An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [10/4, 8:37 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA!* *Arewabook@ayshadansabo* _©️Ayshat Ɗansabo lemu_ *Paid book 08167768704* *Ina mai farawa da yabo tare da ɗinbin godiya ga Allahu (SWT) da ya bani ikon fara wannan rubutu,sannan ina miƙa godiya ga tarin makaranta littafaina waɗanda suka yi mini uziri tare da tayani farin ciki akan ƘADDADAR ZOYA da ya zama bai kammala ga makaranta ba ,a sakamakon saye labarin da aka yi domin a juyashi ya zama film.Sannan ina muku albishir da cewa wannan labari na RAYUWA DA ƘADDARA zai zo muku da tarin faɗakarwa da ɗibin darussa na rayuwa kala-kala,domin kuwa labari ne da zai taɓa ɓangarori da dama.Sannan zai nishaɗantar tare da sanyaya zukatan makarantansa da sassanyar soyayya mai tsayawa a rai,don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta.Sannan kuma babban abin farin cikin shi ne, na sauƙaƙa kuɗin sayen wannan labari,duba da yanayi da ake ciki na matsewar tattalin arziƙi,domin ina ma kowa sha'awar ya shigo cikin tafiyar,don haka Regular zai zo muku akan 400 kacal VIP kuma 700.* *GARGAƊI* *Wannan labari da dukkanin abinda ya ƙunsa mallakin marubuciyar ne,don haka ban amince a juya min labari ko sauya shi ta kowa ce iriyar fuska ba.Ban amince a karanta min labari a kowani kafar sadarwa ba tare izinina ba,yin hakan babban kuskure ne,don haka a kiyaye.* *Chapter 1* *Free page* *SHIMFIƊAR LABARI...* *GARIN ZAZZAU.* Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni da cewa, Zazzau wata daɗaɗɗiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun ɗaruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci. Yadda kalmar ‘Zazzau’ ta samo asali Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro. A wani kaulin kuma ‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’. Asalin Kalmar Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina Bambancin Zazzau da Zariya shine,Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan ƙasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni. Kafuwar Masarautar Zazzau A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Da kuma ƙaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci. Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Haɓe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama. Kuma Zazzau na daya daga cikin ƙasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki. Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi Kafuwar birnin Zariya Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta. Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537. Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya. Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya. Don ta girmama sunan ‘yar uwarta,kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne masarautar Zazzau. Zaria na da ƙofofi da dama na tarihi. *MABUƊI* *ƘOFAR DOKA ZARIA.* Daga cikin ƙofar doka akwai wata unguwa da ake kira da suna jushi, cikin wani ƙaton family house da ake kira da gidan Alhaji Musa Mai Itace.Idan ka shiga daga cikin ƙaton filin wajen gidan,akwai manyan ɓangarori guda biyu masu ɗauke da sasanni.A kowani sasa zaka samu akwai ɗakuna ciki bibbiyu da falo kaman guda uku ko biyu,waɗanda duk matan aure ne a ciki na ƴaƴa mazan gidan da suka gada bayan mutuwan Mahaifinsu Alhaji Musa Mai Itace. Sasa na farko a kuma ɓangaren farko da ke kallon gabas,ɗauke yake da ɗakunan matan aure guda biyu.Kowanne ciki biyu da falo,sai kuma daga waje ta ɓangeren hagu turakan Mai gidan ne mai suna Malam Adamu.Daga zaure kafin ka shiga akwai ɗakuna biyu masu ɗauke da ƙaramin bayi a ciki na samarin ɓangaren,waɗanda duk ba a gari suke karatu ba sai sun zo hutu suke buɗewa su shiga.Matan Baba Adamu su biyu ne, Inna Karimatu da Inna Amina.Dukkaninsu suna da ƴaƴa dashi,ƴaƴan uwargida Inna Karimatu su uku ne, biyu maza ɗaya mace. Abubakar, Usman sai Auta Zainab,sai ƴaƴan Amarya Inna Amina su kuma guda biyu ne duka mata,Aliya da Bushirah. Sai ɓangaren sasa na biyu na Baba Auwalu,mai ɗauke da ɗakunan matan aure guda biyu jere reras suna kallo ƙofar zauren shigowa sasan.Sai ɗaki guda guda ɗaya mai ɗauke da ciki da falo a ware,wanda shi ne matsayin turakan mai gidan.Ɗakin farko na uwargida Inna Hauwa ne,wacce take da ƴaƴa mata guda biyu, Hameeda da Asiya.Sai ɗaki na tsakiya na Gwaggo Salamatu ce,ita Allah bai bata haihuwa ba sai ɓari da tayi ta faman yi har gashi girma ya fara kamata haihuwa bai samu ba.Daga wannan sasan sai sasan kusa da ƙarshe na Baba Mai Itace, kamar yadda ahalin gidan suke kiransa.Amma sunansa na yanka shi ne Malam Lawal Mai Itace, haka jama'ar unguwa suka san shi da shi.Amma da zaran ka shigo gidan da Baba Mai Itace kowa ke kiransa,sabida duk cikin zuriyyan Musa Mai Itace shi ne ya gaje sana'arsa na kasuwancin saye da sayar da Itace,da kuma sarin dabbobi yana kawo wa kasuwar ƴan awaki yana sayarwa.Ɓangarensa duk yafi na sauran girma da tsafta,kasancewar matan nasa duka biyu masu tsananin tsafta ne da kula da muhalli.Ɗakin Uwargidansa mai suna Halimatu da ake kira da Umma shi ne na farko,tana da Ƴaƴa guda uku duka mata,Raudah,Sumayyah sai auta Suhailah.Sai Amaryarsa da suke kira da Anty Safiya,ɗakinta shi ne daga ƙarshe kusa da turakar Mai gidan.Tana da ƴaƴanta biyu, Ibrahim Khaleel sai auta mai suna Maimunatu.Su biyu Allah ya tsayar mata,a haihuwa biyar da tayi suna komawa basa rayuwa. Daga sasan Baba Mai Itace sai na ran gidan baki ɗayanta,wato Hajiya Zuwairah da ake kira da Hajiya Kakah.Ita ce Mahaifiyar duka waɗannan mazan gidan baki ɗayansu,kuma mace tilo cikin mata biyu da Alhaji Musa Mai Itace ya sama haihuwa dasu.Ita kaɗaice ta rayu da Musa Mai Itace har Allah ya amshi rayuwarsa,ya kuma nufa ita ce zata yi masa takaba,domin duk sauran matan da yake aure rabuwa suke yi.Daga Hajiya Kakah sai Amaryarsa uwar ƴaƴansa mata guda biyu mai suna Hajiya Hindatu,ita rasuwa tayi bayan ta aurar da duka Yaran nata Mata guda biyu da suka zama Hajiyoyi a yanzu.Hajiya Murja da Hajiya Aishatu,waɗanda Allah ya ɗaukaka su tare da azurtasu da auren mazaje masu kuɗin gaske.Suna Hajiya Kakah ya samo asali ne daga bakin Babban jikanta Abubakar da suke kira da Yaya Sadeeq,shi ne ya fara kiranta da hakan har sunan ya bita ya kuma ɓatar da sunanta na Hajiyar Mai Itace da ake kiranta da shi ada.Sasan na ɗauke da ɗakinta ne rak,sai wani warin ɗaki ɗaya da take sauke baƙin kwana idan tayi,wanda bata cika samunsu ba sai idan ana wani sha'ani a gidan na haihuwa ko biki. Ɗakinta na ɗauke da lafiyayyen ciki da falo manya masu kyau da tsari,wanda ƴaƴanta suka gatantata da kayan ɗaki na alfarma daidai rufin asirin da Allah ya basu,domin kafataninsu babu wanda za a ɗaga a kira shi da suna mai kuɗi sai dai mai rufin asiri.Sai kuma kasancewar wani dole yafi wani samu komin lacecewa,to hakan ce ta kasance domin duk cikinsu Baba Auwalu da suke kira da Baba Ƙarami, shi ne yafi ƴan uwansa rufin asiri da cima mai kyau.Domin shi kaɗai ne ya tsaya ya yi karatun boko,har ya samu aikin Lacturing a kwalejin FCE da ke Zaria. Ɓangaren hagu na gidan mai ɗauke da babban sasa guda ɗaya,shi ne ɓangaren Amaryar Alhaji Musa Mai Itace, mai suna Hajiya Hindatu.Babban sashi ne mai ɗauke da ɗakunan bacci har guda uku,sai falo da kitchen da aka haɗe daga jikin ɗakin aka ɓusa ƙofarsa ya fita ta waje.Babu kowa cikin ɓangaren a kulle yake domin ƴaƴanta mata biyu da ta bari sune suka mallaki gadon ɓangaren bayan rasuwan Mahaifinsu Alhaji Musa Mai Itace,su kuma kasancewarsu mata da suke gidajen mazajensu sai suka sake zuba kuɗi suka gyara sashin tare da mayar dashi ginin zamani sosai.Sun zuba komi na kayan alatu a ciki, idan ana sha'ani nan suke sauka su da Iyalansu.Hajiya Murja wacce ƴaƴan gidan ke kira da Gwaggo Murja ƴaƴa uku gareta duk mata,Hibbah,Muhaseen da Zakiyyah.Sai Hajiya Aisha da suke kira da Gwaggo Shatuh, Yaranta biyu duk maza,Ayman da Basam. Hajiya Kakah fitinanniyar tsohuwace,domin idan ta tada ballinta bata jin bari,kuma bata isa ta sanya doka akan jikokinta wani ya shata mata layi cikin matan ƴaƴanta ba.Fitinarta da rashin barin kota kwananta ya sanya kaf surukanta ke shakkarta,mutum biyu ne da suka gama da ita basa shayinta wato Amaryar Babban ɗanta Baba Mai Itace da kuma Uwargidan ɗanta na tsakiya Baba Adamu.Waɗanda suka haɗe kansu ba a taɓa jin cikinsu,suna shuka tsiyarsu yadda suka ga dama suna musgunawa abokanan zamansu. Baba Mai Itace ko ince Malam Lawal Musa,shi ne babban ɗa a zuriyyan Musa Mai Itace.Daga shi sai mai bi masa Baba Adamu sai kuma Auta a maza mai suna Baba Auwalu.Sai ɓangaren matan gidan Aishatu da Murja,waɗanda sune ƴaƴa na baya domin basu da tsara a cikinsu su Baba Auwalu duk sun girme musu da ratan shekaru masu yawa. Baba Adamu shi ne ya fara yin aure kafin Baba Lawal ya yi,har sai da ya haifi ɗansa na fari Abubakar Sadeeq sa'an nan Baba Lawal ya auro Uwargidansa Halimatu.Baba Lawal duk da kasancewarsa shi babba sai kuma Allah yasa ya fito a mutum mara kintsi sosai,domin tun yana matashinsa ya zaɓarwa kansa wace iriyar rayuwa na biye-biyen matan banza.Abinda ya hana shi aure da wuri kenan, har sai da Hajiya Kakah ta tashi tsaye sannan ya yi auren.Ya auro Umma ƴar mutanan Kaita da je jihar Katsina a lokacin yana tashen samu da sana'arsa na saida itace da kuma sayar da dabbobi,sabida shi da Baba Adamu tunda suka kammala secondary ɗinsu bayan rasuwar Mahaifinsu sai suka watsar da karatun boko.Sam suka ƙi cigaba da karatunsu sai neman kuɗi,duk kuwa da cewa ya barsu da rufin asirin da zasu iya juyawa har su tallafi karatunsu.Baba Auwalu da ya kasance ƙaramin cikinsu shi kaɗai ne Allah ya ɗaurawa son karatun boko,shiyasa ya maida hankali akan neman ilimi yana kuma haɗawa da sana'arsa ta ɗinki.A haka har ya kammala deegree ɗinsa,ya kuma samu lacturing abin sa yana yi. Ƴaƴan Hajiya Kakah kusan za a iya cewa basu da wani haɗin kai,domin kowa na gudanar da kalar rayuwarsa ne irin yadda ya ga dama.Sam bata tsaya wajen ganin kan ahalinta ya haɗu waje guda ba,ita dai kawai duk wanda yafi faranta mata yafi samu shi ne nata.Sannan ƴaƴansa suma su ne abin so a wajenta,bata damu da ta ga cewa ta haɗa kan ƴaƴanta ba bare har jikokinta su taso suma kansu a haɗe.Baba Auwalu shi ne Auta kuma wanda yafi ƴan uwansa samu,domin bayan lacturing da yake yi yana gudanar da business ɗinsa na noma da kuma sayar da yadikan maza.Sai ya kasance shi ne ɗan gaban goshinta,sannan ƴaƴansa su ne mafiya soyuwa a zuciyar Hajiya Kakah.Daga shi sai Baba Lawal Mai Itace,shi ma yana cikin waɗanda suka shige zuciyar Hajiya Kakah, duk da cewa tana baƙin cikin yadda ya kasance mara cikakken kamun kai.Wanda kafatanin jama'ar unguwar sun san da halin neman matansa,domin tun yana matashinsa an sha kama shi da ƴaƴan unguwa ya saka su a ɗaki yana lalata dasu.Yana da rufin asiri na sa'arsa na saida Itace da Dabbobi,wanda Allah ya sanya masa nasibi a cikinsa.Sosai yake samu da sana'ar saro dabbobi a kasuwannin ƙauye ya sayar,musamman idan aka lokacin sallan layya ya gabato.Baba Adamu shi ne kaɗai bai kaisu samu ba,domin sana'arsa na ɗinkin manyan riguna ba kasafai yake shiga ba,yana dai haɗawa da ƴan buga-bugansa ne kawai yana samun rufin asirin da suka fi ƙarfin ci da sha shi da Iyalansa.Daga bayan nan nema ya samu aikin tuƙi a gidan wani mai hannu da shuni,to Alhajin na kyautata masa matuƙa da gaske,yana kuma biyansa albashi mai tsoka. Allah ya albarkaci Ƴaƴansa da son karatu,musamman Ababubakar da Usman,waɗanda suke matakin kammala deegree ɗinsu a jami'ar KASU(Kaduna state University.Da taimakon sana'arsu ta ɗinki suke taimakon kansu,da kuma yiwa kawunansu hidimar yau da kullum har su taimako Baba Adama da Inna Karimatu da wasu abubuwan.Abubakar ƙwararran telan mata ne,yayin da Usman ya kasance telan maza. Gwaggo Shatu ita ce kusan ƙashin bayan ɗaukar nauyin biya musu kuɗin registration,duk da irin ƙiyayya da rashin jituwar da ke tsakaninsu da kishiyar Uwarsu Hajiya Kakah.Hakan ko kaɗan bai shafi ƙaunar da take wa ƴan uwanta Mazan ba,musamman Baba Adamun da Baba Lawal da duk cikin Yayun nata uku da su tafi jituwa. Kawunan surukan gidan baki ɗaya ba a haɗe yake ba,kamar yadda suka shigo gidan suka fahimci cewa kawunan mazajen nasu ba a haɗe yake ba.Sai suma kowacce ta kama abokiyar sabgarta wacce ta yi daidai da ra'ayinta cikin mata su shida da aka auro a gidan.Matan Baba Adamu Uwargida Inna Karimatu sam bata jituwa da Umma Halimatu,ba kuma komi ya kawo hakan ba sai hassada da take yi da Umman domin ta fita rufin asiri.Baba Lawal ya auro ta ne daga garin Kaita dake jihar Katsina,kuma iyayenta na da rufin asiri bakin gwargwado.Shiyasa aka kawota da komi na rufin asirin da ya zarta na Inna Karimatu da sauran surukan gidan baki ɗaya,dalili kenan kuma da Inna Karimatu ke kishi da ita sosai akan sauran kishin saurinta da bata ɗaukesu wata tsiya ba.Inna Amina kuma sai suka haɗa kai da Uwargidan Baba Auwalu,wato Inna Hauwa,aka ware Gwaggo Salamatu.Ita kuma Umma sai Allah ya haɗa jininta da Gwaggo Salamatun wacce ke da wani irin sanyin hali da rashin haniya,haƙurarriyar mace ce da ko kaɗan bata shiga harkar kishiyarta da Inna Amina da suka haɗe mata kai.Lokacin da aka auro Anty Safiya da ake kira da Anty Amarya, wato kishiyar Umma Halimatu,sai Inna Karimatu ta janyeta a jiki suka haɗe kai domin a dinga cusgunawa Umma.........✍🏻 *Via Aisha Ɗansabo Ibrahim 0504192664 GTbank,shaidar biya ta 08167768704.* [10/4, 8:46 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 2* A hankali ta buɗe manyan idanunta ta sauke akan kyakykyawar fuskar Ummansu,Bakatsiniya fara ma'abociyar kyawu da cikar halitta.Cikin sanyin murya irin na mai ciwo kyakykyawar budurwar ta furta, "Umma ruwa." Wacce aka kira da Umma tayi saurin ɗagowa ta kai dubanta sashin da budurwar ke kwance kan gadon marasa lafiyar,ta miƙe a sukwane ta nufi wajen da wata baƙar leda ke aje daga gefen gadon ta ɗauki pure water ɗaya tana faɗin, "Sannu Raudah,ya jikin naki yanzu?" Budurwa fara mai duhun haske kaɗan,ta sake ɗaura manyan idanunta ma'abota haske da wani irin ƙyalli akan Umman.Cikin muryar shagwaɓa ta ce, "Umma da sauƙi,amma kaina nake jinsa kamar zai rabe biyu sabida tsananin ciwo." Umma ta sake yi mata sannu tana zama daga gefen gadon ta ɓula ruwan ta miƙa mata.Budurwar ta amsa ta sha kaɗan ta miƙawa Umman tana sake komawa ta kwanta,Umma ta aje ruwan tana faɗin, "Zuwa anjima kaɗan za a sallamemu Raudah,gara mu koma gida ki sha na hausa haka nan tunda wannan zazzaɓi sam baya jin magani na annobane kawai." Raudah ta lumshe idanunta tare da sake buɗesu akan Ummanta,sai dai kafin tayi magana muryar Sumayyah ƙanwarta ta doki kunnuwarsu.Umma ce ta amsa sallamar tana bata izinin shigowa,budurwar wankan tarwaɗa mai kyawun halitta ta bayyana a cikin ɗakin.Idanunta akan Raudah da ke kwance ta fara sauke su tana mai cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin,ta isa bakin gadon ta aje ƙaramin kwandon ɗaukar abinci tana faɗin, "Sannu Yaya Raudah,ya jikin naki yanzu?" Raudah ta dubi Sumayyah ta ce, "Na ji sauƙi Sumayyah,ina Auta Suhailah?" Sumayyah tayi murmushi tana sake jinjina yadda Raudah ke ƙaunar ƴar Autarsu Suhailah a ranta ta ce, "Tana wajen Gwaggo Salmatu,idan har ba a sallameki yau ba za su taho zuwa yamma inji Gwaggon." Wannan karon Umma ce ta riga Raudah yin magana ta ce, "Badajimawa ba zamu wuce gida Sumayyah,likitan kawai nake jira ya dawo daga sallah ya rubuta maganin da za ta ƙarisa sha a gida mu tafi,zaman asibitin ya isa haka banda kisan kuɗi ba a komi gwara a koma a jaraba na gargajiya kuma." Sumayyah ta jinjina kai tausayin Ummansu da ƙaunarta na sake yawa a zuciyarta,cikin sanyi da raunin murya ta ce, "Hakane Umma,Allah dai ya bata lafiya ya kuma rufa asiri." Umma ta amsa da faɗin, "Ameen Sumayyahta,me kika iya girkawa yau?" Sumayyah da murmushi akan fuskarta ta ce, "Fatan shinkafa ne Umma,na ga tana son sa kuma na ɗan saka mata tumatir sosai ya ɗanyi tsami yadda za ta iya sha." Umma ta jinjina kai ta ce, "Sannu da ƙoƙari,Allah ya yi albarka,sai ki zuba mata ta sha tunda yanzu ta tashi." Raudah ta yinƙura ta tashi zaune ina sake bin ta da kallo kyawunta na fisgar idanuna.Kyakykyawace sosai fara mai duhun haske,tana da dogon hanci har baka.Akwai ta da manyan idanu farare masu haske da turuwan ciki sosai,gashin girarta mai yalwan gashi da cika ya ƙarawa fuskarta tsananin kyawu.Ƙaramin baki gareta mai ɗauke da pink lips masu taushi da duhu kaɗan,sai dimple da take dashi hagu da dama wanda suka sake ƙawata kyawunta matuƙa da gaske.Eye lashes gareta dogaye,waɗanda idan ta rufe idanunta suke wa idanun rumfa ruf abin sha'awa.Da yawa masu ganinta tana bacci sukan ce har tafi kyau idan tana bacci,sabida yadda kyawunta ke sake fita idan idanunta suka lumshe gashin suka yi ruf dasu zara-zara.Tana sanye ne da wata riga mara nauyi da ta ɗan jama jikinta,hakan ya bayyana cikar dukiyan ƙirjinta tsayayyu masu matuƙar fusgar idanu.A taƙaice dai Raudah kyakykyawar mace ce ta kowace fuska,ta kuma mallaki dirin jiki mai kyau koda take daga zaune zaka fahimci hakan. "Sumayyah Baba baya nan ne tsayin kwanaki biyu da kwantar dani amma ko leƙau?" Raudah ta jefawa Sumayyah tambayar cikin tsananin sanyin murya.Sumayyah tayi ƙasa da kanta tana bata amsa kai tsaye da faɗin, "Yana nan Yaya Raudah,Anty ce babu lafiya ita ma,shi ne fa duk hankalinsa yake a tashe,kinsan su ne ƴan so ba mu....." Umma ce ta katse Sumayyah cikin sauri ta hanyar ɗaga mata hannu tana faɗin, "Ya isa haka Sumayyah! Ashe ban hanaki furta irin waɗannan kalaman ba? Idan bai zo ya dubata ba sai me? Soyayyarsa kuka fi buƙata ko ta Ubangijin da ya halicceku ? Kun raina tawa soyayyar da ƙauna irin ta uwa da babu makwafinsa ne? Kar na sake jin kinyi magana makamancin wannan." Umma ta kai ƙarshen maganar wani irin kwantaccen ɓacin rai na haskawa cikin idanunta.Sumayyah da jikinta ya yi mugun sanyi,sai ta dubi Umma a narke tana faɗin, "Allah ya baki haƙuri Umma,In Sha Allah ba zan sake ba ki yafe mini." Umma ta ce, "Baki yi min laifin da za ki nema yafiya ba,abinda kawai nake so daku shi ne ku riƙa haƙuri da rayuwa a duk yadda kuka tsinci kawunan ku cikinta,ku daina damuwa da bambamci ko fifikon da Babanku ke nunawa a tsakaninku da ƴan uwanku,hakan bakomi bane kada kuma ku ƙullace a zuciyarku domin komi yana da iyakansa,don haka kuyi haƙuri ku daina sanya damuwa a rai." Sumayyah ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce, "Hakane Umma,In Sha Allah zamu daurewa hakan." Rahdah da tayi shiru zuciyarta na ƙuna,sai ta buɗe baki ta ce, "Amma Umma koda sau ɗaya ya leƙo ya dubani atleast zan ji cewa nima ya kula dani." Umma ta haɗe fuska sanin halin Raudah na kafiya da mita,idan har bata kashe maganar ba ta dinga mita akan rashin zuwan Baba Mai Itace ya dubata kenan har su koma gida.Cikin tsare gida ta dubeta ta ce, "Idan an sallameki kar ki tafi gida Raudah,kiyi ta zama har sai Baba Mai Itace ya zo ya ce miki sannu akan gadon asibiti kin ji ko?" Raudah jin maganar da Umma tayi a fusace ya tabbatar mata da cewa ranta ya ɓaci matuƙa da gaske,hakan ya sanyata sake shagwaɓe murya ta ce, "Kiyi haƙuri Umma ni ba haka nake nufi ba,abin ne kawai ya yi mini ciwo ace kwana biyu ina gadon asibiti bai zo ya dubani ba,bare har ya sauke hakkinsa na biyan kuɗin asibiti,duka hidiman ke ce kika yi kuma ba don ya rasa ba sai don kawai mune bai damu da mu ba bare ya damu da lafiyarmu." Raudah ta kai ƙarshen maganar murya na rawa hawaye na biyo fuskarta.Umma ta miƙe tsam ta fice daga ɗakin,domin idan ta cigaba da zama kusa da Raudah tabbas sai ta bige bakinta tunda ita mita ne da ita da shegiyar kafiyar tsiya.Sumayyah ce ta dubi Raudah bayan fitar Umman ta ce, "Yaya Raudah kiyi haƙuri ki bar maganar tunda Umma ta nuna bata so ana yi,amma ni kaina abinda Baba Ya yi ya min ciwo matuƙa ya kuma bani mamaki,domin baki ga yadda yake kashe musu kuɗi ba,babu maganin da bai siya ba duk yabi ya hana kansa sukuni." Rauda ta jinjina kai ta ce, "Babu komi Sumayyah Allah na nan,shi muke roƙa ya zama gatan mu ba shi ba,Allah zai yi mana sakayyah idan har shiga tsakaninmu da shi aka yi." Ta kai ƙarshen kalamanta ƙiyayyar Anty Amarya na sake yawa a cikin zuciyarta. Sumayyah ta ɗauki farantin plastic roba ta zubawa Raudah faten ta miƙa mata tana faɗin, "Gashi Yaya Raudah,ki daure ki cinye koda wannan ɗin ne." Babu musu Raudah ta amsa plate ɗin tana fara cin faten shinkafan.Suna yi suna tattauna matsalolin gidansu da irin ƙalubalen da suke fuskanta a cikinsa,a haka Umma ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama.Sumayyah ta amsa sallamar suna mai bin Umma da kallo,tayi kamar bata gansu ba ta isa wajen da ta gama haɗa komi nasu tana faɗin, "Idan ta gama ki maida komi gida zamu wuce,ya rubuta maganin sai ki je ki sayo a can bakin titin lemu,mu zamu rigaki wucewa gida." Sumayyah da ta gane da ita Umman ke yi,sai ta amsa ta da faɗin, "To Umma,har anyi sallaman kenan?" Umma ta jinjina kai ta ce, "Anyi Sumayyah,na kuma biya kuɗin komi sai fatan Allah ƙara rufa asiri." Suka amsa tare da Raudah a tare,kafin Raudah ta dubi Umma tana bata haƙuri.Umman ta waiwaya ta dubeta tana faɗin, "Matuƙar ba zaki daina yawan mita da wannan nacin maganar ba Raudah,to mun dinga samun saɓani dake kenan domin bana son mutum mai naci da yawan mita." Raudah tayi murmushi tana jinjina girman ƙaunar da Umman ke wa Baba Mai Itace,domin idan ka ji tana faɗa akan yawan mitanta to tabbas ta biyo ta kansa ne akan irin rashin adalcin da ba yayi akan su. Sumayyah ita ce ta taro musu napep har bakin asibitin,ta shiga ta taya Umma fiddo kayansu zuwa napep ɗin.Sai da ta ga tashin napep ɗin nasu sannan ita kuma ta nufi hanyar zuwa wani pharmacy a lemu domin ta nemo maganin da aka rubutawa Raudah. *JUSHI* Mai napep ɗin ya diresu a ƙofar gidan Musa Mai Itace,Umma ta fiddo kuɗinsa ta bashi sannan suka fito daga cikin napep ɗin.Da kanta ta fiddo kayansu tana aje su daga ƙasa,kafin ta waiwaya ko za ta samu Yaron da zai taya su da shiga da kayan zuwa ciki. Cikin sa a sai ga wani Yaro ɗan maƙwaftansu ya zo zai gitta,sai ta kiraye shi tana nuna masa kayan da zai taya su dashi zuwa ciki. Cikin nutsuwa a hankali Raudah ke takawa biye da bayan Ummansu zuwa ciki,suka ɗauki hanyar sasansu tana jin wani abu mai nauyi na taɓa zuciyarta akan irin rayuwar da ahalin gidan keyi na babu ruwan wani da wani.Kwanakinta biyu kenan a asibiti babu lafiya amma ace an rasa waɗanda zasu rufa mayafi su je suyi mata sannu cikin matan ƙannin Ubanta,banda Gwaggo Salamatu da ke da jituwa da Ummansu babu wata mace da ko a waya ta kira ta ce ashe suna asibiti Allah shi sauƙe.Har suka danna kai cikin sasan nasu zuciyar Raudah ƙuna take yi mata,ba kuma laifin kowa tafi gani ba sai na Hajiya Kakah,wacce ciki har da ita karan kanta bata je ta dubota a asibitin ba.Kuma tayi imani da cikinsu Asiyan Baba Auwalu ne da tayi mayawa biyu ko uku ma cikin kwanaki biyun,amma da yake su ba ƴaƴan so bane gashi har ta kwanta ta fito bata ko leƙa ta ce sannu ba. Umma ce ta kwaɗa sallama a tsakar sasan nasu,daga ciki muryar Maimunatu ta amsa sallamar.Suka wuce zuwa bakin barandarsu suka buɗe ƙofar ɗakin Umman suka shige,ko aje mayafi basu kai ga yi ba sai ga muryar Baba Mai Itace daga bakin ƙofar ɗakin yana faɗin, "Halimatu kun dawo? Sannunku da zuwa ya jikin Raudatun?" Wani irin takaici da baƙin ciki ya taso ya lulluɓe zuciyar Umma,ta dake cikin aro jarumta da danne ɓacin ranta ta bashi amsa da faɗin, "Jiki Alhamdulillah! Ta sama sauƙi za a jaraba dafa mata ƴan ganyayyaki ne ta haɗa dasu tunda na asibitin baya yi." Ya ƙarisa shigowa cikin ɗakin yana sauke ganinsa akan Raudah da ko kaɗan bata yi niyyar dubansa ba ya ce, "Hakane ita ma Safiya ɗazu na saka Ashiru almajiri ya nemo ganyayyakin har Hajiya Kaka ta ɓararraka mata,sannu Raudah ya jikin naki?" Ya ƙare maganar idanunsa akan Raudah da zuwa lokacin ta kasa riƙe hawayen da suka cika idanunta.Bata ɗago ta kallesa ba ta ce, "Na ji sauƙi Baba,dafatan mun yini lafiya ya jikin Anty Amaryan?" Da wani irin karsashi ya amsa da faɗin, "Ta samu sauƙi,bari na je na ɗebo miki maganin da Hajiya ta dafa kema sai ki duƙa sha ko?" Raudah ta jinjina kai ba tare da ta iya sake cewa komi ba ta lalubi ɗakinsu ta shige ciki.Umma ta rakata da ido tana sake danne wani azababben ɓacin rai da ke taso mata,Baban nasu ya miƙe yana duban Umman ya ce, "Halimatu kiyi haƙuri ban samu na leƙo ba har aka sallameku,nawa ne aka caza kuɗin maganin sai na fara rage miki tunda kuɗin hannuna duka dashi na biya kuɗin maganin Safiya." Umma ta saka idanunta da kyau cikin nasa tayi masa wani irin duba da ke sanyaya jiki da zuciyarsa a duk sanda ta jefeshi dashi,da wani irin karyayyen sauti ta ce, "Karka damu Baban Raudah,bama sai ka rage mini ko sisi ba,don na yiwa Raudah hidiman neman lafiya da aljihuna ai ban iya asara ba tunda zafin naƙudar da nasha nata bada wani muka raba shi ba,fata dai kullum shi ne Allah ya cigaba da buɗawa Halima hanyoyin samun da zata cigaba da ɗaukar ɗawainiyan ƴaƴanta babu gazawa." Tana kai wa ƙarshe ta shige ɗaya ɗakin da yake mallakinta ne tunda 2 bedroom ne,sai ta ɗauki ɗaya ta bar wa ƴan matan nata guda ya zama mallakinsu.Baba Lawal jikinsa ya yi mugun sanyi da kalaman Umma,domin ya sani maganganu ne masu zafi ta dunƙulasu cikin takaitattun kalmomi ta gaya masa.Jiki a saluɓe ya juya ya fice daga ɗakin,yana ji sam bashi da sauran kuzarin amso maganin da ya yi niyya ya kawowa Raudan. Koda Sumayyah ta dawo siyo maganin ta samu fuskar Umman sam babu walwala,domin da gaske maganganun Babansu ya ɓata ranta da har zai iya kallon idanunta ya gaya mata akan Safiya kaɗai zai iya ƙarar da kuɗinsa wajen nema mata lafiya amma ƴar cikinsa ko oho! Ya manta dukkaninsu suna da girman hakki a kansa,amma shi bai damu da hakan ba burinsa kawai ya fifita Safiya a ko yaushe ita da ƴaƴanta. Dukkaninsu kwanciya suka yi sukai bacci domin kwana biyu ba wani isasshen bacci suka samu a asibitin ba,sai can yamma sakaliya suka tashi suka sallaci sallan la'asar.Raudah na idarwa Sumayyah ta kai mata ruwan wanka banɗaki,ta fito ɗaure da zani ɗaurin ƙirji da ƙaramin hijab ta nufi banɗakin da ke gefen ɗakinsu wanda shi ne mallakinsu da shi suke amfani.Ita ma Anty Amarya nasu daga gefen ɗakinta ta ɓangaren hagu,don haka basu haɗaka da banɗaki kwata-kwata sai dai kitchen kaɗai suke da haɗaka da shi. A wanke bayin yake tsaf dashi,hakan ya sanya Raudah ta yo wankan ta fito cike da karsashi tana sake jin ƙwarin jikinta.Tana fitowa Anty Amarya da Inna Karimatu na fitowa daga ɗakin Anty Amaryan,tayi musu kallo ɗaya tana ɗauke kai tare da gaishesu a ladabce kamar yadda ta saba.Inna Karimatu ta gyatsine fuska ta amsa a gajarce tana ɗorawa da faɗin, "Ya jikin naki,Allah ƙara afuwa ko." Ita ma Anty Amarya ta yiwa Raudah ya jiki a lalace, suna yin gaba zuwa zauren fita daga sasan.Raudah ta shige ɗaki tana jin zafinsu sosai a cikin zuciyarta,idan da sabo yaci ace ta saba da halayyar waɗannan mutanen guda biyu,amma sai dai ta kasa sabawan.Musamman ƙiyayyarta da kullum take hangowa cikin idanun Inna Karimatu abu ne da ke kiɗima zuciyarta,domin tana matuƙar jin tsoron kada ƙiyayyar ya shafi irin soyayyar da gudan jininta ke mata.Jikinta a sanyaye sosai ta shafa mai tare da zura wata doguwar riga mara nauyi ta shan iska,sosai tayi kyau fuskarta tayi fayau irin na wanda ya tashi daga jinya.Ta rame sosai a fuska amma jikinnan na nan a cike luwai-luwai babu rama,dama kuma da wuya kaga tayi ciwon da ramarta zai nuna a jiki sai dai ya nuna a fuskarta kaɗai........✍🏻 [10/4, 8:46 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 3* Raudah na zaune a tsakar ɗakinsu da ke shimfiɗe da kafet ja da ya fara tsufa,amma irin guga da gyaran da yake samu ya sanya zaka gansa fes babu ƙura bare datti sam a kansa.Akwai setin kujeru zagaye da falon masu rangwamen tsada,waɗanda suma yadinsu ya fara nuna alamun tsufa.Daga ƙasan kafet ɗin take zaune wayanta riƙe a hannunta samfurin android mai matsaikacin kuɗi,wanda ta siya da kuɗin sana'o'in da take yi na hannu, na yin su cin-cin buns,alawar madarane,gullisuwa da aya mai suga.Sannan ta iya kitso sosai ana zuwa tana yi har ma a kirata gidajen masu hannu da shunin unguwar tayi musu su biya ta kuɗi mai tsoka,shiyasa take samun rufin asiri da kuma kuɗin yiwa kanta hidimar karatu idan Baban nasu bai ga damar saye ko biyamata kuɗin wasu abubuwan ba.Da yake ta kwana biyu ba lafiya bata kunna wayar ba,shiyasa tana kunna data wayar ta fara hucking alamun saƙonni sun yi yawa abin ka da wayar da ba wata babba can ba.Tilas ta goge whatsapp ɗin baki ɗaya ta sake ɗakko wata ta buɗe,hakan yasa wayar ta samu tsayawa saƙonni suka dinga shigowa na group-group da take ciki na skull da kuma na karatun novels da sauraron wa'azizzikan malaman addini na sunnah.Sannu a hankali take duba saƙonnin tana replaying wanda za ta iya,ta zo daidai kan lambar Yaya Sadeeq kamar yadda suke kiransa idanunta ya sauka akan saƙonsa.Ta buɗe ta karanta wani irin murmushi na kwanciya bisa kyakykyawar fuskarta,kalamaine na tsantsar soyayya da fatan samun sauƙi a gareta,sai kuma ƙorafin rufe wayarta da ta yi da biyo baya.Tana replying ɗinsa ta fahimci yana online,ko mintuna biyu ba a yi ba kuma sai ga kiran shi ya shigo mata.Ta ɗaga wayar cikin shagwaɓe muryar da ke sake susutashi,ta dinga amsa sannunsa a narke tana faman juya idanu tamkar yana a gabanta.A haka ta jiyo sallamar Zainab ƙanwarsa tare da shigowarta baki ɗaya kamar an jefo ta,sai Raudah ta ɗaga kai ta dubeta lokacin da Zee ɗin ke samun wajen zama bisa seater. "Raudah ya jiki,ashe an sallamoki? To Allah ya ƙara lafiya." Zainab ɗin ta furta hakan idanunta akan Raudah da gabaki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take yi da Yaya Deeku tana sauraran tausasan kalamansa.Sai ta ɗagawa Zee ɗin hannu tana ɗan cire wayar daga kunninta kaɗan ta ce, "Ai nayi fishi Zainab,ace kwana biyu ina kwance babu wacce za ta iya wanke ƙafarta ta je dubani,ina nan Jushi ina cikin asibitin Jamawa? Allah ya bamu lafiya daɗin abin ciwo yasan makwancin kowa." Daga haka ta mayar da wayar kunni ta bar Zainab nayi mata wani irin duba.Cikin zallar fusata ta miƙe tsaye tana jifan Raudah da harara ta ce, "To sarkin iya tsiwa da baƙar magana,baki gode biyoki da nayi yanzu har ɗaka ina miki ya jiki ba har sai kin bini da fatan ciwo ko?" Raudah ita ma ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan Zainab ɗin,wacce take baƙa mai kyawu da diri daidai misali.Cikin nuna ko oho ta ce, "Eh an yi miki!" Zainab da ta kasance tsarar Raudan ce,domin kuwa shekarunsu ɗaya tseran watanni biyu ne kacal a tsakaninsu,sai ta sake tsuke fuska ta ce, "Babu laifi kin yi da ƴar halak!" Daga haka ta juya ta fice daga ɗakin.Rauda ta rakata da harara tana jin zafi mai yawa a cikin zuciyarta na irin rashin haɗin kan da basu dashi a cikin ahalin gidansu.Umma ce ta fito daga ɗakinta tana duban Raudah da ta sauke waya daga kunni bayan kammala wayarta da Yaya Sadeeq ɗin,cikin tsare gida ta je fa mata tambaya da cewa, "Ke da waye ki ke magana a tsiwace Raudah?" Raudah ta narke fuska ta ce, "Zainab ce mana Umma,shigowa tayi gaida ni shi ne na salleta akan ƙin zuwa asibiti da basu yi ba." Umma ta ja ƙwafa ta ce, "Ki dai cigaba da nemo min magana Raudah,idan basu je asibiti sun dubaki ba ina sha dubunsu abokanan arziƙina da naki sun je ko? Hakan bai isheki ki godewa Allah ba har sai kinyi ƙorafi?" Raudah ta sake tsuke fuska ta ce, "Umma su da daban mutanen arziƙi daban,su ahalina ne da suka fi kowa kusanci dani,koda ace mutanen duniya duka sun halarci dubani su ɗin ne sukai saura dole abin ya yi mini ciwo,musamman idan na duba ƙarfin jini da zumuntar da ke tsakaninmu dasu,uwa uba ni da Zee da Aliya dukkaninmu tare muka taso,ya dace ace kanmu a haɗe yake duk abinda ya shafi ɗayanmu ɗaya zai ji a jikinsa, amma hakan sam bai samu ba sabida bambamci da nuna fifiko da tun fil azal ya yi katutu a gindin iyayensu mata da kuma Hajiya Kakah mai ɗaurewa abin gindin zama." Raudah ta dakata da kalamanta tana yin ƙasa da kanta sabida irin kallon da Umma ke aiko mata.Umma ta sake jan ƙwafa ba tare da ta ce komi ba tayi gaba ta fice daga falon,domin kuwa bata san me za ta ce ɗin ba tunda dukkanin kalaman Raudah su ne asalin gaskiyar da babu wani kwaskwarima da za a iya musu.Ita kanta rashin haɗin kan ahalin nasu nayi mata ciwo,musamman da ya zama su mata sunfi rinjaye a yanzu,mazan duka su uku ne kacal a cikin ƴan mata su tara da ke gidan.Ashe kuwa suna da buƙatar haɗin kai matuƙar ana so familyn ya ɗaga da kyau ya kuma samu cigaba irin yadda ake fata,domin kuwa babu familyn da zai cigaba babu haɗin kai da ƙarfafa zumunta a tsakanin juna.Musamman idan aka ce ƴaƴa mata sunfi yawa a ciki,sabida su ne ƙashin bayan da in suka riƙe zumunta tayi ƙarfi take ɗorewa,idan kuma suka bijire to cikin daƙiƙa za a iya wayan gari kan ahalin gidan ya tarwatse baki ɗaya. Raudah ta bi bayan Umma da kallo tana sake shan alwashi a zuciyarta cewa ta gama yin shiru akan ire-iren waɗannan halin ko inkulan da ake nunawa,wanda yin shirun shi zaisa abin ya yi ta cigaba ana ƙullin juna a arai.Amma idan za a yi maka ka fito ka nuna abin ya yi maka zafi,to sai a dawo daidai,wanda ya yin idan zai gyara ya gyara in ma ba zai gyara ba ya dai san baka rufeshi ba ka faɗi abinda ke yi maka ciwo a zuci game dashi.Ta miƙe a hankali tana aje wayarta ta fito barandar ɗakin nasu inda Sumayyah ta shimfiɗa tabarma tana bitan littafan Islamiya kasancewar alhamis ce babu Islamiyar a yau,Sumayyan ta yiwa Raudah ya jiki tana jin daɗin yadda jikin ya yi mata ƙwarin da har za ta iya fitowa barandar ta zauna.Raudah ta amsa tana maida dubanta sashin da Umma ke shirin hura wutan gawayi daga wajen kitchen ɗin,ta dawo da dubanta kan Sumayyah ta ce, "Sumy Umman ce za ta yi girkin ke ba za ki yi ba?" Sumayyah ta murmusa ta ce, "Ita ta ce inyi zamana ita za ta yi,kinsan dai halin Umma dama bata faye son a karɓeta aikin girki ba tafi gane tayi da kanta." Cike da gamsuwa Rauda ta gyaɗa kai domin tabbas hakan ne,Umma bata son a taya ta girki sam.Duk aikin da za ka ɗauke mata ta yarda amma banda girki,tafi gane tayi da kanta sai dai su taya ta da gyaran kayan miya ko wani abin daban.Da yake mai zafin jini ce nan da nan ta hura gawayin ya kama,ta ɗaura ruwan tuwon dawan da shi take da sha'awa su ci da dare.Tana aikin suna jefa hira tsakaninta da ƴan matan nata biyu,cikin hakan Gwaggo Salamatu da Suhailah suka sanyo kansu cikin sasan bakinsu ɗauke da sallama.Raudah suka amsa da fara'a tana dire ganinta akan kyakykyawar autarsu Suhailah mai shekaru tara,wacce ta nufo wajanta direct tana faɗin, "Anty Raudah har kin warke dama?" Raudah ta saki murmushi tana janyo Suhailah jikinta ta ce, "Na warke autar Umma,hala unguwa ku ka je ke da Gwaggon taki?" Suhailah ta jinjina kai ta ce, "Kasuwa na rakata Anty Raudah." Raudah tayi murmushi tana gaida Gwaggo Salamatu da ke yi mata ya jiki,sannan ta maida dubanta kan Suhailah tana faɗin, "Lallai Suhailah ki ce kin sha na kasuwa shiyasa baki nemeni ba har muka dawo gida." Suhailah tayi dariya tana faɗin, "Na ji daɗi tunda kin warke,Gwaggo har ta siyo kifi za ta soya miki ta ce mai ciwo yana jin kwaɗayi idan ya samu sauƙi." Raudah tayi murmushi tana ƙin tanka maganar Suhailah sabida surutu ne da ita da rashin sirri irin na Yara,tunda girman jiki ne kawai gareta da shegen wayo. Suna nan zaune a barandar Umma tare da Gwaggo Salamatu suna hira Anty Safiyyah ta fito daga ɗakinta,tayi musu kallo ɗaya ta watsar tana taku ɗai-ɗai ta nufi kitchen.Kamar Gwaggo Salamatu ba za ta tanka ta ba sai kuma ta ɗaga murya ta ce, "Safiya sannu da gida, ya ƙarfin jiki? To Allah ya ƙaro afuwa." Daga bakin ƙofar shiga kitchen ɗin Anty Safiyan ta ja ta tsaya, ta waiwayo ta zubawa Gwaggo Salamatu ƙananun idanunta da suka gama soyewa a bariki ta ce, "Jiki nayi garas sai godiya,tunda gashi da ƙarfina zan shiga madafi in yiwa rabin raina girki." Tana kawai ƙarshen ta saki malalacin dariya ta faɗa cikin madafin ranta fes! Gwaggo Salamtu ta jinjina kai tana mayar da dubanta kan Umma da ke talge ta ce, "Ummansu bari na koma ni ma girkin zan ɗaura,Raudah Allah ƙarfin jiki sai kin ga saƙo idan na kammala girki." Ta ƙare maganar tana maida dubanta kan Raudah,wacce ta maida hankali akan Suhailah dake faman yin game da wayarta da ta ɗakko daga ɗaki.Ta ɗago kai ta dubi Gwaggo Salamatu ta ce, "To Gwaggo na gode Allah bada lada." Daga haka Gwaggo Salamatu ta miƙe tana kallon Suhailah ta ce, "Auta ba za a bini mu koma mu yi girkin bane ?" Suhailah tayi saurin tashi tana faɗin, "Zani Gwaggo ba ni ce zan dafa miki taliyar ba ki ka ce." Umma suka saki dariya Raudah na faɗin, "Lallai Gwaggo yau babban girki za a yi tunda Suhailah ce mai dahuwar." Gwaggo Salamatu tayi dariya tana kama hannun Suhailah suka fice,sosai Yarinyar ta shaƙu da ita kamar yadda ita ma take jin Suhailan a ranta sosai. "Momy! Momy!!" Muryar Maimunatu ke ƙwallawa maman nata kira tana fitowa daga ɗakin nasu duk a lokaci guda.Ta sauke ganinta akan su Raudah da ke zaune suna hiran sana'arta da take son gobe tayi abinda suka ƙare a ciki,cikin wani irin banzar murya ta ce da Raudah, "Yayar su Sumayyah ya jiki?" Raudah ta haɗe rai sosai tana amsata a taƙaice.Ko kaɗan bata sakarwa Maimunatu da take tsarar Sumayyah fuska,sabida yadda ko kaɗan bata da kunya ba ta ganin kowa da gashi sai Uwarta.Hakan ya sanya ita kuma ta kama girmanta a matsayinta na babba a sasan nasu baki ɗaya,sam bata ganin haƙoranta a waje da sunan murmushi ko dariya.Abinda ya janyo Maimunatun ke ɗan shakkarta kenan,sanin halin Raudah na rashin ɗaukar raini.Suka bi Maimunatun da kallo wacce duk kwanan duniya ninka bilicin ɗin da take yi take,ta sake wani irin ɗashewa da fari babu kyawun gani.Gabaki ɗaya ta ɓata kanta ta kuma canza halittar da Ubangiji ya halicce akai na baƙar fata,domin kuwa baƙace sosai ada kamar Momyn nata.Sai dai tana da kyawunta daidai gwargwado,amma bata godewa Allah ba gani take yi sai ta koma fara tamkar su Raudah sannan ita ma za a san tana da nata kyawun.Kuma Babansu na gani amma bai taɓa kwaɓa mata akan hakan ba,domin duk abinda zasu yi basa laifi a wajensa haka uwarsu ta ɗaurashi akan rashin ganin aibunta dana ƴaƴanta komin girman laifin da zasu yi kuwa.Ta riga ta mallakeshi ta wannan fannin sai abinda suke so shi suke yi a cikin gidan,ba kuma wanda iya isa ya ɗaga musu murya ko ƙanƙani. Anty Amaryan ce ta fito daga kitchen ɗin tana aje ganinta akan Maimunatun,wacce ke sanye cikin wasu riga da skat na atamfa da suka matseta matuƙa da gaske.Duk wani albarkatu na jikinta ya gama bayyana,musamman saman ƙirjinta da tana rankwafawa rabinsu ne zasu bayyana a waje.Wani ɗan figigin mayafi ne ta rataya a saman kafaɗarta guda,sai ɗaya ɓarin kafaɗar rataye da wani ƙaramin hand bag. "Kin fito Maimus?" Cewar Anty Amarya idanunta akan tilon ƴarta mace mafi soyuwa a cikin zuciyarta.Maimunatu tayi wani fari idanu tana duban cikin idanun Momyn nata ta ce, "Na fito Momy ya riga ya iso yana mota a waje,sai mun dawo me za a taho miki dashi?" Anty Amarya ta saci duban sashin da su Umma da ahalinta ke zaune,sannan ta maida dubanta kam Maimunatu tana ɗaga murya yadda zasu jiyota ta ce, "Irin kazar nan da ki ka taho dashi shekaranjiya nake so,ai mu dole mu wataya mu ji daɗi tunda kin kawo girma,Allah kuma ya zuba miki farin jinin masu hatiman nasara,ba irin su o'o da babu mashinshini ba,sai ɗaya da aka kama da ƙyar wanda ba a da tabbacin uwar za ta aminta a haɗa jini dashi." Ta kai ƙarshen kalamanta tana sakin ƙaramin shewa tare da shigewa cikin kitchen ɗin,ita kuma Maimunatu ta juya tana kama hanyar fita daga sasan nasu zuciyarta fes da samun lalatacciyar uwar da take barinta cin duniyarta da tsinke yadda take so. "Allah ka shirya zuriyyanka,Ubangiji ka sanya mana hannu cikin tarbiyyan Yaran mu kar ka bar mu da wayo ko dabarar mu ya Allah!" Umma ta furta hakan a cikin zuciyarta tana jin wani abu mai girma na ratsata,domin ko kaɗan irin rayuwar da Maimunatu ta ɗakko yi a cikin gidan ba mai sha'awa ba ce.Amma kuma idan ta tuna karin maganan Bahaushe da kan ce " _Barewa bata gudu ɗanta ya yi rarrafe!_ " Sai ta sake godewa Allah da ya sanya ta fito daga gidan dattijai da suka san tarbiyya suka kuma tsare mutuncinsu.Amma kuma har ila yau zuciyarta kan tsinke ta shiga firgici mai tsanani idan ta tuna cewa shi ma fa Baba Lawal ɗin kansa ba baya bane,idan har za a raba zunubansa tare da ƴaƴansa ne tabbas tana da sauran fargaba da razani mai yawa a cikin zuciyarta har sai randa Allah ya nuna mata aurensu Raudah lafiya.Wani gumi ya tsatstsafo mata ta kai hannu ta sharceshi jikinta na sake yin sanyi matuƙa,cikin dabara da bai wa kai ƙwarin guiwa ta rufe talgen da ta gama domin ya dahu kafin ta kai ga tuƙesa.A hankali ta sauke ganinta akan Sumayyah da Raudah,ƙauna da kuma tausayinsu ya dinga shigarta tana sake yi musu addu'ar neman tsari da kariya daga sharrin wannan zamani da kuma na ibilisan samari mayaudara masu lalata ƴan matan mutane.Can ƙasan zuciyarta kuma tana sake roƙawa Mahaifinsu shiriya da yafiya akan zunuban da ya aikata na keta alfarmar ƴaƴan wasu da ya yi a baya,duk da cewa a yanzu tana da tabbacin ya daina ya kuma yi tuba irin wanda ake so. Raudah ita ce ta fara miƙewa ganin shida har da rabi ta shige ɗaki,ta bar Umma da Sumayyah zasu kwashe tuwan tunda already akwai miyan kuka da zasu yi amfani dashi cikin freezer.Da yake Umman na da madaidaicin freezer da take sana'ar sayar dasu ruwa da yin su zoɓo da ƙanƙarar kuka,sosai take samun alkhairy da sana'ar sabida suna kusa da wata babban makarantar primary na gwamnati ne da ke nan cikin jushin.Baya ga sana'ar sayar da su ruwa da ƙanƙara tana sayar da kayan ƙulle-ƙulle irin su kuka,kuɓewa da sauran kayayyaki na yau da kullum na girki.Sosai kuma tayi suna a sayar dasu mangyaɗa da su omon wanki har ma da sabulai,duk tsukin unguwar ita ce tayi fice a fannin waɗannan sana'o'in.Tana kuma jan zarenta sosai, domin Allah ya dafa mata ciniki kota'ina take samu.Hakan ne kuma ya sake jefa ƙiyayyarta a zuciyar kishiyarta Anty Amarya,da kuma kishiyar saurin da aka haɗe mata kai da ita suka zama tamkar su uku ne mijinsu guda sabida yadda suke kishi da ita.Ba kowa bace kuma sai Inna Karimatu da ke ji tamkar ta buɗe idanu ta ga cewa babu Umma a cikin gidan, sabida yadda take jin tsanarta da yin hassada ga nasibin da Allah ya yi mata a harkar neman na kanta take kuma samun buɗi da rufin asirin da babu macen da ke da sana'aryi mai ƙarfi a cikinsu irin ta......✍🏻 [10/4, 8:49 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 4* Suna zaune suna cin abincin dare bayan sallar isha'i suka jiyo sallamar Hajiya Kakah ta shigo sasan nasu,Umma ce ta ɗaga murya ta amsa sallamar tare da yi mata barka da shigowa.Maimakon su ga ta fara yowa ɗakin Umman sai suka jiyo muryarta a bakin ƙofar ɗakin Anty Amarya tana rafsa sallama,Raudah ta dubi Sumayyah da ke kai loman tuwa baka ta ce, "Kin ji tsohuwar can bama nan za ta fara yowa ba, ikon Allah!" Umma tayi saurin hararar Raudah ta ce, "Raudah ki fita idanuna wallahi! Wai ke komai ne aka yi da bai miki ba sai kin tanka? Da nan da can ai duk ɗaya ne,tunda dukkanmu suna ɗaya muke amsawa na surukanta." Raudah ta ɗan zumɓure baki ta ce, "Umma ke dai kawai baki son a faɗi laifin Kakah da Baba idan sun kauce." Umma ta sake jefa mata harara ta ce, "Eh bana so tunda dukkansu babu abokin wasanki a ciki." Raudah bata kuma magana ba ta maida hankali akan cin soyayyan kifin da Gwaggo Salamatu ta aiko Suhailah dashi ta kowa mata,ita Suhailan ma tuni tayi bacci a cinyar Umma bayan gama cin tuwan da tayi. "Salamu alaikum masu ɗaki." Muryar Hajja Kakah ya doki kunnuwarsu Raudah.Sumayyah ta amsa sallamar tana faɗin, "Sannu da ƙarisowa Hajja Kakah,ko in fito in kamaki ne na san jikin tsufa." Hajja Kakah ta ɗaga labulen ɗakin Umma ta shigo tana faɗin, "Wane ke ƴar nema,ai ni nafi ƙarfin a kamani da ƙwarina nake ras in gaya miki." Umma ta gaida Hajjah Kakah cike da ladabi,ita kuma ta amsa tana kallon Raudah da tayi kicin-kicin da fuska ita a dole fishi take da Kakan da bata je ta dubata a asibiti ba.Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "To ke kuma mai jiki har yanzu babu lafiyan ne ki ke wannan cika da batsewar,ko kodai tsiwar ne ya tashi za a min fitsaran da aka saba?" Raudah ta sake tsuke fuska ta gaida Hajjah Kakan a gajarce,ita kuma ta amsa tana faɗin, "Ya jikin naki Raudah? Allah ƙaro afuwa,ban je na dubaki a asibiti ba nima atini na dinga yi a kwana biyun shi ya sanya,sannu kin ji ko." Raudah ta ce a shagwaɓe, "Hajjah Kakah kenan,jiki na warware ai,Allah ƙara mana lafiya amma dai a dinga kwatanta adalci tunda dai dukkaninmu jininki ne." Raudah ta kai ƙarshen kalamanta tana ƙin duban side ɗin da Umma take,domin ta gama ji a jikinta harara Umman ke zabgo mata.Hajjah Kakah ta miƙe idanunta akan Raudah ta ce, "Ai dama idan har na fita baki nema zagina ba sai an canza miki suna Raudatu,to na gode gara da kika min tukuici da waɗannan kalaman, ladan tasowa na dubaki,kuma gobe da safe ki sani ke ce za ki cika min robobin tara ruwana da wanke mini bayi." Raudah tayi saurin faɗin, "Wallahi Hajjah Kakah bani da wannan ƙarfin,daga fitowata daga asibiti abin babu ko tausayi?Allah ba zan iya ba gara ma ki nema mai miki." Hajjah Kaka ta fice tana faɗin, "Idan baki yi ba sai uwarki ta fansheki tunda a gabanta ki ke min fitsara ba za ta iya gwagwgwaɓe bakin tsiwa da fitsarar taki ba." Umma kaman jira take Hajjah Kakah ta fita ta dirarwa Raudah da faɗa kaman za ta kai mata duka,Raudah ta dinga bata haƙuri tana faɗin ta daina,ba za ta sake kula Hajjah Kakah ba.Umma ta ce cikin ɓacin rai, "Ki daina janyo mini ɓacin rai Raudah,bana son wannan tsiwar taki da rashin kama baki." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Amma Umma kin san idan ba a shiga gonata ba magana ma wahala take mini ko,kuma ita Hajjah Kakah da duk wanda kika ga na daina raga mawa a gidan nan to wallahi hakan ne maganinsu,domin idan mutum yana nuna musu shi sakarai ne sai ayi ta taka shi ana mayar dashi banza." Umma ta jinjina kai tana sake ayyanawa a zuciyarta cewa,Raudah ba za ta canza ba,ita haka halinta yake na rashin barin abu.Amma kuma miskilace ta ƙarshe idan ba ta so magana ko shiga shirgin kowa a gidan ba,sannan bata da rashin kunya da raina babba sai wanda ya zubda girman nasa. Ƙarfe tara da rabi suka ji shigowan Baba Mai Itace sasan,bai nemi inda suke ba kamar ko yaushe idan Anty Amarya ne dashi.Kansa tsaye turakarsa ya nufa bai ko yi tunanin ya sake duba ko ya jikin Raudah yake ba,shigansa bada jimawa ba suka jiyo sallamar Maimunatu.Da alamu tun fitar da tayi da yamma sai yanzu take shigowa gidan,Raudah da Sumayyah suka haɗa idanu dukkaninsu abin na musu nauyi da ciwo a zuci. Daga can ɗakin Baba Lawal ɗin kuwa,yana jiyo sallamar Maimunatu ya yi wuf ya fito yana tambayarta daga ina take? Kafin ta bashi amsa Anty Amarya ta fito daga ɗakinta tana watsa masa wani irin kallon raini.Cikin murya mai cike da isa da gadara ta ce, "Wuce ciki Maimus kin ji." Maimunan ta wucesa tayi cikin ɗakin Uwarta tana sakin wani malalacin murmushi.Baba Mai Ice ya dubi Anty Safiya rai a ɓace ya ce, "Yanzu Safiya irin rayuwar da kika ɗaurewa Maimuna gindi tayi kenan a cikin gidana?" Yadda ya yi tambayar da wani irin karyayyen sauti zai tabbatar maka da cewa baƙin ciki na matuƙar cinsa a zuci.Cikin nuna halin rashin damuwa ta dube shi kai tsaye ta ce, "Ƙwarai da gaske kalar rayuwar dana zaɓa mata kenan,ina sha nima a cikin irin kalar rayuwar ka ganni ka auroni? Ko kana tunanin barewa zata yi gudu ƴarta tayi rarrafe ne? Ko kuwa ka manta bashin da ka ɗauka na mutuncin ƴaƴan wasu yanzu ka ke gudun kar a fanshe a naka? Ka fita idanuna Lawal tun wuri,don wallahi yadda ta taso da farin jini babu wanda ya isa ya yi mata shamaki da jin daɗin rayuwa kamar yadda a baya kai ma ba a yi maka shamaki da morewa bariki ba." Ta kai ƙarshen maganarta tana kai hannu ta shafi gefen fuskarsa tare da sakin masa wani makirin murmushi. Baba Lawal ya ja ƙafafunsa da suka yi mugun sanyi ya juya zuwa turakarsa,wani irin hajijiya na tsananin ɓacin rai ke ɗawainiya da zuciya da gangar jikinsa.Safiya ta zame masa masifa ta kuma zame masa ƙarfen ƙafa cikin rayuwarsa,ya sha yin nadamar aurenta a ƙasan ransa domin sai yanzu ne yake gane kuskuren da ya yi na auro ƴar bariki da suka san juna tun waje ya kawota cikin gidansa yana tunanin zata sauya.Duk iya yadda yake jin baƙin ciki na cinsa a zuci ya sani ba zai taɓa iya ɗaukar wani mataki akanta ita da ƴarta ba,domin ya sha gwada yin hakan amma sai ya ji ya kasa.Da zaran ya haɗa idanunsa dana Safiya ko Maimunatu da sunan ɗaukar mummunar mataki a kansu yake ji zuciyarsa ta tsinke ta raunata matuƙa,daga ƙarshema sai dai Safiyan ta ɓige da ci masa mutunci kamar yadda tayi a yanzu ɗin. Dukkanin kalaman da Anty Amarya ta furta su ga Baba Mai Itace akan kunnuwar su Raudah da Ummansu ne,ba kuma yau ɗin ne karon farko da ta saba furta kalamai masu zafi a gareshi kamar yau ɗin ba.Shiyasa hakan bai zama baƙon abu a kunnuwarsu ba,sai dai a zukatansu suke jin tsananin zafi da ƙunar kalaman.Raudah ta miƙe zuciyarta na mata wani irin suya ta nufi ɗakinsu,ta samu bakin katifarsu ta zauna wasu zafafan hawaye suka shiga gangarowa daga cikin idanunta. "Meyasa Mahaifinsu ya fito a haka?" Raudah ta tambayi kanta da kanta tana ji a cikin zuciyarta cewa,tabbas basu yi sa'ar uba ba,domin dukkanin kalaman da Anty Amarya ke yi na sake jadda hakan a cikin zukatansu.Tunda suka taso suka yi wayo suke ji tana alaƙanta shi da kalmar zina da rayuwar bariki,wanda hakan ke nuna ya bibiyi matan banza a lokacin ƙuruciyarsa.Sun sha ji tana tunasar dashi a irin rayuwar da ya sameta ya aurota har ta zama uwar ƴaƴansa biyu,wanda idan har lissafinsu zai tafi daidai ne to hakan na nuna ita ma a karuwa ya aurota ba kintsatstsiya bace.Ta kai hannu ta share hawayenta tana ji zuciyarta na sake mata nauyi,wani irin abu mai tsananin ɗaci na cika maƙoshinta.Sumayyah ce ta shigo ta dubi ƴar uwarta da ke share hawayen tsananin takaicin kalar rayuwar da Babansu da Anty Amarya ke yi a cikin gidan,ta rakuɓe ita ma daga gefe guda tana faɗin, "Yaya Raudah Baba bai yi mana adalci ba sam!" Raudah ta ɗago idanunta ta sauke akan Sumayyah tausayin kansu da kansu na sake mamaye zuciyarta.Da wani irin sanyin murya ta ce, "Sumayyah na so ace Baba Auwalu ko Baba Adamu su ne suka kawo mu duniya,ko banza basu da abun faɗi da za a dinga bibiyan zuriyyansu da gori ana tunasar dasu zunubin da Ubansu ya kaita tun basu san kawunansu ba,ina jin ina ma Umma Ƙaddararta bata zaɓa mata miji irin Baba ba,domin tabbas aikin Ƙaddarace sabida kota'ina basu dace da juna ba." Raudah ta ƙarisa kalamanta tana share wasu zafafan hawayen da suka sakko daga cikin kwarmin idanunta.Sumayyah ta ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ni ma nasha auna hakan a zuciyata Yaya Raudah,sai dai kawai muyi haƙuri tunda Rayuwarmu da irin kalar Ƙaddarar da ta zo kenan na samun uba kamar Baba." Haka suka dinga tattauna halin da suke ciki su da Ummansu a cikin gidan,har zuwa lokacin da bacci yazo suka yi shirin kwanciya suka kwanta bayan Raudah ta gama waya da masoyinta kuma Yayansu Yaya Deeku. *WASHEGARI...* Ƙarfe tara saura suka kammala dama koko da soya ƙosai,Umma ce tayi ƙosan Raudah kuma ta dama kokon ta juye shi a flask.Umman ta dubi Raudan ta ce, "Ɗakko wancan ƙaramar kular ki zubawa Hajiya Kakah ƙosan ki miƙa mata ɓangarenta tun da zafinsa." Raudah ta zumɓuri baki alamun bata so hakan ba,amma sanin bata isa cewa komi ba ya sanya ta ɗakko kular aka zubawa Hajjah Kakah ƙosan.Sai da ta koma ɗaki ta ɗakko ƙaramin hijab ta sanya sannan ta koma kitchen ta ɗauki kular ƙosan,tana fitowa sukai kaciɓus da Anty Amarya ta fito da ledar bread da kayan tea daga ɗakin Baban nasu.Raudah ta gaida ita a gajarce ta fito daga sasan tana jin ƙarin tsanar matar a cikin zuciyarta,sannan gefe guda tana jiyewa Babansu tsoron yadda zai tashi a gaban Ubangijinsa da shanyayyen ɓarin jiki sabida nuna fifiko da rashin adalci a tsakanin Iyalinsa,matuƙar bai tuba ya daidaita adalci a tsakaninsu ba.Har ta isa sasan Hajjah Kakah saƙa da warwara take yi akan lamarin Babansu da irin halakan da Anty Amarya ke sake jefashi a ciki,tayi sallama daga bakin ƙofar shiga ɗakin Hajjah Kakan tare da tsayawa jiran izinin shiga.Daga ciki Hajiya Kakah ta amsa sallamar tare da bai wa Raudah izinin shiga,ta shiga ta aje kular a kusa da Hajjah Kaka tana mai gaida ita cike da ladabi.Hajjah Kakah ta amsa da kulawa tana kallon Raudah ta ce, "Me kuka yi ne na karin safen yau?" Raudah ta nuna mata kular tana faɗin, "Buɗe ki gani mana Hajjah Kakah." Kafin Hajjah ta kuma magana sallamar Asiyan Baba Auwalu ya shiga kunnuwarsu,ba tare da ta jira an bata izini ba ta danno kanta cikin ɗakin tana faɗin, "Ƴar tsohuwa ina kwananki." Hajjah Kakah aka washe baki tana kallon kular da ke hannun Asiya ta ce, "Ƙalau na kwana Asiyatu,ya Iyayen naki suka tashi?" Asiya ta yatsine baki ta ce, "Ƙalau!" Ta waiwaya ta dubi Raudah da ta sha kunu ta ce, "Yayansu Suhailah ya jiki,ashe kin dawo gida daga asibitin?" Raudah ta ce, "Alhamdulillah na warware." Daga haka bata kuma magana ba sai kallonta da ta mayar kan Hajjah Kakah da ta buɗe ƙosan da ta kawo mata,ganin ƙosai yana turiri sai ta maida murfin kular ta rufe tana janyo kular da Asiya ta aje tayi gaba ta buɗe.Ƙamshin lafiyayyen doya da ƙwai ya bugi hancinansu daga ita har Raudah da ta jirayi ganin ikon Allah,nan da nan fara'a ya ƙaru akan fuskar Hajjah Kakah tana faɗin, "Ma Sha Allah! Auwalu ba dai sanin kan cima mai daɗi ba,me za a yi da wani gayan ƙosai babu mahaɗi babu komi?Raudatu ga doya nan ɗauki guda ki maida mugun yawu." Ta ƙare maganar tana duban Raudah da har ta miƙe tsaye,cike kuma da takaici ta dubi Hajjah tana girgiza kai ta ce, "Allah amfana Hajjah Kakah,ko zaki kawo kular ƙosan a mayar tunda kin sama abin ƙwalaman da yafi maiƙo da daraja?" Hajjah Kakah ta haɗe fuska ta ce, "Daɗina da ke ba dai iya yaɓa baƙar magana ba,to ba zan bayar ba ko almajirina na bai wa sadakarsa,dama kuma sadakan ƙosai falalane dashi musamman idan ka baɗe shi da yaji ka bayar da ɗuminsa duk sai ka wayi gari ka garari maƙiyi." Raudah ta saki murmushin takaici tana juyawa ta baro ɗakin Hajjah Kakah tare da ficewa daga sasan baki ɗaya.Har ta ɗauki hanyar sasansu sai kuma ta ga dacewar ta shiga wajen Gwaggo Salamtu su gaisa ta kuma yi mata godiyan kifin da ta aiko mata,sai ta karya kwana ta nufi sasan Baba Auwalu tana cigaba da takaicin halayyan Kakah na kwaɗayi da nuna fifiko ƙarara.Da sallama ta sanya kai cikin sasan Baba Auwalun,ta tadda Asiya da Hameedah zaune daga bakin barandar ɗakin Inna Hauwa suna karyawa.Plate ne a gabansu shaƙe da soyayyan doya mai ƙwai,sai kofunan shayi biyu a gabansu suna korawa dashi.Suka yiwa Raudah Bismillah lokacin da ta gittasu za ta wuce ɗakin Gwaggon Salamatun,bayan sun gaisa sa Inna Hauwa da ta fito daga madafinsu,sai ta girgiza tana faɗin, "Wallahi na gode a ƙoshe nake." Daga haka ta nufi bakin ƙofar Gwaggo Salamatu tayi sallama,daga ciki Gwaggo Salamatu ta amsa tana bata izinin shigowa.Ta shiga suka gaisa ta cidda ita tana cin zazzafan ƙosan da Umma ta aiko Suhailah dashi ta kawo mata,sanin cewa tana son ƙosai sosai da safe.Daga gefe guda kuma soyayyan dankalin hausa ne da egg,tayi masa haɗin sauce sai ƙamshi yake.Dukkanin sasunan uku babu wacce ke girkin haɗaka da kishiya,tun asali kowa girkinsa yake yi daban sai dai a raba kuɗin cefane a bai wa kowacce.Shiyasa kowa gashin kansa yake ci babu ruwansa da ɗan uwansa,mai ƙarfin sana'a ma sai dai ta ƙara ƙawata abincinta tare da cin duk abinda tayi ra'ayi ita da mai gidanta idan ranan kwananta ne.Juyin duniya Gwaggo Salamatu tayi akan Raudah ta ɗauki dankalin ta ci amma ta ce ta ƙoshi,haka ta haƙura ta ƙyaleta sanin halin Raudah na kafiya.Ta fito daga ɗakin Gwaggon kenan za ta fita daga sasan Baba Auwalu ya fito daga turakarsa,ta gaidashi cike da ladabi ya yi mata ya ƙarfin jiki? Ta amsa a sanyaye tana jin wani abu mai ciwo na danne zuciyarta. "Dama duk sun san bata da lafiya har ta kwanta asibiti amma babu wanda ya yi kara ya leƙa ya dubota?" Raudah ta tambayi kanta tana sake jin ciwon wannan rashin zumunci da rashin haɗin kan na ahalin Hajjah Kakah."A ce ƴar ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya ta kwanta asibiti kuma kuna rayuwa ne a muhalli guda,amma a rasa wanda zai yi kara ya je ya duba maka ƴa? Anya wannan rayuwa da suka ɗaukarwa kansu mai bulle musu ce su da ahalinsu baki ɗaya? " Raudah ta sake tambayan kanta tana tunasar da kanta cewa,ai shima kankat ɗin da ya kawota duniya ta manta ne bai je ba? Sai tayo gaba ta fito daga sasan tana jin cewa tabbas akwai gyara a cikin rayuwar ahalin Hajjah Kakah,kuma babu wacce ke da laifi sama da ita domin ita ce tushen komi. Ta fito kenan daga sasan Baba Auwalun ta ji ƙaran shigowar mota cikin ƙaton filin compound ɗin nasu,wanda rabinsa kaf tsibin Itace ne na Babansu a jirge.Wasu an faskara ba a kai ga kasasu ba,wasu kuma an ware su dami-dami alamun na ƴan sari ne zasu zo su kwashe abin su.Wata baƙar golf ta hango ta shigo cikin filin wajen ta tsaya,sai ta ɗan ja ta tsaya tana son ganin wasu baƙi ne suka yi da safe haka? Idanunta ya sauka akan baƙin matashin da ya fiddo jikinsa daga cikin motar,dogo ne sosai ma'abocin kyawu daidai misali.Sanye yake cikin ƙananun kaya red da suka amsa jikinsa tare da fiddo ƙuruciyarsa na matashi mai ganiyar cin lokacinsa,daga ɗaya ɓarin ma ƙofar ta buɗe,wani matashin ya futo mai hasken fatar da bamai yawa ba.Bashi da tsayi kamar wancan baƙin na farkon,shi kuma yana sanye cikin farar shadda da ya yi masa mugun kyau.Take wani irin murmushi ya ƙwacewa Raudah,ta maida idanunta akan baƙin matashin tana sake gano zallar kyawun da ya ƙaro daga nesa.Cikin nutsuwa ta juya ta ɗauki hanyar shigewa ɓangarensu domin bata da buƙatar wani ya hangota ya tsaida ita a cikinsu,shiyasa cikin sauri ta shige sasansu zuciyarta cike da murnar dawowan zaratan Yayun nasu guda biyu Yaya Abubakar da Yaya Usman..........✍🏻 [10/6, 8:52 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 5* "Ma Sha Allah! Allah ya sanya albarka a cikin iliminku,Ubangiji yasa an yi wa yawan rai ne Sadeeku da Usmanu,Allah kuma ya kawo aikin yi ya ƙarawa sana'ar ɗinkinku da nemanku albarka.Madallah! Madallah!! Da ganin wannan rana da kuka amso sakamakon ku mai kyawun gani." Baba Adamu ne zaune daga ƙasan shimfiɗaɗɗen ledar tsakar ɗakinsa yana jero waɗannan addu'o'in cike da farin ciki.Abubakar da Usman tare da Inna Karimatu ne zaune kewaye dashi fuskarsu ɗauke da fara'a,suka amsa addu'ar Baban nasu cike da farin ciki.Inna Karimatu da kanta ya sake girma ya fashe da tarin alfaharin kammala deegree ɗinsu,sai ta dubi Abubakar tana faɗin, "Yanzu yaushe za a fara turaku bautar ƙasar kenan?" Yaya Sadeeq ya dubeta da walwala ya ce, "Muna saka rai mu tafi a first batch In Sha Allah!" Ta jinjina kai tana sake faɗin, "To Allah yasa,sai batun cigaba da aikin ɗinkin naku,za ku cigaba a Kadunan ne kuna dawowa duk sati kuna dubamu ko kuwa dawowa za ku baki ɗaya ku tare a garin nan da sam babu cigaba a cikinsa sai ƴan hassada?" Yaya Sadeeq ya murmusa yana sake shiga mamakin yadda halayyar Innarsu sam basa sauya ya ce, "Muna can In Sha Allah,ai ba za mu iya rabuwa da Ubangidanmu ba idan har ba wani ƙwaƙwƙwaran aiki ne ya samu gare mu ba,domin wannan sana'ar ita ce mu Inna,mun samu rufin asirin da ba zai ƙidayu ba da ita." Baba Adamu ya jinjina kai ya ce, "Tabbas haka yake,zamanku a can ɗin zaifi kafin ku tafi bautar ƙasar,zama anan Zaria ba zai yiwu muku ba alhali ga inda kuka fi samun rufin asiri sosai." Wannan karon Yaya Usman ne ya yi magana ta hanyar faɗin, "Haka ne Baba,Allah dai ya cigaba da rufa asiri,dama akwai maganar da nake so in sanar daku." Ya ɗan dakata yana kallon fuskar Inna Karima da ta zubo masa idanu.Baba Adamu ya jinjina kai ya ce, "Faɗi maganarka muna sauraronka Usmanu." Yaya Usman ya gyara zama ya fara da faɗin, "Baba dama akwai Yarinyar da nake nema ne a can Unguwar Kawo Kaduna,to Iyayenta sun matsa da in tura magabatana ayi magana koda kuwa ba za a yi auren nan kusa ba, ya zamana dai manya sun shiga cikin maganar." Ya sake dakatawa yana kallon fuskokin Iyayen nasa biyu domin ganin a wani yanayi suke amsar maganar tasa? Inna Karimatu tayi zaraf ta ce,"Gidan waye a can ɗin?Ina nufin wane ne Ubanta,shin akwai maiƙo ko babu? Domin ba zai yiwu ka nemo ƴar da ba za ka ƙaru da Iyayenta ba sai dai kai su yi ta tatse min kai da ɗan abinda ka ke rorowa." Da wani firgici da zallar mamaki Yaya Usman ya dubi Mahaifiyarsu maganganunta na sake kaɗa zuciyarsa,cikin sanyin murya da sadda kai ƙasa ya ce, "Inna Babanta ma'aikacin gwamnati ne, suna da rufin asiri daidai gwargwado,kuma Inna ai ba gidan maiƙo ake dubawa ba,gidan mutunci da tarbiya ake dubi masu nasaba mai kyau." Inna Karimatu ta taɓe baki ta ce, "Haka ne kam,to ammafa kasani rayuwa tayi sauyawar da babu mai son ya raɓi talauci ko jajibo ma kansa ƴar gidan mataulata,wacce komi suka zo suka samu suke handamansa,don haka gara dai kusan ina ne zaku ɗakko aure ehe!" Baba Adamu ne ya riga yin magana wannan karon ta hanyar faɗin, "Kin gama Karimatu?" Inna Karima ta jinjina kai tana wani harare-harare,Baba Adamu ya girgiza kai yana maida dubansa ga Yaya Usman ya ce, "Usmanu ka kwantar da hankalinka,matuƙar dai kuna son junanku kai da Yarinyar to babu matsala,zan sanya a bincika min su wane ne Iyayenta kafin a tura a nemo maka izinin fara zuwa gidansu,kai kuma Abubakar a wani babi ka ke akan zancen aje Iyalin?" Yaya Sadeeq ya dubi Baba Adamu yana yin ƙasa da kansa gami da kwantar da murya ya ce, "Baba ni Raudan Baba Mai Itace ita ce zaɓina, domin ita zuciyata ta jima tana ƙauna har ma mun fara fahimtar juna ni da ita." Ya kai ƙarshen kalamansa yana kallon yadda murmushi mai faɗi ya bayyana a fuskar Mahaifinsa.Sai dai kafin Baba Adamu ya ce komi sai ganin Inna Karimatu suka yi a gaban Yaya Sadeeq,bata kuma jira komi ba ta sanya hannu ta ɗauke shi da mari.Cikin wani irin kakkausar murya take faɗin, "Ƙarya kake yi Sadeeku! Wallahi baka isa ka tozartani ba,ka rasa ƴar wacce zaka so sai ƴar maƙiyiyata da bani da wanda na tsana a duniya sama da uwarta? To bari ka ji tun wuri ma ka iya bakinki kada na sake jin ka furta kalmar so ka jingina shi da jinin Halimatu matuƙar nonona ka tsotsa ka rayu a duniya!" Ta kai ƙarshen kalamanta tana wani irin huci tamkar kumurcin maciji.Baba Adamu ya daka mata wani gigitaccen tsawa tare da nunata da yatsa ya ce, "Karimatu a gabana? A gabana ki ke faɗin kar ya sake danganta kalmar so ga jinin ɗan uwana ciki guda? To bari kiji matuƙar Raudah tana son sa bata da miji sai shi,sai dai duk abinda zaki yi kiyi,ki daina ganin ina zuba miki ido kuna yadda kuka ga dama ke da kishiyar Halimatu ki ɗauka cewa nima kin mallakeni ne,wallahi baki yi wannan isar ba Karimatu, kar nake kallonki zan kuma tabbatar miki da cewa Adamu ba sakarai bane kamar yadda ita ta mayar da Yaya Lawal ɗin sauna." Yana kai ƙarshen kalamansa ya dubi Ƴaƴan nasa ya ce su tashi su basu waje.Kaman jira Inna Karimatu take yi su fice ta sakar masa wani gigitaccen kuka tana faɗin, "Me kake nufi Baban Sadeeq? Wallahi matuƙar ni nayi naƙudar Sadeeq to ko zan yi yawo tsirara bai isa ya haɗa jini da jinin Halimatu ba domin na tsaneta na tsani ahalinta baki ɗa....." Wani irin bugu ya kaiwa bakinta yana huci,cikin zallar ɓacin rai ya ce, "Ashe ko zaki yi yawo tsiraran,domin kuwa aure babu fashi in kinga Sadeeq bai auri Raudah ba ita ce ta ce bata son sa, ko kuma ƙasa ne ya rufe idanuna!" Ya kai ƙarshen maganar yana ficewa a fusace ya bar mata ɗakin. Yaya Sadeeq kuwa suna fita ɗakunansu da ke cikin zauren sasan nasu kowanne ya nufi ɗakinsa,kowanne a cikinsu zuciyarsa babu daɗi.Yaya Sadeeq ɗin ya yi kwance bisa katifar ɗakin nasa yana kai hannu ya dafe kansa,kalaman Inna Karimatu ke yawo a kansa,yana lalubo dukkain halayyar Umma dana su Raudah domin ya gano aibu ko kasawarsu a nagartattun halaye amma ya gaza samun nakasu a tattare dasu.Tun tasowarsa yake son sanin wani irin laifi ko saɓani ne ya shiga tsakanin Innarsa da Umma har take mata irin wannan ƙiyayyar,amma har kwanan yau ya gaza gano wani laifi ko saɓanin da ya janyo wannan kalar ƙiyayyar.Abinda ya fahimta kawai shi ne,Innarsa mugun hali ne da ita da kuma muguwar hassada akan irin yadda Umman ta fita komi na rayuwa.Ya dafe kansa da ke tsananin sara masa yana jin ƙarin ƙaunar Raudah a cikin zuciyarsa mai tsanani,ko kaɗan baya ji akwai barazanar da zai sanya shi ya janye daga neman aurenta domin idanunsa basu taɓa gane masa wata ƴa macen da ta mallaki cikar halitta irin wanda yake so ba sai a jikin Raudah.Tunawa da ya yi basu sama shiga kowani sasa ba tun shigowarsu gidan ya sanya shi ya miƙe ya lalubi wayarsa ya fito daga ɗakin,ya kulle ɗakin nasa ya fito daga zauren yana nufan sasan Hajiya Kakah domin fara miƙa gaisuwa zuwa gareta. "Amincin Allah ya tabbata a gareki ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe!" Daddaɗar muryar Yaya Sadeeq ya furta hakan lokacin da ya isa ga ƙofar ɗakin Hajiya Kakah.Daga ciki ta amsa da wani irin ɗoki ta ce, "Ameen ya masoyin Manzo! Barka da sauka,sannunku da isowa." Yaya Sadeeq ya ɗage labulen ɗakin ya sanya kansa ciki fuskarsa na haskawa da maɗaukakin murmushi.Idanunsa ya sauka akan Hameedah da ke wa Hajja Kakah gyaran falon,ta gaida shi cike da ladabi kamar yadda suka ba.Yaya Sadeeq ya amsa mata fuska babu walwala sosai,domin kaf gidan babu mai ganin haƙoransa a waje sai sahibar tasa Raudah,ita ma ba kasafai ta faye gani ba domin miskili ne shi mare son raini ko ƙanƙani.Shiyasa sam bayi wasa dasu bare su raina shi,iyakarsa dasu gaisuwace sai idan ya yi niyyar yi musu alkhairy ya siya musu wani abin ko ya raba musu kuɗi idan sun zo ganin gida daga Kaduna.Kusa da Hajjah Kakah da ke zaune saman kafet ɗin da ya mamaye tsakiyar ɗakin ya zauna,cikin murya mai cike da karsashi da jin daɗin ganinta ya shiga gaidata a ladabce.Ta amsa cikin farin ciki tana faɗin, "Madallah da amsar sakamako,nayi farin ciki nayi murna ƙwarai,Ubangiji yasa albarka ya kawo aiki mai tsoka ka riƙa kai ni Hajji da Umrah duk shekara Sadeekuna!" Yaya Sadeeq ya saki murmushi ya ce, "Ameen Hajjah Kakah,Allah ya zaɓa mana abin yi mafi alkhairy tsakanin aikin ko kasuwanci." Hameedah tana kammala goge saman TV stand ɗin Hajjah Kakah ta sulale ta fice daga ɗakin,domin sam ta san ba za ta kuma sukuni idan yana cikin ɗakin ba.Hajiya Kakah ta dubi jikan nata mafi soyuwa a zuciyarta sakamakon yawan kyauta da alkhairynsa gareta,ta buɗe baki cike da ƙauna ta ce, "Ameen Sadeeku,sai maganar aje Iyali idan abin yi mai ƙarfi ya samu,duk da cewa wannan sana'ar ta ɗinki kaɗai ya isheku ku ci da Iyali dashi,ina aka kwana,shin ka samu wacce ka ke so ne ko kuwa?" Sadeeq ji yayi gabaki ɗaya Hajjah Kakah ta famo masa mikin kalaman Innarsa akan abinda zuciya da gangar jikinsa ke so da kuma kwaɗayin mallaka.Ya turɓune fuska cike da nuna zallar damuwa ya soma da faɗin, "Hajiya Kakah na samu wacce nake so,kuma ƴar gida ce jinina Raudah,amma Inna tayi rantsuwar ba zan haɗa jini da Umma ba matuƙar tana raye,ni kuma nan duniya banga macen da nake so,nake kuma burin mallaka ta zama matata ba sai Raudah." Ya dakata yana kallon yadda fuskar Hajjah Kakah ya fara tsukewa da matsanancin fishi.Yana dasa aya ta ce cikin karaɗi, "Ita Karimatun ne har tayi kaurin wuyan da za ta furta ba za ka auri jininka ba? To ita kuma a suwa daddawa a kunu ni Zuwairah? Ka kwantar da hankalinka ka ji ko,indai har Raudatu na sonka,kai koma bata son ka tunda kai dai ita ce zaɓinka to zan kuwa nuna ƙarfin ikona wajen ganin anyi wannan auren nan bada jimawa ba." Hajjah Kakah tayi maganar tana huci kai ka ce tana da wani say ne akan Inna Karimatun da akan idanunsu bata iya katabus,amma a yanzu a bayan idanunta gashi ta maze tana yanko zance kamar za ta iya cika masa alwashin da ta sha.Shi ko Yayah Sadeeq kalaman Hajiya sai suka kwantar da hankalinsa,domin yafi kowa sanin halinta na nuna iko akan su jikokinta da bata haɗa soyayyarsu da kowa ba.Cikin nuna farin ciki ya ce, "Allah ya ja kwana Hajjah Kakah,Raudah tana sona ba ma sai kin nuna ƙarfin iko akanta ba,tana baya-baya dani ne sabida tsoron irin ƙiyayyar da Inna ke gwada musu su da Ummansu,abin na min ciwo Kakah tun daga randa na fahimci Umma nagartacciyar uwace da ta ɗaukeni tamkar su Raudah a zuciyarta,bata taɓa min koda kallon banza ba duk da irin yadda Inna bata ƙaunarta,bata taɓa nuna min cewa ina da bambamcin da ƴaƴanta ba,ta ɗaukeni tamkar ɗanta ne ko kaɗan ban ga wani dalili guda ɗaya da Inna zata kafa hujja dashi wajen zurfafa ƙiyayyarta ga Umma ba." Ya dakata da kalamansa yana jin tsananin ɗaci da ciwon yadda Innarsu ta fito a wata iriyar bahaguwar mace mai tsananin hassada da son kanta.Hajjah Kakah ta sake ƙanƙance idanu ta ce, "Baka kaini takaici ba Abubakar,domin nafi kowa sanin bakomi ne a zuciyar Karima game da Halimatu ba sai tsabar hassada da ƙyashin yadda ta fita samun duniya,tana adawa da cigaban da kullum ke samun rayuwar Halimatu na iya sarrafa sule ya zama sisi,gashi kuma ta fita kyawawan halaye da zuciya mai kyau,na sha gwada yiwa Karimatu karatun ta nutsu akan Halima amma da zaran na haɗa idanu da ita duk sai na ji tsoro ya cika zuciyata,daga ita har Safiya na rasa kalar asirin da suka banko mini da duk jarabata bana iya katabus a kansu,amma akan maganar aurenka da Raudah dole in nuna ƙarfin ƙwanjina,in kuma dage da sadaka domin na garara daga dukkanin sharrinsu har Ubangiji ya tabbatar da wannan lamari." Hajiya Kakah ta kai ƙarshen kalaman tana narkewa Sadeeq tamkar za ta saki kuka.Ya dinga rarrashinta tare da bata shawaran yadda yakamata ta bullowa lamarin har ya samu su rinjayi Inna Karimatu burinsa ya cika akan mallakar Raudah.Ya jima sosai a sasan Hajjah Kakan kafin ya yi sallama da ita ya fito ya nunfi sasan su Raudah,yana tafe zuciyarsa na ayyano masa kyakykyawar fuskarta da ya yi kewar gani tsayin watanni kusan uku da basu shigo Zaria ba.Ya doka sallama daga cikin tsakar sasan nasu idanunsa na yawo cikin muhallin da tsafta ya wadacesa,ko'ina a share tsaf simintin tsakar sasan na ɗaukar idanu kamar kullum sai an saka kilin an wanke tsakar gidan.Maimunatu ce ta fito daga ɗakinsu tana amsa sallamar tasa,ta ɗan rusuna kaɗan ta gaida shi tana ƙin kallon fuskarsa domin tana tsanani shakkarsa fiye da Yaya Usman da ke jansu a jikinsa.Ya zuba mata idanu babu ko ƙirfawa yana mamakin irin hasken da ya ga tayi tashi guda,cikin matuƙar tsare gida da tsuke fuska ya ce, "Ke! Uban me ki ke shafawa kika yi irin wannan farin tashi guda? Bleaching ki ke yi sabida baki da hankali ke daƙiƙiyace ko?" Maimunatu ta zumɓuri baki ƙirjinta na dukan uku-uku,cikin aro jarumta ta bashi amsa da faɗin, "Yaya nifa ba bleaching nake ba mayuka ne kawai na samu da suka amshi fatata." Ya maka mata wata uwar harara yana kausasa murya ya ce, "To daga yau kada ki sake shafasu domin kuwa mayukan bilicin ne,idan kuma na cigaba da ganin wannan farin na sake wanzuwa akan fatarki saina ɓallaki a cikin gidannan idiot!" Ya ƙare maganar da tsawa sosai a muryarsa.Hakan ya sanya Maimunatu saurin yin gaba ta suri buta ta nufi banɗaki,dama ta fito da zummar zuwa banɗakin ne ta ji sallamarsa har ta amsa tare da gaida shi ɗin.Cike da ɓacin ran banzayen halayen da tun watannin bayan baya ya fara kula dasu game da Yarinyar ya isa bakin ƙofar ɗakin Umma yana sallama,daga ciki muryar Ummance ta amsa masa sallamar tana masa lale da zuwa.Ya sanya kansa cikin falon yana wadata fuskarsa da murmushi,yayinda idanunsa suka shiga zagaye falon da daddaɗan ƙamshin turaren wuta ke tashi.Cike da ladabi ya gaida Umman,ta amsa da fara'a tana ɗaurawa da faɗin, "An ce sai kun amsa sakamako za ku dawo,har an amsa kenan Sadeeku? To Allah ya sanya albarka yasa yawan rai aka yiwa,Allah ya kawo babban rabo ya tsare manaku a kowani mataki na rayuwa." Yaya Sadeeq ya amsa cikin matuƙar jin daɗin addu'o'in Umma.Shiru ya ɗan ratsa a tsakani kafin Yaya Sadeeq ɗin ya kasa haƙuri ya dubi Umma ya ce, "Umma su Suhailah basa nan ne na ji sasan tsit?" Umma tayi murmushi tana gano dukkanin take-takensa akan Raudah,cikin sanyin muryarta ta furta, "Suhailah na wajen Gwaggonta Salamatu,su Sumayyah na ɗakinsu suna faman zuzzuba tuwan madara a mazubin da suke packaging ɗinsa za a kai shago." Daga haka ta ciri murya tana kiran sunan Sumayyah,cikin seconds ta bayyana a cikin falon idanunta na sauka akan Yaya Sadeeq ɗin.Da wani maɗaukakin murmushi da murnar dawowarsu garin take gaida shi,ya amsa da kulawa yana sake zubawa ƙofar ɗakin nasu idanu.Burinsa kawai idanunsa su sauka akan kyakykyawar fuskar Raudah,Sumayyah tayi masa fatan alkhairy akan kammala karatunsu da amsar result ɗinsu da suka yi cikin nasara.Ya amsa yana sake yaba nutsuwa da hankali irin na ƴaƴan Umman,domin ko Hameedah da take tsarar Raudah bata san tayi tunanin yi musu fatan alkhairy akan kammala karatun nasu ba.Ta juya ta koma ɗakinsu tana sanar da Raudah cewa Yaya Sadeeq sun dawo gashi can a falo,Raudah da zuwa lokacin tayi wanka tana sanye cikin wata straight gown na atamfa pich colour da ya amshi jikinta.Ta ɗago daga manna sticker ɗin RAUDAH'S CUISINE a jikin pack ɗin gullisuwa da tuwan madara da suka gama packaging,ta ɗaura idanunta akan Sumayyah tana faɗin, "Ma Sha Allah! Barkansu da dawowa,bari na ƙarisa manna stickers ɗin in fita mu gaisa." Yadda tayi maganar cike da basarwa ya sanya Sumayyah sakin murmushi,cike da tsokana ta dubi Raudah ta ce, "Kai ke ko Yaya Raudah,duk ya ƙagu ya ganki ne fa, baki ga yadda yake faman kallo ƙofar ɗakinnan ba,wallahi Yaya Deeku ba ƙaramin kamuwa ya yi a sonki ba." Raudah ta harari Sumayyah tana faɗin, "Au kema kin zama ƴar saka idanu ce da gulma Sumy?" Sumayyah ta saki dariya tana faɗin, "Daga faɗan gaskiya kuma Yaya Raudah? Ai kowa ya kalli yadda yake kallonki ya san soyayyarki ce fal a cikin zuciyarsa,ke ma kuma daga yadda ki ke amsa wayarsa kaɗai za a fahimci kina son sa Yaya Raudah,kuma wallahi za ku dace da juna." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Duk ba wannan bane Sumy, ina jin tsoron halayyar Inna Karima da sam ba ƙaunar Umma take ba bare kuma mu,shiyasa a koda yaushe nake ƙoƙarin danne duk wata soyayyarsa da nake ji a cikin zuciyata domin bana son duk abinda zai saka Inna Karimatu ta samu hanyar ɗagawa Umma hankali ko cin mutuncin mu." Sumayyah ta jinjina kai jikinta na mutuwa da kalaman Raudah,domin tabbas ita ma tana hango ƙura idan har Inna Karimatu ta gano irin soyayyar da Yaya Deeku da Raudah ke wa junansu......✍🏻 _Hello my luvly fans!😍Shin labarin ya fara shiga zukatanku ko har yanzu da saura dai? Me ku ke shinshinowa ne cikin wannan tafiyar da kuma rayuwar ahalin Hajjah Kakah? Mu haɗu comment section_ 😍 [10/8, 2:29 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 6* Tunda ta fito daga ɗakin nasu ya kafa mata idanunsa babu ko ƙiftawa,wani irin sassanyan kyawu ya ga ta sake ƙarowa.Zuciyarsa ta sake narkewa cikin ƙaunarta yana sake zurfafa ganinsa akan kyakykyawar fuskarta da kalar ƙaramin hijab ɗin da ta saka ya hasketa matuƙa,kalar baby pink ne da ya fiddo asalin hasken fatarta ya kuma yi mata kyau sosai.Cikin takunta mai cike da nutsuwa ta ƙarisa bakin seatern da ke facing ɗinsa ta zauna,tana mai jin nauyin kaifafan idanunsa da basu daina yawo a kanta ba.Da wani irin sassanyar muryarta ta gaidashi a ladabce tare da kwararo masa addu'an fatan alkhairy game da kammala deegree ɗinsu,ya amsa da wani irin fara'a yana sake jin matsananciyar ƙaunarta na kewaye jininsa. "Habeebty kin amince a yau na nemi izinin fara keɓewa da ke da sunan zance a wajen Baba Mai Itace?" Yaya Deekun ya jefawa Raudah tambayar idanunsa a kanta yana kallon yadda tayi ƙasa da idanunta.Ta ɗago ta dubeshi da manyan idanunta masu haske tana wani narke fuska,da shagwaɓa a cikin muryarta ta ce, "Da wuri haka Yaya Sadeeq? Me zai hana ka fara gabatar dani a wajen Inna kafin ka tunkari kowa da wannan batun?" Yaya Sadeeq zuciyarsa sai tayi wani irin kaɗawa da jin kalaman Raudah, "Kenan ita ma ta san za a iya samun matsala da Mahaifiyarsa sabida irin ƙiyayyar da take gwada musu?" Ya tambayi kansa yana kallonta da wani irin yanayi da idanunta suka kasa jurewa gani akan fuskarsa,sai ta sake yin ƙasa da kanta lokacin da yake faɗin, "Habeebty Inna ba za ta hana aukuwar dukkanin abinda Allah ya hukunta ba,ni dai burina ki bani goyan baya na fara neman izinin Baba Mai Ice,domin na riga da nasar da Babanmu ke ce zaɓina." Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin muryar da ya sanya Raudah ɗago kanta ta dubesa,ya kashe mata idanu guda tare da karyar da kansa ya ce, "Please Raudah!" Raudah sai ta samu kanta da sakin masa sassanyar murmushi kafin ta furta, "Shikenan Yaya Deeku na baka dama." Da wani irin farin ciki ya furta, "Thank u Habeebty,i luv u!" Raudah tayi saurin kai bakin hijab ɗinta ta rufe idanunta wani irin kunya na lulluɓeta.Sai dai kalmar tayi mata daɗi tare da sake jefa wani ƙaƙƙarfan feeling a cikin zuciyarta,ba yau ne karon farko da ya fara furta mata kalmar ba,amma wannan ita ce karon farko da ya furta mata kalmar gaba da gaba kamar hakan.Ya saki wani lallausar murmushi yana sake faɗin, "Ni ba idanu nake so ki rufe ba Habeebty,so nake ki ce u luv me too Baby!" Yadda ya faɗi kalmar Baby ɗin yana kwaikwayon salon yadda take magana ba ƙaramin dariya ya bata ba,ta sake rufe idanu tana dariya ƙasa-ƙasa cikin hijab ɗinta kafin ta furta, "Kai Yaya Sadeeq! Ni fa kunya nake ji!" Sai ya saki lallausar murmushi yana miƙewa tsaye ya ce, "Soon zan fara rage wannan kunyar domin tayi yawa Raudahta,bari na je na ɗan huta a ɗaki kafin Baban ya dawo na same shi da maganar,domin na ƙosa ki zama mallakina tun kafin wani ya kutso ya zame mini barazana." Raudah ta dubeshi wani irin abu na dukan zuciyarta,cikin sanyin murya tayi masa fatan hutawa lafiya tana riga shi shigewa cikin ɗakinsu.Ya bi bayanta da kallo yana jin yadda ƙaunarta ke sake rassa a cikin zuciyarsa,gangar jikinsa na cigaba da amsar wani irin gagarumin feeling da bai taɓa jin hakan akan kowace mace ba sai Raudan.Ya juya ya fito daga ɗakin yana baza idanunsa a tsakar sasan ko zai hangi Umma,ganin babu alamunta sai ya fice ba tare da ya nufi ɗakin Anty Amarya ba.Sam matar bata kwanta masa arai ba,kuma ko kaɗan baya ƙaunar alaƙarta da Innarsa tunda ya fahimci cewa ita ɗin ba ƙaramar hatsabibiya bace,wacce ke taka rawa wajen sake lalata Innarsa da banzayen ɗabi'u da shaiɗana kala-kala. Yana fitowa daga cikin sasan sukai kaciɓus da Baba Lawal a waje,dawowar daga ƙofa kenan ya je duba wasu awakai da aka kawo masa daga Nijar.Yaya Sadeeq ya gaidashi da ladabi sosai,Baba Lawal ya amsa gaisuwar da fara'a yana ɗaurawa da faɗin, "Sannunku da zuwa Abubakar,Allah ya yi albarka ya kawo babban rabo da kuma abokiyar rayuwa ta gari." Yaya Sadeeq ya amsa yana sadda kansa ƙasa kaɗan ya ce, "Baba zuwa anjima idan kana free akwai maganar da nake so muyi da kai." Baba Lawal ya jinjina kai ya ce, "To shikenan Saddiku babu damuwa,Allah ya kai mu lafiya ina nan daga nan har la'asar babu inda zan sake fita In Sha Allah!" Daga haka Yaya Sadeeq ya wuce zuwa ɓangarensu shi ma Baba Lawal ya shige sasan nasa yana tunanin wata magana ce Sadeeq ɗin ke son yi masa? "Baban Raudah baka bada kuɗin karin safe ba,yanzu ina so nayi mana tuwan shinkafa ne ka bani kuɗin cefanen rana don Allah!" Umma ce ke wannan maganar tana zaune daga bakin ƙaramin gadon da ke ɗakinsa.Ya ɗago kai ya dubeta ya ce, "Halimtu ki yi haƙuri ki ranta a aljihunki ku yi cefanen,kuɗin jikina na kwashe na sallami wanda suka kawo mini awakan dana faɗa miki za a wuto dasu daga maraɗi,ragowar dubu ɗaya ce kuma na ba Safiya suyi cefane tunda na san ke kina da abin yi da za ki iya juyamin kuɗin kafin na samu." Umma ta jinjina kai ƙasan zuciyarta na mata wani irin zafi da ƙuna,amma a zahiri murmushi ta sakar masa tana faɗin, "Shikenan babu damuwa,Allah ya cigaba da rufa asiri." Daga haka bata ƙara tofa koda kalma guda ba ta baro masa ɗakin.Tana tafe zuwa ɗakinta ne zuciyarta na mata zafi ainun,domin wannan ɗabi'ar da ya ɓullo da ita na rashin bata kuɗin cefane ya fara damunta.Baya cikin mazan da suka rasa, ko basu da sana'ar da zasu iya ci da Iyali,daidai gwargwado Allah ya gama hore masa domin ba ƙaramin samu yake yi da sana'ar Itace da sayar da Dabbobinsa ba.Ita ce kaɗai yake ganin ƙwanjin ya ɗauki ƙwandala ya basu kuɗin cefanen da zasu ci abinci ita da Yaranta,kullum sai dai ya bai wa Safiya ita kaɗai,su kuma ya kawo uzurinsa ya ce bayi dashi a ranta masa.Rancen da ba zai taɓa sake tada zancen ba bare aje ga maganar biya,ta mance rabon da ya ɗauki naira biyar ya basu suyi cefane bare kuma abin karin safe.Duk daga aljihunta take yi,idan bata dashi Raudah da ke da sana'ar yi ita ce mai bayar da kuɗi a sayi abin karin safe ko ta fita da kanta tayo musu cefanen da zasu girka abincin rana.Da zaran ya raba hatsin ya basu daidai da tauraruwar zuciyar tasa shikenan su ya gama dasu,duk wani kuɗi da za a kashe wajen sarrafa hatsin sai dai su gani a hannun Anty Safiya amma ba dai su ba. Da wani irin ɓacin rai ta nufi ɗakinta tana mai zama daga bakin gadonta hawaye na cika idanunta,ba kuma hawayen komi bane sai na tausayin ƴaƴanta mata.Tabbas bata so a rama dukkanin rashin adalcinsa da zunubansa akan ƴaƴansa,domin haka Ubangiji ya faɗi cewa,duk abinda ka aikata akan ƴar wani tabbas kai ma zai zo ga taka ƴar.Ta janyo jakarta domin duba ƴan canjin da ke ciki sabida bata da wadatan kuɗi duk ta kashe cinikinta a hidimar asibitin Raudah,dama kuma ciwon yazo ne a daidai lokacin da ta kwashe dukkanin kuɗin hannunta ta saro kayan masarufin da take siyawar.Ɗan cinikin da suka yi ta tattaru suka nufi asibitin dasu,kuma cikin hukuncin Allah kuɗin duk suka wuce ba tare da Baban Raudah ya biya sisin kwabon sa ba.Naira ɗari biyar ta zaro cikin jakar,baya ga ita babu komi sai naira ashirin.Ta kasafta kuɗin tas ta ga ba zai ishesu cefanen ba,duba da yadda komi ya tsauwala a halin yanzu.Kayan miyan girkin kansa wuya yake yi,ta yadda cin miya ma sai mai hali da rufin asiri.Ta fito daga ɗakin riƙe da kuɗin ta nufi ɗakin su Raudah,ita kaɗai ta samu a ɗakin Sumayyah na can bayan ɗakunansu tana wankin kayan makaranta da za a koma hutu a ranar monday.Ta dubi Raudah da ke kwance tana danna waya ta ce, "Raudah tashi zaune." Raudah ta aje wayar tana tashi zaune tare da maida dukkanin hankalinta kan Umman.Umma ta ce, "Za a samu ɗari biyar a wajenki?" Raudah ta jinjina kai wani abu mai nauyi da danne zuciyarta,domin tunda ta ji Umma tayi tambayar ta gane yau ma ɗin dai bai basu kuɗin cefanen ba kenan.Da wani rawar murya ta ce, "Akwai dubu ɗaya Umma,bari na baki kawai ki riƙe a hannunki." Umman ta girgiza kai tana faɗin, "Sai dai ki amshi ɗari biyar ɗin ki bada dubu ɗayan Raudah,ki saka hijab ki je ki yo mana cefane tuwo nake son muyi na farar shinkafa saiki haɗo da ledar rufe tuwan." Raudah ta jinjina kai ta ce, "To Umma,bari na tashi na gani ko zan iya fita a ranan nan." Umma da shaf ta manta cewa Raudah ragowar ciwo ce da bata jima da samun sauƙi ba sai tayi saurin dubanta ta ce, "Na manta ne Raudah,kawo kuɗin Sumayyah ta tafi,idan ta dawo ta kammala yin wankin,ko kuma idan ta kammala sai ke ki daure ki shanya muku tunda na ga har da hijaban da ki ke fita da su zuwa makaranta." Raudah ta jinjina kai ta ce, "To Umma bari na zaga bayan na gani." Daga haka ta miƙe tana gyara zaman ɗankwalinta da ya zame,sassalkan gashinta irin na Umman baƙi mai cika da tsayi ya bayyana a sarari.Ta maida ɗankwalin ta ɗaura sosai tana saka silifas ɗinta ta fito daga ɗakin,can bayan ɗakunansu na duka gidan ta nufa.A nan ne da rijiya da kuma manyan igiyoyin shanya da suke shanya kaya idan sun wanke,babban fili ne sosai a wajen da ko kiwo aka so yi za a iya yi ba tare da takura ba.Daga gindin rijiyar mai albarka da idon ruwa sosai ta hangi Sumayyah nata faman ɗauraye musu kayan da ta kammala wankewa,Raudah ta isa wajenta tana faɗin, "Sannu Sumy,Allah baki miji nagari,gaskiya kin yi saurin kammala wankin." Sumayyah ta kashe Raudah da smiling tana faɗin, "Ameen Yaya Raudah,ke ma Allah barki da masoyinki Yaya Deeku." Raudah ta rausayar da kai tana faɗin, "Riƙa cewa idan da alkhairy Sumayyah,domin soyayyah ba shi ne ba, alkhairy muke nema da kuma zaɓin Allah ba abinda zukatanmu ke so kaɗai ba." Sumayyah ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce, "Hakane Yaya Raudah,Allah ya yi mana zaɓi mafi alkhairy Ameen." Raudah ta ce, "Sumayyah je ki Umma na kira za ki yin cefane,ni zan ƙarisa ɗaurayan na shanya." Sumayyah ta kammala ƙarisa ɗauraye hijab ɗin ƙarshe wanda yake mallakin Raudah ne,sannan tayi mata sai ta dawo ta baro wajen." A hankali Raudah ke cigaba da ɗauraye ragowan kayan har ta kammala,tana yi tana tunanin yadda za ta shiga FCE ranar monday da wannan jikin nata da sam take ji kamar bata da ƙwari.Aji huɗu suke a kwalejin FCE da ke Zaria ita da Aliya da Zainab,domin dukkaninsu basu amince su zauna da jahilcin rashin zurfafa karatu kamar yadda su Baba Lawal suka yi sakaci ba.Shiyasa Baba Auwalu da ya yi zurfin ilimin yafi su sanin daɗinsa,shi ya jajirce wajen ganin anbar su Raudah sun ɗaura karatunsu bayan kammala sakandiri.Da fari aure Hajjah Kakah ta so ayi musu ya soke wannan maganar,ya nusar da ita cewa duka nawa suke da za a ce za a yi musu auren wuri ba tare da sun samu abinda suka samu a bokon da muhammadiyan baki ɗaya ba.Da yake a kwalejin FCE ɗin yake ya kuma kai wani matsayi shi ya shiga ya fita ya samo musu admission,ita kuma Gwaggo Shatu ta ce ta ɗauki nauyin biya musu kuɗin registration har su kammala.Tana da wannan ƙoƙarin da aikin zumunci ba tare da ƙyashi ko duba ga baƙar halayya da tsanar da Hajja Kakah ta nuna musu a baya ba,ko kaɗan idan tayi nufin alkhairynta yi take kai tsaye bata waiwayan baya.Hakan ya sanya wani irin ƙaunarta mai tsanani a zukatan su Raudah da dukkanin ahalin gidan,tafi ƴar uwarta Gwaggo Murja kyauta da yawan alkhairy da hidimtawa ƴan uwa cikin ni'imar da Ubangiji ya yi mata.Duk da cewa a zahiri mijin Gwaggo Murja yafi mijinta arziƙi,ita ma kanta tafi Gwaggon Shatun samu domin tana manyan business da take juya manyan kuɗaɗe. Raudah ta fara shanya kayan ɗaya bayan ɗaya,tana yi tana ɗan hutawa idan ta ji ta gaji.A haka ta cika igiyan farko har ta kawo ƙarshensa,ta zo daidai ƙarshen igiyan ta miƙa hannu za ta shanya wani skat ɗin kayanta ta fara jiyo muryar Anty Safeeyah da Maimumatu.Da yake saitin window ɗin uwar ɗakin Anty Safiyan ne daidai wajen da take tsayen,sai ya zamana tana jiyo muryoyin su Anty Safeeyan sosai sanda take faɗin, "Maza ki shaye wannan tsumin ki bani kofin,ke da kanki kika faɗi amfaninsa da irin rawan jiki da sumbatun da ya yi tayi miki,ai tsumin Maman Faridah duniya ne,ga aiki ga kuma magani riba biyu,ni dai burina ki dinga wankansa sosai muna kama manyan kaya a hannunsa,da shi za a riƙa siyan miki kayan ɗaki na garari,ki sakar masa jiki sosai,babu abinda zai faru ko ciki ya shiga zamu ɓarar das....." Ƙafafun Raudah ne suka kasa ɗaukarta,ta sulale zuwa ƙasa tana kai hannu bibiyu ta toshe kunnuwarta wasu irin hawayen da bata san sanda suka ɓalle mata suka shiga zarya akan fuskarta."Yanzu har abin na Maimunatu ya kai hakan? Da gaske bin maza take har ta riga da ta sallama mutuncinta a titi? Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un!" Raudah ta jerawa kanta tambayoyin tana sakin salati daga ƙarshe.Kanta ya yi wani irin nauyi,zuciyarta na bugawa da matsanancin saurin da take ji kamar numfashinta zai sarƙe.Da ƙyar ta iya miƙewa tana kallon saitin window ɗin uwar ɗakin Antyn Amaryar da yake a sakaye,hakan ya sanya ko kaɗan ba zasu iya ganin ko da mutum a kusa ba.Kuma dama idan Ubangiji ya nufeka da mummunan ji ko gani,saika rasa wani abin ma taya akayi ka jiyosa ko ka gansa? Haka Raudah ta ayyana a zuciyarta domin ta san tabbas da sun san da wanzuwarta a kurkusa ba zasu saki jiki da murya suna tattauna irin waɗannan mugayen kalaman ba.Da ƙyar ta iya ƙarisa shanya ragowar kayan ta koma ciki ta nufi ɗakinsu,kwanciya tayi kalaman Anty Safiya na sake mata amsa kuwwa tana ji kamar zazzaɓin da ya tafi mata ne zai dawo."Maimunatu fa,tsarar Sumayyah da watanni uku ne a tsakaninsu kacal! Yanzu ita ce har ta san kalar rayuwar bariki har suke tattauna batun tsumi na maganin mata da uwar da ta kawota duniya kuma ba tare da aure ba?" Raudah ta furta hakan a ƙasan zuciyarta tana jin saukar wasu zafafan hawaye na tsananin tausayin Mahaifinsu,domin kowani masifa Maimunatu ta janyo sunansa za a fara kira ace shiya janyo musu wannan abin kunyar, domin watakila da bai yi kalar rayuwar da ya yi abaya ba da watakila Maimunatu bata fito a haka ba."Meyasa Baba? Meyasa ba ka yi tunanin za ka haifemu watan watarana har mu girma mu ma mu zama ƴaƴa tamkar waɗanda ka ɓata rayuwarsu a baya ba? Meyasa ka zaɓowa Maimunatu uwa irin Anty Amarya?" Raudah ta furta dukkanin tambayoyinta a fili tamkar za ta zauce.Wani irin zafi zuciyarta ke yi tana sake jin ina ma ba Baba Lawal bane ya kawota duniya,domin tunda ta taso ta ji haramci aikata zina da irin azabar da aka tanadarwa mai aikakata idan har ya mutu bai tuba ba ta ji tana ƙyamar zina da mai aikata shi irin ƙyamar da ba za ta iya misaltawa ba.Daga lokacin kuwa da ta gano cewa Babansu ya aikata wannan kalar zunubin,shikenan take jin tsananin ciwon da a lokuta da yawa take jin ciwon yadda ta fito a jikinsa.Har Umma ta shigo ɗakin Raudah bata kula ba domin tunaninta ya yi nisa da gangar jikinta,sai da ta jiyo muryar Umman na kiran sunanta sannan tayi firgigit ta tashi zaune. "Kukan me kike yi kina sambatu ke kaɗai Raudah?" Umma ta jefa mata tambayar tana samun gefen katifarsu ta zauna akai.Raudah ta kai hannu ta share hawayenta tana faɗin, "Bakomi Umma." Wani irin kallo Umman ta jefeta dashi tana faɗin, "Kin sani bana son ƙarya ko ɓata mini lokaci ina nanata tambaya,sanar dani abinda ke damunki tun raina bai ɓaci ba." Raudah tayi ƙasa da kanta tana rasa ta yadda za ta sanar da Umman abinda ta jiyo su Anty Amarya na faɗi.Sai dai sanin ranta ne zai ɓaci idan Umman ta fusata ya sanyata sadda kai tana sanar da ita abinda kunnuwarta suka ji,da wani irin kaɗuwa Umma take duban Raudah hankalinta na mummunar tashi.Cikin wani irin karyayyen sauti ta ce, "Raudah ba kuka zaki yi ba addu'a yafi cancanta ku taya ta dashi,sannan ku sani ita zina masifa ce,fitinan rayuwace da duk wanda ya jefa kansa a cikinta to ƙarshen rayuwarsa nadamace da ba zai taɓa ƙarewa bawa ba koda ko kuwa ya tuba ya bar abinda yake,domin ita zina bashi ce da duk wanda ci sai ya biya,don haka ku ji tsoron Allah ku tsare mutuncinku,kada ku taɓa bari ruɗun duniya ko kuma makauniyar soyayyah ya sanya ku sallama mutuncinku wajen kowani namiji titi." *_This is chapter 6 of my new story! Shin labarin ya fara taɓa zukatanku ko har yanzu da saura dai? Mu haɗu a comment section domin ina buƙatar jin sharhi akan wannan Labari_* 🥲😍 *Ɗansabo na yabawa da yadda ku ke bibiyan labarin* 😘😘😘😘 [10/8, 2:29 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* *Free page* *Chapter 7* Umma ta jima sosai tana yiwa Raudah nasiha masu ratsa jiki da zuciya akan illar zina da haɗarin da ke tattare da ita,har Sumayyah ta dawo ta samesu tare da Raudan a haka.Ta haɗa har da Sumayyan tana cigaba da musu nasiha tare da nusar dasu muhimmanci yawaita yin addu'a da neman kariya daga dukkanin fitintunu na zamani,ta cigaba da faɗin, "Ku dage da yiwa kanku da ƴan uwanku addu'a,ku riƙa haɗawa har da Mahaifinku shi ma,domin yana da buƙatar addu'a game da yadda mace ta sha gabansa,kuyi haƙuri da Rayuwa domin cike take da tarin ƙalubale kala-kala,sannan ita RAYUWA DA ƘADDARA tare suke tafiya da juna,sai dai kawai muyi addu'a idan an tashi jarabtarmu a jarabe da Ƙaddarar da imaninmu zai iya ɗauka,Allah ya tsare mana ku ya tsare mutuncinku da namu baki ɗaya." Raudah suka amsa da cewa, "Ameen Umma,mun gode Allah ya ja kwananki tare da lafiya mai ɗorewa." Umma tayi murmushi ƙaunar Ƴan matan nata da tarin tausayinsu na sake kassara zuciyarta.Tare da Sumayyah suka fice domin ɗaura girki,ita kuma Raudah sai ta koma ta kwanta tana sake jujjuya dukkanin kalaman Umma,tana sake jin ƙauna da alfaharin samunta a matsayin Uwa ta gari da suka yi dace.Tana daga kwancen ta jiyo sallamar Aliyan sasan Baba Adamu,ta amsa daga cikin ɗakin nasu tana jiyo takun isowar Aliya zuwa ɗakin nasu.Da sallama a bakinta ta shigo ɗakin,Rauda ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan baƙar budurwar da ke tsaye ta zubo mata ido.Aliya kyakykyawace kamar Innarsu Ameena,sai dai ita ta biyo baƙin fatar Baba Adamu ne.Cikin rashin walwala Raudah ta dubeta tana faɗin, "Habawa Aliya sai yau kika ga damar shigowa?" Aliya ta ɗan narke murya tana zama daga gefen katifar da Raudah ke kai ta ce, "Afwan Raudah,nima wallahi mura ne ya ɗan kwantar dani,ya jikin naki?" Raudah ta taɓe baki ta ce , "Lafiya lau na warware,ya naki jikin to?" Aliya ta ce, "Da sauki Raudah,ki saki fuskar to mana wannan haɗe gira haka." Raudah ta galla mata harara tana sakin ƙaramin murmushi ta ce, "To ya aka yi? Ya batun shiga skull jibi?" Aliya ta gyara zama sosai tana cire mayafin jikinta ta aje tana faɗin, "Zamu shiga mana Raudah,mu da zamu shiga semestern ƙarshe ina muka ga ta ɓata lokaci,ni wallahi duk na ƙosa mu ƙare wannan jarababben karatun muyi aure ko muma ma huta." Raudah ta zuba mata idanu tana mamakin masifar son aure irin na Aliya,wacce duk cikin su ukun da suka taso kansu ɗaya ta fisu kula samari.Ko a skull lacturers da dama suke sonta,Raudah da Zainab ne kaɗai basu kula kowa,duk nacin samarin FCE sai da suka shafa musu lafiya domin basu basu fuska ba sam.Ta dubi Aliya ta ce, "Aliya manyan mata,wannan aure dai gwara azo ai miki shi tun kafin mu rasa gane kanki,yanzu waye gwanin da za a shafa fatihan da shi mu fara shiri?" Aliya ta saki wani irin murmushi tana faɗin, "Dakta Shamsu mana,shi ne ya yi nasaran sace nan ɗin baki ɗaya Raudah." Aliya tayi maganar tana nuna saitin zuciyarta da hannu.Raudah ta saki murmushi tana tuna wane ne ma Dakta Shamsun da Aliya ke faɗi,domin dai tana da samarin da yawa da take kulawa.Can ta tuno shi, wani lacturer ne a jami'ar ABU da ke Samaru,Aliya ta haɗu dashi ne a cikin FCE ɗinsu lokacin da ya kai wa wani lacturer ɗinsu ziyara.Raudah ta ce, "Allah ya tabbatar da alkhairy Aliya,ai auren abu ne mai kyau,Allah ya yi mana zaɓi nagari kawai." Aliya ta amsa da cewa, "Ameen Raudah,ke ma ai naji cewa Yaya Sadeeq ne gwanin naki har ma ya sanar da Baba,amma jiya har cikin dare na ji Innarsu Zainab na bala'i akan bata amince da maganar ba." Raudah da wani irin abu ya doki zuciyarta,sai tayi saurin duban Aliya ƙirjinta na bugawa da matsanancin ƙarfi ta ce, "Da gaske Aliya? Dama ni na san Inna Karimatu ba za ta taɓa amincewa dani ba." Yadda Raudah tayi maganar cikin karyewar murya ba ƙaramin tausayi ta bai wa Aliya ba,cikin muryar rarrashi Aliya ke faɗin, "Kiyi haƙuri Raudah,In Sha Allah idan har akwai aure a tsakaninki da Yaya Sadeeq za ki aure shi koda kuwa duka duniya ne za su taru domin su hana aukuwar hakan,Baban mu jajirtacce ne da bai yi saken da Innar su Zee tafi ƙarfinsa kamar yadda Anty Amarya tafi ƙarfin Baba Mai Itace ba,don haka ki kwantar da hankalinki ban faɗa miki hakan don hankalinki ya tashi ba,sai don na sani kona ɓoye miki hakan dole za ki sani domin ƙiyayyar da take wa Umma daku a fili yake ma ba a ɓoye ba,kuma kowa yasan son zuciyarta da hassadace kaɗai ba domin kun taka mata ko kun zubar mata ba." Aliya ta ƙare maganar cikin bayyana ɓacin ranta ga halayyar matar uban nata Inna Karimatu,domin suma kansu haƙuri suke da halinta a matsayinta na kishiyar uwarsu Inna Aminatu.Raudah ta ja ajiyar zuciya tana aro dukkanin jarumta ta sanyawa zuciyarta,cikin son danne duk wani damuwa ta ce, "Haka ne Aliya,amma matuƙar Inna Karimatu ba ta amince dani ba,zan cire Yaya a cikin zuciyata koda hakan na nufin rasa rayuwata ne,domin ba zan iya rayuwa da uwar mijin da ba za ta ƙaunaceni ba." Aliya tayi saurin duban fuskar Raudah da ko kaɗan babu alamun wasa a tare da ita,cikin matsanancin damuwa ta ce, "Kar ki masa haka Raudah,domin a kallon da Yaya Deeku ke miki kaɗai za a fahimci cewa bada wasa soyayyarki ta kama zuciyarsa ba,kuma ko kunyi aure bata so na tabbatar ba zai taɓa zama a garin nan dake ba, domin gujewa ɓacin rai da tseratar dake daga dukkan sharrin mahaifiyarsu." Raudah tayi murmushin takaici ta ce, "Waya gaya miki ko birnin sin ya kaini ƙiyayyar da take mini ba zai yi tasiri ba Aliya,kin san sharri da haɗarin auren wanda uwarsa bata ƙaunarki kuwa? Na sha karantawa a littafai duk da ban taɓa ganin ƙiyayyar a zahiri kalar wanda nake karantawa ba,amma zuciyata ba za ta iya ɗauka ba Aliya domin kin fi kowa sanin halina ni mai zafi ce da saurin hasala,maganin kar ayi kar a fara kawai,ƙiyayyar da Inna Karimatu ke ma Umma damu kan mu ba mai sauƙi bace,dama na bashi dama ne domin nayi masa adalci na kuma yiwa soyayyar da yake mini adalci,ina son Yaya Sadeeq Aliya ba zan ɓoye hakan ba,amma soyayyar da nake masa bai yi ƙwarin da zan iya jure matsananciyar ƙiyayya da rashin sukunin da zan fuskanta daga gareta ba,don haka addu'a kaɗai za ki taya ni dashi,Allah ya kawo mana mafita cikin sauƙi ko rabuwar ce ayi irin wanda rayuka ba za su ɓaci ba." Daga waɗannan kalaman Raudah ta kashe bakin Aliya daga furta duk wata kalma data shafi alaƙar soyayyar da Yaya Deeku ke mata.Suka cigaba da hiran skull ɗinsu har zuwa lokacin da Khaleel ya faɗo cikin ɗakin kamar an jefo shi,kyakykyawan Yaro mai shekaru bakwai zuwa takwasa a duniya.Shi ne Autan Anty Amarya wanda daga kansa bata kuma haihuwa ba,ya rugo da sauri ya faɗa jikin Raudah yana faɗin, "Anty Raudah na dawo ki bani gullisuwa." Raudah ta rungumeshi tana jin ƙaunarsa mai tsanani na ratsata,tun yana ƙaraminsa Allah ya ɗaura mata son sa kamar yadda shi ma Yaron ya taso da ƙawazucinta a zuciyarsa.Tun Anty Amarya na masifa akan za a mallake mata ɗa,har ta gaji ta daina domin kuwa Khaleel baya iya yini a wajenta sai ɗakin Umman.A hankali ta fahimci cewa ba cutar mata dashi ake ba,domin Yaro baya zuwa inda ake cutarsa.Cikin sakin fuska Raudah ta shafa kansa tana faɗin, "Oyoyo my boy ka dawo?" Ya gyaɗa kai cike da zumuɗi ya ce, "Na dawo Anty,dama duk na ƙosa na dawo ki dinga bani gullisuwa da alawar madararki ko?" Raudah ta shafa bakin kwaɗayin tana faɗin, "Nima duk nayi kewarka Khaliluna,to me ka kawo min tsarabar hutun da ka je ɗin?" Ya ce cikin sauri, "Biskit kaɗai aka bani sai kuɗi,kuma ina dawowa Anty ta ƙwace kuɗin." Raudah ta saki murmushi tana aje shi gefe guda ta tashi ta ɗakko masa gullisuwa da bata rabo dashi a gidan sabida ƴan skull da ke shigowa siya bayan wanda take kai wa shago,tana kawo masa ya amsa yana sakin murmushi mai yawa akan fuskarsa ya ce, "Na gode." Daga haka ya sake komawa jikinta ya manne yana kallon Aliya da ke harararsa akan yaƙi ce mata komi.Aliya ta dubesa ta ce, "Yanzu Khalil ni kake ƙyalewa sabida bani da abin baka irin na Anty Raudah ko?" Ya kuwa jinjina kai ya ce, "Aike da Anty Zee duka bakwa bani abin ku,Anty Amarya ta ce rowa ne daku ai." Raudah da Aliya suka kalli juna suka saki murmushi,cikin dariya Aliya ta ce, "To shikenan tunda haka Anty ta ce ba zan kuma baka sweet ba, ai za ka je har sasan mu wajen Innarsu Zee ka sameni." Khalil ya yi murmushi yana faɗin, "Ai bana zuwa,nafi son wajen Gwaggon Suhailah ko wajen Umma ko Anty Raudah?" Raudah ta jinjina kai tana ƙara jin sonsa a zuciyarta sabida surutu da wayonsa,gashi duk mutanen da bata shiri dasu baya raɓarsu,Anty Amaryar kanta don dai uwa uwace amma yadda yake damuwa da lamarin Umma sam baya ƙawazucin Anty Amarya sosai. Aliya kusan yini tayi a sasan nasu Raudah sabida dama ita ɗince ta hannun damarta da suka fi shiri fiye da Zee da babu wuya sun haura sama da Raudah,domin dukkaninsu suna da zafi da rashin haƙuri. Kamar yadda Yaya Sadeeq suka rabu da Baba Lawal cewa da yamma ya same shi bayan la'asar hakan ce ta kasance,suna dawowa daga masallacin dake gabansu kaɗan suka zauna daga bakin dakalin ɓangaren su Gwaggo Shatu da wajen yake shiru babu gilmin ƴan shige da fice masu yin siyayya a wajen Umman. "Malam Saddiku ina sauraronka,ina fata dai lafiya?" Yaya Sadeeq ya sadda kansa ƙasa ya soma da faɗin, "Baba dama ina so idan kai mini izini wajen fara tsayuwa da Raudah a matsayin wacce nake fata ta zama uwar Ƴaƴana,na gabatarwa da Baba da ita a matsayin zaɓina." Baba Lawal ya ɗago kansa ya dubi Sadeeq wani irin farin ciki da ba zai zata ba na mamaye zuciyarsa,ya jinjina kai yana murmushi ya ce, "To in banda abin ka Sadeeq ai Auwalu shi za ka tunkara domin shi ne maɗaurin auren Raudah idan da rayuwa,Allah ya tabbatar da alkhairy a tsakanin junanku,ina fata ita Raudar ta san da zamanka ko?" Cike da jin nauyi Sadeeq ya gyaɗa masa kai alamun ta sani.Baba Lawal ya sake jin farin ciki sosai,ya kuma yi addu'a mai yawa akan Allah ya tabbatar da alkhairi.Yaya Deeku duk sai ya ƙosa Baba Auwalu ya dawo ya gabatar masa da zancen Raudah a matsayin wacce ya zaɓa ta zama uwar ƴaƴansa,sai dai Baba Auwalun bai shigo gidan ba sai bayan magriba.Yaya Deekun bai yi ƙasa a guiwa ba ana idar da sallar Isha'i tun a bakin masallaci ya fara yi masa zancen yana son magana dashi,suka ƙarisa gidan Baba Auwalu ya jashi har ɗakinsa suka zauna.Ya dubi Yaya Sadeeq ɗin cikin fara'a yana faɗin, "Sanar dani Sadeeq me ke faruwa?" Sadeeq bai tsaya sanya ba wajen sanar da Baba Auwakun komi,ciki har da kalaman da Innarsu ta fara yi na son kawo masa matsala ga cikar burinsa.Baba Auwalu ransa ya ɓaci,cikin kausasa murya ya ce, "Bata isa hana Allah ikonsa ba,ka kwantar da hankalinka ai matar mutum kabarinsa,matuƙar Raudah matarka ce za ka aureta ko Karima na so ko bata so,domin tayi kaɗan ta ja da hukuncin Ubangiji! Idan har kaga aure tsakaninku bai yiwu ba to dama ka ɗauka ba rabonka bace,zan samu Hajiya Kakah da maganar dama ƙarshen watannan nayi niyyar tara duka ƴan matan akan kowacce ta fiddo zaɓinta tunda karatu ya zo ƙarshe,da zaran sun kammala zamu miƙa su ɗakin miji sai kuma mu ji da da ragowar masu tasowa,sannan ina so dama inyi wata magana game da Yarinyar nan Maimunatu da surutu ya fara yawa a kanta akan yadda take neman ɓarar mana da mutunci,a matsayinku na manya maza a gidan yakamata ku tayamu sanya idanu matuƙa a kanta tare da koran duk wani saurayi mara kamun kai da zai tunkaro ƙofar gidannan,shi ma kuma Yaya Lawal ɗin zan same shi mu tattauna domin bai kamata ya sakarwa mace ragamar kulawa da rayuwar ƴarsa babu control ba." Baba Auwalu ya kai ƙarshen maganar yana jin ɗacin kalaman da abokinsa ya tare shi da shi akan Maimunatu,wacce ya ganta a cikin wani hotel da ke cikin GRA Zaria ita da wani babban magidanci ma ba saurayi ba. Yaya Sadeeq ransa ya yi mummunar ɓaci,hankalinsa kuma ya tashi domin shi ma ya gama fahimtar rayuwar Yarinyar ta fara lalacewa tabbas.Cikin sanyin murya ya ce, "In Sha Allah za mu sanya idanu a kanta sosai Baba Auwalu,Allah ya shirya mana zuriya." Baban ya amsa da cewa, "Ameen." Suka yi sallama da Yaya Deekun,wanda yana fitowa daga sasan Baba Auwalun ya nufi ɓangaren Hajjah Kakah. Daga cikin zauren sasan ya tadda Zainab ƙanwarsa tare da saurayinta suna zance,sun shimfiɗa tabarma daga cikin zauren tare da kunna hasken waya kasancewar babu wuta a lokacin.Saurayin ya gaida Yaya Sadeeq ɗin a ladabce sukai musabaha,Yaya Deekun ya wuce zuwa ciki yana yaba ɗan nutsuwar da ya gani tattare da saurayin Zee ɗin. Da sallama ya sanya kansa cikin harabar sasan,idanunsa ya sauka akan kusan duka ahalin jikokin nata zagaye da ita daga bakin barandar shiga ɗakinta.An kunna babban lanta mai tsananin haske da ya haske ko'ina na tsakar sasan,Hajjah Kakah na zaune a tsakiyarsu gabanta farantin da ta zuba lafiyayyen tuwan shinkafa miyan taushe ne da aka saka manyan kifi a cikin miyar.Daga sasan Baba Auwalu Gwaggo Salamatu da ke da girki a ranar ta aiko,domin dama duk mai girki ita ce za ta sanyawa Hajjah Kaka da mai gidan abinci haka dukkanin matan gidan suke yi.Ya ƙarisa bakin barandar yana sake haɗe face ɗinsa babu ko ɗigon murmushi akan fuskarsa,ƴan ƙannen nasa suka shiga gaida shi a ladabce yana amsa su cike da basarwa.Ya aje ganinsa akan sahibar tasa Raudah,wacce ke zaune kusa da Hajjah Kakah sosai hankalinta amma na kan wayarta ne.A jikinta kawai ta ji idanunsa akanta suke,sai ta ɗago manyan idanunta a hankali ta sauke a kansa.Wani abu ya doki zukatansu a lokaci guda,kafin ta ɗan shagwaɓe murya tana gaida shi.Ya amsa da wani irin kulawa yana sake bin ta da kallo,tana sanye da free gown ne a jikinta sai ɗan ƙaramin hijab da bata rabo dashi a wuyanta sabida ita kanta tasan akwaita da cikar halittar da bata iya gilmayya tsakanin sasunan gidan ba tare da mayafi a jikinta ba.Aliya ita ce tayi saurin tashi ta ɗakko masa kujera domin ya zauna,bai musa ba ya amsa ya zauna yana gaida Hajjah Kakah.Ta ɗago daga kai loman tuwanta tana faɗin, "Saddiku ka shigo,ya naga hannunka rabbana bayan ka saka mini rai zan sha fura?" Yaya Sadeeq ya saki ƙaramin murmushi idanunsa akan Raudah da ke duba waya tana murmushi,haka kawai ya ji ransa na ɓaci wani azababben kishi na mintsininsa domin zuciyarsa na raya masa anya bada samari take chart ba?Maimakon ya fara bai wa Hajjah Kakah amsa sai ya miƙa hannu saitin Raudah yana faɗin, "Habeebty! Give me ur phone." Raudah ta ɗago da sauri tana jin kunyar sunan da ya kirata dashi a gaban kowa ba tare da ko ɗar ba,ta miƙa masa wayar bayan ta ɗan zumɓure baki kaɗan.Ya amsa wayar yana sauke idanunsa akan page ɗin da take karantawa na wani novel da take bibiya a wani group da aka sanyata na karatun novels,sai ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ba zarginsa bane ya tabbata.Bai maida mata da wayar hannunta ba ya dubi Hajjah Kakah ya ce, "Za ki sha Hajjaju, ai yanzu daren ya fara ko? So nake na haɗo miki da wani gashin nama ko bakya ci ne?" Hajjah Kakah tayi saurin dubansa tana faɗin, "Wane mutum ni Zuwairah! Ai kai ma kasan ni da nama kamar tare aka haliccemu,ka ce kawai kar na rufe sasa da wuri akwai cin daɗi yau." Ya jinjina kai yana duban Raudah kai tsaye ya ce, "Habeebty ke ce zaki taya ta kwana yau?" Raudah tayi saurin girgiza kai ta ce, "Hameedah ce yau da tayata kwana Yaya." Bai ji ko ɗar ba ya ce, "Ke za ki kwana ina so muyi magana anan idan na dawo,gobe sai ita Hameedar ta tayata kwana." Hajjah Kakah tayi saurin faɗin, "Kamar kasan nama fi jin daɗin mu kwana tare sabida da ta tashi za tayi mini komi cikin zafin nama babu komawa wannan shegen baccin asaran,amma ita sam bata ƙaunar ranar tayani kwanan ya zagayo kanta." Hajjah Kakah ta ƙare maganar tana makawa Raudah harara,sai dai can ƙasan ranta sosai take jin ƙaunarsu ita da Yaya Sadeeq ɗin.Raudah ta zumɓuri baki tana kallon yadda Yaya Sadeeq ya kafeta da idanunsa da ke da wani irin tasiri a kanta,ya miƙe zai fice daga sasan tayi saurin sake shagwaɓe murya ta ce, "Yaya Deeku wayata please!" Kamar ba zai bata wayar ba sai kuma ya miƙa mata wayan ya jefeta da wani sassanyar kallon da ya ratsa har ɓargonta.Ya fice a sukwane Hajjah Kakah na masa a dawo lafiya,kamar jira Aliya take yi ya fita ta ce, "Shegiya luv! Gaskiya Raudah kina kashe Yaya Sadeeq da soyayyah, ke kinji yadda ki ke masa wata shagwaɓa kamar za ki narkar dashi." Rauda kunya ya rufeta amma sai ta maze ta aikawa da Aliya harara tana faɗin, "Kin shiga uku Aliya da sharri,ni babu wata shagwaɓa dana iya bare har nayi masa na kusa narkar dashi ɗin." Hajjah Kakah da ke saurarensu sai cewa tayi, "Allah dai ya kai mu gobe ayi wacce za a yi tsakanin ni da Auwalu da ya ɗaurewa balagarku gindi wai sai kunyi boko,Yara duk kun fitsare da iya jan zuciyan maza kamar su narke babu ko kunyar idanun tsufa,to ai gara kawai kowacce ta fito da nata tsayayyen a kaiku ɗaki a huta,dama ga waccar jarababbiyar ƴar da ta fara bibiyan maza tana raba musu komi arha a titi,wallahi Safiya ta cuceni ta kuma cuci Lawal,amma ba laifinta bane laifinsa ne da ya auro ragowar bariki ya kawo cikin tsarkakakkun ahalina,shi ma kuma ya cuci kansa da bai zama kintsatstse ba tun a zamanin ƙuruciya,ai gashi a gaban idanunsa ake yawon hotel da ita ana....." Raudah ce tayi saurin katse Hajjah Kaka tana faɗin, "Don Allah Hajjah Kakah kiyi shiru,addu'a ita ce tafi cancanta kiyi ba tashin-tashina ba,ai kema har da naki laifin da bakya iya kwaɓawa akan abinda duk ya kamata." Wajen ya ɗauki shiru, Hajjah Kakah na faman zare idanu,ganin yadda Raudah tayi kicin-kicin da fuska.A hankali su Hameedah suka fara tashi suna yiwa Hajjah Kakah sai da safe suna tafiya sasansu,takaici kamar zai halaka Sumayyah ta miƙe tayi gaba tana jin gabaki ɗaya ta muzanta a gaban su Bushirah domin bata ji daɗin yadda Hajjah Kakah ke yawan tunasar dasu irin zunubin da ubansu ya aikata a baya ba.....✍🏻 [10/9, 2:36 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paida Book 08167768704* _Free page_ *Chapter 8* Misalin ƙarfe sha ɗaya na dare ne,Baba Lawal tare da ƙaninsa Baba Adamu ne zaune a dakalin shiga sasan Baba Lawal ɗin suna magana Maimunatu ta buɗo gate ɗin shigowa gidan irin na da ɗinnan ta shigo.Suka ɗaga kai a tare suna kallon wajen duk a tunaninsu cikin samarin gidan ne Abubakar ko Usman wani ya yi daren dawowa gidan a cikinsu.Idanunsu na sauka akan Maimunatu da ke tunkarosu cikin shigar baƙar Abaya,duka sai rayukansu suka ƙuntata,wani irin abu mai matuƙar nauyi ne ya taso ya danne zuciyar Baba Lawal.Baba Adamu da ya kasance mai zafi duk a cikinsu,shi ne ya daka mata tsawa tare da tsayar da ita lokacin da tayi musu sannu tana shirin giftasu ta shige cikin sasan nasu. "Daga gidan uban wa ki ke Maimunatu ƙarfe sha ɗayan dare?" Baba Adamu ya jefa mata tambayar masifaffun idanunsa fes akan Maimunatu da sam babu tsoro ko kaɗan akan fuskarta,domin zuciyarta ta riga da ta fara bushewa.Cikin yin ƙasa da murya ta bashi amsa kai tsaye da faɗin, "Bikin ƙawata ake yi Baban Zee, shi ne muka ɗanyi dare mun kai Amarya." Ba domin ya amince da abinda ta faɗi ba ya shiga balbaleta da faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,ya kuma sanar da ita lallai gobe da safe ta same shi a sasansa yana son ganinta kafin su wuce makarata tunda gobe monday duk za a koma hutu.Tana shigewa ya maida dubansa kan Baba Mai Itace da takaicin duniya ya gama lulluɓesa ya ce, "Yanzu Yaya akan idanunka wannan Yarinyar ke iya kai wa har wannan lokacin a waje? Koda ace daga yawan biki take kamar yadda ta faɗi hakan sam bai kamata ba,domin rayuwa tayi sauyawar da ko kaɗan bai kamata mu riƙa sakaci da tarbiyan Yaranmu ba,musamman ƴan mata kamarsu da duk mai hankali da zaran ƴarsa ta balaga bashi da sauran sukuni,yakamata ka zama tsayayye a cikin gidanka,domin idan aka ce ka sakarwa mace ragamar tarbiya tabbas akwai ɓarna,musamman ma mata irin Karima da Safiya da sam basu san annabi ya faku ba wajen aikata son zukatansu." Ya ƙare maganar yana sake jin tsanar matar wan nasa da yake da tabbacin tana da kaso mai yawa wajen kangarar masa da Karimarsa da sake ɗaurata akan layin shaiɗana kala-kala.Baba Lawal ya ɗago idanunsa da sukai jajir ya sauke akan ɗan uwansa,shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa game da lalacewar tarbiyar Maimunatu.Da wani irin karyayyen sauti ya furta, "Astagfirullah Allah! Allah na tuba ka duba mini lamarin Iyalina,Adamu tabbas na aikata kuskuren da har a zare numfashi daga gangar jikina ba zan daina danasanin taɓa mutuncin ƴaƴan wasu da nayi a baya ba,tabbas nayi tuba irin wanda Ubangiji ke so,domin tunda na bar zina ban sake marmarin komawa ruwa ba,tun daga randa Allah ya fara tara mini ƴaƴa mata na shiga ruɗu da fargaba mai tsanani,sai dai a yau gashi ina ganin aibun abinda na aikata,domin dama ance ita zina bashi ce,tabbas gashi ina biya da mafi munin ji da gani a cikin zuriyata..." Wasu hawaye masu ɗumi suka sakko daga kwarmin idanun Baba Lawal,yana jin yadda zuciyarsa ke masa tsananin zafi da ƙuna.Baba Adamu da kalaman ɗan uwansa suka taɓa zuciyarsa sai ya ji dukkanin jikinsa ya yi sanyi,ya dubi Baba Mai Itace ya ce, "Yaya ka yi haƙuri,ka kuma sake tuba zuwa ga Ubangiji,sannan ka sanya idanu a cikin gidanka ka kare mutuncin Iyalinka iyakan ƙarfinka,ka zama tsayayyen da mace ba za ta iya lanƙwasaka ba sai ka samu sauƙin al'amura." Baba Lawal ya jinjina kai yana yiwa ɗan uwansa godiya,sukai sallama ba don sun ƙarisa tattauna maganar da suke yi ba.Baba Lawal ya shige cikin sasansa a fusace,yayinda Baba Adamu ya nufi nashi sasan da yake shi ne daga can farko. "Safiya!Safiya!! Kina ina ne?" Baba Mai Ice ya shiga kwaɗa mata kira yana isa bakin ƙofar ɗakin Anty Amarya.Bai kuma jira amsawarta ba ya ɗage labulen ya sanya kansa ciki a fusace,jikinsa har rawa yake sabida tsananin ɓacin rai da ke cin zuciyarsa.Sai dai me, suna haɗa idanu da Anty Safiya ya nemi dukkanin zafin zuciya da rawar jikin da ya shigo dashi na son cin mutuncinsu ita da Maimunatu ya rasa,da wani irin murya da ban san taya zan iya fassara muku ba ya dubi cikin idanun Anty Safiya yana faɗin, "Yanzu Safiya kin ga dacewar budurwa kamar Maimunatu ta kai har ƙarfe sha ɗaya na dare a waje da sunan wai ta dawo daga biki?Haka ta ga ƴan uwanta su Raudah nayi?" Anty Safiya tayi masa wani irin sakartaccen kallo ta ce, "Ka gama?" Ya jinjina kai yana satan duban Maimunatun da tayi musu tsuru da idanu tana kaɗa ƙafa bisa seater,gabanta ledar tsire ne mai yawan gaske a buɗe da alamu zasu fara ci kenan ya faɗo ɗakin.Ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da rintsesu yana jin wani irin kibiya mai tsini na sukan zuciyarsa da tsananin zafi,maganan da Anty Safiya ta fara suka shiga kunnuwarsa kai tsaye lokacin da take faɗin, "Kar ka kuma haɗa mini ƴa da wasu banzayen ƴaƴanka marasa farin jini,suma da ka ke ganinsu biya-biya cikin hijab kasan ta'asar da suke aikatawa a waje ne? Musamman ita Raudar da kullum sake cika take ƙirjinta na tumbatsa,idan ba taɓa su ake yi ana basu taki ba banga ta inda za ta dinga ƙaro kyawu kamar wacce ake wa wankan inji ba,don haka ka cire idanunka akan ƴata ita kaɗai,domin idan an biye ta abinda ka aikata ne babu ƴarka ɗaya da za ta tsira ba a farke mutuncinta an moreta a titi ba,ko ka manta sanda na sallama maka budurcina ne a akan kujerar......" Wani irin tsawar da bai san yadda aka yi ya iya daka mata ba ya katse Anty Safiya daga cigaba da furta zafafan kalaman tozarcin da ta faro,zuciyarsa na wani irin zillo tamkar zai fito daga ƙirjinsa ya nunata da yatsa yana son yin magana amma ya kasa.Ya sauke hannun yana juyawa ya fito daga ɗakin hawaye na wanke fuskarsa,idanunsa suka rufe har baya ganin gabansa lokacin da ya kai kansa ɗakin baccinsa. Tamkar wanda aka jefo haka Umma ta ɗaga idanunta tana kallon Baban Raudah da ya faɗo cikin ɗakin,tana zaune daga bakin gadonsa sanye cikin doguwar riga ta bacci da tayi mata kyau matuƙa.Shigowarta kenan bada jimawa ba bayan ta jiyo sallamar shigowarsa sasan,sai ta cidda bashi cikin ɗakin sai sautin muryarsa da take jiyowa daga ɗakin Safiya.Ta dubeshi tana kallon yadda sam babu sukuni a tattare dashi,tana son ta tambayeshi abinda ke faruwa to amma bata son shiga huruminsa da matarsa.Hakan ya sanya ta ɗauke kai tayi kamar bata kula da yanayin da ya faɗo cikin ɗakin ba,aka ɗauki tsayin mintuna tana sauraren yadda yake sauke wani irin ajiyar zuciya.Ta sake ɗaga idanunta a karo na uku ta sauke akan kyakykyawar black beauty face ɗinsa da idanunsa ke rintse,idanunta suka cigaba da yawo akan hannunsa ɗaya da ya kai ya dafe saitin zuciyarsa da shi.Wani irin abu mai ƙarfi ya fisgi zuciyar Umma har ta kasa daurewa ta ce, "Baban Raudah lafiya kuwa?" Sai lokacin ya buɗe idanunsa da suka firgigitata sabida ganin yadda suka rine sukai jajir,da wani irin karyayyen sauti ya ce, "Halimatu bani ruwa mai tsananin sanyi in sha,in son samu ne ma ki haɗo da ƙanƙara ki zo ki manna mini a saitin zuciyata ko zan samu sassaucin zafin raɗaɗin wutar da ke kama a cikinta.Umma ta rintse idanunta tausayinsa mai tsanani ya lulluɓe zuciyarta,ta miƙe a hankali ta fito daga turakarsa ta nufi ɗakinta.Zagawa tayi ta saitin windon ɗakin su Raudah ta shiga bugawa a hankali,domin tana fitowa suka rufe ƙofar ɗakin kamar yadda suka saba idan ita ke da kwana da ta fita suke rufe ɗakin sai da asuba suke buɗewa idan sun tashi yin sallah.A hankali take buga windon tana kiran sunan Raudah,Raudah da taƙi kwana a ɓangaren Hajjah kamar yadda Yaya Sadeeq yaso,suna kwance ne bisa katifarsu ita da Sumayyah da tayi bacci.Ita kuma chart suke da Yaya Sadeeq ɗin bayan kammala yin wayarsu,jin muryar Umman na kiranta ya sanyata aje wayar ta fito ta buɗe ƙofar falon.Umma ta wuce kai tsaye zuwa wajen da freezernta ke aje ta buɗe ta ɗauki pure water da take siyarwa guda biyu da sukai tsananin sanyi ta fice,Raudah ta bi bayanta da kallo tana mamakin abinda Umman za ta yi da ruwan da suka kusa yin ƙanƙara a daren,domin ta sani daga ita har Baba Mai Itace ba ma'abota shan ruwan sanyi bane.Bata zurfafa wajen tunani ba ta rufe ƙofar ɗakin ta nufi ɗakin baccinsu,wayar ta ɗauka suka cigaba da chart ɗinsu da Yaya Deekunta kafin daga ƙarshe ta kashe data tayi shirin kwanciya. A ɗakin Baba Mai Itace kuwa,ruwan sanyin Umma ta tsiyaya masa a kofi ta miƙa masa.Ya tashi da ƙyar ya amsa kofin tare da ɗaɗɗakawa cikinsa ruwan,ya sake ya miƙa mata kofin a karo na biyu ta juye masa ragowan ruwan ya shanye yana sauke numfashi.Da wani irin sanyin murya ya ce, "Zo zuba mini a ƙirjina Halimatu." Umma ta matsa gareshi sosai tare da taya shi ya zare rigar jikinsa,a hankali ta dinga shafa masa ruwan sanyin bisa ƙirjinsa har sai da ya janye hannuwanta da kansa alamun ya isa hakanan.Ta ja baya tana kasa ɗauke idanunta daga dubansa,zuciyarta na son sanin me ya sabbaba masa shiga irin wannan yanayin haka? Sai dai duk yadda ta so sani ta kasa tambayarsa, ta zuba masa abincin da sam bai shigo gidan da wuri yaci ba sai yanzu ɗin.Kaɗan ya iya cin abinci ya ture yana miƙewa zuwa ƙaramin banɗakin da ke cikin turakan nasa,koda ya fito ya samu Umma ta kwanta domin ita mai baccin wuri ce sabida tashi sallan dare da ya zame mata jiki.Ya yi mata kallo ɗaya yana sake jin matsananciyar ƙaunarta da sake godewa Ubangijinsa da ya azurtashi da kamammiyar mace,kuma haƙurarriya kamar Umman.Ya dinga tuna lokacin da ya aurota shi ya fara saninta,a lokacin gani yake ya tsallake siraɗin da ake cewa mazinaci baya taɓa auren macen ƙwarai sai mazinaciya irinsa.A maimakon ya tuba tun a lokacin sai ya cigaba da sharholiyansa da matan banza,har zuwa lokacin da Allah ya haɗashi da Safiya.Kamar yadda ta faɗi shiya fara saninta,daga baya ne ta dilmiya har ta zama karuwa ta sosai,daga bisani kuma Allah ya jarabesu da son junansu.An sha fama kafin ya amince maganar aure ya shiga tsakani,har sai da uwarta suka haɗa har da asiri kafin ya amince da maganar aurenta.Bayan anyi auren kuma basu bar shi haka ba, suka sanya aka yi asirin da za ta mallakeshi tsaf sai yadda ta ga dama za tayi,asiri da yake gaskiya ne kuma ya ci har fiyayyen halitta, sai suka yi nasara akansa suka kuma samu yadda suke so ɗin.Domin duk yadda ya kai ga jin zafin Safiya bai isa iya ɗaukar mataki mai zafi a kanta ba,sai dai ya furta kalaman da basu kai sun kawo ba.Ba a ɗauki dogon zango ba ya gane dama can talala Allah ya yi masa da fari da ya azurta shi da mace kamar Umma,sai daga bisani aka jarabcesa da Safiya da ta zamewa rayuwarsa ƙarfen ƙafa.Ya kai hannu ya share hawayen da suka zubo masa yana mai ɗaga hannu sama yana faɗin, "Allah na tuba ya Allah!Ina kuma sake gode maka da ka bani mace kamar Halimatu, baka tara mini tarin kara da kiyashi irin Safiya ba. Ya raɓa ya kwanta a gefen Umma ba don yana jin cewa idanunsa zasu iya rintsawa a wannan daren ba,domin har yanzu dafin kalaman Safiya basu gama illata zuciyarsa ba.Musamman yadda take ƙoƙarin jinginawa Raudah mummun ƙazafin da baya fata Ubangiji ya jarabcesa da ji da gabi,idanunsa kawai ya rufe fuskar Maimunatu na gilma masa a lokacin da Anty Safiya ke furta waɗannan miyagun kalaman a gabanta,ya dinga ji zuciyarsa na sake ɗaukan wani irin zafi da ƙuna.A kunnuwarsa Umma ta tashi cikin tsakiyar daren domin gabatar da ibadarta na sallan dare da ya zame mata jiki,ta sauka daga gadon tare da ɗaukar wayarta ta kunna haskensa ta isa ƙaramin banɗakinsa da aka tsafata a cikin ɗakin.Wanda babu matsuguni anyi shi ne kawai na wanka,sai wajen wucewan ruwa da za a iya tsugunawa ayi fitsari kaɗai.Alwala ta ɗauro ta fito ta tada sallah duk akan idanun Baba Mai Itace da ke kwance yana kukan zuci,idanunsa sunyi rayas babu alamun jin bacci ko ƙanƙani.Banda tunanuka da nadamar irin rayuwar da ya yi a baya babu abinda ke kai kawo a cikin zuciyarsa,abu mafi ciwo da nadaman da ke kassara zuciyarsa a lokacin bai wuce na aurensa da Safiya ba.Sai dai ya sani hakan na daga cikin kamun da Ubangiji ya yi masa,domin a nuna masa cewa bai ci banza ba na auren salihar mace da fari irin Umma. Har Umma ta idar da nafilfilinta daidai lokacin da agogo ke buga ƙarfe uku rabi na dare Baba Lawal bai runtsa ba,a kuma daidai lokacin nefa suka ƙyallo wuta.Fitilar ɗakin da sam Umma ta manta bata kashesa ba haskensa ya gauraye ɗakin,ta ɗaga manyan idanunta ta dubi sashin da Baban su Raudan ke kwance.Ga tsananin mamakinta sai ta gansa a zaune ya zubo mata idanu hawaye na sauka bisa fuskarsa,jikinta ya yi wani irin mugun yin sanyi.Ta taso a hankali ta dawo bakin gadon tana zuba masa idanunta ta ce, "Baban Raudah wai lafiyanka kuwa,wani irin damuwa ce haka da ya hanaka rintsawa duk sonka da bacci?" Baba Mai Itace ya jinjina kai yana kai hannu ya ɗauke zafafan hawayen da suka sulmiyo masa,cikin wani irin raunin murya ya ce, "Halimatu ba zan iya rintsawa ba,zuciyata ƙuna da raɗaɗi take mini irin yadda ba zan iya misaltawa ba,nayi nadama Halimatu,tabbas nayi danasanin haɗa jinina da na Safiya!" Ya dakata yana kai hannu ya dafe saitin zuciyarsa da ke wani irin zafi.Umma tayi ƙasa da kanta maganganunsu Anty Safiya da Raudah ta jiyo ɗazu da rana suka shiga dawowa kwanyarta,cikin sanyin murya ta ce, "Mai kuma ya faru Baban Raudah? Ka daina cewa ka yi danasanin aurenta domin auren soyayya ku kai da juna,kuma ta sha faɗin kai ne ka fara saninta a ƴa mace,ka ga ba laifi bane don Ubangiji ya yi mata sakayya ta hanyar haɗaku aure,sannan ita ma a lokacin da ka ɓata rayuwarta kar ka manta Ƴar wani ce,don haka ka daina danasani Baban Raudah domin shi Allah gwanin hikima ne da kuma iya kama bayinsa ta inda basu yi zato ba,ka sake komawa zuwa garesa kana mai ƙasƙantar da kanka da miƙa ƙoƙon bara akan ya kawo maka mafita,ya kuma yafe yawan zunubanka ta yadda zasu taƙaita har su daina bibiyan jininka da basu ji ba basu kuma gani ba... " Wani irin kuka silently ya ƙwacewa Umma,ta dinga yinsa tana jin wani irin tausayinsu na lulluɓe zuciyarta.Shi ma Baba Mai Itace kukan yake yana ji duniyar nayi masa matuƙar zafi,kalaman Umman suke shigarsa tare da sake raunata zuciyarsa.Muryarta ne ya sake shiga kunnuwarsa da wani irin sauti da ke ratsa har kwanyarsa, "Kana da sakaci Lawal wajen dagewa da addu'a da kuma tsayuwar dare,ka sani inda ace yadda ka tuba irin tuban da baka sake aikata zina a rayuwarka ba,da ace ka ɗaura da yin tsayuwar daka wajen riƙe addu'a da yawaita istigfari da tsayuwa a cikin dararen da bayi ke kwance suna bacci,tabbas da ka sake samun nutsuwar zuciya da kuma warwarewar wasu ƙulle-ƙulle da dama da suke kewaye dakai.Da ace zaka dage da gayawa Ubangijin da baya gyangyaɗi bare bacci matsalolinka,tabbas da ya yi maka mafita mai yawa cikin lamuran da kai kanka bakasan sun sha maka gaba ba." Ta ɗan dakata tana sake kallon yadda ya zubo mata idanunsa yana sauraronta da dukkanin nutsuwarsa,hakan ya sanyata ɗaurawa da faɗin, "Sihiri gaskiya ne domin kuwa ya ci fiyayyen halitta,amma da yawa ku maza bakwa yarda da hakan,sai ku shantake ku manta da tsaida azkar bare har ku dage da yawaita yin addu'o'in da zasu kare ku daga sharrin sihiri da ƴan surkulle,kafin ace kwabo sai matsaloli da kaidin mace su kewaye rayuwarku har ku tsinci kanku cikin yanayin da wani idan ya mutu direct wuta zai tafi sabida yadda aka juya zuciyarsa ya danne hakkin iyalinsa tare da cusgunawa rayuwarsu,ka tashi ka yi sallah koda raka'a biyu ne Lawal,ka koka wa Ubangijinka tare da yi masa kirari da yabo da mafiya kyawawan sunayen da yake son a ambacesa da su na AL-HAYYU AL-QAYYUM! Ka roƙesa ya yafe maka ya kuma kawo maka mafita cikin tarin abubuwan da suka dameka game da matarka,wanda ni Halimatu bana son ma in sani,Ina da yaƙinin idan ka jera hakan na tsayin kwanaki sai Allah ya baka mafita a lamura da yawa,ina ma ni ce Hajiya Kakah da sai in ce na wajabta maka tsayuwar dare ya zama ibadar za ka dauwama a cikinta domin da shi ne bawa ke gararan duk wani maƙiyinsa a duniya,sannan kuma ya rabauta ranar gobe ƙiyama,matuƙar zaka dage da kai wa Allah kukan ka a lokacin da da yawan bayi ke tsaka da ƙulla sharri ko yin ƙulunbota a tsakanin al'umma,tabbas Ubangiji zai dubeka ya kuma kare ka daga dukkan sharrinsu,babu kuma abinda zai sameka sai abinda aka riga aka zana shi cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARAR ka." Umma ta kai ƙarshen kalamanta tana kashe Baba Lawal da wani irin kallon da ke kashe jiki da zuciyarsa.Shi kuwa ya zuba mata idanunsa ba ya ko son ɗauke ganinsa daga gareta,domin wasu irin feelings yake ji masu matuƙar ƙarfi na sake fisgar zuciyarsa zuwa gareta."Wace iriyar Rahama da soyayyah Ubangiji ya gwada masa da ya fara mallaka masa irin wannan kalar macen a duniya?" Ya tambayi kansa yana tashi da wani irin sauri ya dunfari banɗakinsa domin ɗauro alwala.Umma ta bi bayansa da kallo tana jin tarin ƙauna da tausayinsa mai yawa a cikin zuciyarta,ta ɗaga hannu sama tayi a addu'a a sarari tana faɗin, "Ya Allah ga bawanka nan Lawal,ka sake yin Rahama da gafara zuwa garesa,ka yafe zunubansa kar ka raba zunubansa da sauran ƴaƴansa da basu ji ba basu gani ba Ya Allah! Ubangiji ka warware dukkanin ƙullin da ke jikinsa idan har akwai sihiri ko ƙulunboto na shaiɗanci mace a cikin al'amarinsa." Ta sauke hannuwanta ƙasa tana kai tafin hannunta ta share hawayen da ke gudu bisa ƙuncinta,ta kalli fuskar Baba Mai Itace a lokacin da ya fito daga banɗakin ya doshi saman abin sallar da ta tashi akai.Sai ta zame ta kwanta idanunta akan sa har ya idar da raka'a biyun da ya yi su masu tsayi,tun a sujadarsa ta ƙarshe take jiyo shasshekar kukansa tana ji zuciyarta na sake shiga rauni da ƙarin tausayinsa.Ta fi kowa sanin koda baƙin cikin lalacewar tarbiyya da rayuwar Maimunatu kaɗai aka barsa an jarabcesa,koda ace babu matsalar zama da mace irin Safiya da bata san mutuncinsa dana aurensa ba ko kaɗan.Tunda bata shayin kallon tsabar idanunsa a gaban ƴaƴansa ta kirashi da kalmar ɗan bariki,bata taɓa jin nauyin kallon idanunsa ta tuna masa da kalar rayuwar iskanci da suka yi abaya ita da shi ba.A she ko ba za a lissafata cikin macen da ta san ciwan kanta ba,bare kuma sanin daraja da girman mijin aurenta.Lokacin da ta ga tashinsa daga saman abin sallar sai ta juya masa baya tana gyara kwanciyarta tara da rufe idanunta tamkar wanda bacci ya saceta,tana jin lokacin da ya hawo kan gadon ya kuma lalubeta ya haɗe jikinsu da juna yana jin tsananin ƙaunarta da ya jima bai ji hakan ba a cikin zuciyarsa......✍🏻 [10/11, 12:20 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo* *Paid book 08167768704* _Free page_ *Chapter 9* "Sumayyatu bani da kuɗi,kiyi haƙuri zuwa wata satin zan baki kuɗin ki siya littafan kin ji ko?" Baba Mai Itace ke wannan maganar idanunsa akan Sumayyah dake shirye cikin uniform ɗinta da suka ɗauki guga sai ɗaukar idanu suke.Ta ɗaga manyan idanunta da suka gada wajen Umma ta sauke akan Baban nasu wani abu na taɓa zuciyarta,cikin sanyi da kuma raunin murya ta ce, "Amma Baba yanzu fa ka bai wa Maimunatu nata kuɗin sayen littafin." Ta dakata tana sake duban yadda nan da nan annurin fuskarsa ta ɓace,cikin kaushin murya ya ce, "To suke nan mini na ɗauka na bata,ke kuma sai ki jira sai na sake samun wasu kuɗin,idan kuma kuɗin cefanen da zan bayar ki ke so na ɗauka na baki sai ki gaya mini." Sumayyah ta miƙe jiki a sanyaye tana faɗin, "Allah ya baka haƙuri Baba sai mun dawo." Ya dubeta yana jin can ƙasan zuciyarsa na rawa,amma a zahiri sai ya buɗe baki ya ce, "A dawo lafiya,a kuma dinga mai da hankali,Allah ya yi albarka Sumayyah." Sumayyah ta ƙarisa ficewa da sauri tana jin yadda zuciyarta ke sake karyewa hayewa na cika idanunta."Har sai yaushe ne zai daina nuna musu bambamci?" Ta tambayi kanta tana sake hasko irin murmushin gayya da Maimunatu ta sakar mata sanda Baban nasu ya ɗauki naira dubu ya bata kuɗin wani littafi da aka ce lallai su mallakesa a satin farko da za a koma domin shi za a fara karanta musu.Ta isa ɗakin Umman zuciyarta na sake ƙuntata matuƙa,tana shiga ta ci karo da Raudah ta fito daga ɗakinsu sanye cikin dogon Jalbab ɗinta na zamani.Wani irin Jalbab mai haɗe da kamar niƙab da idan ta ɗaure jelar ɗankwanlin ta janyo shi zuwa goshinta,ta kuma ja ƙasan hular da ke ƙasan gemunta sai ya zamana ya rufe daga bakin zuwa hancinta.Idanunta kawai ake gani a buɗe,amma duk fuskarta sai ya zamana a rufe yake.Sosai kalar Jalbab ɗin da yake dark coffee ya haske farar fatarta,yanayin zaman jalbab ɗin a jikinta ba ƙaramin kyau ya yi mata ba.Ta dubi Sumayyah da dukkanin damuwa ya bayyana akan fuskarta ta ce, "Sumy lafiya,daga wajen Baba ki ke halan?" Sumayyah ta jinjina kai ta ce, "Don Allah Yaya Raudah ki bani aron dubu ɗaya idan na samu kuɗin zan mayar miki,tunda nima na ɗan fara sana'ar soya aya da tsami gayen nan zan dinga shiga dashi skull ɗin ina jarabawa." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Ga jakata can a ɗaki ki ɗauki dubun da ta rage a ciki." Daga haka ta fito ta nufi bakin kitchen da Umma ke ciki tana ƙarisa aikin safe da ita Raudan ce ta fara,ganin zata yi latti ne ya sanya ta bar Umma da ƙarisa dama kunun tsamiyan da suka fi shan sa da safe. "Umma na fito zamu wuce kada muyi latti,a saka min fanken a leda na ci a can kawai." Umman ta ɗaga idanunta ta kalli Raudah tana jin ƙarin ƙaunarta mai yawa a cikin zuciyarta,ta ce cikin sanyinta, "To shikenan Raudah,amma da kin sha kunun koda rabin kofi ne da zafinsa." Raudah ta saki murmushi ta ce, "To Umma bari na gaida Baba na fito." Daga haka ta nufi ɗakin Baban nasu ta doka sallama daga bakin ƙofar,ya amsa tare da bata izinin shiga idanunsa akan ƙofar shigowa ɗakin. "Baba ina kwana,dafatan ka tashi lafiya,zamu wuce makaranta." Baba Mai Itace ya zubawa Raudah idanu wani abu mai ƙarfi game da ita na kewaye zuciyarsa.Maganganun Anty Amarya ne suka shiga dawo masa yana jin wani irin matsanancin tashin hankali na riskansa,ya sake kafeta da idanunsa kafin ya soma faɗin, "To Raudah Allah ya tsare,ku maida hankali ga abinda ya kai ku banda sakarci ko sakarwa samari da marasa tsoron Allahn Mallamanku fuska,ki ji tsoron Allah wajen kare mutuncinki Raudah kin ji ko?" Raudah da kalamansa a yau suka taɓa zuciyarta,domin bai taɓa furta mata makamancinsu ba sai a yau ɗin.Ta dubesa da wani irin duba da ke bayyana rashin jin daɗin kalamansa,cikin sanyin muryarta mai cakuɗe da shagwaɓa ta ce, "In Sha Allah Baba zamu kiyaye,amma ko dai wani ya kawo ƙaran mune ya ce muna wani abin a skull ɗin,sabida na ji kamar jirwaye ka ke mini mai kama da wanka,wallahi Baba ka tambayi Baba Auwalu da ke aiki a cikin makaranta ka ji,muna iya ƙoƙarinmu wajen kare mutuncinku da namu baki ɗaya." Jikin Baba Mai Itace sai ya yi sanyi,ya dubi Raudah duba mai cike da so ya ce, "Ba haka bane Raudah,lamarin ƙanwarku Maimunatu ne ke bani tsoro da sakani cikin tarin damuwa da kokwanto,bana so ya kasance ku ma kun ɗauki layin da ta bi,duk da cewa na san tarbiyyan da Halimatu ta ɗaura ku akai ba iri ɗaya bane,ku ji tausayina Raudah kar ku yadda ku sallama mutuncinku a titi,sannan ina roƙo ku yafe mini akan dukkanin abinda kunnuwarku suke jiye muku a bakin Safiya kin ji ko?" Raudah ta jinjina kai tana jin wani abu mai nauyi na sake danne zuciyarta,cikin sanyi da raunin murya ta ce, "Baba In Sha Allah zamu tsare kanmu,kuma ku cigaba da yi mana addu'a, Allah zai kare sai mun dawo Baba." Daga haka ta miƙe ta fito daga ɗakin bayan ya yi musu addu'ar samun ilimi mai amfani. "Umma na fito bani fanken kawai na wuce sasan tsuhowarcan mu gaisa,na makara kada ya zamana su Aliya na jirana." Raudah ta faɗi hakan tana duban Umman su da ke zuba kunu a wani ƙaramin flask da take zubawa Hajja Kakah,ta miƙawa Raudah fankenta da ta riga ta ƙulla mata a ledar tana faɗin, "Gashi nan,sai ki haɗa dana Hajjah Kakan ki wuce mata dashi." Raudah ta amsa tana mita a zuci na cewa,ba lallai ma Hajjah Kakah ta ci fanke da kunun ba idan ta samu abin da ya fishi daga sasan sauran ƴaƴan nata. Tana fitowa daga sasan nasu riƙe da flask na kunu da fanken Hajjah Kaka,ta hango fitowar Yaya Deeku daga sasan su.Ta ɗan ɗauke kai daga dubansa tana cigaba da taku a nutse ta doshi sasan Hajjah Kakan,tana daf da sanya kai cikin zauren sasan ta jiyo muryarsa yana kiran sunanta.Ta ɗan waiwayo tana dakatawa tayi tsaye har ya ƙariso,ya dubeta da wani sassanyar kallo yana bin shigarta da kallo daga sama har ƙasa.Wani kishi ne ya turnuƙe zuciyarsa har ya kasa haƙuri ya furta,"Habeebty anya wannan hijab ɗin ya rufe wani abu kuwa? Kin ga irin kyawunki da ya fito ne,please a shigar da hannun nan ciki don Allah kin ji?" Raudah ta ɗago ta dubesa tana shagwaɓe fuska tare da narke murya ta ce, "Yaya Sadeeq gud morning!" Ya sake zuba mata idanu bayan ya amshi flask ɗin hannunta na fanke dana kunun ya ce, "Habeebty ni ba gaisawa nake so ba,kiyi abinda zai rage min zafin da nake ji a zuciyata please!" Raudah ta kalli kanta tana mai maida hannun jalbab ɗin ciki kamar yadda ya buƙata.Ta dube shi ta ga yadda idanunsa ke yawatawa a saman ƙirjinta da ta tabbatar fitan tudunsu ta sama time ɗin da hannun ke waje ne ya sanya shi jin kishi,sai ta ji wani irin kunya ya lulluɓeta har tana saurin juya masa baya.Ya sauke wani sassanyar ajiyar zuciya yana yin ƙasa da muryarsa ya ce, "Babu laifi dai an ɗan rage ganinsu Habeebty,amma don Allah idan akwai hijab ɗin da yafi wannan faɗi da sakewa ki taimakeni ki koma saka su,ina fata dai baki taɓa fita da gyale zuwa skull ɗin ba ko?" Raudah ta dube shi da wani irin narkakken kallon da ya ji tasirinsa har ɓargonsa,cikin shagwaɓe murya ta ce, "Ka tambayi Zee Yaya Deeku,na tabbatar za ta faɗi maka ko cikin mafarki ban taɓa sha'awar saka gyale na fita zuwa haɗararriyar makarantar nan ba." Yaya Sadeeq da ya ji wani sanyi a cikin zuciyarsa,sai ya furta, "Das very good Habeebty,I luv u so very much!" Suka jera kafaɗa da kafaɗa har cikin sasan Hajjah Kakah,Sadeeq na sake jin ƙauna da azababbiyar soyayyar Raudah na kekketa zuciya da jinin jikinsa.Da fara'a sosai Hajjah Kakah ke amsa gaisuwar ƴan jikokin nata da take jinsu a tsakar zuciyarta,ta dubi Raudah da ta miƙe tsaye sabida gudun makara ta ce, "Har za ku wuce makarantar Raudatu? Yanzu Aliya ta fita nan ita ma cikin sauri,Zainabu ne ƴar ikon bata miƙo tata gaisuwar ba tunda ita da uwarta wuyansu ya yi kaurin da ba kullum nake samun darajar da za a tako a gaidani ba. Raudah ta fice da sauri-sauri tana faɗin, "Hajjah Kakah ni dai na wuce sai mun dawo,Baby sai na dawo." Sadeeq ya miƙe ya rufa mata baya yana jin daɗin kalmar Baby da ta kiraye shi a karon farko. "Wait Habeebty!" Ya furta hakan lokacin da ya cin mata tana dab da ficewa daga sasan,ta tsaya tana jin kunyan waiwayowa ta dubeshi.Suka jera da juna yana kasheta da kalaman soyayya masu narkar da zuciya har suka isa ƙofar shiga sasan su Yaya Deekun,suna shirin sanya kai Baba Adamu dasu Zee na shirin fitowa.Raudah wani uban kunya ya rufeta domin kuwa Yaya Sadeeq riƙe yake da jakanta,tayi saurin risinawa ta gaida Baba Adamun idanunta akan Zee da ke bin Yayanta da wani irin kallo.Baba Adamu ya amsa da fara'a yana musu fatan dawowa lafiya daga skull ɗin,ya wuce su kai tsaye zuwa sasan Hajjah Kakah. Zainab da Aliyah suka gaida Yayan nasu,ya amsa yana sake tsare gida tare da miƙawa Raudah hand bag ɗinta.Ta amsa tana dubansa ƙasa-ƙasa kafin shi ma ya ɗan matso kusa da ita sosai yana faɗin, "Take care Angel,banda kula kowa please!" Raudah ta sakar masa murmushi ya wucesu ya shige zuwa ciki su kuma suka nufi ƙofar fita gate ɗin gidan nasu.Suna tafe ne Aliyah na tsokanar Raudah da cewa duk ta fara susuta musu Yaya da soyayyarta,ita dai Zainab bata tanka ba sai ma time to time da take sakin ƙaramin tsaki har suka fito bakin titi suka samu napep da zai kaisu har bakin gate ɗin FCE. "Salamu alaikum masu gida!" Muryar Hajjah Kakah ya ratsa cikin kunnuwan Inna Karimatu da ke jan ruwa daga bakin rijiyan sasansu da ke daga shigowa sasan babu tazara sosai.Ta ɗaga idanunta ta sauke akan Hajjah Kakah da fuskarta sam babu alamun annuri,cikin tsare gida ita ma ta amsa sallamar Hajjah Kakan tana faɗin, "Barka da shigowa Hajjah Kakah,ƙarisa daga cikin ɗakin gani nan zuwa." Hajjah Kakah da ta hango kujera a tsakar sasan sai ta nufi wajen kujera ƴar tsugunon tana faɗin, "Bari na zauna anan Karimatu wajen ma yafi daɗin zama ga hantsi,gama ɗiban ruwan shigowar taki ce ta musamman." Inna Karimatu ta taɓe baki tana faɗin, "To shikenan bari na kai ruwan kitchen Hajjah Kakah.Daga haka ta nufi hanyar kitchen da botikin da ta cika da ruwan,Hajiya Kakah ta rakata da ido tana jinjina kai haɗe da mamakin yadda Karimatun ke ta juyewa zuwa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryan mara mutunci da ɗa'a.Fitowar Innar su Aliya daga ɗakinta ya sanya Hajjah Kakah mai da hankali zuwa ga Inna Aminatu tana amsa gaisuwarta,ta ɗaura da faɗin, "Ameena daga ke har Karimatu dai kun daina zuwa gaidani sai idan kun bushi iska kun yi ra'ayi sabida kun raina mazajenku shi ne nima rainin da rashin albarkan ya shafeni ko? To ku kula da rayuwa na faɗa muku,domin duk wacce ta rainani ta raina uwar da ta kawota duniya ne,sabida idan akwai kara da ɗa'a uwar miji ai uwarku ce." Ta ƙare maganar tana watsawa Inna Amina wata muguwar harara,Inna Amina ta sadda kai ƙasa tana cuskune baki da yin ƙuƙunai ƙasa-ƙasa. Inna Karimatu ne ta iso wajen da wata kujerar zaman a hannu tana zabgawa Inna Amina harara ta ce, "Hajjah Kakah kin ce wajena kika shigo na ga kuma Innar Aliya tayi tsaye a kanki lafiya?" Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "Ni dai Allah ya gani sai da na gama karanta li'ilafi,sannan na bada sadakan ƙosai da zafinsa kafin na tako ƙafafuna zuwa sasan nan,don haka duk sharrinku sai dai kuci kawunanku ku sha baƙin ruwa,ke Amina bani waje bana son gulma." Inna Amina ta wuce a fusace zuwa ɗaki tana jaddada jarabar Hajjah da iya ci maka mutunci idan ta so a cikin zuciyarta.Ta nema kujerar da ke daga bakin ƙofarta da an shiga ɗakin ta zauna,domin so take ta baza kunnuwa ta ji da wacce Hajjah Kaka ta zo wa Inna Karimatun? "Karimatu Saddiku da Usmanu dukkaninsu sun sameni da zancen cewa sun samu matar aure,sai dai shi Sadeeku ya zo da wani ƙauli na cewa wai kin ce ba zai taɓa haɗa jini da jinin Haleematu ba ko miye dalili?" Inna Karimatu ta sake gimtse fuska tare da haɗe girar sama da ta ƙasa ta dubi Hajjah Kakah kai tsaye ta ce, "Dalili kenan bana son ta kuma bana ƙaunarta,sannan ba zan taɓa son jinin Halimatu da ita kanta ba har abada,don haka indai ina da hakkin haihuwar Sadeeq to ba zan taɓa amincewa ya auro mini ƴar maƙiyiyata ba." Hajjah Kakah ta kama baki tana faɗin, "Ƙalu innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Yanzu Karimatu a gabana ki ke maimaita waɗannan munanan kalaman?" Inna Karimatu babu ko ɗar ta jinjina kai ta ce, "Hajjah Kakah ai gara na faɗi miki gaskiya domin ba zan ji kunyar kowa a auro mini ƴar da za ta zame mini masifa su haɗu ita da uwarta su mallake mini shi ba,sai dai inga yana musu bauta ni ko oho,to wallahi ba zai saɓu ba wai bindiga a ruwa,dole ya rabu da Raudah ya je can waje ko cikin dangina ya zaɓo matar aure,ai ba a kanta a fara samun kyau da diri ba,mu ma zuri'armu akwai kyawawu masu nono da ɗuwawu sai ya zaɓo a ciki ya aura amma ba dai jinin Halimatu ba." Tana kai wa ƙarshen kalamanta ta miƙe ta shige ɗakinta a fusace ta bar Hajjah Kakah na sakin salati tana jan majina,sosai take kuka bilhakki na baƙin cikin kalaman da Inna Karimatu ta gaggaya mata babu kunya bare tsoron Mahaliccinta.Ta miƙe da ƙyar tana ɗaga murya ta ce, "Dani ki ke zancen Karimatu,ina ga kin manta wacece Zuwairah amma zan tuna miki,zan kuma tabbatar miki da cewa har yau ba a auro wacce ta isa in yanke hukunci a cikin ahalina ta tada zancen ba,wallahi sai dai ki zaɓa ko aurenki ko kuma auren Raudah da Abubakar Sadeeq matuƙar ina numfashi!" Hajjah Kakah na kai wa ƙarshe ta fito a fusace daga sasan Baba Adamu ta nufi na Baba Lawal.Tun daga zauren shiga sasan take ƙwalla kiran, "Halimatu! Hali dubu!! Kina ina?" Umma da ke daga cikin ɗakin tana ƙullin siga dasu maggi ta jiyo kiran,sai ta saki ƙullin ta fito da sauri tana faɗin, "Na'am Hajjah Kakah." Hajjah Kakah da ta shigo ciki zuwa lokacin,sai ta sauke ganinta akan Umma tana faɗin, "Yauwa mu shiga daga ciki,yau banda lokacin kula kowa wajenki kaɗai na zo." Umma ta jinjina kai ta ce, "To Bismillah Hajjah Kakah mu je ɗaki." Hajjah Kakah tayi gaba Umma na biye da bayanta har zuwa cikin falonta.Ta nemi kujera ta zauna tana sauke idanunta akan yawan ƙullin siga da su maggi da Umma ta tara su,cikin wani irin murya ta ce, "Allahu Akbar! Duk fa wannan rufin asirin da buɗin ake ma hassada da baƙin ciki Halimatu,wallahi babu abinda ke ɗawainiya da zuciyar Karima sai muguwar hassada da adawar da take yi da nasibi da buɗin da Ubangiji ya yi miki akan kasuwancinki,kuma In Sha Allahu tayi ta gani kenan tunda ita dai zuciyarta babu khairan." Umma da bata san inda zancen Hajjah suka dosa ba sai jinjina kai tayi tana murmushi,Hajjah Kakah ta sake gyara zama tana cigaba da faɗin, "Wajenki na zo Halimatu akan batun Raudatu da Sadeeku,na san dai kema zancen cewa suna son juna tuni yazo miki,inma bai zo kunnuwarki ba na tabbatar a kallon rashin kunyar da yake bin ɗiyarki dashi kaɗai zai fassara miki ba ƙaramin tafiya da zuciyarsa tayi ba,don haka kar ki zamo cikin masu cewa za su ja da hukuncin mai duka,domin duka bamu san meke ɓoye ba,babu ruwanki da ƙiyayyar da uwarsa ke miki ki ce ba zaki lamunce masa ya auri ƴar uwarsa kamar yadda ita waccar shashashan ke tada jijiyan wuya tana faɗin ba a isa ba,to ke ki nuna halin dattako da ilimi,ki sake nunawa maƙiyanki ke ɗin mai ilimice da sanin yakamata wacce ba zata shiga hurumin Ubangiji ba,domin shi sha'anin aure addu'a ake binsa dashi ba jayayya da furta munanan kalamai ba." Hajjah Kakah ta ɗan dakata tana kallon Umma da ta nutsu tana saurarenta,hakan ya bai wa Hajjah Kakah damar cigaba da faɗin, "Mun gama magana da Adamu da Auwalu akan cewa ƙarshen watan nan kowacce a cikin su ukunnan da zasu kammala babban makaranta su fito da tsayayye,ita Raudah tunda Allah yasa na gida ne,ina so a fara aje mini goron saka ranar aurenta da Sadeeku cikin ƙarshen watan nan domin so nake na nunawa Karimatu cewa bata isa ba,kuma tayi kaɗan ta hana Sadeeku auren zaɓin zuciyarsa matuƙar nina tsuguna na haifo mata ubansa ta aura,don haka ina so ki kwantar da hankalinki a matsayinki na haƙurarriyar mace da duk cikin surukaina aka shaideki,ki bisu da addu'a Halimatu kada ki yadda ki yi ma abin mummunar fata ko baki kamar yadda Karimatu ta fara,ina fata kin fahimceni?" Umma ta jinjina kai ta ce, "Na fahimceki Hajjah Kakah,Allah ya tabbatar da alkhairi idan akwai,idan kuma babu Allah ya yiwa kowa zaɓi mafi alkhairy a cikinsu." Hajjah Kakah ta jinjina kai ta ce, "Ameen Halimatu,ai akwai ma alkhairy In Sha Allah! Halimatu ke dai kawai ki zuba ido ki kuma bisu da addu'a tunda har Allah yasa na gano ita ma Raudan da gaske shi zuciyarta ke so." Daga haka Hajjah Kakah ta miƙe domin ficewa daga ɗakin,Umma tayi saurin tashi ta ɗauki ƙullin kwatan siga ta saka a baƙin leda ta biyo bayan Hajjah Kakah dashi tana faɗin, "Hajjah Kakah ga wannan kya saka a koko babu dai yawa." Hajjah Kakah ta amshi ledar tana faɗin, "Allah ya yi albarka,bama dole ki dinga cigaba ba tunda Allah ya halicceki da hannun ungu,wasu kuma hannu kaman na ƴan dambe,indai ance maka ungo to abincin da ɗanka ya saka kuɗi ya siyo mai kyau ne,ko kuma shi ya shigo da abin masarufin da dole a ɗibo a baka naka kason,Allah ya yi miki albarka Halimatu ya kare ki daga kaidin ƴan hassada da maƙiya,ki dage da sadakan zazzafan ƙosai bayan kin baɗe shi da yaji,tunda ke mai tsayuwan dare ce dama,to ina tabbatar miki da cewa sai kin gagari kowace shegiya a cikin kishiya ko kishiyoyin saurinki." Umma ta jinjina kai cike da zallar tu'ajjibin halayya irin na Hajjah Kakah da ke canzawa kamar wata hawainiya.Yanzu za tayi dakai anjima ta ce kai ne baka iya mata ba,ta saki murmushi tana juyawa zuwa ɗakinta bayan Hajjah Kakah ta fice daga sasan ba tare da ta lalubi ɗakin ƴar gaban goshin nata Anty Safiya ba.........✍🏻 [10/11, 1:12 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ ayshadansabo* *Paid book 08167768704* _Free page_ *Chapter 10* Umma na cigaba da ƙulla siga da maggin ne amma zuciyarta cike take da tarin ruɗani da damuwa,Allah ya sani har cikin zuciyarta ta yaba da Sadeeku za kuma ta so ya zama miji ga Raudarta.Amma sanin hali irin na Inna Karimatu da irin ƙiyayyar da take gwada mata ya sanya tana tsoron wani al'amari mai girma kamar aure ya shiga tsakanin Raudah da Sadeekun,tabbas tana tsoron halin da Raudah ka iya shiga idan har Hajjah Kakah ta kafe akai wannan haɗin ba tare da amincewar uwar Sadeeku ba.Addu'a ta dinga yi akan matuƙar babu alkhairy Allah warware ƙullin cikin hikimarsa da gaggawarsa,domin tabbas ba za a ji bakinta a cikin batun ba matuƙar ba alkhairy za ta furta ba. Ta kintsa komi bayan ta kammala ƙulle-ƙullenta ta fita zuwa kitchen domin shirin ɗaura girkin rana,sabida bata so Suhailah da Khaleel su shigo gidan bata gama girkin rana ba.Yaron ya riga ya saba da ita matuƙa har fiye da uwarsa,sabida kulawar da take haɗesu shi da Suhailah ta basu Anty Amarya bata tsayawa ta kula da shi kamar hakan ba.Shi kuma Yaro dama wajen duk da aka fi tarairayarsa anan yake,babu ruwansa da rashin jituwan da ke tsakanin Iyayensa. Tana cikin gyaran kayan miya Anty Amarya ta fito daga ɗakinta,hannunta riƙe da ledan cefane da alamu ita ma girkin za ta fara shirin ɗaurawa.Ta kalli Umma ta watsar tana cigaba da tauna cingam ɗin dake bakinta,sai da ta zo ƙofar shiga kicin ɗin ta saki tsaki tana faɗin, "Aikin banza munafurcin wofi,har ni za a shigo ba a nemi inda nake ba sabida ana so a haɗa kai a cuci Sadeeku a aura masa ragowar lacturers,ahayye! Allah sarki!Hala an sha bamu san abinda ake aikatawa a cikin hijaban munafurcin da ake zumbulawa bane,ai shi ɗan iska idan ya cika ɗan iska wallahi baya munafurci da badda kama,fitowa da iskancinsa yake sarari kowa ma ya gane tunda babu ɗan iskan da ya isa ya sauya maka kalar rayuwar da kaso gudanarwa,kuma Sadeeku ba zai taɓa auren ragowa ba koda ace ita ce hurul inin duniya,sabuwa dal zai ɓare a leda tunda ubansa ba ragowar bariki da ya ci ya suɗe bane da za a lulluɓa ragowa akai ma ɗansa." Ta kai ƙarshen kalamanta tana sakin ƙaramin shewa tare da jan mugun tsaki tayi cikin kitchen ɗin.Umma da ke ta gyaran kayan miyanta sam bata ɗago ba,duk da yadda zuciyarta ta kai ƙoluluwa wajen ɓaci da irin kalaman ɓatanci da Safiya ke jingina Raudah dashi.Wani abu mai azabar nauyi da ƙuna ya tokare wuyanta har numfashi na son yi mata wuyan shaƙa,sai kawai ta shiga nanata kalmar Innalillahi har zuwa ƙarshe.A hankali ta ji zuciyarta na samun sassauci,ta kammala gyaran kayan miyan ta nufi ƙofar ɗakinta ta ɗebo ruwa a cikin ƙaton roban tara ruwa da ke barandar wajen ɗakin nata.Ko kaɗan ba tayi gangancin tanka Anty Safeeyah kamar yadda ita ta so hakan ya faru ba,ko kalma guda bata furta ba har ta kammala daka kayan miyan ta kwashe.Kitchen ɗin da tayi niyyar shiga tayi girkin a ciki ma sai ta fasa,ta fito daga waje ta ɓangaren barandar ƙofar ɗakinta ta kafa murhun gawayin a nan.Tana hura gawayin da tafi amfani dashi fiye da itacen da Baba Lawal ɗin ki jibge musu na amfani,tana tunanin idan ta samu faraga ma ƙaramin kamfin gas kawai za ta siya su riƙa maneji dashi suna amfani da abu biyu.Anty Safeeyah ta ƙulu iya ƙuluwa da yadda Umma ta maida ita mahaukaciya karya da ke haushi ita kaɗai,ta dinga roran masifa a tsakar gidan tana sakin maganganu amma Umman tayi biris bata tanka ta ba.Har su Suhailah suka shigo gidan ƙarfe sha biyu da rabi na rana Anty Safeeyah bata koma ɗaki ba,tana tsakar gidan tana sakin habaici da maganganun banza kala-kala.Umma tuni girkinta ya kusa kammala,tunda dama jallof ce na shinkafa da ta haɗa da taliya ta saka wani ragowar kifi da take dashi a aje.Khaleel ya rugo da gudu zai nufeta amma sai Anty Amarya ta kwaso a guje ta suresa suka nufi ɗaki tana faɗin, "Wuce mu je ɗan banza makwaɗaicin Yaro,na faɗi maka idan baka kiyayesu ba sai na ci ubanka,tunda duk abinda suke hilatanka dashi ina siya maka amma kullum zuciyarka na garesu kamar wanda suka lashe kurwansa,wallahi ba don boka ya tabbatar min ba asiri suka yi suka kama zuciyarka ba da sai anyi bala'i akan yadda ka ke liƙe musu kaman kaska." Umma da ke jiyo dukkanin kalaman da Anty Safiyan ke yi sai kawai ta girgiza kai tana sakin murmushin takaici da baƙin ciki,ta kama hannun Suhailah suka nufi ɗaki domin ta cire kayan makarantan kafin abincin ya ƙarisa nuna. Ƙarfe ɗaya su Sumayyah da ke makaranta guda su huɗu suka shigo gidan,kowacce ta nufi sasansu ita da Maimunatu suka jero zuwa sasansu Maimunatun na faman wani harare-harare.Gabaki ɗaya huɗubar uwarta akan ƴan uwanta shi ne kada ta taɓa raɓarsu domin su ɗin ƴan uba ne da babu abinda suke mata sai hassada,haka take karanta mata tun daga ƙuruciya har girmanta,kawo yanzu kuma da idanunta suka gama buɗewa da bariki da sanin daɗin maza.Sai ya zamana babu wanda take kallo da gashi tsakanin Ummansu dasu kansu su Raudah,Baba Lawal ɗin kansa a sakarai take kallonsa tunda uwarta ta gama kwance masa zani a kasuwa a wajenta _,(Kaicon duk wata mace irin Anty Safiya,wallahi ƙalubale ne a gareku matan auren da sam bakwa ragawa mazajenku,ba ku tashi yiwa miji ɗiban albarka sai agaban idanun ƴaƴan cikinsa,wannan babbar musiba ce kuma babban kuskuren da idan kina aikata shi sai kinyi mummunar danasani a lokacin da ba zai yi miki amfani ba,sabida ita ƴa mace da irin tarbiyar da ta tashi ta ga kina wa ubanta take koyi,abin duk da kike yi shi za ta je gidan wani ta aikata,in ma sharran ko khairan,shiyasa tun asali aka ce maza su zaɓarwa ƴaƴansu uwa ta gari,kamar yadda muma mata akace mu zaɓarwa ƴaƴayenmu uba na gari,Allah ya shiryatar damu baki ɗaya)._ Sumayyah ita ma ɗauke kanta tayi har suka shige ciki kowacce ta nufi ɗakin uwarta,tana sanya kai cikin falon nasu Suhailah ta rugo ta rungumeta tana faɗin, "Anty Sumayyah sannu da dawowa,ita Anty Raudah bata dawo ba har yanzu." Sumayyah ta shafa fuskar Suhailah ta ce, "Za ta dawo Suhailah,amma sai can yamma kila,dafatan kinyi karatu mai yawa a skull." Suhailah ta ce, "Nayi sosai Yaya Sumayyah,idan Anty Raudah ta dawo za ki ce ta bani gullisuwa?" Sumayyah tayi murmushi tana faɗin, "Zan ce ta baki,ni ma idan na soya aya nayi tsami gaye zan baki ko bakya so?" Cike da murna Suhailah ta ce, "Ina so mana Yaya Sumayyah." Sumy ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Das my baby luv! Ki ce Allah ya sanya mini albarka a cikin sana'ar kin ji autar Umma?" Suhailah ta ce, "Allah ya kawo kasuwa da yawa irin na Anty Raudah,kema ki dinga sawa a robobi ana kai wa shagon Usy ko?" Sumy ta saki murmushi tana nufan ɗakinsu ta ce, "Haka nake fata autar Umma." Uniform kawai Sumayyah ta cire ta fito ta nufi banɗaki,tana fitowa ta ɗaura alwala ta nufi ɗaki domim gabatar da sallar azuhur da basu yi ba. Suna cin abinci gaba ɗayansu a falon Umma ke bai wa Sumayyah labarin shigowar Hajjah Kaka akan batun soyayyar Raudah da Yayansu Sadeeq.Ta ƙare maganar da cewa, "Sumayyah ki taya ƴar uwarki da addu'a domin muna buƙatar hakan,sabida ina tsoron kaidin maƙiyi,musamman Karimatu da kowa ya fahimci da gaske take ƙina ni da ku baki ɗaya,ban kuma san me na tsare mata a wannan duniyarba,duk iya yadda na yaba da nutsuwa da hankalin Sadeeku zuciyata ta kasa nutsuwa da soyayyarsa ga Raudah,domin ina ji ajikina babu abinda za ta tsinta a cikin aurensa face ɓacin rai,sai dai kuma idan Allah ya riga ya rubuta hakan a cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARARsu daga shi har ita ɗin." Umma ta kai ƙarshen kalamanta a sanyaye tana duban yadda ita ma Sumayyah duk jikinta ya yi sanyi.Da wani irin sanyin murya ta ce, "Hakane Umma,nima ina hango tarin ƙalubale,ba kuma na fata Hajjah ta tunzura ayi komi cikin gaggawa,ya dace ta bari ayi addu'a a kuma bi komi a sannu dokin nuna ƙarfin iko tamkar sake ruru wutar ƙiyayya da tsanarmu a zuciyar Inna Karimatu ne." Umma ta gyaɗa kai ta ce, "Nima dai abinda na hango kenan Sumayyyah,sai dai na ɗauki alwashin ni Halimatu ba zan taɓa tsoma bakina da sunan ja da hukuncin da zata zartas ba,zan dai dage da addu'a ina gaya ma Allah,In Sha Allah shi zai bamu mafita cikin sauƙi,jikina na sake yin sanyi ne a duk lokacin da na fahimci cewa zuciyar Raudah na ƙaunarsa,da ace bata son sa ne da nayi dukkan kasada wajen fahimtar da Hajjah Kakah akan kar ta zafafa,amma yanzu ina magana nawa ne zai fi zafi domin dama suke da fada a wajenta ita da Safiya basa laifi,sai dai su aikata kuskuren da kana shiga cikin maganar kai ne zaka kwana a ciki,don haka waɗannan kawai zan zuba musu,makamina shi ne addu'ata kaɗai!" Umma ta kai ƙarshen maganar tana yiwa Sumayyah nuni da idanunta,nufinta shi ne idanun kaɗai za ta sanyawa Hajjah Kakah da Inna Karimatu akan lamarin har su ga abinda Allah zai hukunta. *Ƙarfe 9:05pm* "Na tara ku ne akan maganar Sadiku da Raudatu,tunda har suna son junansu to ni banga abin ɓata lokaci ba,don haka ina so a cikin satinnan Sadiku ya kawo goro da duk wani kayan saka rana da ake buƙata daga gidan maza,so nake a fara saka lokacin aurenta kafin sauran su daidaita da nasu tsayayyun,sannan kai Lawal ina so ka faɗiwa Maimunatu da uwarta cewa,ni Hajiya Zuwairah ba zan laminci rayuwar yawon ta zubar a cikin ahalina ba,ko dai Maimunatu ta fito da miji a haɗata da Yayyinta a aurar da ita kafin ɓullowar abin kunya a jikinta,ko kuma ita da uwar su haɗa shirginsu su bar cikin ahalina,wannan umurni ne daga gareni kai tsaye tunda ni tamkar sunyi asirin da suka rufe bakina bana iya tsawarta musu yadda yakamata a gaban idanunsu." Hajiya Kakah ta kai ƙarshen kalamanta idanunta akan Baba Mai Itace da ya yi ƙasa da kansa.Baba Lawal ya jinjina kai tare da ɗagowa ya dubi sauran ƴan uwansu su Baba Auwalu sannan ya soma da faɗin, "Na ji Hajiya,In Sha Allah zan isar da umurninki,dama kuma haka muka yanke shawara ni da ƴan uwana akan gara tayi gaggawar fito da miji ayi mata aure,amma maganar Sadiku da Raudah me zai hana abi komi a hankali Hajiya? Ni ina ga abari sauran su fito da nasu tsayayyun sai a sanya lokaci guda,tunda dai ba wani ne zai zo daga waje a shure batun na gida a bai wa dawa ba,in dai ni na haifi Raudah ga ƴan uwana nan su zama shaida cewa, na bai wa Sadiku ita,bata da wani miji sai shi matuƙar bashi ne da kansa ya dawo ya ce baya sonta da aure ba,don haka kiyi haƙuri a daidaita da sauran maneman ƴan uwanta da suka taso kansu guda." Hajiya Kakah ta jinjina kai cike da gamsuwa,idanunta cikin na Baba Lawal ta ce, "Ban ƙi ta taka ba Lawallina,abinda nake so ku fahimta shi ne,akwai shaiɗanan da ke son shigowa cikin maganar matuƙar ban nuna isata da ikona akan ahalina ba,a yau ɗinnnan Karimatu ta gaya mini zafafan kalaman da nayi rantsuwa sai na nuna mata ƙarfin ikona akan ku da zuriyyanku,don haka babu gudu babu ja baya a gaggauta fara saka lokacin auren Raudah da Sadiku a raba goro kowa ya shaidi hakan,in yaso duk wanda aka daidaita da nata manemin sai a faɗi masa lokacin da aka yanke za a yi na ƴar uwarta a haɗe tare,kuma bana so ya wuce watanni uku kacal tunda ance saura watanni biyu suka rage musu su kammala karatunsu baki ɗaya." Hajjah Kakah ta dakata da maganar tana duban duka ƴaƴan nata da suka nutsu suna saurarenta.Baba Adamu ne wannan karon ya yi magana yana faɗin, "Hajiya maganarki akan hanya take domin nima kalaman da Karimatu ke furtawa akan wannan lamarin sun fara kai ni bango,don ni cewa nayi ba domin kar ayi saurin ɗaura musu aure bata kammala karatunta ba ya hargitsa mata lissafi,da nace a ɗaura aurensu a ƙarshen satin nan ma,in yaso a haɗa bikin ayi tare dana ƴan uwan nata daga baya,amma lamarin ƴaƴan yau da basu da haƙuri da kawaici ya sanya ba za a yi hakan ba,amma tabbas gara a tsaida lokaci domin ta gane cewa mu ke da iko da ƴaƴan ba ita ba." Baba Auwalu ya jinjina kai ya ce, "Duka na gamsu da kalamanku,amma ina so in mana matashiya akan zurfafa addu'a akan dukkanin lamuran da suka kunno mana kai suke neman kawo hargitsi da rashin fahimta a tsakanin junanmu,mu bi komi a hankali domin aikin gaggawa mafiya yawan lokuta daga shaiɗan ne,duk wani bore da kalaman banza da ke fitowa da daga bakin Karimatu aikin banza ne domin kuwa tun ran gini ran zane ne,idan har Allah ya riga ya hukunta aure a tsakanin Sadeeq da Raudah cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARAR su tabbas babu mahalukin da ya isa ya hana wanzuwar hakan sai dai idan lokaci bai yi ba,idan kuwa Allah bai rubuta ba duk yadda zamu kai ga son su dasu mallaki junansu hakan ba zai faru ba,don haka mu maida lamura zuwa garesa mu taya su da addu'a sai mu ga komi ya zo ya wuce cikin sauƙi." Baba Lawal ya sauke numfashi a hankali,cikin matuƙar gamsuwa da kalaman Baba Auwalu ya jinjina kai yana faɗin, "Wannan batu haka yake Auwalu,maganarka ita ce abar dubawa." Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "Dukkaninku na ji hanzarinku da shawarinku,sai dai ku sani ba zan taɓa yin kaffarar rantsuwar da nayi ba,don haka ƙarshen wata nake so in ga kayan sanya rana sun bayyana a gabana,ku tashi ku bani waje na sallameku." Tana kai wa ƙarshen kalamanta ta ɗauke kai daga dubansu tana faman huci.Suka tashi gaba ɗayansu suna haɗa baki wajen faɗin, "Allah ya baki haƙuri,za a cika umurninki In Sha Allah!" Ta taɓe baki tana duban Baba Mai Itace ta ce, "Idan ka shiga ɓangarenka ka turo mini Raudah da Maimunatu ina son ganinsu." Baba Lawal ya jinjina kai ya ce, "Za a turo su yanzu,mu kwana lafiya Hajiya." Hajjah Kakah ta amsa shi a dake tana rakasu da wani irin kallo na cewa,dani ku ke zacen. Suna tafe jere da juna ne suna tattauna maganar Hajiya Kakah na dagewa akan lallai a fara sanya ranan auren Raudah da Sadiku,shi ma kuma Baba Adamu da alamu hukuncin mahaifiyar tasu ya yi masa daidai.Hakan ya sanya Baba Lawal da Baba Auwalu yin fatan alkhairy,Baba Auwalun na faɗi ma Baba Adamu cewa,zai yi magana da Sadeeq ɗin zuwa da safe domin a yanzu akwai ayyukan da zai gabatar idan ya shiga cikin gidansa.Sukai sallama da junansu kowanne ya nufi sasansa yana jinjina rigima irin ta tsohuwar tasu,wacce idan ta kafe akan ra'ayinta samun mai sakko da ita sai Allah. "Raudatu maza sanya mayafi ki je Hajiya na son ganinku ke da Maimunatu." Baba Lawal ya faɗi hakan lokacin da yake ɗage labulen ɗakin Umma yana mai sauke ganinsa akan su Raudah dake zaune a falon suna kallo,da yake yinin ranar anbar wuta sosai har daren.Rahdah sukai masa sannu da shigowa tana ɗaurawa da faɗin, "To Baba." Daga haka ta miƙe ta nufi ɗakinsu domin ɗakko hijab ta je amsa kiran mutuniyar tata Hajjah Kakah.Ya saki labulen tare da juyawa ya nufi ɗakin Anty Safiya,da sallama ya shiga cikin ɗakin ya sameta tare da Maimunatu suna zaune a falonta su ma kallon suke yi.Ya dubi Maimunatu ya ce, "Ke! Tashi ki je Hajiya na son magana da ke." Maimunatu ta ɗan zumɓuri baki ta ce, "To Baba zan je." Ya sake haɗe fuska ya ce, "Tashi yanzu ki fice." Anty Safiya ta ɗago kai ta dubeshi ta ce, "Yo wannan kira na mene ne haka da za a azalzaleta?" Bai tanka maganarta ba ya cigaba da tsayuwa har Maimunatu ta miƙe ta nufi ƙofa domin fita,ya bi kayan jikinta da kallo yana faɗin, "Wuce ki ɗakko mayafi mara kunyar banza da wofi kawai." Anty Safiya ta ja ƙwafa ta ce, "Rashin kunya ai gado tayi ta wajen uwa da uba." Baba Lawal bai tanka ba stilll,ya cigaba da tsayuwa har Maimunatu ta ɗakko mayafi ta fice sannan ya shi ma ya rufa mata baya.Kusan a tare da Raudah suka isa ɓangaren Hajjah Kakan,sun samu su Yayah Sadeeq da Yaya Usman a ɗakin suna mata hira.Ganin shigowarsu ya sanya Yaya Usman tashi yana faɗin, "Hajjah Kakah sai da safe." Ta amshi idanunta akan Maimunatu da ta ja tayi tsaye bata da alamun samun wajen zama kamar yadda Raudah tayi,cikin tsare gida ta ce, "Miye kuma haka zaki yiwa mutane tsaye kamar wata soja?" Yaya Deeku ya ɗaga kai ya watsawa Maimunatu wani mummunan kallo,babu shiri ta lalubi kujera ta zauna tana faman zunɓure baki.Raudah ta fara gaida shi ya amsa da kulawa yana aika mata wani irin sassanyar kallon da narkar da zuciyarta,Koda Maimunatu ta gaida shi a tsume ya amsa yana sake kallon yadda Yarinyar duk ta ɓata kanta da bilicin.Ganin alamun magana Hajjah Kakah ke son yi dasu sai ya miƙe ya fice daga ɗakin bayan ya yi sallama da Hajjah Kakah,Raudah ta raka shi da ido tana jin ƙaunarsa a cikin zuciyarta. "Maimunatu ina so ki sani sam ba zan ɗauki kalar rayuwar sakarcin da ki ka ɓullo dashi ba,don haka tun wuri ki fiddo miji cikin samarin da kuke gantalewar tare,idan ba haka ba sai dai ku tattara ke da uwarki da ke ɗaure miki gindi ku bar gidan nan ehe!" Ta dakata tana kallon yadda Maimunatu ke jifanta da wani irin kallo kafin ta buɗe baki tana faɗin, "Hajjah Kakah kema munafurcin da ake ƙulla mini har ya iso gareki kenan? To ni babu ajandar aure yanzu a shafina sai na kammala secondary,wani irin maganar aure kuma ana zaune ƙalau mutum na watayawansa son ransa? Gaskiya ki dai sake shawara su dai da suke son aure kuma sune manya sai a fara kawar dasu,idan iskanci ne ai kowa da kalar nasa bani kaɗai bace ƴar iskar ehe!" Ta ƙare maganar tana kaɗa ƙafafu.Hajjah Kakah ta ja salati kai ka ce mutuwa aka rafka,kafin ta riƙe baki tana faɗin, "Eh! Lallai ba shakka kin san daɗin maza Maimunatu,babu ko kokonto kin haɗa gado da namiji dole ki kalli tsabar idanuna kina gaya mini wannan kalaman babu kunya bare tsoron Ubangiji,tabbas barewa bata gudu ɗanta ya yi rarrafe,Safiya da Lawal sun cuceni da suka yi tarayyan da har suka san juna sukai aure suka haifo mini tambaɗaɗɗiyar jika kamarki." Hajjah Kakah ta ƙare maganar cikin rawar murya sosai.Maimunatu kuwa miƙewa tayi a fusace tana jan dogon tsaki ta fice daga ɗakin,Raudah da tayi mutuwar zaune sai ta rakata da idanunta da ke cike da zallar mamaki da firgicin kalaman da ke fitowa daga bakin Maimunatun.Har Hajjah Kakah ta share hawayenta ta juyo kanta ta kasa ɗaga ido ta dubeta,cikin wani irin sauti Hajja Kakah ta ce, "Kin ga sharrin aurowa kai ragowar bariki ko Raudatu? Kin ga kaɗan daga illar cin bashin zina ko? Ita zina na so gareta,tayi ta bibiyan jini ana ganin masifu kala-kala,yanzu kin ji dai babu kunya bare tsoro ta amsa sunanta na ƴar iska,yo uwarta tayi iskanci da ubanta tun kafin ya auro uwar su haifota,ke kinga laifi ne don Allah ya basu magajiyar da ta gajesu a iskancin?" Raudah ta rintse idanunta tana jin matuƙar zafin kalaman Hajjah Kakah,cikin matuƙar rawar murya ta ce, "Please! Hajjah ki daina furta irin waɗannan kalaman,ki bar abinda ya wuce a matsayin ya wuce,tunda wannan laifin da kuskuren da aka aikata ba ke aka aikata mawa ba,tsakaninsu da Mahaliccinsu ne Hajjah Kakah,kuma shi mai yawan gafara da yafiya ne matuƙar bawa ya tuba izuwa garesa da kyakykyawar niyya,addu'a ita kaɗaice za ki taya Maimunatu dashi,bawai ki dinga furta mata irin waɗannan kalaman ba." Hajjah Kakah ta ja hanci tare da sake share hawayenta ta dubi Raudah ta ce, "Hakane Raudatu kin fini gaskiya,amma ki sani ina matuƙar baƙin ciki da ganin wannan lalacewar a cikin ahalina,ban taɓa ƙaunar Safiya ba domin macen kirki ka ke fata ta dauwama tare da jininka ba watsatstsiya ba,yanzu dai mu koma batun soyayyarki da ɗan uwanki Sadiku,shin da gaske har cikin zuciyarki ya yi miki ko kina da wani da ki ke so bayan shi?" Raudah ta girgiza kai tana faɗin, "Hajjah Kakah me kuma ya kawo wannan titsiyen?" Hajjah Kakah ta aika mata harara ta ce, "Ki bani amsa kawai sarkin baki." Raudah tayi ƙasa da kai ta ce, "Hajjah Kakah ni bani da kowa bayan shi." Hajjah Kakah farin ciki ya cika zuciyarta,cike da ɗoki ta ce, "To ƙarshen wata za a tsaida ranar aurenku Raudatu,don haka ki toshe kunnuwarki ki kuma rufe idanunki akan duk abinda zaki ji ko ki gani daga Karimatu,kada ƙiyayya da adawar da take yi da wannan haɗin ya dameki domin kuwa bata isa ba, tayi kaɗan ta ja dani akan batun aurenku tunda har kuna son junanku,shiyasa nake so ayi komi cikin gaggawa." Raudah ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Hajjah Kakah zuciyarta na wani irin bugawa.Da rawar murya ta ce, "Ƙarshen wata fa Hajjah Kakah saurin me ake yi haka?" Hajjah Kakah ta haɗe fuska ta ce, "Ba huruminki bane,ke dai tunda kin gamsu dashi kina kuma ƙaunarsa to tashi ki bani waje." Raudah ta zumɓuri baki ta ce, "Ni dai gaskiya Hajjah abi komi a sannu gaggawa fa aikin shaiɗan ne." Hajjah Kakah ta ja tsaki ta ce, "Na ji dai,ki gaida Halimatu sai da safe,ki turo Sumayyah na ga alamun ba za ta zo tayani kwanan bane yau." Raudah ta fito daga sasan Hajjah Kakah tana jujjuya hukuncin Hajjah Kakah tana ji sam zuciyarta bata gamsu ba.......✍🏻 *To masu karatu duka anan na kawo ƙarshen free pages na labarin RAYUWA DA ƘADDARA,ba sai na ce muku komi ba game da irin ƙullin da ke cikin wannan tafiyar. Labarin duka yanzu ne za a fara wasan,don haka kada ki bari ayi wannan tafiyar babu ku,domin kuwa baku ji komi ba,kamar yadda yanzu ne zaren labarin zai fara ja.Ku dai kawai ku nuna wa labarin ƙauna ta hanyar yin rufdugu domin cika gidan ahalin Hajjah Kakah,domin jin ya rayuwar ahalinta dana surukukanta zai kasance? Wai shin ma mine ne a cikin RAYUWA DA ƘADDARAR Raudah? Amsar duka na tare da Aysha Ɗansabo lemu,tafiyar ta dabance kamar yadda salon labarin kawai ya sha bambam da sauran labaran da na saba kawo muku,don haka mu haɗu a paid group domin jin cikakken wannan labarin da tarin darussa na rayuwa da ke cikinsa.* *Ina godiya ga ɗinbin masoya masu ƙaunar wannan labarin,Allah ya hore muku kuɗin siya ya kuma rufa asirin mu baki ɗaya duniya da lahira.Akwai promo da zai bai wa kowa damar mallakar labarin akan kuɗi ƙalilan,Bye👋🏻* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels