An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng TATSUNIYAR SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA Daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibaga (wannan tatsuniya ce tsohuwa wadda aka samota daga al'ummar Bantu dake nan Afirka.) A wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Dukkan su yan mata ne, kuma sun isa aure. Rannan sai wannan mutum ya tsallaka ruwa izuwa wani gari domin ziyara. Da isar sa sai yake jin labarin sarkin Garin wanda hamshaki ne yana neman aure, kuma an gwada dukkan yan matan garin amma basuyi masa ba. Dawowar sa gida keda wuya sai ya sanar da iyalinsa. Babbar 'yarsa wadda sunan ta Mpunzikazi, tace zata je domin auren sarki. Mahaifinta yayi murna da haka, ya turawa yan uwa da abokansa na arziki don suzo a rakata izuwa garin ta yadda zata zamo matar sarki, amma sai mpunzikazi tace tafi son a barta taje ita kadai. Washe gari taci kwalliya ta kama hanya, tana cikin tafiya sai ta hadu da Bera. Bera ya matso gareta yace "kina so na nuna miki hanya?''. Sai kuwa mpunzikazi tayi tsaki, tace "gafara nan, waye kai da zaka nuna min hanya?" Daga nan bata kara bi takansa ba ta wuce. Shikuwa sai cewa yayi "indai a haka zaki to bazaki ci nasara ba". Tayi gaba kenan, sai ga kwado yazo gareta. Kwado yace "idan kinaso zan nuna miki hanya". Sai kuwa ta daka masa tsawa, tace "kai kauce, har ka isa kayi magana da matar sarki?" Sai kwado yace kije gaba, zakiga abinda zai faru" Taci gaba da tafiya kenan sai ga wani yaro yana kiwon dabbobi. Da ganinta sai ya matso kusa yana cewa "yayata ina zuwa haka?" Mpunzikazi taja tsaki tace " waye kai da zaka kira ni da yayarka? Kai kauce kabani wuri." Yaro ya kara cewa "ina jin yunwa, ko zaki taimakeni da abinda zanci?" Sai kuwa ta kara daka masa tsawa tace " ka kauce ka bani wuri fa nace!!!" Sai yaro yace " ai kuwa indai haka zakiyo, to ba zaki dawo ba" Mpunzikazi dai ta wuce gaba. Tayi gaba kenan, sai ga wata tsohuwa tana zaune bisa wani dandamalin dutse. Tsohuwa tace "sannu da zuwa 'yar nan ga shawara zam baki: idan kika je gaba zaki ga bishiyoyi suna miki dariya, kada ki sake kiyi musu dariya. Zaki ga kabakin madara da zuma, kada ki sake kisha, sannan zakiga wani mutum wuyansa a saman kansa, yana dauke da ruwan sha, ko yayi miki tayi kada kisha". Sai kuwa Mpunikazi tayi tsaki tace " wannan mummunar tsohuwa da rigima take, ko meye ruwanta dani oho?" Ai kuwa wucewar ta keda wuya, sai ga bishiyoyi na dariya, nan itama ta kyalkyale musu da dariya. Taga kuttun zuma da madara, ta zauna ta sharba, taga mutumin da wuyansa ke saman kansa ya bata ruwa ta karbe tasha. Bayan duk an gama wannan ne ta iso kofar garin. Zata shiga kenan sai ga wata budurwa zata debo ruwa, ashe yar uwar sarkin ce. Budurwar tace da mpunzikazi "yar uwata ina zakije ne haka?" Mpunzikazi tace " wacece ke da kike min wannan tambayar? To nice matar da sarkin ku zai aura" Sai budurwar tazo gare ta tana cewa "tsaya na nuna miki ta hanyar da zaki shiga garin" Amma ina, mpunzikazi bata kula taba, ta wuce kurum abinta. Da shigarta garin sai mutanen garin suka tambayeta abinda a kawota, ita kuma ta fada musu, sai akace mata sarki baya gari yanzu, amma ga hatsi ta girka masa abinci, idan ya dawo zaici. Haka kuwa akayi. Bayan ta gama abinci zuwa yamma, sai ga guguwa na kadawa, alamun sarki ya dawo kenan. Zuwa can aka ce tazo sarki zai ganta. Da shigarta inda sarkin yake sai ta tsorata, domin kuwa wani katon maciji ta gani mai kawuna biyar, a yaren su ana kiransa 'Makanda Mahlanu'. Ta ajiye masa abincin data girka yaci, sai kuwa yace abincin ba dadi don haka bata cancanci zama matar sa ba, nan take ya kanannadeta ya kashe ta. Labari sai yazowa yan uwanta cewa batayi nasara ba. Hakan yasa kanwarta shirin cewa itama zata jarraba. Sunan ta mpunzanyana. Ubanta yace zai tara mutane suyi mata rakiya, tace to baba babu matsala. Da ranar tafiya tazo sai suka fita suka kama hanya. Can sai ga bera a gaban su. Bera yace "yarinya ko kina so na nuna miki hanya?" Mpunzanyana tace "ai kuwa zanji dadi idan ka nuna min ta inda zamu bi". Daga nan sai ya nuna musu inda zasu bi, suka wuce. Sunyi gaba kenan sai ga wata tsohuwa. Tsohuwa tace "yarinya bari na baki shawara, idan kika yi gaba zakiga hanya ya kasu biyu, babba da karama, to karamar zaki bi" Mpunzanyana tace "Nagode babata, zanyi kamar yadda kika ce" Haka kuwa akayi kamar yadda tsohuwa ta fada, suka bi karamar hanya. Daga nan kuma sai ga kwado. Kwado yace " bari na baki shawara, idan kika je garin zakiga wata budurwa a bakin kofa, ki girmamata yar uwar sarki ce, za kuma ace kiyi ma sarkin abinci, ki tabbata kinyi abinci mai dadi, sannan idan kika ga sarkin kada ki tsorata" Mpunzayana tayi godiya ta wuce. Bayan sun isa kofar gari, sai ga budurwa yar uwar sarki. Ta tambaye su abinda ya kawo su, mpunzayana ta fada mata, sai kuwa budurwar ta nuna musu ta hanyar da ya kamata su shiga garin. Shigar su keda wuya aka gabatar musu da hatsi domin tayiwa sarki abinci kafin dawowar sa. Mpunzayana ta natsu tayi girki mai kayatarwa. Zuwa yamma sai taji guguwa na tasowa, alamun sarki ya dawo kenan. Ta dauki abinci ta nufi inda akace mata yake. Ta ganshi katon macici mai kawuna biyar, amma ta dake ba tare da taji tsoro ba, ta gabatar masa da abincin. Da macijin yaci abincin sai yaji dadin sa, yace hakika itace matar dazai aura. Kawai sai taga yayi birgima ya rikide izuwa santalelen saurayi. Akayi biki gagarumi, ya sanyata a gidan sarauta tare da duk yan uwanta. Ya zama yana matukar kaunar ta. Shikenan, kurunkus.. **Darasin Tatauniyar shine; Tarbiyya. Hakika babu mai iya cin nasara a rayuwa matukar yana kaskanta nutane, baya girmama su. Allah ya bamu dacewa amin. This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels