An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng FADAR BARCI Wani Sarki ne da Sarauniyarsa suke mulki a wani gari mai yawan mayu. Duk da cewa Sarkin nan da Sarauniyarsa babu abin da suka rasa na dukiya da jin dadin zaman duniya, amma Allah bai nufe su da haihuwa ba tsawon shekaru, har tsufa ya fara sallamo ma su. Ana nan wata rana, Sarauniyar nan ta fita bayan gari shan iska, ita kadai, har ta iso bakin wani rafi. sai kuwa ta ga wani dan karamin kifi ruwa ya turo shi bakin gaba, ya yi, ya yi, ya koma ciki ya kasa har yana shirin mutuwa. Sarauniya ta ji tausayinsa ta dauke shi ta mayar da shi cikin ruwa. Bayan kifi ya yi nitso cikin ruwa, ranshi ya dawo, sai ya dago kansa saman ruwa ya ce da Sarauniya, "Na san abin da ke damun ku, ke da mijinki, sakamakon taimakona da kika yi, za ki haifi 'ya mace wadda babu kamarta a kyau duk fadin duniyar nan, sai dai wani abin al'ajabi zai faru gare ta." Yana gama fadin haka sai ya shige cikin ruwa abinsa. Shekara ba ta kewayo ba sai da Sarki da Sarauniya suka haifi 'ya mace, wadda ba a taba ganin kyakkyawa kamarta ba. Da ranar suna ta kewayo, Sarki ya gayyato manyan Sarakuna na duniya domin taya shi murna. Ita kuma Sarauniya ta gayyato manyan mayun kasar su goma sha biyu. Duk baki kowa ya hallara, Sarakuna suka cika fada, mayu kuwa kowace ta zo tana sanye da jar hula da jajayen takalmi rike da fararen sandunansu na tsafi. Bayan an ci biki har an kusa watsewa, bakin Sarki suka bayar da kyaututtukan da suka kawo wa abokinsu. Su kuwa mayu sai suka fara ba wa jaririya kyaututtukan sihiri. Ta farko ta nuna ta da sandarta ta ce, "Za ki zama kyakkyawa." Ta biyu ta ce, "Za ki zama mai arziki." Ta uku ta ce, "Za ki zama mai ilimi." Ta hudu ta ce, "Za ki zama mai tausayi da taimako." Haka dai suka ci gaba da ba ta kyautuka har zuwa mayya ta goma sha daya. Har mayya ta sha biyu za ta mike ta bayar da tata kyautar, sai aka ji wuri ya hargitse da kururuwa da hayaniya da iska. Lokacin da wuri ya natsa, kamar daga sama sai aka ga wata mayyar ta bayyana a cikin taron, tana sanye da bakar hula da bakaken takalmi da bakar sanda. Ashe an manta ba a gayyato ta ba wurin biki, ita kuwa ta ji haushin wannan banbanci da aka nuna mata. Sai ta nuna jaririya da bakar sandarta ta ce, "Idan ki kai shekara goma sha biyar za ki soke hannunki da kwarashin saka, nan take za ki mutu!" Tana fadar haka sai ta yi wata irin dariyar keta, ta zama iska ta bace. Hankali Sarki da Sarauniya ya tashi a kan wannan fata na mayya. Ga shi abin da suke nema shekara da shekaru sun samu amma burinsu na barin zuri'a a duniya ba zai cika ba, 'yarsu za ta mutu tun kafin ta yi aure! Nan da nan sai mayya ta goma sha biyu, wadda ba ta bayar da kyautarta ba, ta taso ta ce da Sarki da Sarauniya, "Hakika wannan mayya da ta fita yanzu babbar matsafiya ce, babu mai iya tare sihirinta a nan cikinmu. Amma ni, zan yi iyakar kokarina in rage masa karfi." Sai ta nuna jaririya da sandarta ta ce, "Idan ki ka cika shekara goma sha biyar, tabbas za ki soke hannunki da kwarashi, amma ba za ki mutu ba, za ki kwanta barci wanda ba za ki farka ba sai bayan shekara dari." Bayan an gama biki an watse, Sarki ya sa aka sanar da dukan mutanen gari duk wanda ya san yana da kwarashi, kai koda allura ce, a fito da su. Aka tara kwarashi da alluran garin gaba daya aka kona su. Sarki ya sa doka mai tsanani akan shigo da kwarashi ko allura a cikin garinsa. Da 'yar Sarki ta fara tasawa, dukan kyautukan da mayun nan suka ba ta, suka fara bayyana tare da ita. Ga ta dai ta zama kyakkyawar da babu kamarta, ga hikima da basira, ga tausayi, dukan abin da aka koya mata sau daya, shi ke nan ta rike shi. A kwana a tashi har ta kai shekara goma sha biyar cif, a daidai lokacin ne kuma tafiya ta kama Sarki da Sarauniya zuwa wani gari. Aka bar 'Yar Sarki a gida, ita da masu kulawa da ita. Da ta gaji da zama sai ta tashi tana bi lungu-lungu na gidan domin ta mike kafafunta. Ta zo wani lungu, sai ta ga wani daki da marikin kofarsa ta zinariya. Ta kama marikin kofar ta tura, sai kofar ta bude. Ta kutsa kai cikin dakin, sai ta ga wata 'yar tsohuwa, tukuf da ita, zaune a kan kujera tana saka. Ta kura wa 'yar tsohuwa ido, ta ga yadda take ta surkulle da kwarashi, sai abin ya burgeta. Ta matsa kusa da 'yar tsohuwa ta gaisheta cikin ladabi, ta ce da ita tana so ta koyi yadda ake wannan abu. Ashe ba ta sani ba, 'yar tsohuwar nan ita ce mayyar da ta yi mata fatar mutuwa bayan shekara goma sha biyar. Tsohuwa na jin haka, sai ta mika wa 'Yar Sarki kwarashi da kayan saka. 'Yar Sarki ta karba, tsohuwa ta gwada mata yadda za ta yi. Ta fara sakawa ke nan, sai kuwa kwarashi ya soke mata hannu, nan take ta fadi kasa, sai barci. Ita kuwa mayya ta dauka mutuwa ta yi, ta fita abinta tana farin ciki, burinta ya cika. Barci na dauke 'Yar Sarki, sai komai da ya ke cikin gidan barci ya dauke shi. Dawaki a barga suka soma barci, karnuka da tattabaru da suke kan rufin fada duka barci ya dauke su. Wutar da take a dakin dafa abinci, ita ma ta daskare. Ga mai dafa abinci ta biyo kaza za ta kama ta yanka, ita da kazar duk barci ya yi awon gaba da su. Wani dogari ma ya daga bulala ke nan zai labtawa wani bawa, duka barci ya kwashe su. Har wani dogari can gefe ya daga kofin zai sha ruwa, shi ma barci ya dauke shi. Hatta kudaje da kwarin da suke cikin gidan nan duka barci ya dauke su. Sarki da Sarauniya na dawowa daga inda suka tafi, suna kutsa kai cikin fadar sai barci ya dauke su a kan dawakinsu, duk da dawakin da 'yan rakiyarsu. Labari ya watsu cikin gari, sai ya kasance babu mai matsawa kusa da fadar nan. Shekara bayan shekara, ciyayi da kayoyi da sarkakiya suka fito suka zagaye gidan. Duk shekara suna kara girma, har ya zamanto ba a iya ganin fadar, duk kayoyi da ciyayi sun rufeta. Labarin 'Yar Sarki mai barci ya watsu ko'ina cikin duniya. 'Ya 'yan Sarakunan duniya da sadaukai da dama suka ta yiwo tattaki suna zuwa garin domin su ga 'Yar Sarki mai barci da kuma irin kyawonta da suke jin labari. Amma duk wanda ya zo shiga gidan sai ya ga babu dama, domin kaya da sarkakiya sun rufe gidan, dole ya koma baya. Wasu kuma sukan yi karfin hali su kutsa kai ciki, amma sai sarkakiya ta cukuikuye su, su kasa yin gaba su kasa yin baya, har yunwa ta kashe su. Ana haka, wata rana wani kyakkyawan Dan Sarki ya shigo garin, ya sauka gidan wani dan tsoho. Ya ce yana so dan tsoho ya kai shi fada su gaisa da Sarki. Dan tsoho ya ce babu Sarki a wannan gari, shi da fadarsa duka an sihirce su suna can suna barci, har da wata 'yarsa wadda babu kamarta duk duniya a wurin kyau, an ce kuma ba za su farka ba sai bayan shekaru masu yawa, ni ma na ji wannan labari ne daga kakana. Ko da Dan Sarki ya ji haka, sai ya ce wa dattijo ya nuna masa inda fadar take, yana so ya ga wannan abin al'ajabi. Tsoho ya yi masa kwatance da fadar, kuma ya gargade shi a kan kada ya kuskura ya ce zai shiga ciki, domin mutane da yawa sun halaka. Dan Sarki na isa wurin da fadar take, maimakon ya ga ciyayi da sarkakiya da kayoyi, kamar yadda tsoho ya fada masa, sai ya tarar da fadar zagaye da furanni da ciyayi masu laushi. Ashe ranar ce 'Yar Sarki take cika shekara dari daidai tana barci. Dan Sarki ya kutsa kai cikin fadar, ya ga dukan mutane da dabbobin fadar barci suke yi. Ya yi ta bi lungu-lungu, daki-daki, yana neman inda 'Yar Sarki take, har Allah ya sa ya kai ga dakin. Ya ganta kwance a kasa tana ta barci. Nan take ya kidime saboda da tsananin kyanta da ya gani, sai ya ga duk kyanta da dan tsoho ya yi ta ruruta masa, bai fadi kashi ashirin cikin dari ba na kyanta. Dan Sarki ya durkusa ya kura wa yarinya ido, sannan ya sunkuya ya sumbace ta a kumatu. Yana sumbatar ta sai ta bude idonta, ta yi murmushi, nan take ta farka daga barcin shekara dari. 'Yar Sarki na farkawa, sai dukan abin da ke cikin gidan ya farka daga barci. Dawaki suka ci gaba da kukansu, tattabaru suka ci gaba da fiffikarsu, mai dafa abinci ta ci gaba da bin kaza za ta kama, bawa ya gudu don kada a dake shi da bulala, dogari ya ci gaba da shan ruwansa. Sarki da Sarauniya da 'yan rakiyarsu suka sauka daga kan dawakinsu. Rayuwa dai ta dawo a fadar kamar yadda take a farko. Aka yi ta mamakin wannan al'amari da ya faru. Mutanen gari suka ci gaba da yi wa Sarkinsu biyayya, da ma can ba su nada wani sabon Sarki ba, saboda labarin adalci da taimakonsa da suka samu daga kakanninsu. Sarki ya aurar da 'Yarsa ga Dan Sarki, kuma ya yi murabus ya nada shi a matsayin sabon Sarki. Suka yi zamansu cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai yanke jin dadi ta zo yanke. whatsapp number 08071051138 ===| KARSHE |=== — This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels