An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [7/3, 7:58 PM] Rabi: [9:23PM, 7/2/2022] RSN: https://chat.whatsapp.com/E4JKvmLLlKFDlPYRLgp [9:24PM, 7/2/2022] RSN: BEBE'ARTH CIN AMANA Wattpad@Rashuna Godiya mai tarin yawa ga sarki Allah, wanda babu wani sarki sai shi, shi zai bani ikon fara rubuta wannan littafi, Allah ina rok'onka ka bani ikon rubuta shi dai-dai, ka kuma saka na kammalashi cikin k'oshin lafiya da amici, Allahuma Amin. Na sadaukar da wannan littafi ga mahaifina, don haka ina rok'on duk wanda ya karanta wannan littafi da yayi masa addu'ar Allah ya k'ara masa lafiya da nisan kwana mai amfani, yayi masa tukuici da gidan aljanna sakamakon babban JIGO da ya zamowa ahalinsa Allahuma amin. i love u so much Babanmu abin alfaharinmu Yaya jigon tafiyarmu, Allah bar mana kai cikin aminci. Ina sunkuyar da kaina gami da durk'usawa bisa kawo gaisuwa ga Iyayena na gari, ina adduar Allah ya k'aro d'aukaka da albarka,lafiya wadata, nutsuwa kwanciyar hankali, Amin. Ina yaba muku 'yan uwana, ina rok'on Allah ya k'aro mana d'aukaka da cigaba gami da albarka a rayuwarmu ta duniya da lahira amin. Ina ji da ku, ina al'fahari da ku Allah ya k'ara hada kanmu ya bar zumunci, amin. Falalu Shu'ayb Nababa Na'ima Shu'ayb Nababa Halifa Shu'ayb Nababa Fadila Shu'ayb Nababa Rabee'ah Shu'ayb Nababa Mardiyya Shu'ayb Nababa Abdul Rahaman S Nababa Murja Shu'ayb Nababa Allah kaiwa mahaifanmu tukuici da gidan Al'janna, sakamakon gina KATANGAR k'aunar dake tsakaninmu Allah kuma kar ka bawa wani damar rusa mana ita, Amin ya Allah. Babban tukuici ga yarana. Aseep,Aydha,Abrar,Aseefa. Allah ya kawo albarka cikin rayuwarku, ya k'aro mana zuri'a mai tarin albarka da wadata Amin. 1 ―――――― Da gudunta ta shigo falon, ta na k'walla kiran ‘’Dad‘’ tana nbaza ido taga ta ina zai fito, kacibis sukai a k'ofar da za ta sada ka da falonsa na biyu, jikinsa tai saurin fad'awa tana ruk'unk'umeshi yayin da shi kuma ya k'ara matseta a cikin jikinshi yana me lumshe idanuwansa· ‘’Nayi kewarka Dad‘’ Ta fad'a da siririyar muryarta mai taushi, yayin da shi kuma ya kuma shigar da ita jikinsa sosai kamar zai tsagata biyu kana yace. ‘’Nima nayi kewarki shalelena, amma meyasa ba ki gayan yau za ki dawo ba?‘’ ‘’Suprise zan baka that is why.‘’ Takai k'arshen maganar tana sakar masa kiss a wuya, wanda yai sanadiyar dakatawar maganar da yai nufin yi, jikinsa ya d'au d'umi sosai, yayin da ita kuma ta fara k'ok'arin barin jikinsa amman ta kasa saboda ba k'aramar matsa yayi mata ba· ‘’Dad‘’ Ta fad'a da k'arfi ganin tunaninsa ya tafi wani guri da ban, murmushi ya sakar mata yana me sauke lab'b'ansa kan lab'b'anta ya bata,hot kiss, murmushin itama ta sakar masa ya ja hannunta suka fita daga falon zuwa falo na biyu, dining area suka nufa yaja mata kujera ta zauna, da kansa ya zuba mata abincin ya kuma zauna ya ciyar da ita, wannan ya zame masa jiki ko kuma nace k'aida, muddun yana gari, itama tana gari da kansa zai zauna ya ciyar da ita, inkwa ba ya gida baza taci ba har sai ya dawo. Bayan gama cin abincin nata ya dubeta da kulawa yace· ‘’Yanzu kije ki wanka ki huta sai kizo ki sameni a d'aki mui magana·‘’ Mik'ewa tayi tana murmushi ta d'an durk'usa ta gefensa tai masa kiss a kumatu kana tace.‘’Thank you so much Dad.‘’ Ta juya ta bar falon, yayin da shi kuma yabi bayanta da mayun idanuwansa kamar ya cinyeta d'anya yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa· Idan tana tare da Dad d'inta dukkan wata damuwa mantata take, yanzunma hakanne ya faru da ita, tana barin sashensa damuwar da ke ranta game da mahaukaciyar nan ya dawo mata sabuwa, ta rasa me yasa matar ta shiga ranta ta zauna, tausayi ne ko kuwa son taimakonta ne? babu me bata wannan amsoshin kuma zucitarta ma ta gaza bata, wayo to zai bata? shi d'inma dai babu· Tana shiga d'akinta, wanda tsayawa gaya muku tsaruwar da yayi b'ata lokacine kawai ku k'iyasta, kayan jikinta ta shiga cirewa ta fad'a toilet ta dad'e sosai cikin ruwan d'umi kana tayo wankan ta fito had'e da d'auro alwala, don ta jiyo ana kiran sallah ta masallacin dake cikin gidan, don yanzu lokaci ya juya shida dai-dai ake kiran sallar magariba· Riga mara nauyi ta samu ta zira, ta saka zumbulelen hijabinta ta kalli gabas, yadda ta nutsu ku baza kuce NAFISA ce SHA LELEN Dad ba· Ba ita ta fito daga d'akinta ba sai da ta gabatar da sallar isha tukunna, d'akin Dad ta nufa suyi maganar da zasui don wani nishad'an d'an bacci take ji, idanuwanta har wani lumshewa suke, tare da Mom ta tarar da shi suna hira dukkaninsu murmushi suka sakar mata tare da bud'e hannuwansu alamun ta taho garesu, tsayawa tayi tana binsu da ido, tana tantance tsakanin Mom da Dad wa ya fi k'aunarta amsar da har yau ta gaza samunta a k'wak'walwarta idan tana wannan tunanin kanta,har ciwo yake, kusan had'a baki sukai wajen fad'in· ‘’Tawo mana·‘’ Tsakiyarsu taje ta zauna, ta kamo hannuwansu ta rik'e ta kwantar da kanta a kafad'ar Mom, yayin da Dad ya matso yana kai hannunsa wuyanta· ‘’Baki da lafiya ne shalele?‘’ ‘’UMUM bacci kawai nake ji·‘’ ‘’Yau ba fita kenan?‘’’ Kai kawai ta d'aga masa, Mom tace· ‘’Ai in kika fita sai kin fi jin dad'i, amman bacci da farar safiyar nan ai sai ki gaji da kwanciya kafin gari ya waye tashi maza muje na shirya ki·‘’ ‘’To ai magana zamui da Dad·‘’ ‘’Kwayi maganar idan Allah yai mana yawan rai zuwa gobe‘’ Takai k'arshen maganar tana mik'ar da,ita tsaye, yayin da ita kuma takai dubanta zuwa fuskar Dad ganin baice komai ba yasa ta bin Mom d'in· Hmmmmm masu karatu, idan zan shekara inai muku rantsuwar Nafisan d'azu ce da ta kalli gabas itace yanzu Mom ta shirya ba za ku yarda ba, cewa zakui wannan Rani Mukhraji ce ta cikin film d'in india don basu da maraba hatta k'wayar idonsu, da kyakkyawan murmushin da ke k'ara fito da zallar kyansu, wata arniyar rigace a jikinta black nd white, samanta ne black in me gashi-gashi sai walwali yake,da d'aukar ido k'asan kuma white shikumar kamar net yake, iya kacin rigar guiwarta, sai santala santalan k'afafuwanta dake ta shek'i, ba kwalliya a fuskarta sai jan jambaki kawai da ya k'ara k'awata lab'b'anta masu gwanin burgewa, girarta a gyare take sai ku rantse jagira tayi, sai dogayen eye leshers inta da suke a tsaitsaye gazar -gazar,gashin kanta kuwa yasha gyara sai shek'i yake tai mata parking insa a tsakiyar kanta da black nd white in riborm jelar sai reto take kasancewarsa ba mai cika tsayinma dai ba wani can ba, wata had'ad'd'iyar bandana ta saka black mai d'an fad'i don ta kusa rufe rabin kanta, stone d'in jikinta white ne yane ta walwali, a santalelen wuyanta siririyar sark'a ce ta diamond haka abin hannu da agogo da zobuna. A ko da yaushe ba ka rabata da su, kuma iri da ban da ban, plat in takalmi ta saka white, kasancewarta me tsayi ba ta fiya saka heals din takalma ba, sai dai idan tai ra'ayi· Har cikin mota ta rakata, taso taje gurin Dad Mom ta hana ta, rafar 'yan dubu ta bata, don tasan ba kud'i a hannunta sai A·T·M shiyasa ta bata don ta wutar da ita, cike da jin dad'in wannan soyayya da Mom take mata ta bar harabar gidan, yayin da Mom ta juyo idonta ya sauka akan Dad da ya saki labilen tagar da ya gama lek'e tsaki ta ja had'e da fad'n· ‘’ Jarababbe·‘’ ‘’Yanzu ita kad'ai ta tafi?‘’ ‘’To ni kake so naje na kaita?‘’ Itama ta jefo masa tambayar a zafafe, ganin hakan yasa shi kwantar da kai had'e da fad'in· ‘’Ba haka nake nufi ba, da kin bartan tun da tace bacci take ji, zuwa gobe drivern nata zai fara aiki, shine ma maganar da nake son muyi da ita don ni sam bana son fitarta ita kad'ai·‘’ ‘’Nifa ina jin tsoron d'aukar mata irin drivern da ta lissafa tana so, don kasan nak'i jinin saka ido cikin rayuwata·‘’ ‘’Haba-haba Jamila ni jakin ina ne zan d'auko abinda zai zame mini matsala, kema kin san sam bazai yuhu ba, amman kuma kinsan ya zamo mini farilla na cikawa Shalelena burinta, na samo mata drivermara muni, kuma me tsafta, amman bagidaje ne sam bashi da wayewa, kuma yana da tsagu a fuskarsa har da bille, bashi da asali don nayi bincike sosai a kansa kafin na daukeshi aiki, mahaukaciya ce mahaifiyarshi, kuma ta mutu, a wani gida yake gadi, to shine me gidan ya rasu iyalansa suka koma kano da zama, dalilin da yasa yake neman wani aikin kenan har aka kawosa gurina sai naga shi ya can canta da drivern Shalelena, kuma kan na d'aukesa sai da na kafa masa sharud'a· ‘’Auho, to har naji sanyi a raina, don da har na tsorata da zsbin FANAN kar muje mu d'ebo ruwan da zai dafa kawunanmu gaba d'aya‘’ Takai k'arshen maganar tana dariya yayin da Dad ya tayata kafin su shiga wata hirar ta da ban, wacce sam ba fahimta nake ba· # N·W·A [7/3, 8:01 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 2 A hankali take driving kasancewar akwai baccin sosai a cikin idanuwanta, a haka dai har ta isa harabar k'ayataccen Hotel, wanda sai d'an wane da wane ne ke shigarsa saboda mugun tsadarsa, parking in motarta tayi ta fito tai locking inta, ba ta d'auko komai ba sai rafar 'yan dubun da Mom ta bata, gefen hannunta na hagu ta bi wanda ya sadata da clube in da ya tara maza da mata, musulmai da k'abila yare da ban da ban, ko wanne yana harkar da ta kawo shi, tana shiga gurin aka saka ihu da sowa ana mata kirarin da aka saba, musamman da sun kwana biyu ba su ganta ba. ‘’'YAR DA DUNIYA KE YAYI, KI TAKA A SANNU SHALELEN DAD, SARAUNIYA AMARYA A GIDAN SAMEER‘’ Babu gefen wanda ta kalla, kujera kawai ta jaho ta na yatsina fuska, in da sabo dama sun saba da miskilancin nata, yayin da wasu kuma suke mugun jin haushinta, wasu kuma take birgesu ainun. Sameer ne ya shiga yi musu ruwan kud'i ko ta ina, saboda jin dad'in kalmarsu ta k'arshe, kana ya isa ga gimbiyar tasa da take ta cin magani, kujerar da ke facen inta ya jaho ya zauna, yana binta da wani shu'umin kallo me fito da zulamarsa a bayyane, siririn tsaki ta ja had'e da kautar da fiskarta gefe a dai-dai lokacin wetres in gurin ya ajiye mata tire a gabanta me d'auke da kwalbar giya da glass cup a kai, yayin da Sameer ya saki shu'umin murmushin da shi kad'ai ya san ma'anarsa, kana yayi saurin d'aukar botle in giyar yana k'ok'arin bud'ewa ya zuba mata zazzak'ar muryarta ta ratsa kunnuwansa. ‘’Kar ka wahalar da kanka yau ban jin shanta‘’ Tsayawa yayi yana kallonta rik'e da botle in a hannu, kallon cikin ido tai masa, had'e da d'an zaro idanuwanta ta juyasu gami da cewa. ‘’Yes‘’ Ta mik'e ta nufi filin casu, don jin an saka wak'ar da take mugun k'auna, ta shiga tik'ar rawa ba ji ba gani don FANAN gwana ce wajen iya rawa. Sameer kuwa wani mugun dafi ta zuba masa, wanda yayi sanadiyar sumansa na wucin gadi a zaune, har sai da sowa da tafin da ake mata ya dawo da shi tunaninsa da hanzari ya mik'e yana cin alwashin sai tazo tasha giyar nan da kanta, don yau so yake ta mallaka masa kanta, babu musu babu jayayya, yau yake so yai bankwana da k'ishiriwar da ta dad'e tana damun mak'oshinsa. ―― ‘’ Likita ya jikin nata?‘’ Sai da likitan ya fara zare gilashin idonsa kana ya kalli I.G Mustapha da ya jefo masa wannan tambayar kana yace. ‘’To Alhamdlillh za'a ce, amman muddun ba ta cire tunani da damuwa ba to ciwonta kullum jiya iyau zai kasance, kuma hakan zai haifar da babbar matsala, don yanzu haka ma jininta yai mugun hawa ba komi nake jiye mata ba sai ciwon shanyewar b'arin jiki, Allah dai ya kiyaye faruwar hakan.‘’ A sanyaye I.G Mustapha yace. ‘’Amin, insha Allahu zanyi k'ok'arin gurin ganin na kwantar mata da hankali, dama a kwana biyun nanne abin ya juyo mata, na gode likita.‘’ Daga haka ya bashi hannu sukai musabaha ya fita daga ofis in, d'akin da aka kwantar da ita ya nufa, dukkan familyn gidan suna cikin d'akin ganin shigowarsu yasa suka fara fita d'aya bayan d'aya, daga gefenta ya samu ya zauna had'e da kamo hannunta. ‘’Muddun kema kika bari na rasaki to tabbas banga amfanin cigaba da tawa rayuwarba don ko wa'adina bai cika ba to zan k'are rayuwata ne cikin rashin lafiya, ki taimakeni ki rage tunani da damuwa dan Allah Ummu Aymana.‘’ ‘’Ka sani kaima ina k'ok'arin fitar da komai daga raina, abinne ya juyo mini yake k'ok'arin fin k'arfina, amman insha Allah zan danneshi da k'arfin addu'a kaima ka tayani.‘’ ‘’Rana ba ta hudowa ta fad'i ba tare da na miki addu'a ba Ummu Aymana. Insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe, muna bin komai daki-daki ne don mutumin yana da mugun had'ari, kuma komai yana yinsa cike da wayo, idan ya fuskanci muna bibiyarsa yana iyai mana b'atan dabo, b'atan da baza mu sake ganinsa ba, kiga wuyar da muka sha kafin samuwar tan'ameme inda yake zaune ba, amman insha Allahu sai na kaiwa Hajja shi gabanta ya durk'usa ya nemi yafiyarta.‘’ ‘’Ba yafiyarsa muke buk'ata ba, ya gaya mana inda Fina da Faruoq suke kawai muke da buk'ata.‘’ ‘’Wannan ba matsala ba ce insha Allah kamar yau za kiga Finanki da Farouq a gabanki.‘’ Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace.‘’Allah yasa amin.‘’ Har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba, da ‘’Amin‘’ D'inma shima ya tayata yana jin dad'in yadda yasata cikin farin ciki amman k'asan zuciyarsa fal tarin damuwa da fargaba ne, yana fargabar zatonsa ya tabbata na Faruoq ba ya tare da shi Finan ma bai da tabbas d'in itace.. KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 200 kacal. 09037093702 #N.W.A [7/3, 9:18 PM] Rabi: [10:01PM, 7/3/2022] RSN: https://chat.whatsapp.com/E4JKvmLLlKFDlPYRLgpNaf [10:12PM, 7/3/2022] RSN: Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 3 Filin casun ya shiga ya ruk'o k'ugunta daga baya yana jujjuyata, tasan mutum aya ne zai mata irin hakan, kuma ta gargad'eshi yafi sau ba adadi, neman zare hannunsa daga jikinta take amman ta kasa saboda ba k'aramin rik'o ya mata ba, juyo da ita yayi, ya sak'alo k'ugunta da hannu d'aya, ya rik'e hannunta da d'aya yana jujjuyasu yana sakar mata murmushin mugunta, na babu yadda zaki da ni yarinya, janyota jikinsa yayi ya rungumeta yayin da gurin ya d'au tafi da sowa, in ba Sameer in ba wa zai gigin ko da tab'a farcen Shalelen Dad. Takaici da bak'in ciki ne yasa idanuwanta cika da ruwan hawaye har suka fara zuba, k'ok'arin had'e bakinsu yake Allah ya bata sa'ar gantsara masa cizo a wuya,ba shiri yai saurin sakinta yayin da ta nufi gurin da bottle in wine in yake ta b'incike murfin ta d'aga sama ta farai mata shan hauka, yana tsaye yana kallonta yana murmushi, bayan ya dawo daga azabar zafin cizon da ya tafi. Sai da ta sha kusan rabi kana ta cire kwalbar daga bakinta, ji tayi kanta ya fara wani irin yamutsawa kafin ta fara ganin bibbiyu ta tafi luuu za ta zube a k'asa da hanzari Sameer ya taho zai tarota yana me jin dad'i a ransa yau burinsa na shekaru me yawa zai cika, amman kaishhh kafin ya k'arasa gareta yaji ya gabza uban tuntub'e da wani abu, bai aune ba yajishi a zube a k'asa, hancinsa da bakinsa ya daku da k'asa, wata ratsatstsiyar azaba ce ta ratsa ta k'wak'walwarsa, abinka da namiji haka ya jure wannan azabar ya d'ago yaga a wani hali Fanan take amman wayam babu ita a gurin babu alamunta, da hanzari ya mik'e mutanen gurin suna masa sannu amman tambayarsu yake ‘’Ina Fanan‘’ Babu wanda yaga abinda ya faru da ita saboda duk hankalinsu yayi kan Sameer d'in da zai fad'i, wasu kuma suna can harkar gabansu, hakan yasa ko wanne yace bai ganta ba, da hanzari ya fice zuwa harabar motoci wayam nanma babu motarta, abinne yayi mugun d'aure masa kai. ‘’To ta ya , ta ya ya hakan ta faru?‘’ Wannan itace tambayar da ke kai kawo a kwanyarsa, gurin wetres d'in da ya kawo mata giyar ya nufa ya tuhumesa akan wacce ya bashi ya kai mata ya kawo matan? ya tabbatar masa lallai ita d'in ya kawo mata, kansa ne ya kuma d'aukar cagi muddun dai wannan giyar tasha, baza ta tab'a iya barin gurin ba bare har ta ja mota, wayarsa ya cira ya lalibo number Mom, kira kusan sau uku amma ba tai picking ba, tsaki kawai yake ja ransa duk a jagule, yana jin kishin ace wanine ya d'auki Fanan d'insa, inkwa hakan ya tabbata bazai tab'a k'yale ko waye ba. Duk da k'asan ransa yana son ya d'an rage zafi da ko wata 'yar babyn ce amman haka ya yanke shawarar zuwa gida ya duba Fanan, duk da bai wani yadda za ta iya mayar da kanta gida ba, yana shirin tayar da motar kiran wayar Mom ya shigo, da hanzari yayi picking, ya rigata magana. ‘’Fanan fa, ta dawo gida?‘’ ‘’Ta dawo, me ya faru?‘’ Ta bashi amsa had'e da jefo masa rambaya itama, wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana busar da iska mai zafi kafin yace. ‘’Shikenan kawai Mom sai da safe‘’ Saurin dakatar da shi tayi da cewa. ‘’Kar ka sake ka kashen waya,baka da hak'uru Sameer, ita gaggawa da kake gani gaba d'ayanta daga shaid'an take, abinda mallakinka za ta zama meye na damun kanka kuma?‘’ ‘’Allah ba abinda kike tunani bane Mom, zan dai shigo da safe zamui maganar.‘’ 'Kit ya kashe wayar ba tare da ya jira me za tace ba, ya bi bayan wata Beb da ta wuce tana karkad'a jiki duk ta d'aga masa hankali, dama abinka da wanda yake kusa... Washe gari har kusan shabiyu na rana tana bacci ba tasan inda kanta yake ba, Mom nd Dad kuma ba su bi ta kanta ba don sun san in ta shahu irin haka tana ma kaiwa fin haka tana bacci. A hankula take bud'e idanuwanta da take jin sun mata nauyi sosai kanta yayi mata wani irin dumm, ak'alla ta kai kusan minti ashirin a kwance ba tare da ta motsa ba, tana search in abinda ya faru da ita, ita dai tasan ta tafi luuu za ta fad'i kuma ba ta jita ta fad'in ba, to waye ya tareta, waye kuma ya kawo ta gida? Bata da me bata wannan amsoshin. ‘’Na shiga uku, kaddai Sameer ya samu biyan buk'atarsa a gurina?‘’ Wani b'ari na zuciyarta ya jefo mata wannan tambayar, yayin da d'aya b'arin zuciyar kuma ya kwantar mata hankali da amsar. ‘’Kai ba haka bane ai da zan ji wani sauyi kuma a jikina‘’ A hankula ta yunk'ura ta mik'e, wani k'amshi ne me dad'i ya dabaibaye hancinta, shinshina jikinta ta shiga yi da hannuwanta gaba d'aya k'amshin suke. ‘’ Ni 'yatsu ina na samo wannan k'amshin?‘’ Itace tambayar da ta jefowa kanta, bata da me bata amsar hakan yasa ta yanke shawarar tambayar me gadi wane ya dawo da ita gida, daga haka ta tashi gaba d'aya ta shige toilet, a gurguje tayo wanka da brush had'e da d'auro alwala, saboda tunawar da tayi ba tai sallar asuba ba, gashi tana da case d'in da zasu shiga tun k'arfe goma, gashi yanzu tayi lousing insa, dalilin da yasa kenan jiya tak'i shan wine, amman sai da wancen mayen ya b'ata mata rai har taje ta sha ba tare da ta sani ba. A nitse ta gabatar da sallarta kafin ta shirya a gaggauce ta fito, cikin shigarsu ta laiyoyi da tai masifar yi mata kyau, yarintarta ta kuma fitowa fili, da ace ba a Dalhi bane anan gida nigeria ne to tabbas wani cewa zai kayan kawai ta saka ba lauya bace, duk da anan d'inma akwai wa'yanda suke mamakinta,tana cikin sakawa phart d'inta key Kate tai saurin k'arasowa tana gaisheta had'e da mik'o mata doguwar farar takarda. ‘’Mom ce tace na baki, ta huce Germany kuma ba yau za ta dawo ba, kuma sannan Driver yana zaune cikin sabuwar motar da aka kawo miki jiya yana jiranki.‘’ Kate ta gaya mata duk cikin yaren nasara. ‘’Ok‘’ Fanan tace bayan ta amshi takardar, ta bata key d'in phart d'in nata, ba sai tai mata bayani ba ita ta san me za tayi, daga haka ta nufi gurin sabuwar motar dake d'aukar mata ido, fara k'al da ita sai shek'i take.... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 CIKIN DUNIYARMU complet 500 KATANGA complet 500 CIN AMANA complet 300 #N.W.A #Comment #Share [7/5, 8:09 AM] Rabi: BEBEARTH CIN AMANA Wattpad@Rashuna 4 Tun kan ta k'arasa jikin motar taji k'irjinta na bugawa da wani irin sauri sauri, wanda ba ta san dalilin jin hakan ba, kafin ta k'arasa aka bud'e mata k'ofar gidan baya, wanda alamu suka nuna kenan an hango tahowarta maimakon ta shiga gidan bayan sai ta bud'e gaba ta zauna, saboda ita hakan sam ba ya tsarinta, dalilin kenan da yasa ta zab'i irin drivern da take so, saboda duk yawancin drivern da Dad yake kawo mata k'azamai ne, idan ta zauna gidan gaba warin yai ta damunta, gasu kuma ba musulmai ba warin daud'a da warin kafirci sai ya had'u ya bada wani irin wari mai wahalar shak'a. Kamar yadda ba ta kalli gefen da yake ba, haka zalika shima ko gefenta bai kalla ba ya fara k'ok'arin tayar da motar dama oh reddy Abraham ya bud'e musu k'atoton gate in gidan, tana k'ok'arin tace masa ya tsaya za taiwa Abraham magana taga ya ja ya tsaya a dai dai gurin da Abraham d'in ke tsaye sai a lokacin ta juya ta kalleshi, cike da mamakin ta ya akai yasan abinda ke ranta, akan tsagun fuskarsa idonta ya sauka, tsaki ta ja a ranta tana fad'in ‘’Sam wannan tsagun bai kamaci kamilalliyar fuska irin wannan ba, mtsss yana d'an k'auye ko me ya kawo shi Dalhi oho?‘’ (Chai masu karatu da alamu dai Dad baiyi tunani irin na Fanan ba, ko da yake da fa lauya muke tafe, tunaninta da ban yake, ku muje zuwa dai. ) Jin tsakinta a karo na biyu yasa shi waigowa ya kalleta, saukar idanuwansa cikin nata ya haifar mata da wata muguwar fad'uwar gaba, had'e da jin sauyin yanayi a jikinta, juyar da fuskarta tayi gefe had'e da danne k'irjinta da take jin bugawarsa sosai sai a lokacin taji Abraham yana gaisheta cikin yaren Indiyanci, numfashi ta d'an ja had'e da amsa mishi kafin ta koro masa tambayar da ke damunta, itama cikin yaren da yai amfani da shi. ‘’Abraham nikwa nace jiya waye ya dawo da ni cikin dare?‘’ ‘’A gaskiya madam ba nace ba, don a jiyan ina toilet, fitowa nayi kawai naga motarki a parke, ni kaina abin ya mugun d'aure mun kai, ta yadda akai kika shigo cikin gidan bayan a rufe yake .‘’ Da hannu kawai tayi masa alamun yaje, ta riga ta saddak'ar aljanu ne kawai suka d'aukota daga ita har motarta suka kawota gida, kamar yarda suke mata a 'yan kwanakin nan su kawota k'ofar gida, sai gashi wannan har cikin gidan suka shiga da ita, cikin phart inta shima cikin bedroom inta aka kwantar da ita akan gado, inba aljanun ba waye ya isa ya shigo cikin gidansu wanda yake da mugun tsaro na kata'i. Muryarsa ce mai taushi ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. ‘’Ina mukai?‘’ ‘’Nayi tunanin shima ka sani‘’ Wani kily smile ya saki me d'an sauti, ko kad'an ba tayi gigin juyawa ta kalleshi ba sai dai ta ji sautin murmushin nasa. ‘’Shima idan kika bani damar hakan zan kaiki, sai dai kawai ba na buk'atar zargi ya shiga tsakaninmu daga fara aikina a yau.‘’ ‘’Mtssss ba na son doguwar magana, tana bani ciwon kai‘’ ‘’Ni kuma ba na son tsaki‘’ ‘’Ya kwa zamar maka dole ka koyi yadda ake sabo da shi, tunda har aiki za kai a k'ark'ashina domin shi d'abi'ata ne.‘’ Ta fad'i hakan a zafafe kafin kuma tace. ‘’Muje court in Shiva Raju, baice komai ba sai hanya da ya d'auka yana sakin b'oyayyen murmushi, kafin yace. ‘’Allah huci zuciyar shugabata, tun daga yau ma na fara koyon sabo da fitarsa daga bakinsa, ina kuma fatan hakan ya zamo mini hanyar da zan cireshi daga bakinki gaba d'aya, don ba d'abi'a ce me kyahu ba.‘’ Wani tsakin ta kuma ja wanda yafi dukkan wanda take sauti, kafin ta fara warware takaddar da Kate ta bata, don taga alamun in ta biyewa d'an k'auyen nan ciwon kai zai bata, kawai idan Dad ya dawo za ta sanar masa a canja mata shi.Ba komai takaddar ta k'unsa ba sai sanar mata da yake yayi tafiya zuwa American kuma zai d'auki tsawon kwanaki kafin ya dawo, zai iya kaiwa gab da bikinsu, ya nuna mata tsananin kewarta da zaiyi kafin ya dawo, don idan yayi tafiya ko waya ba sa yi har sai ya dawo, kuma ta kasa sanin dalilinsa har ila yau, har gara Mom suna waya amman sai dai Mom d'in ta kirata ita in ta kira ba za taje ba, kuma har yau ta kasa sanin dalilinsu na b'oyeta ainihin k'asar da zasu je, k'asa d'aya suke zuwa amman zasu gaya mata k'asa biyu mabambamta, wanda cikin biyu babu wacce suke zuwa, duk wata hanya da za ta bi ta san meyasa suke b'oye mata ta kasa sani, a hakan ma ba su san ta san ba ainihin inda suke zuwa suke gaya mata ba. Jin tsayuwarsa yasata numfasawa kafin ta fara yunk'urin fita daga motar cikin sanyin jiki, wata matashiyar yarinya ce da ke tsaye a bakin court in ba ta wuce shrkaru goma sha uku ba ta rugo da gudu ta rungumeta tana kuka har da ajiyar zuciya. ‘’Yi hak'uri yi hak'uri‘’ Shine abinda Fanan d'in ke jajjera mata tana shafa bayanta alamun rarrashi kafin muryar yarinyar ya ratsa kunnenta. ‘’Naji tsoro sosai Aunty, har ina da kacen shigowarki cikin lamarin rayuwata, wallahi nayi tunanin wani abine ya same ki, wanda zaisa nak'i yafewa kaina har abada.‘’ ‘’Babu abinda ya same ni Esha, gaya mini me ya faru?‘’ Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata kafin tace. ‘’Aunty an kori k'arar,kuma sun sanar mini wannan ce damata ta k'arshe tun da bani da lauya da shaidu an rufe case d'in gaba d'aya, yanzu haka ma shi mahaifinsa ya saka ya bar k'asar.‘’ Dafe kanta tayi had'e da ambaton. ‘’Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.‘’ Mahaifiyarta ce ke aiki anan court in, nan ne ya zame mata gida saboda rashin asali har ta haifi Esha wanda tun cikinta na k'arami mahaifinta ya rasu, anan court in Esha ta bud'i ido nan takewa kallon gidansu takewa kallon tushensu, tana da shekaru goma cif ciwo ya sark'e mahaifiyarta ta rasu, anan taci gaba da rayuwa ita kad'ai tana aikin da mahaifiyarta take, kasancewarta kyakkyawa ta ajin k'arshe, tun tana shekara sha uku komai na budurci ya gama bayyana a jikinta, hakanne yasa wani d'an me kud'i yai amfani da RASHIN GALIHUnta yayi mata fyad'e, kuma ya tsallaketa ya barta a bakin court in, ita ta d'auketa ta kaita asibiti, har sai da taji sauk'i ta bata labarin abinda ya faru, ita kuma tai mata alk'awarin k'watar mata 'Hak'k'inta, hakan yasa ta shigar da k'ararsa ga kotu, mahaifinsa kuma yai amfani da dukiyar da yake da ita, ya samu lauya tantiri da ya dinga d'ebo shaidun k'arya, yau itace damarsu ta k'arshe idan ba su kawo shaidu ba, hakan yasata jajircewa sai da ta had'o dukkan wata shaida, sai gashi ta b'ata damar da hannunta, ta karya alk'awarin da ta d'aukar mata, wannan shine karo na ba adadi da giya ke sanyawa ta fadi a case amman ba ta tab'a jin rad'ad'i da b'acin rai irin na yau ba, har ta ji giyar ma ta fita daga kanta sam, saboda case d'in a jiyan ta k'wauracewa shan giyar amman sai da Sameer yayi sanadiyar da ta sha, meyasa meyasa yai mata haka? Wani zugi da tiriri take ji a zuciyarta, ga kuma tausayin Easha da ya dabaibayeta, muryar Br Aditya ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. ‘’Dama na gaya miki bazan tab'a saken da za ki samu nasara a kaina ba, haka zalika wannan da zamu zauna yanzu ma mafi aala kawai ki juya gida.‘’ Yakai k'arshen maganar yana wata shegiyar dariya, wani shegen murmushi Fanan ta saki tana me kallon Easha tace. ‘’Ki kuma bani dama na inganta rayuwarki, wanda nake fatan hakan ya rage zugin abinda ke ranki za ki bini?‘’ ‘’Zan biki Aunty‘’ ‘’Yauwa shiga mota ki jirani.‘’ Kafin ta waiwaya tai masa kallon sama da k'asa taja tsaki ta nufi cikin kotun yabi bayanta yana sakin murmushin mugunta. Sun fafata sosai kafin Allah ya bata nasarar k'watowa bayin Allah marayu hak'k'insu da k'anin majaifinsu ke shirin danne musu, tare da mahaifiyarsu suka rungumeta suna godiya saboda ko sisinsu ba ta karb'a ba domin Allah ta tsaya musu har suka samu nasara, cike da takaici da muguwar tsana Br Aditya ke kallonta yana k'issima a ransa sai yaga bayanta... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira500kacal. 09037093702 CIKIN DUNIYARMU 500 KATANGA 500 CIN AMANA 300 #N.W.A #Comment #Share [7/6, 9:39 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 5 A gajiye ya k'arasa masaukinsa, kasancewar yau yasha yawo da Fanan gurare da dama akan wata shari'a da zasu gabatar nan da sati biyu, kayan jikinsa ya soma cirewa kafin ya fad'a toilet, jikin mirro naga ya tsaya yana d'ayo wani abu daga fuskarsa, abin mamaki sai naga tsagun fuskarsa yake d'ayewa, kenan babu tsagu a fuskarsa?(To dai babu me bamu wannan amsar masu karatu muci gaba dai da bin littafin.) Yana d'ayewa yana sakin murmushin diramarsu da Fanan, ya rasa me yasa idan yana tare da yarinyar yake matuk'ar jin nishad'i a zuciyarsa. ‘’Astagfirillah‘’ Ya furta kamar wanda ya aikata sab'o yana me saurin kawar da tunaninta daga zuciyarsa, ruwan wanka ya had'a ya shige ciki yana me lumshe idonsa, ya d'an jima sosai a ciki kafin yayo wankan ya fito ya shirya cikin kayan bacci farare k'al da su ya kwanta kan lallausan gadonsa yana mai jin nutsuwa a zuciyarsa, rubf da ciki yayi ya janyo laptop insa ya soma aiki a ciki, kafin wayar dake gefensa ta fara ruri tana neman agaji, sai da ya fara gyara zamansa sosai kana ya d'aga wayar yana bada dukkan hankalinsa a kai, bana jin me suke fad'e kawai dai naji yana ambaton ‘'Yes SIR’' Da dukkan alamu da ogansa yake magana, suna kammala wayar wani kiran ya shigo amman naga vidio call ne shi, murmushi ya saki kafin ya gyara kwanciyarsa zuwa rigingine ya d'aga wayar, a tare suka ajiye wata wawiyar ajiyar zuciya · Dak'una fuska tayi tana marairaice idanuwanta cikin nasa kafin tace · ‘’Tsakaninka da Allah yau sau nawa ka tunani?‘’ ‘’Woo ho Fadilaa, meyasa kike son k'ureni ne, kinsan ban iya k'arya ba, kuma in na gaya miki kizo kina jin ba dad'i kuma kinsan duk duniya ina kokawa da wanda zai sanyaki bak'in ciki, burina ko da yaushe farin ciki ya dauwama a rayuwarki·‘’ ‘’ Ni kaine kawai farin cikina, burina kaso ni ni kad'ai ka kula dani, ka riritani, komai kakeyi ya zamto tunanina yana mak'ale da kai, amman kayi hak'uri in na b'ata maka rai·‘’ ‘’ A'a baki b'atan rai ba, kawai dai kinsan bana son kidinga min irin tambayoyin nan, sanin kanki ne ban iya k'arya ba na gaya miki abinda ke raina na sosa ranki ni kuma bana son hakan, kinsan ina matuk'ar k'ok'ari gurin baki dukkan soyayyata‘’ ‘’ Na sani sosai, nima soyayyarka ce take sanya ni yin komai, fatana da burina bai wuce na kasance ni kad'ai a cikin zuciyarka ba da duniyarka gaba d'aya, bazan tab'a iya tarayya da wata ba akanka, ka rik'e mini wannan alk'awarin·‘’ ‘’Bazan gaji da gaya miki ban miki alk'awari ba, saboda ba nine da ikon juya zuciyata ba, amman zan iya danne dukkan abinda nake ji matuk'ar hakan zai sanyaki farin ciki, saboda ban damu da rayuwata ba, rayuwarki kawai na sanya a gaba, sunyi bacci ne?‘’ ‘’Uhmmm, ina jin Aseep ne kawai bai yi ba, suna d'akin Abba·‘’ ‘’Ok, da safe ma gaisa ki shafan kawunansu‘ ’’ ‘’Insha Allah‘’ ‘’To meye labari?‘’ ‘’Labarina yaushe zaka dawo?‘’ ‘’bazan ce ga rana ba, saboda bansan tsawon kwanakin da aikin zai d'aukemu ba, amman in na samu lokaci zanzo,na ganku ko a ranar ne na juyo·‘’ ‘’Tom shikenan, amman nayi kewarka sosai·‘’ ‘’Dan Allah da gaske kike? kalli cikin idona ki gaya mini‘’ Dariya tayi tana saka hannuwanta ta rufe fuskarta alamun taji kunya· ‘’Ashe to ba kewar tawa kikayi ba kenan’’ ‘’Allah nayi kewarka sosai da sosai, nai maka tanadi sosai‘’ ‘’Wayyo dad'i, nesa ba ta maganin kusa, amman za ki ganni soon insha Allah·‘’ ‘’To Allah yasa‘’ ‘'Amin‘’ Bayan kammala wayar tasu sosai Fadila ta zurfafa cikin tunani, tana mugun tsoron shigowar wata rayuwarsu hakan yasa take kaffa kaffa da masoyinta, Allah ya yita mace me mugun kishi, kuma bata da lafiyar zuciya, amman hakan bazai hana idan yaga wata yana so ba Abba ya shige masa gaba, duk da ta san da wuya Faruoq ya yadda ya aikata hakan a gareta kasancewarta me k'arancin lafiya, da kuma girma da kimar mahaifanta da yake gani, wanda har kwanan gobe tasan ba ta cikin zuciyar Faruoq illa soyayyar da yakewa mahaifanta da kuma soyayyar da yake mata ta yaya da k'anwarsa duk kwa k'ok'arinsa da yake na ganin ya cusa soyayyarta har ya bata k'arfin guiwar yarda da hakan· Hashim Abdussalam shi kad'ai mahaifiyarsa ta haifa tun bai fi shekara goma ba mahaifinsa ya rasu, bayan fitar mahaifiyarsa daga takaba ta tattara abinda ya bari ta nufi saudiya ta bar Hashim a hannun k'anin mahaifinsa wanda itama wane a gurinta sabili da auren zumunci sukayi· Ya rayu cikin gidan kanin mahaifinsa rayuwa me inganci ya taso da sana'a irin tasa wato sana'ar Kanikanci (Bakanike) har gyaran manyan motoci yake yi kuma suna kawo masa kud'i sosai har yaso yafi k'anin mahaifin nasa kud'i me amsa sunan mahaifin nasa a yanzu kuma surukinsa, don da 'yar wajensa Ruqayya suke soyayya har an saka musu rana jira ake,ya k'arasa gininsa asha biki, har zuwa wa nnan lokacin mahaifiyarshi ba ta zo ba sai dai waya da sukeyi in ya kirata· Alhmdlilllah ansha biki lafiya bayan kammala ginin nasa, amarya ta tare cikin kwanciyar hankali, zamansu suke lafiya lau babu tashin hankali, tafiya takai tafiya kusan shekaru bakwai babu haihuwa ba labarinta, gashi dukkaninsu Allah yayi su da mugun son yara kamar me, amman haka suka hak'ura suka mik'awa Allah lamuransa suna kai kukansu, duk da Rukayya taso ya k'ara aure yaki sam sabida baya cikin k'addararsa· Ana cikin haka kira ya samesu daga asibiti, mahaifinsu ne tsautsayi ya samesa ,shigar bulet ne a cinyarsa da kafad'arsa kuma sun raunata shi sosai, gefensa wani beautyn yarone yana ta tsanyara ihu, yaron ya d'auka ya bawa Ruqayya yace· ‘’Gashinan amanata ne, idan kuka cuce shi ban yafe muku ba duniya da lahira , ku kirashi da sunana Umar Faruoq·‘’ Iya abinda ya iya fad'a musu kenan ya amsa kiran mahaliccinsa ba tare da sun amayar da tambayoyin da ke cunkushe fal a zuciyoyinsu ba· Mutuwarsa ta rikirkitasu tazo musu da sabon yanayi wanda basu tab'a zatonsa ba, sunyi kuka kuka na sabo da soyayya da kuma kewa gashi kuma ya tafi ya barsu da amana, amanar da ta kusa jefa rayuwarsu gaba d'aya a halaka har sai da ta kai suka bi dare sukaiwa garinsu mahaifarsu 'yan uwansu danginsu, b'atan dabo, babu wanda yasan inda suke bare yaji labarinsu, mahaifiyarta basu fi shekara biyu da aure ba ta rasu, dama su biyu ta haifa ita da qanwarta da take bi mata kuma rana daya akai bikinsu ita Abuja aka kaita, sai waya sukayi ta sanar mata sun bar kano···· KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/7, 3:50 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 6 Kaduna,anan suka dasa sabuwar rayuwa, bayan ya nema musu hayar d'aki d'aya a wani kwarab'ab'b'an gida. Cikin Hashim da Ruqayya bazan iya tantance muku wanda yafi son Faruoq ba dukkaninsu sunai masa soyayya irin ta d'a da mahaifi, dukkan wani buri nasu suka d'auka suka azashi a kanshi,bazai wuce shekara d'aya da rabi ba, amman akwai shi da matuk'ar wayo ga farin jini, yana takawa da k'afafunsa magana ce dai sai gwaranci ba a jin me yake fada, sunsha matukar wuya kafin su samu ya saki jiki da su, don rigima sosai ya dingai musu. Abinci Ruqayya take siyarwa, saboda a lokacin Hashim bai samu garejin da zai dinga aiki ba, da wannan sana'ar tata suke samu su rufawa juna asiri, har Allah yasa ya samu wani gareji yake zuwa aiki can, cikin ikon Ubangiji sai ya fara samun alkhairi sosai har ya kama musu gida su kad'ai don Faruoq yafi sakewa sosai, duk da su yanzu ya sake da su sosai har bakinsa ya d'an fara bud'ewa Ruqayya yana kiranta da Oummi, wanda itace take koya masa idan yace Umma sai ta gyara masa tace ‘’Oummi‘’A haka har ya saba, Hashim kuma Abba daman da hakan ya bud'i baki. Soyayya da k'aunar da sukewa Farouq ta saka sam sun manta da ba sune suka haifeshi ba, don tuni sun dad'e da barin hakan sirri a tsakaninsu, sunyi alqawarin baza su tab'a bari yasan ba sune ainihin mahaifansa ba yanda suke jinsa a ransa suke ganin ko da mahaifansa na,ainihi sun bayyana baza su iya basu shi ba mutuwa kad'ai suka aminta za ta iya yi musu KATANGA a tsakani. Faruoq ya tashi da soyayyar Oummi da Abbansa, shima komai Oummi Abba kamar yadda suma komai Faruoq, duk wani samunsu a hidimta masa suke tafiya a haka har ya isa sakawa a makaranta, suka samu makaranta me kyau suka sanya shi Alhmdlillh kuma ya tashi da kwanya sosai. A haka rayuwa tayi ta gangarawa tana tafiya a hankula har Faruoq ya zama saurayi ya kammala makarantarsa ta secondary, ya kuma zab'i aikin police, Abba ne ya tsaya mishi da wannan aikin nasa na kanikanci har ya shiga makarantar 'yan sanda a lokacin ne kuma Oummi take ta fama da tsohon cikinta sunyi murna sosai lokacin da suka san da zaman cikin, Faruoq ma sai murna yake zaiyi qanwa, yaso sai da Oummi ta haihu kafin ya tafi makaranta amman har ya tafi Allah bai kawo hahuwar ba sai tafiyarsa da kwana biyu ta tashi da nak'uda, abinka da jikin girma kuma tayi doguwar nak'uda sosai sai da ta kwan biyu a asibiti ana shirin mata cs Allah ya kawo haihuwar ta haifi 'yarta mace, sunyi murna sosai har da 'yar uwarta Habiba, da tun fara nak'udarta tace a kira mata ita don tana ji a jikinta kamar baza ta tashi ba duk da itama Habiban ciki gareta na wata bakwai da yake haihuwa take tayi basa zuwa da rai, kusan shekararta biyar ba ta kuma samun ciki ba sai yanzu kuma sun qwallafa rai a kansa daga ita har mijin nata. Ana mayar da ita d'akin hutu ta fara wani azababban ciwon ciki tuni ta sanya aka kira mata Abba ta fara neman yafiyarsa, shi kuma yana bata baki akan ta daina fad'in haka insha Allah zai dainai mata ba mutuwa zatai ba, girgiza masa kai ta shiga yi cikin raunin murya tace. ‘’Ina ji a jikina bazan tashi ba, ka kira mini Habiba.‘’ ‘’Kar ki d'aga mata hankali kinsan ciki gareta itama.‘’ ‘’Na sani ka kira mini ita dan Allah.‘’ Tana rufe bakinta sai ga Habiban ta shigo kamar ta sani, murmushi ta saki tana mayar da kallonta kan Habiban kafin tace. ‘’Kiyi hak'uri zan barki da marayu don ina jin da k'yar zan tashi, ga amanar Faruoq nan da k'anwarsa, ina son bayan kin haihu kici gaba da shayar da ita na baki ita halak malak, ina so ta amsa sunan 'yarki bana son Faruoq yasan d'iyar da na haifa ce saboda hakanne zai bani damar cika burina na had'asu aure, ku sanar mishi 'yar da na haifa itama ta rasu, don Allah kumin alqawarin rufe wannan sirrin tsakaninmu mu uku.‘’ ‘’Insha Allahu Yaya ba mutuwa zaki ba da kanki zaki shayar da 'yarki .‘’ ‘’Ina ji a jikina bazan tashi ba Habiba ku dai kumin wannan alqawarin, bansan ya rayuwar Faruoq zatai ba idan yasan ba mune mahaifansa na gaskiya ba kuma ina son yarinyata ta kasance a k'ark'ashin inuwarsa wannan ce kawai hanyar da zata saka burina ya cika.‘’ Takai k'arshen maganar tana sauke idonta akan Abba da ke bitar kalamanta cikin k'wak'walwarsa, shima zaiso yarinyarsu ta kasance inuwa d'aya da Faruoq to amman ta ya ya?muddun suna son Faruoq yaci gaba da amsa sunan d'ansu na ainihi sai dai dole ta hanyar da Oummi ta kawo d'in, to amman kuma ba cewa akai Oummi mutuwar zatai ba, zafin ciwone kawai yasata yin wayannan maganganu, don su kwantar mata da hankali dukkaninsu sukai mata alqawarin da take so har ta saka Abba ya kira mata Faruoq da kanta ta sanar masa ta haihu yarinyar ba tazo da rai ba, kuka wiwi Faruoq ya nemi guri ya zauna yana yi ya qwallafa rai sosai akan k'anwar tasa, yaso zuwa a washe gari Abba yace yai zsmansa ba sai yazo ba.... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/12, 7:03 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 7 Tsakiyar dare ciwo ya dawowa Oummi sabo a wannan dare kuma ta amsa kiran mahaliccinta, Habiba ce kawai ta sani kuma ba ta sanarwa da Abba ba sai zuwa safiya, jarumta sosai Allah ya saka mishi da kansa yayi mata wanka zuwa k'arfe takwas na safe har an kaita makwancinta, ana tafiya Faruoq yana zuwa kwata kwata ba ya cikin hayyacinshi· Habiba kuwa dauriya kawai take yi amman ga tanan ne sam ba ta jin dadin jikinta mutuwar 'yar uwar tata ta kad'ata yadda ba kwa zato, tana cikin wannan halin kiran waya ya sameta Allah yayiwa mijinta rasuwa sakamakon had'arin mota, fad'uwa tayi a gurin a sume don k'wak'walwarta ta gaza d'aukan wayannan al'amuran, anyi ko wani dabaru a gida amman ba ta farfad'o ba hakan yasa aka nufi asibiti da ita, bincike na farko likitoci suka sanar da in dai ana son cikin jikinta da rai sai an mata cs an ciro shi ba b'ata lokaci Abba ya saka hannu aka shiga da ita· An ciro mata d'a namiji amman k'ank'antarsa ta sanya sai da aka sanya shi cikin kwalba· Jaririyar Oummi kuwa tana cikin asibitin an kwantar da ita saboda lura da akai itama ba ta da cikakkiyar lafiya kuma tana yawan suma· A b'angaren Farouq kuwa rufe kansa yayi a d'aki duniyar gaba d'aya tayi masa zafi, kalamanta yake tunowa sanda zai tafi makaranta ashe ganawar k'arshe sukai yaji muryarta ta k'arshe jiya a waya, yayi kuka sosai kuka na sabo kukan da ya tabbata Oummi ta tafi kenan baza ta dawo garesu daga k'arshe yayo auwala ya kalli gabas yana nemawa Oumminsa rahama gurin Ubangiji· A haka rayuwa ta nutsa taci gaba da tafiya zuk'ata babu dad'i sai dai godiya ga Uabangiji, Habiba ta fauwalawa Allah lamuranta yayin da ta fara shayar da tagwayan yaranta, ba ta b'oyewa dangin mijinta ba ta sanar musu macen yarinyar yayarta ce da ta rasu saboda rabon gado don har sun fara zancen kamar jira suke ya rasu· Macen sunanta Ruqayya suke mata lak'abi da Fadila namijin kuma Abubakar suna kiranshi da Fahad, sun taso kansu d'aya komai nasu iri d'aya Habiba ko kad'an ba ta bam bamta su, in ba su da suka sani ba babu me cewa ba 'yan biyun gaske bane· Bayan shekaru biyar Abba da Habiba (Oummu)suka dai daita kansu sukai aure suka tare a gidan da Abba ya gina anan Kaduna unguwar kawo, Fadila da Fahad suna cikin shekarunsu shida a duniya ajinsu d'aya a makaranta suna primary 3· Faruoq kuwa ya zama d'an sanda yana cikin shekarunsa 21 da d'an albashinsa suke samu su rufawa juna asiri sai kuma d'an abinda Abba ya samo, sosai yake bawa k'annensa kulawa komai ya samu Fadila da Fahad, suma sun shak'u da shi sosai musamman Fadila indai yana gida tana gurinsa a lokacin ne kuma Fadila take yawan suma aka kaita asibiti inda bincike ya nuna tana d'auke da ciwon Hyphatetic (HC)a cikin zuciya yake a hankali yake dakatar da bugawar zuciya idan ba'a ankara ba sai zuciya ta tsaya gaba d'aya kuma aikinsa da tsada bama ayi anan k'asar tamu sai k'asashen waje· Kowa ya jijjiga da jin ciwon da Fadila ke d'auke da shi gashi basu da ko kwatan kudin aikin ko da kwa sun sayar da dukkan abinda suka mallaka haka akai mata 'yan dabaru suka dawo gida zuciyoyi babu dad'i amman dukkaninsu sun d'ebo sabuwar kulawa sun d'ora akan Fadila, Abba ya saka ana yi mata rubutu tana sha cikin ikon Ubangiji kuma sai ta jima ba ta suma ba a haka rayuwa taci gaba da gangarawa da dadi babu dad'i· KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/15, 3:34 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 8 Fadeelah ta tashi da soyayyar Faruoq a zuciyarta musamman yadda yake bata kulawa duk abinda take so shine yake mata, tun ba ta san wata iriyar soyayya take masa ba har ta farga da yadda ta zurfafa cikin soyayyarsa yayin da ta mallaki hankalinta, ta riga da ta san ba ciki d'aya suke da Faruoq ba saboda yadda Oummu ke nuna mata saboda samun cikar burinsu kar ta rayu da soyayyarsa ta 'yan uwantaka tazo ta bijire musu daga baya. Fadeela fara ce k'al irin farin nan me shiga ido, akwai ta da kyau dai-dai misali, suna da shekaru goma sha shida suka kammala secondary Fahad har ya fara zuwa university ita kuma Abba yace sai dai tayi a d'akinta, to da yake dama karatun ba damunta yayi ba sai ba ta wani matsa ba, sam ta kasa saurarar wani saurayi da sunan soyayya, kuma abinda ta lura ma su Abba ba su bata damar hakan ba, ga soyayyar Faruoq tana ta cin zuciyarta wani zubin har ta hanata rintsawa, musamman yanzu da yayi mata nisa yau yana wancen k'asar gobe yana wancen saboda yanayin aikinsa, gashi bai san tana yi ba abinda ta lura ma shi har yanzu yanai mata kallon k'anwarsa da suka fito ciki d'aya. Faruoq H. Abdul Salam copy colour ne, doguwar fuskarsa na d'auke da tsayayyan hanci me kyahun gaske, idanuwansa ba wasu manya bane cen, amman kyawawa ne, don idonsa kad'ai abin kallo ne, suna d'auke da zara zaran eye lashers, ga cwt lab'b'ansa masu gwanin burgewa, babu saje ko gemu akan fuskarsa haka zalika ba ya barin suma kullum kansa a saisaye yake, dogon mutum ne tsayayye Allah yayi mishi suffar k'arfi gashi da k'wak'walwa da jajircewar aiki, saboda naicinsa da iya bincikensa ya samu nasarar shiga hukumar 'yan sanda ta duniya (police interpol) a yanzu yana da shekaru talatin da biyu a duniya, yanayin aikinshi yasha mishi kai ko zancen aure ba ya yi gani yake idan ya tsaya soyayya za ta cinye masa lokaci, yanzu ko zaman gida ba ya yi da wuyq yayi sati a gida, yanzu ma yana Oyo tare da yaransa amintattu Yousuf da Khalil da Sadiq. Abba da Oummu kuwa sunyi d'amarar tunkararsa da maganar auransa da Fadila tun da ta riga tayi candy jiransa kawai suke yi ya dawo asha biki. A daren kwa da ya dawo Abba ya tunkareshi da maganar had'asu auren da suke so suyi da Fadeela inda ya nuna shi sam bashi da burin yin auren zumunci soyayyar da yakewa Fadeela soyayya ce ta k'anwa da yayarsa da suka fito ciki d'aya shi a yanzu ma bai shirya aure ba ya rok'i Abba da kar ya bari Oummu ta ji saboda zaiji kunyarta ya karb'i abinda babu shi a zuciyarsa, hankalin Abba yayi k'ololuwa gurin tashi ko kad'an bai tab'a tunanin Faruoq ba son Fadila yake ba duba da yadda shak'uwa ke tsakaninsu tun da ya jima da karantar Fadilan na sonshi sai yayi tunanin soyayya suke yi, a ranar Abba raba dare yayi bai bacci ba tunani yayiwa zuciyarsa yawa yabi ya cunkushe, mene ne amfanin b'oyewa 'yarsa d'aya tilo da yayi shine mahaifinta na gaskiya idan har Faruoq bai karb'i buk'atarsa ba? Kenan burinsu shi da Oummi zai ruguje, ya rayuwar 'yarsa d'aya tilo za ta kasance idan ta san Faruoq ba sonta yake ba, gashi ba lafiyar zuciya ce da ita ba, don kwanaki Faruoq ya had'a kud'in da zaai mata aikin, amman sai likitocin suka ce zuciyarta ta tab'u, bai zama lallai in akai mata aikin ta rayu ba jin hakan yasa Abba yace a fasa aikin shine suka basu shawarar a kiyaye b'acin ranta, a dunga sanyata farin ciki ko da yaushe to za ta zauna cikin lafiya... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/16, 5:02 PM] Rabi: BEBEARTH https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v [11:51PM, 11/24/2021] Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata. CIN AMANA Wattpad@Rashuna 9 A b'angaren Faruoq ma yayi da kacen k'in amsar tayin Abba, saboda tunawar da yayi ya dad'e da karantar soyayyarsa cikin idanuwan Fadeela duk da k'ok'arinta na b'oye masa kuwa amman idanuwanta suna fallasata, baya da burin wani abu ya samu Fadila ta sanadiyarshi don haka zai aminta da aurenta saboda,gudun fad'awarsu matsala gaba d'aya. Washe gari da safe yaje ya samu Abba akan ya amince da auren Fadilan, amman don Allah kada Oummi da Fadilan su san da ya bijirewa aurenta, zaiyi k'ok'ari gurin sauya soyayyar da yake mata zuwa bigiren soyayyar aure saboda ba ya son abinda zai tab'a zuciyar Fadilan, amman kaish rashin sa'ar da akai Fadilan ta kawo kai d'akin Abban sanda suke maganar ta riga taji komai don haka tayi saurin juyawa ba ta bari sun ganta ba. Faruoq yana k'ok'ari gurin nunawa Fadeela soyayya duk da ba ya jinta a zuciyarsa har yanzu, soyayyar nan da yake mata ta k'anwarsa ba ta canja zani ba, Fadilan ma ba ta nuna masa ta san ya amince da aurenta ne saboda lalurarta ba, duk da in ta tuna hakan ta kan ji ba dad'i a ranta, a haka dai har aka sanya musu rana. Kwatsam a wata ranar Asabar Abba yana gida bai fita ba, haka ma Faruoq yana d'akinsa shima, hutawa yake ranar sai suka ji muryar wata dattijuwa tana sallama, Abba da suke hira da Oummu yace. ‘’Kamar muryar Umma nake ji.‘’ Kafin su amsa mata a tare suna lek'owa, Umman tasa ce kuwa a tsaye ta bisu da kallo gaba d'ayansu, Abbane ya fara cewa. ‘’Sannu da zuwa Umma, yaushe kika dawo daga saudiyar, dama kinsan gidan nan ne.‘’ Wani kallo ta jefeshi da shi kafin tace. ‘'Sannu tatacce mara kunya, yanzu Hashim rashin hankalin naku har yakai ku k'auracewa ahalinku kui musu b'atan dabo saboda tsintaccen muzuru, in Ruk'ayya ba ta da hankali ai kai ka fita hankali.‘’ Gaban Abbane ya yanke ya fad'i, kamo hannun Umman yayi yana k'asa da murya yace. ‘’Umma don Allah ki shiru, kizo mu shiga ciki ki huta.‘’ ‘’Nak'i nayi shirun.‘’Ta fad'a tana fisge hannunta daga nashi kafin ta kalli Oummu tace.‘’Kema Habiba kina tare da su kenan, dama kema ance sam ba'a jin labarinki tun da suka gudu, to ina Ruk'ayyan?‘’ Tana kai k'arshen maganarta Fahad da Fadila suka shigo d'auke da sallama a bakinsu, ganin iyayan nasu a tsakar gida da wata dattijuwa yasa su yin turus suka tsaya kafin idanunta su sauka a kansu ta kuma jefo musu tambayar. ‘’Su waye wa'yannan yaran?‘’ ‘’Umma kizo mu shiga ciki ki huta duk zakiji komai‘’ Cewar Abba yana dad'a kamo hannunta to a yanzu dai ba tayi mishi musu ba ta biyo bayanshi zuwa ciki. Faruoq tun da yaji kalmar TSINTACCEN MUZURU kalmar ta tsaya mishi a zuciya ya rasa me yasa, bacci yake son ya d'auke shi, kusan watansa guda ba ya k'asar sam bai samu hutu ba yau yake son ya samu amman tun da yaji wannan kalmar gabansa ke fad'uwa sam ya kasa samun sukuni innalillahi yake ta ambata a zuciyarsa. Bayan Umma taci abinci tayi sallar la'asar da aka fara kiraye kirayenta, Abba ma ya tafi masallaci shi da Faruoq, Umma ta kalli Oummu tace. ‘’Kusan watana biyu ko uku da dawowa, duk wani dangi in na zaga sai ace ba'a san inda kuke ba, hankalina in yayi dubu ya tashi, gashi kusan shekaru ashirin rabon da muyi waya da Hashim tun da layina ya samu matsala, gashi bai tab'a bani labarin kun yiwa danginku b'atan dabo ba,idan kikaji wahalar da na sha kafin a lalibon inda kuke sai kin rik'e baki.‘' ‘’Allah sarki, shima yana nan kullum sai yayi k'orafin ba ya samun ki a waya, kuma abinda yasa bai gaya miki ba ma kano ba saboda kince masa ba zaki dawo ba har sai ta Allah ta kasance da ke a can, duk magiyar da yake miki akan kizo ko da sau d'aya ne ki koma amman kikace ba za kizo ba, ya damu k'warai da gaske, bare da yaga an d'ebi wayannan shekaru masu tsayi ba tare da kunji muryoyin juna ba, sai ya dinga cewa to ko Umma ta rasu ne, har sai da Faruoq yayi mishi alk'awarin Hajji bana ko zaku had'u a can.‘’ ‘’Yo nima kawai ji nayi hankalina ya yo gida, ina son nazo naga d'ana d'aya tilo ko ya ajiye mini dozin d'in jikokin da yake yawan fad'i?‘’ Murmushi kawai Oummu tayi a dai dai lokacin Abba ya shigo, bayan da ya k'ik'k'iro aike ya aiki Faruoq saboda sam ba ya son sui wannan maganar da Umma yana cikin gidan don haka bai shigo ba sai da yaga tashin motar Faruoq d'in, Fahad da Fadila ma sai da Oummu ta aike su. Komai da ya faru daki-daki Abba ya zayyanewa Umma, mahaifiya ce ita babu damar ya b'oye mata, kuma ta riga ta san Faruoq d'in ba d'ansu ba ne. Umma kuwa salati take da sallallami tana ganin rashin hankalin Ruk'ayya da Hashim, musamman ma Hashim d'in tunda ita Ruqayya mace ce hankalinta ragagge ne. ‘’ Lallai kun cika mahaukata musamman kai Hashim, in banda rashin hankali yaushe zaku b'oye 'yar cikinku saboda ba kwa son tsintattcen muzuru ya san ba ku kuka haife shi don kawai kuna son ku hadasu a inuwar aure, tunda nake ban tab'a jin wannan d'anyan labarin ba a film ko gidan redio ko littafin hausa, amman sai gashi yau a cikin tsatsona, ba sahakka soyayyar da kukewa wannan tsintaccen tafi wacce kukewa 'yar cikinku, to bari kaji a yau d'in nan sai wannan tsintaccen yasan ba kune mahaifansa ba kuma babu ta yadda za'ai na had'a jini da wanda baisan daga inda ya fito ba ‘’ Gurfana Abba yayi a gabanta yana ta bata hak'uri akan tayi shiru don Allah, amman ina ko saurarasa ba tayi sai fad'a take kamar za ta ari baki. Da baya da baya Farouq bayan ya gama jin bayanin Abba ji yake yi anan jujjuya shi ko ta ina wani irin jiri yake yi, kalmomin Abbane suke yin k'ara bita a kwanyarsa da bin bango ya samu ya koma d'akinsa. Tun da yaga Abba ya aikeshi yasan akwai abinda yake son b'oye mishi, akwai wani abu da wannan matar tazo da shi da ya danganceshi Abba ba ya son ya sani shine abinda zuciyarsa ke gaya mishi don haka yayo rivers ya dawo, da ya san abinda kunnuwansa zasu jiye mishi kenan da bai dawo ba ya tafi aikensa sahunsa a likafa, amnan ina k'addara ta gifta dole ne ya san k'addarar dake zagaye da shi cikin rayuwarsa. Kansa ya rik'e da hannuwa biyu yana jin kamar zai rabe gida biyu, abinda yake ji cikin zuciyarsa so yake ya gaza yafi k'arfin kwanyarsa rintse idanuwansa yayi da suka kad'a sukai jajir yana ambato sunan Allah daga haka yaji hawaye ya fara zuba daga idanuwansa sai ya fara jin sauk'in abin daga zuciyarshi. Kuka yayi sosai kukan da ya jima baiyi kamarsa ba don tun mutuwar Oummi rabon da yayi irin wannan kukan, daga bisani ya karb'i k'addarar da Allah ya rubuta masa da hannu biyu don ba shi da jaa da hakan bazai zamo mutum me kokawa da k'addararsa ba haka zanen k'addararsa ya rubuta zai rayu tare da mahaifan da basu suka kawo shi duniya ba, amman sun masa abinda bai zama lallai wa'yanda suka kawo shi duniya sui masa ba, yama godewa Allah da ba garari yayi a duniya rayuwarshi ta gurb'ace gaba d'aya ba, baiyo shi da mahaifa ba amma ya bashi mahaifan da suke sonsa fiye da son da sukewa 'yarsu da suka kawo duniya, anya kuwa za'a samu tamkar Oummi da Abba kuwa? kai ina bazai yuhu ba, su d'in na daban ne mutane ne masu girma da kima a idanuwansa bashi da wasu wanda suka fiye mishi su a cikin duniyar nan, in da ya godewa Ubangiji da sai da ya karb'i auren Fadila hakan ya faru da bai karb'a ba da wani idon zai d'aga ya kalli Abba?Bashi da shi bashi da wani karsashi bare idon da zai d'aga ya kalli Abba, mafi aala kawai sai dai su nemeshi su rasa gaba d'aya... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/17, 8:48 AM] Rabi: BEBEARTH CIN AMANA Wattpad@Rashuna 10 Har Fadila da Fahad suka dawo Umma na fad'a da sababi, ta rungume Fadila tsam-tsam a jikinta tana jin k'aunarta mai girma a zuciya, (Dama ance abin cikin k'wan yafi k'wan dad'i) Bayan Umma ta gama zayyanawa Fadila komai, fadila ta d'ago idanuwanta da suka jik'e jagab da hawaye tana kallon Abba, wata iriyar soyayya da k'auna iyayanta sukewa Faruoq ko wata iriyar soyayya ce tabbas ta girmama girma mafi k'ololuwa, ta rayu tsawon shekarunta da mikin bata da mahaifi, ashe mahaifiya ce ba ta da ita, suna tare da mahaifinta cikin gida d'aya suna shak'ar iska d'aya, amman ya b'oye mata shi d'in mahaifinta ne ba shakka soyayyar da sukewa Faruoq ta ninka soyayyar da suke mata. Rarrafawa tayi ta isa gabansa kafin tace. ‘’Anya kuwa Abba kana sona?‘’ ‘’Waye zai haifi 'ya yace ba ya so Fadila?‘’ Ya fad'i haka kafin ya janyota ya rungumeta yaci gaba. ‘’Tsawon shekaru mukai muna buk'atar haihuwa ba mu samu ba sai a kanki, munyi farin ciki mun nuna godiya ga Ubangiji, tun kina ciki muke miki soyayyya har kika zo duniya soyayyar ta rikid'e ta koma zallar k'auna,munyi hakane ba don ba ma sonki ba sai don nuna soyayyarmu gareki, Faruoq rainanmu ne munsan bazai tab'a barinki ki wulak'anta ba ko da bayan ranmu, kuma idan ya san ba mune mahaifansa ba zai shiga damuwa damuwar kuma har ke za ta tab'a, babu wanda zai so ace ya tashi bai san asalinsa ba, abin da ciwo, wannan ciwon muke jiyewa Faruoq, kuma muna son muganku a cikin inuwq d'aya domin ko mun mutu muna da yak'inin ba mu barki a hannu mara inganci ba, Faruoq zai kula da ke fiye da kulawar da zaiwa kansa bazai tab'a CIN AMANARMU ba.‘’ ‘’Amman kunfi son Yaa Faruoq a kaina Abba?‘’ ‘’Dukkaninku muna sonku, shi soyayyar da muke masa mai had'e da tausayi da tausayawa ce.‘’ A dai-dai nan Faruoq ya shigo d'akin, idanun nan nasa sunyi jahur na ban mamaki, kallo d'aya Abba yayi masa ya sunkuyar da kansa, bashi da wata tambaya tun da ga amsar nan ya karanceta cikin idanuwansa da suka birkice, wani mugun tausayi da k'arin k'aunarsa yaji ya shigesa, shi kuwa Faruoq kallon Abba yake yana jin wata sabuwar soyayya mai silki da zallar k'aunarsa na kuma huda k'ofofin zuciyarsa suna shiga, ga wani girma da kimarsa da ke kuma shigarsa, da me zai biya wa'yanna bayin Allahn? Bashi da shi har k'arshen numfashi sai da zai rik'e musu 'yarsu tamkar zinare, bazai tab'a barinta tai kuka da idanunta ba zai kuma kiyaye b'acin ranta, zai rik'eta rik'o mai inganci, bai san so ba bai san ya yake ba, bai tab'a d'and'anasa ba amman zai k'ok'arin d'and'anasa a kanta ya kuma kulle zuciyarsa ga kowa don Fadila aka halicce shi don kuma ita kad'ai zai rayu har k'arshen numfashi wannan alk'awari ne ya d'aukarwa kansa. (To masu karatu ga Farouq dai ya d'au alk'awari, shin zai cika wannan alk'awarin? Ya manta mutum bashi da damar tsara rayuwarsa, rayuwa gaba d'aya tana hannun wanda ya haliccemu ne haka zalika zuciya baka da ikon sarrafata indai akan abinda take so ne, ku muje zuwa dai.) ‘’Abba bani da bakin godiya gareku, bani kuma da abinda zan biyaku, Allah ne kad'ai ya san da me zai biyaku, ina rok'on kaci gaba da amsa sunanka na mahaifina domin bazan tab'a iya kankare hakan daga zuciyata ba, na gwada sau shurin masaki na gaza d'aukar hakan cikin kwanya da zuciyata.‘’ Rungumeshi Abba yayi kafin yace. ‘’Har bayan mutuwata kai d'anane Faruoq, sunanka bazai tab'a canjawa ba, ko da mahaifanka sun bayyana, domin ina ji a jikina zasu bayyana lokacine bai yi ba, kai d'in d'an BABBAN GIDA ne Faruoq k'addara ce kawai ta kawoka nan.‘’ Umma ji tayi jikinta yayi sanyi, duk makaman da ta d'iba da duk ta watsar da su ta amshi Faruoq a matsayin jikanta shi ma ya amsheta a matsayin kakarsa bai duba abinda ya faru a baya ba yayi mata uzuri domin hakan yana cikin k'addararsa zai san kansa bai zo a cikin masu asali ba haka zanen k'addararsa yake yana kuma godiya ga Ubangiji da ya bashi tsarkakan ahali cikin duniya. Ansha bikin Fadila da Faruoq cikin amincin Ubangiji, Abba yana mai godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana, ko da mutuwa ta riskeshi a yanzu zai kwanta a kabarinsa cike da kwanciyar hankali domin bai bar tilon 'yarsa a hannun da zata wulak'anta ba. Watansu tara cif Fadila ta haifi d'anta namiji wanda yaci sunan Abba suna kiransa da Aseef, shekara d'aya tsira ta kuma haihuwar namiji wanda yaci sunan Shugaban Faruoq d'in a gurin aiki I.G Mustapha, saboda k'auna da soyayyar da shugaban nasa yake mishi (Duk wani mataki da faruoq din ya taka a gurin aiki to da taimakon IG Mustapha ne, wanda gaskiya da rik'on amana da k'warewar aikinsa ne suka siya mishi soyayya gurin shugaban nasa har yake jinsa tamkar d'an da ya haifa. )suna kiransa da Abrar, kaf wanda ke zaune k'ark'ashin inuwa d'aya sa IG Mustapha sai da yazo barka kuma kowa da abin arzik'insa a hannu, Hajja ce kawai ba ta samu zuwa ba saboda rashin lafiyar da take fama da ita sai aka kai mata shi har gida, gaba d'aya ahalin IG sun d'ora soyayyarsu akan Abrar har ma Aseef d'in basu bari a baya ba, ji sukeyi tamkar jininsu ne ya haifesu, wanda hakan ya haifar da k'arfaffan zumunci tsakaninsu. Sai da Abrar ya shekara biyu sannan ta kuma haihuwar mace wacce taci sunan Oummi suna kiranta da Aydha, yanzu shekararta d'aya da haihuwa amman tana tafiyarta, shekarar Fadila yanzu a duniya ashirin cif-cif Faruoq yana da talatin da shida, har zuwa yanzu soyayyar da Faruoq yake mata ba ta canja zani ba, ita kuwa ba ta da wani buri da ya wuce taga zallar soyayya da k'aunarta cikin k'wayar idon mijinta, ta riga ta,mutu, mutuwa sosai cikin zallar k'aunar mijinta tana tsoron wata ta kutso cikin rayuwarsu musamman yanzu da Faruoq din ya kuma gogewa kwarjini da cikar haibarsa suka kuma bayyana, kud'i sun zauna masa sosai don tun daga kan Abba zuwa kansu ba wanda baije hajji da umara ba duk k'ark'ashin dukiyar Faruoq d'in, a haka ma wai don ya tsayar da zuciyarsa akan halal insa bai tab'a amsar cin hanci da rashawa ba don sam baiga amfanin haram ba face azaba da zaka d'and'ana gurin Ubangiji. Sam ba a son ranta ya tafi Dalhi gudanar da aikin da ya tafi yi can ba, haka kawai sam taji ba ta aminta da tafiyarsa ba amman bata da dama da ikon hanashi, aiki ne da Shugabansa ya tura shi saboda ya aminta da shi, sai dai ita tana jin kamar acan ne zuciyarsa zata bud'e wanda ba ta fatan hakan za taso su k'arashe rayuwarsu a hakan, Faruoq yana da girma da kima kuma ubane, Yaya,d'an uwa, miji, masoyi a gareta wanda ita matsayin da take hanga cikin idanuwansa baza su wuce, k'anwa, mata, sai kuma girma da kimarta su kad'ai tasan matsayin da take da su a gareshi, shekararsu hud'u da aure bai taba furta mata kalmar ina sonki ba ko kalamai na shauki da soyayya, wanda zasu fito ta aminta daga k'asan zuciyarsa suka fito, idan tayi k'orafi yakan ce. ‘’Ita soyayya ka aikatar da ita a zahirance yafi ka zauna kana wa'yanna shirmen.‘’ Tana buk'atar jin wannan sautin tana kuma mararinsa, shin yaushene za ta samu? ‘’ Fadeela, wani irin zurfaffan tunani kikeyi hakane?‘’ Muryar Oummi ce had'e da jijjigata suka dawo da ita daga dogon tunananin da ta tafi, baza ta iya cewa ga tsawon awoyi nawa ta d'iba tana wannan tunanin ba, wanda ya makantar da ita ya kuma kurmantar da ita, don Aydha ce a hannun Oummi tana ta kuka, Oummin na ta k'wala mata kira ba ta san ana yi ba, sai da ta kai ga jijjigata sannan ta farga, karb'ar Aydha tayi cikin sanyin jiki ta fara jijjigata kafin tayi shiru ta fara shayar da ita har kuma lokacin Oummi na tsaye a kanta tana karantarta had'e da damuwar da ke kan fuskarta kafin ta kira sunanta. ‘’ Fadila‘’ ‘'Na'am Oummi’' Ta amsa a sanyaye. ‘’Ina so ki lalubo hankali da tunaninki a duk inda suka tafi, shi namiji da kike ganinsa mijin mace hud'u ne, kuma bashi da wani dama da iko na tsara dukkan rayuwarsa yadda zata kasance sai yadda Ubangiji ya yardar masa, zakiga mutum yana da burin k'ara aure amman idan Ubangiji bai yardar masa ba da guda d'ayan nan zai koma ga mahaliccinsa wani kuma yana da burin kuma Allah sai ya nufesa da k'arawa, wani kuma sam bashi da buri ko sha'awar k'ara aure amman idan hakan yana cikin k'addararsa bai isa ya gujewa hakan ba, don haka ina shawartarki da ki dawo hankalinki ki mik'awa Allah lamuranki, duk yadda yaso yayi rayuwarku ba ku isa ku canja hakan ba, don haka zaifi ki sanyawa zuciyarki salama, musamman ke da ba lafiyar zuciya ce da ke ba, ki rok'i Ubangiji Allah yasa babu kishiya cikin k'addararki, in kuma akwai Allah ya baki ta kirki wacce ba za tazo ta ruguza muku rayuwa ba hakan yafi da ki zauna kina k'untatawa zuciyarki.‘’ Tana kawowa nan ta juya ta fice, ta barta ta samu sararin yin tunani akan shawararta, ta kwa yi donkwa wani sanyi taji sosai zuciyarta tana yi, tana kuma yarda da amanna da shawarwarin da Oummi ta bata. .... KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai. Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/19, 1:09 PM] Rabi: BEBE'ARTH CIN AMANA ®️NAGARTA WRI.. ASOCIATION Wattpad@Rashuna 11 Zaune yake cikin mota yana zaman jiranta ta fito, K'arfe bakwai tace masa yazo saboda akwai shari'ar da zasu gudanar k'arfe tara na safe to tana son shiga kafin lokacin ya cika saboda akwai abubuwan da za ta k'arasa. Suit ne a jikinta bak'ak'e, sai shek'i suke da walwali sun matukar amsarta sun zauna a jikinta sun fito mata da k'uruciyarta da zallar kyahunta, d'an k'aramin farin hijabin da ta saka shine ya bam-bamta ta da 'yan k'asar bacin haka rantsuwa zakai kace ba asalin Bahaushiya bace wanda ita kanta yaune taga damar saka hijabin kuma shima Faruoq ne yayi mata magana wanda har ya kusa kaisu ga yin fad'a amman haka kawai kuma sai taji tana son bin umarninsa bacin haka tafi son ta saka bandana wacce za ta rufe mata rabin gashinta a haka za ta fita duk inda taga dama duk kuma inda take so saboda aladar k'asar ta riga tabi jikinta,kasancewar anan ta tashi ta bud'i idanuwanta amman duk da haka ba ta yin shigar nuna tsuraici shima kuma taimakon Mama Ma'u ne saboda idan ta Dad da Mom ne ko da daga ita sai pb ne za ta fita babu me hanata bare ya tsawatar mata, da ba dan Mama ma'u ba ma haka za ta tashi ba ta san musulma ce ita ko kafira ba. Kamar ko yaushe tana tunkarar motar zuciyarta na bugawa da sauri da sauri har Easha ta rigata isa jikin motar ta bud'e gidan baya ta shiga, ta kusa isa gab da motar Sameer yasha gabanta yana k'ureta da mayun idanuwansa, ko d'aga kai ta kallesa ba tayi ba saboda ta riga ta san waye zai mata hakan, kuma k'amshin turarensa ya sanar da ita, kaucewa ta fara k'ok'arin yi ya kuma tare hanya kafin yace. ‘’Kwana biyu me ya hanaki zuwa cluve, kuma in na kira wauanki ba kya ansawa, in nazo ki hanani ganinki?‘’ ‘’Saboda duk bana ra'ayi.‘’ Ta bashi amsa kanta tsaye, wani shu'umin murmushi ya saki me sauti kafin yace. ‘’Lokacinki ne yarinya, kiyimin duk abinda kikaga dama nima lokacina ya kusa farawa daga ranar da kika zama mallakina, kuma ina miki albishirin Mom na dawowa za'a tsayar da ranar biki, cire wannan kidahumin abun duk ya ragewa Baby face inki kyau.‘’ Yakai k'arshen maganar yana kawo hannu zai fusge hijabin tayi saurin ja baya tana doka masa harara kafin tace. ‘’Sameer na gaya maka ka fita hanyata, ina da abu me muhimmanci ka zauna kana b'ata mini lokaci.‘’ ‘’Hanya da ni da ke Fanan ai ta gama had'ewa babu zancen na fita daga ciki, idan sauri kike ki shige muje na kaiki a motata.‘’ Kai ta d'aga ta kalli Faruoq yayi mata nuni da ido alamun taje, girgiza mishi kai tayi k'walla na son zubowa daga idonta, da harshen hausa wanda ya san Sameer d'in ba ji yake ba yace. ‘’Ki bishi kuje, babu abinda zai faru insha Allah, zamu sameku a can.‘’ Wani wawan tsaki sameer ya saki kana yace. ‘’Sai wannan kidahumin drivern ya baki umarni zaki bini?‘’ ‘’Ya fiye mini kai ai, saboda shi bai tab'a k'ok'arin keta mini haddi kamar yadda kake k'ok'arin yimin ba.‘’ Wani tsakin ya kuma ja had'e da zubar da miyau. ‘’Amman kin cuceni da kikace wancan jakin abin ya fini, dubi fa kansa da bak'ar fuskarsa ga wani uban tsagu a fuska, amman wallahi kin cuceni Fanan.‘’ Murmushi ta saki ganin ta saka ransa ya b'aci, Sameer kyakkyawa ne na bugawa a jarida, wacce duk wacce mace idan ta sameshi tayi damkatakar a fannin kyau amman babu kyahun zuciya, ko kusa baza ki hada kyahunsa da na Faruoq ba duk da shima Faruoq d'in tsagun fuskarsa ne suka bata kyahun nasa sai sal-sal in kansa da bak'in fuskarsa sai dai kuma idanuwansa masu mugun kyau ne wanda in har ya d'ora idonsa kanta sai taji wani bak'on yanayi yana shigarta idan kwa tsoautsayi yasa idonsu ya had'u guri guda sai taji kamar wani dafine me girma ke fitowa daga idonsa yana shiga cikin nata idanuwan. Inda yayi parking in motarsa ta nufa ba tare da tace masa komai ba, shikwa sai da ya zabgawa Faruoq wata muguwar harara kamar shi ya masa laifin, kafin yabi bayan Fanan in. Suna fita Faruoq ya mara musu baya suna tafe suna hira da Easha wacce yacewa ta dawo gidan gaba, sam ban san wata hira suke ba na kasa jiyo muku, sai da ya fara ajiyeta a schl in da ta fara zuwa, shekara uku za tayi tana zuwa kafin ta zana takardar gama secondar, duk abinda ya danganci tun daga Nursery zuwa Secondary a cikin shekaru ukun nan za ta iya komai indai ta mayar da hankali akai sosai. Sameer yana ajiyeta ya juya akan zaije ya dawo kafin su fito daga shari'ar, shikwa Faruoq fitowa yayi daga motar ya hau samanta ya zauna yana bin duk mutanen da ke zirga-zirga a gurin cike da nazari. Bayan shud'ewar awoyi biyar zuwa shida ta fito daga cikin kotun murmushi d'auke akan fuskarta saboda nasarar da take jiyo k'amshin samunta, duk da yanzun ma alk'alin ya kuma d'aga k'arar zuwa sati biyu masu zuwa, taga alamun shima siyeshi ake k'ok'arin yi amman Allah ya fishi da ikon Ubangiji sune zasui nasara akansu, sam ba ta ji k'walla mata kiran da Faruoq yake ba akan ta kauce sakamakon bulet in da aka harbo yayo saitinta da gudu ya k'araso gabanta yana k'ok'arin janyeta bulet in ya sauka a kafad'arsa, yayin da police in gurin suka ankara suka sakarwa wanda yayo harbin harsashi shi kuma ya fara k'ok'arin tserewa. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share [7/20, 8:22 AM] Rabi: 12 Rintse idanuwansa yayi yana jin yadda bulet in ke shigewa jikinsa, kan kice meye rigarsa duk ta b'aci da jini, Fanan kuwa duk ta gigice sai faman sannu take masa. Itace taja motar suka nufi hospital gaba d'ayanta a firgice take Allah ne kawai ya kaisu lafiya yaso ma ya karb'i tuk'in ta hana shi, a ranta kuwa sai mamakin dauriyarsa da k'arfin halinsa take, da itace bulet ya ratsa ta jikinta ta tabbata sai dai a d'auketa a sume, gashi shi kuma har fad'i yake a bashi yayi driving. A gurin cire bulet inma nan taga ikon Allah, don k'in fita tayi akayi a gabanta, rintse idanuwansa kawai yayi ba tare da yace uffan ba ko kuma razana ba, ta tabbata da itace indai idonta biyu za'a cire mata to sai an samo majiya k'arfi sun rik'eta 'yan asibitin kuwa sai dai dukkaninsu su toshe kunnuwansu don wallahi sai ta cika asibitin da ihunta da karaginta, can k'asan zuciyarta taji ta watso mata tambayar. Anya kuwa wannan karanne bulet ya fara ratsa jikinsa kuwa? Gaskiya dai banjin hakan, wata zuciyar ta bata wannan amsar. Kallo aya tayi mishi ba ta kara marmarin sake kallonsa ba, saboda babu riga a jikinsa kuma k'irarsa tayi mugun firgitata wani irin mirdaddan jiki ne da shi, wanda da alamu akwai suffar k'arfi a tattare da shi, rik'o aya yayiwa mutum to tabbas sai yaji iji a jikinsa. Mamakin yadda taga fatarsa tana wani irin glowing sam ba ta nuna yana cikin yanayi na wahala ba har da zaizo yana aikin driving inta da alamu dai Dad bai mishi wani cikakken kallo ba kafin ya daukeshi aiki ba,don tabbas ta fara zargin ba aiki ne ya kawo Faruoq cikin rayuwarsu ba akwai abinda yazo koma menene dai tayi alkawarin sanya mishi idanu har sai ta binciko. Rigar tasa dai ya mayar saboda shi kansa ba zai so fita a haka ba, dad'in ves kenan da ya sakata s ciki bashi da wata damuwa, hannu d'aya na rigar ya yage sai ta zamana me hannu aya saboda ciwon nasa ya samu sakewa ga kuma bandejin da aka nad'e kafad'ar tasa da shi. A wani pharmacy ta tsaya ta siyo magungunan da aka rubuta mishi sannan ta kalleshi tace. ‘’A wani anguwa kake naje na ajiyeka?‘’ ‘’Kar ki damu madam zan hau nape ko taxi ya ajiyeni, muje dai gida inga kin shiga gida lafiya hankalina zaifi kwanciya.‘’ ‘’Bana son taurin kai kana buk'atar hutu yanzu, ya kamata na saukeka gida ka kwanta ka huta.‘’ "Ta ya kike tunanin zan bari ki kaini ki kuma juyo ke kad'ai, in baki sani ba ya kamata kisan rayuwarki ake buk'ata ko ta wani hali, don haka ya zama dole ki daina fita ke kad'ai sai tare da masu tsaronki don kiyayewar lafiyarki, duk da na san bakya buk'atar takura cikin rayuwarki kinfi son rayuwar 'yanci wannan dalilin ne yasa kika k'i amsar masu tsaron lafiyarki to yanzu lokaci yayi da zaki amshesu." "Har yanzu banjin zan iya rayuwa duk inda zanje sai da mutane a zagaye da ni, don haka har yau ban shirya amsarsu ba, duk wata kariya da zasu bani baza ta wuce wacce wanda ya halicce ni yake bani ba, ka gaya mini unguwar da zan ajiyeka, bana son doguwar magana.‘’ "Saukeni anan.‘’ kawai ya fad'a da kakkausar murya, ba tace uffan ba ta gangara gefen titi a hankula tayi parking yana k'ok'arin fita tace. "Na baka wutun wata guda, idan kaga baza ka iya cigaba da aikin ba kuma to sai kayi zamanka ba sai ka dawo ba saboda kar wani tsautsayin ya kuma samunka, nima duk da banji dad'in hakan ba na so ni harbin ya sama ba kai ba, don haka na gode da wannan kariyarma da na samu." "Idan kikai wasa da rayuwarki kanki kika cuta ba Faruoq ba." Yana fad'in hakan ya b'alle murfin motar ya fita, yana fitowa taxi tazo wucewa ta gabansa yayi saurin tsayar da ita ya fad'a ciki saboda ganin bai akko mutum ko aya ba sai da ya shiga ya zauna kana ya gayawa mai taxin inda zai ajiyeshi, Fanan ba tayi wani tunani ba kawai ta bi bayan wannan me taxin sunyi nisa da tafiya tana ankare da duk inda me taxin yake ba tai aune ba ta nemi inda suka shiga ta rasa, babu yadda ta iya haka ta juya ta nufi gida a mugun gajiye saboda kwana biyu ba tayi tuk'i ba shiyasa take jin muguwar gajiya da mutuear jiki gaba aya. Kate ta saka ta had'a mata ruwan wanka mai d'an zafi ta shige ciki, tana mugun son zama cikin ruwan wanka irin hakan take hasasho musu ita da mijin da zata aura su shiga cikin ruwan wanka su dade suna wasansu na masoya a ciki, amman kuma ba ta hasasho hakan da Sameer ta rasa me yasa sam ba ta jinsa a ranta da cewar wai shine mijin da iyayanta suka zab'ata, duk wata hanya da zata rusa auranta da Sameer ta duba ta laluba ba ta hango ta ba amman kuma har yau tak'i yardarwa da ranta shine mijinta. Har sai da ruwan ya huce kana ta bud'e gurin da zai fita kafin ta sakarwa kanta shower bayan ta sanya hular da za ta bawa gashinta kariya don kar ya jige, don ita sam ta tsani taji gashinta a jik'e drayer ma wahala yake bata don ko wankan tsarki tayi kate ce take busar mata da shi yanzu kuwa da suke tare da Easha ita keyi mata,don ta karbi kusan rabin ragamar aikin da kate in take mata, duk da wani abin Fanan in tana hanata tana nuna mata ita ba aiki ta d'auketa ba,wankin kai kuwa dama ba tayi a gida sai dai taje saloon. Bayan fitowarta daga wankan zama tayi akan stool in mudubin tana bin kanta da kallo, ita kanta da kanta fatarta tana mugun burgeta saboda yadda take da wani shek'i da santsi,wanda santsinta baya barin ruwa ya zauna a jikinta, idan ba tab'ata kayi kaji danshi ba to ko tace wanka tayi k'aryata hakan zakai saboda babu ko d'igon ruwa a jiki kuma ba bushewa tayi ba tsabar santsin fatarta ne, mayukanta desighners masu mugun tsada da kyau ta d'auko ta fara shafe jikinta da shi, ko wani loko da sako na jikinta sai da ta bi ta shafe shi kafin ta fesa body spray a jikinta kafin ta nufi gurin da kayanta suke, wata doguwar riga ta d'auko ta saka iya kacinta guiwarta kuma siririn hannu gareta, rigar ta amsheta kuma ta mata kyau sosai kana ta fito dining area kawai ta nufa don 'yan hanjinta har nannad'ewa yake saboda yunwa ko kyakkyawan kari ba ta tsaya tayi ba saboda shariar nan da ta saka a gaba, dama tunkan ta shiga wankan ta gayawa kate ta sama mata sassauk'an abinda za ta sanyawa cikinta ta ajiye mata shi kan dining in ta fito za taci. Bayan ta gama cin abincin ta barwa kate sallahun in hud'u yayi ta samu wani yaje ya auko Easha daga makaranta, za ta shiga ta kwanta don haka ba ta buk'atar ganin kowa, ta fad'i hakanne don ta san dole Sameer zaizo nemanta, cikin duvet mai matukar dumi ta shige ta rufe idanuwanta tana son baccin da ba ta samu tayi jiya ba ya sureta kafin lokacin sallar azahar ya k'arasa, a hankali baccin ya fara d'aukarta kafin ya d'auketa gaba d'aya. #N.W.A #Comment #Share [7/20, 8:22 AM] Rabi: BEBE'ARTH CIN AMANA ®️NAGARTA WRI.. ASOCIATION Wattpad@Rashuna 13 Tashi tayi yau da son zuwa beach ta kwana biyu ba taje ba kuma tana samun nishad'i a gurin in taje, kuma dama yau hutu take don ko gun aiki baza taje ba,da yamma in taje beach daga can sai ta huce club shima an kwana biyu ba'a lek'a ba, wuni tayi akan gado sai sallah ke tada ta, tana yin sallar la'asar kuwa ta fesa wanka ta fice, sun had'u da Easha da aka d'aukkota a makaranta a gate taso ta jirata ta shiryo su fita tare tak'i ba don komai ba sai don zata club kuma ba ta son zuwa gurin da Eashan. Easha tana shiga ciki wayar Faruoq ta dinga kira amma ba'a d'aga ba, tana so ta sanar masa ne Fanan ta fita ita kadai gashi kuma bai daga ba, a bangaran Faruoq d'in kuwa bacci yake yi kuma wayar tashi a silent take, da zazzzafan zazzab'i ya kwana wanda hakan yasa bai samu wani isashen bacci ba sai yanzun shiyasa baccin nasa yayi nauyi. A kasalance ya farka duk da yanzu jikin nasa da sauki zazzabin ya sauka, wayarsa ya fara dubawa wanda ya tarar da tarin miss call in Fadila, sai kuma na IG guda biyu, wanka yake buk'ata a yanzun, don in yace duk zaiyi waya da su to bashi da karfin yin hakan, kuma yasan zai shafe awoyi suna kan layi, kamar ance ya duba k'aramar wayarsa da yake fita da ita anan ya tarar da misa call daga landline in gidansu Fanan, haka kawai jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa don haka kawai ya danna gurin kira, Easha dake zaune a falo hankalinta gaba aya a tashe yake taji k'arar kira da gudu ta isa gurin ta d'aga, jin muryar Faruoq in yana hello ta saki ajiyar zuciya kafin tace mishi. "Aunt ce ta tafi Beach na armiana ita kad'ai kuma ta tafi, a k'alla yanzu zata shafe awa da tafiya." "Ok, kisa wasu daga cikin securityn gidan su bi bayanta." Kawai yace yana kashe wayar, siririn tsaki yaja yana dafe kansa,shi sam ya rasa taurin kai irin na wannan yarinyar. Zaune take a bakin ruwa, k'afafuwanta a cikin ruwan tana cillcillasu tana tsotsar water millon had'e da lumshe idanuwanta, ta dad'e sosai a zaune a gurin kafin wani da bak'ak'en kaya a jikinsa yazo ya zauna a gefenta, k'aramar bindiga ya fito da ita yana d'ora mata gefen cikinta had'e da fad'in ta biyo bayanshi ko ya tarwatsa kayan cikinta, tashi tayi kamar munafika ta bishi zungui zungui hantar cikinta na mugun kad'awa sunan Allah kawai take ambata cikin ranta akan ya kawo mata dauki, suna gab da isa bakin motar da suka ajiye zasu k'ursumata a ciki Securityn gidansu suka iso idan d'ayansu ne ya fara sauka a kanta za'a sakata cikin mota, da hanzari suka sakarwa me k'ok'arin sakata cikin motar harbi a k'afa, ashe ba shi kad'ai bane da wasu cikin mota nan suka fito suka hau sakarwa juna harsashi, d'aya daga cikinsu kuma ya rik'e Fanan yana kuma k'ok'arin turmutsata cikin motar, wani duka tayi mishi da guiwarta a mazantakarsa kafin ta arci na kare, ji tayi kawai taci karo da mutum, a razane ta d'ago da kanta ganin Faruoq ne yasata mayar da kanta jikinsa ta ruk'unk'umeshi had'e da fashewa da kuka, wani siririn tsaki yaja had'e da fad'in. "Ni cikani, ba zaki iya bawa kanki kariya ba, tunda ke taurin zuciya gareki ba'a isa a sakaki yin abinda baki da ra'ayi ba, ai da sai ki bisu kije inda suke son kaiki in yaso sai ki nuna musu taurin ran naki." A hankali ta sake shi tana shashshek'a da ajiyar zuciya har lokacin hawaye basu daina zirarowa daga idonta ba, gaba d'ayanta a tsorace take a kuma firgice, kallon yadda hawayen nata yake zirarewa yake yadda sam ba ya tsaiwa saboda santsin fatarta, ji yayi hakan yayi mugun dakar zuciyarshi, kautar da kansa yayi daga kan fuskarta, hade da fadin. "Sai ki shige kije su mayar dake gida, gobe ma kya kuma fitowa ke kad'ai." Tare da security uku suka tafi a cikin motarta yayin da d'aya kuma ya tafi kai mutum biyun da suka samu rauni daga cikinsu, suma kuma sun samu sun raunata mutum uku daga ciki biyu sun samu nasarar tserewa yayin da suka damk'a ukun a hannun police in da suka k'araso, a bakin titi tacewa me jan motar ya tsaya saboda tana son bin bayan Faruoq a yau ta kuma gasgata zarginta a kansa, babu salsal in kansa, sannan kuma yau fuskarsa batai wannan bak'in ba, kuma ace a rabuwarsu ta jiya kawai gashi ya samu fitowa a kansa, sai dai kuma in firgicewar da tayi ne yasata ganin hakan, akan idonta ya fito ya tari taxi don haka ba jinkiri tace subi bayan mai taxin kar su kuskura ya kubce musu, a take suka bi umarninta duk da su basu san bayan wa tasa su bi ba, duk sunyi tunanin ko duk cikin aikinta ne. Tun daga Hotel in da ya saka me taxin yayi parking zarginta ya kuma ninkuwa, daga can gefe ta saka sukai parking, ta karb'i wata 'yar k'aramar bindiga a hannunsu ta jefa cikin handbag inta tace su jirata anan yanzu zata fito, da sassarfa ta biyo bayansa amman sam ta nemi inda ya shiga ta rasa ,kamar ance ta d'aga idonta sama sai ta hangoshi a hawa na biyu, da sauri taje ta shiga lifta. Zagaye ta dinga yi ta rasa takamaiman wani daki ya shiga, a hankali ta kuma sauke idonta kan k'ofar da take zargi don ba ta gama rufuwa ba tana d'an rawa alamun baa dade da shiga ba, a b'angaran Faruoq kuwq da sassarfa ya shige d'akin hankalinsa a mugun tashe, tsabar hankalinsa ya kasa kwanciya da tafiyar Fanan beach duk da yasa securityn gidansu su bi bayanta haka kawai yaji shima gara yaje, tsabar saurin da yake zubawa ya manta bai shafa bakin abinda ke karawa fuskarsa baki ba da kuma hular k'walk'wal in da yake sakawa, kawai tsagun fuskar ya saka ya fice, sai a dawowar nan tasa ya ankara, inda Allah ya taimakeshi babu wani daya daga cikin securityn da ya ganshi, itama Fanan in yana adduar Allah yasa bata ankara ba, yana shiga tsagun fuskar tasa ya d'aye kafin ya tube kayan jikinsa ya zira rigar wanka, yana kokarin shiga toilet yaji kamar ana k'ok'arin shigowa d'akin ba tare da an danna kararrawar neman izini ba, kuma idonsa ya sauka akan k'ofarsa da ba ta gama rufuwa ba, da sauri ya juyo ya zaro bindiga cikin drowar mudubi yaje ya mak'ale daga bayan k'ofar, a hankali take turo k'ofar k'irjinta na dukan tara tara amman kuma daukko jarumta take tana dorawa kanta, hannunta me rik'e da bindigar ne ya fara bayyana, hannu yasa ya janyota gaba d'aya ya jinginata jikin k'ofar had'e da d'ora bindigarsa a kanta, gashi ita kuma ya rike hannunta me bindigar a ciki rik'o ba na wasa ba... Hidima ake sosai sai gyare gyare ake sai ka rantse shirin gagarumin biki a keyi amman ina shiri ne akeyi na Birthday in jikokin Hajja, Fina da Faruoq, kowa na gidan idan ka ganshi cikin farin ciki yake da annuri, ko ina na gidan manne yake da hotunansu window siz suna yara ba sufi shekaru bibbiyu ba. A hankali IG yake turo wellchair in da Hajja ke kai, wacce take amsa sunan surukarsa kuma yayar mahaifiyarsa, gefensa Ammi ce (Ummu Aymana) wacce ta murmure kamar ba tayi ciwo kwanakin baya ba, a gaban wani kyakkyawan teburi suka tsaya, dake dauke da wasu cake guda biyu masu hawa kusan takwas, tun a ido idan ka kalli cake in kasan zai matuk'ar dad'i, nan mutanen gidan, wanda yawancinsu 'yan aiki ne, sai makotan da ake zaman amana, wanda duk suka zamar musu tamkar 'yan uwa kasancewar Familyn nasu ba masu yawa bane, suka zo suka kewaye bayan tebir d'in, nan fitilin gurin suka hau wani walwali mai matuk'ar kyau, nan mutanen gurin suka hau tafi suna Happy Birthday Fina nd Faruoq, Hajja na k'ok'arin yanka cake, Islaha mai aikin Fadila ta taho rik'e da hannun Aseef da Abrar, wanda ta kawosu bisa umarnin Fadilan, saboda ita baza ta sami zuwa ba, ganin tahowarsu shine ya dakatar da Hajja daga yanka cake in, da gudu Abrar yaje ya haye kan cinyarta Aseef kuma yayi gurin Ammi don sunfi d'asawa, Aseef da Abrar suna wanke musu wani kaso da radadin dake zukatansu na rashin Faruoq da Fina, wanda sanadiyar cin Amana yasa duk suka bar duniyarsu... Anan na kawo k'arshen free page, 'yar uwa duk dad'in Haram Halak ta fishi, daure ki mallaki naki don nasan akwai tarin tambayoyin da zaku so jin amsoshinsu,200 ne kacal, sameni a layina don samun yadda zaki payment insa cikin sauk'i. 09037093702 #N.W.A #Comment #Share An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels