An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [2/7, 11:31 PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna ___________________ *ONE* *KANO* K/B/layi. Kallon abincin da suke ci nayi, hawayen idona yana son zubowa kan kuncina, gashi har a zuciyata yunwar nake ji amma bazan iya ciba, kallon Safnah nayi nace. "Pls my Safnah ke ki bani tunda su sun hanani. ” Dariya tayi mini tace. "Ai yasin yau indai baza kici da kanki ba sai dai ki hak'ura.” Juyawa nayi zan bar gurin da suke, hawaye na sakkowa bisa kuncina sai ji nayi Aysha tace. "Tsaya Teema Nazz na baki ai ni dake bata b'aci.” Juyowa nayi na galla mata harara, alamar naji haushi kenan, muryar Aunty Sakina naji tana cewa. "Rabu da su Teemah zo nan na baki da kaina.” Share hawayena nayi na isa gareta, ta 'yebi abincin a plate ta shiga bani, du³ baifi cokali goma ta bani ba nace mata. "Na k'oshi. ” Saboda sanin halina yasa bata matsa mini ba ta bani ruwa nasha. Misalin k'arfe 8:30pm shine dai² lokacin tashinmu daga aiki, muka yiwa Aunty Sakina sallama, har lokacin babu wacce naiwa magana ina fushi dasu har muka tari adai daita sahu, Safnah da Sarat aka fara saukewa a kunya store, mu kuma aka wuce damu layin d'an dare me nama, Aysha ce ta fara shiga gida saboda gidansu ne a farko har lokacin ban kulata ba sai kumbura fuska nake. Da sallama na shiga d'an madai daicin gidan namu, da hanzari na isa gaban Ummi da idonta yayi jazur saboda hayak'in ice, karb'ar abun fi fitawar nayi daga hannunta ina. "Ko da zan fita sai da na gaya miki kada kiyi aikin awarar nan komi dare na dawo zanyi.” "Ina tausaya miki ne *MUNASSAH* kin fita tun safe, kin dawo da daddare me makwan ki wuta sai ki hau wani aikin. ” "Amma Ummi kece fa kike gaya mini, duk wuyarnan da muke sha wata rana sai labari, kinsan matsalar ciwonki ba'a so kuna zuwa gaban wuta, dan Allah Ummi ki mini alk'awarin baza ki sake ba.” Shafa kaina tayi tace. "Na miki alk'awari Munassa, Allah ya albarkaci gabanki da bayanki, ya baki yara masu ladabi da biyayya fiye da yarda kike mini. ” Takai k'arshen maganar tana d'auke k'wallar idonta da sauri don kada na gani. "Amin” Nace ina cigaba da fi fita wutar har ta kama, sannan naja hannun Ummi zuwa d'aki, bayan mun zauna na kalleta nace. "Ummina albishirinki. ” "Goro, Munassata, nasan duk abinda zai fito daga bakinki me matuk'ar dad'i ne, gaya mini ina jinki. ” "Ashe ana kaiwa su Yaa Nazee ziyara mu bamu sani ba, sai d'azu naji ana hirar, wai ana kai musu garin rogo, suger gyad'a me gishiri, k'uli² amma ba dakakke ba, indome, kayan shayi, bread, ruwa na leda ko na jarka, man shafawa, maclean sabulun wanka da na wanki.” Katseni Ummi tayi da cewa. "To mu yanzu ina muka ga kud'in siya masa dukkanin abubuwan nan?” "Ai dama na fad'a ne don kiji irin abubuwan da ake kai musu, nidai yanzu ina da 1000 gobe insha Allahu zanje, zan kashe masa 800, nayi kud'in mota da 200, awara ma sai na dawo zan soya don kar na makara, dama na gayawa Aunty Sakina ba zanje goben ba. ” "Allah yashi miki albarka Munassa, bazan gaji da gaya miki wannan kalmar ba a ko da yaushe, Allah ya yaye mana wannan duhun rayuwa da muke ciki ya kawo mana haske cikin RAYUWARMU.” "Amin Ummina. ” "Ga abinci can d'auko kizo na baki.” "A'a Ummi nidai na k'oshi.” Bata matsa mini sai naci ba saboda tasan halit tata, ko ya naci abinci to ya isheni amma in har na k'ara to ranar bazan kwana lafiya ba, Abba da Yaa Nazee sunsha sintiri dani asibitoci har da na k'asashen waje akan rashin cin abincina, k'arshe har suka gane halitta ta tace daga Ubangina. __________ *KATSINA* K/Durbi "Mom kenan, a tunaninki zan bar wata ne ta haifawa *MIQ* 'ya'ya bayan ni na kasa haifa masa? ” A k'ufule wacce aka kira da Mom tace. "To ba gashinan ba kin barsa sun k'etare k'asa shi da matarsa, duk da kasancewarsa babban soja hutun wata guda 'ya d'iba don ya bawa matarsa kulawa, ke kin saki baki da hanci, da nayi magana kice don kina sonshi ne, ni yarda na tsani na bud'e ido na gansa haka na tsani ganin mutuwata, ko zanyi yawo tsirara bazan bari a haifi jika a gidan nanba, yarda nima ban dire d'a ko d'aya a cikinsa ba. ” "Hmmmm Mom kenan, kina bani ma'maki, sai kace ba nonoki na tsotsa ba, to bari kiji gobe ko jibi zakiji tafiyata England, kuma wata d'aya da mutuwar *FAREESA* da Babyn cikinta zanyi aikin k'arshe na gama, ma'ana zanyi tsafin da baya sakin mutum sai dai idan ya mutu, zan hana dukkanin matansa haihuwa tare dashi, kuma zan hanasa yin aure ko da d'aya daga cikinmu ce ta mutu, domin shi da aure sunyi hannun riga sai dai in a lahira. ” Tana kawowa nan ta juya ta bar falon....... *ALK'ALUMAN NAGARTATTU* [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [10/2/2020/4:52 PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna _________________ *TWO* *KANO* K/L/D/me nama Washe gari sai aro kurfoti nayi a mak'ota, naje na siyo gawayi na hura na barwa Ummi sauran aikin don na shirya na tafi gurin Yaa Nazz, saboda gudun kar na tafi taga ana zuwa neman awarar ta hura ice ta soya. K'arfe 8:30Am nayiwa Ummi sallama zan tafi, ta bini da addu'ar Allah ya tsare na kuma gaishe mata da Yaa Nazee, a lokacin har an fara layin siyan awara. Naje dai² k'ofar gidan su Aysha ita kuma ta fito zata tafi gurin aiki, aikuwa tace sai ta bini munje tare, ban b'oye mata ba nace mata nerata 200 kacal ta mota, sai kuma kud'in da zan masa siyayya, aikuwa tace muje itama tana da 200. A dai-daita sahu muka tsayar, nace masa kurmawa prison, yace 300 mukace 200 in zaka, yace mu hau, har ya fara tafiya damu nace masa. "Kayi yanke damu, kar ka bi damu ta *TEEMA NAZZ* .” Yace kuwa. "To.” A dai² bakin gate in gidan ya ajiyemu, komawa mukai da baya bayan mun sallamashi muka lalubo kantin da zamui masa siyayya, garin rogo na siya masa gwangwani 4 suga gwangwani 2, madara gwangwani 2, gyad'a me gishiri gwangwani 3, sai ledar pure water 2. Anan bakin gate in sai da aka fara cage kayanmu tukunna muka shiga, wata rumfa na gano, da bencina a jajjere mutane ne fal a gurin b'arin mata da ban na maza da ban, gefe muka samu muka rakub'e ina jin kaina yana jujjuyawa. 'Ko da wasa ban tab'a tunanin k'afata zata tako gidan nan ba, sai gashi wai yau Yayana mafi soyuwa a gareni shine a cikin gidan, ba tare da hak'k'insa ba face k'aharu, sai gashi dalilin haka nima na tako k'afata cikin gidan, wanda ko a mafarki ban tab'a tunanin hakan ba, idan kuma ina tunanin yadda Rayuwarmu ta taso tun farko, ko da wai idan akace Rayuwarmu zata juya kamar yanzu bazan yarda ba, lallai mutum baya sanin rayuwa juyi² ce sai hakan ya faru a kansa, ko kad'an ban tab'a tunanin DUNIYARMU zata sauya a lokacin kad'an ba, sai gashi gaba d'ayama ta wargaje.' Wasu siraran hawaye ne suka shiga biyo kuncina, zuciyata bata kuma tsinkewa ba sai da naji wasu suna tattauna abubuwa na ban tausayi, kifa kaina nayi na saki kuka har da shashshek'a. Da aka kwashi 'yan layin gaba suka shiga Aysha ce tayi saurin zama a gaban itama, saboda idan muka tsaya layi sai yazo kanmu zamui matuk'ar dad'ewa, me karb'ar sunan wa'yanda akazo gurinsu ne yazo yana karb'a, da akazo kan Aysha ta tab'oni nace masa. "Nazirr Abdulhamid Bak'o.” Yace. "Wata Anguwa?” Nace. "K/Naisa.” An d'an jima da karb'ar sunayen, sannan akace muzo mu shiga, da muka shiga ma sai da aka bincika kayan kowa, sannan aka bamu wani d'an kati kowa ya sak'ala a wuyansa, idan wani ya fito babu shi to ba za'a barshi ya fito ba ya zama d'an ciki, ina kallon Aysha tana kuma damk'e nata ta cikin hijabi, wani d'aki muka shiga muka zazzauna a benci, sannan wa'yanda akazo gurinsu suka fara shish shigowa, ina hango Yaa Nazee na fashe da wani irin kuka, shima k'asa yayi da kansa yana kuka k'asa², nidai bamu samu damar magana dashi ba, sai Aysha ce take ta tausarsa, can na d'ago kaina muka had'a ido dashi, idonsa d'aya ya kumbura wani kukan na kuma fashewa dashi, ina jin gandirobar dake gurin yana nasiha da adaina kuka, yace mu tashi lokaci yayi, kayan da muka kawo masa Aysha ta bashi, sai a lokacin ya bud'i baki da k'yar yace. "Abba bai mutu ba yana nan da ransa. ” Ji nayi wata juwa zata zubar dani daga zaune Aysha tayi saurin rik'oni, shikuma gandiroba ya tisa k'eyarshi waje, ya fita yana waiwayonmu, Aysha ce ta rik'oni muka fito, ina jin wani yana. "Ki daina mana kuka, bama son kuka munfi son kuyi mana addu'a. ” Da muka zo fitama ina jin gandirobobin suna cewa. "Idan kinsan kuka zaki dinga zuwa yi kada ki kuma zuwa.” Kan muje gida, ciwon kai da ciwon k'irji ya sark'e mini, amma haka na dinga daurewa don kada na tayarwa da Ummi hankali, d'aki na sulale na shige na kwanta. _Abba yana raye bai mutu ba._ To shin yana ina, dama k'arya aka mana akace ya mutu, to meyasa aka aikata hakan?” Bani da me bani wa'yan nan amsoshin a yanzu dai. Kuka me rad'ad'i da zafi na fashe dashi, ina jin kaina kamar zai dare gida biyu, haka zalika k'irjina ma wani irin suka yake mini. _________________ *ENGLAND* Kwance take cikin yalwataccen k'irjinsa tayi lamo, sam bata k'aunar abinda zaiyi sanadiyar barinta jikinsa, a cikin bawon wanka suke don ruwan d'umin sosai yake mata dad'i, hannu ya saka ya shafo cikinta, nan take yaji Babyn yana wutstsilawa a cikin, wata dariya ya saki yace. "Zumata kinji kwa yarda Babyna yake wul wulgawa?” Dariya tayi itama tace. "Haba Zumana, ni da abin yake cikina amma kake tambayata naji? ” "Wallahi tsabar farin cikine yayi mini yawa, wannan shine k'wanmu na takwas a duniya, ina kuma fatan da ya zamo rayayye, kar shima yabar CIKIN DUNIYARMU a yayin da muka fara saka ran rayuwa dashi. ” Shafo fuskarsa tayi cikin sanyin murya da karayar zuciya tace. "Kada ka damu Miq, insha Allahu wannan Babyn rayayye ne sai dai ni nakan ji kamar zan tafi na bar CIKIN DUNIYARKU, kuma ina jin kamar ta silar zuwansa duniya duhun dake lullub'e da rayuwarka zai yaye haske ya bayyana a gareka.” "In sha Allahu baza ki bar Duniyarmu ba Reesah, zamu rayu dake tare da Babynmu bi izinillahi Rabbi. ” "Amin to.” Tace tana kuma shigewa jikinsa, wankan sukayi suka fito, yana shafa mata mai itama tana shafa masa a haka har suka gama shiryawa, wayarsa dake kan mirror ce tayi k'ara yaje ya d'auka, yana ganin me kiran ya wani saki lallausan murmushi. "My Sumyy.” Shine farkon abinda ya fara fad'a, yayin da hakan yazo dai² da bugawar k'irjin Fareesah. "Haba My Miq, shine ka d'auke matarka kuka yi nesa dani bayan kasan rayuwata tana tattare da taku.” Ta fad'i hakan a shagwab'e "Sorry my Sumy ai tana haihuwa zamu dawo insha Allah. ” "Kai dai kawai ka d'auke matarka kun tafi ne, saboda kana zargin ana kashe maka 'ya'yane.” "Subhanallahi! Daina fad'in haka Sumy, sai kace banyi tawakkali ba, kuma ban yadda da k'addaraba? Duk yarana da suke mutuwa dama Allah yayi ba masu tsawon rai bane, don haka kar in kuma jin kin fad'i haka. ” Cikin fashewa da kukan kissa tace. "To ai kaine ka rabani da kanka, bayan kasan yadda nake zama idan har baka tare dani, bana jure rashinka idan har ya wuce na kwanakin da kakewa matanka, pls ka taimakawa rayuwata mana, kuma ita kanta Fareesah tana buk'atar kasancewata tare da ita. ” "To² naji my Sumy, nima ai nayi kewarki sosai, don haka Faisal zai shirya miki komai, gobe iwar haka muna tare da juna. ” Wani ihun farin ciki ta saki ta sakar masa mahaukacin kiss ta wayar, Fareesah kuwa k'irjinta ne ya shiga dokawa ta dinga binsa da kallon tsoro......... ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [11/2/2020/5:29 PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna ________________ *THREE* *KATSINA* G.R.A Tsallen farin ciki tayi, bayan ta ajiye wayar, ta nufi sashen Khadija. A kwance ta tadda ita kan doguwar kujera tana danna wayarta, ko sallama ba tayi ba ta shiga ta tsaya a kanta. "To sarkin 'yan kishi, gobe in Allah ya kaimu zanbi bayan mijina, ke kuwa da waccen da bata da amfani sai dai ku zauna kuyi zaman gida.” Wani kallon sama da k'asa Khadija tayi mata kana taja tsaki tace. "Mugun nufinki ne zai kaiki can, kuma insha Allahu k'udirinki akan Miq bazai tab'a cika ba, da sannu zai gane ke ba masoyiyar shi bace mak'iyiyarsa ce, idan mu munyi k'ok'arin fahimtar dashi kin dak'ile duka hanyoyin to ina me tabbatar miki da baki yiwa Allah wayo ba, akwai abinda zai zame miki izina kan mugun nufinki akan *MIQDAD*” "Hmmmm Khadija kenan, har yau baki sanni ba labarina kike ji, wai ta yaya ma za'ai na barki haka bayan kinsan dukkanin sirrinmu? To in baki sani ba yau ki sani, nice nan nai miki tsafin da yake danne harshenki aduk sanda kikayi k'ok'arin fallasa mini sirrina, na barki da abin a ranki yai ta damunki a zuci, kina gani zanci gaba da aikata mugun nufina amma babu damar ki kub'itar da shi, in baki sani ba yau ki sani na d'aure zuciyar Miq gaba da baya, duk wani wanda zai kawo masa suka a kaina bazai tab'a yarda ba, daga k'arshe ma k'iyayya ce zata biyo bayansa ga duk wanda yazo masa da sukata, nafi k'arfin tunaninki Khadija, haka zalika na wuce sanin da kika mini, a cikin sirrin nawa ma kaso d'aya kika sani cikin kaso dubu, kuma baza ki tab'a furta kaso d'ayan nan ga kowa ba, muddun kikai yunk'urin fad'e kuwa sai dai gawarki, don haka ni gobe zan tafi gurin mijina, sai kici gaba da kula da komi na gidan, kamar yarda kikace mugun nufina ne zai kaini, to tabbas shine zai kaini, idan kin isa masoyiyar Miq ta gaskiya kina iya kub'utar da Fareesah da abin cikinta daga tarkona tun kafin na isa, ni na tafi sai kuma mun dawo. ” Har ta juya zata fita, sai kuma ta dawo da baya tace. "Au na manta, Camera d'in da kika saka, bata isa ta d'aukar miki komi ba akan abinda muka tattauna, shiyasa nace Khadija baza ki tab'a jaa dani ba don na wuce saninki gaba da baya, har yanzu baki gama sanin wace ce Sumayya ba, a duba camera lafiya. ” Ta fita tana sakin murmushin mugunta, hannun Khadija na rawa ta d'auko camera da ta mak'ala jikin bango ta saita babu abinda take gani face duhu dumd'in, sai kuma taga wani irin halitta ta ciki ya k'walla k'ara yana kiran sunanta, wata iriyar k'ara ta saki, ta sume daga inda take zaune, Sumayya da taji k'arar ta saki yalwataccen murmushi. Fareeda tana daga sashenta taji k'arar Khadija, aikwa da hanzari ta nufo sashen nata don ganin lafiya, ganin Khadijan a sume ya firgita ta, ' Ita kuwa Khadija me ke damunta a rayuwa haka, a cikin 'yan kwanakin nan duk ta firgice, ta fice hayyacinta?' Ruwa ta samo ta shafa mata a fuskarta, wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki, kana ta fashe da wani irin kuka, kuka take kamar ranta zai fita, Fareeda tun tana tambayarta abinda ya faru har ta zuba mata ido, kuka take sosai, kuka irin wanda ka rasa mafitar nan, ji take zuciyarta tana mata wani irin ciwo. 'Wan nan wata iriyar matace mara imani, meyasa Allah ya sanyota cikin Duniyarmu? Ya Allah ya Ubangiji ka kawo mana k'arshenta, Allah kar ka bata ikon cikar burinta, ya Allah ka kawo silar da Miqdad zai gane ba k'aunarsa take ba, sam bata cikin jerin masoyansa itace ta farko a jerin mak'iyansa.' Fareeda da taga tak'i yin shiru, kuma ga dukkan alamu bata k'aunar ta san sirrinta, don haka jiki a sanyaye ta tashi ta fita, sai taji tana tausayawa Khadijan fiye da yarda take tausayin kanta, ita idan bata jin dad'i gurin Miqdad tana jin dad'i gurin iyayanta, ita kuwa Khadija babu uwa ba uba, ga dangi babu dad'i, ga miji ma babu dad'i, ga kuma k'aunarsa da Allah ya jarabceta da ita. _____________ *ENGLAND* Kallon Fareesah yayi da ta k'ureshi da kallo, ya d'age mata gira d'aya ya k'arasa gareta, d'agota yayi ya sanyata cikin jikinshi, tana jinta a jikinsa ta saki wani irin kuka da bata san dalilinsa ba, dabar barcewa yayi gurin tambayarta lafiya? "Nima ban san meyasa ba, amma ina jin a jikina kamar zuwan Aunty Sumayya zaizo da sabon wani lamari. ” "Babu abinda zai faru insha Allahu, kar fa ki manta duk cikin matana babu me k'aunarki sama da Sumy, tsabar soyayyar da take mini ce tasa take matuk'ar son abinda nake so, shiyasa take matuk'ar baki kulawa, wallahi Sumayya tana sonki ni na gas gata hakan kuma bata kishi dake kamar yarda su Khadija suke kishi dake, tsananin son da take mana ne shiyasa take son kasancewa tare damu, idan ban mata abinda take soba, sai taga kamar don ita bata haihuwa ne shiyasa nake gudinta, don haka kar ki damu da zuwanta, idan tazo d'inma wata k'arin kulawa zaki samu daga gareta. ” "To amma sai nake ganin ba ayiwa su Khadija adalci ba, in ni ka taho dani saboda haihuwa to ita fa Aunty Sumayya. ” "Shissssss Fareesah yi bacci, kada ki saka mini ciwon kai.” Ya fad'i hakan tare da gyara mata kwanciya a jikinsa, lamo tayi a jikinsa cikin zurfin tunani, ita dai Allah yana gani ba tayi na'am da zuwan Sumayya ba sam ²......... ALK'ALUMAN NAGARTATTU [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [12/2/2020/6:05PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna PREE PAGE ________________ *FOUR* *KANO* Duk yadda nakai ga juriyar kada Ummi ta ga'no ni sai da ta ga'no ni, ilai kuwa hankalinta yayi mugun tashi, ganin haka yasa na k'ara k'arfafa jikina, na nuna mata naji sauk'i, amma sai cewa tayi dole sai munje camise, nace. "Ummi kar ki damu naji sauk'i, idan munce ma camise d'in zamu da wani kud'in to? ” "Da kud'in awarar zamuje, ai lafiya itace gaba da komi Munassah.” "A'a ki bassa Ummi nidai naji sauk'i, ciwon kaine kawai, shima yanzu zan siyo magani nasha, tunda idan muka tab'a kud'in awarar da me zamu juya gobe? Awarar nan da ita muke samu muna rufawa juna asiri, tunda aikin da nake shi sai wata ake biyanmu. ” "Tom shikenan, bari na lek'a gidan Hajiya Safiya ko Baffa ne na bashi ya amso miki maganin. ” "Tom" Nace da ita ina rik'e kaina da yake mugun sara mini, maganar Yaa Nazee ce kawai ke yawo a kwanyata, na kasa samun matsayar shin na gayawa Ummi ko kuwa? Tana mik'a kud'in ta dawo, ta d'auko awarar da ta ajiye mini da kunu ta bani naci, babu laifi naci awarar sosai, saboda ina sonta, tana gama bani Baffa ya kawo maganin shima ta bani nasha, ina sha kuwa bacci yayi awon gaba dani, bani na farka ba sai kusan k'arfe 5:00Pm, jikina a mugun kasale na tashi, Ummi ta had'a mini ruwa me zafi da ta d'ora mini kan kwal bayan ta gama girki, wankan naje nayo abina, sai naji jikina a hankula yana war warewa, shiryawa nayi, sannan na tayar da sallah, bayan na idar ne nake cewa Ummi anyo siyayyar kayan awarane? Shine tace ai taga banjin dad'i shiyasa ta bari a wuta gobe, nace mata ai zan iya, da k'yar dai ta bani kud'in naje na siyo kayayyakin, ina zuwa muka had'u muka gyara waken nakai markad'e nan mak'otanmu, ana markad'an nazo na tace na had'a wuta na gingima tukunya akai na zuba, kasancewar ina da maka mashi ga kuma icen me ci nan da nan awarar tayi. Ko da mukazo kwanciyar bacci haka nayi ta sak'e²n ko na gayawa Ummi abinda Yaa Nazee yace, amma kuma ina gudun kar ciwonta ya tashi, a haka dai har bacci yayi awon gaba dani. K'arfe 11:00Am na gama siyar da awarata, ina tashi daga kan aikinta wanka nayi na shirya cikin doguwar rigata bak'a da hijabi fari, sallama nayiwa Ummi ta bini da addu'ar Allah ya kiyaye. Ina zuwa da murna da farin ciki Aunty Sakina ta tarb'eni. "Ai da har naji ba dad'i da Aysha take gaya mini baki da lafiya, don har na fidda ran zuwanki, sai gaki kuma.” Murmushi nayi don nasan dalilinta nayin murnar,saboda costomars d'intane, duk wanda yazo ni yake tambaya na kawo masa abinci, akwai wa'yanda in bana nan ma basa cin abinci a gurin, saboda ba wai yaban kai ba a duk ma'aikatan ta nafi kowa iya tsara girkuna kala² shiyasa ta tsani taga ban zoba, kuma take bani kulawa sosai da sosai. "Nasan ai kinfi kowa damuwa da rashin zuwana Aunty Sakina, shiyasa na daure na taho saboda ke kad'ai” Na fad'a ina kallon su Safnah, dariya tayi, don ta gane da su wa nake, aikuwa sai Safnah cewa tayi. "To dama wa yake nemanki? Da kizo da kar kizo mu duk d'ayane a gurinmu.” Jan hannuna Aunty Sakina tayi ba tare da na bawa Safnah amsa ba tana. "Kinga taho muje kiyi aikin gabanki, in ba haka ba Safnah baza ta k'yaleki ba, bayan ita ba abinda ta iya sai tuwon semo.” Dariya nayi na juya inaiwa Safnah gwalo da tasha kunu. Daga zuwana na shiga yin abubuwan da nasan anfi zuwa cinsu, kuma nafi kowa k'warewa a kansu. Tuwon rice agushi stew nayi da tuwon rice with okro stew da kuma tuwon semolina with okro da tuwon maiz with kuka soup. Nan da nan aka fara cika restaurant d'in, wasu na shiga wasu suna fita Kuma har da masu yin take a way d'insa, ban manta wani Alhaji, kullum anan yake cin abincin rana da dare, rannan yana cikin cin Vegetable jollof rice with fruits tsabar santi sai cemini yayi. Dan Allah in dinga zuwa gidanshi ina masa girki zai ninninka mini albashin da Aunty Sakina ke bani, karaf kuwa sai a kunnen Aunty Sakinan, aikwa ta rufe da masifa ba ji ba gani, kun san dai yaren mutum ba sauk'i in aka tab'osa, tun daga ranar idan yazo take hanani zuwa kai masa abinci sai dai wata da ban ta kaimasa, ko kad'an Aunty Sakina bata k'aunar abinda zaisa na bar aiki tare da ita, hakanne yasa albashin da take bani ya zarta na su Safnah. Kamar kullum k'arfe 8:30PM muka tashi daga aiki, yau dai a mota hira muke tayi saboda basu yimin wulak'ancin bada abinci ba, Sarat ce tace. "Nufin Aunty Sakina fa ko aure kikai baza ki daina aiki da ita ba ko? ” Aysha tace. "Haba dai sai kace ana hauka, ko wani miji ne zai yarda da irin aikin, bare ma muna fatan dukkanmu Allah ya kawo mana sauyin rayuwa. ” Safnah tace. "Hakane Aysha, amma ita Aunty Sakina a haukanta yarda Teema ke kawo mata kasuwa baza taso abinda zai rabasu ba ko da da aure, mu kuwa ba haka zamu so ba, muna son Allah ya bawa ko waccenmu gidan hutu da kwanciyar hankali yadda zamu manta da irin rayuwar da mukai a baya. ” "To Allah yasa. ” Nace, muka amsa da Amin dukkaninmu, dai² nan akazo layin su Safnah, sauka sukai suna yimana sai da safe, har muka isa layinmu babu wanda yace wani abu tsakanin ni da Aysha, kowa da kalar tunanin da yake a ransa. Ina shiga gida naji gyaran muryar Ummi a band'aki, don haka kawai sai na juya gidan Maman Amira don nace mata na dawo ta markad'an waken, ina tsaye kuwa aka markad'an na d'auko, akan sallaya na tadda Ummi tana lazimi, tunda na shiga take jero mini sannu tana shi mini albarka, sai da na tace, sannan na hura ice na d'ora, kan kice meye wannan na gama nayi wanka, nayi shirin kwanciya, duk yadda Ummi taso naci abinci amma na k'i, rik'o hannunta nayi nace. "Ummina. ” "Na'am Munassata.” Nafi awa nawa ina tauna maganar da zan gaya mata amman na kasa furtawa sai da naji tace. "Munassa, ki gaya mini abinda ke damunki, a yanzu baki da kowa cikin duniyar nan da zaki gayawa matsalarki sama dani. ” Sai da na k'ara damk'e hannunta sannan a hankula nace. "Wai Yaa Nazee ne yace mini Abba yana nan da ransa bai mutu ba. ” Zumbur Ummi ta mik'e tana bina da kallo......... Kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu, tun kafin na gama bada pree page. *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa. Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam. Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi. Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450. Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:- 07067364721 Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:- Firdausi Salisu Aliyu 0430001991 GTB Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:- 07067364721 [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [13/2/2020/7:14PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna PREE PAGE __________________ *FIVE* *KATSINA* G.R.A Tun cikin daren jiyan Sumayya ta shirya kayanta tsaf na tafiya, da safe Faisal ya kirata ya shaida mata jirginsu zai tashi k'arfe 12:00AM, aikuwa 11:30 yazo ya d'auketa, bata k'ara bin takan Khadija ba, bare kuma Fareedah, Mom ma a waya ta kirata ta shaida mata jirginsu zai tashi zuwa England, nanfa Mom ta buga shewa ta shiga zubaba mata kirari, a can England kuwa tunda aka kira Miqdad aka gaya masa jirginsu ya taso ya kasa samun sakat, sai zumud'in zuwan tauraruwarsa yake, Fareesah kuwa ta zama 'yar kallo, ga k'irjinta ke ta faman bugun lugude har yanzu, tana jinma yau kwata² cikinta bai motsa ba. Tun ana saura awa d'aya jirginsu ya sauka miq yacewa Fareesah ta shirya su tafi airport ita kuwa tace baza ta ba, aikuwa fad'a sukai kace² shi ya rasa dalinlin da yasa dukan matansa suke fito da kishinsu fili, sab'anin Sumayya akwai ta da b'oye kishi, bata tab'a barinsa ya fito fili, gashi kuma itace duk a binda yace yana so itama zata soshi ko da kuwa bata son abun a ranta, kuma abu ko kore ne yace mata jaa ne zata bishi akan hakan, hakanne yasa yake matuk'ar girmamata a zuciyarsa, saboda yasan duk dalilin soyayyar da take masa ne yake jawo wa'yannan abu buwan. Tana sauka a jirgi idonta akansa ya fara sauka, wani lallausan murmushi ta saki, tana jin tarin soyayyarsa da k'aunarsa na gudana cikin k'ofofin jikinta, tana son Miq soyayya mara iyaka, kuma tana matuk'ar kishinsa, hakanne yasa ta kore duk wata mace daga zuciyarsa, Fareesah ce kad'ai har yanzu ta kasa cireta daga zuciyarsa, ta rasa ta ya yarinyar ta kama zuciyarsa katamau haka har ya bata wani bigire na da ban a birnin zuciyarsa, amma ba komi idan ta kasa cireta daga zuciyarsa ai dole ta bar duniyarsa, don alk'awari ne tayi matuk'ar tana raye baza ta bari Miq d'inta ya kamu da soyayyar wata mace da ban ba ita ba, tayi matuk'ar k'ok'ari ma da ta bari Fareesah ta kawo har iwar haka cikin duniyarsu ita da Miq d'inta. Da gudu ta iso gareshi ya wara mata dukkanin hannuwansa ta shige cikin k'irjinsa da tayi matuk'ar kewa, wata kyakkyawar runguma yayi mata, baisan da yayi matuk'ar kewarta ba sai yanzu da yajita cikin jikinsa, Sumayya da ban ce cikin matansa, akwai ta da tsafta ta jikinta da muhallinta, kullum cikin gyaran kanta take, matsalarta d'aya ce girki, shine abinda bata iya ba sam² anan ne kawai Fareesah ta kere mata, amma har kyahun sura da fuska duk ta kere musu. "Welcome my Dear.” Taji saukar muryarsa cikin kunnenta, lumshe idonta tayi tana jin wata sabuwar k'aunarsa na zagawa ta koina a jikinta, cikin muryarta me matuk'ar dad'i da ke saukar masa da kasala tace. "Thanks my Miq, I really Miss you over.” Jan hannunta yayi suka nufi mota, tana tambayarsa Fareeda yace mata. "Na barta gida ne bata jin dad'i.” "Subhanallah! Amma shine ka barta ka taho, me makwan ka zauna sai kamin kwatancen gidan na taho, maza² ja motar muje, kar wani abu ya same ta.” Tunda ta fara maganar yake kallonta da tausayawa, da zata san cewa tayi baza tazo tararta ba ya ya zata ji? Ita tana can tana kishin banza da ita, ita gashi tana nan tana rawar jiki a kanta daga yin k'arya bata da lafiya, to ta ya zai had'a wata mace da Sumayya a zuciyarsa? Karb'ar key d'in tayi daga hannunsa ganin bazaiyi sauri ba taja motar da gudu, shi kuma sai binta yake da kallon tsumamman love. Tunda ya fita ya barta take shan kuka babu k'ak'k'autawa, ta rasa ta yaya² zata fahimtar da Miq Sumayya ba masoyiyarsa bace ta asali, duk ta inda ta b'ullo sai taga Sumayyan ta dad'e da toshe hanyar, ta riga tayi masa dabaibayi me matuk'ar wahalar kuncewa. A inda ya tafi ya barta anan suka zo suka sameta taci kuka ta k'oshi idanuwan nan sunyi luhu² sunyi jazur, da gudu Sumayyan tazo ta tallafo ta jikinta tana jajjero mata sannu, ita kuwa Fareesah wata sabuwar tsanar Sumayyan taji ta kamata, a fakayce ta zabga mata harara, murmushi Sumayyan tayi tana kallon Miq. "Miq ai ba muga ta zama ba gwara mu tafi asibiti ko don lafiyar Babynmu. ” Baice mata k'ala ba yayi shigewarsa d'akinsa, tana ganin yabar falon ta saki Fareesan daga jikinta, dama ji take yi kamar ta rik'e garwashin wuta, wani banzan kallo ta jefeta da shi tayi k'asa² da muryarta gurin fad'in. "Ni nasan lafiyarki k'alau, kinyi hakanne don kawai kar kizo tara ta, saboda kina bak'in cikin zuwana inda kuke, to ko zaki had'iyi zuciya ki mutu sai na kasance tare da Miq, ke ba wai kina murna gaki me miji ya d'aukoki kun taho, saboda ke kad'aice me haihuwa cikinmu, to ko zaki ajiye masa 'ya'ya dubu baza ki tab'a kai matsayin da na kai a zuciyarsa ba, ganin damata ne yasa na barku kuka taho a lokacin saboda akwai abu me muhimmamci da nake, don haka sai hak'uri yau nice da zumarki, haka kike kiranshi ko? ” Ta tambayeta tana d'age mata gira d'aya, k'asa Fareesah tayi da kanta ba tare da tace mata komi ba, sai tsananin tsanar Sumayyan dake yaho a cikin jikinta, kuka take matuk'ar sonyi a yanzun amma baza ta iya yi a gabanta ba, mik'ewa tayi da k'yar ta shige d'akinta ta rufo k'ofa, zubewa tayi a gado ta saki wani sabon kuka me tarin bak'in ciki, tun sanda taji tattaunawarsu da Khadija, taji Sumayyan tana furta kalmar tsafi, ta gasgata zatonta akan ba haka Sumayyan ta bar Miq ba, daga baya ta koma gurin Khadija babu yadda batayi da Khadijan ba akan ta gaya mata matsalarta da Sumayyan, amma fir tak'i sai kuka da take kamar ranta zai fita, kuma tayi mata gargad'i akan ta fita sabgar Sumayya idon har tana son kanta da lafiya, tun daga lokacin take cikin muguwar matsala, gashi bata da wanda zata gayawa matsalarta Miq d'inne shikuma matuk'ar akan sukar Sumy ne bazai tab'a saura ranka ba. Kuka take sosai, ita sai a yanzu ma take alak'anta mutuwar duka 'ya'yanta da Sumayyan. Bayan shigewar Fareesah d'aki, Sumayya ta tab'e baki ta nufi d'akin da taga Miq d'inta ya shiga, a kwance ta taddashi akan gado yayi rigin gine, kwanciya tayi akan faffad'an k'irjinsa, ta saka hannunta kan gemunsa dake ta shek'i da k'yalli tana wasa dashi, d'aya hannun nata tana yawo dashi a k'irjinsa tayi k'asa da muryarta gami da narkar da ita tace. "My Miq, don Allah kazo ka lallab'ata muje asibiti, ni ko ba don ita ba, ko don Babynmu ai maso muje, tunda muna son mu rayu dashi CIKIN DUNIYARMU, amma ba yadda banyi da ita ba, daga k'arshema ta kullo k'ofarta. ” Shiru yayi mata, ya lumshe kyawawan idanuwansa, ta kuma cewa. "Miq da kaifa nake.” Ta fad'a a shagwab'e. Janyota jikinsa yayi ya shiga yimata sabon wasu launuka, yana nuna mata ba k'aramin kewarta yayi ba,don yasan hakanne kawai zaisa ta manta da batun Fareesan, itama kuwa batai k'asa a guiwar bud'e masa sababbin pagikan da baisan dasu ba.......... Kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu, domin akwai babbar tafiya a gaba. ALK'ALUMAN NAGARTATTU *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa. Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam. Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi. Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450. Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:- 07067364721 Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:- Firdausi Salisu Aliyu 0430001991 GTB Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:- 07067364721 [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [17/2/2020/4:20PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat Fitattu 6 na siyarwane, idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 PREE PAGE _______________ *SEVINE* *KANO* Kuka nake sosai, ina jijjigata ina kiran sunanta, ganin ko motsi bata yi ya sakani na yo waje da gudu, kacib'is mukayi da Innan katsina, rik'oni tayi tana tambayata lafiya? Kasa bata amsa nayi, sai nuna mata ciki da nake da hannu, don magana baza ta iya fita ba a halin da nake ciki ko kad'an, cikani tayi, ta shiga ciki da hanzari, ni kuma nayi waje, har da gudu nake had'awa kafin na isa titi na taro adai-daita, ko da nazo na tarar Inna ta tallafota jikinta tana ta kuka, nace. "Inna na samo mota kamota mu tafi asibiti. ” Ina fad'ar hakan na shiga d'aki na harhad'o abinda Allah ya hore mana nazo muka kamata muka saka a mota, muna rik'e da ita ta gefe da gefe muka tafi, tsabar gi gita ko rufe gidan namu banyi ba. Taimakon gaggawa aka bawa Ummi, ance jininta ne ya hau sosai, yanzu dai anai mata k'arin ruwa an rubuta mata magun guna, kud'in dake hannuna da wanda Inna tazo da su dasu na had'a mukai amfani. Kwanan Ummi hud'u a asibitin aka sallamemu, taji sauk'i sosai, su Safnah har da Aunty Sakina duk sunzo sun dubata, ban jigata sosai ba kasancewar ga Inna ita ke lura da ita, kuma Ummin taji dad'in zuwan Innan, naji Innan tana gaya mata sai ta kwana biyu kafin ta tafi, saboda wa'yanda takewa aiki basa nan, ragowar kud'in da ya rage mana dasu nayo siyayyar awara, Inna ce ma ta k'arb'i aikin awarar ta hanani nayi, don haka washe gari da huri na tafi gurin aikina. A kwana biyun nan na samu sok'i, kasancewar zuwan Inna, gurin aiki da wuri nake zuwa na lura Aunty Sakina ma taji dad'in hakan, don yanzu cinikin nata ya kuma bunk'asa. ______________ *ENGLAND* Wani d'aki da ban ya shiga ya kulle kansa, k'wak'walwarsa wani irin juyawa take, magan ganun Fareesah ne kawai ke yawo a kwanyarsa, sosai magan ganun nata suka zurfafa tunaninsa har suka haddasa masa zazzafan ciwon kai. Sumayya kuwa tsafinta ya nuna mata Fareesah bata san komai game da ita ba, sai dai tana zargin abinda ke tsakaninta da Khadija, kuma ta shirya d'amarar kunce k'ullin da tayiwa Miq, hatta camera da ta saita a gidan tsafinta ya nuna mata, wani shu'umin murmushi ta saki a ranta tace. 'Fareesah kenan, kinyi kad'an ki warware mini dukkanin shirina, zan mik'aki inda babu ke babu dawowa cikin duniyar Miq da Khadija bare kiyi yunk'urin kare su daga tarkona, dukkaninsu tarkona ya riga yabi jinin jikinsu shi da barinsu sai ranar da numfashinsu ya d'auke gaba d'aya, zanyi gaggawar aikata shirina akanki Fareesah tun kafin ki b'illo mini da hanyar da bazan iya toshe ta ba.’ Fitowa tayi ta nufo d'akin Fareesan, ita kuwa Fareesah tun fitar Miq daga d'akinta bata bari kuka yaci k'arfinta ba ta shiga band'aki ta d'auro alwala ta kalli gabas, hakanne yasa ko da Sumayya tazo sai ta tarar da ita tana sallah, toilet d'in d'akin ta duba taga miq d'in ba ya ciki don haka sai ta fita, tana tunanin inda ya tafi to, gashi yabar wayoyinsu a d'aki, a falo ta zauna tana jiran ta inda zai b'ullo. ________________ *MISRA* Ya dad'e da sanin matarsa da 'yarta ba k'aunar tilon d'ansa suke ba, amma sun riga sun saye zuciyarsa da yaudarar riyar soyayya, wacce ta shiga jikinsa ta cud'anya da jinin jikinsa, abu kad'an bazai tab'a iya ganar dashi yaudarar riyar soyayyar da suke masan ba, abin mamaki shine, shi kansa ya kasa d'aukar mataki a kan hakan, duk sanda yayi yunk'urin nema masa taimako sai yaji abin ya fita daga ransa sam, amman ta dalilin abokinsa kuma amininsa sai da sukaje gurin wani malami don nema masa taimako, shine malamin ya sanar musu tsafi akayi masa me wuyar sha'ani, akwai wata bishiya a misra, itacen bishiyar zai samo, da ya samosa insha Allahu tsafin dake jikinsa shi da yaron nasa zai war ware, wannan shine dalilin zuwansa k'asar, ba tare da kowa ya san inda yaje ba, amman yau tsahon watansa guda a k'asar, duk sanda ya fita da niyar samo itacen saidai ya tsince shi a wata hanya ta da ban......... ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: [2/16, 6:04 PM] RASHUNA: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I [2/16, 7:47 PM] +234 903 709 3702: *BEBE'ARTH* [2/11, 10:57 PM] *CIKIN DUNIYARMU* 1⃣ Follow me on whatpad @Rashuna ________________ *SIX* *ENGLAND* Bayan lafawar komai, sunyo wankansu tare sun gama shiryawa, da kulawa Sumayyan ta kalleshi tace. "Dan Allah Miq kaje ka gano Fareesah, ko bakayi don ita ba, ai kayi don Babynmu dake jikinta. ” Ba tare da yayi magana ba ya tashi ya fita, don ya gaji da naci irin na Sumayya tai nanata zance kenan har sai an mata abinda take so. Tana kife akan gadon tun d'azun tana ta shan kukanta ya shigo, da,sassarfa ya isa gareta ya d'agota, saboda ganin irin kwanciyar da tayi. "Baki da hankali ne zaki irin kwanciyar nan, ko so kike ki kashe mini d'aa. ” Cikin shashshek'ar kuka tace. "Ai gara ni na kasheshi tunda ba sonshi kake ba, har ka zab'i a kashe mana shi. ” Sumayya dake bakin k'ofa tana jiyo abinda suke cewa maganar ta sauka a kunnenta, gabanta ne ya yanke ya fad'i, kaddai Fareesah ta san abinda ya kawo ni nan? Ta shiga tambayar kanta, idan kwa ta riga da ta sani, aikina yana gab da lalacewa, da sauri ta bar bakin k'ofar ta koma d'aki Ita kuwa Fareesah bata ma san ta furta wannan kalmar ba ko d'aya, yayin da shima Miqdad in ya sanya maganar tata a shirme, wata kyakkyawar runguma yayi mata, yana hura mata iska me matuk'ar d'umi a kunnenta, lak'was tayi a cikin jikinsa tana jejjero ajiyar zuciya, cikin sanyin magana yace. "Ki rage kishi zumata, ki koyi kishi irin na Sumy. ” "Nikam nafi son na k'are rayuwata da irin nawa kishin, domin na gasgata kishina ba bak'in kishi bane, kishi ne irin wanda ko wace mace zata so tayi koyi dashi, ba irin na Sumayya ba, Sumayya bak'in kishi ne da ita me matuk'ar muni, wanda babu mahaluk'in da zaiso yayi koyi da irinsa, amman kai idanuwanka sun makance akan Sumayya, ka toshe kunnuwanka babu ta yarda za'ai ka fuskanci inda ta saka gaba, ka ruga ka bata dukkanin wata yarda taka da amincewarka, yayin da nikuma nake ji a jikina ha'intarka take.” Kallonsa tayi cikin ido, ta sakar masa murmushi, don tana ganin yadda ya k'ufula, k'iris yake jira ya fashe tana tab'o masa 'yar gaban goshinsa, tashi tayi taje ta rufe k'ofarta ta saka mata key, sannan taci gaba. "Ina jii a jikina kamar rayuwata ta kusa zuwa k'arshe, sai naji bana son na tafi na barka cikin mugayen mutanen dake zagaye dakai amman kai baka sani ba, kuma kak'i ka bawa kowa damar da zai fuskantar dakai, a matsayina na masoyiyarka bazan bar duniyarka ba har sai na fara haska maka wani abun, ko da ta sanadiyar hakan zaka rabu dani.” Tv ta had'a, sai ga vidion abubuwan da suka faru tun daga shigowarsu ta d'azu, cike da mamaki da al'ajabi Miq ke kallon Sumayya, murmushi me ciwo Fareesah tayi, sannan tace. "Na rasa ta yadda zanyi na fuskantar da kai yadda Sumayyan ke d'aukarmu a bayan idonka na rasa, domin ta riga ta toshe dukkan wata kafa, amma sai d'azu tunanin had'a camera ya fad'o mini, shine dalilin da yasa nayi hakan, don ka gani da idonka kafi gas ga tawa, ba nayi hakanne don na b'ata tsakaninku da Sumayya ba, sai dai nayi hakanne don na gyara mu'amalar dake tsakaninmu a b'oye, ina so kabi Sumayya a hankula ka binciketa, ba wai ka tare ta nake nufi ba, ina nufin ka saka mata ido, domin akwai wani b'oyayyen al'amari tsakaninsu da Khadija, kuma Khadija ce ke azabtuwa da hakan, babu yadda banyi da ita ba ta gaya mini abinda ke faruwa tak'i, k'arshe ma cewa tayi idan ina son cigaban rayuwata na fita hanyar Sumayya. ” Share k'wallar idonta tayi sannan ta k'arasa gabansa ta rik'e hannuwansa biyu idanuwanta na tsiyayar hawaye taci gaba. "A kullum bani da wani buri da ya wuce na fuskantar da kai kuskuren da kakeyi a rayuwa, duk yayin da nayi yunk'urun yin hakan da fad'a muke k'arewa, amma yau dole na gaya maka, ko da zamuyi rabuwar da babu dawowa cikinta. A matsayin ka na shugaba a tsakaninmu, dukkanmu mu hud'un hak'k'inmu ya rataya a kanka, kuma dole ne ka saukewa ko waccenmu hak'k'inta da ya rataya akanka, amma bakai hakan ba, ni da Sumayya kawai kawai kake sauke mana hak'k'ok'inka, su kuwa biyun me sukai maka, baka tsoran Allah ya kama ka da hak'k'insu? Barema Khadija bata da kowa a duniyarnan da zai kula da lamarinta sai kai, amma ka banzantar da lamarinta, gashi tana cikin k'uncin rayuwa, duk tabi ta lalace, amma ka kasa fuskantar hakan, a hakan kake ikirarin Sumayya ta rik'e maka gidanka? Macen da bata san ta sai.....” "Dakata Fareesah” Ya fad'a a tsawace, bud'e k'ofar yayi ya fice a fusace yana doko mata k'ofar. ___________ *KANO* Kwana Ummi tayi tana jujjuya maganar da na gaya mata, tabbas tayi zaton hakan, duba da yadda ba suga gawarsa ba, zuwa kawai akai aka sanar da mutuwarsa, to shin yana in me yasa akai musu k'aryar ya mutu? Duk yadda akayi akwai wani abu a k'asa, tasan irin mugunta ta Baffa Sule, babu abinda bazai iya aikatawa ba don cikar burinsa, zata iya yuyuwa ma da bakinsa a sharrin da akawa Nazir, tabbas zata iya yuyuwa hakanne, don jin amsarta kuwa ya zama dole ta jure taje ta gano Nazir, domin jin wasu amsoshin daga bakinsa. Wannan tunani da tayi shine dalilin da yasa tace gobe muna sayar da awara zamuje gurinsa, aikuwa washe gari mukai sa'a awararmu ta k'are tun k'arfe goma na safe, aikuwa muka shirya muka tafi. Tun a runfar da ake zama Ummi ke sharb'ar kuka tana sharewa, nikuma sai yau Allah yasa zuciyata ta dake, me karb'ar sunane yazo na gaya masa sunan wanda muka zo gurinsa, can jimawa sai gashi yazo, yace mana wanda mukazo gurinsa an canza masa prison, nace wacce aka kaisa, yace suma basu sani ba, tun a gurin Ummi tace bibbiyu take gani, ji take kamar ana jujjuyata, nima dai dauriya kawai nake, a haka dai Allah ya kaimu gida lafiya, kamar jira ake mu shiga Ummi ta yanke jiki ta fad'i, kanta nayi ina kiran sunanta gami da sakin wani marayan kuka...... *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa. Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam. Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi. Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450. Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:- 07067364721 Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:- Firdausi Salisu Aliyu 0430001991 GTB Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:- 07067364721 [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [22/2/2020/5:53PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat *GASKIYA D'AYA* Asisi B Aliyu Fitattu 6 na siyarwa ne, Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 PREE PAGE _______________ *NINE* Cire Fareeesah yayi daga jikinsa ya mik'e a hankula yaje ya bud'e mata k'ofar, tana ganin shine ta fad'a jikinsa gami da sakin kukan munafurci, rik'ota jikinsa yayi yana tambayarta lafiya, cikin kuka tace. "Nemanka nake tayi tun d'azu, kayi tafiyarka ka barni cikin yunwa.” Shi wallahi ya manta da wani abinci ma, kansa ya shafa yace. "Ai muna da abinci a kitchen muje na baki.” Ya ja hannunta zuwa kitchen d'in, ko da yaje sai ya tarar babu abincin sai Left over tuwo nd miyar kuka, kawai, kuma shima kad'an ne, yasan Fareesah ce ta ajiyesa zata ci, don haka sai yace mata tazo suje suyo take a way, cewa tayi baza taje ba yaje shi ya dawo, tayi hakanne don ta samu damar aikata shirinta yanda ta so, d'aki ya koma ya d'auki key d'in mota ya fice, ita kuwa maganin da tazo dashi ta d'auko ta faffesa shi cikin Tuwo nd miyar kuka d'in da yace na Fareesah ne, baza kice an sakawa tuwon komi ba, sai ita da ta saka, falo ta dawo ta zauna tana zaman jiransa. Fareesah kuwa zamewa tayi ta kwanta akan gadon, wasu sabbin hawayen na biyo kuncinta, wayar Miq d'in ta d'auka ta turawa Dad da sak'on Miq d'in bacci yake, in ya tashi zata gaya masa, zai kirashi, daga haka ba ta san sanda bacci ya kwasheta anan ba. Bai wani jima da fita ba sai gashi ya dawo, dama Sumayya ta tanadi plate d'inta da spoon don haka yana kawowa ta hau ci, shi kuwa kasa cin komi yayi haka kawai yake jin gabansa na yawan fad'uwa, kamar wani sabon al'amari zai faru da shi, d'akin da yabar Fareesah ya shiga, sai ya tarar tana bacci, zama yayi a gefenta ya zuba mata idanu yana ta kallonta. Wayarsa ya d'auka, anan yaga miss call d'in Dad d'insa, da hanzari ya danna kiran wayar Dad d'in, ringing d'aya zuwa uku ya d'auka. "Hello Dad kana lafiya? ” "Lafiya lau Sadauki, da fatan kaima haka, don hankalina ne ya kasa kwanciya har sai da naji muryarka cikin kwanciyar hankali. ” Murmushi yayi cike da soyayyar mahaifin nasa kana yace. "Lafiya lau nake wallahi, kaima ka san babu abinda zai samu sadaukinka matuk'ar duniyarsa na tare da Fareesah, amma a kwana biyun nan tana yawan fad'in zata bar duniyata, kuma ina jin tsoron haka. ” Yakai k'arshen maganar kamar zai fashewa mahaifin nasa da kuka. " Ka daina damuwa, insha Allahu lafiya k'alau zata haihu, kuci gaba da rayuwarku cikin duniyarku tare da 'yarku ko d'anku.” Cikin sanyin jiki yace. "To Allah yasa.” "Amin” Dad d'in yace kafin ya jiyo muryar Sumayya ta wayar tana kiran Miq d'in, k'irjinsa yaji yayi wani irin bugu sannan yace. "Muryar wa nake ji Sadauki? ” Bakinsa na rawa saboda tsoro dak'yar ya tattara kalmomin sunan nata yace. "Su may ya ce. ” "Muddun na kafa maka doka indai akan Sumayya ne sai kabi ka rusheta gami da mutstsiketa, bansan meyasa kake min haka ba Miqdad, alk'awari ka d'aukarmun sai kuma gashi ka karya mini shikenan kaje gaka ga Sumayyan nan, duk abinda ya biyo baya babu ruwana. ” K'it ya kashe wayarsa, yana jin wani rad'ad'i a k'irjinsa, shikenan zai kuma rasa jikansa karo na tara kenan, shidai yana jin bashi da rabon ganin jikansa a duniya, tunda Mariya ta shigo duniyarsa yake ganin ba dai² ba, ga shi sun had'u ita da 'yarta sun had'u suna ruguza musu rayuwarsu. Miq kuwa wani mugun tashin hankali ne ya ziyarcesa, bugun da k'irjinsa yake akan da ya ninku, me Daddy yake nufi da duk abinda ya faru babu ruwansa, meyasa har yanzu Daddy ya kasa gane Sumayya baza ta tab'a iya cutar da abinda ya dangancesa ba, Har yaushe ne zai dinga zargin ita take kashe dukkanin 'ya'yan da Fareesah ke haifa? Tsintar kansa yayi da addu'ar Allah ya raya abinda ke cikin Fareesah ko don Daddy ya daina zargin Sumayya. Cikin d'an baccin da ya d'auketa, ta fara jin yunwa, a hankula ta bud'e idonta, ta saukeshi kan Miq da ya zurfafa cikin tunani, ba tabi ta kansa ba ta nufi kitchen, tuwonta ta d'auka ta nemi guri a kitchen d'in ta hau ci, sai da ta cinyesa tas hankali kwance sannan ta tashi ta nufi d'akinta, wanka tayi, ta gabatar da sallar isa'i had'e da shafa'i da wutiri, sannan tayi shirin kwanciya, tabi lafiyar katifa don wani azababben bacci take ji, aikuwa tana kwanciya baccin yayi awon gaba da ita. Miq kuwa Sumayya tayi nasarar cire dukkan wani tunani daga kansa, bayan yayi sallah, wanka sukayo sukai shirin kwanciya, sam ta hanasa zuwa gurin Fareesah don batai aiki akan camera d'in gidan da ta saita ba, tana so ta gani da idonta ita ta bata abinda taci ta mutu, shikuwa Miq ziciyarsa da hankalinsa gaba d'aya suna gurin Fareesan. Mafarki tayi wai Sumayya ta zuba mata wani abu cikin tuwon da taci, a firgice ta farka ta had'a tv ilai kuwa sai ga Fareesan na fesa maganin, wata zuface ta karyo mata, tana zulumin abinda Sumayyan ta bata taci, auwala tayo ta kalli gabas tana kaiwa Allah kukanta, akan kar yabar Sumayya taci nasara akan mugun nufinta akanta, kusan kwana tayi tana sallah domin baccinma yak'i zuwa kwata² ta riga ta saba bacci a jikin zumarta, sai gashi yau yayi mata nisa. Sai da tayi sallar asuba gari ya fara washewa, tana zaune kan sallaya tana jan carbi bayanta da mararta suka fara ciwo, tun tana daurewa tana cije baki har yaso yafi k'arfinta, ga cikinta da yake mata wani mugun ciwo, a durk'ushe ta k'arasa bakin k'ofa ta bud'e, gudun kar ta mutu ita kad'ai cikin d'aki, da jan jiki ta isa falo tana k'walawa Miq kira. A kwance kawai yake, amma ba bacci yake ba, zuciyarsa da tunaninsa suna ga Fareesah tun da yayi sallar asuba yake son zuwa ya ganota, amma ji yake kamar an d'aure masa jijiyoyin jikinsa an hanashi fita, yana ji tana kiran sunansa tun yana jin sautin muryarta har ya zamto ya daina ji, ita kuwa a halin yanzu ta riga ta galabaita babu wani k'arfi ko kuzari a tattare da ita bakinta yayi wani irin bushewa na azaba, tun Sanda take kiran Miq d'in Sumayya idonta biyu ta farka amma tayi kamar bata tashi ba, sai da ta tabbatar ta galabaita sannan ta farka, kallonsa tayi tace. "Kaje ka gano Fareesah kuwa? ” Idonsa ne ya kawo ruwa, ya kasa magana, wani tausayinsa taji ya lullub'eta, duk fa sanadiyar sonsa da k'aunarsa take aikata wa'yannan abubuwan, dirowa tayi daga gadon tana. "Ya kamata dai muje mu gano me ciki. ” Bata jira me zaice ba tayi gaba, a yashe ta tadda Fareesah a falo kamar matacciya, wani irin ihu ta saki da ya saka zuciyar Miq harbawa, sai a lokacin yaji wani k'arfi yazo masa ya fito da gudu ganin Fareesah cikin wannan halin ya kuma tsinkar da Zuciyarsa........... [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [19/2/2020/6:00PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat *GASKIYA D'AYA* Asisi B. Aliyu Fitattu 6 na siyarwa ne, Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 PREE PAGE _______________ *EIGHT* Gashi kuma a yau yake son komawa kan ayyukansa, ga abinda yazo nema bai samu ba, haka dai zai hak'ura ya koma, in yaso ya gayawa malamin abinda ke faruwa dashi a hanyar zuwa samo itacen bishiyar, wayarsa ya d'auka ya danna kiran wayar dan nasa, amma haka tai ta ringin ba'a d'aga ba, ji yayi hankalinsa yayi mugun tashi, tunawa yayi ai tare da matarsa sukayi tafiyar, don haka sai ya juya akalarsa ga kiran wayar matar tasa. Fareesah dake karatun al'qur'ani bayan ta idar da sallar taji wayarta na k'ara, sai da takai aya, ta kuma ci sa'a wayar bata katse ba da hanzari tayi picking ganin Daddy ne ke kiranta. "Hello d'iyata kuna lafiya? ” Shine abinda ya fara cewa, sai da tayi murmushi sannan tace. "Lafiya lau Daddy, da fatan kuma haka. ” "Alhamdlillah D'iyata, ya kwanan jikata, ko kuma jikana? ” Murmushi tayi cike da kunya batace komi ba, murmushin shima yayi, don yasan baza tayi magana ba, hakan ne ke faruwa tsakaninsu idan har ya tambayeta jikansa, duk cikin matan d'an nasa, su biyu kawai yake matuk'ar k'auna, daga ita sai Khadija, amman kuma sai dai ya nuna musu soyayyar a b'oye, saboda bai isa yayi ta gaban matarsa ba, sai dai in soyayyar 'yarta zai nuna. "To Allah dai ya rabaku lafiya, ya kuma yi albarka, na kira number Sadauki d'in ta tafi amma bai d'aga ba ko lafiya? ” Yaci gaba, don yasan amin d'inma sai dai ta fad'eta a zuci. ” "Ina kitchen ne ni, amma bari naje na dubo. ” Kawai ta tsinci kanta da yin k'aryar hakan. "Ok, tom, kice masa ina jiran kiransa. ” Daga haka ya datse layin. Da k'yar ta yunk'ura ta tashi, bayan ta ajiye wayar, saboda cikinta da yayi mata nauyi, yau ji takeyi cikin nata ya kuma yo k'asa sosai, don yauma saura kwana hud'u EDD d'inta ya cika, duk da duk haihuwar da tayi tana k'ara sati biyu a kai, a hankula take takawa har ta fito falon, idontane ya fara sauka kan Sumayya, ita kuwa Sumayyan cike da bak'in ciki take binta da kallo, ji takeyi kamar taje ta shak'eta ta mutu, ta huta da ganinta tare da bakin cikin jikinta, d'auke kanta Fareesan tayi, ta nufi d'akin Miq d'in, duka wayoyin nasa ta tarar akan mudubi, amman shi baya ciki, d'iban wayoyin tayi ta fito dasu, d'aya d'akin ta nufa don tana tsammanin yana ciki, murd'a k'ofar tayi, aikuwa ta bud'e, ganin haka yasa Sumayya tayo gurin da hanzarinta zata shigo d'akin, Fareesah tayi saurin rufe k'ofar tare da sanya mata key, gano shi tayi a kwance rik'e da kansa, cike da tausayinsa ta isa gareshi, dukkanin k'arfinta ta saka ta d'ago kansa ta aza bisa cinyarta, ga mamakinta hawaye ta gani bisa kuncinsa, wani zazzafan tausayinsa taji ya kamata, lallai abun babba ne, tunda taga hawayen soja, duk tsawon shekarun da suka d'iba tare bata tab'a ganin ko da d'igon k'wallarsa ba, wannan ya tabbatar mata ba k'aramin ciwo yake ji a zuciyarsa ba, hannu ta saka tana goge masa hawayen, ji takeyi kamar itama ta fashe da kukan, wara idanuwansa yayi akan fuskarta, nan taga yadda idanuwansa sukayi jazur dasu na ban mamaki, a hankula ya rik'o hannunta cikin sanyin murya yace. "Zumata, ki dinga mini addu'a, duk da nasan kina yimin, wallahi ban san abinda ke damuna ba, nasan kwata ² bana saukewa Khadija da Fareeda hak'k'insu, amma ban san dalili ba, wani zubinma gara Fareeda tunda mahaifiyata tana tirsa sani akanta, amma Khadija ni na san har ga Allah tana matuk'ar hak'uri dani, don ba k'aramin k'wararta nake ba, kuma wallahi wani gefe na zuciyata yana matuk'ar tausayinta amma duk yayin da nayi yunk'urin tallafo rayuwarta sai naji na kasa, sannan na rok'eki dan Allah kar ki kuma yimini zancen Sumayya, wallahi kwanyata ba ta tab'a iya zurfafa tunani kan Sumayya, a duk sailin da nayi niyar yin hakan, na kanji kaina kamar zai dare ya rabu gida biyu, ni kad'ai na san irin azabar da nake sha, idan har kina son cigaban rayuwata to babu ruwanki tsakanina da Sumayya. ” Wani kukane yazowa Fareesah jin lafazinsa na k'arshe, to tabbas babu tantama Sumayya ta riga ta tsaface Miq, banda haka wannan wata iriyar rayuwace haka? Ganin tana kuka ya sakashi mik'ewa zaune ya rungumota jikinsa. "Sorry Zumata, bayan haka ban san me zan gaya miki ba ki fuskanceni, dan Allah ki cire dukkanin wata damuwa daga ranki, ko don lafiyarki da ta babynmu.” Shiru tayi masa ba tare da tace komi ba, sai shashshek'ar kukanta ne ke tashi kawai, bakinsa ya saka saitin kunnenta yana hura mata iska a hankula. Cike da takaici da bak'in ciki Sumayya ta bar bakin k'ofar, ganin Fareesah ta rufeta, d'aki ta koma ta d'auki wayarta ta danna kiran wayar Mom, ringing d'aya ta d'aga. Babu sallama ba komi ta hau fad'in. "Mom nidai na gaji wallahi, na k'agu naga Fareesah tabar duniyar Miq d'ina, zuciyar Miq an halicceta ne domin Sumayya kad'ai, nayi matuk'ar k'ok'arima da na kawo har iyanzu ma tare da wata cikin zuciyarsa, gashi ga dukkan alamu kamar ta san wani abu game da ni, dan haka wallahi a yau ko gobe zakiji labarin mutuwarta. ” "Dakata Sumayya, wai ke meyasa baki da hak'uri ne ko kad'an, ita gaggawa da kike gani k'arshenta ba ya yin kyau, domin daga shaid'an take, kika kaho har iyanzu ma tare daa ita, bare 'yan kwanakin da suka rage miki, kinsan sarai dai kika bata tasha yanzu zata haihu lafiya ba tare da komi ya samu abinda ke cikinta ba, itace kawai zata mutu, amma idan kika bari ta fara nak'udar shine burinmu zai cika.” "Nidai gaskiya na gaji Mom, kinga kuwa rashin mutumcin da take mini, yanzuma k'iri² ta hanani ganin Miq d'in, idan na cigaba da rayuwa da ita cikin duniyata, to tabbas nan da kwana biyu zakiji labarin mutuwata, don haka nidai zan bata, ko da yaron bai mutu ba ma kasheshi ta yadda muke kashe sauran.” Bata saurari me Mom d'in zata ceba ta datse layin tayi cilli da wayar kan gado, ta nufo d'akin kamar mahaukaciya, knocking take da iya k'arfinta kamar ta b'alla k'ofar ta shiga... Kuyi hak'uri na jina kwana biyu da kuke, da kuma gajeran typing, bamu da wuta ne har yanzu ba'a gyara ba, ba koyaushe zan dinga k'arar da chargin nawa ba a typing. Free page ya kusa zuwa k'arshe, don haka masoyana kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu. AL'K'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [23/2/2020/5:46PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat *GASKIYA D'AYA* Asisi B Aliyu Fitattu 6 na siyarwa ne, Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 FREE PAGE _______________ *TEN* Da gudu ya koma ya d'auko key d'in mota ya sunkuceta ya fita da ita da gudun gaske, Sumayya saurin d'auko mayafi tayi tabi bayansa, don ta san bazai zaman jiranta ba, cikin mota ya sakata ya zaga ya shiga mazaunin driver da hanzari Sumayya ta shiga gefen ko dai daita zamanta ba tayi ba yaja motar da gudun gaske, dama tuni an dad'e da wangale gate d'in, suna isa asibitin Emergency aka nufa da ita aka shiga bata taimakon gaggawa, daga miq har Sumayya sintiri kawai suke a bakin k'ofar d'akin da aka shiga da ita, Sumayya addu'a take Allah yasa su shek'a barzahu daga ita har abin cikin nata, yayin da Miq ke addu'ar Allah ya sauketa lafiya, gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa, ak'alla za'a d'auki wasu awoyi uku kafin likitan ya fito yace masa, sun samu numfashinta ya dai daita, amma kuma bata da k'arfin da zata haihu da kanta, ta riga ta galabaita sosai k'arfin nata ya k'are gaba d'aya, don haka aiki za'ai mata, abubuwan da duk ake buk'ata ya bashi, yaje ya biya kud'in da za'ai mata aikin, sannan ya kawo musu abinda suke buk'ata da kuma kayan haihuwa. Hawaye ne ke zuba a idonsa sosai yayin da yake saka hannu a takardar aikin da za'ai mata, gani yake kamar shi ya janyo mata, da ace ya fito a sanda take kiransa da duk hakan bata faru ba. Tunda aka shiga da ita d'akin da za'ai mata aikin suke sintiri a k'ofar d'akin shi da Sumayya, sosai itama ta nuna damuwarta a fili, ko wace addu'a tazo bakin Miq yinta yake gaba d'aya ya fita daga cikin nutsuwarsa, a k'alla sun d'ebi tsahon awonni hud'u basu fito ba, tun daga nan zuciyar Miq ta sare gaba d'aya, yana ganin likitocin sun fito k'irjinsa yayi wani irin bugu, kamar daga sama yaji d'aya daga cikin likitocin yana gaya masa sunyi nasarar ciro abinda ke cikinta, amma bata zo da rai ba ka shiga tana son ganinka, ya mik'awa Sumayya gawar yarinyar a kwali. Kalmar Innalillahi kawai bakinsa yake furtawa ya kasa ko da k'wak'k'waran motsi, ji yayi k'afarsa tayi masa wani d'an iskan nauyi dak'yar ya iya janta ya nufi d'akin, a hankula ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga. ________________ *KANO* Ashe Ummi tana cikin damuwa sosai b'oye mana takeyi, amma damuwar Yaa Nazee sosai tayi mata illa har ciwo yake neman fin k'arfinta, tsakiyar dare take tashi tasha kukanta, sannan tayi sallolinta na nafila takaiwa Allah kukanta, yaudai sosai ciwon yake son fin k'arfinta, ni kuwa tun tashina nake lura da ita ko gurin aikima k'in zuwa nayi, nima haka nake jin gab'b'an jikina duk sun sare, ji nakeyi duniyata tayi mini wani iri na da ban, irin wannan yanayin shi na dinga ji a sanda Abba zai bar duniyarmu, shiyasa yau gaba d'aya hankalina yake kan Ummi, tsorona kawai kada ta bar duniyata, don idan ta barta ban san yadda rayuwata zata k'are ba, gani nake ma gaba d'aya duniyata ta wargaje, ni da murmushi kuwa mun riga munyi bankwana, Allah ma ya kiyaye, shine abinda d'aya b'arin zuciyar tawa ya gaya mini. Duban Ummi nayi nace. "Ummi sai nake ganin kamar baki da lafiya. ” Murmushin k'arfin hali tayi ta shafa kaina gami da cewa. "Lafiyata k'alau Munassah kada ki damu yanayi ne kawai. ” Nidai kawai naji tane amma hankalina ya kasa kwanciya, kwata ² na k'asa d'auke idona daga kanta, nabi na manne mata, babu yadda ba tayi dani ba akan na tafi gurin aiki amma fir nak'i, duk sona da awara ranar ko gutsire ban iya sakawa a bakina ba har Inna ta gama sayar da ita, duk yanayin da nake ciki tana lura dani itama duk haka take jin zuciyarta wani iri. Rik'o hannuna tayi d'aya hannun nata kuma ta saka shi a kaina tana shafawa, kallona take, yanayin kallon da take mini kamar tana tausaya mini ne, tace. "Munassah, kiyi hak'uri da dukkan wani sabon al'amari da zaizo miki cikin duniyarki, ita rayuwa juyi² ce, kinga dai yadda rayuwarmu ta faro cikin jin dad'i da walwala, ba mu tab'a tunanin zata juya mu fuskanci rayuwa irin wannan ba, amma duk hakan yana cikin K'ADDARAR RAYUWARMU, jarabawa ce da Allah yake mana don yaga k'arfin imaninmu, don haka Munassah ina kuma umartarki da hak'uri akan dukkan wata rayuwa da zaki fuskanta anan gaba, kada kiyi k'azafi ga kowa, ki rayu da kowa lafiya, kada kici mutumcin kowa, ki zama ta kowa, kar kuma kici amanar wanda ya yadda dake, kiyiwa kowa kyakkyawan fata, kada ki tab'a damuwa da masu miki sharri ko hassada domin sune gishirin rayuwarki, idan kika rik'e wannnan babu abinda zai girgiza duniyarki, Allah ya albarkaci rayuwarki d'iyata ya baki ikon karb'ar ko wace iriyar rayuwar da zaki karb'a anan gaba da hannu bibbiyu.” A dabarance ta goge k'wallar idonta ba tare da na gani ba, ni kuwa kuka na fashe dashi don zuciyata ta kasa jurewa, ban san dalilin Ummi na yimini nasiha haka ba, duk da tana yimin d'in amma na yau da ban yake da na kullum, ganin ina kuka yasa Ummi ta shiga lallab'ani, kuma ta dinga k'arfafa jikinta don naji dad'i muka dinga yin hira gaba d'aya har Inna. Waje jen sallar la'asar jikin Ummi ya tsananta, duk dauriyarta sai da na gane na fita taro adai daita kawai don mu kaita asibiti, ko da na taro motar na dawo sai na tarar da ita jikin Inna, jikinta gaba d'aya ya saki, kan Inna kuma a k'asa tak'i d'ago ido ta dubeni, ga dukkan alamu kuka take, zaman 'yan bori nayi gaban Ummi ina rik'o hannunta........... Kaishhhh masoya a CIKIN DUNIYARMU anan na kawo k'arshen free page me bbuk'atar jin yadda duniyar su Miq, Fareesah, Sumayya, Kadija, Fareeda, Munassah take k'arewa yana iya biyo number da take a sama, sai na jiku masoyana kar ku manta yanzu aka fara tafiyar, littafin yazo muku da sabon salo tare da tab'a zuciyar me karatu. ALK'ALUMAN NAGARTATTU [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [24/2/2020/10:24PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat *GASKIYA D'AYA* Asisi B Aliyu Fitattu 6 na siyarwa ne, Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 _______________ *ELEVEN* *KANO* Hannunta na kama na d'aga sai naga ya saki ya dawo k'asa, wani kuka ne ya zo mini me d'aci, kuma ya tsaya iya mak'o gwaro, daga haka nidai ban san me ya kuma faruwa ba, na dai farka na ganni jikin Inna tana rik'e da carbi har lokacin hawaye na zuba a idonta, sai mutane dake zaz zau ne a d'akin, bin kowa nake da kallo kamar wata sokuwa, anan mukai ido hud'u da su Aysha suka cemini. "Sannu Teemah ya hak'uri? ” Rintse ja ja yen idanuwana na yi ya yin da k'wal k'walwata ta tuna mini abinda ya faru, wani d'aci zuciyata take mini, k'irjina nayi mini zafi da rad'ad'i, babu wanda zai fuskanci irin yanayin da nake ji sai wanda ya d'and'ani irin abin da na d'an d'ana, hannun Inna na kama na rik'e k'am nace. "Inna Ummi” Sababbin hawaye ne suka biyo kuncinta na mugun tausayina tace. "Kiyi hak'uri Munassah, Allah ya saka mana gado me wahala, duk tsananin k'aunarka da mutum, dole wata rana sai ya tafi ya barka, kuma kaima irin ranar tana nan tana fakon ka, Ummi ta tafi inda ba za ta tab'a dawowa ba, har an riga an dawo daga kaita, addurmu kawai ta ke buk'ata a halin yamzu tun daga yanzu ya kamata ki fara aiki da nasihar da ta bar miki. ” Kau da kaina gefe nayi, idanuwan gaba d'aya sun soye hawaye yak'i zuwa, kawai tasbihi nake ja a zuciyata. 'Wai meyasa Ummi ta tafi ta bar Duniyata? Bayan ta san Abba da Yaa Nazee sun dad'e da barin CIKIN DUNIYARMU, shine itama ta ta fi ta barni, yanzu ya take so na yi da rayuwata, dama ashe ta san mutuwa za ta yi shi ya sa d'azu ta dinga mini nasiha? Ya Allah ga baiwarka me raunan niyar zuciya, Allah ka jib'anci lamurana, ka bani ikon cinye dukkanin jarabawo yin da nake fuskanta cikin rayuwata, Allah Ubangiji ka sa hakan shine hanyar shigata jannatul firdausi, Amin ya Allah' Sai a lokacin wasu siraran hawaye suka biyo kuncina, na kuma rintse idona nak'i yadda na bud'esa ko kad'an, gani nake idan na bud'e zanga Ummita, wayyo rayuwa, shikenan ta tafi itama, ya Allah, na kuma furtawa a zuciyata don gudun yin sab'o, yayin da duka 'yan d'akin tausayina ya dinga tsin tsinka musu zuciya. ______________ *ENGLAND* A hankula ya tura k'ofar ya shiga, a kwance ya hangota an gark'ama mata wannan robar, ga na'ura a gefenta ta nan ake ganin numfashinta, zuciyarsa ce ta kuma tsin tsinkewa, tausayi da nadama gami da zazzafar soyayyarta su suka kuma lullub'esa, kamar mara laka haka ya taka ya isa gaban gadonta, hannunta ya kama ya rik'e k'am yana kallon fuskarta, gani yayi fuskarta ta kuma yin kyau, tana bada wani annuri, ga wani murmushi da take saki, kamar murmushin bankwana, baiyi aune ba, sai tsintar kansa yayi yana tsiyayar hawaye, wata takarda ta saka masa cikin hannunsa, sannan ta sakar masa sanyayyan murmushi gami da matsa hannunsa, ji yayi k'irjinsa ya buga a lokaci d'aya, yayin da ita kuma tayi wata shak'uwa, idanuwanta suka k'ak'k'afe na urar da ke gefenta ta tsaya cak da aiki, amma murmushin dake fuskarta bai b'ace ba ko kad'an. Kuyi hak'uri da wannan, nasan zaku ce yayi muku kad'an, wallahi kamar na kece da kuka haka na rubuta wannan page d'in. ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [25/2/2020/6:30PM] *FITATTU SHIDA* *CIKIN DUNIYARMU* BEBE'ARTH *HASKE A DUHU* Aisha M Mahmud (Meeesherh lurv) *DUHUN DAMINA* Maryamerh Abdul (Kwaiseh) *SARA DA SASSAK'A* Qurratul'ayn *ZAMANINA NE* Munayshat *GASKIYA D'AYA* Asisi B Aliyu Fitattu 6 na siyarwa ne, Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi: 07067364721 _______________ *TWELVE* Ba shi kansa ba hatta jinin jikinsa ji yayi ya daskare gaba d'aya, har doctor d'in ya shigo, su dama sun tabbatar da ba za ta yi tsawan rai ba, hakanne ma yasa ba'a fita da ita d'akin hutu ba, jan zani yayi ya rufe mata fuska, har lokacin Miq ya kasa ko da k'wak' k'waran motsi, Nurse ce ta shigo ta k'ofar baya hannunta d'auke da jaririya nad'e da shawul fari k'al, karb'arta doctor d'in ya yi ya d'ora ta kan cinyarsa, sai a lokacin doctor ya lura da suman da Miq d'in yayi, d'aukar jaririyar yayi ya mik'awa nurse d'in ita yace ta tafi da ita, sannan ya shiga bawa Miq d'in taimakon gaggawa bayan ya adana masa takardarsa, ganin duk taimakon da ya basa amma bai farfad'o ba, sai ya gangarosa akan gadon marasa lafiya don ya canja masa d'aki, anan ne Sumayya dake tsaye da gawar jaririyar farin ciki fal ranta, tun kan ma taji mutuwar Fareesan, amma kuma ta d'auko damuwa sosai ta aza bisa fuskarta, hankali tashe ta tunkari likitan tana tambayarsa me ya faru, shi kuma a lokacin ya kira ma'aikatan asibitin sun gungura gadon da miq d'in ke kai, kallonta yayi cike da tsana, amma ya shanye yace. "Ki kira can gida nigria ki sanar musu mutuwar Fareesah da abinda ta haifa, na saka a nema muku ticket kafin nan kan dare zaku isa nigeria, Miq kuwa ina jin sai nan da kwana uku zai iso, duk wanda ya tambayeki shi ki gaya masa haka, yanzu ki bada gawar yarinyar za'a had'ata da ta mahaifiyarta, kije gida ki had'a muku kayanku.” Yana kaiwa nan yabi bayan inda aka nufa da Miq don ya ceto rayuwarsa, yayin da Sumayya tayi zaman 'yan bori tana risgar kuka wiwi² sai da tayi me isarta, sannan ta rarrashi kanta ta mik'e, mota taje ta shiga ta nufi gida, wayar Mom ta fara kira ta yi mata albishir, me makon tayi salati sai ta saki wata uwar shewa, kashe wayar Sumayya tayi, haka kawai kuma sai taji wani b'ari na zuciyarta ba ya farin ciki da mutuwar Fareesan, inama kawai ta sani d'an cikin nata ta kashe kamar yadda ta ke wa sauran, wayar Khadija ta kira ta sanar mata, kuka Khadijan ta fashe dashi ta sume a zaune, Dad ta kira ta sanar da shi mutuwar, shi kuma a lokacin yana shirin shiga jirgi zai isa nigeria, saboda a yaune Allah ya bashi nasarar ciro itacen bishiyar, sosai mutuwar Fareesan ta dake shi, duk tsanin son ganin jikansa da yake son yi, sai yaji ko kad'an bai damu da mutuwarsa ba, kamar yarda ta mutuwar Fareesan ta dake sa, inama iya jaririn aka d'auke aka bar mu su Fareesan, bai aune ba sai ji yayi hawaye na sauka akan kuncinsa, wayar mahaifin Fareesan ya laluba don ya gaya masa mutuwar, duk da bai damu da rayuwarta ba, matarsa ta raba su. *KATSINA* G.R.A Gida ya cika damtsan da 'yan uwa da abokan arzik'i, domin mutuwar Fareesah ta zaga dangi, kowa ya iso ana jiran isowar gawarta, masu kuka nayi, masu farin ciki nayi, mahaifiyar Miq da danginta murna suke da mutuwarta, a cewar su itace tabi ta mallake Miq da dukiyarsa, yanzu dai gashi ta bar musu cikin duniyar, sai su kwashi abinda suke so, sai magariba gawar Fareesah ta iso nanfa gida ya k'ara b'arkewa da koke² ma'aikatan gidan kaf kuka suke da mutuwar Faresah, domin ta kasance me matuk'ar alheri a garesu, Khadija kuwa har aka yiwa Fareesah wanka ita da jaririyarta aka sallacesu ba ta san inda kanta yake ba. Jama'a dai masu raka ta gidanta na gaskiya Fareesah ta same su, sai fatan dacewa da gidan aljanna, domin ta samu shaidu a bakin mutane da dama, mahaifinta yaji mutuwar d'iyar tasa sosai, har sai da tsimin soyayyarta ya taso masa, yayi kuka sosai na tunowa da irin wahal halun da tasha a sanda tayi rayuwa a inuwarsa, har sai da Dad ya cirota daga k'angin rayuwa ya had'ata aure da d'ansa, gashi yanzu ta bar duniyar baki d'aya, sam bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ta dalilin kuma makirar mace da ya ja jibowa kansa bala'i. Daddy da mahaifinta su suka dinga karb'ar gaisuwa a bakin mutane tunda Miq ba ya nan, tun da Khadija ta far fad'o tak'i sakin jikinta, mutuwar Fareesah sosai ta girgiza duniyarta, Sumayya ma tana nuna damuwarta a fili don cire zargi daga idanuwan mutane, a haka dai suka ci gaba da kar b'ar gaisuwa har aka yi sadakar uku babu labarin Miq. ******** *KANO Tun ranar da Ummi ta rasu, rabona da d'an d'ana abu kenan a bakina, bana sha'awar komai dake cikin duniyar nan, babu kuma wani abu da zance yana bur geni a cikinta, lallami da nasihai ba wanda Inna ba ta yi mini ba, amma haka ta hak'ura don nak'i cin komai, ban da ruwa da nake sha, shi ma kad'an ne ke tafiya, sosai ake zuwar mana gaisuwa, 'yan Teemah Nazz kuwa babu wanda yazo in kika cire Baffa Amadu da matarsa da kuma Nucyy, itace k'awata kuma aminiyata a sanda mukai rayuwa a cikin gidan Teemah Nazz, sun tausaya mini sosai, da kuka muka rabu da Nucyy, ta karb'i number Inna saboda gudun wata rana, ni dama yanzu bani da wata waya, don bani da nutsuwar yinta ma. Sai a yau da akayi sadakar uku sai ga Baffa Sule, yace zuwa yayi ya d'aukeni wai Hajiyar Kaduna tace a bata ni, Inna tayi jan ido tace ba inda zanje, ko Hajiyar makka ce ba ta kaduna ba, amanata aka bata don haka babu wanda ya isa ya karb'e ni a hannunta, baran² dai sukayi da Inna har yace mu fice masa daga gidansa, hakanan dai muka d'ebi abinda zamu iya d'auka a cikin gidan muka fito ina wai wayen sa, domin anan ne na rasa Ummita. Yamma lis muka shiga motar katsina, ku gano mini sanda zamu isa, kifa kaina nayi na dinga risgar kuka wanda ya haddasa mini ciwon kai har da zazzab'i me zafin gaske, kan muci rabin tafiya ma na fara fita daga hayyaci na........ ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [27/2020/9:50PM] _______________ *THIRTEEN* *ENGLAND* Idan ya farka fusge² kawai yake yana wata iriyar firgita, hakanne yasa Doctor Hisham yayi masa alluran bacci masu matuk'ar k'arfi, wanda har sai da ya yi kwana uku kafin yasan inda kansa yake, a hankali ya bud'a idonsa da ya ke jin yayi masa matuk'ar nauyi, jin sa ya ke ma kamar ya kumbura, rik'e saitin zuciyarsa ya yi da ta ke masa rad'ad'i. 'Yanzu shi kenan Fareesah ta bar duniyarsa? ta tafi inda ba za ta tab'a dawowa garesa ba har abada, ta kuma tafi ta bar shi da gib'i a zuciyarsa, domin rashinta garesa hakan zai dinga azabtar da ruhinsa, Fareesah da ban ta ke a cikin zuciyarsa da ba zai iya misalta muku yarda ta ke ba, bai kuma sanin ta yi nisa cikin zuciyarsa ba sai da ya tabbatar da ya yi rashin ta gaba d'aya a cikin duniyarsa, wayyo mutuwa! Me ya sa ba'a shawara da ke ne? Dan da kinyi shawara da ni ba zan bari ki d'auke mini Zumata ba, ni zance ki fara d'aukewa ita ki barta, ya Allah' Ya fad'i hakan a can k'asan zuciyarsa, Dr.Hisham ne ya shigo, murmushi yayi don ganin ya farka, shi kuwa Miq ko kallon inda ya ke bai yi ba, toilet ya shiga ya had'a masa ruwa me zafi² don yaji dad'in jikinsa, da lallami da lallamawa ya samu ya shiga wankan, tun da ya fito daga wankan jallabiya kawai ya zira, ya jero sallolin da ake binsa, yana kuma kaiwa Allah kukansa, bayan ya idar ya jingina da k'arfen gadon, sai a sannan yaji hawaye masu matuk'ar d'umi na sauka akan kuncinsa, tausayinsa ne ya lullub'e Dr Hisham, lallai ya kamata yayi kuka, domin Allah ya d'auke masa macen da tafi soyuwa a ransa, tun da soyayyar da ya ke wa Sumayya ba daga Allah take ba, soyayya ce ta sihiri wacce take k'ok'arin juyar masa da k'wak'wal wa, me k'ok'arin saitasa a hanya ga shi kuma sun raba ta da duniyar baki d'aya, amma kuma ta bar abin da zai zame musu izina, wanda take fatan sanadiyar kasan cewar ta ne zai kawo kawo sauyi cikin duniyar Miq baki d'aya. Waya ya kira, yana ajiye wayar sai ga wata nurse ta shigo d'auke da jaririya a hannunta tana nad'e da wani shawul pink me matuk'ar laushi, kar b'arta Dr. Hisham yayi, nurse d'in ta juya ta fita, kallon Miq d'in yayi da ya tsunduma cikin kogin tunani, sai ambaliyar hawaye ake akan fuskarsa kamar wani mace, d'ora masa jaririyar ya yi akan cinya, d'agowa ya yi ya kallesa ya kuma kalli abinda ya d'ora masa, alamu yana son k'arin bayani, takardar da Fareesah ta bawa Miq da Dr.Hisham ya d'auke masa, ita ya d'auko ya basa kayansa, karb'ar takardar yayi yana war wa re wa, sai a lokacin ya tuna da Fareesah ta dank'a masa takarda a hannunsa, rungume jaririyar ya yi a k'irjinsa, yana jin soyayyarta na huda duk wata k'ofa ta zuciyarsa duk da bai san jaririyar waye ba. _Zumana, na san a san da zaka karanta sak'ona na riga da na jima da barin duniyarka, dan haka ina me neman afuwarka idan har na tab'a sab'a maka a zamana tare da kai._ _A yau Allah ya azurtamu da samun k'aruwa ta 'ya'ya biyu duk mata, kuma da kaina na haihu ba tare da an mini aiki ba, amma yarinya d'aya ba tazo da rai ba, ni na rok'i abokinka Doctor Hisham da yace yarinyar da na haifa ta mutu, kar a san 'yan biyu na haifa, saboda idan mak'iyanka suka san da rayuwarta to itama zasu kasheta ne kamar yarda suke kashe mana 'ya'yan da muka haifa_ _Na san baza ka yadda da magana ta ba, amma Sumayya tana d'aya daga cikin mak'iyanka, ba zance itace take kashe mana yaranmu a baya ba, saboda ba ni da wata hujja k'wak' k'wara, amma ina shaida maka itace ta zuba mini magani a tuwona dan naci na mutu ni da abinda ke cikina, ka duba camera da nace maka na saka za kaga komai, kayi bincike sosai akan mutanen dake zagaye da rayuwarka, ta hakanne zaka gano makasanka, bance ka aminta da kowa ba, ga yarinyarmu nan ka kula da ita kamar ina raye, kar ka bari tayi maraici ko kad'an, kuma ban yarda da kowa ya san da rayuwarta a duniya ba har sai asirin makasan babanta sun bayyana, Daddy kad'ai na aminta da ya san da rayuwarta a duniya, idan ta girma ka bata labarina ka gaya mata ba a son raina na tafi na barta ba, da zab'i aka bani bazan so na tafi na barta cikin tsumman haihuwa ba, ka gaya mata ina sonta, itama ta rayu da soyayyata._ Tun da ya fara karantawa yake zubar da zafa fan hawaye, Dr Hisham yace. "Bayan ka kawo ta, na samu na ceto rayuwarta, sai kuma haihuwa ta tawo gan ga² duka 'ya'yan biyu a lokaci d'aya suka fad'o, ni na tabbatar da d'aya ba tazo da rai ba, shine ta rok'e ni akan nace ita ta haifa kuma ba tazo da rai ba, ita kuma d'ayar aka fita da ita ta k'ofar baya, takadda da biro tace na bata don tana jin kamar mutuwa zatayi, tana cikin rubutun num fashinta ya fara ciccijewa, shine na saka mata robar shak'ar numfashi, tun da naga tana ta yafitar hannu nasan kai take so na kira mata, hakanne yasa nace kazo tana nemanka, abinda yasa kwa nace maka aiki za'a mata, don na d'auke hankalin Sumayya ne don tana da matuk'ar wayo da dabara, ni kaina na sha gaya maka ban yarda da Sumayya ba, amma duk sanda zan kawo maka maganarta da fad'a muke k'arewa, idan da baka tashi ka binciki me ke faruwa da rayuwarka ba, ka tashi tsaye yanzu don ganin rayuwar jaririyar nan cikin duniyarka....... ” ALK'ALUMAN NAGARTATTU [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [6:37PM/1/3/2020] _______________ *FIFTEEN* Motarsu zata shiga cikin gidan kenan aka kira wayarsa, ganin Daddy ne me kiran ya sa ya yi picking da hanzari. "Sadauki, idan ka iso kafin kaje gida ina son ka fara biyowa ta gurina. ” "Toh” Yace masa ba tare da yace masa ya riga da yaje gida ba, yacewa driver d'in nasa me suna Jhon. "Mu juya k/durbi.” K'ok'arin kwana ya fara yi da motar, yayin da motocin da ke biye da su suma sukai kwana suka mik'i titi, sun san bazai huce Daddy ne yayi masa kiran gaggawa ba. Tunkan su iso me gadi ya riga ya wangale musu gate, saurin bud'e masa motar aka yi ya fito cike da k'asaita, fuskar nan kamar hadarin kaji, cikin gidan ya dosa shi kad'ai ba tare da wani ya bi bayansa ba, saboda sun san ba ya son hakan, suna gama aikin sune yayin da ya shigo gida. Mom ya tarar a falo, tun da ta jiyo jiniyarsu zuciyarta ta gama b'aci, wata muguwar tsanarsa take ji tana taso mata amma ta yi k'ok'arin danne ta tun kafin ya shigo, hannu ta bud'e masa kamar yadda ta saba a duk sailin da ya yi tafiya, murmushi yake ya isa gareta, kamar yadda itama ta d'auko murmushin k'arya ta aza bisa fuskarta, rungume shi tayi tana shafa kansa. "Welcome My Son.” Sannan ta karyar da muryarta gurin fad'in. "Ya k'arin hak'urinmu?” Barin jikinta ya yi, yace. "Alhmdlillh Mom, na sameku lafiya? ” "Lafiya lau. ” Tace tana jan hannunsa zuwa saman Daddyn, kallonta kawai Daddy yake, yadda ta k'ware da nuna yaudararriyar soyayya, murmushi yayi yana kawar da damuwar da ke ransa, sai da suka zo har gaban Daddyn sannan ta saki hannunsa, ta juya tana bari ta saka a kawo masa abin motsa baki, durk'usawa yayi gaban Daddy yana gaishe shi, hannu ya saka yana shafa kansa yace. "Allah ya yi maka albarka Sadauki, ya k'arin hak'urinmu?” "Amin ya Allah Dad, hak'uri Alhamdlillah.” mik'ewa Dad d'in ya yi yana me d'aukar hularsa da ke kan kujera yace. "Tashi muje fita zamui.” Ba tare da ya tambayeshi inda zasu ba ya mik'e ya biyo bayansa, sun fito kenan ita kuma Mom zata shigo da tray a hannunta sukai kacib'is, damuwa ta d'ora kan fuskarta gami da cewa. "Ya zaka fito bayan baka motsa baki ba? ” zamu fita da Dad ne, amma ki ajiye mini in na dawo zanci, kamar sakara haka ta bisu da kallo ba tare da ta tambayi Dad d'in inda zasu ba, sab'anin da da ko wani hali su biyun suke ciki a gabanta za'a kashe matsalar, babu wani sirri tsakanin Daddy da Miq wanda Mom bata sanshi ba, zuciyarta ce ta kasa nutsuwa har sai da ta kira wayar Sumayya ta gaya mata abinda ke faruwa, Sumayya tace. "Shiyasa kenan bai shigo ba, ina ta zaman jiransa, to ma dai ko me suke k'ullawa dole mu sanshi, tare da yaransa suka fito? ” "A'a naga motar Dad d'in suka shiga yanzu suke k'ok'arin fita. ” "Ok tom bari na saka Rahama ta taresu ta bi bayansu don ta gano mana inda zasu. ” "Allah yayi miki albarka. ” Mom tace tana ajiyar zuciya, sai taji hankalinta ya d'an fara kwanciya ta kuma cewa. "Amma sai kince ta lura fa sosai kar wannan kumurcin ya gano ta. ” "Kar ki damu Mom Rahma ta gwanance a bin mutum a baya ba tare da ya ankare shi take bi ba.” "Tom shikenan maza kirata naga sun fita yanzu. ” tana gama fad'in haka ta datse layin ta zauna kan kujera tana dafe kai. Daddy ne ke jan motar Miq na gefensa suna hirarsu ta d'a da mahaifi, wanda ma mafi akasari akan aikinsu suke tattaunawar,a haka suka gangaro kan mutuwar Fareesah, anan ya zayyanawa Daddy duk abubuwan da suka faru. Tun isowar su babban titin da zai kar kasa su gida hud'u yake ankare da wata mota dake bin bayansu amma kuma bai gayawa Dad ba, duk yadda akayi me bin bayan nasu k'wararre ne, yasan abinda yake yi, murmushi kawai ya saki ya turawa Faisal sak'o ta waya. " _Kuzo tare da wasu mutanen, amma kar ka kira su john su na barosu gida su jirani na dawo, muna kan titin UMYUK wata mota ce ke bin bayanmu, ina so ku gano mini mutumin dake cikin motar kawai, motar bak'a ce k'irar venza amma an cire number ta_ Cigaba sukayi da hirarsu da Dad hankali kwance, shi kuwa Faisal yana ganin sak'on suka bazamo suka taho, kar kasuwa suka yi har suka cimmasu, suna ganin motar su Miq ta huce suka had'a wani uban goslow, dukan setiarin Rahma tayi cike da mugun b'acin ran ganin abinda ke faruwa, gashi har motar ta shige ta. Ji tayi ana k'wank'wasa glass d'in motarta, zuge glass d'in tayi, ganin mutumin dake tsaye gabanta sai da k'irjinta ya buga. "Hey Madam, ina number motarki? ” ya fad'a da wata iriyar muryarsa da kaji ta kasan bai iya hausa ba sosai, d'auko number motar ta yi ta mik'o masa gami da cewa. "Cirewa ya yi zanje yanzu a saka mini. ” bai yarda ba sai da ta d'ebo masa takardun motar dukansu ya duba sannan ya bata, Faisal yana gefe yana ganinta ya ganeta, wani murmushin takaici ya saki, don ya san Sumayya ce ta saka ta, amma har yanzu mai gida yak'i fahimtar wani irin zama Sumayya take yi dashi. Ko da goslow d'in ya ragu kwata² Rahama ta rasa wata hanya su Miq suka bi, haka ta juyo cike da sanyin guiwa, ta kira Sumayya ta sanar mata, ita kanta Sumayya ba taji d'ad'i ba sam, addu'arta ma Allah yasa ba ganowa Miq d'in ya yi ana binsa a baya ba. Gurin Malam Jadda su Daddy sukaje, ya basu addu'oi masu k'arfi da zasu lazimci yi, ta hakanne ragowar tsafin dake jikinsu zai sakesu kuma ko da wani aka yi musu bazai shige su ba, sai da ya basu rubutu suka sha a gurin, saboda gudun kar su tafi dashi matansu su gano suna neman magani, godiya suka yimasa suka ajiye masa alheri me yawa, Daddy yaji dad'in maganinsa saboda yaga canji sosai gurin Miq, tunda har ya bud'i baki yace yana zargin Sumayya da mutuwar Fareesah, ai kuwa an samu babban cangi, kuma har ya iya b'oye mata yarinyar da aka haifa masa tana raye, sakamakon da da duk haihuwar da Fareesan za ta yi Sumayya ce take fara d'aukar jariran, ai kuwa yanzu dole ya godewa Ubangiji, ya kuma godewa amininsa da ya jajirce gurin ganin sunzo gurin malamin. A hanyarsu ta dawowa ma hirar Sumayan sukai ta tattaunawa Daddy yana k'ara masa haske akan irin makircin Sumayya da uwarta, kuma hatsabibabbu ne dole sai a hankula za'a d'ana musu tarko, don muddin baka iya kama b'arawo ba to wata rana shi zai kama ka, dan haka dole ne suma su saka rigar yaudara suci gaba da nuna musu har yanzu tsafinsu yana aiki a jikinsu hakanne zasu samu muk'ullin nasarar da suke nema. Bai yarda ya shiga ciki ba suka yi sallama da Dad gudun kar Mom ta matsa masa sai yaci wani abun kawai ya shiga mota suka bar harabar gidan, Shinkafi yacewa John ya nufa da shi, sauran motocin suka rufo musu baya, jiniyar motocin su ce kawai ke tashi a titi har suka isa shinkafi, dama tuni me gadi ya jiyo jiniyar tasu ya wage musu babban gate d'in gidan duka motoci hud'un suka shige ciki, bud'e masa motar akai ya fito ya nufi ciki. Mudansir k'aninsa ya gani da wata yarinya da bai san wace ba a falo suna shek'e ayarsu, ransa yaji ya mugun b'aci, ya tsani wannan halayyar, amma duk sanda yazo gidan sai yaci karo da irin haka, ba damar yayiwa Inno maganar sai tace babu ruwansa, ya barsu su wataya su da gidan mahaifinsu, rayuwar turai sukeyi ba irin rayuwarsa ta gidadawa ba, wani siririn tsaki yaja, ya daka musu wata uwar tsawa, sai a sannan suka ankara da mutum a tsaye a kansu, saurin sakin juna sukayi, mudansir yayi saurin yin ciki da gudu saboda bai manta irin masgar da yasha ba a wancan karan da ya tab'a kamasa, amma ranar Inno ba ta nan, shiyasa ya samu damar jibgarsa iya san ransa, wani kallon banza da k'yama ya jefi yarinyar dashi, sim² tayi ta fice tana duk'ar da kai. "Kai kuma meye haka? ” Inno ke cewa Mudassir dake faman b'uya a bayanta, ya kasa magana sai nuna mata hanya yake da hannunsa, siririn tsaki taja ganin Miq yakewa wannan mak'yar k'yatar........... [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [29/2/2020/7:55PM] _______________ *FOURTEEN* Kuma matse yarinyar yayi a k'irjinsa kamar ance za'a k'wace ta, yana jin wata zazzafar soyayyarta na shigarsa, d'agota ya yi ya na kallon kyakkyawar fuskarta, ya kasa gane tsakanin shi da Fareesah da wa yarinyar take kama, amma dai farar fatar Fareesah ta d'auko, bakinsa ya saka a kunnenta ya yi mata addu'oi gami da mata hud'uba, sannan ya d'agota ya ci gaba da kallon fuskarta hawaye na d'iga a idonsa. "Na yi alk'awarin baki kulawa fiye da rayuwata, kuma na baki dukkanin wata soyayya, ba zan barki kiyi maraici ba kamar yarda mahaifiyar ki tace, kuma na miki alk'awarin yin bincike akan abinda Sumayya ta bawa Fareesah, wallahi ko wa na samu da hannu a kisan mahaifiyarki bazan barshi ba ko kad'an, Allah ya bani ikon rik'eki amana da cika miki alk'awarin da na d'aukar miki, ya kuma raya mini ke cikin aminci da salama bisa koyarwar Ma'aiki (S.A.W) Amin.” Ta dad'e sosai rungume a k'irjinsa daga bisani ya mik'awa Dr.Hisham ita. "Wa ka ka kaiwa ita, yau har tsawan kwana hud'u? ” "Matata Haaya na kaiwa ita ta ke bata madara. ” "Ka maida mata ita, idan na yanke yadda za'ayi da ita zan dawo, yanzu zanje na nemi ticket a yau nake son isa nigeria.” "Da zaka bar mana ita, wallahi nayi maka alk'awarin rik'eta amana ba tare da ta yi kukan maraici ba.” "Zancen na bar Fareesah a hannunka Dr. bai taso ba, Sumayya ta san matarka k'aramin ciki ne da ita, dole zata bi diddigin ta yadda akai aka samu wannan yarinyar, kuma ta san da cewa kaine ka karb'i haihuwar Fareesah, ina son yiwa Sumayya wasa da hankali fiye da yadda tayi wasa da nawa, ka yi hak'uri Dr. wai ba na hanaka bane don ba zaka iya rik'e mini ita ba sai don wannan hujjar tawa, na gode k'warai da gaske, Allah yabar Zumunci.” kallonsa Dr. d'in ya yi yace. "Wani suna ka saka mata?” "FAREESAH.” "Allah ya raya mana.” "Amin, muje ka sauke ni gida. ” Fitowa su ka yi ya bawa Nurse Fareesan akan ta mai da ta gida, shi kuma yaje ya sauke Miq d'in a gidan. Tun da ya shiga gidan mamakin Sumayya kawai yake, ya kuma gas gata zancen Fareesah domin ya nemi camera sama da k'asa ya rasa, da dukkan alamu Sumayyan ce ta d'auke, koma dai mene ne ya yiwa kansa alk'awarin bincike akan duk wani me motsi cikin duniyarsa, zai shayar dasu ruwan mamakin da basu tab'a tunanin shansa ba, kaya ya sauya zuwa k'ananun kaya da suka kuma fito da kyahun haibarsa, danma fuskar nan a murtuke take kamar murmushi bai tab'a zama akanta ba, babu abinda yake matuk'ar k'ona masa rai irin yadda Fareesah ta dinga kiran sunansa akan ya kawo mata d'auki amma yayi biris da ita, zuciyarsa na san zuwa amma gan gar jikinsa ta hana. Ko da ya je ya samu jirgi zai tashi zuwa nigeria k'arfe biyu dai², don haka sai ya komo gida kafin lokacin ya cika. *KATSINA* ______Kafin mu isa katsina na fita hayyacina sosai, muna sauka daga mota na shiga shara ra amai, cike da tausayawa Inna take duba na tana jero mini sannu, mota ta tsayar mana da zata kaimu gidan da take a zaune. G.R.A naji tace da shi, muka shiga, a k'ofar wani danka'areran gida 50 by 50 ya ijiye mu, duk tsaruwar Teemah Nazz, sai naga wannan gidan ya taka shi a kyahu sosai wai tun kan ma na shiga ciki, sai da ta k'wank'wasa me gadin a tsorace ya dinga tambayar waye, ya yi tambayar ne ma kar yaje uban gidan nasa ne yayi isowar dare, Inna ce ta yi masa magana sai naga ya bud'e, gaisawa sukayi sama² saboda ta na rik'e dani, wani yanki naga munbi daga gefen gidan muka tsaya bakin wata 'yar k'ofa, muk'ulli ta saka ta bud'e sai gamu cikin wani falo me matsakaicin kyau, d'aki d'aya ne kuma a cikinsa, cikin d'akin muka shiga ta kwantar da ni akan gado, ta shiga toilet ta had'a mini ruwa me d'an d'umi naje nayi wanka, ko da na fito daga wankan sai na tarar ta had'a mini tea me d'an kauri, kasancewar ta na da komi na buk'ata a ciki, bayan na sha ta bani paracetamol shima na sha, ban jima da shansa ba wani wahalallan bacci ya kwasheni, ba ni na farka ba sai da ana kiraye²n sallar asuba, tun da Ummi ta rasu rabon da nayi bacci me nauyi irin wannan, garau da ni na farka, amma sai na fad'a cikin tunanin rayuwata tun da ba sallah zanyi ba ina cikin hutu ne. Da gari yayi haske ne bayan munyi wanka mun shirya, sai Inna tace mini bara ta shiga su gaisa da mutanen gidan, ni ba zan bita ba sai me gidan yazo ta gabatar da ni a gurinsa tukun, to kuma sai ga Inna ta dawo tana kuka ba, hankalina ne ya tashi na shiga tambayar ta lafiya, tace mini matar me guidance ta rasu yau kwana uku kenan, tana da kirki wallahi babu ruwanta, ta iya zama da duka kishiyoyinta k'alau, haihuwarta takwas duk suna mutuwa, wannan shine na tara ta mutu itama yarinyar ta mutu, ni kaina sai na ji ba dad'i naji ina tausayawa me gidan. Tun tasowar jirginsu ya kira Faisal ya sanar masa, yayin da shi kuma ya tanadi motar da za'aje d'auko sa, tuni motoci hud'u na alfarma sun isa filin jirgi don tarosa, gaba d'aya yaransa ne a cikin motocin, yana fitowa daga jirgi gaba d'aya suka sassara masa, sai suka ga fuskarsa ta kuma murtukewa akan ta da, ko da yake ai dole ne wannan mutuwa da aka zabga masa, bud'e masa gidan baya aka yi ya shiga nan motocin suka fita daga filin jirgin a layi. Jiniyar motocin su ce ta isa ga me gadi tun shigowar su layin, don haka tun kan su k'araso ya riga ya wangale gate d'in, Sumayya da fitowarta daga wanka kenan ta jiyo jiniyar sai ta saki murmushin farin cikin Miq d'inta ya iso gareta, yanzu babu wata mace cikin zuciyarsa da zasuyi go gayya da ita........ ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [6:55PM/ 9/3/2020] Follow me on wattpad @Rashuna Fitattu shida na siyarwa ne idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tuntub'emu ta wannan layin 07067364721. __________________ *SIXTEEN* Tura sa gabansa ta yi cikin yanayi na b'acin rai tace. "To gashinan dake sa na gani, tun da kai baka da mutumci baka kuma da zuciya, kare yabi duk ya cinyeta, ban da haka sau nawa zance maka ka fita sabgar yarana? Ka barsu su mori k'uruciyarsu don kai kana rayuwar gida danci sai kace kowa ma sai ya yi, to ka bar ganin ran nan ka dake shi na k'yaleka, to wallahi ka kuma kuskura hannunka ya tab'a jikinsa sai ka fuskanci b'acin ran da ban tab'a saka ka ciki ba.” Wani k'ulu lun bak'in ciki ne ya tokare masa wuya har wani d'aci² yake masa amma haka ya danne dukkanin b'acin ran da yake ji ya d'auko daraja da martaba ta mahaifiya ya risina yana ba ta hak'uri, Mudan kuwa tuni ya sirare ya gudu, ba tare da tace masa uffan ba ta k'arasa falo ta zauna kan kujera, haka ya kuma danne zuciyarsa da take mugun taso masa ya biyo bayanta, kuma risinawa ya yi a gabanta yana gaisheta, fuska kawai ta yatsina ba tare da ta amsa gaisuwar ba tace. "Me ya hana ka tura musu kud'i wannan watan? ” "Ban samu nutsuwa bane, ga kuma rashin da ya same mu.” Ya ce mata hakanne kawai amma a zahirin gaskiya ya yi wa kansa alk'awarin bazai kuma tura musu kud'i suna kashesu ta hanyar banza ba, ya shirya d'aukar dukkan wani mataki da Inno d'in zata d'auka. "Mutuwarta ba ta dame ni ba, don ni har na manta ma da anyi ta, don haka ka tura musu kud'i a yau d'in nan, don na gaji da rigimar da suke mini akan ba kud'i a Accaunt d'insu.” "Tom shikenan Inno, insha Allah zan tura musu.” "Yauwa to, sai kuma maganar Fareeda naji matsaloli da yawa daga gareta, watakan wulak'anta amanar da na baka kake yi saboda baka sona kafi son mahaifinka shiyasa kafi daraja amanar da ya baka, ko kuma dan itace ke haifa maka 'ya'yan da basa rayuwa, saboda 'ya'yan Allah bani ne don aci ga'do? ” Kasa magana ya yi tsabar jin yadda rad'ad'in magan ganunta ke tafar fasa zuciyarta, cigaba tayi da zuba masa ruwan masifa har da cewa a cikin watan nan taji labarin cikin Fareeda idan kuwa ba haka ba za ta yi matuk'ar sab'a masa, shi dai bai tanka mata ba ban da hak'uri da yake ba ta ya taso ya fito zuciyar nan tasa kamar zata kama da wuta, ido biyu su ka yi da Mahbub dake tsaye bakin k'ofa yana tsiyayar hawaye na tausayin wan nasa, ya rasa me yasa Inno take yimasa haka, bayan shine me matuk'ar yimata biyayya da kuma faranta masa rai, ji yayi zuciyarsa ta kuma karyewa amma ya danne ta saboda kada yaransa suga hawayensa, amma alamun b'acin rai gaba d'aya sun bayyana kan fuskarsa, girgiza kafad'ar Mahbub ya yi alamun kada ya damu ya fice, ita kuwa Inno k'wafa ta yi a ranta ta na cewa. 'Dole gobe na ziyarci malamina, don na fara ganin wasu sababbun al'amura na kunno kai.' Key ya sakawa phart d'insa don ya san Sumayya taji shigowarsa kuma wajibine sai ta biyo bayansa shi kuma a halin da yake ciki yana buk'atar kad'aici, rage kayan jikinsa ya yi ya fad'a toilet, ruwa ya sakarwa kansa ko zaiji sanyi a zuciyarsa, amma sanyin ya gaza zuwa har sai da ya had'a kansa da guiwa ya shiga risgar kuka, don yana jin wannan ce hanyar kawai da zata rage masa zafin rad'ad'in da yake ji a zuciyarsa, 'Wai me yasa ne duniyarsa tazo masa a haka, a yaushe ne kuma zaiyi alfahari da duniyarsa, ya rasa soyayyar mahaifiya tun yana tsumman goyo, haka ya taso rayuwarsa cikin garari mahaifinsa ne kawai ke k'aunarsa fiye da k'aunar da yakewa kansa, a tunaninsa Mom ce ke masa soyayyar da ya rasa gurin mahaifiyarsa ashe yaudararriyar soyayya take masa, farautar rayuwarsa take tun yana yaro, me yasa Allah bai bata sa'ar rabani da rayuwar duniyar baki d'aya ko na huta da rad'ad'in da nake fama da shi na zuciya?' Astagfirillah ya shiga na na tawa cikin zuciyarsa don ganin yana k'ok'arin yin sab'o, Allah yana rubutawa dukkanin wani bawansa irin rayuwar da zaiyi cikin duniya tun kafin yazo cikinta tana nan tana zaman jiransa, an d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe, yana matuk'ar godiya ga Ubangijin da ya jarab ceshi da irin wannan rayuwar, yana kuma fatan ya cinye wannan jarabawar da kyakkyawan sakamako. Kukan da ya samu ya yi sai yaji zuciyarsa ta d'an yi sanyi, yayo wankan ya fito, jallabiya ya saka ruwan toka da ta saukar masa har k'asa,ya feffeshe jikinsa da turaruka masu dad'in k'amshi, masallaci ya nufa don yaji ana kiran sallar la'asar hakanne ma yasa ya d'auro auwalarsa, bayan ya gabatar da sallar ya dad'e yana lazumi daga bisani ya mik'awa Allah kukansa, yana fitowa daga masallacin phart d'in Sumayya ya nufa, nocking d'aya yayi aka zo aka bud'e, Nana ce 'yar aikinta da hanzari ta bashi hanya tana risinawa had'e da d'iban gaisuwa, cikin kulawa ya amsa gaisuwarta ya nufi d'akin Sumayyan, tana kwance a gado tayi zurfi cikin tunanin dalilin da yasa Miq d'inta ya yi mata haka, ace ya shigo cikin gidan nan tun d'azu baizo gareta ba ita kuma taje ta tarar ya sakawa k'ofarsa key, ko dai mutuwar ce har yanzu ba ta sakesa ba? Ta tambayi kanta, sai kuma ta bawa kanta amsa da ai ko mutuwar ce ba ta sakesa ba yaci ace ya nemeta, ba taji alamun shigowarsa ba sai dai k'amshinsa tuni sun kawowa k'ofofin hancinta ziyara, lumshe idanuwanta tayi ta wara su bisa kyakkyawar fuskarsa, kallon juna suka tsaya suna yi, shi yana mamakin dalilin da yasa ta sakawa zumarsa abinda taci ta mutu, yayin da ita kuma take jin zazzafar soyayyarsa na kuma bijiro mata, tashi ta yi taje ta fad'a jikinsa ta na sakin kukan kissa, wani takaici yaji ya kama sa, amma haka ya danne domin yana buk'atar nasara akan dukkanin mak'iyansa na b'oye don haka dole ne ya saka rigar yaudara, wata kyak kyawar runguma yayi mata a k'irjinsa ya shiga tambayar ta abinda ya faru yana yi kamar yana mata rad'a a kunne. "Kawai naji ba dad'i ne ace wai ka shigo gidan nan tun d'azu ba tare da idanuwana sun sauka a kanka ba, amma tunda yanzu na ganka ka wanke laifinka, ya k'arin hak'urinmu, da kuma k'arfin jikinka?” Wani birkitaccen murmushi ya saki da yake kuma birkita ta cikin zallar k'aunarsa da shauk'insa kana yace. "Naji dad'i da na wanke laifina don bana buk'atar nayi laifi ko kad'an gurin gimbiyata, hak'uri Alhamdlillah, nima kuma naji sauk'i.” "To Allah Ubangiji ya jik'anta yasa aljanna ce makomarta, ya k'aro mana dangana a zuk'atanmu” "Allahuma Amin.” yace yana k'ok'arin zare ta daga jikinsa ita kuma tana k'ara shigewa jikinsa a kunne ya rad'a mata. "Pls kiyi hak'uri mana, da daddare har sai kin gaji da kwanciya a jikina. ” "Ba na fatan ganin ranar da zan gaji da kwanciya a jikinka Miq, ina zaka? ka barni mana a jikinka pls.” "Zan lallek'a su ne naga ya suke. ” Ji tayi k'irjinta ya yi wani irin bugu, wani azababben kishi ne ya taso mata iya wuya amma tayi k'ok'arin danne shi, murmushi ta k'ak'alo tana sakin fara'a tace. "Amma naji dad'i sosai da hankalinka ya karkata garesu, dama haka nake so ko da yaushe ka dinga kwatan ta adalci a tsakaninmu. ” Tana kawowa nan ta bar jikinsa, murmushi shima ya yi yace. "Ai na san k'aunar da kike mini baza ta bari ki so na tashi ranar alk'iyama da shanyayyen b'arin jiki ba. ” Ba tare da ya jira amsarta ba ya fice daga d'akin ya barta cikin tunanin maganarsa, a dai² phart d'in Fareesah ya tsaya ya k'ura masa ido kamar ance zai ganta a tsaye a gurin, ganin hawaye na son sauka kan kumatunsa yasa shi barin gurin ya nufi phart d'in Khadija....... [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:4PM/10/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *SEVENTEEN* A kwance take a tsakiyar gado ta yi matuk'ar nisa cikin tunanin yanzu ita haka rayuwarta za ta k'are tana kallon Sumayya tana aikata mugayen aiyuka amma babu halin da zata tona mata asiri? Yanzu dai ga shinan tayi nasarar kashe Fareesah da Babyn cikinta, yanzu kuma kowa zata kashe nan gaba, cikin ita da Fareeda ko wace zata samu ciki? Inama ace itace zata samu ciki ko ta kashe ta ta wuta da wahal halun rayuwar da take ciki, tun tasowarta take rayuwa cikin k'unci babu wanda ya damu da irin rayuwar da take ciki, sai Miq da ya tsamo ta cikin k'angin rayuwa kuma ya kawota cikin duniyarsa me matuk'ar rikici da rikitarwa. Tsabar tayi nisa cikin tunanin ba taji alamun shigowar mutum ba sai saukar tafin hannunsa akan kuncinta taji, a razane ta bud'e ido, don ta yi matuk'ar tsorata, ba ta tab'a tunanin ganinsa ba, ko a mafarki ba ta tab'a tunanin akwai ranar da Miq zai tako k'afarsa zuwa d'akinta ba, tun da ya aurota ya kawo ta gidansa bai kuma tako k'afarsa cikin d'akinta ba, idan har ta na son magana da shi sai dai taje phart d'insa ta same shi. Murza idonta ta yi don ta kuma tabbatarwa da kanta shi d'inne, yayin da shikuma tausayinta yayi matuk'ar kama masa zuciya, janyota jikinsa ya yi ya rungume ta yayin da ita kuma ta saki wani marayan kuka me k'arasa raunana zuciya, kuka take yi sosai kukan da ya dad'e yana cinta a zuciya amma ba ta samu ya fita ba sai yanzu da ta samu babban masauki, bubbuga bayanta yake yana lallashin ta kamar wata k'aramar yarinyar, ya san da ya cutar da rayuwarta, kwata² ba ta samun kulawa a gurinsa, yanzu da ace mutuwa ta riske shi ba tare da ya gyara kuskurensa ba me yake tunanin zai tsinta a lahira? Cikin raunanniyar murya da nadama yake cewa. "Ki yafeni Khadija, ki kuma bani damar gyara kuskuren da na tafka duk a baya.” Kasa magana ta yi har sai da tayi kukanta me isarta, kana tace. "Ban tab'a rik'eka a zuciyata ba, a kuma ko wace rana sai na nema maka yafiya gurin Ubangiji, idan mutum yayi maka alkhairi daga baya yazo ya maka sharri to ba'a son ka dubi sharrin nasa ka dinga tuno alkhairinsa hakan ne zaisa ka yi yafiya gareshi, don haka alkhairinka gareni bazai tab'a sakawa naga laifinka ba Miq, kayi matuk'ar nisa a zuciyata, nisan da bazan tab'a iya dawo da kai baya ba. Ya hak'urinmu na Fareesah?” Jin kalaman nan nata sai suka kuma k'ara mata girma a zuciyarsa. "Hak'uri Allahamdlillh Khadija, na gode Allah da yasa kika zamo mace mai duba alkhairi ba sharri ba, nayi alk'awarin gyara kuskurena kuma ina fatan Allah ya shige mini gaba. ” "Allah ya rahamsheta, ita kuma yarinyar da muka rasa Allah yasa me cetonmu ce, ya kawo mana wasu masu albarka.” "Amin ya Allah, me ke damunki haka duk naga kin kuma ramewa? ” "Mutuwar Fareesah ce ta dokeni wallahi, kawai sai fatan Allah ya k'ara mana dangana. ” zameta ya yi daga jikinsa yana k'ok'arin mik'ewa. "Ya kamata dai kije kiga likita, gobe da safe zan saka a kaiki insha Allah, bari na lek'a Fareeda. ” "Tom Allah ya kaimu, gashi bani da komai na d'an tab'awa saboda ban saka ran ganinka ba.” "Kar ki damu.” Kawai yace mata yana ficewa daga d'akin, tasowa tayi ta rakosa har bakin k'ofa. A falo ya tadda Fareeda ta na waya, ta na ganinsa ta yi saurin katse wayar, ba tayi tunanin zai neme ta ba ko kad'an, duk yadda akai Inno tayi masa fata² ita kuwa ba ta san yanzu ta gaji da zama da shi ba, hanyar da zai bata takar darta kawai take buk'ata, tun da dai babu amfanin auranta da shi, abinda akayi auran don shi bazai tab'a yuyuwa ba, to zaman me zata zauna yi? Ana yin sadakar bakwan Fareesah zata nemi takardar ta. Tsira mata lumsassun idanunsa ya yi, ya na mata kallon tuhumar da ta tsorata ta bakinta na rawa ta shiga gaishe shi, wani shegen murmushi ya saki ya amsa gaisuwar ta ta gami da cewa. "Na sameki lafiya? ” "Lafiya lau.” tace ba tare da ya kuma cewa komi ba ya fice, sashen Inna ya nufa yana sakin murmushi don ya san zai samu kulawa matuk'a, knocking ya yi a lokacin Inna na toilet sai Munassa dake zaune ta jingina bayanta da kujera ta zurfafa cikin matuk'ar tunani, Inna ce ta yi mata gyaran murya sai a sannan ta ankara, ji tayi k'irjinta ya bada wani irin bugu, jiki ba k'wari taje ta bud'e k'ofar, idanuwansu ne ya gauraya guri d'aya, a lokaci d'aya bugun zuciyarsu ya sauya k'irjinsu ya shiga dokawa, juyawa ta yi ta koma ciki shi kuma ya shigo zuciyarsa cike da tunanin wace ce ita? Cikin d'aki ta shige ba tare da ta tsaya a falon ba, dai² nan Inna ta fito, fuskarta ce ta fad'ad'a da murmushi ganin Miq a tsaye, "Ka tsaya ka zauna mana.” Tace da shi, ta shiga kitchen ta d'auko plate nd knife, Apple ta d'auko a fridge ta yan yanka a plate d'in ta had'o da lemon gouva ta kawo masa, murmushi ya yi yace. "Sannunki Inna, Allah ya saka da alkhairi.” "Amanarka fa aka bani, kuma ina jinka kamar d'an da na tsuguna na haifa.” "Ni d'anki ne Inna, ki ma cire kamar d'in nan. ” Murmushi ta yi tace. "Sai naji mutuwa kuma? ” "Wallahi kuwa Inna, ya za'ayi da ikon Ubangiji?” "Babu kuwa sai hak'uri, Allah Ubangiji ya jik'anta ya gafarta mata, Allah ya kawo wasu yaran masu albarka.” "Amin Inna. ” Yace yana kai apple d'in bakinsa. "Naji mutuwar sosai wallahi, rana d'aya suka mutu da Yayata dake kano, wannan yarinyar da kake gani 'yarta ce, mariniya ce ba uwa ba uba, amanarta mahaifiyarta ta bani shine na taho da ita, ina neman alfarmarka ta zamana tare da ita a gidan nan.” "Haba Inna, nan fa gidan d'anki ne, kina iya kawo duk wanda kika ga dama cikinsa ya yi rayuwa, Allah ya jik'anta ya baku dangana. ” "Amin ya Allah, na gode da karam cinka, Allah ya k'ara tsareka daga sharrin mak'iya.” "Amin Inna. ” Yace yana cigaba da cin tufar kafin wayarsa tayi ringin............ Naji k'orafinku, tun ina free page na bayar da uzurina na rashin wuta, wutarmu ta lalace har yanzu bamu da wuta sai yawan kai chargi ba ko yaushe zaka k'arar da chagin gurin typing ba, hakanne yasa randa naga ina da isasshen chargi nake muku typing, idan kuwa kunga na kwana biyu ban turo ba to matsalar chargi ce. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [8:14PM/11/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *EIGHTEEN* Daddy ne ke kiran wayar tasa, da hanzari ya yi picking. "Assalamu Alaikum.” "Amin wa'alaika salam, gani a cikin gidan, kana ina? saboda ba na son kowa ya san nazo. ” "Ina gurin Inna, amma bara na fito.” "A'a yi zamanka bara nazo. ” Yana fad'in hakan ya datse layin, yayin da shi kuma ya ci gaba da cin tufarsa har Daddyn ya shigo d'auke da sallama, d'auke da fara'a Inna ta amsa masa sallamar ya shigo ciki ya zauna, gaisawa suka yi cikin mutumci, kana ta tashi ta shiga kitchen, sai gata d'auke da tuwon alkama and okro stew, Munassa ce tayi mata shi d'azu, amma ita ko da lauma d'aya Munassan ba tayi ba. Saving d'insa ta yi ta mik'a masa tace. "Ga mutuminka. ” "Kamar kwa kin san ban zauna naci abinci ba, na kwa gode. ” Miq ne yace. "Au Inna ni shine ko tuwon baki bani ba, da yake Daddy ne ga shinan kin basa. ” "To ai naga ba ku had'a hanya da shi bane shiyasa, amman indai zaka ci bari na sako maka. ” "A'a bar shi, bayan ba'a bani ba tun farko.” "Ci ne dai baza kayi ba shiyasa ka fake da haka. ” Daddy da ke danna loma yace. "K'yale shi ai ya bar dad'i wallahi, anya kuwa ba zakiyi murabus ki komo K/durbi da zama ba? ” Murmushi Inna ta yi, don ta san santi ne ya saka shi fad'in hakan don itama tuwon ya yi mata dad'i sosai, Miq ne yace. "Ai Daddy mai rabamu da Inna sai mutuwa.” Saboda ya saka laumar tuwon a baki bai samu ya bashi amsa ba, shi kuwa Miq ji ya yi tuwon ya ba sa sha'awa, d'aukar spoon d'in ya yi yai loma d'aya ia bai aune ba sai gani ya yi sun cinye tuwon tare tas, Inna sai dariya take masa, sai cewa ya yi. "Ai don yunwa nake ji shiyasa na iya ci, amma ba cin haka me zanyi da tuwo?” Ba wanda ya kulasa sai dariya da suka fashe masa da ita, murmushi shima ya yi yana shafa kai ya d'auki lemon guova ya kora da shi. "Inna gurinki nazo da magana mai muhimmanci.” "Tom ina saura ranka Alhaji. ” "Da fatan dai mu kenan a gidan? ” Har za tace eh sai kuma ta tuna da Munassah sai cewa ta yi. " A'a akwai yarinyata a d'aki, 'yar Yayata ce da ke kano, to yau kwananta hud'u da rasuwa, mahaifinta kuwa zai yi wajen shekara d'aya da rabi da rasuwa.” "Allah sarki, Allah ya jik'ansu ya yi musu rahama.” "Amin.” suka amsa baki d'aya, kallon Miq ya yi yace. "Sadauki ba mu guri, ita tunda tana d'aki ba jin tattaunawarmu za tayi ba. ” Murmushi kawai ya yi ya tashi ya fita. Kamar yarda Miq ya bashi labarin mutuwar Fareesah da rayuwar Babynta da aka b'oye haka shima ya bawa Inna, kana ya d'auko takardun wasu daga cikin kadarorinsa da ya mallakawa tilon jikarsa ya dank'awa Inna kana yace. "Na baki wannan labarin ne don na aminta da ke, ke kad'ai ce nake ganin zan bawa amana ki rik'e mini ita amanar kwa da ko cikin 'yan uwana ba zan iya bada ita ba, ki rik'e wa'yan nan takardun a hannunki saboda idan na ajiyesu gurina Mariya ta na iya binciko su kuma duk sunan little Fareesah ne a jiki, yardar da nayi da ke da kuma amanar da ke tsakaninmu itace ta saka na kuma damk'a miki wannan amanar wacce ko shakka ba nayi zaki rik'e mini ita k'am².” "Ina fatan Allah Ubangiji ya tayani rik'on wannan amanar, amma kamar yarda Miq yace zaman Fareesah a hannun Hisham ba zai yu ba, saboda Sumayya ta san Hisham, kuma dukkan wani motsi da Miq yake yi akan idonta ne, ta na da wayo, ta na ganin wani abu da bai mata ba dole za ta yi bincike a kansa, na dad'e da zargin da saka hannunta a mutuwar yaran da Fareesah ke haifa, kawai na yi shiru da bakina ne. ” "To yanzu dai na kasa samun matsayar inda za'a ajiye yarinyar wallahi, duk inda na waiga sai naga hakan bazai yu ba, ba na son itama su kashe mini ita wallahi, amma kuma na rasa ya ya zanyi wallahi, shi yace raino zai kaita wani guri da ban ni kuma ba na son hakan.” "Insha Allahu babu abinda zai same ta, amman idan ba'a samu matsaya ba dole ba yadda za'ai sai dai ya kaita rainon. ” "Tom shikenan, zan dai duba na gani kafin nan kan ranar bakwan Fareesah, tun da yace washe garin ranar zaije ya kai yarinyar raino. ” Yana kaiwa nan ya mik'e da shirin tafiya, Inna ta k'walowa Munassa kira don ta gaishe sa, cikin muryarta da ta kuma yin k'asa sosai ta amsa ta fito sanye da hijabi, har k'asa ta tsuguna ta gaishe shi ya dubeta cike da tausayi, hak'uri ya dinga ba ta yana mata 'yan nasihu, Inna tace. "Ai ina jin sai na nema mata rubutun dangana, tun ranar mutuwar har yau ba taci wani abun kirki ba. ” Kallonta ya yi yace. "Ita mutuwa wajibi ce akan kowa, muma duk daga haka muka rasa namu iyayan, kuma muka yi hak'uri, rashin cin abincinki ba shi zai dawo miki da ita ba, kin san ta riga ta tafi inda ba zata tab'a dawowa ba, don haka ki fauwalawa Allah lamuranki sai kiga komai yazo miki cikin sauk'i, amman rashin cin abincinki sai dai ya saka miki wani ciwo da ban azo ana fama dake, don haka ki daure ki dinga cin abinci kinji 'yata.” D'aga masa kai tayi idonta yana son zubar da hawaye, dama abinka da mai danshin ido. "Yauwa, ko zaki sha fura a kawo miki? ” Nanma d'aga masa kan ta yi yace. "A'a ni da bakin ki nake son ki mini magana. ” "Eh zan sha.” Ta fad'a muryarta na rawa, sallama ya yi musu ya tafi yace za'a kawo mata furar insha Allah. _____________________ An yi sadakar bakwai d'in Fareesah, Inna ma sai da tayi d'an abin sadaka na mutuwar Ummi, gobe ne Miq yace zai tafi england amman kuma har yau Daddy bai samu tsayar yar shawara ba, duk wani tunani yayi aamma ya kasa samun matsaya d'aya, wata shawara zuciyarsa ta yanke masa to itace yake ta tunanin yadda zai b'illo mata, idan ya tuno da abinda yaji d'azu Sumayya na gayawa mahaifiyarta sai yaga shawarar da ya yankewa ransa itace dai² da yadda zasu nuna musu izina akan duk abinda Allah ya riga da ya tsara babu wani mahaluk'i da ya isa ya ja da shi, wannan tunani da ya yi shine ya kuma k'arfa fa mishi guiwar bin shawarar zuciyarsa, amman dole ne sai yaji ta bakin wacce shawarar ta shafa......... [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:19PM/10/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *NINETEEN* Bayan ya gama tsayar da abinda zuciyarsa ta yanke masa, Amininsa ya kira, Alhaji Abdullahi mai tangaran da ya tafi kaduna gurin matarsa da ke can a yau bayan anyi Addu'ar bakwan Fareesah, shawararsa ya nema akan abinda ya yankewa zuciyarsa, ai kuwa ya bashi goyan baya d'ari bisa d'ari, kuma yace idan komai ya kammalu ya d'auki ragamar yin komai anan ba tare da sanin kowa ba. gani kuma ya yi dare ya yi, idan har ya fita to idon Mom na kansa, hakanne yasa ya sakawa k'ofarsa key ya shiga toilet nanma ya saka masa key gudun kar Mom ta shigo, wayar Miq ya kira, sai da ya fara tambayarsa yana ina, da fatan ba ya tare da kowa, yace masa eh kana yace ya had'asa da Inna. A lokacin Inna ta na ta zabga g'yangyad'i, Munassah na gefenta a kwance cikin nazarin rayuwa ji ta yi ana nocking, tsoro ne ya kamata, ita tun zuwanta gidan mai gidan kawai ta sani, shi kad'aine yake shigowa kullum ya gaishe da Inna, wani lokacin yaci abincin da suka girka, girgiza Inna na yi nace ana knocking, fir gigit ta farka, ta fita don ta bud'e k'ofar a ranta ta na cewa. 'Ko waye cikin daren nan? ' Tun fitowarsa daga sashensa Sumayya ta hangosa, bayansa ta biyo ba tare da ta masa magana ba, abinda ba ta sani ba yana ankare da tana biye da shi, hakanne ya saka Inna ta na bud'e k'ofar ya mik'a mata wayar. "Sai da safe.” Kawai yace ya juyo, itama Sumayyan da ta hango ne yasa ba tace komai ba ta rufe k'ofar ta juya ciki. Da mamaki yake kallonta, irin bai san ta biyo bayansa ba. "Ke kuma ina zaki da tshohon daren nan?” "Gurin Inna zani hira, tun da dai yau ka mini nisa.” Ta fad'i hakan ta na jin wani d'aci a ranta, murmushi ya yi a ransa yace. 'Lallai Sumayya makira ce ba kad'an ba, tun zuwan Inna gidan bai fi sau d'aya ta shiga inda take ba, saboda ko da suke a k/durbi ba shiri suke tsakaninsu ba, amma kuji wai hira zata gurinta, lallai ta raina mini hankali, da ada ne fa da tsafinta ke yawo a jikina yadda zanyi da maganarta? me kwa zai hana, tun da sau wajen nawa tana raina maka wayo irin haka, amman kuma ta riga ta gama nata wasan, yanzu ni aka bawa fagen.' Rungumota jikinsa ya yi, ya shiga gaya mata wasu kalamai da bai bari na jiyo muku ba, ya nufi sashenta da ita. Wayar da ya bata ce ta hau ringing, ganin Daddy ne ke kiran yasa ta yi tunanin ko shi yace ya kawo mata wayar, picking ta yi d'auke da sallama a bakinta, daga d'aya b'angaren Daddy ya amsa mata sallamar, kuma k'asa ya yi da muryarsa sosai wadda Innan ce kawai ta san me yake fad'a, ni kuwa duk tsurkuna na kasa jiyo muku tattaunawar Inna da Daddy in ban da sai da safe da naji sun yiwa juna, bayan yace ta bawa Miq wayar, tace ai wayar ya kawo mata kawai ya tafi, d'aya layin Miq d'in ya kira yace masa ya d'aga tafiyarnan zuwa jibi. ____________ Washe gari na ji Inna ta na ta yiwa Munassa k'us² ina ta kasa kunnena naji me take ce mata amma ko kad'an na k'asa jiyowa, can dai na ji Munassan tace. "Inna a yanzu ke kad'ai nake gani naji dad'i, bani da kowa cikin duniyata idan ba ke ba don haka duk yadda kika juya duniyata hakan dai² ne a gareni, bani da wani zab'i a yanzu sai abinda kika yanke a kaina, kuma nayi miki alk'awarin biyayya akan duk abinda kika sakani muddun hakan zai sanya ki farin ciki, don ni a yanzu babu wani sauran farin ciki da ya rage mini cikin duniyata. ” K'walla ce ta zubowa Inna ta tausayina tace. "Allah ya yi miki albarka Munassa, insha Allahu nan gaba zaki yi alfahari da hakan, ni na san babu nadama a cikinsa sai tarin alkhairi, ina ji a jikina ta dalilin hakan zaki shiga cikin yalwar farin ciki mai d'orewa.” Daddy ta kira a wayarta ta gaya masa yadda suka yi da Munassan, godiya ya shiga yi mata sosai, kana ya yiwa amininsa tex a waya, yana gani ya shiga ya goge shi. misalin k'arfe goma 12 na ranar sak'o ya shigo wayar Daddy da hanzari na lek'a don na gano me aka rubuto, Alhamdlillah an, kawai na hango Daddy ya hankad'ani ya d'aga wayar sama, ganin fuskarsa nayi da annuri ta na ta walwala da annushuwa, ya d'auki key d'in mota don shi kad'ai yake buk'atar fita, tun a motar ya kira Miq yace su had'u a k'ofar guga, gidan Miq d'inne da yake gininsa amma ba'a gama ba, Daddy bai jima da zuwa ba sai ga Miq d'in yazo, motar Daddyn ya fito ya shiga, kallonsa Daddy ya yi yace. "Sadauki.” "Na'am Daddy. ” "Na yanke hukunci ba tare da saninka ba, a karo na biyu kenan ina yimaka hakan, kuma ina fatan kamar yarda ka yimini biyayya a wancen kayi mini biyayya a wannan, ba wai ina yimaka hakan bane don na nuna k'arfina na mahaifinka ba, sai don ina son kuma gina maka rayuwarka da ake neman rushewa, duk wani tunani nayi na wanda zan bawa rik'on jikata na rasa, saboda ina tsoron a rabani da ita hakanne yasa na yanke wannan hukunci, don shine abu mafi sauk'i a gareni, an d'aura maka aure yau d'in nan da .... .” Kuyi hak'uri da wannan ban jin dad'i wallahi. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [6:9PM/13/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY* "An d'aura auranka yau d'in nan da Munassah, wannan yarinyar da ke gurin Inna, tun ranar da na fara ganinta tausayin ta ya yi mugun shigata, naji kuma ina sonta, hakanne yasa na shigo da ita cikin zuri'ata, don ina jin a jikina ita alkhairi ce a garemu, dalili na biyu da ya saka kuma na shigo da ita ahalinmu shine, ina son na inganta rayuwarta, zan tafi da ita London zan saya mata gida a can, zan kuma nemi wacce zata zauna da ita, sannan zan sakata a makaranta na kuma bata amanar jikata, nan da shekaru biyar jikata ta girma itama kuma ta kammala karatunta zata dawo cikin gidanka da zama a zuwan 'yar yar Inna ce auranta ya mutu, a lokacin ne za'a fara buga wasan, ba sai na gaya maka abinda zaka yiba, amma ni na san zaman yarinyar a cikin gidan sai mak'iyanka da ke b'oye sun fito, tarko zakai ta d'ana musu da ita, kuma bance bayan dai daituwar al'amura ka raba auranka da Munassa ba, ko bayan raina idan ka yi hakan baka kyauta mini ba, bazance ban yafe maka ba, saboda ban nemi umarninka ba a sanda na d'aura muku aure, nidai ina fatan ka rik'eta a matsayin iyalinka har k'arshen numfashi. ” Ba k'aramin gir giza zuciyarsa ta yi ba a sanda Abba yace ya d'aura masa aure da wacce ko sunanta ma bazai ce gashi ba, a hak'ik'anin gaskiya shi bai jin zai kalli wata mace da soyayya ko kuma ya amsheta a matsayin matarsa ba domin bashi da wata zuciya mai numfashi da ta rage masa a b'angaran soyayya, tun da Fareesah ta mutu itama ta mutu murus, abu d'aya ne zaisa ya karb'i auran nan da Daddy zai masa shine don a rik'e masa 'yarsa cikin amana, kuma kamar yarda ya tsarawa ransa nan da shekaru biyar zata dawo cikin duniyarsa amma kuma bai san ta wani b'angare ba sai gashi Daddy ya kawo masa hanya mafi sauk'i, amman kuma da ya sani bai d'aura aure tsakaninmu kawai a biyata kud'in aikin da za ta mana, ni dai da ya bi shawarata tun farko hakan zance masa ayi, amma babu komai, al'amura suna dai-daituwa zai sawak'e mata ko don itama ya bata 'yancinta. Numfasawa ya yi yace. "Ka da ka damu Daddy, kamar yadda na maka biyayya a na farko wannan ma ina mai shaida maka ba za ka yi kuka da ni ba sai dai ka yi alfahari da ni, gaba d'aya muk'ullin rayuwata yana hannunka Daddy duk ta inda ka bi da ni ta nan zan b'illa, ba na fatan ganin ranar da zaka ce mini na bi hanya na canja wata hanyar da ban, ina matuk'ar alfahari da kai mahaifina, gaba d'aya duniyata kaine ke zagaye da ita. ” Shafo kansa yayi ya shiga shi masa albarka yana jin dad'i da godiya ga Ubangiji da ya bashi d'a d'aya tilo tamkar da dubu. "Idan Allah ya kaimu goben kai ka fara yin gaba, zuwa jibi kuma sai ka samemu a London d'in, saboda za'ai mata shirye²n tafiya, ka saka Faisal ya kaita can kaduna gidan Mai tangaran, a can za'ayi mata dukkan wasu shirye² na tafiya, kuma ina tunanin a can zan samu matar da zan had'asu tare, ni kuma gobe zanje kadunan jibi jirginmu ya d'aga, sauran abinda ake ciki kuma zamui waya, amman fa a kula sosai kar wani ya ganta tare da ku, don Inna tace mini babu wanda ya san da zamanta cikin gidan sai mu, mai gadi ne kawai, shima kuma ba ganeta zaiyi ba nan gaba. ” "Tom insha Allah za'a kiyaye, Allah ya k'ara girma ya kuma bamu nasara, ya d'oramu akan mak'iyanmu.” "Amin” Suka ce a tare kana suka yi sallama ya fita ya koma motarsa, da gudu ya ja motar ya na jin zuciyarsa ba dad'i, ace wai yau kwana takwas da mutuwar zumarsa ya yi aure, anya kuwa Zumarsa zata yafe masa? don ya yi mata mugun laifi, laifin da da za ta dawo cikin duniya baza ta tab'a jin dad'insa ba, ya tabbata da shine ya mutu to har yanzu tana gadon asibiti ba ta san wanda ke kanta ba, sai gashi shi kuma har ya kuma wani auran, duk da bashi da masaniya da auran har sai da aka riga da aka d'aura amman zuciyarsa sam tak'i gas gata masa bai yiwa zumarsa shahararran laifi ba, kafin ya isa gida kansa ya d'au mugun chargi don hakane ma yasa ya kulle phart d'insa baki d'aya, tex ya yiwa Faisal da. _Ka sayo wannan abin da mata ke rufe fuska, ka kaiwa Inna kace ta bata ta saka ta fito ku tafi, kaduna zaka kaita gidan Alhaji mai tangaran._ yana tura masa ya sulale ya kwanta yana mai zurfafa tunaninsa. Duk wata dauriya na yi don ganin ban yi kuka ba don ka da Inna taga kamar matsa mini ta yi, amma har ga Allah zuciyata ba na jin dad'inta kuka kawai nake buk'atar yi ko zan ji sanyi a raina, nik'af Inna ta kawo mini tace na saka zamu tafi, karb'a na yi na d'aura a fuskata, dama sanye nake da hijabi har k'asa, rungume Inna na yi na fashe da kuka, rungumeni itama ta yi a jikinta tana sakin kukan da take b'oyewa, itace ta yi juriyar cireni daga jikinta tace. "Kije ana jiranki, kiyi hak'uri shekara biyar kamar yauce, kamar kinke yin karatu ne k'asar, kuma kema makarantar zakiyi a can, Allah yana tare da ke a ko ina, da fatan kin d'au takardun naki?” D'aga mata kai nayi don bazan iya magana ba a halin da zuciyata take ciki, ganin na tsaya nak'i motsi yasa Inna ta kamo hannuna muka fito, motar tana bakin k'ofar, Inna ta bud'e gidan baya tace na shiga. "Allah ya kiyaye ya tsare, ya kuma kaiku lafiya.” Ban iya amsawa ba sai a zuci, sai da taga ya zuzzuge glass d'in motar ya fara janta a hankula kana Inna ta koma ciki. Ticket ya siya mana guda biyu, ko d'ar banji ba saboda na saba shiga jirgin dama, shi kuwa Faisal kasancewar yau ne farkon shigarsa jirgi a mugun tsorace yake da jirgin zai ta shi, mamaki ne ya ishe shi da yaga ko d'ar babu alamunta a fuskata. A sashen 'yan aiki na gidan anan aka saukeni, sai washe gari wani yazo ya d'aukeni mukaje passport, da yake aikin na kud'ine nan da nan aka mini visa, ranar da daddare Daddy yazo, amma ban gansa ba sai washe gari da jirginmu zai d'aga, tare zamu tafi da Gwaggo Zulai, dattijuwar mata ce dake aiki a gidan mai tangaran d'in. Gidan da muka sauka madai daicin gida ne, falo ne a cikinsa sai two bed rooms, gidan ya tsaru iya tsaruwa, Daddy sunyi waya da Miq yace masa sai washe gari zai iso london d'in saboda wata 'yar matsala da aka samu, shikuwa Daddy yana da abinda zaiyi washe gari ko harkar makaranta ta a hannun a bokinsa ya barta, don haka daga nan London d'in sai ya sauka a England yaje yaga jikarsa da zuciyarsa ta kamu da soyayyarta tun kan ya ganta, amman bai tafi ba sai da ya bar mana komai na buk'ata. A d'aki d'aya muka kwana da Gwaggo, saboda ni ba na son kwana ni kad'ai a d'aki, a kwana d'aya da muka yi tare ta fara nuna kulawarta sosai a kaina, ko abinci da nak'i ci ma duk ta bi ta damu kanta. Ni kad'ai ce a falon, Gwaggo na kitchen na had'o mini tea ta nace sai na sha tunda nak'i cin abinci, k'ararrawa naji an kad'a ta neman izinin shigowa, tun kan naje na bud'e naji gabana ya yanke ya fad'i, jiki ba kwari na isa bakin k'ofar, d'an lek'awa na yi don naga waye, idona na sauka a kansa zuciyata ta yi wani irin harbawa, kuma kad'a k'ararrawar aka yi, hannuna na kar karwa na saka na bud'e k'ofar, yana gani an bud'e ya ja siririn tsaki yana kuma gyarawa Fareesah kwanciya a k'irjinsa............ [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:32PM/15/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY ONE* Hanya na bashi ya huce, kaina a k'asa ba tare da na dube sa ba, sautin muryarsa na ji a kausashe yace. "Ba zama nazo yi ba.” juyawa na yi zan koma ciki, yayin da shi kuma ransa ya yi mugun b'aci, hannunsa d'aya ya saka ya fisgoni da k'arfi ya jingina ni jikin k'ofa, rintse idanuna na yi ruwan hawaye suka biyo kuncina. "Me kike ji da shi da zaki tafi ki barni a tsaye, ko an gaya miki sa'an wasanki ne ni? ” Girgiza masa kai nayi wasu sababbin hawayen na kwaranyowa bisa kuncina, wata arniyar tsawa ya daka mini gami da cewa. "Ba'a mini magana da ka, ki bud'e baki kimin magana ko yanzu na sassab'a miki.” Cikin muryar kuka nace. "Yi hak'uri. ” Rintse isonsa ya yi ya bud'e yana kau da kansa gefe saboda sam bai son ganin zubar hawayen nata, haka kawai sai yake jin zuciyarsa ba dad'i. "Bcikinani dogon bayani da zan miki game da auranmu saboda kin riga da kinsan komi, Fareesah amana ce a gurin ki, kada ki sake wani abu ya samu rayuwarta idan kwa kika yi wannan saken to ki kuka da rayuwarki, kashedi na gaba kuwa shine kada zuciyarki ta kamu da soyayyar mahaifinta,don ni bani da wata zuciya mai numfashi da ta rage mini a fannin soyayya, mahaifiyarta ita kad'aice macen da nayiwa son da bazan tab'a yiwa wata 'ya mace da ban ba, na sota fiye da so babu misali bare na nuna, don haka na yi miki alk'awarin al'amuranmu suna dai daituwa zan baki takardarki kema ki samu 'yancinki. ” Bud'e fuskar yarinyar ya yi ya k'ura mata ido wani b'ari na zuciyarsa yana jin kamar bazai iya shekaru biyar ba tare da ya sakata a idonsa ba yayin da d'aya b'arin zuciyar tasa ke gaya masa dole ne ya jajirce ya kuma cije har zuwa nan da shekaru biyar d'in ma's u zuwa ko don b'atar da tunanin Sumayya, wani kyakkyawan kiss ya sauke mata a kumatu da goshinta kana ya mik'o mini ita, hannu na saka na karb'eta ina jin wani mugun takaicinsa a raina, an gaya masa ni wawiya ce da zan bari zuciyata ta kamu da sonsa? Ko an gaya masa shi kad'aine zuciyarsa ta daina numfashi a fannin soyayya, da zuciyata zata kuma son wani da tun akan Ahmad za ta fara yadda ya matsa mini da neman soyayyata daga k'arshe haka ya hak'ura don ya kasa samun damata. "Ki kula. ” Shine abinda yace mini bayan na ansheta ya juya ba tare da ya k'ara furta ko da kalma d'aya ba, rufe k'ofar na yi na dawo ciki ido biyu mukai da Gwaggo, hannu na saka ina goge hawayen fuskata, ina tuno nasihar Ummi gareni, kamar kwa ta san wani sabon al'amarin zai tutso kai cikin duniyata, hannu Gwaggo ta mik'o mini na bata Fareesah, mik'a mata ita na yi ina zarcewa d'aki don ina buk'atar zubar da hawayen da suke mini mugun rad'ad'i a idanuwa. Washe gari Daddy yasa aka kawo mini akwatina cike da kaya na alfarma guda shida, na jikarsa guda goma na Gwaggo guda uku, ni kuma har da sabuwar wayata mai bala'in kyau har da sim a ciki, satinmu guda na fara zuwa makaranta, Gwaggo na mugun kulawa da mu tun da ta lura ba na iya cin abinci sosai da kaina ta ke bani har sai nace mata na k'oshi, a hankula na ji soyayyar Reesah na shiga raina, jinta nake kamar d'iyar da na haifa da cikina, a haka rayuwa ta fara mik'awa ina karatuna cikin kwanciyar hankali, na mai da kai sosai gurin ganin na yi abin da zanyi alfahari da shi, kuma ko da Yaa Nazee da Abbana sun dawo duniyata zasu yi matuk'ar alfahari da ni, Daddy yana yawan lek'o mu haka zaizo su sha wasa da jikarsa, har ta riga ta saba da shi sosai, shi kuwa Miq ba ma a zancensa don yanzu harkokin aikinsa ma sun ishe sa, bare kuma dama bazai k'ara waiwayen su ba har sai sun komo nigeria, tsakaninsa da matansa kuwa yana kwatanta adalci sosai, duk wani k'ok'ari na Sumayya don ganin ta kawar da hankalinsa daga kansu abin ya ci tura, duk wani tsafi da za ta yi yak'i kama sa don sosai ya tsaya kan adduoi da shan rubutun da Malam Jadda ke yi masa, inda hankalinta ya kwanta, da taga har yanzu soyayyarta na nan cikin zuciyarsa amman duk da haka sai da suka shirya wani plane d'in da zata k'ara d'aga darajarta a cikin gidan, k'imarta ta kuma fitowa, kowa da kowa ya k'aunaceta k'auna mai girma don za ta kawo hasken da dukkanin matan Miq suka gaza kawowa. Ta b'angaran Inno kuwa Miq ya k'aurace mata gaba d'aya saboda ta yi mugun matsa masa kan turawa su Mudan kud'i a Accaunt d'insu, shikuwa fir yak'i sai dai duk wata ita zai tura mata a nata Accaunt d'in, tun da ya fahimci kud'insa take so ba shi ba, duk wani asiri da take kuma bunko masa har yau Allah bai bata nasara ya kama sa ba. Shekarar Reesah uku a duniya amma Allah ya bata kafirin wayo, magana ras a bakinta kamar 'yar shekara biyar, hakanne yasa Daddy ya sanyata a makaranta, duk zaton Daddy Miq yana zuwa gurinmu, kuma ko da wasa ban bashi k'ofar da zai san Miq d'in ba ya zuwa ba, a yanzu jin soyayyar Daddy nake mai matuk'ar girma a zuciyata, jinsa nake tamkar mahaifina, don shima ya d'auke ni tamkar d'iyarsa, duk wani abu na more rayuwa yana yimana shi bare da yaga yadda nake ji da jikarsa, don wallahi ba k'arya ba ina matuk'ar k'aunar Reesah a raina don itace ta dawo da murmushi kan fuskata, ta kuma dawo da dariya kan fuskata, har na ji ina son cigaba da rayuwa tare da ita na har abada, muna waya sosai da Inna [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:4PM/10/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY TWO* Har take ce mini Nucy ta kirata ta na nemana aikwa nace da Inna ta turo mini number da ta kira tan, da na kirata kuwa munsha hira sosai anan take gaya mini Abbanmu ya aikowa da Abbansu wasik'a yace a bamu, ga shi yanzu ta rasa ta yadda takardar za tazo gurina, nace mata idan na dawo zan nemeta, ranar naci kuka kamar zan yi me, wa takan dai ya tabbata Abba yana raye a duniya, ko wani azzalumin ne ya raba shi da Duniyarmu ba ki d'aya, a ina yanzu yake rayuwa? Me ya hana shi dawowa garemu har ga shi Ummi ta bar Duniyarmu baki d'aya? Sai naji gaba d'aya na matsu na koma nigeria ko don naji me takardar da Abbana ya turo ta k'unsa. Karatuna ya mik'a sosai Daddy ya saya mini mota ya saka aka koya mini, yanzu a ciki nake zuwa makarantar a sauk'ak'e abina, amma fa Allah² nake na kammala karatuna na koma gida, sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji na kammala karatuna tare da nasarori masu yawa, a lokacin Reesah na nurthry two, a washe garin ranar da muka yi graduation muka d'ungomo zuwa nigeria, mu muka fara yo gaba kafin Daddy ya taho saboda tsaro, dama mun riga mun yi sallama da shi tun a can. Inna ta yi matuk'ar farin cikin ganin yadda na koma, alamar hutu duk ta bayyana a jikina, fatata har wani yellow² ta ke yi, yau kwananmu uku da dawowa amma bamu saka shi a idonmu ba, ashe wai ba ya gari sai jiya da daddare ya dawo. ___________ " *REESAH*” Na biyota da gudu ina kiran sunanta, don ban kula da ta fito ba sai yanzu da naga tana k'ok'arin kaiwa bakin gate. Cak ya tsaya sakamakon jin sunan da na ambata zuciyarsa tana masa wani irin dokawa, Sumayya dake gefensa ta tsaya tana kallon yarinyar da nake k'wallawa kira zuciyarta na harbawa yayin da shikuma ya sauke idonsa a kaina, ganin irin kallon da yake min yasani nazarin kayan dake jikina, doguwar riga ce ta shaking material da ta bi jikina ta kwanta, kaina ba d'ankwali sai perking in kaina da nayi a tsakiya, saurin d'auke idonsa yayi daga kaina ya maidasa kan yarinyar da nake kira lokacin ita har ta isa gurin me gadi tana masa surutu. 'Yau tsahon shekaru kusan biyar kenan rabon da ya ganta, tun tana jaririya ya danne zuciyarsa ya raba kansa da ita dan cimma wani buri nasa' Saurin basarwa yayi ya k'arasa ga bakin motarsa, sojan dake jiransa ya bud'e masa gidan baya ya shige, shi kuma ya zaga ya shiga ya tada motar suka bar harabar gidan, motocin da ke jiransa a waje suka bi bayansa. Da sassarfa na k'arasa gurin me gadi na d'auki Reesah ina. "Sai na fara d'aure miki k'afafunki tukunna zaki shiga taitayinki da fita yawo.” Sumayya dake tsaye tun d'azu ta kasa motsi tabi bayanmu da ido cikin dokawar zuciya, har muka shige sashin da yake mallakinmu, sashin Khadijah ta nufa fuuuuuu kamar zata tashi sama. Ina shiga na kulle k'ofar don gudun kar ta sake fita, sannan na ajiyeta nace maza ki tafi gurin Inna, d'aki na shiga ina rik'e saitin zuciyata dake dokawa tun d'azu, yau tsawon shekara biyar kenan rabon da na sakashi a idona, magan gananusa kawai ke yawo a zuciyata. _Mahaifiyarta ita kad'ai ce macen da nayiwa son da bazan tab'a yiwa wata 'ya mace da ban ba, na sota fiye da so babu musali bare na nuna_ Wannan maganar tafi ko wace magana yi mini zafi a zuciya kuma ban san dalilin haka ba wani siririn hawayene ya biyo kuncina. 'Wai yaushe ne zanyi alfahari da DUNIYATA? Na taso DUNIYATA zagaye take da mutane uku, ABBANA, UMMANA, YA NAZEENA gashi yanzu babu ko d'aya a CIKIN DUNIYATA tun lokacin da na rasasu nayi bankwana da murmushi, dariya farin ciki da nishad'i har sai da REESAH ta shigo DUNIYATA. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: .*BEBE'ARTH* [7:4PM/17/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na kud'i ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY THREE* "Khadija kin ga kwa abinda na gani? ” Da kamar Khadijan ba za ta yi magana ba, sai kuma tace. "Me kika gani? ” "Wasu bak'in fuska na gani a cikin gidan nan mana, kuma sashin wancen munafukar matar naga sun yi.” "To ai sai kije ki tambayi munafukar matar ko kuma ki bari in mijinki ya dawo ki tambayesa.” "Ai bai da masaniya da zuwansu, kuma gani na yi kece me shiga gurinta zaki iya sanin ko su waye.” "Toh baki gani dai dai ba, don ban san da zamansu ba, yau kusan kwanana biyar rabon da na shiga gurin Inna.” Tsaki ta ja ta fice ba tare da tace komai ba, haka kawai sai ta ji wani b'ari na zuciyarta bai yi na'am da bayyanar wa'yan nan halittu cikin duniyarta ba, bare ma da taji ana kiran sunan yarinyar da sunan da tafi tsana sama da komai a duniya, itama Khadijan tsaki ta ja, tabi bayanta da haramatsalaabinta ta d'auka ta fito ta nufi sashin Inna don ta kwana biyu ba ta lek'a ba, Innan ta samu a falo ta na cin vegetable jollof rice with fruits, sai Reesah da ke wasa a gefenta, gurin Reesah ta dosa ta d'agota tana sakar mata murmushi. "Inna ina kika samo kyakkyawar yarinya haka? ” Ta fad'a tana dariya, don Allah ya saka mata k'aunar yara a zuciyarta. "Jika tace.” Inna tace da ita. "Allah sarki, ina Mamanta?” Ta na d'aki ta na sana'arta, uban yarinyar ne ya rasu amma har yanzu tak'i ta sakawa zuciyarta dangana. ” "Allah sarki, Allah ya yi masa rahama.” "Ya sunanki? Ta kalli Reesah tana tambayarta. "Reesah.” Tace mata cikin muryarta ta yara, murmushi Inna ta yi tace. "Sunanta Fareesah, mahaifiyarta ce me kiranta da Reesah. ” "Allah Sarki, itace ta biyu da na sani mai sunan nan bayan murgaiya. ” "Ehi, ni kaina sai da na tuno ta, mace mai kirki da sanin ya kamata, ita kad'aice ke shigowa muna gaisawa a kulli yaumin, ai naji mutuwa wallahi. ” D'an murmushin yak'e Khadija ta yi, tace. "Ai nima kawai ji nake wani sa'in ban son fita, amma ina son in dinga shigowa muna gaisawa.” "Ai ba komai Khadija, hakanma da kike shigo mini ina jin dad'i, kin d'aukeni da mutumci ba a 'yar aiki ba, matso muci abinci.” Matsawa ta yi, don tun da ta shigo abincin ya burgeta, kamar yarda ya burgeta a ido haka ya yi mata matuk'ar dad'i a baki tace. "Inna ta yi dad'i wallahi sosai, haka nake so naga na iya girki. ” "A'a toh, tun yaushe nake fama da ke ki koyi girki kink'i ki mai da hankali ki koya, a ce duk cikin ku ukun babu wacce ta iya girki sai dai yazo gurina yaci, da babu ni kuwa duk matsayinsa sai dai ya dinga yawan restaurant.” "Wallahi Inna ina mugun jin haushin rashin iya girkina, ni kenan kullum cikin cin indomea.” "Idan dai har da gaske kina son koyan, Munassa babu abinda ba za ta koya miki ba, don itace ma ta yi wannan girkin.” " Kai aikuwa ta yi mugun iya girki, na yi k'awa wallahi, na manne mata kenan har sai na gwanance a fannin girki, bara naje mu gaisa. ” Ta fad'a tana nufar d'akin, murmushi Inna ta yi, tana mugun k'aunar Khadijan a ranta, kuma duk tausayinta ne ya janyo hakan. Da sallama ta shigo d'akin, ta sameni a zaune idanuwana sun kod'e saboda kuka, amsa mata sallamar na yi, ita kuwa a ranta cewa take. 'Dole Reesah kiyi kyau, ashe haka mahaifiyarki take da bala'in kyau.' Hannu ta mik'o mini, nima da yake na gane nufinta na mik'a mata nawa hannun. " I am Khadija, nice matar mai gidan nan ta uku, ina son mu zama freind, Inna ta gaya mini wani abu game da ke, ina son zaki dinga koya mini girke ²." " I am Munassah, ba matsala, duk sanda kika shirya ki mini magana. ” "Thanks. ” Tace da ni ta na sakar mini murmushi ta juya ta fita. Sai bayan sallar isha'i ya shigo gidan, sashinsa ya nufa yaje ya yi wanka, sannan ya fito sanye da k'ananun kaya, yunwa yake ji sosai, hakanne yasa ya nufi sashin Inna. Bayan sun gaisa, taga yana cil cilla ido murmushi ta yi tace. "Ta yi bacci tun d'azu, tana d'aki. ” Murmushin shima ya yi, ya nufi d'akin yana mamakin yadda aka yi ta san abinda ke ransa. Ina zaune na jingina bayana da jikin gado, idanuwana a rintse suke, sai da zuciyata ta fara dokawa, sannan na jiyo dad dad'an k'amshin turaransa, ko da naji tsayuwar mutum a kaina hakan bai sa na bud'e idanuwana ba, jin shirun ya yi yawa ba shi da alamun yin magana yasa na bud'e idanuwana aikuwa suka yi kyakkyawan masauki a cikin lumsassun idanuwansa, saurin yin k'asa da nawa idon na yi ina jin zuciyata na Harbawa. Na san d'iyarsa yazo gani, hakanne yasa na cireta daga jikina na kwantar da ita kan gado na fita daga d'akin, ina fita ya zauna kan gadon yana shafa fuskarta cike da so da k'auna da kuma mugun tausayin kansu ga baki d'aya, d'agota ya yi ya rungumeta a k'irjinsa ya jima sosai a haka daga bisani ya kwantar da ita ya fito, ina ganin ya fito na ta shi na koma ciki. White macaroni and vegetable sauce with drink, Munassa ta yi, yana fitowa Inna ta zubo masa, dama saboda shi Innan tace wa Munassan ta yi, tun a lomarsa ta farko ya san d'an d'anon abincin ya sauya, amma baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa, sai da ya kammala ya d'an huta kana ya yiwa Inna sai da safe ya fito, phart d'insa ya koma don yana da aikin da zaiyi a lap top d'insa, yana shiga kuwa ya duk'ufa sosai akan aikinsa, da yake kwanan Sumayya ne itace ta shigo cikin wata fitinanniyar rigar barci, ganin aiki yake yasa ta nemi guri ta kwanta, don ta san ba ya had'a komai da aikinsa. ****** Wata shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanina da Khadija, girkuna kala² nake koya mata kuma ta mai da hankali sosai, Fareeda kuwa ban santa ba ma, ban sani ba ko ita ta sanni, Sumayya ta san dalilin zuwana gidan da kuma ni d'in wace ce, abinda ke mugun damunta shine ganin yadda mijinta ya d'auki soyayyar duniya ya d'orawa Reesah, idan idonta ba gizo yake mata ba wani zubin Reesah har kama take mata da murgarya Fareesah hakanne yasa ta d'auki tsanar duniya ta d'ora mata, ga shi duk inda Miq yake tana manne da shi sai dai idan ba ya gida, in tai masa maganar sai yace sunan zumarsa da take da shine ya janyo komai, nan fa hankalin Sumayya ya yi k'ololuwar ta shi musamman yanzu da ta lura in ya shiga cin abinci gurin Inna yana mugun dad'ewa akan wanda yake yi da, hakanne yasa take zargin wani abu na afkuwa tsakaninsa da Munassa, duk da ta yi masa tsafin da babu shi habu k'ara aure a duniya amman haka kawai take jin hankalinta ya gaza kwanciya, ta ma fara zargin akwai wata b'oyayyar manufar da ta saka suka shigo musu duniyarsu, kuma ta d'auki k'udirin binciko manufarsu ko ta halin k'ak'a. Wata tsadaddiyar makaranta, mai matuk'ar k'ok'ari Daddy ya saka Reesah, Faisal ne ya yi komai da komai na makarantar ta ta, ya saka shi ya kawo mini wata arniyar mota a ciki nake kaita na d'aukota don ban yadda kowa ya kaita ba, amma Miq yaso na bari a dinga kaita, ba ya k'aunar fitar da nake yi sam, amma ya rasa ta yadda zaimin magana kar na d'auki zancensa da wata manufa, hakanne yasa ake bin bayana idan zan kaita na d'aukota saboda tsaro. Yau mukai da Nucy naje filin jirgi na anshi takardar da Abba ya kawo mini, ta aiko wani d'an uwansu da zaizo katsinan, ta ba shi number wayata nima ta bani tasa, ina d'aukan Reesah daga makaranta na zarce filin jirgi, ashe wanda Miq ya saka ya dinga bin bayanmu yana can waya bai lura na ja motata na yi gaba ba, ina zuwa filin jirgin, jirginsu na sauka, tsayawa na yi har sai da ya sauko, layina ya fara nema yace mini ya sauka, nace nima ina cikin filin jirgin, gurin da nake na kwatanta masa yazo, bayan mun gaisa ya bani takardar na yi masa godiya mukai sallama na taho, wata mota da ban naga tana ta binmu a baya, gabana ne ya yanke ya fad'i, ga Reesah ta cikani da uban surutu, k'ara gudu na yi da tawa motar ba sai naga itama motar ta k'ara gudu ba, wani irin murd'awa cikina ya yi na mugun tsoro....... ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:4PM/20/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY FOUR* Gudu nake sosai yayin da k'irjina ke kuma gudun lugude, ga gari ya yi bak'ik' k'irin ya had'e murtuk ruwa na son sakkowa, ina gano motar ta mudubi ta na k'ara gudu, wani layi kawai na gani na yanka cikinsa da gudu ba tare da na san ina zan b'illa ba in na bisan, ina ta sharara gudu sai da na yi nisa sosai da naga basa bina sai na tsaya, fitowa na yi na d'auki Reesah da ta yi bacci ta gaji da mini surutu ba na kula ta, rufe motar na yi nai mata key, tafiya na dinga yi a k'afa, sai da na tabbatar na yi nisa sosai, ga kuma ruwa da ya fara sakkowa kuma na rasa 'yar mafakar da zan fake, ga shi ba na son ruwa ya jik'a mini Reesah ko kad'an, wani d'an kango na gani na shiga ciki sai naga ba wani d'an gurin da zan samu mu fake, ga shi na fara jiyo k'arar mota kamar ta na yowa gurin, lafewa na yi daga wanlafiya lungu, na saka Reesah a ciki na yi mata rumfa dan kar ruwa ya jik'ata, duk da haka sai da na cire hijabin jikina na lullub'eta da shi, haka ruwa yaci gaba da sauka a kaina ga shi ba d'an kwali a kaina. "Hello Hajiya, yarinyar nan fa ta shiga layin da idan muka shigesa akwai babbar matsala, saboda tun tuni ta fuskanci muna binta a baya. ” Rai a b'ace Sumayya tace. "Garin ya kuka yi saken da ta gano kuna biye da ita? So na yi ku taka mini kansu da mota gaba d'aya. ” "Ai Hajiya Yarinyar tana da matuk'ar wayo ne.” "To dai duk yadda za'ai kar ku bar bakin layin na tabbata za ta fito don ba ta san gari ba.” "Ok to Hajiya an gama.” Zagaye d'akin ta shiga yi ta na addu'ar Allah yasa ta fito su kama ta, ko kuma su b'ata gaba d'aya a huta, don ta san muddun ta tsira ta dawo gida ba za ta kuma saken da zata fita ita kad'ai ba. Inna ta kasa zaune ta k'asa tsaye, hankalinta idan ya yi dubu ya ta shi, duk da tace mata za ta biya filin jirgi ta anshi sak'o ai yaci ace ta dawo, duba da yanzu ga shi har an kusa kiran sallar la'asar, kuma tana ta kiran wayarta sai dai ta gama ringing d'inta ta katse ba tare da ta d'aga ba, hakanne yasa hankalinta ya kuma dugun zuma ko zama ta kasa yi addu'arta kawai shine Allah yasa suna lafiya, ganin abun ba na k'are bane ta kira wayar Miq ta sanar masa, ba sai hankalinsa ya fi na Inna mugun tashi ba, a birkice ya taho gida, Samaila da ya saka ya dinga binsu a baya da mota ya kirawo ya tambayesa garin ya akai ya dawo ba tare da su sun dawo ba, ya gaya masa abinda ya faru ai bai bari ya gama rufe bakinsa ba ya kikkifa masa wasu mahaukatan maruka had'e da fad'in duk abinda ya same su ka kuka da kanka don ba za ta yi maka kyau ba, phart d'insa ya nufa, sai ga shi ya fito da wani zagayayyen abu mota ya shiga ya jata da kansa da gudun gaske yayin da suka rufa masa baya had'e da sakin jiniya. "Kaiii Na Lami kamar jiniya nake jiyowa fa.” "Eh itace ya kamata fa muyi ta kanmu. ” Ai kanma ya gama rufe bakinsa Na Lami ya ja motar da gudun gaske, su na barin gurin motar Miq na dira, mamaki ne ya kamani ganin ta wannan zagayayyen abin yake ganin hanya, wai ashe ya mak'alawa Reesah zobe a hannunta, zoben da shi ya san me ya taka a kansa, to wannan zoben da ya saka mata shine dalilin da yasa wannan abun ke nuna masa hanyar da suke, hanyar ya mik'a sai kuma yaga motar Munassan a pake a gefe, fita ya yi ya dudduba baiga kowa ciki ba, wani daga cikin yaran nasa ya saka ya d'au motar tata ya kaita can gida, kana koma motar yaci gaba da tafiya har sai da yazo bakin kangon da suke ciki sai zagayayyen abun ya hau k'ara d'in², tsayawa ya yi cak, yaransa da ke bayansa suma suka tsaya ba tare da sun kashe jiniyarsu ba. Sai yau na tabbatar da in ka shiga tashin hankali kanka yana kullewa, sai a yanzu tunanin waya ya fad'omin, me yasa ban kira Inna ba a kawo mana d'auki? Gashi kuma yanzu na baro wayar a mota bare na kira ta, wani kuka ne yazo mini mai d'aci, kaina har wani juyawa yake saboda ruwan dake sauka a kansa, ruwan da ya tsagaita zai kuma dawowa mai k'arfin gaske, jikina ban da rawa babu a binda yake, na riga na saddak'ar sai na kwanta mugun ciwo, sanadiyar wannan ruwan da ke sauka a kaina don gara ruwan ya yi mini illa da na fita wani abun ya sameni ya sami Reesah gara ya tsaya iya kaina, wani ikon Ubangiji kuma har lokacin Reesah ba ta farka da ga baccin ba, ana haka na jiyo k'arar motoci da jiniya, jin mota ta tsaya a dai² gurin da muke sai da zuciyata ta yi wani irin harbawa, gaba d'aya na kuma firgicewa, shikuwa Miq fitowa ya yi ya shiga dube² d'aya daga cikin yaransa ya fito da lema zai kara masa ya dakatar da shi da hannu, duk da ya san matsalar da zai fuskanta idan har ruwan ya tab'a sa, amman a ganinsa mai sauk'i ce idan har yaga ruhinsa ga baki d'aya, saboda wani b'ari na zuciyarsa yana gaya masa kamar zoben ne kawai aka yadar a nan, kamar ance ya lek'a kangon ya lek'a. Doguwar riga ce a jikina ta swiss less, kaina ba d'an kwali sai parking d'in kaina da na yi a tsakiya, gaba d'ayana na jik'e sharkaf, tsayawa ya yi yana kallona zuciyarsa na dokawa na ban mamaki, bugun da tawa zuciyar take yi ji nake tafi tasa bugu, alamun tafiya kawai nake ji amma ban san waye ba duk da hancina ya jiyo k'anshin turaransa amma na k'aryata hakan, kawai na gama saddak'arwa an riga an yanka kawunanmu an gama. "Munas....” Ji ya yi sunan ya kakare a mak'o shinsa juyowa na yi don na gas gata zatona, ji na yi zuciyata ta sanya ya na nemi dukkanin wani tsoro da fargaba na rasa, Reesah da ke kwance na d'auko na mik'o masa ita, bai karb'e ta ba sai kallona da yaci gaba da yi cike da tausayawa, musamman da yaga hijabina na cire na nannad'eta da shi, sannan na kareta kar ruwa ya tab'ata yayin da ni ruwan ya yi mini jagab, kar b'arta ya yi don ganin ruwa na neman jik'ata, mota yaje ya kaita tare da ce mini kar na fito sai gashi ya dawo da wata jibgegiyar riga a hannun ta kakinsa ce ma, da kuma hijabina da na nannad'e Reesah da shi, hannu ya mik'o mini ba musu na mik'a masa nawa hannun don ina buk'atar taimakon da gasken gaske, rigar ya saka mini yana mai shigar da idonsa cikin nawa, yana gani yadda ya wani kod'e saboda kuka, hijabin ya saka mini ya rik'oni a jikinsa muka fito don bazan iya tsaiwar da kaina ba. Gidansa da ke k'ofar guga ya nufa da mu, amma ya kira Inna ya sanar mata an ganmu don ta samu ta kwantar da hankalinta, tun kafin mu isa nake kar karwar sanyi wani wahalallan zazzab'i na son rufeni, ko da mukaje shine ya d'aukoni don babu wani k'arfi da ya rage mini a jikina, Faisal da yazo yanzu shima ya kawo mana kaya shine ya d'auko Reesah ya biyo bayanmu da ita a lokacin ruwan ya gama daukewa gaba d'aya, a kan gado Faisal ya kwantar da Reesah ya ajiye mana ledar kayan, shima Miq ficewa ya yi ya barmu, da k'yar na iya raba kaina da jik'ak'k'un kayan, wani d'an littafi ne ya fad'o daga aljihun rigar da Miq ya saka mini, d'aukarsa na yi na ajiye a gefena, doguwar riga ce 'yar kanti, ita na saka na kwanta a gefen Reesah ina mamakin wannan bacci nata, ta dad'e rabon da ta yi bacci irin wannan, haka kawai sai naji wani b'ari na zuciyata na son sanin mai littafin nan ya k'unsa, hakanne yasa na janyo shi na bud'e a pagin farko sai naga an saka; _Sunana Miqdad Muhammad Mahmud_ Mur mushi na yi don dama ina son sanin mai rayuwarsa ta k'unsa, kuma kuma ma's u karatu na san kuna son kuji labarin Miq dalla² ta yadda zaku cigaba da fuskantar labarin cikin sauk'i, sai dai ku sani muna da sauran tafiya a gaba... Idan kun jini Asabar, lahadi, litinin shiru ku mini uzuri hidimar biki ce, idan kuma na samu lokaci zaku iya ganin post d'ina. ALK'ALUMAN NAGARTATTU [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:23PM/26/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY SIX* Nocking ya yi mini, gyara kwanciyata na yi gami da cewa. "Shigo. ” Shigowa ya yi d'auke da Reesah a hannunsa yana janye da akwatinmu. 'Wai yana nufin mun dawo gidan nan ne ko kuwa? Na tsinci zuciyata da tambayar haka, ban kai ga bawa kaina amsa ba naji yana. ''Ki sauya mata kaya.” Wa ta kan wanka sukayi don shima ga shinan ya sauya kaya sai zuba k'amshi yake mai saka zuciya nutsuwa. Sai da yaje bakin k'ofa kana yace. "A da kata da zuwan makarantarta tukunna. ” Ya na fad'in haka ya fice, akwatin kayan na bud'e na saka mata kayan bacci kawai tun da a lokacin gari har ya fara duhu, wankan nima na yi nai shirin bacci tun da ina cikin hutun sallah, kwanciya na yi na bar Reesah ta na ta 'yan wasan ninta, don bacci ba yanzu wannan bacci da ta sha haka, littafin na janyo cike da zumud'in cigaba da karantawa na d'ora daga in da na tsaya. _Sai da na kammala karatuna na secondary Daddy ya yi aure, bayan ya samu wacce ke matuk'ar k'aunarsa shi a ganinsa, amman kuwa ba shi take so ba dukiyarsa take hank'oro, saboda talakawa ne su fitik, mijinta ya rasu ya barta da 'yarta d'aya tilo, itama haifaffiyar katsina ce sun matuk'ar gwanance a sihiri da tsafi, tsafin nasu ne ya kama Daddy har yasa ya aureta ta taho tare da 'yarta, zallar soyayya da k'auna ta ke nuna mini wacce ko kwatan kwacinta ban samu a gurin Inno ba, a gaban Daddy da bayan idonsa haka take nuna mini soyayya wacce ko kad'an ba zanyi tunanin soyayyar k'arya bace, ashe ita ta shigo cikin duniyarmu ne don ta wargaza mana ita gaba d'aya daga bisani ta turamu inda babu mu ba dawowa cikinta, k'alu bale d'aya ta fara fuskanta shine na rashin samun cikin da ta yi, babu yawan da ba ta yi ba don samun haihuwa Amma Allah ya hanata, hakanne yasa ta fara hasashen had'amu aure da 'yarta Sumayya._ _Bayan kammala karatuna na secondary makarantar sojoji da ke london Daddy ya kaini, a can na yi karatuna har na kammala tare da samun nasarori masu tarin yawa, bayan dawowata gida na fara laluben in da mahaifiyata take tun da ita ba ta neme ni ba, ashe ma tana cikin garin katsinan a unfuwar shinkafi, bayan rabuwarsu da Daddy da shekara biyu ta yi wani auran, ba laifi shima mijin da ta aura da kud'insa, sai dai ko farcen Daddy bai kama ba ko kad'an, 'yan biyu duk maza Allah ya azurta su da su Mudansir da Mahboub, sai kuma Allah ya jarabceta da mugun soyayyarsu yadda ba ta zato, shekarunsu goma a duniya Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar ta girgiza duniyar Inno sosai da sosai, bayan mutuwar kuma sai ta koma kan kasuwan cinta, taci gaba da bawa 'yan biyunta soyayya da mugun gata, gatan da babu kwab'a ko nuna ba dai-dai ba a cikinsa, hakanne yasa suka ta so a mugun sangarce komai suka yi dai -dai ne gurin Innonsu, bayyanar Miq cikin duniyarsu sun yi matuk'ar farin ciki, bare ma da suka ga ya zama young miloniar, Inno ta yi farin ciki duk da har lokacin ba ta jin soyayyarsa kamar yadda take jin su Mudan, hakanne yasa ta fara asircesa yadda za ta juya dukiyarsa fiye da yadda yake zato._ _Da tsafinsu zuciyata ta kamu da matsanan ciyar soyayyar Sumayya wacce ba na had'ata da komai, Daddy ya yi matuk'ar farin ciki, hakanne yasa nan da nan aka sha bikin Sumayya da Miq ba b'ata lokaci wanda Inno sam ba taso hakan ba itama har sai da suka tsafaceta tukunna, shekararsu biyu da aure babu haihuwa ba labarinta, ga shi Daddy yana matuk'ar son ganin jikansa, shikuwa Miq soyayyar Sumayyansa ce kawai a ruhinsa, tashin hankali babu wanda Mom ba ta yi ba na rashin haihuwar Sumayya, babu inda ba su karad'a ba don ganin ta samu ciki amman shiru kake ji, tsoron Sumayya d'aya kada Miq yace zai mata kishiya ta na matuk'ar k'aunar abinta, kuma ta na bashi kulawa yadda ya kama ta, baza ta tab'a lamuncewa ganinsa tare da wata halitta ta da ban ba ita ba, idan har Miq ya mata kishiya duniyarta ta ragargaje gaba d'aya, ana cikin haka Fareesah ta shigo cikin duniyarsu._ _Fareesah 'yar abokin Daddy ce, a bayan layin su Miq suke, Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa, kwata² ba tayi sa'ar matar uba ba, ta azabtar da ita fiye da zaton masu karatu, b'angare d'aya da zance ta yi mata gata shine da ta koya mata girki, shine kawai gatan da ta mata, ganin irin matsin rayuwar da take ciki, don ko mahaifin nata ba ta jin dad'insa ta zigasa ya bayar da ita sadaka shine Daddy yace ya nemawa d'ansa auranta, ai ji ta yi kamar ta had'iyi zuciya ta mutu, ita da ta so rayuwarta ta k'are a wahala sai ga shi Allah ya tsamota lokaci guda..._ AlK'ALUMAN NAGARTATTU [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [10:59PM26/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY FIVE* Alamun tafiya na jiyo da sauri na b'oye littafin, Miq ne ya shigo tare da wata mata a bayansa, zama matar ta yi kusa da ni, shikuwa Miq ficewarsa ya yi bayan ya ajiye ledar da ke hannunsa, tsintar bakina na yi da gaisheta, murmushi ta yi mini kana tace. "Wani yanayi kike ji a jikinki?” Sai a lokacin na fuskanci likita ce. "Kaina ke d'an mini ciwo, sai wani sanyi da nake ji yana shiga ta, kunnuwana sunyi mini dumm gaba d'aya, hancina ma ina jinsa a d'an toshe.” "Ok, bara na rubuta miki magun guna, amma zan miki allura saboda kariyar zazzab'in da yake son kama ki.” Magun gunan ta rubuta ta fita, a falo ta same shi, takardar magun gunan ta bashi, shikuma ya kira Faisal ya bashi ya siyo magun gunan. Bayan fitarta komawa na yi na kwanta ba tare da na sake bud'e littafin ba, can jimawa sai gata ta sake dawowa, tambayata ta yi naci abinci nace mata a'a, janyo ledar da Miq ya ajiye ta yi tana. "Ina to abincin ya ajiye miki. ” Ilai kuwa abincin ne a d'an soson take a way, bani ta yi na ci, haka na dinga kai lomar abincin da k'yar saboda ta matsa mini, kafin na ture shi nace ya isheni, tunanina ma yanzu shine idan Reesah ta farka tea za ta nema kuma ban san ya zanyi ba, ga shi ina buk'atar wayata da takardar da na anso, kuma shi wannan hamshak'in baice mini komai ba, a mota ma da nace masa motata da na ajiye ban ganta ba kawai ce mini ya yi an kaita gida, ga shi yanzu ina buk'atarta kuma yazo ya zubemu a nan, ko meye dalilinsa oho,kuma ko ya tambayi abinda ya faru da mu, muryar matar ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi. "Ta so to na miki allurar.” Juya mata bayana na yi ta mini allurar lailaya mini ta yi sannan tace na cigaba da lailayawa, ta bani magun gunan na sha, sannu na mata, ita kuma ta mini Allah k'ara sauk'i ta fita, kwanciya na yi ina jin bacci na son fisgata ga shi kuma yamma ne ban son yin bacci kuma babu abinda zai d'ebe mini kewa, Reesah ce ta farka cike da rigimar shayi za ta sha, rasa yadda zanyi da ita na yi na rik'o hannunta muka fito falon gidan, ba kowa a falon, wata k'ofa na gani da take kallo k'ofar d'akin da muke ciki, hannuna na rawa na murd'a handle d'in k'ofar tun kafin na kai ga shiga ciki na ji an saki wani siririn tsaki mai d'an sauti, kansa ne ke masa matuk'ar ciwo hakanne yasa yazo ya kwanta, bayan ya kashe wayoyinsa baki d'aya saboda bai son takura da damuwa, k'arar bud'e k'ofar da yaji ne yasa ya saki tsakin ba tare da ya juyo ba, ji na yi Reesah ta zare hannunta daga nawa ta nufi kan gadon da gudu, kan gadon ta hau ta na lek'a fuskarsa, murmushi ta saki tace. "Papa” A hankula ya bud'e lumsassun idanuwansa yana jin zuciyarsa na sanyi, janyota jikinsa ya yi yana mik'ewa zaune tare da ita, idanuwansa ne suka sauka a kaina, kallon mamaki ya tsaya yana mini, ni kuwa tun d'azu na k'asa had'a kalmomin da zanyi amfani da su gurin fad'in buk'atar da nazo da ita, dago kaina na yi da zummar gaya mishi Reesah ce za ta sha tea, idanuwana ne suka samu masauki cikin nasa, wani irin abu ne naji ya tsirga mini ta tsakiyar marata yana tsirgawa ta cikin jinina, rintse idanuna na yi har lokacin bai janye idanuwansa daga kaina ba yana jiran jin abinda ya kaho ni, bakina na rawa nace. "Reesah ce za ta sha tea. ” Ina gama fad'i ban jira cewarsa ba na bar d'akin. Wayarsa ya kunna ya kira Faisal ya kawo masa kayan tea, don babu komai a gidan, ya kuma biya ya anso mana kayanmu. Ruwan zafi ya jona a kettle Reesah na ta zuba masa surutu har ruwan ya tafasa sai kuma ga Faisal d'in ya zo, cup ya d'auka ya had'a mata shayin, zuba mata idanu ya yi yana kallonta yana jin wata soyayyarta na ratsa masa zuciya, a hankula yaji ciwon kan da ke damunsa ya na raguwa. Ina shiga d'aki kwanciya na yi, ganin zaman shirun ya isheni yasa na janyo littafin nan na bud'e shi na soma karantawa. _Mahaifina haifaffan garin katsina ne, shi kad'ai ne gurin iyayansa kuma dukkaninsu sun rasu sun bar masa tarin dukiya mai yawa bayan sun gina masa rayuwa har sai da ya zama babban soja wanda ake ji da shi saboda k'warewar aikinsa na tsakani da Allah, Mahaifiyata mai suna Ruk'ayya muna kiranta da Inno itama 'yar katsina ce sunyi aure da mahaifina auren so da k'auna, tare da ita yake yawon duk inda aiki ya kama shi zuwa, to ita irin wayayyun matan nanne ga mugun asiri duk ta bi ta mallakesa komai sai da izininta yake yi, da ta samu cikina kuwa babu abinda ba ta sha ba don ya zube amma ko gezau cikin bai yiba Allah ya riga ya rubuta sai nazo cikin wannan duniyar mai cike da harzik'in rayuwa, bayan haihuwata ba na samun wata gamsas shiyar kulawa daga gareta a gurin mahaifina kawai nake samun kulawa da soyayya had'e da riritawa hakanne yasa na taso da soyayyarsa mai girma a zuciyata, kuma kaman ninmu da shi sak kamar an tsaga kara, tun ina yaro ya kwad'aita zuciyata da son zama soja kamar shi hakanne yasa nima na girma da burin zama babban soja tamkar mahaifina_ _Laifi kad'an zan yiwa Inno za ta rufeni da duka, kwata² ba ta k'aunata ko kad'an wani duka da ta mini ta farfasa mini jikina Daddy ya k'asa jurewa hakan ya yi mata matsiyacin duka itama ya farfasa mata jikinta, fad'a sukai ga garumi wanda ya janyo musu tashin hankali mai girma har sai da ta kai ga yai mata saki d'aya ba tare da yaso hakan ba, saboda yana matuk'ar sonta, gashi kuma ta bashi farin cikin duniyarsa Miq, haka ta tsallake ta bar duniyarmu babu hanyar da Daddy bai bi ba don ya dawo da ita amma fir ta k'i, daga k'arshe dai sai katsina ya dawo da ni gurin Inna mai musu hidimar gida sanda suna katsina, don a yanzu ba shi da wani shirin yin aure, a gurin Inna naci gaba da karatuna cikin kulawa da soyayya._ Alamun tafiya na jiyo na yi saurin b'oye littafin na koma na kwanta. ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:37PM/31/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY EIGHT* _Wani dattijon mutumi na gani a durk'ushe a k'ofar gidan, dafa sa na yi hakan yasa ya d'ago kansa ya kalleni, idanuwansa sun yi matuk'ar jaa na ban mamaki, rik'o hannuna ya yi yace._ " _Bawan Allah ka taimake ni ka ceto rayuwar marainiya, ta na cikin gidan nan ka taimakeni dan Allah._” _Ba tare da nace masa komai ba na koma mota wani k'arfe na dauko, duka d'aya naiwa k'ofar ta bud'e, na tusa kai ciki mutumin ya biyo bayana tare da sauran mutanen da ke waje, d'akin da nake jiyo ihun naiwa wani irin duka da k'afata ya wangale, wata budurwa na gani, an rabata da komai na jikinta, rintse idanuwana na yi ina kiran sunan Allah a zuciyata, yayin da mutanen suka rufe mutumin da ke neman haike mata da duka, shikwa dattijon nan kallonta yake da jikinta duk ya fashe saboda duka, rik'e saitin zuciyarsa ya yi ya na jin rad'ad'in tausayinta, wani bargo ya d'auko ya lullub'eta da shi, kuka ta fashe da shi ta na jin dama mutuwa tazo ta risketa za ta fi buk'atar hakan sama da komai akan irin wannan rayuwar da take cikin duniya._ Juyawa na yi da nufin mik'a mutumin a hannun hukuma rik'o hannuna ya yi gami da cewa._ " _Zan had'aka da abu mai girma domin ni wannan amanar da aka barmin ta fi K'arfina, Khadija ba ta da kowa da ya rage mata a duniyar nan sama dani, kuma amana ce a gareni, mahaifanta sun rasu sanadiyar had'arin jirgi, tun daga sannan rayuwarta ta shiga tangard'a, 'yan uwan mahaifinta suke neman ganin bayanta don su samu damar cinye dukiyarta, na tabbata yanzu ma su suka turo a wulak'anta_ _rayuwarta bayan sun samu goyan baya a gurin mai d'akina sun siyeta da abin duniya, ina mai rok'onka da kayi nesa da ita daga garin nan, ina kuma son ka aureta dan Allah ba don ni ba._ _Guiwoyinsa biyu ya saka a k'asa ya rik'e k'afata gam yaci gaba._ " _Allah ne ya aikoka cikin Duniyarmu don ka tsame Khadija daga k'angin rayuwa, duk da ban sanka ba amma zuciyata ta na gaya mini kai alkhairi ne a rayuwar Khadija, ka taimakeni ka kuma taimaki tsufana da maraicin Khadija, ka aureta don ka_ _tsameta daga cikin wannan rayuwar, don idan ka tafi ka barmu ban san da mai zasu zo mana nan gaba ba._” _Tari ne ya sark'e sa, ya fara wata iriyar shak'uwa gigicewa Khadija ta yi ta ruk'unk'umesa ta na kira sunansa gami da cewa._ " _Kar ka tafi ka barni Baba idan ka barni ban san ya rayuwata za ta k'are ba, kai kad'ai nake ganin soyayyata cikin idanuwanka bacin kai bani da kowa a duniyar_.... _Maganar ta ce ta tsaya cak, sakamakon ganin numfashinsa ya daina kaiwa da komowa, wani marayan kuka ta saki mai saurin narkar da zuciya, tun da nake a duniya ban tab'a jin tausayin wani mahaluk'i sama da Khadija ba, fita na yi ba tare da na waigo na kalleta ba, mutanen har sun fashe sakamakon mutumin ya samu ya arce sai sauran munafukai masu jiran a kashe komai a gabansu, mota na shiga, wata zuciyar ta na ce mini na tafi wata kuma ta na ce mini kar na tafi na bar rayuwar Khadija, idan na tafi na barta bazan tab'a samun nutsuwar zuciyata ba saboda magan ganun dattijon ne ke yawo a kwanyata._ _Hakanne yasa na koma cikin gidan, a lokacin mutane har sun fara taruwa da alama mutuwar tasa ta fasu, a yadda na bar Khadija a haka na sameta, sai dai ta saka kaya a jikinta, hannunta kawai na kamo na fito da ita don idan na tsaya magana banjin za ta saurareni, wata mata ce ta biyo bayanmu ta na tambayar inda zan kaita, ban tsaya sauraranta ba na saka Khadijan a mota na shiga na jata da gudun gaske, ina jin ta ta na ihun kiran b'arawo._ [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:4PM/29/3/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY SEVEN* _An d'aura Aurena da Fareesah ba tare da saninmu ni da Sumayya da Mom ba, bayan kammala d'aurin auran Daddy ya d'aukota ya nufo gidana da ita, had'amu ya yi a falo gaba d'ayanmu ya ga batar da ita garemu ta lallami da nasihohi, yace kuma amana ce a garemu idan muka cutar da ita Allah zai saka mata, duk da zuciyar Sumayya ci take kamar wuta haka ta daure ba tare da ta nuna b'acin ranta ba wanda hakan ya k'ara mata girma a zuciyata na kuma ji na tsani yarinyar tun kan naga fuskarta amma zan yi biyayya ga mahaifina zan kuma rik'eta amana kamar yadda yace, Mom ma da taji zancen ta ji ba d'ad'i sosai, hankalinta ya yi mugun tashi amma haka ta danne ba tare da ta nunawa Daddy ba, sai ma tausayin Fareesan da ta nuna tana ji, hankalin Daddy kasa kwanciya ya yi, gani yake kamar rayuwar Fareesah za ta kuma shiga matsi, hakanne yasa yace Inna ta daho kusa da mu ko don ta dinga kula da Fareesan._ _Sam ba na shiga sabgarta, babu ruwana da ita, kullum k'ok'arin Sumayya na ganin ta dai daita tsakaninmu ne ni kuma ina bijirewa, yayin da a b'oye ita take kulle zuciyata don ka da Fareesan ta yi tasiri a cikinta, abinda na lura da Fareesah kuma shine, ta na da sanyin hali babu ruwanta ga ibada da ta shiga jikinta ta zauna, ga kuma tsararran girki da kullum take yimana muna tand'ewa, sab'anin Sumayya da ko tukunya ina jin ba ta san yadda ake d'orawa ba, a hankali kuma sai naji hankalina yana kwantawa da Fareesah har wani bigire na zuciyata yake gaya mini ta dalilinta zan samu sanyin idaniyata, wannan ne yasa na raba musu kwana da Sumayya, ai kuwa Sumayya ta shiga tashin hankali mara misaltuwa ba tare da ni na gane hakan ba, don ba ta nuna mini ba, farkon fara tarayyata da Fareesah anan na kuma gano bam bancinsu da Sumayya, a zahiri Sumayya ta fi Fareesah kyau, a bad'ini kuwa Fareesah ta kerewa Sumayya fiye da zatonku ma's u karatu, ina mugun samun nutsuwa gurin Fareesah wanda a hankali ta fara samun mazauni a zuciyata kafin na bata babban matsayi a cikinta._ _Ba zan iya misalta muku farin cikin da na shiga ba yayin da na gano Fareesah na d'auke da gudan jinina, Sumayya ma ta tayani farin ciki wanda hakan yasa ta k'ara k'aimi a zuciyata na ji kuma ina mugun tausayinta, hakanne yasa nake k'ok'arin b'oye zallar cikina, Sumayyan ce ta shiga bawa Fareesah kulawa fiye da zatona, ni duk a ganina soyayyar da take mini ce ta janyo haka, ashe tana yi ne don ta samu hanyar da za ta b'arar da cikin, sai kuma Allah bai bata sa'a ba, tsafinta sam yak'i kama Fareesah, har sai da Fareesah ta haihu lafiya sumul, farin cikin da na shiga bazan iya gaya muku shi ba, bare kuma Daddy uban gayya, sai dai kaish kafin suna Allah ya karb'i abinsa, kuka ya dinga yi muka rasa me yake janyo hakan, da aka kaisa asibiti ma cewa sukai lafiyansa lau, babu yadda muka iya haka muka karb'i wannan k'addarar da hannu bibbiyu._ _Haihuwar Fareesah uku yaran na mutuwa, kuma duk an rasa me yake janyo hakan, ashe wai Sumayya ce duk ke soka musu allura guda takwas a tsakiyar kansu, har sai ta tabbatar sun lume baki d'aya, ana haka naje kano d'aurin auran wani abokina, munzo hucewa ta wani gida na dinga jiyo ihun mace, kuma ga mutane nan a bakin k'ofar gidan, haka kawai sai na k'asa jurewa hakan na tsaya a dai- dai k'ofar gidan...._ Gobe suna bai zama lallai nai typing ba, yau d'inma da k'yar na samu na yi, ku yi hak'uri babu zama ne. ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [7:4PM/2/4/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *THIRTY* Juyi na yi na gyara kwanciyata gami da rufe littafin, lumshe idanuwana na yi ina girmama rashin imani na Sumayya a zuciyata. 'To yanzu shi yasan ta na aikata abubuwan nan kuma yaci gaba da zama da ita, ko kuma ina jin dai akwai wani abu da ya barwa zuciyarsa sani.' Knocking d'in da naji ne ya katse mini d'an gajeran tunanin da na tafi, ta shi na yi da k'yar don wani bacci ne ke son fisgata, bud'e k'ofar na yi mukai ido hud'u da Daddy, kyakkyawan murmushi na saki gami da cewa. "Reesah ga Daddy. ” Da gudu ta baro wasan da take ta nufosa, d'aga ta ya yi ya cilla ta sama ya cafo suka saki dariya a tare kana ya juya ya nufi falo da ita, biyo bayansu na yi har lokacin murmushi yak'i barin fuskata don ina matuk'ar k'aunar Daddy, jinsa nake tamkar mahaifina, akan kujera suka zauna da ita ta na ta masa surutu, har k'asa na tsuguna na gaishe sa, murmushi akan fuskarsa ya amsa mini yana sakawa rayuwarmu albarka. "Kici gaba da hak'uri da Sadauki, wata rana kece ta farko da za ki fara fad'in alkhairinsa, kuma ina mai tabbatar miki za kiyi alfahari da kasancewar sa cikin duniyarki, kamar yadda shi ma akwai rana mai zuwa da zaiyi alfahari da ke, don ke d'in kin zamo masa alkhairi shi kuma zai zamo miki haske cikin rayuwarki, ka da abin duniya ya saka ki canja daga yadda na sanki, duk wani abu da mutum zai tara ko yana so ko ba ya so dole haka zai ta fi ya barsu kuma tafiyar da babu dawowa cikinta, ka da kici amanarsa, kar kuma ki bari a ci amanarsa, da shi da Fareesah dukkaninsu amana ne a gareki, ina fatan kuma Allah ya ta ya ki rik'on amanar. ” "Amin” Nace, yaci gaba da cewa. "A hak'ura da zuwa makarantar Fareesan har zuwa sanda abubuwa zasu dai daitu, don ba mu san wani mak'iyin ne ke farautar rayuwarku tun kan ma ya san hak'ik'anin ku d'in su waye ba, zuwa gobe da safe zai zo ya maida ku gida, ni nace ya barku anan d'in saboda ina buk'atar ganin jikata. ” Ya kai k'arshen maganar yana jan karan hancinta, don ta k'ura masa ido tana ta kallonsa kamar ba ta tab'a ganinsa ba. "Ba mutuwa dai zan yi ba yanzu, har sai Mommynki ta haifo mini jikoki dozin.” Yakai k'arshen maganar yana dariya, murmushi nima na yi ina sunkui da kaina cike da kunya. "Daddy Mommy za ta siyo mini k'anne da yawa?” Reesah ta fad'a cikin maganarta ta yara. "Eh za ta siyo miki da yawa da yawa ma." Ya ba ta amsa, sauka ta yi daga jikinsa ta saki tsalle da murna, murmushi ya yi irin nasu na manya kana ya mik'e gami da cewa. "To zo muje ku karb'o tsarabarku.” Yana mai rik'o hannunta ni kuma na biyo bayansu, sojoji ne birjik a harabar gidan, bud'e motar ya yi ya bawa Reesah ledarta da ban nima tawa da ban, rik'o hannunsa Reesah ta yi gami da cewa. "Daddy anjima za ka dawo?” "Eh” Yace mata gami da sakar mata murmushi ya shafa kanta. "Allah ya yi miki albarka, ya kare ki ga dukkan wasu azzaluman mutane, masu son ganin bayan rayuwarki da ta mahaifinki.” Daga haka ya shiga motarsa ya jata yana jin zuciyarsa wani iri da ban yayin da nikuma na janyo hannunta muka koma ciki ina mai jin soyayyarsa na k'ara girma a zuciyata, rigima Reesah ta so ta yimini da k'yar na lallasheta na bud'e mata alawoyin da Daddy ya kawo mata. _A tsaye suke suna hirarsu ta d'a da mahaifi cikin annushuwa da farin ciki sai k'yak'yata dariyarsu suke, baiyi aune ba yaga wata mace ta silalo ta bayan Daddyn fuskarta lullub'e da wani bak'in yadi ta caka masa wuk'a a wuyansa, wata gi gi tacciyar k'ara ya saki gami da kiran sunan Daddyn._ Gaba d'aya zufa ta keto masa da ya farka daga mummunan mafarkin da ya yi, Khadijah ma a firgice ta farka ta na tambayarsa lafiya, bai furta mata ko da kalma d'aya ba, don ji yake bazai iya d'aga harshensa ba muddun bai ji lafiyar Daddynsa ba, hannunsa na rawa ya lalibo numbersa ya kira. Cikin bacci Daddy yaji wayarsa na k'ara, cike da tunanin mai kiransa a cikin wannan tsohon daren ya lalibo wayar ya yi picking da hanzari don gudun ka da ta katse, muryarsa cikin bacci yace. "Sadauki lafiya? ” Wata wawiyar ajiyar zuciya ya saki, gami da furta Alhamdlillah cikin kyakkyawan furuci. "Lafiya lau Daddy, dama na kira ne naji lafiyarka. ” "Kar ka damu Sadauki, babu abinda zai faru da mu sai abinda Allah ya rubuta mana cikin rayuwarmu, duk abinda kaga ya samu bawa dama muk'ad dari ne, ka dinga tunawa da hadisin nan da yake cewa: Da dukkanin al'umma za su had'u don su amfanar da kai da wani abu to ba zasu tab'a iya amfanar da kai ba sai dai da abinda Allah ya rubuta a gareka, kuma da zasu had'u akan su cutar da kai da wani abu ba za su tab'a iya cutar da kai ba sai dai da abinda Allah ya rubuta a kanka, an d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe. Don haka dukkan wata rayuwa da za ka fuskanta ka karb'eta hannu bibbiyu Allahn da yake jarabtarka yana nan sane da kai, akwai ranar farin ciki tana nan zuwa, sai dai ina fatan lokacin yazo sanda nake kusa da duniyarka ba sai na yi nesa da ita ba, yanzu ka yi kwanciyarka ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru sai abinda Ubangiji ya tsara mana.” Jikinsa ne yayi sanyi k'alau, yana jin yadda gabansa ke fad'uwa a kai² har sukai sallama ya kashe wayar, alwala ya yi ya kalli gabas don ko ya koma ya kwanta baccin ba zai zo ba. Washe gari da safe Mom ta fice ba tare da sanin Daddy ba, abinda ba ta sani ba yana ankare da ita ta na fita yabi bayanta, shima kuma abinda bai sani ba tayi hakanne don ya biyo bayanta, cikin wani gida yaga ta shiga, ba tare da tunanin komai ba ya bi ta a baya, don idonsa ya rufe da sanin abinda ya kawo ta cikin gidan. K'asa kunne ya yi jikin k'ofar da ya ga ta shiga, muryar Sumayya ya ji tana. "Mom, yau Allah ya cika mini burina ina d'auke da ciki wata biyu, duk da ba cikin Miq d'ina bane amman kuma zai taso a d'ansa, zanyi amfani da wannan cikin don ganin na k'unta tawa duk wanda ya shigo Cikin duniyarmu ni da Miq d'ina........ ALK'ALUMAN NAGARTATTU. [4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH* [8:12PM/1/4/2020] Folow me on wattpad @Rashuna. _Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_ __________________ *TWENTY NINE* _A cikin sati guda Daddy ya d'aura aurena da Khadija, bayan ya ji duk abubuwan da suka faru da rayuwarta shima ya yi mugun tausaya mata, ba'a samu rikici ko tashin hankali ba daga gurin Sumayya da Fareesah, ko wacce ta yi mugun fahimtata, k'arara nake hango tausayin Khadijan a idanuwan Fareesah, watana guda da auran Khadija Inno ta hura mini huta sai na auri Fareedah._ _Fareedah 'yar k'anwar Inno ce uwa aya uba aya, tun da ta d'an tasa mahaifiyarta take son na aureta, hakanne yasa ta dinga amfani da Inno don ganin buk'atarta ta biya, tana son aurena da Fareedah ne don su samu dukiyata yadda ya kamata, bare ma idan burinta ya cika Fareedan ta samu haihuwa tare da ni, don a yanzu Daddy ba shi da wani buri da ya huce yaga jikansa tun kafin ta Allah ta kasance a garesa hakanne yasa suke kwad'ayin ganin jikan nasa ya fito daga tsatsansu don sun san zai samu matuk'ar ga ta mara misaltuwa_ _Kwata² ban bawa Inno fuskar auran Fareeda ba hakanne yasa nake kakkauce mata, don ni har ga Allah bani da ra'ayin yin mace sama da d'aya sai gashi kuma mata uku suna cikin k'addarata kuma babu yadda na iya Allah ya riga ya tsara hakan tun fil azal, to ashe ma Inno tana ta shirye²n bikina da Fareeda sai ana ya gobe d'aurin aurena da Fareeda aka kaiwa Daddy katin d'aurin auren ba tare da ni na sani ma, kirana Daddy ya yi ya nuna mini katin gami da mini nasiha akan na yi biyayya a gareta mahaifiyata ce aljannata na k'ark'ashin k'afarta idan har ina buk'atar shigarta to itama sai na mata biyayya kamar yadda nake masa ko ma fiye da hakan._ _Haka na tara matana na labarta musu auren da Inno ta k'ak'aba mini, suma sun karb'i sabuwar k'addarar da tazo mini da hannu bibbiyu._ _Had'ad'd'an gida na tafka ko wacce na mata phart d'inta da ban, Inna ma na yi mata na ta da ban, phart d'ina ne a tsakiyar gidan, na Sumayya da Fareesah a gefen damana, na Khadija da Fareeda a gefen haguna, na Inna kuma daga gefen gidan._ _Cikin matan nan nawa Sumayya da Fareesah ce kad'ai ke samun lokacina, kuma dukkaninsu suna matuk'ar k'ok'arin ganin sun dai daita tsakanina da sauran matan nawa amman hakan sam ya faskara, Fareesah ta sha yin fishi da ni haka za ta gaji ta sauko, ita kuwa Sumayya dama na munafirci ne, ba yadda ba tayi ba don ganin ta cire soyayyar Fareesah daga raina sai dai ALLAHN da ya dasa ta har yau bai bata damar cireta ba, kuma tana nunawa Fareesan soyayya da kulawa,ina yawan samun masu kawowa Sumayya suka amman ba wanda nake bawa fuska k'arshe ma sai dai mu b'arke da fad'a, sai da Fareesah ta yi haihuwa shida duk Sumayya na kashesu ba tare da ansan me take aikatawa ba, mun jajje neman magun guna gurare da dama an tabbatar mana ba sanyi ne ko zafi ne ke kashe mana yara ba, rayayyen ne Allah bai kawo ba, to dama abokin Daddy yana ta gaya masa mugayen halayen Mom da suke a b'oye yak'i yadda da shi, hakanne yasa ya dinga nema masa magani a b'oye, a hankali shima tunaninsa ya fara dawowa jikinsa, hakanne yasa ya kuma zuba ido akan takun Mom da Sumayya har ya fara samo haske kad'an daga cikin b'oyayyan halinsu hakanne yasa ya kuma mik'ewa tsaye gurin nemawa d'ansa magani._ _Khadija ta sha kama Sumayya tana tsafi amma kuma sam ta k'asa gayawa kowa, itama Sumayyan ta san Khadijan ta ganta hakanne yasa ta yi babban shiri a kanta, haihuwa ta bakwai da Fareesah ta yi shine Khadija ta kama ta tana sokawa jaririn allura a ka, firgita iya firgita ta yita da gudu ta nufi sashen Inna don ta san ko taje ga Miq ba zai saurareta ba, amman ko da taje gurin Innan kasa furta kalma d'aya ta yi, sai kuka da ta fashe da shi, ga abinda take son fad'i ya tsaya mata a mak'oshi kuma babu damar fitar da shi, tun daga lokacin nutsuwa ta bar jikin Khadija don sosai Sumayya ta sakota gaba, duk wani mugun abu in za ta yi ta daina b'oye mata don ta san ba za ta tab'a fad'e ba, sanin abinda take aikatawa shine babban kuskure a rayuwar Khadijan._ _Cikin da Fareesah ta kuma samu a shine suka yanke shawarar tura ta lahira gaba d'aya har abin da ke cikinta, yayin da shikuma Daddy ya k'udurci abu a ransa ba tare da ya sanarwa kowa ba, cikinta na shiga wata takwas Daddy ya turasu England ba tare da sanin kowa ba, ya kuma hana sa gayawa kowa daga cikin matansa, a lokacin da zasu tafi ne kuma ta gano abubuwan da ke faruwa tsakanin Sumayya da Khadija, babu yadda ba ta yi ba Khadijan ta gaya mata abinda ke faruwa amma fir ta k'i._ _Shikuwa Daddy ya tura su England ne ba wai don bai yadda da k'addara ba sai don k'ara gasgata makasan jikokin nasa yana tare da su. sai da ya yi masa gargad'i sosai kada ya sake ya sanarwa da kowa k'asar da suka tafi._ _Dr Hisham abokinsa ne tun na yarinta, shima d'an katsina ne a England ya yi karatunsa na likita shine suka rik'esa aiki a can, dalilin da yasa kenan yasa Daddy ya zab'i su tafi England._ Mun riga munyi abubuwan da suka faru a baya, sai kuma kuci gaba da biyo alk'alamin Bebe'arth don war ware muku abubuwan da ke gaba. Mai buk'star cigabansa ya sameni Kai tsaye a wannan layin 09037093702 ALK'ALUMAN NAGARTATTU An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels