsar bacin rai a cikin idanunta saidai fuskanta bai nuna hakan ba shima hakan bai sashi ya tsagaita ba don hakan bazaisa yayi shuru ba. Cikin muryarta mai tafe da wani irin salo mai jan hankali ta soma Magana ‘’so yanxu kana ganin babu abunda nakeyi akai ne?well likitocin nan kasar ma top notch doctors ne kuma there are one of the best in the whole world and I trust them, khaal I know what is best for him, babu wanda zai nunamin damuwa akan matsalar big baby, so please idan kazoo ne akan wannan maganar ka ajiyeta don I know what is best for him baka fini sanin abunda zai taimakeshi ba don nice komai nashi, so please..’’ta karashe tana mai kallon cikin idanunshi babu ta kunya balle ganin girmansa Fadin irin bacin ran da dattijon da suke kira da khal yake ciki ma bata lokaci ne, yau yaga karshe rashin mutunci wajen yar dan uwansa, yarda aka haifa a gaban idanunsa. Wani irin heavy abu yaji a kirjinsa kamar an buga mashi dutse, haka yayi saurin runtse idanu yana danne abunda yake ji. Mikewa yayi tsaye ba tareda ya kalleta ba yace ‘’shikenan na barku kuyi abunda kuka ga yayi dace, saidai ina tunasar dake, ba’a wasa da amana duk qanqantarta zan samu ganinshi yanxu?’’ Cikin sauri ta dago ta maida dubanta gareshi da jajayen idanunta kafin ta maida dubanta ga agogon rolex dake maqale a hannunta ‘’I’m sure he’s asleep by now, don…’’ Kasa daukan wulaqancin yayi don haka yayi saurin katseta ta hanyar cewa ‘’ ba damuwa na barku lafiya’’ Yana kaiwa nan ya masu sallama ya nufi hanyar futa, harya fuce hidaya bata bar kallon hanyar dayabi ya fuce ba, tafarfasar da zuciyarta keyi kamar an zuba tafashen ruwan zafi, su fadwa kuwa kasa cewa uppan sukayi sai zuba mata idanu da sukayi suna kokarin karantar reaction dinta, ‘’tirkashi ana wata ga wata,interesting’’ fadwa ta fada a zuciyarta tana mai tunanin wani abu. Ganin ta mike tsaye yasa suka bita da idanu harta wuce hanyar stairs anatse kamar wata dawisu. Kallon juna sukayi atare kowannen su da irin tunanin dake yawo a zuciyarshi… MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍) ❤️🔥Romantic love story❤️🔥 Written by QueenMarh Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai… Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya. The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃 Enjoy!!!!! Free page Chapter 2-3 * Saman hidaya ta wuce anatse, tsayawa tayi tana kallon parts din dake saman, duk girman gidan nan part biyun nan yafi haduwa, daya na gefen hannun dama dayan kuma na hagu, saidai kofar part din daman yafi kyau sosai don wata iriyar koface mai shegen girma da kyau security door, handle din kofar ma automatic digital biometric lock ne irin na zamani wanda ba kowa ne ke shigan wajen ba. Ta dauka yan mintuna qalilan kafin ta kauda idanunta daga wajen ta nufi hanyar dayan part din dake hannun hagu . Chak ta tsaya ba tare da ta sake daga kafarta ba da niyar tafiya Jin karar bude kofar dayan part din, da mamaki take kallon kofar don ganin wani gwanin ne zai fito daga part din a wannan lokaciin don shige da ficen part din saida izinin ta, don ta gindaya sharudan shiga part din. Da mamaki take kallon maid din data futo, ga hawaye akan fuskanta, gaba daya kana ganinta kasan she’s stressed daga yanayin yanda take tafiya, tana sanye cikin uniform dinsu na aiki, hannunta rike da tray mai kyau, asaman tray din an daura wani bowl na corn beef porridge sai glass din ruwa’. Maid din na ganin madam gaban ta ya fadi, shikenan tata ta qare, daman tsoron data dunga ji Kenan na qin futowa don idon ta futo da abuncin ma matsala ne don job dinta ne ta tabbatar anci abuncin sannan kuma akwai time schedule da aka bata na musamman na yanda zata kula da abunda ya shafi part din bayan wannan ma akwai kashaidin da aka bata akan duk sanda ta tsallake rules din to fa sallamarta za ayi. Duk inda karfe hudu tayi babu maid din dake zuwa part din kwata kwata hatta saman ma basa haurowa gaba dayan su. A cikin gidan akwai over 10 maids daban daban banda waenda ke kula da alamuran daya shafi premises din gidan. Dauke ganin ga daga kan maid din tayi ba tare da ta ce mata qala ba ta nufi hanyar dayan part din, maid din na ganin haka kawai ta sauka kasa don tasan an sallameta Kenan, ita a dadinta ma don har wani sign of relief ta sauke. Hanyar walkway din dazai sadata da living room tabi, babu sautin dake tashi sai karar hills din dake kafarta na saint Laurent red color wanda ya fidda clean kyawawan yatsunta. Kamshin bakhoor ne kawai ke tashi a parlorn sai sanyin ac daya bade ko’ina, tana karasawa tsakiyan parlorn ta tsaya tabi ko’ina da kallo, babu datti ko digo, har sparkling wajen keyi, parlor yayi mugun haduwa komai na parlorn black and gold ne. Motsin dataji ne yasa ta maida dubanta ga hanyar kitchen din part din nata, wata budurwa ce ta fito sanye da uniform riga da wando irin na dayar maid din saidai color ya banbanta don ita wannan blue ne hannunta rike da electric cleaner da alamu gyara ta gama yi, tana ganin madam din ta tayi saurin rissinawa kanta a kasa. ‘’wani time ne ya kamata a gama aikin yamma?’’ Hidaya ta tambayi maid din tana mai kallonta irin kallonda zan fassarashi da kaskanci. Jikin yarinyar ne ya soma kyarma kanta a kasa ta soma rarraba idanu ‘’4pm madam’’ Yarinyar ta bata amsa da harshen larabci wanda baya futa sosai saboda ba yar kasar bace yar Senegalese ce. ‘’shekaranki nawa kina aiki anan? Wani agency ne suka kawo ki nan? Bakisan rules dina bane? Duk inda 4 ta wuce bana son ganin kowa a part dina?’’ Yarinyar harta soma kuka don tsoron abunda zai biyo baya cikin shesheka ta soma Magana ‘’jiya aka kawo ni ma’am, ina cikin waenda akayi recruiting sabbin workers this month madam, I’m sorry madam ban sani bane’’ ‘’you must be very stupid,you’re fired’’ A kidime yarinyar ta dago jin abunda madam din tace, sanin cewa ayanda ma’aikatan data tarar a gidan ke yawan fada bata son hayaniya yasa ta hadiye kukanta daya ciyota, don ba’a musayar yawu da ita, har a lokacin tana nan tsugunne bata motsa ba. Ba tareda ta kalleta ba ta wuce hanyar bedroom dinta idanunta har lokacin sunyi jaa sosai,tana shiga dakin ta banko kofar,yarinyar kuwa haka ta mike ta fuce inda wata yar aikin daban ta fito daga cikin kitchen din part din hannunta rike da tray an daura glass jug mai shegen kyau sai glass cup da wasu vitamins a gefe, kana ganin yarinyar kaga yar india itakuma. Hanyar bedroom din madam tabi tare da shiga cikin bedroom din,don aikinta Kenan itakuma duk abunda ya shafi harkar personal buqatun madam din, tana shiga cikin mintuna qalilan na soma jin karar fashe fashen abubuwa daga cikin dakin, kafin daga baya kuma aka bude kofa, yarinyar data shiga ce ta fito a rikice ta rufo kofar kafin ta sauka kasa itama. Mamaki bai hana ni shiga don ganin me ke faruwa cikin bedroom dinba, a tsaye take hannunta rike da wani document data taho dashi daga office, sai kuma wayarta dake yashe a kasa don wani muhimmin call ta dunga expecting tunda safe sai yanxu akayi responding dinta sai gashi kuma abunda take buqata din bai samu ba saima wasu dogayen dokoki da aka fado mata wanda dole sai an bi dokokin ne zata samu abunda take so,Rayuwar ta yanxu gaba da baya aiki ne kawai tasa a gaba. Babu abunda take sai zagayen dakin from one end to the another, tama rasa tunanin da zatayi, ‘’I have to do something cikin gagagwa, wannan ne kawai last chance da nake dashi to make it mine, wallahi wallahi bazan yi kaffara ba, bazan taba bari taheel groups ya kubuce daga hannu na ba, no never not now and not ever.’’ Hannunta ta sanya a daidai tsakiyar goshita tana wani nazari kafin ta dafe kanta ‘’dole ne nayi shiri I need to plan accordingling, bazan taba bari legacy din famyln nan da sacrifice din da Abii yayi ba to go to waste I can’t let them have it all inaa’’, Haka ta dunga safa da marya tsakanin dakin abubuwa da dama sun tsaya mata arai, ga wannan matsalar data kunno mata da taso ta kasheta cikin sanyi ba tare da sanin kowa ba sai gashi plans dinta suna neman rugujewa, na biyu kuma ga maganar khaal data tsaya mata arai. Gaba daya dakin ma ta haukata shi saboda bacin ran da take ciki, daman ta haka take sauke takaici akan duk abunda ta samu na anfani, nan take zata tarwatsa shi ya tashi daga amfani, Wayar ma na daya daga cikin abubuwan da suka tarwatse don da alamu tana gama wayar ta wullata kasan tiles, gefe kuma glass jug dinnan ne da maid ta shugo dashi akan wani stool, gabanta kuma glass cup ne afashe da wasu kwayoyin vitamins. Kallon papers din take jikinta har kyarma yake kamar mazari kafin ta watsa su kan gado ta wuce hanyar wani glass petition….. Zuge glass din tayi nan take bathroom dinta ya bayyana sai wata yar kofa a gefe da alamu closet ne, toilet din ta fada, saida ta dauka yan mintuna kafin ta fito daure da towel, jikinta luwailuwai kamar fatar jariri, hanyar walk in closet room tabi inda aka zagaye dakin da wajen ajiye kaya daban daban, gefe guda kayan maza ne a wajen hakan ya tabbatar min da qila na mijinta ne. Bata tsaya ko’ina ba sai wajen kayanta, wasu kayan zaman gida ta zaro masu laushi kafin ta ajiye su kan table din dake tsakiyan closet din, tana ajiyewa ta nufi wajen wasu drawers, nan ta soma jawowa ta fiddo da kayan shafenta da kamshi, komai dai is organize ba a cewa komai, saida ta gama shiryawa tsaf ciki kayan kafin ta nufi wata drawer daban inda a jikin drawer an manna wani tag da manyan harufa ‘’first aid’’ Bude wajen tayi ta zaro wani roban magani da plate din daura maganin, kafin ta fuce daga closet din. ** **UNITED STATES ** San Diego California 11:55pm Cikin sauri sauri take tafiyar dukda hasken daya gauraye street din hakan baisa ta daina jin fargabar data fara jiba tun da ta sauka daga motar data ajiyeta, sanye take da riga da wando jeans, kayan sun amsheta don tana dan jiki, gashin kanta ya sauko a har bayanta, babu abunda take zai zabga sauri, hankalinta yayi gaba kawai wanda hakan yasa ban hango yanda yanayin fuskanta yake ba,Daidai hanyar wani street tabi inda aka rubuta Boulevard California street a jikin symbol dake nuni da hanyar ne zai kaika har street din, motar data sauketa ne kirar benz ta wuce ta gabanta inda daga gaban motar matukin ya zuge aka dago mata hannu, cikin matsuwa ta daga masu hannu itama kafin su wuce, babu abunda ke tashi sai kida wakar hip hop daga cikin motar, cikin abunda bai wuce minti biyar ba ta dunga wuce titin dake street din wanda iska ke kada bishiyoyin kan hanyar sai gidaje masu shegen kyau terrace a man manne an tsara gidajen da bricks masu shegen kyau. Ganin ta tsaya chak nesa da wani gida yasa na zuba mata idanu,kallon hanyar dazai sadata da gidan take inda aka saqala wani symbol ajikin ginin gidan da manyan rubutu kamar haka, (Barr Majeed res flat c) maido da dubana nayi wajen inda take kallo ganin ta kurama symbol din idanu kafin ta sauke wata nauyayyayyar ajiyar zuciya ganin babu motar dady kafin ta shige cikin gidan cikin sassarfa daman ta tabbatar bayau zai dawo ba, mummy kuma na night duty a asibiti saboda doctor ce. Bata tsaya a ko’ina ba sai daidai stairs din dazai sadaka da kofar cikin gidan,leqe ta soma yi kamar mara gaskia ganin lights din windows din gidan duk a kashe yasa ta tsugunnawa ta cire igiyar takalminta duka biyun kafin ta fiddo da kafarta, bata da haske saidai skin dinta yana glowing don irinsu ake kira da caramel complexion, kamar bata taba taka kasa ba, yatsun kafafunta sunsha nail paint pink sai wani zoben kafa data saqala, tana fiddo da kafar tayi saurin bude back pack dinta mai kyau, wata abaya ta zaro ta zura akan rigarta kafin ta tura takalminta cikin jakar, tana gamawa ta haura stairs din da baifi guda uku ba harta tsaya gaban kofar, ta dauka kusan minti daya anan tsaye kafin ta daga hannunta ta danna door bell, tana dannawa sau daya ta janye hannunta ta tsaya chak, ta dauka kusan minti biyu a tsaye jin shuru yasa ta sake danna door bell din, daidai nan aka bude kofar, wata mata ce ta bude kofar, idanu yarinyar ta zuba ma matar ganin hankalin matar adan tashe, itama kallon ta matar ta soma yi da yanayin shigar jikinta. Matsa mata gefe matar tayi ba tare da tace mata uppan ba harta shugo ciki kafin ta rufe kofar, tana rufewa matar ta wuce ba tare da ta sake waiwayonta ba don ta tsaya chak a tsaye kamar munafuka ‘’nanny bee I’m sorry’’ Chak matar ta tsaya jin abunda tace, karasowa yarinyar tayi ganin haka kafin ta kamo hannunta ta cigaba da Magana ‘’nanny bee bansan time ya tafi har haka ba, please I’m sorry na saba alkawari’’ ‘’where…are.. you coming from’’ Wata kaushashiyar murya ce daga cikin sitting room ta doki kunnenta, nan take gabanta ya fadi dam batama san lokacin data saki hannun nanny bee ba, nan take idanunta suka soma kawo ruwa, yau tata ta kare, badai muryar dady take jiba, daman yau zai dawo? But mummy tace mata sai Monday zai dawo yau kuma Friday, shikenan tata ta kare yanxu tsoronta irin punishment din dazai bata saboda last warning ya bata, nan take ta soma hawaye har tsoron juyowa take ji don ta bama hanyar sitting room din baya. Wani magidanci ne a zaune akan kujeran sitting room din, parlorn yayi dim saboda lights din parlor ba’a kunne suke ba sai side lamp dake kunne guda daya wadda haskenta bai gauraye parlorn ba, fuskarshi kawai na iya hangowa, fari ne sosai ga hanci kamar biro, suman kanshi a kwance cikin wata hula fara tass, yana sanye da farar jellabiya ya daura kafa daya kan daya yana girgizawa da alamu ranshi a bace yake sosai duba ga yanda yayi Magana,daman zaman jiranta yake yaga ta yanda zata shugo, dawowanshi 5 hours ago, da farko yayi tunanin ko tana daki ne, don kwata kwata daya dawo baiji motsinta ba kuma yasan time din dawowanta daga school ya wuce, saida yaje dakin ya tabbatar da bata nan koda ya tambayi nanny bee wadda ita ke kula da ita tun dawowan su nan California tun tana karama harta girma zuwa yanxu, nan ta shaida mashi inda ta fada mata zata je kuma da saninta ta futa ita kuma dalilin barinta datayi ta futa shine ta shaida mata cewa zataje School prep na upcoming exams din su don shiga higher institution. Saida ta wuce time din daya kamata ta dawo ya soma fada sosai saidai kuma yasan ba laifin nanny bee bane don haka kawai ya zauna anan parlor don yaga gudun ruwanta da rashin hankalin ta don ranshi yayi mugun baci kuma yayi alqawarin this time around saiya koya mata hankali don daman ya bata last warning amma duk da haka ta tsallake sharudan daya gindaya mata. Wannan karan bazai saurarin mommyn ta ba kwata kwata daman itake hanashi displine dinta yanda ya kamata. Yana nan zaune har sha biyu saura, fadin irin tashin hankali da baqin ciki hade da bacin ran da yake ciki ma bata lokaci ne, bai gama tabbatar da maya ta kangare ba sai yanxu. 11:55pm dot kuwa saiga karar doorbell, har nanny bee ta fito daga bedroom dinta ta bude kofa baice komai ba don bata lura dashi a zaune a parlorn ba daman itama hankalinta ya gama tashi tun bayan time din datace zata dawo ya wuce, harga allah tana masifar son maya shiyasa bata iya hanata wasu abubuwan. ‘’nanny bee excuse us please’’ Sunkuyar dakai nanny bee tayi don sai taji kunya ya lullubeta saboda batajin dadin abunda maya keyi musamman da kulawanta ke hannunta. ‘’okay sir, goodnight’’ Tana kaiwa nan ta wuce bedroom dinta, maya dai kasa motsawa tayi sai data sake jin muryarshi ‘’come here this instant!’’ Cikin saurin ta karaso parlorn har tana tuntube da rug din dake tsakiyan sitting room din, kyam ta tsaya a tsaye tana danne hawaye dake neman zubo mata, saida taji yace sit kafin ta zauna a kasan tana facing dinshi, har lokacin bata bari sun hada idanu ba, shima daga nan bai sake ce mata komai don tunanin yanda zaiyi dealing dinta yake bayan wannan ma kokarin danne bacinranshi yake akan don ko dukanta bai taba yi ba saidai yayi mata fada sosai. ‘’explain your self, and mind you, karki sake kimin karya’’ ya fada a kausashe yana mai rufe idanunshi da sukayi jaa sosai alamun bacin rai ‘’’daddy I’m sorry please’’ ‘’hold your sorry maya, ay ban yanke maki hukunci ba tukunna, start speaking now!!!!!’’ ya karashe da fada sosai. ‘’nace daga ina kike?’’ ya daka mata tsawa A furgice ta dago tana rarraba idanu da hawaye suka wanke mata su sharr, ‘’birth…day..partyn Zara’’ ‘’what!!! Ya daka mata tsawa nan take jininta ya sake boiling, bakinta har rawa yake wajen furta ‘’daddy I’m sorry please, wallahi bazan sake ba I’m sorry please’’ Runtse ido yayi ya sake bude su akan ta kafin ya dan rage murya ya soma Magana cikin dacin rai ‘’maya kina mace?kina mace kika fita party sai midnight zaki dawo? Daman abunda kikeyi Kenan bada sanina ba? Gaba daya shekarunki nawa? Youre just 17 maya?,I’m so disappointed in you, and wallahi this time around zanyi maganin ki sosai’’ Ya karashe yana haki saboda tsabar bacin rai ‘’your phone, tablet, gaming pads, laptop and your keys drop them now’’ ya fada yana daka mata tsawa, jikinta har kyarma yake tsabar tashin hankali, nan ta soma fiddo su gaba daya daman a ciki bag pack dinta yawanci take ajiyewa. Wani irin kukan baqin ciki ne ya kubce mata lokacin data zaro car keys dinta wanda ko hawa motar bata taba yi ba daman birthday present ne daddyn ya saya mata for her 18th bithrday in the next 3 months, inda ya bata amma saita shiga sha takwas kafin ta fara tuqawa, yanxu shikenan, ko hawa batayi ba zai kwace, and duba ga yanda ranshi ya baci sosai dinnan tasan da wuya ya sauko sosai don taga tsantsar bacin ran da bata taba gani ba daga wajenshi, daman yawanci mummy ke shawo kanshi yanxu gashi bata nan balle ta taya ta bashi hakuri. Ajiyesu tayi tass a kasan tana hawaye saida ta gama tass kafin yace ‘’get out of my sight now!!’’ ya daka mata tsawa, cikin furgici ta miqe tsaye ta wuce hanyar stairs, koda ta hau sama wani daki ta bude daga wajen wani corridor, tana bude kofar ta banko ta tare da wulla Jakarta kan gado ta afka kan gadon itama sai hawaye, dakin nata komai pinkish nay an gata, harda tv station da makeup station, sai wani tamkeken round gado shima pink sai net daya zagaye shi gaba daya. Ko’’ina frame din hotunan ta ne zagaye a dakin inda tayi kyau sosai da kananun kaya masu kyau, maya dai akwai kyau babu laifi, bata da haske sannan akwai ta da idanu masha allah. Saida tasha kuka sosai akan gadon kafin ta mike zaune, kallon agogon gefen beside dinta tayi ganin karfe daya da rabi yasa ta mike ta soma rage kayan jikinta, anan kasa ta yasar da komai ya rage daga ita sai yar bra dinta da wani dan mini shorts pink color, toilet ta nufa direct,shima yasha adon pink, daga kan hangers dinta zuwa shower komai da toilestries komai in pink color, gashi fess fess babu kazanta saima kamshin dake tashi. Wanka tayi ta nado jikinta da towel kafin ta futo anatse tana goge hawayen idanunta da suka kasa tsayawa, kwata kwata bataso haka ba, waya itace rayuwarta, gaba daya gadget dinta dady ya karbe yanxu ya zatayi, ta yaya zata yi communicating da friends dinta abundai ya tsaya mata sosai arai don ko kayan barci bata saka ba ta hau bed dinta ta shige cikin duvet ta kwanta. Asuba nayi daddy ya kwankwasa dakinta, tana jin knocking ta tabbatar da shine nan take kuwa tayi zumbur ta mike zaune don daman idan yana nan wannan barcin nata ajiyeshi takeyi a gefe, ‘’tashi kiyi sallah’’ daddy ya fada daga bakin kofar ba tare da ya shugo ba ‘’na tashi daddy’’ ta amsa shi da gaggawa tana goge idanunta da suka kumbura tum kafin ta mike zaune ta wuce bathroom. Alwala tayi kafin ta fito ta wuce katuwar closet dinta, fadin yawan suturar ta ma bata lokaci ne don sunfi kala dari, anjera su fess fess, wata pink jellabiya ta dauko ta zura ta tare da janyo wani katon hijab dinta kalar milk, bata tsaya rufe closet dinba ta wuce wajen praying section na dakin nata,sallaya ta fara shimfidawa kafin ta tadda kabbara. Cikin yan mintuna qalilan ta idar da sallah, bata ma tsaya yin azkar ba ta cire hijab din da jallabiyan ta yasar anan kan sallayan kafin ta hau kan gado taja duvet dinta ta kwanta. Karfe takwas daidai daddy ya sauko daga sama, sanye yake da farar jellabiya, sai a lokacin na kare mashi kallo da kyau, kyakyawan magidanci ne fari tass ga hanci,yana da suman kai mai santsi da gashin baki wadda ya fidda kyawun fuskanshi, dining area ya wuce ya zauna daidai nan aka danna doorbell daga waje, ko ba’a fad aba yasan mummyn maya ce don haka ya gyara zama akan dining din ya soma hada tea, Nanny bee ce ta fito daga kitchen saye da uniform dinta, saida ta tsaya suka gaisa da daddy kafin ta wuce hanyar shugowa cikin gidan, ‘’assalam alaikum’’ Nanny bee ce ta tayi amsa sallamar tata kafin ta amshe jakar hannunta da lapcoat dinta. ‘’welcome ma’’ ‘’thanks nanny bee’’ matar ta amsata agajiya, Atare suka nufi sitting room ina matar ke tambayarta ‘’ina baby?tana barci ko?daddy ya dawo’’ ‘’yes ma, ya dawo yana dining area, maya bata tashi ba tukunnna’’ Cikin sassarfa matar ta karasa dining area inda mummy bee ta wuce upstairs zuwa dakinta don ta ajiye mata kayayyakin ta. Da sallama ta karaso dining din fuskanta dauke da murmurshi mai kyawun gaske, daidai nan daddy ya miqe tsaye don daukan brown sugar dake dan nesa dashi. Da sauri matar ta karaso ta rungumeshi ta baya tsam a jikinta tana mai sauke wata ijiyar zuciya. Shiko chak ya tsaya bai juyo ba saima hannunta data saqalo a kugunshi daya riqe gam. ‘’welcome back hubby, I missed you so so much kyakyawana’’ Wani irin murmushi ne ya kubce mashi lokaci guda dayaji sautin mujryarta, sai ya nemi fushin maya daya kwana dashi aranshi ya rasa shi tass kamar an wanke mashi zuciyar. Sakinshi tayi kafin ta zagayo inda yake ta zuba mashi mayun idanuwan nan nata masu shegen sheqi da kyau. Kallonta yake sosai babu kakkautawa yana ayyana irin kewarta daya yi a cikin zuciyarsa da begenta. Sai alokacin nima na zuba mata idanu don ganinta da kyau, sanye take da doguwar riga peach color mai adon dutsina a saman rigar sai tayi rolling kanta da mayafin kayan asaman kanta, rigar tayi masifar yi mata kyau don ta amshi jikinta sosai, itakam komai ma karbarta yake yi don da wuya ta saka abu baiyi mata kyauba. Matar batada jiki kwata kwata saidai akwai shape mai jan hankali, batada hasken skin irin pauu dinnan saidai daga ganin fatarta kasan tana shan gyara don tana da healthy skin. Tana da kyawun fuska mai kyau ga hanci itama ba laifi saidai baikai na daddyn ba, daga ganinta bazata wuce 38-39 haka ba. Shafo gashin bakinsa tayi ganin ya shagala da kallonta kafin ta danyi mashi fari mai jan hankali ‘’daddy wannan kallon fah?’’ Ta karashe tana kashe mashi idanu, murmushi kawai ya sake yi kafin ya soma Magana ‘’bana gajiya da kallon ki ne my cutie, welcome back, ya aiki? Kin gaji ko’’ Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta maida mashi da murmushin da yake mata ‘’wallahi kuwa daddy na gaji sosai bari naje na watsa ruwa saina sauko muyi break fast din tare’’ Sakin hannunta yayai kafin ya zauna yace ‘’okay’’ …..saman ta wuce direct bata tsaya ko’ina ba saida ta leka dakin maya, ahankali ta bude kofar ganin tana barci yasa ta rufo mata kofar. Dakinta dake gefe kusa da wani bedroom daban ta wuce, tana shiga daki ta sauke ajiyar zuciya tare da yin miqa. ‘’alhamdulillah’’ ta furta kafin ta karasa cikin bedroom din, dakine ne mai kyau da tsari, babu wani tarkace sosai saima books dake ko wani sako na daki, dresser ta kuwa yasha kayan shafe da gyaran jiki da gashi. Mayafin kanta ta soma warware nan take gashinta ya zubo kasa inda tasha kitson kalaba wanda ya sauko har dantse kafadarta, toilet ta wuce direct bayan ta ajiye mayafin akan gado inda nanny bee ta ajiye mata laptop bag dinta da wasu files data shugo dashi harda handbag dinta. Cikin mintuna qalillan ta fito daga cikin bathroom sanye da towel da alamu wanka tayi sai kamshin ke tashi daga jikinta. Agurguje ta gama shiri ta tsaf cikin wata hadaddiyar sexy riga red dukda rigar is decent hakan bai hana sexy jikinta fitowa ba. Turarukanta masu tsada ta feshe a jikin nata kafin ta zura wata yar hula ta fito hannunta rike da wayanta inda wani call ya shigo mata related to office. Kasan ta sauko cikin nutsuwa, kamshinta ne yayi mashi sallama inda ya zuba mata idanu kafin ya dan kauda kanshi saboda nanny bee data fito da flask a hannu, yana ganin darajar nanny bee sosai don dattijuwa ce don zata haifeshi harma da ita matar tashi. Dining din ta karaso har okacin wayan na kunnenta, saida ta gama wayar ta kalli nanny bee ‘’sannu nanny b, thank you for the breakfast’’ Murmushi nanny bee ta mata ‘’babu komai madam, akwai abunda zaku buqata yanxu? Zanje nayi ma maya breakfast kafin ta tashi’’ Dagowa daddy yayi ya kalli nanny bee din don jin abunda tace, nan take ranshi y abaci ya hade rai ‘’ba nace adaina yi mata wani special treatment breakfast ba? Idan tana buqata ta dunga futowa tana dafama kanta, ko kuma ta sauko taci wanda kowa yaci’’ Kallonshi mummy tayi jin abunda yace kafin ta sauke kanta kasa ba tare da tace komai ba, ‘’okay sir’’ nanny b ta amsa shi kafin ta juya Tsaidata tayi ta hanyar cewa ‘’nanny b, please a tado’’ ‘’okay sir’’ nannay b ta amsashi kafin ta nufi hanyar stairs, sai alokacin mummy ta kalleshi ‘’daddy wani abun ya faru ne jiya?’’ Bai kalleta bay a bata amsa ‘’bari yar taki ta sauko saiki tambayeta’’ Mummy najin hakan ta tabbatar da wani abun ya faru jiya, sanin halinshi yasa bata sake cewa komai ba saima zuba hada tea data soma yi. Bangaren maya da kyar ta tashi, don babu yanda nany b batayi ba akan ta fito daga duvet dinnan taqi, wai barcin bai siheta ba saida taji cewa daddy yace a kirata tayi saurin miqewa ta sauko daga ita said an short da bra, toilet ta wuce while nanny b ta futa daga dakin. Brush da wanka maya tayi sharp sharp kafin ta fito, closet dinta ta bude ta fara duban abunda zata saka, tashin farko ta watsar da komai dake cikin drawer daga duban rigar sakawa, duk cikin kayan zaman gida dake cikin drawer are revealing, don bata son kaya masu nauyi kwat kwata shiyasa take kwaso su idan sunje shopping da mummy, wat riga maid an siririn hannu ta dauka ta zura, rigar rubber ce so saita kama ta sosai amma kuma tayi mata kyau don itama akwai kyau masha allah, ita kyanta ya futa daban don kamar ruwa biyu ce, ta dauko mummy ta wani bangaren kuma ta dauko daddy ta wani shashen, batada hanci dai kamar iyayen nata. Gashin kanta datayima mini twist fixing yanda baza a ganeba ta nannade tayi bun kafin ta feshe jikinta da turaruka kamar zatayi ruwan turare. A chan parlor kuwa har sunyi nisa wajen yin breakfast, takun tafiyarta da kamshinta da yayi masu sallama yasa suka dago gaba dayanshu daga daddy har mummy, kallo daya yayi mata ya kauda kanshi, ita kuwa tana ganin mummy aguje ta karaso dining din ta rungumeta ‘’mummyyyyyyyy’’ ‘’sakeni karki ballani, bakisan kin zama katuwan baby ba’’ mummy ta fada tana dan buge hannunta data nado a wuyanta. Dariya maya tayi kafin tace ‘’nayi missing dinky mummy’’ ‘’missed you more baby, zauna kiyi breakfast’’ Daddy dai yana jinsu baice masu qala ba saima shan tea da yakeyi. Tanan gefenshi maya ta zagayo don nan ne mazauninta don koda yaushe a tsakiya suke sakashi idan zasuci abunci. Zama tayi anatse kafin ta dan kalli gefenshi ‘’good morning daddy’’ Saida ya karasa shan tea din dake bakinsa kafin ya amsata a gajerance ‘’morning’’ Cikin natsuwa suke Karin kumallo, babu sautin dake tashi sai na spoons da plate, daddy ne ya fara gamawa, miqewa yayi ya kalli bangaren maya ‘’this should be the last time da zaki dunga yawo babu hula akanki da irin wannan kayan a cikin gida sannan wannan hair style din ki chanza shi, ki nema decent kitso kiyi,’’ Yana kaiwa nan ya wuce sama ba tare da ya sake kallonsu ba, mummy dai mamaki y agama cikata don this is the first time yayi Magana akan shigarta da saka hula, don kwata kwata maya bata son saka hula akanta, sannan kaya shima yasan bata son masu nauyi. Bangaren maya kujwa tunda ya fara Magana har yakai aya bata dago idanunta ba, sai aynxu ta tabbatar ranshi y abaci sosai da abunda tayi jiya saidai batayi tunanin abun zaikai ga haka ba. Yana wucewa mummy ta kalleta fuskanta adan hade ‘’maya!!, me ya faru jiya? Kinyi wani laifin ne kuma? ‘’ Hawaye ne ya soma zubo mata tana kallon mummyn nata ‘’mummy wallahi ba wani abu nayi ba, wai saboda na dawo late jiya shine daddy ya kwace min komai nawa harda phone na’’ ‘’kinyi laifin Kenan?haba maya ko gajiya bakyayi?, did’nt I warn you akan Maganar dawowa daga school?, me kika tsaya yi har kika dawo late?’’ ‘’nidai mummy dan allah ki bashi hakuri ya bani wayana da laptop dina, ni motar daya bani ma ya rike na hakura kawai ya bani wayada da ipads dina’’ Kwafa mummy tayi kafin tace ‘’babu ruwana kedashi tunda bkyaji’’ ‘’mummy please, ke kadai ce hope dina dan allah karki ce haka, wallahi mun kusa fara exams kuma dole zan buqaci gadget dina please’’ ‘’naji’’ mummy ta amsata a gatse. Shuru maya tayi tana rausaya kanta dukdan mummy taji tausayinta, wanda hakan ke tasiri, da zarar ta zubda kwalla shikenan, don mummy tana bala’in sonta sosai don ita kadai ce allah ya mallaka masu, tun bayan haihuwar allah bai sake basu haihuwa ba shiyasa mummy ta dauro son duniya ta maka mata dukda tana sa ido akanta saidai ita tana da soft point akan maya wasu abubuwan bata hanata saboda son da take mata, daddy ne dai baya tolerating kwata kwata don baya son ta kangare ko ta dauki aladun da rayuwar yayan nan kasar. Saman mummy ta bishi bayan ta gama breakfast, bata tsaya ko’ina ba sai master bedroom dinshi, da sallama ta shiga bedroom din,kamshinsa ne yayi mata sallama hade da sanyin ac, dakin nashi ya hadu sosai, har book shelve ne a cikin daki. Ganin baya nan yasa ta wuce hanyar bathroom, alamun saukan ruwa ya tabbatar mata yana wanka. Kai tsaye ta shige bathroom ta rufo kofar, after like an hour sai gasu sun fito atare, fuskansu dauke da murmurshi, yana biye da ita a baya. ‘’wife bakya tsufa’’ Rufe fusknta tayi da tafin hannunta ‘’jarumina Kenan, allah yabarmin kai majeed din bahijja’’ Bata karasa Magana bay a janyo ta jikinshi gam ya soma aika mata wasu sabbin saqonni masu rikitarwa, nan take itama ta soma bashi wuta don itama babu dama, duk duniya majeed bayajin zai taba samun mace kamar badiyya, badiyya ta jiyaer dashi dadin da baya sha’awa a waje kwata kwata, ita din dai, musamman a bangaren auratayya tsakanin miji da mata, allah yayi mata wata baiwa da kyautar da shi kadai yasan irin yanda yake ji a tattare da ita shiyasa yake masifar sonta kamar ranshi. Sun dauka kusan awa biyu kafin komai ya lafa lokacin har sun sake wani wankan. Anan bedroom dinshi ta sauya kaya don daman akwai few kayanta anan incase. Mummy ce da kanta ta taya shi saka kaya ta feshe shi da turarensa na tom ford. ‘’hubby please ayima maya afuwa, ta fada min abunda ya faru jiya, dan allah kayi hakuri majeed dina bazata sake ba I promise’’ Zuba mata idanu yayi yana kallonta tare da karantarta, shi zai iya cewa kamarma tana nuna ta fishi son maya ne, baice komai ba kawai ya kauda kanshi gefe, ganin haka yasa jikin mummy yayi sanyi. Da mamaki taji hannunshi cikin nata ‘’wife duk abunda kikaga inayi akan maya I’m trying to do what is best for her, ki tuna fa mu baqi ne anan mu ba turawa bane, maya is trying to collide with character din turawa da abubuwan dasuke normalizing wanda kinsan haramun ne, bana son ta kangare, I want what is best for our only child, yanda kike qaunarta haka nake sonta sosai, im being strict towards her saboda idan muka zaman soft gaba dayanmu zamuzo muna regretting upbringing dinta, so please allow me to displine her don tasan cewa tayi ba daidai ba okay?’’ Jikin mummy ne yayi sanyi dajin maganar tasa don tabbas yayi gaskia ita kanta bazata so maya ta lalace ba, don haka tayi saurin girgiza mashi kai alamun gamsuwa ‘’thank you dady, kayi gaskia allah ya shirya mana’’ ‘’ameen wifey’’ matsota yayi cikin kulawa ya sumbaci kumatunta. ** MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍) ❤️🔥Romantic love story❤️🔥 Written by QueenMarh Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai… Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya. The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃 Enjoy!!!!! Free page Chapter 5-6 3 months ago (wata uku da suka wuce) FCT Nigeria………. Dutsen habuja wani gari ne dake a baya bayan garin abuja, yawancin mazauna garin basuda arzikin zama cikin ainihin garin Abuja,sai ya kasance masu zama a cikin garin zaman rufin asiri sukeyi saboda rayuwar Abuja sai mai arziki. Acikin garin akwai anguwar datafi fuce a cikin garin wadda ake kira da kayefi, anguwace me qunshe da tarin jama’a don anguwar a cunkeshe take da mutane, both chiristians da musulmai harma da waenda basuda addini,a bangaren culture kuwa babu wanda babu a aguwar, gwari, yarbawa, igbo, igala duka,haka zalika ginin aguwannin cikin layin kwata kwata basuda kan gado don yawanci gidaje ne na haya barkate don ko hanyar da mota zata kutsa cikin layin babu. Yawan mutanen anguwan yasa aka samu qarancin tsafta a anguwar saboda yanda mutane ke sana’a daban daban acikin anguwar don su rufa ma kansu asiri su samu na cin yau da gobe. Da sallama wata dattijuwar mata ta shigo daya daga cikin gidajen haya a anguwar kayefi anan bayan garin Abujan,dan karamin gida ne daga waje mai kofar karfe, labulen zauren gidan ta dage inda ta sanya kafarta cikin tsakar gidan, hayaniyar da akeyi daga ciki ne ta karade tsakar gidan inda wasu mata da mazan gidan ke hada hadan su kowanne yana abunda ya shafe sa. Wato daga cikin gidan dakuna ne kusan guda biyar a jere, sai dan tsukeken tsakargidan da bandaki sai wata yar rumfa da alamu anan sukeyin girki. Ragowar Goron dake hannunta ta wulla cikin bakin ta kafin ta rike sandar dake taimakonta wajen tafiya don tana da kiba sosai gashi girma yazo don kamarma dan dingisawa takeyi, sanye dattijuwar take da atamfa riga da zani sai wani mayafi kore kore. Tana karasowa tsakar gidan ta soma tari saboda hayaqin daya bade tsakargida inda yake fitowa daga rumfar girkin su. Matan dake zaune a tsakar gidan sunsha daurin kirji sai faman zazzaga masifa suke tsakanin,daman sun saba, don dawuya ayi wuni guda ba tare da anyi fadan nan ba kamar kaji. Mazajensu kuwa suna kallonsu ko qala bazasu ce masu ba, mazauna gidan maqotansu kuwa babu wanda yake shiga irin wannan fadan saboda daga hakan yake jawo babbar matsala. Takalman kafafunta ta soma zarewa ta ture su gefe guda hannunta rike da leda, ta soma takowa daidai hanyar rumfar girki kafin ta dan leka tare da daga murya tace ‘’keeee sabeeha?? wannan hayakin fah? Babbake gidan zakiyi ne?’’ Yarinyar dake tsugunne a bakin wata runfa daga chan tsakar gida sai faman rura wuta take kamar ranta zai fita don iccen kwata kwata bashida cii saboda yanayin garin yau ayi rana gobe ayi ruwa, takai kusan awa guda a tsugunne tana faman abu daya, gashi rana ta fito kwal sosai don rufin langa langa ne wanda hakan yasa zafin ya hadar mata biyu ga zafin rana gana wuta don kusan kowa ya daura tukunyar girkin rana. Jin sautin muryar kakarta yasa ta saurin juyowa ta mike tsaye don nufin hanyar fucewa daga rumfar,gyaran mataccen hijab din jikinta ta soma yi don yayi mata yawa sosai gashi ya kode,ta wajen wuyan hijab din ta tattaro shi ya rufe rabin fuskarta, babu abunda ake iya hangowa sai hazel eyes dinta da sukayi jaa masu daukar hankali da ido, gashin idanunta sunyi wara wara saboda hawayen dake zubo mata saboda hayakin data shaqa, wajen brows dinta kuwa a cike yake da gashi har yana neman hadewa baqi wuluk dashi. Saida ta fito sarari sosai na kalleta dakyau, daga ganinta tana da dan haske saidai wahala data kodar da ita, bata da wani tsayi sosai saidai baza ace da ita gajeruwa ba, kana ganinta kaga yarinya danya shataf don bazata wuce shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba, hijab din jikinta yasa na kasa gane yanayin jikinta saidai bata da wani qiba, kafarta sanye da baqin silifas daya soma cinyewa. Tari ta soma yi tana mutsiqa idanunta da sukayi jaa kafin cikin ladabi ta soma Magana tana mai kokarin karbar ledar hannun inna ‘’sannu da dawowa inna’’ Kallon fuskanta inna tayi idanunta yayi jaa sosai gashi sai kaurin hayaki takeyi ga uban zufa data tsatsafo mata. Adan fada fada inna ta soma Magana ‘’wannan hayaqin fa? Ni mai larurar idanu ay sai ki karashe min ganin nawa ‘’ Inna ta karashe tana mata wani irin kallo, shuru yarinyar data kira da sabeeha tayi tana mai sauraronta saida takai aya tukunna kafin ta soma Magana cikin ladabi. ‘’inna iccen ne ba…ya ci’’. ‘’ke har yanxu hada icce ya zame maki wani jan aiki,ina uwar taki’’ Kanta ta sauke kasa tana mai duban jar kasan dake tsakar gidan don ko sumunti ba ayi ba ,’’bata dawo ba ’’ ta bata amsa Saurin runtse idanu inna tayi don yana yanar da idanun nata keyi cikin yan kwanakin nan yasa ganin ta ke neman daukewa dukda bata bari kowa yasan da yanayin da take ciki ba. ‘kin gama dahuwar kwan?’’ ta sake wullo mata tambaya ‘’eh na gama tun daxu, abunci rana ne nake kokarin daurawa’’ ta bata amsa a natse. ‘’zoki bani ruwa mai sanyi in kashe kishirwar dana kwaso,’’ Tana kaiwa nan ta nufi hanyar dazai sadata da dakin su, kofar dakinsu na daga chan saqo, daga gefe kuma wani daki ne karami. ‘’inna ka dawo’’ wata matar gwari dake kokarin daurama yarta robar dafaffiyar masara ta sayarwa ta soma Magana. Kallon inda take inna tayi kafin ta washe baki don ita kadaice suke mutunci a gidan dan sauran kwata kwata basuda mutunci ‘’maman chidi na dawo, ina chidin yake’’ ‘’shege yaro ya tafi yawo’’ matar ta bata amsa ‘’yara daman ba’a rabasu da yawo, miqon masarar hamsin’’ ta karashe tana wucewa ‘’toh,’’ Karbar masarar sabeeha tayi kafin ta bi bayan innar har suka zo daidai kan damali kofar dakinsu inda suke yawan zama musamman idan ana kwalla rana saboda wajen akwai dan damshi damshi, tabarmar dake ajiye a wajen sabeeha ta warware ta shimfida kafin ta nufi uwar dakin su, labulen dakin ta daga tare da saka kai ciki, dakin bashida wani girma da alamu ciki da parlor ne don naga harda yan kujeru guda biyu sai ledar daki saidan fridge, daga gefe kuma wata yar yaloluwar katifa ce, ko’ina fess fess babu qazanta sai kamshin turaren tsinke dake tashi. Direct inda dan mataccen fridge dinsu yake ta nufa ta bude kafin ta zaro pure water guda daya mai dan sanyi. Tana fitowa a zaune ta tadda inna yanda ta barta tana bude ledar data shugo dashi, yar shinkafa ce ta auno masu ta awo kwano daya sai taliya itama wadda ta auno saidan manja da maggi da kuka. Anatse sabehaa ta tako inda inna ke zaune kafin ta zauna gefenta cikin ladabi tace ‘’inna ga..shi’’ Kurama fuskar ta ido tayi data danyi duhu, baka ganin komai sai kwayar idanunta sai dan karan hancinta,saboda yanda ta janyo wuyan hijab din daidai wajen bakinta. Ruwan hannun nata inna ta karba tana mai yin wani tunani da yake bata mamaki tun da sabeeha ta soma tasowa. Saida ta shanye ruwan tass kafin ta kalleta tace ‘’jeki karasa abuncin kizo ki tafi, karta dawo ta fara zazzaga masifar fitar ki data saba, ni na kasa gane wannan wani irin abu ne, yoh idan baki futa ba kema kin nemo mana abunda zamu rufama kanmu asiri ya zamuyi?, wallahi bazai yuwu ba kuwa, mun gajii nema don haka kema saikin nema na kanki wallahi,zaman banza bazai yuwu ba, ni yanxu da futa ke neman yimin wahala ga ciwon kafa’’ Cikin sanyi tace ‘’toh’’ Mikewa tayi ta wuce hanyar rumfar girki, maficin data ajiye a gefe ta dauka ta soma rura wutar, saida ta dauka kusan minti goma ta samu wutar ta kama da kyar, hamadala tayi kafin ta mike da robar shinkafar data tsince tsakuwar ciki ta juye cikin tukunyar. Bakin rigiyar dake hanyar bandaki ta nufa ta janyo ruwa a buta ta wuce bandaki, dakyar ta karasa cikin bandaki kamar zatayi kuka saboda dattin daya yi, kuma da safe saida ta wanke shi tass kafin mamanta ta futa don duk safiya saita wanke mata idan tazo shiga,sha’anin gidan haya dai sai a hankali, shiyasa yawanci bata shiga bandakin cikin gidan, idan ma zata shiga sai bayan mamanta ta futo nan ne take samun damar yin wanka idan bata samu shiga a wannan lokacin ba haka zata hakura saita futa. Ruwan butar data debo ta tutule ta dauraye inda zatayi amfani dashi kafin ta futo. A gurguje ta gama dafa dafadukar shinkafa, ta juye cikin kular su dukda dahuwar bataji kayan kamshi ba da nama hakan baisa kamshin abuncin yaqi fitowa ba. Dakinsu ta nufa da kular lokaci inna ta wuce ciki, ganin bata parlor yasa ta ajiye inda take ajiyewa koda yaushe. Cikin uwar dakin ta shiga da sallama, a kwance ta tadda inna kan gadon karfensu sai kwasar munshari take, gefenta masarar data gama ci ne ta yasar anan kan gado. Kauda kanta tayi ta wuce wajen da akwantin kayanta ke ajiye gefen sip, budeshi tayi ta zaro wani hijabi wanda shima yadan soma kodewa, tana zarowa ta rufe akwatin ta fito daga cikin dakin zuwa parlor. Hijab din jikinta ta soma zarewa daidai nan aka daga labulen dakin nasu, cikin sauri ta sauke hijab din ba tare da ta cire shi ba. Kamar an wulloshi haka ya shugo cikin dakin, kallo daya tayi mashi yana sanye da riga yar shara sai wani wandon jeans daya dan yage daga kasan wandon, idanun nan nashi jajawur kamar gauta,dauke idanunta tayi da sauri daga kanshi kafin tace‘’sannu da dawowa kawu’’ cikin ladabi Baima tsaya amsata ba yace ‘’an gama abinci?’’ ‘’eh an gama’’ ta bashi amsa ‘’zubo min’’ ya karashe yana wucewa wajen kujerar parlor, Abuncin ta zuba mashi kafin ta ajiye mashi a gabanshi sannan ta dauko pure water ta ajiye mashi. tana gamawa ta janyo robar kwan da take futa sayarwa kafin ta fuce daga dakin, saka hijab din da batayi ba Kenan. Silifas dinta ta zura ta fuce daga gidan nasu dayayi gaja gaja, haka ta dunga kutsa layikan anguwan kafin ta fito hanyar titi, har lokacin bata cire hijab dinnan daga fuskanta ba. Saida tazo dadai bakin titi inda suke tsayawa kafin ta dan tsagaita, yara ne da yawa harda waenda basu kaita shekaru ba kowannen su da abunda yake saidawa, masu saida muruci, masara gyada, ayaba da sauransu. Da ansamu traffic haka zasu wuce wajen motocin nan suna tallata abubuwan da suke saidawa, daman titin yawanci matafiya ne suke wucewa,haka ta dunga bada himma itama wajen saida kwan zabo har saida takai wajen karfe biyu da rabi kafin ta wuce tsallake wajen wani gidan mai inda anan ne take samu ta shiga bandakin wajen don yana da tsafta sosai kuma akwai fanfo da bokiti, wani sa’in ma anan take yin wanka idan bata samu tayi daga gida ba. Bangaren mata ta nufa ta wuce bandakin ta dauro alwala kafin ta fito anatse da hijab din nata. Masallacin kusa da bandakin ta wuce, da sallama ta shiga wajen,kamar koda yaushe yana nan fess fess don ana kula da wajen sosai. Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke saboda wani irin ni’ima zataji ya sauko mata, tana samun natsuwa da zarar ta zo cikin masallacin nan. Babu mutane ko daya a cikin masallacin don haka ta nufi wani sako ta tada kabbarar sallah, ta dade sosai wajen sujud tana pouring abubuwan dake cikin ranta, kafin ta salleme. Tana idarwa ta jingina da bango ta lumshe idanunta, tunanin rayuwarta shekara hudu da suka wuce ta fara, a lokacin idan da za ace mata rayuwar ta zata juya haka zata musa dukda bata samu rayuwar yanci ba, sallamar dataji ne yasa ta amsa ba tare da ta bude idanunta. Ta dauka kusan minti goma a haka kafin ta bude lumshenshun idanunta ta mike, daidai nan matar datayi mata sallama daxu ta fice daga masallacin, bayanta tabi da kallo kafin ta nufi hanyar futa itama, daidai nan idanunta ya sauka akan purse, kamar bazata dauka ba chan kuma wani tunani yazo mata tunawa da lokacin da ta shigo ita kadaice sai matar data futa yanxu. Cikin sauri ta dauki purse din ta fuce daga cikin masallacin tare da daukan bucket dinta data ajiye a bakin kofar masallaci. A gaggauce ta zura silifas dinta tabi bayan matar har tazo daidai wajen da matafiya suke parking motocinsu, ware idanu ta soma yi tana fatan ganin matar, cikin ikon allah kuwa ta hango ta don wani gold peachy mayafi ta saka kuma shi ta gani a jikinta dazu da zata futa daga masallacin. Ganin matar na shirin shiga zabgegeiyar motar ta yasa tayi saurin hanzarta karasawa wajen motar har tana haki. ‘’assalamu alaikum hajiya hajiya dan…tsa..ya’’ Chak matar ta tsaya kafin ta juyo, masha allah, matar fara ce tass ta dan manyata sosai, daga ganinta kasan hajiya ce babba mai ji da nera,kallonta matar tayi kafin ta ajiye wayar dake maqale a kunnenta. Kallonta sabeeha ta tsaya yi kirjinta na bugawa kafin tace ‘’hajiya kinyi mantuwar jakarki’’ Ta karashe tana miqa mata purse din nata, cikin sauri matar ta kalleta kafin ta kalli purse din, da mamaki matar ta sake ta kallon yarinyar ‘’subhanallahi a ina na yarda purse din?’’ ‘’ah masallaci ne kika barta’’ sabeeha ta amsata Murmushi matar tayi kafin ta amshi purse din ta bude, zunzurutun dollars din dake ciki suna nan intact harda identifications card dinta da atms dinta duk suna nan, mamaki ne ya lulube matar don babu wanda zaiyi irin wannan tsuntuwar ya maidota. ‘’kai amma nagode sosai kinji yarinya’’ ‘’ba damuwa hajiya’’ ta karashe tare da juyawa ‘’tsaya’’ matar tsaidata, kafin ta bude bayan motarta, handbag dinta ta bude ta kwaso wasu kudade da bata ma san ko nawa bane kafin ta rufe motar ta fuskanci yarinyar Kallon kudin da matar ke miqa mata tayi kafin ta dago da fuskanta ta kalleta ‘’karba wannan, nagode sosai kinji ko,’’ ‘’ah ah hajiya basai kin ba..ni ko..mai ba’’ Matar Bata jira amsanta ba kamo hannunta ta danqa mata kudin kafin ta juya tana mamaki sosai, ashe akwai honest mutane wannan generation din, kuma yar talla ma abun mamaki. Da mamaki sabeeha ta dago ta kalli matar tare da hannunta, kudi ne masu yawa don akalla zasu kai dubu goma, tana kokarin yin Magana matar ta tada motarta ta fuce daga gidan man. Kallon kudin sabeeha tayi kafin ta dauka bokitin ta ta fuce daga cikin gidan man, saida ta tsallaka titi kafin ta dan tsagaita, kudin cinikin datayi na kwai ta fara irgawa, dubu uku ne daman, qullesu tayi ta saka cikin robar, kafin ta maida dubanta ga kudin da matar nan ta bata shima irgawa ta farayi tana tunanin me zatace a gida, chak ta tsaya da irgen ganin wani dan passport photograph, kyakyawar fuskar matar nan taci karo dashi, da mamaki take kallon passport din ‘’wayyo, yanxu haka batasan ta hado dashi ba’’ sabeeha ta fada kafin ta ciro passport din sannan ta nannade kudin. Hanyar gida ta nufa cikin sauri saboda yau tayi yamma sosai, daman tsoronta kar mamanta ta dawo shiyasa kullum inna ke nanata mata akan ta dawo da wuri gashi yau takai har wajen uku da rabi. Hankali atashe ta shigo layin nasu har ta karaso gidan, da sallama ta dage labulen zauren gidan, daidai nan aka watso kaya waje, kallon kayan tayi kafin ta maida dubanta ga wanda ke watso kayan. ‘’get out ungrateful woman’’ wani mutumi ya fada ‘’papa kemi, why are you doing this to me, wallahi bazanje ko’ina ba, bazan tafi nabar yaya na ba saboda ka kawo yan iskan matanka’’ Tass bayaraben ya wanke ta da mari, dafe kuncinta matar tayi kafin itama ta dago ta wankeshi ji kake tass, Karshe dai dambe suka fara babu kunyar ganin idanun mutane da yayansu haka suka dunga jibgar juna, mutanen cikin gidan kuwa babu wanda yace dasu qala, sabeeha dai kauda kanta tayi gefe hankali a tashe don lokacin data shugo har an fara kiraye kirayen sallar la’asar wanda hakan ke tabbatar mata da mamanta ta dawo. Fadin irin tashi hankalin dake kwance cikin idanunta bata lokaci ne don kamar har jikinta rawa rawa ya fara. Tsallake kayan tayi ta nufi hanyar dakinsu, silipas din kafafunta ta cire kafin tayi sallama a natse. Labulen dakin ta daga tare da shigewa ciki, gabanta ne ya bada dam ganin maman ta a zaune gefenta kuma kawarta ce kuma aminiyarta. Kamar munafuka haka ta shugo tsakiyan dakin kafin ta tsugunna, ‘’barka da hutawa ina wuni mama’’ Daya daga cikin su ce ta kalleta babu yabo ba fallasa tace ‘’yauwa’’ Dayar kuwa ko kallon inda take batayi ba, saima maida hankalinta datayi wajen rubutun da takeyi a cikin memo, ganin haka yasa sabeeha wucewa uwar dakinsu, a zaune ta tadda inna tana ta faman qulle qullenta data saba. Sallamar da sabeeha tayi yasa ta saurin dagowa ta kalleta, ‘’ke kuma sai yanxu kikaga damar dawowa?, me kika tsaya yi?’’ Karasowa tayi kusa da innar ta ajiye bokitin kwan a gabanta kafin ta fiddo kudin dake ciki tace ‘’yau banyi ciniki ne da wuri ba ne shiyasa’’ ‘’ay ga uwarki nan zaki mata bayani ne bani ba, miqon kudin, yau nawa kika samu?’’ ‘’duka na sayar’’ sabeeha ta bata amsa. Washe baki inna tayi tana karbar kudaden kafin tace ‘’jeki dauki ragowar abunci kici’’,…da toh ta amsata kafin ta mike ta dauki kular, budewa tayi kamar yanda tayi expecting daman ba wani da yawa zata samu ba don haka ta hakura ta zauna kawai ta soma turawa, allah ya taimaka bata fiye cin abunci sosai ba dama dai ruwan lipton ne, bata gajiya dashi, saita sha ruwan lipton kusan sau goma arana indai zata samu ba zata damu da abunci ba. A parlor kuwa sai bayan wucewar ta ciki suka cigaba da Magana, ‘’yanxu ke hadiza barin yarinyar nan kikayi tana futa? Ko tsoro bakyaji?’’ ta karashe tana mai kallon wadda ta kira da hadiza ‘’jamila ya kikeso nayi toh?, nayi duk yanda zanyi akan inna ta daina bata tallan kwan nan taqi,jiyama da haushi na ta kwana, wai dole ta fita nema itama’’ ‘’hmm bakya hango risk din dake cikin barinta ta fita ne shiyasa baki tsaya tsayin daka ba, amma idan ta tsohuwar nan ne ko cikin dan kudin kayan da kike sayarwa ay zaki iya fidda yar dubu ki dinga bata duk sati kina toshe mata baki’’ Nunfasawa hadizar tayi kafin tace ‘’wallahi bazata karbi dari biyar ba, kinsan cinikin nawa takeyi idan ta daura mata kwan nan kullum?’’ ‘’nidai wallahi shawara nake baki, karkiga wai yanxu an shafe shekaru wallahi karamin kuskure zakiyi komai zai dawo kanki musamman idan dangin uban…’’ Saurin katseta hadizar tayi ta ta hanyar cewa ‘’dan allah Jamila kibar zancen nan,kinsan yanda na tsani maganar na,ni yanxu zan samu dubu goman?’’ Jamila ce ta kalli aminiyar tata kafin tace’’ gaskiya yanxu bazaki samu ba saidai nanda karshen wata idan anyi albashi,’’ Shuru hadizar tayi tana wani tunani kafin tace ‘’wallahi Jamila ina buqatar kudin nan da gaggawa, matar nan bata da kirki indai ba kai mata nayi ba bazata bani sarin kayan nan ba, gashi mun shiga karshen shekara, yanxu zakiji mutumin nan ya fara doka sallama daki daki, ’’ ‘’toh gaskia saidai kisan yanda zakiyi don wallahi nidai banida dubu goma yanxu, kema wallahi kinyi rashin tunani da kika sayar da gidanki, yan kudaden da kika dawo dasu da business kika fara dakin rufama kanki asiri, haka kikazo kika dunga kashesu kamar babu gobe, samun muhalli nakai a wannan lokaci ay ba karamin rufun asiri bane yanxu gashi wata nayi duk sai kibi ki rikice akan dubu hamsin a wannan tsinannan gidan,’’. ‘’hmm Jamila kinfa san dalilin sayar da gidan da nayi, shikennan zan hkura har zuwa lokacin, inkin karba albashi saiki bani’’ hadiza ta bata amsa Daga nan wata hirar suka shiga sai wajen yamma liss jamila tayi masu sallama. Sabeeha dai bata fito ba tana nan zaune a dakin nasu kusa da inna don tsoron haduwa take da maman nata. Tunawa da wanke wanken dake jiranta yasa ta miqe jiki a mace ta tattara na cikin dakin kafin ta fuce, anan parlor ta tadda maman nata, fuskan nan nata a hade, kallo daya tayi ma sabeeha ta watsa mata wani kallo dayasa ta dauke idanunta cikin gaggawa kafin ta sunkuyar da kan nata. ‘’zo nan’’ Takowa sabeeha tayi ta karaso kafin ta durkusa gefe ‘’dan ubanki me kika tsaya yi kika dade? Shuru sabeeha tayi jikinta na kyarma don duk a tunanin yau dukanta zatayi saboda yanda ta hade fuskarta sosai, ‘’ki amsa ni nace dan ubanki, me kika tsaya yi har kika kai wannan lokacin?’’ Bakinta da kyarma dan tsoro ta soma Magana, ‘’wallahi ban tsaya komai ba, sallah kawai na tsaya nayi bayan na sayar da kwan, shi..ne shi..ne’’ Sanin tana kakarewa wani sa’in cikin Magana musamman idan a tsorace take yasa hadiza saurin cewa ‘’shine mai?’’ ‘’wata mata ce ta yarda Jakarta shine na tsinta na bata, dalilin daya tsayar dani kenan’’ ta kaarshe tana sheshekar kuka kasa kasa ‘’matso nan’’ hadiza ta umarceta babu alamun wasa a tattare da ita Rarrafawa tayi ta karaso dab da maman nata, tana kaarsowa ta damko gaban hijab dinta kamar zata shake mata wuya tace ‘’wallahi idan baki fada min abunda ya tsayar dake ba sainaci ubanki, ba karfe biyu kike dawowa ba meya tsaidake har akayi la’asar? Idan kikamin karya wallahi ranki sai yayi mumunan baci,wurin wa kika tsaya?’’ ‘’na rantse da allah mama ban tsaya ko’ina ba, wallahi gaskia na fada maki, inbanda matar nan wallahi ban hadu da kowa ba, kingama har kudi ta bani’’ Sakinta hadiza tayi ganin tana kokarin zaro kudade, wani irin kallo ta jefe ta dashi bayan ta kalli kudin da take miqo mata hannunta har karkarwa yake saboda tashin hankali ‘’uban waye ya baki wannan? Dama ke yar iska ce ban sani ba yaushe kika fara iskanci?’’ Saurin runtse idanu sabeeha tayi daman tasan haka zata kasan ce don tsoron hakan ne yasa ta boye kudin, ‘’idan baki daina kukan munafurcin nan ba saina kashe ki anan wallahi, daman iskanci kika fara ban sani ba? Ke ko iskanci kike yi saiki bari na sani eh?’’ ‘’wallahi mama bana iskanci, kinga hoton matar ma, acikin kudin na tsinta’’ Ta kaarshe tana miqa mata passport photograpy din, karba maman tayi kafin ta kurama picture din idanu, saida ta dauka kusan minti biyu babu ko kiftawa tana kallon hoton, nan take idanunta yayi jaa sosai ta maida kallonta ga sabeeha wani sabon tashin hankali ya wanzu a fuskarta ‘’ina kika samu wannan?’’ ‘’a cikin kudin da matar ta bani naga hoton,’’ ta amsata da gagagwa ‘’dama chan kinsanta ne?’’ ‘’wallahi ban santa ba, a masallaci ta yarda purse dinta shine na dauka na bata, shine tayi min godiya ta bani kudi’’ ‘’Ba nace karki sake kiyi mu’amala da mutane ba?uban waye yace maki idan aka yarda abu ana tsinta a baiwa mai shi,ko na taba ce maki idan kin dauki abu ki maidawa maishi inama ruwanki da abun wani? ‘’ ta karashe tana daka mata uban tsawa dayasata qamewa kyam, tana masifar tsoron mama kamar ranta. Zufar dake keto mata ta sharce kafin ta sake jero mata tambayoyi ‘’a haka kika futa yau?, me matar tace maki?’’ ‘’eh haka naje, godiya kawai tayi min’’ ta amsata ‘’tashi kije’’ Sabeeha najin haka ta mike tsaye ta tattare kwanukan parlor wanda kawu yaci da wanda maman taci duka ta fita dasu. Tana fita kuwa hadiza ta miqe tsaya, babu abunda ke kwance a fuskanta sai furgici da tashi hankali, hannunta har karkarwa yake saboda tsabar tashin hankali mara misali, hijab dinta dake gefe ta zura kafin ta fuce daga cikin parlor. Koda ta fito batabi takan mutanen tsakar gidan ba ta fuce daga gidan gaba daya kamar zata tashi sama. Hanyar gidan su Jamila ta nufa don yana dan nesa dasu, cikin mintuna qalilan ta karaso gidan, shima gidan haya ne saidai baikai nasu yawa ba don dakunan haya uku ne kawai a gidan. Ko sallama batayi ba ta wuce bangaren Jamila, kamar daga sama kuwa Jamila ta ganta hankali atashe ‘’hadiza lafiya inace yanxu nabar gidanku ko nayi mantuwa ne? Hannunta hadiza taja suka zauna akan kujera mai zaman mutun biyu kafin ta mika mata hoton da sabeeha ta bata. Kallon hoton Jamila tayi tana tunanin ko lafiya don bata dago komai ba kwata kwata, muryar hadiza ce ta katseta ‘’na shiga uku Jamila,duba kiga’’ ‘’wace wannan din’’ Jamila ta tambayeta Kallonta hadiza tayi kafin tace ‘’ki duba da kyau mana’’ ‘’kinga dan allah kimin bayani, wacece wannan din’’ Jamila ta karashe tana gyara zaman dan kwalin kanta ‘’bata maki kama da yan gidan su ba?’’ zaro idanu Jamila tayi cikin kidima tace ‘’toh fa, ina kika samu wannan to?’’ ta karashe tana kallon idanun Jamila, bata ma kaiga jin amsarta ba ta gane abunda take hasashe. Cikin kidima itama ta miqe tsaye, ‘’na shiga uku ni Jamila, kinga abunda nake fada maki ko?’’ Jan hannunta hadiza tayi ta zaunar da ita kafin tace ‘’dan allah Jamila ki bani shawara ya zanyi eh?’’ ‘’ay saida na fada maki hadiza, wallahi da kanki zaki jefamu cikin masifa, sau nawa na fada maki ki daina barin yarinyar nan tana futa, wallahi idan dagin ubanta suka…..’’ Saurin toshe mata baki hadiza tayi idanunta yayi jaa sosai lokaci guda kuma bacin rai ya dabaibaiye fuskarta ‘’dan allah karki mana bakin fata, ay wallahi bazan taba barin haka ba ko bayan raina wallahi har abada, a yanxu dai yata ce ni kadai nina haifeta kaf duniya babu wanda ya wuce ni, kuma babu wanda ya isa ya rabani da ita tunda duniya ta shaida hakan nina tsugunna na haifeta kuma na rantse da wanda ke busa min rai bazan taba sakin ta ba, wannan alwashi ne dana dauka’’ Ganin haka yasa Jamila sauya zancen tace ‘’toh yanxu ya zakiyi kennan’’ Nunfasawa hadiza tayi tana kumfar baki ‘’bani kiga saida safe’’ Ta karashe ta nufi hanyar futa daga dakin jamila bayan ta karbi passport din, ko amsa gaisuwar yayan Jamila da suka dawo daga islamiyya batayi ba ta fuce daga gidan. Koda ta fito nan take taji wani irin ciwon kai ya saukar mata, zuciyarta a cunkushe don nan take komai ya soma dawo mata, wannan baqin cikin, hatred dinnan da ta kwashe shekaru da dama tana dakonshi ya dawo mata fill a zuciyarta. Take bakar zuciyarta ta dawo kamar sabuwa, babu abunda jikinta keyi sai karkarwa don tana da zafin zuciya sosai daman yanxu ne ta danyi sanyi saboda girma dayazo mata. A wannan yanayi ta karaso gida lokacin har an soma kiraye kirayen sallar magrib, a tsakar gida bakin dakali ta tadda inna, ko kallon inda take batayi ba balle ta amsa tambayarta daga inda take. Uwar daki ta shige ta zauna bakin gado tare da zare hijab din jikinta da zufa ta wanke shi tass, ta shafe wajen awa guda tana saka da warwarewa a cikin zuciyarta har akayi sallar isha’I kafin ta samu ta mike dakyar ta dauro alwala. Sabeeha kuwa taga lokacin futarta da dawowarta don tana runfar girki ta daura masu abuncin dare tuwo da miyar kuka, mamakin maman nata take koda yaushe, baka taba iya contemplating mood dinta kwata kwata, yau she’s soft gobe kuma she’s opposite, maganganun da sukayi dazu ya tsaya mata arai sosai, ayau da ace iskanci take to fa babu wanda zai fara sani sai mamanta saboda ta santa ciki dabai, don ko kalar nunfashin da take futarwa mamanta ta sani ballatana kuma motsinta. Ko tsoronta dake kunshe a cikin ranta bazaisa tayi iskancin bama, don a duk duniyan nan babu wadda ta zagaye rayuwarta kamar mahaifiyarta, duk wani motsinta akan mahaifiyarta, shiyasa tun bayan dawowar su Nigeria bata kara futa ba da sunan zuwa makaranta ba, gashi ta haneta mu’amala da kowa don ko qawa bata dashi, bata ma san menene qawance ba saboda she has a very dark experience lokacin tasowarta saboda halittarta, kowa is just a stranger to her hatta maqotansu da suke zaune gida daya mamanta bata yarda tayi mu’amala dasu ba kwata kwata, daga inna sai mamanta sai kawu wato qanin mamanta Kenan, shiyasa take nan kamar mai rayuwar qunci mara freedom. Tun tasowarta da girmanta bata taba barinta ta zama socialize ba, bata taba barinta ta shiga cikin mutane ba, she hid her to the world gaba daya, tun bayan da ta fara zama budurwa, bata taba koda taka kofar gidan suba lokacin suna tsohon gidan su kafin yanayin yau da kullum yasa zaman nasu ya gagara a cikin gidan ….. A lokacin da suka koma gidan haya ko tsakar gidansu bata futa kwata kwata, bata isa tayi koda dogon nunfashi ba saboda how highly strict with movement dinta da maman ta take,duk wani motsinta saida izinin mahaifiyarta abun yakai hatta kalar nunfashin da zata futar da duk motsin da zatayi saida izinin mahaifiyartaa, shin wannan so ne ko kuwa wani abun ne daban? Haka take yawan tambayar kanta koda yaushe. Free page 7-8 MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍) ❤️🔥Romantic love story❤️🔥 Written by QueenMarh Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai… Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya. The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃 Enjoy!!!!! Matar Taj (destined with you🩵🤍) Free page Chapter 7-8 Washe gari da asuba ta tashi as’usual kamar kullum, a parlor ta kwana saboda kawu bai kwana a gidan ba, daman yawan ci asabar da lahadi ne kawai yake kwana a gidan, sauran kwanakin kuma achan tasha yake yi saboda sana’arshi ta tukin motar haya, kano to Abuja line. Saida ta fara yin sallar asuba kafin ta fara gyaran parlorn nasu inda ta tattara katifar, da dan qyallen zanin da take shimfidawa a kan katifar don katifar soso ne kawai ba bu komai a jikin katifar,sai kuma hijab din da take luluba dashi dayan kuma dashi take sallah. Ragowar kayan wanke wanken da sukaci abunci dashi ta kwashe ta fita dasu don wankewa. Gaba daya gidan basu tashi ba sai mazajensu dake futa aiki,wannan yasa take futowa tayi duk wasu ayyukanta da wurwuri kafin sauran matan gidan su fito, don ko dibar ruwan rijiyar gidan ma layi sukeyi. Zama tayi ta soma yin wanke wanke cikin natsuwa ga sanyi asuba dake busawa, sanye take da hijab din datayi sallah dashi, hijab dai koda yaushe bata rabo dashi, kuma yana nan yanda take sakawa ta rufe bakinta dashi. Saida ta gama wanke wanken tass ragowar omon kuma ta wanke dayan hijab dinta dashi don gaba daya guda biyun nan ne kawai take dashi kuma shi take sawa koda yaushe shiya duk suka kode saboda wanki dukda wanki ma wani san’in babu omo take yi saidai ta tsalma cikin ruwa ta dauraye shi. Tana gamawa ta shanya kan qauren langa langan da take shanya wajen, lokacin har matan sun soma futowa. Wanke toilet din ta fara yi kafin ta koma dakin nasu, da sallama ta shiga, inna nata sharbar barcinta, mama kuma na gefenta a zaune, da alamu bata dadw da tashi ba, zaman jirata daman takeyi don bata shiga toilet din saita wanke kafin tayi amfani dashi. Cikin ladabi da biyayya ta tsugunna, har kasa ta soma gaisheta ‘’ina kwana mama, an wanke bandaki’’ Kamar koda yaushe bata fiya amsa ta ba, saidai kawai tayi gyaran murya, yau dinma ko gyaran muryar batayi mata, ganin haka yasa ta sake maimaita abunda tace, sai a lokacin maman ta dago ta kalleta kafin tace ‘’naji’’ jikinta ne yayi sanyi don duk a tunaninta har yanxu fushi take da ita, fushinta kuwa ba karamin tashin hankali bane a wajenta. Sum sum ta fuce daga dakin don daura abunda zasu karya dashi, tuwon jiya ta dumama ta juye a kular, lokacin mama harta futo tay wanka ta koma ciki. Daga baya ma saiga inna ta futo itama,dakyar take tafiya saboda qibar da take dashi sosai, wani sa’in ma saboda qibarta cikin dare bata iya futa yin futsari saidai tayi a poo saboda tana da saurin sakin mara saboda ciwon sugar da take dashi. Dakin ta sake komawa da kulolin tuwon data dumama,tana shiga ta ajiye bayan sun gaisa da inna, kafin ta wuce parlor ta zauna taci nata wanda ta zuba ma kanta. Bayan yan mintuna qalilan ta koma daki ta kwashe kwanukan da suka gama ci kafin ta fuce dasu. Kallon inna hadiza tayi kafin ta danyi gyaran murya, ‘’inna daga yau sabeeha bzata kara futa tallan nan ba’’ Wani irin kallo inna tayi mata tana kokarin yin sakacen hakori kafin tace ‘’saboda me Kenan?’’ ‘’inna ni na haifi yarinyar nan kuma nike da iko da ita, bana son tallan nan saboda haka bazata kara futa yin wani tallah ba ko aike ma karki sake barin ta taje, nitun usuli na nuna maki bana so bansan meysa ki….’’ Saurin katseta inna tayi ‘’iko sai allah, yau ni hadiza kike cewa ke kika haifi yarki?shin idan taje tallan nan ba rufin asirin mu bane?, kuma idan taje tayo tallan nan ay duk rufin asirin mu ne tunda koba komai dai zamu samu nacin yau harda dumame, ke wai hadiza na kasa gane maki, wannan tsawalawan da kike yi akan yarinyar nan na menene ke a ganin ki wannan tarbiyya ce kike mata?’’ ‘’ni ba wannan maganar nake maki ba inna, inma don ribar da kike samu ne zan dunga baki dubu duk sati’’ Shuru kawai inna tayi bata sake ce mata komai ba, don talla kam saifa ta tura ta. Haka ta karashe shirinta ta fuce daga gidan zuwa gidan matar da take ma aikin abunci, matar babbar event planner ce a cikin garin abuja, sannan tana harkar abincin gidan buki da duk wasu events, da kyar hadiza ta samu matar ta dauketa aiki, inda take bata dubu talatin duk wata. Yau Friday, yawanci ayuukan ranar sunfi yawa saboda akwai orders din abunci da yawa. Karfe sha daya daidai kuwa inna ta sata dora dahuwar kwai, tana gamawa ta zuba a roba, saida inna ta kora mata kashedin dawowa karfe daya daya daidai kafin ta fuce, tunda ta fita gabanta ke faduwa babu dalili. Bata kai karfe dayan bama ta sayar da duka kwan kafin ta dawo gida, ba karamin dadi inna taji ba kuwa don haka ta daura damara don bata ga dalilin da zaisa ace wai baza a tura ta tallan ba yanda suke fama da talaucin nan, ita dai ba yar gwal bace da za ace ta futa nema ba. Saida yanma tayi likis hadiza ta dawo a gajiye, gajiyar data kwaso ma baisata ta tambayi inna ko ta bar sabeeha ta futa yau ba don tasan inna akwai taurin kai. Haka suka shafe sati guda, inda hadiza na futa inna zata daurama sabeeha kwan nan, kafin ta dawo, akwai ranar da sabeeha ta futa da kwan bakin titi kamar kullum, da mamaki Jamila wadda ke shirin tafiya wajen aikinta ta ganta, koda ta ganta ita sabeehan bata ganta ba. Jamila tayi mamakin ganinta sosai, don batayi tunanin hadiza zata barta ta sake futa ba. Saida ta dawo daga aiki ta wuce gidan hadizan ko uniform din jikinta bata tube ba,tana zuwa gidan ta samu hadiza a uwar daki, inna kuma tana tsakar gida tana hira da maman chidi, sabeeha kuwa tana bakin murhu ta daura sanwar dare. Da sallama Jamila ta shiga dakin, a zaune ta tadda hadiza, ganin ta tsaya a bakin kofa yasa hadiza cewa ‘’karaso mana jamila’’ Zama Jamila tayi tana fuskantar kafin ta soma Magana ‘’wai ni hadiza maisa yanxu kikayi sanyi ne sosai?’’ ‘’me kika gani yasa kikace haka?’’ Hadizar ta tambayeta tana kallonta da mamaki. ‘’hmm babu komai daxu sai naga sabeeha a bakin titi gaban wata katuwar mota ashe baki hana ta tallan ba allah dai ya kauda bacin rana’’ A razane hadiza ta kalleta, ‘’ban gane ba, wace sabeehar ba’’ Wani irin kallo Jamila ta mata irin kinma raina ma kanki hankali. ‘’akwai wata sabeehan ne bayan wadda kika san nake magana a kanta,’’ ‘’innalillahi, wallahi Jamila saida na fada ma inna karta kara bata tallan kwan nan’’ Miqewa Jamila tayi tare da saba Jakarta a hannu ‘’shikenan ay, idan kare na yawo zabo ma na yawo wata rana sai sun hadu, yanxu ya kamata tun wuri kisan abunyi, shawara dai dayace na baki, akaro na biyu ni kinga tafiya ta’’, Tana kaiwa nan tayi fucewarta, tun bayan tafiyar Jamila kasa sukuni hadiza tayi, yanda kasan Jamila rura mata wutar tashin hankali tayi, haka kawai ta kasa nutsuwa, washe gari haka sukayi kacha kacha da inna kamar ba mahaifiyarta, itama sabeehar bata barta ba don saida ta daketa sosai kamar zatayi mata illa, duk dan bata fada mata kan cewa inna ta cigaba da daura mata talla ba, ita kuwa baiwar allah bata ma san ta hana inna daura mata tallan ba. Ranar dai sabeeha taga sauyi sosai tattare da uwar tata, sauyin da tun bayan dawowar su rabon data ganshi, nan take tsoronta ya sake ninkuwa akan na da, abubuwan da suka gabata shekarun baya suka soma dawo mata, don a lokacin ne hadiza ke displine dinta acewarta don wahala dai tasha wahala both emotionally and physically wajen mahaifiyar tata tun kafin ta mallaki hankalinta, sai ayanxu asalin maman nata ya dawo, wato hadiza nada zafi sosai, bata da sauqi, she’s not soft at all, wata iriyar zuciya ce da ita, ta raini zuciyar ta tsahon shekaru da dama da hatred. Satin sabeeha daya a gida ba tare da taje tallan ba, inna ma dai bata sake bata tallan kwan ba saboda yanda hadizar ta dauko da zafi zafi sosai, bayan wannan ma yanxu innar tayi laushi sosai saboda yanayin rashin lafiyarta dake neman dawo wa. Akwai ranar da inna ta tashi da tsananin rashin lafiya, gaba daya jikinta ya sage, ranar daga sabeeha sai inna agidan, lokacin da abun ya tsananta sabeeha na tsakar gida tana wankin kayan maman nata, saida ta gama kafin ta daura musu abunci. Duk wannan hidimar data dunga yi bata shiga daki ba, saboda ayyuka da suka sha mata kai. Hadiza kuwa ranar taje aiki,don ranar juma’a ce kuma akwai ayyuka da yawa da zasuyi saboda abuncin sadaka da sukeyi duk sati da ake biyansu sunayi. Tunda suka fara aikin nan basu suka zauna ba sai wajen karfe uku na rana, dama a daidai wannan lokacin ake zuwa daukan abuncin sadakar…. Karfe hudu daidai ta dawo gidan gaba dayanta kana ganin ta kamar susutacciya, direct dakinsu ta nufa hankali atashe, a kwance ta tadda inna, bata ma bi takan innar ba don duk a tunaninta barci take,cikin sip dinsu ta bude tare da dage kayayyakinta da suke a ninke, chan kasa ta zura hannunta ta zaro wani tsohon hoto, yan mata ne guda uku cikin hoto daga gefe kuma sai wani sauri, ta dan dade sosai tana kallon hoton kafin ta maida hoton cikin drawer, ko tsayawa rufe drawer ma batayi ba ta futa daga dakin. Bata wani dade ba sai gata ta dawo kuma, this time around tadan samu natsuwa saboda maganganun da sukayi da Jamila. Ko takan sabeeha batabi ba da ke gaisheta ta wuce daki, sai alokacin ta maida dubanta ga inna dake kwance yashar kamar gawa ga wani kumfa kumfa dake futowa daga bakinta har ya soma bushe, hankali atashe hadiza ta karaso gaban gado kafin ta soma cewa ‘’inna, inna, wannan kumfar fa innalillahi wa inna ialihi rajiun’’ Idanun innar a bude ga hawayen dake saukowa bakinta kuma ya soma karkarcewa gaba daya ta qame gatanan dai tana jin abunda hadizar ke fada saidai ta kasa yin komai, takasa motsawa komai na jikinta ya sandare. ‘’inna!!! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku ni hadiza’’ hadiza ta doka ihu hankali atashe, sabeeha data shugo da kwanan abuncin su tana jiyo ihun maman nata yasa ta ajiye abuncin anan dakin ta wuce cikin uwar daki, itama gaba daya hankalinta ya gama tashi sosai tana tsaye baki kofar shugowa dakin, juyowa hadiza tayi ta kalleta hankali a tashe ta soma Magana . ‘’ke tafi gidan Jamila ki kirawota’’ Cikin saurin sabeeha ta futa daman da hijab dinta a jikinta, gidan Jamila ta wuce direct dukda batasan gidan ba saida tayi tambaya don bata taba zuwa gidan ba, ana nuna mata gidan kuwa ta shiga da sallama, duk ta burkice, Jamila na ganin shugowarta ta saki baki don mamaki, ‘’ina wuni’’ sabeeha ta gaisheta, ‘’lafiya dai?’’ ‘’mama ce tace nazo na kiraki, in…inna ce’’ Jamila najin haka ta zari hijab dinta dake baki kauren kofa kafin ta fuce sabeeha na biye da ita a baya. Gidan suka shiga a tare, matan gidan har sun fifito saboda ihun hadiza da suka dunga ji tana faman kiran ‘’inna ki tashi karki mutu, ki rufan asiri’’ Dakin Jamila ta shiga, inda ta tarar da hadiza na faman jijiga inna, har lokacin idanunta a bude suke tarr, karasowa Jamila tayi don dubata, tabbas abinda tayi hasashe ne ya tabbata, ita ma gaba daya lokaci guda hankalinta ya tashi ‘’hadiza mu kaita asibiti yanxu kafin abun ya tsananta’’ Tana kaiwa nan suka fara kokarin daukan inna, kasa daukanta sukayi saida Jamila ta fita, allah yao baban chidi na nan, shine ya shugo ya goyo innar, hadiza dai babu abunda take sai kuka, haka suka fito gaba dayansu har waje, ga anguwar a chunkushe take babu motoci, haka suka fito bakin titi hankali a tashe. Daidai nan motar taxi din kawu ta shawo kwana,daman ya dawo ne yaci abunci ya koma kan aiki, hadiza na ganinshi ta tsaidashi, bata ma tsaya yi mashi bayani ba suka shiga gaba daya cikin taxi din yaja suka wuce wani asibiti dake nan duten habujan. Asibitin government ne saidai kuma yaji jiki sosai, don kwata kwata babu kayan aiki, haka suka dunguma da inna cikin asibitin. Da kyar aka samu likita guda daya ya fara dubata, tashin farko yace masu wannan matsalarta tafi karfin asibitin da basu da ayyukan da zasuyi mata taimakon gaggawa, don kamar ta samu paralyze,jin wannan kalma ta daga ma hadiza hankali sosai, haka suka sake dungumar ta suka wuce cikin garin Abuja. Daidai federal hospital suka tsaya, Jamila ce tayi masu jagora inda kawu ya goyo inna dake nan jikinta babu progress ko kadan saima idanunta daya soma rufewa alamun shima yana gab da qafewa. Taimakon gaggawa aka fara yi ma inna inda manyan likitoci suka shiga da ita wani daki emergency, sun dauka kusan awa guda suna kokarin gano daga inda matsalar ta fara, saida sukayi mata wata allura wadda zatayi stabilizing system dinta kafin su fara yi mata test. Bayan awa gudan nan saiga likita ya futo, nan ya soma masu bayani, inna na dauke da liver cancer wanda taci taci ta sosai, wanda dole sai an cire mata wannan hantar don ta lalace, na biyu kuma tana dauke da diabetes wanda shima yayi mata tsanani. Cikin kidima hadiza ta soma kuka, saida Jamila ta bata baki kafin tayi shuru, nan doctor ya cigaba da yi masu bayani. ‘’kamar yanda nace, dole sai an cire mata wannan hantar zata rayu inba haka ba zata iya mutuwa Indai ta kara kwanaki talatin ba tare da an cire ba, don cancer ce kuma spreading takeyi.’’ ‘’likita nawa ne kudin aikin?’’ jamila tayi saurin tambayarsa ‘’dubu dari takwas ne’’ Dafe kirji hadiza tayi tsabar kidima, ina zata samu dubu dari takwas yanxu, matarda ko dubu dari da zata ce nata ne na kanta bata dashi. Tsabar tashin hankali zaman dirshen tayi a wajen sai Jamila c eke bata baki. Ranar dai sun kwana cikin tashin hankali, ga kudin asibiti da kudin gado da aka kira masu kusan dubu talatin, a rana guda Kenan fah. Kwanan inna uku ta farfado,gaba daya jikinta yanda suka kawo haka yake, abunci ma saita roba ake dura mata,ga chachar kudin asibiti, don tsakanin kwana ukun nan sun kashe wajen dubu tamanin. Maganar kudin aiki kuwa babu inda zasuje su samu wannan kudin, tashin hankalin hadiza Kenan, ranar da kawu ya zauna da innar hadiza ta samu ta koma gida don ta dan huta don ita ke zama da ita tsawon kwanakin. Sabeeha dai kullum tana zaune a gida tana jimamin rashin lafiyar inna don kwata kwata mamanta bata bata fuskar zuwa asibitin bama. * Da sallama hadiza ta shugo gidan Jamila, tana zaune a parlor tana cin taliya, ganin yanayin hadiza yasa ta ajiye taliyar gefe, ta miqe ta wank hannunta kafin ta dawo parlor. ‘’duk kin rame wallah, ki dai na sama kanki damuwa, insha allah zamu samu mafita. ‘’jamila wace mafitar Kenan? Wata guda fa akace? Ina zan samu wannan uban kudaden? Nunfasawa Jamila tayi kafin ta soma Magana cikin hikima ‘’inada mafita guda daya, koba komai zatayi maki maganin matsalolinki guda biyu a duniyar nan’’ Gyara zama hadiza tayi tana sauraronta, haka kawai sai taji sanyi aranta. ‘’in kin tuna kwanaki na baki wata shawara ko?, mezai hana ki amince kawai ni zansan yanda zanyi ayi chuku chukun da akeyi’’ Shuru hadiza tayi tana nazarin shawarar data bata, ‘’toh ya zamuyi kenan?’’ ‘’kinga baban jamilu (mijinta kenan) yana harkar agency din matafiya, yasan komai game da abubuwan daya shafi matafiya da yanda wassun su suke chuku chuku ta hanyar shiga kasashe waje daban daban, akwai wata agency da take kai yara aikatau zuwa kasashe daban daban a fadin duniya har sai wanda kika zaba,’’ Dan tsagaitawa tayi don karantar yanda hadizar ta bata attention sosai. ‘’hadiza mai zai hana ki turata aikatau itama, kinga kudin da ake samu wallahi da yawa ba kadan bane, don yana kaiwa wajen dubu dari uku ko yafi haka ma, duk wata, idan har kin amince zan tambayr maki baban jamilu saiki zabi kasar da sukafi badawa da yawa ki tura ta kawai, kinga kin huta da damuwar ganinta a gabanki, sannan kuma zuwanta chan zai magance maki matsalar inna da matsalar mu, ko ba komai dai tabar maganar dangin ubanta ta kau, kije kiyi tunani akai ’’ Nunfasawa hadiza tayi kafin ta dubi Jamila, ‘’jamila ay babu maganar zuwa nayi tunani, na amince kawai, ki mashi maganar, aturata da gaggawa, bamuda lokaci’’ Wani irin murmushi Jamila tayi kafin tace ‘’yanxu kika dauko hanya, karki damu ay tunda kin amunce Magana ta kare, zansa yayi mata komai, abunma zaizo da sauqi tunda an taba mata passport, idan na mashi bayani zan aiko ki bada tsohon passport dinta wani sabo za ayi mata kawai yanxu’’ Wani irin sanyi hadiza taji jin wannan shawarar da Jamila ta bata, haka ta koma gida tana mai jin sauqin abunda ke ranta. Bayan mijin Jamila ya dawo nan ta mashi bayani, da murnarshi kuwa ya amince wajen taimaka masu don daman su kamar masinjoji ne a harkar, idan ka kawo mutane zaka samu kaima naka kason, wannan yasa yaji dadi shima,nan ya buqaci ta karbo passport din yarinyar kawai don shi za a buqata, da daddare kuwa Jamila ta aika hadiza ta bada passport din. Cikin kwana biyu mijin Jamila y agama komai, daga kan passport dama a kungiya za a kaisu, ana tara yara kamar guda sha biyar haka sai a tura su, acikin kudin aikinsu za a zari kudin kawosu da za ayi sannan agency zata zari nata kason sauran kuma sai a turo ma iyayen yara. Bayanin daya shafi inda za a kaita da aikin da zatayi duk bai shafi hadiza ba kawai tunda taji mijin Jamila yace agency din suna bada albashi kusan dubu dari uku wani sa’in ma yana fin haka, hakan yasa ta amince kawai. Washe gari da safe kuwa da asubah hadiza ta tashe ta baiwar allah bata ma zan meke faruwa ba., ‘’na baki minti biyar jekiyi wanka ki futo kisa kayan nan’’ hadiza ta bata umarni tana mai yi mata nuni da wani koren kaya da hijab. Saida ta gaisheta kafin ta fuce tsakar gida cikin sauri, duk sanyin asubar nan haka ta debi ruwa a rijiya tayi wanka, ko tsayawa dauraye bandakin batayi. Tana gamawa ta maida hijab dinta tundaga bandakin kafin ta wuce cikin daki, kayan da maman nata ta bata ta fara saka wa, dakin kwata kwata babu haske dim dim, hakan yasa na kasa ganin yanayin jikinta, yawanci itadai koda yaushe tana cikin hijabi, Tana gamawa ta ganin maman nata bata dakin yasa wuce tsakar gida don daura dumamen da za akai asibiti. Bata ma kaiga dora tukunyar ba maman nata ta futo daga daki, sanye da hijab. ‘’ajiye tukunyar nan kizo mu wuce’’ Ajiye tukunyar tayi ta nufi inda maman nata take, daman already da silifas dinta a kafarta. Lokacin da suka fito haske ya bayyana don gari ya soma washe wa, Gidan Jamila suka wuce direct, da sallama suka shiga,Jamila ce a tsakar gidan tana hidimar abuncin yan makarnta. Sama sama suka gaisa da hadiza kafin su wuce cikin daki, wasu yan maganganu sukayi sabeeha dai na daga tsaye ta raqube a gefe har suka fito, kallon inda take hadizar tayi kafin tace ‘’ki zauna anan’’ Cikin girmamawa ta amsa da toh kafin hadiza ta fuce. Anan tsakar gidan ta samu waje ta zauna, har gari ya washe sosai, karfe takwas daidai mijin Jamila ya futo tare da jamilar suka wuce. Sabeeha dai binsu take da idanu duk ta soma tsorota har suka zo wani waje inda aka rubuta Aj agency service, cikin wajen suka shiga, wajen cike yake da mutane ga wasu yan mata da maza kamar ta harda wasu manyan mata dukkansu da irin kayan jikin da mamanta ta bata,idanu ta soma zaro wa tana tunanin ko menene dalilin kawo ta da akayi nan, mijin Jamila shima anan yake aiki so yana zuwa already yayi masu bayani daman sunsan da zuwanta, nan wani mutumi yayi mata nuni da inda sauran yaran suke don ta zauna. Shikuma mijin Jamila da ita jamilar suka shiga wani office,wani mutumi ne a zaune, gaisawa suka farayi kafin mijin Jamila ya soma Magana ‘’alhaji mun taho da yarinyar, zaku iya ajiyeta na shekara goma ma idan kunaso babu matsala saidai kudin da aka bamu ne, shine nace tunda ita ba’a yanke mata lokacin dawowa ba ko za a kara mana’’ ‘’kaifa masinja kasan yanayin aikin nan, dubu dari fa muka baka, gaskia bazan iya kara wani abunba’’ Jamila ce tayi saurin tsomo baki ‘’haba alhajin allah, mu fa bamuda matsala, ce maka akayi ku riketa, idan ma shekaru dari zatayi tana aiki karkashin ku mu bamuda matsala, ko dan wannan ya kamata a kara mana wani abun mana’’ ‘ ‘’ah toh mu gaba ta kaimu, zan kara maku dubu goma’’ Godiya sukayi mashi kafin ya irga kudaden ya basu suka fuce daga wajen. Samun waje tayi daga gefe chan ta zauna gaba daya ta fara furgicewa da tsoro, don bata taba shiga cikin hayaniyar mutane haka ba. Su kuwa Jamila da mijinta suna amsar kudin su suka kara gaba abunsu suka barta tana zare idanu. Tana nan zaune cikin yaran har wajen karfe goma kafin a fiddo dasu waje inda akayi parking wata katuwar bus. Daga nan aka basu umarnin shiga cikin bus din, sai a lokacin sabeeha ta tabbatar da something is wrong? Ina ne nan ta tambayi kanta, ina za a kaita, nan take ta soma hawaye. Har suka shiga cikin bus din bata bar hawaye ba. Shin ina za akai sabeeha? Ku biyoni don sanin wata duniyar sabeeha zata shiga, Siyar da ita su Jamila sukayi? Da sanin mahaifiyarta kuma? Ko kuwa Da gaske aikatau din za a kaita wata kasar daban? Inda bata san kowa ba? Gashi bata iya mu’amala da mutane ba. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Free page Chapter 9-10 Texas high class restaurant Abuja. Mota ce kirar range rover rr2023 fara tass tayi parking a cikin parking lot din dake cikin restaurant din, manyan manyan motoci masu class ne parke a wajen aqalla bazasu wuje guda biyar ba. Saida aka dauka kusan minti biyu kafin abude kofar motar, cikin natsuwa ta fito daga cikin motar gaba daya, sanyayan murmushi ne kwance a fuskar mata, daga ganin ta babbar macece data manyanta,sanye take da jan lace na manyan mata masu aji da bakin mayafi wanda ya haskata sosai, hannunta rike da hermes hand bag baka, wuyanta zagaye yake da Sarkar gwal, haka zalika hannayenta, daga gani yar gayu ce don tasan fashion sense , bata da qiba kwata kwata saidai kana ganin fuskanta kasan ta manyanta, idanunta kuwa wani dan siriri glass ne akai,tana da wani irin calm appearance. Rufe motar ta fara yi kafin ta soma takowa zuwa cikin restaurant din, saida tazo bakin kofar ta sauke wani murmushi wanda ke bayyanar da hakoran. Fuskar data hango daga cikin restaurant din ne kawai yasa ta sauke wannan murmushi, guards din dake wajen ne ya bude mata kofa kafin ta sanya kafafunta cikin restaurant din, daga ciki kuwa mutane ne a zaune kan wani dogon table,akalla zasu kai su goma a zaune, kowannensu hankalinsa nakan plate din dake gaban su, kamar daga sama sukaji daya daga cikin yaran na fadin ‘’nanna, nanna’’ Da sauri duk suka juyo don ganin ko da gaske ne nanna dince, suna tabbatar da ita dince kuwa duk suka miqe tsaye cikin farin ciki da murna, qananun yaran ne suka taho a guje, suka rungumeta, yaran sunsha cute kaya masu kyau, iyayensu kuwa duk miqewa sukayi suma cikin farin ciki suna kallonta. Tun daga nesa ta soma Magana ‘’wai wai Anne ashe haka muka tara iyali masha Allah’’ Dariya duk suka fara yi har ta karaso wajen tables din, samarin dake tsaye ne suka fara duqawa zasu gaisheta rungumosu ta fara yi daya bayan daya cikin farin ciki. ‘’barka da sauka nanna’’ ‘’barka dai sufyan, Abal din anne yaushe kuka dawo daga school ya uk’’ Abal ne ya amsata ‘’alhamdullah, munzo holidays su ya sufyan kuma sun gama ay’’ ‘’Ahh masha allah, abun babu wuya‘’ Sunkuyar dakai sukayi gaba dayansu suna murmushi atare. Iyayensu ne mata suka fara gaisheta suna duqawa suma don bata girma ‘’barka da zuwa nanna’’ Kallon wadda ta fara gaishe ta tayi ‘’ah ah matar babban yaya, na sameku lpy?’’ ‘’lafiya lau nanna’’ ta amsata cikin ladabi, sauran matan ma haka suka dunga gaisheta tana amsa su. Gyaran murya da akayi ne yasa ta dago kafin ta sauke wani qayataccen murmushi, cikin hanzari ta tako har inda dattijuwar datayi gyaran murya take, kamannnin su sak babu makusa, kana ganin su kasan jini jini ne aduk inda yake,kamannin harta baci sosai banbancinsu kawai daya ta fi daya manyanta. ‘’yaya…’’ ta fada tana mai rungumeta tsam, Rungumeta itama dattijuwar tayi tana mai farin cikin ganin yar uwarta Saida suka dauki kusan minti biyu a haka kafin su saki juna, wadda yaran nan suka kira da nanna ne tace ‘’happy 60th birthday yaya, allah ya karo shekaru masu albarka da nisan kwana’’ Atare duk suka amsa da ameen, sai alokacin ta samu suka gaggaisa da sauran da basu gaisa ba, gaba daya an taru full family gwanin birgewa, surukai da matan surukai duka, harda jikoki. Lokaci guda wajen ya kachame da hira sosai inda nanna ta zauna kusa da yar uwarta anne suma suka fara hira. Hannun anne na cikin na yar uwarta don murna, nanna da anne yan uwa ne, ciki daya suka fito,anne ce babba sai nanna mabiyarta dukda ta girmeta sosai. Rarraba idanu nanna(grandma) ta soma yi kafin ta maida dubanta ga matar Sameer ‘’ina babban yayan ne ban ganshi ba?’’ Cikin ladabi da kunya matar ta dago ta kalleta ‘’ay ya tafi wani course a Europe yau wata guda kenan’’ ‘’Ayya shiyasa kennan’’ nanne ta fada tana mata murmushi. Sallamar da akayi ne yasa suka dago gaba dayansu, wadda ke gaba ce ta soma fada, ‘’wai ace mutun ya tsaya yangan banza da wofi, wallahi next time kika kara bata min lokacin bazan kara jiranki ba shirman banza kai, kai kuma hamad ka riqe package din da kyau karka yarda cake din’’ Wanda ta kira da hamad kanshi na kasa ya rike wani package da hannu daya,dayan hannunshi kuma key din mota ne da wayanshi, saurayi kyakyawan gaske black beauty, bazai wuce 22 years ba gefenshi kuma wata yar budurwar yarinya ce akalla bazata wuce 18 years ba, sanye take da wata doguwar rigar material datayi mata kyau, baka ce kuma kamanninta daya da hamad din saidai shi yafita kyau, hannunta itama rike da wayaa latest iphone fuskanta tasha makeup a wadda ya amsheta, wadda ke gaba da alamu mamansu ce. ‘’sannu da zuwa anty fadila’’ yaran suka fara fada suna gaisheta, sai alokacin ta dago don gaisheda anne, ganin nanna yasa ta sauri waro idanu tare da tahowa cikin sauri ta rungumeta ‘’nanna, saukan yaushe’’ Dariya nanne tayi ta rungumeta tsam itama tana mai jin dadin ganinta tace ‘’my daughter, nayi missing dinku wallahi, how are you ya mai gidanki’’ Murmushi tayi wanda yasa duk mutanen wajen suka zuba mata idanu, don da wuya murmushin anty fadila ya futo shiyasa kowa yafi son anty bahijja don ita tafi faran faran ga son mutane sosai, anty fadila kuwa akwai fada bata daukan nonsense, gashi ta iya dressing don ta iya buga naira a jikinta, to kudin ne ma gashi nan kamar zai kashesu. ‘’yana nan lafiya nanna, ya turkey,fatan kin dawo Kenan shekara kusan biyu fa rabonmu dake’’ Murmushi nanna tayi kafin tace ‘’na dawo Kenan insha allah bazan koma ba,’’ Yaranne suka soma cewa ‘’yay’’ suna murna, Sama sama fadila suka gaisa da matar Sameer kafin ta maida dubanta ga anne tare da taya ta murnar cika shekara sittin a duniya. Hamad ne ya karaso ya tsugunna har kasa ya gaisheta kafin Laila itama ta rungumeta tana mai farin cikin ganinta. Haka suka gama celebrating 60th birthday din anne cikin jin dadi da murna har mutanen US saida suka kirasu sukayi video call inda suka taya anne murnar cika shekara 60th a duniya kafin su wuto gida. Saudi Arabia…… Karfe biyar daidai jirginsu ya sauka a international airport dake garin jedda, daya bayan daya suka fito, gaba daya suka sauko daga jirgin inda wanda ke jagorantarsu ya jagorance su zuwa wajen barrier din dake controlling shige da fuce na kasar, mazan na daga gaba while matan ba biye dasu har suka shigo cikin airport din, checking dinsu aka fara yi daya bayan daya don ganin information dinsu, basu wani samu matsala da immigration din ba don haka ana gamawa dasu suka fuce daga airport din. Bayan sun fito daya bayan daya wanda ke jagorantarsu ya soma karbar passport dinsu kafin su shiga bus din da aka tanadar masu ta agency company don tabbatar da babu wanda ya gudu. Sanyayyiyar ni’ima ce tare da fargaba ta saukar ma sabeeh lokacin data shaqi iskar qasa mai tsarki,harga allah hankalinta yana gida musamman mamanta da inna dake kwance asibiti. Rarraba idanu ta dunga yi har suka shiga cikin bus din, at that point ta hakura kawai ta barma allah komai, don babu abunda yayi saura kuma,baiwar allah saita zama wata iri, kuka dai tasha kuka kamar babu gobe, tsoron da take ji ya wuce musali, matar da suka taho tare ma bata ganta ba don bata shugo cikin bus dinba, abunda yafi bata mamaki atare duk suka fito juyawar da zatayi kuma ta nemeta ta rasa ta. Sauran yan matan ma rarraba idanu suka dunga yi, wasu daga cikin su murna suka dungayi gashi a saudia wasu kuwa hankalinsu tashi yayi don basu san ya rayuwar kasar take ba. Tafiyar minti talatin sukayi suka karaso company, dukda garin bai soma washe ba amma inkaga yanda mutane ke hada hadarsu kamar da rana. Fitowa sukayi daga cikin motar kafin a wuce dasu cikin agency din, mazauni aka basu da ruwa da apple kafin gari ya waye. Wanda ya jagorancesu ne ya nuna masu inda bandaki yake da wajen yin sallah na musulmai, mazan dai mikewa sukayi suka wuce wajen sallah while matan kuwa suka kasa miqewa saboda tsoron karsu bata, sabeeha ce kawai ta iya dannewa ta miqe ta wuce bandakin, saida ta biya buqantunta ta dauro alwala har tayi sallah a wajen sallah kafin sauran su shiga wajen suma. Suna nan zaune har wajen karfe goma har aka kawo wasu daga wata kasashe daban kafin a tattara su waje guda, wata agreement paper aka basu kowanne don yayi sighing kafin a rarraba masu wani tag mai dauke da sunayensu a jiki tare da sunan agency kafin kowannensu ya saqala tag din a wuyanshi. Sorting dinsu masu agency din suka fara yi base on shekarunsu da abunda suka fi kwazo wajen yi kafin a fara futar dasu, don tun daga kasashensu ake masu training kafin a kawo su, agency din data kawo sabeeha ma AA agency Kenan itama tana karkarshin waenda ke kawo masu aiki dukda basa bin dokokin daukan yan aikin saboda su basa yin wani training suke aiko wa, wasu daga cikin yaranma basu san inda za a kaisu ba ake daukosu kamar su sabeeha Kenan, don saida suka shiga jirgin matar nan take mata bayanin komai. Wasu daga cikinsu manyan company za a kaisu wasu kuma gidajen da sukayi requesting maids za a kaisu, wasu daga cikinsu ma har asibiti za a kaisu shara da dai sauransu, wasu gidan abunci, wasu har makka ana kaisu suyi aiki a masallaci. Sabeeha dai bata san inda aka wullata ba, haka aka tasata da wasu a gaba acikin motar agency su kusan biyar. Tunda ta zauna cikin motar take bin titin garin da kallo dukda sunyi zaman kasar waje da maman ta kafin su dawo rayuwar talaucin da suke ciki hakan baisa ta danyi kauyanci ba da mamakin wai yau itace a kasa daban, gaba daya tunaninta yayi nisa ya tafi wani wajen har suka karaso wani gida, sunanta da balaraben daya dauko su ya kira ne yasa ta saukowa daga cikin motar, wata jakar goyo ya bata kafin su shiga cikin gidan. Gidan bashi da wani girma sosai, irin tsoffin ginin nan ne wanda ya dan kwana biyu, ciki suka shiga inda mutumin ya jagorance ta, hannunshi rike da wata paper. Koda suka kwankwasa kofa wata balarabiya ce ta bude kofar, daga ganinta ta dan manyanta, mutumin ne yayi mata bayani cikin harshe larabci kafin ta karbi paper din tayi sighning, tana signing ya wuce ba tare da ya kalli sabeeha ba. Matar kuwa ganin ta tsaya a tsaye kamar wadda za a sace,sai faman zare manyan idanuwanta take, hakan ya sata ta mata nuni da hanyar cikin gidan. Ciki matar ta shige sabeeha na biye da ita, gida ne gidan bene bashi da wani girma sosai. Anan kasan matar tayi mata nuni da wani dakin kafin ta mata bayani da turanci kan cewa ta shiga tayi washing up. Dan turanci da take ji ne yasa ta gane abunda take nufi, duk da karatunta baiyi zurfi ba, kanta kawai ta sauke kasa kafin ta shiga ciki,hawayen da take kokarin hana kanta yi ne ya sauko mata lokacin data shiga cikin dakin, dakin shake yake da abubuwan da sun kai kusan shekara ba ayi amfani dasu ba, hardasu tsohon keken dinky da wasu robobi, duk kura ta gama bade dakin gashi dakin bashi da wani girma sosai. Jefa idanunta tayi wajen wata kofa, kusa da kofar akwai wani dan karamin gado, anyi laying gadon da zanin gado kamar anan ake kwana don harda pillow da abun luluba a wajen. Takowa tayi har bakin wajen kafin ta ajiye yar jakar da mutumin nan ya bata akan gadon, bakin kofar tabi ta leka ganin bandaki ne a wajen yasa ta dawo ta zauna akan gado. Wani irin barcin gajiya ne ke fuzgarta, ga tsoron daya addabeta na sabon waje. Tana nan zaune barci ya dauke ta ba tare da saninta ba, saida ta shafe wajen awa biyu kafin ta tashi da kugin ciki saboda yunwa data addabi cikinta, tunawa da apple dinnan da aka basu yasa ta bude jakar, kaya ne kamar uniform kala uku a ciki riga da wando, gaban kowacce riga an rubuta sunan agency din a jiki harda phone number su a jiki. Ajiye kayan tayi a gefe ta dauki apple din ta fara yi tana hawaye,saida ta cinye tass harda kwallon kafin ta shiga bandakin ta tara ruwa daga fanfon sink din tasha abunta tana kuka. Satin sabeeha uku a cikin wannan gida, acikin kwana ukun nan abubuwa da dama sun faru wanda suka firgitata suka hargitsa mata tunani sosai, wato aikintaa gidan shine kula da wani tsoho, inda ita zata dunga kula da komai nashi don baya tafiya kullum yana kan kujera, tsohon yana da masifa sosai ga rikici, itake wanke kayan da yake kashi da futsari akai, itake zama ta bashi abunci dukda idan ta kawo watsa mata yake a jiki, wani sa’in har marinta yakeyi ko ya jefeta da objects, su uku ne kawai a gidan daga ita sai wannan tsohon sai matar wadda da alamu itace guardian din tsohon. Zataci zata sha saidai kuma wannan rikicin tsohon ne ke tayar mata da hankali, data zauna babu abunda take sai kuka, gashi wannan yar tashi dataji ya fara kuka zatazo ta balbaleta da masifa wani sa’inma harda mari take hada mata. Watan sabeeha guda a gidan wanda ya zame itace maid ta farko datakai har wannan lokacin, har zuwa wannan lokaci babu abunda ya sauya game da wannan tsoho da take kula dashi,kullum in zatayi aikinta kuwa zata saka uniform dinnan ta daura koren hijab din da aka basu tare da facemask dinnan kafin ta fara aikinta, mask dinma har ya fara tattogewa saboda tsufa don wankeshi takeyi. Akwai wata ranar laraba, matar gidan bata nan daga sabeeha sai tsohon nan a gidan, bayan ta gama ayyukanta lokacin cin abuncinsa nayi ta zuba mashi ta wuce dakinsa don ta bashi, tana zuwa ya fara watsa mata abunci yanda ya saba yana masifa, yana cikin wannan masifar yana larabci ya cizge mask din nata, daidai nan yarsa ta dawo, jin ihunsa yasa ta taho aguje zuwa dakinsa, tana zuwa dakin ganin tsohon yashe a kasa duk yabi ya tsorata yasa ta juya don ganin inda yake kallo, sabeeha ce a tsaye itama tana kuka yanda yake kukan, ta janyo hijab ta rufe fuskanta, nuni tsohon ya dunga yi da sabeeha cikin furgici ya fara cewa ‘’shaytan shaytan,’’ Ba matar kadai ba har itama sabiha saida hankalinta ya tashi sosai,ganin haka yasa matar ta korata akan tabar daki. Da daddare kuwa saiga motar agency tazo don tafiya da ita, haka ta tattara kayan nan nata guda uku ta tura a jaka tabar gidan. Agency aka maidata ko kwana batayi ba aka dungumeta aka kaita wani gidan daban, wannan gidan da aka kaita bata samu wani matsala ba da matar gidan dukda shima aikin kula yara ne da raino aka bata, abu dai na tafiya tiryan tiryan aka sake korarta a gidan don ko wata bata cika ba, shima nan gidan yaran gidan ne suka nuna masa son ta don haka aka koreta. Koda aka dawo da ita agency with same complain hakan yasa suka fara bincikarta don sanin dalilin korarta da akayi cikin wata biyu da zuwanta. Nan suka gano facial appearance dinta ne ke jawowa a koreta, wannan dalilin yasa suka yanke shawarar turata gida Nigeria kawai dukda da wuya ake samun waenda ke yin irin aikin da information dinta ya nuna ta iya kuma ta kware which is mai kula da mara lafiya ko raino(caregiver/nanny) don shine aikin da yafi wahala sosai kuma ba kowa ke karban irin wannan aikin ba, baiwar allah ita bata ma san mijin Jamila aikin daya rubuta ta iya ba Kenan. Nan suka fara preparation din turata Nigeria don basa son abunda zai shafi imagine business agency dinsu. Taheel group of company Wani mahaukacin building ne mai shegen girma da haduwa, fadin irin tsaruwar building din daga waje ma bata lokaci ne don ya gaji da haduwa gashi yana da tsayi sosai yakai international standard, tsagaye yake da mirror glass, daga gaban company din a rubuta Taheel group of company da manyan harufa tare da logo din companyn, mutane sai shige da fuce sukeyi. Wasu manyan motoci ne suke shugowa cikin company inda aka rubuta factory asset a jikin motar, cikin gaggawa matukan motocin suka fito bayan sunyi parking, cikin motar cike yake da mutane, daya bayan daya suka fara fitowa gaba dayansu da kwalaye a hannunsu da alamu protest zasuyi, guards din bakin entrance dinne suka tsaya don hana su shiga cikin premises din, mutane ma’aikata kuwa haka suka dunga lekowa don ganin ikon allah, su kuwa protesters dinnan mai zasuyi banda ihun dole a kara masu kudin aiki saboda yanxu sun kwashe wata biyu Kenan sunayin wani project na wasu kaya da sukeyi a factory, babu dare babu rana haka suke aikin nan saboda pressuring dinsu da akeyi wanda sunsan daga wajen acting ceo ne wato Hajiyar da kanta gashi anqi kara masu kudin albashi wannan dalilin yasa suma suka fito protest. Daga chan saman last floor kuwa, office daya ne na acting ceo wato wadda ke rike da mukamin ceo temporary kafin heir din company ya karba responsibility dinshi, daga kofar shiga office dinma kasan irin haduwar da zaiyi daga ciki, kamar wani A class hotel saboda da girma, katon table dinta ya cika bari guda na cikin office din inda akan table din documents ne sai katuwar desktop da laptop na brand din apple sai landline daga gefe, tsakiyar table din kuwa wani katon glass name plate ne akai inda aka rubuta chief executive officer Hidaya Talal Taheel. Office din nata tsit baka jin komai sai karar ac dake tashi,a tsaye take daidai wajen glass mirror wall din office din wanda daga ciki zaka iya hango na waje, hannunta rike da cup of coffee, tana sanye da wata riga daidai gwaiwanta plain burnt orange color sai wandon rigar wanda yazo mata har kasa, kafarta kuwa sanye take wani hill baki sai kanta data nade shi da wani silk black veil, fuskan nan nata babu digon fara a, she looks so so serious, saida ta kare masu kallo sosai daga nan wajen wall din kafin ta juya cikin isa da aji ta soma takowa wajen desk din office dinta, zama tayi tare da janyo file din gabanta, budewa tayi ta karanta file din tass kafin ta danna wasu number dake jikin lanline din, nan take tasa ayi mata connecting da securities din entrance, lokacin da call din ya shigo cikin gaggawa security din ya daga saboda security call box dinsu na kusa da inda mutanen keyin protest, a gaggauce ya amsata kafin ya fito waje ya soma Magana ‘’we have a call for abdullah head of factory service’’ Abdullah dake tsaye hannunshi da rike da board yana jin an kira sunanshi ya tako inda securities din suke, atare suka shiga cikin landline box din, inda daya daga cikin securities din ya bashi landline din, mutanen dake waje dai zuba masu idanu sukayi don jin dalilin kiran head dinsu. Magan daya biyu tayi mashi kafin ya sauke wayan, yana saukewa ya fito wajen mutanen ya tsaya tare da daga hannunshi don su bashi attention. ‘’na samu Magana da madam, and ta buqaci ganina yanxu, inason ku natsu zanje muyi negotiating yanxu.’’ Ihu duk suka farayi cikin murna kafin su zazzauna anan kasan gaban company don jiran dawowanshi. Daga cikin company executive secretary ya jagoranceshi don ba kowa ne yake zuwa ganin madam ba balle a shiga office dinta sai manyan shareholders da mutanen da suke partnership dasu don ceo ba karamin muqamin ba ne dukda ita acting ceo ce. Cikin lift suka shiga inda secretary ya danna floor din da zasu tsaya,daman floor goma ne, inda madam take kuma 9th floor ne. Button din floor dinma na office dinta ya fita daban don duk wanda ya shiga cikin lift din zai tabbatar da wajen na daban ne. Suna karasowa kofar lift din ta bude, secretary n agama Abdullah na biye dashi abaya, saida suka wuce office din excutive secretary tukunna suka kaiga nata offce din. Saida secretary yayi knocking kafin ta basu access wanda nutton din access door din na jikin table dinta. Ciki suka wuce Abdullah sai rarraba idanu yake yi yana kallon ikon allah, ay inbanda ya gani da idanunshi zai iya karyata akwai waje kamar haka a doran kasa, yasha ayyuka a companys daban daban dukda yafi dade anan saboda sune yan farko farko da marigayi taheel mutun mai nagarta ya daukesu aiki. Wata kujerar baqi dake facing din table dinta secretary ya nuna mashi, zama yayi yana washe bakin kafin ya soma gaisheta, wato kudi duniya ne duk girmanka shekarunka dole saika girmama wand aka kusan haifa ma. Bata amsashi ba haka zalika bata dago ba saida ta gama abunda take kafin ta dubeshi da kyau, wannan file din ta mikama secretary ya miqa mashi, karba Abdullah yayi yana mai sauraron dalilin miqa mashi da akayi. Cikin muryarta mai dauke da iza da isa ta soma Magana ‘’abdullah Muhammad right? Dagowa yayi ya kalleta yace ‘’yes madam’’ ‘’why are you trying to tarnish my image?, shin kasan idan nakai karar ka zan iya charging dinka for defame of reputation’’ Wani irin kallo ya mata kafin ya soma Magana ‘’cikin book of record na rules din companying nan ya bamu daman yin protest akan abunda ba ayi mana daidai ba’’ ‘’and who said your part of the company? Youre fired 10mins ego’’ Hankali atashe ya dago zaiyi Magana ta dakatar dashi ta hanyar daga mashi hannu ‘’ouff no need for that, check that profile first then I have 2 reasonable options for you’’ Jin haka ya sashi bude file din, fadin irin tashi hankali daya garzayo mashi ma bata lokaci ne, sunanshi ne baro baro a cikin file din inda takardunci suka tabbatar bashida qualification din shigowa company din ya shugo, daman requirement din dole sai kana da background ma’ana babu any criminality record da good education qualification, shi kuwa an taba kamashi lokacin about 20 years ago shi kanshi bazai iya tuna dalilin kamashin da akayi ba saidai yasan tabbas lokacin da yarinta akanshi, yanxu kuwa komai has been buried danko matarshi bata sani ba balle yayanshi, cikin sauri ya dago ya kalleta idanunshi sunyi jaa sosai, bamanashi kadai ba harda wasu abubuwan da babu dadin ji daya dangance shi da iyalanshi tayi digging and shes using it against him ko ince take threathning dinshi akai. Yau shekara goma sha biyar Kenan yana aiki da taheel group, tun lokacin ubanta na raye, kuma shi ya daukeshi aiki ma, mutumin kwarai wanda yasan darajar mutane dukda yana da arziki mai tarin yawa hakan bai rufe mashi idanu bay au gashi lokaci yazo da yayanshi suke wulaqanta waennda suka taimaka masu suka daukaka company, don idan babu mutanen nan babu yanda za ayi companying ya dunga moving dukda kudi suke basu, acikin employee din company din masu kula da harkar factory suna da amfani sosai, shiyasa ake basu mahimmanci sosai don da gumunsu suke yin komai. Kaste mashi tunaninshi tayi har lokacin coffee dinta na hannunta tayi relaxing bayanta akan kujerar ‘’I know wat you’re thinking right now but ina tunanin ba wannan ya kamata kayi ba, don’t be corny,’’ Ajiye cup din coffee din tayi ta mike tare da takowa har wajen masaukin baqi kafin ta zauna opposite dinshi fuskanta babu alamun digon rahama ta soma Magana ‘’inada option biyu da zan baka masu sauqi, na farko ka sauka kasa ka tattara workers dinnan ku koma bakin aikin ku, maganar qarin kudin salary ku cire shi daga aggender dinku don ko penny bazan kara ba, you don’t owe me an explanation for that, na biyu zaka iya miqewa ka fuce min daga office like I said’’ Ta dan dakata kafin ta duba agogon danyen gold din dake hannunta ‘’like I said this is 25mins Kenan da sallamarka, sannan ka jirayi charges din da zanyi pressing su kuma waenchan nasan how I will deal with them, anyways ko ban fada maka ba kasan how I will deal with them just how I did with you, and lastly I want to give you a sounding warning wallahi wallahi babu wanda ya isa yayi tarninshing image dina ya zauna lafiya, I’m going to sue yall and rot you in jail mark my words, this is how I do my business, yanxu zabi ya rage naka‘’ Tana kaiwa nan ta miqe ta wuce wajen sit dinta, Abdullah kuwa kasa motsawa yayi tsabar tashin hankali, bai taba tunanin matarnan bata da Imani ba sai yau, bai taba tunanin zaka haifi da yaqi gadar ubansa ba, shes completely opposite din mahaifinta. Turkashi, wani irin zufa ne ya wanke mashi fuska anan zaune, yama rasa irin tunanin da zaiyi saida secretary yace yazo ya futa kafin ya dawo daga tunanin daya fada, koda ya fito daga office din saida yayi kwalla don wannan ba karamin cin mutunci tayi mashi ba da girmanshi da shekarunshi, gashi yanxu ta bashi zabin da dole saiya dauki daya, na farko idan yace zai dau gaskiyar daya fito protesting to fa abin zaiyi affecting dinshi da iyalanshi don da wannan aikin ya dogara, na biyu kuma ta bangaren mutanen dake karkashinsa a matsayin san a head, sun bashi amanar su akan ya karbo masu encin su da halaliyar su sai gashi yanxu ya rufa dashi. Kwallar data zubo mashi ya sharce yana mai jin wani irin nauyi a zuciyarci, matar nan ko shekarun da yayi yana masu bauta dukda suna biyanshi bata gani. Haka ya fito premises din company jiki a mace, suna ganin shi kuwa duk suka mike daga zaune suna mai farin cikin jin ko anyi dace, gaba daya zagaye shi sukayi suna jiran jin furucin da zaiyi, abunda ya fada masu ba karamin tayar masu da hankali yayi ba nan suka tabbatar ba ayi dace ba, suna kokarin cigaba da protest din ya roke su akan su bari saboda madam tace duk wanda yake son barin aiki to zai iya cigaba da protest din wanda kuma yake son aikinsa ya koma factory. Zuba mashi idanu sukayi gaba daya suna mamakin furucinsa, kamar ba head Abdulla ba mai sn gaskia,lallai tabbas akwai matsala kuwa, ganin kamar basa sauraronsa yasa ya juya ya shiga cikin motar factory din, wasu daga ciki haka suka biyoshi a baya wasu kuwa qin bin bayanshi sukayi don gani suke kamar shima an saye shi ne. Shiko tausayinsu ya dinga ji, karshe dai sai juya katuwar factory bus din yayi suka koma factory house, sauran kuwa suna nan tsaye secretary ya fito,hannunshi rike da papers dinsu ta sallama kusan guda ashirin, hidaya dake zaune a office tana hango duk abunda yake faruwa daga cikin laptop dinta saboda akwai cctv cameras ta kowani lungu da sako dake cikin company. Tana kallo secretary ya watsa masu takardar sallamarsu inda ya umarci securities su fitar dasu. Ranar dai ma’aikata sunga tashin hankali, gashi babu wanda ya isa yayi questioning dinta sai shareholders. On top korar datayi masu saida tayi pressing charges akansu, wasu ma basu san hawa ba basu san sauka ba ake laqaba masu sharrin abunda basuyi ba, haka aka dunga kamasu ana kullesu. A office kuwa haka aka dunga circulating magana saidai babu wanda ya isa yace uppan don itace oga kwata kata, familynsu sunfi kowa shares a companyn don ko share din gaba daya shareholders din bazai kai koda rabin nasu ba suke da 75% shares sauran 25% kuma na sauran shareholders dinne dukda ba a raba nasun ba ita da qannenta saboda ba ayi presenting heir din company ba har yanxu. Bangaren hidaya kuwa hankali kwance ta cigaba da ayyukan dake gabanta ba tare da tsoro ko fargaban komai ba, yanda take jin kampanin nan ba a cewa komai, zata iya yin komai don kare martabar family business line dinsu, bangaren completion she’s compatative kowa ya shaida haka, when it comes to business bata da sauqi kwata kwata. Wayar hannunta ta kura ma idanu tana wani dogon tunani, cikin call log dinta ta shiga, wata special number ta kura ma idanu inda tayi saving da big baby T, ta dade idanunta akan wayar ta zurfafa cikin tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar kawai. Tana ajiyewa karar message yayi popping, wayar ta dauka ta bude message din, ganin sunan khaal yasa ta ajiye wayar ba tare da ta bude message dinba. Duban screen din laptop dinta tayi inda ta fara duban wani business proposal da Gucci brand suka tura masu, saida tazo daidai wani slide ta tsaya, rubutun slide din ta zuba ma idanu ina aka rubuta ‘’possession of control, authority, influence is power!!!’’ Ta dade sosai tana kallon wannan rubutun ko kifta idanu ta kasa, saida ta dauka kusan minti biyar kafin ta sanya hannu tayi banging laptop din ta mike tsaye ba tare da ta dauki komai ba ta zari handbag dinta ta fuce daga office din tana dialing wasu numbers a wayanta. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 11-12 Update!!!! Agency… Zaune take har wajen karfe biyar a zaune,babu abunda ke miqar da ita sai shiga bayi ko sallah, gaba daya tayi laushi abun tausayawa,babu abunda take tunani sai rayuwarta, ba karamin tausayin kanta take ba, tun tasowarta sai yanda akayi da ita kamar kaya,tunda mutanen nan suka jinginar da ita anan basu sake waiwayonta ba, ita dai tasan cewa maidata gida zasuyi ayanda taji suna fada. Tana nan zaune ogan agency din gaba daya da wasu yaranshi suka fito daga office din nasu, fuskarsu a washe suka karaso reception inda suke ajiye ma’aikata. Har suka karaso kanta na kasa ta lula duniyar tunani, saida daya daga cikinsu ya kira sunanta kafin ta dago, da mamaki take kallonsu su uku a tsaye akanta suna washe baki. Sanin bata jin larabci yasa daya daga cikin su ya kalli ogan nasu yace ‘’sir kana ganin bazaamu samu wata matsala ba idan muka tura ta?’’ Kallonshi ogan yayi kafin ya dan hade rai ‘’bana fatan haka, kai ni banma damu ba kasan irin kudin da zamu samu kuwa ta dalilin yarinyar nan?, ‘’ Daya daga cikin su ne ya sake Magana ‘’but sir, kasan dalilin da yasa ake korarta daga aiki, what if hakan ya jawo mana matsala’’ ‘’na rigada nasan da wannan kuma inada plan akan wannan, this girl is the only option we have dole mu turata’’ ‘’but sir yanda…’’’ Katseshi ogan yayi da gaggawa kafin ya dubi sabeeha da tayi tsuru kanta a kasa. Jin kalamanshi na karshe yasa hankalinta ya tashi sosai, ta shiga rudu, dukda bata gane wasu abubuwan da suka fada da larabci ba, abunda ya danfi tsaya mata arai shine abunda ogan ya fada, me suke nufi Kenan waennan mutanen kodai inda za a cutar da ita zasu kaita? Tambayoyin data dunga yima kanta Kenan saidai ta tabbatar koma menene daga yanda suke Magana akai ba alkhairi bane. Wata takarda suka bata domin tayi signing kafin daya daga cikinsu ya jagoramceta zuwa motar da zata tafi da ita. At that point ta gama saddaqarwa kuma, sai yanda allah yayi da rayuwarta. Tafiyar minti ashirin ta kawosu wani waje wanda ta kasa tantance ko’ina ne, driver ne ya futo ya bude mata motar kafin yace ‘’fito’’ Futowan tayi da Jakarta a hannu kamar za a kwace mata, shine yayi gaba kafin ta bishi a baya har suka shigo cikin wajen, har suka shiga wani daki bata tantance taqamaimai wajen don kamar dakuna ne burjik a bulding din. Suna shiga ciki driver ya mata nuni da wajen zama kafin shima ya zauna a gefe. Zaman minti goma sukayi kafin a bude kofar shugowa, mutane ne guda biyu suka shigo, daya nag aba dayan kuma na biye dashi a baya. Miqewa driver yayi cikin ladabi ya gaishesu kafin ya basu waje. Sabeeha na ganin haka ido ya raina fata, ko gigin dago da idanunta batayi ba don cike suke da tsoro da fargaba. Zama daya daga cikinsu yayi while dayan na tsaye yana fuskantarta da kyau, gyaran muryar da akayi ne yasa ya maida dubansa ga ogan nasa. ‘’I’m sure kasan dalilin kawoka nan danayi ko?’’ ‘’yes sir’’ ya amsa shi ‘’okay inason ka fada mata abunda zan fada yanxu da yarenku yanda zata fahimta sosai. ‘’okay sir’’ wanda ke tsayen ya sake bashi amsa. Magana wanda ke zaunen ya fara cikin harshe larabci har yakai aya kafin ya nunfasa ya maida dubanshi gareta don jin response din da zata bayar, shi kuwa dayan yana ganin haka ya soma fassara mata yanda zata gane cikin harshen hausa don daman shi interpreter ne, aikinsa Kenan anan kasar, kuma yana samun kudi sosai. ‘’zakiyi mamakin kawoki nan da akayi, ba komai bane yasa aka kawo sai dan wani aiki da zakiyi mana cikin sirri, bawai muna neman yardarki ko amincewarki bane, dole kiyi abunda zamu umarceki inba haka ba rayuwarki da rayuwar iyayenki zata salwanta’’ Wani irin quuu cikin sabeeha ya bada lokaci guda, take taji wata irin zufa ta keto mata babu shiri, abu daya ne kawai ya fado mata rai a daidai lokacin nan shine ambaton allah, cikin gaggawa ta soma allahumma ajirni fee musibati, harta dan soma daidaitawa, tafin hannunta babu abunda yake sai zuba. Mutumin ne ya sake Magana da larabci harya kai aya kafin daya ya sake fassara mata, ‘’aikin da zakiyi mana aiki ne mai sauqi na leken asiri,sannan kinada kaso mai yawa a ciki idan muka samu abunda muke nema, akwai takardar yarjejeniya da sa hannunki a ciki,saboda haka kamar yanda nace komai cikin sirri za ayi, idan har kika bari asirin mu ya tonu to rayuwarki da rayuwar mahaifiyarki da rayuwar duk zata shiga hadari,’’ Wata waya mutumin ya tura mata gabanta, sai a lokacin ta dan dago, bata yarda ta hada idanu dashi ba saboda harda soma hawaye tsarabar rudanin data shiga. ‘’ga wannan wayar, zamu dunga kiranki don jin bayanan da zaki samo mana,’’ Balaraben na kaiwa nan ya miqe ya fuce daga dakin, shiko interpreter kallonta ya cigaba dayi yana mai jin tausayinta, ita kuma kaddararta Kenan? Ina tasan waennan mutanen har sukayi clashing da ita. ‘’zan baki shwara daya yarinya, kiyi abunda suke so inba haka ba duk abunda suka fada hakan zai tabbata’’ Sai a lokacin ta dago ta kalli mutumin, typical bahaushe ne dukda shigar da yayi ta larabawa kana ganinshi kaga bahaushe. Mikewa yayi ‘’muje ko’’ yayi gaba ta bishi a baya, da kyar take daga kafafunta don sun sage, har izuwa lokacin babu abunda take sai innalillahi a zuciyarta har suka shiga motar. Tafiyar munti talatin sukayi kamar tafiyar bazata kare ba, sabeeha dake zaune gaba daya ta gama hargitsewa futsari ne kawai batayi ba a zaunen nan, babu abunda ke mata yawo akai sai maganganun wannan mutumin da ko fuskarshi kasa kallo tayi don daga yanda yake Magana bazaiyi Imani ba. ‘’leken asiri? Wani irin leqen asiri ne zatayi kuma idan batayi ba za a kashe mata iyayenta harda itama?,’’ abunda take tambayar kanta Kenan tana kuka kamar yarinya. Yanda take kukan ma cikin sanyi abun tausayi, sautin kukan ma baya futa kwata kwata, sai ajiyar zuciya. Alamun tsayawa da akayi da mota ne yasa ta dan dago kanta, nan take cikin ya sake hautsinewa don bata taba ganin mahaukacin gida mai shegen girma ba kamar wannan, dukda garin yayi duhu hakan baisa anguwar tayi haske ba bauu kamar hasken rana, saida aka gama buncikar su tsaf don ta baya suka biyo saboda tanan ne outsiders ke shigowa ko idan za ayi delivery na wasu abubuwan amfani, front gate kuma masu gidan ne ke shiga tanan sai family relations haka. Parking driver yayi kafin ya futo ya bude mata kofar baya, futowa tayi anatse jikinta kamar an fasa kwai. Driver na gaba tana biye dashi ta baya har suka karaso wata kofar shiga ciki, daga bakin kofar ya danna bell din shiga, cikin yan mintuna qalilan aka bude kofar. Kallonsu maid din tayi daga shi har sabeehan kafin ta buqaci sanin zuwan su, drivern ne ya miqa mata takardu bayan ya mata bayanin daga inda yake, matar na ganin haka ta tsaidashi kafin ta koma ciki. Bata dade da shiga ba saigata ta dawo da papers din a hannunta, wasu yan maganganu tayi mashi kafin ya juya yayi tafiyarshi yabar sabeeha anan tsaye. Maid din kuwa kallonta ta dunga yi daga sama har kasa kafin ta mata nuni da cikin gidan. Sauke ajiyar zuciya tayi kafin ta sanya kafafun ta, wani irin sanyi taji tare da sauyin bugun zuciyarta lokacin data sako kafarta cikin backyard din,da garden ta fara cin karo inda yasha kayan lambu da flowers masu kyan gaske, ko’ina fes fes sai haske daya bade ko’ina, haka suka miqi hanyar backyard dinnan har zuwa wata kofa again daga chan gefe, ciki suka shiga, ashe hanyar backdoor ne da zai kaika zuwa kitchen, yanda fadi da girman da kitchen din yake da saida gaban sabeeha ya fadi, mata ne a cikin kitchen din don zasu kai su kusan biyar, kowacce tana ta faman shige da fuce da warmers, wasu daga cikinsu kuma suna yin dishes a cikin machine, wasu kuwa sorting kayan abunci suke a cikin freezer da store. Kallonta maids din suka dunga yi, kowannen su ya zuba mata idanu sai yan qus qus da suka fara yi suna nunata har suka fuce daga kitchen din ita da matar. Wata hanya suka miqa har zuwa wasu dakuna dake nan ajere har kusan guda biyar, daya daga cikin dakin matar ta bude suka shiga sabeeha na biye da ita. Daki ne babba mai dauke da bunk bed guda biyu, kowannen sama da kasa, dakin fess fess babu qazanta saima kamshi da sanyin ac dake tashi, kowanne bunk akwai wajen ajiyar belongings din mai gadon. Empty gadon dake kasa matar ta nuna mata, kafin ta soma Magana cikin larabci, ‘’wannan ne gadon ki, ki huta zuwa gobe za’a nuna maki ayyukanki okay?’’ Kallon bakinta sabeeha ta soma yi don fahimtar abunda ta fada saida takai aya kafin tayi mata nuni da gadon, nan ta fuskanci abunda take nufi gashi daman ta dan soma koyon larabci ba laifi. ‘’shukran’’ sabeeha ta amsata cikin natsuwa. Matar na fita sabeeha tabi dakin da kallo, fatanta allah yasa ba ita kadai zata kwana anan dakin ba don tunda suka shigo hankalinta yaqi kwanciya, sai take ganin kamar idan ta rufe ido a cikin gidan za a iya kasheta saboda yanda abun yayi yawa, daga kan tsaruwar gidan da girman gidan ma. Gefen gadon da matar ta nuna mata ta zauna tana mai tuna abunda mutumin nan ya fada mata, wannan ay an kawota inda zata hallaka ne, tunanin dalilin kawota ta dunga yi, meysa zasu kawota liken asiri? Me zatayi masu? Meysa sai ita?’’ haka ta dunga tambayar kanta babu amsawa. Tunawa da batayi salla ba yasa ta nufi wata kofa dake cikin bedroom din, as she expect toilet ne babba ma kuwa mai tsafta. Alwala ta fara yi, tana gamawa ta soma jin surutai daga cikin dakin, tana futiwa kuwa ta tadda maids guda biyu, abunda ta lura dasu shine uniform din dake jikinsu ba irin na waenda ta gani bane, gashi kuma kowanensu daga wata kasa daban aka kawosu saboda yaren data ji sunayi. Zuba mata idanu sukayi yanda itama ke kallonsu cikin face mask dinta, hijab kuwa yana nan maqqle a jikinta kamar matan malam, kwata kwata bata rabo dashi. Saurin sauke kanta tayi ganin yanda suke mata wani irin kallon mai kama da na tausayi. Wajen gadon ta ta nufa ta zauna tana mai tunanin yanda zata tambaye su gabas, gashi bata san ta yanda zata fara ba. Bude kofar da akayi ne yasa suka dago gaba dayan su, kallon wadda ta shugo sabeeha tayi, kanta daure yake da dankwali ba kamar sauran ba sannan gata dai baqar fata ce saidai bata tantance koi ta din yar ina bace ba don batayi kama da Nigerians ba kwata kwata, kamar irin kabilun nan na yankin Africa. Takowa budurwar tayi inda sabeeha take kafin tayi mata murmushi, itama murmushin ta maida mata dukda baa a ganin fuskarta. ‘’sannu fa whats your name’’ ‘’sabeeha’’ ta amsata cikin natsuwa. ‘’where are you from?’’ yanda budurwar ke Magana sounds so friendly hakan yasa hankalin sabeeha dan kwanciya kadan kafin tace ‘’nigeria’’ Da mamaki budurwar ta kalleta don tabbatarwa, dukda bata ga fuskanta da kyau ba saidai idanunta da yanayin girarta yasa budurwar cewa ‘’nigeria hausa igbo or Yoruba?’’ Da mamaki sabeeha tace ‘’hausa’’ ‘’wow!! You’re hausa?, by the way I’m from Africa as well but Ghana, and I can speak hausa as well but not flueintly’’ ‘’nima na zauna a Ghana da mamana’’ sabeeha ta amsata Sama sama budurwar ta dunga janta hira har sabeeha ta tambayeta gabas, nan ta nuna mata, ba karamin dadi sabeeha taji ba data hadu da wannn yar Ghana din, taso ace ma dakin su daya saidai ita abunda ya shafi harkar kitchen take, abunda yasa tazo yanxu ma saboda ta tambayi ko sabeehan musulma ce don ita kadaice musulma anan bangaren maids. Sallah kawai tayi, ta dade sosai a zaune tana rokon allah, har wannan yar ghanan ta sake dawowa ta kawo mata abunci don taci. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 13-14 Update!!!! Ba karamin dadin haduwa da yar Ghana nan yayi ma sabeeha ba dukda ita bata iya sabo da muamala da mutane ba.Saidai ita wannan akwai jan mutane a jiki sosai hakan yasa ta jin dan sauqin abunda take ji aranta. Sauran yan dakin kuwa wani irin kallo suke mata,babu wanda yace mata ci kanki a cikin su, daman su uku ne kawai sai ita kuma ta hudu. Karfe sha daya nayi duk suka fara shirin kwanciya daman saboda sai an gama hidimar gidan kuma sai masu gidan sun kwanta kafin suma su kwanta saboda karsu buqaci wani abu. Sabeeha dai na kan gado tana rarrabaa idanu har suka kashe fitilian dakin, ganin haka yasa itama ta kwanta cikin fargaba, ga saqe saqen da zuciyar ta ke mata game da maganganun wannan mutumin da bata ma san koshi waye ba, menene aihanin kudirinshi akanta? Meysa sai ita? ga nan wajen da aka kawota da sunan leqen asiri bata ma san taqamaimain mey zatayi anan din ba. Hawaye ne masu dumi suka soma ambali akan fuskanta, tunawa da mahaifiyarta babu abunda take tambayar kanta akai sai ‘’meyzaisa mahaifiyarta ta turo ta nan?, shin haka daman kowa ke rayuwarshi ko kuwa itace rayuwarta tazo a haka? Bata san mene farin ciki ba ko kadan dukda tana masifar qaunar mahaifiyarta, tana farin ciki da ganin mahaifiyar.’ Tana cikin wannan tunanin tana hawaye har barci ya zugeta mai nauyin gaske saboda makwancin data samu is confortable, gado ne daidai mutun daya ga bargo harda ac a dakin nasu. Karfe biyar daidai karar alarm ya karade bangaren nasu na ma’aikatan gida, afurgice sabeeha ta mike zaune don yanda karar ya sauka a kunenta saida yasa gabanta yayi mugun bugu, hasken dakin nasu ne daya bade ko’ina yasa ta duban dakin da kyau, daya bayan daya waennan maids din suka soma saukowa daga gadajensu cikin gaggawa, bandakin nasu suka fara shiga daya bayan dayan kamar yan boarding kafin suyi shiri ciki uniform dinsu na aiki tsaftsaf, kallonsu sabeeha ta dunga yi har suka gama suka soma fita daga dakin, tana jinsu suna yaren su suna kallonta har suka fice ba tare da sunce mata ci kanki ba. Ita kuwa da mamaki ta bi kofar da suka fita da kallo,komai looks so weird to her, gashi bata san mey zatayi ba ganin duk sun fita gaba dayan su. Tana nan zaune wadda ta shigo da ita jiya ta shigo dakin,gasheta sabeeha tayi kafin matar ta soma yi mata bayani, da farko wajen drawer ta nuna mata inda kayanta na aiki suke ajiye dasu toothbrush harda pad da dai sauransu. ‘’rule number shine ki kasance cikin tsafta koda yaushe,ki shiga kiyi wanka saiki saka uniform dinki ki fito’’ matar ta fada Tana kaiwa nan ta fuce tabar sabeeha a tsaye, kamar yanda matar nan ta umarce ta hakan kuwa tayi, tana yin wanka ta saka uniform din ta zumbula hijab tare da mask dinta kafin ta fito daga dakin. Koda ta fito rasa hanyar da zatabi tayi don kofofin wajen sunyi yawa, saida ta jiyo hayaniya da karar kwanuka da cokula daga wani saseh daban haka yasa ta nufi hanyar, allah ya taimaketa kuwa hanyar kitchen ne, da sallama ta kara kitchen din muryarta chan kasa kasa, gaba daya maids din kowannen su yana ta hada hadan ayyuka babu wanda yabi ta kanta, wannan matar kuwa na tsaye sai bada orders take, ayi wanchan ayi wannan, daman itace ogansu gaba daya, saida ta lura da sabeeha a gefe tukunna kafin ta doso inda take. Kallonta daga sama har kasa matar tayi, nan take ta hade rai tamau ‘’rule no 2, you cannot dress like this, its so unhygienic, bakisan protocols din aykin ki bane’’ Kallon bakinta sabeeha ta dunga yi don kwata kwata bata gano inda matar ta nufa ba, saidai yanayin yanda take Magana strictly hakan ya tabbatar mata da kamar tayi abunda ba daidai ba, wannan yar ghanan nan ce ta matso inda suke ta fassara mata kafin ta koma wajen aykin ta don matar akwai masifa. Komawa dakin su sabeeha tayi cikin tashin hankali, ita kwata kwata bata saba yawo haka ba ko agida ma, idan ta saka kaya babu hijab dinnan sai taji kamar tsirara take yawo, wannan yasa koda yaushe take yawan saka hijab. Haka nan ta hakura ta soma zare hijab din nata harda dan hawayenta, tana cireshi ta ninke ta ajiyeshi gefen gadon kafin ta fuce daga dakin. Kitchen din ta koma, daidai nan daya daga cikin maid din dake futa da abunci a cikin wani serving trolly ta shugo kitchen din, sabanin sabeeha na tsaye daga bakin kofar suka kusa yin karo da juna, wanda hakan ya janyo attention mutanen kitchen din ya dawo kansu ‘’excuse me, watch your step please’’ Maid din ta fada tana mai kallon sabeeha, itama kallonta sabeeha tayi kafin ta sauke idanunta hannunta na gaban rigarta tana kokarin kare kirjinta. Gaba daya kitchen din zuba mata idanu sukayi, gata dai bata da kiba kuma itadai bazaace mata doguwa ba kuma baza a kirata da gajeruwa ba saidai allah yayi mata sura mai fuzgar hankali, baga mace bama balle namiji, full option, she’s well curved and pictured kamar an zana surarta saboda yanayin kayan jikinta riga da wando na aiki Kenan. Tsugunnawa tayi ta kwashe savage din da suka zube a kasa kafin ta miqa ma maid din dake tura trolly din, ….No wonder take ta fama kakkare kirjinta ashe a cike suke kamar zasu yaga rigar jikin nata kuma daidai jikinta, a hakan ma bata ji hutu ta koshi bama tukunna,masha allah kamar yar Brazilian don sune masu irin perfect shape dinnan da ba kowa keda irinshi ba, one ina million Kenan. Gyaran murya da akayi ne yasa duk suka koma kan ayyukansu, sabeeha dai na daga tsaye a gefe tana kallonsu suna abubuwan su cikin kwarewa. ** Cikin isa ta soma sauko daga stair din cikin shigarta mai aji, babu abunda kake ji sai sautin takalminta da kamshinta, hanyar dining ta nufa hannunta rike da Jakarta. Waigowa sukayi gaba dayansu suna kallonta daya bayan daya harta karaso dining din, itama binsu tayi da kallo, suna zaune har sun fara karyawa, afiya, fadwa da barad. Wajen zamanta ta nufa kafin gaba daya suka soma gaisheta, amsa su tayi kafin maid din dake tsaye ta soma serving dinta as usual, daman ita bata cin abunci sosai daga coffee sai dan low calories English breakfast. Baka jin komai sai karar cokula a dining area din, fadwa ce ta fara gama breakfast din kafin afiya, basuyi gigin tashi ba saida hidaya ta gama tukunna kafin ta miqe tana mai duban afiya dake zaune ta hade rai. Barad ne ya fara futa daga dining din yana mai kissing din aunties din nashi a kuma kafin yabar dining din. ‘’naga kinyi requesting for kudade masu yawa,na tura maki approval letter’, anything else’’ ta karashe tana mai dubansu su biyu Da mamaki duk suka dago suna kallonta, don kwata kwata basuyi expecting haka daga wajenta ba. Kallon juna fadwa da afiya sukayi kafin suyi murmurshi, godiya sukayi mata kafin ta fuce daga dining din, head of maids na biye da ita da Jakarta a hannu. ‘’Ma’am yarinyar da aka kawo wadda zata kula da part din sir…’’ Tsayawa chak hidaya tayi tana wani nazari kafin ta dubi head of maids din, ‘’I trsut her with you make sure ba a samu matsalar da aka samu ba da previous one’’, ‘’okay ma’am’’ Maid din ta bata amsa kafin ta rufe mata matar dake janta zuwa office, barad na daga gefenta don ita ke kaishi school da kanta. Futar matar nan ce daga kitchen din ya baima yar Ghana daman jan sabeeha, gaisawa sukayi kafin yar Ghana ta soma tambayarta akan aikin da aka bata. ‘’a bangaren ina aka saka ki?, girki ko gyare gyare?’’ ‘’bata fada min ba’’ sabeeha ta bata amsa cikin nutsuwa Nunfasa yar Ghana tayi kafin tace ‘’hmm ina maki fatan dai a wannan bangare guda biyu zaki yi aiki don…’’ Zuba mata idanu sosai sabeeha tayi don jin abunda take shirin fada, ganin haka yasa yar gana rage murya don suna da dan yawa a kitchen din ‘’kinga ayki a gidan nan yana da wasu qalubale daban daban,’’ Samun kanta tayi da cewa ‘’menene qalubalen?’’ Nunfasawa yar Ghana tayi kafin tace ‘’akwai wani part a sama wanda muke kira da demon palace, mudai da muke aiki anan kasa bamu taba zuwa saman ba kuma basusan menene a saman ba, saidai muna kallon duk wadda aka tura aiki chan saman bata wuce kwana daya biyu tabar aiki a gidan nan, a yanda naji ma wadda ta dade da ayki a bangaren bata wuce sati guda ba tabar gidan nan a burkice, shiyasa na tambaye ki don sanin inda zakiyi aiki’’ Wani tunani ne ya fado ma sabeeha nan take ta danji gabanta ya fadi, ‘’menene a saman to?’’ Yanda tambayar ma ta futo daga bakinta ita kanta batayi tsamanin haka ba. ‘’hmm babu wanda ya sani, saboda duk waenda sukayi aiki acahn din basa fadin komai game da part din, mudai musan nothing comes good daga part dinnan, wata qila wani mummunan abu ne a wajen’’ Bata kaiga idawa ba sukaji alamun matar ta dawo kitchen,lokacin wajen karfe tara na safe, kallon inda sabeeha take matar tayi kafin tace ‘’muje’’ Binta abaya sabeeha tayi har suka fuce daga kitchen din, girgiza kai kawai yar Ghana tayi tana mata fatan allah yasa dai ba saman za a kaita ba, don idan da anan kasa zatayi aiki da tuni head(head of maids) ta nuna mata ayyukanta, bangare su sabeeha kuwa zuba idanu ta dunga yi don ganin inda za a kaita don ba karamin tashin hankalinta yar Ghana tayi ba da batun part din saman nan da babu wanda yasan menene a saman, binta kawai take a baya har suka shiga cikin gidan tana sauraron bayanan da take mata. ‘’madam bazata samu ganinki ba, so ni zan maki bayanin ayyukanki’’ Girgiza mata kai sabeeha tayi kanta a kasa har suka soma hawa sama, ita tunda suka shigo ma ta burkice don baza ta iya cewa ga daga inda suke fito. ‘’aikinki ba kamar kowanne aiki bane, record dinki ya nuna kin kware ta bangare caregiving, so ina fatan baza a samu wata maatsala ba, sannan akwai rules din ayyukanki, abu na farko da zaki kiyaye dashi shine your job is confidential, you can not tell anyone irin aikin da zakiyi da condition din sir, idan kika kuskura kika fada kuma’’ Dan tsayawa matar tayi kafin ta juyo ta maida dubanta ga sabeeha,’’ba sai na fada maki mai zai buyo ba, just keep that in mind’’ Dam dam gaban sabeeha ya bada, idan har batayi kuskure ba wannan aikin da za a bata shine aikin da aka turo ta tayi liken asiri akai ko menene?, maganar mutumin nan ce ta fado mata arai ‘’idan kinje zaki san irin aikin da zakiyi’’ Tabbas wannan ne abunda yake nufi Kenan, hannunta har wata irin zufa ne ke tsatsafo mata, sai a lokacin ma ta lura da stairs suke hawa. Haka suka dunga hawa stairs din mai tsayi kafin su iso saman, kallon wajen sabeeha tayi kirjinta na tsananta bugu kamar ana buga ganga, bin matar ta dunga yi kamar raqumi da akala har suka karaso petion din dake tsakanin part din guda biyu. Nuni head tayi mata da bangaren hannunta na dama ‘’babu ruwanki na nan bangaren, sannan chan’’ Tayi mata nuni da dayan part din, ‘’anan ne zaki yi aikinki as a caregiver’’ Takowa suka soma yi har zuwa part din kafin head din ta dannan security pins, ‘’wannan ne pin din shiga ciki, daga ni sai wadda zata kula da wajen sai madam ne kawai muka san pin din, kin gane me nake nufi?’’ Girgiza kai kawai sabeeha tayi kafin su shige ciki, suna shiga maid ta rufo kofar, nan take haske ya bade ko’ina hanyar walkway zuwa cikin part din, gefen wajen kofar maid din ta dan latsa wani electric dispenser nan take sanitizer ya futo, hannunta tayi sanitizing kafin ta umarci sabeha datayi hakan itama. Tana gamawa ta soma cire takalmin kafarta daga gefe akwai wani rack da aka jera crocs, daya head ta dauka kafin ta bama sabeeha dayan. ‘’rule number 2, you should be very clean sosai, sannan duk sanda kika shugo ki tabbatar kin saka mask and kinyi sanitising hannunki, uniform dinki should be clean as well,ko digon datti a kayanki is not allowed’’ Girgiza mata kai tayi alamun gamsuwa dukda a tsorace take sosai,ciki suka fara shiga, haske ne ya gauraye ko’ina bau nan take komai ya bayyana, parlor ne mai girma da kyau fari qal komai is organise babu wani karikice sai camera’s ta kowanne lungu da sako acikin parlorn. Sabeeha dai bata ma tsaya duban parlorn da kayu ba don tunaninta yayi nisa da abunda matar nan ke fada ma da wanda yar Ghana ta fada mata ga kuma wanda aka turo ta akai. Saida suka zo dan nesa da kofar dakunan cikin part din matar ta tsaya, ‘’karfe shida zaki fara aikinki, sannan daga inda karfe hudu tayi ki tabbatar kin gama komai kin sauka kasa, daya daga cikin ayyukan da zakiyi shine gyaran part din nan, akwai kitchen da duk wani abubuwan buqata,’’ ‘’the most important part of your job shine,kula da movement din sir,da abuncinsa, sai medication dinsa,sannan akwai timetable din abunda yafi buqata on a daily basis zaki samu wannan a kitchen, and lastly I will advice you duk abunda zakiyi kiyishi cikin natsuwa banda hayaniya saboda baya son hayaniya.’’ ‘’waye kuma sir?’’ abunda ya fado ma sabeeha arai Kenan, tasan me caregiver ke nufi, saidai abunda bata gane bane shine dalilin da yasa aketa wannan boye boyen da wannan ka’idojin, komai looks so strange. Kofar dake facing dinsu suka nufa, nan matar ta bude ta soma mata bayani, ‘’nan ne activity room din sir, duk ranar Friday zaki dunga kawoshi nan’’ Kallon wajen sabeeha tayi, wajen cike yake da kayan wasa na yara, babu abunda babu mota ne jirgi da keke dadai sauransu da mamaki take kallon wajen har suka fito daga dakin. Nuni da kofar tsakiya matar tayi kafin tace ‘’nan ne kuma bedroom din sir,first thing first by 8 dot yake tashi so duk abunda kikeyi na gyara ki tabbatar kin gama kafin lokacin, idan zaki shiga bedroom din ba’yin knocking saboda baya son any sound ko karar komai, zaki bashi first medication dinshi by 8:30 dot, sannan kafin yaci abunci zaki taimaka mashi yayi wanka ya shirya by 9 zaki bashi breakfast, sai second dose of medication dinshi’’ Jin haka yasa sabeeha shiga tunanin waye wannan sir din, kalaman matar dataji ne da yanda komai suke yin shi cikin tsari da ka’idoji yasa ta soma tunanin to kodai raino aka sake kawota, to amma rainon da zatayi ne leken asiri?, ita gaba daya ma kanta ya burkice da ala’amarin, ‘’that’s all for now, zuwa gobe zaki fara’’ matar ta karashe tana mai nufar hanyar futa daga part din sabeeha na biye da ita a baya. Kasa suka sauka, maids din dake gyara gyare suna kallonsu ta wutsiyar idanu kamar hankalisu baya kansu, saida sukaga head ta wuce kafin daya daga cikin su ta soma Magana kasa kasa ‘’nandini, ayna fada maki, wannan a sama zatayi aiki kai amma I pity her,’’ Dayar da aka kira da nandini ce tace ‘’to me she looks like she’s happy, bata san inda ta jefa kanta ba, ki duba kiga yanda last maid dinnan ta gudu, ta bani tausayi ko kwana biyu bata yi, ni im curious wallahi, menene a saman nan’’ Matsowa dayar tayi ta rada ma nandini wani abu a kunne……… Bayan sun sauko daki sabeeha ta koma na bangaren su, tana shiga babu kowa a dakin don koda suka sauko daga sama ta gansu suna aikace aikace anan kasa, daman yan dakin nasu bangaren aikace aikace suke handling. Zama bakin gadonta ta doka uban tagumi, tunani kala kala na yawo a kwanyar kanta. California…… Envision academy high school……. School Bus ce ta fito daga cikin school din, dauke da student, babu abunda ke tashi a cikin bus din sai hayaniyar yara, maya da gang dinta na zaune daga gefe su uku ashe wata yarinya suka saka a gaba suna bullying,yarinyar na gabansu a tsugunne maya ta daura kafar ta akan labs din yarinya, su kuma student me zasuyi banda dariyar mugunta, saida aka zo first stop kafin wasu few daga cikin student din suka fita daga cikin motar ciki kuwa harda maya da kawarta inda suka shige cikin yaran da suka futa don kar a gansu. Suna fitowa maya da kawarta kloe suka yanki wata hanya cikin sauri gudun kar driver yayi noticing din futar su, saida sukayi ma bus din nisa kafin su dan tsagaita, dariya kloe ta fara kafin ta maida dubanta ga maya ‘’kai babes this is the toughfest part of running away from school, I can’t wait to be 18 and free muyi mu gama exams’’ ‘’hmm, nima kaina na gaji da guje gujen nan just to have fun, meysa sai lallai mutun ya zama 18? Other countries baa yin haka’’ Daidai nan suka karaso kan titi inda wata mota ke parke daga gefe, cikin hanzari suka karasa wajen motar, maya na gaba while kloe kuma na daga baya. Suna shiga wanda ke zaune mazaunin driver ya miko hannu zai rungumeta, ‘’come here babe’’wani irin kallo ta watsa mashi wanda ya sashi komawa mazauni yana mai kunna mota, saurayi ne white American yasha wasu kananun kaya, daga baya kuma kloe ce ita ma da nata saurayin black American, Wanda ke bayan ne yace ‘’girls where are heading to?’’ Maya ce tayi saurin cewa as usual, tana kaiwa nan wanda ke tukawan ya zugi motar suka bar wajen. Basu tsaya a ko’ina ba sai a wani wajen shakatawa, wajen kamar restaurant, ciki suka shiga, inda daga nan basu tsaya ko’ina ba sai wani sirrintaccen bangare dake cikin restaurant din, kamar koda yaushe zaida wannan black American din yayi Magana da mai wajen don abokin yayansa ne kafin abarsu su shiga ciki don ba a yarda underage su shiga. Wurin so very dim sai blue light kamar dare, maza da mata na zazzaune kowanne yana harkarshi da drinks a gabansu wasu kuma na cin abunci wasu kuma hayaki suke busawa. Zama sukayi wajen da suke zama koda yaushe inda sukayi nasu order drinks din, wannan white ameriacn dinnan dai yana kusa da maya, da alamu saurayinta ne don daga yanda yake ta faman bata hakuri kamar yayi mata laifi ne. ‘’shut up u cheater,’’ ta daka mashi tsawa wanda yasa hankalin kowa ya koma garesu ‘’maya please’’ kloe ta fada tana kallonta don suna zaune opposite dinsu. Hannunshi ya sake sanyawa ya riko nata ‘’bebz please im sorry, there nothing between us, its just accidental kiss please’’ Ajiye juice din maya tayi ta maida dubanta gareshi, ‘’you’re a cheater and a liar, you think I’m stupid? Kiss by accident? For goodness sake rick Zara is my friend, how could you kiss her and call it by accident, I see both of you with my 2 eyes’’ Shima saurayi harzuka yayi yana mai kallonta ‘’look, I don’t fucking care about the kind of thought you have on this, how many times do I have to apologies, I’m done please’’ Kallonsu kloe tayi da saurayinta don ganin yanda zasu kare, kamar yanda sukayi hasashe kuwa sai gani sukayi maya ta sauko lokaci guda, don bata taba taba yarda yayi fushi shima don tana masifar son nick kamar ranta, shiyasa duk abunda yakeyi take daga mashi kafa, gashi bai wani girmeta sosai ba, he’s just 22. ‘’okay but promise this should be the last time’’ Amsata yayi yana mai hugging dinta so tightly, ganin haka yasa kloe gyaran murya tana mai duban saurayinta tace ‘’I told you, bazata iya hakura dashi ba’’ ‘’what are you gossiping?’’ maya ta karashe tana duban kloe da saurayinta, kafin ta tabe baki ta maida dubanta ga black American dinnan tace ‘’ I cant stay long guys, daddy nay a dawo and its been a week now bai koma ba, my phone has been seized, so lets just do what we have to do, how far with the?’’ Bata gama fada bama ya zura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wata yar takarda ya ajiye a gabansu kowa ya tura mashi gabansa harda maya. Wani irin murmushi maya tayi mai wuyar fassara kafin ta dauki nata nannadaddiyar paper ta soma warwarewa jikinta har tsuma yake….. ** Abuja Nigeria. Gidan Marigayi alhaji santuraki.. Safiyar juma’a Kenan, yau gidan a cike yake tam saboda dama duk Friday ake taruwa a cikin main house bangaren Anne duk da estate daya suke kuma kowa da part dinshi. Matan uncle Sameer babban dan gidan anne kennan da aunty fadila da iyalanta duk sun hallara ga jikoki harda da yaya ma. Rana irin ta yau ta zame masu kamar double celebration saboda ayau uncle Sameer zai dawo daga Europe after shekara daya Kenan da tafiyarshi zuwa wani course. Yaran duk suna zaune a sitting room na kasa don gidan nada girma sosai while iyayen su kuma suna sama wasu kuma suna kitchen ana hidimar girki dasu. Anty Laila (uwar gidan uncle sameer)ce ta shigo dakin da sallama don zuwanta Kenan gidan, don bata samu tazo da wuri ba saboda ta dan tsaya don shirye shiryen tarbar mai gida don anan gidan ta zai sauka, Da sallama ta shugo cikin dakin, anne dake zaune akan gado da wasu tarkacen takardu a gefenta ne ta dago ta kalleta tare da amsa sallamarta fuskanta babu yabo ba fallasa, nanna ce ma dake zaune kan kujera tana cin dambun sadakar Friday da aka kawo ne ta kallata cikin fara’a tace ‘’ah ah matar babban yaya sai yanxu’’ Sunkuyar dakai anty Laila tayi harta karaso tsakiyar dakin ta zauna kan carpet tace ‘’barka da hutawa nanna, barka da huta wa anne’’ ‘’barka dai’’ suka amsata a tare ‘’ya iyali, yau mai gidan naku zai dawo ko’’ nanna ta fada tana mai kallonta ‘’eh yau zai dawo insha allah’’ ‘’toh masha allah ga dambu bismillah’’ nanna ta fada tana mai kallonta ‘’alhamdulillah nanna, sai zuwa anjima zan diba’’ Shuru ne ya biyo baya adaidai lokacin fadila ta shugo dakin hannunta rike da mubin, yaron(aunty mubina) amaryar uncle sameer kenan. ‘’mubin dai akwai barci yaron nan shiyasa yake burgeni’’ Jin muryarta yasa suka dago suka kalleta banda anty Laila da kanta ke kasa, kallon inda take fadila tayi kafin tace ‘’ashe kin iso’’ Kamar anty Laila bazatyi Magana ba tace ‘’eh yanxu na shugo’’ Tana kaiwa nan ta mike ‘’bari na sauka kasan’’ Nanna ce kawai ta amsa ta da toh, anne kuwa hankalinta na kan pappers din dake gabanta, anty fadila na kwantar da mubin ta dubi hanyar futar da anty Laila tayi kafin ta tabe baki tace ‘’hmmm’’ Kallonta nanna tayi fuskanta ya dan sauya tace ‘’haba fadila, har yanxu dai bakwa jituwa da yayar taki?’’ ‘’nanna bazaki gane bane, Tsakani na da ita waye ya kamat ya gaisar da wani?’’ Rai adan bace nanna tace ‘’lallai fadila, karkiga wai don tare kuka taso, matar wan k ice kuma uwar yayansa, dole ki bata respect dinta, anne kina kallon wannan shashanci da girmansu’’ Sai a lokacin anne ta dago ta kallesu cikin glass din dake fuskanta ‘’ay sun san daidai basai nayi Magana ba, and besides ita da take babba itace ya kamata taja girmanta’’ ‘’anne please karki goyi bayan kowa a alamarin nan saboda wani abu chan daya faru a baya wanda ya zama tarihi’’ Kallon yar uwar tata anne tayi tace ‘’hajara!!’’ Jin yanda anne ta kira nanna yasa anty fadila fucewa daga dakin, tana futa kuwa anne ta kalli nanna tace ‘’bana son a sake maimaita maganar nan, bana bin bayan kowacce a cikin su, laifin shi Sameer dinne daya bar hakan ta kasance shiyasa bana Magana akai’’ Nunfasawa nanna tayi kawai kafin ta maida hankali wajen abuncin da take ci. Fadila na futa daga dakin kuwa ta sauko kasa zuwa kitchen, a tsaye ta tadda anty mubina da masu aiki suna ta hidima, karasowa tayi har inda suke tayi kafin tace ‘’amaryar babban yaya, baki koma daki kin hutaba?, kije ki huta tunda mubin yayi barci nakaishi dakin anne’’ Juyowa mubina tayi hannunta duk flour gashi tasha apron da alamu dai aykin takeyi bil hakki da gaskia, ‘’anty fadila ay mun kusa gamawa, cake dinne kawai ked an daukan lokaci’’ ‘’toh shikenan, bari naje na dubo ko hamad sun dawo daga kai sadakar tunda naga an sauko daga masallaci, wannan yar banzan yarinyar ashe guduwa tayi ta barki’’ Dariya kawai mubina tayi kafin ta maida dubanta ga ayyukan dake gabanta. Anty Laila kuwa bayan ta futo kasan ta sauko ta hakimce akan kujera, tana nan zaune fadila ta sauko ta wuce kitchen harta futo daga kitchen din ta sake komawa sama, su inti da amla da kareem sai wasansu suke…. Basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara da rabi bayan kowacce taje tayi ma anne sallama. Part din anty Laila yana opposite na anty mubina, sai part din anty fadila dake chan nesa dasu sosai, sai kuma wani part din daban, duk sun zagaye bangaren anne dake a tsakiya……. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 15-16 Update!!! Saudi Arabia…!!! Washe gari da safe kamar safiyar jiya haka alarm din bangaren ma’aikata ya soma qugi, agurguje kowa ya tashi duka maaikatan harda sabeeha, lokacin wajen karfe biyar daidai. Sabeeha na zaune cikin hijab dinta kamar ko da yaushe, saida suka gama kafin ta shige bathroom din tayi wanka tare da dauro alwala, saida ta gama ta maido da hijab dinta ta futo daga bathroom din. Agurguje tayi shirinta cikin uniform lokacin kusan duk maaikatan dakin duk sun fuce, aggagauce itama ta gama saka kayan nata ta tada kabbarar sallah, tana idarwa ta cire hijab din ta ninkeshi a gefe kafin ta zura mask dinta ta fuce daga cikin bangaren nasu. Anatse take tafiya kamar wadda kwai yafashe ma a jiki, jikinta duk a mace game da wannan sabon almarin cikin rayuwarta wanda ya hanata sukuni, tunani iri iri daban daban nayi mata yawo akai ga tsoro ga fargaba. Lokacin data shugo main house babu kowa a kasan hakan ya bata damar tsayawa don yin nazarin inda zata bi kafin taje saman,tana cikin wannan tunani sauran masu gyaran main house din suka shigo suma, bin inda suke bi itama ta soma yi harta gane inda zata nufa. Lokacin data karaso saman bin wajen ta soma yi da kallo, nan take idanunta ya sauka dayan bangaren nan, wani abu ne yazo ranta kafin ta yaqice ce ta nufi part din da zatayi aikinta. Tana zuwa bakin kofar ta tsaya ta saka pins din tare ba bude handle din kofar ahankali kamar mara gaskia, tana budewa ta sa kai ciki. Tana shugowa wajen ya bade da haske, sanitizing hannunta ta farayi kafin ta cire takalmin dake kafarta ta zura crocs kamar yanda head ta nuna mata jiya, tana gamawa ta wuce cikin parlor. Bin ko’ina ta soma yi da kallo kamar yaune ta taba ganin wajen, babu digon datti ko daya saima kamshi dake tashi, kwata kwata batayi gigin kallon wannan kofofi guda biyu ba saima dayar kofar dake wajen dining data nufa wanda haka ya tabbatar mata da nan ne kitchen, hanyar tabi ta shige cikin kitchen din a natse kafin ta sanya hannu ta tura kofar. Gasping breath dinta tayi tare da sauke ajiyar zuciya saboda yanda kirjinta ke bugawa tunda ta shugo cikin part din wanda ta alaqanci hakan da fargabar da take ciki, dan yanxu ta qayyade koma menene a nan saman to abun cutarwa ne saboda tunawa da maganar da yar Ghana tayi mata akan cewa previouse ma’aikatan da sukayi aiki anan din ko kwana biyu basayi suke barin aiki anan saman shiyasa kowa ke tsoron nan din, ga yanda aka zuba uban dokoki. Sauke ajiyar zuciya tayi tana mai addua aranta na neman tsari ga allah, ta dan dade a tsaye tana rarraba idanu kafin ta yunkura ta fara duban ko’ina, time table din abuncin da zatayi yana nan an mannashi jikin fridge sai wani dan box din medication da date harda time a jiki, saidan karamin timer dake reading time komai dai cikin sauqi. Neman abun shara ta soma yi da mopper, tana ganin komai ta kwaso ta koma parlor ta soma gyara, allah ya taimaka ta iya gyaran ma sosai saboda gidan data baro bayan aikin kula datayi har da gyaran daki tana yi, agidan wannan tsohon kuwa har abunci tana dafawa irin nashi wanda matar gidan ta koya mata musammam idan ita bata gidan. A gurguje ta gama komai saboda babu datti ko digo sai yar kurar da baza a rasa ba, dakin activity room ta shiga, nan ma saida ta gyara ko’ina ta goge kafin ta fito, duk wannan abubuwan da takeyi cikin natsuwa takeyi gudun kartayi wani kwakwara motsin. Mamakin kayayakin wasa dake dakin activity ta soma yi, wasu abubuwan wasan ma tun tasowarta bata taba ganin su ba, yaran larabawa dai suna shan gata. Kitchen ta koma ta soma preparing abunda ke rubuce a timetable din, duban date ta fara yi a jikin time table din, yau Wednesday, abunda ke rubuce ne a wajen ya dan bata mamaki don ruwan zafi kawai ta gani da just 1 apple for breakfast, wakeyin Karin kumallo da ruwan zafi zalla bama ruwan shayi ba sai kuma slice of apple, sanin bata da hurumi a cikin dokokin da aka bata yasa ta bude fridge din, babu wani abun kirki a cikin fridge din na ci saidai fruits da chcolate sai vegetables… Apple din ta zaro guda daya ta soma slicing kafin ta jona ruwan zafi a heater kettle lokacin wajen karfe takwas tana gamawa ta samu waje anan kasan kitchen din ta zauna ta tankware kafafunta. Duk bayan yan mintuna qalilan haka zata dubi time gudun kartayi kuskure har barci ya soma dibanta a nan zaune, haka nan ta hana kanta barcin nan har wajen karfe takwas rabi daidai. 8 dinma nayi alarm din kan timer dinnan yayi ringing, a furgice ta miqe tsaye jikinta na bari ta nufi wajen kettle din ta sake reboiling ruwan, tunawa da saiyasha magani a cewar matar nan yasa ta bude wannan box din ta zaro pack din magungunan ranar kafin ta dauka ruwan dake jere a wajen ta fuce daga kitchn din. Daidai bakin kofar dakin ta tsaya, sai a lokacin taji wani sabon tashin hankali ya tunkarota, she’s just so anxious haka kawai. Kai tsaye ta bude ahankali gabanta na bugawa kafin ta shige cikin dakin, dakin duhu babu wani haske kwata kwata daga inda take tsaye, dagowa tayi ta fuskanci cikin dakin, sai a lokacin ta dan hango hasken rana dake haskowa daga wajen labulen dakin. Takowa ta soma yi anatse ba tare da tayi making any movement sound ba har ta karaso tsakiyan dakin, shuru ta danyi tana yin nazari nan take haske ya zagaye ko’ina ya gauraye dakin, duban ko’ina ta soma yi da kyau, daki ne babba sosai mai dauke da gado dayasha beddings sai carpet a tsakiya, ko tv babu sai gefe kuma wata kofa ce kamar wani dakin daban kuma. Duban gadon tayi ganin babu kowa akai kuma babu alamun da akwai mutun a dakin yasa ta danji sauqin fargabar da take ciki, ‘’toh ay babu kowa nan’’ ta fada aranta ‘’kila yaron yana bandaki’’ ta sake fada aranta, don daga yanda wannan matar ta fada cewa karfe takwas yake tashi, shuru shuru dai tana tsaye har wajen minti goma babu wani motsin, hakan yasa ta tunanin anya lafiya kuwa. ‘’first love’’ furucin data faraji Kenan, tabbas taji anyi magana saidai ta kasa gane daga ina ne tajiyo wannan sound din dake futa ahankali, dube dube ta soma yi har idanunta ya sauka wajen labulen nan dake facing dakin, chan kuma ta hango tudun abu ta wajen labulen wide glass din dakin ahankali ta soma takawa zuwa wajen, tsugunnawa tayi daidai wajen curtains din sannan ta fara yaye labulen, tundaga yatsun hannunshi daya ajiye agefenshi zuwa bayanshi that is so wide zuwa sumar kanshi da take akwance kamar gashin jariri da alamu an aske mashi gashin ne ma amma ya fara fitowa,zaune yake ya tankware kafafunshi ya hade su waje guda ya zuba ma windown fararen idanu babu ko kiftawa. Afirgice ta koma da baya, hankalinta atashe azuciyar ta fara karanto addu’oin tsari kamar an kira sunan shi kuwa ya juyo ya kalleta, shima saida yadan razana. Lafiyayyan saurayi ne zankadede a zaune, fari tass dashi, yana da yalwan gashin jiki da gashin baki daya cika mashi round innocent face dinshi, akalla zai kai shekaru talatin da yan kai a doran duniya, yana da wani irin kyawu da cikar haiba masha ALLAH gashi da girman jiki na mazan taka(masculine) dukda a zaune yake. Kallon juna suka soma yi tsakanin shi da ita,sabeeha dai kasa dauke idanunta tayi akanshi, saboda kamar anyi magneting idanunsu waje guda babu abunda take tambayar kanta sai wannan ne sir din? Shi wannan din mutun ne? tsabar furgici ma kallon shi take kamar aljani saboda kyawun shi ya wuce musali. Shikuwa ganin tana kallonshi yasa ya zuba mata idanu shima, jikinshi harya soma jaa, take yanayin fuskanshi ya sauya zuwa na furgici har jijiyoyin kanshi sun bayyana rado rado, sanye yake da wata farar riga mai dogon hannu sai wando shima fari tass masu laushi,, zumbur ya mike tsaye wanda yasa ta dago da kanta sosai kamar tana kallon sama don yana da tsayi sosai, saita zama kamar wata yar dwarf a gabanshi, bakinshi ya soma juyawa kamar wanda ke son yin Magana ‘’who are you?’’ ya fada a hasale, wannan kalmomi sune kalma ta biyu daya furta da kunnenta ya jiyo mata, Inda take ya soma dosowa kamar wani zaki, ‘’who are you?’’ ya sake fada yana binta daf da daf, tana ganin haka ta koma baya cikin sassarfa har tana harde kafafunta, saida suka karaso tsakiyar dakin ya fara dube dube da alamu yana neman abunda zai dauka ya buga ne a kasa, ganin babu komai a kusa yasa shi kwala uwar kara wanda yasa sabeeha burkicewa sosai, take ta saki maganin da ruwan duka a kasa, ‘’na shiga uku’’ta furta bakinta na karkarwa, wata uwar tsawa daya sake doko mata yasa ta zubewa a kasa sai hawaye wiwi, tata ta kare, wannan mai kama da aljanun ko mahaukaci ne? shiyasa ake ta tsoron hawa sama kenan,abunda yazo ranta Kenan. ‘’dan..dan allah kayi hakuri, karka min komai dan allah’’ ta karashe tana mai hade hannenta waje daya tana rokonshi, hwayenta kuwa basu bar tsayawa ba kuma daga gani ta torota sosai. Wannan kukan nata ya sashi sarewa anan take kawai, sai yaji wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyarshi kamar an zuba mashi ruwan sanyi a kirjinshi, he was never soft towards kowa sai first love dinshi, baitaba yarda da kowa ba sai first love dinshi don duk wanda aka kawo don kula dashi tsoronsu yake ji kuma baya son ganin su kwata kwata, shi a ganin shi saboda su ne first love bata zuwa wajen shi kuma bata kulashi, sai gashi a karo na farko yaji wani iri game da wannan din. Nan take ya tsugunna a gabanta kamar wani dan yaro dan shekara goma, musculine hannunshi ya dago ya dora shi akan fuskanta dake cikin mask, nan take ta bude idanunta data runtse ta sauke shi akan fuskanshi, ‘’í’m so..rry don’t cry’’ Mamakin yanda yake yi da fuskanshi da yanda yake goge hawayen idanunta take yi, wasu abubuwa yake yi kamar wani dan karamin yaro, hawayen fuskanta kuwa basu bar kwaranya ba dukda yana goge su don kamar tunzurata yake yi dayin hakan, ‘’don’t cry for me please’’ Ya sake fada yana mai hade fuskanshi abun tausayi kamar zaiyi kuka shima, ai kuwa kan kace me shima yayi zaman dirshen a gabanta ya soma kuka wiwi kamar karamin yaro, mamakin hakan ya sata dan tsagaitawa nan take kuwa ya soma bugun kasan tiles din da kafafunshi har yana zungurinta, tashin hankali, nan take itama ta zabura sai kuka jikinta har rawa yake yi tsabar furgici, ita abun da ya tayar mata da hankali shine, ya za ayi ace dingiqin zabgege mutun dinnan ne yake kuka kamar yaro, haka suka dunga kuka daga shi har ita kamar kananun yara suna nan zaune aka budo kofar dakin kamar za a balla kofar, maido da dubansa yayi ga kofar nan take kuwa ya miqe cikin sassarfa ya nufi wajen kofar baiyi wata wata ba ya rungume hidaya data shigo dakin hankali a tashe kamar an wullota. Kankameta yayi sosai jikinshi na rawa, yanda ya rungumeta kamar wani dan karamin yaro, itama dai sai ta zama wata yar kif a gabanshi, hidaya dai kasa motsawa tayi tana mamakin wannan al’amarin, bubuga bayanshi ta soma yi don ya saqalo hannayenshi a arms dinta tana mai duban maid din ranta a mugun bace., Yana nan a jikinta ta soma jan shi zuwa bakin gadonsa ta zaunar dashi, sabeeha dai tunda ta dago sau daya ta kallesu bata sake dagowa ba haka zalika kukan nan nata bata dainayin shi ba. Hidaya na zaunar dashi ya matso kusa da ita ya kwantar da kanshi kan kafadarta, ‘’first love, she’s crying, for me tell her to stop crying’’ Ya karashe yana nuna sabeeha dake zaune dabas a kasa, kallon inda take hidaya tayi kafin ta maida dubanta gareshi, ‘’clean those tears’’ ta bashi umarni nan take, shi kuwa yana gama sauraronta ya goge fuskan tass, yana mai kallon ta yana murmushi sosai saboda dadin ganinta, shidai idan kaganshi yayi murmushi to sai idan yaga first love dinshi. Miqewa hidaya tayi tsaye, kamo hannunta yayi da sauri kamar zaiyi kuka irin yanda kananun yara keyi, ‘’sit down and let go of my hands’’ ta bashi command, ay kuwa tana karashewa ya koma ya zauna ba tare da ya sake koda motsawa ba. Tana ganin haka ta nufi hanyar futa tana mai kallon inda sabeeha ke zaune, ‘’ke kuma fito’’ Tana kaiwa nan ta futa daga dakin, miqewa sabeeha tayi tana mai kallonshi, yanda kasan baya fidda nunfashi yanda ya zauna ya natsu sosai, futa itama tayi daga dakin kafin ta janyo kofar. A sitting room ta tadda hidaya dake zaune cikin shiri da alama office zataje, ta daura kafa daya kan daya fuskannan babu annuri, karasowa sabeeha tayi dan nesa da matar kafin ta tsugunna anan wajen har kasa. ‘’ke are you stupid? Bakida hankali ne kema aka kawoki ko kina da mentality, where are you from? Wani agency ne suka kawo ki?’’ abunda hidaya taso fada mata Kenan, saidai ta hana kanta da fadin hakan don yanxu dole ta hakura da duk maid din data dauka don kula dashi saboda bazaiyiyu a barshi shi kadai ba koda yaushe gashi ita kadaice a gidan ya yarda da ita sosai,wannan yasa ta hadiye duk wani abun dake bakinta ta soma Magana with so much class. ‘’whats your name’’ ‘’sabeeha’’ ta bata amsa ‘’I’m sorry for that, patient ne,wannan da kike gani brother nane, he’s battling with amnesia caused by brain damage, nasan kin tsorata da shi, he’s not harmful at all sannan baya yin anything weird or strange, he’s just mentally unstable’’ Tunda ta fara Magana kan sabeeha na kasa bata dago ba haka zalika itama hidayan ita take kallo dukda bata ganin fuskanta saidai kwayar idanunta, ‘’brain dinshi ke controlling mind dinshi, shiyasa yake acting kamar 13 year old child, which was the neurological effect of the amnesia, ba wani abun zakiyi mashi ba fa ce kula dashi da maganinshi sai movement dinshi that’s all’’ Sai a lokacin sabeeha ta dago don da farko bata gane bayanan matar ba sai a yanxu,ko ba a fada mata ba tasan wannan itace madam din da head tace bazata samu ganinta ba, nan take taji wani iri aranta, a nata tunanin da farko ta dauka mahaukaci ne ganin yanda shima ya dunga kuka saida wannan matar ta mata bayani ta gane cewa ashe ba mahaukaci bane, larura ce dashi. Nunfasawa madam din tayi don this is the first time ta zaunar da wata kaskantacciyar caregiver tayi ma bayanin shi, shima hakan ya zama dole ne don bazai yuwu ace ita zata kula dashi koda yaushe ba tunda maa’’aikatan guduwa suke yi, ita kuma bazai yuwu tabar ayyukan gabanta ba saboda situation dinshi, shiyasa ta zaunar da sabeeha tayi gaslighting dinta yanda bazata yi kokarin barin aikin ba dukda tasan yana da hot temper musamman idan abun kan nashi ya motsa ko idan ya furgita. ‘’zaki iya kula dashi ko bazaki iya ba babu wanda zai maki dole ‘’ hidaya ta tambayeta Shuru sabeeha tayi tana nazari, yau ita ake bama zabi? Tunawa da wani abu yasa ta kawai tace mata eh don bata da wani zabi, da sauqi ma dai tunda matar tace bazai mata komai ba Katse mata tunani hidaya ‘’ina fatan zakiyi aikin ki daya kamata?’’ Samun kanta tayi da amsata ‘’yes madam’’ ‘’great decision, I hope you know that your job is confidential, wannan maganar no one is allowed to know about this, so be careful’’ Cije lebe tayi don taso ta danyi threatning dinta saidai kuma bzatayi hakan ba saboda plans din da take dashi. Wasu yan maganganu ta fada mata game dashi kafin ta miqe tsaye, dakin suka nufa atare, yana nan zaune yanda tabarshi kmar statue, tana karasowa kusa dashi ta kama hannunshi, nan take kuwa ya sauke mata wani murmushi mai sanyaya zuciya, he looks so innocent. ‘’big baby, wannan ce new friend dinka kaji’’ ta nuna sabeeha dake bayanta kamar munafuka, ‘’she will play with you okay? She’s my frind as well bazatayi maka komai ba, nasan you will be friends with my frend ko’’ Kallonshi hidaya tayi gashi nan dai a haka saika rantse lafiyarshi kalau, gashi da wani irin kwarjini da cikar haiba,kuma kamar lafiyayyan mutun, Hannunta ya sake rikewa cikin nashi hakan ya sata zamakusa dashi kan gado, fuskanta ya shafa cikin so da kaunar ta yace ‘’yes first love, if she’s your friend then we are friends’’, murmushi tayi mashi tare da zame hannunta daga nashi ta mike, ‘’I love you first love’’, ya fada ahankali kamar helpless child,batace mashi komai ba ta juya inda sabeeha ke tsaye a bayanta ‘’if there’s any issue zaki iya kiran line dina direct daga landline’’ tana kaiwa nan ta fuce tana mai yima sabeeha murmushi don ta dago da fuskanta. ‘’okay ma’am’’ Hidaya na futa ta dubi agogon hannunta tana mai yin tsaki rai adan bace, saboda tayi latti sosai gashi yau din is a very important day saboda suna da share holders meeting. Bayan futar hidaya wani irin sanyi sabeeha taji aranta, batayi tunanin haka madam din take so nice ba, gashi shikuma wannan dan uwan nata abun tausayi,maido da dubanta tayi gareshi ganin disappointed expression akan fuskanshi. Takowa tayi inda ta zubda magungunan ta kwaso su da ruwa kafin ta komo inda yake,tsugunnawa tayi har kasa tana mai kallon fuskanshi, shiko da sauri ya dauke fuskanshi daga dubanta a shagwabe, ganin haka yasa ta cewa ‘’Hii’’ Qin juyowa yayi saida ta sake cewa ‘’hii’’ nan ba shuru, ganin haka ya sata cewa ‘’ka manta madam tace nima na zama friend dinka?’’ Sai a lokacin ya juyo ya kalleta, dukda bai ganin fuskanta both yanayin yanda idanunta ke nuni da murmushi tayi mashi hakan yasa shima ya mata murmushi, baiyi wata wata ba ya sauko daga kan gadon ya zauna zaman dirshen a kasan ya kamo hannunta yana mata murmushi, ganin haka ya sata miqa mashi maganin hannunta, tabe baki yayi kamar yaga abun kyama, ‘’haba friend dina, kasha sai muyi wasa’’ hakan data fada kuwa yasa shi washe mata baki ya bude bakin shi, zuba mashi maganin tayi kafin ta bude ruwan ta bashi a baki. Yana gama sha ya tabe baki irin yanda yara keyin kafin yace mata ‘’thank you’’ da mamaki ta dago ta kalleshi, yanda ya fada zaka rantse wani mai hankali ne ya fadi hakan. ‘’whats your name friend?’’ ya tambayeta yana kura mata idanu alamun son jin abunda zata fada ‘’sa..bee..ha’’ ta bashi amsa, dariya yayi ya maimaita abunda ta fada, ‘’zan iya kiranka da friend?’’ Girgiza mata kai yayi shima yace ‘’nima zan kiraki da friend okay?’’ Sun dan dade a zaune tana kallonshi shiko wasa yake da kananun yatsun hannunta don sai hannun nata ya zama dan karami a cikin tafin hannunshi. Duk yanda sabeeha tayi ta karbi hannunta kin sakar mata yayi haka ta zauna tana kallonshi yanata faman jujuya yatsunta ita mamakin wai ace babba haka ne yake abubuwa kamar karamin yaro, daga yanda yake Magana da shagwaba da yanda yake murmushi kamar karamin yaro, yanayin yanda halittarshi take idan ba a fada maka ba zaka rantse lafiyar shi kalua kuma yasan inda kanshi yake, take taji wani irin tausayinshi aranta, ashe ita da take ganin bata samu jin dadin rayuwa ba kamar kowa har take questioning ko shin ita din ta daban ce ashe akwai mutanen ma da su they are helpless, basu san ma inda kansu yake ba, nan take ta yi godiya ga allah daya barta a yanda take, shi kuma wani irin tausayin shi ne ya fara yawo cikin jikinta, allah kadai yasan what he’s going through. Lokaci guda taji kawai she want’s to help, don taimakon wanda ke neman taimako ba karamin lada mutun ke samu ba. ‘’friend?’’ ta kira sunanshi Kallonta yayi kamar wani mara wayo yana mata murmushi, ‘’kana son muyi wasa’’ Da murnarshi kuwa ya girgiza mata kai, mikewa sabeeha tayi hannunta na cikin nashi, ganin haka ya sashi shima ya mike, koda ya mike a gabanta saida gabanta ya fadi, he’s so huge, ga girma ga kyau, komai nashi ya fita daban, daga ganinshi kasan ba karamin mutun bane, saurayi ne mai jini a jika saidai lalura da take kan kowa wanda allah ya kaddara saita shafe shi babu makawa kuma kowa da irin kaddararsa. Da kyar ta samu ta zame hannunta daga cikin nashi dukda yana kokari sake chapke hannun nata, ‘’bari na kawo maka breakfast sai muyi wasa okay?’’ ‘’okay friend’’ ya amsata Juyawa tayi ta nufi hanyar futa daga dakin, harta fuce yana kallonta yana murmushi, kitchen din ta nufa ta duako mashi apple dinnan da warm water kafin ta dawo dakin. Da sallama ta shigo, bin idanunta ya soma yi da kallo yana karantar abunda take fada, saida ta karaso har inda yake kafin shima ya maimaita abunda tace, kallonshi ta tsaya yi confusedly, kamar mai koyon abubuwa haka yake, wani irin tausayinshi ne ta sake ji kamar tayi kuka haka kawai taji she’s so emotional. ‘’friend sit’’ tana fada kuwa ya zauna, Miqa mashi apple din tayi tace ‘’bismillah’’ ‘’bismillah?’’ ya sake fada yana kallonta confusedly, ‘’ína nufin ka karba kaci’’ nan ma kallonta ya dunga yi saida tace ‘’eat’’ tukunna ya karba. Abunda ta lura dashi kamar yana koyon abubuwa ne yanxu, ko kuma maybe saboda lalurar tashi ne yasa shi haka oho. Yana kokarin cin apple din tace ‘’ga ruwan’’ Karba ya sakeyi yana murmushi yace ‘’thank you’’ Tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi, kwata kwata bata yarda ta dauke idanunta daga ganinshi ba har y agama cin apple din a natse kamar wani hamshakin babban mutun, ita dai har yanxu wanna abu mamaki yake bata sosai, yana gamawa ya miqa mata glass din ruwan daya sha. Juyawa tayi ta sake futa daga dakin kafin ta sake dawowa, lokacin data dawo ya cire rigar jikinshi gaban dayanta, yana kokarin zame dogon wandon jikinshi, tana arba dashi kuwa tayi saurin runtse idanun ta ‘’na shiga uku ni fatima’’ juyowa yayi a tsorace ya kalleta, mazugin wandon na hannunshi bai kaiga saukewa kasa ba, takowa ya somayi don ya dan tsorata sosai saboda baya son ihu ko hayani ko sound ko kadan, hakan na furgitashi sosai, yana karasowa baiyi wata wata ba ta riko rigar jikinta kamar zai shige jikinta, take ta damke bakinta kuwa don kiris ya rage ta doka wata uwar kara jinshi a bayanta. Karjarwar da jikinta ya soma yi ne yasa shi sake rikota sosai, ‘’friend friend, I’m scared’’ Wannan furucin nashi ne ya sata jin wani irin,sai a lokacin ta tuna fa bashi da lafiyar kai, kuma yana abune kamar yaro don haka ta dan dake ta juyo ba tare da ta sake kallon jikin shi ba tace ‘’sorry friend don’t be scared, me zakayi?’’ ‘’I want to shower and play friend’ Sai a lokacin ta tuna dole ita zata taimaka mashi yyi freshen up don haka ta soma kokarin zame rigar ta daya qanqame ba tare da ta sake kallonshi ba, hannunta ya sake rike wa don har lokacin a furgice yake, bata hanashi ba haka ta nufi hanyar kofar data gani a dakin, cikin ta shiga yana biye da ita, koda ta shiga kofofi biyu ne a wajen, daya daga cikin kofofin ta bude kafin su shige a tare. Duk wani abunda tasan zai buqata wajen wanka saida ta hada mashi, yana tsaye daga gefe ya rike gefen rigarta, saida ta gama ta nuna mashi wajen wanka ‘’bismillah’’ Kallonta ya sakeyi sai maida mata abunda tace nan take tace mashi ‘’you can freshen up now’’ tana kaiwa nan ta soma cire hannunshi daga rigarta, yana ganin haka kuwa ya sake damqe rigar, ‘’wait for me friend’’ Waro idanu sabeeha tayi jin abunda ya fada, ganin yana shirin janta zuwa wajen bathube din hakan ya sata kallonshi don dole badan taso ba ‘’no, zan jiraka a waje’’ Haba wa tana fadin haka ya soma bubuga kafarshi a kasa kamar yaro, tashin hankalin da ba a saka mashi rana, yanda kasan tayi kuka haka take ji, anya zata iya wannan abun kuwa. Wata dabara ce tazo mata ranta ‘’friend zan jiraka a waje kaji?, idan k agama sai muyi wasa tare’’ Tana fadin haka kuwa ya saketa yana murmshi, tana ganin haka kuwa tayi saurin fucewa daga bathroom din tana haki. Dayan dakin ta bude, wanda take tunanin nanne closet dinshi,kayan dake wajen kusan duk iri daya ne, fararen riga da wando, ko color daya babu, agurguje dai ta kwaso kayan ta ajiye mashi akan gado kafin ta fuce daga dakin. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 17-18 Update!! Koda ya fito bai ganta ba sai yaji babu dadi aranshi,shiryawa yayi yanda hidaya ta nuna mashi don yana jin maganarta sosai yana gamawa ya zauna bakin gadon. Tunda ya zauna ya zubama kofar shugowa dakin idanu ko zai ganta, sabeeha kuwa bata koma dakin ba saboda an gindaya mata sharudan shiga dakin, daman zata bashi maganin shi ne saita bashi breakfast daganan kuma saita taimaka mashi yayi wanka daga nan kuma bazata sake shiga dakin ba sai da yamma idan tazo bashi second dose. Bayan Futar sabeeha daga dakin batayi gigin komawa dakinba saboda koba komai namiji ne kuma yana buqatar privacy bayan wannan ma bata son ta gane ma kanta abunda bai kamata ta gani ba saboda baya cikin hayyacinshi, don tundaga yanda ya soma kokari zame wandoshi kuma ya ganta ta tabbatar akwai gyara sosai a al’amarin. kasa ta koma bayan ta kakkashe komai yanda head ta fada mata, harta sauko kasa yana ranta, saitaji kamar ta koma don ganin ko ya futo daga toilet din ko bai futo ba ko yana buqatar wani abun. Jiki a mace ta shiga dakinsu, gaba daya tama manta da cikinta don ko karyawa batayi ba kuma it’s past 10, yar Ghana da tsegumi ashe tana ankare da ita don ta jiyo lokacin da sauran maids ke gulman ta. Abuncinta ma itace ta karbi nata ta ajiye mata don a pack pack ake basu kullum safe rana da dinner. Koda ta shiga ko zama batayi ba saiga yar Ghana ta shugo itama da pack din abuncinta a hannunta,’’new comer’’ Yar Ghana ta kirata,juyowa sabeeha dake shirin zama bakin gadon tayi tana mai kallonta, cikin sassarfa yar Ghana ta karaso inda take kafin ta miqa mata pack din data shugo dashi, ‘’ga break dinky na karba maki’’ Murmushi sabeeha ta yi duk da ba a ganin fuskanta kafin ta sanya hannu biyu ta karba pack din tace ‘’nagode.’’ Murmushi yar Ghana tayi kafin ta soma rage murya ‘’ina aka kaiki?’’ Shuru sabeeha tayi tana kallonta kafin ta sauke kanta kasa tace ‘’sama wajen madam’’ Shuru yar Ghana tayi tana kallonta cikin nuna rashin yarda da abunda tace, chan kuma sai tayi murmushi tace ‘’na dauka wannan wajen aka kaiki, thank god ba nan bane, bari na koma wajen aikina bye’’ Girgiza mata kai kawai sabeeha tayi kafin ta zauna nan bakin gadonta,pack din nata ta bude, fries ne sai kwai da aka soya yasha albasa. Bismillah tayi kafin ta soma turawa cikin natsuwa, duk sanda zata kai bakinta haka zata dan janye mask din ta tura kafin ta maida shi. Bayan ta gama zamanta tayi anan dakin ta doka uban tagumi, tunanin wannan mara lafiyan ne ya fado mata arai. Taheels groups….. Zaune take cikin kayataccen office dinta, the most trusted secretary dinta na gabanta, ga kuma wasu file dake ajiye akan table din office din, gaba daya yau ranta a mugun bace yake tun daga gida, ga kuma abunda ta riska anan office. Kallon agogon dake maqale a hannunsa yayi kafin ya maida dubansa ga madam din nasa, ‘’ma’am lokaci yayi fa’’ Tafin Hannayenta data rufe fuskanta dashi ta sauke kasa, sai kuma fuskanta data dago ta zuba mashi waennan idanuwan nata masu firgitawa, karantar facial expression dinta is so hard don gaba daya bazaka iya tantance a wani yanayi take ciki ba. Mikewa tayi tsaye tare da ture kujeran dake bayanta kafin ta sagayo ‘’lets go’’ Tana kaiwa nan ta nufi hanyar futa, shikuwa da hanzari ya bi bayanta da wannan files din, cikin takun isa ta fito daga cikin office din nata ma’aikata duk wanda ya ganta saiya tsaya yadan duqa mata cikin respect dukda bata bi ta kansu ma kwata kwata. Bata tsaya ko’ina ba sai shareholders hall, secretary yana biye da ita a baya, koda tazo bakin kofar hall din shine ya bude mata kofar kafin ta shige ciki. Mutanen dake zaune cikin hall dinne wanda akalla zasu kai su kusan guda goma sha biyar ne sukayi saurin mikewa don girmamata, bata tsaya wani amsar gaisuwarsu ba ta nufi hanyar wajen zamanta na musamman a tsakiyan dogon table din. Zama tayi kafin kowannen su ya zauna suma, shuru ne ya biyo baya baka jin komai sai saukar nunfashin manyan mutanen dake zaune. Secretary ne yayi opening meeting din kafin ya fara koro masu bayanin progress din da aka samu a wannan shekarar, hidaya dai binsu take da kallo daya bayan daya tana jiran taji wanda zai fara Magana, cikin waenda ke zaune kuwa harda uncle khal don shima shareholder ne sai sauran mutane da sukayi investing kudadednsu da waenda sukeyi partnership dashi. Daya daga cikin manyan mutanen ne ya katse secretary, mutumin kowa yasanshi he’s so bold kuma shi baya wani rufa rufa, don haka ya soma Magana ‘’wannan bashine purpose din meeting dinnan ba, munyi’’ Sai a lokacin hidaya ta dago ta kalleshi, babban ne sosai don a haife zai haife ta kuma yana cikin waenda suka dade sosai suna investing a cikin company ma’ana sune waenda suka dade a cikin company kuma suna bada gudumawa sosai don ganin cigaban company tun marigayi taheel na raye. Yanda take kallonshi haka yake kallonta, babu wani conering ya cigaba da Magana ‘’dalilin wannan meeting din shine, munason sanin dalilin dayasa wanda ya kamata ya karbi ragamar wannan company dinnan baiyi presenting kanshi ba har yanxu, yau kusan wata takwas Kenan, a yanda ka’idar business dinnan take da kowane company shine dole heir din owner of the company ne zai gaji wannan company ko next person In line’’, Hidaya najin haka ta maida dubanta ga uncle da ya hade hannayenshi a kirjinshi yana kallon wannan show din, ‘’madam munason sanin dalilin presenting dinshi bayan kowa yasan yanxu he’s 30 kuma wannan ne ka’’idar company, we understand your help and contribution in making this company standing on it’s on, but…’’ At this point idanunta sunyi jaa sosai, shi kuwa bai tsagaita bay a cigaba, ‘’but you’re not enough madam, you can’t run the company ko badan ka’ida ba, babu inda aka yarje mace ta rike company anan kasar, a woman can’t rule the company, that’s a disgrace to the taheel family and the company reputation as well’’ Yana kaiwa aya gaba daya office din suka karade da cewa ‘’yes, that the fact’’ Kan kace me nan take hall din ya kacame, wannan yace kaza wannan yace kaza, saida hidaya ta bari suka gama tass har lokacin kallon uncle take dake mata wani irin kallo,irin na barki dazu, Runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta daga hannunta biyu ta daki table din dake gabanta, nan take duk sukayi tsit bakajin komai. Babu tsoro babu fargaba ta daga ma secretary hannu, cikin hanzari kuwa ya miqa mata wannan file din, yana miqa mata ta bude cover din file din kafin ta watso masu shi gaba daya, Daya bayan daya suka soma dauka papers din don karantawa, ‘’idan kun gama karantawa let me know’’ Tana kaiwa nan ta hade hannayenta a kirjinta tana jiran su gama, nan take kuwa suka soma zuru zuru da idanu don kowa da sunanshi a jikin papers don da duk abubuwan da sukeyi ta bayan fage, sunan uncle ne kawai babu a ciki, wanda yayi Magana ta fara pointing babu tsoron komai ta soma Magana ‘’you!!! with due respect, inason ka fada min waye a cikinku ya kamata na miqa ma company dinnan?’’ ‘’you!!’’ ta sake fada tana nuni da wani dake gefenta, shi har ya soma balle maballin buttons din suit dinshi tsabar tashin hankali. ‘’kai dake da record of molesting workers, da harassment tsakanin ni da kai waye yafi dacewa ya jagoranci wannan company?’’ Mutumin najin haka ya sauke kanshi kasa, idanunshi sunyi jaa sosai, wannan shine babban embarrassment din da akayi mashi agaban bainar jama’a kuma manya kamarshi. Wata iriyar dariya tayi mai bayyanar da hakoranta kafin ta tafa hannunta ta maida dubanta ga dayan dake gefenshi tace ‘’and you… kaida kake da record of homosexuality, gayzism, kana nufi kaine ya kamata yayi ruling wannan company din?, how are you all better than a woman ku fada min’’ Daya daga cikinsu ne ya dake, daga gani zaiyi kafiya yace ‘’mu bamuce muna son amsar legacy din family dinku ba, what we just want to know shine maysa har yanxu heir din wannan company din bazai karba muqaminshi ba’’ Shuru hidaya tayi ta kasa cewa komai sai kuma chan ta saki wani murmushi, ‘’seems like you’re are not understanding this language’’ Jin haka ya tabbatar masu da abunda take shirinyi, wata bankadar zatayi masu gashi kowa yana tsoron kar ta fidda wani abun nashi don basu taba tsammanin hatsabibya bace ba sai yanxu, ‘’we’re done for today’’ Uncle ya fada yana miqewa, sauran mutane na jin haka kuwa suka mike kowannensu ya soma fita daga hall din, gaba dayan su tashin hankali ne karara a fuskansu, gashi a junan su ma baqin ciki suke ma juna kuma basa kaunar juna gashi lokaci guda wannan la’ananniyar ta tona ma kansu asiri a junansu. Suna fita tayi ma secretary nuni da hannu akan ya basu waje, yana fita kuwa ta kalli khaal kafin ta soma tafa hannayenta tace ‘’wow, wow, wow, wonderful, that’s a great attempt khaal, ni da kai kasan cewa idan mutanen nan suka san cewa wanda suke tambaya akai is not mentaly stable zasu iya komai don ganin sun karbi wannan company din daga hannu mu, kana tunanin zan bar haka ta faru?, no never, this is my parents legacy, my parents hard work, abuh and ummuh, so this is just the beginning khaal’’ Tana kaiwa nan ta mike ta fuce daga office din ta barshi saqe a tsaye, hannunshi daya dungule yayi jaa sosai kamar gauta. Hidaya kuwa na futa secretary ya mara mata baya zuwa office, wani irin sign of relief ta sauke kafin ta kalli secretary ‘’mun tsallake wannan, nasan bazasu hakura ba, zasu ta kawo hari with much questioning, inason kayi providing komai, da yanda mukayi planning komai’’ ‘’okay ma’am’’ ya amsata kafin ya fuce yana murmushi. Bayan futarshi Kenan ta, ta bude wata safe locker, wayoyi ne guda biyu sai wasu papers a cikin locker din, daya daga cikin karamar wayar ta zaro kafin ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma Magana anaste ‘’bana son dogon bayani, so guda nawa ne suka shigo hannu?’’ Daga chan ne aka bata amsa kafin ta sake cewa ‘’okay!!’’ Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta maidata cikin locker din kafin ta maida dubanta ga papers din dake cikin safe locker, tunani ta soma yi chan kuma kawai sai ta rufe locker din ta cigaba da ayyukan dake gabanta. Bangaren sabeeha, karfe uku da rabi nayi ta koma dakin nashi, a hankali ta soma bude dakin kamar wata barauniya, dakin duhu dum yanda kasan dare yayi babu haske babu sound din komai kamar babu rai a cikin dakin, ahaka ta dunga rarrafawa ta karasa tsakiyar dakin, sai data karaso bakin gadon ta samu dan hasken bedside lamb, Bin kan gadon ta soma yi da kallo, barcinsa yakeyi hankali kwance hanunshi rike da wani puzzle solver da ake jujuyawa, ya nado jikinshi da pillow ya rungume. Tsugunnawa tayi agaban gadon ta zuba ma innocent kyakyawar fuskanshi idanu daga kan lashes dinshi da sukayi zaro zaro ga dogon siririn hancinsa a mike kamar pile zuwa ga lips dinshi da suke a cike sunyi jaa kamar ansa mashi filler ga sexy jaw line dinshi mai daukar hankali sosai, kasa dauke idanunta tayi daga jaw line din nashi don wajen is so attractive duk da bata san attracting dinta wajen yake ba,maido da dubanta tayi ga huge kirjinshi zuwa ga arms dinshi, ya zakalo hannunshi ya rungume pillow a kirjinshi, ya rike wannan puzzle box din da yatsunshi, daga ganinshi yana amfani da musles equipment saboda yanda ya damke pillow din kamar za a kwace mashi pillow din har jijiyoyin hannunsa sun bayyana. Samun kanta tayi kawai da murmushi ganin yanda yayi wani irin juya bakinshi alamun kosawa da barcin, samun kanta tayi da qin tashinsa saima kallonshi data cigaba da yai harta sakankance lokaci ya kure. Kokarin tashinsa ta soma yi saidai tsoron yanda zai tashin take don ance yana furgita, wata dabara ce tazo mata kai don haka ta daga dan karamin hannunta ta soma shafa karan hancinsa ba tare da tayi making sound movement ba ko hakan zaisa ya tashi, shuru dai babu motsi saima nunfashi da yake saukewa a hankali, ta dade tana hakan harta maida tafin hannunta kan bare fatar skin din fuskanshi mai laushi kamar na sabon jariri, shafa fuskan nashi ta soma yi ko hakan zaisa ya tashi har zuwa wajen silk gashin sajen fuskanshi daya zagaye fuskan nashi, dukda hakan ma datayi shuru ganin haka kawai yasa ta miqe ta futo daga dakin bayan ta tabbatar yana nunfashi. Lokacin data futo karfe hudu yayi kowa ya sauka kasa gaba daya maids babu wanda ya tsaya anan saman don wannan dokar ba a tsallaketa. Hidaya…… Bayan wannan shareholder meeting dinnan bata bar office dinba sai wajen yamma liss, school din barad ta fara zuwa suka daukeshi kafin ta dawo gida. Akan hanyarsu ta dawowa gida ya soma nuna mata medal din da aka bashi na competition din da sukayi kuma yaci second position, kallon medal din kawai tayi kafin ta kalleshi, first tambayar datayi mashi is ‘’why would you take second position, ban haifi danda za a wuceshi a komai ba so buckle up and make me proud next time with a first position, not this rubbish okay’’ Girgiza mata kai kawai yayi in response, Bawan allah yana jinta ta gama kanshi a kasa, yau kwata kwata baya cikin jin dadi saboda koda yaushe shi mai faran faran ne, dalilin fushinshi kuwa shine kowanne student parents dinshi na zuwa suyi supporting din yayansu, but shi babu wanda yazo mashi, daman daddyn shi yafi bashi attention akan harkokin nan shiyasa yafi shaquwa da daddyn nashi akan mamanshi, wannan yasa koda yaushe yake missing dinshi sosai. Koda suka karaso gida kamar koda yaushe maids na tsaye suna jiranta, daya na kula da harkar barad while dayar kuma tana daukan Jakarta da sauran files dinta da sun dawo. Saukowa tayi daga cikin motar maids din na mata sannu da zuwa, idanunta ne ya sauka akan motar dake parke a parking lots, barad daya zagayo yana ganin motar kuwa shima ya saki jakarshi a wajen ya ruga da gudu cikin gidan tsabar murna ya soma kiran ‘’daddy!! Daddy is back’’ Kwasar jakarsa maid dinshi tayi kafin ta shige ciki, hidaya na gaba suna biye da ita a baya harta shige cikin gida. Su afiya na zaune a second sitting room suna zaman da suka saba na kallo da ci, barka da zuwa sukayi mata kafin ta wuce, suka bita da idanu, afiya dai har yau a kule take da alamarin yayar tasu, wani sa’in kuma inta tuna da rayuwar su a baya sai taji wani irin tare da tausayin yayar tata don tun bayan mutuwar ummuh ta koma wata iri gaba daya don tana masifar son ummuh dinsu sosai, yanxu kuwa she’s not friendly at all,komai harshly take yinshi, dama dama su kannenta ma, suna samun wani soft side of her. Saman ta wuce direct zuwa, koda ta karaso saman saida ta dan tsaya ta dubi part din big baby, ayanxu ta tabbatar yana barci don haka ta wuce bedroom dinta kawai. Da sallama ta shugo parlorn part din nata, da barad taci karo da wani babban mutun sak kamar barad din har kamarsu ta soma baci, wasa sukeyi sosai mutumin na mashi chakulkuli barad na dariya yana fadin ‘’daddy stop daddy!!’’ Kallonsu hidaya tayi kafin ta kauda kanta gefe ta nufi hanyar bedroom dinta, mutumin da barad ya kira da daddy ne ya kalleshi kafin yayi sqeezing face yace ‘’wake squeezing face kamar haka’’ kyalkyale da dariya barad yayi harda buga kirjin dadyn nashi yace ‘’that’s mummy’’ nan take suka kyalkyale da dariya, Saida suka tsagaita kafin barad ya kalli dadyn nashi yace ‘’daddy please zan iya ganin uncle taj? I missed him so much I want us to play, daddy Please please ‘’ Shuru dadyn yayi kafin ya shafa kanshi cikin lallami yace ‘’I’m sorry barad, uncle baya jin dadi kaji? He needs medical attention ka bashi time tukunna, ka tuna last time abunda ya faru ko?,’’ ‘’but daddy inason naje wajenshi’’ ‘’no barad you can’t mummy zatayi fushi dakai, you can’t play with him for now, ka manta that little incident daya faru’’ Sauke kanshi kasa barad yayi cikin rashin jin dadi don shine yayi causing, ‘’yes daddy,but I’m sorry bazan kara hakan ba’’ ‘’yes you made a mistake ka bude kofa ka fito da uncle kunyi wasa ya fadi a bene,shiyasa mummy bazata bari ba, and I’’m hoping bazaka sake hakan ba’’ ‘’Yes daddy’’ Ya amsa mashi ‘’good boy,’’ mikewa daddyn yayi yana mai nuna mashi hanyar bedroom dinshi yace ‘’go and freshen up boy, kana yin tsami’’ Dariya sosai barad yayi kafin yace ‘’dad sunkuyo na fada maka wani abu’’ Rankwafowa mutumin yayi barad na ganin haka kuwa ya kama fuskan dadyn nashi ya dannan hammatarshi a wajen, nan take daddyn ya soma kakarin amai da wasa, nan take suka kyalkyale da dariya, yanda suke communication da juna gwanin burgewa don daga gani akwai soyayya mai karfi tsakaninsu. Yana wucewa daki ya sauke wata ajiyar zuciya kafin ya nufi bedroom din nasu, da sallama ya shiga cikin bedroom din, da ita yayi arba, tana tsaye tana kwance takalmin kafafunta data nannde kafafunta da igiyarsu, karasowa yayi cikin kulawa ya zauna bakin gadon, tunda ya shigo bata dago ba haka zalika ba tace mashi kala ba. Fuskarshi a hade ya nufi hanyar dresser ya soma kwance tie din dake wuyanshi, saida y agama ya cire agogon hannunshi ya ajiye kan dresser din kafin ya zame belt din kugunshi, yana gamawa ya wuce cikin closet ba tare da yace mata ci kanki ba itama kuwa bata tanka mashi ba saima kokarin zare takalmin nata da takeyi, tana gama warware igiyar ta mike da takalmin a hannunta ta nufi closet room dinsu, juyowa yayi ya mata kallo daya kafin ya cigaba da zame wandon daya rage mashi, itama kallo daya tayi mashi ta wuce wajen closets dinta, duk wani accessories dinta ta soma cirewa kafin ta maida dubanta gareshi yana kokarin daura towel a kugunshi, ‘’ka dawo ashe’’ ‘’yes’’ ya bata amsa kai tsaye kamar bashine y agama wasa da barad ba, Daga yanda ya amsa mata tasan cewa daga inda suka tsaya Kenan zasu cigaba, kamar yanda ta saba gaslighting akan mutane dukda duk yanda taso tayi akanshi ya gagara don shi baya yin shuru kwata kwata shiyasa take shakkansa sosai, ‘’wai meysa bazamu tsaya on a one page ba eh,as my husband abunda nafi buqata shine support dinka bawai ka dunga….?’’ ‘ Tsagaitawa yayi daga abunda yake ya juyo ya mata kallo daya kafin ya girgiza kanshi ya cigaba da abunda yakeyi, tana ganin haka ta cigaba da Magana….. ‘’I made you who you are today Jamid, your parents your siblings, kowanen su suna under my wealth shelter meysa kai bazan juyawaka yanda nake so ba? Why can’t you support me kodan saboda……..’’ ‘’’hidaaaaaaayaaaaa!!! Ya daka mata wata uwar tsawa daya sata yin gum ta zuba mashi idanunta da sukayi jaa sosai, ‘’point of correction, you don’t owe me, because I’m your husband, and we have two different personalities, bazaki taba sakani abunda banyi niya ba, I will never work for you nor under you,kuma duk abunda nasan kinyi ba daidai ba saina fada maki, so keep that in mind’’ yana kawai ya fuce daga dakin. Yana futa ta doka wani uban tsaki kawai ta cigaba da abunda take, what she wanted from him was just an apology ‘’I’m sorry’’ saidai bata jin zata taba samu daga wajenshi, don tana masifar shakkarsa sosai, bata kawo mashi wargi ko kadan ita kanta ta rasa dalili. Karfe tara daidai ta fito daga closet room cikin shirinta na kwanciya,yau ko sauka kasa yin dinner ma batayi ba, babu abunda take sai kamshi mai dadi sosai, tana sanye da sleeping dress baqa mai sirirn hannu kamar vest wadda ta sauko mata har wajen gwaiwarta Akwance ta taddashi ya bata baya don he’s not ready for her drama, itama kuwa kwanciyanta tayi ta juya mashi baya. Sunyi nisa sosai cikin barcin wayarta dake gefen bedside ta soma ruri,karar wayan yakai kusan minti goma yana yi saida jamid ya mike zaune ya dubi inda take kwance ‘’hidaya!! Hidaya!!’’ ‘’uhm’’ ta amsashi don barcin nata baiyi nisa ba, ‘’ki tashi mana, bakiji wayanki na kara bane’’ Tsaki tayi kafin ta miqa hannunta ta miqe zaune, duban screen din wayar tayi kafin ta shiga app din dake detecting warning alert din gidan, rai adan bace tace ‘’what sort of nonsense is this’’ Dubanta yayi kafin yace ‘’whats the issue’’ ‘’Big baby ne’’ ta bashi amsa kai tsaye rai a bace. Yana jin haka hankalinshi ya tashi lokaci guda ya mike tsaye ya zura bedroom slippers dinshi ‘’haba hidaya, yanxu kinsan cewa warning alert din dakinsa ne shine kika zauna calmly kamar ba komai ba? What if wani abu ne ya faru?’’ yana kaiwa nan baima bi ta kanta ba ya fuce daga dakin rai a bace. Yana fita saida ta dauki kusan minti biyar kafin ta miqe ta bi bayanshi. Direct part din big baby ya nufa kai tsaye, yana zuwa a gaggauce ya danna pin din dakin ya shige ciki. Daga yanda yake sassarfa zaka gane hankalinshi a tashe yake, dakin ya bude tare da danna light din dakin, nan take ko’ina ya bade, jefa idanunshi ya soma yi cikin bedroom din nan take ya soma jin sound din kukan shi sosai, yana daga zaune bakin gado daga chan sako ya nannade jikinshi gaba daya. Karasowa daddy barad yayi inda yake kafin ya tsugunna a gabanshi, ‘’Taj!!! Taj!!!, calm down okay?’’ Dagowa taj yayi jikinshi sai faman kyarma yake kamar wanda ya kwana yana zazzabi, idanunshi gam ya kullesu, farar rigarshi kuwa ta baci da jini da alamu ya yanke hannunshi da wani abun ne, Dafa kafadar shi daddyn barad yayi kafin yace ‘’taj open your eyes, it’s me, uncle jamid’’ Saida yaji hakan yayi saurin bude idanunshi, dukda ya gane uncle jamid din hakan bai sashi ya dawo daidai ba, hakoranshi sai faman gogayya suke da juna kaf kaf tsabar tsoro. Ture hannunshi dake kafadarsa ya somayi bakinshi na karkarwa ya soma ihu ‘’no no, I’m scared, first love please help me’’ A daidai nan hidaya ta shugo dakin, tun daga nesa ta tsaya ta harde hannayenta tana sauraron yanda jamid keta faman rokonshi akan he should calm down don gaba daya ya hade jikinshi waje daya kamar wanda za a yanka, saida ta shafe yan sakanni kafin ta karaso inda suke. Zama tayi bakin gadon nashi kafin ta soma Magana ‘’big baby’’ Yana jin sautin muryarta ya bude idanunshi tar akanta, rarrafawa ya somayi har zuwa inda take kafin ya rungume kafafunta, gaba daya y agama burkicewa babu abunda yake sai kuka ‘’first love don’t leave me alone, stay with me please, I’m scared.’’ Tunda ya soma Magana bata ce kala ba saima kallon suman kanshi data soma fitowa datayi, ga kafarta daya qanqame kamar her life depend on it, ga laps dinta daya jiqa da hawaye. Jamid dai kallonshi yake cikin tausaywa da kaunarsa, aduniyar nan bai bata ganin wanda ke qaunar yar uwarsa kamar yanda taj ke kaunar hidaya ba tun kafin wannan lalurar ta sameshi, tun tasowarshi da girmashi bashida kamar hidaya gaba da baya, babu wanda ya isa yayi comparing hidaya da kowa don tana da space na musamman a zuciyarshi dukda yanxu ya samu wannan amnesia din hakan bai sashi identifying dinta ba, kaunarta kuwa taa nan daram a cikin zuciyarshi. Haka zalika har a yanxu ma babu wadda ya yadda da sai hidaya, ita kadai ke iya controlling dinshi. Sun dauka kusan minti biyar a haka kafin hidaya ta soma shafa kanshi, ‘’shuuu, stop crying I’m here’’ ..Ta fada tana mai dago fuskanshi da yayi gaja gaja, ‘’wipe those tear’’ ta bashi umarni, nan take kuwa ya soma goge hawayen nashi yana gamawa ya kamo hannunta ya riqe gam cikin nashi, har zuwa lokacin yana tsugunne a gabanta, wayarta dake rike a hannunta ta dauka ta soma dialing number head. Head dake ta faman sheka barcinta tana jin karar wayarta tayi zumbur ta mike, ganin sunan madam yasata saurin daga wayar cikin hanzari tana kokarin goge miyau din dake yawo a gefen bakinta. ‘’yes madam’’ Daga chan bangaren ne aka soma Magana, tana cikin sauraron madam din tayi saurin miqewa hankali atashe, dan blanket veil dinta ta janyo ta yafa akan rigar baccin dake jikinta kafin ta zura takalminta ta fuce daga dakin da take kwana, Bangaren maids din gyare gyare ta nufa direct, tana shiga ta kunna futilar dakin kafin ta buga masu kofar dakin yanda duk zasu tashi A furgice kuwa duk suka tashi, kallonsu ta soma yi daya bayan dayan kafin ta maida dubanta ga gadon sabeeha ‘’where’s this new maid, you!!’’ ta yi nuni da sabeeha dake faman rarraba idanu, ‘’fito’’ Ta bata umarni, hankali a tashe sabeeha ta miqe, sanye take da hijab dinta sai janyoshi datayi ya rufe mata fuskanta ya rage idanunta ne kawai a bayyane, Futa head tayi kafin tabi bayanta hankali a tashe, sauran maid kuwa babu abunda suke sai tsaki bayan futarsu saboda tashinsu da akayi cikin tsakar daren nan wajen karfe uku, gashi zasu tashi da wuri, Suna fitowa head ta dubi inda sabeeha take tace ‘’what mess have you caused? Matsalata da irin ku black people dinnan idan kuna abu kamar marasa kai, just simple instruction baku iya bi ba?, now what stupidity have you done?’’ Tunda suka fara tafiya head take surfa mata masifa ita kuwa baiwar allah gaba daya hankalinta baya kan maganganun head din don hankalinta a tashe yake, babu abunda take sai tambayar kanta shin me tayi? Gaba daya jiya ta fara aikin fa? Hartayi abunda ba daidai ba. Suna karasowa part din headmaids ta fara shiga ciki sabeeha na biye da ita, zuciyarta na faman lugude tsabar tsoro, koda suka karaso bedroom dinshi head ta tsaya ‘’ki shiga’’ A tsorace sabeeha ta sanya hannunta kan mabudin kofar kafun ta shiga bakinta dauke da sallama, jamid ne kawai ya amsa sallamarta da mamaki, kallonta yayi daga sama har kasa kafin ya dauke idanunshi daga kanta. Mikewa hidaya tayi, taj na ganin haka shima ya miqe yana mai kokari kamata da kyau, kallonshi tayi ‘’big baby seat down’’ Tana fadin haka kuwa ya zauna anan kan gadon idanunshi na kanta don baya son ta tafi, takowa ta somayi har inda sabeeha take kafin ta daga hannu ji kake tasss tass tass, ta kwashe sabeeha da maruka both sides din fuskanta, cikin sauri jamid ya karaso inda suke ya janyo hidaya baya rai a bace yace ‘’hidayaaa’’ Hannu ta daga mashi rai a bace, akan me zai jata baya tana kokarin saitama wannan dumbhead din kai, lokaci guda sai bacin ranta ya koma kanshi, bata kaunar irin abubuwan da yake mata wanda babu wanda ya isa yayi mata irin haka sai shi, Taj dake zaune kukan sabeeha na mashi eco a kunne, kasa hakura yayi dole ya miqe tsaye baima san ya tashi ba ya nufi inda suke,take shima ya soma hawaye yana jan hannun hidaya ‘’first love please I’m sorry, don’t hit her please, she’s our friend remember?’’ Haka ya dunga maganganun da baima san me yake cewa ba yana jan hannun hidaya irin yanda yara keyi, ‘’stop it’’ ta daka mashi tsawa, ‘’go back and seat down’’ Wannan tsawar datayi ba karamin abu bane a wajen taj, don baya kaunar yaga tana fushi dashi ko kadan, nuni tayi mashi da gadon shi, Saurin sakin hannunta yayi ya nufi gadon ya zauna kanshi a kasa, har wani irin zazzabi ne ya rufe shi lokaci guda, ga wani azababben ciwon kai daya kawo mashi ziyara, jikinshi har rawa yake ga jijiyoyin kanshi da suka fito rado rado. Saida ya zauna hidaya ta maida dubanta ga sabeeha kafin tayi kwafa ta fuce daga dakin rai a bace. Bayan futarta jamid ya dubi sabeeha dake kuka innocently harda shesheka abun tausayi, ‘’I’m sorry about that okay?bansan me kikayi ba but Please be careful next time okay?, ranta ne ya baci sosai that’s why tayi acting that way’’ Tsagaitawa sabeeha tayi da kukan tana sauraron yanda yake Magana anatse cikin mutunci, girgiza mashi kai kawai tayi alamun gamsuwa ‘’you’re the new caregiver right?’’ ‘’yes sir’’ ta amsa shi. ‘’please work on his injuries okay?’’ Girgiza mashi kai sabeeha tayi kafin ya fuce daga dakin ya barta a tsaye. Sauran hawayen dake kan fuskanta ta goge, kafin ta maida dubanta ga inda yake zaune a bakin gadon ya runtse idonshi gam jikinshi na faman karkarwa. Takowa ta soma yi anatse har zuwa inda yake zaune, tsugunnawa tayi a gabanshi tana mai kallon fuskanshi, kawai saita fashe da kuka ganin yanda fuskanshi yayi jaa sosai ita a tunaninta shima ko bugunshi akayi, har zuwa lokacin bata san taqamaimain laifin datayi ba saidai koma menene ta yanke shi ne a dalilinshi ne. Idanunshi ya bude ya sauke akanta yana kallon yanda take kuka, hannunshi ya dago ya dora akan fuskanta, hannun nashi dake kan hijab din fuskanta tabi da kallon, wani irin dumi ne taji ya ratsa fuskan nata wanda ke futowa daga tafin hannun nashi ‘’don’t cry for me friend’’ Runtse idanun ta tayi ta dora hannunta akan nashi dake fusknta, wani irin zafi taji sosai kamar wuta, hannunshi is so soft kamar bai taba amfani dasu ba. Sun dauki kusan minti biyu a haka, ta kasa sauke hannunshi daga kan fuskanta, ga wani mixed feeling dake shiga cikin jininta, lokaci guda ya shiga ranta sosai, tausayinshi ya gama yi mata katutu arai, da zuciya daya taji tana son shiga cikin rayuwar shi ta hanyar taimakonshi da kulawa dashi don iya abunda zatayi mashi Kenan. Bakinta na rawa ta soma Magana ahankali cikin muryarta mai kwantar da hankali ‘’sir, you’re burning up,’’ Zame hannun nashi tayi daga kan fuskanta ta maida dubanta ga hannun nashi, jinin data gani ne yasa ta tuna da maganar wanda ta tarar tare da madam wanda take tunanin shine mijinta, Mikewa tayi tsaye yana ganin haka shima ya miqe yana mai jan hijab dinta, kallon hannun nashi tayi kafin ta daga kanta don ganinshi, ‘’I’m scared friend bazan iya zama ni kadai ba’’ ‘’zaka rakani?’’ Girgiza mata kai yayi kafin ya sauke mata murmushin sa mai tsada, wanda ya sata kasa dauke idanunta akanshi, yanda yake murmushi zaka rantse lafiyar kalau, he looked so matured. Batace komai ba ta nufi hanyar fita yana biye da ita har suka wuce zuwa kitchen, bin hanyar ya dunga yi da kallon kamar yau ya taba shiga wajen, suna shiga kitchen ta nufi wajen da taga first aid box, janyowa tayi ta soma budewa kafin ta zaro spirit da cotton wool harda wound plaster. Komawa sukayi dakin yana biye da ita a baya har suka karaso bakin gadon, ‘’seat down friend’’ Tana fada kuwa ya zauna, tsugunnawa tayi tana mai kallon hannun nashi, mika mashi hannunta na dama tayi yana ganin haka kuwa ya daura hannunshi akan nata, goge mashi hannun ta soma yi da spirit, ‘’ouch’’ ya furta A dan furgice sabeeha tace ‘’sorry, sorry akwai zafi ko’’ Girgiza mata kai yayi, haka ta gyara mashi hannun kafin ta saka mashi plaster, tana gamawa tace ‘’ka kwanta kayi barci friend’’ ‘’no I don’t want to, nasan tafiya zakiyi kamar yanda first love ta tafi, I’m scared don’t go please’’ ya fada cikin rada, ganin haka ya sata zama a kasa tace ‘’bazan tafi ba friend, ka kwanta to’’ Tana fadin haka kuwa ya kwanta, dan motsawa tayi yana jin haka yayi saurin kamo hijab dinta ya riqe gam, Haka suka zauna yana kallonta tana kallonshi, gashi idanunshi tarr yaqi yin barcin saboda baya iya barci dole saida maganinshi shiyasa ba a skipping lokacin maganinsa, ganin kusan har karfe hudu yasa ta miqe tsaye,yana ganin ta miqe kuwa shima ya mike har yana kokarin karo da ita, matsawa tayi baya kadan kafin tace ‘’toh ka bari nayi sallah’’ Da mamaki yake kallonta yace ‘’no firnd zaki tafi ki barni ne, lets go together’’ Shuru sabeeha tayi tana tunanin yanda zatayi dashi, don taso ya barta ta futa ta koma part dinsu ko alwalar ne ya barta ta dauro saita dawo nan, ganin hakan bazaiyuwu ba kawai ta nufi hanyar bathroom dinshi a tsorace. Yana biye da ita a baya ta tsaya tana bin bathroom din nashi da kallo, kallonda batayi ba bathroom din ba daxu, komai fari qal qal ya hadu ba kadan ba, zata iya rantsuwa akan bata taba ganin bathroom mai girma sosai kamar daki irin wannan ba,.. wajen wash hand basin ta nufa yana biye da ita, alwala ta dauro yanata kallonta hart agama, tana idawa ta juyo sauran kiris su gwaru don suna dab da juna. ‘’muje toh’’ Matsa mata yayi ta wuce kafin yabi bayanta kamar jela har suka kaarso tsakiyan dakin, da kyar tayi indicating kibla kafin ta kalleshi tace ‘’ka zauna a bed dinka toh, babu inda zanje I promise zanyi sallah ne’’ ‘’Sallah’’?? ya maimaita abunda ta fada confusedly, da mamaki ta kalleshi tace ‘’yes sallah,’’ Yanda tace kuwa hakan yayi ya samu waje a bakin gadon ya zauna, bai yarda ya dauke idanunshi akanta ba harta tada kabbara, ta dade sosai tana jero salloli tana addua harta sallame. Hannayenta ta daga tana mai kai kukanta wajen allah kamar kullum ta dade sosai tana addua. Duban agogon dakin tayi ganin wajen kusan biyar da kwata hakan ya sata mikewa ta fara sallar raka’atainul fjir, tana idarwa ta dubi inda yake zaune, yana kallonta har wani tagumi ya doka ya zuba mata idanu. ‘’friend kaje kayi alwala’’ ‘’alwala?,’’ ya sake tambayarta Nunfasawa sabeeha tayi tana tunanin how he react, tambayr kanta ta somayi kodai bai iya bane, bata kawo wani negative thinking aranta ba ta nufi inda yake tace ‘’friend muje toilet’’ Da saurin shi kuwa ya mike suka wuce bathroom, ‘’duk abunda nayi kaima saikayi okay? Wannan ibada ne, idan kanason allah ya baka duk abunda kake so sai ka dunga yi lokacin ta okay?’’ ‘’yes firnd’’ ya fada da murnarsa, alwala ta somayi yana kwaikwayonta ita kuwa tana mashi bayani har suka gama, suna idawa suka fito, anan kan carpet ta tsaya yana gefenta ‘’kaga sallah danayi dazu? Irin shi zamuyi yanxu okay?’’ ‘’yes firnd’’ ya fada sounding so excidetedly, Tada kabbara tayi yana kallonta shima ya yayi, haka ta soma karatu a bayyane shima yanayi har suka idar, suna idawa ta kalleshi ‘’kaga yanxu allah will answer all your prayers duk abunda kake so you can ask allah’’ ‘’zan roki allah yasa first love kartayi fushi dani, I want to be seeing her everyday’’ ya karashe sounding childish Murmushi kawai sabeeha tayi batace komai ba haka suka zauna, tana lazimi tana koya mashi wani abubuwan, abunda ta lura dashi kamar koyon abubuwa yake, and it looks like ya mance da wasu abubuwan daya shafi addininshi. Suna nan zaune ya soma gyangyadawa, surprisingly don da wuya yake iya bacci idan bai sha magani ba, kan kace me sai kawai jin kanshi tayi akan shoulder dinta, saita zama wata yar dul a gefenshi, juyoda kanta tayi tana kallon tsakiyan gashinsa dake shoulder dinta, curly gashinsa babu abunda suke sai wani irin kamshi mai dadi, wani ririn murmushi ne ya subce mata kawai, saita samu kanta da tofa mashi addu’oin data iya da ayar allah. Shiko barci ne mai nauyi ya dauke sa peacefully, sun dan dade a haka ta soma yin hannunta ya qage saboda yana da girma sosai, Rasa abunyi tayi ganin bata da wani option yasa ta soma mashi Magana cikin rada bayan ta riko hannunshi da hannayenta gudun karya furgita ‘’friend, friend, tashi ka kwanta’’ Kunnenshi ne ya soma jiyo mashi muryarta, take kuwa ya bude idanunshi ahankali da suka soma yin jaa ya zuba mata su, a shagwabe ya tabe baki ya soma miqewa, da taimakonta ta ya kwanta a kan gadon don barci ne mai karfi ya soma fusgarshi. Yana kwanciya ya kama hannunta yaqi saki haka nan ta hakura ta zauna a bakin gadon idan barcin nasa yayi nisa saita zame ta futa. Tana nan zaune itama tana zabga hamma har barcin ya sureta ta lafe akan gado hannunshi na cikin nata…. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 19-20 Update!!! Bangaren su hidaya, bayan futarta daga dakin rai a bace ta koma daki, babu abunda take sai sintirya tsakanin dakin, jira kawai take ya shigo bedroom din ta sauke mashi ruwan masifa kamar zata iya. Kamar yasan jiranshi take kuwa yana shugowa ya hade rai sosai, ‘’jamid wai meysa baka da burin daya wuce ka nuna min ban isa ba?, how dare you stop me from….’’ ‘’stop you from maltreating wanda ke kasa dake?’’ ya katseta,yana mata wani irin mugun kallo. ‘’shin kasan kuskuren datayi ne?,did you even know abunda zai faru idan kayi kuskuren rashin bashi maganinsa akan lokaci kuma cikin qai’da according to yanda doctor shi ya fada ba?, look duk abunda ya shafi big baby bana wasa dashi kuma bazan taba barin wata stupid caregiver ta yi sanadiyar abunda zai jawo mashi wata matsalar daban’’ Hannayenshi ya nade a kirjinshi ya zuba mata idanu yanda take Magana idonta a rufe babu mutunci, daga yanda take wannan abun yasan abunda zai biyo ba wanda baya jin zai kara barinta ta sake tafka babban kuskuren datayi achan baya dukda yasan ba kuskure tayi ba. Saida ya bari takai aya kafin ya sauke wani murmushi wanda shi kadai yasan me hakan ke nufi kafin ya raba ta gefenta ya wucewarshi ba tare da yace mata ci kanki ba. Ba karamin haushin hakan taji ba don takai wuya sosai, binshi tayi hark an gado ta cigaba da masifa akan big babyn nata rai a bace, yana jinta yayi banza da ita. **** Karfe takwas daidai ya soma bude idanunshi, bin ko’ina ya soma yi kafin ya miqe zaune yanda yake yi as’ual koda yaushe idan ya tashi, saurin juyowa yayi gefen gadon jin sautin nunfashinta na sauka akan hannunshi don ta rike hannun nashi tam daidai fuskanta, baiwar allah barcin ma kamar a wahale take yinshi don a zaune take sai kanta data daura akan lausassan gadon nashi. Samun kanshi yayi da kallonta haka kawai ya kasa dauke idanunshi daga kanta, lashes dinta da sukayi zaro zaro ya zubama idanu, maida dubanshi yayi ga hannunta dake cikin nashi, daidai nan aka bude kofar bedroom din nashi. Daddy barad ne ya shigo a natse cikin farar jellabiya, karasowa yayi cikin dakin da mamaki yake kallon taj dake kallon caregiver nashi, ‘’TAJ’’ Dagowa yayi ya maida dubansa ga dadyn barad kafin ya washe bakinsa fararen hakoransa suka bayyana, ‘’uncle’’ ya furta kamar wani karamin yaro, cikin sauri ya fuzge hannunta dake cikin nashi ya mike tsaye zuwa inda dadyn barad ke tsaye, sai a lokacin sabeeha ta farka dalilin zame hannunshi da yayi cikin nata,duban inda ya nufa tayi kafin tayi saurin miqewa tana mai sauke kanta kasa. Rungumesa daddyn barad yayi tsam a jikinsa yana mai shafa suman kanshi ‘’sai yanxu zaka kulani Kenan, jiya ay qin qulani kayi saida first love dinka tazo’’ Sakinsa taj yayi yana murmushi harda girgiza kai kamar yaro yace ‘’jiya?? First love? Ina first love dina, batazo ba ban a ganta ba uncle jamid, I want to see her please’’ Sanin yana yawan mantuwa wasu lokutan musamman idan abunda ya furgita shi ne da wuya memory din abun ke dawo mashi yasa jamid cewa ‘’zatazo yanxu, how are you?’’ ‘’I’m fine uncle jamid, ina new puzzle box dakace zaka kawo min da da colate?’’ ‘’yana nan na boye maka zan baka okay’’ Cikin murna taj ya soma shafa sajen fuskanshi tare da bitting lower lips dinshi yanda ya saba musamman idan yana cikin farin ciki ko idan ya samu abunda yake so, wannan character nashi yana nan bai sauya ba koda kuwa ya samu matsalar kai, kallonshi jamid yayi cikin tausayawa da kaunarshi, Jan hannunshi taj yayi har zuwa inda sabeeha take kafin ya kalleta yana mai rike hannunta itama ‘’uncle kaga new friend dinmu nida first love,’’ Girgiza mashi kai yayi har zuwa lokacin mamakin taj yanda ya taddasu yake, ‘’friend uncle Zai kawo min cholate, kema kina son cholate ko’’ Sautin ajiyar zuciyar data sauke ne tare da girgiza mashi kai yasa jamid kallonta yana mamakin yanda akayi ta samu courage din kwana tare da taj din, yayi mamaki sosai don taj baitaba yarda wani ya kwana tare dashi ba ko yazo kusa dashi musamman caregivers din da ake kawo mashi don su kula dashi, baya son ganinsu kwata kwata in baa hidaya ba baya qaunar kowa a kusa dashi, shima don ya dage ne sosai yana chusa kanshi yasa yake yarda dashi wani sa’in. Yanda yazo ya tadda su abun ya bashi mamaki, abunda ya tsaya mashi arai har yake tambayr kanshi shine shin wannan improvement ne ko kuwa yaya?, don abun yayi surprising dinshi sosai. ‘’you can go now, I will take it from here’’ jamid ya fada yana mai duban sabeeha ‘’sir zan taimaka mashi yayi freshen up, sannan time din medication dinshi yayi’’ Kamar mai tsoron Magana haka ta karashe maganar ‘’okay!!’’ ya amsa Hannunta dake cikin na taj ta zame kafin ta wuce bathroom, duk abunda tasa zai buqata saida ta ajiye mashi ta shirya mashi bathtube sannan ta saka mashi maclean a jikin electric brush dinshi kafin ta fito. Tana kokari daukan mashi towel dinshi sai gashi ya shugo toilet kamar an wulloshi, kallonshi tayi ganin yana faman daga kafafunshi ga gumi na saukan mashi, idanunta ne suka sauka akan inda hannunshi suke, ya rike mazugin wandonsa yana kokarin zame wandon, cikin sauri ta dauke idanunta daga wajen harta yi tsuru tsabar tsoro, ‘’friend I want to pee pee pee help me pls’’ Hankali a tashe sabeeha tace ‘’toh ka tsaya in futa saikayi’’ bakinta har karkarwa yake towel dinma har ya fadi ba tare da saninta ba ‘’friend button ….button… my trouser…. Yaqi futa’’ ‘’na shiga uku ni sabeeha’’ sabeha ta fada aranta, hanyar futa ta nufa cikin tashin hankali, cikin sauri kuwa ya kama hannunta gam don ta gefenshi tazo giftawa, gabanta ne ya bada dam, ta kasa motsawa ma, ‘’help me pls’’ itace Kalmar data doki kunenta dukda ta gama tsurewa ‘’sir ka bari na kira maka uncle saiya taimaka maka’’ Kamar zaiyi bori haka ya soma yi mata, ‘’noo please pee zai futo ki cire min’’ ‘’innalillahi !!! sir bazan…’’ Baima jira me zata ce ba ya janyo ta kamar yar kaza zuwa gabanshi sai ganinta tayi yar tsulum wajen kwankwasonshi, kamar zatayi kuka ta soma Magana ‘’kai wai ina aka taba haka, da girmanka zan cire maka wando, ni wallahi bazan cire ba’’ ta karashe tana mai fiddo da manyan idanunta Tashin farko kawai sai jin kukansa ta soma yi, sai a lokacin ta tuna lalurar sa, gaba daya idan ba kukan nan yayi ba mancewa takeyi yana da tunani da kwakwalwar yara, haka nan badan taso ba kamar zatayi kuka ta dan duqa kadan har hannunta na karkarwa ta soma kama igiyar wandon nashi, gaba daya ma ta burkice ta rasa yanda ake zuge wando, shi kuwa mai zaiyi banda mazari don a matse yake sosai daman suna tsaye ne shida uncle bayan futarta ya dameshi akan saiya dauko mashi puzzle dinshi, futar uncle din keda wuya ya fado toilet din don daman duk safiya abunda yake farayi Kenan pee, Wannan tazugen wando dai ta kyar aka warwareshi, daga shi har ita kamar marasa wayo babu wanda yayi tunanin sauke wandon kawai gaba daya instead of warware tazugen, shi daman idan har zaiyi using toilet kamar yanda hidaya ta koyar dashi saiya warware mazugin wandon kafin ya sauke shi kasa. Sabeeha na gabanshi harta samu ta kunce wando, tana kwancewa kuwa yayi saurin sauken wandon kasa ba zato ba tsammani, cikin hanzari ta koma baya saura kiris ta fadi tana mai runtse idanunta, allah ya taimaka da shorts a jikinshi kuma ta rufe idanun nata gam. Shi baima bi ta kanta ba ya nufi hanyar wc, ita kuwa tuni ta bama kafafunta iska kamar ana ingizata ko waigowa batayi ba ta fuce daga bathroom din, closet room ta nufa ta fito mashi da kayan sawanshi kafin ta fuce zuwa kitchen. Anaste ta fara harhada mashi breakfast dinshi, just one boil egg ne sai ruwa, tana gamawa ta gyagyara inda ya kamata kafin ta dauka maganinshi ta koma bedroom din. Lokacin data shugo harya gama shiryawa ya zuba ma kofar dakin idanu yana son ganin first love, ganin sabeeha yasa yaji babu dadi, don tunda safen jiya daya ganta bai sake ganinta ba kuma hakan na itching dinshi sosai, memory din abunda ya faru a daren kuwa ya rigada ya goge a kanshi. Da sallama a bakinta ta karaso tana mai kokarin goge abunda ya faru dazu daga ranta, ganin shi looking sad yasata tsugunnawa gabanshi tace ‘friend!!’’ Dago da jajayen idanunshi yayi ya zuba mata still fuskanshi na bayyanar da baya cikin walwala yace ‘’yes!’’ ‘’why are you sad?me kake so’’ Kamar jira yake kuwa saiga hawaye na yawo akan kyakyawar fuskarshi ‘’first love, I missed her so much’’ Wani irin tausayinshi ne ya kwanta mata a zuciya kamar tayi kukan itama, yan karamin tafin hannunta ta sanya ta soma goge mashi hawayen ‘’zatazo yanxu kaji?, don’t be sad please okay’’ ‘’da gaske?’’ ya fada exicitedly Girgiza mashi kai tayi ‘’yes da gaske nake yanxu kasha maganinka sai nab aka breakfast sai muyi wasa’’ Haka ta lallaba shi ya karba maganin yasha kafin ya danyi relaxing, kitchen din ta koma ta dauko breakfast ta kawo mashi yaci, ‘’friend!!’’ ‘’naam, friend’’ ta amsa shi ‘’first love zata zo?’’ ya sake tambayarta ‘’yes zatazo yanxu’’ ta amsa shi Bayan yan mintuna kalilan sai ganinshi tayi kuma yana hamma, taimaka mashi tayi ya kwanta ko minti biyu ba ayi bay a soma sauke ajiyar zuciya ahankali sai barci. Sauke ajiyar zuciya sabeeha tayi tana kallon innocent handsome fuskanshi, yana da cikar gira sosai baki wuluk,ga bakinsa mai dan girma lebensa yayi jaa kamar jini zai futo,ga jaw line dinshi da idan ta kafa ma wajen idanu bata son cire idonta a wajen, yana da attractive structure so cute irin ta cikakkun maza masu aji da class, samun kanta tayi da dan duqawa tayi mashi addua kafin ta dauka cup din daya sha ruwa dashi ta fuce dashi bayan ta jawo mashi duvet ta rage mashi haske dakin nasa. Kofar part din ta bude ta futo a natse, lokacin wajen karfe goma daidai, hidaya dake kokarin haurowa saman fadwa na biye da ita ne suka tsaya gaba dayansu suka zuba mata idanu, sabeeha bata lura dasu ba saida ta rufe kofar ta juyo nan tayi arba dasu, lokaci guda cikinta ya duri ruwa don bata manta marukan data sha ba ‘’ke uban me kike yi anan? Are you insane har kinada guts din presenting kanki a cikin gidan nan after what you’ve done?’’ Da mamaki fadwa ke kallon hidaya jin abunda take fada sai a lokacin ta gane cewa wannan din maid ce daman don ta ganta babu uniform ne yasa ta kasa gane wacece wannan hidaya ta bari har take shiga dakin Taj, ko suma ba barinsu take suna shiga ba dukda suma basu nuna sun damu da shiga dinba. Muryar jamid da sukaji ne yasa suka maida dubansu gareshi, hannunshi na rike cikin na barad sun fito daga part din su. ‘’what she did was a mistake saboda batasan cewa ba a skipping maganinshi ba,’’ Rai a bace hidaya ta maida dubanta gareshi, yanda take kallonshi haka yake kallonta yana hango fire din dake cikin idanunta. Fadwa dai hannayenta na harde tana kallon ikon allah don sai yanxu ta soma gane kan zancen nasu. ‘’you can go’’ ya umarci sabeeha. Kamar munafuka haka ta sauke kanta kasa ta nufi hanyar sauka kasa, tana sauka shima suka sauka shida barad daman zasu fita outings ne yau weekends. Cije lebe hidaya tayi kafin ta nufi hanyar part dinta,fadwa na ganin haka tabi bayanta. A sitting ta tadda ta ta daura kafa daya kan daya, skin dinta a bayyane don rigar data saka ta zaman gida ce wadda bata saukar mata har kasa ba, rigar ya amshi jikinta don bata da qiba kwata kwata. Zama gefenta fadwa tayi kafin ta soma Magana ‘’ukty are you okay?’’ Murmushin takaici ta sauke tana mai dubanta tace ‘’yes,what where you saying dazu?’’ ‘’daman!! Maganar bilal ne’’ (mijinta) Wani irin kallo hidaya ta mata tana sauraronta da kyau ‘’ukty please, meysa bazaki yi accepting dinshi ba? Wallahi he love me so much and he’s..’’ ‘’shiii…..,fadwa na hanashi zama a gidan nan ne?’’ ta jefo mata tambaya ‘’no ukty but ina ganin meyzai hana shima ki barshi ya fara aiki anan taheel company’’ Wata iriyar dariya tayi kafin tace ‘’yaushe zaku girma ne keda afiya?,’’ ‘’ukty please, muma munada share a cikin company nan, we can choose to work there’’ ‘’ke badan na tsaya mana ba kin isa kiyi tutiya da wannan company din? Kinsan to what extend na kai har yanxu cikin company? Did you know what I had to do just to keep our legacy?kinsan sacrifice din danayi?..please idan bakida wata maganar mai muhimmaci ki futa kawai I need some space’’ Mikewa tayi ta wuce daki tabar fadwa anan zaune, rai a bace, Meysa ukty ke masu haka ne?, why dole saida ikonta za ayi komai, wannan abun yana damunta sosai. Haka nan ta futa daga dakin rai a bace. Bangaren sabeeha tana komawa dakin su ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere, lokacin data shugo babu kowa a bedroom din don haka ta shiga bathroom tayi wankanta ta shirya tsaf cikin uniform dinta. California… ‘’maya maya’’ nannybee ta soma kwala mata kira hankali a tashe, cikin bathroom ta sake lekawa hankali a tashe, ‘’ina yarinyar nan ta tafi ne?’’ Rufo mata dakin tayi ta sauka kasa, tunawa da maganar daddyn daya umarci ta saka mata idanu sannan ta dunga updating dinshi akan absence dinta yasa ta nufi wajen landline badan taso ba, direct line dinshi ta soma dialing daidai nan aka bude kofar shugowa cikin gidan, hayaniyar su ce data karade gidan yasa nannybee ajiye wayar ta nufi inda suke, sanye take da kayan barci data barta dasu a jikinta kafin ta sauka dauko mata breakfast dinta, kawayenta na biye da ita su kusan hudu, kowannen su yasha kananun kaya sun dame. ‘’hello nanny bee’’ haka suka soma gaisheta daya bayan dayansu, murmushi kawai tayi masu tare da welcoming dinsu tana kallon maya, Cikin gidan suka karaso suka yada zango a sitting room, kan kace me parlorn ya karade da ihun su da hirarrakin sun a yan mata, ‘’go and frenshen up mana kafin su karaso its about to go down today’’ kloe ta fada tana kallon maya ‘’ku jira ni yanxu zan sauko please’’ maya ta fada tana wucewa sama. Orders din da sukayi aka soma deliverying, kayan ciye ciye daban daban kamar waenda zasuyi house party. Within few minutes saigata ta sauko cikin riga da wando wanda suka amsheta pink sai gashinta datayi packing dinshi a tsakiya, duk da bata da wani qiba da shape hakan baisa kayan sunyi mata kyau ba. Tana shugowa parlor suka miqe gaba dayansu suna Shewa, ‘’ouu let the party begins’’ ‘’oh yess’’ ta amsa su Katuwar speaker dake nan parlorn su ta kunna masu suka fara rawa, kidan gaba daya ya gama karade wajen block dinsu kamar gidan party, nanny bee dai babu yanda batayi ba akan su rage saboda mutanen neighbourhood din basa son kara bayan wannan ma throwing noisy party a neighbourhood din is prohibited, haka suka wuni suna sha’anin su kwata kwata babu wanda yaji knocking din da aka dunga yi. Sai wajen karfe biyar wutar gidan ta dauke gaba daya, rai a bace maya tace ‘’what the hell is going on?, kodai electricity bill din ne ya kare’’ ‘’gaskia call your parents, kofa gamawa bamuyi ba gashi su tom basu zo ba’’ Knocking din da akayi yasa suka tsagaita da surutan da suka fara, ‘’who’s knocking kuma, daddy baya nan mummy kuma sai wajen midnight zata dawo’’ ‘’let me check’’ kloe ta fada tana nufar hanyar kofar entrance din. Saurin yin baya tayi ganin police a bakin kofar, ‘’who’s the owner of this property’’ Cikin saurin kloe tace ‘’maya, come over’’ Tasowa maya tayi ta karaso inda police din suke, ‘’are you the owner of the property?’’ suka sake tambayarta ‘’yes, I’m the daughter of the owners’’ ‘’you’re under arrest for violating the regulations of this compound’’ Hankali a tashe maya ta kallesu tace ‘’what have I done, who reported me? For what?’’ Bai amsata ba yasa sauran officer din suka shigo suka saka su a gaba zuwa cikin moto, nannybee bata san me ake ciki ba saida ta fto lokacin ana shirin saka su cikin motar, turawa fa basu daukan wargi, dan report kawai neighbourhood din suka kai kusan guda biyar wanda haka yasa dole police suka zo suka tafi dasu. Hankali a tashe nannybee ta soma kiran line din mummy, kiran duniya ta dunga mata bata sameta ba saboda suna cikin operation room, dan dole haka ta soma dialing number daddy, kiran farko kuwa ya daga wayan, lokacin yana kokarin barin san francisco zuwa ga los angeles daman tafiyar 30mins ce gaba daya, saboda akwai wani case da yake handling dole saiya bar garin zuwa wani garin ya samo concrete evidence. Yana ganin call dinta kuwa ya tabbatar da ba lafiya ba, cikin sauri ya dauka call din. Hankali a tashe ya ajiye wayar, ga ranshi yayi mugun mugun baci sosai, haka nan duk importance din aikin nan nasa ya barshi ya juya zuwa san diego. A gurguje ya nema flight zuwa san diego allah ya taimaka akwai jirgin da zai tashi don haka ya nemi ticket a gurguje. Bashi ya iso ba sai wajen karfe shida lokacin garin ya soma duhu, daga airport zuwa police station dinma akwai traffic sosai, ba karamin bacin rai ne kunshe a ranshi ba, allah kadai yasan me zaiyi ma maya, abubuwanta gaba suke karayi kusan kullum. 7 dot ya iso police bureu dake cikin san diego city, a gurguje ya bada sunanta ga officer din dake counter din wajen ‘’maya Majeed please, I’m her father’’ Ciki suka shiga inda suka bashi waje ya zauna, officer daya kawosu ne ya soma mashi bayanin charges da report din da aka shigar da kudin damage din da zai biya ga electry line dinsu da aka kashe gaba daya dole saiya biya tax. Yana daga zaune saida ya kashe over 4000 dollars akan minor mistake na maya, at that point ko ganinta baya son yi, bai taba saka tunanin dukan yaro a cikin rayuwar shi ba, saidai yau yana jin kamar ya mata duka sosai. Saida ya biya komai suka rakashi har inda aka kullesu, koda suka karasa tana daga zaune idanunta yayi jaa sosai tasha kuka, gaba daya friends dinta sun kira iyayensu sunzo ita kadai ta rage. Fito da ita sukayi suka wuce gida, taxi ya tsaida masu suka shiga don motarshi na gida saboda daga airport ya biyo nan din. Suna isowa mummy ta iso itama gidan,already ta kirashi bayan taji daga wajen nanny bee, dady ne ya fara futowa kafin itama ta futo daga taxi din, da gudu ta karasa wajen mummy dake tsaye hankali a tashe tana jiran fitowarsu, rungumeta tayi tsam tana hawaye, ‘’mummy I’m sorry please’’ Ko kallon inda suke majid baiyi ba ya wuce cikin gidan daman tunda suka shiga cikin motar bai ce mata tak ba har suka iso, babu abunda take kuwa sai kuka kuma yana jinta yayi banza da ita don har zuwa lokacin yana processing irin hukuncin da zaiyi mata daidai da ita. Kallon fuskanta da tayi gaja gaja mummy tayi kafin ta kamota zuwa cikin gidan, gaba daya ranta a dagule yake da alamarin, tasan wannan karan kam bazasu kwashe ta dadi ba da daddy don ta hango tsantsan bacin rai akan fuskanshi. Koda suka shiga nanny bee na tsaye hankali a tashe, gaba daya laifin kanta take gani na qin hana maya, son da takeyi mata ne ke sawa take hana ta yin wasu abubuwan saboda tausayinta da takeji, iyayenta are very busy parents, basuda time din ta saboda aiki, wannan yasa ta taso da kadaici da rashin kusanci da iyayen nata musammam daddy. Har cikin bedroom dinta mummy ta rakata tayi wanka nanybee ta kawo mata abunci taci kafin mummy ta bata maganin ciwon kai. Saida ta tabbatar ta natsu kafin ta kashe mata wutar dakin nata ta koma zuwa bedroom dinsu. Da sallama ta shiga dakin, a zaune ta taddashi har zuwa lokacin ranshi a bace yake,karasowa tayi inda yake bakin gado ta zauna gefenshi kafin ta soma Magana cikin hikima ‘’daddy!!’’ Dagowa yayi ya kalleta idanunshi yayi jaa sosai, ‘’majeed dan allah kayi hakuri, yarinta ke damun maya,’’ ‘’yarinta? Bahijja yarinta fa kikace? Are you listening to your self kuwa, where’s she?’’ ‘’na sata barci, ‘’ Ta bashi amsa kai tsaye. Wani irin mugun kallo yayi mata kafin yace ‘’barci? Bahijja wani sa’in kina bani mamaki?,kinsan asarar da yarinyar nan ta jawo mana? Kin san me zatayi nan gaba, after all she has done kin sata barci?wallahi kinji na rantse bahijja wallahi this time around I’m going to deal with maya, duk abubuwan da takeyi ina Kauda idanu this time around bazanyi ba, and don’t even think of saying a word kinji na fada maki’’ Yana kaiwa ya miqe ya fuce daga dakin, tana ganin futarshi tabi bayansa, dakin maya ya nufa kai tsaye ya bude kofar ya kunna lights din dakin, barcinta take hankali kwance kamar ba itace tayi aika aikar nan ba, ‘’maya!!!’’ ya doka mata uwar tsawa, tashin farko ta mike zaune zumbur, ‘wani irin furgici ne ya durar mata ganin daddy nata a tsaye, daidai nan mummy ta karaso cikin bedroom din, ‘’step out now’’ ‘’daddy please I’m sorry bazan sake ba please’’ ‘’shut up your dirty mouth, I said out to, don’t make me repeat my self, ‘’ Ya karshe hannunshi har karkarwa yake tsabar bacin rai, ‘’mummy please talk to dad dan allah, wallahi banason zuwa displine room dan allah’’ Tana kaiwa nan ta karaso inda mummyn take ta boye a bayanta, ‘’daddy please, for god sake laifi tayi kuma tayi nadama, maya is not a kid fa da za a kulleta a daki, she will be 18 in a month’’ ‘’bahijjaaaaa!!!!,’’ ‘’majid please….’’ At that point ranshi ya gama baci sosai, ba maya ba hatta mummyn ma ta gama bata mashi rai sosai. Kasa cewa komai yayi kawai ya fuce daga dakin cikin bacin rai sosai, shi kadai yasan meke cikin ranshi da matakin dazai dauka akan sus u duka ma. He’s trying so hard to understand bahijja, wani sa’in yana kauda ido sosai akan rashin jin da maya keyi saboda maya kadai ce yarsu, kuma bazasu sake haihuwa ba saboda matsalar mahaifa da bahijja ta samu bayan haihuwar maya. Wannan rana dai cikin bacin rai sukayi gaba dayansu daga daddy har mummy, haka suka kwashi wajen sati guda babu wanda ya kula wani cikin su, maya kuwa harkarta ta cigaba ba tare da damuwa ba, ita dadinta daya mummy ta bi bayanta, saidai ta gindaya mata sharuda sosai tare da warnings akan cewa idan ta sake ta sake maimaita abunda tayi bazatabi bayanta ba. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 21-22 Update NIGERIA ABUJA Santuraki family… Yau family an tashi da jimamin mutuwar babban aunty amarya (matar uncle sameer), gaba daya cikin shiri suka fito inda zasu je gidan gaisuwa, already uncle Sameer ya wuce da aunty amarya chan gidan gaisuwar don tunda asuba aka kirashi aka shaida mashi, lokacin ma ba’a bangarenta yake ba yana bangaren anty Laila don kwananta ne ya zagayo a ranar, anne ce da nanna suka fito cikin shiga ta mutunci da alfarma sai sauran matan gidan, anty fadila da yaranta mazan, hamad da laily karama sai sufyan da abil, kananun ne kawai aka bari a gida wajen nannies dinsu. Gaba daya suna tsaye a compound din har kowa ya futo gaba dayansu banda anty Laila, Anty fadila ce tayi saurin cewa ‘’mamanku fah’’ Anty fadila ta fada tana mai duban su abil,kallon juna suka fara yi shida sufyan, ‘’tace driver zai taho da ita’’ Tabe baki antie fadila tayi kafin ta shige cikin katuwar lexus inda hamad ke driving motar while sufyan ke driving dayar motar dasu anne ke ciki. Cikin anguwar GRA dake cikin maitama suka nufa, anguwar ta masu shi ne don anguwar dai ta hadu sosai, daidai wani babban gida suka karaso, daga wajen gidan mutane ne burjik. Parking sukayi kafin su firfito, uncle Sameer ne yayi masu iso zuwa cikin gidan inda mahaifiyar aunty amarya ke karbar gaisuwa. Gidan kana shiga kasan anyi rashi babba don ko’ina shuru mutane ana zazzaune,Allah ya jiqan musulmai baki daya wanda suka rigamu gidan gaskiya, muma idan tamu tazo allah kasa mu shika da Imani Ameen. Har cikin babban parlor hajiya babba suka nufa da sallama inda suka fara gaggaisawa da mutanen dake parlor, anne ce ta farayi ma hajiya babba gaisuwa kafin su nanna dasu anty fadila, ba karamin dadi hajiya babba taji ba ganin dangin mijin diyar tata. Anty fadila ce tayi saurin cewa ‘’ina aunty mubina’’ ‘’tana ciki, bari a kirawo ta’’ hajiya babba ta fada ‘’ah ah bari na shiga daga ciki’’ anty fadila ta fada. Cikin dakin ta shiga nan ma dai akwai mutane amma basu kai na parlorn ba, mubina na daga zaune bakin gado, ta dafe kanta da alamu kuka take kanyi har zuwa yanxu, ga mubin a gefenta yana ta barcinshi hankali kwance. Gaisawa ta farayi da matan wajen kafin ta karasa inda mubina ke zaune, jin an dafa ta yasa ta dago, ganin anty fadila yasa ta soma share hawayen fuskanta, idanunta sunyi jaa sosai, ‘’aunty fadila kunzo?’’ ‘’munzo mubina, ya hakurin mu allah yayi masa rahama, ai duk mun zo harda su anne duk suna parlor’’ ‘’ameen anty fadila nagode bari naje parlorn’’ Atare suke wuce parlor inda su anne sukayi mata gaisuwa da sauran yaran harda samarin gida gaba daya. Wayar aunty fadila ce tayi ringing, ganin wanda ke kiranta yasa tayi saurin picking call din, ‘’wa alaikum salam’’ ta amsa sallamar da akayi daga chan bangaren kafin ta sake cewa ‘’tohm gani nan zuwa’’ Ajiye wayar tayi kafin ta miqe ta fuce daga parlor, daidai tsakar gidan inda babu mutane sosai ta hangoshi daga chan nesa, cikin sassarfa ta karaso inda yake tsaye, babban mutun ne magidanci, kamanin su daya sosai don kamarma har ya fita kyau saidai girma dayazo mashi sosai, yana sanye da farauncle Sameer Kenan. ‘’gani yaya ya hakuri, allah ya jikan sa’’ ‘’ameen ya Allah’’ ya amsa ta ‘’banga Laila ba ku kadai kuka zo?’’ Tabe baki anty fadila tayi kafin tace ‘’mun barta a gida tace wai driver zai kawo ta’’ Girgiza kai kawai yayi kafin yace ‘’shikenan, bari na koma gidan’’ Sallama tayi mashi kafin ta koma ciki shi kuma ya shige motarsa zuwa chan zuwa gida. Tafiyar minti ashirin ta kawoshi gidan, daidai apartment dinsu yayi parking kafin ya futo. Da sallama ya shigo cikin gidan, babu kowa a kasan sai househelp din dake fama kwashe kayan wasan yara, ‘’barka da dawowa’’ ‘’barka dai,’’ ya amsata kafin ya wuce saman, bai tsaya ko’ina ba sai bedroom dishi dake chan saman, da sallama ya shiga bedroom din, ko’ina tsaftsaf sai kamshin bakhoor dake tashi. Wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin manyan kasa, yana gamawa ya zari key ya wuce bedroom din anty Laila. Da sallama ya bude dakin yasa kai ciki, dakin lum lum babu haske sai karar ac, hasken dakin ya kunna kafin yakai dubanshi ga tsakiyan gado, da mamaki ya hangota kwace hankali kwance, karasawa yayi har bakin gadon ya zuba mata idanu ‘’laila laila’’ ya soma kiranta, Saida ya taba kafadunta kafin ta farka, kallonshi tayi kafin ta kauda kanta gefe ta miqe zaune, daga ita sai wata doguwar rigar barci da alamu ko wanka ma batayi ba, ‘’sai yanxu ka dawo tun asuba?’’ Ran shi ya dan soma baci, yanayin yanda take mashi maganar kamar bata san daga inda yake ba da kuma dalilin futar tashi, ‘’eh sai yanxu na dawo, maysa baki buyosu ba kunzo gaisuwa?’’ A hasale ta amsashi, ‘’basu fada maka nace zanzo daga baya ba’’ ‘’kewai Laila yaushe zakiyi hankali ne? rasuwa fa akayi ma yar uwarki? Wannan wani irin shahsan ci ne, ke kullum sai kin jawo ma kanki abun Magana sannan kizo kina kuka kina cewa bana kyautata maki bana bin bayanki? Yanxu ke hakan ya dace? Duk gidan nan gaba daya sun tafi ke kina daga kwance’’ ‘’kaga Sameer karka qara hadani da matarka, ka taba ganin inda kishiyoyi suka zama yan uwa? ni ba yar uwata bace ba, sannan mutuwa allah na tuba wanda ya tafi ya tafi Kenan, zuwana bazai dawo dashi ba, kuma naga dai bance bazan zo ba, mutuwar nan fa kowa anyi mashi ita saboda ka daina wasu maganganu don ka nuna min matarka ta fini shiyasa yan uwanka ke min abunda sukaga dama suka raina ni basa ganin mutunci na’’ ‘’laila kishi fa ba hauka bane ba, you better stop this nonsense, girma kikeyi ba rage maki shekaru ake ba’’ ‘’naji ka fadi duk abunda zaka fada, daman baka ganin laifin kowa sai nawa’’ tana kaiwa nan ta fashe da kuka ‘’wallahi Sameer na gaji, na gaji da wannan wulaqancin da yan uwanka ke min’’ ‘’wake maki wulaqancin? Fada min particularly’’ ya bata amsa ‘’kowa ma, kaga yanda fadila ke yi min, fisabilillahi kamar banice matar wanta ba, saboda tambarin agola da nake dashi a gidan nan, hatta anne ma ba sona take ba kuma na sani wallahi na gaji kaf danginka babu wanda ke sona, ita matar da aka auro maka ay ba a mata haka, sunfi janta a jiki ni kuwa da nake bare an kawo ni agola bani da qima da mutunci’’ Mikewa tayi tsaye rai a bace tana share hawaye shiko babu abunda yake sai kallonta ‘’laila, duk maganganun da zakiyi ya tsaya akan su fadila amma karki sake sako anne a ciki, sannan kina maganar basa kaunarki basa janki a jiki, ya akayi kika san basa kaunarki bayan ke kike janye jikin ki daga wajen su, bakya kaunar kusanci dasu, ke gani kike kinfi karfin shiga cikinsu’’ ya bata amsa shima ranshi ya dan soma baci. ‘’daman gaskia ce dai ba a son jinta,’’ ‘’bana son jin wata Magana daga bakinki, kije ki shirya kizo mu wuce’’ Kai tsaye ta amsashi, ‘’bazani ba’’ ‘’saboda me?’’ ‘’banyi ra’ayi ba’’ ta amsa shi kafin ta shige bathroom tayi ramming kofar bamm Ranshi yakai kololuwar baci sosai, when it comes to Laila tasan yanda zatayi ta bata mashi rai, yau shekara nawa Kenan abunda takeyi kullum gaba yakeyi, ada abun nata ba komai bane ba saboda bata comparising yanxu kuwa tunda ya auri aunty mubina bata da Magana sai ba a sonta a tsane, which shi yasan ba haka bane kuma duk wani problem daga ita ne, a komai saita nuna ta isa. Fucewa kawai yayi daga gidan ya koma gidan gaisuwa, basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara na dare, inda suka bar aunty mubina da Laila karama saboda zata zauna da ita. Saudi Arabia….. A yau sabeeha ta cika sati biyu ciff a gidan da aka turo ta liken asiri, gaba daya tama manta da wani batun leken asiri. A cikin sati biyu nan wata iriyar shakuwa ce ta wanzu tsakaninta da TAJ sosai, ita ke mashi komai, ita ke kula da duk wani abunda ya shafe shi, a cikin kwanakin ta gano halayenshi da abubuwan da baya so da wanda yake so. Ta bangarenta ba karamin tausaya mashi take ba, don gaba daya a yanda ta fuskance shi da yanda yake abubuwa da tunaninsa gaba daya na yara ne, don kamar an shafe gaba daya tarihin rayuwar na shekarun baya an sako mashi na lokacin da yake yaro, ko sallah ma bai iya ba idan yana yi kamar dan koyo, abunda yafi bata mamaki dashi shine he’s very smart sosai, don duk abunda ta koya mashi ciikin lokacin qanqani yake dauka, gashi yana bala’in son yayar shi madam Kenan, wannan soyayya sabeeha ta shaida ta don bata taba ganin irin wannan ba, bashi da Magana sai first love first love, idan abunci zaici first love, idan barci zaiyi zaice yana son ganin first love, wani sa’in haka kawai zata taddashi yana kuka yana kiran first love indan ya kwana biyu bai ganta ba. Ta bangarenshi kuwa, bashi da friend din data wuce sabeeha ita kadai ce friend din daya fara yi, kullum ita ke wasa dashi yanxu ita ke bashi abunci, yana ji da ita sosai saboda first love dinshi tace mashi friend dinta ce saboda haka shima friend dinshi ce, don babu abunda hidaya zata fada ko ta nuna tanaso shi kuma yaqi wannan abun. Yau weekends duk kowa na gida ana hutawa, hidaya na part dinta while su fadwa na wajen garden ita da afiya. Zuwan doctorn big baby da hidaya tayi hiring yasa ta futowa zuwa part din nashi, yau sati guda Kenan rabonta da zuwa part din wanda hakan ba karamin dadi ya mat aba don ya bata damar concentrating akan abubuwan dake gabanta da ayyukanta, sai a lokacin take jin data kori sabeeha datayi dana sani don wannan ce first caregiver din data dade har warhaka tana handling situation din taj, don da kansu suke guduwa saboda idan abun nashi ya tashi tsorata su yake yi don handling mai irin lalurar shi ba abu bane mai sauqi, daddyn barad ne ya shigo da doctor din sai wasu maza kamar ma’aikatan dake karkashin sa ne, saman ya jagorance su har zuwa part din, daidai nan hidaya ta fito daga nata part din, gaisawa sukayi da doctor kafun su nufi part din nashi, itace ta bude masu kafar kafun su shige daga ciki. Ko’ina fess fess babu qazanta as always don part dinshi kwata kwata ba a barin shi unhygienic. Daidai nan sabeeha ta futo don bashi maganinshi na yamma, tana sanye da uniform dinta kalar ruwan kasa sai face mask data rufe fuskanta dashi, ‘’step out’’ Hidaya ta bata umarni, hakan kuwa yasa ta tattara abubuwanta ta fuce daga dakin gaba daya. Cikin bedroom dinshi suka shiga, hidaya ce ta fara shugowa, yana zaune ya kafa ma kofar idanu yana jiran ganin sabeeha, cikin murna da farin ciki kuwa ya miqe tsaye har zai tunkaro inda yake ta daga mashi hannu hakan yasa suka karaso, wani iri dadyn barad yaji ganin yanda tayi mashi shima kanshi taj din saida yaji babu dadi, don he was so happy ganinta kawai da yayi, yanda yake wage baki kamar an mashi albishir da wani abu mai muhimmaci. Su doctor na biye dasu a baya har zuwa inda yake, zama hidaya tayi baking ado inda ayke zaune kafin ta riko hannunshi, saida doctor suka karaso ya soma zaro ido, har jijiyoyin kanshi sun soma firfitowa rado rado alamun yana neman furgita. ‘’big baby’’ ta kira sunanshi, gaba daya attention dinshi ya tattara ya bata dukda tsoron ganin doctor dinnan da yayi, daman normally idan zasu zo kuka yake yi saboda allurer da suke mashi duk wata, baya so kwata kwata, ga wani abu da suke zuwa dashi kamar inji wanda suke saqala mashi a kanshi, wannan abun yana tayar mashi da hankali sosai. ‘’look at mee, your’re a good boy ko?’’ Girgiza mata kai yayi alamun eh kafin ta sake cewa ‘’bana son wannan kukan naka, ka natsu, im by your side kaji?’’ Saida ta tabbatar tayi capturing mind dinshi kafin ta dubi doctors din,babban dake cikin su ne yace ‘’sir ko zaka dan bamu waje’’ Ya fada yana kallon daddyn barad, wani irin kallon hidaya jamid yayi, tana ganin haka ta kauda kanta gefe kafin tace ‘’ba damuwa, you say anything a gabanshi’’ Gyaran murya doctor yayi kafin ya karaso inda taj din ke zaune ‘’hello handsome how are you, na kawo ma cholate’’ Cikin murna kuwa yace ‘’da gaske’’ ‘’yes amma saika tsaya mun gama dubaka saina baka ka yarda’’ Girgiza mashi kawai taj yayi kamar wani dolo kafin yace ‘’no injection please uncle’’ ‘’babu injection I promise’’ Sauran yaran doctor ne suka karaso da abun gwajin kwakwal war tashi, abun is handy ana connecting dinshi da computer, inda sauran igigiyoyin kuma kamar hula haka zaka nada su akanshi. Haka suka fara sassaka mashi wannan wireing din akanshi, saida suka tabbatar sun saka ta ko’ina kafin daya daga cikinsu ya dauko wani dan syringe mai shegen tsayi kamar allurer doki, shidai daddyn barad na daga tsaye yana kallonsu. Sai da suka shanmace shi dayan ya tsira mashi wannan doguwar allurer, idanunshi har sun soma jaa don saida aka soma zuba ruwan allurer ya tabbatar allurer dai akayi mashi, nan take ya fashe da kuka kuwa, hidaya dai idanu kawai ta zuba mashi, saida kukan ya isheta tace ‘’shut up, kai karamin yaro ne kake kuka’’ ‘’madam ayi hakuri karamin yaron ne ay ayanxu,’’ doctor ya fada, Jin haka yasa ta hade rai sosai, taj kuwa tunda tace yayi shuru dinnan haka ya gume baki yana hawaye idanunshi sunyi jaa sosai ya kafa mata idanu dasu ko gajiya da kallonta baya yi, dadyn barad dai kasa kallonshi yayi don ba karamin tausaya mashi yake ba, yau wata takwas Kenan da faruwar wannan mummunan hadarin daya sauya mashi rayuwarshi lokaci guda, Taj was a definition of a perfect young innocent man, he’s the sweetest yet the most controlling duk da he’s tough musamman ga waenda bashida kusanshi dashi, daga danginsa sai danginsa gaba da baya, da wuya mutun ya shiga rayuwar cikin sauqi don he’s very tough with his lifestyle. Bayan an gama mashi wannan allurer kawai sai ya soma jijiga, hidaya dai miqewa tayi sauran yaran doctor nan suka zauna inda ta tashi suka ririke shi, wannan jijigar tashi effect din allurar ne, saida suka tabbatar ya futa hayyacinshi kafin doctor ya soma duba kwakwalwarshi da emotions dinshi don komai yana reading ta cikin laptop din, ya dauka kusan minti goma yana dube duben shi kafin ya sa yaran suka cire mashi wannan wiring din daga kanshi, a daidai wannan lokacin kuma jijigar ta lafa, kwantar dashi sukayi kafin likitan ya duba pulse dinshi, ganin komai normal yasa suka dan tsaya nay an mintuna, don allurar cikin minti ashirin take sakin mutun gaba daya. Ai kuwa lokacin na cika sai gashi ya bude idanunshi ya zuba masu idanu daya bayan daya harya sauke akan hidaya, cikin sauri kuwa ya miqe zaune ya riko hannunta, ‘’first love, yaushe kikazo, I missed you please karki tafi!!’’ Ba tare da ta kalleshi ba tace’’doctor, whats his progress?’’ Nunfasawa doctor yayi kafin ya soma koro mata bayani, ‘’gaskia babu wani changes, saidai he’s stable kawai, brain dinshi na functioning saidai babu wani alamun change a tattare dashi.’’ Daddyn barad ne yayi saurin katse shi, ‘’wannan barcin da yake yi all the time fah?’’ ‘’effect din magungunan shi, idan baisha sub a brain dinshi bazat huta ba, saboda zata dunga confusing dinshi da wasu flash memories dinshi na baya’’ ‘’ya za ayi yayi recovering idan bamu barshi ya samu wannan flash memories dinba? Stopping him from having wannan memories din bazaisa a samu any progress ba, are you kunsan yanayin aikin ku kuwa?’’ Doctor ne ya kalli daddyn barad don baima son koshi waye ba, ‘’sir are you a doctor ne?’’ ‘’no I’m not, but dis is a common sense, babu aynda za ayi yayi regaining memory dinshi idan har aka hanashi hakan’’ Sai a lokacin hidaya ta soma Magana ‘’jamid please, are you going to teach him how to work ne?’’ Dakatar da ita doctor yayi ta hanyar cewa ‘’first of all, you need to understand the psychological and medical reasons din daya sa yake shan wannan medication din, first of all, ayanxu his brain works like a child, sannan kwakwalwarshin ita ke controlling mind dinshi, kaga yanxu both 2 are connected, dalilin dayasa muka hanashi ya samu wannan flash memory din kuwa shine, any flash daya zo mashi zaiyi confusing mind dinshi dake controlling brain dinshi wanda hakan zai iya jawo mana wata matsalar, brain din itace center of universe din komai nashi, zata iya saka zuciyarshi ta buga ma tunda ayanxu ma he’s not normal, ina fatan wannan bayanin yayi maka’’ Nunfasawa jamid kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, wasu yan bayanai hidaya tayi mashi game da abubuwan daya shafesu kafin suyi mata sallama, suna gab da futa taj ya soma Magana ‘’first love ina friend, I was waiting for her yanxu ta futa, kin ganta? Yau munyi wasa nida ita’’ washe baki yayi excitedly yana bata labarin Tsayawa doc din yayi yana sauraron bayanan nasa da mamaki, na farko abunda ya bashi mamaki shine ya akayi ya tuna event din dazun na futar yarinyar don bai kamata ace ya tuna ba saboda allurar tana da karfi sosai wanda karfinta kesa wanda akayi ma ya manta da duk abunda ya faru dashi a ranar, da wannan tunanin ya futa daga part din da yaranshi, daddyn barad kuma yayi masu rakiya don shifa yana jin kamar bai yarda dasu ba kwata kwata. Suna fita suka tadda sabeeha tsaye bakin kofar part din hankalinta a tashe , da mamaki duk suke kallonta ganin haka ya sata cewa ‘’sir baisha maganin shi na yamma ba’’ Daddyn barad ne ya amsata ‘’don’t worry about it kije’’ Tana wucewa doctor ya bita da idanu kafin ya sauke wani murmushi ta gefen baki. Bayan tafiyarsu doctor hidaya ma bata wani dade ba ta futo daga part din big baby ba ta wuce nasu, bata dade da shiga ciki ba kuwa saiga daddyn barad, tasan maganganun daya saba zai mata don haka ta zauna ta daura kafa daya kan daya. ‘’hidaya, kina ganin wannan…’’ Daga mashi hannu tayi alaman ya dakata ‘’jamid please not today, na fada maka koma menene indai akan batun big baby ne don’t ever question me, wannan tambayoyin da kake ma doctors din shi na menene? I trust them so please’’ Saida ya bari ta kai aya, kafin yayi wani murmushi mai kama da na taqaici kafin yace ‘’at this point ke nake tsoro HIDAYA!!!!!!!’’ Yana fadin haka ya fuce daga bedroom din, harya fuce bata bar kallonshi ba tana mamakin abunda ya fada, ‘’me yake nufi Kenan da wannan furucin nashi?, itafa har yanxu tana jin akwai abunda yake boye mata wanda bata sani ba, shike sashi questioning dinta koda yaushe, yanda yake kallonta anya kuwa bai gano…… Saurin kauda tunanin tayi “no that’s impossible’’ ta bama kanta amsa, nan take wani irin fargaba ta durar mata,….. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 23-24 Update!!!! Washe gari da safe tun kafin alarm dinsu yayi ringing ta tashi, don yanxu ta fara gane komai na gidan da yanda alamuran gidan ke tafiya, wanka ta fara yi ta saka uniform dinta kafin ta fara nafilfilu, ta dade sosai kanta a kasa tana kiran sunan allah har alarm dinsu yayi kara. Karfe biyar daidai ta fito daga part din nasu na ma’aikata kafin ta wuce sama, kamar kullum yauma ko’ina shuru babu motsi saima haske daya bade ko’ina, saman ta wuce cikin natsuwa kanta a kasa, daidai nan daddyn barad ya futo don zuwa sallah, gaishesa tayi kafin ta wuce part din taj. Koda ta shiga part din batayi gigin shiga bangarensa ba saida ta gama gyaran parlorn kafin ta nufi bedroom din. Lokacin data shiga yana daga zaune kamar kuwa jiran ta yake yi, murmushi yayi mata wanda ya sata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yau bata shugo ta taddashi yana kuka ba kamar kullum, “friend!!!” “Naam friend good morning” Ta amsa shi, murmushi kawai yayi mata kafin yace “first love batazo ba?” Yanda yayi maganar abun tausayi, saida ta karaso ta gane yanayin da yake ciki, he looks so pale, bakinshi ya vushe sosai yayi fariii tarr kamar wadda ke jinya, ga idanunshi sunyi jaa sosai. Haka kawai taji kamar he doesn’t sound like yanda yake koda yaushe, “friend kayi brush?, ga breakfast na kawo maka” Daidai nan ta karaso bakin gado ta dan duqa don ajiye tray din gefen bedside table. Kallon corn soup din yayi, take ya soma jin wani abu ya soma zuwan mashi maqogaron shi kamar amai, batama lura dashi ba ta dauka bowl ta miko mashi, daidai nan kuwa ya soma kakarin amai, lokaci guda ya burkice, amai yake son saidai cikin nashi babu wani abun arziki a cikinsa da zai amayar, ganin yanda yake struggle tare da riqe maqogaron shi yasa ta saurin ajiye bowl din hankali atashe. “Subhanallah!! Menene? Wani abun ke damunka” Nuni yayi mata da bowl din kafin ya kauda kanshi gefe, “bana so” Sai a lokacin ta lura da abuncin ne baya so, gashi batasan ya zata ya ba, abunda aka rubuta kenan a breakfast timetable dinshi kenan, gashi dole saiyaci abunci zaisha magani. “Baka son wannan?” Ta karashe tana nuna mashi bowl din, girgiza mata kai yayi abun tausayi, “meysa baka so?” “I hate it” ya sake fada “Kayi hakuri kasha kaji friend saboda ka samu kasha magani Okay?” Juya mata baya yayi a shagwabe tare da nade hannayenshi a kirjinshi “no noo banaso” Ya karashe kamar zaiyi kuka. “Friend dan Allah ko kadan ne kaji? Kaga maganinka ma baka sha ba kar lokaci ya kure” “I don’t want to” “Idan baka sha ba first love zatayi fushi dakai” sabeeha ta fada hoping hakan zaisa ya sha, ai kuwa bata gama karashe maganr bama ya juyo ya zuba mata idanunshi, idanunshi da sukayi jaa ya zaro mata shi “zatayi fushi sosai?” “Eh zatayi fushi dakai sosai” Sauke idanunshi yayi kasa irin yanda yara keyi kamar bazaice komai chan kuma ya hadiye wani irin miyau mai daci a bakinsa Hannunsa ya miqo mata, hakan yasa ta ajiye mashi bowl din a akan lap dinshi. Kallon bowl din yayi kafin ya runtse idanunshi ya soma diban soup din yana kaiwa baki daga yanda yake sha zaka gane baya so kwata kwata kuma baya mashi dadi a baki, saida yasha kusan rabi kafin ya maido da dubanshi gareta yace “friend ya isheni” “Saura kadan friend ka shanye please kaji? Bana son first love tayi fushi okay?” Haka nan ya cigaba da sha harya shanye tas da kyar, sabeeha na ganin haka tayi saurin karban bowl din tace “yauwa friend,” “Friend zanje toilet please i what to pee” “Okay tohm” sabeeha ta amsa shi tana dan yin baya don ta bashi hanya ya wuce. Kafafunshi ya soma saukewa kasa kafin ya miqe, taku daya yayi ya soma yin baya kamar zai fadi, cikin hanzari sabeeha ta karaso ta kama hannunshi, wani irin zafi taji dayasa ta sakin hannun ta kalli fuskanshi, layi taga ya soma yi wanda ya sata tsorata lokaci guda ta sake taba hannun nashi, yanda kasan daman neman makafa yake gaba daya ya sakar mata jikinshi, wani irin wahalallen nunfashi ta sauke “ wayyo allah na, zaka karyani” Tururin da jikinsa ke fitarwa yasa hankalinta ya koma kanshi gaba daya “friend are you okay?, jikinka akwai zafi,” Baya jin abunda take fada ma gaba daya saboda yanda gaba daya yaji wani irin dummm a kunenshi lokacin daya miqe “Zanyi pee” Da taimakonta suka karasa cikin bathroom din, hannunshi har zuwa lokacin yana cikin nata, koda yazo yin pee din ita ta taimaka ta zare mashi mazugin tana kauda ido kafin ta fuce daga bathroom din. Dakin ta koma ta kwashe bowl din kafin ta fuce zuwa kicin. Ta dan dade kafin ta dawo cikin dakin saboda wanke bowl din datayi, da mamaki ta karasa bathroom din ganin kamar bai futo ba, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta cewa “ka gama?” Nan ma shuru babu response, hankalinta ne ya soma tashi,bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta bude kofar ta sa kai ciki, ganinshi a kasa helplessly yasa ta karasowa cikin sauri, babu abunda yake sai kakarin amai gashi aman yaqi zuwa, da sauri ta karasa inda yake ta tsugunnawa, gaba daya ya gigice, babu abunda yake sai kuka, yana jinta a kusa dashi ya nanukota, jikinta har rawa yake. Daburcewa sabeeha tayi hartama fi shi shiga tashin hankali ganin yanda yake faman tura jikinshi ga nata, aman dake maqale a moqogoron shi ne ya soma zubowa, gaba daya ya amayar da wannan soup din a jikinta wajen gaban rigarta, baiwar allah ko kyankyaminsa bata ji ba saima dabbing bayanshi data dunga yi, struggling sosai ya dunga yi wajen amayar da abunda ke cikinshi tass, ga jikinshi yayi wani irin zumm sosai. Saida ya gama tass kafin komai ya dan lafa mashi ya kwantar da kanshi a kafadarta jiki a mace ,gaba daya ya gama batasu daga shi har ita, “friend i want to see first love please,” Fashewa yayi da kuka don daman idan yana rashin lpy irin wannan indai ba hidaya ya gani ba sai yayi ta kuka. Wani irin kuka ne ya zo ma sabeeha, allah ya bata wata iriyar raunaniyar zuciya mai rauni, tana da tausayi sosai, musamman idan taga mara lpy, lokacin da aka tafi da inna asibiti kwana tayi tana kuka, duk da zaman su da inna ba wani dadi yake ba hakan baisata tausaya mata ba lokacin da za a kaita asibiti, balle kuma wannnan daya gama shiga ranta saboda lalurar shi, “I’m so sorry friend, wallahi bansan ranka baya so ba da bazan baka ba, i’m so sorry please kaji” Sun jima anan zaune, gaba daya ta zama kamar wata yar tsana a zaune gashi ya rufeta ruff da girman jikinsa daman gata ba tsayin kirki ba ga dan jikin nan nata. Saida taji ya daina kukan kafin itama ta tsagaita, miqewa ta soma yi ya ruko hannunta “don’t leave me please, karki barni yanda first love ta barni, stay with me, i don’t want to be alone” Wannan furuci nashi ba karamin narkar mata da zuciya yayi ba don saika rantse mai hankali ne yayi maganar, tasan yana da rashin lpy amma kuma bata san dalilin dayasa kullum yake daki ba dukda ta yanke hakan saboda rashin lafiyarshi amma harga allah yana buqatar yan uwanshi a kusa dashi koba komai shima mutunne kuma yana da zuciya ta dan adam bai chan chanci wannnan ba, saidai tunawa da kaddarar sa kenan yasa ta jin wani irin. Hannunshi da jijiyoyinsa da suka futo rado rado ta zuba ma idanu don fatarsa fara ce tass, samun kanta tayi ta komawa ta tsugunna a gabanshi ta riko hannunshi “bazan barka ba friend, i promise,” Murmushi kawai yayi mata kafin ta taimaka mashi ya miqe zuwa wajen basin, wanke mashi baki tayi da kanta kafin ta rakashi har bedroom ya kwanta ta jawo mashi duvet ta rufe shi. Toilet din ta koma ta gyara shi tsaf sannan ta gyara gaban rigarta daya bata mata kafin ta futo, lokacin data fito har ya soma barcin wahala, sai a lokacin ta tina baisha maganinsa ba, don dole badan taso ba sai dan tsoron kar abunda ya faru kwanaki yasa ta soma tashinsa ahankali, maganin ta bashi yasha kafin ya koma, Zama tayi daga chan gefe a kasa ta hade kafafunta a kirjinta ta zuba mashi idanu. He look so innocent, daga yanda yake barcin ma kasan a wahale yakeyi don daga ganin yanda yake furzar da numfashi zaka san yana jin babu dadi. Zaman awa kusan biyu tayi barci ya soma daukan ta tana gyangyadawa har ya fuzgeta, ba ita ta farka ba sai wajen karfe daya, cikin sauri ta tashi zuwa bakin gadon sa, yanda ta barshi haka ta taddashi yana barci peacefully, ko gyara kwanciyar baiyi ba yana mai fuskantar ceiling, jikinsa kwata kwata baya motsawa badan nunfashi da takeji yana futarwa ba zata rantse ko matacce ne, gaba daya jikinsa ya saki. Taba shi ta soma yi a hankali, don jin ko da zafi jikin nashi, bataji wani zafi ba hakan ya tabbatar mata ya sauka zazzabin nashi, hamdala tayi ta dauke hannunta daga wuyanshi. ,Futa tayi daga dakin ta sauka kasa zuwan part dinsu don gabatar da sallar dhuhur. Saida ta idar da sallah yar ghana ta shugo bangaren su, murmushi sabeeha tayi mata don yanxu sun saba sosai, “kin dawo?” Yar ghana ta tambayeta. “Eh na dawo,mouryoum” (sunan yar ghana kenan) “Ay nazo dazu inata nemanki ban sameki ba, ashe baki dawo ba, kinsha aiki” Hijab dinta datayi sallah dashi ta nannade tana mai sauraron yar ghana, “ayyuka ne sukayi min yawa yau shiyasa ban sauko ba” Kallon dakin yar ghana ta soma yi, ganin sauran yan dakin basa nan yasa ta jan sabeeha zuwa bakin gado ta zaunar da ita kafin tace “sabeeha niko inason tambayar ki wani abu out of curiosity” Zama sukayi bakin gadon sabeeha kafin yar ghana ta cigaba da magana “dan allah menene a saman nan?,” Atsorace sabeeha ta kalleta tana mai kokarin karantarta “meysa kike son sanin abunda ke saman?” “Ba komai, I’m just so curious, ki fada min kinji” “Ni bansan menene a saman ba” sabeeha ta bata amsa tana mai kauda kanta gefe, cije lebe kawai yar ghana Tayi kafin tace “zan baki kudi in kika fada min” Wani tunani ne ya zoma sabeeha, ta kasa gane wannan yar ghana din da yanda take yawan tambayarta da bugar cikin ta akan al’amuran dake sama, kullum zille mata takeyi ta hanyar fada mata bata sani ba saidai yanxu ta fara bata tsoro don yawan tambayar nata yayi yawa, wata dabara ce tazo mata wadda batama san ta iya ba. “Ni gaskia ban sani ba, amma nasan head ta sani idan kinaso zaki iya tambayarta saita fada maki” Hankali a tashe yar ghana tace “ah ah bazan iya tambayarta ba ni fa daman kawai I’m curious ne” Tabe baki sabeeha tayi kafin ta miqe tace “ki bari toh ni zan tambayar maki ita” “Ki rufa mana asiri, wannan maganar zaisa a koremu daga ni har ke” Toilet sabeeha ta wuce tana kunshe dariyar data zo mata, yanxu ta kara tabbatar da wannan yar ghanar tana da gulma sosai. Hidaya!!!! Anatse ta futo daga office, hannunta riqe da jakarta, employees dinta gaba daya babu abunda suke sai gaisheta, ko sau goma kuwa zata sauko sai sun sake gaisheta wannan policy din da kowa ya daukar ma kanshi kenan gudun kar a koreshi, wani baqin shade ne akan fuskanta, tasha mur bakin nan yasha red matte lipstick, yau dai a bossy hidayarta tazo office din, basement ta sauka wajen private parking lot dinta, key din dake hannunta ta danna Nan take blue LV car dinta ta hau kara, tana karasowa inda motar take ta bude tare da shigewa ciki, har zuwa lokacin wayarta ruri takeyi, Jakarta ta wulla gefe kafin ta kunna motar. Connecting wayarta da motar tayi kafin tayi reverse, maganganu ta soma yi cikin turanci, kafin call ya shiga, harkar smart digital kenan, nan take call din ya shiga, ringing daya akayi picking, “go and pick up barad” tana kaiwa nan ta futo da haddaiyar motar tata daga basement din, gate din futa daga wajen ma daban ne don an kebar da wajen just for ceo. With high speed ta hau kan titi tana murza steering, kallon dash board din motar tayi ganin call na sake shigowa da wata unknown number, kara speed tayi kamar zata tashi ranta a mugun bace, tafiyar minti ashirin tayi ta karaso wani beach, sai a lokacin ta rage speed din motar tata, wata hanya tabi daga gefe inda ya kaita har wajen jiragen ruwa na cruise sai na wasu containers, daidai wajen tayi parking kafin wasu armed guard sukazo suka amshi key din don yin parking, bata tsaya amsa gaisuwar su ba ta wuce wajen tafkeken boat dinta, mutanen dake kula da boat din na ganinta sukayi saurin karasowa suna duqa mata, “welcome ma’am” ba tare data amsa su ba tace code 5 Sanin mai hakan ke nufi yasa sukayi saurin bin bayanta, nan take suka soma kunna engine boat din cikin gaggawa, Ita kuwa tana shiga ciki ta samu waje ta zauna, fadin irin tsaruwar cikin boat dinma bata lokaci ne yanda kasan gida, babu abunda babu aciki ga girma. Tundata zauna take girgiza kafafunta da yasha zobunan kafa kaf kaf, shade din fuskanta na nan gar zuwa lokaci, bini bini take duban agogon dake hannunta, saida suka dauka wajen awa guda kafin jirgin ya tsaya, kamar jira take kuwa tayi saurin miqewa ta dauki jakarta ta futo cikin qasaita. Kallon wajen ta soma yi, yau wajen wata guda kenan rabonta data zo wajen nan sai gashi wannan useless mutanen nan suna son su saka mata ciwon kai. Island ne mai shegen girma sai wani tafkeken gidan guda daya tal da ake hango shi daga nesa, gaba daya ciyayi ya rufe gidan, wajen nada shegen girma kamar daji. Futowa tayi ta nufi hanyar cikin island din ko tsoron wajen bata ji, ni kaina mai kawo maku rahoto saida na danji tsoro, baka jin komai sai kukan tsintsaye da ciyayi. Daidai bakin gate faya zagaye gaba daya wannan dajin ta tsaya tare da scanning kanta, nan take gate din ya bude,inda motar dake parke a wajen ta karasa, driver dake zaman jiranta yana sanye da uniform fari kal ne ya bude mata kujerar baya, zama tayi ta hakimce kafin ya rufo kofar. Hannu ya daga mata ya rissinar da kanshi alamun gaisuwa kamar he’s deaf baya ji, hannu kawai ta daga mashi yaja motar suka miqi hanyar. Sun kai wajen minti biyar kafun su karaso gaban wannan babban gidan dana hango daga bakin island din. Gida ne babba sosai ba karami ba, bata ma jira driver ya bude mata kofa ba ta futo. Taku dai dai takeyi harta karaso bakin kofar shiga gidan, thump print dinta ta saka kofar ta bude. Abun mamaki daga waje dai gida ne mai kyau saidai daga ciki babu komai empty, takun tafiyarta yasa suka juyo a rikice, maza ne su kusan hudu gabzaza suna zaune akan kujerun karfe suna cin abuncin, suna ganinta kuwa suka mimike tsaye sukayi layi kafin su soma sunkuyar da kansu, “welcome ma’am” Bata amsa su ba ta tsaya a gabansu, daya bayan daya ta bisu da kallo rai a bace, daya daga cikin su ne ya dauki kujera ya ajiye mata daga gefe kafin ya koma gefe ya tsaya wajen da sauran suke tsaye. Kallon kujerar tayi kafin ta kaida dubanta ga abuncin da suke ci, lokaci guda taji wani maqoqon bakin ciki ya zo mata, takowa tayi inda suke har gaban wanda ya ajiye mata kujera, babu zato babu tsammani sukaji tasss tass har sau uku, saurin dafe wajen yayi sauran na ganin haka sukayi kneeling a gabanta, “Har kuna da time din cin abunci?,shin kunsan problem din dake gaban mu idan har ya tabbata akwai wanda yasan da wannan al’amarin?” Wanda ta mara ne yayi saurin duqawa shima, “we’re sorry ma’am” “Sorry will not fix this? Wani irin useless mutane ne ku da bazaku iya aiki ba tare da kuskure ba? Looks like kuna son nayi wiping dinku ne?” A tare suka soma cewa “no ma’am” “Now tell me how did you handle it?” Rarraba idanu suka somayi daya bayan daya suna kallon juna, ogan su ne yayi karfin halin cewa “madam kinsan bamu taba yi maki kuskure ba, kuma na tabbatar maki wannan karan ma bamu bar any lead da zai nuna cewa intentionally hit and run ac….” Shade din fuskanta ta cire,bacin rai kwance a idanunta, dukda sun tabbatar mata basuyi wani mistake ba tana jin this is not right,” Wani irin disgusting kallo tayi masu a kaskance bayan ta dakatar dashi kafin tayi pointing dinsu daya bayan daya da hannunta “be sure of what you said, don wallahi kusan abunda zai biyo baya idan har kunyi wani kuskuren” Tana kaiwa nan ta fuce daga cikin gidan tana furzar da nunfashi mai zafi, idanunta har wani kif kif sukeyi tsabar masifa. Tana fita kuwa suka miqe taaye suna kabe wandunan su. “Kai wannan matar fah kamar she’s a psychopath, zata iya yin komai wallahi,” Ogan su ne ya kalli wanda yayi magana kafin ya shago wuyanshi yace “ba saida na fada maka kan cewa karkace komai ba? “ “Sorry sir” “Ina footage din, yau babu wanda zaibar wajennen, inason mu sake duba footage din again and again” “Yes sir” Karfe uku da rabi daidai sabeeha ta koma part din, dakinsa ta wuce direct bakinta kunshe da sallama, tundaga bakin kofar dakin ta soma jin fitar nunfashinsa kamar yana battling da breath dinshi. Karasowa inda yake tayi hankali a tashe, yana nan kwance kamar an qame shi, nunfashi sa ne kawai ke fita da kyar tsabar zazzabin dake cinshi. “Friend friend are you okay” Duvet din ta yaye mashi, ya jike jargab gaba dayanshi,tabashi ta soma yi don ya tashi don duk a tunanin maybe mafarki yake yi saboda ayanda yake nunfashin da yanda zufa ta wankeshi saida taji zafin ne ta gane cewa zazzabin da yayi dazu ne ya dawo mashi. “Friend friend” ta soma kiranshi, shuru babu response, at that point hankalinta ya gaba tashi, gaba daya tama rasa ya zatayi, takai wajen kusan 30mins shuru babu response, wani tunani ne yazo ranta, to kodai ya suka ne? Ta tambayi kanta, bata jira bama kanta amsa ba ta wuce bathroom ta debo ruwa a bowl ta dawo bedroom din, wash cloth ta tsoma cikin bowl din kafin ta soma shafa mashi a fuskanshi, nan ma dai shuru, ta dade sosai tana goga mashi tana hawaye har ruwan yayi sanyi, lokacin ana maganar wajen karfe hudu, kamar da wasa ta dago taga idanunshi sun soma budewa, idon yayi jaa sosai, Hamdala tayi kafin tace “meysa Kaqi tashi? Hankalina duk ya tashi na dauka wani abu ne ya sameka” Da hausa tayi maganar so bai gane abunda take nufi ba don haka kawai ya zuba mata idanu, wannan ruwan data goga mashi a jiki ya sashi jin sanyi sosai, saida ya farka nema zazzabin yayi doubling, take ya fara karkarwa kaf kaf, hakoranshi na gogayya dana juna, burkice dai sabeeha ta burkice sosai don unexpectedly ya fara jijiga ba kamar dazu da yake barci ba kwata kwata baya motsawa, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” ta furta ganin idanunshi na neman qafewa, “na shiga uku don Allah meke damunka? Ka fada min menene?zazzabin ne?” Ta sake tambayarshi hankali a tashe, burgimar daya farayi ne yasa ta shiga wani sabon hankali, kankace me bata ankara sai ji tayi dimm ya fado kasa, cikin sauri ta nufi hanyar fita daga dakin harma part din gaba daya, karar dataji na futowa daga sitting room dake saman ne yasa kawai ta nufi wajen hankali a tashe kamar an jeho ta, fadwa dake zaune tana waya afiya kima na daga gefenta tana cin pizza tana kallo suka zuba ma sabeeha ido da mamaki, jikinta na kyarma ta shugo bedroom din. Kallonta sukeyi afiya ce tayi saurin cewa “ke bakida hankali ne, wannan illiterate dinfa ko harda mahaukata ne suke mana aiki” Fadwa ce data gane ta tayi saurin katse wayarta ta kalli afiya tace “thats new maid din big baby” “Oh da alamu itama haukan ya taba kanta kenan” afiya ta fada sounding so annoyed Fadwa ce kawai ta kalleta tace “me ya shugo dake? “Madam, frien…. Sorry sir ne bashida lafiya” Afiya ce tayi saurin cewa “daman wayace maki shi mai lafiya ne? Ni bansan wake kawo irin waennan africans din nan ba? They are the stupidest people” Sauke kai sabeeha tayi hawaye na gangaro nata, fadwa ce ta sake cewa “go and do your job properly” Jiki a Mace sabeeha ta juya ta fito daga part din, gaba daya ta rasa ya zatayi, wajen wa zataje? Tunawa da head yasa ta saurin sauka kasa tana hawaye, daidai hanyar dazai kaita ga dakin head tayi karo da yar ghana, kallonta yar ghana tayi ganin duk ta burkice yasa ta cewa “sabeeha? Are you okay?” Sabeeha batama lura da ita ba ta wuce dakin head, ciki ta shige ta rufo kofar, duve dube ta soma yi ganin bata nan yasa ta saurin fitowa, a bakin kofa ta sake tadda yar ghana a tsaye, “ina head?” “I dont know but maybe tana kitchen” Kitchen din sabeeha ta nufa hankali a tashe, tana shiga ta hangota cikin sauri ta karasa inda take ganin babu kowa a kitchen din. “Head, please ki taimaka min, sir bashida lafiya” A burkice head ta soma duban kitchen din kafin ta janyo hannunta suka fuce daga kitcehn din, wani corridor sukabi inda take tabbatar da babu kowa a wajen kuma babu wanda zai jisu “Ke bakida hankali? Wayace maki zaki iya wannan maganar a ko’ina? Shin kin manta you’re not to disclosed abunda ya shafe shi ba?” “I’m sorry head, wallahi bashi da lafiya he’s sick” Buge mata baki head tayi “and wayace maki daman mai lafiya ne shi? Ina mai baki shawara idan har kinason rayuwarki da lafiyarki dole sai kinbi yanda aka kayyade maki, dont ever step down and say a word about abunda ke sama” Tana kaiwa nan ta fuce, sabeeha dai hawaye bata bar yinshi ba anan tsaye, wannan wani irin masifa ne haka, ayanda take ganin yanda yake wahala zai iya mutuwa wallahi, tunawa da kalamanshi da yayi mata dazu inda yake ce mata karta barshi yasa ta komawa zuwa saman, a daidai nan ta bakin kofar kitchen din ta hango yar ghana a tsaye ta labe,bata ma tsaya bi takanta ba don ba wannan ne agabanta ba yanxu ta wuce sama. Koda ta karaso sama tana jiyo yanda fadwa da afiya ke hirarsu suna kallo, tsugunnawa kawai tayi ta soma hawayen takaici, dukda batasan alakarshi dasu ba amma yanda taga kammanin su ta tabbatar yan uwansa ne suma, ranta yayi mugun baci da yanda suka amsa ta lokacin data shiga wajen su, wannan wani irin ahali ne? Ta soma tambayar kanta? Ita tasan mara lafiya zama ake dashi shi kuma wannan gudunsa akeyi saboda wani dalilin daban wanda bata san koma menene ba saidai tana jin harga allah ba ayi mashi adalci ba. Tana nan tsugunne dadyn barad ya karaso saman shida barad, daman shi yaje ya daukosa yau, tun daga bakin stairs ya fara jin sheshekar kukan nata, da mamaki kuma ya ganta a zaune bakin kofar dakin tana kuka. “What’s going on here?” Cikin sauri sabeeha ta dago kanta, ganin wanda ke gabanta ya sata miqewa cikin gaggawa, “akwai wata matsala ne?” Ya sake tambayarta Kamar jira kuwa take ta girgiza mashi kai “sir please friend bashida lafiya” Shuru yayi yana wani nazari, ganin yanda take kuka yasa shi kallon barad yace “go and freshen up okay?” Yana kaiwa nan ya nufi part din taj, kofar ya bude sabeeha na biye dashi har cikin bedroom din, tun daga nesa ya hangoshi a kasa kamar matacce ga hannunsa daya ballaqe shi gefe, cikin hanzari kuwa jamid ya karasa inda yake ya juyoshi, jikinshi ya koma jawur, har zuwa lokacin karkarwa yake, “Innalillahi, whats going on here? Me ya sameshi?” Jiki na bari sabeeha ta soma bayani, “sir tun safe yake zazzabi bayan na bashi medication dinshi sai yayi barci By 3 na dawo zan bashi second dose shine naga baya motsi. Duk rikicewar sabeeha bata kai jamid ba, jijiga taj din ya soma yi “Tajudeen hey hey!!! Open your eyes” Ay Inaaaa taj baya ji kwta kwata, idanun nan sun rufe ruff, rasa abunyi jamid yayi, tunani kala kala Na yawo a ranshi, karshe dai kawai yayi deciding daukarshi gaba daya, “Zoki taimaka min” Matsowa tayi ta kama hannunshi don taimaka mashi, dakyar take jan hannun tana zufa harda nishi, haka nan jamid ya daukeshi duk da shi namiji ne dakyar ya daga shi ya sashi a bayanshi don yana da girma sosai masha Allah. “Bude kofar” ya umarci sabeeha, Kofar ta bude ya fito dashi a bayansa, sabeeha na biye dasu tana kuka har suka fito daga part din, suna nufin sauka kasa saiga hidaya ta hauro last stair,da mamaki take kallon abunda idanunta ke ganar mata, tabbas big baby ta hango a bayan jamid. Ganin yana neman wuceta yasa ta saurin damqo hannunshi ta daka mashi tsawa kamar ba mijinta ba “Jamiddddddd…whats going on here whats this? Are you out of your mind ina zaka kaishi?” Yasan halinta don haka ya amsa ta “bashida lafiya he’s in a critical condition?” “Wait what? Ina zaka kaishe then?” Wata iriyar tsawa ya daka mata “Shin bakiji me nace bane? He’s in critical condition and you’re still questioning me?” “Toh daman wa yace yana da lafiya? Look jamid babu inda zaka kaishi, zan kira medical team dinshi suzo yanxu” “Hidayaaaa!!! Meysa bakida tunani ne? Whys your heart sore? Shin kina jin abunda kike fada kuwa” “Majid!!!!!” Itama ta daka mashi tsawa, su fadwa tuni suka fito suka tsaya suna kallon ikon allah “ how dare you? How dare you? Kai waye nashi? Who are you to him? His guardian angel or what? Ni ce guardian dinshi? He’s under my care saboda shi kadai ne kanina, kana son ka nuna min ka fini sonshi ne ko ka fini damuwa dashi? You’re making me look at you as a hypocrite,” Yanda kasan ta buga mashi arrow a kirji haka yaji, yau hidaya da bakinta ke fadin mashi cewa tana kallonshi a matsayin hypocrite? Kasa motsawa kawai yayi, badan taj yana da special waje a tarihin rayuwar shi ba daya barshi da ita kawai saidai bazai iya ba dole ya zama strong and komai zata ce bazai taba saka shi giving up akan taj ba saboda karfin alqawari. Wayarta ta daga ta soma dialing heath team din dake kula dashi. Bawan allah taj yana nan ya gama galabaita sabeeha kuwa kukan da take ya wuce musali dukda kunshe kukan takeyi don karya futo fili, fadwa da afiya kuwa kamar suna kallon tv, yau wata takwas kenan rabon da su ganshi sai yau, ya chanza sosai kamar bashi ba, Taj mai kwalisa mai class da girman kai da aji shine ake fada akanshi, idan ance masu he will look helpless kamar yanxu zasu rantse karya ne,tabe baki afiya tafi ita ranta ya gama baci ganin yanda ake ta fada akanshi, sai taji tsanarshi na ninkuwa a ranta, whys the world revolve around him? Kowa is trying to protect him, abunda yafi damunta shine yanda hidaya ta tsaya akanshi, ita wannan abun yana damunta sosai. **** Cikin yan mintuna kadan saiga health team sunzo, lokacin jamid ya maidashi daki ya kwantar dashi. Cikin gaggawa suka soma dubashi suka sa mashi ruwa da allurori irin nasu na masu matsalar amnesia, wani irin special care aka bashi na gaggawa har aka samu ya soma dawowa daidai. Saida doctor ya tabbatar masu cewa zaiji sauqi kuam he’s stable kafin ya fita da team dinshi. Sabeeha na rabe daga gefe ta kasa tafiya, baiwar allah ta tsorata sosai. Hidaya ce ta futa ba tare da ta kalli inda sabeehar ke tsaye ba, tana fita jamid ya miqe shima, “please take care of him dan Allah karki bar kusa dashi i trust you okay?” Girgiza mashi kai tayi alamun gamsuwa kafin ta karasa bakin gadon ta zuba mashi idanu abun tausayi. Majid na fita dakin su ya wuce, yana shiga ganin bata dakin yasa ya wuce closet room, kofar ya banko ya shiga, yana shiga ya ganta tana kokarin rage kayan jikinta, “Hidaya!!!” Wani irin kallo tayi mashi, “ please bani da time din wannan surutan naka? Na fada maka whatever comes around matiqar yayi involving big baby ne babu ruwanka, don babu ruwana da kai mijina ne duk abunda nayi…” Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa “Wow,hidaya, you always don’t fail to amaze me so impressive, bazan tsaya muna jayayya dake ba but inason ki sani, babu wanda ya sanki sama dani? Ciki da waje, i know all your movements da intentions dinki, kina ganin wannan abubuwan da kikeyi shi zai rufe abunda ke zuciyarki dana karanceshi tun shekaru da suka wuce? Idan har zaki yaudari duniya ni bazaki taba yaudarata ba, i’m warning you, don’t try my patience, mu tafi a haka har allah ya bashi lafiya, saidai ina so kisan cewa ko me zakice bazai taba hanani shiga al’amarin taj ba, you can never stop me, duk abunda zakiyi kiyi,” Yana kaiwa nan ya fuce rai a bace. Saurin runtse idanunta tayi da sukayi jaa sosai, ya zatayi da jamid, ya zatayi da jamid, kamar mahaukaciya haka ta soma watsar da kayan dresser dinta, me yake nufi kenan? Dole yasan da wani abu kenan,? Whats in his mind? Tabbas tasan jamid shi yafi kowa saninta da halinta tunda shike zaune da ita saidai bata taba tsammanin zaiyi threatening dinta ba, Zarya ta soma yi tsakanin dakin tana tunani, “i need to do something, kafin lokaci ya kure” Ta fada ma kanta…….. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 25-26 Washe gari da safe likitan dake kula da Taj ya sake dawowa don duba lafiyarshi, lokacin da suka shigo sabeeha na daga zaune tana goge mashi jikinsa da ruwa mai dumi, gaba daya ya zama pale har zuwa lokacin barci yakeyi ga drip din hannunshi daya kare da ba a cire ba. Jamid ya shugo dakin yafi a irga, duk after an hour sai ya shigo ya duba sa. Ba karamin dadin ganin yanda sabeeha ke kula dashi yaji ba, a yanda yaga alamu ma kamar batayi barci ba kwata kwata, daga yanayin idanunta he can tell how worried she is, sai yanxu yake ganin asalin yanda ake damuwa da mutun tsakani da allah dukda basu da wata alaqa su kuwa yan uwanshi kuma jininshi babu wanda ya damu kamar haka. Hidaya ce ta fara shugowa sai doctor dake biye da ita a baya yana mata bayani. Jamid na daga tsaye a gefe while sabeeha ta shiga bathroom don zubarda sauran ruwan. Gaisawa jamid yayi da doctor, hidaya kuwa ko kallon inda yake batayi ba daman ba a dakinsu ya kwana ba, dayan dakin ya tafi. Yan dube dube doctor yayi kafin ya cire mashi drip din hannunshi, wasu magunguna ya futo dasu da wasu allurai ya soma yi mashi, yana gama wa ya soma masu bayani akan magungunan da za a dunga bashi kullum saboda kar zazzabin ya dawo. “Meysa bai tashi ba har yanxu?” Jamid ya jefo masa tanbaya “Saboda alluran da akayi mashi na zazzabin yana da karfi sosai, kuma tasu allurar ba normal injection bane kamar na normal mutane “Inason bayanai akan magungunan shi da progress dinshi, hope hakan babu matsala?” Murmushi kawai doctor yayi kafin ya dubi hidaya data kauda kanta gefe, “no problem sir” Girgiza kai jamid yayi ya nade hannayenshi a kirji, hidaya dai ranta ya gama baci, ashe dai da gaske yake, hada ido sukayi da doctor kafin ya girgiza mata kai, tsaki kawai ta doka wanda yasa suka kalleta gaba daya. “Babu wani matsala yanxu, kawai yana buqatar proper care ne, nayi mamakin zazzabin shi daya sauka da wuri haka na dauka ma zan dawo na tadda he’s still having it, looks like kunyi natural remedy don shi kadai ke sa zazzabi ya warke lokaci guda ba kamar medication ba, medication process yana daukan lokaci” Girgiza kai jamid yayi alamun gamsuwa daidai nan sabeeha ta sake futowa da wani warm ruwan data sauyi harda wash cloth a hannunta. Kallonta sukayi gaba dayansu, ita bata ma lura dasu ba don jamid ta bari anan tsaye, kallonta doctor yayi kafin yace “madam, i have a suggestion, i think keeping her around him so that she can keep an eye on him is safe, don naga last time danazo na ganta anan” “Okay doctor” hidaya ta amsashi, godiya sukayi mashi kafin ya fuce. Yana futa majid ya kalli sabeeha yace “please keep an eye on him” “Okay sir” ta amsa shi shima fucewa yayi don ranshi a bace yake da hidaya ko kallonta baya son yi, sai a lokacin hidaya ta kalli sabeeha dake tsaye da bowl a hannu. Hanyar futa daga bedroom din ta nufa said atazo daidai bakin kofar tace “futo” Bin bayanta sabeeha tayi lokacin harta zauna akan kujera ta daura kafa daya kan daya, sabeeha na karasowa ta dan tsaya nesa da ita kafin ta duqa, kallon ta da kyau hidaya tayi tana wani tunani mai zurfi, at this point babu abunda ke ranta sai abunda tasa kanta, ko hango risk din batayi, bayan wannan ma bata da wani option daya wuce wannan din. nuni tayi da fuskar sabeeha tace “Remove that thing” Sai a daidai lokacin sabeeha ta dago da idanunta don ganin abunda take so ta cire, nan take ta soma rarraba idanu, tsoro da fargaba babu wanda bai dirar mata ba, “i said remove that thing” A tsorace sabeeha ta soma daga hannunta zuwa ga fuskanta, wani irij fargaba takeji da abunda zai biyo ba, idanunta harya soma kawo ruwa, hannunta kuwa har karkarwa yake. Hidaya dai kafa mata idanu tayi tana kallonta harta soma zame mask din dake fuskanta,Kasa dauke idanunta tayi daga kanta na yan seconds, gaba daya na kasa gane reaction din hidaya don kafa mata idanu tayi kawai kamar mai nazarin wani abu,kafin tayi mata wani disgusting look “kamar yanda doctor yayi suggesting zaki iya zama tare dashi, karki sake ki barshi shi kadai, keep an eye on him” “Okay madam” sabeeha ta amsata. Hidaya na fucewa sabeeha ta miqe jiki a mace ta koma bedroom din bayan ta maida mask din fuskanta, lokacin data shiga ya soma bude idanunshi da sukayi mashi nauyi, sabeeha bata lura dashi ba saida taji ya kira ta, cikin hanzari kuwa ta karasa inda yake, “friend friend ka tashi? Ya jikinka? Are you okay now? Meke damunka yanxu? I was so worried about you” Murmushin nan dai da baya dainawa yayi mata, kokarin tashi ya sake yi ta taimaka mashi ya zauna da kyau, bakinshi ya bushe yayi jaa sosai har wata yar rama yayi, “friend” ya furta ahakali “Yes me kake so friend?” Ta amsa shi “Ina first love dina, inason naganta please” shuru sabeeha tayi tana jin babu dadi, wata dabara ce tazo mata tace “laa, yanxu ta fita anan a ta kwana tare dakai” Washe baki yayi yace “da gaske?” “Yes, lokacin kana barci, tace you should get well soon kuma ka dunga shan magani zata zo ta ganka anjima” “I missed her” ya fada yana sauke kanshi kasa gwanin ban tausayi, “And she missed you too” ta amsa shi Da taimakon sabeeha yayi wanka ya shirya don ya danji karfin jikinsa sosai saboda allurar da akayi mashi, sabeeha sai nan nan take dashi, tana son ta dafa mashi abu saidai tana tsoron abunda zai biyo baya gashi fridge dinshi babu komai sai abunda aka rubuta za a dunga bashi, wannan corn soup din kuwa tayi alqawarin bazata sake bashi ba. Saida ta tabbatar yaci abunci kafin ta bashi magungunan da doctor ya bayar na zazzabi yasha duka da magungunan shi. Hidaya na komawa daki ta shiga study room dinta, tana shiga ta rufo kofar study room din, Daki ne cike da littafai sai table din da take amfani dashi wajen karatu ko research, wajen wani katon frame ta tsaya, hannunta ta sanya ta tura frame din nan take wani dan secret cupboard ya bayyana, hannunta ta sanya ta bude cupboard din nan take wani safe ya bayyana, pins din safe din ta saka ta bude, kudade ne different currency daban daban a ciki sai wasu documented papers, daya daga cikin document din ta dauka ta soma budewa, ta dade sosai tana kallon rubutun dake kan paper kafin ta dauke idanunta “wannan ne kawai zaisa komai ya dawo hannuna, thats the only way i can keep this legacy, I’ve come this far, i can’t give up” Haka ta fada a fili kafin ta maida paper cikin safe din ta rufe. Karfe daya daidai na dare ya miqe zumbur kamar wanda aka tsugunla, ko kallon inda sabeeha ke zaune baiyi ba ya sauko da kafafunshi, hannunta dake ajiye gefen gadon ta dan rankwafa bata ma san barci ya tafi da ita ba ya taka, nan take taji wani irin zafi ya ratsa kwakwalwarta, a razqne ta bude idanunta tayi yar kara don daya taka ta kamar ya balla mata yatsunta. Idanunshi dake rufe ya budesu ya soka dube dube kamar mahaukaci, ganin babu abunda zai kama yasa ya nufi bango ya soma bugun kanshi yana wata kara, a razane sabeeha ta miqe da gudu ta karasa inda yake, “Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta doka salati, “Friend friend” ta soma kiranshi, ina baya ji kwata kwata kanshi harya soma fashewa, wato wata iriyar jijiga yake yi kamar mai tabin hankali, tunda ya dafe bango da hannayenshi biyu yake bugun kanshi ga jini ya soma fitowa Wani irin mahaukacin tsoro ne ya durar mata ganin yanda ya sauya kamar bashi ba, “na shiga uku, dan Allah ka bari, zaka jika kanka ciwo wallahi, dan allah ka bari friend i beg you” Hannunshi na dama daya kama bango dashi ta rike da hannayenta, hauka fa yake muraran don kwata kwata baisan inda kanshi yake ba. Kuka sosai ta fashe dashi tana buga kafarta a kasa “dan allah ka bari, friend ka bari,zakayi ma kanka illa” Ay bata karasa ba ya gabje hannunta ta fadi wanwas a kasa har tana bugun damtsen hannunta, baima san yayi hakan ba ya cigaba da bugun kanshi, at that point ya gama jigata, ihunshi ya ninka na wanda ya soma yi, fuskanshi yayi jina jina, Saurin miqewa sabeeha ta sakeyi ta koma wajenshi ta dafa shi, “ka bari dan Allah” Haka ta dunga mashi magiya har muryarta ta soma dishashe wa, ganin fa yaqi dainawa yasa ta juya zata fita daga dakin, ko taku biyu batayi ba ya damqo ta, tare da shaqe mata wuyanta, kamar wani mai aljanu haka ya dunga jujuya idanu. Wani irin kakarin amai ta so mayi, idanunta take sukayi jaa sosai suka fito, hannayenshi biyu daya shaqe ta ta riko wajen damtsen sa, a wannan lokaci har kamshin mutuwa sai dataji, saboda mummunan riqo da yayi mata bana wasa ba, gashi namiji ne ingarma,struggling ta dunga yi da hannunshi, ihun ma da take son yi ya gagara, take jikinta ya saki hannunta dake riqe ta damtsen sa ta saki, idanunta ya soma rufewa jiki a ta sulale, binta yayi har kasan, kamar ance ya bude ido kuwa kawai sai ya saketa ya soma komawa da baya “no no no no” ya dunga furtawa a gigice, bangon ya sake komawa ya dunga bugun kanshi yana fadin no no no Sabeeha data sulale da kyar ta tattaro nunfashinta dake barazanar barin gangar jikinta, batayi giving akanshi ba dukda ta tsorata da makurar dayayi mata gaka ta sake komawa inda yake tana kuka, ganin babu sarki sai allah kawai ta rungumeshi ta baya tare da saqalo hannayeta wajen cikinsa, sai ya zamana gaba dayanta tsayinta bai wuce wajen ba.Muryarta ce ta soma dawo dashi inda ta soma sauke ajiyar zuciya ga hawayenta dake zuba akan rigarshi, she’s so weak ta jigata sosai haka nan ta soma mashi magana, “dan Allah ka bari, zaka jika kanka ciwo, first love zatayi fushi dakai please ka bari friend dan Allah,” “Leave me alone!!!” Ya daka mata tsawa a shagwabe “No bazan barka ba, dan Allah ka bari ka daina jima kanka ciwo i beg you” Shurun dataji yayi da bugun kan nashi sai kuma kasan daya zube yasa ta sakeshi, abu kamar tsafi lokaci guda kawai kanshi ya warware ya dawo big babyn shi, kanshi ya shafa yana mai duban hannun nashi, “friend jini, ciwo ne ciwo ne bana so” ya soma blabbering hankalinshi a tashe, “Friend tsaya kaji, zan cire maka shi ka daina kukan nan please” Kankamota yayi sosai duk ya gama burkicewa, wani sabon tashin hankali, wannan jinin da ya gani ya sake burkita shi don baya son ganin jini ko kadan, gashi jinin har sauka yake akan fuskanshi, “bloo….” Luuu ya sume, binshi sabeeha tayi tana kiran sunan Allah, waze kawo masu dauki yanxu? Innalillahi. Kofar da aka bude ne cikin hanzari yasa ta kallon wanda zai shugo, jamid ne ya shigo, hidaya na biye dashi a baya. Cikin tashin hankali hidaya ta karaso inda suke tana kallon yanda jini ke bin fuskanshi, nan take ta burkice itama “mey ya sameshi? Meya faru? Me kikayi mashi” Jamid daya karaso ne ya ture hidayar gefe ya duqa gaban taj, hankali a tashe ya soma tatttaba fuskanshi “taj taj, me ya sameshi, wannan jinin fah?” Sabeeha ce da hidaya ta bangajeta gefe itama ta soma magana tana hawaye, “wallahi bansan mey ya sameshi ba, yana barci kawai ya tashi ya fara bugun kanshi, na rokeshi ya bari yaqi” “Meysa baki zo kin kirani ba?, bana ce maki ki kira landline dina ba?” Kallon hidaya sabeeha tayi kafin ta sunkuyar da kanta, “Innalillahi what’s happening with my brother, big baby? Hey! Hey wake, wai meke faruwa ne, ki fada min me kikayi mashi? Whys he bleeding? Kasheshi zakiyi? Me kikayi mashi haka? “Wallahi maam banyi mashi komai” sabeeha ta fada tana hawaye ga sheshe qar kuka “You useless idiot Dibo ruwa” Ta karashe tana yoma sabeeha wani irin kallon,hanzari kuwa ta miqe ta wuce bathroom ta debo ruwa aka soma yayyafa mashi, saida jamid ya shafa mashi wajen sau uku kafin ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya soma bude idanunshi da suka kumbura, da hidaya ya fara cin karo, duk yanda jikinshi yayi tsami hakan bai sashi tashi zaune ba ya rarrafa wajenta ko kallon inda jamid dake gabanshi baiyi ba ya yunqura zuwa inda take ya rungumeta kamar zai shige jikinta, kuka sosai ya dunga yi mata yana kiran sunanta, jamid dai miqewa kawai yayi ya kasa kallon sa don zai iya zubda mashi hawaye, taj abun tausayawa ne, wai ace gashi nan dai mutun kamar kowa saidai hankalin ya banbanta, shin yaushe ne zai samu sauqi a cikin rayuwarshi wannan yaron? Abunda ya bama jamid mamaki shi yasa shi juyowa yana kallon hidaya data soma kuka itama, “I’m sorry big baby, I’m so sorry ka yafe min please bazan kara barinka ba i promise, I’m so sorry, majid mu kaishi asibiti, wallahi i dont care about our family reputation anymore,i don’t care about the family or what so ever, bazan kara grouding dinshi ba, his mental state is what i will focus on, I’m so sorry taj, abun duniya da company legacy dinmu yana neman rudana har yakai ka ga hallaka,” Kuka fa take yi sosai, daga ita har taj din, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi don abun kamar almara, kamar ba hidaya ba? Anya kuwa?” Saida ta sake kiran sunanshi ya dawo daga dogon tunanin daya fada ya kalleta “jamid call an ambulance right now please, mu kaishi asibitin, ka kira khaal ma, inason mu kaishi duk inda ya kamata, i can’t stand to see my only brother loosing it, i can’t lose him, wallahi taj is my life, he’s my everything, shiyasa I’m over protective over him kuke ganin kamar bana mashi adalci” Jamid dai kanshi ya kasa daukan abunda yake ji kuma yake gani, sai abun ya zama kamar drama take shimfidawa don he can’t believe it, hidaya? Hidayar dai daya sani? Mai shegen kafiya? Da shegen girman kai? Da dagawa? Saurin kauda tunanin dake barazar rudashi yayi ya soma dialing number doctor, don ya karba numbershi dazu dayazo tafiya don sanin abubuwan daya shafi taj da progress dunshi. Ringing daya kuwa ya dauka don he’s available 24/7, “doctor, we have a emergency muna son kazo yanxu” Daga chan ne akayai magana kafin jamid ya kashe wayan, bayan kamar munti goma sai gasu sun iso, ko da yaushe they are allowed to enter don haka koda sukazo tahlia street din basu sha wahala da security din dake patrol din dare ba anan anguwar saboda anguwa ce ta masu kudi sosai kuma suna samun threat kodayaushe musanman family taheel. Cikin gaggawa doctor ya soma dubashi, allurai akayi mashi sannan sukayi mashi dressing ciwon nashi. Saida ya gama aikinsa kafin ya masu sallama akan washe gari zai dawo zai masu bayanin komai after an yi mashi running test din kwakwalwarshi. Sallama yayi masu ya tafi, gaba daya kasa motsawa sukayi anan suka kwana harda hidaya, sai wani nan nan take da taj din, jamid dai kallonta kawai, yanxu tunaninshi baya kanta sai taj ya farfado tukunna. Washe gari doctor ya sake dawowa, har zuwa lokacin bai farfado ba, jamid harya fita ya dawo, nan ya tadda hidaya, shifa lamarin tsoro yake bashi saidai ta bashi tausayi ganin yanda kamar ta damu sosai saidai sanin halinta yasa ya kauda tunaninta aranshi kawai. Koda suka gaba gwaje gwajen su doctor ya soma masu bayani. maida dubansa yayi ga hidaya hannunshi na rike da file din taj din. “madam this is a not a good sign” “ dalilin dayasa nace wannan is not a good sign shine, daman na fada maki, ba tun yanxu ba, kanshi ya soma tabuwa, ba komai ya kawo mashi haka ba sai maybe akwai abunda ke triggering dinshi, is there any sabon activity da yake yi?” “Babu” ta amsa shi, “shiyasa na hana kowa muamala dashi saboda abunda ka fada min” ta sake bashi amsa yanda kasan sun tsara yanda suke maganar, yana fada tana bashi amsa, “hold on a second!” Jamid ya dakatar dasu, “Kuyi min elaborating yanda zan gane da kyau? Menene dalilin dayasa kika hana kowa mua’amalar dashi” Ajiyar zuciya doctor ya sauke kafin ya soma jero masa bayani, “sir, maganar gaskia stage din da yake yakai traumatic, wannan yasa mukayi blocking duk wani abu da zaisa ya tuna rayuwarshi a baya saboda wannan zai iya leading to trauma kuma wannan shine babban risk din condition dinshi yanxu ma haka we should be thankful akwai wani a kusa da shi don da babu kowa da zai tsayar dashi zai iya kashe kanshi don abun na triggering dinshi” Hankalin majeed ba karamin tashi yayi ba, hidaya dai na daga zaune ta rike hannunshi taj din tana sauraronsu harda dan hawayenta. “So what’s happening to him doctor?” “A gaskia for now dole haka zamu hakura har ya wuce stage din,ma’ana dole abar wani a kusa dashi kuma abun da ya faru jiya kan iya faruwa Koda yaushe anytime, sannan i must say, who ever is staying with him should be someone who knows him so well and knows how to calm him down” Jamid ne ya kalli hidaya yace “as far as i know yafi yarda da hidaya akan kowa” “No sir” doctor ya katse shi, hidaya dai cije leve kawai tayi jin abunda jamid ya fada “Sir, i will advice kar madam ta Zauna dashi, zamanta dashi is the biggest risk, saboda ita kadai ce bai mance ba, saboda tana da matsayi babba a zuciyarshi da gangar jikinshi, ganinta koda yaushe kan iya jawo wata matsalar daban” Charab hidaya ta chapke, “wannan dalilin yasa na hana kowa kusantar shi ciki kuwa harda kai da khaal harma dani kaina, I’m doing all of this for him,” Jamid dai bai kalleta ba saidai yana sauraronsu daga ita gar doctor din. “So what do you suggest?” “Ina ganin wannan yarinyar dake zaune dashi, why not ita ta zauna dashi koda yaushe, she’s the only person da bai taba sani ba a rayuwarshi achan baya, and ina ganin keeping her around will help him in someway” Tunani jamid ya soma yi, “but kace leaving her around him will be risk, and you advise a barta tare dashi how those that make sense?” “Majid please, kamar yanda doctor yace lets do whats best for him, … ” ta katseshi. Maido da dubanta ga doctor tayi tace “doctor please what else? Please let us know abunda ya kamata ayi?” “For now, zamu cigaba da monitoring dinshi saidai kawai wannan yarinyar ta kasance tana tare dashi kawai” Godiya hidaya tayi mashi shima jamid ya mashi kafin ya fuce daga dakin, yana futa jamid ya kalli hidaya “ki je ki huta, i will take it from here” Kamar jira kuwa take tace “okay kafin ta miqe” Kissing kumatun big baby tayi kafij ta fuce daga dakin, jamid dai har zuwa lokacin mamaki yake. Hidaya na fita ta wuce bedroom dinta,wayarta ta zaro ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma magana “good job,” Tana fadin haka ta kashe wayan ta danyi yan danne dannen ta kafin ta ajiye wayar ta wuce bathroom. Doctor na fita ya shiga motarshi daman baizo da health team dinshi ba, yau shi kadai yazo, yana shiga motarshi ya soma waya, “successfully……” yana fadin haka ya kashe wayar ya fice daga compound din. … Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 27-28 Update!!! Da sallama ta shugo dakin, tsakanin jiya da yau harta fada, wajen wuyanta yayi jaa sosai sanadiyar shaqeta dayayi, babu wanda ya lura da hakan, “good morning sir” Ta gaishesa cikin ladabi, “morning” ya amsa ta Yana son tambayarta abu saidai kuma baya son yasa ta fara tunanin wani abu dakyar dai ya soma mata magana cikin dabara, “did he do that?” Nuni yayi da wuyanta, ashe ya lura, sunkuyar da kanta tayi kasa ta kasa bashi amsa, sai hawayen dake shirin zuwan mata. “I’m sorry about that but why didn’t you call me?” Nan ma shuru tayi ta kasa ce masa komai, saida ya sake maimaita tambayar “karkiji komai tell me why?,“ Harga allah tsoro take ji saidai yanda taga ya damu yasa take jin kodai ta fada mashi, amma ta ina zata fara? Me zata ce mashi, madam ce ta hanata kira ko me? Zaima yarda da hakan kuwa? yatsun hannunta ta soma murzawa yawanci haka take idan tana tsoron fadin abu, ita kanta ta kasa gane alamuran dake gudana a gaban idanunta, komai is questionable daga wunin jiya zuwa daren jiya, Tattaro sauran maganar data rage mata a baki tayi ta soma magana “sir i couldn’t leave him, sabod aina tsoron inna tafi wani abu zai sameshi” Badan ya gamsu ba ya girgiza mata, sun dauki kusan yan mintuna a haka kafin ya kalleta yace “shekarun ki nawa?” “I’m 19 sir” ta amsa shi. Girgiza kai yayi yana tunani, Haka kawai he just feel like explaing to her about the condition, bayani ya soma yi mata da avunda doctor yace, to his surprise sai yaji ta amince, dukda yaga abunda taj din ya mata a wuyanta, she’s willing to stand by him. Ba karamin mamakin haka jamid yayi ba, toh kodai dan kudi take yin duka wannan? Ya tambayi kanshi tunawa da yanda take kula dashi da nuna damuwa dashi ya tabbatar mashi kudi bazaisa tayi hakan ba maybe haka take kuma zuciyarta ce mai kyau. Fita yayi ya barsu a daki, koda ya fito bai wuce ko’ina ba sai gidan khaal don ya mashi bayanin al’amarin taj din. Da daddare taj ya farfado, kamar koda yaushe hidaya ya sake tambaya, saida sabeeha ta lallaba shi kafij ya hakura. Cikin dare wajen karfe daya kamar jiya da daddare haka yauma ya tashi ya soma dube dube,sabeeha baiwar allah tuni ta farka daga gyangyadin data soma, yau allah ya taimaka bai tashi ya dunga bugun kanshi ba sai kukan daya dunga yi yana marin fuskanshi, kuka sosai ya dunga yi babu yanda batayi dashi ba yaqi dainawa, karshe ma dai itama kukan ta somayi tana hadashi da allah ya bari, saida ya jigata dan kanshi ya hakura har safiya idanunshi a bude, sunyi jaa har wani baqi baqi dukayi daga wajen fatar eyelid dinshi. Sabeeha dai ta maidashi kamar tv, sai kallonshi take gwanin ban tausayi. Karfe biyar daidai saiga jamid yazo, babu yanda baiyi dashi ba akan ya kwanta yaqi, saima kuka daya cigaba yana kiran first love first love dinshi. Lokacin sallah nayi jamid ya tafi ya barsu shida sabeeha, mikewa tayi ta dauro alwala anan bathroom din kafin ta futo ta tada sallah, ta dade sosai tana mashi addua, tana idarwa ta juyo ta kalleshi. Ya rame sosai ya chanza kamar bashi ba, he was so lively cikin kwanakin da suke wuce amma tsakanin jiya da yau ya chanza gaba daya. After 1 week Yau cikon sati guda kenan da wannan situation din na taj, saidai abun ya dan lafa ba kamar ranar da doctor yazi ya dubashi ba da next day. Sabeeha na kula dashi sosai haka zalika jamid, shima kullum yana tare dasu don shi baya futa office zuwa caffeee dinshi, shi ke da companying caffe mocha, dan karanin kamdani ne dake producing traditional coffee, hidaya kuwa kullum tana hanyar office kullum, ba laifi tana shugowa dakin tana dubashi saidai yawanci lokacin da take zuwa yaja barci. Su afiya da fadwa kuwa rayuwar su sukeyi hankali kwnace ba tare da sun damu ba, basu ma damu dasu san meke wakana da rayuwar dan uwan nasu ba. Tunda ba a saka su a ciki ba suma basu kai kansu ba don babu abunda zasu iya mashi. Saturday morning…. Karfe bakwai daidai sabeeha ta samu ya koma barci, saida tabbatar yayi nisa kafin ta fito daga bedroom din tayi gyare gyaren ta, tana gamawa ta sauka kasa, don kullum saita sauka ta sauya kayanta. Tunda ta sauko maids dinnan suke kallonta suna tsegumi, batabi ta kansu ba don basu ne damuwarta ba, abu daya daya dan dameta shine rabonta dataga yar ghana tun ranar data sauko kasa neman head, harta kamata tana labe, tundaga ranar bata sake ganin ta ba, gashi bata shiga al’amarin sauran maids din balle ta tambayesu inda take. Wanka tayi tana gamawa ta koma kitchen, inda ake ajiya masu abuncinsu na maid ta nufa, daya daga cikin pack din ta dauka ta koma daki. Saida taci tayi nak ta dauki hijab dinta data wanke a toilet ta futa dashi donta shanya. Wajen shanyan nasu yana daga baya wajen garden, babu kowaa wajen sai birds din dake kara a wajen da sauran kananun dabbobi da aka ajiye don kawata wajen. Tana gama shanyar ta juyo, a razane tayi baya ganin daya daga cikin maida din gidan, kallonshi tayi shima ya kalleta, duban wajen ya soma yi ganin babu kowa yasa ya fidda wayan dake hannunshi ya zura mata a aljihun gaban rigarta kafin yace “incoming call for you” Yana kaiwa nan kamar iska yabar wajen, gaba daya sabeeha ta gama tsorata, tama rasa me zatayi tana nan tsaye wayar ta soma ruri, cikin sauri ta zaro wayar daga aljihun nata, number ce ke kira, wani irin tsoro ne ya durar mata “meyzaisa wannan maid din da bata taba ganinshi ba dukda ba futowa take compound ba balle ta sansu don maza ke kula da compound din, meysa ya bata waya? Gashi kuma ana kiran wayan gashi kuma ya tafi” Daukan wayan tayi tasa a kunenta ba tare da tace uffan ba, wata kausashshiyar murya ce ta daki dodon kunenta. “You’re doing a good job,muna monitoring duk wani movement dinki,ive never taught you’re this smart, abunda bamu taba tunani ba kuma hankalin mu baizo wajen ba kin nuna mana hanya, firstly to gain your target trust, wonderful for that, Secondly yanxu aikin naki zai fara,” Jikin sabeeha ne ya soma rawa, dube dube ta soma yi hankali a tashe, babu abund atake sai innalillahi a zuciyarta, tabbas ta gane wannan muryar, muryar mutumin daya zo yace mata zatayi leqen asiri anan, gaba daya tama manta sai yanxu, ashe suna kallonta, tsoro ne ya durar mata, me mutanen nan suke so? Mene dalilin kawota da sukayi? Har yanxu kanta ya kasa daukan komai Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa “Don’t worry your self, aikinki mai sauqi ne, like i said yanxu ne ma zaki fara aikin naki, i don’t want to say abunda zai biyo baya idan kika kuskura kika bata mana plan, by now kinsan dalilin dayasa muka kawo ki gidan, your part of work is so simple” “Sir please meysa kuka kawo ni gidan nan mai zan maku?” Sabeeha ta fada adan tsorace, gaba daya attention dinta ya koma ga wayar. “Just do as i said, idan kikayi hakan rayuwar mamanki will be spared” “Mamana?, sir dan Allah kuyi hakuri, ni wallahi bansan may zan maku ba” “Its so simple, now listen…” Ya dade sosai yana mata maganganu a wayar kafin ya kashe, confusely sabeeha ke kallon wayar, ta kasa gane meysa yace tayi abunda yace tayi, ta dade soaai tana tunani har tazo to a conclusion, tabbas akwai wata boyayyi a cikin wannan gidan, gidan nan cike yake da abubuwa da dama wanda kanta ya kasa warware mata. Khaal…. Da mamaki Khaal ya tashi da kiran hidaya, rabonshi da ita tun lokacin daya zo akan maganar taj, tun daga ranar kawai ya zuba mata idanu. Shiri yayi cikin kamala, kafin ya futo,”abuh!!! Abuh!!!” Wasu yara suka taho a guje wajenshi, yaran suna kama dashi sosai, da mamaki yake kallon su, “karku buge fah” Mamansu ce ta fito sanye da abaya da alamu futa zasuyi, kyakyawa ce Masha allah, a kalla zata kai shekaru talatin da yan kai, takowa tayi ta rungume shi kafin tace “ya habibi” “Habibty, daga shopping sai ina?” “Zan kaisu disney land daga nan zamu sawo gida my love” Murmushi yayi mata kafin yace “nima zanje tahlia” Shuru tayi jikinta yayi sanyi lokaci guda tace “allah yasa yau ka samu ka ganshi” “Ameen” ya amsa ta Kissing dinta a kumatu kafin ya futa. Khaal is about 58years amma in ka ganshi zaka ce bazai wuce shekaru talatin ba, yayi aure very late hakan yasa bai da yara manya, ba kamar dan uwanshi ba taheel da yayi aure yana mid 20s dinshi. Motarshi ya shiga ya fuce daga compound din yana zullumin kiranshi da hidaya tayi. Gidan ya nufa direct, lokacin daya karaso doctor taj ya karaso shima, gaisawa sukayi da khaal kafin su shiga daga ciki, Khaal tunda yaga doctorn taj din hankalinshi ya dan tashi, yasan dai jamid yazo mashi da bayanin situation din taj din don shike zuwa ya fada mashi abunda ke faruwa game da taj din. A tare suka karaso cikin main sitting room, babu kowa a ciki don haka suka samu waje suka zauna, jamid ne ya fara saukowa da mamaki don baiyi tsammanin ganin khaal din ba, yanxun hakan ma ya fito ne don ya wuce gidanshi, gaisawa sukayi har kasa ya rusuna kuwa ya gaishesa kafin ya zauna “yanxu nake shirin zuwa chan gida ay” Murmushi khaal yayi yace “zuwan ne nima i wasn’t expecting it” Da mamaki jamid ya bude baki zaiyi magana saiga hidaya ta sauko, afiya na gefenta da fadwa, karasowa sukayi suka gaishe da khaal, hakimar ma yau fiska a sake ta gaishesa, mamaki dai bai sa khaal da jamid rufe baki ba. Shuru ne ya biyo baya kafin hidaya ta soma magana “akwai dalilin daya sa na taraku saboda decision din dana yanke akan big babu, which I believe kuma ga doctor dinshi, ya bani kwarib gwigwa akan hakan” Gyara zama khaal yayi a zuciyarshi yana hamdala don tabbas kiran nan datayi mashi akan lafiyar taj dinne saidai yayi mamakin yanda akayi harta sauko haka kuma ta nemeshi? Wannan abun ya bashi mamaki sosai. “Base on yanda doctor shi yayi mana explaining situation din da yake ciki yanxu which I believe duk kun sani, I’ve come to conclusion which I believe zai taimaka mashi sosai kuma its a step that maybe or may not lead to his recovery but I’m trying to believe it will” Sabeeha ce ta sauko kasan, kanta a kasa, yau gaba daya bata jin dadin jikinta kwata kwata, da head taci karo tana shirin fitowa daga kitchen da maids a bayanta kowannensu hannunta riqe da baverages, saida ta bari suka wuce kafin ta nufi hanyar shiga kitcehn din. Karo suka kusa yo da maid din data fito, cikin sauri sabeeha tayi baya, “sorry about that” sabeeha ta fada, dayar maid din da suka kusa gwarawa kuwa kasata zube da alamu ko rashin lafiya take yi, kallonta sabeeha tayi tace “are you okay?” “No, I’m burning up, please help me with this” Taimaka mata sabeeha tayi ta miqe kafin tace “you can go and have a rest, zan gyara maki” Godiya maid din tayi mata kafin ta fuce daga dakin, tana futa sabeeha ta kwashe abubuwan da suka zubar kafin ta sauya wasu, daman savate ne, tana gamawa ta juya ta futa daga kitcehn din, kalle kalle ta somayi don neman inda head sukabi, rasa hanya tayi don haka harta juya kuma ta tsaya, ganin head yasa ta tsaya har suka karaso, “what are you doing standing here? “Sorry head, batajin dadi ne shine na karba” “Jeki ajiye ki fito” head tayi commanding dinga. Takawa ta somayi, bugun zuciyarta na tsananta, harta shugo ciki, lokacin data shugo doctor nayi masu bayanin situation din da tak ke ciki, sannan ya dora da kanshi ya soma tabuwa, tana jin wannan ta saki savage box din batama san tayi ba, juyowa sukayi gaba daya su suka kalleta, dakata doctor yayi yana jiran ta futa kafin ya cigaba don dukda ya ganeta, Statement din da hidaya ta jefo masu yasa duk suka juyo suna kallonta, babu ins atake kallo sai inda sabeeha ke tsaye don tana kallonta saboda opposite inda take sabeeha ta tsaya, “you come here” Kafafunta ne suka soma kyarma, kamar munafuka haka ta karaso wajen, sauran duk suka bita da idanu, daga chan gefw sabeeha ta tsaya kafin hidaya ta maida dubanta gare su. Jamid ne yayi dakewar cewa “what did you just say?” Maido da dubanta tayi garesa tace “i said zanyi ma big baby aure!!!!!!” “Aure?” Fadwa ta fada tana kallon hidaya surprisingly “Ukty you must be joking, wa kike ganin zai auri mahaukaci? Good for nothing man? Mai kwakwalwar yara wow this is too much gaskia ukty you’re doing too much,” Afiya ta fada a gatsale. Wata uwar tsawa hidaya ta daka mata “don’t you dare say that again, and yes, aure zanyi ma taj because I believe shine best decision. Jamid ne ya sake kallonta rai a bace yace “hidaya are you sure kinsan me kike fada kuwa?” “Yes i do,” ta bashi amsa kai tsaye, yana kokarin sake magana khaal ya daga mashi hannu, “Waye zaki aura ma TAJ din?” Khaal ya tambayeta yana mai kallonta, lallai bai taba tunanin haka hidaya take so heartless ba, jamid dai kasa komai yayi ranshi yayi mugun baci, lallai yau ya tabbatar hidaya bazata taba chanzawa ba, shi yasan definitely akwai wata a kasa. “Her!!!!!” Dammm gaban sabeeha ya bada ganin ana nunata, saurin sauke kanta tayi kasa furgici bayyane a idanunta, kallonta suka komawa yi daga kan khaal zuwa su afiya da fadwa, “maid??? Wow” fadwa ta fada a ranta “Wannan personal caregiver din taj ce, kuma ita ce zata zama MATAR TAJ” Maido da dubansu sukayi ga hidaya, khaal ne yayi saurin cewa “a maid?” “Yes” ta amsa shi kai tsaye, Su fadwa dai kallon khaal sukayi suna jiran jin abunda zai ce, “Ba opinion dinku nake nema ba its a decision dana yanke as big babys guardian and next if kin,kuma I believe hakan ne daidai kuka nasan koda ace baida mental issues bazai bijire decision dina ba” Rai a bace khaal ya runtse idanunshi kafin ya bude, ranshi yayi mugun baci, wato hidaya ta maida taj kamar wani object din da zatayi abund ataga dama dashi abu har ya kaiga ta qasqantar tashi, yasan she’s the one who made the whole world for him, kuma ita ce number one dinshi saidai bai taba tsammanin abun nata yakai ga haka ba, he’s still confuse akan alamarin hidaya trying so hard to understand her da intentions dinta saidai yanxu komai ya baiyyana a fili. Ba zato ba tsammani sukaji amsar khaal “okay!, ba damuwa, she will be taj legal wife and i approve it but inason na san meysa ita?” “Saboda ita ke kula dashi kuma ita kadai ce ta dade dashi ba tare da wani problem ba” Wani irin murmushi hidaya tayi kafin ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya, ta dauka zata samu matsala da khaal sai gashi komai yazo gidan sauqi. Jamid dai runtse idanunshi yayi kafin ya bude, ya kalli hidaya, idanunshi sunyi jaa sosai, “Amma inason naji daga bakin wannan maid din,” Khal ya fada yana kallon sabeeha datayi sukan tsaye,kallonta khaal yayi kafin yace “what’s your full name?” Khal ya tambayetaq “Sa..bee..ha dalhatu” Ta amsa shi muryarta na breaking, “sabeeha cire mask din fuskanki” Tabe baki hidaya tayi don tasan me zasu tarar bayan ta cire kuma bata damu ba. Kanta na kasa ta soma laluben fuskanta hannunta na karkarwa, mask din ta soma zamewa ahankali har tayi nasarar cireshi gaba daya, tana cirewa suka zuba mata idanu, afiya ce ta furta “what the fuck..” bata ma san tabfurta ba, dagowa ahankali sabeeha tayi ta zuba masu idanu suma kallonta sukeyi kamar sunga tv, afiya sai tashi tayi rai a bace tabar sitting room din. Kallonta khaal yayi yana mamakin hallita iri irin a fadin duniya daban daban. Idanunta dake rufe ta bude, yarinya ce danya shaf, wallahi tsarin fuskanta ya masifar haduwa kamar an kerata daga wajn girarta zuwa idanunta, ga hancinta mai tsayi wanda ya kara ma fuskan nata kyau, bakinta… Lallai dan adam tara yake bai cika goma ba, duk kyawun da allah yayi maka sai an samu wani bangaren akasin hakan,halittar da allah yayi mata wadda ta fita daban shine bakinta, bakinta yayi wani zumbutu dalilin hakoranta da sukafi karfin fuskan nata, saida ta sakin bakin hakoran suka baiyya guda takwas reras kafa kafa kamar kacha,(gatso) ta gaban hakorin har wani kore kore yayi alamun hakoran marasa lafiya ne. Wannan part of hallittarta ta aje mana wani baqin fenti a cikin tarihin rayuwarta tun tasowarta. Saida khaal ya gama kallonta kafin ya sake jefo mata tambaya, “zaki iya auren sa?” “Khal??? Why are you even asking” hidaya ta fada “Ay ba a aure sai an samu yardar both parties, tunda shi hes not in right sense ita ay tana da hankali so dole musan idan ta amince” Sabeeha dai shuru tayi tana tuna maganar mutumin nan da sukayi waya dazu, “duk wani abu da za a tambayeki akai ko za a nemi amincewar ki karkiyi gardama, just say yes inva haka ba komai zai iya faru da ke harma dashi wannan mahaukacin” Cikin ta ne ya duri ruwa sosai, batama tsaya wani dogon tunani ba kawai tace “na amince” Wani irin disgusting kallo hidaya tayi mata kafin ta maida dubanta ga khaal, “ina son aurensu a yau” Bai musa ba yace mata “okay amma inada sharuda uku,” Gyara zamanta tayi tana sauraronsa “na farko wannan yarinyar you’ll allow her do her duties as his wife not his caregiver cinshi shan sa, when it comes to time for decision akanshi da komai nasa, sannan duk abunda taga ya dace akanshi tayi deciding babu ruwanki a ciki” “What??” “Yes sannan na biyu daga ranar da any of them ya nuna bayason wannan auren za a raba shi, and lastly hiding and grounding him has to come to an end” Shuru tayi na yan seconds, badan batada wani option ba babu abunda zaisa ta yanke wannan mummunar shawarar, Da mamaki yaji tace “okay” Wani irin murmushi kawai khaal yayi ya girgiza kanshi, tabbas akwai abunda hidaya ke shiryawa, kuma akwai kwakwaran dalili dayasata yanke wannan shawarar, the last thing da zasuga hidaya tayi shine wannan, jinjina rashin tunani da rashin mutunci irin nata kawai yake yi…. Saida suka gama magana ta fuce daga sitting room din, sabeeha na tsaye saida jamid yace ta tafi tukunna kafin ta tafi, likita kuwa already shima ya fita ya rage daga khaal sai jamid. “Khaal maysa ka amince bayan kasan kudirinta” “Jamid I’m still giving her benefit of doubt, i still dont want to believe intentions dinta,” “Then why did you agree” jamid ya sake tambayarshi don ya bi ya damu “Because i trust my instincts, mu zuba mata idanu” “Yanxu khaal aurar dashi za kayi? What if ya dawo hayyacinshi? Kana ganin bazai jawo matsala ba? Bamusan yarinyar nan ba? Bamusan ya rayuwarsu da gidansu yake ba? What if akwai problem” “Kaga hidaya? Bazata taba yin komaiba ba tare da tayi dogon bincike da tunani ba, tasan komai game da yarinyar nan, her family and all, jamid dont worry kaji, allah zai shige mana gaba, i have a feeling that the outcome of this will be good” “Shikenan khaal yaushe za ayi auren” “Anjima after dhur, a masallacin nan tahilia” Khaal ya amsa shi. *** Bayan salat dhuhur jamid ya miqa auren SABEEHA dalhatu ga Khaal wanda ke wakiltar TAJUDEEN taheel. Babu mutane da yawa cikin masjid din, su shida ne kachal according to yanda sunnah ta qai’dar, mutun uku shedu, sai biyu dake wakiltar wanda zasu aurar sai malamin dake jan sallah a masallacin. Harda certificate khaal yayi sighning na aurensu bayan an daura da sadakin ta har riyal dubu ashirin. Tunda aka daura auren Jikin jamid yayi sanyi, he’s having weird feelings about this, yana jin wannan auren da akayi ba dan alkairi akayi shi ba don yasan hidaya sarai, saidai ya kasa gane dalilin dayasa tayi suggesting hakan, kamar yanda khaal yace, yayi fatan alkhairi kawai, hakan yayi. sallama khaal yayi mashi bayan ya bashi copy of the halal marriage certificate din kafin ya tafi shi kuma ya wuce gidan. Koda ya shigo sama ya wuce direct, neman hidaya ya soma yi a saman bai ganta ba, kwata kwata bai kawo tana part din taj ba. Zama yayi ya dafe kanshi tunani kala kala Na yawo a kwakwalwar shi,tunawa da wani abu yasa ya wuce part dij taj. Anatse bude kofar da mamaki ya ganta zaune gefen taj wanda murna ta gama lullubeshi saboda ya ganta a kusa dashu, hakoranshi sun kasa rufuwa tsabar murna, karasowa jamid yayi har inda suke kafin ya kalleta, murmushi tayi mashi tace “kun dawo ashe?” “Yea mun dawo, fito ina son muyi magana” Daman tasan hakan zata kasance don haka ta miqe ta rada ma big baby abu a kunne nan take ya qalqale da dariya yace “first love ina jiranki please ki dawo” “Okay big baby” Shi ya fara fitowa tana biye dashi a baya saida suka zo daidai bedroom din nasu ya janyo hannunta ya tura ta cikin part din ya rufo kofar. Hannunta ta nade a kirjinta tana kallonshi tana jiran abunda zai ce mata “hidaya, bana son wani boye boye, fadamin menene dalilinki na auren?” “Saboda shi ne what is best for big baby?” “In what aspect?” Ya sake doka mata tambaya “Bakaji abunda doctor ya fada ba ko sai na maimaita maka?” “Kina tunanin bansan abubuwan da kikeyi its for your own benefit bane? What do you want this time around?” Wata iriyar dariya tayi kafin tace “jamid listen to me, i don’t care what you think rn, all i know is, I’m doing what is best for him, so please stay out of this” “Hidaya kiji tsoron allah” “In banji tsoronsa ba kai zanji tsoro?” Ta gaya mashi magana kafin ta wuce bedroom, certificate din auren data gani kan coffee table ne ya tabbatar mata anyi auren, ba karamin dadin hakan taji ba dukda bata nuna masu a fili ba, saidai wannan ne kadai last option. Bangaren sabeeha, ta kasa gasgata abunda kunenta ya jiyo mata a sitting room, tunda ta wuce bangaren su na maaikata ta zauna samun kanta tayi da zuba da hawaye mara dalili, gaba daya ta shiga confusion, na farko ta kasa gane menene kudirin wannan mutumin daya turota leqen asiri, sannan abunda yafi daga mata hankali sosai har taie tambayar kanta shine, wanene wannan mutumin, meysa yake controlling dinta, sannan ya akayi yasan da maganar aure? Tun kafin ayi maganar har ya umarceta akan ta amince, karta yi gardama, fatanta daya da takeyi shine allah yasa hakan ba anyi shi bake don ayi amfani da ita don a cutar da friend, don sai yanxu take ganin komai is revolve around him, tasan tana kula dashi amma meysa za a aura mata shi? Mey zata ce ma mahaifiyarta? Why the need of the aure? Waima wani irin aure? Basu san ta ba bata sansu ba? Anya babu cutarwa a cikin wannan abun?””innalillahi wa inna ialaihi rahiun” ta soma furtawa, take hankalinta ya sake tashi sosai, gashi shes confuse babu wanda zai bata amsa kawai saita fashe da kuka, yaj dakin su kuwa mey zasuyi banda kallonta babu wanda yayi attempting yaje wajenta don yaji meke damunta. Ranar dai ko part din taj din bata sake komawa ba saboda wani matsanancin ciwon kai daya saka ta a gaba. Bangaren su fadwa, afiya babu irin zage zagej da batayi ba har fadwa ta gaji da ita “Ke wai mene ruwanki? Why would you care?” Fadwa ta tambayeta, “Dole na damu mana, wallahi tallahi na tsani ukty, bana kaunar ganinta akan wannan mahaukaci, yanxu ta manta ta sanadiyarshi yanda komai ya sauya mana? Farin ciki mu? Jin dadin mu da komai? Yanxu harta manga yanda muka taso cikin kunci? Childhood dinmu babu walwala babu komai dukdan saboda shi?, wallahi idan har ku bakwa kishin ummuh to wallahi ni inayi, ” Kuka ta fashe dashi “ why would she care? Maysa zata so shi fiye damu? Meysa zata damu dashi fiye damu? Why?“ “Shiyasa nace wani sa’in kanki wallahi kamar na kifi, you’re so annoying, yanxu kukan na menene kikeyi? Ta rigada tayi deciding so sai me?” “Malama karki fada min maganar banza, ba tun yanxu ba ke ma nasan kina bin bayanta mteww, duk abunda takeyi akanshi baki taba complain ba kamarma ke baki damu ba kwata kwata, i need fresh air i cant with all of your nonsense” tana kaiwa nan ta fuce daga dakin **** Zaune suke cikin wani parlor babba, daya na zaune wajen masaukin baki, daga gefe kuma wani saurayi ne a tsaye, suna nan zaune saiga wani mutumi ya fito, babba ne mutumin don ga furfura ne ta mamaye fuskanshi gaba daya, yana da qiba sosai, sanye yake da farar jallabiya sai rawani da yayi a kanshi, wata baqar jaka ce a hannunshi, yana karasowa parlorn wanda ke tsaye yayi saurin matsowa ya karbi jakar. Na zaunen ne yayi saurin miqewa yana girmama shi, kallonsa babban mutumin yayi kafin ya zauna, dariya ya soma yi “great job doctor!” “Thank you sir” Kallonshi mutumin ya sakeyi kafin yace, “kana da kaso mai tsoka saboda wannan labari daka bamu, akwai ticket dinka to bangkok, your new job awaits you from there” Da sauri ya miqe ya karbi jakar “thank you sir thank you sir” “You can go now” Fucewa doctor yayi yana murna, don wannan ba karamin kaso ya samu ba, yayi mamaki sosai kuma akan just dan information din daya basu,wannan abu yayi mashi dadi sosai. Yana fita mutumin ya kalli yaronshi yace “prepare babban kamfanin gidan yada labari, gobe inason a tashi da latest labari kai rikitarwa kan dan taheel kuma heir of the company is mentally unstable, zanga ta yanda za ayi wannan kamfanin ya cigaba da bunkasa, over this years sai yanxu zamu samu damar kawar dasu daga industry dinnan hahahahaha” “But sir ya zamuyi da wannan likitan?” “Wipe him off,kasan duk wanda yamin aiki yana gamawa bana barin shi da rai saboda threat so just finish him” “Okay sir” Yaron ya amsa shi kafin ya futa daga parlor, wata iriyar dariya babban mutumin yayi kafin yace “its high time” hahah Abdullah ibn basit kenan, babban competitor kuma tantirin dan kasuwa, yana cikin Manya manyan masu kudin tahlia district sannan yana kasuwanci daban daban, duk wani harkar business da taheel sukeyi shima yanayi, yana da baban campany saidai baikai taheelz ba don shi bai dade da shiga kasuwancin ba, ba kamar taheels ba da su kasuwancin su suka gaje sa daga wajen iyayensu har yayi accending to yayansu. Abdullah ibn basit shine babban dan adawar taheel, tun kafin marigayi taheel ya rasu har zuwa bayan mutuwarsa, bayan mutuwarsa ya dauka kamfanin zai durkushe sai kuka yazo yafi da ma habaka, babu irin bibiya da harin da abdullah baya yi ma taheel company, amma abun yaci tura shekara da shekaru ya kasa samun abu guda daya dazai kama wanda zai sashi ya danqwafar da kamfanin a bayan fage kenan, a gaban duniya kuwa an shaida abdullah as aminin taheel kuka na hannun damanshi don shine wanda ya maida abdullah mutun a yanxu, ya dauke shi ya bashi aiki a companyn shi lokacin da bashi da kowa har ya maidashi mutun ya ajiye shi a kusa dashi. ABUJA… Kallon maqudan kudin dake gabansu jamila tayi kafin ta kalli mijinta, “jamila, anya wannan abun kuwa babu wata matsala? Wannan uban kudade ki duba fa ki gani?” “Mai gida mai kake nufi kenan? Waye zai sani? Kaga ni wallahi babu abund aya shafeni, kudi kuma wallahi kashesu zamuyi muma mu shigo gari, wannan miliyan biyun ka ajiyesu kason mu ne sauran miliyan daya dake account dinka kuma zamu dinga bawa hadiza da kadan kadan karta fuskanci wani abun” “Amma hadiza bamusan fah wani hali yarinyar nan ke ciki ba, an kira mu ne kawai an bamu kudi kuma ance saboda ita, Basu fada mana mene kudinrinsu ba fah? Da dalilin turo kudin? nidai tsoro nake ji wallahi” “Kai matsalar ka kenan in kasan haka ne meysa kayi karyar kaine mariqin ta kuma maisa kayi karyar iyayenta duk sun mutu ? Ay naga son kudin ne kaima yasa kayi karyar, saida muka karba kuma zakace wani tsoro kake ji?, amma dai tsaya yanxu da gaske daga chan kasar saudiyyan aka aiko? To saboda me? Kai koma dai saboda menen oho chan ta matse masu, koma mey ya sameta achan ko sayar da ita akayi wannan ba damuwata bace ba, ita kanta uwarta ba damuwa zatayi da hakan ba dukda bazan fada mata ba” “Toh shikenan” mijin jamila ya amsa ta. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 29-30 Saudi Arabia….. Monday morning!!! Washe gari ta kama monday, wannan rana ta kasance rana wadda mutane da dama suke jiran zuwanta, hidaya tun wajen karfe bakwai ta bar gida don ko breakfast batayi ba. Jamid ne ya kai barad school kafin ya dawo, lokacin daya dawo wajen karfe takwas na safe, abubuwan da suke faruwa tsakanin jiya da yau sun tsaya mashi arai ga fargaba da yake ji, anan compound din soma jin hayaniyar ma aikata sun hade waje daga, da mamaki yake kallonsu don sunbar ayyukan da sukeyi. Kauda kanshi yayi daga kansu kawai ya wuce cikin gidan, bai tsaya ko ina ba sai hanyar dazai sadashi da stairs zuwa sama daidai nan fadwa ta fito daga bangaren ta, batama lura da jamid ba ta nufi wajen tv ta kunna news wayanta na hannunta, daman kiranta mijinta yayi ya shiada mata abunda ke faruwa. Rasa ma wace tasha zata shiga tayi . Headline din da jamid yaji ne yasa ya tsaya chak bai sake daga kafarshi da niyar tafiya ya yayi saurin maida dubanshi ga tv din, ga headline nan a kasa anyi rubutu da manyan harufa, “ reported news; heir of taheel groups has been grounded and hidden to the world because of amnesia” Saurin chanzawa fadwa ta sakeyi ta shiga wani news channel din, nan ma cece kuce akeyi akan wannan breaking news din, akan company taheel, da gudu jamid ya sauko kasan baima san sanda ya warce remote din hannunta ba ya soma kara volume don jin abunda ake cewa, Nan take kuma aka sauya headline din zuwa sabo, inda aka hasko hidaya a zaune zatayi press conference, dabas jamid ya zauna akan kukera yana kallon tv babu ko kiftawa, Intoduction ta farayi kafin reporter din suka fara mata tambayoyi, “ madam shin da gaske ne heir din kamfanin taheel group kuma qani a wajenki yana fama da ciwon hauka? Madam meysa kuka boye wannan? Munason musan dalilin da yasa duniya bata san da haka ba?” Saida ta gama jin tambayoyin su wasu ma sukarta sukeyi da tambayar, suna gamawa ta soma magana. “Na farko wannan official announcement zanyi Tabbas heir din kamfanin taheel group yana fama da critical traumatic amnesia wanda yasa bayyanashi ya zame mana babban threat a gareshi da mental illness dinshi” “Does that mean grounding dinshi kukayi for your benefit ko saboda kada tattalin arzikin kamfanin ku sauka?” “Noo, i can’t publicly explain why but saboda health dinshi ne” Wani reporter ne daya rufe fuskanshi da mask yace “does that mean situation dinshi is critical kenan meaning hauka yakeyi kenan?” Shuru tayi suka zuba mata idanu sai faman haskata ake da cameras, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi akanta yana jiran jin abunda zata ce, to his surprise sai yaji tace “ yes, situation dinshi is critical, i dont want to use the word hauka but i can say something similar cause he’s like good for nothing” Wannan statement datayi ba karamin hargitsa komai tayi ba mutane sunyi mamaki sosai don kamar tayi destroying komai, Wani ne cikin reporters yace “yanxu a wani mataki taheel group yake ciki? Zaku sayar da kamfanin ne? Ko zaku bari wannan ya zama downfall din legacy din? As we all know babu yanda za ayi companying yayi running without the heir” Murmushi hidaya tayi kafin ta kalli wanda yayi magana tace “bazamu bari gumin iyayenmu da a sacrifice din da sukayi mana ya tafi a banza ba,“ “Babu yanda za ayi mahaukaci yayi rulling company madam…” Hannu ta daga masu, kafin ta sauke ta dago wata yar paper, tana daga zaune ta mike tsaye, “i Hidaya taheel, the present acting ceo of the taheel group will take over responsibility of the company as the legal ceo” Nan take aka soma hotuna masu zooming suka soma zooming documents din, kowa da abunda yake son fada. Wannan reporter daya tambayeta kan cewa taj mahaukaci ne ya sake jefo mata tambaya, “How is that possible? A yanda muka san law din business industry dinku babu yanda za ayi mace tayi ruling musamman idan akwai heir?” Kai tsaye ta amsa shi, “you mean heir din da is not stable? Well there is, papers don’t lie, i am legally the chief executive director of the taheels, my brothers sickness bazaisa mubar abunda iyayen mu sukayi building ya lalace ba,we’re sorry for hiding this from the world, we did it for the sake of our only brother for his protection, thank you” Tana kaiwa nan ta fuce daga conference room din, babban lawyer kamfanin taheel na biye da ita a baya, reporters kamar mayu haka suka soma kiranta madam madam madam, harta fuce. Bayan ta shiga motarta tare da lawyern ta sauke wani sigh of relieve,” weldon madam your decision of hitting 2 birds with a stone is absolutely incredible” “Thanks barr” ta amsa shi. Wasu papers ya miqa mata tayi sighning duka kafin yace “madam you’re the current president of taheel groups, congratulations” “Thank you, ka ajiye copy din zan karba original document din” “Okay ma” Gaba daya paper documents din ya tattara ya bata kafin su wuce office. Jamid daya gama kallon tashin hankali, miqewa yayi cikin sauri ya wuce gidan khaal, koda yaje gidan shi shima already yaga abunda hidaya tayi. “Khaal na fada maka, na fada maka wallahi wallahi hidaya bazata taba chanzawa,wannan rashin lpy taj is an opportunity to her, and tayi using dinshi to her benefit,“ Shuru khaal yayi yana wani nazari kafin ya kalli jamid yace “jamid, ina ganin we wrongly accused her, intentions dinta are pure kuma protecting taheel groups tayi” Da mamaki jamid ke kallo khaal, babu abunda yake nema sai karin bayani, News paper dake gefenshi ya dauka ya bama jamid din, take ya soma karantawa, jarida ce da aka buga ta tun daren jiya za a fidda ta ayau, abunda aka rubuta dai babu dadin ji duk kuma akan taj, wasu irin concrete false evidence aka tattara akan cewa yana drugs wanda shine sanadiyar samun amnesia da yake dashi yanxu wadda ta zama critical sosai, wanda kowa yasan me hakan ke nufi. Da mamaki jamid ya dago, khal ne yayi saurin cewa “wannan jaridar itace first headline data fito kafin hidaya Tayi conference, badan ta hada conference dinnan ba da tuni companyn taheel a rufe shi gaba daya, wannan yasa aka dakatar da futarda wannan news din,” Girgiza kai jamid yayi yace “how? Waye zai yi wannan? Ni ina zargin duk aikinta ne” “Mutun daya nake zargi Abdullah ibn basit” Gingina kai jamid yayi kawai, sai ya kuma fara jin rashin dadi game da yanda ya dunga zarginta. “Ni wannan abun ma yamin dadi, saboda koba komai boyeshi da akeyi zaizo karshe. Khal ya fada yana mai kallon jamid Ya dade sosai wajen khaal suna tattaunawa kafin ya koma gida. Taheels residents….. Duk abunda ya faru yau kwata kwata afiya bata sani ba, hasali ma fada suke ita da fadwa don ta daina mata magana, hidaya kuwa haushinta takeji sosai ba kadan ba. Karfe shida hidaya karaso gida, ba karamin yaqi tayi ba a office donma tana da gagarumar shaida wadda babu wanda ya isa yayi jayyaya da takardar, a take kuwa suka soma ganin asalin rashin mutuncinta don yanxu kamfanin ya dawo hannunta gaba daya, duk wanda tayi niyar kora har cikin shareholders zata iya yi, gaba daya kowa ya shiga taitayinsa. Lokacin data shigo babu kowa ya kasa, daidai zata wuce sama afiya ta fito daga dining room, wani irin kallo afiya tayi mata mai wuyar fasaara kafin ta doka tsaki, fadwa dake shirin fitowa daga dining room din don dinner sukayi, ganin abunda afiya tayi yasa ta zaro idanu, “ke baki da hankali” fadwa ta fada “Eh bani dashi” afiya ta amsa ta kai tsaye, “ ni banida munafurci kamar ke,” ta karshe tana mai dauke kallonta ga fadwa ta maida kan hidaya “ukty wallahi i hate you, i hate you so much” kuka ne ya sake kubce mata, “yanxu har kin manta da halin da ummuh ta shiga? Kin manta pain din datayi suffering dashi over the years? Kin manta abunda yayi sanadiyar mutuwarta? Why ukty, why? Maysa bakya kishin ummuh? Tana kabari amma na tabbatar tana allah ya wadai da protecting wanda yayi sanadiyar mutuwarta da kikeyi,” Idanun hidaya sunyi jaa sosai, fuskanta ma haka ta koma jaa lokaci guda tsabar bacin rai, Jan afiya fadwa ta soma yi tana kokarin hanata magana ta daka mata tsawa “dallah kyaleni, ni ban iya munafurci ba saina fada mata gaskia, wallahi wallahi wannan hatred din bazai taba barin zuciyata ba” Kauda kai hidaya tayi kafin ta runtse idanunta ta bude su tarr, hannun afiya ta damko ta soma janta zuwa part dinta, fadwa na biye dasu hankali a tashe, suna shiga hidaya ta saki hannunta ta wanke fuskanta da mari, saida ta mareta wajen sau uku kafin ta kalleta da jajayen idanunta ta nunata da yatsa, “how dare you? How dare you say that eh answer me, ke a tunaninki da wannan karamar kwakwalwar taki ina yin wannan abubuwan ne saboda me? Saboda ina son TAJ? The child that destroyed our family? The child that destroy our happy home with our parents? The child that brings so much sadness to ourselves? Ehhh!! Answer me” ta karashe tana girgizata da hannunta, “Let me remind you, ranar da taj ya bayyana a gidan nan akwai wanda ya kaini shiga tashin hankali? Daga ke har fadwa bakuda hankali bakusan meke faruwa ba a lokacin, I’m the only person who knows pain din da ummuh ta shiga, baku san komai ba don bakuga komai ba, her lonely nights, her painful days, the pain in her eyes, the screams of her pains zaki iya tunawa? Eh answer me nace zaki iya tunawa?,” Ta daka mata tsawa mai rikitarwa wanda yasa ta furgita, hawayen fuskanta na kwaranyowa babu qaqaautawa, “tunawa da wannan kadai yakan sakani samun sleepless night, kina tunanin ina rufe ido ba tare da wannan tsohon baqin cikin daya dade kwance a zuciyata ba? How dare you say that na zabi protecting wanda yayi sanadiyar baqincikin daya kwanta a zuciyarta har yayi sanadiyar mutuwar ta? How dare you” Kallonta suka somayi gaba dayansu kuka ya gama wanke masu fuska, hidaya dai idanu sunyi jaa, babu hawayen ko kadan, “I’m sorry ukty I’m sorry wallahi na dauka….” “Shii, shut up, ay ban gama ba” ta karashe tana kallon cikin idnaun afiya da jikinta ke kyarma. “Kina tunanin daukanshi da nayi na reneshi? Na rufe kaff rayuwarshi daga ni sai ni gaba da baya, Na hanashi kusantar kowa, na bashi soyayyar da babu uwar datayi ma danta irinshi don ko barad dana haifa banyi mashi irin soyayyar nan ba, sannan na tura shi karatu wata kasa chan sannan nayi pampering dinshi na bashi duk abunda yake so anan duniya duk kina tunanin nayi hakan ne saboda ina sonshi? No!!!!!!!!!!!!! I only did that don na juyashi son raina, to have him on my palm,” Nunfasa tayi kafin ta cigaba, har hannunta na karkarwa “na nuna mashi so ne fiye daku da kuke jini na saboda ta wannan hanyar ne kawai zanyi yanda nake so dashi and thats the only way i can make him miserable, inajin takaici sa baqin ciki idan na tuna wani part na jini na na running a jikinshi,” “And lastly ina son ku sani gaba dayanku, a duk duniyar nan babu wadda naso kamar ummuh, ko abuh banyi mashi irin son danayi mata ba, Wanda yayi sanadiyar mutuwar ta shine babban maqiyi na, kuma bazan taba bari yayi enjoying wannan rayuwar ba yanda ummuh tayi suffering over that year, i will make him miserable thousand times over and over, ko ganin sa bana sonyi, kuma na tabbatar wannan hatred din saidai idan mutuwa nayi, so you better open your eyes clearly kisan yanda akw tafiyar da rayuwa yanxu keep that in mind” Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin rai a bace, gaba daya memories din komai ya dawo mata, all the painful moments da hatred. Jama’a Allah ya kaimu monday zamu shiga cikin labari, by next week free page zai kare💃🏻😭 Yanxu ainahin farkon shirin zai fara😆💔 Sabeeha dai ta zama matar taj, hidaya ta samu abunda take so, company ya dawo hannunta gaba daya…. Shin me zai faru nan gaba? Hidaya ta daura damarar shiryama TAJ miserable life, wato a yanxu ma somun tabi ne kenan?… Ku biyo ni don sanin abunda zai faru a cikin labarin Matar TAJ…. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 31-32 Farkon labari. Asalin ahalin Taheel Abdullah Tajudeen. Taheel Tajudeen babban dan kasuwa ne, business tycoon wanda ya sha’hara kuma ya zama jajirtattce a cikin fashion business industry, yayi fuce sosai a kasar saudi inda duk duniya babu wanda bai shaida nasarorin daya samu ba, yana da yaya uku tal a duniya wanda allah ya mallaka mashi, danshi na farko shine Taheel Abdullah tajudeen wanda ya gaji sunan mahaifinshi da sunan kakan sa sai mabiyinshi Abdul gaffar Tajudeen (khaal) sai Halima tajudeen. Wannan ahali sun taso cikin soyayyar mahaifinsu har allah ya dauke ran mahaifinsu don mahaifiyarsu ta dade da rasuwa, a lokacin kowannen su ya taso da raayin abunda yakeso, Abdullah shine wanda ya ya taso da kudirin riqe legacy din familyn, inda yayi karatu bangaren business kuma cikin ikon allah yayi expanding family business dinsu har ya wuce yanda mahaifinsu yabar masu business din. Tsakanin yan uwan nan akwai wani special connection tsakanin su musamman abdullah da khaal, saboda yanda mahaifisu ya koyar dasu son juna da kuma yarda da junan su. Basu taba samun wani misunderstanding ba tsakanin su sabida yanda basa yima junan su baqin ciki ko hassada. Khaal bai taba nuna son shiga harkar family business dinsu ba dan shi aikin government ya zaba, don haka koda akazo zaban wanda zai gaji taheel company as heir bai nuna disagreement ba ya cire hannunshi gaba daya daga business din ya barma dan uwanshi wato abdullah. Shekaru sun jaa sosai inda abdullah yayi aure kuma auren soyayya,inda ya auri fattu ya ga babban dan kasuwa a bangaren southern arabia kuma abokin kasuwanci ga late taheel tajudeen, aure ne dai akayi shi badan soyayya ba saidai business inda mahaifinta ya roki alfarmar su hada hannu don taimakekeniyar juna, duba ga hakan zai kara daukaka taheel company yasa abdullah ya amince kuma ya aureta amma badai don soyayya ba saidai kuma kasancewar shi mutun ne na kwarai kuma mai cikon alqawari da addini yasa bai tauye mata komai ba ya nuna mata so da qauna, ta bangaren fattu kuwa so take mashi sosai kamar ranta, da farko bata amince dashi ba sai daga baya,rayuwa mai dauke da kwanciyar hankali da farin ciki da kula fattu ta shimfida masu ita da abdallah, harkar company kuwa sai bunqasa take sosai. Bayan shekara daya da aurensu allah ya albarkacesu da ya mace wadda suke kira da hidaya, hidaya ta taso da soyyayar iyayenta, musamman fattu (ummuh) fattu na masifar son hidaya kamar ranta, haka zalika hidaya itama ta taso da kaunar mahaifiyar ta sosai fiye da soyayyar da take ma mahaifinta, halayenta da dabi’un ta sak na mahaifiyarta, bata daukan raini sannan akwaita da girman kai sosai. Tun bayan haihuwar hidaya allah bai sake basu wata haihuwar ba kuma basu damu ba har takai shekaru goma ciff a duniya, acikin wannan shekaru abubuwa da dama sun sauya inda ummu ta soma shiga harkar business din taheel company as assistant director, she was so into the business don sai alokacin ta fahimci dalilin da yasa iyayenta are so obsessed with harkar business. Kudi dai da fame ba a magana don ya shigeta sosai wanda hakan yasa ta daura damarar rike mijinta sosai don tun farko tasan ba auren soyayya sukayi ba, but ita kam sonshi take kamar hauka, samun hidaya cikin rayuwarsu kuwa ba karamin ci gaba bane a wajen ummu, Lokacin da ummu ta gane policy din company din kan cewa wanda zai gaji wannan comapny din dole sai da namiji ba karamin tashin hankali ta shiga ba don tana da dogon buri, anan ne hankalinta ya soma tashi game da rashin haihuwar su saboda tasan idan har bata haifa da namiji ba to fah khaal ne zai karba wannan company din idan har mijinta baya raye wanda bata fatan hakan kwata kwata wannan ne ma yasa qiyayyar khaal ta fara wanzuwa a ranta dukda tasan he’s not into the business kuma bashi da raayin haka, kanwar su halima kuwa ita aurenta ma tayi a kasar waje, tun bayan tafiyarta bata sake dawowa ba, wannan dalilin yasa suka fara neman magani ita da abdallah don sanin dalilin rashin haihuwar. Da farko sun samu matsaloli sosai ta bangaren lafiyar fertility wanda daga baya kuma cikin ikon allah ta samu wani cikin. Fadin irin murnar da ummuh tayi da samun cikin nan bata lokaci ne don ta kwallafa rai sosai akan cikin kuma burinta akan cikin nan ya wuce misali don ta tabbatar ma da kanta da namiji zata haifa wannan karan. Bangaren Taheel abdullah yayi farin ciki shima da samun karuwar tasu saidai shi bai wani damu da da namiji ko mace ba duk wanda allah ya bashi shi mai godiya ne da Hakan, kulawa ta musamman dai yana yima fattu sosai don ayanxu kam zaman lafiya sukeyi sosai. Bayan wata tara fattu ta haifi diyarta mace, ba karamin tashin hankali fattu ta shiga ba don burinta na haifar namiji bai cika ba, wannan yasa taqi amincewa da sanin gender din babyn dake cikin mararta. Bayan kwana bakwai baby taci sunanta fadwa, Daga kan haihuwar fadwa ne mafarin sauyawar fattu ya fara afkuwa, kwata kwata kudirinta da burinta yana ga samun power da fame,soyayyar da hidaya ta samu wajen mahaifiyarta kwata kwata fadwa bata samu ba, haka fadwa ta taso ta fara girma har fattu ta sake samun wani cikin bayan shekara uku shika da kyar aka samu cikin don sun kashe kudi sosai, wannan karan kam hankalin fattu a matuqar tashe yake don bata san yanda zatayi ba idan ta sake samun ya mace, hankalin ta kwata kwata bai kwanta da cikin ba haka dai take rainonshi saidai burin nan har zuwa lokacin yana nan. After nine month allah ya sake bata haihuwar mace,(afiya) this time around frustration yasa tayi giving up kawai, abunda yasa hankalin ta ya kwanta ma shine ganin yanda khaal baya nuna interest akan company din hakan yasa ta fan tsagaita. tsakanin fadwa da afiya kuwa bazan ce ga wadda ta jata jikinta sosai ba, kwata kwata bata jansu a jikinta saboda burin dataci na haihuwar maza sai kuma allah ya bata mata, matsayin hidaya dai yana nan aranta, tana masifar sonta kamar ranta. A sannu a hankali ta soma jan su fadwa da afiya suma, lokacin data karancesu gaba daya fadwa is so smart and snicky while afiya kuma is so slow, hidaya dai har zuwa lokacin itace bold and strong among them don halinta irin na mamanta kamar photocopy. Mahaifinsu kuwa ba karamin so yake masu ba su duka, baya banbancesu kwata kwata haka suka taso cikin soyayya da kulawa, a definition of a big happy family indeed, kwata kwata basu taso da wani hatred ko wani abu a ransu ba, daga su sai iyayensu, saima dai khaal da ummu ke janye su daga jikinsa, don shi kam ba karamin threat bane a wajenta, ganin wannan farin cikin da kwanciyar hankalin yasa fattu ta sassauta burikan da take dashi ta maida hankali kan ahalinta wato mijinta da yayanta. A shekarar da hidaya ta cika shekaru sha takwas cip a duniya, a lokacin kuma fadwa na da shekaru takwas while afiya na da shekara bakwai. A daidai wannan gab’a komai ya sauya masu, rana mafi muni ta bayyana a garesu, ranar data tarwatsa duk wani farin ciki da kwanciyar hankali na wannan ahali, wannan rana itace ranar da abdullah ya bayyanar da tajudeen taheel tajudeen ga yan uwansa. Wannan rana ta kasance rana mafi muni da baqin ciki a zuciyar fattu,lokacin da abdullah ya bayyanar da danshi daya tilo wato tajideen. Safiyar ranar lahadi.. Zaune suke a sitting room na kasa, hidaya dasu fadwa na wasansu while fattu na aikace aikacen ta daya shafi office din datake running, sallamar da suka ji ne yasa duk suka dago gaba dayansu, Khaal ne ya shigo hannunshi rike dana kyakyawan yaron da bazai wuce shekaru shida ba gaba daya a duniya, sai abdallah dake biye dashi a baya, saurin miqewa fattu tayi tana mai kallonsu, daya bayan daya take kallonsu har ta maida idanunta kan yaron, tsantsar kamannin su da abdallah harta wuce musali saidai abdullah daya fi yaron haske sosai, karasowa sukayi cikin sitting room din, inda khaal ya zauna bayan sun gaisa da fattu, daman gaisuwar sama sama ce, kallon yaron khaal yayi kafin yace “jekayi wasa da yan uwan ka” Wani irin damm gaban fattu ya bayar, kwata kwata ta kasa dauke idanunta akanshi, samun kanta tayi da tambayarshi “habibi waye wannan?” Kasa hada idanu yayi da ita saima dauke ma ganinta da yayi yace “muje bedroom inason zamu tattauna akan wani muhimmin abu” Bata musa mashi ba tabi bayanshi suka haura saman, suna karasawa saman jikin ta har bari yake, kofar bedroom dinma bata kaiga rufewa ba ta nufi inda yake. Zuba mashi idanunta da sukayi jaa tayi kamar tasan daman akwai wani abun a kasa sai dai kuma jiran confirmation da takeyi daga wajenshi, Hannunta ya janyo ya riqe gam cikin nashi kafin ya soma magana “habibity! I want to tell you something, please karki tayar da hankalinki okay? Kaddara ne kuma tana kan kowa” Girgiza mashi kai ta sake hannunta dake cikin nashi yana karkarwa, “I’m listening, ina fatan dai ba wani abu bane serious, ko?” Tunda ta soma magana ya kasa hada idanu da ita, tabbas baiyi mata adalci ba bai kyauta mata amma ta yaya zai fara mata bayanin nan? Ya za ayi ta gane? Ya za ayi ta saurare shi? Matan saudi babu abunda suka tsana kuma suka kyamata kamar kishiya, da kayi masu kishiya gwara sun bar maka gidan ka auro wadda kake so, wasu daga cikin su suna yarda da second wife saidai abunda yafi tsananta kuma yafi cin mutunci a wajensu shine mijin da yaje yayi aure a boye ba tare da sanin matansu ba, shi nashi is even worst don yayi auren ne kuma cikin sirri harda ‘da shekaru wajen bakwai da suka wuce, kuma ba tare da saninta ba. Hannunta dake cikin nashi ta cizge, idanunta sunyi jaa sosai sai hawaye dake shirin kwaranyo mata, “da gaske ne kenan,” Saurin dagowa yayi jin furucinta, da mamaki yake kallon bakinta dake furta, “wannan yaron danka ne?” “Yes” ya amsa ta, Wani irin jiri ne ya soma divanta, tuni tayi baya zata fadi ya taro ta, cikin sauri ta buge hannunshi tayi baya idanunta sunyi jaa sosai, “I’m sorry fattu,” “Shekara nawa kenan? Tun yaushe?” Ta jefo mashi tambayan nan “Fattu duk wannan bashida amfani yanxu, listen to me…” Saurin katse mashi hanzari tayi “abdallah!!!! Me kunne na ke shiri jiyo min? Wannan wani irin cin mutunci ne kayi min abdullah? Why why whyyyyy? Aure kayi a boye ba tare sa sani na ba for how many years? For 7years? Innalillahi wa inna ilahi rajiun? For good seven year? Kaci amata abdallah, ka cuceni?” “Fattu please calm down” Idnaunta da sukayi jaa ga hawaye kwance akai ta zuba mashi “don’t tell me calm down, you have no right to do such” “Fattu please wannan dalilin yasa na kasa fada maki kamar yanda nace kaddara bata wuce kan kowa, i know you’ll be hurt shiyasa ban fada maki ba” “Abdallah na gwammace na dauki wannan pain din shekaru da suka wuce akan yanxu shin Kasan abunda akayi kuwa? Kaci amanata kayi aure a baya na wannan shine d most humiliating abu da zan fuskanta a duniya, shin kasan ma’anar auren da kayi bada sanin na ba? Shin kasan tabon da kayi min a anan duniya? Ka mance da culture dinmu ne? Duk matar da hakan ta faru da ita tana da tambarin….” “Fattu!!!!!! Abunda nayi addini bai haramta ba, aure nayi na sunnah, idan addini bai haramta ba then why abunda community zasu ce zai dameki?” “Aure ba haram bane ba shiyasa nace daka fada min tun wuri, wannan abu da kayi is the most disgusting and evil doing, how could you? Shin kasan me hakan ke nufi kuwa? Kayi aure this all time bada sani na ba? In my entire life da tarihin iyaye na bamu taba fuskantar wannan humiliation din ba yanxu sai akaina? Kayi min babban tabo da har abada bazai goge ba?Duniya zata kalleni da wannan and the worst part shine harda da? Harda da????? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun?”””” Nan take ta sake burkicewa ta fashe da wani matsanancin kuka sosai, ihu zagi insult words babu wanda batayi mashi ba, yaci amanarta yaci amanarta ya cuce ta wannan auren da yayi ba karamin bakin fenti yayi mata ba harda da, da ace babu yaro da sauqi ita bata ma damu da sanin ya akayi yayi auren ba, amma yanxu idan duniya ta san da wannan shikenan, she can’t face the world don anan kasar sun maida abun kamar wani babban zinibi, abunda yafi tsaya mata shine gashi ita bata taba haifar da namiji ba, abu ya gama tarar mata, ga auren boyen daya boye mata, ga yaro kuma da namiji, at that moment ji tayi dama mutuwa kawai tayi akan ta fuskanshi wannan baqin tabo a gaban duniya, ita kanta to her self batajin she can accept this, Babu yanda abdallah baiyi ba don rarrashinta amma kiff ta rufe ido, jikinta har rawa yake yi don abun ya shigeta sosai, “fattu please” “No please get out get out bana son sake ganin fuskanka abdallah yalla yalla get out,” ta karashe da larabci Hidaya data hauro saman babu abunda bata ji ba, saida taji motsin futowar abuh yasa ta labe a corridor don kar ya ganta, yana futa kuwa fattu tayi banging kofar, girgiza kanshi kawai yayi yana tausaya mata, dole zata shiga irin wannan hali daman yayi hasashen haka, kasa ya sauka zuwa wajen khaal, Yana wucewa hidaya ta karasa bakin kofar, tun daga bakin kofar ta soma jin kukan ummuh, kuka sosai takeyi tana screaming da larabci, words of insult babu wanda bata rafko ma abdallah. Bangaren su abdallah, yana karasowa kasan ya tadda yaron zaune shi kadai wajen kayan wasan su fadwa, suna wasa hardashi, jiki a mace ya karaso inda khaal yake zaune kafin ya zauna,kallon yanayin shi khaal yayi hakan ya tabbatr mashi da abunda yayi hasashe, haka nan ya fara tausasa shi yana bashi words of encouragement tunda babu yanda za ayi da wannan alamarin. Bangaren fattu haka ta wuni a dakin nan tana kuka kukan baqin ciki, bata taba tunanin zata taba fuskantar rana irin ta yau ba, bata taba kawo hakan ba kwata kwata abun yazo Mata unexpectedly, bata jin zata taba yafema abdallah akan wannan abun da yayi mata. Hidaya dake tsaye bakin kofa har barci saida tayi ta farka, kuka dai itama babu wanda batayi irinshi ba tana mai sauraron yanda mahaifiyarta ke kuka. She was so shattered, dukda batasan karfin laifin mahaifinta ba but damuwanta shine kukan da mahaifiyarta keyi. Haka aka shafe wata guda fattu na cikin kunci, abu dai gaba yake yi kullum, kullum tana kulle a daki ta rame ta jeme sosai, idanunta sunyi ciki ciki kamar ba fattu ba, duk wanda ya rabe ta korarshi take, abdallah kam bata yarda ma ta ganshi, ta tsaneshi yanda ta tsani mutuwarta, hidaya ce kadai ke samun shiga wajenta, duk sanda ta shiga dakin a zaune zata taddata ta kafa ma window idanu. Taj kuwa yana samun kulawa wajen sabuwar maid da abdallah yayi employee wadda zata kula dashi, bangaren su fadwa da afiya basu san meke faruwa ba don gaba dayan su ba wani wayo ne dasu ba, saidai sun fuskanci mahaifiyarsu tana cikin kunci don rabon da su ganta har sun manta. Yau dai abdalla kasa hakura yayi wajen karfe goma na dare ya wuce dakin fattu, allah yaso kofar a bude take don hidaya bata dade da futa ba don hado ma mamanta tea ko zata sha don kwata kwata bata cin abunci ta zama kamar wata kurma bata cin komai bata cewa kala sai kuka. Koda ya shigo dakin a bakin gado ya tadda ta, ta rame sosai daga ita sai rigar barci da alamu kayan ma sun jima a jikinta kuma dasu take kwana take wuni, gashin kanta duk ya yamutse ya barbarzu don kwata kwata bata bashi attention don bashi ne a gabanta ba. Batasan da zuwanshi ba sai ganinshi datayi a gabanta ya duqa yana mai kamo hannunta, cikin sauri ta zame hannunta ta sauko daga kan gado kamar taga wani abun kazanta, saurin kauda kanta tayi don ko ganin shi bata san yi. “Meysa ka shugo min daki? I taught nace maka ko ganinka bana son yi? Bana son mu shaqi koda iska daya ne dakai munafiki, azzalumi, maci amana” Yaji zafin maganarta amma hakan bai sashi nuna mata ba yace “fattu kiyi hakuri, ya kamata ace komai ya wuce, please, yaranki are loosing you, I’m losing you too, you’re not your self, dan allah kiyi hakuri mu hadu mu kula da yaranmu please” Wani irin mugun kallo tayi mashi kafin ta raramo mashi wasu manyan curse word “munafiki, annamimi, wasu yayan zamu runguma? Don’t ever call your self a father, you are nothing but a hypocrite, you’re worst than a devil” Marin daya sauka ne akan fuskanta yasa ta dagowa tana kallonshi, jikinta har tsuma yake, shima ranshi a mugun bace yake sosai don bai taba tunanin zata kirashi da wannan mugayen kalaman ba dole yayi putting some sense akanta. Ba zato ba tsammani yaji saukan mari shima a fuskanshi, the next thing kuwa sai shaqo mashi colar datayi “har kai ka isa ka mareni? Har ka isa ka sanya tafin hannunka akan tsaftattciyar fuskata? I hate you, na tsani saninka da nayi arayuwata, you’re nothing to me but a peace of shit, na baka komai a duniyar nan na baka yaya har uku saboda ban baka namijin ba shine ka kasa hakura saika cuceni ka nunama duniya abunda zasuyi min dariya akai? babu abunda zaka sakamin dashi sai wulaqanci mafi muni? Ka kawo min shegen danka cikin gidana sannan kace min wai mu hadu mu kula da yaranmu? Kana tunanin after all you have done komai zai koma yanda yake ne a da? Eh?” Ta kurma mashi uban kara tana mai dukan kirjinshi kamar mahaukaciya, saida tayi mai isarta kafin ta soma jifanshi da abubuwa, “get out, get out, you made me who i am now, ka maida rayuwa na miserable, kaima you will Never have that peace of mind cause i will never fogive you for this kuma ka fuce min da wannan tabon daka kawo min gidannan ka futar min da shegen danka daga gidana don wallahi bana kaunar ganinka da shi, out!!!!” Yana futavta soma fashe fashe,duk wani abu dake cikin dakin saida ta tarwatsa shi da hannunta, jikinta yayi jaa sosai gashi harda jini, hidaya dake tsaye ta labe tana jin duk abunda ya faru, kasa rikewa tayi itama ta fashe da kukan saida abuh yabar dakin ta samu damar shiga bedroom din, tana shiga ta karaso inda ummu ke tsugunne tana kuka, lallashinta ta soma yi amma ina, tea din data kawo mata ma watsar dashi tayi a gefe sannan ta daka mata tsawa “get out!!!, bana son ganin kowa “ Dan dole haka hidaya ta fuce daga dakin tana kuka tana waiwayon mahaifiyar tata. Bayan ta koma dakinta kasa kwanciya tayi haka nan ta sake futowa don zuwa duban mahaifiyar tata lokacin wajen karfe uku na dare, koda ta shiga magaifiyarta ta hango tana kokarin committing suicide a jikin wani karfen chandelier, cikin hanzari hidaya ta taho a guje ta tallabo kafarta tana kuka tana ihu,lokacin fattu harta jigata, badan zuwan hidaya ba da tuni ta mutu, da kyar hidaya ta samu ta kunce mahaifiyar tata kafin ta rungumeta tana hawaye, “ummu please, karki tafi ki barmu, ina rokonki please ki koma yanda kike kiyi hakuri, bazan iya rayuwa babu ke ba” Saurin tureta fattu tayi kafin ta kamo kafadunta ta damke su tace “meysa zaki shugo? Wayace ki shugo?” “Ummu mutuwa zaki fah? Kashe kanki zakiyi? Ya zamuyi” Jijigata fattu ta somayi kafin tace “listen, mahaifinki yaci amanata ya cuceni, ya kawo wani dan daya haifa da wata matar, ya kulla wannan cin mutuncin da ya sanya duniya ta dunga kallona da wannan embarrassment din, look into my eyes, ko bayan raina don’t ever accept that child, don’t ever let him have all this power, make his life miserable as the result of what his parent makes me go truh, kinjini, don’t ever” Ta karashe tana kuka, saurin girgiza mata kai hidaya tayi tana mai mata alkawari. Bayan kwana biyu abubuwa sun dan sauya saidai har zuwa lokacin fattu tana cikin kunci, ba laifi tana yin wanka saidai abunci ne har zuwa yanxu bata ci kwata kwata. Kuka kuwa duk dare saitayi shi, abdallah kullum saiya lekata saidai kuma baya bari ta ganshi don yanxu hauka takeyi mashi tuburan, bangaren su afiya kuwa sun fahimci tun zuwan abuh yayi da wannan yaron mamansu ta sauya, kuma suna ganin yanda take kuka sosai in sunje wajenta sai tayi ta korarsu, haka suka taso da wannan kuncin a ransu sannadiyar wannan yaron. Bangaren tajudeen kuwa daman yaro ne miskili, babu ruwanshi da shiga harkar kowa, baya magana ma sosai saboda bashi da yarda, daga abuh sai wannan nanny din dake kula dashi, daman tun tasowarshi bai taso da sanin mahaifiyarshi ba infact bazai iya cewa ga fuskanta bama don bai taso da ita ba. Su fadwa da afiya yanxu sun daina wasa dashi kwata kwata, kullum yana zaune shi kadai a daki don ko futowa baya yi saboda tsoron haduwa dasu afiya karsu dakeshi, har aka sauya mashi school zuwa irin tasu hidaya, baya magana kwata kwata saboda bashi da sabo. Ranar wata laraba hidaya ta shiga bedroom din fattu don kai mata abunci, a yanayin yanda ta ganta ba karamin tashin hankali ta shiga ba don ta taddata kwance a kasan bathroom cikin, cikin hanzari hidaya ta karasa inda take tana mai kiran sunanta “ummuh ummuh” shiru babu response, cikin tashin hankali ta soma taba ta amma ina kwata kwata bata motsi hankali a tashe ta sauko kasa dai dai nan khaal ya shugo gidan da motar ambulance daga asibiti, wannan rana ta kasance rana mafi muni a cikin wannan ahalin, abuh ya mutu sanadiyar heart attack daya samu while ummuh kuma ta yanke jiki ita ma ta fadi zuciyarta ta buga, Babu wanda yakai hidaya shiga tashin hankali da kidima don ita ce tasan zafin mutuwar, tayi kuka sosai ta futa hayyacinta. Bayan kwana arba’in kula dasu hidaya ya dawo hannun khaal, shike kula dasu da alamuransu gaba daya harda taj. It was a tough moment of life for all of them harda khaal daya rasa dan uwansa saidai yayi alkawarin kula dasu kamar nashi don bai taba aure ba. Haka suka taso gaba dayansu, hidaya bata magana kwata kwata duk abunda ke wakana a gidan bata cewa uppan, haka zalika taj, bata kaunar ganin yaron nan kwata kwata, khaal kuwa yana kokari sosai wajen ganin ya kula dasu, da farko ya shaida yanda hidaya ta tsani taj sai kuma daga baya yaga sauyawanta lokaci guda, sai ya zamana babu wanda take da kusanci dashi daya wuce taj, ko su fadwa bata nuna masu so yanda take nuna mashi, tana kula dashi sosai haka ya taso bashida abunda yake so sama da hidaya, kukan shi hidaya, farin cikin shi hidaya komai nashi itace. Hidaya was so smart, ta gama karatunta inda ta karanci business alokacin tana da shekaru ashirin da biyar chir a duniya, a lokacin ne ta nuna tana son shiga harkar business dinsu wanda khaal bai musa mata ba ya barta don daman shi yana kula ne kawai da dukiyarsu badai don san ranshi ba yake kula da company din ba Kuma inheritance yayi decending daga mahaifinsu zuwa kansu. A lokacin su fadwa da afiya sun kammala secondary education suna kokarin shiga collage of education leaving taj behind don ba a sakashi a school da wuri ba, lokacin daya kammala duk sunyi nisa sun barshi, a wannan lokacin ne kuma hidaya stand on her feet,ta soma bujire ma khaal, itace ke da say a gidan, itace ke cewa kaza za ayi kuma dole ayi. Khaal respected her as the elder of the family don yana son ta zama itace madafar da kannenta zasu jingina, ko bayan ranshi shima wannan yasa bai taba hana ta ba idan tayi making decision akan kannenta, lokacin da taj ya cika shekaru goma sha bakwai ciff a lokacin ya gama karatunshi wannan yasa ta yanke shawarar turashi kasar waje, khaal bai musa ba ya barta ta turashi karatu a england, inda itace ta mashi komai daya dangancin school din kuma ta kaishi da kanta, she provided duk abunda tasan zai buqata na gata da komai kafin tabarshi achan kasar. Taj yayi kukan rabuwa da ita sosai don yana masifar sonta kuma ya shaqu da ita…. Ayi hakuri da wannan zuwa gobe zan cigaba bana jin dadi ne wallahi. Thanks for understanding. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 33-34 After 10years Bayan shekara goma da tafiyar taj, abubuwa da dama sun sauya ciki kuwa harda haduwar hidaya da jamid har zuwa ga auren su, sai kuma matsalolin da khaal ya fuskanta wajen hidaya,bashida control kwata kwata akanta, babu abunda ke gabanta sai aiki, arzikinsu kuwa alhamdulillah ya bunqasa sosai wajen sau uku, da taimakon hidaya da khaal, don ita ke running companyn. Maganar taj kuwa tun bayan tafiyarshi ta hana kowa ya kusance shi ciki kuwa harda khaal, babu yanda baiyi ba akan ta dunga barin shi yana zuwa gida amma kiri kiri tace ah ah abarshi yayi Karatu, daga bangaren taj din shima bason dawowan yake ba don ya gama sabawa da nan din, gaba daya rayuwarshi da girmanshi duk anan yayi, and beside hidaya na zuwa ganinshi all the time wanda hakan yafi mashi komi a rayuwa kuma babu abunda ya nema ya rasa don ta gama bashi komai da ta san zai nema. Damuwar khaal akanshi daman bata wuce sanin me yakeyi achan din ba, dukda hidaya ta kasa ta tsare akanshi ta hana kowa kusantarshi hakan baisa khaal ya barshi ba, shima haka zai shirya yaje har chan England din don ganinshi saidai duk sanda Zaije cikin rashin sa a baya samun shi wanda hakan duk shirin hidaya ne, da zarar khaal zaije ganinshi saita tura taj din vacation duk dan karta bari su hadu wannan yasa ya taso hidaya ce komai nashi, bai damu da kowa ba sai hidaya. Da farko khaal bai kawo komai aranshi ba saboda yanda take son taj din sosai sai daga baya da abubuwan nata suka fara yawa ne yasa ya miqe tsaye akan taj, ya fara tunanin meysa take hakan,maysa bata son ya dawo? Daga karshe dai haryazo ya fara zargin ko saboda bata san ya karbi mukamin da take dashi a company ne? Tsoronshi daya daman akan hakan ne don baya fatan ranar da zatazo su fara samun matsala a junan su, duba da yanda kuma take son shi sosai wannan ya sashi jin ba hakan bane don haka ya zuba mata ido kawai har zuwa lokacin da taj din zai kai shekara talatin a duniya, da zarar yakai wannan shekaru dole ya dawo ya karbi legacy din family din. Duk karshen wata hidaya ke zuwa ita kadai ta duba shi, haka zata shirya taje ta kwana biyu sannan ta dawo. Har ya kammala karatunshi na degree fannin engineering for 5 years wanda shima itace ta zaba mashi abunda zai karanta din zuwa masters daya sake yi, bayan ya kammala ta sake saka shi dora wani karatun. A ranar da taj ya cika shekaru ashirin da tara khaal ya samu hidaya da maganar dawowan shi, Lokacin daya fara maganar dawowan nashi bata nuna mashi komai ba Saima shaida mashi datayi zai dawo idan ya kammala second degree dinshi da yakeyi, wannan excuse din data bayar yasa khaal yyi shuru bai sake cewa komai ba, ana nan har shekara ta sake zagayowa inda taj ya cika shekara talatin cir a duniya, nan ne fa khal ya miqe tsaye shima akan dole sai taj ya dawo saboda ya karbi responsibility dinshi a matsayin shine da namiji a Cikin familyn, babu irin matsalar da khaal bai samu ba daga hidaya, inda ta nuna mashi cewa babu wanda ya isa ya fada mata yanda taj zaiyi rayuwarshi, she’s doing what is best for him, kuma karatun da yakeyi shi zai amfana, duk wannan excuses din data dunga bayarwa are not valid to khaal, don ya kasa gane wannan wani irin karatu ne, taj yabar saudi yana da shekaru sha bakwai a duniya and now it’s over 13 years. sai a lokacin ya fara ganin true intentions dinta saidai har zuwa lokacin yaqi aminta da hakan ne, kwata kwata bata ganin girmanshi kamar ba kanin mahaifinta ba, har tazo ta kaiga bashida ta cewa akan alamuran family din, wannnan abu yayi mashi zafi sosai har ya fara tunanin rabuwa da ita da qannen nata suyi abunda sukaga dama don su afiya ma sun kangare, sai abunda sukaga dama sukeyi, saidai tunawa da dan uwansa da amanar daya bar mashi yasa kawai ya danne duk abunda ke mashi zafi ya cigaba da hakura da abunda takeyi. Da taimakon jamid da shareholders khaal ya samu yayi forcing dinta dole ta sashi dawowa, ranta yayi mugun baci ganin harda jamid a cikin waenda suke jayyaya da ita akan taj, babu irin isa da bata nuna masu ba akanshi saidai tasan tunda shareholders suka shugo alamarin dole ta hakura kuma babu yanda zatayi ta sauya yanda rules din suke, saidai har zuwa lokacin bata nuna masu taqa maiman dalilin daya sa ta hanashi dawowan ba saima nuna masu shine baya son dawowa da takeyi. Hidaya dai tsara ma taj rayuwar da zaiyi tayi, tun achan england ta chusa mashi qiyayyar dawowa kasar, saida ta tabbatar ya saba da nan din sosai har yaji baya son barin kasar. England Wayarshi dake cikin aljihunshi ce ta soma ruri, daga kwancen da yake ya ajiye dumbells dake rike da hannyenshi guda biyu, dagowa yayi zaune ya gyara zamanshi kan weight bench, greyish idanunshi da gashin ido suka kwata luff luff akai ya soma budewa, bin wajen yayi da kallo mutane maza da mata jajayen fata kowa na hada hadarshi, daman yawanci anfi zuwa during weekends. Kyakyawan saurayi ne ajin farko, gashi fari tass shima, zufa ta gama wanke shi sanadiyar workout din da yakeyi incoming call din ya katseshi, Sanye yake da fitness hoodie mai gajeran hannu da ta dan kamashi don ana iya hango shatin 6packs din dake a shafe wajen cikinshi, gefen damtsen hannunshi wani dan baqin zane ne kamar tattoo dan karamin, sai wani short da leggings daya saka daga ciki, kayan sunyi masifar amsar jikinshi dayake maintaining physique dinshi, he’s so fit and huge. Wayar dake ta faman ruri ya zaro yana mai kallon screen, ganin wadda ke kiranshi, ya sashi saurin cije lebenshi da sukayi jaa kafin ya sauke wani irin sanyayyan murmushi mai melting zuciyar mata. Daga wayar yayi cikin hanzari ya soma magana yana mai lumshe idanunshi ya sauke ajiyar zuciya sound of relief Puffy lips dinshi ya soma motsawa ahankali “First love!!!” Ya furta cikin muryarshi wadda bata futa sosai at the same time yana lumshe ido jin muryarta kadai. Saurin miqewa yayi, wayar har zuwa lokacin tana hannunshi don akwai airpod a kunneshi, dagowa nayi don kallon asalin height dinshi, yana da tsayi da jiki mai kyau, masha allah kawai za ace. Magana akayi daga chan wadda ya sashi sakin wani irin murmushi kawai. Wayar ya zura cikin aljihunsa kafin ya duki katon bottle dinshi ya nufi hanyar futa daga gym din. Toilet din gym din ya fara shiga ya cire hoodie din tashi yayi wanka kafin ya sauya kaya zuwa waenda yazo dasu wasu arnayen english wears designers. Sense of dressing dinshi is just different, daga gani yasan irin shigar dake mashi kyau. A gurguje ya gama ya saqala agogoshin sannan ya saka wani shade baqi ya futo da back pack dinshi. Daidai inda motarshi take ya nufa ya danna keys din, cikin arniyar sport car din tashi ya shiga, yana shiga ya kunnata kafin yayi reverse yabar wajen. Anatse yake driving cikin kwarewa, fuskanshi har zuwa lokacin dauke da murmushi, hannunshi daya na kan steering yana murzawa cikin kwarewa ga sound din cool music na tashi. Tafiyar minti goma ta kawoshi airport, yana parking ya fito bayan ya rufe motar tashi. Cikin airport din ya nufa bai tsaya ko ina ba sai private lounge na arrivals,yana zuwa ya soma dube dube ko zai ganta, daga chan nesa kuwa ya hangota a tsaye tana waya, tana sanye da abaya sai baggage dinta dake gefenta. Ganin fuskanta kawai ya sashi sauke wani irin murmushi mai wuyar fassara. Takowa ya soma yi har zuwa inda take, sai a lokacin ta lura dashi, sanin abunda zaiyi yasa ta daga mashi hannu alamun ya dakata, chak kuwa ya tsaya yana murmushi yana kallon fuskanta ba tare da ya damu da gwale shin datayi ba don harya bude hannunshi yana shirin rungumeta, kallo daya ta mashi ta dauke kanta daga kanshi, saida ta gama wayan kafin ta maido da dubanta gareshi, fuskanshi kawai ta zuba ma idanu, ya kara kyau ba kafan ba compare to last zuwan da tayi, shi kamar ma kullum kara kyau yakeyi da cikar ido. Cikin british accent dinshi a shagwabe yace “first love” kafin ya rumgumeta gaba daya, “i missed you so much first love” Shuru kawai hidaya tayi tana mai sauraronshi harya gama kafin ya saketa, “daga ina kake? I’ve been waiting” “Sorry for keeping you waiting first love” Ba tare da ta kalleshi ba fuskanta na nan yanda take ba yabo ba fallasa, duban agogon hannunta tayi kafij tace “next flight dina zai tashi in the next 10 mins, seat let’s have a chat” Zama sukayi yana kallonta da mamaki, ganin haka ya sata cewa “ba zama nazo yi ba, i had to stop by saboda inason muyi magana.” Attention dinshi gaba daya ya bata ya natsu sosai cikin ladabi yace “okay first love” “Get ready by monday inason ka dawo saudi” Cikin sauri ya dago yana kallonta, girgiza mashi kai tayi alamun yes kaji abunda na fada, “No but” ta katseshi don tasan abunda zai fada kenan, Sunkuyar da kanshi kawai yayi yace “okay, i will” ya amsa ta cikin ladabi. “You’re going back for good,” ta sake fada ba tare da ta kalli fuskanshi ba, fuskanta a hade kamar hadari babu digon murmushi ko dariya Gabanshi ne ya fadi, meysa first love zatace haka, ayyukanshi na nan fa? Tech Business company dinshi da yake running fah? yana son ya tambayeta dalilin hakan saidai bazai iya ba don hakan kamar jayyaya ne da ita. Sama sama suka danyi discussion kafin time flight dinta ya gabato har lokacij ya cika kafin ya mata sallama, har cikin wajen check in ya rakata kafin suyi sallama. Jiki a mace ya dawo, bai tsaya ko ina ba sai tech company dinshi, wajen kamar repair shop ne da harkar kere keren abunda ya shafi karfe da motoci technically, babban elegant tech shop ne sosai mai girma ba kadan ba, yana da employers sunkai su goma kowanne yana aikinsa da bangaren da yake ma aiki, tsayawa yayi yana kallon wajen, “Autofix,” Nan take ya fara tunanin yanda ya fara wajen, tun tasowarshi yake son harkar motoci, he’s so into automotive technology, wannan yasa yayi karatun engineering, koda ya fada ma hidaya bata musa mashi ba ta amince akan yayi abunda yake so wanda hakan ya mashi dadi sosai don a ganinshi tayi supporting abunda yake so, wanda hakan yasa yake jinta sosai aranta, Wajen ya kasance one of his happy place kuma its like his dream he build it da kanshi tun wajen bai zama abunda ya zama ayanxu ba, daman yana da passion din wannan. Wannan autofix din nashi ya samu recognition a England city, don ba karamin waje bane, yana harka da manyan company’s inda suke kawo mashi ayyukansu daya shafi kere keren abubuwan fannin electronical technology. Yana cikin top members na desiging team din hyundai,wannan yasa ya zama popular sosai achan. Wajen ya zama popular for both maza da mata masu zuwa da motocin su, matan ma dai zuwa suke saidai su zuwansu saboda owner din wajen ne, saboda he’s resistable, babu wanda ya taba tunanin shi ba citizen kasar bane don yana da connections sosai. Wannan nasarorin daya samu hidaya bata sani ba kwata kwata, don bashi ne a gabanta itadai duk a ganinta wannan part din daya zaba shine daidai dashi as long as baya tunanin dawowa. ***** Tsaye suke a wajen parking space din arrival,hidaya na daga tsaye tana receiving call while su fadwa da afiya suna daga tsaye bakin mota,cikin yan mintuna kalilan saiga mutane sun fara fitowa daga gate din international arrival, kallon gate din fadwa da afiya suka soma yi, yau ce rana ta farko da zasu sanya shi a idanunsu tun bayan tafiyar shi, saida aka gama fitowa gaba daya basuga alamun shi ba. “ni zan koma cikin moto na nikam…” fadwa ta fada Kasa karasa maganar dataso yi tayi inda idanunta sukayi capturing dinshi yana fitowa majestically, saurin tabo afiya fadwa tayi, A natse yake tafiya yana tunkaro inda suke hannunshi rike da baggage dinshi sai dayan kuma ya rike jacket dinshi, fuskanshi sai walqi takeyi don ya tara beard wanda ya qara ma fuskanshi kyau sosai, dukda yana jin wani irin fargaba hakan baisa ya sauya yanayinshi ba, gaba dayansu sakin baki sukayi banda hidaya da ta bama bangaren da yake futowa baya tana amsa waya. fadwa ce ta kasa boye expression dinta beneath her breath tace “wowwwww” afiya dai tabe baki kawai tayi tana kallon ikon Allah don ya chanza gaba daya kamar bashi ba, shekara goma sha uku kenan. TAJ kenan, the charismatic handsome young man, he’s a definition of perfection tafiya yake majestically cikin kananun kaya, fuskanshi yasha wani baqin glass daya haska fuskanshi. waige ya soma yi kafun idanunshi su sauka kan hidaya data juya baya, dukda baiga fuskanta ba jikinshi ya bashi itace saboda kaunar da yake mata koya makance zai iya sensing intana waje. gaba daya baima gane su fadwa ba don tun bayan tafiyar shi bai Kara ganinsu ba don basa zuwa duba shi chan england. Yana karasowa ya rungume hidaya “first Love” Katse wayar datakeyi tayi tare da hadiye wani mugun miyau, lokaci guda wani irin baqin ciki ya turniketa, ta dauka kusan second talatin a haka kafin ta daidaita natsuwar ta tare da sauya fuska kamar ba ita ba ta juyo inda yake fuskanta dauke da murmushi “welcome back big baby, finally Ka dawo Zan samu peace of mind” Murmushi yayi wanda ya fadada fuskanshi ya Kara mashi kyau ya sake kallonta yace “I’m so happy to see you,meysa kika tsaya a cikin rana? Banason kina wahalar da kanki first love” Hannunshi ta dan saki ta kauda kanta gefe tace “dole nazo Ay na tarbeka my baby brother” Gyaran murya ta danyi kafin ta kalli inda su fadwa ke tsaye kamar gumaka suna kallonsu, kowacce da irin abunda take ayyanawa a ranta “Bakaga sisters dinka bane?” Hidaya ta tambayeshi tana kallon inda su afiya ke tsaye Maido da kallonshi yayi ga inda take mashi nuni, daya bayan daya ya kallesu, yanayin fuskanshi ya dan sauya kafin ya karasa inda suke ya rungumesu ba tare da yace masu komai ba. Fadwa ce kawai ta iya ce mashi “welcome” afiya kuwa cikin motar ta koma tana takaicin dalilin da zaisa hidaya ta tilasta sai sunzo daukan shi. Bangaren hidaya bazaka taba iya tantance a wani irin yanayi take ciki ba saidai deep down tana jin wani irin tashin hankali da bacin rai a zuciyarta da wannan dawowar tashi. Wannan rana ta kasance mafarin da zai sauya rayuwar shi da kaddarar shi, ranar da rayuwar shi zata sauya daga rayuwar daya saba, ranar da farkon babin rayuwarshi mai dauke da sarqaqiya zai bude. Cigaban labari…. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 34-35 Cigaban labari….. Bayan futar hidaya daga bedroom din fadwa ta kalli afiya daketa faman zubda hawaye, itama ranta ba karamin baci yayi ba ta soma magana ‘’ay daman saida na fada maki, kanki kamar na kifi,how could you even think about that?’’ Saurin kamo hannunta afiya tayi ‘’haba fadwa, meysa baki fada min tun wuri ba, wallahi bansan haka abun yeke ba’ na dauka duk wadannan abubuwan da ukty keyi saboda tana sonshi ne’’ ‘’Ke baki da Ido ne saina fada maki? Saurin fuzge hannunta tayi daga na afiya tare da yi mata kallon kin bani mamaki kafin ta fuce daga bedroom din rai a bace itama. Tana fita afiya tayı saurin share hawayenta, nan take kuma ta sauke wani murmushi mai wuyan fassara akan fuskanta. Bangaren hidaya daga bedroom din afiya direct ta wuce study room dinta dake sama, idanunta yayi jaa sosai, fadin yanayinta a wannan lokacin bashi misaltuwa, tana shiga ta rufo kofar daidai nan jamid ya fito daga bedroom dinsu, kallon study room din nata yayi kafin ya kauda kanshi ya fuce daga part din nasu. sabeeha dai tunda ta shiga dakin su bata fito ba, gaba daya ta gama shiga confusion da wannan ala’amarin dake faruwa da ita, tsoro fargaba babu wanda baya yawo a cikin ranta, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa, aure dai data sani, yau itace keda aure akai, kuma auren wanda baima san ina kanshi yake ba, kuma aurenda babu sanayyar iyayenta akai sannan itama an yi conering dinta, don harga allah bada saninta haka abun zai juye ba, haka ta kwana tana hawaye, ta rasa dalilin dayasa ita rayuwar tazo a haka, mey zata cema mahaifiyarta?.yanxu idan aka kamata fa a matsayin yar leqen asiri?, bama wannan ba, ayanxu dai ta tabbatar ana son ayi amfani da ita ne wajen cutarda wannan mara lafiyan, abunda ta Kasa ganewa shine meysa za a turota nan gidan, kuma maysa ka aura mata shi? da wannan tunanin barci barawo ya fusgeta washe gari ta kama talata, shirinta ta fara yi yanda ta saba koda yaushe cikin uniform dinta, gaba daya jikinta a mace daga yanayin yanda take shirin ma, tana gamawa ta fuce daga bangarensu na yan aiki. saman part dinshi ta wuce direct, kamar kullum saida ta fara gyaran part din cikin natsuwa kafin ta nufi dakinsa lokacin wajen karfe takwas na safe. koda ta bude kofar dakin sanyin ac ya bugeta take taji wani irin yanayin mai wuyar fassara ya risketa, haka kawai taji wani irin sauyi a tattare da ita, kallon inda yake kwance tayi, ganin bashi kwance sannan bedside lamp dinshi a kunne ya tabbatar mata da ya tashi, a gurguje ta gyara mashi beddings din gadon kafin ta shige closet room dinshi ta debo mashi kaya riga da wanda masu laushi farare tass wanda ya saba sakawa. tana kokarin ajiye mashi su a bakin gado taji yo ihu daga toilet din. cikin saurin ta ajiye kayan ta nufi wajen toilet din ta soma knocking ‘’friend are you okay?’’ yana jin muryarta ya fashe da kuka, ba tare da tunanin komai ba sabeeha ta bude kofar tana mai kokarin rufe idanunta don bata san a wani yanayin zata taddashi ba, kasa rufe idanun nata tayi ganinshi jikin bangon bathroom din jikinshi har bari yake ya tamke idanunshi baima ga sabeeha ba, kallon bathroom din sabeeha ta soma yi don ganin abun da ya tsorata shi haka, idanunta ne ya sauka kan dan karamin kenkeson dake crawling a wajen, maido da dubanta tayi gareshi inda yake pointing abun,kasa dauke idanunta tayi daga kanshi, yana daure da towel a waist dinshi, take taji wani irin tausayinsa ya mamayeta, ya za ayi ace wannan katon ne ke tsoron dan wannan mininin abun, baifi ya takeshi da kafarshi ba. hannunshi ta kamo cikin sauri ya waro idanunshi don ya tsorata sosai, ganin sabeeha ya sashi saurin rungumeta gaba dayanta ya rufe ta ruff, cikin sauri ta rufe idanunta, yauce rana ta farko data taba jinta jikin namiji kaff duniyar nan, abun yazo mata a bazata, saurin hankadashi tayi ya koma baya, kokarin dawowa ya soma yi zai rungumeta tayi saurin dakatar dashi, ‘’kaga na dauke abun bazai maka komai ba’’ kallon tiles din yayi ganin babu kyankyason yasa ya sauke wani murmushi har kumatunshi na lobawa, fuskanshi har wani walqi takeyi saboda annuri, bata san lokacin da itama ta sauke wani murmushi ba, ‘’thank you bibi’’ da mamaki sabeeha ke kallonshi jin sunan daya kirata dashi, ‘’waye bibi?’’ da yatsan shi yayi nuni da ita tare da dungure mata goshi, ‘’you!! you’re my bibi my hero, you save me’’ samun kanta tayi da kallon lebenshi dake furta sunan, ‘’yanxu wannan ne aka yima aure jiya? aure dai na mata da miji?, saboda me? why? what’s the reason?’’ haka ta dunga saqe saqe cikin zuciyarta, motsin data ji daga bedroom din ne yasata saurin juyawa ta futo daga bathroom din shima ya biyo bayanta. kallonsu jamid dake tsaye yayi, saurin gaishesa sabeeha tayi kafin ta fuce daga bedroom din, kallonta jamid yayi harta fuce kafin ya maida dubansa ga taj dake tsaye da towel rike a kugunshi don bai iya kullewa ba sosai. excitedly ya soma magana fuskanshi dauke da murmushi ‘’good morning uncle’’ ‘’morning big baby’’ jamid ya amsa shi yana kallon fuskanshi, hannunshi jamid ya kama suka zauna bakin gado ‘’how are you today?’’ jamid ya sake tambayarshi yana mai kokarin janshi a jiki sosai ‘’i’m fine uncle, i slept well’’ kallonshi jamid ya soma yi yana wani tunani, kwata kwata babu wani improvement a tattare da rashin lafiyar taj, wannan abu yana damunshi sosai. ‘’taj’’ ya kira sunan shi ‘’yes uncle’’ ‘’zanje england zaka bini?’’ shuru taj yayi kamar mai nazarin wani abu harda sanya dan yatsa a gefen bakinshi, ‘’uncle england? ina ne england?’’ ‘’bakasan england ba? achan fa ka taso har kayi karatu ka manta?’’ confusely yake kallon jamid, ganin haka yasa jiki a mace jamid yace ‘’never mind me je ka shirya’’ Jamid na zaune ya shirya fess fess abunshi, sabeeha ta shigo da breakfast dinshi da maganin shi ta ajiye ta fuce don ta basu waje, bata dade da futa ba jamid shima ya futo daga bedroom dinshi hannunshi rike da medication din taj. Bayan futarsa da awa guda ya sake dawowa tare da barad wanda keta faman murnar zuwa wajen taj din don rabonshi daya gansa tun ranar daya futo dashi ya fadi. a zaune suka ya tarar da taj din yana ta faman juya puzzle box dinshi,gaba daya attention dinshi na ga abun,jamid baiyi mamakin ganinshi zaune ba don yasan already wannan medication din nashi ke sashi barci, saidai ya kasa gane dalilin da zaisa ace wai the only solution to his problem shine a barshi ya dunga barci, dukda yasan he’s risking it, haka kawai yaji bayason ya barshi yasha maganin. cikin saurin barad ya zame hannunshi daga na daddyn shi ya wuce wajen taj din, cikin murna ya soma magana ‘’uncle taj’’ da mamaki taj ke kallonshi yana pointing dinshi, ‘’you!! you!!’’ take ya kyalkyale da dariya, shima barad din dariya ya soma yi . saurin rungume taj din barad yayi ‘’i missed you uncle taj’’ ‘’i missed you too my old friend, i have a new friend now’ tunda baka zuwa wajena muna wasa’ a shagwabe barad ya kalli taj din, ‘’toh ay mama ne ta hanani zuwa’’ ‘’who’s mama?’’ ya tambayeshi, jamid ne yayi saurin katse su, budo kofar da akayi ne yasa suka zuba ma kofar idanu, taj ne yayi saurin cewa ‘’bibi, come and see my old friend’’ saqe sabeeha tayi tana kallonsu harda taj din, don tasan by this time daman tana zuwa dubanshi ne don yawanci a daidai wannan lokacin barci yakeyi. ***** karfe biyar daidai hidaya ta shigo gidan, hayaniyar data soma ji ne yasa ta dan tsagaita da karasawa part dinta, bangaren taj ta nufa inda take jiyo hayaniyar,budo kofar tayi daidai nan taj ya wullo pillows din da aka jera ma sitting room din, daman wasa suke yi shida barad yanda kasan sa’anni, sabeeha kuma na daga gefe a tsaye tana kallonsu tana murmushi, this is the second time dataga taj din ya futo parlorn ga kuma barad dake wasa tare dashi. yana ganin wadda ta budo kofar yayi saurin wurgar da pillows din ya nufi inda hidaya take ya rungumeta tsam a jikinshi, barad dai tsoro ya hanashi karasowa inda suke don yana daga nesa. sabeeha ma saida gabanta ya fadi tsabar tsoron abunda zai buyo baya, hidaya dai kasa gane meke faruwa tayi don by this time tasan barci ya kamata yayi. ‘’first love, kinga old friend dina yau ya dawo, i’m so happy, wasa ma mukeyi’’ saurin banbareshi tayi daga jikinta tana mai kallon sabeeha rai a bace tace ‘’what’s going on here,’’ ganin tana fada yasa taj cewa ‘’first love karkiyi bibi fada please i’m sorry bazan sake ba’’ ko kallon inda yake hidaya batayi ba tana mai kallon sabeeha, ‘’baki bashi medication dinshi bane?’’ ‘’na bashi ma’am, an hour ago yasha’’ shuru hidaya tayi tana nazari, meke faruwa ne? to kodai yanxu medication din ya daina mashi aiki ne daman doctor yace za akai lokacin da maganin zai daina masa aiki. saurin kauda tunanin tayi tana mai kallon barad ‘’wayace ka shugo nan’’ ta karashe cikin fada tana mai fusgo shi, duban sabeeha tayi ‘’take him back to his bedroom now!!’’ tana kaiwa nan ta fuce da barad, tana futa taj ya fashe da kuka,da kyar sabeeha ta jashi suka koma bedroom tana bashi hakuri, ‘’bibi, nayi ma first love laifi, i’m bad boy ko’’ marin fuskanshi ya soma yi yana kuka ‘’i hate my self’’ saurin rike hannunshi sabeeha tayi ta zaunar dashi a kan gadonshi kafin ta soma goge mashi hawayen dake fuskanshi ‘’no friend you’re a very good boy, kuma first love tana sonka sosai kaji, ka daina kuka idan baka son tana fushi dakai;’’ haka ta dunga lallaba shi harya hakura, washe gari da safe haka jamid ya sake shugowa da sassafe, yana nan zaune sabeeha ta shugo da breakfast dinshi da maganinsa, tana futa jamid ya kwashe magungunan ya boyesu a aljihunsa don kwata kwata jiyan dayaga babu abunda ya faru da taj yasa shi jin bai yarda da medication dinn ba kawai bayan wannan ma har zuwa yanxu baya jin ya yarda da hidaya da wannan doctor din. wunin ranar kuwa jamid yana tare dashi yana karantarshi tass. Haka aka shafe sati guda jamid na dauke magungunan taj din yana boyesu ba tare da sabeeha ta sani ba don baya son hidaya tayi blaming dinta, wannan yasa da zarar ta kawo magungunan yake boye su ba tare da sanin kowa ba. sabeeha dai ba karamin mamaki ta dunga yi ba ganin yanda ta din ya daina barcin kamar yanda ya saba, sai kawai ta fara jin qila ya soma samun sauqi ne shiyasa ya daina barci kwata kwata bata kawo cewa dauke maganin jamid yakeyi ba. taj dinma shi kanshi dadi yakeji sosai, ya samu sakewa, kullum yana tare da barad suna wasa, da zarar mamanshi na gaf da dawowa daga aiki kuwa zai fita daga part din gudun kartayi mashi fada, don ta hanashi zuwa wajen taj din kwata kwata. weekends.. yau weekends kowa yana gida gaba daya, harda hidaya dasu afiya, zaune suke akan dining suna yin break fast, hidaya na hakimce akan kujerarta ta daban, gefenta kuma barad ne dasu fadwa gabansu kuwa shaqe yake da abunci kala kala kamar mutane goma ne sazuci. saukowa suka somayi daga stairs, sabeeha na biye dasu a baya, tunda suka soma saukowa daga stairs din taj ke kalle kalle, hannunshi na cikin na jamid ya rike shi gam, ganin ya tsaya yasa jamid cewa ‘’muje’’ exicitedly ya kalli jamid yace ‘’uncle wajen first love zaka kaini?’’ ‘’yes taj muje ko’’ karasowa sukayi dining din, babu wanda ya lura dasu saida sukaji muryar taj din, ‘’first love!!!’’ damm gaban hidaya ya bayar, for a second dataji yanda ya kiranta kamar yanda yakeyi kafin ya samu wannan amnesia din, sakin spoon din dake hannunta tayi ta dago tana kallonshi da jamid a tsaye ga sabeeha a bayan su, cikin sauri taj ya saki hannunshi dake cikin na jamid ya nufi inda take ya tsaya a gabanta harda bubuga kafa ‘’good morning first love,’’ kasa magana hidaya tayi sai wani irin mugun kallo da take aika ma jamid, maids din da suke shugowa da abunci kuwa da mamaki suke kallon taj din don basu taba ganinshi ba sai yanxu, gashi daman kowa yasan da labarin cewa akwai dan uwansu mahaukaci dake zaune a gidan. afiya da fadwa kuwa kallon juna suka soma yi don yau kam akwai drama. kokarin rungumeta ya soma yi ta hankadashi baya, wannan abu yayi ma jamid zafi sosai aranshi, ‘’whats this? whats going on here? meyakeyi anan kasa, uban waye ya sauko dashi? da izninin wa? who dare to do so?’’ jamid dai nannade hannayenshi yayi yana kallonta, tuni taj ya burkice yana kokarin kamo hannunta kamar mahaukaci, ‘’first love i’m sorry’’ haka ya dunga maimaitawa wanda ya sata daka mashi tsawa ‘’shut up, dukanka akayi ne?,why are you sorry?waye ya sauko dakai? kukan me kakeyi?’’ afiya ce tayi saurin cewa ‘’yoh ukty mahaukaci yasan abunda yake yi ne eh?’’ saurin mintsininta fadwa tayi taja bakinta tayi shuru, ‘’ni ne nan na sauko dashi, kuma da iznina, as from today tare damu zai dunga breakfast, babu amfanin boyeshi tunda kin rigada kin bayyanawa duniya halin da yake ciki, so there no need of keep him grounded’’ kasa magana tayi tana mai kallon jamid ranta a bace, wani irin murmushi ya sauke daga labbanshi don yasan bazata ce komi ba, kuma ko hauka take bazata taba kawo maganar magani ba kuma yasan abunda ke ranta kenan, and tasan dazarar ta kawo maganar zaiyi questioning dinta don haka ta dauki wayarta ta fuce daga dining din. tana futa su afiya ma suka miqe suka bar dining din, jamid bai damu ba don daman yasan halin su daya, don haka ya kalli taj dake ta faman kuka ‘’kana son ayi maka dariya ko?, ka manta na fada maka kai big boy ne?, ka daina kuka okay? big boys don’t cry’’ saurin share hawayenshi kuwa yayi ya zauna kusa da barad. sabeeha dake tsaye kamar munafuka dukta tsure, saida su hidaya suka fice ta sauke wata ijiyar zuciya, kamar daga sama taji muryar jamid, ‘’zo ki zauna muyi breakfst’’ ‘’no sir nayi breakfast’’ ‘’i insist please, zauna kiyi breakfast damu’’ haka nan ta zauna daga chan sako badan taso ba duk a tsorace take gashi ta takura sosai don gaba daya hidaya tsoro take bata. bangaren hidaya tana hawa sama ta soma dialing number doctor, yana dagawa ta soma magana ‘’doctor ina son a chanza ma yaron nan medication, wadannan basa aiki, inason ka nemo very strong sedation seems like wannan daka dora shi akai ya daina mashi aiki’’ daga chan bangaren doctor ya samsa ta ‘’but madam, wanna maganin is the strongest and safest among, idan aka bashi wanda yafi wannan za a iya samun matsala’’ ‘’i dont care’’ ta daka mashi tsawa, ‘’just do your job properly idan baka san matsala’’ sanin halinta ya sashi cewa ‘’yes madam’’ sannan ya kashe wayar. Tana kashewa ya soma dilaing wata number hankali a tashe, ‘’sir you need to talk to boss urgently, abubuwa sun fara sauyawa fa, dole ku fara first move dinku’’ tsaywa yayi ya gama sauraron wanda yake waya dashi kafin ya kashe bayan ya karbi umarnin da aka bashi. wunin ranar taj a kasa yayishi shida sabeeha da barad, haka suka dunga zagaye duk girman gidan, maaikata nata kallonsu,masu tsegumi nayin nasu, jamid kuwa yana biye dasu a baya yana kallonsu, ba karamin dadi ganin taj din a haka yayi ma jamid, koda ya tuna expression din hidaya dazu daya sauko dashi sai yayi murmushi, shi kadai yasan abunda ke ranshi. sai yamma liss suka shigo cikin gida, hidaya dake sama bata san abunda ke faruwa ba, fadwa daman tana bedroom dinta while afiya kuma ta futa. washe gari ta kama sunday, yauma jamid saida ya sauko dashi kasan, ba laifi hidaya bata nuna komai ba don harda ita aka zauna akayi breakfast din, su afiya kuwa babu abunda suke sai mocking taj da abuncin yara, jamid dai yana kallonsu baice masu qala ba, sabeeha kuwa tuni ta gudu bata ma tsaya ba balle jamid yace mata ta zauna dasu tayi breakfast wanda bata fatan rana makamancin haka ta bayyana. kiran da afiya tayi ma maid yasa suka maida hankalin su kan abunda take cewa ‘’kuje ku hado ma baby brother na cereal, irin na barad kunsan shima yaro ne’’ tana kaiwa nan ta kalli taj dake gefenta ‘’zakasha ko baby brother?’’ da murna kuwa ya amsa ta ‘’yes, i will’’ ‘’yauwa good boy zanje shopping anjima zan sayo maka kayan wasa’’ ta karashe tana shafa fuskanshi,shi kuwa ya dunga karkace kai kamar yaro fadwa kuwa mai zatayi banda dariya, tun tana kunshewa harta fito fili, hidaya kam bata ce masu kala ba hankalinta nakan abunci. misalin karfe biyar suna zaune a sitting room na kasa, sabeeha na zaune a kasa while taj da barad suna kallon cartoon a tv,sai jamid dake gefensu yana danna laptop, saukowa hidaya tayi zuwa nan sitting room din don haka kawai taji akwai abunda jamid ke shiryawa wanda ta kasa gane koma menene. zama tayi anan kasan da mamaki kuwa ya kalle ta don hidaya dai hidayar daya sani tafi karfi tazo kasa ta zauna haka kawai saida dalili, shugowar afiya da sallamarta yasa suka dago, hannunta rike da ledoji manya, daidai nan fadwa ta shugo cikin parlorn itama ta zauna don jiran ganin abunda afiya zatayi don da gayya ta tafi yin shopping dinnan. ‘’heyy!! baby brother’’ cikin murna ya mike zuwa inda take ‘’yes’’ ‘’i got all of this for you harda kaya na saya maka jeka gwada su’’ excitedly kuwa ya karbi kayan ya wuce sama ya sako su kafin ya sauko, dagowa sukayi gaba daya suna kallonshi, kayan kwata kwata basuda fasali, mixup din kayan kamar wani mahaukaci, ga hula daya kafa da wani dan gajeran wando, gaban rigar kuma an rubuta ‘’i’m a mad dog’’ gaban hidaya ya tsaya yana nuna mata’, ’first love, sister ta bani new cloth, i love it yay’’ kallon kayan hidaya tayi kafin ta danyi murmushi, ganin yanda he is so excited about kayan yasa ta cewa ‘’you look handsome big baby’’ wani irin dadi ne ya ziyarceshi lokaci guda, first love ta yaba first gift na kaya da aka bashi, har cikin zuciyarshi yaji yana son kayan, afiya dake zaune tana tauna chewwing gum ce tace ‘’wowww, its says i’m a mad dog its so beautiful, i love the print out yayi maka kyau sosai’’ sai a lokacin jamid ya dago ya kalli taj din, ba tare da ya nuna komai ba kawai ya kauda kanshi gefe. hidaya kuwa miqewa tayi tabar parlorn ta wuce sama, fadwa na biye da ita, ganin haka yasa afiya ma tabi bayansu. suna hawa saman hidaya ta kalli afiya rai a bace ‘’wannan childish play dinfa? shi yasa kika kirani akan na sauko kasa? you think all of this is a joke? kina tunanin wannan wasan yara ne?’’ ‘’ukty i thought..’’ ‘’shut the fuck up, don’t play dumb with me,karki sake yin wannan shirmen, what are you trying to implyi by doing that? ke baki iya siyasa bane? don’t you dare spoil my plan, idan kika sake any suspicious move kamar wannan zan hukuntaki stick that to you dumb brain’’ tana kaiwa nan ta fuce daga bedroom din, dariya fadwa ta soma yi irin ta keta ‘’shiyasa nace duk cikin mu kece mai kwakwalwar kifi,’’ ‘’karki fada min maganr banza mana’’ afiya ta karashe rai a bace ‘’an fada din, bakida da wayo, bakida kissa, ke kwata kwata kanki kamar an zuba dumb waste’’ ran afiya ya baci sosai, bata ma tsaya ta saureta ba ta fuce daga dakin, tana futa ta zaro wayarta ta soma dialing wani international number datayi saving da snitch, ana dagawa ta soma magana, ‘’when are you coming back, zan baka hadin kai’’ daga chan bangaren ne akayi magana kafin ta sake cewa ‘’i don’t care anymore lets do it’’ …. Matar Taj (destined with you🩵🤍) Written by Queenmarh✍️ Free page Chapter 37-38 Update San diego california. Tun bayan abunda ya faru daddy ya saka ma maya ido sosai, yanxu bata futa kwata kwata sannan kawayen ta ma hanata mua’amala dasu, daga school sai gida take dawowa. duk wani rayuwar jindadi yayi canceling, no parties,no bad influence friends. Ba karamin misunderstanding suka samu ba shida mummy akan wannan don ita a ganinta kamar sun takure mayan ne,kuma girma takeyi she’s an adult tunda takai 18. bangaren maya kuwa babu abunda ya sauya, for the mean time ta rage abubuwan da takeyi don ta lura daddy yayi fushi sosai, saidai ko wata daya ba ayi ba ta cigaba da abubuwanta data saba ba tare da sanin iyayen nata ba, daman damuwarta karya hanata allowance dinta da yake bata. kullum zata shirya shirin school, tana futa ta shiga bus dinsu zata sauya hanya ita da su kloe, makarantar ma bata zuwa kwata kwata har suka gama final test batayi participating ko daya ba. koda school authority suka bukaci ganin daddy da mummyn babu wanda ya bayyana saboda yanayin aikin su, bayan wannan ma basuyi tunanin wani serious issue bane, wannan dalilin yasa basu ma san meke faruwa ba. **** Yau ta kasance 18th birthday din maya, tama manta gaba daya da ranar don yawanci haka shekarun zasu zagayo babu excitement, daman burinta bai wuce iyayenta su kasance da ita ba a ranar kamar wannan saidai hakan bai samu ba saboda koda yaushe suna aiki, basu da time dinta, wani sa’in suma mantawa sukeyi saidai mummy tana kokari don ganin she spends quality time da mayan. kamar koda yaushe yauma saida ta sauya kayanta zuwa na uniform daga chan wajen yawonta kafin ta dawo gida. a jigace ta dawo saboda ciwon mara dake nukurkusar ta wanda yasa tabar wajen partyn nasu ta dawo gida. nanny bee ce ta bude mata kofa ta shigo bayan ta karbi school bag dinta. cikin fara’a nanybee tace ‘’welcome back baby’’ ‘’thank you nanny bee mummy fa?’ ‘’mummy ta futa an kirata emergency a asibiti, daddy kuma ya kira daxu, he was concern about you’’ ta amsa ta anatse cikin gidan suka shiga tana gaba nanybee na biye da ita, maimakon ta wuce bedroom dinta saita wuce sitting room tayi kwanciyarta kan 3 seater, ganin yanda ta jigata yasa nannybee ajiye mata backpact dinta a gefenta ta wuce kitchen, ko minti daya batayi ba ta dawo da glass na favourite juice dinta. ‘’are you okay baby?’’ nany bee ta tambayeta kamar zatayi kuka tace ‘’nannybee, i’m having cramps’’ ‘’sorry baby,yanxu haka bakisha magani ba ko? bari na dauko maki’’ saurin katseta maya tayi’ ‘’no nannybee, inadashi a jaka na zansha’’ ‘’Happy birthday baby, i pray you stay beautiful and strong, you’re growing so fast’’ da sauri maya ta kalli nannybee, sai kawai taji hawaye na shirin zubo mata, matar nan tana kaunarta sosai kuma ta damu da ita sosai, she’s always there for her musamman lokacin datafi buqatar iyayenta akusa, jinyar rashin lafiya da dak wata damuwarta duk nanny bee ce kawai ta sani saboda itace ke tare da ita koda yaushe, ita tama manta da wani birthday dinta ashe ita bata manta ba saurin miqewa tayi ta rungume nanny bee tana hawaye ‘’thank you nannybee, thank you for always being there for me,no one cares for me except you, ke kadai cekika damu dani, daddy da mummy basu damu dani ba’’ share mata hawaye nanny bee tayi cikin dattako da nasiha ta soma magana, ‘’no baby, babu wanda yakai iyayenki sonki da kaunarki okay?, karki sake cewa basu damu dake ba, your daddy loves you so much shiyasa yake futa don yayi providing for this family, mummy ma taimakon alumma takeyi, she’s out there saving lives which i believe kinsan that’s a very good thing kuma duk abunda sukeyi sunayi ne don ki samu rayuwa mai inganci kinji ko’’ tabe baki tayi ta koma kan kujeran ba tare da tace komai ba, girgiza kai kawai nannybee tayi harzata juya tace ‘’bari na saka maki warm water kiyi hot bath zakiji sauki okay?’’ ‘’no nannybee zan huta sai anjima, bana son hawa saman yanxu’’ anan kasan nanybee ta barta ta wuce kitchen don cigaba da abubuwan da takeyi. bangaren maya kuwa barci ne ma ya fusgeta mai nauyi, bayan awa daya wajen karfe hudu ciwon marar ya tsananta wanda ya sata farkawa cikin gaggawa laluben jakarta ta somayi,bata son sha magani saidai idan ya tsananta indai bata sha ba wahala take sha sosai, idanunta yayi jaa sosai da alamu ta fara jigata sosai, neman maganin ta somayi bata gani ba, out of annoyance kawai ta soma zazzage jakar gaba dayanta a kasa,gaba daya abubuwa dake cikin jakar ta watsar anan kasa, cikin ikon allah kuwa taga maganin, ballar guda biyu tayi ta jefa bakinta sannan ta kora da juice din da nany bee ta kawo mata. komawa ta sakeyi ta kwanta tana jin relief kafin wani barcin ya sake fuzgarta anan kwance. karfe biyar daidai daddy yayi parking a harabar gidan, anatse ya fito cikin shigarshi ta suit baki wadda tayi mashi kyau sosai, hannunshi rike da flower rose da wani gift box da aka rubuta ‘’happy birthday princess’’ wayar dake maqale a kunnenshi ya fara kokarin katsewa yana cewa ‘’na dawo yanxu,’’ daga chan barin mummy ta amsa shi ‘’okay daddy, nima na fito yanxu, i will stop by the bakery zan karba cake danayi order,’’ ‘’okay love’’ ‘’hope ka sayo mata gift as you promise?, dan allah majeed yau babu fada, lets spend qaulity time with her, ita kadai allah ya bamu dan allah’’ murmushi kawai daddy yayi ‘’anya baki fini son maya ba kuwa?, tell me wa kika fi so? ni ko maya?’’ abunda ta fada ne ya sashi dariya kafin ya kashe wayar ya danna doorbell. nannybee ce ta bude tare da welcoming dinshi,cikin fara a ya amsa sannnan ya tambayi ko maya ta dawo, nan ta shaida mashi tana parlor tana barci. daidai nan suka karaso parlor din, miqa mata office bag dinshi yayi don ta wuce dashi sama. tana wuce ya maida dubanshi ga maya datayi rub da ciki tana da shakar barcinta, kallon fuskanta ya soma yi yana mai jin son diyar tashi sosai aranshi, takowa ya soma har inda take sai a lokacin ya lura da jakarta data watsar anan kasa. gyara mata kwanciyanta ya soma yi ahankali ganin tayi nisa sosai cikin barcini don karta fadi, saida ya gama ya ajiye mata flower din da gift box din a gefenta don tana tashi ta gani. yana gamawa ya soma kiran nannybee don ta tattara abubuwan makarantarta data watsar, kira biyu yayi ma nannybe ya dakata yana mai kallon abubuwan dake yashe a kasa, tsugunnawa yayi ya fara tattara abubuwan jakar ya hadesu waje guda har yazo kan yar takardar dake lekowa daga cikin zip din jakar,haka kawai yaji gabanshi ya fadi lokaci guda, nanndewa ya karasa yi don farin abunda ke ciki harya soma zazzagowa. da mamaki yake kallon takardar da powder dake cikin takardar, kuma daga jakar maya, kamar wanda ke tsoro haka ya soma shinshinar powder, take ya runtse idanunshi, babu abunda yake furtawa sai innalillahi wa inna ilaihi raji’un a cikin zuciyarshi, take idanunshi yayi ja, kanshi kamar an buga mashi guduma tsabar tashin hankali. knocking da akayi ne yasa nannybee da barci ya dauketa ta fito, cikin saurin ta karasa wajen kofar ta bude, ‘’welcome back madam so sorry na barki tsaye barci ne yadan daukeki’’ murmushi mummy tayi mata ‘’ba komai nannybee, daddy ya dawo ko baby fah?’’ ‘’yes ma’am, ya dawo,duk suna ciki’’ cake din dake hannunta ta mika mata kafin ta shiga daga ciki hannunta rike da paper bag data sayo ma maya kayan zagi datafi so. chak mummy ta tsaya ganin daddy zaune a sitting room, batama lura da maya ba saida ta karaso inda suke, ‘’yadai daddy’’ dago da jajayen idanunshi yayi ya sauke akan kyakyawar fuskanta kafin ya suake wata ijiyar zuciya kawai ya mike yabar parlor. da mamaki mummy ke kallonshi harya fice ma ganinta. maya na tashi kuwa taga surprises din da suka kawo mata ba karamin dadi kuwa taji ba. washe gari da safe daddy ne ya fara futa, bai tsaya ko’ina ba sai school, ba karamin buncike yayi ba daman gashi lawyer, saida yayi buncike sosai kafin ya dawo gida rai a bace jiki a mace. mummy dai ta kasa gane mashi don ya sauya gaba daya, daga jiya zuwa yau gashi yaqi fada mata komai. washe gari haka ya sake futa bai dawo ba sai dare koda ya dawo ma lokacin daya dawo mummy na night duty bata gidan dagashi sai maya. rabonda ya ganta tun ranar birthday dinta sai yau daya shiga bedroom din nata, a kwance ya taddata tana barci don haka ya soma tashinta, tashin duniya ya dunga mata taqi koda motsawa, wani abu ne yayi ringing a mind dinshi kamar ance ya dago kuwa ya kalli fuskanta, gefen bakinta wani farin abu kamar ta shafa powder, lokaci guda idanunshi sukayi jaa ya rasa me zaiyi ma gaba daya. bai taba tunani maya ta lalace sosai ba bai taba kawo cewa zaiga rana irin ta yau ba, yau yarshi ce ke shaye shaye kuma na muyagun kwayoyi da manyan muyagun substance, innalillahi wa inna iaihi rajin un, he was so shattaered and angry at the same time, blaming kansa kawai yakeyi da upbringing din daya bata, da sangartata da mummy tayi, sai ayau yake dana sanin dawowa kasar nan da sukayi don bai amfane su da komai ba, dondai promotion da suka samu duk a banza tunda gashi diyarsu tazo ta dauki halayen turawa wanda su a wajensu is a normal thing for an adult, su kuwa ya saba addinin musulinci kuma yar musulmai. futa kawai yayi daga dakin, haka ya kwana cikin baqin ciki da regrets. yau ta kasance weekends, mummy na gida haka zalika daddyn ma bai futa ba. zaune suke kan dining mummy na shirya daddy breakfast, shugowar maya cikin dining area din yasa suka kalleta gaba dayan su. cikin murna ta karaso inda mummy take tayi pecking din kumatunta ‘’good morning daddy and mummy’’ mummy ce kawai ta amsata kafin ta zauna. anatse sukayi breakfast suna gamawa daddy ya kalli maya, ‘’jeki haka kayanki’’ cikin murna ta dago tana kallon daddy, don daman ta shirga mashi karya kan cewa zasuje school camping, pecking dinshi tayi excitedly tace ‘’wow, daddy ka barni zanje?, thank thank daddy i love you’’ kasakarasa cin abuncin maya tayi tsabar farin ciki ta miqe zuwa bedroom dinta ta soma shirya kayanta a katon akwatinta, qananun kaya ta kwaso masu kyau da daukan hankali sai sauran abubuwan data zata buqata tana gamawa ta sauko da box din nata da laptop dinta da komai. a sitting room ta tadda daddy da mummy a zaune, mummy ma ba karamin dadi taji ba ganin daddy ya bar mayan zata je camping din. ‘’daddy na gama’’ kallonta ya soma yi sama da kasa kafin ya zura hannunshi cikin aljihunshi ya zaro gaba daya substance dinnan nata daya tsinta a jakarta da wanda ya samu a dakinta lokacin daya shiga ya dunga tashinta, ashe saida ya buncike ko’ina ya tsinto inda take boyesu. a kidime take kallon hannunshi dake nuna mata, wani irin dumm ta soma ji akanta, tabbas wannan usher din da taketa nema ne wanda saurayinta ya bata, dayan kuma kloe ce ta sammata, ina daddy ya samu wannan kenan. ‘’ga wannan kin manta dashi’’ kamar mara gaksia ta soma magana ‘’daddy ba nawa bane ba’’ ‘’oh kinsan menene kenan huh?’’ jikinta ne ya soma kyarma don daman shike fara haskota idan bata da gaskia, kallonsu mummy ta soma yi daya bayan daya ‘’daddy whats this? whats going on’’ afusace ya miqe ‘’ga ta nan ki tambayeta bahijja, gata nan let her speak for her self’’ tuni jikin maya ya dau kyarma, shikenan yau asirinta ya tonu, ‘’ka fada min meke faruwa mana’’ rai a bace ya soma magana ‘’bahijja diyarki, diyarki shaye shaye takeyi, shaye shayen ma na miyagun kwayoyi wanda ke cutarta young youth kamarta, it has been introduce to her by her friends da saurayinta, gata nan ta fada maki’’ tuni zufa ta wanke maya, ya akayi daddy yasan da wannan, ‘’maya kin cuci kanki, tarbiyar danayi maki kenan?, how could you?, why following this wrong path why? me kika nema kika rasa a duniyanan nan? shin kinsan wannan abun how many effect zai maki?, kinsan irin illar da yakeyi? how could you?, ‘’ ‘’stop daddy stop it, wani shaida kake dashi daya nuna cewa wannan din na mayan nan?, how could you even think about that?’’ ‘’bahijaaa!!!!!!!!!!! shin kina sauraron kanki kuwa? wallahi i’m beginning to blame all of this on you, laifinki ne, bakya sa ido kwata kwata akanta, a matsayinki na doctor? how can you not even tell diyarki na shaye shaye eh???what kind of a mother are you?, toh bari kiji, nine mahifin maya, na fiki iko da ita don haka tak, tak karna sake jin kin furta kiyi min shuru i will make decision on her’’ take mummy ta fashe da kuka, ganin maya ta tsugunna tana rokon daddyn ‘’daddy wallahi bazan sake ba, don allah kayi hakuri, wallahi wallahi bazan sakeba.’’ ‘’get up, dauki box dinki lets go’’ ya umarceta ‘’majeed ina zaka kaita’’ mummy ta fada tana hawaye, ko kallon inda take baiyi ba ya fuce,maya na biye dashi a baya da akwatinta mummy naji na gani ya futa da maya, nanybee dake tsaye a gefe itama hawaye takeyi sosai, tashin hankali kenan, keys mummy itama ta dauka tabi bayansu saidai sunyi mata nisa. saida ta gaji da zagaye ta dawo gida ta soma dialing number majeed, gaba daya hankalinta ya gama tashi hawaye kuwa ta kasa dainawa. bayan futarshi da awa daya sai gashi ya sake dawowa, mummy dake sama tanaji karar motarshi ta sauko kasa, anan sitting room ta taddashi ‘’majeed ina kakai min yata? haba majeed yau koda ace abunda yafi shaye shaye maya keyi bai kamat aka yanke hukunci cikin fushi ba daga baya kuma kazo kana dana sani? maya ma yata ce kuma inada iko akanta nima tunda nina tsugunna na haifeta’’ ganin duk ta burkice yasa shi janyo hannunta ya zauna da ita, lokaci guda kawai ta bashi tausayi baisan lokacin daya rungumeta ba saida ta ta soma dawowa daidai tukunna ya saketa yana mai kallonta. ‘’ki kwantar da hankalinki bahijja, ban yanke hukunci ba saida nayi dogon tunani, kina tunanin duk abunda tayi zan kaita inda zata cutu ne? haba bahijja, maya ita kadai ce diyarda allah ya bamu, kuma son da nake mata ne yasa na yanke wannan hukunci don ina ganin shi kadai zaisa ta natsu kuma ta fuskanshi alqibla’’ ‘’dan allah ina ka kaita tana ina’’ baiyi niyar fada mata ba amma ganin yanda ta damu yasa shi cewa ‘’nigeria’’ cikin sauri ta mike, ‘’haba majid nigeria? ita da wa? wazai kaita?’’ ‘’ita kadai, this is the first step to allowing her understanding her mistake’’ ‘’haba majeed, rabonmu da nigeria tun tana nigeria, bata san kowa ba achan, yanxu ya zaayi ace ka tura ta ita kadai,’’ ‘’bahijja calm down, na kira anne, zata sauka acahn’’ hankali bahijja idan yayi dubu ya sake tashi, ‘’anne?why? meysa zaka yanke hukunci ba tare da shawartata ba’’ ‘’saboda nine mijinki, kuma nike da iko daku, ina da damar yanke hukunci and thats final, maya is staying with anne, ta gama zaman nan har abada’’ ‘’toh wallahi nima kuwa bazan zauna ba, na gwammace nabar aikin nawa, i cant stay babu diyata’’ tana kaiwa nan ta fuce ta barshi nan zaune, daman hakan yakeso, lokaci guda kuma kawai sai yayi hamdala bai taba tunanin hakan ba, over how many years kenan yana convincing dinta akan su koma taqi, tunda suka dawo bai taba samun kwanciyar hankali ba daidai na kwana daya tunawa da shine sanadiyar samun matsala datayi da mahaifiyarta saboda ta dage sata aureshi, she choose him over her family shiyasa yake masifar sonta kamar ranshi baya iya dogon fushi da ita. *** Saudi!!! Taheel group of company. zaune suke gaba daya manya manyan company, babu wanda ya taba expecting wannan kiran gaggawan a daidai wannan lokacin, khaal na daga zaune sai sauran shareholders kowa na jiran karasowar hakimar don jin dalilin tarasu datayi. cikin mintina qalilan saigata ta shugp cikin hall din, walking majestically as always, mikewa sukayi gaba daya saida ta zauna kafin suma suka zauna, ba tare da wani bata lokaci ba soma magana ‘’na tara wannan urgent meeting dinne saboda zanyi announcement’’ kallon juna suka fara yi gaba daya khaal dai tunda ya zauna ya nade hannunshi yana sauraronta, haka zalika idanunshi na kanta, daman yayi exepecting haka saidai not soon enough. babban lawyer dake kula da harkokin compny ne ya shugo da wasu takardu a hannunshi yana zuwa ya tsaya sama wajen da suke yi announcement, copies din dake hannunshi ya miqa ma secretary din hidaya don ya rarabawa kowa, tun kafin ma lawyer ya soma magana mutanen wajen suka fara kallon juna khaal dai ko kallon paper baiyi ba. nan lawyer ya soma bayani, ‘’according to the commercial law of companny section 288 act 102,’it is stated that mai jinya ko mai rashin lafiya bazai taba zama director ba, cutar data kama ga cutar barin jiki, matsalar kwakwalwa dadai sauransu that will enable to work, with the provision and hardwork of the acting ceo i hereby pass special resolution to mrs hidaya taheel tajudeen to be the director of this comapany as she is the only next kin to the heir and the major shareholder with 60% share, duk wanda is against this will face the trade law’’ tsit kakeji ciki ya duri ruwa waenda basa shiri da ita tuna hankalinsu ya tashi. maido da dubana nayi ga khal, gaba daya yanayinshi ya sauya, the outcome of this ya gama bashi mamaki, yaushe hidaya ta zama the only person with hiegest share?, ina share din taj? that means ta dauke nashi kenan or what? don yasan shike da 40%, ita kuma 10% sauran 10% kuma na afiya ne da fadwa. ashe all the time she has already prepare her self kuma tazo ne lokacin da babu wanda yayi tsammanin hakan. lawyer ne ya sake tambayr ko akwai wanda yake against hakan, babu wanda yayi magana don haka a take aka bata mukamin wanda ta dade tana shiri akanshi. hidaya dake zaune ko kallon inda khaal yake batayi ba, daya bayan daya shareholder suka fara zuwa suna congratulating dinta, kowa da abunda yake ransa. saida aka gama ta wuce office hankali kwance babu abunda ya dameta, mutane kuwa dake aiki a company sai cecekuce akeyi. tana zaune a office saika khaal ya shugo a fusace, daman tasan zaizo don haka she’s ready for him, hannunshi na karkarwa ya soma pointing dinta ranshi a bace ‘’hidaya!!! ina shares din taj? so this was your plan? daman dalilin dayasa kika bayyanama duniya lalurar tajudeen kenan, to use that don ki samu abunda kikeso? why are you so heartless?, me yaron nan ya maki?, why?’’ wani irin murmushi tayi na rainin hankali, kafin ta sauya fuska kamar bata san me yake magana akaiba ta soma rage murya, ‘’with due respect sir, babu yanda za ayi mahaukaci ya kula da wannan company din, ni kuma nazan taba bari legacy dinmu ya tafi a banza ba, wannan hardwork din abuh ne da ummuh’’ ‘’sai akace maki taj din bazai samu sauqi ba? maysa zaki tureshi gefe? he’s the only heir to this company’’ idanunta lokaci guda sukayi jaa, ‘’no khal, i am the director now, i make my self the ceo so i be the heir, why cant you understand me eh? i’m doing dis for all of us and besides ni ce next of kin kuma i’m responsibie for taj, what ever decision i make babu wanda ya isa yayi questioning dina’’ ‘’karya ne hidaya, youre doing this for your self, kinayi ne don kanki kawai,saidai inason ki sani i will never allow this never, and let me remind you idan kin manta bari na tuna maki, ayanxu bake kadaice keda iko akanshi ba legally, his wife!!! matar da kika aura mashi, his first legal wife nada iko akanshi fiye dake so keep that in mind’’ yana kaiwa nan ya fuce rai a bace, yana futa ta miqe tsaye ta soma zubar da abubuwan dake kan table dinta, idanunta yayi jaa sosai, hankali a tashe, bata taba tunanin auren datayi ma taj zai zama threat a gareta ba, gaba daya tama manta da batun auren don daman tayi mashi auren ne saboda ta samu access to all his share, don bazaiyiwu tayi tranferring komai cikin sauki ba sai yana da aure wannan yasa ta yanke hukuncin tayi mashi aure’wanda hakan yazo a daidai lokacin da yayi rashin lafiya, wannan yasa ta umarci doctor ya bashi medication din dayafi karfin kwawalwarshi. shuru tayi tana nazari, yanxu duk wannan plans din datayi idan ta sake wannan auren zai iya ruguzawa ba tare da ta ankare ba, how could she be so stupid ta kasa yin auni da dogon nazari akan wannan? meysa tsohonnan ke shiga gabanta ne? why why!!!’this old man, karka fara abunda bazaka iya karashewa ba’, ni hidaya babu wanda ya isa yayi threatning dina’ ta fada aranta. nan take ta soma wayoyi daban daban ta dade tana waya kafin ta tattara komai nata ta futo daga office din. Bangaren sabeeha, hankalinta ya kwanta sosai, tunanin da takeyi ta rage saboda ganin yanda taj ke cikin farin ciki, duk inda yake tana wajen don jamid ya umarceta akan ta dunga sa ido sosai akan taj din, yanxu ya fara sakewa sosai kamar kowa, sannan ta gama karantar kowa na gidan, daga kan afiya zuwa ga fadwa, kwata kwata basa son taj, mugunta ma suke mashi musamman afiya dake mocking dinshi a sunan tana sonshi kiri kiri, wannan abu yana yima sabeeha zafi saidai bata isa tayi magana ba, don ko jamid shima baya ce masu komai hasali fuska yakeyi kamar baisan sunayi ba, kullum zasu sauko kasa ita da taj haka zaita zagaye gidan, inda yafi son zuwa kuwa garden ne, kullum suna chan yana zaune tana gefensa yana kallon garden din ga dawisu na yawo a wajen, yanxu haka ma suna daga zaune tana kallonshi ta doka uban tagumi shi kuwa babu abunda yake sai kallon ruwa dake futa daga pipe yana ambaliya a wajen, gaba daya ta shagala da kallonsa saida taji splash din ruwa a fuskanta wanda ya sata kallonshi, dariya ya soma yi mata ‘’hahah kalli ruwa a fuskan bibi na’’ itama dariya ta soma yi, tana shirin magana ya sake splashing dinta, take kuwa ta miqe ‘’ka bari zaka cjqani’’ bai saurareta ba ya daga pipe din gaba daya ya cigaba da watsa mata ruwan, gudu ta somayi yana binta yana dariya, itama dariyan ta somayi saida ya jigata jagab shima ya jiqa kanshi, bai kyaleta ba saita ruwan ya daina zuwa gaba daya kafin ya tsagaita. matsowa tayi inda yake tana goge fuskanta ta soma magana yi a shagwabe tace ‘’jibi yanda ka jiqa kanka, saikayi mura ko’’ ‘’mu tafi ciki ka sauya kaya’’ jin yayi shuru yasa ta dago ta kalleshi, idanunshi kuri ya tsaida waje daya akanta, bin idanun nashi tayi da kallo harzuwa inda yake kallo, bata gama processing abun da yake ma kallonba a jikinta sai jin hannushi tayi kan nipple dinta da yayi pointing out shatinsa ya futo sosai saboda jiqewar da kayanta yayi ga boobies dinnan sun fito muraran abunda take masifar jin kunya a jikinta, daman ita ba gwanar saka bra ba, batadashi ba sai wata half vest da take dashi kuma take amfani dashi. ‘’bibi what is this’’ ya sake tabo dayan nipple din nata, tsikar jikinta ne ya tashi lokaci guda, a razane ta kalli hannunshi nashi, mamaki ya gama cikata bata ma san lokacin data buge hannayenshi ba duka biyu ta juya tana furta allahumma ajirni fi musibati, wani irin tsoro ne ya durar mata don babu zato ba tsammani taji hannunshi, juyowa ya sakeyi yana mai son sake ganin koma menene a wajen tuni ta toshe da hannayeta biyu kamar ta nutse a kasa, abunda bai taba faruwa da ita ba ‘’bibi menene wannan?’’ ya sake tambayarta ita dai kauda idanunta tayi gefe ta kasa kallonshi balle ta bashi amsa, shafa kirjinshi ya soma’ ’oh!!! inada irinshi nima, but bibi meysa naki babba?’’ rasa abun cewa tayi kawai ta nufi hanyar barin wajen, yana ganin haka kuwa ya bi bayanta, afiya dake hangosu ta sama kasa gasgata abunda idanunta suka gane mata tayi. hidaya na dawowa afiya da fadwa suka je wajenta da rahoto,saida afiya ta zayyane mata komai, da mamaki hidaya ke kallon afiya jin abunda ta fada, ‘’wai ukty bakiyi tunanin waennan abubuwan bane kika aura mashi mace?, namiji ne fah? bakya tunanin wani abu ya….’’ afusace ta kalleta ‘’shut up, dont even think about that,’’ fadwa ce ta dora da, ‘’wai ukty kinqi fada mana komai, allow us to avenge with you’’ kallonsu tayi daya bayan daya kafin tace, ‘’kudai kawai kusa ido, this is just the begining’’ ‘’but ukty wannan yarinyar fa? meysa kika aura mashi ita kinsan asalinta ne? bakya tunanin wannan auren zai zama..?’’ afiya ta tambaya ‘’kina tunanin zata aura mashi mai asali ne,mteww? ‘fadwa ta fada nunfasawa hidaya tayi sounding unbotherded ‘’gobe zata bar gidan nan,’ Wannan litaffi paid book ne, gake buqata zai iya tuntuba na ta whatapp 08032542629 Rukayya umar. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels